Recent Updates

Nakasa Ba Nakasa Bace Hausa Novel


 



        *NAKASA BA KASAWA BACE*


                             *PAGE 1*


                                NA

             *AYSHA ALIYU GARKUWA*


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

 

                        Book One 


~26/2 2020... 8:06 PM~



*28 February  2020. 9:10 Am*



*BISMILLAHI ina farawa da sunan Allah mai yawan rahma da jink'ai.  Alhamdulillahi na godewa Allah mahaliccina daya bani rai da lfy da nitsuwa, da konciyar hankali ya kuma ƙaramin ya buɗa min tunani na ya haskamin nazarina har na samu daman fara wannan sabon littafi nawa mai suna NAKASA BA KASAWA BACE ya Allah ina riƙonka da ka tsare min Al'ƙalami na daga rubuta sharri da abinda zai zamewa bayinka guba ko fitina, ya rabbil izzati ka tsarkake min tunani na ka kame min hannu na daga rubuta wani abinda zai zame min da-na-sa-ni duk ƙanƙantarshi, ya Allah ka bani rai da lfyar gama littafin nan lfy-lfy,  dani da masu karatun baki ɗaya*



_Wannan shafin forkon nakine ƙanwata kuma mai babban suna Fatima Sardauna, ina tayaki farin cikin gama  littafinki SOORAJ  lafiya, Allah ƙaro miki basira da hazaƙa, Allah ya bada ladan faɗakarwa_



Nakasarsa bata zama kasawa a gareshi, domin hausawa kance Babu nakasasshe sai kasasshe!

ya kasamce mai zarrar da ko lafiyayye marar nakasa bashi da irinta, Rayuwarshi madubine ga dukkan nakasassu, kana abar birgawace ga dukkan lafiyayyu kana abin so da sha'awar ko wanne bawa mai imani a zuciyarshi yadda sunanshi yake haka zahirinshi da bad'irinshi yake *SAIFUDDEEN* Muhammad Ahmadu  managarci ne salihi mai yawan fasaha da tawakkali kekyawane irin ken da ke tsantsar haiba.



Ɓiggiren tushe da asalinsu Saifuddeen.


Asalin su FULANIN DUKKU NE NA JIHAR GOMBE.

*DUKKU* wani yankine daga yankunan Gombe wanda ya kasance yankin fulanine masu tsananin kyau uwa uba fulanine masu fafutukar neman ilimi na bankƙare biyu duka wato ilimin Arabic da kuma Boko.

 Al'ummar Dukku sunyi fice da zarra tako wanna sashin shiyasa, suke ko ina cikin mutane masu daraja masu kima da cikar kamala.


*DUKKU diyam sad'i na kosam*


Malam Ahmadu shine kaka gasu Saifuddeen,

 Malamu Ahmadu asalin bafullatanin Dukku ne gaba da baya, 

nannen tushensa iyaye da kakanni, 

babban Malami da babu kamarshi a fad'in Dukku a waccan lokacin.

 Mafi akasari yaran garin a gunshi suke karatu, dan yanada tsankgaya mai girma , sai dai shi baya tara al'majirai, kowa yazo yayi  karatu kana in an tashi kowa ya koma gida, 

shiyasa yaran anguwannin nesama suke zuwa karatu, kamar yaran Sirinkiyo, Katafila,  Fada, da nan Dugge, kai wasu daga shabewa ma suna zuwa makarantar, wanna yasa ya shahara a cikin Dukku domin masarautar Dukku da kanta tanaji dashi, domin shine limamin masallacin fada. 


Allah ya azirta shi da kadararorin filayen cikin garin Dukku da tarin gonaki wanda yawan cinsu ya gajesu ne a wurin mahaifinshi wanda sune suka sari dajuka da tsaunikan  Dukku da kewaye kasan cewar wancan lokacin ba'a saida gonaki saida ka shiga daji ka sari fili ka gyarashi shike nan ya zama naka wahalakar ya mallaka maka shi. 


Malam Ahmadu yanada matarsa d'aya  mai suna Bintu Allah ya azurtasu  da yara uku.

Babban d'ansu sunanshi Muhammad Bella shine mahaifinsu Saifuddeen,  sai mai binshi Aliyu sai autarsu Aisha suna kiranta Dada.


Sun taso cikin had'in kai da tausayin juna, babu raini ko kad'an sai girmamawa da tausayawa. 

 Yayiwa  yaranshi maza aure.

Bello mahaifinsu Saifuddeen kenan mutun ne mai mutunci da kamala yanada nitsuwa shiyasa aka had'ashi aure da d'iyar goggonshi mai suna Fatima amman ana kiranta da Bisije, yaranta ku su Saifuddeen suna kiranta  Ummi.

Ummi kenan, wacce mahaifiyarta k'anwar Malam Ahmadu ne, Ummi marainiyace dan rana d'aya ta rasa iyayenta saka makon gobara da ya cisu dere d'aya, ita kuma lokacin an kaita yaye gidan kakunsu, shiyasa ta tsira, ba nisa tsakaninmu kakanin nasu suka rasu, shiyasa rik'onta ya dawo gidan Malam Ahmadun kawunta kenan.


Bello ya rayu da matsalar makarai tattare dashi, 

wanda yakan tashi time to time yana matuk'ar wahal dashi shiyasa, 

iyayenshi suka zab'i a had'ashi da Bisije Ummin kenan anaga tunda yar uwarshi ce zatayi hak'urin zama dashi, 

bayan an gama yin komai  na buk'atun hidimar aure, 

sannan akayi auren Bisije da Bello, 

anyi biki lfy an watse lfy. 


Ranar da aka watse abokan Bello na shirin rekoshi gidanshi inda yayi gina cikin asalin family house in nasu.

kawai sai suka sameshi ya toni rami mai zurfi kana ya had'a k'irarai ya shirga itatuwa ya hura wuta, 

wai zai fad'a ciki, 

nan abokanshi Ashiru da Hamisu sukayi kanshi da gudu suka kamashi, sai fizgewa yakeyi wai su barshi zai fad'a cikin wutar yana me ce musu. 

Wai a k'asan wutan al'jannace su barshi ya fad'a ciki.

Wannan abu ya tada hankali yan uwa da abokan arzi a daren ranar dole Hamisu da Ashiru,

a gidanshi suka kwana don in an barshin zai kashe kansa, sabida makaranshi ne suka motso, k'aninshi Aliyu da Dada kuwa sai rarrashin Amarya suke,

wacce taketa kuka. 

To mafarin bak'in cikin Ummi kenan tun randa aka watse bikinta ta fara shiga toskun rayuwa sabida, 

daga ranar duk bayan wata biyar sai cutar Bello ta tashi wani lokacinma yakan tashi sau uku a shekara, sai dai Alhamdulillahi abun baya sashi duka ko fad'a sai dai yakan tashi tsakiyar dare yayita  yawo yana zagaye cikin garin Dukku, 

kana duk inda ya samu masallaci sai ya tsaya yayi sallah raka'a biyu. 

Sannan yana tafiya yana karatun qura'an da k'arfi.


 Kafin gari ya waye sai muryarshi ta disashe, kana sawunshi su kumbura.

Mahaifinshi Malam Ahmadu dama yan uwanshi kab suna nema mishi mgn amman Allah baisa anyi dace ba. 


Haka shekaru sukayi taja Ummi tana ta hak'uri da d'an uwanta mijinta, koda kawunta yayi yunk'urin raba auren sai tayi ta kuka tace ita kam a barta dashi, acewarta in ita ma 'yar uwarshi ta gujeshi wa zai zauna dashi, dole Malam Ahmadu ya barsu yana mai ci gaba da yiwa d'anshin addu'ar samun lfy.

Har tsawon shekaru da dama, 

inda Allah ya azurtasu da yara shida uku maza uku mata. 

Nuruddeen shine babba sai Rahma, kana Saifuddeen sannan Raihana sai Raliyya sannan Auta Hayatuddeen sakalin Ummi da Hamma Saifuddeen. 

k'anin Bello Kuma Aliyu har yau matarsa bata tab'a koda b'ariba.

su Nuruddeen na kiranshi Bappa Ali, kana Dada ma tayi aure suna kiranta Goggo Dada.

Ita kuma tunda tayi haihuwar fari bata kumaba, Ahmad shine sunan d'an nata kuma sa'an Saifuddeen ne.


Ana cikin haka ne kuma Allah yayiwa Malam Ahmadu rasuwa. 

mahaifinsu  Abba kenan daga ranar kula da d'aliban ya dawo hannun bappa Ali, da kuma Abban in yana cikin haiyacinshi. 

kafin bintu ta fita takaba ne itama Allah ya mata rasuwa sakamakon cutar murd'a na dare d'aya.

Daga nan Abba da bappa Ali da goggo Dada suka k'ara ruggume juna bisa amana da gsky da tausayawa d'an uwan nasu.


Yara kuwa sun fara girma ciwon mahaifinsu na ci musu tuwo a kwarya musamman Nuruddeen da Raihana sai Saifuddeen wanda a lokacin yakeda shekara goma sha uku kana ya gama primary school inshi, har  yaci gaba da secondary school inda yake JSS 1

shi kuwa Nurruddeen tuni yayi nisa yana Ss 3 Raihana Ss 2 da yake tsakaninsu da Saifuddeen akwai 'yar tazara,

a gefen Arabic kuwa tun sunada shekara goma sha bbbiyu sukayin sauk'an alƙur'an mai girma.


So tuni Saifuddeen ya sauk'e Qur'an tun shekarar data gabata lokacin kanninsu na raye dan yanada 12 years yayi sauk'a kamar sauran yayunshi  tuni  ya meda hankalin kan hadda da sauran littafai da ake musu a isilamiyarsu. 


Saifuddeen yana ta murnar zai tafi JSS two wata rana kwatsam ya tashi da wani irin azabebben zazzabi mai tsananin zafi, 

kwana yayi yana firgita, 

da safe kuwa yana tashi sai mura ba tari amman  yanzu yanzu hancinshi na zubda ruwa kana hancin yayi jazazir hakama idanunshi, 

ganin haka Ummi ta kama hannunshi taje ta nunawa wata makociyarsu tsohuwa iya shatu kakar Salisu abokin Saifuddeen, 

tana nuna mata jikin Saifuddeen d'in.

 Tana gani tace k'end'ace bak'on daurane zata fito mishi ga kuma azabebben zazzab'in sank'arau daya rufeshi,

haka yasa ta nemi tsink'aro da gero ta barzasu ta jik'ashi da ruwa sannan ta kurba sai ta fesa mishi a jikinshi, 

cikin ikon Allah kafin dare duk Sun feso sun fito birjink a jikinshi har cikin tafin k'afafunshi zazzabin sank'arau kuma tamkar zai hallakashi.

Koda dare yayi Ummi ta d'aukeshi suka koma side inta, 

abu kamar mafarki koda gari ya waye sai aka samu jikin Saifuddeen yayi sumut duk bak'on dauran nan ya b'ace ya koma cikin jikinshi ya k'ume yaro sai karkarwa yakeyi dan zafin zazzabi ga kuma sank'arau da ya hanashi sukuni wanda har cikin kunnenshi yakeji yana bada sautin dummmm, 

ba irin mgnanin da ba'a bashi amman sunk'i su kuma fitowa a lokacin kuma ba'a wani damu da batun asibitiba ko riga kafinshi ba'a fiye yiba a garin. 

haka dai Saifuddeen yayi ta shan wahalar sheretuwannan da zazzafan zazzab'in sank'arau  daga k'arshe yayi sanadin kuram tashi.


Wannan al'amari ba k'aramin girgiza family ensu yayiba don Saifuddeen yarone mai shiga rai, gashi da nitsuwa da al'kunya 

iyaye da da 'yam suna matuk'ar sonshi ran da aka gane Saifuddeen ya zama kurma a ranar anga tashin hankalin Bello Abba kenan hakama Nuruddeen daya dawo makaranta aka gaya mishi, kuka yayi tayi dan duk k'annenshi yafi k'aunar Saifuddeen Hayatuddeen kuwa lokacin shekaranshi 4 so baisan meke faruwa ba

yakan dai yi kuka in yaga suna kuka.

A Daren ranar jikin Abba ya tashi a wannan ranar ne karo na forko da ya rink'a ihu tamkar yaro k'arami.

K'arfe biyu dai-dai na dere  ya kama hannun Saifuddeen dake bacci ya mik'ar dashi, kana ya jashi suka fito haka ya rink'a janshi koro-koro duk inda suka samu masallaci sai ya sashi suyi Al'wala suyi nafila raka biyu kana suci gaba da tafiya. 


Saida akayi sallan asuba sannan suka dawo gida, nanma dan yaga Saifuddeen  d'in yanata kuka. 

Suna dawowa Ummi ta jawo d'anta ta ruggumeshi cikin kuka take tambayarshi ina sukaje, 

baki ya bud'e da nufin ya kuma gwada yin mgna amman ina ya kasa, hakan ya sashi kife kanshi jikin gini yana wani irin gurnanin azabebben kukan da duk mai imani sai ya tausaya mishi babu mai sanin zafi da kun'an da yakeji a ranshi sai wanda ya tab'a shiga irin wannan halin ace an haifeka lfy ranatsaka nakasa ta sameka, so yake ya bud'i baki ya yiwa Umminshi bayanin yadda yakeji amman ina Allah bai bashi damar hakanba ganin ya kuma kife kanshi jikin ginin ya sake zazzafan shesshek'an kukane yasa Yayanshi mik'ewa ya nufi inda yake.


Da Sauri Nuruddeen ya kamoshi,

 hannu yasa ya tallabe kanshi cikin tsananin kuka da tausayawa k'anin nashi murya na rawa yace.

"Saifuddeen...!!! 









                                  BY

       



              *NAKASA BA KASAWA BACE*



                        *PAGE 2*



                                  NA

               *AYSHA ALIYU GARKUWA*


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇



 _Ga masu buƙatar biyan kuɗin karanta wannan littafi na Nakasa ba kasawa bace.ƙowa a buɗe take, turo katin mtn na 300 kacal ta wannan layin 09097853276. Ko kuma ka/kiyi transfer ta bank account na 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ka/kiyi screenshot shaidar biyanki ki turo min, sabida kids samu damar karantawa koda na gama free page_





 "Saifuddeen  magana kake son kayi ne?."

 cikin tsananin kukan ya rink'a gyad'awa Nuruddeen  kai.

 Duk da k'arfin hali irin na Ummi  tuni kuka takeyi dan tausayin d'an nata wanda yaci sunan babanta.

shi kuwa Nuruddeen cikin mamaki ya kalli k'anin nashi cikin kad'uwa yace.

"Kana ji nane idan nayi Mgna kana gane me nake cewa ne?."

 kanshi ya jujjuya kana ya zame hannunwan Nuruddeen daga rik'on da ya mishi sannan ya tsuguna a gaban Nuruddeen d'in tafin hannunshi yasa ya lailaiye yashin tsakiyar gidan nasu kana yasa yatsarshi ma nuniya ya fara rubutu da harshen fullanci yace.

"Ya Nuruddeen bana jin kuma naji na kasa yin mgna, cikin mak'ok'orona kamar an cusheshi kunnuwana sunyi dim bana jin komai, 

Amman da ina ganin bakinku ina gane abunda kuke fad'a."

sai ya kuma d'ago kanshi ya kalli Nuruddeen daya rusuna yana karantar rubutun yana kuka tamkar an musu mutuwa, 

hannu yasa ya share hawayen fuskar Nuruddeen d'in kana yaci gaba da rubutu da harshen hausa yace.

"Ya Nuruddeen ku nema min mgni mana, insamu irink'a Magna kamar kowa, ku kaini a bud'e min kunnena mana in rink'a jin muryar Ummi na da naku ku rink'a hira dani."

Ruggumoshi Nuruddeen yayi tare da sakin kuka murya na rawa yace.

"In sha Allah zan nema maka mgni Saifuddeen zan tattare dukkan buk'atun rayuwata zan jinginesu zan gina taka rayuwar, don gobenka tayi kyau."

Sai ya kuma tsaidashi tare da matsawa baya suna fuskatar juna yace.

"Saifuddeen kana gane abinda nike fad'i maka?."

 kai ya gyad'a mishi, da sauri alamun eh yana ganewa, ganin haka Nuruddeen yayi wani murmushi da yafi kuka ciwo a zuciya tare da cewa.

"Saifuddeen kayi murmushi kamar yadda nayi."

 ba musu yayi murmushin da har saida dimples enshi duka uku suka lotsa biyu na kumatun gefe dama da gefe hagu d'aya kuma na tsakiyar d'an gemunshi, 

murmushin ya kuma fad'ad'awa ganin itama Ummi tana murmushi still su duka hawaye na kwaranya a idanunsu,

Abba kuwa tuni ya mik'e bisa taburmar dake tsakiyar gidan da yake konciyan zafine, kwanan woje akeyi,

kuma har yayi baccin da ya kwana bayiba.

Shi kuwa Nuruddeen hannunshi ya d'aura kan k'ahon zuciyarshi kana ya fara mgna yana murmushi still hawaye na zuba yake cewa.

"Saifuddeen *Babu nakasasshe sai rago*, kasa a ranka ita. Nakasa ba kasawa bace, 

in sha Allah ni d'an uwanka Nuruddeen zan baka dukkan kulawa zaka rayu kamar ko wanne mai ji da gani da mgna, kada ka kareya shi nakasa baiwace ta Allah wonda yakewa wanda yakeso, 

lokuta da dama bahaushe na karin mgnar da kan zama izina misali inda suke cewa, wani hanin ga Allah baiwane."

sai ya kuma sharte hawayenshi kana yaci gaba da cewa.

"Zan nema maka mgni iya raina da mutuwa, amman kasa a ranka mgni baya canza k'addarar mutun,

kasa aranka wani hanin ga Allah baiwace.

Kasa a ranka Allah yayi maka rahamar tsare maka harshenka daga sobon Allah ne kasa aranka Allah ya tsare maka kunnenka daga jin zantuka na haram ne da aikata sabon Allah, kamar yadda haka abin yake ga makaho Allah ya tsare mishi idanunshi daga ganin Haram, 

Saifuddeen zan yi iya iyiwana kan ciwonka dana mahaifinmu har sai dai in yafi k'arfina."

 tuni Rahma da Raihana suketa kuka, Hayatuddeen ma dake gefen Ummi kuka yakeyi ganin yayunshi na kukan.

Kuka sosai Ummi takeyi dan tausayin Nuruddeen yaro k'arami Allah ya jarab ceshi ya d'ora mishi nauyin jinyar uba da k'ani bugu da k'ari shike ciyar dasu, 

domin sam Abba baya iya noma makaranshi sai su murdeshi haka yasa shima Nuruddeen baima iya nomanba, 

kasan cewar su Abba sun gaji tarin filaye a wurin babansu wanda shima babansu a wurin babanshi ya gada,

to nauyin rayuwarsu ya ta'allaqa da su bada jinginan filayen ana noma ana basu yan wasu kud'ad'e da zasu iya ciyar dasu. 

To amman da yake larurar jinya ta shiga sai ya zama kud'in basu isarsu, 

wasuma in sun karb'i gonakin basa basu kud'in jinginar wasu kuma suyi ta bayarwa har kud'in yafi k'arfin yadda zasu iya maida musu su bare su amshi gonarsu dole sunaji suna gani gonakinsu suke fin k'arfinsu, 

uwa uba ga Bappa Ali k'anin Abba irin mutanennan masu saude-saide.

Shiyasa tun bayan rasuwan iyayensu  motsi kadan sai ya saida gona. 

Yaje yayi tabin masu magani wai zai nemawa Abba mgnin jikinshi wai ko Allah  zaisa ya rabu da makaranshi,

 kwana kad'an abu yayi sanyi in ya sake tashi sai yafi na baya.

bud'e ido Ummi tayi jin abinda Nuruddeen yake fad'i, rubutun gaban Saifuddeen ta zubawa ido inda yake cewa.

"Ya Nurudeen makaranta nafa ya zanyi inyi karatu? banaji bana iya Magna, gashi next week zamu fara exams, isilamiya ma an kusa ayi musabak'a Ya Nuruddeen ta ina zanyi karatu ta yaya zan bada hadda?."

wannan tambayar tashi itace tasa kukan Nuruddeen k'aruwa yana kuka yake cewa.

"Zakayi karatu Saifuddeen, in sha Allah zakayi karatu boko da Arabic, in Allah ya yarda nakasarka bazata zama tawaya ba." 

kai ya gyad'a alamun gamsuwa kana ya koma bayan Abbanshi ya konta time to time hawaye na zubo mishi yana sharewa, a haka yayi bacci kasan cewar basuyi bacci ba daren jiya yawo suka kwana sunayi. 


Allah sarki Nuruddeen daga wannan ranar, 

ya fara fafutukar nemawa Saifudddeen mgni amman ina, 

k'addara ta rigayi fata, domin wannan abune da muka sani a k'asar hausa, some times k'enda tana sanadin makanta, kuramta gurguntaka, koma tab'uwar hankali gaba d'aya wa Al'ummarmu musamman in lokacin zafi akayishi. Kamar dai yadda ta kasance akan Saifuddeen.


Haka dai rayuwa tai ta tafiya yau fari gobe summa, 

a cikin wannan yanayin aka aura da Rahma tunda ta gama Secondary school inta, 

inda aka aura mata Sadik dan abokin abbansu Hamisu.


Shi kuwa Saifuddeen, ya bar zuwa makaranta dan ko yaje malaman basu wani meda hankali kanshi,

 kuma gashi babu makarantar nakasassu a Dukkun,

sai dai yana zuwa islamiya,

kuma  Alhamdulillahi malam suna matuk'ar kula dashi, 

a wannan lokacin akwai wani babban malami su abokin Malam Ashiru ne wanda shida kanshi yake ware Saifuddeen ya koyar dashi, yakan bashi hadda ya kuma, iya in yazo sai ya zauna dashi ya bashi takardu ya rubuta mishi abinda ya koyar dashi kuma Alhamdulillahi da kai yake kawo komai yadda ya kamata, 

wasu lokutanma har shike karb'ar haddan na k'asa dashi kuma duk k'ank'antar batan da akayi Saifuddeen  zai gane har yayiwa yaran gyara ta hanyar rubuta musu komai.


kusan shekara biyu da faruwar abun kenan wanda tuni Saifuddeen yana da haddan izu 37 a kanshi yana kuma karanta littatafai na addini sosai kamar Hadisai, tauhit, Nahawa, kulasatul nurul yak'in, da kuma tajweed  dan yama fi maida hankali kan tajwweed a cewar shine zai taimakawa karatunshi ya gane kurenshi da kanshi ya gyarawa kanshi, kana sosai yake bibiyar littafan koyan larabci.

Zuwa wanna lokacin ya saba da kuramtarshi, Nuruddeen kuwa har yau yana nema mishi mgnin. 



Ranar wata Jummu'a da dare Nuruddeen shida Abba da Bappa Ali suna zaune suna hira kamar yadda suka saba

gyara zama Nuruddeen yayi kana ya sunkuyar da kanshi sannan ya kuma d'agowa ya kallesu, cikin sanyin murya yace.

"Bappa Ali, ya batun karatun Saifuddeen ne? kunyi shiru bakuce komai ba, kuma tun kwanaki naketa binku a saida gona d'aya, a saya min machine, tunda na iya na koya a mashidin abokina Adnan,

tunda akwai makarantar kurame a cikin Gombe, kullum da safe sai in tafi dashi in kaishi makaranta ni kuma na wuni yin acabana, 

in zan dawo da yamma in d'aukoshi mu dawo tare, kunga baiyi nesa damuba kuma zai samu ilimi, kana mun sauk'e hakkinshi daya rataya kanmu, kuma mun cire mishi nakasar zuciya, kana mun ink'anta rayuwarshi, sannan zai samu k'arin fasaha da basira ta yadda zai k'ara samun experience,

sannan mu rabashi da barace."

shiru yayi ganin duk sun zuba mishi ido, 

su kuwa yabawa sukeyi da shawararshi domin sun san gsky ya fad'i. 

hakan yasa Bappa Ali gyara zama tare da cewa. 

"In sha Allah hakan za'ayi Allah yayi maka al'barka Seyo da yake haka suke kiranshi *Seyoji ko Seyo duk d'aya ne* kakmar fillancine da take nufin FARIN CIKI a hausave.

murmushin jin dad'i Nuruddeen yayi kana ya kalli Abbansu da yake zubda hawayen tausayinsu yace.

"Abba kada kayi kuka, in sha Allah watarana muma zamuyi farin ciki, Allah zai sauqaqa mana zafafan k'addarorinmu ih zuwa dad'ad'aan k'adarori domin dukkan tsanani yana tare da sauk'i, 

ku dai kuyita mana addu'a."

cikin sanyin murya Abba yace. 

"Allah yasa haka Seyo na Allah ya al'barkaci rayuwarka ya baka damar rik'e k'annenka."

Amin Amin ya rabbil izzati. Suka amsa a tare.


Tofa daga wannan ranar akasa wata yar madaidaiciyar gonarsu a kasuwa cikin ikon Allah a wata d'aya akayi cinikinta aka basu kudin.


A ranar da aka basu kud'i a ranar Bappa Ali ya shiga cikin birnin gombe ya sayowa Nuruddeen mashin d'in bajat sabuwa dal,

 kana daga ranar suka fara cuku-cukun nemawa Saifuddeen gurbin karatu a makarantar kurame ta Gombe. Special education Gombe state,

cikin sa'a aka sama mishi takardar shaidar ya zama d'alibinsu zai ci gaba daga JSS two, kasancewar da sa hannun Malam Ashiru abokin Abbansu kuma Saifuddeen kanshi na ja sosai domin nakasarsama kamar k'ara zaburar dashi tayi. 


Daga wannan ranar kullu yaumin fisha'i.

 Nuruddeen zaiyi sammakon baro Dukku tare da Saifuddeen suna shiga gombe ya kaishi makaranta kana shi kuma ya shiga cikin gari yayi ta kabo-kabonshi tun baisan anguwaninba har yazo ya saba ya goge ya zama idon gari, 

sai sun karya suke tahowa kana shabiyu nayi zai kaiwa Saifuddeen abinci duk da ana basu abinci a makarantar kasan cewar sashinta  boarding school ne kana kuma akwai yan jeka ka dawo in har iyayenka zasu iya d'aukar dawainiyarka. 

A ranar forko Saifuddeen ya had'u da abokinshi Is'haq makaho wanda suka shak'u sosai har yan uwan is'haq sun san Saifuddeen da Yayanshi Nuruddeen, hakama Nuruddeen yasan yan uwan is'haq dan har gidansu yana zuwa, 

dan in an bada hutu Saufuddeen kan biyo Seyo gombe ya kawowa abokinshi ziyara su wuni suna hira da yake shi Is'haq iyayenshi a gombe suke cikin anguwar Fada, 

shi Is'haq makahone kuma shima k'enda ce sila makantan shi dan ya bawa Saifuddeen lbri suna hira ta hanyar is'haq yayi Magna shi kuma Saifuddeen ya rubuta mishi amsa a wayarshi da yake iyayen is'haq sunada yar wadata sun saya mishi waya.


Haka rayuwa tai ta tafiya mashin d'innan ba k'aramin rufa asirinsu Ummi yayiba, 

suna samun komai a wadace, shi kam Nuruddeen ya jingine batun nashi karatun dama dukkan buk'atun rayuwarshi burinshi ya gina rayuwar Saifuddeen. 


Tuni rayuwa ta mik'e, sai dai kullum jikin Abba na yawan tashi, 

Rahma ta haifin d'anta na fari mai suna Faruq, har ta kuma haifi na biyu mai suna Adam. 


Tuni Saifuddeen ya tafi SS 3 shida abokinshi Is'haq da wasu sauran yan ajinsu karatu sukeyi sosai babu kama hannun yaro kuma. Alhamdulillahi kwakwalensu na ja.



Tuni Raihana ma ta fara zama yar budurwa  hakama Raliyya Hayatuddeen ma tuni ya tafi primary 3.


Bappa Ali kuwa har yau Allah bai bashi haihuwa ba, 

Kuma shike jan ragamar makarantar da mahaifinsu ya bari. 

Goggo Dada kuwa tun haihuwanta na fari bata kumayin koda b'ariba tuni d'an nata Ahmad ya girma domin  sa'an Saifuddeen ne shi.

 Alhamdulillahi su Saifudddeen sun kammala makarantar especial education lfy, 

har anyi bikin yaye d'aliban 

kana yanzu sunata shirin zana jamb dan samun gurbi a jamir'ar G.S.U wanda shine burinsu. 


Ana cikin haka Allah ya yiwa mijin Rahma rasuwa, 

dole ta dawo gida da yan yaranta Faruq da Adam daga nan nauyin kula dasu ya dawo kan Nuruddeen, 

abu ya had'e mishi gashi yanzu jikin Abba ya tsananta tsawon shekara guda kenan da abun ya tashi bai kuma sakeshi ba koda na dare biyu ne, duk ya rame ya lalace sai tsawonshi daya k'ara fitowa kana farinshi ya k'ara baiyyana 

hancin nan nashi har kan baki, 

gashi yanzu baifi gonaki shida bane ya rage musu, sai filayen cikin gari, 

inda sunada fili a biyu a Sirinkiyo da katafila duk sunada fili anan, 

sai kuma nan gidansu na gado da yake Dugge nan kusa da Fadan Dukku d'in .


dole ciwon Abba yasa aka saida gonaki biyu ya rage musu hud'u, 

inda suka zuba kud'in wurin nema mishi mgnin.

 Sukaje bauchi wurin wani Mlmi irin masu Islamic kemis innan, 

nan duk kudaden suka k'are dan magungunansu da tsada, 

Alhamdulillahi jikin ya d'anyi sauk'i sosai.

Sai kuma wani mak'ok'o ya fito mishi nanfa, suka fara jinyar asibiti kuma, amman ina abu sai gaba-gaba yakeyi, 

ta kai matakin da ko tsawonshi baya iya mik'ewa.

Bappa Ali yace a kuma saida sauran gonakin amman Abba ya hana acewarshi kada su Kuma saida komai a kanshi dan yasan wannan ciwon ba barinshi zaiba kar yazo ya mutu bai barwa yaranshi komaiba, 

 sun so suk'i bin shawararshi amman sai yace bai yafe musuba in suka kuma saida wata kaddararshi dan jinyarshi, 

su bari in ya rasu suyi duk yadda sukaga dama da kaddarorin da suka rage dole suka hak'ura, badon sun soba, haka yasa Nuruddeen zagewa da yin acaba don samo kud'in da za'a nema mishi mgni, wani lokacin sai k'arfe goma na dare yake baro gombe ya nufi Dukku.

Saifuddeen kuwa shike kula da Abban tunda yana gida, 

bappa Ali ma yanzu bai fiye zamaba yana tafiye-tafiye dan yana bin kasuwannin k'auye yana aune-aunen kayan abinci. Still kuma dai yana kula da d'aliban sun,  dan da safe baya tafiya sai ya karantar dasu na safe, kana in ya dawo da deddere bayan sallan isha za a hura wuta a tsakiyar tsangayar daliban su zazzauna kan itatuwan dake zagaye da wutan ayi ta karatu, sai k'arfe tara da rabi ake tashi, 




Yau asabar da sanyin safiya Nuruddeen ya fara shirin tafiya gombe, 

sai ya kuma fasa ya dawo ya zauna tsakiyar k'annenshi Raihana nayiwa su Faruq wonka dan Faruq ya fara zuwa makaranta, Abba kuwa yana zaune jingine da pillow, 

kana Saifuddeen na gefenshi yana sa mishi sugar a cikin kunun koko da Ummi ta dama musu, kana Rahma kuma tana toya musu kosan da zasu had'a da kunun suyi karin kumallo dashi, 

Raliyya kuwa wonke-wonke takeyi.

gefen Ummin shi ya zauna tare da tonkoshe kai irin yadda Saifuddeen keyi sannan yace.

"Na fasa tafiya yanzu yau sai azahar zan tafi."

cikin disashewar murya Abba yace.

"Meyasa?."

ajiyan zuciya yaja tare mik'e k'afafunshi kana ya yayi murmushi tare da cewa.

"Yau dai abincin Ummina zan ci."

Rahma ce ta juyo ta kallesu tare da cewa. 

"Kuma dama d'an malele zamuyi yau Ya Seyo nasan kai kana son d'an malele, 

ba irin Saifu ba da yake cewa muma mmki muke bashi wai shi baiga abin ciba a dan malele."

Hayatuddeen ne ya tura baki tare da cewa. 

"Gskyan shi ai, dan malele fa abincin matane."

murmushi Ummin tayi tare cewa. 

"Kada ku damu kowa zaici abinda yakeso, nasan Autana da Hamma Saifunshi da Abbanku suna son d'anwake, ni kuwa da sauran muna son d'an malale shiyasa nace ayi duka biyu kowa yaci abinda yake so."

murmushi sukayi baki d'aya kana sukaci gaba da hira, 

sannan Rahma ta gama tuya ta kawo musu tsakiyarsu nan suka zauna sunaci suna hira, 

saidai Ummi da Saifuddeen sam basuci wani mai yawa ba, 

shi kuwa Nuruddeen sosai yaci kosan nan yana korawa da koko.

cikin kula Nuruddeen ya kalli Ummi tare da cewa.

"Lfy kuwa Ummi naga kinyi shiru da yawa, ko kokon baki shaba, gashi kin san Saifu bazai ciba muddin yaga kina cikin damuwa."

murmushi tayi sai kuma ga hawaye, 

da sauri Saifuddeen ya zuba mata idanu lokaci d'aya idanunshi sukayi jazir. 

shi kuwa Nuruddeen kasa had'iye abincin bakinshi yayi dan ji yayi ya mishi d'aci ranshi na suya, 

tuni shima hawaye suka ciko mishi ido, 

Rahma kuwa mik'ewa tayi ta shiga d'akinsu haka nan tausayin Umminsu da kanta da Saifuddeen yasata kuka tuno mijinta daya tafi ya barta, kana ga uba ba lfy. Kuka ne sosai ya rufeta tuno sam Umminsu tunda tayi aure take cikin k'uncin rayuwa. 


Shi kuwa Nuruddeen cikin k'arfin zuciya ya sharce hawayenshi, kana ya d'ago kanshi ya kalli Ummi da ta zubawa Abba ido tana kuka, 

cikin raunin murya yace.

"Ummi". kai ta juyo a hankali kana ta zuba mishi ido,

 shi kuwa murmushi yayi still hawaye na zuba, 

cikin k'arfin guiwa da yak'ini yace.

"Ummi ki kalleni, ki cewa k'annena su kalleni."

sai ya kuma share hawayenshi kana ya kalli Saifudden daya zuba mishi ido ko k'ibtawa bayayi sannan yaci gaba da cewa. 

"Ummi na kada kiyi kuka, ki meda idanunki da buk'atun rayuwarki dana k'annena dana yaran k'anwata a kaina, dai zan iya kula daku, Ummi na kada kiyi kuka, kin ganniko ni d'innan nine farin cikinku, kin manta wanne suna kuka bani inkiya SEYO fa kike cemin to kuyi imani da Allah ku yarda da kaddara mai kyau ko akasinta, ku kalleni ni zan jure d'awainiya daku iya rai da mutuwa."

sai ya kuma kamo hannun Ummi da Abban su cikin rawan murya yace.

"In sha Allahu Ummi na ni d'innan sai na kaiku makka da madina birnin ma'aiki, insha Allah ni d'innan zan share hawayenku, 

Ummi in dai fa ina raye to insha Allah bazakuyi kukaba."

sai ya kuma kalli Saifuddeen kana yace. 

"Gamu Allah ya baku zaratan yara kyawawa muminai salihan bayin Allah, 

ko ni na gaza zama gatanku in sha Allah Saifuddeen zai zama Garkuwar ku kuma zai saku farin ciki, zai kula daku ya ruggumi buk'atunku."

Raihana ce ta sharte hawayeta tare da cewa.

"Dan Allah ya Seyo kubar kukannan haka kallifa yadda kukasa Abba da Hamma Saifu kuka, please Ummi ki rink'a bamu k'arfin guiwa kada ki bari hawayenki suna zubowa."

jin haka yasa Ummi share hawayenta kana tasa hannu ta share na Saifuddeen da Seyo, shiko Saifuddeen ya share na Abbansu daya gaza cewa komai dan ya lura jikinsu ne ya fara basu zai mutu ya barsu da maraici. 


Daga nan sai kuma suka d'an sake, 

haka dai sukayi ta hira har Rahma ta gama musu abinci, kowa yaci abinda ransa keso. 


Bayan anyi sallan azaharne, Seyo ya biya wurin mai kayan miya ya sayi naman miya dasu tattasai. al'basa, atraruhu. sannan yakuwa da alaiyahu da ganyen al'basa. Kana ya nufo gida a tsakiyan gida ya samu Ummi da Aunty Nina matar Bappa Ali, 

nan yazo ya zauna yana dariya cikin yanayinshi na raha yace.

"Yau kam Ummi na k'uruciya takeji, kalli yadda tasha duma." 

dariya sukayi baki d'aya kana yaje ya d'auko wuk'a da tire da babban roba ya debo ruwa a ciki kana yasa gishiri sannan yazo ya zauna gefenta ya fara wonke ganyen.

 Bayan ya gama wonke ganyen ya tsanesu ya sakasu bisa tiren kana ya mik'e tsaye hannunshi dak'e jik'e har yana d'igar da ruwa, ne ya kallesu kana ya nunawa Ummi su sannan yayi mumurshi kana ya fara yarfasu yana watsar da ruwan yana barin jikin hannun nashi, still yana murmushi ta tare da tonk'oshe kanshi bisa kafad'unshi ya kalli Saifuddeen daya shigo yanzu hannunsa rik'e da carbi, 

k'ara yarfa hannun nashi yayi a karo na bakwai sannan ya kallesu dukansu kana cikin yanayinshi na mai matuk'ar fara'a yace.

"Na gama! Ummi na gama!! Na gama!!! Nawa aikin na kammale komai saura kuma Saifuddeen zai k'arisa, kada ku tab'a komai ku barshi da wannan aikin zaiyi komai yadda ya kamata fiyema da yadda ni zanyi ko yadda zakuyi."

Zurui Ummi tayi tare da zuba mishi idanu, 

Rahma kuwa murmushi tayi kana tace. 

"Kai Ya Seyoji gani ni mace ga Raihana ga Ummi ga Raliyya duk bamuyi aikinba sai Saifuddeen namiji."

matsowa yayi kusa da Saifuddeen Kana ya had'e hannayensu wuri d'aya ya rik'e hannun Saifu gam cikin nasa kana ya kalli Rahma sannan yace.

"Wannan aikin nashi ne daga yau, ai ba aikin mata bane na mazane, shi zai iya ke bazaki iyaba."

Ummi kuwa ajiyan zuciya ta sauk'e kana tace.

"Yau kam bazaka je Gombe bako?."

sakin hannun Saifuddeen yayi kana ya gyara tsayuwarshi sannan yace.

"Zanje Ummi yanzuma zan tafi."

shiru sukayi baki d'aya kana Saifuddeen ya tsuguna a gabanshi yayi rubutu kamar haka.

"Ya Seyoji ka bari mana tunda bakayi sammako ba ka bari kawai sai gobe."

dafa kafad'unshi yayi kana yace.

"Saifuddeen ai tafiyar yau dolece a kaina dolen dole sai naje.

Dan ina son samo maka kud'in hidimar karatunka.

kana ga Faruq ma an kusa neman school fees, 

ga Rahaina tace min auren k'awarta ya kusa zasuyi anko kaga dole in dage in isarmuku.

Gashi naga Leda carpet d'in Ummi na ya fara yagewa."

cikin kula Ummi tace to. 

"Allah ya kiyaye hanya ya kaika lfy ya dawo da kai lfy, Allah ya baka sa'a."

"Amin Amin ya rabbil izzati." ya amsa kana ya juya ya shiga d'aki inda Abbansu yake, ya dade a cika sannan ya fito,

yana isewa inda suke ya kama hannun Saifuddeen yajashi suka nufi gaban Ummi sannan yace.

"Kin ganshi Ummi  yaron kin nan ko yanada  wata baiwa ta musamman a jikinshi, kuma ki kula zaki iya ganowa, 

shiyasa ni bama zan fara yin aureba sai na fara yi mishi aure."

dariya sukayi baki d'aya kana yace. 

"To Ummi na tafi."

Aunty Nina ce matar Bappa Ali wanda tun d'azu batayi mgnaba sai yanzu tace. 

"Allah ya bada sa'a in kana dawowa ka siyo min a gwalima."

har ya juya zai fita sai ya kuma juyowa tare da zaro ido kana ya tab'e baki sannan yace.

"Kawai Aunty Nina kice mun kusa mu zama mu bakwai."

kai kawai ta kauda dan ta sanshi da iya zolaya, 

daga nan basu kuma cewa komai ba, 

yaja hannun Saifuddeen suka fita, 

sun dad'e suna tsaye a bakin masallacin dake k'ofar gidansu. 

bisa dukkan alamu mgna mai mahimmaci yakewa k'anin nashi, 

har ya tada mashin d'in sai ya kuma kashewa ya sauka da sauri kana yayi cikin gida.

Yana shiga gaban Ummi ya d'an rusuna kana yace.

"Na manta Ummi bance miki kada kiyi kukaba shiyasa na dawo, 

dan Allah Ummina kada kiyi kuka dukkan tsanani yana tare da sauk'i."

kai ta jinjina tare da cewa.

"To Nuruddeen insha Allah bazanyi kukaba."

mik'ewa yayi tare da cewa. 

"To na tafi, hankalina a kwance tunda nasan bazakiyi min kukaba."

yana fita ya kuma tasa Saifuddeen da Hayatudden a gaba yai ta musu nasiha, 

kana ya kuma hawa mashin d'in ya kunna, 

still ya kuma kashewa ya sake komawa cikin gida kawai sai ya tsaya yayi ta kallon cikin gidan nasu baki d'aya, kana ya kuma dawo da hankalin shi da dubanshi kan Ummi, ya kai 5 minutes yana kallonta tana kallonshi amman babu wanda yayi mgna cikinsu, 

hakama yayi da Raihana da Raliya, 

Rahma kuwa tana ganin yadda yaketa binsu da kallo sai kawai taji hawaye na kwaranyo mata, 

kuma ta kasa cewa komai, 

shima Nuruddeen hawayen ne yaji suna zubo mishi, sanin in Ummi taga hawayenshi hankalinta zai tashi, 

sai yayi maza ya fita.


Hannun Hayatuddeen ya kamo ya saka cikin na Saifuddeen kana yace.

"Ka rik'eshi fiye da yadda uwa zata rik'i d'anta, ka hanashi kukan maraici, ka hana Ummi kukan k'unci, ka zamewa su Rahma Garkuwa kada ka bari yaranta suyi maraici."

sai ya kuma kalli Hayatuddeen kana yace.

"Autanmu kaga Hamma Saifunka ko to ba Yaya bane kawai a wurinka ubane a wurinka, kayi mishi dukkan biyayyan da d'a zaiwa ubanshi ku had'a kanku, ku had'a hannu ku share hawayen Ummi da yan uwanmu matannan. Ni kam Addu'a kawai nakeso daga gareku."

Duk sun kasa motsi domin shi dai Saifuddeen kalaman Yayanshi ya sakar mishi kasala, shiko Hayatuddeen, ido kawai ya zubawa fuskokinsu ya kalli wannan kana ya juyo ya kalli wannan.

Shi kuwa Nuruddeen, tada mashin d'in nashi yayi sannan ya takata, 

ya k'ara masowa gab da Saifuddeen suka kalli juna kana yayi murmushin da yasa hawayen shi kwaranyowa a idanunshi ,cikin zubda hawaye murya na rawa yace.

"Saifuddeen babu nakasasshe sai rago, kuma nasan kai ba rago bane, 

Saifuddeen kasa a ranka Nakasa ba kasawa bace."

yana fad'in haka ya ja mashin d'inshi ya tafi, yana woiwoyosu, Hayatuddeen kuwa sai hannu yake d'aga mishi, shiko Saifudddeen addu'a ya rink'a mishi a ransa. 



A cikin Gombe kuwa, Nuruddeen yana shiga gari yana bisa babban titin tashan Dukku yana isowa dai-dai Tashan Dukku yazo dai-dai bakin tashar kenan shi yana shirin wucewa, kana wata mota ta fito cikin tashan  dai-dai lokacin da Nuruddeen yazo bakin wurin, wannan motar birkinta ya d'an kubcewa  matuk'inta.

Cikin rashin sa'ar takan birkin  tayi kan Nuruddeen.....!!!





  

                           By

             *GARKUWAR FULANI*

8/


               *NAKASA BA KASAWA BACE*



                        *PAGE 3*



                                  NA

               *AYSHA ALIYU GARKUWA*


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇



_Wannan page ɗin nakune gaba ɗayanshi ƴan Hukuncin Allah fans Especially Mom Asas, Zee Ya'u, Jannart Salis, ina muku fatan al'khairi._


~Gareku masu buƙatan biyan kuɗin littafin ,turo katin mtn na ɗari uku, ta wannan layin 09097853276 ko transfer ta nan 0005388578 jaiz bank Asha Aliyu Garkuwa~


 Cikin tsananin razana da tsoro jiki na rawa mai jan motar ya fara kiciniyar taka birki.

Amman ina abin ya gagara, tuni birkinta ya kubce mishi, ido ya zaro da sauri lokacin da yaga motar tashi ta nufi kan Nuruddeen gadan-gadan

ji kakeyi k'uuuuuiyyyyhh.

motarnan ta bugu machine d'in Nuruddeeen bugu mai tsanani wanda yasa, Nuruddeen yayi tsalle yayi sama kana ya fad'o kan bump d'in tsakiyar titin, 

"Innalillahi'wa'illaihi rajiun. Hasbunallahu wani'imal wakil."

Shine abinda tarin mutanen dake zageye da Nuruddeen suke fad'i,

yayinda wasu suka ma kasa mgna sai d'aura hannu sukayi a kai, kana wasu sai jujjuya kai sukeyi.

mai mota kuwa da ker ya samu ya fara sarrafa motar har ya samu ta tsaya, 

yana fitowa da gudu ya nufi inda dandazon mutanen suke,

kutsawa yayi tayi tsakiyar mutanen har ya samu ya isa, 

ido ya rumtse da k'arfi cikin tsananin fargaba ya sunkuyo kan Nuruddeen da yake konce lib bisa titi, ida nunshi a rufe kirib sai numfashin shi dake korar juna, 

da sauri ya tallaboshi tare dagowa ya kalli mutanen cikin tashin hankali yace. 

"Ku taimaka min mana in d'agashi in sashi a mota."

wani k'ak'k'arfan matashi ne, 

yayi maza ya sunkuyo ya ciccibi Nuruddeen kana cikin, d'aga murya yace. 

"Biyoni."

yana fad'in haka ya juya ya tsallaka titin zuwa d'aya hannun kana ya nufi cikin asibitin MUSABA dake fuskantar tashan Dukkun, 

cikin rawan jiki mutumin ya mik'e kana yabi bayanshi.

suna shiga Reception suka nufa, 

ganin sun shigo hajaram majaram yasa Nurse's yin kansu  da tambayar meke faruwa, 

cikin kad'uwa mutumin nan yace, 

"Accident ne ku taimaka doctor ya dubashi."

juyawa sukayi suka kalli juna, kana d'aya daga cikinsu tace. 

"Ko an gayawa doctor bazai dubashi ba sai an nemo police."

jin haka yasa mutumin nan juyawa da sauri ya fita, 

gudu-gudu sauri-sauri ya tsallaka titin kana ya nufi wurin motar tashi, yana shiga ya nufi Gombe division yana zuwa ya musu bayanin abinda ke faruwa, 

ba b'ata lokaci suka had'ashi da police d'aya, kana suka tafi tare, 

suna zuwa Doctor in ya amsheshi bisa sa hannun hukuma kana fara  bashi taimakon gaggawa, sannan daga bisani ya ce su tafi Medical Center. 

Ba b'ata lokaci suka amshi shawararshi suka tafi can, 

suna zuwa aka amsheshi.


shi kuwa police yasa d'aya police d'in yaje ya d'auki machine d'n nashi ya kaishi officensu.

kana sun samu wayarshi y'ar Nokia dake jikinshi tanan aka kira Bappa Ali aka sanar mishi meke faruwa.


Lokacin da aka gayawa Bappa Ali yana cikin garin kurugu da yake ranar larabace, 

to yaje cin kasuwa, 

ana gaya mishi bawan Allah ya bar duk abinda yakeyi ya nufi cikin Gombe kai tsaye Medical Center din ya nufa, inda yana zuwa fargabarshi ta k'aru domin tunda Nuruddeen ya fad'i bai sake bud'e idanunshi ba kuma uwa uba yana konce tamkar gawa komai sai an mishi ga roba a hanci da baki da k'asanshi wannan abu yayi matuk'ar firgitashi, duk da k'arfin zuciya irin na bappa Ali sai da yayi ta kuka, 

mutumin daya bugi Nuruddeeen ma sai kukan yake sabida kukan da Bappa Ali keyi ya matuk'ar karya mishi zuciya sai hak'uri yake bashi da neman yafiyarsu. 

Cikin raunin murya yake cewa. 

"Ku gafar ceni tsautsayine, nayi iya k'ok'arina inga na tsare motata bataje ta bugeshi ba amman ina Allah ya k'addara faruwar hatsarin bani da tsumi ko wayo bare k'arfin hanawa."

sai ya kuma sharte hawayenshi kana yaci gaba da cewa. 

"Tunda nake ban tab'a shiga cikin tashan Dukku ba, sai yau, ashe ashe ban saniba masifa ke kirana."

shi kuwa Bappa Ali ya gaza cewa komai domin da ganin mutumin ya girmeshi kuma bisa dukkan alamu mutum ne mai daraja da ka ganshi kasan mai kamalane, 

shi kuwa mutum shirun Bappa Ali sai ya sa mishi rauni yana ganin shike nan ya  cucesu,

yana bashi hak'uri yana tuno dalilin zuwanshi tashan, 

dan matarshi da ta kasance yar Ngalda to kullum shi ke kaita to yau kuma har ya shirya zai kaita sai kuma motocin kayanshi suka iso, so shiyasa yace bari ya kaita tasha ta shiga motar kasuwa, to shinefa ya kaita kenan yana fitowa wannan hatsarin ya auku.



Bappa Ali kuwa ganin yanata bashi hak'uri ya sashi yin k'arfin halin cewa. 

"Ba komai Allah ya bashi lfy, ai shi tsautsayi ba ta inda baya wakana."

sosai mutumin ya d'anji sanyi kana yace. 

"Wacce uguwa kuke ne?."

cikin sanyi Bappa Ali yace.

"Har Dukku muke."

da sauri yace.

"Ina mamanshi?."

kai ya jinjina kana yace.

"Mamanshi da babanshi duk basu saniba, suna Dukku ni kuma dama ina Kurugu to da aka kirani sai na taho nand'in. 

Yanzu in ba matsala in akwai masu kula dashi zan wuce Dukku inje in sanar musu."

cikin kad'uwa yace.

"To kai waye d'inshi ne?."

"Ni bappanshi ne k'anin mahaifinshi kuma mahaifin nashima baida lfy."

kai ya jinjina kana ya zaro kud'i a aljihunshi sannan ya mik'a mishi tare da cewa. 

"Ba matsala zan kula da komai kayi maza kaje ka sanar musu."

k'in amsar kud'in yayi, shi kuwa mutumin ya sashi karb'a a dole. 


Haka dai ya amshi kudin badon ya soba ya tafi, 

shi kuwa mutumin shida kanshi ya zauna wurin kana ya bada duk abinda ya dace na jinyar Nuruddeen. 



Shi kuwa bappa Ali daya koma Dukku jiki a mace yayiwa Ummi bayani sai dai ya boye mata hak'ik'anin halin da Seyojinta ke ciki, yace mata da sauk'i sosai baiji ciwoba an dai mishi allurar bacci ne dan ya huta. 

To shiyasa hankalin ta bai tashi sosaiba, 

Saifuddeen kuma tun lokacin da Yayan nashi ya tafi sai yaja hannun Hayatuddeen suka tafi gidan Goggo Dada, to shiyasa bappa Ali bai tarar dashi a gidaba, 

kuma gidan Goggo Dada nada d'an nisa don ita a Shabewa take. 

Abba kuwa baida lfy ba damar yaje, 

haka yasa Bappa Ali ya juya shida Adnan babban abokin Nuruddeen d'in, 

kana sai Rahma. 


Koda sukaje gaba d'aya hankalinsu ya tashi ganin yadda Nuruddeen ke kwance tamkar gawa Rahma tayi ta kuka tamkar ranta zai fita, 

Adnan yanata rarrashinta, 

Bappa Ali kuwa mutumin ne keta rarrashinsa.


Ganin dare ya fara nisa yasa Bappa Ali cewa Rahma ta koma dan har takwas na dare yayi, 

jin haka yasa mutumin nan k'iran d'anshi mai suna Arabi yazo.

Kana yace ya maidata Dukku da motar da yazo, 

ba musu ya d'auki Rahma ya maidata Dukku,

yana ajeta ya juyo Gombe. 

Ita kuwa Rahma jiki a mace ta shiga gida, 

Ummi dasu Saifuddeen da Abba dasu Raihana suka tasats a gaba da tambayar ya jikin nashi. 

sanin in ta gaya musu gskyar halin da yake ciki ba mmki jikin Abba ya tashi, Ummi ta k'ara shiga damuwa dan haka sai tai ta ce musu jikifa da sauk'i, 

koda Ummi ta bata abinci sam ta kasa ci, sai hawaye da take zubdawa time to time, kana tana sa hannu tana goge hawayen dan kar Ummi ko Saifuddeen su gani dan sam ta lura hankalin su a tashe yake. 

haka dai sukayi ta jimantawa juna kana sukayi shirin bacci da nufin gari na wayewa Ummi da Saifuddeen zasu shirya suje. 

Rahma kuwa har ta konta Ummi ta kuma biyota d'akinsu tana k'ara tambayar yanayin jikin nashi nanma dai boye mata gskyar tayi. 

a haka dai suka kwana da fargaba. 


A can Gombe kuwa k'arfe d'aya dai-dai na dere Nuruddeen yace ga garinku,

Allah sarki rai bak'on duniya,

bayan likitan ya sanar musu ya cika, 

Bappa Ali kam sai ya rasa inda zaisa ranshi kawai sai ya shiga d'akin da gawar yake yayi ta zagaya gadon yana wani irin azabebben kuka maicin zuciya da tada hankalin mai sauraro, 

Adnan kuwa kanshi ya kife gefen kan Nuruddeen yana wani irin sassayan kuka mai zazzafan hawaye, 

hakan mutumin nan tunda aka gaya musu ya zame a wurin ya zauna bisa kujera yana kuka mai ban tausayi yanayi yana tasbihi da hailala, 

sabida hankalin shi yayi matuk'ar tashi tunda yasan shine sanadin mutuwarshi. 


Bayan an d'auki gawar an kaita macuwari, 

su kuwa duk su uku sai suka nufi masallacin dake cikin asibitin bayan sunyi al'walane suka fara nafifili da k'auna Qur'an  tare da yimishi Addu'a. 



Koda gari ya waye mutumin nan yayi duk kan abinda ya kamata kafin a basu gawan, 

Aka yi mishi wonka aka shiryashi kamar yadda musuluncin ya tanadar mana, 

bayan an gama kimtsashi ne, suka barshin nan cikin asibitin tare da Adnan kana shi kuma ya d'auki bappa Ali ya nufi gidanshi dake Fantami, 

nan ya sanar musu abinda ke faruwa, 

kana ya fara gaiyatar jana'izar, 

bayan ya gama abinda ya sauwaqa sai kuma suka nufi Dukku.


Suna isa sukayi cikibus dasu Saifuddeen da Ummi da suke shirin tafiya yanzu.

ganin Bappa Ali da wani mutum a cikin zazzafar mota  yasa zuciyar Ummi karaya, 

sai tayi maza ta koma cikin gida, 

yayinda Saifuddeen kuma ya zubawa Bappa Ali idanu tamkar zai mannasu a jikinshi duk sun kasa yin Magna tuni mak'ota sun taru a wurin anata tambayar jikin Nuruddeen, 

amman ba mgna Bappa Ali sai jujjuya kai yakeyi yayinda mutumin nan kuwa yaketa zubda hawaye, 

ganin haka duk aka gane cewa Nuruddeen baya raye.


Ita ku Ummi tana shiga cikin gida da sauri Rahma dasu Raihana sukace.

"Ummi meya faru." duk da taji abinda sukace amman ta kasa mgna sai nufar inda Abba ke zaune tayi yayinda shi kuwa yayi mutuwar zaune, 

cikin rawar murya tace.

"Bappan Saifu ne ya dawo shida wani mutum."

wani irin zabura Abba yayi sai ya kuma koma ya zauna da sauri sabida azabar da yaji mak'ogoronnshi na mishi.

Dai-dai lokacin kuma Bappa Ali da mutumin nan suka shigo, 

gefen Abba suka zauna kana Ummi kuwa ta matsa can gefe ta zauna bisa kujera yar tsuguno gaba d'aya jikinta tsuma yake zuciyarta na harbawa da sauri-sauri, 

shi kuwa Abba ido ya zubawa mutumin da ya tasashi gaba yana kuka da shesshek'a a hankali,

cikin firgita da rauni murya can k'asa Abba ya kalli k'anin nashi da matarshi da yaranshi baki na rawa yace.

"Innalillahiwa Inna'ilaihi rajiun."

sai ya kuma rumtse idanunshi wasu zafafan hawaye ne suka kwaranyo mishi masu tsananin k'una murya can k'asa yace

"Mutuwa ta barni ta d'auke Seyo na ko?."

cikin zubda kolla bappa Ali ya gyada mishi kai, 

ido ya rumtse kana yayi murmushi tare da cewa.

"Hmmm Seyo na ya tafi ya barni! nasan nima bazan kai bad'i iwar hakaba, zan bishi zanbi bayanshi, Aliyu na tausaya maka zan tafi in barka da nauyi, 

Saifuddeen zai d'auki nauyin da shekarunsa basu kai ya d'aukaba."

kawai sai suka had'e kai suna kuka, 

hakama su Raihana da Raliyya da Hayatuddeen Amman Ummi da Saifuddeen da Rahma sun gaza kuka domin ance wani zafin ya wuce inda hawaye yake.

Mutumminan kuwa shima kuka yakeyi cur-cur da hawayenshi yana basu hak'uri.


Ita kuwa Ummi wani abu mai tsananin k'arfin taji ya tsoki k'afon zuciyarta ya danne kukan da takeji tana son yi, 

hakama Rahma sai d'anta Faruq daya tasa a gaba yana kuka ita kuwa sai dafe zaciyarta dake barazanar tarwatsewa tayi kana zuba musu idanu tamkar zautacciya.

Aunty Nina kuwa matar bappa Ali fargaba yasa cikin jikinta b'arewa. 

Saifuddeen kuwa Allah ne kad'ai yasan abinda yakeji a ranshi, in ya kalli Ummi da Rahma ji yakeyi tamkar zai fad'i ya mutu dan tsananin zafin da k'una da zuciyarshi ke mishi. 

shi ko Abba yunk'ura yayi a hankali ya tashi kana ya kalli k'aninshi yace.

"Ina gawar take?."

cikin tausayawa mutumin nan ya mishi bayani kana duk masu zuwa jana'iza a dauko motocin a tasha ya biya kudinsu, 

nan aka dugguzuma aka nufi Gombe.

bayan sallan azahar aka sallaci gawar, sannan akaje aka binneshi, 

motocin  nan suka jidi mutanen Dukku suka meda su, kafin su dawo duk yan uwa da abokan arzik'i an hallara tuni Goggo Dada ma da tazo, 

dama Ahmad da babanshi kam dasu akaje gombe.


Nan sukayi zaman makoki na kwana bakwai, 


mutumin nan shima yayi zaman makoki a gidanshi na tsawon kwana uku,randa akayi sadakan bakwai yaje Dukku ya k'ara basu hak'uri,

nan sukace sun yafe, domin k'addarace ta rigayi fata sannan shi kuma yayi musu al'khairi sosai dan harda kayan abinci ya kawo musu

tuni kuma ya fara azumi settin d'in da zaiyi.



Rayuwa dai taci gaba da tafiya a haka.

Yau da dad'i gobe akasin haka.

Abu da dama ya faru cikin watanni ukun nan. 


   Bayan wata uku

Ranar wata asabar bayan sallan magrib,

duk suna tsakiyar gida, Ummi ta tasa Rahma dasu Raihana da Raliyya suna d'an hira, 

Saifuddeen kuwa da Hayatuddeen suna gaban Abba.

mik'ewa Abba yayi kana ya kalli Ummi da yaranta da suke shawarar a saida kayan d'akin Rahma a kaishi asibiti ai mishi aikin mak'ok'on .

murmushi ya d'anyi kana ya d'auki butar dake gefenshi tare da nufar hanyar ban d'aki  yana mai ce musu. 

"Uhumm Rahma kenan, kada ku yarda ku saida wani abunku a kaina fa, domin wannan ciwon nawa tabbas wata rana shine ajalina."

d'an tsayawa yayi jin Rahma na cewa.

"Dan Allah Abba kayi hak'uri  mu kaika asibiti, bazamu iya ganinka hakaba."

murmushi ya kumayi kana yace. 

"Rahma iyayena mafa haka sukayi ta nema min mgni k'arshe har suka rasu ban samu lfy ba, hakama k'annena gaba d'aya Ali ya saida gonakinmu da filayanmu na gado, 

a kan nema min mgni yanzu du-du du gonaki ukune suka rage sai wannan filin da ke can bayanmu wanda shi kuma dama nine na sayeshi da sunanku.

dan haka ku dena wahal da kanku ai sauk'in yazo."

yana fad'in haka ya juya ya nufi bayan gidan,

a dai-dai bakin k'ofar ya fad'i.

Wanda kafinma a d'agashi ya  cika.

Wannan rana anga tashin hankalin wannan ahlin, 

dole Abba kwanan keso yayi, 

washe gari da hantsi akayi mishi sutura, wanda tuni k'ofar gidansu ta cika da al'ummar annabi.

Bayan an mishi sutura an kimtsashi kamar yadda musulunci ya koyar damu 

anzo za'a d'auki makar ne za'a fiddashi.

da sauri Bappa Ali  ya kalli Saifuddeen daya rik'e makarar yanayin wani irin kukan da yasa dukkan bani adam dake wurin zubda zazzafan hawaye, 

tuni shima Bappa Ali sai ya zame kana ya ruggumi Saifuddeen da Hayatuddeen dake ruggume dashi, kuka sukeyi wanda duk kan mai imani zai tausaya musu. 

shi kam Saifuddeen duniya ta mishi zafi ji yakeyi tamkar bai tab'a farin cikiba, fata yake inama shima mutuwar tazo ta d'aukeshi. 

tausayin kanshi da mahaifiyarsu da k'anneshi da yayarshi yakeji tamkar zai d'auke numfashi sa. 

Man Liman ne suka janye bappa Ali kana Baba Hamisu yasa hannu ya janye hannun Saufuddeen daga rik'on da yayiwa makarar. 

Baba Ashiru kuwa da wani abokinshi wanda kuma malamin islamiyarsu Saifuddeen ne sune suka kamashi ganin yanayin da yake ciki, 

cikin sanyi Baba Ashiru ya cewa Hayatudden.

"Deen je  ka kawo min ruwa. 

cikin kuka ya mik'e kana ya kawo ruwan amsa yayi kana ya kalli Saifuddeen da idanunshi sukayi jazir tamkar zasuyi aman wuta, ganin bazai k'arb'a bane yasa Malaminshi amsar ruwan ya kai mishi har baki, 

kana cikin sanyin murya yace. 

"Saifuddeen kasha ruwa zakaji sanyi a ranka."

a hankali ya fara shan ruwan domin jin zuciyarshi yake tamkar ana soya mishi ita, 

ajiyan zuciya ya rink'a sauk'ewa akai akai kana hawayenshi suka tsagaita, 

Ya Nuruddeen d'inshi ne ya fad'o mishi a rai, tabbas da yana raye da bazai bari kukansu ya tsanantaba, 

wani numfashi yaja kana ya kalli Malamin nashi da yake ce mishi.

"Tashi muje woje Saifuddeen muje ka tsaya a sallaci gawan mahaifinka, 

kayi mishi addu'a a madadin kukannan da kake mishi, ka sani dukkan tsanani yana tare da sauk'i in sha Allah muna zatawa d'an uwanka da mahaifinka rahama, kada kayi musu kuka domin su mutanene na gari musu imani da tawakkali basu da abakan musu bare na fada ko gaba, 

ka sani babu maraya sai rago, kuma nakasa ba kasawa bace.

Kada kayi ta kuka domin kukanka shi zaisa yan uwanka kuka, kuma kukanku shi zaisa mahaifiyarku kuka har ta kai ga ta kamu da wata cutar ka daure ka jumre ka zama Garkuwarsu."

Cikin tsanani rauni ya mik'e  tare da yi mishi alama da yaji zai bari, 

daga nan sukaje suka sallaci gawar kana aka kaita makwancinta. 

Nan aka zauna zaman makoki.


Yau akayi sadakan Uku, duk da haka Bappa Ali dasu Malam Ashiru da Baba Hamisu dasu Saifuddeen d'in suna zama dan akwai masu zuwa gaisuwa. 

Bayan sallan azahar ne duk suna zaune a gindin bishiyar limis dake harabar massalacin k'ofar gidan nasu, 

wasu maza su uku sukazo wanda kusan abokan Abban ne bayan sun gaisa ne d'aya daga cikinsu ya zurawa Saifuddeen idanu yana kallonshi ido cikin ido, 

shi kuwa Saifuddeen bai kauda idanshi bane dan ganin mutumin yana jujjuya kai alamun zaiyi mgn to sanin in ba kallon bakinshi yakeyi ba bazai gane abinda yake fad'anba shiyasa ya tsurawa mutumin ido,

shi kuwa mutumin cikin jujjuya kai yace.

"Allah sarki duniya mutuwa bata zabi, 

Allah bai barin wani dan wani yaji dad'i."

sai ya kuma kalli su Bappa da Malam Ashiru da suke jinjina kai sannan ya meda hankalin shi ga Saifuddeen tare da cewa. 

"Da ana bawa mutuwa zab'i  ai da an bata zab'i ta d'auke wannan nakasasshen ta bar Nuruddeen da shike kula da rayuwar k'annenshi."

da sauri su Bappa Ali suka zaro ido tare da cewa. 

"Subahanallahi Mala Bala wannan wanne irin mugun furuci ne?."

kai jinjina musu tare da jaddada musu cikin rashin iya mgna yace. 

"A ai gsky ne Malam Ashiru shi wannan dame zai amfani kanshi ma bare ya amfami wasu, 

yaron dashi da dutse bashi da banbanci ai su Rahma sun tagaira da mutuwa ta d'auke Nuruddeen ya bar musu mara amfani, 

ko su da kansu ai zasuce da mutuwar ta had'a uban nasu dashi wannan kurman ta yashe su ta bar musu Nuruddeen."

cikin tsananin b'acin rai Malam Ashiru yace. 

"Kai tafi daga nan gaisuwa kazo ko cin zarafi?."

Bappa Ali kuwa ya gaza cewa komai sai idanu ya zubawa Saifuddeen wanda ya rumtse idanunshi da tsananin k'arfi dan azabar b'acin ran kalaman da Mala Bala ya mishi gashi abokin mahaifinshi ne ba daman ya mishi wani abun.

Sauran abokansu biyun da suka zo tare da Mala balanne suka mik'e cikin jin haushin kalamanshi suka sallami su bappa Ali tare da basu hak'uri sannan suka tafi. 


A daran wannan ranar Saifuddeen yayi kukanda bai tab'a yiba, 

inda yake ganin inama shi mutuwar ta d'auke ta bar Ya Nuruddeen d'inshi a ranar mutuwar ta dawo mishi sabuwa a ranshi, 

tausayinsu Rahma da Ummi ya hanashi sukuni ya zaiyi ya kula da rayuwarsu? haka dai kwanaki sukayi ta tafiya



Randa akayi sadakan bakyai duk yan uwa suka watse gida ya rage su kadai.

Hakan yasa  suka zauna sukayi ta kuka. 


Washe gari da safe duk suna tsakiyar gidan time to time in Ummi ta kallesu sai tayi ta zubda hawaye. 

ganin haka duk sai jikinsu yayi sanyi, 

Rahma kam tuni kuka takeyi dan ita kam rayuwa ta mata zafi ba miji ba uba ba yayansu jigonsu, wanda suke ganin zai zama gatan nasu kuma gashi kurmane. 

jin kukan Rahma yasa Ummi tsananta kukanta, 

shi kuwa Saifuddeen idanu ya rumtse sabida ba abinda yafi tsana a duniya kamar yaga hawayen Umminshi,

 Raihana kuwa ruggume Hayatuddeen tayi tana kuka Raliyya kuwa su Faruq ta ruggume. 

Suna cikin haka sukaji sallama, 

cikin sauri Ummi ta d'ago kanta jin muryar Bappanta k'anin babanta da Goggonta, sai matar Bappan nata iya bukku muguwar mace, shiyasa Ummi take rayuwa tamkar bata da dangin Uba. 

da sauri ta taso ta nufi Goggonta, 

kan taburma suka zube nan raunin Ummi ya tashi ganin danginta kife kanta tayi kan cinyar Goggo Rabinta d'in ta saki wani marayan kuka. 

itama Goggo Rabi kukan takeyi dan tausayawa d'iyar yayanta.

hakama Bappa idintan shima kukan yakeyi dan tausayawa rayuwar Ummi da yaranta, 

ita kuwa Iya Bukku sai wani mugun kallo na rashin imani take bin su Rahma dashi. 

Yayinda shi kuwa Saifuddeen ita ya zubawa idanu ganin mugun kallom data juyo tana yiwa Ummimshi. 

cikin tausayawa Goggo Rabi ta d'ago Ummi cikin sanyin murya tace.

"Kiyi hak'uri Bisije dukkan tsanani yana tare da sauk'i, ki dena musu kuka Allah yana sane dake da marayunki."

murya a disashe Ummi tace. 

"Goggo Rabi ya zanyi ina zan shiga a duniyar nan inji dad'i wa zai rik'e min yarayuna wazai tallafawa maraicina dana yarana da marayun jikokina?".

sai ta kuma juyowa ta kalli Bappa idin nata cikin rawan murya tace.

"Bappa ya zanyi wa zai zama gatanmu wa zai zama garkuwarmu, tunda shima bappan su Rahma ba wadata yakeda shiba, sana'ar me zanyi in rik'e yarana?."

kafin Bappa idin yayi mgna tuni iya bukku ta cab'e mgnar da cewa.

"Wannan kurman d'an naki mai kama da dutse shi baida amfanin komai ne?."

sai ta kuma tsuke fuska dan bata son bappa idi yace zai d'aukesu su koma garinsu dasu, 

da sauri ta kauda kanta lokacin da ta kalli Saifuddeen sabida wani irin mugun kallo daya watsa mata. 

sai kuma ta tsuke fuska kana taci gaba da cewa. 

"In dai bazai amfanekiba ai sai ku jefar dashi ku huta da ciyar da mai zubin mutanen b'oye yaro tun yana k'arami ni tsoro yake bani dan wannan kyawun nashi ya zarta na mutanen mu. 

 in kuma bazaki iyaba, tunda ke jakar 'ya'yace akan yaranki zaki mutu, 

to sai ki shiga cikin gari kije gidajen masu kud'i kina musu share-share da wanke-wanke da girki, suna baki dubu 6 a wata kullum kuma kina kwatsawa zugan yaran naki tuwo, nasan harda k'anzo zasuke baki."

wani irin mugun kallo da tsana Saifuddeen yake cilla mata,

domin tunda yake a duniya bai tab'a jin mgnar da tai mishi zafi kamar wannarba, kana bai taba jin mutun mai munanan kalamaiba kamar iya Bukku ba.

Goggo Rabi kuwa kai ta rink'a jujjuyawa alamar batajin dad'in kalaman da matar yayan nata takewa d'iyar yayanta marigayi. 

Bappa idi kuwa sunkuyar da kanshi yayi dan yasan motsi kad'an zaiyi iya Bukku zata solleshi. 

Raihana ce ta share hawayenta tare da murgud'a mata baki kana tace. 

"Allah ya kiyaye Umminmu tayi ai katau a gidajen wasu, 

kuma Hamma Saifunmu ba k'aton banza bane kurwarshi kur sai dai kici kanki wlh yafi k'arfinki,

har zakice mishi baida amfani to in sha Allah aniyarki kanki zata kom...!"

da sauri tayi shiru dan bugun da taji Ummi ta kaimata a baki tare da cewa.

"Raihana ki kiyayeni fa, banfa miki irin wannan tarbiyarba maza tashi ki bar nan."

cikin sanyi ta mik'e tare watsawa iya Bukku harara kana tace. 

"Kiyi hak'uri Umminmu bazan k'araba."

Goggo Rabi kuwa ji tayi kamar ta goya Raihana dan dad'in ta sulle iya Bukku. 

shima bappa idin dad'i yaji. 

shi kuwa Saifuddeen, Ummi ya zubawa ido yana karanto bac'in ranta, 

sai ya kuma juyawa ya kalli Rahma da ta sunkuyar da kanta hawaye na zubo mata. 

itako Iya Bukku cikin masifa da rashin mutunci tace. 

"Kaji hegiyar yarinya mai kama da aljan kujiye min fitsarerriyar yariya da uwarta bata haifeta da bisimillaba, 

ke har kin kai ki zageni? 

to na fad'a bashi da amfani, ai da yana da amfanin da ya tsare muku maraicinku, 

ya zauna kamar dutse ya wani zuba min shegun idanunshi ya had'e wannan fuska tashi mai kama data al'jamu."

sai ta kuma ja tsaki kana ta mik'e tsaye tare da juyowa ta kalli Saifuddeen da zuciyarshi ke tafarfasa da sauri ta kauda idonta daga kanshi sabidah arararda yake watsa.

cikin k'arfin hali tace. 

"Wannan da gani rabi mutum ne rabi aljan, mutun da aljan.

Dan duk zuriyar kakanunku babu kekyawa kamanshi wannan kyau bana Allah da annabi bane, hege mai jajen kunnuwa da labban baki."

sai ta kuma juyo ta fuskancesu baki d'aya kana tace.

"Bisije in kin yarda da shawarata wlh ki kaishi bakin kogi dan da gani wannan d'an ruwane, 

in kuma kingi to ki bashi k'ok'on bara yaje yayi ta bara a cikin Gombe nasan wasu ko dan kyanshi zasu bashi sadaka, tunda nakasasshene bararce kawai aikinshi ai."

cikin zafin rai Rahma ta mik'e tare da tsuke fuska kana tace. 

"Bamu jikiba! aniyar kura tabi daji!

k'anina ba nakassashe bane, domin nakasar zuciya itace sahihiyar nakasa ba nakasar gangan jikiba. 

In sha Allah har abadan Saifuddeen bazaiyi bara ba, in Allah ya yarda hannunshi bazasu tab'a rik'e k'ok'on baraba.

Kuma acan zuriyarku ne ba kyawawa mu ki kallemu gaba d'ayanmu ba mummuna ki kuma bincika zuriyarmu kab kyawawane waya ce miki Baddukke yana muni bare bak'i, 

to mu mune dukku jinin Dukku bamu da mutuwar zuciya, 

bare muyi maula, 

ki kama bakinki sai randa muka nemi al'farma a wurinki kafin ki gaya mana ba sugari,

in kyawun Saifuddeen ke baki tsoro to sai dai ki makance. Ke! da kin san k'uruciyar Abbanmu sanda yanada lfy da suma zakiyi in kin ganshi, dan haka mu kyau gadanshi mukayi ki dena cewa k'anina d'an ruwa eh!."

shiru Ummi tayi dan tasan Rahma nada hak'uri k'ureta akayi, 

Raliyya kuwa sai harara taketa dokawa iya Bukku, 

Goggo Rabi kuwa murmushin jin dad'i take.

Bappa idi kuwa tsorone ya rufeshi yasan in sun koma zaisha rashin mutunci dan sunfi kwana biyar da jin mutuwar tace bazasu zoba da yake can garin Hashidu suke. 

shi yayi ta lallabata kan dole su zo, to yasan kanshi zata huce cewa zatayi da gayya yasata suka zo dan jikokinshi suci mata zarafi, 

shiyasa duk sai ya tsure da yake dama mijin tacene. 

Ita kuwa iya Bukku mari ta yarfawa Rahma, 

wanda yasa suka mik'e gaba d'ayansu kana cikin masifa tace. 

"To me amfanin kyan naku?  Uban naku da yayi kyau d'in ina da aljani ya rayu a jikinsa ya zama mahaukaci tuburan. 

To wane rana kyan naku ya muku, 

tunda gaki ke bazawara baki auruba ga kuma kitika-kitikan yan mata har biyu suma basu auruba, 

wata k'il basu da ko mashunshini, 

gaya min me amfanin kyan naku, uwar rashin kunya?."

gaba d'aya jikin Saifuddeeem b'ari yakeyi sabida zafin zuciya irin na kurame, 

ita kuwa Rahma rik'e hab'arta tayi tana kuka hakama Ummi. 

Itako iya Bukku cikin iya bak'ar mgna taci gaba da cewa. 

"To tunda baki san amfanin da kyan naku zai mukuba, ni bari in gaya miki, 

kuje ku fara *KARUWANCI* nasan tabbas zakuyi kasuwa, kuyi karuwanci ku tara kudi dan nasan shima wannan Saifuddeen  aljanin uban naku kanshi zasu dawo dan haka kuje kuyi karuwanc...?"

bata kai ga k'arishe mgnarba ta kurma wani irin razanenne ihu da ya cika unguwar baki d'aya. 

bata ida dawowa haiyacintaba ta kuma kurma wani azabebben ihu, 

sabida wasu zafafan maruka da Saifuddeen ya yarfa mata, 

wanda a take sai ga hagwaranta a biyu a k'asa. 

Ihu ta kumayi jin yasa k'afarshi ya tad'eta ta zube kasa rakacab ji kake d'im kamar an tila kayan wonki, 

cikin rufewar ido da fita haiyaci Saifuddeen  ya zaro ball inshi ya tsula mata d'aya zai kuma na biyu ne Ummi ta rik'o hannunshi tana kuka tana cewa. 

"Saifuddeen ka rufa mana asiri muji da maraicinmu, 

gaishemu fa sukazo yi."

Raliyya kuwa da Raihana sai murmushin jin dad'i suke yayinda Hayatuddeen yake tsalle yana cewa. 

"Allah shi k'ara Ummi barshi ya dakata hegiya mai k'aton d'uwawu."

iya Bukku kuwa ai tana samun Ummi ta rike mata Saifuddeen cikin tsananin gigita da tsoro, 

ta mike ta wawuri takalmanta a hannu gabas ta nufa a gigice sai ta kumayi kona tayi yamma kana ta juyo arewa, ganin har yanzu dai bata gane hanyar fitarba sai ta kuma yi kudu cikin tsananin gudu ta fita tare da cewa. 

"Rabi, malam ku fito mugudu, aljanin sun motsa dama ba nace muku ruwa biyu bane shi ku fito mu gudu karya kashemu."

ita kam Goggo rabi niyarta zata tsaya,  to ganin yayanta yabi matar tashi a guje shiyasa itama tabi bayansu a saba'in suka bar garim Dukku akan baburdin Bappa idin.


 A cikin gidan kuwa Raihana da Raliyya da Hayatuddeen sai su kalli juna kana suyi yar dariya.

Cikin fad'a Ummi ta watsa musu harara, kana ta fuskancesu da kyau dan duk sun tsaya sunyi cirko-cirko sun tasa a gaba cikin nuna b'acin ranta tace. 

"Dariyar me kukayi? dan baku da wayo baku san halin da muke cikiba, wani farin cike muke dashi da har zai saku dariya? 

kema Rahma da nake miki kallon mai hak'uri ashe ba haka bane."

sai ta kuma nuna Raihana tare da cewa. 

"Duk kece kika jawo abinnan da baki tanka mataba da tayi ta bari, 

amman sai kika tsafe ido zaki zageta bayan kunsan ba hak'urine da itaba."

sai ta kuma juyawa ta kalli Saifuddeen nan take sai zuciyarta ta raunata cikin zubda hawaye da rawan murya tace. 

"Babana meyasa kayi haka?  ka mance yanzu bamu da kowa a duniya dole muna buk'atar taimakonsu."

cikin tsananin kunar zuciya ya tsuguna k'asa ya fara rubutu da sauri yayinda hannunshi har rawa yakeyi dan bac'in rai.

"Dan Allah Ummi karki sake cewa bamu da kowa, 

kin mance munada Allahn daya haliccemu shine mai rayawa mai kashewa mai badawa mai hanawa shine wanda ya mana gida biyu duniya da lahira, 

shine mai azirta bayinshi a duk sanda yaso shine yake ciyar da dukkan abin halitta, kuma muma shine zai cidamu,

shine gatan kowa kuma muma zai zama gatanmu baifa mance da muba. 

Ummi koke da kike yarsu dame suka amfaneki a rayuwarki? bare mu jikokin d'an uwansu da ya rasu shekaru da dama. 

Ummi ki kalleni nayi al'k'awari in sha Allah zan nema da k'arfina da lfyta zan kula daku iya iyawata, karki sake kaiwa kowa kukanki ki kaiwa Allah shi zai biya miki buk'atunki ba gajiyawa bare gori.

Ummi kiyi min addu'a ki sanya min al'barla in sha Allah ni d'innan zan cidaku in kuaa shayardaku in jinyaceku in suturtaku."

ita kam Ummi ta kasa cewa komai sai ido ta zuba mishi domin yana tsugune sai rubutu yakeyi in inda yake ya cika kana sai yaja baya yanayi jikinshi na rawa cikin zubda hawaye taci gaba da bin rubutun da yakeyi tana karantawa. 

"Ummi rabuwarmu dasu shiyafi al'khairi domin muddin tana zuwa tana fad'i mana mugayen kalamai wata rana zan karya mata wuya,

Ummi na karkiji tsoro in sha Allah k'annena bazasuyi karuwanciba ni kuma bazanyi baraba bare maula, kema bazakiyi aikatauba, ki kalleni ki gaya min dukkan matsalarki kiyi shawara dani ko k'annena kada ki gayawa kowa matsalarki ki sirranta matsalarki damu yaranki.

Insha Allah zan fara neman sana'ar yi dan rik'eku ke dai ki samin al'barka."

Rahma kam sai hawayenta take shartewa, 

su Raihana kuwa sai binshi suke suna karanta abinda yake rubutawan. 

Ita kuwa Ummi da sauri ta isa inda yake hannunta tasa tsakiyar kanshi cikin k'arfin hali tace. 

"Ya Allah kayiwa wannan bawa naka Saifuddeen al'barka ya Allah ka yalwata mishi samunshi hagu da dama rabbi ka al'barkaci duk abinda ya tab'a ya wahidun k'ahhar ka bud'a mishi k'ofofin samu gabas da yamma kudu da arewa.

Ya Allah ka kauda asara da gafala da tab'ewa daga gareshi dashi dama dukkan yan uwa musulmai, ya rabbil izzati ka al'barkaci rayuwar Saifuddeen ka raya minshi ka shirya minshi ka bashi arzik'i mai al'barka wanda musulmai da musulunci zasu al'fahari dashi ya ka bud'a mishi k'ofofin samu ka yalwata arzik'inshi."

kasan cewar tunda ta dafa kanshi ya d'ago kai ya kalleta shiyasa yake gane abinda take cewa, 

yana kallonta still yatsarshi na k'asa yana.

 Rubuta "Amin Amin Ameeen ya rabbil izzati".

daga nan suka zauna tayi ta musu nasiha mai ratsa jiki. 


Bappa Ali kuwa da matarshi suna side d'insu sam basu san meya faruba. 



A daren ranar Saifuddeen yaje ya samu Bappa Ali da fefanshi da biro, 

nan yake neman izinin bappan nashi da kuma shawarshi cewa. 

A d'auki machine d'in Nuruddeen a bawa wani d'an mak'ocinsu Salisu wanda shima d'an acaba ne to dama na haya yake karba, to kuma an karb'e machine d'in wai mai ita zai saidata ya cikata ya sai sabuwa, 

ba musu bappa Ali ya yarda dan yasan ko ba komai balance d'in zai taimakesu, 

shi kuwa Saifudden gyara zamanshi yayi kana ya rubutawa bappan nashi cewa. 

Kullum da safe in Salisu zai tafi zai bishi su tafi tare, 

in yaje zai shiga cikin kasuwan Gombe zai nemi sa'ar da zaiyi."

da fari Bappa Ali yak'i kasan cewar yanaga Saifuddeen d'in kurma ne, 

to amman da suka dunguzuma sukaje wurin Ummi sai ta kauda kai yadda Saifuddeen d'in bazai ga bakintaba tace. 

"Ba matsala Ali barshi yaje, in mun hanashi zaiga ko dan yanada nakasane, mukuma bamu son hakan to amman ai kasuwa saida jari, 

amman tunda yace a barshi yaje,to mu barshin in yaje yaga ba abinda zai ai zai bar zuwa, mu kuma bishi da addu'a Allah ya taimaka mishi."

cikin sanyi bappa Ali yace.

"To shake nan ba matsala Allah ya bashi sa'a."

"Amin Amin." sukace baki d'aya.


Daga part d'in Ummi woje suka fita, 

sukako yi sa'an samun Salisu a harabar matsallacin k'ofar gidan nasu.

Nan bappa Ali ya mishi bayanin yadda sukayi, aiko dad'i kamar ya kashe Salisu, 

ya kuma yarda da shared'in zaike zuwa da Saifuddeen su kuma dawo tare. 

A take bappa Ali ya bashi Key d'in machine d'in. 

sannan ya wuce cikin sangayarsu ya fara ratsa tsakiyar d'aliban nasu. 

shi kuwa Saifuddeen gida ya koma ya sanarwa Ummi yadda sukayi, ita ko Ummi sai addu'a da samishi al'barka takeyi.

A daren ranar Ummi da Rahma da Raihana da Bappa Ali kusan kwana sukayi sunayi mishi addu'ar samun madafa da sa'a. 

Shi kam Saifuddeen baiyi bacci a ranar bare ya rumtsa, 

Kwana yayi yana neman yardar Allah da sanya al'barkanshi ya bashi sa'a a cikin k'udurin da yayi. 


Washe gari da sanyin safiya Saifuddeen ya shirya bayan ya karya Salisu ya shigo yace su tafi. 

gaban Ummi ya tsuguna kanshi ta dafa tare da sa mishi al'barka.

sannan su Rahma suka mishi addu'a baki d'ayansu kana suka fita suka tafi. 



Suna shiga Gombe Salisu ya wuce dashi k'aramar kasuwa,

gab da San Hussen mall ya ajiyeshi, 

kamar yadda sukayi tun jiya da dare, 

bayan ya sauk'ane Salisu ya kalleshi tare da cewa. 

"Ana yin sallan magrib kazo ka tsaya a nan, dan zanzo in d'aukeka mu tafi in munyi sa'a bayan isha mun isa Dukku."

cikin nuna alamar ya gane ya gyad'a mishi kai alamar toh. 

Salisu na ganin haka yaja machine inshi gaban wata yar budurwa data tsaidashi, 

lokaci d'aya suka shirya kud'in da zata bashi kana ta hau yaja ya tafi. 


Shi kuwa Saifuddeen juyowa yayi ya zubawa makeken wurin San Hussain d'in idanu a lokacin tun forkon-forkon bud'eshi kana wurin ba'a wani gyarashi sosaiba kamar yanzu ba,

ajiyan zuciya yayi lokacin daya karanta sunan wurin, 

sai kuma ya k'auda kai kana yayi tafiya kad'an yazo dai-dai mashigar kasuwan, 

inda zai bulla ta babban layin na k'aramar kasuwan.

ida nunshi ya lumshe kana ya bud'esu a hankali hannunshi ya had'e wuri d'aya kana ya fara karanto addu'o'i yayi kusan 16 minutes yana addu'o'in kana ya shafa a fuskarshi kasan cewar da d'an sanyin safiya ne wurin bai cika jama sosaiba kuma kowa sauri yake ya wuce ya isa wurin sana'arshi ya bud'e. 

bayan ya shafa addu'ar ne yayi bisimillah tare da d'ago k'afarshi ta dama ya shiga cikin kasuwan. 

Sannan ya mik'e gabanshi samb'et, yana tafiya a hankali. 

har yazo dai-dai wani babban shagon seye da sayarwa inda mata keta shiga da fita irin masu zuwar sassafen nan shagon kuma cike yake mak'il da atampopi, shadda, laces, material, voyels, su wagbari, gyalulluka. da dai sauransu, 

ido ya zubawa yaran shagon kowa na hidiman gabanshi. 

a hankali ya kalli saman shagon inda yaga an rubuta. 

Alhj Ishaq,

murmushi yayi dan sunan mai shagon ya tuno mishi sunan abokinshi wanda kusan sau biyu kenan yana zuwa Dukku bayan Abba ya rasu. 

juyawa yayi d'aya sashin inda yaga wani k'aton shagon mai cike da gyalulluka da dogayen riguna, 

kana ya kalli d'aya sashin inda yaga k'aton shagon saida takalma, 

sai kuma kusa da inda yake shagon masu saida yadin hijabai ne da masu d'in kasu.

shiru yayi sai ya kuma ci gaba da tafiya ganin ya b'ata kusan 30 minutes a wurin. 

A hankali yake taku har ya isa konan shagunan alhaji Yawale, 

shiga yayi nanma ya dad'e a tsaye sai kuma yayi baya ganin kusan irin kayayyakin wancan shagon ne daya wuce, 

kan babban layin ya dawo kana yaci gaba da tafiya, 

Dai-dai shagunan ba mishkila ya tsaya yana kallon yadda mutane ke cike a wurin mazansu da matansu yara da k'anana, 

ido ya d'an zubawa yaran shagon ganin kowa da abinda yake aunarwa kuma awu mai kyau irin awunda musulunci ya yarda dashi, 

sunan shagon ya kalla sai kuma yayi murmushi ganin sunan shagunan ba mishkila a ranshi yace.

 "Eh tabbas kam ba mishkila."


A takaice dai a wanan ranar kam kusan aikin daya wuni yi kenan ya zaga wannan layin ya zaga wancam layin, kana yana bin bakin shaguna yana kallon abubuwan dake ciki da yadda suke mu'amala da costumers insu, yana jin yunwa na k'ak'ularshi amman bai kulaba in lokacin salla yayi ya sayi pure water yayi al'wala yabi jam'in inda duk yaga ana haramar salla.


Kafin magrib ya gaji lik'is. 


koda magrib ta kawo kai sai yaga anata rurrufe shaguna hakan yasa ya fita, 

bakin inda Salisu ya ajiyeshi, 

yana tsaye a wurin ya hango tsallaken titin anata Al'wala haka yasa shima yayi Al'wala kana ya tsallaka yaje akayi sallah dashi. 

yana dawowa Salisu na isawa,

babu b'ata lokaci ya hau suka fara tafiya, 

sunzo dai-dai wani wurin masu tuwo-tuwo Salisu ya tsaya kana yacewa Saifuddeen. 

"Zo muje muci abinci kafin mu tafi naga alamun kamar ba abinda kaci."

juyawa yayi kalli wurin da Salisu ya nuna mishi, 

baki ya tab'e kana ya girgiza mishi kai tare da nuna alamar kamar yana kekyamin abincin wurin. 

murmushi Salisu yayi dan tabbas yasan Saifuddeen mutunne mai tsananin tsabta da gayu kuma yanada kyakyani, 

dan yasan iya tsawon yarintansu bai tab'a ganin ya sayi koda ko kosai ko wani abuba cikin abubuwan da ake kawowa a yar majalisar k'ofar gidansu ba. 

So dan haka sai ya hau machine d'in yaja tafiya kad'an suka isa wurin mai shayi, kana yace.

"To mu shiga nan kasha koda shayine."

Still tab'e baki yayi tare da juya kai, 

alamun bazai shaba. 

ganin haka Sakisu ya kuma jan machine d'in, kai tsaye hanyar tashan Dukku ya nufa dashi, 

suna zuwa dai-dai bakin gate d'in Abba bakery yayi parking kana ya sauk'a sannan, 

yacewa Saifuddeen.

"Zo muje nan ko zaka iya cin gashin wannan."

a tare suka shiga inda daga mashigar wurin mai naman yake, 

ganin wurin fes komai a killacene yasa, 

Saifuddeen yarda ya zauna a wurin, 

naman d'ari biyar Salisu ya saya musu, kana ya shiga cikin asalin Abba bekery ya sayo musu yogurt k'ananun robabin guda biyu. 

nan sukaci duk da Saifuddeen bai wani ci mai yawaba yanka hud'u yaci bai kuma k'arawaba sai yogurt yasha.

 Tuni kafin lokacin an kira isha'i haka yasa sukayi sallan

kafin suka nufi hanyar Dukku. 



Suna isa gida Ummi tai ta murna ganin ya dawo lfy kuma gashi babu alamun wahala, 

shi kuwa Saifuddeen yaki yace mata komai sabida gudun kada ta hanashi zuwa gobe. 


Washe garima kamar jiya suka shirya suka tafi bayan Umminshi tayi ta mishi addu'ar samun nasara.


A inda Salisu ya ajiyeshi jiya yauma nan ya ajeshi, 

bayan yaja ya tafine shi kuma ya nufi bakin mashigar kasuwar, 

yauma kamar jiya saida yayi addu'a kafin ya shiga da k'afan dama. 

Kai tsaye layin masu kayan yara ya shiga a hankali yake bin shagunan daki-daki yana kallon yadda suke gudanar da kasuwancin su, mata masu ciki nata shege da fice, a hankali yake taku cikin nitsuwa.

duk wanda ya ganshi sai ya k'ara juyawa ya kalleshi sabida bak'ak'en kayan da ya saka ba k'aramin haskashi sukayiba farinshi ya k'ara fitowa hancin nan har baki, uwa uba sumar kanshi tafi sawa ana kallonshi sabida duk wanda yaga sumar zai tunanin balarabe ne,

fatar k'afafunshi da tafin hannunshi kuwa sunyi jazir, in ya taka k'afar tamkar jini zai tsillo. 

Dai dai bakin wani k'aton shago ya tsaya, 

yana tsayuwa kenan yaji an.....!





                               By

    



             *NAKASA BA KASAWA BACE*


                        *PAGE 4*


                            NA

             *AYSHA ALIYU GARKUWA*


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


                     Free page 


*Wannan page ɗin kuma nakunw ƴan Hukuncin Allah fans two, ina al'fahari daku,*


*Ga masu son saya turo katin Mtn na 300 ta nan 09097853276 ko ta asusuna 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa* 


Yaji An d'an matso kusa dashi har  jikin wanda ya matso kusa da shid'in na gogan nashi jikin hakan ya sashi juyowa a hankali ya d'an kalli matashin da bazai zarta sa'anshi ba, 

ganin d'an saurayin yana murmushi ya sashi d'an murmusawa, 

shi kuwa saurayin cikin fara'a ya mik'a mishi hannu ganin haka shima Saifuddeen ya bashi hannu, fuska cike da fara matashin ya fara mgna cikin bagwariyar larabcin, dan a zatonsa Saifuddeen balarabene,

sosai Saifuddeen ya zuba mishi ido tare da mmki dan ya gane zaton saurayin, haka yasashi k'ara tsurawa bakin matashin ido lokacin daya kuma ci gaba da mgna cikin larabcin shuwa'arab yace.

"Barka da zuwa, shigo daga ciki, me kake so?."

kai kawai Saifuddeen yake jujjuya mishi alamun a a ba abinda zai saya, 

shi kuwa saurayin murmishi ya kumayi dan a zatonsa Saifuddeen baya gane irin nashi larabcin ne haka ya sashi juya harshe eh zuwa hausa yece.

"Kai wannan balarabe ba dai kyauba Masha Allah, ko me kakeso ne oho."

wani dake cikin shagon ne yace. 

"Jabeer wai me yake sone, jiya mafa na ganshi a bakin shagon Alhaj ishaq."

murmushi wanda aka kira da Jabeer yayi kana yace. 

"Ai bai gane larabcina."

cikin zuba mishi ido wancan din yace. 

"To yaje gaba wala Allah a samu mai iya mishi irin yarenshi."

daga nan ya juya yaci gaba da sabgogin jera kayayyakin. 

Shi kuwa Saifuddeen gane abinda suka cene ya sashi juyawa ya ci gaba da tafiya. 

daga nan yayi ta bulayi har azahar koda yaga ana al'wala  shima ya zaro goma ya sai pure water  yayi al'wala kana ya nufi inda ya hango ana jam'i yana zuwa ana tada ik'a.

Bayan an idar da salla ya d'an jima a zaune yana addu'oi saida yaga an fara nannad'e taburman sai ya mik'e yaci gaba da yawatawa.

kanshi ya kule ya rasa ya zaiyi dan sam cikin kasuwar babu mai kula kowa kowa sabgar gabanshi keyi, kana duk bakin shagon da yaje ya tsaya sai ai ta mishi gwarancin larabci, duk da yana ganewa to amman  dame zai basu amsa tunda shi kurmane, 

haka yasa ake zaton bai gane larabcin ne tunda yawanci yan koyone ke gwada iyawarsu.

jin ya gaji da yawone yasashi shiga layin masu kayan kitchen nan ya samu inuwa dai dai bakin wani babban shago ya tsaya bencin dake gefe yaja ya zauna, 

yana kallon yadda ma'aikatan keta cinikaiya da masu sayyya kasan cewar ramadan ya kusa baifi wata biyu ya rageba shiyasa kasuwan masu kayan kitchen  ke gudu, 

sabida mata kan sabunta ababen aiki dan samun yalwatuwarsu.

d'aya daga cikin yaran shagon ne ya kalleshi da kyau kana yace. 

"Mai gida Allah yasa dai kana jin hausa?."

da sauri ya gyad'a mishi kai alamar. "Eh inaji."

shi kuwa murmushi yayi sannan yace.

"To me kakeso?." da sauri ya jujjuya mishi kai alamar.

 "Ba abinda nakeso."

gane abinda yake nufi yasa yaron shagon yace. 

"Hutawa kakeyi kenan?." still kai ya gyad'a mishi alamar eh. 

ganin kamar baison mgnane yasa yaron ya shareshi yaci gaba da sabgoginshi. 

Shiko Saifuddeen gyara zamanshi yayi tare jingina da jikin k'ofar shagon. 

mata nata shiga da fita, 

sai ya kuma tsargu ganin yadda aketa kallonshi,

har ya mik'e zai tafi sai ya kuma tsayawa ganin wani kekyawan Dottijo fari k'al dashi dake bisa keke bayan keken wani k'aton kwaline dake cike da lododi manya-manya irin k'atti sosai d'innan wanda in kayi sayayya mai yawa ake saka maka kayanka ciki, 

sai kuma tsaka-tsakiya sai yan saffa-saffa sai k'anana kana sai masu layi-layin nan sai kuma k'ananu irin mai gida ya kasa d'inna.

hannu ya mik'a ganin wannan kekyawan dottijon yana mik'o mishi kullunan lododin yana ce mishi. 

"Tai maka min mana yarona mik'a musu lododin, 

ka amso min kud'in na jiya, ba sai na sauk'a bisa motar tawa ba".

ya k'arishe mgnar cikin fara'a, 

shima murmushi yayi kana ya amshi ledodin ya juya cikin shagon inda yagga babban ogansu ya zaro kud'i ya irga gudan dubu guda uku kana da d'ari biyar, 

yana mik'owa Saifuddeen d'in yana kuma kallon Dottijon tare da cewa. 

"Barka da yamma baba Bello, kaga ko kamar kasan lododinmu sun k'are."

cikin sakin fuska dottijon yace.

"Kace nazo a dai-dai kenan?."

shiko mai shagon bayan ya karb'i lododin da Saifuddeen yake mik'o mishi sai ya kuma kalleshi kana ya kalli Dottijon tare da cewa.

"Kai Baba yau kam inaga a bamu na dubu biyar, 

sabida kar muzo gobe bakazo da wuriba su gaza mana."

da sauri tsohon yace.

"To ba matsala."

bayan ya amshi kud'in da Saifuddeen yake mik'o mishi ne sai ya kuma bashi wasu banduran lododin, 

da sauri ya amsa kana ya bawa mai shagon.

ganin alamun bakin mai shagon yana cewa.

"To Baba bello Allah bada kasuwa sai gobe kuma."

da sauri ya juya, ganin Dottijon na ce mishi. 

"Ngd ko d'an saurayi."

 kai ya gyad'a mishi tare da zura mushi ido ganin yaja keke nai ya tafi.


A hankali ya juya yaci gaba da tafiya bai jima da fara bulayinba yaga anata shirin Sallan la'asar daga nan shima yayi harama. 

Bayan an idarne ya koma layin masu robobi nan yayi ta yawatawa, 

hardai aka kira magrib ganin anata rurrufe shaguna ya sashi fitowa, inda yayi sallan magrib jiya anan yauma yayi salla yana dawowa kuma ya samu Salisu ya iso.


Daga nan bakin kasuwan bakin General hospital sukana nufa, 

inda daga bakin titin ta d'aya gefen akwai wata mai saida abinci sanin tanada tsabta ne yasa Salisu kawosu nan, 

amman Saifuddeen k'in ci yayi, 

sai dai Salisu yaci kana ya nuna mishi wani shagon fura da nono, 

gane yana sone yasa Salisu shiga ya seyo mishi k'aramar roba saida yasha sukayi sallan isha kafin suka d'auki hanyar dukku. 



Bayan sun isa shi Salisu yayi gidansu da machine d'in shi kuwa, Saifuddeen kai tsaye cikin gida ya nufa a tsakar gida ya samesu zaune, 

gefen Umminshi ya zauna kasan cewar akwai wuta duk suna ganin juna, 

da sauri Rahma ta kawo mishi abinci kana ta kunce bakin zaninta ta kunto 50 sannan ta kalli Hayatuddeen dake tsaye alamar zai fita ganin Saifuddeen dinne ya hanashi fita, 

hamtsin d'in ta mik'a mishi tare da cewa. 

"Ingo jeka gidansu Ya Adnan ka seyo mishi ruwan sanyi."

da sauri ya amsa tare ficewa. 

Ummi kuwa cikin kula tace. 

"Ya kasuwa?."

kai ya jinjina mata cikin son boye yanayin da yake wuni a cikin kasuwar.

Rahma kuwa ido ta zuba mishi tare da cewa.

"Saifuddeen gobema zakaje ne?."

da sauri ya gyad'a mata kai dan baya son su karaya.

Raihana kuwa cikin karya wuya tace.

"Hamma Saif me kake sayarwa ne to?."

ido ya zuba mata cikin rashin son yi musu k'arya ya girgiza mata kai alamar babu

da sauri Raliyya tace. 

"To me kakeyi?."

sai ya kuma juyo ya kalli Ummi ba tare daya amsawa Raliyya ba, 

cikin sanyi take ce mishi. 

"To Babana me amfanin zuwan, kalli jiya da yau duk baka wuni damu ka tafi har Gombe kuma kaje ba wani abu kakeyi ba ai gwara ka hak'ura ko?."

murmushin k'arfin hali yayi kana ya fara rubutu a k'asa.

"Ummi wai har kin karaya ne?   To ki aro jarumta ki yafa ai komai a hankali yake zuwa,

ai mai nema baya fushi, yoh su masu shagunan da kansu wata rana zasu bud'e ko asi basuyiba kuma haka bazaisa gobe su k'i zuwaba, kedai kiyi ta min addu'a in sha Allah, Allah bazai hanani abin yiba."

sai ya kuma kalli Rahma dasu Raihana yace.

"kuyi tamin addu'a in sha Allah dukkan tsanani tare yake da sauk'i."

cikin samun k'warin guiwa, sukayi mishi addu'a.


Bayan yaga sun saki Randi sunata hirane sai ya mik'e yad'auki bokiti ya debi ruwa a randa kana shiga d'anshi wanda da shida Nuruddeen ne, 

farar jallabiyarshi ya d'auka da boxer inshi kana ya fito hannunshi rik'e da kondon wonkanshi ban d'aki ya nufa yaje ya shiga wonka.

Ya jima kafin ya fito daga cikin d'an madaidacin bayan gidan nasu da aka lailayeshi da fulo d'in siminti, 

shaddan na can gefe kana wurin wonkan anyishi da mazaunin siminti da kuma inda zaka ajiye sawunka. 


A hankali yake tafi bisa dukkan alamu baison kasa ya bud'e mishi sawune, 

d'akin nashi ya shiga, 

inda yake gyare tsab sai k'amshin turare yakeyi wanda ishaq ne ke saya musu tare, 

ko ina a kimtse kodan babu tarkece sosaine,

 leda carpet ne a malale a tsakiyar d'akin wanda sai Shek'i yakeyi alamun ya wadatu da tsabta sai katifarshi shimfid'e a gefe wanda yasha gyara sai pillows biyu a 

gefen katifar.

can daga k'asa kuma wata yar madaidaciyar durowa ce, 

inda gefe d'aya ya jera kayayyakinshi dake wonke a goge, sai d'aya side in kuma littafanshi ne a jere daga sama har k'asa kama dana boko na islamiya dana allonsu wanda wasu tun na kakansu ne, sai wani dogon madubi dake lik'e a jikin ginin daga sama har zuwa k'asa dan zaka iya kallon tsawonka duk ta cikin madubin

sai wani dan abun aje takalma kana sai fankar k'asa da kuma wani d'an k'aramin randar tabo da sai naso yakeyi alamun ruwan ciki da sanyi 

sai butarshi a gefe kana can gefen durowar kuma sallayanshi ne ke shimfid'e. 

Mai ya shafa sannan ya fito tsakar gidan tuni Hayatuddeen ya dawo har yayi bacci hakama su Faruq.


Gefen Umminshi ya zauna tare da tonk'oshe sawunshi abincin da Rahma ta ajiye mishi ya jawo,

bud'ewa yayi sai ya kuma yi murmushi ganin tuk'ek'k'en tuwan shinkafa da miyar busasshen zogale wanda yasha kifi, gyada, attaruhu, da albasa, wanda aka had'esu da kifi, 

kana ga wake dasu kayan d'and'ano

miyar sai k'amshi take, Allah ya sani Saifuddeen nason miyar zogale shiyasa Umminshi ke yawan yin miyar in dai tanada halin yinta da yake miyar tanada cin kud'i.

ledan ruwa d'aya ya d'auka tare da b'ulawa kana ya wonke hannunshi ya fara ci,

ita kuwa Ummi ido ta zuba mishi tare da cewa.

"Yayanka Adnan yazo ya sallameni d'azu wai zai tafi karatu har Zaria."

kanshi ya d'an jinjina alamar Ayyah, 

sai ya kuma yi mata alamun Allah ya kaishi lfy.

Amin Amin tace, 

bayan ya d'an ci abincin ne ya wonke hannunshi Raihana ta kwashe kwanukan kana ta dawo sukaci gaba da hira.

Suna nan a zaune Bappa Ali da Aunty Nina ma suka shigo yi mishi barka da dawowa nan sukayi ta hira. 


Washe gari da sassafe Rahma ta hura wuta tayi d'umame kamar yadda suka saba, 

da sauri ta d'auko pillet ganin Saifuddeen ya fito cikin shirin tafiya, 

yau k'ananun kaya yasa wanda sukayi masifar yi mishi kyau blue Jeans ne a jikinshi sai bak'ar riga mai farin rubutu a jiki, 

kanshi ba hula hakan ba k'aramin haskashi yayiba, 

yana shiga d'akin Umminsu tana binshi a baya, 

bisa kujerarta irin zauna kaci doya nan ne ya zauna, 

ita kuwa Rahma mik'o mishi fillet d'in tayi kana ta jawo kolban man shanun da suke sawa in sunyi d'umame, 

bud'ewa tayi tare da tsiyaya mishi kana ta mik'e ta koma kitchen robar dakekken yajin borkono ta d'auko sannan ta dawo barbad'a mishi tayi, 

sannan ta d'auki kofi ta nufi d'akinshi ruwa ta d'ebo mishi a wannan randar tashi, 

sannan ta kawo mishi tare da cewa. 

"Kaci kafin ku tafi."

kai ya gyad'a mata kana ya kalli Umminshi dake shirya Hayatuddeen yanata zumbura baki, murmushi yayi tare da jawo hannun Hayatuddeen yana mishi tambaya irin tasu ta kurame ya tambayeshi me ya sashi fushin.

Bakin ya kuma turawa kana ya rab'a jikin Saifyddeen d'in tare da cewa. 

"Hamma Saif ba Adda Rahma bace tayi d'umame kua tasan ni bana cin d'umame hakama Faruq da Adda Raliyya."

murmushi yayi kana ya jawoshi ya ajiyeshi gefenshi, 

a hankali yasa cokalin da Rahma ta mik'i mishi ya gutsuri gayan kana ya dandalo miyar da taketa k'amshin man shanu,

bakin Hayatuddeen ya kai, 

tura baki yayi tare kwabe fuska kana yace.

"Na k'os. "

bai k'arisa mgnar  tashiba yayi shiru, 

jin ya sa mishi loman a bakinshi, lumshe ido yayi tare da fara sarrafa abincin, 

saida ya had'iye kana ya bud'e idanunshi tare da cewa. 

"Dad'i wlh miyar tayi dad'i Faruq zo kaci."

Ummi kam da Raihana dake shirya Faruq tuni dariya sukeyi, shima Saifuddeen dariya yakeyi har saida dimples nashi suka lotse sosai kana fararen hak'oranshi suka baiyana  manyan idanunshi ya lumshe tare daci gaba da basu abincin a baki, 

aifa sukaci sukayi nak, sannan suka tafi makaranta, 

ita kuwa Raihana da sauri ta fita tace.

"Adda Rahma ki samishi wani abincin su Faruq sun cinye wannan,

harda santinsu."

dariya sukayi kana Rahma ta samishi wani yana cikin cine Salisu ya shigo nan sukaci tare kafin suka fita suka tafi.



Yauma kamar kullum Saifuddeen wuni yayi yana yawo da bulayi a kasuwa, 

sai da magrib tayi ya fito, kana yayi salla kafin Salisu yazo ya d'aukeshi yau ma fura da nono yasha da zasu tafi.


Haka dai Saifuddeen yayi ta fama yawo da wahala a cikin kasuwar Gombe har tsawon kwana bakwai, 

to a ranan ne kuma Salisu ya basu balance ensu kamar yadda sukayi duk sati zaike basu dubu biyar.


 Koda ya karbi kud'in Bappa Ali ya kaiwa su, 

shi kuwa Bappa Ali k'in amsarsu yayi yace ya kaiwa Ummi kud'in zasu samu abinda zasuke sarrafa cefenen abincin.

da yake har yanzu sunada sauran abincin da baban Arabi ya kawo musu.


Shi kuwa Saifuddeen sai ya zare dubu biyu ya bawa bappan nashi, amman sam yak'i karb'a acewarsa ai da yanada hali shine ya kamata ya basu,

to dai ganin Saifuddeen ya b'ata rai ya sashi amsar 1k yasanya al'barka.

Shiko yaje ya bawa Ummi dubu uku sannan ya d'auki dubu d'aya.

Ummi kam sai sanya mishi al'barka takeyi.


Washe gari kamar kullum suka shirya suka tafi cikin. Gombe a inda ya saba sauk'eshi yau ma nan ya sauk'eshin, bayan Salisun ya tafi shi kuma Saifuddeen sai ya d'anyi tattaki zuwa bakin mashigar kasuwar, addu'a yayi kamar kullum kana ya shiga da k'afar dama, 

yauma bakin shagunan yayi tabi har kusa k'arfe shad'aya lokacin rana ta tsala zafi ya fara, 

sai ya nufi layin masu robobi, 

yana zuwa shagon wani bayerbe sai ya tsaya, 

bokatin kand'e tsirara ya saya wanda wasu ke cemai ganta sarai, 

bayan sun gama ciniki cikin mgnar kurame ya bashi dubu d'ayannan, 

kana bayerben ya bashi canjinshi, 

daga nan ya nufi wani layin tafiya kad'an yayi sai gashi a wani babban shago da yake cike da d'ima-d'ima  firiji masu tsawo da masu fad'i. 


Yana zuwa d'aya daga cikin yaran shagon yace mishi. "Kana son ruwane?."

da sauri ya gyad'a mishi alamar eh. 

shi kuwa yaro bud'e wani k'aton firiji yayi kana ya juyo ya kalleshi, sannan yace.

"Leda nawa kake so?."

hannunshi ya d'ago kana ya had'a yatsunshi biyu yayi mishi alama da leda biyu yakeso.

cikin mmki yaro ya kalleshi kana ya kawo mishi leda biyun sannan yace mushi.

"Kai kurmane?."

murmushi Saifuddeen yayi kana ya gyad'a mishi kai tare da mik'a mishi d'ari biyun,

amsa yayi tare da bashi canjinshi kana yace. 

"Kuma naga kamar kana gane abinda nake fad'i ko?."

still kai ya gyad'a tare dasa lododin ruwan cikin bokatin daya saya d'in, 

a take botikin yayi sanyi sabida ruwan yanada tsananin sanyi wasu har sun fara yin k'ank'ara, 

shi kuwa yaron shagon ashirin ya kuma zarowa a al'jihunshi kana ya mik'a mishi tare da cewa.

"Gashi nayi maka ragin naira 10 cikin ko wanne leda akan yadda muke sararwa Allah ya baka sa'a inka k'arema kazo zan ajiye maka mai sanyi."

cikin murmushi Saifuddeen ya jujjuya mishi kai alamun baya son ragin, kana ya juya ya nuna mishi sauran yaran ya mishi alamun da sai dai in suma duk za'ayi musu ragin,

cikin sauk'e numfashi yaro yace.

"To sadaka na baka."

fuska ya had'e kana ya tsuguna gefe tare da rubuta mishi.

"Bara nazo makane da zakace sadaka ka bani? in sadaka kakeson badawa kaje gidan marayu da gajiyayyu, ni karka kashe min zuciya, 

ka dai ajemin mai sanyi in wannan ya k'are zan kuma zuwa."

hannu yaron ya bashi sukayi musabaha lokacin daya karanta rubutun kana yace.

"To kayi hak'uri abokina sai ka dawo d'in."

kai ya jinjina kana ya juya hannunshi rik'e da botikin. 

ya fara bin layi-layi yana yawo, 

amman babu wanda yace mishi kawo, 

har ruwan ya fara rage sanyi. 

cikin gajiya ya dawo bakin shagon masu kayan kitchen inda ya huta jiyan nan, inda ya zauna jiyan yauma nan ya zauna ya tasa batikin a gabanshi.

yaron jiyan ne ya kula dashi cikin fara'a yace.

"Balarabe yauma ka zone?."

cikin gajiya ya lumshe mishi idanu alamar eh,

shi kuwa yaron shagon cikin karantar yanayinshi yace. 

"To yau ma hutawa kazo yine ko zaka sayi abune?."

da ido ya nuna mishi botikin pure water enshin,

cikin sauri ya zaro ido tare da cewa. 

"Wai kai dama tallan ruwa kakeyi ne?".

Kai ya gyad'a mishi tare gyara zamanshi,

cikin sanyi yace.

"To wai kai kurmane naga jiyama har ka tafi body language kakeyi min."

still sai ya d'aga mishi gira duka biyu alamun eh shi kurmane.

da sauri yaron ya kalli alajin shagon cikin tausayawa yace. 

"Abba kalli wai wannan Balaraben kurmane kuma wai ruwa yake saidawa."

sai ya kuma kalli Saifuddeen tare da yin rau-rau kamar idanunshi zasu zubda hawaye, 

ganin haka da sauri Saifuddeen ya jujjuya mishi kai sannan yasa hannunshi bisa idanunshi alamun kar yayi kuka.

still shima wanda ya kira da Abba sai ya zuba musu ido tare da cewa. 

"To Hisham kafi ubangijin daya halicceshi a haka sonshi ne? 

kada kayi kuka kasa mishi rauni, 

ai ita Nakasa ba kasawa bace,

bare wannan mai nagartane Kaga dai jiya kun dad'e tare amman duk bamu gane kurma bane kuma kaga yana gane duk abinda muke cewa. 

So shi bai sa nakasar jikinsa ta zamar mishi na zuciya ba."

Jin haka sai Hisham ya sharshe hawayenshi kana yayi murmushi tare da bawa Saifuddeen hannu yace. 

"Daga yau kai aboki nane."

shima Saifuddeen murmushi yayi, 

shi kuwa Alhaji Ibrahim al'barka ya samusu.

Sai ya kuma kalli costumers insu da suke cike da shagon inda d'aya daga cikinsu ta kalli botikin ruwa tare da cewa. 

"Yauwa mai ruwa bani biyu, wlh tun d'azu nakeji k'ishin kamar zai karni."

gane abinda tace yasa Saifuddeen d'auko guda biyu ya mik'a mata, 

amsa tayi tare da bashi ashirin d'in, 

shi kuwa Alhaji Ibrahim cikin iya kula da bak'inshi yace.

"A a Hajia bar kud'in."

sai ya kuma kalli Saifudddeen tare da cewa. 

"Basu ruwan kowa ya d'auki yadda zai isheshi."

ai nan matan nan kowa ta d'auka wasu bibbiyu wasu d'addaya wasuma cikin  hand bags nasu suke ajiye ruwan,

tuni sun d'auke yafi rabi. 

lissafi akayi don lokacin ne forko-forkon da pure water ya tashi daga d'aya biyar ya koma d'aya goma, 

to nanfa had'a lissafi inda kud'inshi ya kama d'ari da hamtsin. 

aifa sai yaji k'arfin guiwa ya mik'e yabi layin masu saida gonjo wanda kusan a rana suke, 

cikin k'udurar ubangiji ya saida ruwan tsab, 

ba tare da yin k'asa a guiwaba yaje ya kuma saro leda biyu, 

nan sai ya fito bakin kasuwa nanfa 'yan acab'a suka rink'a saya wani a take yake shanye leda biyu wani har leda uku ya saya bar masu sayan d'ad'd'aya,

kana masu taxi ma wasu sai su sayi lada hud'u su aje cikin yar durowar motar nasu. 

Cikin awa d'aya wannan leda biyun suka k'are, 

ai da sauri ya kuma komawa ganin azahar tayi sai ya amso leda d'aya, 

kafin kace kobo ya k'are dan masuyin Al'walene sukayi ta kiranshi suna saya,

ganin saura d'aya sai yayi Al'wala dashi ganin a layin shagonsu Jabeer yake sai yaje ya ajiye botikin a barandar shagunsun gefen gadajen jarirai, 

sahun salla ya shiga, 

bayan an idarne ya yi addu'o'inshi sannan yaje d'aukan botikin nashi, Jabeer na ganinshi yace. 

"Aboki balarabe dama har yanzu kana k'asar tamu ne?."

hararan wasa Saifuddeen ya cilla mishi dan ya gaya mishi shi bafullatanine ba balarabeba, so da yake Jabeer yanada far-far da jama da wasa da dariya sai yace shi dai yasan sai in satoshi akayi daga saudia.

botikin ya d'auka kana ya d'an harari Jabeer tare da tsuke fuska irin na abokai sannan ya bashi hannu.

da sauri Jabeer ya kamo hannunshi tare da cewa. 

"Yoh ai dole ma in baka hannu ko zan samu ka rab'a min farinka da laushin hannunka."

dariya yaran shagon sukayi baki d'aya, 

kana sai ogansun yace.

"Gashi dai duk muna inuwa fanka na kad'awa muci abinda mukeso, shi kuma gararamba kawai yake a kasuwa amman in ka ganshi sai kace daga fadar masarautar saudia ya fito."

cikin had'e fuska Saifuddeen ya zaro biron dake aljihun rigar Jabeer kana ya fara rubutu a tafin hannunshi yana gamawa ya nunawa ogan nasu tafin hannun nashi, 

kusan a tare suka lek'o da idanunsu bisa tafin hannunshi cikin mmki suke karanta rubutun da yayi da fillanci. 

"Oga ba gararamba nakeyiba fa inada sa'a ta nima ba yawon banza nake a kasuwarba pure water nike saidawa."

cikin mmki suka kalli juna tare da had'a baki wurin cewa. 

"Ikon Allah kunga wlh da gaskene fa bafillacene."

shi kuwa ogan nasu murmushi yayi tare da cewa.

"Eh gskyarka ba gararamba kakeyiba ai shi mai sana'a ba matsiyaci ba, 

yanzu je ka kawo mana ruwan dan yanzu zamuci abinci."

aifa da jin haka ya juya ya fita su kuwa sai Al'ajabi sukeyi, 

yanzu dai sun tabbatar shi kurmane kuma bafillatanine kana yana gane abinda ake fad'i in yana ganin bakin mutun.


Leda biyu ya kuma sarowa cikin sa'a kafinma ya isa wurinsu rabin ledane ya rage, 

nan suka d'auka to ganin bai ishesu bane sai ya kuma komawa ya dauko leda biyu. 

kai tsaye wurinsu ya nufa

nan suka k'ara guda uku. 

sun bashi kud'inshi ya juya zai tafi kenan sai yaga wannan dottijon mai keke wanda suka tab'a had'u a shagonsu Hisham kusan tsawon sati d'aya daya gabata kenan, 

still yauma kamar ranar dottijon ya kalleshi tare da mik'o mishi banduran leda guda hud'u irin kitika-kitikan ledojin da in an sayi koda katifan jarirai zai iya shiga ciki kai hatta gadon jariran zai iya shiga cikin ledan, 

kana in zaka sai setin kayan sanyi dana abin goyo dasu rigunan yara dasu setin mayukansu da takalma duk leda d'aya zata iya d'aukansu dan irin manyan ledodi bak'ak'ennan ne, 

sai kuma masu binsu sai masu zane bak'i da yellow nan, 

cikin alamun gajiya dottijon yace. 

"Yauwa yarona dan Allah mik'a musu."

da sauri ya ajiye botikin nashi  kana ya amshi ledodin ya juya ya mik'awa Jabeer dake kusa dashi, 

sai kuma ya kalli ogan nasu ganin yanayiwa dottijon mgna.

"Yauwa Baba bello ya a bamu ledodin na dubu hud'u dan na dubu ukun basa isanmu sabida yanzu iyayen yara sun fara sayayyan kayan sallan yaransu ga masu haihuwa nan nata zuwa ga yan mata da samari masu sayan kayan aure."

murmushi dottijon yayi kana yace. 

"Masha Allah ai haka mukeso domin cini kinku shine namu, 

domin sai kunyi ciniki da muyi tunda mu duk kasuwa abin mune k'arshen saya dole sai an gama sayyaya ake tuna sayan leda."

Jabber ne ya murmusa tare da cewa. 

"Gashi kuma kasuwar taku da yawan al'barka take duk mai saida abu dole sai ya sai naku."

murmushi sukayi baki d'aya kana Alhaji Adamu ya mik'owa Saifuddeen 4k d'in sannan shi kuma ya mik'awa dottijon amsa yayi tare da sasu a aljihu sannan ya kalli Saifuddeen da kyau kana yace. 

"Ngd matuk'a yarona Allah ya maka al'barka."

Amin Amin duk suka amsa harda Saifuddeen daya amsa a zuciya,

Jabeer kuwa cikin tsokana yace.

"Kai Baba bello wannan fa balarabene."

ba tare da mmkiba Dottijon yace. 

"Yoh ai ba musu in akace hakanma."

Tahir ne dake gefe ya d'an bugi k'eyan Jabeer kana ya kalli Dottijon yace. 

"K'aryafa yakeyi maka baba bello shi ba fulatanine kawai dai kurmane."

da sauri Baba bello ya kuma kallonsa cikin tausayawa yace. 

"Allah sarki bawan Allah dama ance ko wani d'an adam tara yake bai cika gomba, wato kai kuma nan tawayar ka take."

sai ya kuma kalli Saifuddeen da kyau sai ya sauk'o bisa keken nashi. 

hannunshi yasa ya jawo wuyan Saifuddeen yadda zai iya ganin tsakiyar kanshi ido ya zura mishi tsawon 38 minutes shi kuwa Saifuddeen shiru kawai yayi ya bashi kai d'in, 

bayan ya gama dubawa yace. 

"Masha Allah lallai kam wannan kan naka zai d'auki nauyin abu da yawa, 

domin magergerar gashi tushe ukune a kanka wanda ba kowa Allah ke yiwa wannan halittarba."

shiru sukayi yayinda shi kuwa Dottijon ya kalli Alhaji Adamu tare da hawa kekenshi kana yace. 

"Akwai al'khairi cikin yin mak'otaka dashi."

daga nan yaja kekenshi ya tafi, 

shi kuwa Saifuddeen d'aukan botikinshi yayi tare da bin bayanshi, 

yana ganinshi ya nufi shagon masu d'inka hijabannan da alamun suma a wurinshi suke sayan leda. Har zaibi bayanshi sai kuma yaga ana kiranshi a shagon alhaji ishaq haka yasa ya nufi can. 

Pure water suka sassaya bayan sun bashi kud'in ya juyo kenan sai yaga Dottijon nan tuni ya bar wurin, 

to sai kawai yaci ga da zageye da ruwan, 

amman sai cinikin yayi d'ib tun bayan azahar ya d'aukosu amman har la'asar basu k'areba, 

to saida aka kira sallan la'asarne sai kuma akayi ta saya ana al'wala nan ya samu wannan leda biyun suka k'are. 

To koda aka idar da salla ya gaji sai ya koma layin shagon ba mishkila ya zauna ya zuba musu idanu yana ganin yadda aketa seye da sayarwa yana kallon yadda suke ink'anta awunsu. 

Ya d'an jima a wurin sai biyar dai-dai ya mik'e a ranshi yake cewa.

"Uhmm Saif tashi kaje ko leda d'aya ka samu ka saida kafin magrib ai yafi zaman mutuwar jiki da zuciyan."

daga nan yaje ya k'aro leda d'aya, 

to kuma lokacin rana tayi sanyi ba ciniki sosai, 

ya jima yana yawo kafin ya samu aka sayi gwara shida na arba'in kenan daga nan yaita zagayawa, 

tuni ya gaji dan yau kusan wuni yayi bisa sawunshi, 

saida magrib ta gabatone akayi ta saya nan ya saida kab sai gwara d'aya da ya bari na al'walanshi. Bayan yayi alwalan ne ya bawa Jabeer botikin ya ajiye mishi a shagonsu, 

sannan ya fito bakin gate d'in fita kasuwar yana lissafin bag nawa ya saida a cikin ranshi yace. 

"Alhamdulillahi leda goma cib na saida, ya rabbil izzati kayiwa wannan kasuwa tawa al'barka ya Allah ka jib'anci lamurana ka fad'ad'amin hanyar samu in samu damar tallafawa k'annena marayuwa da mahaifiyata da yayata da marayun yaranta, 

bayan anyi sallan magrib d'inne ya dawo inda Salisu zaizo ya sameshi yana ko zuwa Salisu na isa, 

yauma kamar jiya shi dai fura da nono yasha shi kuwa Salisu ya sai nama yaci.

daga nan sukayi sallan isha kafin suka kama hanyar Dukku. 


Bayan sun isa wonka yayi ya canza kaya kana yazo yaci abinci, 

sannan ya fita woje sugar ya seyo da madara da Lipton sai biredi d'aya. 

kafin ya dawo duk sunyi bacci sai Ummi da Rahma.

Rahma ya mik'awa ledan kana ya zauna gefen Ummi data zuba mishi ido, 

cikin kula tace. 

"To kuma d'an dubu d'aya daka amsa d'inne zaka kasheshi a kanmu? buk'atunka zakayi dashi ba namuba ai dubu ukun nan zasuyi min sati ina cefene kullum d'aribiyar zata isheni cefenen dere da rana, tunda munada gari da shinkafa harda sauran taliya da mai da manja."

mik'e sawunshi yayi kana ya fara rubutu a k'asa yana bata lbrin ai ya fara sana'ar saida ruwa kuma Alhamdulillahi sana'ar tana gudu dan ya samu ribar 700 a wunin yau kawai.

Cikin tausayawa Ummi tace. 

"To Babana ka dai nuna kai sana'ar tayi maka, amman ni tausayinka nikeji kaje kayita wuni a rana kana yawo da robar ruwa, amman Allah ya baka sa'a yanzu asusu zan saya zaka rink'a tara kudin in ka samu jari dai ka fara wata sana'ar kabar wannan."

cikin girmamawa da shak'uwa da tsantsar biyayya ya gyad'a mata kai tare da fara rubutu a k'asa yace. 

"To Ummi na yadda kikeso haka za'ayi."

sai ya kuma kalli Hayatuddeen dake konce yayi  pillow da cinyar Ummi ture kanshi yayi kad'an kana ya zame ya konta tare dasa kanshi gefen na Hayatuddeen da nufin wai zasuyi hira.

Amman ina tsananin gajiyar yawon daya wuni yanayi ne yasa tuni yayi bacci.

ganin baccin zai nisane yasa Rahma sa hannu ta d'an mari kumatunshi a hankali ya bud'e ido,

sai ya kuma kalli Ummi dake shafa suman kanshi  da alamun bacci a idanunta.

cikin sanyi ya mik'e kana ya musu saida safe sannan ya kamo hannun Hayatuddeen da nufin suje d'akinshi su fara kwana tare amman sai k'ara mak'ale Ummi yakeyi hakan yasa ya barshi, yaje ya shiga kana suma suka shiga. 


Still yauma kamar jiya cikin ikon Allah ya saida leda goma kamar jiya.

Koda ya koma ya samu tuni Ummi ta sai asusu ta zura mishi d'aribar din jiya dan ya sai musu kayan tea na d'ari da biredin d'ari kana ya bata sauran d'aribar d'in duk cikin ribarshi 700 d'in jiyan,

kana jarinshi kuma na nan. To Alhamdulillahi yauma haka ya samu kamar na jiya, 

toh sai ya bawa Ummi duka kud'in tasa 500 a asusu 200 kuma ta d'auka ta ajiye dan 'yan buk'atunsu irinsu omo ko kud'in break d'insu Hayatuddeen da Faruq 

haka dai lokaci yaita shud'ewa.


Duk randa Salisu ya basu kud'in balance kuma zai bawa bappa Ali 1k kana ya damk'awa Ummi 4k d'in. 



Alhamdulillahi rayuwafa ta fara juyawa kasuwa na tafiya tuni Saifuddeen ya saba da mutane da dama,

wani lokacin har leda 14 yake saidawa inda yake samun riba kusan 900,

sosai yayi abokai sa'anninshi  manyan mutane kuma na son mgnanshi sabida yanada dad'in zama ga tsabta da girmama na gaba dashi.

Abu gaba-gaba yanzu harda robobin Faro, yake sara dasu Fanta,  Coca-Cola,  molt etc. Wanda yawanci matasa shi kan seya.


Yanzu ya saba da wahalar da yawon da ranar saidai ya d'anyi duhu farinshi ya disashe sabida rana da yake shiga. 

Yana yawan had'uwa da Dottijon nan baba bello, mafi akasari shike mik'awa mutane leda su bashi kud'i ya bawa baba bello, 

Alhamdulillahi yanzu littafi da biro yake yawo dasu a aljihu duk mgnar da kai mishi zai baka amsa, 

wasu da dama dan suga rubutunshi suke son Magna dashi sabida Allah ya mishi baiwar iya rubutu in yayi tamkar na'urace tayi.

da yawa da Balarabe suke kiranshi wasu kuma suce Saifuddeen balarabe.


Azumi nata gaba towa dan yanzu baifi 8 days ya rage Ramadan ba, 

Yayinda dukkan Al'ummar musulmai keta shirye-shiryen azumi.

kuma zuwa yanzu kusan tsawon kwana 46 da kafa asusun Saifuddeen. 

To ga azumi yana zuwa gaba d'aya ya rasa sana'ar da zai kama dan yasan cikin azumi cinikin ruwa bazaiyi guduba  tunda duk musulmai baki a rufe yake. 

Yana dai ta nazarin abin yi amman har zuwa azumi saura kwana uku bai tsaida sana'ar da zaiba da fari yayi niyar ko zai koma saida dabino dasu kwakwane sai ya kuma ga sana'ar yawoce kuma ga azumi so yasan zai wahala, 

a haka dai yau kam yayi niyar yin shawara da abokinshi Jabeer ko Hisham, duk da yaso ace da is'haq zai shawarar to is'haq kuma yanzu ya fi kwana 36 da tafiya Abuja wurin yayanshi Rabi'u kuma acan zaiyi azumi dan shida Ummarsu ne suka tafi, 

dan bayan ya fara zuwa kasuwar da sati d'aya ne yaje gidansu Is'haq sai ya samu ranar sukayi sammakon tafiya Abuja.



Yau tunda yaje yaketa sintirin saida ruwanshi dasu Fantan har sai bayan la'asar ya je shagonsu Hisham da niyan zai tattauna dashi sai ya samu tuni ya tafi gida ya kai cefenen dare. 

haka yasa ya wuce shagonsu Jabeer yana zuwa suka zauna dan lokacin mata sun d'an tsagaita, 

rubutu yayi na neman shawarar sana'ar da zai fara saida ya gama rubutawa kana ya mik'awa Jabeer takardar dai-dai lokacin daya karb'a dai-dai lokacin kuma baba Bello ya iso wannan dottijon. 

karantawa Jabber yayi kana ya kalli Saifuddeen da yake mik'o mishi banduran ledodin daya amsa a hannun Dottijon cikin yanayinshi na wasa da dariya yace. 

"Yoh balarabe ga sana'ar da zakayi a hannunka ai kawai ka fara saida leda, gashi dama Baba bello bai saida leda a Ramadan kaga sai ka karb'eshi bayan salla in an dawo sai ka bashi sana'arshi kai ka koma pure waternka ko?."

Ido suka zuba mishi baki d'aya, 

shi kuwa ba tare daya bi ta kan kallon da duk suke mishiba ya matso kusa da Dottijon cikin nitsuwa yace. 

"Kana ji ko baba Bello  shi Balarabe ruwa yake sedawa da kayan zak'i irin namu na yara, 

to kuma kaga ga Ramadan yana zuwa to duk abin saidawa in dai na cine cinikinshi ya mutu da rana sai dai in darene, 

to kaga ita kuma kasuwa da rana takeci, 

shi kuma d'an dukkune kullum zuwa yake da safe bayan sallan isha yake komawa, 

toh shine yaketa nazarin wani abu zai fara saidawa cikin azumin, 

da yayi zaton zaike saida dabino da kwakwa to gsky itana sana'ar yawace kuma kada yaje garin talla ya tsalli dabino ya afa a baki."

Ya k'arishe mgnar cikin tsokana da wasa, 

k'eyarshi Saifuddeen ya bugi tare zare mishi irin yadda akewa yara masu surutu, 

dariya sukayi baki d'aya  ganin yadda Jabeer ya tura baki tare da cewa. 

"To nayi shiru."

shi kuwa ogansu Jabeer gyara zama yayi tare da cewa.

"Baba Bello bananma da wuri zaka shiga itikafin ne?."

cikin kauda zancen Dottijon yace.

"Waya ce da kai itikafi nake shiga, 

kawai dai ina ajiye kasuwancin ne da ramadan sabida tsufa yazo kuma azumi na wahaldani."

Murmushi kawai Alhaji Adamu yayi sabida yasa Baba Bello itikafi yake shiga shi kuma yana b'oyewa sabida gudun riya, 

shiyasa yake ce musu hutun Ramadan kawai yakeyi. 

shiko Dottijon cikin kulla ya kalli Saifuddeen kana murya a tausashe yace. 

"Yaro na zaka iya yawon bin shago layi-layi kana raba musu ledodi, suna yi maka biyan bashin daddawan k'auye?."

murmushi yayi tare da gyad'a mishi kai alamar zai iya.

Shiko Dottijon sauk'owa yayi daga kan keken nashi kana ya zauna kusa da Saifuddeen cikin tattausan lafazi yace.

"Kullum in azumi yayi ina barin kasuwa duk costomomina sai dai suyi ta kame-kamen sayan leda wurin wasu, 

anayin salla kuma da kwana biyu zan dawo to duk masu kawo musu sai su bari inci gaba da kawo musu kamar kullum to amman tunda gashi bana Allah ya had'ani da kai, in dai ka amince kayi al'k'awarin rik'e amana to zan kaika wurin babban dilanmu da yake bamu talla bisa farashi mai sauk'i, 

zaike baka kaya ba tare da ka bashi ko asiba, 

sai kai kuma ka tallata ka d'ora ribarka, 

misali yau in ka kawo bazasu baka kud'iba sai gobe in ka kawo musu sai su baka kud'in na yau, 

na yau kuma sai ka kawo musu na gobe.

to wasu ba ruwansu kana kai musu zasu biyaka, 

wasu kuma dole sai goben, 

to anan amanar da nakeso ka rik'e zan kaika gaban dilanmu amatsayin kai jikanane dan in baisan wani nakaba bazai bakaba, 

in ya amince zai baka kuma zan had'aka da costomomina baki d'aya, nasan duk masu amana da gsky ne, suma kuma zan basu amanarka kada su ganka bakaji su cuceka, nasan zaka iya kasuwancin kam tunda kayi karatu zaku rink'ayin komai a rubuce."

cikin lumshe ido Saifuddeen ya had'e hannunsu wuri d'aya kana ya jinjina mishi sannan ya zaro biro ya fara rubutu a tafin hannunshi saida ya gama kana ya nunawa Jabeer nan Jabeer ya fara karanta abinda ya rubutan. 

"In sha Allah Baba bazan kasance mara gsky ba a cikin had'akarmu, 

nayi alk'awarin rik'oda gsky da amana bazan kunyataka ba, 

ga Oga Adamu da abokina Jabeer da sauran maikatan shagon nan su zama shaida, Allah kuma ya bamu sa'a ngd matuk'a Allah ya k'ara lfy da wadata."

Murmushi sukayi baki d'aya, 

daga nan Dottijon nan yayi gaba Saifuddeen na binshi a baya har shagon babban dilansu na leda, 

nan ya gabatar dashi ga Alhaji Babayo, 

ba wani dogon bincike Alhaji Babayo ya aminta da Saifuddeen sabida ganin Baba Bello ne ya kawoshi Dottijon da sunfi shekaru 20  suna tare a harkar leda.

shi kuwa Baba Bello ya musu bayanin Saifuddeen kurmane amman yana gane duk abinda ake cewa in yana ganin bakin mutun.

an yarda tuni an rattaba sunan Saifuddeen a jerin sunayen masu amsar talla, 

yasa hannu shaidu sun saka hannu.

daga nan suka juya Baba Bello ya tasa Saifuddeen a gaba duk inda yasan yana kai ledodi saida ya nuna musu Saifuddeen yana ce musu jikanshi ne, kuma shi zai rink'a kawo musu Leda cikin azumi har sai bayan sallah shi zai dawo, 

to dama duk kostomominshi sun san da baya kawo musu leda cikin azumi to sai sukaji dad'in wannan ci gaban koda sukaje shagon Alhaji Ibrahim baban Hisham yaji dad'in abun sosai ya sanya albarka haka dai duk wunin wannan ranar kam sukayi shi ranar bag d'in pure water takwas kawai ya saida sai dai ya saida su Coca-Cola sosai.

Sun bari akan sai ana gobe azumi zai fara tallan ledan tunda ranar Baba Bello zayi zuwan k'arshe sai kuma bayan sallah.



Anayin sallan magrib Salisu yazo ya d'aukeshi kamar kullum, 

yau wurin mai shayi sukaje kwai aka soya musu da indomi kana sai ruwan tea, 

bayan sunci ne sukayi sallan isha, kana suka kama hanyar Dukku. 



Koda suka isa Saifuddeen na sauk'a Salisu ya zaro dubu biyar d'in balance ya mik'ashi,

amsa yayi kana ya zare 2k ya bashi yace yaje ya sayawa Mamanshi sugar da Lipton baiso karb'a amman dole ya amsa, 

shi kuwa Saifuddeen yana shiga gida kai tsaye d'akin Umminshi ya shiga inda ya sameta ita da Aunty Nina suna hirarsu.

Bayan sun gaisane ya mik'e tare da yiwa Ummi alamun bari yaje yayi wonka.

To tace mishi kana sukaci gaba da hira, 

shi kuwa solle jikinshi yayi suk'al kana ya shafa mai tare da fesa turare,

canza kaya yayi sannan ya nufi tsank'aya wurin Bappa Ali duk da yasan yau al'hamis ne ba karatu so ya kuma san canne wurin zaman Bappa Ali ko yaushe bayan sun gaisane ya mishi bayanin canjin sana'ar da zaiyi da tsarin kasuwancin    da dokokinshi, 

sosai Bappa Ali ya gamsu da hakan addu'a yayi da fatan al'khairi.

Koda ya tashi tafiya sai ya kwaso cinikinsa na yau duka da riban da jarin duk dubu 3 ne. 

sai ya kuma zaro da sauran dubu ukun balance d'in ya had'asu inda suka bashi dubu shida kenan. 

Cikin nitsuwa ya mik'awa bappa Ali. 

Cikin tsuke fuska da fad'a bappa Ali yace. 

"Me zanyi dasu?  shin ba nacema Ka dena bani kud'iba in dai ban bakaba to ai baici ka baniba, 

fatana Allah ya bud'a maka yadda zakayi kaci gaba da rik'e marayun k'annenka dani bappanku na gaza rik'ewa."

da sauri ya girgiza mishi kai kana ya rubuta mishi. 

"Dan Allah Bappa Ali ka amshi kud'innan in dai ba rainawa kayiba, meyasa kullum in na baka abu baka amsa, 

to in ban makaba waye zanyiwa kainefa uba a garemu ka sanya al'barka a lamarinmu in bani dashi zan baka ne?."

to ganin ranshi ya b'acine yasa Bappa Alin  amsar tare da samishi al'barka.


Har ya tashi sai ya kuma zauna ganin Bappa Alin ya rik'o hannunshi bayan ya zaunane yake shaida mishi wannan mutumin daya kad'e Nuruddeen ya kawo musu kayan azumin. 

Kama daga shinkafa, taliya, doya, Couscous, indomi, mai, manja, magi, gishiri, onga, kwai madara da Milo sugar Lipton, da kud'i 10k.

wani irin tsuke fuska Saifuddeen yayi tare had'e rai sai ya kuma yiwa bappa Ali alamun tambayar sun karb'ane?. 

kai bappa Ali ya gyad'a mishi alamar eh sun amshi kayan, 

cikin takaici ya...





                                By

                      *GARKUWAR FULANI*

8/


              *NAKASA BA KASAWA BACE*



                           *PAGE 5*



                                  NA

               *AYSHA ALIYU GARKUWA*


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇



 _Wannan shafi gaba ɗayanshi tukuicine da saudaukarwa ga Umar ibrahim Wambai, Allau rabbi ya baka lafiya!_


    Free page🤝🏻


A hankali ya koma ya zauna, rai a b'ace ya fara rubutu.

"Meyasa kuka karb'a ne? Bappa Ali wancan karonma da ya kawo saida nace muku kada ku amsa! 

ai tunda muka rasa Ya Nuruddeen mgna ta k'are munce mun yafe mishi to me sa zayi ta d'awainiya damu, ko yana zaton abinda yake mana zaisa mu manta tabon daya zama sanadin samuwarshi a ah'linmu ne?."

Gyara zama bappa Ali yayi kana ya fuskanceshi cikin sanyi yace. 

"Kana tuhumarshi kan shine ya kashe mana Seyo ne?."

da sauri ya girgiza kansa alamar a a.

Shiko Bappa Ali ido ya kuma zuba mishi tare da cewa. 

"To haushinsa kakeji ne? Kodai baka yafe mishi bane?  Ko baka yarda cewa k'addara bace da tsautsayine ya rufta mishi?."

cikin lumshe ido yake jujjuya kai,

sai kuma ya bud'e idanun nashi da tuni sunyi jazir dan tuno d'an uwanshi da k'unar da yakeji a ranshi.

murya a tausashe Bappa Ali yaci gaba da cemishi.

"Nima da Umminka k'in amsar kayan mukayi, 

koda aka shigar da kayan su Mudassir nasa suka fara fitar da kayan, 

ganin ana fidda kayanne ya sashi cewa aiyi mishi sallama dani, 

niko sai blnace ya shigo daga ciki sabida lokacin akwai yara a wojen suna karatu."

shiru Bappa Alin yayi tare da sharte guntayen hawayenshi kana yaci gaba da cewa. 

"Yana shigowa gaban Umminka dasu Rahma ya durk'usa duk da girmanshi da shekarunshi da arzik'inshi ga d'anshi Arabi wanda zai kai sa'an Seyoji yana ganin mahaifinshi ya rusuna a gabansu shima sai ya rusuna."

Cikin zubda hawaye Bappa Ali yaci gaba da cewa. 

"Suna durk'usawa sai Alhaji Gid'ad'o yayi ta zubda hawaye cikin rawan murya ya kalli Umminku dasu Rahma hawaye na zuba yace.

"Kuyi hak'uri ku gafarceni, nasan duk abinda zan muku bazaku tab'a farin ciki dashiba, 

nasan na cutar daku cuta mafi muni tunda na kashe muku Garkuwarku, 

wlh bawai dan in biyaku bane ko wani abu yasa nazo na kawo muku yan wannan kayan ba a a, 

sai dan nasan nine na kashe me ciyar daku kullum hankali na baya konciya in na tunaku saina rasa sukuni tunda na buge Nuruddeen dan Allah ku gafarceni ku dena k'in abinda nake kawo muku halal inkune tunda na kashe mai cidaku."

cikin rawar murya da zubda Hawaye Ummi tace.

"Ba kaine ka kasheshiba dan babu mai rayawa da kashewa sai Allah, nasan kwananshi ne ya k'are, 

amman in mun amshi kayan Saifuddeen zaiyi fad'a ranshi zai b'aci shiyasa bazamu amsaba."

da sauri Arabi yace.

"Dan Allah Ummi ku amsa ku bawa Saifuddeen hak'uri hankalin Abbana a tashe yake tunda ya buge Nuruddeen please Ummi ku amshi abincin nan wlh in baku amsaba zaiga kamar baku yafe mishi bane."

rumtse ido Bappa Ali yayi kana yaci gaba da cewa. 

"Jin haka yasa ni cewa ba komai mun yafe musu mun kuma gode Amman kada ya k'ara kawo mana wani abun. 

haka yasa sukaji dad'i sukayi ta godiya suka tafi suna k'ara bamu hak'uri.

To kaji yadda akayi dan haka ba laifin kowa bane fashe ni Aliyu in kuma  na maka laifi  sai in kwashi kayan in meda musu."

da sauri ya jujjuya kai kana ya rubuta mishi. 

"Kayi hak'uri bappa Ali, duk abinda kayi ya zauna."

to daga nan ya shaida mishi dama yau zai fasa asusunshi da niyar gobe in zai tafi yaje da kud'in ya sai musu kayan abinci mu samman cefenen ramadan da cin kud'i.

bayan ya karanta ne ya kalleshi cikin gwarin guiwa yace.

"Yanzu dai to kada ka fasa asusun ka bari sai azumi ya d'anyi nisa in yaso ka fasa kayi hidiman kayan sallah."

cikin gamsuwa ya jinjina kai tare da cewa. 

"Ba matsala hakan zanyi."

daga nan suka d'an tattauna shirye-shiryen Ramadan, 

nan Bappa Ali yake sanar mishi an gayyaceshi cewar zaiyi tafsir a masallacin Fada har zuwa saba'an watan ramadan d'in. 

nan kuma yace Saifuddeen d'in zaike fassarawa kurame kuma da hannu tunda da dare zaike yin tafsir d'in zai fara k'arfe 8 a tashi 9 nan dai suka gama tsara komai yadda zai tafi. 


Daga nan wurinshi kai tsaye woje ya fita wurin abokanshi Mudassir k'anin Ya Adnan sai Salisu da Saminu dan gidan sarkin Dukkun sai kuma Warisu, 

duk su lafiyayyune sai dai sun matuk'ar iya body language sabida abokanshi ne tun na yarinta, 

bakin titi sukaje suka zauna iska na kad'awa suna tsaka da hira Ahmad yazo d'an Goggo Dada cikin body language Saifuddeen yace mishi. 

"Kai a daren nan ka ratse wannan dajin naku, 

to ni dai bani raka."

sai ya kuma duggure kan Ahmad dake dariya tare da cewa. 

"Yaseen sai kun rakani, yo kewarkuce ai ta sani zuwa, 

tunda ka fara zuwa Gombe ka rage zuwa Shabewa Dada ma sai cekiyarka takeyi."

Sai ya kuma harari su Warisu da Saminu yace. 

"Su dama wad'annan al'barkacinka suke zuwa,

shine wai Dada tace ai dama saida karenka kake ganin karen wani, ba gashi yanzu tunda ya Seyo ya rasu bata kuma ganin abokanshi ba."

sai kuma yayi dariya kana yaci gaba da cewa. 

"Shine yanzu da zan fito nace to Dada bari inje in cekinta miki karnukan naki tunda kice saida karenka kake ganin karen wani."

dariya sukayi baki d'aya  kana suka kai mushi bugu,

Mudassir ne yace. 

"Hege Ahmad d'an iya juya mgna, 

ai hausace haka ba wai tana nufin mune karnukanba."

shi kuwa Saifuddeen mik'a yayi tare da lumshe ido kana ya amshi wayar Saminu rubutu yayi kana ya bawa Warisu karantawa ya farayi da d'an sauti. 

"Hege mai dogon k'afa yau zamuyi mgnaninka yaseen bazamu rakaka ba, 

dan ni baccima nikeji."

suna jin haka duk sukayi dariya. 

Nan dai suka zauna sukayi ta hira, 

daga bisanu dole suka raka Ahmad har shabewa suna tafe suna hirarsu ta abokai tamkar ba dareba. 


So koda suka dawo dare ya d'anyi nisa basu wani tsayawa ba kowa ya nufi gida. 


Shiko Saifuddeen yana shiga gida ya samu Umminshi da Rahma suna hira inda Rahma take goge mishi kayanshi data wonke mishi 

tsakiyarsu ya zauna ita Rahma tana k'asa ita ko Ummi tana kan kujera, 

haka yasa ya zauna k'asa kusa da Rahma sannan ya jingina kanshi kan cinyar Ummi wanda take rik'e da k'afafun Hayatuddeen tana yanke mishi farce. 

numfashi ya furzar kana ya d'ago ya kalli Umminshi dake shafa kanshi,

murmushi yayi kana ya lumshe ido tare da bud'esu ya zuba matasu alamun yana sauraronta

Cikin kula tace. 

"Yau Alhaji Gid'ad'o yazo."

ga mmakinta sai taga ya gyad'a mata kai kuma fuskarshi ba fushi,

sai ta kuma sa yar yatsarta manuniya ta shafa gashin girarshi ta kontar dashi kana tace. 

"Na k'i amsar kayan nida  bappanku, to kuma sai yayi ta kuka yana bamu hak'uri dole bappanka yace mu amshi kayan."

murmushi yayi kana ya gyada mata kai sannan ya amshi rezar hannunta ya juya ya fuskanceta da kyau kana ya kamo hannunta ya fara yanke mata farcen hannunta, 

saida ya yanke na yatsu biyu kana ya kalleta tare da dungule hannunshi ya mik'ar da babbar yatsarshi yayi alamun jinjina, 

sannan ya jujjuya mata kai alamun karta damu ba matsala. 

sai ya kalli Rahma ya lumshe ido ya d'aga hannu yasa bisa goshinta ya sharte mata zubafar data tsastsafo mata sabida zafin anyon.

 Murmushi tayi tare da zare bakin igiyar daga jikin kuros d'in, 

dan ta gama gugar nashi har ta goge uniforms d'insu Hayatuddeen da Faruq na boko da islamiya.

gyara zamanta tayi suna fuskantar juna, 

a hankali ya bud'e bakinshi kana ya had'a lips enshi da alamu furta.

"Sannu Addana ngd."

lumshe ido tayi tare da cewa. 

"Godiya kuma  a kan me?."

zuba musu ido Ummi tayi tana jin so da k'aunar yaran nata da tausayinsu na ratsa mata zuciya musamman Saifuddeen, 

hannu ta d'aura bisa kan Saifuddeen d'in, shafawa takeyi a hankali tare kallon yadda ya manna kanshi bisa cinyarta murya a tausashe tace. 

"Babana kayi shiru kamar ranka baiso mu amshi kayan bako?."

jujjuya mata kai yayi kana suka juyo suka kalli Rahma data shafa k'afarshi tare da jan 'yan yatsunsi biyu kana tace.

"Kada ranka ya b'aci muma bisa dole muka amsa bawan Allah nan har durk'usa mana yayi yana kuka yana bamu hak'uri, 

k'in amsar kayan zaisa yayi ta zaton ko bamu yafe mishi bane."

murmushi yayi tare da lumshe ido cikin kurma-kurma dayin body language ya had'a hannunshi duka biyu ya karkad'a kana ya shafa gemunshi tare da nuna musu kunnenshi alamun yace.

"Ba komifa na fahimta, ai Bappa Ali yamin bayani."

sai ya kuma kalli Ummi kana ya gyara zama sannan yayi mata bayanin canjin kasuwancin da zaiyi, 

haka nan Ummi ta tsinci kanta cikin farin ciki dan wannanma wata alamace dake nuna Saifuddeen inta yana tare da mutanen kirki nagari kuma wannan ya nuna mata kasuwa tasan da Saif d'inta. 

"Alhamdulillahi Babana Allah ya sanya al'khairi yasa ka fara harkar a sa'a rabbi yasa ka shiga da k'afar dama."

Amin Amin suka amsa shida Rahma, 

kana ya mata bayanin fasa asusunshi nanma tace. 

"Hakan yayi yadda bappankun yace haka zakayi, 

ka bari tukun kaga yadda kasuwar ledan take."

kai ya gyad'a mata kana sukaci gaba da hirarsu har zuwa 11:36 pm sannan sukayi saida safe, 

Rahma ta tafi d'akinsu ita dasu Raihana Ummi kuwa ita da Autanta da Faruq, 

shiko Saifuddeen d'akinshi ya tafi,

koda yaje buta ya d'auka al'wala yayi sannan yazo yayi nafilfili daga bisani ya fara karatun Qur'an  yayi kusan awa biyu sannan yayi addu'o'in da neman sa'a da nasara a kasuwancinsa ya rok'i Allah ya tsareshi da cin amana sannan daga bisani ya mik'e ya kashe wutan d'akin kana ya matso da fankanshi kusa da gadon tare da k'ara gudun fanka,

gefen katifar ya zauna tare da yin addu'o'in bacci qulhuwa 3 falaqi 3 nasi 3 sannan ayatul kursi'u 1 ya shafa sannan ya konta da hannun dama, 

a hankali ya gyara konciyarshi tare da yin mik'a ido ya lumshe yana mai mamakin Al'amarin halittarshi a ranshi yake cewa. 

"Anya kuwa ni lafiyeyye ne."

sai ya muka juya rigingine ya kuma yi mik'a still ba sauyi ajiyan zuciya yaja tare da barin abin a ranshi kana ya fara tasbihi dan ya samu bacci ya saceshi cikin k'ank'anin lokaci kuwa yayi bacci abunshi.


Washe gari kuwa kamar kullum da sassafe suka tafi gombe shida Salisu nan suka wuni kasuwancinsu, 

bayan sallan isha suka koma Dukku.


washe gari wanda ana gobe za'a d'au Azumi sabida ana zaton ganin wata yau,

wanda ranar ne kuma Baba bello zai sallami kasuwa sai kuma bayan salla.


Ranar sammako sukayi sosai shida Salisunshi k'arfe bakwai dai-dai na safe suka isa birnin bubayero,

bayan Salisu ya sauk'eshi sai ya tsallaka bakin tashar gombe line, 

ya fara d'aukan irin masu kai aike tasha da sanyin safiyan nan.


Shi kuwa Saifuddeen yazo dai-dai mashigar kenan yaga Jabeer ma, 

da sauri Jabeer ya iso gabanshi tare da bashi hannu cikin fara'a yace. 

"Tab Lallai wannan balaraben dukkun da himma kake wato in junin wani sammako kai a tafe ka kwanako?."

hannu yasa ya d'an bugi k'eyar Jabeer irin ya cika surutu nan.

shi kuwa Jabeer kama hannunshi yayi suka nufi cikin kasuwar da yanzu ake shirin bud'eta sai ya kuma kalli Saifuddeen tare da d'aga mishi gira kana yace.

"Ko dai kudin aure kake nema ne wannan iya sammako haka har ka rigamu mu yan cikin gari, 

nima dana fito yanzu yaseen Ya Adamu ne ya matsa wai inzo in kimtsa shagon yau zuwa jibi kayanmu zasu iso zamu fara baza hajar cinikin salla ne."

 murmushi ya d'anyi kana ya jinjina mishi hannu alamun mgninka ai.

suna isa shagon Jabeer ya bud'e sannan ya fara kikimtsa wurin, 

yayinda Saifuddeen ke taiyashi, 

tuni suka kimtsa shagon suka gyara komai yayi ras, 

kafin su gama tuni kasuwa ta fara cika duk masu shaguna sun firfito da kayayya kinsu

cikin yin mik'a alamun gajiya.

Jabeer ya kalleshi tare da cewa.

"Yauwa Balarabe jirani bari inzo."

kai ya gyad'a mishi kana ya konta bisa tattausan sallayan daya shimfid'a cikin shagon ga iskan fanka na kad'ashi ido ya lumshe tare da gyara kinciyarshi. 

Shi kuwa Jabeer yana fita bakin tashar ya nufa inda wasu masu saida abinci suke, 

soyayyan dankali da kwai, 

sai gasashiyar kaza ya sai musu kana ya shiga shagon gefen wurin ya saya musu Faro k'ananun roba guda biyu,  sai molt, 

kana ya juya rik'e da ledojin ya nufi cikin kasuwar.


Bayan ya isa ya tsallaka wani dandamali da akayi wanda yake shamaki tsakanin masu shago da masu sayan kaya,

kusa da Saifuddeen d'in ya zauna  bubbud'e musu takardun abincin yayi kana ya kalli Saifuddeen dake konce yanata tab'e baki cikin tsuke fuska yace. 

"Ka tashi muyi breakfast."

fuskar ya kuma ya mutsawa tare da jujjuya mishi alamun bazai ciba ya koshi, 

ido Jabeer ya tsura mishi domin tabbas yasan wannan d'abi'ace ta fulani yin fulaku wa kowama.

shi kuma Saifuddeen tashi zaune yayi ganin kamar ran Jabeer ya sosu sai ya d'auki ruwa kana ya b'alle marfin sannan ya d'an sha ruwan har kusan rabin robar,

a hankali yayi gyatsa kana ya ajiye goran ruwan sannan ya d'auki na molt,

ya fara k'ok'arin mik'ewa da sauri Jabeer ya rik'o hannunshi kana yace. 

"Meyasa ne kake min haka shin baka d'aukeni aboki bako bare in kai matsayin amini."

kai ya jujjuya mishi kana ya zaro bironshi tare da ballan takarda ya rubuta mishi. 

"Am so sorry my friend, wlh a k'oshe nake Ummi ta cika min ciki da d'umame yau da kanta taimin dan Adda Rahma taje gidan Goggo Dada can ta kwana, 

kana ni bana cin kaza, 

shiyasa,

 sannan dankalin kuma ba irin suyan da nake so bane akayi shiyasa bazanci ba, 

ai dani da kai yanzu mun zarta abokai mun zamma aminai,

ka fahimceni."

yana karantawa yace.

"To gaya min me Kakeso in sayo maka?."

amsar takardar ya kumayi ya juya bayanta kana ya rubuta mishi. 

"Am sorry Jabeer ba wai nak'i ci bane haka nan badan wani abu ba because inada wani banzai kyakk'yani wanda ni kaina yana damuna ba ko ina nake iya cin abinciba.

Kaga zansha molt baka tab'a lura daniba haka nake wuni bani cin komai wani lokacin sai dai in had'a molt da pic milk sai insha."

tabbas Jabeer yasan hakane so duk da haka baiji dad'in rashin cin nashiba, 

amman dole ya hak'ura dan Saifuddeen da wuya yaci, shi kuwa Saifuddeen tsallaka madandalin yayi kana ya nufi shagonsu Hisham wanda yau cikansa ya zarta na kullum, 

bayan sun gaisane yaje ya amshi botikinshi sabida lokacin wasu nata karya kumallonsu so zasu buk'aci ruwa da kayan zak'i. 

cikin sa'a kuwa a safiyar  yayi ciniki kusan na 3,500 

sha d'aya dai-dai ya kuma komawa da nufin k'aro ruwan sai ya samu Baba Bello ya iso yazo wurin yana nemanshi, 

haka yasa ya ajiye botikinshi anan shagon su Kabir kana suka juya suka nufi dilan ledodin. 


Bayan an gama warewa Baba Bello adadin da yake amsa kullum, 

sai aka rubuta sunan Saifuddeen dasa hannun shi dana baba Bello kana akasa kud'in kayan da akabashi ganin yawan kayanne da yawan kud'in yasa Saifuddeen yiwa Dottijon alamun.

"Kayan basuyi yawaba kuwa?."

Murmushi Baba Bello yayi kana ya fara loda ledodin a k'aton kwalin dake bayan kekenshi, 

saida ya loda kusan rabin ledodin kana ya hau kekenshi sannan ya kalli Saifuddeen cikin yin kasa da murya yace. 

"Kada Ka damu ai zan had'aka da customers d'ina duka, 

kaga duka-duka kayan dubu hamsin nake amsa dama,

nakan sa na ishirin da biyar, 

in fita inje in rarraba in ya k'are inzo in kuma kwasar rabin. 

Yanzu muje duk zamu rabashi sai mu dawo mu debi sauran."

cikin gamsuwa ya gyad'a kai kana yabi bayanshi. 

tafiya kad'an suka isa shagon wani mai saida takalma bayan sun gaisa Dottijon nan ya d'ebo banduran leda takwai, 

ya bawa Saifuddeen kana ya juyo ya kalli mai shagon tare da cewa. 

"Alhaji bala ga Jikana ya fara kawo muku daga yau, 

insha Allah kullum zaike kawo muku kamar yadda nakeyi daku sai in Allah ya kaimu bayan salla."

wanda aka kira da alhaji bala kuwa cikin kula ya irgo dubu 4 ya bawa Dottijon kana yace. 

"To baba Bello Allah ya kaimu bayan sallan, Allah ya sadamu da al'khairi."

Amin Amin, yace kana suka shige shago na gaba nanma ya basu kaya suka bashi kud'i. 

haka dai sukayi tayi har suka gama wanda suka kwason kana suka koma suka kwaso sauran kashi d'ayan. 

Kai tsaye shagonsu Jabeer sukaje inda sukace a basu na dubu 5, nanfa Saifuddeen ya basu suka bashi kudin na jiya ya bawa baba bello, 

Jabeer nata musu tsiya wai.

"Tab ku dai kam kun more dan ko bamu sayarba ku dai kun sayar."

dariya sukayi kana sukaci gaba dan inda sabo sun saba da shek'iyancin Jabeer.

daga nan suka zagaya har layin masu kayan kitchen nanma shagonsu Hisham suka saya, 

sai kuma suka mik'e babban layi har kan shagunan ba miskila, 

cikin sa'a suka sameshi shida kanshi bayan baba bello ya mishi bayanin Saifuddeen ya gamsu kana yace. 

"To Baba Bello Allah ya taimaka mana, 

yanzu ni daga gobe ya rink'a kawo min na 15k dan shaguna na babbar kasuwama za'a rink'a kai musu da na kasuwar mata da shagunan cikin unguwanni dan naku  ledodinku suna da kyau, muna jin dad'insu."

shiko Saifuddeen murmushi yakeyi yana ganin darajar mutumin sabida duk inda yaranshi sukayi awu sai ya amshi kwanon awun ya kamfata ya zuba a ledan wanda aka gamawa awun,

yara sai godiya sukeyi.

daga nan suka ci gaba da rabawa har layin masu kayan kolliya.

Wasu na 5k wasu 4k wasu 3k wasuma na 1k wasu ma na 500 yayinda wasu 6k ko 7k kowa dai dai-dai cinikaiyarshi yake karb'a

Koda suka gama sai suka tafi can dilan nasu, 

a hankali baba Bello yaja hannunshi suka d'an koma gefe, 

kana ya fito da kudin da suka tattaro ya had'a kansu, 

sannan ya irga inda ya samu kud'in dubu hamsin da shida ne da d'ari uku. 

Gyara zama yayi kana ya ware dubu hamtsin sannan ya kira d'aya daga cikin yaran shagon ya bashi kudin ya irga, 

sannan ya d'auko wani babban littafi yaja gud a kan sunan baba bellon tare da rubuta bama binshi ko asi, 

sai bayan salla in ya dawo. 

Sai kuma yasa sunan Saifuddeen k'asan na Baba bello tare da rubuta .

"Munada kayan dubu hamsin a wurinshi."

sai ya kuma basu littafin sukasa hannu shima yasa hannu daga nan ya koma bakin aikinshi. 

Su kuwa su Saifuddeen cikin nitsuwa Baba bello ya kalleshi tare da bashi 2k sannan yace.

"Kaga wannan ribanane na jiya, 

ladan yawon da nasha yi cikin rana, 

kuma kaima zaka iya samun haka a kullum koma fiye da hakan cikin duk kayan dubu goma ina samun ribar dubu d'aya da dari biyu, 

wani lokacin in naga kasuwa bata gudu duk bandir din dubu goma sai inbi dubu d'aya rak kaga kenan duk fakitin dubu d'aya ina bin nera d'ari d'aya kacal ne, 

kuma Alhamdulillahi a cinikin da nikeyi dubu hamsin kullum ina samun dubu shida ko biyar in na rage farashi na, 

ta iya yiwuwa kai ka samu fiye da haka tunda kai yanzu ana hidiman cinikaiyan salla, 

dole masu shaguna suna k'ara sayan leda, 

kaga misali yanzu ba mishkila daga sayan na dubu 5 yanzu yace gobe na dubu 15 zaka kai mishi, 

kaga Alhamdulillahi kasuwa ta fara a sa'a, dan haka kai gobe kayan dubu 60 zaka amsa, 

yanzu zan gayawa shi Alhajin in dai ka buk'aci k'ari to ayi maka."

cikin jin dad'i da tsananin mamaki Saifuddeen yake kallonshi domin jin k'udurar ubangiji. 

Mutun nawa ke raina kasuwar leda rashin sanin al'barkan dake cikinta ne yasa haka da yawa raina riba ke wahal da matasanmu da ganin sunfi k'arfin sana'a kaza sai kaza ko a a su sunyi karatu sunfii k'arfin talla a kasuwa sai zaman office.

cikin kurmanci yayiwa baba bello godiya tare fatan al'khairi.

Shi kuwa Baba bello 2k d'in ya kuma bashi tare da cewa. 

"Amshi wannan ka sayawa Mamanka sugar ka kai mata taci al'barkacin sana'ata."

Da sauri ya girgiza kanshi alamun a a bazai amsaba ai ya gama mishi komai ma daya bashi aron sana'arshi ba tare daya mishi hasadan abinda zai samuba. 

Shiko Dottijon cikin girma da isa yace.

"Bana son musu a tsakaninmu da mahaifinka ne ya baka zaka k'i amsane?

niko da ace Allah yasa inada d'a da na bashi ai bazaik'i amsaba sai daima yace in k'ara mishi dan haka maza karb'i kud'innan."

cikin tsananin ganin darajar Dottijon yasa hannu ya amshi 2k  d'in kana ya mishi godiya. 

Shi kuwa Baba bello, 

ubangidan nasu yayiwa bayanin kan ba mmki Saifuddeen ya nemi k'arin leda. 

cikin mutuntaka ogan nasu yace.

"Ba matsala aimu haka mukeso."

daga nan ya sallamesu, kana ya yafito Saifuddeen sannan ya hau kekenshi, 

yana janta a hankali kana Saifuddeen na binshi a baya har sukaje bakin titi, 

cikin kula ya bawa Saifuddeen hannu da sauri Saifuddeen ya bashi  nashi hannun sai kuma ya zuba mishi ido jin ya rik'e mishi hannun cikin bada shawara yace. 

"Ita sana'a bata yiwa mutun yawa, 

kaga shi leda cikin awa uku duk zaka gama kaiwa kostomominka ka kuma tattara kud'i har ka biya kana ka zare ribarka.

To in dai ka gama da wuri to zakafa iya saida ruwanka d'in in kaga alamun zai saidu, 

in kuma Kaga bazai saiduba tofa kada ka zauna banza ka samu sana'ar da  zaka had'a dana ledan kafin bayan sallan ka komawa ruwan."

Cikin gamsuwa ya jinjina kai alamun in sha Allah hakan zaiyi. 

shi kuwa Dottijon ya jima yana mishi nasiha da rik'o da amana da tattali, 

sannan daga bisani sukayi sallama shi dottijon ya kama hanyar gidanshi kana shi kuma Saifuddeen ya koma cikin kasuwa ya d'auki bitikinshi ya kuma saran ruwa. 

Koda Jabeer ya ganshi yai ta mishi tsiya wai shine sana'a goma mgnin baccin safe. 


Haka dai ranarma ya wuni saida kayan sanyinshi, 

saida akayi sallan isha suka kama hanyar dukku wanda tuni anga wotan Ramadan, 

gaba d'aya al'ummar annabi gobe za'a tashi da azumi. 




Kamar yadda ko wanne gida ke shirin d'aukan azumi hakama gidansu Saifuddeen domin. 

bayan yayi wonkane yaje ya samu Umminshi da Adda Rahma da Raihana,

nan ya gayawa Umminshi lamarin kasuwar sai dai bai gaya mata ribar da Dottijon nan ya gwada mishiba don baison ya fad'ad'a burinshi kan ribar gudun kada ya shigar da son zuciya. 

Rahma ya kalla wacce ta kawo mishi abinci cikin sanyi tace.

"Yauwa Saifuddeen wannan k'awar Raliyya Salma sun zo d'azu tace wai in gaisheka in ka dawo." 

ta k'arishe mgnar tana murmushi da son ganin fuskarshi dan tasan sam Saifuddeen baya shiri da Salma 

Shi kuwa yi yayi kamar bai gantaba bare ya gane me take fad'i dama in baya son mgna da mutun haka yakeyi. 

Ummi kuwa ido ta zuba musu tana murmushi, 

abincin ya d'an tsakura kasancewar shi baida yawan cin abinci.

saida ya d'an gyara zamanshi kana ya kalli Hayatuddeen dake gefenshi tare da mishi tambayar azumi nawa zaiyi?."

cikin d'oki yace. 

"30 zanyi ko d'aya bazan shaba."

dariya Ummi tayi jin Raliyya na cewa.

"Ko kuma ko d'aya bazakayi ba ko?."

cikin dariya Rahma tace.

"Ai kam saidai hakan."

shi kuwa Saifuddeen hannun Faruq yaja tare da cemishi shi kuwa nawa zaiyi. 

yatsunshi uku na tsakiya ya d'aga alamun zaiyi uku da yake duk sun iya kurmanci.

Raihana kuma tana tsakiyar gida tanata kiciniyar tafasa tea da yin miyar asuba, 

miyar dege-dege take musu dan Ummi dubu d'aya ta bada  Hayatuddeen ya sayo musu hanta da jan nama, 

tofa shine aka gyarashi tayi miyar ganyen albasa da yaji kayan miya dana d'an-d'an dan aji dad'in yin sahur.

koda ta gama tafasa tea d'in da tasa citta da kanumfari, 

sai ta d'ura a filas kana miyar kuma ta barshi a tukunyar sai ta dorashi saman kanta sannan taja kitchen d'in ta rufe sai da asuban Rahma zata k'arisa aikin.

tana rufe kitchen d'in taje sukaci gaba da hira, 

nan Saifuddeen ya bawa Ummi shawarar a hana Aunty Nina girki dan tana laulayin wani cikin, 

to shiyasa yake son a hanata girki su had'a tukunyar,

sosai Ummi taji dad'in haka dan itama taso hakan sabida tasan Bappa Ali mutum ne mai kawaici  tana sane cutar mijintane ya medasu basu da wasu yawan kadarori. 

koda Saifuddeen ya tashi daga nan k'ofan Bappa Alin ya nufa inda ya samu Aunty Nina tana kiciniyar hura wuta a murhun gawayi yayinda shi kuma bappa Ali, 

yake ruggume da Qur'an  alamun zai fita masallaci. 

nan ya gaya mishi shawarar da suka yanke shida Umminshi. 

bawan Allah Bappa Ali sai yake jin kunyar wai shi ya kamata yaci dasu ya gaza sai kuma shima su ciyar dashi, 

da fari kamar bazai yardaba to dole dai ya yarda dan Saifuddeen ya kafa ya tsare haka ya hak'uri,

sannan suka kama zance tafsir d'in da zasu fara gobe ya jaddawa Saifuddeen ya shirya dashi za'ake zuwa bayan sun gama mgnane ya fita wurin abokanshi. 



Salisu ya samu da Mudasir sai Warisu ganin Saminu baya nanne yasa suka raja'a gidan sarki gidansu Saminun kenan, 

a d'akin saminu suka yada zongo sunata hira, 

har dai dare ya fara nisa kafin suka fito, 

Warisu ya shiga gidansu shima Mudassir yayi hanyar gidansu.

Saifuddeen kuma da Salisu tare suke tafiya dan kusan katangar gidansu d'aya ne. 

suna isa bakin masallaci Saifuddeen ya zaro biro kana yayi rubutu a jikin takardar daya b'alla. 

"Yauwa Salisu dama inaso in gaya maka an rage balance enka ka rink'a bada dubu biyu duk sati,

sai mu rink'a tasowa biyar dai-dai na yamma kafin a kira magrib kuma mun iso dukku kaga zamuyi bud'a baki a gida kuma zamu dena tafiyan dare, 

in kuma gari ya waye in yaso ana fitowa masallaci mu tafi tunda ba batun jiran karyawa."

cikin tsananin jin dad'i Salisu ya ruggumeshi tare da cewa. 

"Kai Alhamdulillahi wlh ka kawo shawara mai kyau, amman dubu biyu yayi kad'an gsky zan dai bada 4k tunda du-du du dai awa d'aya da rabine aka rage. 

Ngd matuk'a Allah bar zumunci da k'auna my friend."

cikin sanin mutuncin juna ya kuma ce mishi. 

"No kai dai kabar 2k d'in ai kaima kanada buk'atun kanka dana iyayenmu."

cikin sanin ya kamata Salisu yace. 

"To naji na kuma gode, amman gsky 3k zanke badawa kada ka cemin komai."

jin haka yasa Saifuddeen rubuta.

"To Allah ya musu al'barka."

da haka sukayi sallama, 


Koda ya shiga gida tuni su Ummi sunyi bacci acewarsu kada suyi dogon hira su zo su makara.


Shima hakance a wurinshi shiyasa yanayin wonka yayi al'wala yazo yayi konciyarshi. 



2:00 Am Ummi ta farka kamar yadda Ummi takeyi ko wanne lokaci in dai cikin Ramadan ne, 

kana ta bud'e k'ofa ta fito tsakar gida yayinda iska mai sanyi ke kad'awa, babbar taburma ta shimfid'a kana ta fito da wani d'an madaidaicin cainis carpet amman irin na da fa,

ta shimfid'a bisa taburmar kana ta ajiye hijabinta da carbinta da Qur'an sai lantanta mai wadaceccen haske. 

al'wala tayi kana kana taje baki k'ofar d'akinsu Rahma kira d'aya ana biyu Rahma ta amsa.

Itako Ummi tana jin Rahma ta amsa ta koma bisa taburmar ta fara nafila, 

Rahma kuwa tana tashi ta tada Raihana Raliyya.

sun jima kafin suka tashi, 

suna fitowa duk sukayi al'wala kamar yadda aka sabar musu tun basu kai hakaba,

kana sukazo ko wacce tayi iya nafilar da zata iya daga bisani suka fara karatun Qur'an.

Yayinda tuni Saifuddeen ma ya tashi yazo ya tashi Hayatuddeen sun je bakin k'ofar d'akinshi bisa k'aramar taburma ya shimfid'a musu sallaya,

suka fara nafila  bayan sun zauna sun fara tilawa ne ba jimawa Hayatuddeen ya fara gyangyad'i yana rab'awa jikin Hamma Saifuddeen d'in nashi tuni bacci ya sureshi shiko Saifuddeen gyara mishi jinginar yayi kana yaci gaba da tilawarshi. 


3:20 Am Rahma tayi addu'a tare da shafawa kana ta mik'e ta cire hijabinta ta ninke ta ajiye gefe sannan ta shiga kitchen ruwan zafi ta d'ora bayan ya tafasa ne ta d'an zuba man gyad'a cikinshi kana ta d'ebo couscous dai-dai misali tazo ta zuba kana ta meda marfin ta rufe, 

sanan ta harhad'a kofuna tare da pilet da cokula, 

ta fitar taje ta jera bisa babbar taburmar, 

kana ta dawo ta d'auki filas d'in duka biyu babban da k'aramin, 

sannan ta koma kitchen d'in, 

bud'e tukunyar tayi tare da duba couscous d'in yayi lugub yadda akeso kuma yayi wasar-wasar bai kwab'e ba amfanin zuba man gyad'an kenan, 

sauk'e tukunyar tayi ta ajeshi gefe sannan ta mik'e ta sauk'o dana miyar ta d'orashi kan rushin. 

sai ta kuma sauk'o da kuloli guda biyu d'an madaidaci shi ta fara zubawa saida ta cikashi yadda zai iya isar mutun ukuma, 

kana ta kwashe sauran duka a babbar kulan, 

sannan ta kwashi kulolin ta kaisu bisa taburmar, 

tana dawowa ta bud'e tukunyar miyar da sai bol-bol yakeyi sai mai da tsokokin da suka yiwa miyar k'awanya, 

tukunyar ta d'auka baki d'aya kana ta d'auki d'an k'aramin kulan miyar, 

tana fitowa ta zauna gefen taburmar kana ta kalli Raihana tare da cewa.

"Na mance ban d'auko biredin nan ba, 

tashi ki kawoshi yana d'akin Ummi."

to tace tare da mik'ewa ta nufi d'akin. 

Ita kuwa Rahma miyar ta saka a k'aramar kulan tare da tsokoki kusan shida kana tasa k'ashi biyu, 

sannan ta d'auki k'aramin filas d'in nan ta had'a da kulolin kana ta amshi biredi d'aya a hannun Raihana da ta iso da su a hannunta, 

cikin nitsuwarta tace. 

"Yauwa Raihana bari in kaiwa su Bappa Ali nasu ke kuma ki sa mana ki sawa d'an uwana."  da yake haka take kiran Saifuddeen wasu lokutan 

ba musu Raihana ta tsuguna tare da fara zuba musu, 

shi kuwa Saifuddeen da sauri ya mik'e yaje ya amshi abincinsu bappa Alin kana yayi mata nunin da ta koma taci abinci bari shi ya kai musu. 

To tace mishi kana ta bashi kulolin, 

sannan ita kuma ta koma ta zauna kofi ta d'auka tea ta had'a mishi mai kauri ta san ba wani abinci mai yawa zai iya ciba, 

bayan ta had'a mishi ne sai ta kuma d'iba mishi couscous d'in tare da sa mushi miyar hantar a d'an k'aramin side  soup tuni Raihana kuma ta gama had'a musu nasu a tire, 

ta ajewa kowa kofin tea a gabanshi.

bisimillah sukayi tare da addu'a sannan suka fara sahur d'in.

Shi kuwa Saifuddeen koda ya dawo tuni k'arfe hud'u ta kusa gefen Umminshi ya zauna tare da d'aukan kofin tea d'in da Rahma ta had'a mishi ya fara sha, 

ido ya lumshe jin k'amshin citta da kananfari da masoro da ganyen na'a-na'a, yana sha yana lumshe ido ko dan dama shi yana son tea yana nan kamar buzu,

ita kuwa Ummi cikin kula tace.

"Babana kaci abincin mana kanata shan ruwan zafi."

ido ya zuba musu yadda suka had'u su duka sunaci a kwano d'aya sai ya tuna mishi da baya, wanda baushe ke cewa kowa ya tuna bara baiji dad'in banaba,

idon ya kuma bud'ewa yana mai tunanin dah

ita Ummi taci da yaranta mata shida Nuruddeen kuma tare sukeci da Abbansu da bappa Ali koda last year haka sukeyi, 

sai gashi bana kuna ba Abba ba Nuruddeen bappa Alinma da yake raye baizoba sabida rashin d'an uwanshi, 

oh mutuwa wato dama haka abin yake ta rabaka da macecce ta rabaka da rayeyye, 

gashi Hayatuddeen yanata baccinsa. 

itako Ummi kamar ta gane me yake tunawa sai ta d'an gyara zama sannan ta zare cokalin cikin abincinshi ta saka cikin tiren da sukeci tace. 

"To muci tare, kada kayi zurfin nazari gamu Allah ya barmaka mu gashi nanda bad'i kuma zakuyi taci da autana."

ganin ta tsareshi da ido ne kuma in baiciba bazata ji dad'iba yasa ya d'anci kad'an kana ya kuma amsar kofin tea d'in da Rahma take rik'e dashi tana sha kurb'a biyu yayi kana mik'a mata sannan ya mik'e da sauri. 

ruwan wonka ya d'iba sannan ya shiga d'akinshi ruwan randar sanyinshi ya d'ansha kana ya d'auko soson shi da makilin da burosh.

a nitse yayi wonkanshi yana fitowa ana kiran assalatu. 


Dama tuni su Ummi sun gama sahur d'insu har Raliyya ta tattare wurin. 

D'akinshi ya shiga kasan cewar yau jumma'a ace kuma azumine, 

shiyasa ya zaro wani tattausan yadi mai sauk'in kud'i fari k'al rigar anyi mata d'inkin zamani anyi d'an aiki da yellow zare,  bayan ya gama sa kayan sunyi d'as a jikinshi sai yasa hular zannabukar mai d'an surkin yellown zare sai takalma suma farare masu d'an ratsin yellow.

Sosai yayi wani irin baiyanennen kyau, 

wanda gani d'aya zakayi mishi kasan Allah ya masa cikar halitta da haiba, gaba d'aya alamun zarra da tsurar cikekken d'a namiji sunata baiyana a jikinshi tuni muryarshi tayi kauri alamun cikar balaga da d'an dad'ewa,

gwarabanshi suna ta hab'aka yayinda duk wani sashi na jin d'an adam dake iya fidda gashi, 

nashi sunata yabanya, 

hatta gefen kunnenshi yana ta nuna alamun tsirowar saje, 

hakan sharabanshi da singalalin hannunshi da k'irjinshi, 

tuni gashin girarshi ta zama d'aya daga cikin abinda ke Jan hankalin mutane ih zuwa ga kallonshi dan gashin girarshi har had'ewa suka bisa karan hancinsa,

hakama gashin idanunshi zar-zar dasu lips enshi kuwa jazir dasu ko yaushe kamar an shafa musu man baki zakaga suna shek'i sirarane sai dai sunada d'an fad'i da taushi dan ko d'an dannesu yayi da harshenshi sai kaga wani wurin ya lotso ya kuma yi fari,

yana kuma janye harshenshi zakaga ya koma janshi, 

yatsun hannunshi da sawunshi kuwa suma kansu abin ganine.


Tsayuwa  yayi gaban wannan dogon madubin hannunshi rik'e da turare, 

feffesawa yayi a jikinshi yadda bazaiji gafinshi a mak'oshinsa ba. 

carbi ya d'auka kana ya fita nan ya samu Raihana ta tada Hayatuddeen da Faruq sunyi al'wala,

shiyasa ya tasasu a gaba suka nufi masallacin k'ofar gidan nasu. 


Bayan an idar da salla su Hayatuddeen suka tafi gida shi kuma  sai ya d'an zauna yayi azkar saida ya gama sannan ya mik'e ya fita a harabar tsank'ayarsu ya samu Salisu na jiranshi. 

Dan haka sai yayi sauri-sauri ya shiga gida a tsakar gida ya samesu duk suna ninnike hijaban da sukayi salla dasu, 

Ummi kuwa har yanzu carbine a hannunta gefenta ya d'an rusuna kana ya motsa lips enshi a hankali alamun. "Ina kwana?."

"lfy lau Babana har zuku tafi ko?."

tace dashi cikin kula kai ya gyad'a mata alamun eh,

sai ya kuma gaida Adda Rahma kana su Raihana suka gaidashi,

Raliyya kuwa tuni ta har-had'a kwanun wonke-wonke tana wonkewa.

da sauri Ummi tace. 

"To Allah ya kiyaye hanya ya kaiku lfy ya dawo daku lfy." sabida jin Salisu nata danna mishi hon

Amin Amin suka amsa baki d'aya kana ya mik'e ya fita.


Suna isa gombe kamar kullum Salisu ya ajiyeshi kana yaja ya tafi ya fara aikinshi. 

Shi kuma cikin masallaci ya shiga, 

baccin da baibane ya dan fara fizgarshi haka yasa ya konta, 

cikin k'ank'anin lokaci yayi bacci. 

8:00 Am ya farka da sauri ya mik'e, 

ya fita harabar wurin ruwa ya saya yayi al'wala sannan yazo yayi walaha, 

daga nan ya nufi cikin kasuwa.


Yana shiga kai tsaye dilansu ya wuce yana zuwa ko yayi sa'a ba layi sosai tofa nan take aka bashi na 60k ganin bashi da wurin zubasu ne sai yace musu bari yazo, 

shagonsu Hisham yaje yace musu kwali yakeso nan take suka bashi yankekken kwalin Gas 

yana amsa yaje ya cika kwalin da lododin. 

Da shagon ba mishkila ya fara dan yafi kusa dashi kuma yasan me yawa zasu karb'a zasu rage mishi nauyi,

yana zuwa kuma ya samu shagon a cike mak'il da masu sayan abubuwa irin su Gero, kunu gyad'a kunun wake k'osai, waken awara. 

Rid'i, sugar, madara, acca, al,kama, masara, maiwa, shinkafa, dawa, fulawa,  da dai sauransu a k'alla yaran shagon sun kai goma amman still ga layin masu awu, 

d'aya daga cikin yaran shagon ne ya yafitoshi tare mik'o mishi 5k d'in jiyan kana yace.

"Alhaji yace yau na 15k zaka bamu ko?."

kai ya gyad'a mishi kana ya sunkuyo ya rink'a mik'o mushi faket-faket na ledodin hawa-hawa kamar dai yadda yaga Baba Bello ya basu jiya.

Yana basu ya rubuta kana ya bawa yaron shima yasa hannu, 

daga nan ya fara bin duk shagunan da  Dottijon ya nuna mishi, 

inda yasamu wasu basu firfitoba, 

sai ya wuce gaba, wasu a dawowa sai ya samu suna bud'e shagun nasu sai ya basu,

yana basu suna bashi kud'in na jiya, 

haka dai tuni kafin k'arfe sha d'aya ya gama rabawa,.

Cikin nitsuwa ya koma rumfar dilan nasu inda ya had'a lissafin kud'in ya samu dubu hamsin da shida ne ga 2k d'in da Baba Bella ya bashi jiya nan ya had'asu wuri d'aya 8k kenan.

wato fad'in farin cikin da Saifuddeen yayi a wannan lokacin bazai yuwuba.

Kawai sai yayi sujjada  ya godewa Allah gashi yau da ribarshi kusan 8k.

ai cikin aminci da farin ciki ya basu kud'insu 50k dai-dai kana aka d'auko littafi akayi alamar ya biya na jiya sai kuma na gobe 60k cikin tsananin farin ciki yasa kud'inshi a al'jihu kana ya bar shagon da zummar sai gobe.


Tuni kasuwa ta cika tayi tambul sabida yawanci akanzo da sanyin safiya koda maraice sabida yanayin azumi ba'a zuwa da tsakiyar rana. 


Bayan ya gama rabawanne 

sai ya kuma d'auko botikin pure water inshi ya saro leda d'aya, 

dan bin shawaran baba bello amman ina a gari na gombe garin musulmai zakayi yawa har ka gaji cikin kasuwar gombe da wuya kaga arne ba irin kasuwar Yolanmu ba, 

ita kasuwar gombe du musulmaine sai yerobawa da terawa kuma duk masallatane bana ce ba kirsoticiba amman gsky basu da yawa.

ganin wahalar banza zaisha sai ya rabawa Al'majirai ruwan.


Shagonsu Jabeer yaje wai ko su d'an tab'a hira amman ina sai ya samu shagon mak'il da mata ba ko hanyar wucewa, 

dole ya wuce shagonsu Hisham still nanma shagon cike yake da mata,

gun bayarben nan mai robobi yaje canma kazalika, 

koda ya koma shagonsu Kabir mai ruwa kuma sai ya sumu sun rufe wai saida yamma zasu dawo su bud'e.

gefen shagon nasu ya zauna ya lumshe ido yana nazarin to sana'ar me zaiyi, 

ya dad'e yana tunani a ranshi yake cewa.

"Alhamdulillahi Allah ban raina sana'ar daka baniba, 

Allah kaine mai badawa ka kuma k'arawa mutun ya rabbil izzati ka nunamin wata sana'ar da zanyi mana kar in wuni zaman kare a karofi."

yana gama fad'in haka a ranshi sai ya bud'e idanunshi yana bud'esu ko sai kan wani mai saida omo irinsu Good mama kilin Zep viva sabulun kamaru da dai sauransu.

da sauri ya mik'e yaje ga saurayin mai amalanken kana ya yagi takarda ya rubuta mishi cewa, 

shima yana son saida su omon ya nuna mishi inda zai sara, 

cikin gatsali da zoleya saurayin yace.

"Hahaha kanada amalanken ne, ko akai zaka d'ora kana da kud'in jarin ne?."

rubuta mishi amsa yayi cewa a kwali zasu bashi zai d'aura a kai. 

cikin zolaya ya nuna mishi shagon da suke sari, 

aiko yana zuwa sai yaga suma shagon ya kawo musu leda koda ya rubuta wa mai shagon dalilinshi ba b'ata lokaci ya bashi su Omo kan ya saida ya d'auki ribarshi ya kawo mishi uwar kud'i. 


Kamar wasa ya aza kwalin su omo yana yawo koro-koro sak'o da luggu, 

amman ina ko asi bai saidaba. 

har azahar har yayi niyar in yayi salla zai maida musu sai ya kuma fasa, 

koda akayi salla sai yaci gaba da zagaye har ya shiga layin yan badaru, 

nan aka fara kiranshi ana saya kad'an-kad'an sai gashi kafin la'asar ya saida stab yana had'a kudin yaga dubu hud'u ne kuma kayan 3,500 aka bashi kenan yaci ribar d'ari biyar a ciki dan harda irin manyan nan na 500.

koda ya kai kud'in sai ya kuma amsar wani cikin ikon Allah shima ya saida.

aifa ranar da Jabeer ya ganshi dasu Omo da sabulu ya mishi tsiya wai ko dai aure yake bid'ane.


K'arfe biyar saura ya maida kwalin oman da sauran nan ya samu ribar 200 lissafin ribarshi yau dubu takwas kenan, 

hamdala yayi kana ya duba agogon hannunshi ganin biyar saura kwata, 

sai ya nufi gaban wani mai dabino, 

mudu d'aya ya saya, kana ya fito bakin kasuwar inda yaga mai kankana dasu lemu da ayaba kankana ya saya babba da k'ari kana ya sayi lemun d'ari uku, 

duk dai dubu d'aya ya kashe tsakanin dabino da lemu da ayaba, 

ganin saura 7 minutes buyer ta cika sai ya gangara gefen masu nama/naman 1k ya saya,

sannan ya sayi su tattasai, albasa, attaruhu, karas, kabeji. da dai sauransu a ta k'aice dai 3k ya kashe kana sannan ya adana 5kbda zummar in ya koma zaiyi musu asusunsu da ban ribar omo d'ari takwai d'innan kuma ya barsu a aljihu ko ya rink'a jin kud'i a jikinshi. biyar dai-da Salisu yazo suka tafi. 


Alhamdulillahi sun isa Dukku rana tanayin mudun kuyangi alamun ta kusa fad'uwa.

inda ya samu tuni Rahma sarkin aiki ita da Raihana sun gama komai, 

inda sukayi kunun gyad'a mai kyau, da tea daya sha kayan k'amshi sai soyayyan doya daya sha kwai dasu albasa da citta kanumfari onga,

sai kuma tea wanda akayi dan Saifuddeen da Bappa Ali, 

kana sai jolof d'in taliya da yasha kifi,

sannan sai biredi da aka soya da kwai sai kuma su dabinon da kankana da ayaba da lemun daya kawosu yanzu. 

da sauri Raihana ta amshi ledodin kana ta mik'awa Adda Rahma ledan naman dasu tattasan, 

ita kuma ta d'ebo ruwa a roba tare da d'an tarfa gijishi kana tazo wonkesu ayaban da kankanan da lemun kafin ta yankasu kana dabinonma ta wonke,

shi kuwa tuni ya shiga wonka yana fitowa yasa Hayatuddeen yaje ya kira mishi Salisu, 

kafin ya shafa mai ya fito har sun taho tare, 

kana su Ummi sun gama shirya komai Raliyya ta kaiwa Aunty Nina nata sannan na bappa Ali da ban, 

tuni ita kuma Rahma ta had'awa Saifuddeen nashi da abokinshi,

su kuwa duk sunyi al'wala kowa na zaune rik'e da carbi, 

yayinda Raliyya ke rik'e da dabino a hannu alamun kiran salla kawai take jira Raihana kuma ruwa tafi bege, 

ana kiran salla duk sukayi addu'a kana aka fara bud'a baki, 

da sauri Ummi ta rik'e hannun Raihana kana tace. 

"Ki fara da dabino kafin kisha ruwa."

da sauri ta amshi dabinon.


Su kuwa Saifuddeen da Salisu dabinon sukaci bayan sunyi addu'a sannan suka sha kankanar da Adda Rahma tayi mata mayafi da garin madara, 

saida sukayi gyatsa kana suka mik'e jin ana shirin tada ik'ama a massalacin nasu yasa suka kuskure baki kana suka tafi dan dama duk sunyi al'wala suna fita harbar matsallacin ana...!








                                By

                   *GARKUWAR FULANI*



      *NAKASA BA KASAWA BACE*


                      *PAGE 6*



                                  NA

               *AYSHA ALIYU GARKUWA*


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇



```Hukuncin Allah fans one ku na musamman ne a gareni fatana, Allah ya bar zumunci da ƙauna a tsakaninmu```


_Littafinga na kuɗine nairanki ɗari uku kacal ya biya miki buƙata ,turo katin mtn na 300 ta wannan number 09097853276 ko transfer ta 0005388578 jaiz bank Aisha Garkuwa Aliyu, sai ka/ki turo shaidar biyanki ta wannan number 09097853276_

 

free page


 Suna isa harabar masallacin suka d'an k'ara sauri sabida tuni liman ya kabbarta. 

Bayan anyi salla an idar duk sai kowa ya firfito dan a d'anci wani abu, wasu kuma zafine yasa suka fito sabida babu wuta kuma basu da gen kana in mutun ya wuni da azumi tofa lokacin da kasha ruwa zufa na iya keto maka.


To hakane ta kasance dasu d'in. 

da yawa cikin gida suka shisshiga, 

haka ma su Saifuddeen da Salisu tare da Mudassir da suka samu a masallacin, 

suna shiga Ummi suka gaida kana suka wuce d'akin Saifuddeen inda suna shiga wuta ta dawo,

dan haka cikin farin ciki suka zauna Rahma da kanta ta kawo musu abincin suma tea sukace zasu sha dan haka ta kawo musu kana ta aika musu ruwan sanyi soyayyan doya da kwan sukaci suna korawa da ruwan tea da yaketa k'amshi,

daga nan kuma cikinsu ya cika, 

suna cikin hira sukaji an kira sallan isha, 

kusan a tare suka mik'e sukaje suka sabunta al'wala a tsakar gidan kana suka nufi woje suna fita suka shiga sahu, bayan anyi isha sai kuma aka fara yin sallan asham. 

Suma su Ummi suka sabunta al'wala kana suka fara sallan.


Bayan an idar duk an fiffito ne sai Bappa Ali yacewa Saifuddeen zasufa tafi masallacin fada yanzu zasu fara tafsir d'in dan takwas ta kusa. 

Mudassir ne ya kalllesu kana yace, 

"Bari inje in cewa Ummi tafa ajiye mana jolof d'innan in mun taso tabsir zamuci dan ni in nazo konciya sai naci abinci."

dariya sukayi mishi kana Warisu dake bayansu yace. 

"Anya ko kai bafullatanine Mudassir dan gaskiya fulani basu da yawanci."

Ahmad ne da shima yanzu ya iso yace. 

"Yoh ai shi iyamburi ne bakaga yadda yayi k'atoba."

shiko Mudassir shafa cikinsa  yayi tare da cewa. 

"Me yafi raina."

dariya suka kumayi sai Saifuddeen da yaketa murmushi sai kuma Warisu ya kalli Saifuddeen kana ya kallesu tare da cewa.

"Ni ai ko dan kar inyi k'aton ciki zan yiwa kaina k'aidar ci abinci, 

wlh da nasan yadda zanyi in koma kamar Saifuddeen da nayi na koma, 

kalleshi komai na jikinshi dai-dai da shekarunsa, 

shiyasa yake tafiya da kenshi da k'uruciyarshi,

wlh koda namiji d'an uwanshi in ya ganshi sai ya kuma kallonshi in ka ganshi kamar balarabe ko ba indiye."

cikin kauda kai Saifuddeen ya d'an shafa suman kanshi tare da mishi alamar. 

"Kai Warisu in naga wani kyau."

daga nan suka shiga cikin gida bisa taburmar da Ummi ke zaune suka zauna bayan sun gaisane ta kallesu cikin kula tace.

"Ya kamata ace iwar haka kuna wurin tafsir, ku rage yawon dare kun san wannan wata ta musammance ga musulmai."

mik'ewa sukayi da sauri sai kuma Mudassir yace.

"Yauwa Ummi a ajiye mana taliyar nanfa in mun taso zamuci."

cikin jin dad'in had'in kan yaran tace. 

"Ba matsala sai kun dawo."

daga nan suka juya har sunje bakin k'ofa tace. 

"Ahmad kwana zamuyi ko."

cikin tsiya wasu Salisu yace.

"No Ummi ba kwana zanyiba ai inada yan rakiya."

yana fad'in haka sukayi ca a kanshi wai bazasu rakashi ba.

ita kam Ummi da murmushi ta rakasu. 


Bayan sunje suka samu anata taruwa manya da yara da dottab'ai duk an cika can ta wojen gidan sarki kuma wani rumfane da mata ke taruwa a ciki.


Suna shiga duk sukayi gefen da aka ajiye mazaunin malam, 

wuri d'aya suka zauna yayinda tuni, 

Saifuddeen kuma ya zagaya bayan Bappa Ali da alarammanshi Abdurahman gyara tsayuwarshi yayi gefen d'an agajin dake bayansu Bappa Alin. 

shi kuwa Bappa Ali da alarammanshi gyara abin sautin mgnar dake gabansu sukayi tare da d'an sunkuyawa kan Qur'anen dake bud'e a gansu inda bana zasuyi tabsir d'in ```suratul Maedah.```

shi kuwa Saifuddeen ta cikin glass d'in table d'in gabansu yake ganin fuskar Bappa Ali ras har yadda zai gane motsin bakinshi da abinda yake fad'in. 

dan haka ya maida hankalinshi bisa bakin bappan nashi. 


Bayan anyi addu'a an bud'e taro kana ya kuma jero addu'o'i. gyara zamanshi yayi kana cikin sakekken sauti yace. 

"Alhamdulillahi Allah ya kawomu watan Ramadan tun kafin mu shiga cikin tafsirin namu zan d'anyi tsokaci ga yan kasuwanmu."

sai ya kuma d'ago kanshi ya d'an kalli taron jama'ar dake cike da masallacin ido ya d'an zuba musu tare da ci gaba da cewa.

"Shi watan Ramadan wotan rahama ne da jink'ai da kuma tausayin juna. Amman abin takaici abin haushi tun gabanin zuwan watan zakaga wasu musulman suna k'arawa kayayyakin sana'arsu kud'i domin suyi tsada, maimakon su rage musu k'ud'in domin tausayawa juna da tallafawa tallakawa."

sai ya kuma tsagaita. shi kuwa Saifuddeen tuni yake fassara abinda yake fad'in da body language yadda masu matsalar ji zasu iya gane komai a sau k'ak'e. 

cikin nitsuwa Bappa Ali yaci gaba da sharan fage akan bayanin Ramadan inda yake cewa. 

"Yana daga cikin fa'idojin azumi, 

Azumi na sanya bawa godewa ni'imomin Allah mad'aukaki. 

Azumi na taimaka wa bawa gurin barin abinda Allah ya haramta.

A cikin azumi akwai  tsanani ga shaid'an da raunatashi.

Sannan Azumi na karya k'arfin sha'awa mu samman ga matasanmu. 

Azumi na gadar da samin rahamar Allah da jin k'ansa. 

Azumi na koyarwa bawa tsoron Allah, da tausayin na k'asa dashi.

Azumi na tafe da wasu falaloli na musamman, 

da yawa sai a azumi suke samun dama da k'arfin guiwar shiga itikafi.

Itikafi shine keb'ewa ko zama cikin masallaci domin ibada.

Mafi falalan itikafi lokacin goman k'arshe, yin itikafi sunnace mai k'arfi

yin itikafi a masallacin jumma'a idan kwanakin da za'ayi sun had'a da jumma.

Idan zaka shiga itikafi zaka shiga kafin fad'uwar rana a daren da kake son fara itikafin. 

Mustahabbi ne ga maiyin itikafi ya keb'ance da ibadu yawan salloli, zhikiri, addu'a, karatun Qur'an, tuba, istik'afari, salatin annabi, da dai sauransu domin nemar kusanci da yardar Allah.

Mai itikafi idan ya gama kwanakin da yayi niya zai fitane bayan fad'uwan rana. 

Baya halatta ga mai yin itikafi ya fita zuwa  duba mara lfy da kusantar iyali. 

Amman mai itikafi zai iya fita domin abinda ya zama dole kamar buk'atu irin na d'an adam, 

kamarsu zagayawa bayan gida da neman abinda zaici.

Idan rashin lfy ko jinin haila suka zowa mai itikafi,

 zasu fita idan ya samu sauk'i ko ta samu tsarki sai a dawo."

gaba d'aya wurin anyi tsit ana sauraron bayanin malam Alin.

daga nan ya d'anyi k'arin bayani game da azumin kanshi inda yake cewa. 

"Abubuwan k'i ga mai azumi, 

 Kaiwa matuk'a gurin kurkuran baki da shak'a ruwa. 

Sumbatar iyali da makamancin haka ga wanda baya iya mallakar kanshi. 

D'andanon abinci badon buk'ata ba. 

B'ata lokaci  kawai wasannin banza da surutai marasa amfani. 

Zarcewa da azumi kwana biyu zuwa sama."

A k'arshe yace a tak'aice abinda ya kamata ga mai azumi ya kiyaye harshensa daga dukkan maganganun banza zagi annamimanci giba isgilanci da sauransu kodako a social media ne.

Daga nan suka shiga cikin tafsir d'in nasu gadan-gadan,

mutane sun nitsu wurin jin fad'in allahu subahanahu wata ala.


K'arfe tara dai-dai aka tashi, Saifuddeen ne ya karb'i d'an jakar Quran d'in bappan nashi kana suka wuce gida da abo kanshi, 

suna shiga su suka wuce d'akinshi shi kuwa ya bi bayan bappa Ali da jakarshi saida suka shiga ya bashi sannan ya juyo ya nufi side insu, 

murmushi yayi ganin suna fito daga d'akinshi suna zuwa tsakar gida Ummi kuwa taburma ta shimfid'a musu kana ta zuba musu zazzafan colof d'inan a tire tare da basu forks Mudassir ne ya amshi cokulan ya raba musu kana suka fara ci, 

Raliyya kuwa babban kofi ta d'auka ta d'ebo musu ruwan randar d'akinshi ta kawo musu, 

shi kam bai kula abincinba suma basubi ta kanshiba dan sun sanshi sam baida cin abinci,

Warisu ma kad'an yaci ya ajiye spoon d'in sabida baison yayi teb'a

suna gamawa suka sha ruwa kana suka fita suka raka Ahmad har shabewa sannan suka dawo, 

tuni sha d'aya tayi shiyasa kowa ya nufi gida.


Yauma da dare kamar jiya haka Ummi ta tashi yaranta, 

sai k'arfe uku Rahma ta tuk'a musu tuwon shinkafa dama kuma Raihana tayi musu miyar zogale tun da dare. 

to yau Saifuddeen ya d'anci mai d'an yawa kana yasha tea, 

suna gama sahur din ya shiga wonka kafin ya fito anyi assalatu, 

so alwala yayi tasa Hayatudden a a gaba suka tafi, 

su Ummi kuma sukayi nasu a gida. 

Ana idar da salla ya fara azkar nashi sai da ya gama sannan ya shiga suka gaisa da Ummi kana ya bata 5k d'innan yace ta sama musu asusu na daban ta rink'a sasu, 

ita kam Ummi tayi mmkin yawan kudin to ganin yana sauri Salisu na jiranshi yasa ta barshi ya tafi sai ya dawo suyi mgna. 


Suna isa Salisu ya sauk'eshi a bakin masallacin bakin kasuwan, 

shi kuma ya wuce kabo-kabonshi. 

shi kuwa Saifuddeen cikin masallacin ya shiga kamar jiya yayi baccin awa d'aya da rabi kana yana farkawa yayi Al'wala yayi walaha raka'a  biyu sannan yayi addu'o'inshi kafin ya fito ya nufi cikin kad'uwa. 


Yana shiga kai tsaye dilansu na leda ya shiga inda ya samu mutun biyu a gabanshi dole yabi layi, 

bayan an basu shima aka bashi na 60k Lamar na jiya kenan k'arfe 10:00 Am dai-dai suka bashi nashin, 

with full confidence ya fara bin layi-layi shago-shago lungu da sak'o yana raba musu suna bashi kud'in na jiya, 1:35 pm ya gama rabawa da yake kusan fiye da rabin kasuwar duk a wurin baba bello suke sayan ledan to shiyasa yake dad'ewa yana yawata kasuwan da k'afa tunda shi bashi da keke kamar baba bello,

yana gamawa yazo ya had'a lissafin kud'in ya samu dubu settin da bakwai da dari biyu, cikin aminci ya basu 60k d'insu  sannan ya adana ribarshi a jikinshi godiya yayi musu bayan an rubuta ya dawo da kud'in na jiya, 

tafiya yake yana nazari shifa gani yakeyi kamar kyauta suke bashi kud'in duk da ko azabar nauyin kwalin da yake azawa a k'afad'anshi na dama aikine mai matuk'ar wuya ga yawo cikin rana har ji yake k'afafunshi suna yum-yum dan azaban rana da nauyin kayan da yake azawa a kafad'anshi.


Ganin azahar ta kawo kai yasa ya zauna ya d'an huta dan yana jin kafad'arshi na mishi ciwo ga zafin ranan da yabi sai yake jin wani irin azabebben k'ishi ,

ganin an kira salla yasa ya mik'e yaje yayi al'wala kana ya shiga sahu, 

bayan an idar ne ya mik'e a gajiye yana tafiya a hankali yaje ya karb'i omo dasu sabulu, 

sai kuma ya zage da talla dan yanada burin ya maida Raihana da Raliyya makaranta in kes dai ace sun gama koda d'an Secondary school,

yana kuma fatan ya ink'anta karatun Hayatuddeen da Faruq da Adam kuma yana fatan Allah ya hanasu sake tsammatan abinda zasuci daga wurin wani.


Da wannan tunanin ya zage yaketa yawa tawa cikin ikon Allah ranar ribar  1,200 ya samu. 

Ganin ya fara ganin jirine ya sashi neman inuwa ya zauna saida ya huta sannan ya maida sauran omon.


ganin hud'u da rabi tayi sai yaje shagon ba mishkila gero ya auna mudu shida sai wake mudu shida sai sugar mudu d'aya da rabi, 

daga nan yaje ya sayi mai k'aramin galam sai ya saya musu lemu da ayaba da kankana, 


A tak'aice dai ya kashe dubu uku d'ari biyun nan sai dubu biyar ya bari su kuma na sawa a asusune. 


Biyar na cika Salisu yazo nan suka kama hanyar Dukku, cikin sa'a suka isa da sauran rana. 

Yauma kamar jiya tare da abokanshi sukayi bud'a baki. 

ana idar da sallan asham suka tafi tabsir.

koda suka dawo suka ci abinci sannan suka raka Ahmad. 


Yana dawowa ya sumu Ummi a tsakar gida, 

bisa taburma Rahma na gefenta tana bacci yayinda take ruggume da Adam. 

gefenta ya zauna ita kuwa Ummi tea ta had'a mishi sannan ta bashi, 

yana sha ne taje ta d'auko asusun duka biyu yana ganinta da asusun ya d'an kaikaice tare da cusa hannunshi a aljihun wondon  Jeans d'in jikinshi zaro kud'in yayi tare da mik'a mata, 

cikin kula ta amsa kana ta irgasu ganin dubu biyar ne sai ta fuskanci da kyau cikin maganar kurame tace mishi. 

"Kud'in waye ne."

kurb'an tea d'in ya d'anyi bayan ya had'iye ne sai ya nuna mata kanta.

fidda numfashi tayi tare da gyara zama dan tasan in abu nashine in ta tambayeshi na waye ne sai yace mata natane haka yasa ta gane kud'in nashine cikin tsoro da tuhuna da gudun masifun zamani wanda dole in kaga d'anka da kud'i ka bincikeshi ina ya samesu a hankali tace mishi. 

"Ina ka samesu?  Me kayi aka baka su?  Ya jiya ka samu da yawa yauma kuma gasu da yawa gashi harda su gero naga ka seyo Babana ina tsoro duk da tabbas nasan halinka amman kud'in sunyi yawa."

Allah sarki Saifuddeen ganin firgici a fuskarta ya sashi ajiye kofin tea d'in kana ya juyo suka fuskanci juna da kyau, 

a hankali yasa hannu ya kamo nata hannun cikin sama mata nitsuwa ya mata bayanin komai yadda ya samu kud'in duk da body language yakeyi so Ummi tana bala'i gane body language shiyasa wasu lokutan takanyi mgna dashi cikin mutane ba mai ganewa sai Rahma, 

sai kuma yanzu sun lura Hayatuddeen ma yana ganewa kad'an-kad'an ajiyan zuciya ta sauk'e lokacin daya gama yi mata bayi, 

sai tayi murmushi tare da hamdala kana ta godewa Allah, 

sai kuma ya fara rubutu a gefensu kamar haka.

"Yauwa my Ummi ko kefa kada kiji tsoro Saif d'inki da halal zai cigar daku ya shayar daku ya tufatar daku da guminshi."

kanshi ta shafa tare da samishi al'barka shi kuwa rubutun ya kumayi.

"Amin Amin ya rabbil izzati.

Yauwa Ummi batun gero da wake da sugar kuma, 

a jik'a geron sai a markad'a ayi kamu a rink'a dama kunu kullum da yamma sannan d'auki wake mudu d'aya kullum a surfa ayi k'osai da yamma sai asa a manyan kwanuka a rink'a kaiwa bakin masallaci sadaka, 

gobe zan sayi dabino a rink'a had'awa da dabinon."

Allah sarki Ummi ji tayi tamkar ta ruggumeshi sai kuma taji wasu zafafan hawayen farin ciki,

 cikin raman murya tace. 

"Ya Allah ya yimaka al'barka babana Allah ya k'ara maka imani da tausayi ya Allah ya bud'a maka k'ofofin samu mai al'barka in sha Allahu nida kaina zan rink'a wannan aikin har zuwa k'arshen Ramadan su Rahma da Raihana kuma suyi na gida."

Wani irin farin ciki yaji yana ratsashi sabida ganin yasa mahaifiyarshi farin ciki.

ita kuma cikin bada shawara ko ince neman izininshi a matsayinshi namiji kuma babba tace. 

"Goggonku Dada ta aiko Ahmad d'azu yake cemin wai dan Allah a bata Raliyya mana taje suyi azumi acan zata d'an taimaka mata da aiki."

cikin sanin makamar girma ya rubuta mata.

"Ummi in dai kin yarda ba matsala dan na yarda da tarbiyar Goggo Dada, amman ki gayawa Bappa Ali in ya amince ai sai taje."

kai ta jinjina kana tace.

"Shi na fara gayawa kasan ai bazai hanaba yace taje ba matsala."

gyara zamanshi yayi ya kalli Rahma data zuba musu ido, 

sai kuma tayi maza ta rufe ido wai ita bacci takeyi. 

Jin sautin murmushin sane ya sata tashi zaune kana tace. 

"Yoh tun d'azu na farka sai naga kamar hirran sirri uwa da d'an lelenta sukeyi shine nayi likimo ai, kai kuma da yake ka shahara da body language ko kallonka akeyi jikinka ke gaya maka kawai sai naga ka zuba min wannan fararen idanun naka."

dariya suka d'anyi baki d'aya kana ta zauna sukaci gaba da hira, 

inda itace ta amshi kud'in ta cusasu a asusun babban goggonin milo.


Daga nan sukaci gaba da hirarsu tasu ta rayuwarsu sai shad'aya suka shiga. 


Shi kam Saifuddeen saida yayi wonka sannan ya yayi al'wala kana yazo ya shafa mai tare da fesa turare wanda wannan al'adar rayuwarsa ce domin Saifuddeen mutunne mai tsananin tsabta sam baya son k'azanta ko kad'a shiyasa yakeda kenkeyani over.


Washe gari kamar kullum yayi suka tafi gombe da kafin bakwai na safema sun isa, 

baccinshi ya d'anyi na awa d'aya da rabi kana daya tashi yayi walahan shi kamar yadda ya saba, 

sannan ya shiga cikin kasuwa ya fara rarraba ledodinshi ana bashi kud'in na jiya yana bada wani, cikin awa hud'u da kad'an ya gama rabawa ya had'a kud'insu 60k sannan ya ware ribanshi dubu bakwai da d'ari biyu, 

yaso yayi ragin d'ari bibbiyun saman to kuma sai ya shawarci Jabeer sai yake ce mishi kada ya rage dan kar ya zama yayi azarb'ab'i a kasuwar ledan tunda du du du a wata d'aya ne zaiyi sana'ar kar yayiwa baba Bella  shisshigi  to da wannan

 shawarar ya hak'ura.


Daga shagonsu Jabeer wucewa yayi yaje ya amso omo aifa nan ya samu sa'an shiga layin masu wonki da guga sukayi ta kwasan sabulun kamaru da omon ranar ribar 2k ya samu a omon ma, 

da zai koma ya saya musu naman miya da kuma fruits.



                          ********


Rayuwa ta ja yau da gobe asarar mai rai, 

kwanaki sun tafi tuni azumi ya shigi jikin al'ummar annabi 

anyi dibi-dibin goma na marmari gashi har an shiga goma na wuya inji hausawa da fad'i.

Cikin izinin Allah an gama na wuyan ma yau, gobe dai na d'okin sallah za'a fara. 

Iyaye da yan uwa da masu wadata dama talaka kowa na hidimar d'inkunan sallah. 


Saifuddeen ya k'ara sabawa da mutane sosai ko ta ina an sanshi a kasuwar sabida dalilai uku sana'arsa ta yawoce dole yana ratsa ko wanne lungu, 

sannan shi kurmane da hakane duk wanda ya had'u dashi baya manceshi kana shi mai gsky da amanane da yawan ibada  to sai Allah ya sanya soyayyarsa a zuk'atan bani adam.

Uwa uba Allah ya yalwata mishi surarshi da kyau mai d'aukar hankali yana da muhibba, kima, daraja, kamala, haiba, da cikar zati, 

so wadannan abubuwan sukasa ya sanu tako ina.

Alhamdulillahi kasuwarshi kuwa sai son barka dashi dama Ummi da Rahma sai godewa Allah suke suna k'arawa sabida sune kad'ai suka san kullum sai yasa dubu buyer a asusunshi, sauran na saman kuma da balance d'in machine dasu sukeyi buk'atun yau da kullum, 

ribar omo kuma yaci gaba da zurawa a asusun ribar pure water.


Abota tsakanin shi da Jabeer  da Hisham da Kabir kuwa sai gaba-gaba sun shak'u sosai yanzu ya saba da wani yaron shagon Alhaji ishaq Ibrahim  shima yaron yana sonshi, sosai hakama wani shagon ba miskila Bello sun saba over amman shi ya girmi Saifuddeen sosai so da yake Saifuddeen ya gaya mishi sunan Abbanshi gareshi shiyasa yana kiran Saifuddeen da Bingel am d'ana kenan.


Rayuwa ta mik'a d'aura kwalin ledodi a kafad'a da Saifuddeen yake yawan yi sai ya d'an canza mishi salon tafiya 

sai ya d'an karkace ka d'an mu samman ta samanshi karkacewar da bafa zaka ganeba sai in ka zuba mishi ido sosai baranma   in ka sanshi kafin ya fara tallan ledan ne zaka gane hakan sosai, 

wannan 'yar karkacewar sai ta zama wani abu da yake jan hankalin mutane a gareshi domin daga saman wuyanshi zakaga time to time yana tonk'oshe wuyarshi irin yadda manyan sara kuna keyi sabida nauyin rawani da k'asaita, 

da yawa kuma cewa sukeyi kyanshi ne yasa yake hakan wai a zatonsu rigimace da izza,

sabida in dai ka kalli yadda yake tafiya to sai kayi zaton d'an sarkine ko matashin d'awisu domin dama  a nitse yake sai tafiyarshi da tsarinshi suka koma tamkar na jarumI R.K na seris film d'in Madubalah wanda aka tab'a nunawa a Bollywood 

in ka ganshi sai kayi zaton tsantsar izzace da gadara da tak'ama kasan cewarsa karma ba ko yaushe yake mgna ba sai wasu suke zaton miskilanci ne.


Yakan je gidansu Is'haq time to time musamman in yaji zafi ya matsa mishi sai ya ajiye omonshi yaje yayi wonka ya canza kayan inda zaisa na is'haq sabida bashi da shamaki a gidansu is'haq so yawan tsabtarshi yasa kawai wasu ke masa kallon tabbas rigimace tunda gashi a wuni d'aya a kasuwa sai a ganshi da kaya kala biyu, 

in yaje gidansu is'haq yakan amshi wayar step mother in is'haq din su gaisa ta hanyar rubutawa juna text.


Kullum duk bayan kwana uku zai sayi wakenshi mudu shida geroma haka sannan sugar mudu d'aya da rabi sai mai k'aramin galam da dabino mudu d'aya.

Umminshi ta dama koko ta toya kosan a kai masallacin k'ofar gidansu.


Yau jumma'a kana ana tsula zafin rana kowa ido yayi zuru-zuru sabida k'ishi da yunwa mazauna inuwama suna shan zafin azumin bare masu k'ananan sana'o'i irin Saifuddeen mai sai da leda da yan dako da yan garuwa da masu gonjo da kafintocin sama da kuma 'yan acab'a da direbobi.

Gashi yau shine azumi na 20,

Sosai Saifuddeen ke azabar jin k'ishi hakane yasa k'arfe hud'u dai-dai ya maida omo inda yauma ya samu riba sosai, 

dama ya gama had'a ribar leda wanda yanzu masu sayan sun d'an k'ara sabida karatowan salla yasa cini kaiya k'aruwa. 

Shagon ba miskila yaje yana isa Bello ya kalleshi cikin kula yace.

"Bingel yau ba omon ne?."

cikin gajiya ya lumshe ido tare da sharte zufar da yakeji da hankicib d'inshi cikin gajiya ya lumshe ido tare da mishi alamun akwai ya gajine yasa ya maida. 

cikin kalato yawu Bello yace.

"Gsky kam bingel am azumin yau yanada dad'i."

murmushi sukayi baki d'aya kana Saifuddeen ya nunawa Bella d'anyar shinkafa da fulawa da sugar da geron

sai yaga kuma kamar bai fahimtaba hanne yasa shi zaro biro ya rubuta mishi cewa yana son d'anyar shinkafa da fulawa da sugar.

cikin kula ya auna mishi kana ya bashi kud'inshi shi kuma ya bashi ledodin daya zuba shinkafar a ciki.

Karb'a yayi sannan ya wuce ya sayo mai dasu yis,  dan yana son a rink'a had'awa da  masa a sadakan da ake kaiwa masallacin.

Sai kuma ya sai kayan marmarin daya saba saya, sannan yaje layin masu nama, 

zabbi ya saya guda uku aka yanka aka fige aka gyarasu.

sannan ya fito bakin inda Salisu zai sameshi nan ya irga sauran kud'in inda ya samu ya shigesu sosai yau dubu uku zaisa a asusunshi,  

yana zama ba jimawa Salisu yazo sauk'e wota mata kuma lokacin biyar saura aifa yace kawai su tafi gida, 

to dama shima Salisu ya gaji kawai sai suka kama hanyar dukku. 


Suna isa gida Hayatuddeen da Faruq suka tarbeshi, 

da murnarsu bayan ya ajiye ledidin yayiwa Ummi alamun tayi musu ferfesun zabbin da asuba suci ko da biredi da tea

ai kam Raihana murna ta rink'a  wai zata huta yin miyan asuba.

Shi kuwa gefen Rahma ya zauna sai ya kuma manna kanshi a kafad'arta cikin nuna tsantsar alamun gajiya domin Saifuddeen yana da tsoron wahala to kuma Allah ya jarab ceshi da ita, 

cikin tausayawa ta shafa fuskarshi dan gaba d'aya jikinshi rawa yakeyi, 

cikin tausayawa tace.

"D'an uwana sannu yau azumin da wuya anyi rana."

ido ya lumshe yana mai jin azabebben k'ishi,

a hankali ta kalli Ummi da tuni idonta sun cicciko da hawaye, 

sai ta kuma kalli Raihana cikin sanyin murya tace.

"Raihana kai mishi ruwan wonka."

da sauri ta mik'e duk da tana jin wahalan azumi amman tasan dole ya fita shan zafin rana, 

a randar tab'onsu ta d'iba saida ta cika mishi botiki sannan ta kai mishi bayan gida wanda yana wonke stab dan shi kad'ai ke amfani da bayan gidan tunda Nuruddeen da Abba suka rasu Hayatuddeen har yanzu bayan gidansu Ummi yake zuwa. 

Tana kai ruwan taje ta d'auko mishi kondon sosonshi ta kai mishi sannan tace.

"Hamma na kai ruwan."

kai kawai ya iya gyad'a mata kana ya k'ara lafewa jikin Adda Rahmanshi,

jin hannun Ummi a kan gishinsa ne ya sashi d'ago kai ya zuba mata idanu,

ganin alamun zatayi kuka sai ya yunk'ura ya mik'e jiki na rawa,

cikin sanyi tace.

"Babana baka da lfy ko."

kai ya jujjuya mata a hankali kana yasa hannunshi kan cikinshi da yake a d'akale bafa irin d'akalellen cikin maceba a a irin nasu na maza, 

sai ya kuma nuna mata mak'oshin sa alum k'ishi yakeji, 

cikin kula tace.

"Je kayi wonka zakaji sanyi Babana."

Kai ya gyad'a mata sannan ya juya a hankali ya shiga kayan da zai sa ya d'auka sannan ya shiga bandakin, 

yana shiga ya zare kayan jikinshi duka sannan yaje ya zauna bisa dutsen wonkan da yaketa shek'i da yake a inuwa yake baiyi zafiba, 

surarshi ya k'arewa kallo idon ya zuba kan mararshi a ranshi yace. 

"Hmmm yau kam kaji haza bayan baccinma har b'uya kayi ka koma cikin cikina ko?."

sai kuma ya fara watsa ruwan. 


To Alhamdulillahi da yayi wonkan ya ji dama-dama gashi yana fitowa ana kiran salla, 

al'wala yayi wanda tuni Ummi na gabanshi rik'e da dabino da surki mai d'umi,

dabinon ya amsa addu'a yayi kafin yaci guda uku, 

da sauri ya jujjuya kanshi alamun shi bazai sha surkinba. 

infa da sabo Ummi ta saba don haka yake ba komai yake ciba kuma zai tace maka yana jin yunwa kana kawo mishi abinci in ya tsakuri kad'an sai ya cire hannu wai ya k'oshi.

da sauri Hayatuddeen ya mik'o mishi pilet d'in su kankana to nan ya amshi fork a hannun Raihana sannan ya fara sokawa jikin kankanan da Rahma ta zuba mishi madara da sugar kad'an sabida ta sanshi da son zak'i, 

ido kawai Ummi ta lumshe tana kallonshi sai yana tuno mata k'uruciyar Abbanshi, 

bai shanye rabinshi bama yayi wani sassanyan gyatsa tare da mik'ewa wai ya k'oshi kenan, 


jin ana tada kabbarane yasa Ummi bata hanashi fitaba, 

shi kuwa kama hannun Hayatuddeen yayi suka fita zuwa masallacin. 


Suma su Ummi sukayi haramar yin sallan.


Bayan an idar da salla, suna fitowa, Mudassir, Warisu, Salisu.

Suka nufi cikin gidansu Saifuddeen kai tsaye a babbar taburmar da Ummi ta saba shimfid'a musu suka zauna. 

Rahma mace ta mik'e a hankali ta fara jero musu abin motsa baki, kankana da ayaba da dabinon suka fara ci, sunaci suna hira Rahma kuwa ita da kanta ta matso gefensu zama tayi tare da yi musu harara sannan ta jawo kulan dake gabanta cikin fidda numfashi tace. 

"Daga yau bazan sake biye mukuba, 

kun sani yi muku yambos wallahi ba k'aramar wuya na shaba kirba doyan nan wuya gareshi, gashi Raihana k'in tayani tayi wai ai nike biye muku."

Saminu da yanzu ya shigo tare da Saifuddeen ne ya harari Raihana tare da cewa.

"Yan ubanci zatayi mana shareta Adda Rahma ran salla ke kad'ai zamu bawa barka da salla."

tab'e baki Raihana tayi tare da cewa.

"Kada ku bani mana ni dama ban rok'aba."

Muddassir ne yayi d'an gyaran murya kana ya kalleta cikin tsuke fuska da bada umarni yace.

"Ni bazanma ci wannan yambos d'inba, yanzu ki d'an soya min dankali."

tura baki tayi tare da mik'ewa tana cewa.

"Ni wlh na gaji kuma yunwa nakeji."

Ummi ce ta d'anyi dariya kana tace. 

"Zo Raihana taho nan ga dankalin dama na soyawa Bappa Alinku na kuma d'iba musu zoki basu nasan Mudassir  so yake ya wahal min dake."

da sauri Saminu yace.

"To ni  kuma indomi nakeso mai ruwa-ruwa yaji yaji da al'basa."

 dariya sukayi baki d'aya dan sun san bazata iya musa mishiba, 

sai kuma suka zuba musu ido jin tana ce mishi. 

"Yanzu ne kakeso ko sai kun taso daga tabsir ne zan maka?."

ido ya lumshe kana ya zuba mata ido cikin sanyi yace.

"Ki huta sai mun dawo zamuyi aikin tare."

Ummi kam kauda ido tayi Warisu kuwa da Salisu tuni suketa hirarsu,

Mudassir kuma tuni ya zuba musu yambos d'in har ya fara ci Adda Rahma kuma tea tai ta had'a musu, nan suka fara ci sunaci suna hira. 

Shi kuwa Saifuddeen gefen Ummin shi ya rab'a a hankali ya konta tare da d'ora kanshi a cinyarta, gyara zamanta tayi dan yaji dad'in konciyar,

kanshi ta d'an shafa cikin ido ta zuba mishi ganin sosai fa ya rame hancin shi  zuwet har bisa baki idanunshi sun k'ara fitowa, 

farinshi ya k'ara baiyana cikin kula ta kalleshi ganin ita yake kallo tace. 

"Tashi mana Babana kaje kaci abinci da yan uwanka ai zakafi jin dad'in cin."

sanin in bai ciba hankalin ta bazai konta bane ya sashi yunk'urawa ya tashi zaune sannan ya amshi cup d'in da Adda Rahma ta cika da zazzafan tea mai k'auri sai k'amshi yake, gyara zamanshi yayi kana ya mik'awa Warisu hannunshi alamun ya bashi abinda suke ci d'in, 

ganin Warisu zai kwatso mishi da yawane ya sashi nuna mishi yatsa d'aya alamun guda d'aya zai bashi, 

kauda kai wWrisu yayi kana ya mik'o mishi guda biyu, 

fuska ya d'an had'e dan shi cikinshi ya cika da ruwan da yaketa sha, ya kuma san Ummi zata sashi dole ya cinye biyun da ya sako mishi, 

haka kuwa akayi dole ta sashi yaci sannan ta samishi soyayyan dankalin turawa, nanma yanaci yana d'an korawa da tea d'in a haka dai yaci kad'an.


Jin an fara kiran sallan isha yasa suka mik'e duka dan yin al'wala, dai-dai lokacin kuma Ahmad ya shigo shida Raliyya,

da sauri Rahma tace. 

"Ke Raliyya meya kawoki a daren nan?."

kai ta d'an rausayar tare da gaida su Saifuddeen sannan ta zauna gaban Ummi cikin sanyi tace.

"Kai Adda Rahma ai nida Ya Ahmad ne muka zo nayi kewanku ne especially Hamma Saifuddeen, shiyasa nace yau mu taho tare kuma tare zamu koma."

Cikin fad'a Saifuddeen ya mata alamun da kada ta sake biyoshi gwara tazo da rana.

kai ta gyad'a mishi kana itama ta d'auki buta dan yin al'wala.


Su kuwa suna gamawa suka nufi masallaci koda akayi insha akayi asham, suna fitowa suka shiga cikin gida ruwa suka sha sannan suka nufi hanyar fita dan tafiya wurin tabsir kamar kullum, 

har sunje bakin k'ofar fita Ummi tace.

"Ahmad ka dawo da wurifa ku tafi kasan Raliyya yanzu zatayi bacci anan."

juyawa yayi ya d'an kalli Raliyya cikin lumshe ido yace.

"Shike nan in tayi bacci sai in goyata mu tafi gida abinmu."

Warisu ne ya d'an bugeshi tare dayin k'asa da murya  yace.

"Kai a gaban Ummin kake mata wannan kallon kamar wani tsohon maye."

ita kuwa Ummi cewa tai. 

"Asheko yau sai dai ku kwana anan."

dariya sukayi kana suka fita, 

Raihana kuwa da sauri ta isa gaban Saminu da shi yanzu yake shan ruwan, 

cikin kauda kai ta mik'o mishi dabinon data ciko hannunta dashi guga bakwai ya tsinta kana yace.

"Ya isa sai mun dawo."

"To". tace dashi a sanyaye.


Daga nan suka fita suka tafi masallacin fad'an Dukku. 


Ita kuwa Ummi ita da kanta ta shiga kitchen dan k'arisa aikin ferfesun zabbin data fara dan tasan yau Rahma ta gaji sosai, 

Raliyya kuwa k'ofan bappa Ali ta nufa wurin Aunty Nina, 

Raihana kuwa Attaruhu da al'basa ta d'auko tazo ta zauna gefen Rahma da keyiwa su Hayatuddeen homework shida Faruq, d'an k'aramin bilandan dake hannunta ta had'a kana ta yayyanka su ta jajjagasu sannan ta juye a roba mai marfi, 

Hayatuddeen kuma saura su kankana da ayaban da akaci ya d'an rage guntayen yake ci shifa a dole baya son cin abu mai nauyi a rayuwarshi.


Ummi kuwa a kitchen tuni gidan ya cika da k'amshi dan zabbin sunji kayan had'i bayan ta gama zuba komai ne sai ta rufeshi bisa rushin yaci gaba da bararraka, 

tea ta kuma tafasawa ta d'ura a filas sannan ta fito gudan dubu ta bawa Hayatuddeen ya sayo musu sabon biredi, guda biyu,

da sauri ya mik'e ya amshi kud'in yana zuwa ya kwaso biredi har guda hud'u.


Yana shigowa ganinshi da ledodi har biyu yasa Rahma cewa. 

"Kai amman dai kai kam Hayatuddeen kaga ta kanka shin ba biyu aka aikeka ba?."

da sauri Ummi tace. 

"Barshi ai bazai b'aciba nida nakeda samari yanzuma sun kusa dawowa."

Raihana ce ta d'an harareshi kana tace. 

"Ai shiyasa yake komai na sakalci sabida yasan ba abinda za'ayi mishi ana tab'ashi kad'an Ummi da Hamma Saifuddeen zasuyi ta fad'a."

sai ta kuma kalli Rahma daketa dariya tace. 

"Baga irinta nanba ai harda ke ake sakaltashi."

dariya sukayi baki d'aya ganin yana yiwa Raihana gwalo, Raliyya kuma da yanzu ta shigo dungure k'enyashi tayi nan suka fara 'yar tsamarsu ta sak'o da sak'o.


Daga bisani suka zauna suna hira cikin nitsuwa Raliyya ta gyara zamanta sannan ta fuskanci Ummi a hankali tace. 

"Ummi Ya Ahmad yamin d'inki kala biyu ya kuma sayamin takalmi da mayafi ya kuma yiwa Faruq da Adam  ma,

sai ya kuma yiwa Hayatuddeen dashi da Hamma Saifuddeen iri d'aya."

cikin mamaki Ummi tace. 

"To shi Ahmad duk samunshi a kanku zai k'are ne, yayi ta zaman d'inki yana shan wuya ya kuma k'arar da samunshi a kanku ai wannan d'awainiya tayi yawa."

cikin sanyi tace. 

"Wlh yana wahala kam Ummi kwana fa yakeyi yana d'inki, to amman kuma yana samun kud'i kinsan ya iya d'inki wasu ma daga bajoga da Ngalda duk shi suke kawowa d'inki gashi nan dukku duk ba wani tela daya fishi iya d'inki kinga fa duk zuriyar gidan sarki shi suke bawa d'inki tunda Ya Saminu ya hadasu dashi."

sai ta kuma kalli Raihana tare da cewa. 

"Ai naga kema Ya Saminu ya bada aiyi miki dunkuna har kala uku, d'aya atampa ce d'aya kuma lace d'aya kuma shadda ce kedashi iri d'aya."

shiru tayi kamar bataji ba dan kunya takeji bata son a gane Ya Saminun sonta yakeyi tunda yace mata sai ya gama karatunshi, dan yanzu yana level 2 a G.S.U kunsan duk abokan Saifuddeen sun wuceshi da shekaru biyu sanadin nakasar daya samu ta sashi tsagaitawa da karatunshi sai daga baya da Nurudden ya kawo shawarar ya fara zuwa gombe dashi yana kaishi makarantar kuramen.

so shi Saminu shiyasa bai fiye zaman Dukku ba Salisu kuma kusan shine ya rik'e kakarshi inna shatu, 

Mudassir kuwa yanzu iyayensu hankalinsu na kan karatun Ya Adnan da yake karatun likita yakeyi shiyasa basu bi ta kan mudassir ba tukun tunda sunaga shi Adnan ya kusa gamawa ason ransu sai sun gama da Adnan sannan su dawo kan Mudassir.

Warisu kuma yak'i ya nemi sana'a sai dogon buri to shima mudassir ai da yanada sana'a da duk sun d'auki nauyin karatunsu tunda su ba nauyin ciyar da wasu a kansu, to Saminu kuma da yake d'an gatane dan sarki kuma shalelenshi shiyasa tuni yayi nisa a karatunshi shiyasa ma yakeda damar yiwa Raihana hidima


Ganin Raihana tayi kamar bata jisu bane yasa suka kauda zancen. 


Suna cikin haka suka jiyo hayaniyarsu Ahmad alamun sun dawo daga wurin tabsir d'in.


Bayan sun shigo duk suka zauna bisa taburma

 sunata hirarsu ta abokai matasa, 

ganin Ahmad ya sake ko a jikinshi kamar ba har Shabewa zasu komaba ne yasa Ummi ce mishi. 

"Kaida zaku tafi kuma shine harda konciya kallifa har tara da kwata tayi."

sai ta kuma juyo ta kalli Raliyya dake konce kanta bisa sallayar da aka ninnenke.

"Ke maza tashi ku tafi."

cikin alamun bacci tace to,

Saifuddeen kuwa gyara zama yayi tare fuskantarsu cikin body language yace dasu.

"Ba inda fa zaku tafi a daren nan ku bari gobe kwa tafi da safe."

ido Ahmad ya zaro tare da cewa. 

"To uban wa zaimin d'inkunan da na yanka na ajiye da kake cemin mu kwana."

hararan shi Saifuddeen yayi tare da rubuta mishi.

"Uban uwarka ne zai maka d'inkin."

dariya Ahmad yayi sosai yayinda Ummi taketa hararansu tare da ce musu. 

"Kada ku sake samin kawuna a shirmenku kuyi da iyayenku banda salihan iyayenmu kam da suka bar duniya da dadewa."

cikin dariya Ahmad yace. 

"Yoh dama wa zaice iyayenshi ba salihaiba mu nan gani muke duk duniya ba salihai kamarku."

shi dai Saifuddeen murmushi yayi had'i da shafa k'eyanshi da Ummi ta d'an dungura.

kana sai ya kuma tsuke fuska sannan ya musu alamun, dolefa su Ahmad su kwana da shi kad'ai yazo kamar kullum da zasu rakashi so tunda ya taho da Raliyya kuma dole su kwana, 

ita kam Raliyya tuni ta b'ink'ire, 

shi kuwa Ahmad tsaki yaja tare da cewa. 

"Yaseen d'inku nanka sai bayan salla zan maka su, tunda dama gashi har yanzu baka kawosuba kuma kasan tun kafin azumi nake rufe karb'an d'inki amman da yake kai d'an gadarane da can da saya maka akeyi ma kullum wai sai ishirin da d'aya ga watan kake mik'o min dinkin ka kakuma samin naci dole in d'inka maka."

Tab'e baki yayi tare da d'aga mishi girarshi duka biyu alamun dolenka ai, 

Warisu da su Salisu kuwa kanshi sukayi da cewa kadafa yayi musu al'k'awarin teloli. 

mik'ewa yayi ya nufi d'akin Saifuddeen tare da ce musu.

"Kunga kada ku d'aura min jakar tsaba kaji su bini su tsatstsageni ni tuni na gama dinkunan maza yanzu na mata nakeyi,  sai irin nasu Saifuddeen da basu badaba. 

Saminu kuwa shi tuni yana bakin k'ofar kitchen ta woje yayinda Raihana keta ciki inda take dafa musu indomin, 

sunata yar hirarsu, 

nan ta dafa musu ta gama komai a wani babban tire ta juye musu kana ta jera musu fork sannan ta fito yana binta a baya suka isa a tsakiyar su ta ajiye musu tiren zazzafan indomin da yaketa k'amshin sai dafaffan kwai da tasa guda shida kowa daddaya kenan, 

tana ajiyewa Ahmad daya canza kaya yasa jallabiyar Saifuddeen ya fito nan suka yiwa tiren zobe sunaci suna hira, 

shi kuwa Saifuddeen kwan kawai ya fasa yake d'anci kana ya kalli Ummi data yunk'ura ta mik'e cikin body language yace mata ta zubo musu ferfesun in    gama kai ta gyad'a tare da mishi alamun dama abinda ya tada ita kenan, 

kai tsaye kitchen ta nufa kasan cewar zabbin guga ukune shiyasa ta  zuba musu d'aya da rabi sannan ta d'auko biredi biyu kana tazo ta ajiye a gabansu aifa tuni Mudassir yayi gyaran murya tare da cewa. 

"To yaseen ni dai na k'oshi da indomi ferfesun zansha."

dariya Ahmad yayi tare da cewa.

"Ni kuma dama mura nakeyi."

nanfa suka ture tiren indomin wanda dama kad'an ya rage, 

nan suka fara cin tab'arb'ashin naman zabin da biredi, 

duk sun nitsu sunaci shi kuwa Saifuddeen kad'an yaci sannan ya juyo ga Adda Rahma da Raihana Raliyya da suke ci a tare ido ya d'an lumshe ya musu alamun.....!









                          BY

                     *GARKUWAR FULANI*



              *NAKASA BA KASAWA BACE*



                               *PAGE 7*



                                  NA

               *AYSHA ALIYU GARKUWA*


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇



_Pleees in kin san baki turo kuɗinki ba,kada ki wahal da kanki ki wahaƙ dani, ga nan hanyoyin da zakibi ki biya dan Allah masu cewa ina zan biya to gata inda zaku biya, katin mtn na 300 ta wannan number 0909783276 ko kuma ka/ki turo ta ac na 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo shaidar kin biya ta wannan number 09097853276 to kina yin haka ko baki cemin komaiba zan saki a groups ɗin da zanke post. Kada kuce zakuyi min transfer ɗin katin etisalat bana so! In kuwa kikayi to yaseen sadaka kika bani, gareku masoyana mutanen Niger ga number da zakuyiwa mgna +22788137740 500CF zaku tura_



Zai sha tea.  Da sauri Raliyya ta mik'e ta shiga kitchen tea d'in ta had'a mishi kana ta dawo ta bashi sanan ta zauna sukaci gaba da hirarsu suna kuma cin ferfesun,

shi kuwa gyara zama yayi ya d'an matsa ya basu daman su sake dan kamar sun matsu zaman taburmar ta d'an musu kad'an.

Bayan sun gama cine, Hayatuddeen ya mik'o musu buta da sabulu suka wonke hannayensu sannan suka sha ruwa,

daga nan suka mik'e zasu tafi, ganin haka yasa Ahmad da Saifuddeen mik'ewa suka rakasu k'ofar gida nanma suka d'an tab'a hira sannan kowa ya nufi hanyar gidansu.


Bayan sun shigo gida ne Saifuddeen ya shiga wonka kafin ya fito kuwa tuni Hayatuddeen da Raliya da Raihana sunyi bacci dan sun san anjima kad'an Ummi zata tashesu dan dama in an shiga goman k'arshe tafi tashinsu da wuri, 

Ahmad kuwa da bai saba baccin dareba sai hira yake ta yiwa Ummi da Rahma.


Yana fitowa ya shige d'akinshi mai ya shafa tare da fesa turare sannan ya dawo inda suke nan suka d'an tab'a hira suna cikin hirar Saifuddeen yayiwa Rahma alumun ta kawo asusun shi gane abinda yake nufi yasa ta mik'e ta nufi d'akin Umminsu asusun duka biyu ta kwaso tana zuwa ta mik'a mishi sannan ta zauna, 

k'aramin asusun ya b'alle sannan ya juye kud'ad'en a tsakiyarsu tare da musu alamun su tayashi had'a kan kud'in, 

nan duk suka fara harhad'e kan kudad'en ganin Ahmad ya fisu had'a mai yawane yasa duk suka mik'a mishi na hannunsu, 

amsa yayi ya had'a dana hannunshin kana ya fara irgasu, 

shi kuwa Saifuddeen mik'awa Rahma babban asusun yayi tare da mata alamun ta medashi, 

Ummi kuwa gyarawa Hayatuddeen konciyarshi takeyi.


Bayan ya gama irgasune ya d'ago kai ya kallesu ganin kowa harkar gabanshi keyi ya sashi yin gyaran murya wanda yasa suka d'an kalleshi, 

cikin d'an bud'a kafad'u ya bugi cinyar Saifuddeen haka yasa ya zuba mishi ido shi kuwa Ahmad murmushi yayi tare da cewa. 

"Alhamdulillahi Ummi munyi kud'ifa wlh dole a fara ce damu alhazai."

cikin dariya Rahma tace.

"Toh al'hazai nawane asusun naku?."

gyara zama yayi tare da cewa. 

"Kud'infa da yawa har dubu hamsin da takwas ne da d'ari biyu ne."

cikin jin dad'i Ummi tace. 

"Alhamdulillahi Allah ya musu Al'barka."

Amin Amin sukace baki d'aya,

shi kuwa Saifuddeen gyara zamanshi yayi kana yayiwa Ahmad alamun ya cire dubu takwas da d'ari biyun saman ya bawa Ummi su, 

haka kuwa yayi dan yana gane maganar abokinshi kuma d'an uwanshi, cikin lumshe ido Ummi tace to ni me zanyi dasu?."

kanshi ya tonk'oshe hagu da damanshi sannan cikin mgnar kurame ya mata bayanin, 

"Ta karb'esu in akwai wad'anda take son yiwa wani ihsani tayi amfani da kud'in."

gane abinda yake nufi yasa tayi murmushi tare da cewa. 

"To Allah ya saka maka da mafi kyawun sakamako Allah ya bud'a muku k'ofofin samu, 

wannan zan sayi kayan yara koda kala uku ne a bawa ungiyar marayu."

kai ya jinjina mata alamar hakan yayi, 

sai ya kuma yiwa Ahmad alamun ya cire dubu goma ya ajiye mishi, 

bayan ya cire goman ne sai ya amshi sauran 50k d'in sannan ya zare dubu biyar ya bawa Adda Rahma yace ta d'auki dubu biyu ta bawa Raihana da Raliya 1-1,500  godiya tayi mishi sosai kana yasa 45k d'in a aljihunshi tare da musu bayanin dasu zai musu kayan salla.


Daga nan sukaci gaba da hira har zuwa 12:15 Am na dare jin masallatai sun fara tahajjudi yasa basuyi batun wani bacciba kawai sukayi al'wala suka nufi masallacin fada dan ba'ayi a masallacin k'ofar gidansu.

3:12 Am aka idar da tuhajjdin, 

daga nan kowa ya nufi gidansu, 

suna dawowa suka samu Rahma tana kitchen tana d'umama musu zabin, Ahmad ne ya nufi kitchen d'in tare da cewa. 

"Adda Rahma nifa ferfesun nan ya ishen, me zaki dafa mana a sauk'ak'e?."

mik'a tayi tare da yin hamma kana tace. 

"Dama nayi miya tun da dare dan nasan Ummi tafi son tuwo to nayi miyar bisasshiyar kub'ewa yanzu kuma na tuk'a tuwon semo."

"Yauwa to yafi kam."

cewan Ahmad yana juyawa yayi tsakar gidan inda ya samu Saifuddeen konce yayi pillow da cinyar Ummi, 

suna zaune a nan dasu Raihana da Raliya har Rahma ta gama komai, kamar kullum Saifuddeen ne ya karb'i na gidan Babba Ali ya kai musu sannan ya dawo, 

yau ya d'anci abinci sosai al'barkacin Ahmad, 

bayan sun gama yin sahur d'insune ya mik'e sauri-sauri ya shiga wonka dan ganin an kusa kiran salla, 

yana fitowa Ahmad ya shiga  kafin ya fito tuni anyi assalatu, 

yana fita ya kimtsa yasa wasu kayan Saifuddeen wanda shi kuma tuni ya kimtsa cikin k'ananun kaya wanda sukayi matuk'ar mishi kyau, 

tare suka fita zuwa masallaci inda Hayatuddeen ke gabansu.


Suma su Ummi tuni sunyi haraman salla.

Ana idar da sallan Ahmad da sai hamma yakeyi ya yunk'ura zai tashi da sauri Saifuddeen ya kamo hannunshi tare da mishi alamun yayi azkar tukun, 

tsaki ya d'an ja tare da cewa.

"Kai ni bacci nakeji."

bai kulashiba kuma bai sake mishi hannuba dole dai ya zauna sukayi azkar d'in a tare.


Suna shiga gida sauri-sauri Ahmad ya gaida Ummi sannan ya nufi d'akin Saifuddeen k'ure iskar fankar yayi sannan ya tura k'ofan d'akin kana ya hau bisa katifar yayi lub tuni bacci yayi awon gaba dashi. 


Shi kuwa Saifuddeen bayan ya gaisa da Ummi da Rahma su Raliya suka gaidashi sannan ya tambayesu me sukeso ya saya musu kayan salla,

kab d'insu zabi suka bashi so da haka ya fita ya nufi k'ofar gida inda Salisu ke jiranshi, 

yana zuwa suka gaisa kana ya hau yaja machine suka tafi. 


Bakwai dai-dai suka isa, Saifuddeen na sauk'a Salisu yaja machine ya tafi, 

shi kuma Saifuddeen kamar kullum cikin masallacin nan ya wuce dan baccin da yakeji yau yafi na kullum,

yana shiga ya koma gefe ya konta yana tasbihi a ranshi tuni bacci mai dad'i ya figeshi, 

sai k'arfe tara da kwata ya tashi al'wala yayi sannan yayi walaha bayan ya idar ya fita ya tsallaka titi ya shiga cikin kasuwar da tuni ta cika tayi mak'il da bani adam.


Kai tsaye layin kantin kwari ya nufa inda nanne layin da dilansu yake, 

yana zuwa ya samu ba kowa a gabanshi nan aka ware mishi aka bashi, daga nan ya cika k'aton kwalin nan ya azashi a kanshi ya fara bin layi-layi lungu da sak'o yana raba musu suna bashi kud'in na jiya. 

Cikin awa hud'u ya gama, to yau sai bai nufi karb'o omonba sai ya wuce shagon Alhaji ishaq mai atampopi dasu laces materials shadda da dai sauransu.


 Yana isa Alhaji ishaq d'in da kanshi ya tarbeshi fuska a d'an sake yace. 

"A Balarabe yau babu omone?."

numfashi ya d'an fidda kana cikin yanayin zafin rana ya mishi nuni da kaya yakeso zai saya, 

gane abinda yake nufi yasa Alhaji ishaq d'in nuna mishi ya tsallako ya shigo daga ciki dan ganin mata sun cika bakin shagon nashi mak'il ,

yana tsalla kowa ya shiga Ibrahim ya bashi hannu suka gaisa irin gaisuwar nan ta abokai, 

cikin bada umarni Alhaji Ishaq d'in ya cewa.

"Yauwa Ibrahim kama fini gane mgnarshi maza kula da lamarinshi ka bashi duk abinda yake so a farashin sari."

cikin jin dad'i Ibrahim yace.

"Toh ba matsala."

sai ya kuma maida hankalin shi kan paper da Saifuddeen ya bashi inda ya rubuta mishi.

"Ina son atampa masu kyau da taushi guda biyu ka bani masu kyau na Ummi nane, 

sai ka bani laces guda uku masu kyau Adda Rahma orange color takeso Raihana kuma lemon green da ratsin  white take so,

Raliya kuwa  red mai ratsin yellow color,

sai ka had'a musu da atampa d'ad'd'aya masu kyau fa."

cikin kula Ibrahim yace.

"Ba matsala."

sai ya kuma juyo ya fara zabo atampopi da laces masu kyau yan ma dai-dai tan kud'i,

duk wanda ya zaro in ka ganshi saikayi sha'awarshi. 

nan ya gama zaro kusan laces kala goma atampa goma, 

duk ya jibgesu gaban Saifuddeen, 

nan shi kuma Saifuddeen ya fara zab'o wad'anda zai saya laces uku ya zaro sai atampopi biyar biyu na Ummi ne,

sosai ya zabo masu d'an karen kyau.

 Wata mata dake cikin taron matan da suka cika bakin shagon ne ta zuba sshi ido tace.

"Kai wannan kekyawan yaro ya iya zab'an abu mai kyau gsky nima to shi zan bawa zab'i."

murmushi mutanen wurin sukayi dan gsky ta fad'i. 

shi kuwa Ibrahim kud'insu ya rurrubuta mishi, 

bayan ya amshi takardar ya karanta rubutun Ibrahim sai ya rubuta mishi amsa da cewa. 

"Nima in nazo nan ba a farashin sari nake baku ledodina ba so nima kada kuce bazakuci riba a kainaba ai ita kasuwa ba k'arya bace kuma dan riba akeyinta sai ni kuma ba sarin zanyiba so naji duk yadda kuka saidawa saura laces in nan nima haka zan biya, 

dan haka samin su a leda."

dole a dai yadda suke saidawa kowa a haka ya biyasu.


Daga nan sai ya nufi shagon Alhaji Yawale nan ya sayi wasu datsastsun yaduka masu hegen kyau yad'i ashirin ya saya dan sun bashi tabbacin yadi uku zai isha kamanshi d'inkawa dan haka ya sai yadi ashirin, yayi lissafi yadi tara shida Salisu da Ahmad yadi tara kuma Warisu da Mudassir da Saminu yadi biyun sama kuma Hayatuddeen.

sai ya kuma sayan wani yad'i mai kyau yadi shida uku nashi uku kuma Faruq da Adam, 

bayan ya gama biyan kud'in sai ya kuma fito ya nufi shagon su Jabeer nan ya sayawa su Rahma gyale daddaya wanda zai shiga da kayansun duka bibbiyun, 

kana yaje shagon masu d'inka hijabai ya d'inkawa Umminshi hijabai guda biyu, 


sannan daga nan ya fito da ribanshi na yau ya sayawa Faruq da Adam kayan kanti kala daddaya.

Bayan ya gama had'a kayayyakin da ya sayan sai ya samu kowa ya samu kala bibbiyu sai Hayatuddeen ne ya samu kala d'aya, 

so shiyasa ya ciro sauran kud'in nashi ya saya mishi wani yad'i kalanshi mai kyau, 

daga nan ya had'a kayanshi kab wuri d'aya cikin irin k'attin ledodin nan, 

sannan yaje ya ajiyeshi a shagonsu Hisham daga nan yaje ya d'auko omonshi yayi ta zaga yawa, 

Alhamdulillahi yau garin akwai lumshi alamun hadarin forkon damuna sai manyan gajumare masu yiwa sararin samaniya rumfa.


Ya saida omon sosai inda ya samu riban 2,700.

Ganin yamma tayi sai ya saya musu fruits  na 700 d'in.

ganin biyar tayi sai ya fito inda Salisu zai sameshi ba tare da ya d'auki kayan daya saya ba,

ya barsu a shagonsu Hisham sabida yana son sai gobe in yazo ya sayawa Goggo Dada da Aunty Nina da Bappa Ali kafin ya meda kayan, 

sabida yanaga in ya medasu yau tamkar ya waresu ne. 


Koda ya koma yayiwa Ummi bayani, 

Ahmad kuma yau bai zoba a zatonshi Saifuddeen zaizo ne.


Washe gari kuwa kamar yadda yayi niya haka yayi, 

daya gama hada ribarsa na jiya sai ya sayawa Goggo Dada turmin zani hakama Aunty Nina sannan ya sayawa Bappa Ali shadda mai kyau.

daga nan ya hada kayan sannan ya tafi tallan omonshi. 


Biyar dai-dai suka nufi dukku suna isa Dukku, 

kamar kullum bayan sun gama komai ne sunje tabsir sun dawo ne ya fito da kayan yayi musu bayani  sannan ya bawa Ahmad kayan tare da cewa yau Salisu ne zai maidashi da mashin, 

Saminu kuwa nan yake ce musu.

 "Yauwa ni nama manta ban gaya muku ba na saya mana takalma da huluna, wanda zamuyi fitan idi dashi dama d'inkin naso in yi mana to sai naga takalma da hulunan zaifi armashi."

sosai suka cika da farin ciki nan Salisu kuma yace.

"To ni kuma zan saya mana agogo masu kyau."

Ahmad ne ya kalli Saifuddeen da yake mishi bayanin wannan 10k d'innan ya sayi kayan d'inki dasu. 

harara ya mishi tare da zaro kud'in dan dama ya taho dasu dan ya zargi hakan bashi kud'in yayi tare da cewa.

"Ingo amshesu inada kayan d'inki kai dai ba ka saya ba ka kuma bani to ba ruwanka da batun d'inki in naga dama in d'inka na iyayenane da abokaina da k'annena da yarana in naga dama ink'i dinka naka in d'inka na kowa.

Ga dai kud'inka nadai ci naman dubu d'aya a cikin kud'in jiya."

murmushi yayi tare da amsar kud'in ya sasu a aljihu.

daga nan Salisu yaje ya fidda machine inshi yazo ya maida Ahmad can Shabewa.


Tun daga ranan Ahmad ya fara d'inka nasu na maza. 


Shi kuwa Saifuddeen washe gari da yaje kasuwa takalma ya sayawa su Rahma da Ummi dasu Hayatuddeen duk da saida yayi ciko da ribar omonshi na yau d'in.


Washe gari kuma da ya kuma zuwa yan kunne da sarka ya sassaya musu. 


A takaice dai saida yayi kwana biyar baya ajiye ribarshi, 

a cikin haka kuma ya kuma ya kuma sayan wani kayan yad'i shida ya bada d'inki cikin kasuwar kayan shida abokinshi Is'haqnshi.


tun randa akayi azumi ishirin da biyar ya gama hidiman dinkin salla da komai, 


Daga nan kuma yaci gaba da zura kud'i a asusunshi. 


Yau saba'an wota ishirin da bakwai kenan, 

kuma yau yayi cinikin omo sosai, 

k'arfe hud'u dai-dai ya shiga gidansu Is'haq, 

Imran na ganinshi yayi sauri ya isa gareshi cikin murna yace.

"Hamma Saifuddeen gobe Ya Is'haq zai dawo yace min shi dai bazaiyi salla a Abuja ba."

kamo hannun Imran yayi wanda bazai wuce sa'an Hayatuddeen ba murmushi yayi tare da shafa kanshi sannan suka shiga parlour Baban Is'haq.

cikin fara'a yace.

"D'an halak kak'i ambato ko yanzu nake jajenka ka kwana biyu baka lek'oba ashe kana tafe."

kanshi ya d'an shafa tare da yin murmushi kana ya rusuna gaban Baba cikin body language suka gaisa har yake shaida mishi gobe Is'haq zai dawo,

sun jima suna hira daga bisani ya mik'e tare da cewa.

"Bari yaje yayi wonka."

daga nan ya fito parlour Mommy ya nufa step mom d'in Is'haq kenan bayan sun gaisa ne ta bashi key d'in d'akin Is'haq da woyarta dan tasan zasu gaisa da abokinshi.


Yana shiga d'akin Is'haq wonka ya farayi sannan ya fito ya canza kayan inda tuni ya wonke wanda ya cire ya shanya.

gefen gadon Ishaq d'in ya zauna tare da fara rubuta mishi sak'o kamar haka.

"Assalamu alaikum, ya gida da Ramadan, Baba ya cemin gobe zaka dawo ko?."

jim kad'an sai ga amsa.

"Wa alaikissalam, nayi fushi da kai yau kwana nawa baka zo gidaba kullum sai na tambayi imran."

bai ida gama karanta amsarba wani sak'on ya kuma shigowa. 

"Eh gobe zan dawo ya Rabi'u yayi mana d'inki komai iri d'aya yace wai ai mu tagwaye ne.

A gombe zamuyi salla ai ko?."

murmushi yayi tare da rubuta mishi. 

"Allah ya dawo daku lfy ka cewa Ya Rabi'u ngd matuk'a Allah bar zumunci da k'auna, ina Ammi na nayi missing nata tare zaku dawo ai ko. 

Hahhm Imran k'arya yakeyi ko last week nazo ai yanzuma hidimar kasuwane ke hanani zuwa yanzuma sauri nake zan tafi."

daga nan kuma ya mik'e ya fita, 

har ya mik'a Mommy woyar sai kuma ta mik'o mishi tare da cewa mishi gafa wani sak'on yana amsa yaga abinda ke rubuce. 

"Dole fa a gombe zaka zo muyi salla, naga kak'i ka bani amsar inda zakayi salla, 

to kuma nasha gaya maka inaso mu kasance cikin ungiyar. 

Joint national association of persons with disabilities,

(Jonapwd) gombe state chapter.

All the best!. domin k'ungiyace mai daraja da mahimmanci kungiyace mai zaburar da nakassasu domin su dogara da kansu ta hanyar yin rayuwa kamar ko wanne mai lafiya suna jan hankalin da nusar da nakassasu cewa itafa Nakasa ba kasawa bace, kuma babu nakasasshe sai rago, 

suna gina zuk'atan duk nakasashen dake k'ark'ashinsu da nunin nakasar zuciya fa itace sahihiyar nakasa ba irin tamuba ta jiki, 

so a sallan ya kamata muje garesu domin had'a hannu dasu."

da sauri ya rubuta mishi amsa da cewa. 

"To ba matsala Allah ya kaimu na amince."

 yana tura mishi amsar ya sallamesu ya tafi kuma har cikin ransa ya gamsu da shiga cikin sahun members d'in k'ungiyar dan yaga sunada kekyawar niya.


 Koda ya koma kasuwa bai wani sake d'aukan Omo ba shagonsu Jabeer yaje suka d'an zauna suna hira dan mutane sun d'an tsagaita shigowa shine ya bawa yaran shagon damar d'an hutawa.


Ganin hud'u da rabi ta godata ne ya sashi mik'ewa tare da bawa Jabeer hannu, 

musabaha sukayi sannan sukayi sallama.

Daga nan shagonsu Hisham yaje inda ya samu suma ba mutane da yawa ko dan yanzu kasuwarsu ta d'anyi k'asa sai 'yan tsirarun da suke zuwa sayan kulolin abincin salla.

kusan tare suka fito da Hisham inda yake tambayanshi.

"Gobema zaka zoko?." 

kai ya gyad'a mishi alamun eh sannan ya nuna mishi yatsunshi biyu tare da mannasu a goshi alamun rannan salla ma zaizo amman ba kasuwa zai shigoba zaizo wurin best friend nashi."

cikin happy Hisham yace.

"To in kazo zaka isa gidanmu ko?."

ido ya d'an jujjuya kana ya mishi alamun.

"To ai ban san gidanku ba."

gane abinda ya ke nufine yasa Hisham cewa.

"Mu dai-dai ta lokacin da zaka zo sai inzo in sameka a bakin shagonmu sai mu tafi tare muje ka gaida Mom ena."

paper da biro ya zaro kana yace mishi. 

"Jabeer ma yace dolefa wai sai naje gidansu wai Umminshi na son ganina so shi rubuta min address insu yayi, kaga kaima gwara kawai ka rubuta min address naku in sha Allah, in Allah ya nufa fa sai kaga nazo."

cikin gamsuwa Hisham ya rubuta mishi tare da cewa. 

"In sha Allah, zama kazo."

dai-dai lokacin kuma suka isa bakin San HUSSAIN MALL inda nan Salisu zaizo d'aukan shi, 

daga nan sukayi sallama da Hisham, shi kuwa  Saifuddeen ya isa gefen masu fruits ya sassayi abinda ya sauk'ak'a, yana gamawa Salisu na zuwa daga nan suka tafi *Dukku d'iyam sad'i na kosam,* garin da ruwa yafi nono tsada, amman fa banda gidansu Saifuddeen dan su har rijiyoyi biyu ne a gidansu d'aya ruwan dad'i d'aya na zartsi,  shiyasa duk 'yankin unguwarsu a gidansu ake zuwa d'iban ruwa, rijar dad'in ruwanshi sanyin ko yaushe ruwanshi k'alau ,na zartsin kuwa ko lokacin hutunrune in ka jawo ruwan sai ka sameshi da d'umi dai-dai yin wonka. 


Suna isa.

Kai tsaye ya kusa kai cikin gida,

a tsakar gida ya samu Ummi rik'e da botiki, 

bisa dukkan alamu ta gama tuyan masa da k'osan dan duk ta sasu cikin manyan kulolin da cikin kayan Rahma suka fito dasu,

ga kuma tukunyar dama kunu yana bisa murhu amman ba ruwa a ciki,

daga can gefe kuma Raihana ce konce lib da alamun bata da lfy,

sai Rahma dake kitchen tana aikin girki,

Hayatuddeen ne da Faruq suka rugo a guje suka nufi inda yake tare da yi mishi oyoyo,

d'aga Faruq yayi sama cak ya ruggumeshi kana yasa hannunshi na dama yana shafa tsakiyar kan Hayatuddeen wanda tuni ya amshi ledan hannunshi,

Ummi kuwa ido ta zuba mishi sosai ya rame alamun rashin hutu k'arara a jikinshi.

gabanta ya iso tare da dire Faruq cikin fidda numfashi ya kalli botikin hannunta kana ya kalli tukunyar dake bisa murhu,

cikin body language yace mata. 

"Baki sa ruwa ba." 

kai ta jujjuya tare da lumshe ido sannan tace.

"Yanzu zan jawo ruwanma."

juyawa ya d'anyi gefen dama inda randunansu ke jere taku kad'an yayi ya isa inda randunan ke jere bubbud'esu yayi duk babu ruwa a ciki sai kad'an-kad'an ,

gaban Ummin ya dawo tare da mata alamun, 

"Ya akayi ba ruwa a randunan me Raihana keyi da bazata ja ruwan ba tunda Raliyya bata nan Hayatuddeen kuma bazai iya dan rijiyoyin suna da d'an karen zurfi, 

Rahma kuma na fama da aiki."

juyawa tayi a hankali ta nufi can gefen wata k'atuwar bishiyar maggoro da rijiyoyin ke k'asanta duk suna cikin inuwan bishiyar da sauri yabi bayanta,

suna isa ya zura gugar a cikin rijiyar dad'in, ita kuwa Ummi da sauri ta rik'e tare da cewa.

"Je ka huta zan ja ruwan ita Raihana yau tun da safe cikinta ke ciwo,

Rahma kuma jiya ta yanke a 'yar yatsarta garin yankan lemu."

da sauri ya jujjuya mata kai kana yaci gaba da zura gugan alamun shi zai ja ruwan. 

Ita kuwa Ummi tausayinshi ne ya rufe mata zuciya da jiki tasan muddin in dai yana nan tofa baya tab'a yarda taja ruwa, to shi kuma in dai yaja ruwa sai hannunshi suyi jazir musamman yatsunshi da sai sunyi alamun d'ura ruwa, Ummi tafi kowa sani jikin Saifuddeen baya juran wahala yana tsoron wuya so amman sai yake b'oye musu hakan da jarumtar zuciyarshi da take tirsasa gangan jikinshi jajircewa koda ko zai wahala.

ido kawai ta zuba mishi ganin yadda yake jan ruwan da karsashi tamkar baya jin wahalan,

yana cika botikin yaje ya juye mata rabin a tukunyar rabin kuma ya juye a rand'a kana ya yafito Hayatuddeen tare da nuna mishi d'an k'aramin botiki alamun ya d'auko yazo suna kai ruwan rand'a,

da sauri Hayatuddeen ya mik'e tare da suran botikin.

daga nan sukaci gaba da d'iban ruwan in ya cika botikin shi sai ya cikawa Hayatuddeen sannan su d'auka a tare suje su juye a rand'a. 

Ita kuwa Ummi tuni ta koma gindin murhunsu na wojen tanata hidiman dama kunun Rahma kuma na kitchen tana k'arisa aiyukanta.


Cikin k'ank'anin lokaci suka cika randa biyu sun fara sawa ana ukun ne Rahma ta fito daga cikin kitchen d'in tana ganin Saifuddeen ne ke jan ruwan tayi maza ta isa gindin rijiyar cikin sauri tasa hannu ta kamo igiyar gugan tare da cewa.

"Ka bari haka ya isa, Ummi ya za'ayi ki barshi yaja ruwa kinsan yanzu hannunshi zai d'uri ruwa."

cikin kula Ummi tace. 

"Yak'i ya barni inja kin san ba yarda zaiba, kuma bazai bari mu zauna ba ruwa ba."

fuska ta kwabe ganin ya amshi gugar yaci gaba da jan ruwan,

cikin sanyi tace.

"To ka rink'a ja nida Hayatuddeen zamu rink'a jida,

ni da ka bari ma dan na aika Mudassir yazo kuma nasan in yazo in na sashi ba k'i zaiyiba."

cikin k'arfin hali ya nuna mata alamun karta damu,

daga nan sukaci gaba da jan ruwan.


Suna gamawa ya cika botikin ya shiga wonka, 

tuni Ummi kuma ta gama dama kunun, 

inda Raihana da cikinta ya d'an lafa ta tashi zaune ta jingina da bishiyar dimurin dake tsakiyar gidan nasu kusan nanne wurin zamansu,

Rahma kuma duk ta had'a komai na bud'a baki har miyar asuba tayi musu tunda Raihana maiyin bata da lfy,

Hayatuddeen kuwa tuni Ummi ta d'ora mishi kulan masa ya kai ya dawo kana ta d'ora mishi na k'osan tare da bashi robar dake cike da dabino a hannu bayan ya dawone ta kuma aza mishi kulan kunun tare da cewa.

"Zaka iya ko autana?."

cikin dakiya da jarumtar da yake koya a wurin Hamma Safuddeen d'inshi yace.

"Eh Ummi zan iya."

kai ta gyad'a sannan tace.

"To in kaje kace a sauk'eka kada kace zaka sauk'e da kanka dan bazaka iyaba."

juyawa yayi yana fita tare da cewa.

"To, duk da yaso yayi irin na Hamma shi duk abinda ake tunanin bazai iyaba sai ya yin, to amman ina ai shi Autan Ummi akwai ragwanci over.

Shi kuwa Saifuddeen bayan yayi wonka yana fitowa ana kiran salla.

Ummi da kanta yau ta zuba mishi madara da sugar bisa kankanan ta kuma wonke mishi dabinon, 

yana isa inda suke ya zauna gefe bisa wani dutse wanda nan suke zama suyi al'wala, Faruq ne ya mik'a mishi buta yayinda Ummi kuma ta mik'o mishi dabinon, 

Ummi da Rahma da Raihana duk tafin hannunshi suka zubawa ido ganin sunyi jazir tamkar ka tab'a jini ya tsallo, 

kan yatsunshi kuma sunfi ko ina yin ja, 

cikin muryar ciwo Raihana tace. 

"Dan Allah Hamma kada ka sake jan ruwa kalli yadda tafin hannunka sukayi fa."

yi yayi kamar bai gane me take cewaba.

Ummi kuwa kamar tasa kuka takeji dan tausayinshi, 

Rahma kuwa hannunta tasa ta shafi tafin hannun nashi ganin duk inda ta shafa sai jinin wurin ya gudu wurin yayi fari sai kuma a take wurin yayi ja kamar da, 

sai kuma duk suka juyo kan Raihana dan ganin ta kamo hannun Umminta ta rik'e gam alamun, 

ciwon cikin nata ya murd'a, 

gaba d'aya jikinta rawa yakeyi dan azaba,

kusan a tare suke ce mata sannu,

shi kuwa Saifuddeen nuni yayiwa Ummi da ta, 

had'awa Raihana zuma da ruwan zafi ta bata tasha."

cikin gane abinda yake nufi tace. 

"Na bata ta sha tunda da yamma nace tasha amman tak'i wai ita sai ta kai azuminta, to sai yanzu da auta ya kai dabino masallaci yace ansha ruwa to shine ta amshi ruwan zafin da zuman tasha yanzu kuma inaga cikin ya kuma murd'awane."

sai kuma suka bita da idanu ganin ta mik'e da sauri ta zari butan dake gaban Saifuddeen d'in ta nufi band'akinsu,

tuni kuma Al'adar tata ta iso har ya d'an b'ata mata zani, 

ai da sauri Saifuddeen ya rumtse idanunshi dan yanada tsananin k'yank'yani yanzu haka bazai sake cin abin hannun Raihana ba har sai yaga ta samu tsarki tana salla, 

Rahma kuwa dariya tayi tare da cewa. 

"Hmmmm Deeen kenan tunda kai na mijine ai da sauk'i, 

sai dai kuma tunda zakayi aure ba mmki wata ran kayiwa matarka wonki."

kame jikinshi yayi alamun tsikar jikinshi ya tashi da batun wai shi dai yayiwa matarshi wonkin wannan k'azantar, 

Ummi kam tuni ta bar wurin shi kuwa yawu ya tofar kana ya d'auki pillet d'in kankana ya mik'e tare da yiwa Adda Rahman tashi alamun Allah ya kiyasheshi da sharrin bakinta, dariya tayi tare da bin bayanshi da ido, 

tabbas tasan su duka zuriyarsu kyawawane amman babu wanda ya kai Saifuddeen ita kanta wani lokaci ganinshi take tamkar balarabe ko ba indiye, 

gashi komai nashi da nitsuwa da tausayawa, 

gashin k'eyanshi ta zubawa idanu har saida ya b'acewa ganinta.

Shiko yana fitowa woje yayi gefen su Warisu nan suka shanye kankanan a tare amman time to time yakan rumtse ido in ya tuno jinin da ya gani sai ya kuma tofar da minyau.


Ana idar da salla suka shiga gida inda suka samu, 

yau kuma awaran couscous Adda Rahma tayi musu sai masan da ta d'iba musu cikin na masallaci sannan tayi musu miyan alaiyahu da tontok'oshi wanda da miyar zasuci masan,

sai kuma tea da ta kawo musu amman ba madara, dan azumi yazo k'arshe mafi yawanci cefenensu yayi k'asa

sai kuma kunun gyad'a, 

nan sukaci sukasha kamar kullum,

sannan suka tafi jin tabsir wanda yau zasu rufe 27 ga watan Ramadan d'in kenan.


Suna dawowa ta kawo musu tuk'ek'k'en tuwon shinkafa da miyar ganye wanda miyar asubane to da yake miyar da d'an yawa shiyasa ta tuk'a musu tuwo, 

a zatonta bazasu wani ciba amman kuma sai gashi sun cinye tas yau harda Saifuddeen da yake abinda yake sone Warisu ne ya d'anci kad'an.


Bayan sun gama cine Ahmad ya firfito musu da d'inku nansu baki d'aya, 

sosai sukayi mmkin yadda ya gama d'inkunan cikin k'ank'anin lokaci kuma d'inkunan sunyi kyau sosai da salon tsarin d'inkunan wannan shekarun.


Nan Saifuddeen ya bawa kowa nashi,

duk sukayi godiya dama tuni Saminu ya kawo musu takalmansu da huluna Salisu kuma ya kawo musu ogogunansu.

Daga nan duk sukayi sallama suka tafi sai Ahmad da yace yau nan zai kwana,

to bayan su Mudassir sun tafine Bappa Ali da Aunty Nina ma sukazo yiwa Saifuddeen godiya nan sukaci gaba da hira, 

a nanne Saifuddeen yace dasu, 

Hayatuddeen zai rink'a zuwa wurin Ahmad ya rink'a koya mishi d'inki,

to kuma duk sunyi na'am da hakan daga nan suka d'an tab'a hira sannan duk sukayi saida safe suka watse.


 Washe gari kamar kullum suna isa ya d'an shiga massalaci yayi baccin awa d'aya da rabi yana tashi yayi al'wala yayi walahanshi,

yana fitowa kai tsaye layin da zai sadashi da kantin kori ya shiga, 

yana isa d'ab da kantin korin ya tsaya a bakin shagon Malam Habu mai saida mayukan shafa da turatuka powder da dai sauran kayan kolliya na mata, 

Sadiq na ganinshi cikin fara'a yace. 

"Barka da isowa Balarabe."

murmushi yayi tare da mishi alamun bafulatani dai daga nan suka d'an gaggaisa da mutanen layin sannan ya isa dilansu na ledan yana zuwa aka bashi kamar kullum sannan ya fara zazzagayawa ya rabawa kowa. 


Koda ya gama sai ya d'auko omonshi nan yayi ta zagayawa sosai kuwa yau ya sayar koda ya gaji ya koma shagon Malam Habu ya zauna yana d'an hutawa dan yana son yaje gidansu Ishaq to ya kuma yanaga kada yaje ya samu basu isoba da wannan tunanin ya bari sai gobe yaje, 

cikin body language ya tambayi Malam Habu ko yasa inda gidan Baba Bella yake?."

kai ya jujjuya alamun gsky bai saniba to amman sai ya bashi shawaran yaje ya tambayi Alhaji Aliyu  dilansu na ledodin kenan dan yana kyautata zaton shi zai san unguwar da Dottijon yake,

nan yake cewa Malam Habu ya mantane Alhaji Aliyu baya k'asar ya tafi umrah,

to nan yace ya tambayi yan shagonshi wata k'il zasu sani, 

toh fa abu kamar da wasa ya tambayi duk mutanen da yake zaton zasu san gidan Dottijon nan baba Bello amman duk sai kowa yace ko unguwar da yakema basu saniba yayinda wasuma sai suke mmki da ce mishi ba yace kai jikanshi bane to ya za'ayi kai jikanshi baka san gidanshi ba sai mu. 


Shi kuwa Saifuddeen ribarshi na yau na omo dana leda harda riban omon jiya ya had'an kud'in 10k da nufin zai yiwa Baba bello ihsanin yayi hidiman salla, 

to kuma gashi ya rasa wanda yasan gidan, 

dole haka ya hak'ura sannan ya bawa malam Habu ajiyan wannan 10k d'in dan ya rigada yayi niyar wannan kud'in Dottijon zai bamawa.



K'arfe biyar nayi Salisu yazo suka tafi Dukku.


Washe gari kuwa ta kama ranar ne ishirin da tara ga watan Ramadan wonda ana zaton ganin watan salla yau ko gobe dan haka da zai fita tafiya gombe sai ya harhad'a duk sauran kud'ad'en da yake adanawa ya sasu a aljihu ya tafi dasu. 

To koda ya gama rarraba ledodinshi kamar kullun ya saro omonshi yayi ta yawatawa har aka k'arfe uku saura kwata bayan ya had'a ribarshi ya wuce ya maida omonshi daya rage,

daga nan ya wuce shagon Alhaji Kabiru wanda ake saida duk wani kayan d'and'anon miya kama daga Magi, raico, onga gishiri kafi  Mai, Manja, fulawa, madara, sugar, sufageti, macaroni, indomi. da dai sauransu suna bada sari suna saida kad'an-kad'an kuma suma shine ke saida musu ledodin da suke zubawa kostomominsu  kaya in sunyi sayayya.

Sun saba sosai da Alhaji Kabiru dan shima yanada d'anshi kurma shiyasa yake tsananin son Saifuddeen,

yana isa bak'in k'aton shagon nasu ya zaro pepar da biro ya rubuta musu duk abinda yakeso,

nan Alhaji Kabiru ya amsa da kanshi ya ware mishi duk abinda ya lissafa bayan ya gama sasu a leda cikin nitsuwarshi yace.

"Masha Allah Saifuddeen Allah yasa Isma'il d'ina ya zama mai nagarta kamarka, kalli yanzu wasu manyan magidan tama basuyi azamar cefenen sallaba amman gashi kai tuni ka gama komai abinka."

kai ya d'an sunkuyar tare da gyara hannun riganshi sannan ya d'ago kanshi tare da yin murmushi cikin girmamawa ya amshi ledan da yake mik'o mishi sannan ya bashi kud'inshi tare da mishi godiya da sallama sannan ya juya ya tafi.

Layin masu yankan kaji yaje nanma ya sashi zabbinshi guda biyar ya bada kudi kana yace musu in sun gyarasu su sa mishi su cikin firij sai k'arfe shida da rabi zaizo ya amsa, 

dagana kuma ya sayi jan nama na dubu 3 sannan ya wuce layin masu tattasai, inda yaje ya sayi,

Tattasan, attaruhu, tumatur, al'basa, kabeji, karas, green beans. Da dai sauransu, 

sai ya kuma sayi dankalin turawa kond'o d'aya, 

daga nan ya wuce shagon da yake saran pure water inda ya samu Rabi'u nan ya sayi katon d'in fanta da Coca-Cola sai rabin ledan molt sannan ya had'a duk su tattasai ya kai aka marked'a mishi sannan ya ware wasu tattasan da taruhu da al'basan kuma wanda ba'a marked'aba ko za'a buk'acesu hakan.

Kana ya harhad'a duk abinda ya sayan a shagonsu Rabi'un dan yasan shi da masu nama suna kai har dare kuma dama ya gayawa Salisu yau sai anyi sallan isha zasu kama hanyar tafiya dukku, 

k'arfe uku da rabi dai-dai ya gama duk sayyarshi sannan ya nufi masallaci ganin anata haraman sallan la'asar, baya an idar da sallan ne ya kama hanyan gidansu Ishaq wanda shi kuma tun jiya yake zuba idon ganinshi.


K'arfe hud'u saura mai machine ya sauk'eshi k'ofar gidansu Ishaq dake cikin tudun wadan nan layin fad'a,

yana sauk'a ya nufi cikin gidan, 

tare da sallama a ranshi ya shiga. 

Mommy ya samu a tsakar gida mai aikinsu tana mata kitso,

tana ganinshi ta fad'ad'a murmushinta tare da bud'a baki cikin d'aga sauti tace. 

"Wa alaikassalam lale marhabin da Saifudddeen Ishaq ina kake ga amininka ya iso."

shi kuwa gefenta ya rusuna tare da gaita, 

shi kuwa Ishaq da Imaran da Mamansu kusan a tare suka fito, 

yana ganin ishaq ya mik'e ya nufi inda yake yayinda shi kuma ishaq k'amshi turaren Saifuddeen d'inne ke masa jagora,

ruggume juna sukayi lokacin da suka had'u sai kuma ishaq ya sakeshi sannan ya ware hannunshi ya manna bisa fuskan Saifuddeen cikin raha yace .

"Iye iyeh my friend watoma kai azumin nan k'ara maka kyau yayi ka ganka kuwa yadda kayi kyau."

dariya sukayi baki d'aya dan ganin yadda Ishaq yakeyin abu kamar mai gani,

shiko Saifuddeen wayar ishaq ya karb'a tare da rubuta mishi.

"To kanari sarkin zance da wanne idon kaga kyan nawa?."

da sauri ya kauce ganin Ishaq d'in zai kai mishi bugu shi kuwa Ishaq cikin fara'arshi yace.

"To kai da wanne kunnen kaji abinda nace?."

murmushi yayi tare da kuma rubuta mishi amsa a wayarshi da duk abinda aka rubuta sai ta fad'i amman shi kad'ai yake gane irin yadda sautin mgnar ke fita dan ko kanaji bazaka ganeba,

"Ni da idanuna na gane abinda kake cewa."

murmushi yayi tare da kamo hannun aminin nashi yace.

To ni kuma da idon zuciyata da tafin hannuna na gane kyawunka."

daga nan kuma sai suka nufi gaban Mama da taketa binsu da ido tana murmushi cikin fara'a tace. 

"Yoh ai ba damuwa Saifuddeen ta amininka kake ni kam ko ka kulani."

kanshi ya shafa tare girgiza mata kai kana ya tonk'oshe kai alamun afwan Mama, 

daga nan suka gaisa sannan suka shiga parlour Mama nan sukaci gaba da hira suna cikin hira Mama ta fito daga bedroom, 

wani d'an k'aramin kwali mai kyau ta mik'owa Saifuddeen, wanda ya zubawa kwalin idanu cike da mmki ya kalli Mama da take ce mishi.

"G...!







                                     By

                      *GARKUWAR FULANI*

8


              *NAKASA BA KASAWA BACE*



                              *PAGE 8*



                                  NA

               *AYSHA ALIYU GARKUWA*


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


  

_Wannan shafin shima Sadaukarwa ne ga Umar ibrahim Wambai fatan al'khairi da addu'ar samun lagiya a gareka da dukkan masu larurar jinya cuta ko wacce irice._


*Jinjina da fatam alkhairi tare da tarin godiya mai ɗimɓin yawa ga ƙungiyar Nakasassu ta jihar Gombe, joint national  association of persons with disabilities. Gombe state chapter. All the best!!!!.👍🏻 (Jonopwd)  ina godiya a gareku bisa samun goyon bayanku da bani ƙarfin guiwa da karsashin akan rubuta wannan littafin nawa ,ngd matuƙa da yabawarku gareni*


_Ina mai baku haƙuri masoyana masoyan littafaina, dan Allah duk masu turo min hoton katin mtn da suke saya dan biyan kuɗin karanta littafi pleees ba hoton zaku turo minba numbers ɗin zaku rubuto ku turomin ku ɗan hutar dani aiki, sannan masuyi min transfer ɗin katin etisalat dan Allah ku bari. Katin mtn zaka/ki turo min na 300 kacal a wannan number 09097853276 kuma dashi nakeyin whatsapp, ko kuma ku yuro ta asusuna 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa sai ka/ki turo min shaidar biyan naki ta wannan number dai har lau 09097853276. Dan Allah banda kira bana son kira, sai dai in kayan mata kikeso to nan ki kirani, masoyana na Niger ga number da zakuyiwa magana ita zata gaya muku katin da zaku tura +22788137740 500CF zaku bada. Dan Allah masu taɓayata tsoffin littafaina ku bari,nima bani dashk ku nema a gruops zaku samu_




 "Gashi wannan inji Yayanku yace a kawo maka."

ido ya zubawa Mama kamar bai gane me take fad'a mishiba, 

Ishaq kuwa hararanshi ya d'anyi da idanunshi da in ka gansu zakayi zaton masu ganine,

mik'a hannunshi yayi da lalube ya amshi kalin wayar da Mama ke mik'awa Saifuddeen tare da cewa. 

"Kawo shi nan Mama shi wannan d'an naki fulaku ne ke damunshi."

mik'a mishi tayi sannan ta koma gefe ta zauna tare da jawo wata leda mai d'an girma ta kuma mik'o mushi,

ganin yadda fuskarta yayi alamun bata son ya mata gardama ne yasashi sa hannu, 

 ya amsa tare da yin murmushi cikin kurma-kurma yayi mata godiya tare sa hannu ya karb'i kwalin wayar  da Ishaq ke mik'a mishi wanda SIM card d'inshi na mtn yana ciki da yana cewa. 

"Dama ai na san halinka kai komai aka baka sai kace baka so har yau baka d'aukeni d'an uwanka ba, 

sai kayi ta nuna min fulaku ni kuma da yake banda zuciya duk abinda na gani a wurin Ummi amsa nakeyi."

amsar woyar yayi tare da yiwa Ishaq d'in alamun to ya isa sarkin k'orafi, 

sai ya kuma kalli Mama tare da mata alamun ta mishi godiya a wurin Ya Rabi'u,

sai ya kuma amshi wayar Ishaq ya rubuta sak'on godiya ya turawa Ya Rabi'u babban yayansu Ishaq kenan, 

daga nan kuma suka nufi d'akin ishaq nan sukayi ta hira.

Suna cikin hira  Saifuddeen ya duba time ganin lokacin salla ya kusane ya sashi mik'ewa ya shiga wonka yana fitowa ya shafa mai tare da canza kaya yasa kayanshi daya cire jiya ya wonke imran kuma ya goge mishi.

Shima ishaq wonkan ya shiga yana fitowa ana kiran sallan magrib, 

suna shirin fita imran ya shigo d'auke da tire yana cike da kayan bud'a baki, 

dabino sukaci sannan suka sha kankana da abarba daga nan suka fito, suka nufi masallacin fadar masarautan Gombe bayan an idar da salla ne kuma suka dawo gida, 

nan sukaci abinci sannan suka zauna suna hira a parlour Mama nan ishaq ya ware mishi d'inkunan da Ya Rabi'u ya musu d'aya riga da wondo ne da babbar riga sai takalmi da hula,

sai d'aya kuma riga da wondo d'inkin zamanin sai boxers and vest guda uku-uku,

sai ledar da Mama ta bashi kuma atampa ce da shadda sunsha d'inki atampar dai-dai Adda Rahma shaddan kuma dai-dai Ummi, 

godiya yayi sosai, 

daga nan ya had'a komai sannan sukaci gaba da hira,

dan yau ana tsumayin ganin wata.

A dukku kuwa su Warisu da Mudassir kamar kullum sukaje sukaci abinci a gidansu Saifuddeen.


Shi kuwa Saifuddeen a Gombe  ganin lokacin sallan isha yayi ne yasa suka fita sukaje masallaci akayi sallan isha rashin samun labarin ganin wata yasa akayi asham d'inma.

Bayan an idar ne sun dawo gida suka shiga parlourn Baban Ishaq zaune suka sameshi yana kallon tv, ganinsu yasa ya maida hankalin shi a kansu, 

cikin nitsuwa suka gaida su nan yayi musu bayanin k'ungiyar su ta nakasassu da yake son su shiga wato (Jonapwd), sosai ya musu bayani ya k'ara da ce musu.

"Shi abu na taron jama'a yanada amfani da fa'ida domin hannu d'aya baya d'aga jinka, 

shiga k'ungiyar yanada amfani domin tamkar taimakekeniyace a gareku dan saida had'in kanku zai zama maganarku zatayi tasiri wa kunnuwan jama'an gari dama gwamnati,

saida had'in kan k'ungiya da zaku samu damar yak'an barace da k'arfafawa mutanenku guiwa ta yadda zaku fahimtar dasu Nakasa ba kasawa bace."

Cikin gamsuwa suka gyad'a kai dan shi Saifuddeen yana gane abinda Baba yake fad'a da matsin bakinshi shi kuwa Ishaq yana jinshi, ganin sun gamsune yasashi ci gaba da cewa.

"Dama naje nayi mgna da shugaban k'ungiyar na mishi bayaninku, kuma na shaida mishi in anyi salla lfy zan kaiku."

still kansu suka gyad'a cikin alamun amincewa,

daga nan yayi musu nasiha da basu k'arfin guiwa daga bisani Saifuddeen yace zai tafi,

nan ya mishi addu'an komawa lfy, 

shi kuwa ishaq ya rakashi parlour Mama ya d'auki kayanshi sannan ya rakashi har woje saida ya hau machine yaja ya tafi sannan ya koma cikin gida. 


Shi kuwa Saifuddeen yana isa kasuwa ya had'a kayanshi duka sannan ya dawo bakin kasuwa inda yasan Salisu zaizo ya d'aukeshi,

bai jima da zuwaba kuma Salisu ya iso daga nan suka kama hanyar Dukku.


To a wannan shekaran dai azumi talatin akayi.

Ranar salla duk al'ummar musulmai kowa da ko ina ana cikin farin ciki,

duk inda ka gibta ido cikin garin dukku zakaga kowa cikin cikar sura da haiba.

K'arfe tara dai-dai akayi sallan idi,

ana idarwa Saifuddeen da abokanshi da suke cikin shiga iri d'aya suka kama hanyar gida,

kasan cewar sun canza hanyar komawa ne yasa suka fito gab da k'ofansu Saminu, 

dan haka nan suka shiga suka gaida iyayen Saminu daga nan suka shiga parlour Hajja Mama mahaifiyar Saminu, 

inda k'anwarshi Sakina tayi ta jero musu abin ci da sha, 

nan suka zauna suka d'anci, 

suna fitowa gidansu Saminu suka wuce gidansu Warisu.

Dalinshi tana ganinsu tai ta farin ciki tare da sa musu al'barka nan ta kawo musu fura da nono, sunsha nonon sosai daga nan suka fito suka shiga gidansu Mudassir nan suka samu ya Adnan ya dawo jiya da dare,

yana ganinsu yace.

"Iye Umma zo ki ga 'yan samarinku, wlh yarannan sun girma sosai fa kalli duk sun kusa kamoni tsawo fa."

Bud'a kafad'u sukayi tare da had'a baki sukace.

"Kai Ya Adnan mun kamo ka dai kawai zaka ce."

Umma dai sai murmushi takeyi, 

shi kuwa Adnan kamo hannun Saifuddeen yayi tare da cewa.

"Duk baku da kunya Saifuddeen ya fiku mutunci, dan ku gani kuke kunma fini."

sai ya kuma kalli Ahmad dake tsare fuska cikin raha yace.

"Kai Ahmad me na had'e fuska haka?."

tab'e baki yayi tare da cewa. 

"Au ashe dai baka mance niba ai wlh ya Adnan baka da kirki, kullum Dada sai tayi cekiyarka in taga Mudassir tace wato kai kam tunda Ya Nuruddeen ya rasu ka yanke zumuncin dake tsakani."

da sauri ya juyo ya kalli Ummanshi dake cewa.

Ai wlh shi Adnan sam baida k'afa dama Nuru shike sashi ziyara, 

kullum in yazo sai nayi ta binshi yaje amman sai ya zama ko fitan baya so."

da sauri ya katsesu tare da cewa. 

"Kinga ko Umma wlh yanzuma niyata shabewa zan tafi dan wlh nima kaina nayi kewan goggo Dada tun rasuwar Abba ban kuma ganintaba."

shi dai Saifuddeen baibi ta kansuba, 

shiko Ya Adnan bayan sun shiga d'akin Umma ne shi kuma ya fita. 


Kai tsaye gidansu Saifuddeen ya nufa, 

yana shiga ya samu Ummi a tsakar gida cikin shiga ta salla, 

tana ganinshi ta fad'ad'a fara'arta cikin jin dad'i tace. 

"Lale marhabin da Ya Adnan yaushe a gari mutanen Zaria."

cikin sakin fuska ya zauna bisa taburmar data shimfid'a mishi cikin sakin fuska yace. 

"Jiya da dare ne Ummi shiyasa ban shigoba."

gyara zama tayi tare da cewa. 

"Ayyah sannu da hanya."


"Yauwa sannu Ummi ya gida yasu Saifuddeen ina auta Hayatuddeen."


juyawa ta d'anyi ta kalli k'ofar d'akin Rahma cikin d'an d'aga murya tace. 

"Auta ga Ya Adnan d'inku."

jin haka yasa Hayatuddeen fitowa da sauri,

 ita kuwa Ummi juyawa tayi ta kalli Adnan tare da cewa.

"Yanzu ya dawo idi shida Faruq to wai zai tafi shabewa wurin Goggo Dada da yake Adam da Raliya suna can shiyasa suketa d'okin zasu tafi can."

shi kuwa Hayatuddeen yana zuwa ya ruggumi Adnan yayinda Faruq ke bayanshi da sauri ya iso ganin Adnan na mik'o mishi hannu ruggumesu yayi baki d'aya yana jin tausayin yaran da k'aunarsu yana tuno irin so da k'aunar da Nuruddeen ke musu.

ita kuwa Ummi cikin sanyin sautin da ganin Adnan ya tuna mata d'anta ta kalli Rahma da yanzu ta fito ganin Adnan ne yasa ta koma cikin d'aki da sauri, 

jin muryar Ummi na cewa. 

"Rahma fito mana kizo ki kawo mishi abinci."

cikin sanyin murya tace. 

"To Ummi bari insa hijabi."

daga nan sukaci gaba da hira, 

cikin kula Ummi tace. 

"Ya karatu yanzu kam ka kusa gamawa ko?."

gyara zama yayi tare da cewa.

"Alhamdulillahi Ummi ai nama gama."

cikin jin dad'i tace.

"Alhamdulillahi nayi farin ciki Allah ya taimaka ya baka aiki cikin sauk'i."

ido ya lumshe ganin Rahma data rutsuna gabanshi, 

sai ya kuma kauda kai daga gareta tare da sauk'e numfashi kana ya kalli Ummi tare da cewa.

"Amin Amin Ummi aiki kam ya samu ma da yake karatun likitanci ne samun aikin ba wuya, 

next week zan koma gombe dan na samu gurbin aiki a medical senta gombe harma sun bani gidan zama a can a jerin gida jen ma'aikatan su."

Sosai Ummi tayi farin cikin wannan labarin, 

daga bisani ta tashi taja hannun Hayatuddeen da Faruq da tace.

"To muje in had'a muku kayanku, 

kai Auta baka ganin girmanka sai kayi ta zama jikin mutane."

murmushi yayi tare da zaro kud'in 'yan ishirin-ishirin ya bawa Hayatudden guda goma hakama Faruq aifa nan sukayi ta tsalle suna murna, cikin had'a fuska Rahma tace. 

"Baku iya godiya bako?."

da sauri suka juyo tare da cewa.

"Ya Adnan mun gode Allah ya saka ya k'ara bud'i."

Amin Amin yace,

tuni su kuma sunbi bayan Ummi, 

shi kuwa Adnan idonshi ya d'an lumshe tare da sa yatsunshi biyu ya d'an ja jelan kitson Rahma dake har bisa kafad'unta, 

da sauri ta d'an juyo tare da cewa. 

"Wash Allah na ya Adnan zafi."

girarshi d'aya ya d'aga mata tare da cewa. 

"Raguwa kawai."

ido ta lumshe da sauri jin yana cewa. 

"Kinji na gama karatu har na sama mana aiki, 

bakice komaiba."

idon ta ta d'an bud'e tare da cewa.

"Nayi mana addu'a ai ya Adnan."

gyara zamanshi yayi ya kalli gefe ganin Ummi ta fito zata shiga d'akinta cikin yin k'asa da murya yace. 

"Kinga sauran burinmu na gaba, 

yanzu dai na kusa in baiyana kaina gaban bappa Ali ya aura min ke in rik'e 'yar k'anwata in sata farin ciki."

da sauri ta kuma rufe ido, 

shi kuma sai ya d'an d'aga murya tare da cewa. 

"Yunwa fa nakeyi bani abinci inci."

hararanshi ta d'anyi sannan ta zuba mishi abincin ganin zai fara cine yasa ta yunk'ura zata tashi, 

sai kuma ta koma ta zauna jin ya kamo hijabinta, 

dole ta zauna suna d'an hira yana cin abinci.

har saida ya k'oshi sannan yace.

"Nafa yi amarya."

ido ta d'an zaro alamun tambaya, 

murmushi yayi tare da cewa. 

"Bafa amaryar da za'ake konciya da ita a gadoba machine ne kasia na saya mana."

cikin jin kunya tace. 

"Masha Allah, nayi farin ciki."

juyawa yayi ya shiga d'akin Ummi kud'i ya zaro yan d'ari-d'ari rafan dubu uku ya mik'awa Ummi, 

amsa tayi tare da sa mishi al'barka ta kuma yi godiya,

daga nan ya fito tare da cewa su Hayatuddeen su fito ya kaisu gidan goggo Dada aifa da murnarsu suka fito,

suna fitowa Raihana kuma dake k'ofan bappa Ali tana taya Aunty Nina kirba fura itama ta fito nan tace zata bisu,

nan take ta shirya suka fita suka nufi shabewa.


Su Saifuddeen kuwa ranan sun zazzagaya gidan yan uwa da abokan arzik'i, 

sai bayan sallan magrib suka dawo gidan Ummi inda dama sukace tayi musu miyar kuka da tuwon semo wai sun gaji da cin kayan maik'o,

aifa sukaci sukayi hanik'an,

har sha d'aya na dare Ahmad yace shifa zai koma aiko sukace yasin bazasu rakashi ba, 

dole Salisu ne ya maidashi.


Ishaq kuwa ranan wuni yayi yana zura idon ganin Saifuddeen,

yayi ta gwada kiranshi kuma woyar tashi bata shiga, 

haka ya hak'ura ya kwanta da niyar gobe da sassafe zai tafi dukku.


 Washe gari kuwa  Saifuddeen yayi kolliya na gani na fad'a  dan zaije gidan Abokan Abbanshi Baba Hamisu kakansu Faruq kenan da kuma Malam Ashiru,

yana gama kimtsawa ya d'auki turare ya feshe jikinshi dashi kayan sunyi matuk'ar mishi kyau shida Hayatuddeen da Ahmad ne wanda Ahmad d'inne ya d'inka musu shi, 

yad'in voyel ne mai ruwan madara yadin mai gidan dara-dara, sai surfani bak'i da akayi aikin d'inkin, 

sai kuma takalmi bak'i mai ratsin fari da hula zanna bukar bak'i da ratsin farin,

sosai kayan sukayi d'as da jikinshi yayi wani irin mashahurin kyau da korjini.


Pillows inshi ya d'an d'ad'ad'aga alamun yana duba abu,

sabuwar woyarshi ya d'auka sannan ya fito ya nufi d'akin Ummi yana kunna woyar,

gefen Ummi ya zauna wacce take shan fura da nono mai sanyi.

da sauri ta mik'a mishi kofin kai ya jingina da gado kana ya amshi kofin, 

kurb'a ya d'anyi sannan ya fara rubutu a woyar da tun randa ya dawo daya sata a caji ta cika ya cireta ya ajiye bai kuma bin ta kantaba sai yanzu,

rubutu yayi sannan ya nuna mata fuskar woyan. 

"Ummi zanje in gaida su Baba Ashiru kuma zan isa gidan Baba Hamisu ma, kuma ya kamata inje dasu Faruq da Hayatuddeen,

gashi kuma suna gidan Goggo Dada."

bayan ta karanta ne ta d'an gyara zama kana tace. 

"To kaje ka cewa Salisu ya d'aukosu mana."

kai ya gyada cikin gamsuwa daga nan yasha fura da nonon sannan ya fita yaje ya gayawa Salisu, cikin k'ank'anin lokacin Salisu ya d'aukosu.


Bayan sun dawo ne ya tasasu a gaba suka tafi Katafila inda nan gidan Baba Ashiru yake,

suna shiga matarshi ta tarbesu a mutunce bayan sun gaisane tace su isa yana k'ofanshi tare da abokanshi

nan ya tasa keyarsu Hayatuddeen suna isa suka samesu a harabar wurin yana tare da abokanshi a ciki harda Malamin isilamiyar su Saifuddeen, 

yana ganin Saifuddeen ya saki murmushi tare da cewa.

"Masha Allah Saifuddeen d'alibina, yanzu kuwa  nake mgnarka."

da sauri ya isa inda suke cikin girmamawa ya basu hannu duk ya gaidasu d'aya bayan d'aya,

Baba Ashiru kuwa rik'e hannun Hayatuddeen yayi yana shafa kanshi, 

shi kuwa Malaminsu Saifuddeen cikin iya mgnar kurame yayi ta tambayar Saifuddeen bayan rabuwa nan yake sanarwa Saifuddeen shima ya k'aura ai yanzu baya Dukku jiya da yamma yazo dan ziyartan 'yan uwa da abokan arzik'i,

hira sukayi sosai dan Malamin nasu yana tsananin son Saifuddeen dan ya yarda da tarbiyarshi tun yana ji gashi yasan yaron yanada tsananin ilimi da fahimta.

koda suka tashi tafiya sai Saifuddeen ya d'an sunkuyo kud'i ya zaro a aljihunshi 'yan d'ari bibbiyu kimanin dubu bakwai dubu biyu ya ware ya ya ajiye a gaban Baba Ashiru sannan ya kuma zaro dubu biyu ya ajiye a gaban Malamin nashi ya kuma ajiye a gaban d'aya abokin nasu dubu biyu kana ya maida dubu d'aya cikin al'jihunshi,

kusan a tare suka had'a baki wurin cewa.

"A a haba dai Saifuddeen in bamu baka ba ai baza mu karb'a daga gareka ba."

kai ya rink'a jujjuya musu alamun dan Allah kada suk'i amsa su karb'a su samishi al'barka.

Cikin sanyi Baba Ashiru yace. 

"Deen ai sai ka sani jin kunya ni ya cancanci in taimaka muku, amman na gaza sabida lamarin yau da gobe ya hana."

kanshi ya rinka jujjuyawa alamun kada yak'i karb'an kud'in, 

sai ya kuma kalli Malamin nasu dake cewa. 

"Kud'in sunyi yawa ai Deeen."

wayarshi ya d'an zaro yayi rubutu kana ya bawa melanin nashi wayar, 

amsa yayi tare da fara karantawa yana karatun yana murmushi cikin dottaku yace. 

"Bodd'i ta girma ai yanzu ta bar kukan zuwa makaranta ta daina genged'i in zata bada hadda,

to ta gode niko zan saya mata sweet dan har yanzu tana nan da son shan zak'i tunda ka koya mata."

murmushi Saifuddeen  yayi tare da nuna Hayatuddeen yayi alamun tambaya ko ta kai Hayatuddeen d'in tsawo, 

da sauri ya gyad'a mishi kai tare da cewa. 

"wai ai tafi Hayatuddeen tsawo yanzu kusan shekaru biyar fa rabonka da ita tun randa ka bar zuwa Islamiya, nima tunda ka fara spacial education ban kuma ganinkaba saida ka gama daka gama d'inma sai rasuwar Abbanku na kuma ganinka."

murmushi yayi kana yayi alamun a gaidata daga nan ya sallamesu ya tafi.


Kai tsaye gidan Baba Hamisu ya wuce dasu Faruq,

 bayan sun gaisa ne ya bashi sauran dubu d'ayan nan sannan ya bar Faruq da Adam anan dan suyi d'an kwana biyu. 


daga nan ya tasa keyar Hayatuddeen suka nufi gidan su Aunty Nina dan yi musu gaisuwan salla, 

suna fitowa yaji alamun saqo ya shiga woyarshi dake cikin aljihunshi,

yana dubawa kuwa yaga sak'on Ishaq ne yana ce mishi yazo Dukku fa gashi ga Ummi, 

so jin haka yasa suka kama hanyan gida.

 Yana shiga ya samu suna zaune a tsakar gida bisa taburma, 

Ishaq sarkin surutu sai hira suketayi da Ummi da Adda Rahma, 

suna shiga imran yayi sauri ya mik'e yaje ya ruggumi Saifuddeen tare da cewa. 

"Oyoyo Hamma Saifuddeen yau kam nima nazo gidanku, Umminka ta bani fura da nono nasha."

kanshi ya shafa tare da jinjina mishi,

 Hayatuddeen kuwa tuni ya isa jikin ishaq sunata surutu dan duk masurutane, 

Ummi da Rahma kuwa sai murmushi sukeyi, 

yayinda Ishaq yake cewa Hayatuddeen.

"Yauwa Autan Ummi kaga yau na kawo maka abokinka imran autan Mama."

da sauri Hayatuddeen ya juyo ya kalli Imran tare da cewa. 

"Shima autane?."

cikin dariya ishaq yace. 

"Eh shima autane kuma sakali irinka."

aifa daga nan Hayatuddeen da imran suka d'inke dan sakalcinsu iri d'aya  ga tsawonsu dai-dai.

ranan Ummi da Ishaq da Saufuddeen da Adda Rahma da Aunty Nina tare suka wuni koda yamma tayi Ishaq yace dole Saifuddeen ya rakashi Shabewa dan zaije ya gaida Goggo Dada ya kuma ga Raihana da Raliya dan yayi missing d'insu, 

aifa haka suka d'unguzuma da su Saminu da dama yake son bin bayan 

Raihana nan sukaje suka gaida Goggo Dada,

daga bisani suka dawo dole Ummi tasa Ishaq da Imran suka kwana.


 Washe gari suka tafi da Saifuddeen. 

saida yayi kwana biyu  a gombe sunje gidansu Jabeer da Hisham har gidansu Ibrahim duk sunje, kana Baban Ishaq ya tasasu gaba shida kanshi ya kaisu k'ungiyar (Jonapwd)  nan take sukayi duk abinda ya kamata na shaidar suna cikin members d'in k'ungiyar. 

Daga nan suka ziyarci abokan su da suka yi makaranta d'aya. 

Sannan ranar da zai koman yaje ya wuni a kasuwa dan hutun salla ya k'are. 

to a ranar ya tambayi Alhaji Aliyu gidan baba Bello ina yake, 

to cikin sa'a ya samu Alhaji Aliyu da kanshi ya d'aukeshi sukaje gidan Baba Bello dake cikin jeka da fari, 

nan suka samu ashe baida lfy shiyasa tunda akayi salla bai dawo kasuwa ba,

yayi farin cikin ganin Saifuddeen sosai bare da Alhaji Aliyu ya yaba mishi nagartan Saifuddeen d'in, 

shi kuwa Saifuddeen wannan 10k d'in ya zaro ya bashi ya yace ya nemi mgni sannan ya d'anyi cefene, 

yayi godiya sosai hakama matarshi Inno sunji dad'in sosai,

sannan yace ba matsala Saifudddeen yaci gaba da kasuwancin shi, sai in Allah yasa ya samu lfy, in ya dawo sai suci gaba da kasuwancin.


Da haka dai sukayi sallama suka tafi.


 Tun daga ranar Saifuddeen yaci gaba da kasuwancin sa ba kama hannun yaro, sosai fa harkan leda ta amsheshi harkalla taci gaba, ya k'ara sabawa da mutane sosai, 

duk sati yakan ware ribar kwana biyu ya yiwa baba bello sayayyan kayan abinci, 

na dubu goma sannan ya bashi dubu biyu ya rik'e wannan abu yasa sam Baba Bello bai kuma sha'awan komawa kasuwancinsa ba tunda yanaga ya huta da wahala kuma ya lura hannun Saifuddeen yanada al'barka duk abinda ya kama yana cin gaba.


Shi kuwa Saifuddeen ribar kwana biyar d'in yake had'awa yayi sayayyan abincin gidansu to zai yi mako biyu kuma yana saka ribanshi a asusu,

riban omonshi kuwa da pure water daya ya koma sai yake ajiyesu dan hidiman yau da kullum.


Ya Adnan kuwa tuni ya fara aikinshi gadan-gadan shida Dukku sai dai ziyara. 

Tuni Mudassir ma yaci gaba da karatunshi a G.S.U inda a gidan Adnan d'in yake zama, 

Ishaq ma tuni yaci gaba da karatunshi.

Hakama Saminu shima yayi nisa a karatunshi.


Salisu ma yanzu ya ci gaba da kanshi sabida Saifuddeen ya rege mishi kud'in balance sosai to sai in bashida darasi yake fita aiki dan ya samu damar yin hidimomin karatunshi da kula da kakarshi.



Hayatuddeen kuwa tuni ya fara koyan d'inki a wurin Ahmad da shima yanzu yanata cuku-cukun ci gaba da karatunshi inda yake son kafin ya koma cikin gombe Hayatuddeen ya gware a d'inkin,

shi kuma sai ya tafi da kekenshi zaije yaci gaba da karatu, 

duk cikinsu Saifudddeen ne da Warisu sune basu samu daman ci gaba da karatun suba.


Sai dai shi Saifuddeen tuni ya samu ya gamawa Raihana da Raliya cuku-cukun karatunsu tuni ma Raihana kam ta k'are secondary school.


Yanzu hankalin Ummi ya fara konciya, 


Tuni Ya Adnan kuma ya baiyana soyayyarshi da Rahma amman biki yace sai next year kowa yayi farin ciki da haka. 


Koda Ahmad ya koma gombe gidan ya Adnan d'in shima ya zauna.



Kasuwa tayi al'barka kullum Saifuddeen baya fashin zuwa shida Salisunshi,

yana zuwa zai rarraba leda sai ya d'auko omonshi bisa kai sannan ya rik'o botikin pure waternshi dasu Coca-Cola yayi ta yawatawa kuma Alhamdulillahi sosai yake ciniki Allah ya sawa kasuwancin nashi al'barka.


Kota ina yanzu an sanshi a kasuwar gombe. 


Yanzu duk kostomominshi suna da number shi yanada number su, 

duk mai buk'atan kaya zai kirashi ya kai mishi misali in ledodin su ya kare suna son k'ari ko in suna son abin sha mai sanyi ko omo to kawai sai su mishi text.

Zuwa yanzu duk abo kanshi suna da woyoyinsu.


Yau jumma'a tunda sanyin safiya da suka shigo ya gama reba lododinshi har ya d'auko omonshi da da kayan sanyinshi yanata zagayawa.


K'arfe d'aya dai-dai na rana ya shiga bakin shagonsu Jabeer ya d'an zauna dan abin sanyinshi ya k'are kuma ya gaji shiyasa ya zauna dan ya d'an huta kafin ya d'auko wani, 

sunata d'an tab'a hira da Jabeer

bai jima da zamanshi yaji wayarshi na babureshin cikin al'jihunshi na k'irjinshi alamun sak'o ya shiga, a  hankali yasa hannunshi ya zaro wayar,

yana dubawa yaga Alhaji Kabiru ne mai shagonsu Mai, Manja, Maggi, kafi, da dai sauranshi.

Bud'e sak'on kana ya karanta sak'on.

"Saifuddeen kawo mana ruwa mai sanyi da molt guda hud'u sai fanta d'aya."

amsa ya maida mishi cewa. 

"To gani nan zuwa."

daga nan ya mik'e tare da zaran botikin,

cikin sabo Jabeer yace.

"Allah ko Balarabe wlh ka rink'a hutawa fa."

kai ya jinjina mishi tare da mishi alamun ai.

"Me nema baya gajiya in dai yana samun d'an na kashewa a sama."

daga nan ya juya ya tafi. 


Koda yaje ya ciko botikinshi da kayan sanyin kai tsaye ya nufi shagon Alhaji Kabiru. 

Yana zuwa sai ya samu suna can cikin shagon bisa dukkan alamu bak'i yayi kuma manyane masu cikar haiba.


Amir ne d'aya daga cikin yan gidan shagon Alhaji Kabirunne ya kalli Saifuddeen tare da cewa. 

"Yauwa Balarabe tsallaka ka shiga can ciki yana tare da manyan bak'i ne su zaka kaiwa ruwan sanyin. 

jin haka sai ya tsallaka ya shiga, 

kai tsaye gefen da suke ya nufa,

yana isa Alhaji Kabirun yayi murmushi tare da cewa. 

"Yauwa Saifuddeen balarabe, bamu ruwan sanyi Faro roba hud'u da molt roba hud'u sai ka mik'o min fanta d'aya kasan ni nafi son fanta."

cikin girmamawa fuska k'unshe da murmushi ya matso ya mik'a mishi fantan kana ya rusuna gabansu ya fara zaro gorunan Faro dana molt.

Yayinda tuni idanunshi yana kan d'aya daga cikin bak'in inda yake cewa. 

"Gsky Alhaji Kabiru in dai kanada daman saran wannan kaya to wlh ka zuba jarinka domin kamfaninne ya kawo mana talla har gida, 

sun bamu tabbacin tabbas akwai riba mai tarin yawa, 

to ni kuma naga bazan iya yin harkallan ni d'aya ba."

ci gaba yayi da kallon bakin mutun tare da mik'a mishi roban Faro,

still yana kallon bakin mutum inda yake cewa. 

"Koda bashi ne kaci muyi sarin nan in sha Allah zamuji dad'in hark'allan."

sai kuma ya juyo ya kalli d'aya daga ciki wanda ke cewa. 

"Ni kaina last week nayi sari yanzu hakama bani da kud'i kuma wlh bashi zanci dan nasan in sha Allah zamu samu riba."

d'aya daga cikin sune yace.

"Kai bani ruwan nan zansha ka tsaya kana kallon bakin mutane."

Alhaji Kabirun ne yayi d'an murmushi tare da cewa. 

"Alhaji Sani ai wannan yaron irin Isma'il nane kurmane baya ji."

jin haka yasa wanda aka kira da Alhaji Sani ya d'an tab'a Saifuddeen tare da mishi alamun ya bashi ruwan, juyowar da zaiyi ne yayi dai-dai da lokacin da Alhaji Sani yayi wata mgnar da ta sa Saifuddeen  t...! 







                              By

                   *GARKUWAR FULANI*



           *NAKASA BA KASAWA BACE*


                                *PAGE 9*


                                    NA

                  *AYSHA ALIYU GARKUWA*


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇




    _Ga masu buƙatar sayan littafin Nakasa ba kasawa bace, turo katin mtn na 300 kacal ta wannan number 09097853276. Ko kuma ka/kiyi min transfer ta asusuna 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ka/ki turo screenshort na shaidar ka/kin biya_



~Wannan shafi nakune mutanen Group ɗin Nakasa ba kasawa bace fans two ina al'fahari daku~


Free page




Tsurawa fuskokinsu ido cikin hikima yake nazartan zantukan da sukeyi, 

wanda ya rasa madosar zancen, 

mik'ewa yayi a hankali ya fara nad'e gammon da yake sawa a kanshi kafin ya aza kwalin omon,

yana mai ci gaba da nazartan kalaman wanda aka kira da Alhaji Sani yana cewa.

"Nan da wata biyu zasu rufe sararwan,

dan haka muyi k'ok'ari mu samu mu sari koda kad'an-kad'an ne, 

Company ya talla ta mana ne dan sanin mune manyan costumes d'insu na nan jihar Gombe, 

sun kuma bani tabbacin tabbas nanda wata hud'u Maggi zaiyi tsada sosai kusan ninka kud'inshi zaiyi,

domin ya bani misalai da dama, 

sun kuma ce wannan damace da aka bawa kuduncin Nigeria, to shiyasa suma musulmanmu suka nemi da a bawa arewacin Nigeria samun wannan garab'asar dan sanin arzik'in musulmi yanada fa'idoji da dama."

d'aya daga cikin sunne ya kuma cewa. 

"Ni kam in sha Allah zan k'ok'arta in samu koda kad'an ne."

gyara zama Alhaji Kabiru yayi tare da zaro kud'i yana mik'awa Saifuddeen yayinda hankalinshi ke kan abo kan nashi, 

cikin nitsuwarsa yace. 

"To zanyi k'ok'ari inga ko zan samu wasu 'yan kud'ad'e na da nike bin bashi sai in sa hannu a ciki."

cikin farin ciki sukace. 

"Alhamdulillahi to Allah yasa ka samesu."

Amin Amin yace tare da kallon Saifuddeen da ya juya ya fita zuciyarshi cike da sak'e-sak'e haka kawai yake son yaji tushen zancen.


Su kuwa bayan sun gama tattauna yadda abin zai wakana.

Nan suka sallami Alhaji Kabiru suka tafi.


Saifuddeen kuwa yana fita yaci gaba da zageyenshi na tallan omo da kayan sanyin nashi,

bai fito kasuwarba har k'arfe shida na yamma dan tunda azumi ya wuce suka dawo kamar da sai bayan sallan isha suke komawa.


Yana fitowa yayi al'wala yayi sallan magrib yana fitowa ya samu Salisu na jiranshi, 

daga nan bakin Al'kasim suka tsaya nan suka d'anci abinda ya sauwak'a sannan suka wuce Dukku.


Bayan kwana uku da zuwan su Alhaji Sani wurin Alhaji kabiru suka kuma zuwa, 

kan su jaddada da mishi batun kadafa ya d'auki abun a shirme ya dai ce musu yana nan yana tabin wad'anda yake bin kud'in.


Iya bukku kuwa ,tun randa suka koma ko mai sunan Saifuddeen taji an kira sai gabanta ya faɗi.

A cewarta ba ita ba dukku har gaban abadan, dannan wannan kurman matashin daya zubda mata haƙora biyu a karonsu na forko. Tofa tabbas in antayi artabu dashi a karo na biyu kanta zai sare ya bata a tafin hannunta, Goggo Ummi kuwa da Bappan ta sunji daɗin hakan a ransu, kuma sunada niyar sake ziyartarsu.


Yau tunda Saifuddeen ya gama raba ledanshi kana ya yawata da tallanshi har la'asar bayan anyi salla ne ya nufi gidansu Ishaq dan sunyi dashi zaije su Ahmad da Saminu da Mudassir ma duk sunyi dasu zasuje dan sun kwana biyu basu had'uba,


Hud'u dai-dai duk suna had'e a d'akin Ishaq yayinda gari yayi duhu sabida tasowan hadari, 

Mama kuwa tuni tai ta musu hidima dan dama sun ce mata danbun zogale sukeso, 

nan suka zube suna hira sunaci, 

Ahmad ne ya kalli Saifuddeen da yayi shiru alamun nazari had'iye abincin bakinshi yayi sannan ya kalli Saifuddeen tare da cewa. 

"Saifuddeen kaci dambun mana."

Kai ya jujjuya mishi alamun bazai cima,

cikin kula yace mishi.

"Meyasa bazaka ciba?."

Mudassir ne ya d'auki ledan pure water ya b'ula kana yashanye fiye da rabi sannan ya kalli Ahmad tare da cewa. 

"Ka manna Saifuddeen da zab'en abinci ai baicin dambu."

jin haka yasa Ishaq mik'ewa tare da cewa. 

"Yes haka nefa kaga ni nama mance bari inje in gayawa Mama tayi mishi d'anwake  dan na lura yana son abincin mata."

dariya sukayi baki d'aya sannan ya fita, 

Saminu kuwa gyatsa ya d'anyi tare da cewa. 

"Au ashe dama d'an wake cimar matane?."

kai Saifuddeen ya jujjuya mishi alamun a a kam. 

fitan Ishaq ba jimawa sai gashi ya dawo nan sukaci gaba da hira. 

Bayan kamar awa d'aya da rabi sai ga Imran ya shigo da tire,

kai tsaye gaban Saifuddeen ya ajiye, 

sannan ya juya ya fita, 

shi kuwa Saifuddeen tiren ya jawo wanda aka cika d'an madaidaicin pilet da d"anwake sai dafaffan kwai guda uku a sama sai mai da magi da yaji,

nan ya fara ci sosai yaji dad'in d'anwaken, 

Mudassir ne ya kalleshi tare da cewa. 

"Oga ba tayine?."

hararanshi ya d'anyi tare da nuna mishi kulan dambun cikin mishi alamun kunci nabanku. 

Ahmad kuma tab'e baki yayi tare da cewa. 

"Ahab barshi da d'anwake ko rabi nai bazai ciba zaice ya k'oshi, sai dai ka ganshi yana ture pilet d'in."

ana cikin haka Allah ya sako iska mai sanyi wanda yake nuni da hadarin ya watse lokaci d'aya gari ya washe.


Shi kuwa Saifuddeen baici rabinba ya ture pilet d'in kana ya mik'e ya shiga bathroom,

nan sukayi ta mishi tsiya wai yana nan kamar kifi,

wonka yayi yana fitowa ya bud'e durowan Ishaq ya canza kaya sannan ya kallesu tare da musu alamun shi zai tafi,

sai ya kuma kamo hannun ishaq tare da mishi alamun ya tafi, 

nan suka mik'e duk suka fita  daga nan duk suka salami juna. 


K'arfe 11:15 pm Saifuddeen ya mik'e tsaye tare da ninke sallayan da yayi sallan shafa'i da wutiri, a kanshi  

bakin katifarshi ya zauna tare da yin addu'a ya shafa a jikinshi sannan ya kwanta ta b'arin dama. 

Can misalin k'arfe biyu dai-dai ya farka bakinshi d'auke da addu'a, 

a hankali ya bud'e idanunshi yana mai tuno mafarkin da yayi, 

salati ya kumayi ya sanarwa mahaliccinshi, 

jingina yayi da jikin pillow sai ya kuma lumshe idanunshi tare da son nazartan mafarkin nashi, 

sai ya kumayi saurin bud'e idanun nashi  dan ganin abin ya dawo mishi tamkar yana ganinshi a majigi, 

a hankali ya mik'e ya fito tsakar gidan nasu inda ya samu ashe anyi musu ruwan sama kamar da bakin gwarya,

cikin nitsuwa ya wuce bandaki fitsarin da ya matseshi yayi sannan ya fito bakin barandan k'ofan d'akinshi ya tsuguna yayi al'wala sannan ya mik'e ya shiga d'akin kana yayi ta nafilfilinshi.


Washe garin da rana irin rana tayi fed'e-fed'e d'innan lokacin gari ya d'anyi zafi sai inuwan gajimare kad'an-kad'an, 

sosai ya saida kayan sanyin koda ya gama kafa na uku, sai ya wuce shagon su Jabeer nan sukayi ta hira har aka kira salla bayan sunyi salla kuma sai ya wuce shagon Alhaji Kabiru yana isa ya samu yaran shagon duk sunata hidiman jera kayayyakinsu bisa dukkan alamu sarin da sukayi ne ya iso,

shi kuwa Alhaji Kabiru yana cikin shagon bisa alamu lissafi yakeyi, 

ganin haka sai Saifuddeen ya tsallaka ya shiga ciki can kusa da shi ya zauna cikin body language ya gaida Alhaji Kabiru da tuni ya gama lissafin ya had'a takardun wuri d'aya, 

cikin mutuntaka da dattaku ya amsa gaisuwar Saifuddeen,

sai ya kuma kalleshi ganin yana mishi alamun tambyar ina woyarshi, 

murmushi yayi tare da cewa.

"Wayata gata a aljihuna."

kai ya jinjina mishi kana ya mishi alamun ya fitar da ita zasuyi mgna,

gane hakan ya sashi zaro woyar,

daga nan ya suka fara mgna ta inbox nasu suna musanyan text messages,

sosai Alhaji Kabiru ya nitsu yana kallon text d'in da Saifuddeen ya tura mishi inda yake cewa. 

"Assalamu alaikum, Alhaji ya gida ya kasuwa, 

Allah ya taimaka."

sai ya rubuta mishi amsa da. 

"Wa alaikassalam  lfy lau Saifuddeen, Amin Amin. Naga kamar  muhimmiyar mgna kakeson muyi, kada ka damu ka d'aukeni kamar mahaifinka ni ina ina jinka tamkar Isma'il d'ina."

Sosai Saifuddeen yaji dad'i mgnar hakan ya sashi murmusawa tare da rubuta mishi. 

"Ngd matuk'a Alhaji." sai ya kuma yi shiru bai kuma rubuta komaiba ya rasa ta ina zai faro zancen gane haka yasa Alhaji Kabiru dafa kafad'unshi cikin bashi k'arfin guiwa yace.

"Ina jinka."

shi kuwa rusunar da kai yayi tare da rubuta mishi. 

"Kayi hak'uri Alhaji ka gafarceni ranan asabar d'in da ya gabata, ka kirani na kawo maka ruwan sanyi, inda nazo na sameka da bak'i to nayi laifin fahimtar maganganunku, sai dai kuma  naji ina sha'awar sanin  kasuwancin da suke tallata maka,

in akwai damar da nima zan iya sa hannuna a ciki nima zanyi."

yana tura text d'in sai ya sunkuyar da kanshi, 

shi kuwa Alhaji Kabiru murmushi yayi bayan ya gama karantawa cikin kekyawan fahimta ya dafa kafad'un Saifuddeen wanda ya sashi d'ago kai ya zuba mishi ido alamun jin na bakinshi. 

Gyara zama yayi tare da zuba mishi idanu cikin sanyin sauti alamun yana son su sirranta zancen yace.

"Me zai hana zaka iya mana, ai duk abinda mai ji zai iya na kasuwanci in sha Allah zaka iya,

sai dai kuma fa wannan al'amarin da kamar wuya."

da sauri Saifuddeen ya gyara zama tare da fuskantarshi   yana mai kallon motsin bakinshi ta yadda zai fahimceshi da kyau shi kuwa Alhaji Kabiru cikin tsarkakan zuciya ya fara mishi bayanin kasuwancin. 

"Company Maggi ne suka kawo mana tallan Maggi a sirrance a matsayinmu na manyan dilolin maggi, 

sun tallatama mana ne dan suna mana sha'awar ci gaba, 

sun bamu sirrin company cewa nanda wata biyar magi zaiyi tsadan da bai tab'a yiba, 

sun k'ara da ce mana mu fito da kud'ad'enmu mu sari maggin mu ajiye sun sanar damu cikin wata biyar zuwa bakwai company zai k'ara tsadan magi sun bamu tabbacin in sha Allah babu batun fad'uwa sai dai cin riba, 

in dai bamuci riba ba toko bazamuyi asaraba."

sai ya kuma d'an tsagaita tare da kallon kekyawan fuskar Saifuddeen kana cikin tausayawa yace.

"Tabbas nasan akwai riba dan yar daddunmu ne suka sanar mana dan son ci gaban junanmu, 

to matsalar uku daga cikinmu duk last week mukayi sari bamu da kud'i a k'asa asalima kaga sai yau kayan ya isomu, 

sannan masu zuwa sari su zo su sara wanda yawanci bayan wata d'aya suke dawo da kud'in. 

To da fari company wata biyu suka bada k'a'idar rufe sarin dan kamar bonanza ne  zasuyi mana to sai kuma suka maida k'a'idar wata d'aya.

to shi kanshi uban gidanmu Alhaji Sani wata uku da suka gabata ne ya gama ginin sabon gidanshi inda ya k'aura ya koma yanzu, 

to bashi da kud'i sosai a k'asa da zai ranta mana."

ganin yayi shirune yasa Saifuddeen gyara zamanshi tare rubuta mishi.

"To magin kuma kamar na k'asa da nawa zasu bada sarin?."

Numfashi Alhaji Kabiru ya furzar tare da cewa. 

"To ai anan gizo ke sak'a domin sun san in sukace kad'an-kad'anne da yawa zasu iya sara, 

so sai suka d'an saka hikimar da suma zasu samu wani abu, 

sun bada tabbacin cewa mafi k'arancin sarin da zasu bada shine na 2 million, 

tofa shisa duk jikinmu yayi sanyi da abun."

cikin d'imuwa Saifuddeen ya maimaita 2 million to shi tunda aka haifeshi yazo duniya baima tab'a ganin dubu dari biyar cikakku bama, 

kai ya rink'a jujjuyawa da a zatonshi ko irin d'an sarin 100k ne zuwa 200k nan zai iya zaton zai samesu in ya fasa asusunshi, 

tab'ashi da Alhaji Kabiru yayine ya dawo dashi daga duniyar tunanin daya tafi  kai ya rink'a jujjuyawa jin tambayar da Alhaji Kabirun ya masa cewa. 

"Kanada kud'in sari ne?."

ganin yanata jujjuya mishi kaine yace.

"Shiyasa nace abin da wuya ni du'du du yanzu dubu d'ari biyar nake dashi, 

in samu wanda zamu had'a hannu muyi sarinma abin ya gagara ya rigada yanzu cinikaiya ta d'anyi k'asa, amman kaje kayi shawara in kanada yadda zaka samu 500k d'in kamar nawa sai mu had'a in sha Allah zan samu su Alhaji Sani sai mu had'a da wasu in an samu."

Cikin rauni da sanyi Saifuddeen ya jujjuya mishi kai tare rubuta mishi. 

"Kud'in sunfi k'arfina bani da hanyarsu ko dalilinsu. 

Ngd matuk'a da bani kulawa da shawara naji dad'in yadda kamin kekyawar fahimta."

Cikin kula ya kalleshi ganin yana shirin aza kwalin omonshi a kai alamun zai tafi murya a tausashe yace. 

"Ba komai Saifuddeen wlh ni ina jinka tamkar d'ana na cikina,

na kuma yarda da amincinka, 

muyi ta Addu'a Allah ya bamu sa'a."

A saman labb'anshi ya amsa da Amin Amin kana ya juya ya fita shagon.


Daga nan yaci gaba da tallanci yanayi cikin nasara, 

randa yayi kwana biyu da zuwa wurin Alhaji  Kabiru, da dare ya sake yin wani mafarki ma kamacin wanda yayi ranan, 

sosai abin ya d'aure mishi kai al'wala yayi sannan yayi ta karatun Qur'an washe gari, ana fitowa sallan asuba yaga Sabir k'anin Saminu yazo gaban Bappa Ali inda ya shaida mishi wai babanshine ya aikeshi kan yazo ya gaya mishi yana son ganinshi anjima shida Saifuddeen.

jin haka bai wani damu Bappa Ali ba dan akwai alak'ar zumunci a tsaka ninsu in abi ya shafi na addini to ana nemanshi. 


Sai dai da yaji yace shida Saifuddeen shiyasa ya hana Saifuddeen tafiya cikin gombe yace Salisu yaje kawai shi Saifuddeen yau bazai jeba sai gobe in Allah ya kaimu da haka Salisu ya tafi. 


K'arfe tare dai-dai na safe Saifudddeen da Bappa Ali suka isa fadan masarautan Dukku.

Bayan anyi musu iso suka isa har cikin masauk'in bak'i.

 Cikin mutuntaka suka gaisa da mai martaba da Wazirinshi da sauran wad'anda ke wurin,  

daga bisani Sarkin ya gyara zama tareda murza rawanin kanshi cikin salon mgnar sarakuna  yace.

Malam Ali kunga na aika a kira minku da sanyin safi ko?."

kai Bappa Alin ya gyad'a tare da cewa. 

"Eh shine ma dalilin zuwanmu domin amsa kiranka."

kai ya jinjina cikin salon adalcin sarauta yaci gaba da cewa. 

"To batun dai filin nan naku na Dugge ne da filin yayanka na nan bakin kasuwa shine dai dililin kiran naku yau ma, 

in baka mantaba kwanaki nayi maka mgnar cewar akwai masu son filin walau saya walau haya shi filinku na Dugge d'in sunce su ko haya ne a basu, to da nayima mgna kace min baka da hurumin saida filin domin filin nakune kai da d'an uwanka ne Bello mahaifinsu Saifuddeen ka shaida min cewa yanzu filin na magada ne yaran shi kenan da kai.

To kuma company layin waya na mtn suna tayi mana zirya a gari sabida sun tabbatar mana da cewa, sun samu igiyoyin services a cikin filin naku koda na sanar musu bani da hurumin saida musu filin sabida na magadane to sun kuma dawowa kan cewa ko hayane a basu filin duk shekara zasu rink'a biya, 

nanma na kuma jaddada musu bani da hurimin filin, to sunci gaba da duddubawa cikin garin dukku amman Allah baisa sun samu wani wurinba da zasu samu su kafa na'u'rarsu ta services, 

to shiyasa suka kuma dawowa gareni da neman al'farman a basu hayan filin zasu rink'a biyan kud'i mai tsoko cikin ko wanne shekara,

to ganin sun dameni nace bari in kuma kiranka kaida Saifuddeen d'in in sanar muku sannan kuyi shawara da juna."

ya k'arishe mgnar cikin son jin ta bakinsu, 

shi kuwa Saifuddeen numfashi ya d'an fesar a hankali kana ya zubawa bappa Ali idanu cikin alamun nuna mishi duk hukuncin da ya yanke yayi dai-dai.

gane hakan yasa bappa Ali yin mgna cikin mutuntaka yace. 

"To ba matsala in sha Allah zamuje gida muyi shawara da mahaifiyarsu Saifuddeen d'in da kuma yayarshi Rahma da k'anneneshi dan jin ta bakinsu tunda suma sunada hak'k'i a ciki."

cikin mutuntaka yace.

"To ba laifi, sai naji shawarar da kuka yanke, 

amman nace musu su dawo jibi suji yadda mukayi daku."

Sai ya kuma yi gyaran murya tare da cewa. 

"Yauwa to sai batun filinku na nan bakin kasuwa, 

wanda kace min filin Bello ne mahaifinsu Saifuddeen ka shaida min cewa baka da ko sulai d'aya a kud'in sayan filin, 

to kuma kasan tun last  year hukumar bankin nan na GT bank sukayi ta zirya kan suna son sayan filin dan suna son su bud'a cibiyar bankin nasu a nan dukku, 

to rashin amincewarka yasa suka hak'ura duk da sunyi ta nacin filin, 

a cewarsu wai rigima kuke musu, 

to kaga bayan nan kuma A. A Rano ya buk'aci sayan filin dan bud'e gidan mai nanma kak'i bada fuska, 

dole ya hak'ura yaje ya nema a mashigan hari."

sai ya kuma d'an tsagaita tare da kallon yadda suke zaune cikin kamala da cikar haiba, 

kanshi ya juya ga wazirinshi da Garkuwanshi kana sai sauran tsirarun mutane, 

cikin tattausan lafazi yaci gaba da cewa.

"To fili dai na yaran d'an uwanka ne kamar yadda kasha jaddada min na kuma fahimceka baka son shiga hakk'insu ne ko ince kana gudun kar ka zama sanadin rabuwansu da kadarar mahaifinsu, 

to nima bana son takuraku ko in saku yin abunda bakuyi niyaba, 

to amman ba yadda zamuyi domin wannan filin ya kasance fili mafi girma da daraja gashi a bakin hanya gashi a bakin kasuwa gashi babban filine to wannan dalili yasa idanun manyan masu hannu da shuni ke kan filin dan duk abinda akeso za'a iya yi a wurin, 

hakan yasa tun makon daya gabata hukumar ACCESS BANK suketa yi mana zirya, 

na gaya musu duk yadda akayi a baya to sai sukayi ta k'ara farashin yadda zasu sayeshi sama da yadda sauran suka sayeshi a baya, har ta kai da sun ninka kud'in,

to shiyasa nace bari dai in sanar muku in kun amince la basa in kuma kunk'i amincewa bani da abin cewa, 

sai dai kuma dole ku dage kuyi koda shaguna ne a wurin domin kauda idanun mutane."

jin yayi shiru alamun ya dasa aya ne yasa Waziri cewa. 

"Wannan gsky ne babu dole cikin cinikin, amman kuyi k'ok'arin gine wurin in har bazaku saidaba."

cikin kamala Bappa Ali yace. 

"To ba matsala ai Alhamdulillahi tunda zuwa yanzu Saifudddeen ya girma ya kuma mallaki hankalin kanshi, 

ya kuma ji komai dan haka zamuje gida zamu tattauna duk abinda ya dace, 

kana in mun yanke hukunci zamu zo mu sanar muku, 

amman yanzu sai munje mun sanar da mahaifiyashi da k'annenshi dama yayarshi."

gyaran murya Garkuwa yayi tare da cewa. 

"To ba matsala muna jiranku sai munji shawarar da kuka tsaidan."

Shi kuwa Saifuddeen wani kekyawan murmushi yayi wanda ya k'ara baiyana asalin kyanshi kai ya jinjina musu alamun sai kun jimun. 

To da haka dai sukayi sallama suka tafi gida. 


Koda suka koma gida kai tsaye sashin Ummi suka nufa inda suka shige har cikin d'aki kana Saifuddeen  ya kira Rahma,

nan  Bappa Ali ya musu bayanin duk yadda sukayi da sarki,

to ita Ummi cewa tayi ba matsala a kamfanin Mtn d'in hayan filin ko ba komai ai zasu rink'a samu ribar filin, 

shima Bappa Ali ya amince da hakan hakama Saifuddeen da Rahma, to duk dai sun amince bayan sun gama mgnar wannan filin sai kuma Bappa Ali ya kalli Ummi cikin mutuntaka da tausayinta a matsayinta na yar goggonshi kuma matar yayanshi murya a tausashe yace. 

"To sai kuma batun filin su Saifuddeen d'in na bakin kasuwa ya kuka gani, 

kun ga dai tsawon shekara ake bibiyar filin wanne hukuncin kuka yanke?."

shiru Ummi tayi ta nisa cikin nazari tana tuno mafarkin da tayi kwana biyu da suka gabata inda taga Abbansu Saifuddeen tamkar a zahiri yana ce mata. 

"Kada ki hanashi saida filin, a saida ki kuma bawa Saifuddeen kud'in kada ki damu d'anki zai kula da komai."

to a ranar wuni tayi tana nazarin wanne filin ne zata bari su saida sai yau ta samu amsar dan haka cikin nitsuwa tace. 

"Ni dai a karan kaina na amince a saida filin, 

dan banga amfanin zaman nashiba tunda ba komai muka gina a wurinba."

sai ta kuma kalli Saifuddeen cikin kula da yanayinshi tace. 

"Babana ko kana da kud'in da zaka gina mana shaguna ne a wurin?."

da sauri ya girgiza mata kai dan shi Allah-Allah yake su amince a saida filin,

murmushi tayi tare da cewa. 

"To ya ka gani ka amince a saida ne?."

murmushi yayi tare da lumshe mata ido kana ya bud'esu a hankali sannan ya zaro woyarshi tare da rubuta mata.

"A tambayi Adda Rahma dasu Raihana in sun amince dai to ni na amince na kuma amincewa Hayatuddeen tunda shi har yanzu k'ara mine."

yana gamawa ya mik'awa Ummi bayan ta karanta ta mik'awa bappa Ali shima yana karan tawa ya mik'awa Rahma, koda ta karanta murmushi tayi tare da zubawa k'anin nata idanu cikin sanyin muryarta tace. 

"Ni na amince Raihana da Raliyya kuwa amincewar Ummi itace tasu, tunda suma har yanzu yarane gwara Raihana za'ace ta kai matakin balaga."

murmushi yayi tare da mata alamun ta kira Raihana.

Koda ta kira wota da akayi mata bayani sai ida nunta suka cika da hawaye cikin rawan murya tace. 

"Bappa Ali ka cewa Hamma Saifuddeen  yayi duk abinda ya dace a kan duk abun da mahaifinmu ya bar mana ba sai an nemi shawararmu ba."

itama Rahma sai cewa tayi. 

"Damu da kadararmu ai duk kaine Garkuwarmu."

to nanfa suka tsaida mgna akan za'a saida filin. 


Cikin ikon Allah a kwana biyar aka gama duk mgnar filin da za'a kafa services d'in da kuma filin da za'a gine Access bank. 

Jin kud'in hayan filin services d'inma ya matuk'ar bawa Ummi Mamaki inda sukace duk shekara zasu biya one million,

sannan filin bakin kasuwar kashi uku suka rabashi in duka ce kashi biyu zasu saida d'aya kuma zasu ajiye kasan cewar filin k'atone eka-eka ne bila adadin,

to bankin sun amince dan kashi biyun zai ishesu suyi gininsu mu samman in sunce bene zasuyi har filin zai zarta zatonsu, million biyu da dubu d'ari uku da hamsin aka karkare cinikin a cikin fadar masarautan dukku, ranar ma Saifuddeen bai je kasuwaba. 


Sai washe gari tun da sanyin safiya suka tafi shida Salisunshi, 

koda yaje sauri-sauri ya raba ledodinshi kana ya wuce shagon Alhaji Kabiru inda yayi kicibis dashi yana shirin fita zaije gidan Alhaji Sani, 

koda Saifuddeen yace mishi zai sari magin ya samu kud'in da ake buk'ata sosai Alhaji Kabiru yayi mmki, 

dan haka sai ya d'aukeshi suka tafi gidan Alhaji Sani, 

shima kanshi Alhaji Sanin yayi mmki sai sukaji tsoron sharrin zamani dan haka sukace dole sai yazo da manyanshi an gaya musu ina ya samu kud'in, 

bai damuba ya basu tabbacin zai kawo manyan nashi.

Koda suka dawo kasuwa ranan bai saida pure water ba, gidansu Ishaq ya wuce, 

ya kuma yi sa'a ya sameshi a gida nan ya tad'a mishi komai nan take kuma Ishaqn ma ya bashi k'arfin guiwa ya k'ara da cewa. 

"Alhamdulillahi dama jibi Ya Rabi'u zai shigo Gombe kaga zai zauna maka matsayin lawyernka mai kare dukiyarka da kadarorinka sannan yasa hannu a lamarin dan gudun kada su cutar da kai ko su damfareka zan kuma sanarwa Babanmu ma dan ya kasance da saninshi."

ruggumeshi Saifuddeen yayi tare rubuta mishi sak'on

godiya.


daga nan ya koma kasuwa ya d'an zazzagaya da ruwan. 

Shi kuwa Ishaq Saifuddeen yana tafiya ya sanarwa babansu tare da neman shawararshi ya amince ya kuma basu k'arfin guiwa sannan ya kira barrister Rabi'u ya sanarmishi komai yace ba matsala sai ya shigo Gomben.


Shi kuwa Saifuddeen koda ya koma gida, 

cikin nitsuwa yayiwa bappa Ali bayanin komai.

 Cikin nisan nazari da zurfin tunani Ummi da Bappa Ali da Rahma suke karanta duk bayanin da ya musu, 

tun randa ya fara kai kaya shagon Alhaji Kabiru da yadda yake sonshi da yadda ya samu su Alhaji Sani suna tattauna batun tallan sirri da company maggi ta kawo musu, 

da yadda yaje ya sameshi da mgnar da yadda ya gaya mishi batun yawan kud'in sarin da ake buk'ata, ya kara musu da cewa ya gayawa Ishaq shi kuma zai  gayawa Babansu, da Babban yayansu Barrister Rabi'u dan yasa mishi hannu a cikin lamarin ya tsaya mishi a matsayin lawyer inshi.

Ya kuma sanar musu cewar suma su Alhaji Kaburu sunce sai sunga iyayenshi sunji inda ya samu kud'in kafin su amince da batunshi.

Gyara zama Bappa Ali yayi tare da fuskarshi kana cikin sauk'e numfashi yace.

"To inaga dai mu barshi ya gwada mu gani, domin bahaushe yace matsoraci bashi zama gwani ko shi wanene, 

mu bada yak'ini a kanshi tunda munada makama kuma ba da ka za'ayi abinba kamar yadda abokinshi ishaq ya bada shawara hakan za'ayi, 

dan su kansu sun tsorita da batun yadda yace yanada kud'in shiyasa sukace sai sunga iyayenshi kinga alamun gsky kenan domin da 'yan damfarane ce mishi zasuyi kada ya gayawa kowa har uwa da uba in yana dasu kada ya gaya musu,

in kin amince ni dai na amince na kuma gamsu da kasuwancin."

Ya k'arishe mgnar yana kallon Ummi da Rahma jinjina kai Ummi tayi tare da cewa. 

"Ba matsala Allah ya bashi sa'a ya sanya al'khairi da al'barka a cikin lamarin ni na amince."

sosai Saifuddeen yaji dad'in amincewarsu domin suna bada dukkan yardansu a kanshi tamkar bashida nakasar komai, 

shi kuwa Bappa Ali cikin nitsuwa yaci gaba da cewa. 

"Zan je in samu Malam Ashiru abokin ya Bello, in mishi bayanin komai sannan muje gomben mu samu Babansu Ishaq da shi barrister Rabi'un sannan muje wurinsu Alhaji Kabirun sai mu tattauna duk abinda ya dace."

cikin nitsuwa Rahma tace. 

"Hakan yayi Allah ya shige mana gaba."

Amin Amin sukace baki d'aya sannan suka tashi daga taron nasu.


Washe gari tun da asuba bayan an fito masallaci Bappa Ali yasa Salisu ya kaishi gidan Malam Ashiru bayan sun gaisa ya mishi bayanin abinda ke tafe dashi kan batun Saifuddeen,

sosai suka tattauna a kai nan suka tsaida cewar gobe zasuje su samu su Alhaji Kabirun.


Salisu na dawowa suka d'auki hanyar gombe suna isa Saifuddeen ya rarraba ledanshi kana yaje shagonsu Alhaji Kabiru ya shaida mishi cewa gobe iyayenshi zasu zo cikin mutuntaka alhaji Kabirun yace to sai sun zo d'in.


Daga nan Saifuddeen ya wuce gidansu Ishaq  yana shiga yayi kicibis dashi da a tsakar gidan, 

a tare suka shiga parlour Babansu nan ya samu Ya Rabi'u ya iso, bayan sun gaisane suka tattauna lamarin nan ya sanar musu gobe ma su Bappa Ali zasu zo sundai ajiye zance sai goben.



Washe gari kuwa koda su Bappa Ali da Baba Ashiru suka taho da babban yayansu Samisu yariman Dukku kenan kai tsaye gidansu ishaq suka wuce.

sosai suka samu tarba ta mutuntaka, 

suka gaggaisa sannan sukayiwa juna k'arin bayani,

daga bisani suka sa ishaq yayiwa Saifuddeen text cewa sun isofa a ina zasu had'u dasu Alhaji Kabirun.

Yana ganin text d'in ya wuce shagon Alhaji Kabiru d'in ya gaya mishi cewar sun isofa, 

cikin kula ya mik'e tare da cewa. 

"To muje can gidansu abokin naka sai muyi musu jagora zuwa can gidan Alhaji Sanin."

cikin jin dad'in haka Saifuddeen ya gyad'a mishi kai sannan ya juya yabi bayan Alhaji Kabirun, 

motarshi suka shiga kai tsaye suka isa gidansu ishaq sosai Alhaji Kabiru yayi mamaki ganin manyan mutane dan barrister Rabi'u sanannene hakama mahaifinshi baraden Gombe, ga kuma Yariman dukku ga kuma Malam Ashiru da Bappa Ali wanda da ka gansu kaga kamala irin ta malaman addinin musulumci. 

bayan sun gaggaisa ne kuma suka mimmk'e suka nufi gidan Alhaji Sani wanda tuni Alhaji Kabiru ya mishi bayanin zuwansu a waya. 


G.R.A suka nufa inda nanne anguwar gidan Alhaji Sanin yake, 

suna isa mai gadi ya bud'e musu gate ganin tsaleliyar motar ya Rabi'u a gaba wanda Saifuddeen da Ishaq ke ciki a baya Yariman Dukku kuma yana gaba kusa da Barrister Rabi'un, 

sai kuma motar Alhaji Kabiru wacce Malam Ashiru da Babba Ali ke ciki Babansu Ishaq kuma na gaba kusa da Alhaji Kabirun, 

suna shiga harabar gidan sukayi parking, 

suna firfitowa wanni d'an matashi wanda zai kai sa'an su Hayatuddeen ya iso gabansu cikin nitsuwa ya gaidasu, 

kana ya kalli Alhaji Kabiru tare da cewa. 

"Abba ku shigo ciki inji Daddy na."

shafa kanshi yayi tare da cewa.

"To  Sulaiman." sai ya kuma juyawa ya kalli su Babba Ali tare da cewa.

"Bisimillanku mu shiga ciki."

to sukace kana suka biyo bayan yaron da aka kira da Sulaiman ,wanda yake rik'e da hannun Alhaji Kabiru yana cewa.

"Abba ina Isma'il baka zo min da shiba."

dai-dai lokacin kuma suka shiga cikin tamfatsetsen parlour yayinda Alhaji Kabiru yayi sallama tare da cewa Sulaiman.

"Isma'il baya nan ai sun tafi Yola shida Maminshi."

sai kuma yayi murmushi ganin Alhaji Sani ya nufi gaban Babansu Ishaq cikin mamaki yace.

"A a yau inada manyan bak'i kenan kaida kanka Baraden Gombe ai da kayi aike ka kiranima zan amsa kiran."

Sai ya kuma kalli su Bappa Ali dake cikin shiga ta kamala cikin sakin fuska yace. 

"Marhabikun ku iso ku iso."

cikin kamala suka zazzauna shi kuwa Alhaji Sani cewa Sulaiman yayi.

"Sulaiman maza je ka kawo musu abin sha."

da sauri yaron ya juya ya fita ba jimawa ya dawo da wani babban tire cike da ababen sha mai sanyi, 

sai ya kuma juya da sauri ya fita, 

yayinda tuni su kuma suna gaggaisawa, 

cikin nitsuwa Sulaiman ya kuma shigowa tare da tire cike da fruits ya ajiye bisa stol dake tsakiyansu, 

sannan ya fara ajiye musu gorunan ruwan dana juice sai cup d'ad'd'aya a gabansu.

yayinda tuni su kuma suna tattauna abinda ya kawosu, 

sosai Alhaji Sani ya d'auki abin da mahimmanci dan ganin manyan mutane suna cikin lamarin,

nan take yayi musu k'arin bayamin sannan suka bashi kud'in da dama sun taho dasu nan shaidu suka sa hannu,

Barrister Rabi'u da Barrister Salman yayan Saminu kenan Yariman dukku suka rattaba hannu ga manyan shaidu. 

A nan take kuma sukayi mgnar hayan shagon da in kayan sun iso zai ajiyeshi. 

ba tare da b'ata lokaci ba Alhaji Kabiru ya shaida musu akwai wani shago can k'arshan layinsu amman a luggune,

murmushi Babba Ali yayi tare da cemishi.

"Ba matsala nawane kud'in hayan."

Alhaji Sani ne ya d'an gyara zama tare da cewa. 

"Shagunanshi ne ai, in kunaso ku biya kud'in wata shida in kuma kunga ba matsala ku biya kud'in shekara d'aya yadda dai kasuwa ta kama."

Barrister Rabi'u ne ya kalli Bappa da Saifuddeen tare da cewa.

"In dai da hali  ku biya kud'in shekara d'aya."

da wannan shawarar bappa Ali ya biya kud'in shekara d'aya, 

sannan Saifuddeen yasa hannu a cikin dukkan takardun da ya kamata na company maggi  daga nan suka gama komai sannan suka sallami juna a mutunce suka tafi.


Koda suka koma gida kuma Bappa Ali ya fito da sauran kud'insu na hayan filinsu da za'a kafa services ya nunawa Ummi dasu Saifuddeen dan cikinsune ya biya hayan shago,

nan kuma suka tsaida shawarar bappa Alin ya sari kayan abinci tunda dama sana'arsa ce aune-aune.

nan bappa Ali ya fara sari a duk kasuwannin da yake zuwa kamarsu. 

Ngalda, bajoga, Nafad'a,  Hashidu, dogon ruwa, kiri, Malam Sidi, Kurugu, kumo, Dad'in kowa D'ukul togo.  Da dai sauransu.

kasan cewar lokacin Kaka'ace amfanin gona ya nuna so kayan abinci yana araha inda tuni masu kud'i keta sara suna boyewa da nufin sai yayi tsada su fitar to wannan dalilin yasa Bappa Ali fara sara da kekyawar niya dan taimakawa masu k'aramin k'arfi yayi aniyar zai canza salon wannan kasuwancin da ya sara ya ajiye in yayi tsada shi kuma ya fitar ya fara saidawa a farashi mai sauk'i. 

to nanfa ya k'ara k'aimin bin kasuwannin k'auyuka yana sarar buhuhhunan su.

 Masara, Dawa, Gero, Maiwa, Shinkafa, Rid'i, kalwa, Wake, Gyad'a, da dai sauran kayayyakin abinci, 

cikin wata biyu duk ya gama sarin inda ya cika tsoffin d'akunan iyayensu duka biyu da buhunan kayan abincinshi.



Tuni Magginsu Saifuddeen kuma ya isa har an shirgesu a babban shagon da Saifuddeen d'in ya kama haya inda aka cikashi mak'il da katon d'in MAGGI mak'il kana aka ja shagon aka rufe, yayinnda shima burinshi irin na Bappanshi ne.

Ya kuma ci gaba da sana'o'insa da ya saba, yana kula da ahlinshi da ahlin Baba Bello, 

yana kuma zura ribar shi a wani sabon asusunshi d'aya saya dan wancan asusun tuni ya cika a cewarsa sai ya cika asusu uku kafin ya bud'esu duka.


             Bayan wata bakwai da saran Maggin kenan

Rayuwa taci gaba da gudana yau dad'i gobe akasin haka abu da dama ya faru.


Ana cikin haka rana tsaka Maggin da aka sani a hud'u goma sai gashi yayi gauron zabbi ya koma biyar ashirin kusan ninkin ba ninkin kenan, 

yayinda yan kasuwa masu harkan magging da sun samu sun sara suketa farin ciki anata hidimar kasuwa anata hidima. 


kusan tsawon mako uku kenan da farashin maggin yayi sama, 

wanda yayi dai-dai da cikin tsakiyar damuna ne sama ruwa k'asa ruwa, kayan abinci yayi tsada, 

tuni talaka ya fara shiga hau'ula'in rayuwa, 

bappa Ali da Saifuddeen kuwa tuni sun fara shirye-shiryen bud'a kasuwancin nasu Yau jumma, kuma tun bayan sallan la'asar aketa zuga ruwa kamar da bakin gwarya,

dole cikin ruwan Salisu da Saifuddeen suka kamo hanyar dukku,

daga gombe har cikin Dukku ruwane yake dukansu tamkar zai jasu ya tafi dasu,

k'arfe shida dai-dai suka isa cikin dukkun sauri-sauri gudu-gudu Saifuddeen ya shiga cikin gida lokacin da Salisu ya sauk'eshi dan har lokacin ana d'an yayyafi irin na alamun ruwan ya d'auke sai yaf-yaf  ruwan keyi.

Yana shiga kai tsaye d'akin Umminshi ya nufa dan wannan al'adarshi ce muddin ya dawo ko ruwa ko iska ko dare ko rana sai ya fara shiga inda take ya ganta ta ganshi kafin ya wuce d'akinshi,

yayinda ita kuwa Ummi duk nisan dare bata tab'a iya yin bacci har sai taga dawowanshi, duk ruwa kuma bata rumtsawa sai taga ya dawo. 

Yana isa bakin k'ofarta yasa hannu ya bud'e labule, 

murmushi yayi ganinta zaune ta zubawa k'ofar idanu yayinda Hayatuddeen ke konce yayi pillow da cinyarta Rahma kuwa na gefenta tana gugan kayan data wonke,

Raihana kuwa nayiwa Ummi kitso, 

ajiyan zuciya Ummi tayi tare yin murmushi ganin gudan jininta, 

cikin tausayawa Raihana tace. 

"Sannu da hanya Hamma Saifuddeen."

kai ya jinjina mata alamun yauwa.

Rahma kuwa ajiye anyone d'in tayi tare da cewa.

"Saifuddeen jeka canza kaya kalli yadda ka jik'e jilik sanyi zai kamaka illah fa."

cikin body language yace da ita. 

"To."

sai ya kuma yi musu alamun ina Raliya dasu Faruq."

gane abinda yake nufine yasa Ummi ce mishi. 

"Suna wurin Aunty Nina."

kai ya jinjina dan yasan dama su Faruq suna son zuwa wurin Aunty Ninan wacce tuni ta haifi d'anta  wanda akayiwa Abba mai suna shiyasa su Rahma ke kiranshi da Abban tuni yaron ya girma har yana rarrafe.


Juyawa yayi ya nufi d'akinshi daga bakin k'ofa ya mik'a hannunshi ya jawo towel inshi dake shanye a kan k'ofanshi, botiki ya d'auka ya cikashi da ruwa kana ya d'auki kondon soson wonkenshi,

ban d'akinshi ya juya ya nufa dan jin ruwan ya d'auke kit.


Wonka yayi fes sannan ya d'aura towel d'in ya fito, 

buta ya d'auka yayi al'wala sannan ya shiga d'akinshi mai ya dauka kana ya zauna bakin katifarshi murze jikinshi yayi ciki da woje sannan ya mik'e tsaye ya zaro tattausan boxer inshi fari k'al ya fesheshi da turare sannan ya saka, 

yana gama gyara zaman boxer d'in a k'ugunshi ya konce towel d'in ya d'anyi taku biyu zuwa uku sannan ya isa bakin k'ofar wore towel d'in yayi ya shanshi kan k'ofar, 

sannan ya juya ya isa bakin 'yar durowar tashi ya zaro farin vest fara kal ya fesa mata turare yasa sannan ya kuma zaro bak'ar jallabiya ya zurata a jikinshi, 

sai ya kuma feffesa turaren, 

sannan ya matso gaban madubin shin hannu yasa ya gyara suman kanshi da yake konce lib sai shek'i yakeyi wayarshi ya zura a al'jihu sannan yasa takalmanshi dake bakin k'ofa ya fita. 


A tsakar gida ya samu su Ummi dasu Raihana da Hayatuddeen suna al'wala,

kitchen ya lek'a ganin Rahma na kwasar abinci, 

ganinshi a bakin k'ofa yasa tayi murmushi tare da cewa.

"Yauwa je kayi salla ana idarwa ka dawo yau miyarka nayi tunda naga hadari nasan zaka dawo da yunwa."

murmushi yayi tare da mata alamun tayi sauri ta gama lokacin salla yayi, 

sai ya kuma kalli fuskarta ganin alamun saida tayi al'wala kafin tazo ta fara kwasan tuwon shiyasa ya juya ,

ya kamo hannun Hayatuddeen da Faruq da yanzu ya shigo suka nufi masallaci.  


Koda aka idar da salla, basu dawo gidaba nan ya zauna da Hayayuddeen da Faruq saida akayi sallan isha sannan suka fito.

a  bakin masallacin Saifuddeen ya kamo hannun Warisu sai ya kuma yafito Salisu tare da musu alamun su zo suci abinci,

kasan cewar yanzu su ukune rak suka rage a dukkun dan Ahmad, Samuni, Mudassir,  duk suna cikin gombe,


Cikin yamutsa fuska Warisu yace.

"Tab aini bani cin abinci da dare dan wlh kun sani bani son k'iba, 

gwara kai Saifuddeen jikinka ba irin nau bane."

Salisu ne ya d'an harareshi tare da cewa.

"Kuma in sha Allah wata rana sai kayi k'iba."

sai ya kuma juyo ya kalli Saifuddeen tare da cewa. 

"Ni kam a koshe nake muna dawowa na samu iya shatu tana kwasar tuwo tayi wannan hegiyar koriyar miyar nan tata kad'a kwarya yunwace ta sani cinta dole."

dariyar mugunta Warisu ya mishi tare da cewa. 

"Hege ka dai biyewa wannan tsohuwar yaseen sai ta toshe maka kwanyarka da koriyar miyar nan ka zama huhulahu."

yana fad'in haka ya juya da sassarfa ya gudu ganin Salisu zai kai mishi duka, 

shi kuwa Salisu hamma yayi tare da cewa. 

"Kaga mai jajayen kunnuwa ni zanje inyi bacci saida safe."

daga nan sukayi saida safe, shi kuwa yasa Hayatuddeen da Faruq a gaba suka shiga cikin gida yayinda Bappa Ali ke binsu a baya.


Suna shiga tsakiyar gidan ana dawo da wutar nepa,

kai tsaye d'akin Ummi suka shiga suna shiga ya mik'awa Raihana woyarshi tare da mata alamun taje ta sa mishi caji a d'akinshi, 

da sauri ta karb'i wayar kana taje ta jona wayar sannan ta dawo.

tana shiga kuma Rahma ta kalleta tare da cewa. 

"Je kitchen ki kawo musu abincinsu."

to tace tare da juyawa ta nufi kitchen d'in, 

Ummi kuwa gyara zamanta tayi tare gyara sallayan da take zaune a kai sannan tayiwa Saifuddeen d'in alamun yazo ya zauna,

kai ya gyad'a mata kana yaje ya zauna a gefen damanta Hayatuddeen kuma ya zauna gefen hagunta yayinda Faruq ya zauna gabanta,

Adda Rahma kuma kan gadon ta hau ta kwanta tare yin mik'a sannan ta bugi k'afad'an Raliya da tuni ta fara bacci yayinda Adam ke bisa ruwan cikinta, 

a hankali ta bud'e ido, 

sai ta kuma yunk'ura ta zauna jin Rahma na cemata.

"Ke tashi kije ki shiga kada kiyi bacci anan ki d'auki Adam ku tafi tare."

Kai ta gyad'a kana ta mik'e ruggume da Adam ta fita ta nufi d'akinsu, tana fita Raihana na shigo musu da abincin.




                           By

       



        *NAKASA BA KASAWA BACE*


                               *PAGE 10*


                                 NA

               *AYSHA ALIYU GARKUWA*


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇



                         Free page



_Ga masu buƙatar sayan littafin turo katin mtn na 300 kacal ta wannan Number 09097853276. Ko ka/yi transfer ta bank ac na 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa_




A gaban shi ta ajiye tiren, sannan ta d'an zauna gabanshi kular miyar ta bud'e sannan ta zuba mishi miyar a pilit mai d'an zurfi sai ta kuma bud'e na kulan ta sako mishi malmala biyu duk da tasan da wuya ya cinye d'aya ma, 

kolban man shanun da Ummi ke mik'a mata ta karb'a bud'e marfin tayi ta tsulala man shanun mai d'an yawa, sannan ta jawo gongonin dakekken yajin borkonsu wanda yakeda ta k'amshi kanamfari da tafarnuwa d'an kad'an,

spoon tasa ta d'an motso miyar da yake wadace da kifi banda da busasheshen nama dariko kana ga wadacecciyar gyad'a da saida ya bulbulo mai,

robar da ta zubo ruwan wonke hannu ta mik'a mishi, 

jawo robar yayi ya fara wonke hannunshi. 

Ita kuwa Raihana wani pilet d'in ta kuma d'auka tasa malmala d'aya kana ta zuba miyar a kan tuwon sannan tasa man shanun tare da tarfa yajin borkonon a kai, 

sai ta kuma kalli Hayatuddeen daketa yamutsa fuska shida Faruq cikin had'e fuska tace. 

"Ku tashi kuci abinci."

Hayatuddeen ne ya zame ya konta tare da cewa. 

"Ni wlh bazanci tuwoba na k'oshi."

shima Faruq had'e fuska yayi tare da cewa.

"Shima bazai ci tuwoba."

tura musu pilet d'in tayi tare da cewa. 

"Kada Allah yasa kuci, cikina ko cikinku hegun yara sai iyayi da son k'arya talaka yace bazaici tuwoba."

Ummi dai sai ido ta zuba musu, 

Rahma kuwa murmushi tayi sanin halin Raihana da gajin hak'uri bata jurar rainin wayo hak'urinta kuma ragaggene, 

shi kuwa Saifuddeen gyara zamanshi yayi sannan ya jawo hannun Hayatuddeen da Faruq ya gyara musu zama sannan yasa hannu ya gutsuri d'an k'aramin loma tare da dandalo miyar sannan ya mik'awa Faruq wanda shi biyewa Hayatuddeen yake bawai baison tuwon har haka bane, bud'e baki yayi da sauri dan yana matuk'ar jin dad'in yaga Uncle inshi na bashi abinci a baki, 

murmushi Saifuddeen yayi sannan ya kuma gutsuro loma ya dandali miya ya mik'awa Hayatuddeen dake zuzzumbura baki, 

a hankali ya bud'e baki ya amsa dan dama muddin Hayatuddeen yaci tuwo tofa sai dai in Saifuddeen ne ya bashi da kanshi,

cikin lashe baki Hayatuddeen d'in yace. 

"Adda Rahma miyar tayi dad'i yaseen kinfi Adda Raihana iya girki."

dariya sukayi baki d'aya yayinda tuni Raihana ta hatsala ta kai mishi bugu wanda ya kauce ya rab'a jikin Umminshi, 

ita kuwa Raihana mik'ewa tayi ta fita ganin Saifuddeen ya sauya fuska, 

shiko Saifuddeen loma ya kuma gutsura ya d'an dandali miyar da taketa nason man shanu da man kuli yasa a bakinshi, 

idanu ya lumshe dan jin d'and'anon miyar nasa yawun bakinshi tsinkewa, 

tabbas yasan yan uwanshi sun iya girki ko dan gada sukayi wurin Umminsu. 

daga nan yaci gaba da basu abinci, yana basu yanaci, saida sukaci sukayi hanik'an sannan Adda Rahma ta tattare filin,

ganin Faruq ya fara hamma yasa Ummi ce musu.

"Maza ku hau gado ku kwanta saida safe."

da sauri suka hau suka konta tare da yin addu'a, 

shi kuwa Saifuddeen alama yayiwa Adda Rahma da taje ta kira Bappa Ali, 

kasan cewar tana ganewa yasa ta juya ta nufi side d'in Bappa Alin.


ita kuwa Ummi ta fito da asusun Saifuddeen duka uku dan ya mata alamun ta fitar dasu.


Ita kuwa Rahma da sallama ta shiga d'akin Aunty Nina wacce take yiwa Abba nabkin cikin kula ta zauna gefenta tare da karb'an yaron taci gaba da sa mishi kayan sanyin dake gefensu cikin sanyinta tace. 

"Anty Nina Saifuddeen ke son mgna da Bappa Ali,."

mik'ewa tayi tare da cewa.

"To bari in gaya mishi."

to tace sannan ta fara kiciniyar sawa Abba hula shi kuwa sai zillewa yakeyi.

Ita kuwa Aunty Nina tana zuwa turakan Bappa Ali tace.

"Malam, 

Saifuddeen ke son Magna da kai."

kai ya jinjina tare da cewa. 

"To gani nan zuwa."

daga nan ta juya taje ta gayawa Rahma da tuni ta gama kimtsa Abba, 

mik'ewa tayi tare da bata yaron sannan ta fita ta tafi.


Tana shiga ba jimawa shima bappa Ali ya shigo da sallamarshi,

kan kujera ya zauna yayinda suna fuskantar juna dasu Saifuddeen,

pepar da biro Saifuddeen ya matso dashi kana yayiwa Rahma nuni data zauna ta harhad'a kan kudad'en asusun da suka farfasa shida Ummi suka juyesu bisa k'aramin sallayar Hayatuddeen.


Gyara zama yayi sannan ya fara rubuta mishi abinda yasa ya kirashi.

"Bappa Ali kar dai har kayi bacci na tasheka?."

kai ya jujjuya tare da cewa. 

"A a banyi bacciba Saifuddeen dama nima inason mu tattauna."

murmushi yayi tare da rubuta mishi.

"To dama tun last two weeks nace ma maggi yayi tsada ko yayi ma fiye da yadda aka zata, 

to shine nake son in sanar maka muyi shawarar yadda zamu saida, 

sai kuma batun ribar ledodin da nike saidawa ina sawa a asusu to shine wannan yanzu muka fasa asusun."

ita dai Ummi tana saurarinsu yayinda ita kuwa Rahma taketa had'a kud'ad'en in ta had'a dubu tara  sai tayi musu d'amara da cikon na goma kana sai ta ajiyesu.


Shi kuwa bappa Ali cikin nitsuwa yace. 

"Eh lallai farashin Maggi ya k'aru sosai, ga kuma na kayan abinci ma ya k'aru matuk'a buhunan wake da na saya kan dubu 12 yanzu ya zama 30k ake saidashi, masara dubu 8 na sassaresu gashi yanzu sun koma dubu 15 ,

Kalwa na sayeshi buhu dubu tara-tara to gashi yanzu buhu dubu ashirin da biyar, 

gero na sayeshi buhu dubu bakwai yanzu ya koma buhu dubu sha hud'u.

Gaba d'aya kayan abinci sun tsefe sunyi tsananin tsada talaka na fama da yunwa manoma sun saidashi tun yana araha gashi yanzu zasu dawo suna sayanshi da tsada  kuma a yanzun suke fama da noma damuna tayi zurfi sama ruwa k'asa ruwa, 

to dama na ajiyeshi ne kan haka yanzu zamu san yadda zamuyi mu sakeshi da araha yadda talaka zai samu sauk'in saya."

cikin jin dad'i Ummi tace. 

"Madallah da mai zuciyar imani inama ace duk masu dama da kud'i suna haka to tabbas da masu sayanshi dan muguntar sai yayi tsada su fiddashi da sun bari."

shima Saifuddeen murmushi yayi cikin jin dad'in yanaga zasu samu damar taimakawa marasa k'arfi ya rubuta musu. 

"Yauwa Bappa Ali wannan abu yayi kyau, 

Magging ma dole zamu sake fara shinsa dan talaka ya samu yadda zaiyi."

jinjina kai bappa Alin yayi tare da cewa. 

"Yauwa to muga ya lissafin zaiyi,

kaga lokacin dana sai wake ana saida mudun akan d'ari da goma, 

kaga yanzu kuma ana saida mudun akan d'ari biyu da saba'in,

to Alhamdulillahi dama ana kasuwa dan ribane, 

dan haka mu zamu rink'a saida mudun wake akan d'ari da talatin, mudun gombe kenan mudun kano da sauran garuruwa masu amfani da kwanon sha kuwa in munyi kiyasti da kud'in mudunmu zamu saida musu mudun akan d'ari biyu da settin

sab'anin sauran mutane dake saida mudun akan d'ari biyu da saba'in a mudun gombe mai cin gongoni takwas zuwa tara

kaga ko wanne mudu minbi ribar naira ishirin kacal fatanmu Allah ya musu al'barka ya kuma sa kasuwar ta d'aure."

wasu zafafan hawayen farin cikine ya rufe Ummi dan tana ji a jikinta ahlinta masu cikar imanine da zarra. 

Shima Saifuddeen murmushi yakeyi da godewa Allah da tsarkake mishi zuciyarshi data ahlinshi, 

shi kuwa bappa Ali ciga yayi da cewa.

"Lokacin dana sarin kayan mudun masara naira 100 ne yanzu kuma mudun ya koma d'ari da tamanin, 

to mu zamuke saidashi bisa d'ari da ashirin munyi ragin naira sattin akan farashin sauran mutane munbi ribar naira ishirin."

sai ya kuma gyara zamanshi tare yi mishi lissafinsu dalla-dalla gaba d'aya sun karya farashin kayan abincin nasu inda suka rink'a bin ribar naira ashirin-ashirin kacal, 

sai a buhunan kalwa da rid'ine, sukaci ribar naira hamsin-hamsin a kan ko wanne mudu, 

dan shi ba kayan abinci bane baya zama dole sai mutun ya saya musammam rid'i wanda shi kamfanunnuka ne ke sayanshi ana fiddashi k'asashen k'etare.

inda suka tsaida farashin sari kuma akan buhun shinkafa sharshera sun sayeta dubu tara to yanzu ana saidata dubu sha shida to su dubu goma sha d'aya suke saidata sukanbi ribar dubu biyu a cikin ko wanne buhun shinkafa.

Rahma da kanta ajiye irgen kud'in tayi ta zuba musu idanu domin tabbas tasan k'anin mahaifinta ya cika adalin malamin d'an kasuwa,

shi kuwa bappa Ali gyara zama yayi yaci gaba da cewa.

"Gero da dawa duk ribar dubu bibbiyu zamubi akan ko wanne buhu sab'anin sauran mutanen dake bin ribar dubu bakwai da d'ari biyar-biyar.

Sosai sukaci gaba da lissafin inda a cikin ko wanne buhun rid'i da kalwa suka bi ribar dubu biyar-biyar sab'anin wasu dake bin ribar dubu goma sha d'ad'd'aya.


Saida suka gama lissafin kab sannan ya gaya mishi yawan buhunan ko wanne abu inda buhunan masaransu kawai sun kai d'ari da biyar 

sai buhun gyararriyar shinfaka mai cin mudu tamanin inda ake saidashi dubu talatin so su kuma sun barshi kan dubu sha bakai sunci ribar dubu uku cikin ko wanne buhu,

nan suka kiyasta komai,

sannan ya karb'i takardar da Saifuddeen ke mik'o mishi inda yake ce mishi.

"Duk cikin katon d'in maggi akwai ribar da ta kusa uwar kud'in,

sabida MAGGIN naira goma ya koma d'aya rak za'a k'ara ya koma ashirin, 

to ribar tayi yawanda talaka shine da wuya,

dan haka sai nayi tunanin mai zai hana mu mu rink'a saidawa uku goma tunda dama hud'u gomane mu rink'a bin kwaya d'ad'ad'aya,

sannan ana saida ledan akan d'ari biyu da hamsin a da can wota bakwai baya yanzu kuma ledan ya koma d'ari hud'u dai-dai shine nace to nawa ya kamata muke sakin ledan?."

murmushi Bappa Alin yayi dan ganin umarninshi Saifuddeen ke jira cikin nitsuwa yace.

"Kabi riba kad'an mai al'barka  kabar ko wanne leda akan d'ari biyu da saba'in kaga ai dama can hamsin d'in sama ribar tasuce a company a d'ari biyu ake basu.

Kaga kuma kai a kasuwane in ka sakeshi da yawa abokan kasuwancinka zasuji haushinka zasuga zaka kashe musu kasuwane hakan kuma zai iya jaza maka matsala shiyasa badon hakaba da d'ari biyu da hamsin d'in zaka saidashi ko ya kuka gani Hajia Ummi."

kai ta jujjuya mishi cikin jin dad'i tace.

"Allah dai yasa Alhaji Ali Allah ya sa munada ranon zuwa makka da madina birnin ma'aiki."

Amin Amin sukace baki d'aya sannan taci gaba da cewa. 

"Wannan ai mgnar ta uba da d'anshi ne ni saidai in sanya al'barka ina kuma nema muku tsari a wurin rabbil izzati."

gyara zama Saifuddeen yayi tare da rubuta musu.

"Eh hakanma yayi Bappa Ali amman kada ka damu ni zanbi hamsin d'in a cikin ko wanne leda, 

shagunan zanbi in musu talla in zasu sara zan basu a farashin da d'in amman suyi min al'kawarin saidawa shida ashirin sab'anin biyar ashirin d'in da suke saidawa, 

kaga zai zama uku goma kenan,

ni zanbi k'aramar ribar, 

a dai wannan sarin in yaso a sari na gaba in naga hakan bazai yuwuba sai inbi sahunsu tunda nima dole da tsadan zan sara."

sosai suka gamsu da wannan shawarar suka k'ark'are komai aka gobe in yaje zaiwa su Alhaji Kabirun tallan.


Shi kuwa bappa Ali cikin nitsuwa yace.

"Dole zaka ci gaba da rik'e shagon nan da aka ajiye maggin, 

lokaci yayi da zaka samu sauk'in wahala, 

zamuje a gyara kayayyakin in an samu wasu sun sara to sai a samu akori kura a cikata da kayayyakin abincin ta kai shagon sai a fara saidawa."

cikin gamsuwa Saifuddeen ya rubuta musu.

"Hakan yayi shike nan kuma nasan Warisu zai kular mana da komai,

zan kuma yiwa ba mishkila talla nasan zai sara kuma zai bari a farashin da zamu bari dan nasan shi adalin d'an kasuwane mai imani".

sosai sukaji dad'in wannan zaman nasu, 

yayinda tuni Rahma taketa famam irga kud'in ganin ta kusa gamawa ne yasa duk suka zuba mata ido dan suna jiran suji nawane kud'in.


Minti hud'u tsakani ta d'ago kanta tare sauk'e numfashi cikin sakin fuska da sanyin muryarta tace. 

"Kud'in dukansu dubu  d'ari uku da tamanin da biyar ne kud'in baki d'ayansu."

sosai yawan kud'in ya basu mamaki sai dai kuma idan suka tuna kusan tsawon shekara d'aya kenan yake tara kud'in da iriyar azaba da hawala da yake sha ruwa da iska zafin rana da wahala sai suga wahalarsa tama zarta kud'in, 

amsarsu Bappa Ali yayi tare da mik'awa Ummi yace tasa musu al'barka cikin murmushi tace.

"Allah ya sanya musu al'barka."

Amin Amin sukace baki d'aya kana Bappa Ali ya kalli Saifuddeen cikin kula yace.

"To ga dai kud'i su kuma me zakayi dasu?."

gyara zamanshi yayi tare da tonk'oshe k'afafunshi ido ya d'an lumshe sannan ya rubuta musu.

"Duk shawarar da kuka bada hakan za'ayi."

da sauri bappa Ali yace.

"A a ka gaya min me ka shawarta kaida zuciyarka?."

kanshi ya d'an sunkuyar sannan ya rubuta musu.

"Dama ni tunanin da nayi, machine d'in Salisun nan ta tsufa yanzu wahal dashi kawai takeyi shiyasa ko balance d'in da keret yake had'a 1,500 gashi yanzu ya fara karatu yana buk'atar kud'i to shiyasa nayi tunanin ko zan saida tsohuwar sai in in saya s mishi sabuwa, 

zaifi jin dad'in aikinshi zai samu yadda zai kula da ah'linshi da karatunshi muma kuma balance d'in zai taimakawa cefenen gida na yau da kullum."

sai ya kuma yi shiru ya zuba musu idanu

ganin suma shi suka zubawa idanun alamun sun gamsu da bayaninshi suna kuma son jin k'arshen mgnar, 

sai ya d'an had'e yatsunshi tare rubuta musu.

"Sauran kud'in kuma inason zanci gaba da karatuna, 

zan yi idimar karatun kama da hidimar sharan fage da saurauran hidimomi na sabbin d'alibai da suke harin zuwa jami'a dole in samunda su Jamb waec da Neco to dole akwai kashe kud'i."

Rahma ce ta fara yin Magna cikin jin dad'i tace. 

"Alhamdulillahi burin Ya Seyo zai cika, 

yayi kyau naji dad'in haka."

Ummi kuwa cikin sanyi tace. 

"To ya zakayi da kasuwancin naka kuma?."

kai ya jinjina tare da cewa.

"Raba leda ba wuya cikin awa uku ana hud'u nake gamawa, 

sannan akwai uzuri tsakanina da abokan kasuwancin na in banje bama ana rabamin kinga kwanaki da banda lfy ma Jabeer ne ya rarrabawa costumes d'ina, 

kinga duk lakacin da bani da darasi inada damar kasuwanci na, 

sai dai cinikin pure water dasu omo nane zaiyi k'asa."

cikin bada k'arfin guiwa bappa Ali yace.

"Hakan yayi Allah ya taimaka ya kuma bada sa'a.

ni kuma in sha Allah daga gobe zan fara d'aukan Warisu zan fara nusar dashi da koya mishi harkan awu da sanar dashi farashin sari da sayan d'ad'd'aya,

dole in koya mishi awun kanshi gudun kar yaje yayi ta tauye mudu."

sosai dai suka zauna suka tattauna yadda komai zai tafi,

shi kuwa Saifuddeen dubu d'ari ukun ya ware kana ya d'auki na saman ya rabawa Ummi da Bappa Ali dubu goma-goma, 

ya bawa su Rahma da Aunty Nina dasu Raihana dubu biyar-biyar,

Su Warisu, Saminu, Salisu, Ahmad Mudassir, kuwa duk suma dubu  biyar-biyar ya ware musu shi kuma yasa saura a al,jihunshi.

da zummar zai bawa Jabeer da Hisham dubu biyar-biyar sai ishaq inshi dubu biyar shima.


Inda yasan machine bajat zataci kusan dubu d'ari da ashirin, 

saura kuma zai ajiyesu dan hidimar karatunshi.


Da haka dai sukayita hira sai har kusan shabiyu na dare sukayi saida safe kana duk suka mik'e kowa yayi makoncinsa zuciyarshi cike da farin ciki.

 

Washe gari kamar yadda suka tsara hakan Saifuddeen yayi ya tallatawa su Alhaji Kabiru Maggi ba musu kuma suka amince dan ai sune da riba mai yawar, 

yayinda Alhaji Sani kuma yaketa taraddadin shigo da yaron cikin harkarsu a cewarshi karfa ya lalata musu kasuwa so amman ya amince da tsarin,

nan take suka buk'aci daya basu account number inshi,

Allah sarki Saifuddeen sai yau ya tuna da wata abba tashi account number shi dan shi tun last year bayan s Ya Rabi'u ya aiko mishi woya da ishaq ya matsa mishi dole sukaje suka bud'e account number d'in da shi a lokacin yanaga account d'in baida wani amfani,

dan babu ko sisi a ciki in bada wanda ya bud'e dasu babu ko asi a ciki dan shi lokacin yafi ganewa asusunshi, 

murmushi yayi jin dad'in ya haddace komai na account d'in a kanshi, 

nan take ya basu account number,

inda sukayi sallama da cewa sai gobe zasu tura mishi, 

inda sun saye kashi biyu cikin  kashi uku na kayan.


Daga wurinsu kuwa wurin Bello ya nufa na shagon ba miskila nan yayi sa'a ya samu ogon nasu ya mishi bayanin komai,

cikin farin ya amince nan take suka tsadance suka kuma ajiye farashinsu dai-dai dana juna,

inda ya koka mishi da zai samu yana son ya ara mishi d'aya daga cikin yaran shagonshi dan yaje ya kyautata awun yaran shagonsu tunda su sabbin shigane, 

cikin aminci da mutunci da kamala da cikar imani ba kyashi bare hasada ba miskila ya amince inda yace Bello zai koma ya kula da lamarin shagon su Saifuddeen nan ya gayawa Saifuddeen farashin yadda yake sallaman yaran shagonsu a kullum da kuma k'arshen wata, 

shima Saifuddeen ya amince duk da yawan kud'in yasan wannan shine adalcin da ubangida zaiwa yaran gidanshi gudun kada su zama masu zagon k'asa.


Daga nan ya shirya yaje makarantarsu yayi cuku-cukun komai daya dace dan ci gaba da fafutukar neman damar shiga jami'ar G.S.U.


Shi kuwa Bappa Ali a ranar ya fara nunawa Warisu harkan kasuwancin inda yaji dad'in haka sosai, dan ko ba komai zai samu damar kula da kanshi da ah'linshi.


Washe gari kuwa saiga Saifuddeen yanata ganin ruwan miliyoyi a account number inshi,

wanda Alhaji Sani Da Alhaji Kabiru da ba miskila suka turo mishi, 

a ranar su Alhaji Kabiru suka kwashi kayan maggin da suka sara a wurin Saifuddeen suka kai sito insu.


Bappa Ali kuwa ya nemi akori kura guda biyu yasa aka lodawa ba miskila kayan daya sara a d'aya motar, 

d'ayar kuwa yasa aka loda wanda zasu ajiye a shagonsu, 

nan aka tafi da Warisu da Bappa Alin bayan yan gama sassauk'e kayan ko wanne an ajiyeshi a muhallinshi, 

sai Bello da da Warisu da Bappa Ali suka tare a shagon su Ssifuddeen d'in nan suka k'ara kimtsa komai sannan bappa Ali yayi musu nasiha da suji tsoron Allah su kyautata awun mudunsu, nan kuma sukayiwa shagunan layinsu ihsani da kayan abinci dama duk wanda yazo gilmawa ta gaban shagon nansu, 

hakan yasa a take duk layin nasu suka san da shagon dan sanadin bada ala koron.


Wasa-wasa kasuwa dai nata d'an tafiya, 

sai dai yawanci masu sarine ke saya, 

dan masu sayan d'ad'd'aya basu fara sanin shagonba tukun, 

tuni kuma masu dattin zuk'ata sun fara suka suna wani cewa. 

"Yoh aiyi dai mu gani, nanda yaushe wai maye yayi amarya tuni zai lamushe abarsa,

sabida wasun gani suke Saifuddeen yazo da wani salo na kashe musu kasuwa da hanasu riba mai yawa, 

to dama in ubangiji yayi niyar d'aukaka d'an adam a bakin masu hasada zai d'aukakashi tuni masu hasadan dake k'ananun Magna ne yasa kasuwar gombe ta cika da batunsa inda kamar da wasa suka rad'awa shagon dama layin suna wai , 

*ALHAJI BUTU* wai alhajin araha kenan, 

abu kamar wasa sai ga sunan shagon dama layin ya zauna hakan. 


Cikin mako uku kasuwanci yaci gaba da gudana, 

yayinda Ssifudddeen kuwa har yau bai fasa tallan ledanshi dasu omoba,

ana kuma ta shirye-shirye fara WAEC.


Sun gama zana exam d'in WAEC, hakama NECO tuni kuma ya zana JAMB inshi bayan wasu makonni sakamon jarrabar na Jabm ya fito inda ya samu 220 kuma Alhamdulillahi waec da neco d'inma result yayi kyau matuk'a gaya.


Bayan wata hud'u, tuni Saifuddeen ya samu nasarar zama cikekken d'alibi a Gombe state university.


Warisu da Bello kuwa sosai kasuwa take tafiya dai-dai da yanayin cinikin sabbin shaguna masu araha, 

a dai-dai lokacin ne kuma komai na kayan abinci ya dawo gida a hannun manoma, 

tuni masu hannu da shuni sun fara rige-rigen saye kayayyakin abincin dan b'oyeshi sai yayi tsada su fiddoshi.


A kuma dai-dai lokacin ne company layin Mtn suka kuma biyansu kud'in hayan filinsu da suka kafa services nan suka had'a kud'in suka rub'anya jarin kayayyakin abinci da bappa Ali zai sararo musu. 


Kamar bara haka banama bappa Ali da Saifuddeen sukayi, 

bayan sun harhad'a cinikinsu suka ware asalin uwar kud'insu sannan suka ware tarin ribar da suka samu na gefen maggi da kuma sauran kayayyakin abincin da kud'in hayan fiinsu Alhamdulillahi kasuwa kuwa tayi Al'barka dama ance kad'an mai al'barka yafi mai yawan da akasa dan zalumcin,

ware kud'in sukayi na maggin jarin da ribar wanda ya basu million uku , 

sai suka rabasu suka kuma saran maggi million biyu,

sannan suka d'auki million d'aya suka sari 'yan kayayyakin masarufi kamarsu, 

spaghetti,  macaroni,  indomi, sugar, fulawa, da buhunan madarar awu ajiniyo moto, suka had'a da sarin maggin nasu.

Sai kuma suka had'a jari da ribar kayan abincin dana hayan bappa Ali ya fara bin kasuwannin k'auyuka yana sari babu kama hannun yaro,

saida ya cika d'akunan iyayensu mak'il ,

sannan ya fara sara yana sawa Warisu na kaisu kasuwa cikin shagonsu tuni shago ya cika mak'il, 

masu sari sukayo musu caa ko yaushe kazo bakin shagon zaka samu dafifin mutane mata da maza manya da yara, 

ganin haka yasa Saifuddeen fasa asusunshi na wata hud'un ya fito da kudad'en suka sari buhunan al'kama da acca suka had'a a ciki.


Nan fa kasuwa ta d'auka sosai da batun shagon Butu da yawa suna son sanin asalin mai shagon kuma sun gaza ganewa, 

dan wasu kance ai shima wannan shagon butun reshen shagunan Ba miskila ne da yawa kuma suna yarda da haka ganin babban yaron shagon ba miskilan a shagon butun Bello kenan, 

wasu kuma na cewa shagon Bappa Ali ne, wasu ko na cewa na Warisu ne,

sam dai mutane basu gane sahihancin zancenba sunata kame-kame dai,

Saifuddeen kuwa time to time yake lek'a shagon.


Salisu kuwa sosai yake jin dad'in sabuwar machine d'in da Saifuddeen ya saya mishi inda yaketa karatun shi a F, C, E Gombe.


Su Ahmad da Mudassir kuwa Karatu yayi nisa hakama Salisu, 

tuni Saminu kuwa sune masu gama wannan shekaran.


Yayinda Saifuddeen kuwa sune 'yan level 100.


 Bayan shekara d'aya, kasuwa taci gaba da gudana komai yana tafiya dai-dai da tsari na taimakon talakawa da marasa k'arfi.

Kullum jarinsu habaka yakeyi da d'an riban da suke bi da kuma kud'in hayansu, 

inda kayan masarufi yake mallakin jarin Saifuddeen ne halak d'inshi ba surkin kud'in gadonsu. 


Yau kusan wata d'aya kenan Saifuddeen da Bappa Ali sunata kan harhad'a cinikinsu na tsawon shekarar suna ware ribar su da hauhawar jarinsu.

Koda suka gama had'e komai sai suka fara ware hak'insu Bello da Warisu sunka biyasu biya mai daraja a matsayinsu na masu kula da kasuwancin, 

daga nan kuma suka ware adadin zakkar da zasu fidda na shekarar bayan sun gama ware zakkar tasu, 

sun bawa wad'anda shariya ta misalta da a basu sai kuma suka fara shirye-shiryen sari tako wanne sashi inda Bappa Ali zai sarar musu kayayyakin abinci a kasuwannin k'auyuka kamar yadda suka saba, 

shiko Saifuddeen zai yi musu sarin kayan masarufi wanda wasu direct daga company yake musu sarin shiyasa suke samun damar sakin farashinsu da rahusa,

dole zuwa yanxu sunfi k'arfin shago d'aya hakan yasa suka nemi k'arin hayan wani k'aton shagon dake kusa da nasu, ba b'ata lokaci aka basu da yake na Alhaji Kabiru ne,

cikin kwana uku aka had'a shagunan sannan aka barsu da k'ofofi biyu.


Ya Adnan kuwa tuni ya isar da batun soyayyarshi da Adda Rahma ga manya tuni mgna ta kankama dan iyayensu Adnan sun san nagartar Rahma tunda a gabansu ta girma shiyasa basuyi wata rigimaba,

tuni antsaida ranar aurensu bayan sallan layya da mak'o d'aya.


Saminu kuwa ya gama karatunshi har ya samu damar tafiya bautan k'asa mgnar sosayyarshi da Raihana kuma tanata kankama har iyaye sun shiga, 

an bari a kan cewa sai ya gama bautan k'asanshi ya fara aiki sannan ayi musu auren.


Mudassir da Ahmad da Ishaq ma duk sun kusa gamawa.


Hayatuddeen kuwa shima yana shekararshi ta k'arshe a primary school,

Faruq kuwa yana primary 3 Adam na primary 2,

Raliyya kuma tana SS 1.


Abba yaron Bappa Ali shima ya girma har an yayeshi.


Rayuwa dai taci gaba da gudana cikin nasara da ci gaba.


Anyi bikin Ya Adnan da Rahma lfy an watse lfy,

ta tare a gidanshi dake cikin Gombe wanda yake cikin jerin gida jan ma'akatan lfy na   Medical Center Gombe, 

wannan had'i yayi matuk'ar yiwa Ahmad da Mudassir dad'i dan dama a gidan Ya Adnan d'in suke sukewa kansu girki a cewarsu yanzu sun huta sun samu mai musu girki.


Bayan bikin da mako ukune Ya Adnan yaje har dukku da batun yana son a basu Faruq da Adam a cewarsa zai rik'esu,

to Ummi dai tak'i amincewa ganin ya tasa gabata da magiya ne yasata ce mishi Saifuddeen ne ya hana ba itaba kuma shi yana can gomben,

jin haka yasa Ya Adnan tura mishi text cewar,

yana son ganinshi gobe, yana ganin text d'in ya maida mishi amsa da to Allah ya kaimu.

daga nan Adnan ya sallami Ummi ya tafi gidansu a nan ya wuni sai da yamma ya koma.


Washe gari da safe Salisu da Saifuddeen ko breakfast basu tsaya yiba suka wuce cikin gombe,

kasan cewar basu da lectures   da wuri sai zuwa k'arfe biyu so kai tsaye gidan ya Adnan suka nufa,

a harabar gidan Salisu yayi parking, 

sannan suka nufi bakin mashigar ainihin  cikin gidan,

a bakin k'ofa suka tsaya door bell suka d'an danna, 

jim kad'an aka bud'e k'ofar ganin Ahmad ya bud'e musu k'ofar ne yasa su yin murmushi shima murmushin yayi tare da bawa Salisu hannu tafawa sukayi cikin salon gaisuwa ta abokai da suka shak'u da juna, 

sai ya kuma juyo ya d'aga hannu alamun zai tafa hannu da Saifuddeen da k'arfi irin yadda yayi da Salisu, 

shi kuwa Saifuddeen ganin haka yayi saurin janye hannunshi tare da rab'awa gefenshi ya wuce yayi cikin parlour,

cikin dariyar shek'iyanci Ahmad ya kalli Salisu da shima dariyar yakeyi, sai ya kuma juyo ya kalli Saifuddeen da tuni ya isa tsakar parlour suna ruggume da juna shida Mudassir, dariya ya kumayi tare da cewa. 

"Hege mai d'an karen son jiki da tsoron wahala."

cikin dariya Salisu yace.

"Yaseen gskyanshi nima d'in ai bani kuma yarda ka kima min wannan hannun naka, kalli yadda hannuna yayi jazir hege mai suffar samudawa."

duka ya kaiwa Salisu,

da sauri ya kauce tare da cewa. 

"Wayyo Ya Adnan kaga Ahmad ko."

da sauri Rahma ta yunk'ura zata tashi ta fita jiyo muryar Salisu tasan sarai da Saifuddeen suka zo.

Shi kuwa Ya Adnan da sauri ya jawota jikinshi tare da cewa.

"Ina zakije?."

fuska ta d'an marairaice tare da cewa. 

"Parlour zanje kaji su Saifuddeen sun zo."

ido ya d'an kashe mata tare da cewa.

"Barsu suyi ta sabgoginsu muma muyi namu in mun gama ma fita."

cikin sanyi tace.

"Allah ko nayi missing Saifuddeen tunda akayi bikin nanfa bai zoba."

mik'ewa yayi tare da kamota ya tsayar da ita sannan yace.

"To muje muyi wonka."

a dole ta bishi suka shiga bathroom.


Su Ahmad kuwa a falo hira sukayi tayi na yaushe gamo, 

daga nan suka shiga kitchen suda kansu suka fara kiciniyar had'a breakfast nasu.

to Ahmad da Mudassir su sun iya sun saba, 

Salisu da Saifuddeen kuwa basu iyaba, 

shiyasa suka kame suka zauna gefe,

Ahmad na fire dankali shi kuwa Mudassir yana kiciniyar tafasa musu ruwan tea.


Bayan kamar 35 minutes Rahma da Adnan suka fito a tare a parlour ta tsaya tana kasa kunne dan jiyo ta inda hayaniyarsu take,

jinsu a kitchen ne yasa tayi sauri ta nufi kitchen d'in tana shiga duk suka juyo murmushi tayi musu ganin duk suna murmushi, 

sai kuma Saifuddeen yayi saurin tasowa ya iso gabanta murmushi ya kuma yi tare da mata alamun,

"Iye-iye kinyi kyau fa."

kunnenshi ta d'an rik'e tare da d'an matsewa da d'an k'arfi, d'an tsalle yayi tare da yarfa hannu,

Ahmad kuwa sai tsalle yakeyi yana dariya tare da cewa. 

"Yauwa Adda Rahma matse da kyau."

Mudassir kuwa fuska ya kwab'e tare da cewa. 

"Please Adda Rahma sakar mishi kunne kinsan baya son wahala."

Salisu ne yayi dariya tare da cewa. 

"Kaji banza to waye ke son wahala, 

kuma a yar wannan matsarne wahalar."

shi kuwa Saifuddeen hannunshi d'aya yasa ya kamo d'aya kunnenshi cikin body language ya mata alamun ya tuba.

ganin haka yasa ta sakar mishi kunne tare da cewa.

"Zaka sake yin sati uku har kusan hud'u baka zoba kuma kana cikin lfy."

Kai ya jujjuya mata yana mai shafa kunenshin,

daga nan sukaci gaba da hira tana mai tayasu aikin nanda nan suka gama girkin suka jera komai a dinning table, 

daga nan suka zauna suka karya,

Saifuddeen ne ya fara cire hannu sai kuma Rahma sannan Salisu nandai duk sukaci sukayi nak, 

suna gamawa Ahmad ya tattare wurin sannan ya nufi d'akinsu dan yana son watsa ruwa, 

Salisu ne yabi bayanshi sai kuma Mudassir.


Ya Adnan kuma gyara zama yayi tare da cewa.

"Ummi ta gaya maka dalilin kiran da nake maka ne?."

kai ya jujjuya mishi  alamun a a,

cikin nitsuwa Adnan yaci gaba da cewa. 

"To batun Faruq da Adam ne naje jiya dan zan d'aukosu su dawo nan da zama a gabanmu zamufi samun konciyar hankalin da damar basu kulawar da ta dace a matsayinmu na iyayensu, sai Ummi tace min wai ai ka hana, 

shiyasa na nemeka inji dalilin da yasa zakace kada a bamu su."

kanshi ya d'an sunkuyar cikin dottaku da sanin ya kamata ya kuma d'ago kanshi tare da mishi mgna cikin body language yace.

"Ba komai kawai dai naga gidan naku a cike yake gasu Ahmad sannan kuma kace zaku k'ara dasu Faruq,

kuma nasan Baba Hamisu bazai amince ba."

murmushi Adnan yayi tare da cewa. 

"To jiyan ai saida na fara zuwa wurin baba Hamisun na nemi al'farma kuma ya amince, hakama Bappa Ali sai dai in kai d'inne zaka k'i amincewa ban saniba ko ban dace da a bani su bane."

da sauri ya jujjuya mishi tare da zaro wayarshi ya rubuta mishi.

"Ba haka bane Ya Adnan wlh bana son rabuwa da yaran ne, 

hakama Ummi itama suke d'ebe mata kewa, 

sannan Hayatuddeen shima sune masu d'ebe mishi kewa tun kafin ayi auren yaketa cemin kar in bari Adda Rahma ta tafi da yaranshi fa."

ita kam Rahma ido ta lumshe lokacin da Adnan ke karanta rubutun, 

tasan duk farin cikinta sukeso tasan irin son da Saifuddeen kewa su Faruq, 

tasan shi kuma ya Adnan yana son yaran sosai kuma yasan zatafi samun farin ciki in suna kusa da ita ido ta zubawa mijin nata kuma abokin yayanta jin yana cewa. 

"Dan Allah da sonka da manzosa ku bamu yaran nan mahaifiyarsu zatafi samun nitsuwa tashi d'aya a rabata da yaranta abin da ciwo a rai."

da sauri Saifuddeen ya zubawa Rahma idanu ganin tana zubda hawaye alamun tabbas tana tare da kewan yaran nata.

Hannunshi yasa ya sharte mata hawayenta sannan ya amshi wayarshi tare da rubuta musu. 

"Kiyi hak'uri Adda Rahma kada ki zubda hawayenki  kinsa Raihana da Raliya zasuyiwa su Faruq duk abinda uwa ke yiwa d'anta kinsan Ummi kuma zata basu ink'antacciyar tarbiya,

ni kuma zan zame musu uwa uba."

kai ta jujjuya tare da cewa. 

"Na sani Saifuddeen na sani ai ni kaina ka zame min uwa uba bare yaran da nasan ka fini sonsu duk da ni na aifesu."

 sai kuma hawaye yaci gaba da zubowa ganin hakane yasa Saifuddeen mik'e tare rubuta musu.

"To ba matsala zan kawo muku Adam amman kuyi hak'uri bazan iya baku Faruq ba."

murmushi yayi ganin itama tana murmushi shi kuwa Ya Adnan dariya yayi tare da cewa.

"To Hamma Saifuddeen mun gode a hakanma,

dan naga yanzu ka zama kaine babba  a kanmu."

dariya sukayi baki d'aya sannan suka mik'e suka dawo parlour  

cikin kula Rahma tace.

"Saifuddeen zo ka duba bedroom mana ka kashe min kud'i kuma baka zo ka duba kayan d'akinba kaga yadda parlour kam yayi kyau ko d'an uwana."

murmushi yayi tare da mata alamun.

"No shi bazai shigaba komai yayi kyau."

sai ya kuma mata alamun in akwai abinda take buk'ata ta gaya mishi, cikin jin dad'i tace. 

"Ka gama min komai d'an uwana ba abinda baka yi minba komai sabo ko budurwa bazata nuna min sabbin kayaba."

sai ta kuma kalleshi tare da cewa. 

"Yauwa dama ina son in ce maka kasa su Raihana su jerawa Ummi tsoffin kayan d'aki na d'in nata kuma ta bawa Goggo Dada su."

kai ya jinjina mata alamar to,

sannan ya nufi d'akinsu Ahmad nan sukayi ta hirarsu ta abokai, 

sai k'arfe tara Saifuddeen ya mik'e ya shiga bathroom wonka yayi yana fitowa yasa kayan Ahmad  daga nan suka fito da shirin tafiya dubu uku ya bawa Adda Rahma kana ya bawa Ahmad da Mudassir dubu bibbiyu sannan suka sallamesu suka tafi.


A daren ranar yaje ya gayawa Baba Hamish batun ya Adnan ya nemi da a basu Adam.

Cikin aminci baba Hamisu yace ba matsala a basu. 


Washe gari ya rarrashi Ummi ya samu ya kai musu Adam.




                        *************


Lokaci yaja kwanaki sun tafi makonmi sun gibta sun juye ih zuwa shekaru. 

Rayuwa taci gaba da tafi, 


Al'barka yanata ratsa dukiyar marayun nan yayinda adalcin Saifuddeen yake tasa dukuyar habaka, 

tausayinshi da gskyanshi da taimakonshi da yawan sadakanshi ya zamewa dukiyarshi Garkuwa.


Abubuwa da yawa sun faru a shekarun nan.


Tuni Saminu ya fara aiki a kaduna har an aura mishi Raihana. 

Suna can kaduna garin gwamna mai mata had'i da mota. 


Ahmad da mudassir da Ishaq ma sun gama karatunsu, 

tuni har ishaq ya samu gurbin karantarwa a jimi'ar Gombe state University, 

wanda wannan abu yake matuk'ar bawa mutane mamki ganin gashi makaho kuma yayi karatu kuma gashi har yana karantarwa.


Mudassir  kuwa da Ahmad basu samu aikin yiba kasan cewar yanayin k'asar ne digiri ya zama ruwan dare ko wanne gida da akwai sai dai samun aiki sai d'an talaka yayi dace,

wannan dalilin yasa Saifuddeen ya jawo Ahmad da Mudassir cikin kasuwancishi cikin ikon Allah kuwa taurarinsu suna haskawa kasuwancinsu yaci gaba,

kasan cewar dama shi Ahmad business administration ya karanta shi ya bawa kasuwansu damar habaka gabas da yammaka kudu da arewa.


Alhamdulillahi shima kanshi Saifuddeen da Salisu sun gama karatunsu,

to amman basubi ta kan neman aikiba, 

dan a ganinsu duk sunada sana'a kawai dai sun nemi ilimin ne dan shine gishirin rayuwa,

to ta inama zasu fara tunda sunaga Ahmad da Mudassir ma shekaru biyu kenan har zuwa uku da gamawarsu basu kuma samu aikinba bare su da kwanannan suka gama bautan k'asarsu.


Zuwa Yanzu ko bappa Ali bai san adadin dukiyar da Allah ya azurtasu da shiba shi,

Saifuddeen ne kad'ai yasan k'a'ida da adadin dukiyarsu, kasan cewar shi yana ajiye komai a rubucene yanayin hakane kuma dan ta hakane zasu san adadin zakkar da zasuke cirewa duk shekara.


Ganin harkar k'arfe ya karb'i Salisu to sai ya bare kud'i kimanin 3 million ya bawa Salisu ya fara zuwa sarin motoci a Cotono da mota biyu rak ya fara sari yan million d'aya da rabi-rabi cikin ikon Allah a ko wanne mota ya samu ribar dubu dari  uku-uku, koda ya ware kud'in mai da kud'in sauran uzururruka da kud'in da ya biya wanda ya tashi d'auko motor ya samu sauran ribarsa dubu dari uku da hamsin,

nan yaje ya bawa Saifuddeen su,

shi kuwa Saifuddeen yace bazai karb'i ko asiba, 

yace yaci gaba da tara ribarsa randa ya samu ya tara koda 5 million ne sai ya maida mishi kud'inshi million ukun shikenan daya bashin,

shi kuma ya d'auki wannan na ribar tashi yaci gaba da sari ya samu jarinshi kenan da haka, 

ya k'ara da cewa ya bar mishi su halak malak.

to fa daga nan Salisu ya fara harkar mota babu kama hannun yaro kuma Alhamdulillahi harkar ta amsheshi.


Shagunanshi a kasuwa kuwa yanzu Warisu da Bello da Mudassir suke kula dasu yayinda Ahmad kuma ya zama tamkar manajansu,

shine ma'ajiyinsu yakan fita zuwa su Lagos onitsha da dai sauransu yayi musu sarin kayan masarufi, direct to company.


Bappa Ali kuwa shine mai sarin kayan abinci ciki da wojen gombe Alhamdulillahi yanzu abun ya hab'aka shiyasa yawanci da Warisu yake shiga sauran k'auyuka na sauran jihohi kamarsu.

Bauchi, Jigawa, Jos, da Adamawa musamman kasuwar cigari ta adamawa inda nanne dilar manoman shinkafa na jihar.



Ummi taje makka ta sauk'e farali hakama bappa Ali da goggo Dada,

shima Saifuddeen yaje tare da Adda Rahma Ya Adnan kuwa ya biyawa kanshi da mamansu so duk a shekara d'aya sukaje.


To da yayi niyar Raihana da Raliyya duk zasuje shekarar data gabata, 

inda yacewa Hayatuddeen yayi k'ok'arin haddace izu arba'in kafin nan to zai had'a dashi suje, 

aiko Hayatuddeen yasa himma, 

to yanata shirye-shiryen biya musu hajjin kwasam,

sai Alhaji Kabiru ya kawo mishi tallan wani gida dake kusa da gidanshi a nan federal low cost.


Koda ya samu Ummi da Bappa Ali da zancen sai Ummi tace ya bar batun biya musu hajjin ya bari sai wata shekar in Allah ya kaimu, 

a cewarta kadarar babban filin da mahaifinsu ya bar musune suka saida suka kama sana'ar dan haka yayi k'ok'ari ya sai wata kadarar da zata ke tuna mishi da gadon da mahaifinsu ya bar musu.

shi yaso ya biya musu Hajjin to amman fir Ummi tak'i hakama bappa Ali dole ya hak'ura yabi ra'ayinsu.


Sai dai kuma  cikin ribar ledanshi da yake tarawa tsawon shekaru da balance d'in machine d'in da Salisu ya rik'e tsawon shekaru da kuma wanda iro yake kawowa har yanzu da kud'in ne yace zai sai gidan sabida baya son tab'a wannan dukiyar gadon nasu yafi son ya sayi gidan da guminshi shi d'aya yadda zai zama halak makal d'inshi, 

Ummi da bappa Ali sun amince da haka to amman kud'in nashi basu wuce rabin kud'in gidanba dan haka sai ya ranci sauran rabin kud'in a cikin tarin ribarsu na shekarar da zumar zai biya kud'in da balance d'in machine d'inshi da kuma ribar ledodinshi da omonshi da su pure water da ribarshi na gefen kayan masarufi wanda yanzu k'atun firijine ya saya ya ajiye a bakin shagonsu sannan yana saran omo yana sawa a gefe kuma har yau yakan rarraba leda ya kuma had'a kud'insu ya basu sannan ya cire ribarsa, 

to duk wani abu daya sani dukiyarshice ta kanshi wanda ya tara da guminshi to a account number daya kuma bud'ewa na musamman yake sa kud'in a ciki.

so hakan ne yasa suka amince da hakan cikin wata biyar akayi cikinikin gidan aka gama, 

sosai cinikin gidan ya zabge asusunsu Saifuddeen ya kuma sashi cin bashi,

sai dai kuma duk wanda yaga gidan yasan lallai tabbas gidan yaci wannan milliyoyin kud'in.


To fa tun randa Hayatuddeen yaga gidan ya kasa ya tsare dolefa su k'aura su bar dukku, 

haka zai tasa Ummi da Saifuddeen a gaba harda kukanshi shidai a bar wannan k'auyen dashi.


Ahmad da Mudassir kuwa har yau a gidan Adda Rahma suke, 

ita kuwa Adda Rahma har yau Allah bai basu haihuwa da Ya Adnan d'intaba.

Warisu da Salisu kuwa suma yanzu an kusa bikinisu inda sun gina 'yan madaidaitan gida jensu a cikin unguwar Dubai cottars.


Ishaq kuwa shima yanzu ya fara taka k'asa, 

tuni yayi gidan kanshi saidai har yanzu bai fara neman aureba,

yafi maida hankalinsu wa kula da k'ungiyarsu ta,

Joint national association of persons with disabilities,

(Jonapwd)  gombe 

state chapter. All the best!!!  yayinda yanzu shi har ya samu muk'amin ciyaman a kungiyar,

Saifuddeen kuwa bai fiye zuwa ofishin nasuba sai dai yana matuk'ar bada taimako da dukiyar da Allah ya bashi ta sanadin nema da guminshi kusan akwai kason daya ware duk wata yakan saka a asusun k'ungiyar, 

baya zuwa amman hannunshi na zuwa sai dai in zasuyi Mittin mai girma da mahimmanci to Ishaq na sashi zuwa bisa dolen-dole da zaran an gama mittin kuma zai tafi.


Ahmad kuwa soyayya yake zubawa Raliya sosai.


Yauma kamar kullum Hayatuddeen ya tasa Ummi da Saifudden da Rahma da tazo duba jikin Mamansu Ya Adnan a gaba,

 fuska ya kwabe tare da tura baki cikin kalato hawayen dole yace.

"Dan Allah mu bar zancen auren Ya Ahmad da wannan yar cukului d'in shin nan."

bai kula Raliyya dake watsa mishi hararaba yaci gaba da cewa.

"Ni dai dan Allah ku rufa min asiri mu k'aura mu bar wannan gari na dukku wallahi ni dai na gaji da garin nan."

cikin irin son da iyaye ke yiwa 'yan autansu Ummi tace. 

"Wai ni kam ku saurari autana d'innan mana yace muku ya gaji da dukku."

fuskarshi ya kuma kwab'ewa tare da cewa 

"Ba waninnan Ummi ai duk kece kikak'i ki amince na san in kin cewa Hamma na mu k'aura dai zai yarda."

Rahma ce ta gyara zamanta cikin sanyin muryarta tace.

"Wallahi Allah ko Ummi nima ina son ku k'aura ku dawo cikin gombe kusa dani, 

ku ganifa bani da kowa a can dan ma Allah yayi Mamansu Ishaq tanada kirki,

wlh ko Ya Adnan ma cewa yayi ya dai kamata ku dawo gombe ko dan karatun Raliya da Hayatuddeen,

dan cewa yayi ya kamata ace Raliya taci gaba da karatu ta samu koda N,C,E ne tunda sun nacewa juna ita da Ahmad kuma shi yace bai yi aure a gidan hayaba, 

gashi kuma ya kasa k'arisa ginin gidanshi."

shi dai Saifuddeen ido ya zuba musu dan shi kanshi ya gaji da wannan zirga-zirgan kuma yana son faranta ran Hayatuddeen da Faruq,

shiru sukayi jin Faruq na cewa.

"Nima dai wlh na gaji da k'auyen nan yaseen ko mu k'aura mu koma gombe, ko kuma inbi Ya Adnan in koma gidansu."

cikin nitsuwa Ummi tace. 

"To Saifuddeen ka jisu ko?."

Kai ya gyad'a mata alamun eh yaji, 

cikin sanyi tace.

"To nima da kaina ina son mu koma cikin gombe ko dan tak'aitawa Saifuddeen zirga-zirgan da yakeyi kullum yana hanya tsakanin Gombe da dukku, 

to sai dai haka kawai in na tuna mu k'auran sai inji zuciyata ta tsinke wani azabebben fargaba yazo ya rufeni shiyasa jikina ke mutuwa."

Da sauri Rahma tace. 

"In sha Allah ba komai sai al'khairi kawai dai inaga fargaban rabuwa da inda kika saba ne shiyasa kikejin hakan."

kai Ummi ta jinjina dan kamar ta gamsu da mgnar Rahma, 

cikin sanyi tace.

"To na amince Babana in dai kana son mu k'aura to na amince."

da sauri Saifuddeen ya kalli Hayatuddeen da Faruq da suka durk'usa gabanshi suna ta magiyar dan Allah yace shima ya amince."

kai ya gyad'a musu alamar to ya amince.

Ido suka zazzaro gaba d'ayansu dan ganin wani irin...!





                         By

                *GARKUWAR FULANI*

8/18/20, 7:51 PM - Ummi Tandama: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


       *NAKASA BA KASAWA BACE*


                              *PAGE 11*

          

                                  NA

             *AYSHA ALIYU GARKUWA*


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇



~Dan Allah kuyi haƙuri masu cewa in rufe group bazan rufeba! Sabida inada dalilin barinshi a buɗe~


_Lale marhababikun masoyan littafin Nakasa ba kasawa bace ina maraba daku, turo katin mtn na 300 kacal ta wannan number! 09097853276. Ko ka/yimin transfee ta bank ac na 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, pleess ku fahimceni ɗari uku nace kuma ga number da zaki turo tanan ko ac no ɗina_



_Dan Allah dan soyayyarmu da annabi kuji tsoron Allah ku dena tambayata tsoffin littatafaina, sai kuzo ku haɗani da Allah in ban kulakuba inji ba daɗi, dan Allah 🙏🏻 ku bari bana so! Pleees fans ɗin hukuncin Allah da suka saya wai yanzu basu dashi ku dena tambaya bana so😡ku tambaya a gruops ɗin Hukuncin Allah,  bana son shegen takura da rashin tausayi ,fisabilillahi a wuni zan samu pc sama da 1000, masu sabon littafi da masu son tsoffi da ƴan gaisuwa da wasu ga tarin rashin fahimta nayi bayani inda za'a turo kuɗin da adadin da za'a turo amman sai kaji ana, Slm Aunty Aishs ta ina zan turo/ koko Garkuwa nawane kuɗin littafin koma kece Garkuwa en nace eh sai ace wai  ,a a ƙarya kike ba kece  Garkuwa ba, ko kuma wai Garkuwa nake nema, koko wai dan Allah turo min littatafai masu daɗi jifa kamar ni baiwarsu ce ƴan gab da kano kawai yaseen ku ba ƙanenne uwata bace da amsa muku zai zame min wajibi_




 Zabura da yayi tare zurma ihu mai cike da jin dad'i sai ya kuma zaro woyarshi dake cikin al'jihunshi samfarin infinix Hot 5 wanda a lokacin ita ake yayi, kid'i ya kunna tare da fara zabga rawa baji ba gani,

yayinda Faruq ma ke take mishi baya,

cikin yanayim fad'a Saifuddeen ya watsa mishi harara tare da mishi mgna cikin body language yace dashi.

"Irin godiyar da ya kamata ka yiwa Allah kenan bisa wannan ni'imar da yayi mana? rawa da ihu shine kaga ya dace?."

kai ya jujjuya mishi yana mai ci gaba da jujjuya k'ugunshi ganin haka yasa Saifuddeen yi mishi alamun cewa. 

"To na fasa tunda hakane tunda bazaka nitsuba sai randa kayi hankali ka nitsu zamu k'auran."

da sauri ya nitsu tare fuskantar gabas kana ya gyara tsayuwarshi sannan yayi sujjadar godiya ga Allah,

yana d'agowa daga sujjadar ya fuskanci Hamma Saifuddeen d'in nashi cikin sanyi yace.

"Hamma Saifuddeen na nitsu dan Allah kada ka fasa kaji d'an uwana."

k'ara matsoshi yayi ganin bai kulashi ba sai ya kuma raunata fuskarshi sannan murya na rawa yace.

"Na tuba Abba."

cikin tausayin yaron Saifuddeen ya gyad'a kai dan duk sanda zai nuna mishi biyayya irin na d'a da uba to yakan ce dashi Abba.

tsalle yayi ganin Hamman nashi ya huce,

sai ya kuma lallatsa wayarshi sannan ya kara kunne jim kad'an aka d'aga.

Cikin tsananin jin dad'i yace.

"Hello Imran al'bishirinka."

A can d'aya sashin kuma cikin d'aga sauti da yanayin rawan kai da rigima irin na Hayatuddeen Imran k'anin Ishaq yace.

"Goro fari k'al ba dukke bani insha."

dariya Hayatuddeen yayi tare da cewa.

"Da kenan!  yaseen yanzu Bagombe nake, 

Hamma na da Ummi da Bappa Ali sun amince zamu k'auro."

wani wawan zabura imran yayi tare da zurma tsalle ya saki ihun da saida Ishaq dake gefenshi ya mik'e tsaye Mama kuwa dake bedroom ta fito parlour da gudu tana cewa.

"Innalillahi Imrana lfy kuwa meya sameka."

rawa yayi ya kuma juyawa sannan cikin karad'i yace.

"Su Hamma Saifuddeen zasu k'auro zasu dawo gombe,

yanzu Hayatuddeen yake gaya min."

sai ya kuma manna wayar a kunne tare da cewa.

"Hello Ba dukke kace wannan shekarar tamu ce lokacinmu ne kace birnin gombe zai amsa da rayuwar zafafan samari."

tsalle yayi tare da cilla woyar tashi  jin Ishaq ya kama mishi kunne cikin yarfa hannu yake cewa. 

"Wayyo Ya ishaq na tuba."

"K'arya kake baka tuba ba nasan ina sakeka zankaci gaba."

cewar Ishaq kenan Mama kuwa cikin farin cikin k'aurowar dasu Hayatuddeen zasuyi tacewa ishaq.

"Kai maza sakarmin kunnen d'an autana,

barshi yayi farin ciki, 

nasan kaima d'in zakayi naka tsallen a side d'inka."

dariya sukayi baki d'aya kana suka zauna a parlour sukaci gaba da hirar, 

mik'ewa Imran yayi ya d'auki wayarshi dake gefen Mama, 

Suleiman ya kira wani abokinshi da suke yawan mgnar Hayatuddeen dashi ana d'aga woyar Sulaiman d'in yace.

"Hello Sulaiman."

da Sauri d'aya abokinsu mai suna Zakariyya wanda shine ya d'aga woyar Sulaiman d'in yace.

"Hege to ba Sulaiman bane Zakine."

dariya suka kece dashi baki d'ayansu sannan imran yace musu.

"Ba dukkenmu fa zasu k'auro zuwa nan cikin Gombe."

Sulaiman dake gefene yana jinsu yace.

"Yanzu Isma'il yamin text yake gaya min wai yaga Hayatuddeen ya fad'a a cikin what's app group d'inmu wai zasu dawo cikin gombe."

nanfa sukayi ta murnar dawowar da Hayatuddeen zai a kusa dasu dan sun saba sosai a media kuma duk sanda Hayatuddeen yazo gidan Adda Rahma to ranar dai su duka a gidanta suke wuni,

Imran, Hayatuddeen,  Sulaiman, dan alhaji Sani, sai Isma'il d'an Alhaji Kabiru,

Sai Zakariyya wanda d'ane ga wani babban malamin da k'asarmu baki d'aya ke ji dashi,

kani kuma ga wani babban Pilot,

k'ani kuma ga wata shaharartiyar 'yar jaridar da taurarinta ke haska tutatar yayinda iska ke kad'a igiyar budurcinta kenta ya zama tamkar manuniya a gareta, *Zaleeha* sai kuma wasu sauran 'yan uwanshi...!

 

                        *****


Wata uku akayi anayiwa gidan duk kan gyare-gyaren daya kamata duk da dama gidan bashi da wani makusa yau aka gama komai na gyaran gidan. 



Washe gari kuwa da Saifuddeen yazo shida Salisu a wata zazzafar motar da ys sarota a wannan satin.

kai tsaye gidan Adda Rahma suka nufa,

 nan suka had'u baki d'aya, 

Saifuddeen, Ishaq Salisu Ahmad, Warisu, Mudassir,

suka nufi federal law cos sukaje ganin gidan.


Suna isa gidan duk suka shagala da ganin kyau da girman gidan uwa uba da tsaruwarshi.

Gidane mai girma wanda yakeda zagaye da dogayen bishiyoyin nan na gidajen 'yan gayu ga kuma gajerun fulawi da yayiwa k'asan dogayen bishiyoyin nan k'awanya, sai daga cikin gidan wanda yake da wadaceccen parking lot ta gefen dama,

wanda zai iya d'aukan motoci bakwai zuwa takwas,

sai d'an wani d'aki mai girma wanda yakeda bathroom a ciki,

sai yar barandarshi ta gefen barandar kuwa akayi wani d'an rumfa mai girma in ka ganshi kamar d'aki wanda shima

 yakeda bathroom a ciki,

can gefen hagu kuwa BQ ne mai d'an girma wanda yakeda d'an madaidaicin parlour sai two bedroom ko wanne da bathroom a ci sai  d'an k'aramin kitchen da dinning area, 

kana fitowa harabar gidan zaka fuskanci wani tsarerren gini mai tsananin kyau da d'aukar hankali,

daga harabar gidan wani babban corridor ne wanda ko motace zata iya ratsawa ta nan ta wuce, gefe da gefen corridor d'in duk fulawowine a shuke kansu dai-dai sunyi cib-cib dasu sunyi kore shar, 

sai kuma fitilun dake biye da layin d'an dakalin da abakinshi aka zagaye fulawin

tafiya mai d'an nisa zakayi zaka ratsa ta wani dank'areren  side mai girma wanda yake d'auke da wasu plat masu azabar kyau,

 plat d'in guda biyune wanda suna gab da gab da juna,

daga tsakiyarsu anyi wani rawun da fulawowi masu d'an karen kyau da d'aukan hankali colors d'insi green and yellow sai ratsin pink suna da d'an tsayi sai hamyoyin shiga cikin zagayen fulawowin aka bari guda biyu, 

bima'ana ko wanne part akwai kofar shiga ta gaban barandar.

cikin rawun d'in kuwa wata yar madaidaciyar bishiyar mangoroce wacce bata da tsawo sosai dan wasu ganyayenta har suna tab'a fulawowin sai  'yan k'ananun fulawowin da akayi musu zubin zanen  heart daga nan tsakiyar heart d'in kuwa sai tattausan ciyawar grass carpet koro shar dashi, 

sai wasu tim-tim d'in fulawowin da in ka gansu zakace kujerun zamane dan suna zagaye da heart d'in,

sai wani dogon k'arfe da kwan fitala guda buyi a jikin k'arfen,

 sai kuma wani d'an pompo dake nan gefen wurin kusan dashi akeyiwa fulawin wurin ban ruwa.

Sai bakin barand'ar mashigar Part d'in duk suma suna zagaye da fulawowi,

barandar irin mai fad'in nanne, 

marfin k'ofar parlour kanshi abin kallone,

kana shiga daga ciki wani tamfatsetsen parlour ne mai girma, 

wanda daga gefen dama akwai wata k'ofar wanda kana shiga cikin zaka ratsa wani parlour mai girma wanda yake d'an madaidaicin dinning area, 

sai bedroom mai girma wanda yakeda babban bathroom,

sai kuma gefen hagun asalin banban parlour da aka fara shiga, 

wani tamfatsetsen dinning area ne mai girma wanda sai ka taka wasu step guda uku kafin ka hau wurin dinning d'in,

daga nan cikin dinning d'in gefenshi k'ad'an wani d'an corridor ne wanda gab da mashigar corridor akayi wani d'an wuri kamar na ajiye firij sai wata babbar k'ofa dake  ciki wanda yake d'auke da tam fatsetsen bedroom mai girma sai bathroom shima k'ato,

sai d'aya gefen na cikin wurin dinning area d'in,

wanda yakeda kofofi uku d'aya kofar wani d'an madaidaicin d'akine wanda yakeda d'an ma daidaicin bathroom, 

sai d'aya kofar shi kuma d'an k'aramin d'akine babu bathroom bisa dukkan alamu sito ne,

sai kofar dake gaba dashi shi kuma wani tamfatsetsen kitchen ne wanda yake,

daga cikin kitchen d'in kuma akwai wata kofar da kana bud'ewa bakiyat nasune  sai dai bakin kofar anyi wani k'aton baranda irin na asalin mashigar babban parlour, 

sai dogon luggu da yayiwa part d'in kawanya sai manyan igiyoyin shanya da ke d'aure guda uku sai pompo a dake wurin, 

sannan sai jerin fulawowi da futilun dake mammane jikin ginin.

wanda koda da dare ne zakaga kamar da ranane.

to shima d'aya part d'in haka yake, 

wannan ciki da parlour da dinning area ne kawai ke tsakaninsu.


daga nan kuma sai can cikin gidan wanda gidan samane mai girma.

kana shiga asalin wannan corridor direct har bakin k'ofar shiga cikin part d'in dake k'asan gidan saman ne inda gefen shi kad'an akwai bishiyar dabino wacce take 'yar d'ugus da ita sai yawan haihuwa.

wanni k'aton parlour ne mai d'auke da wani babban dinning area, sai wani dogon corridor wanda yakeda kofofi biyu suna fuskantar juna bedroom ne da bathroom nasu masu girma, 

sai kuma can gefen hagun parlour kuwa wani d'an matakalane mai hawa d'aya wanda  kofar kitchen ne a wurin sai sito dake manne da kitchen d'in.

Sai kuma wata k'ofar da takeda girma kana bud'ewa zaka ratsa cikin wani d'an parlour mai d'auke da bedroom.

Sai shimfidaddan steps d'in dake tsakar parlour wanda zaka hau ya sadaka da asalin saman.

Wanda kana hawa saman zaka ratsa wani tamfatsetsen parlour mai girma wanda yakeda two bedroom sai dining area  da kitchen sai kofa d'aya rak wanda zata sadaka da wata 'yar baranda mai kyau wanda aka zagayeta da k'arafun silver masu shek'i wanda in kana daga cikin barandar zaka ke hango asalin tsakiyar wannan part mai plat guda biyun nan.

Kana daga windows d'in parlour ma zaka kalli duk abinda ke guda a tsakiyar wad'annan part d'in da asalin harabar gidan. 

Sai kuma can bayan gidan saman wanda yake d'auke da wani babban garden mai tsananin sanyi wanda yake zagaye da fulawowi da itatuwa kamarsu Ayaba, goiba, dabino, mangoro, tsada, d'inya, gwanda, sai bishiyar giginya,

sai babban sweeming  pull wanda yake zagaye da kujerun silver sosai wurin yakeda d'an duhu dan duhun itatuwan daga d'an gefe kad'an kuwa rufumfa ce guda d'aya rak sai dai tanada matuk'ar girma, 

daga can gefe kuwa akwai fili mai girma wanda za'a iya tada wani part d'in.


Fentin gidan  white and purple ne mai tsananin kyau sai shek'i yakeyi kasancewar fentin mai maine.


Gida kam dai masha Allah mak'i gani ya kauda idanu maso gani yayi son barka. 


Sosai tsarin gidan yayi matuk'ar burgosu, 

Addu'a sosai sukayi tare sanya al'barka,

sunata yiwa Saifuddeen tsiya wai saura a shiga babin batun aure tunda ya tara.


Nan Bappa Ali yasa musu ranar k'auran saura wata d'aya nan gaba.


Yayinda Hayatuddeen kuwa yaketa mita wai anja lokacin yayi yawa, 

waishi wallahi ya gaji dan haka zai k'aura in yaso su biyoshi daga baya shi dai ya gaji da zaman Dukku.




Yau saura sati uku su k'auro sosai hidimomi sukayiwa Saifuddeen caa a kanshi, 

danma Ahmad dasu Salisu suna samun lokacin tayashi hidima,


 Yau tunda da Saifuddeen ya gama abinda yakeyi a kasuwa, 

ya wuce shagonsu yana isa ya samu bakin shagunan na cike mak'il da mutane maza da mata yara da manya masu sari da masu sayan kad'an-kad'an,

ratsawa gefe yayi ya shiga cikin shagon inda Ahmad ke zaune yanata had'a kan kudad'en cinikin da sukeyi, 

Warisu, Mudassir, kuwa sunata aunarwa masu sayan kad'an-kad'an Bello kuwa yana fama da masu sari 

a d'aya sashin kuwa masu barone  cike sai yara masu zuwa sarin pure water a kattin girijin da Saifuddeen ya ajiye a bakin shagon,

wanda yawanci Ahmad ke kula da cinikin,

matsowa yayi kusa da Ahmad suka ci gaba da harhad'a kan kudad'en, 

tare da lissafi da ware na gegen magi da ban da ware na gefen kayan masarufi da ban dan su jarin Saifuddeen ne halal d'inshi sai kuma gefen kayan abinci.

Bayan sun gamane Ahmad ya d'ago kai ya kalleshi cikin fidda numfashi yace.

"Har ka gama ne yau?."

kai ya gyad'a mishi tare da mishi alamu da body language yace.

"Na gama so nake kazo muje wurin kafin tannan ya gama aikin kayan."

kai Ahmad ya jinjina tare da mik'ewa yaje gaban firijin nan ya rink'a d'aukan katon d'in juice da ledodin pure water yana sawa cikin firijin saida ya ciccikasu baki d'aya sannan ya  dawo cikin shagon mik'a yayi tare da cewa. 

"Wach Allah na."

sai ya kuma juyo ya d'an harari Saifuddeen tare da had'e fuska sannan yace.

"Kai yaseen na gaji bazan iya wahalar nanba."

sai ya kuma kalli Saifuddeen dake hararanshi da alamun kai dai ragone.

bud'e marfin robar faron daya d'auko yayi saida ya sha rabinshi sannan yace.

"Hege kai kuma waya kaika tsoron wahala, 

gsky aiyukan shagunan nan suna mana yawa, 

dole za'a nemi sabbin ma'aikata koda mutun biyu ne,

sam bamu da hutu wuni muke sunkuyawa da tashi, 

shiyasa in dare yayi sai mu zama kamar tsoffi masu 70 years,

wannan a haka mutun yace zayi aure ai matar taga ta kanta."

mik'ewa Saifuddeen yayi tare kallon Ahmad da yaci gaba da cewa.

"Bari in d'auki jakar kud'in nan inzo mu tafi, 

amman sai mun biya ta GT bank na ajiye kud'in sai mu wuce ko?."

kai ya gyad'a mishi alamar to.


A tare suka foto bakin shagon inda kasiyar Ahmad take, 

shi ya fara hawa kafin Saifuddeen ya hau kana yaja suka tafi,

kai tsaye GT Bank suka nufa,

tare suka shiga bayan sun gama hidimarsu suka fito nan suka kama layin bello sabon kud'i inda jerin kafintocin jihar gombe suke cike birjic,

suna isa wurin kafintan suka samu an gama komai an kimtsasu an lik'esu cikin leda,

suna isa Babban kafintan ya kira biyu daga cikin direbobin motocinsu na kwasar kaya ih zuwa gidanjen costumes d'insu,

sukazo suka kwashi kayan aka loda a motocin, 

sannan matasa uku suka shiga wanda su zasuyi jeren,

suna gaba motocin na binsu a baya,

suna isa Ahmad ya sauk'a ya karb'i key d'in gidan a hannun Saifuddeen sannan ya bud'e musu gate d'in yazo ya shiga suma sukabi bayansu.


Daga nan suka fara shisshigar da kayan suna shigarwa cikin can asalin cikin gidan. 

Ahmad ke musu bayanin yadda  zasu sassaka kayan dan su basa gane body language d'in da Saifuddeen zai musu,


Bedroom guda biyu dake cikin parlour dake k'asan suka fara kimtsawa suka kafa gadajen tare da durowowin da mirrors d'in, 

sannan suka sassaka katifun, 

sai kuma suka dawo cikin parlour suka kimtsa lumtsuma-lumtsuman kujerun masu kama da kiran royal sai dinning table mai azabar kyau da suka shiryashi a dinning area,

sai da suka gama kimtsa parlour sannan suka shiga d'aya kofar da zata sadasu da d'an karamin parlour da bedroom nan gado durowar suka kafa, 

parlour kuma suka barshi ba komai, 

sai kuma suka haura sama can suna shiga parlour bedroom d'in dake hannun dama suka shiga nan suka kafa gado da durowa da duk sauran kayan gado sannan  

suka dawo falon nan suka samu Ahmad ya firfito musu da sauran kayayyakin da suka saya suka tara a d'aya bedroom d'in kamarsu cainis carpet da labulaye sai zannuwan gadaye da TV,  Firij da dai sauran kayan wuta.

daga parlour saman suka fara saka labulayen masu azabar kyau da shek'i kalarsu  pink and white, hakama kujerun da carpet d'in.

bedroom d'in da suka kafa gado suka shiga nanma suka sa labulayen masu kalar ja da fari,

zanin gado ma red and white sai carpet shima red and white,

suka gama kimtsa komai sannan suka dawo parlour suka ajiye d'an madaidaicin firij a cikin dinning area wanda shi bai samu damar samun dinnin table ba,

sai katon TV da suka manna a parlour,

daga nan suka sauk'o k'asa suka gama shirya koma inda kalan labule da carpet suke  white and people.

sai tv da firij da suka ajiye komai a mazauninshi, 

sai kuma suka shiga d'an k'aramin parlour nan suka malale tattausan carpet a tsakiyar parlour sannan suka lik'a tv a jikin bongo, 

daga nan suka ajiye d'an k'ank'anin firij a parlour.


Daga nan kuma suka shiga cikin kitchen d'in suka shirya durowowin kitchen d'in na sama da k'asa sannan suka ciccibo kwalin gas suka zo suka sashi a mazauninshi sannan suka had'a ma sank'alin sink da bakin pompo sosai kitchen din yayi kyau.



Sosai gidan yayi kyau komai yayi ras,

daga nan Saifuddeen ya biyasu kud'in aikinsu kana ya sallamesu,

sannan suka dawo parlour suka zauna shida Ahmad bisa kujerun suka zube suna shak'ar k'amshin sabon fenti da k'amshin sabbin kayan d'aki inda ya had'e ya zama daddad'an k'amshi, Ahmad ne yayi mik'a tare da cewa.

"Masha Allah gida yayi kyau sosai, 

sai dai nasan Hayatuddeen zaiyi mitar an sa mishi k'aramin tv a d'an k'aramin parlour shi."

murmushi Saifudddeen yayi tare yin alamun.

"Ai zaiyi fushi kam dan zaice ban sa mishi kujeru a parlournba."

dariya Ahmad yayi tare da zaro wayarshi daketa ringing  da sauri ya d'aga ganin Salisu ke kiranshi.

"Hello Salisu ya kake."


"Lfy lau Ahmad ya kasuwa?."


"Alhamdulillahi ya naka kasuwan?."


"Lfy lau wlh, ina kake ne nazo shagonku ban sameka ba."


gyara konciyarshi yayi tare da cewa.

"Muna gidan Saifuddeen d'azu nai ta kiranka baka picking call."

Numfashi Salisu ya fesar tare da cewa.

"To gani nan zuwa ku jirani."


"To sai ka zo." cewar Ahmad har zai katse kiran sai kuma yace. 

"Kana inane yanzun?."


"Ina nan cikin shagonku."


"Yauwa to d'an taho mana da abin sanyi,

sannan ka d'an biya ta tashan dukku ka biya Abba bekery ka sama mana abinda zamuci dan wlh ni yunwa nakeji."


Dariya Salisu yayi sannan yace.

"To ba matsala a cici,

 ci ba k'iba asaran gaya kawai."

yana fad'in haka ya katse kiran, 

sannan ya juya ya kalli Mudassir dake dariya dan yana jiyo mgnar Ahmad kad'an-kad'an ,

sai ya kuma nuna Warisu da idanu yace. 

"Nida Ahmad ci kamar gara,  amman bama k'iba, ga oga Warisu kuwa yanata yiwa kanshi k'aidar ci amman a banza sai zuba k'iba yakeyi."

hararanshi Warisu yayi tare da cewa. 

"Kada ka damu yaro nima zan sace."

dariya sukayi baki d'aya, 

sannan Salisu yace. 

"Yauwa ina son shinkafa buhu biyu d'anya da gumi sai buhun semo, da katon d'in spaghetti and macaroni indomi. d'ad'd'aya

Sai kuma mai manja magi sugar fulawa.

Bello ne dake tsaye ta woje yace. 

"To an gama Warisu had'a mishi lissafin kud'in da zai bada."

to Warisu yace kana ya jawo Calculator dake gabanshi ya fara had'a lissafin, 

yayinda tuni shi kuwa Bello ya had'a kayan duka,

sannan Warisu ya fad'i lissafin nan take ya biya kud'in sannan ya kira 'yan baro guda biyu suka kwashi kayan suka fita Salisu na biye dasu a baya.


Suna zuwa inda yayi parking motarshi ya bud'e but d'in motar kana ya loda kayan daga nan ya sallami yaran suka tafi shi kuma ya shiga mota yaja ya tafi direct Abba Bakery ya nufa ya sai musu abinda zasuci kana ya shiga cikin federal law cos,


Yana isa ya kira Ahmad yazo ya bud'e mishi gate sanan ya shiga da motar, 

daga nan ya bud'e but d'in motar suka fara jidan kayayyakin sukayi ta shigarwa cikin sito d'in parlour da aka gyara.


Sosai Ahmad yaji dad'in kawaicin da Salisu yayiwa Saifuddeen,

shima kanshi Saifuddeen mutuncin Salisu ya k'aru a ida nunshi duk da bashi da matsalar kayan abinci amman yaji dad'in kyautar.


Nan sukaci suka sha sai bayan sallan la'asar suka fito,

suna fitowa gidan Alhaji Kabiru suka shiga nan sukayi sa'an samunshi a harabar gidanshi yana shirin fita, 

bayan sun gaisane yacewa Saifuddeen.

"Ya kamata ka samu mai gad'in da zai zauna a gidan dan barin gidan haka ba mai gadi baiyiba."

kai Saifuddeen ya gyad'a mishi alamun za'ayi hakan.

shi kuwa Alhaji Kabiru buzayen dake zaune can harabar gidanshi ya nuna musu wani d'an ma daidaicin dottijo dake tsakaninsu kana yace.

"Ga wannan dottijon yanada kirki dama shine a gidan kauran masu gidan ne yasa nace ya dawo nan kafin a samu mai d'aukanshi aiki."

cikin gamsuwa Ahmad yace.

"To shike nan ba matsala kawai ya koma can yaci gaba da aikinshi."

cikin jin dad'in nitsuwar yaran Alhaji Kabiru yayi musu bayanin kud'in da ake biyanshi sun amince da za'a biyashi hakan, 

nan take ya kwashi kayanshi ya koma gidan akan za'a rink'a bashi abinci daga gidan Alhaji Kabiru kafin su Ummi su k'auro.



Shirye-shiryen k'aurafa ya kankama Bappa Ali ya kwashi d'alibanshi sukaje sukayi kwana uku a gidan suna sauk'an karatun Qur'an da sadaka maganin masifa, 

bayan sun gama suka dawo gida, 

sannan Adda Rahma kuwa ta fara shirya musu waliman k'aura.

Raihana ma da Saminunta sun baro Kd zuwa gombe dan ayi k'auran a idansu,


 Imran kuwa shida kanshi yaje gidajen abokanshi ya gaggayacesu suzo tarban abokinsu ba dukke,

Saifuddeen kuwa ya sanarwa abokanshi Jabeer, Hisham, Ibrahim da dai sauransu.


A dukku kuwa Aunty Nina sai kuka takeyi dan tasan zatayi kad'aici dan rabuwa da Ummi da yaranta zai shiga jikinta, 

hakama goggo Dada maman Ahmad sai kukan k'auran sukeyi. 


Ranar k'auransu ya kama jumma'a ,

'yan uwa da abokan arzik'i da mak'ota duk sunyiwa Ummi da ahlinta rakiya suna masu kewar rabuwa da juna.


A nan Gombe kuwa sun samu taron iyayen abokan Saifuddeen da Hayatuddeen sai Adda Rahma da mak'otanta da 'yan sirarun k'awayen da ta saba dasu.  iyayen Jabeer, Hisham, Ibrahim, Sulaiman, Kakar Zakariyya,  da matan Alhaji Kabiru duk sun zo,

anyi walima lfy, Ummi ta shiga ran matan dan tanada sakin fuska da mutunta mutane. 


Bayan kwana ashirin da biyu da k'auransu duk bak'i sun tafi sai Ummi da yaranta da sabon gida da sabuwar Rayuwa.


 Sauri-sauri Hayatuddeen ya fito daga cikin d'an k'aramin falonshi gaban Ummi ya zauna wacce Raliyya ke yanke mata farce.

fuska ya d'an tsuke tare da cewa.

"Ni wlh a matse nake a gidannan an wani lik'ani a wannan kurkukun side d'in kamar yaro,

kuma ko share min d'akinma Raliya batayi sai a barmin komai a hargitse."

tsaki Raliya taja tare da cewa.

"Ai ni ba baiwarka bace da zaka hargitsa komai kace ni in gyara maka."

harara ya watsa mata tare da cewa. 

"To ni macece ni da zanyi shara?."

ita dai Ummi idanu ta zuba musu inda sabo ai ta saba da tsamar Raliya da Hayatuddeen da d'an korensu Faruq, 

murmushi tayi jin Raliya na cewa.

"Eh baka iya kimtsa kanka da kayanka ba amman ka iya sabule wondo ka tsallake ka barshi a tsakiyar falo dan gaka isshashe kai kanada Raliya baiwa mai yi maka tattara."

Faruq ne ya mik'e tare da cewa.

"To ai yana jin bacci ne lokacin shiyasa."

tura baki tayi kana ta sharesu,

shi kuwa Hayatuddeen meda hankalin shi yayi kan Ummi cikin lallab'ata yace.

"Ummi kin yiwa Hamma Saifuddeen batun sauyin makarantar da zai mana ne?."

kai ta gyad'a mishi kana tace.

"Eh na gaya mishi yace zai bincika makarantar data dace daku."

ido ya kashewa Faruq sannan ya k'ara motso Ummi cikin sanyin lafazi yace.

"Ba na gaya miki cewar akwai wata sabuwar makaranta MATRIX nan bayanmu kadan a kan hanya gab da  kuros mai k'ollo nan hanyar F, C, E , makarantar tanada kyau kice masa ya samu nan kinga kusa da gidane koda k'afama zamuje ko Faruq."

da sauri Faruq yace. 

"Eh mana kinga kun huta bamu kud'in machine."

da sauri Raliya ta mik'e kalon tara saura kwata tayi musu tare da cewa.

"Kan bala'i wannan makarantar da sai yaran manya makarantar da sai dai d'an talaka ya gani da ido shine zakuce shi kukeson Hamma Saifuddeen ya saku ko tausayin shima ku bakwaji kaji hegun yara da girman kai da son k'arya da papa, tab lallai aiki ya sameku yaseen Ummi karki yarda zasu talauta miki d'a dan sunga yana musu duk abinda suke so."

da sauri ta kauce ganin Hayatuddeen ya kai mata duka, 

d'akinta dake fuskantar d'akin Ummi ta shige da gudu tana musu dariyar mugunta.

shiko Hayatuddeen wayarshi ya zaro ya amsa kiran Imran wanda yazo dan d'aukan Hayatuddeen suje gidansu Zakariyya dan gaida kakarshi ta fad'i ta gurd'e a hannu.

bayan Imran ya shigo sun gaisa da Ummi, 

sai suka sallameta suka fito.


A bakin gate suka d'an tsaya wurin Baba buzu,

cikin yanayin sun fara sabawa dashi sukace.

"Baba bari muje gidansu Zakariyya."

murmushi yayi tare da cewa.

"Auho kuce wanda yace zai bani kakarshi in aura in inaso ko?."

Cikin shek'iyamci Imran yace.

"Yauwa to ita zumuje dubowa, me zaka kawo mu kai mata?."

goro ya fiddo cikin aljihun rigarshi irin gara ga nakan nan na buzaye, 

ya mik'awa Hayatuddeen su tare da cewa.

"To gashi ku kai mata wannan."

aifa dariya suka sa sannan suka amsa suka tafi.

gidansu Isma'il suka biya sannan suka nufi hanyar da zai sadasu da ceceniya kasan cewar ba nisa sosai tsaka ninsu.


Suna isa,

 Zakariyya na jin muryarsu ya fito da sauri yana isa inda suke ya basu hannu suka tafa tare yin murmushi suna cikin haka sukaji wata zazzak'ar murya mai dad'in sauraro tana cewa...!



                             By

              *GARKUWAR FULANI*

8/18/20, 7:52 PM - Ummi Tandama: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


       *NAKASA BA KASAWA BACE*


                              *PAGE 12*

          

                                  NA

               *AYSHA  ALIYU GARKUWA*        



🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇



      

Cikin d'an d'aga murya take cewa. 

"Zakariyya! Zakariyya!!  Zakariyya!!! wlh bana son raini kazo ka bani wayata."

cikin d'aga murya Zakariyya yace. 

"Ank'i a bada d'in uwar masifa k'arfinki ya kwata miki aikin kawai ke ba dama mutun ya tab'a woyarki sai kiyi ta rashin mutunci."

dariya Imran yayi tare da cewa.

"Yaseen yau sai mun zuk'e cajinki."

dai-dai lokacin ta fito daga ganinta yayar Zakariyya ne dan suna d'an kama kekyawace ajin forko tanada cikar sura, 

idanu ta zubawa Hayatuddeen da yake kallonta tare da cewa.

"Wannan itama irin Raliya ce ko sai hegen masifa."

Zakariyya ne yayi dariya tare da cewa. 

"Haka suke dan sun samu sun fimu da sharu uku zuwa hud'u kacal sai sukeji kamar sune suka haifemu."

da sauri ta iso ta wabce wayarta dake hannun Imran kana tace.

"Hegu kawai masu jajayen fuskoki."

cikin tsiya Zakariyya yace.

"Shima samune kina bak'in cikin jar fatanmu."

tsaki taja tare da cewa.

"Hauka kawai me abin jin haushi duk kunyi kalar zabiya kuma dai baku fini fari ba."

dariya Imran yayi sannan yace.

"Ke dai dama kina bak'in ciki ace Zakariyya ya fiki kyau."

juyawa tayi tana cewa. 

"A ina ka tab'a ganin namiji yafi macce kyau."

cikin sauri Hayatuddeen yasha gabanta tare da cewa.

"Yaseen na miji nafin mace kyau kin ganki duk da kyanki Hamma Saifuddeen d'ina ya fiki kyau, in kin ganshi keda kanki zaki shaida hakan."

bata bi ta kansuba ta shiga cikin parlour inda kakarsu ke kwance tanata raki, 

bayanta sukabi da saurinsu suna shiga suka gaida Kaka sannan suka zauna gefen ta. Cikin kula tace. 

"Imarana ya gida?."

ba tare da ya juyo ya kalletaba yace. 

"Lfy lau Alhamdulillahi Mama tace in gaidaki da jiki."

"Ina amsawa." ta bashi amsa tare da juyawa tana kallon Hayatuddeen da yake nunawa Zakariyya abu a wayarshi tace.

"Kai Hayatu hankalin ka duk yana kan waya,  Umminka tana lfy ko."

still idanunshi na kan wayar yace. 

"Nace miki ki dena cemin Hayatu, ki cika min sunana Hayatuddeen ko kuma kice min Deen in kuwa Hayatun kike son fad'i to kice Hayat."

dariya budurwannan tayi ganin yadda Tsohuwar taketa buga mishi harara,

Isma'il ma da babu bakin mgna sai murmushi yakeyi

Imran ma dariyar yayi dan da yaji dariyar Budurwar ne yasashi kallon inda take kallo,

d'ago kansu sukayi suma suka kallesu jin dariyar tayi yawa,

Zakariyya ne ya kad'a baki yace.

"Haba dai Inna ai wannan kallo sai ya razanamu, dan Allah ki rage idanunki."

sai ya kuma kalli yayar tashi cikin tsigar tsokana yace.

"Ke ashe ga wacca ta b'ataki da k'uru-k'urun idanu bamu ankara ba."

jin haka ai yasa ta haiyayak'o kanshi wai ya zageta mai k'uru-k'urun idanu,

ita kuwa Inna baki ta tab'e tare da cewa.

"Wannan dokoki na kiran sunanka ai sai 'yan boko ni ba abinda ya shamin kai Hayatu zan kiraka."

dariya yayi sosai jin Imran na ce mata.

"To inna ba sai mu shigar dake makarantarba mu samu ki haddace sunan ba Dukke."

shi kuwa Zakariyya sanin bayanshi Inna takebi yasa ya mik'e yana tarfawa yayar tashi tsiya,

ganin Inna tak'i ta kulashi yasa ta sunkuyo ta zari hand bag nata tare da car key d'inta dake gefen jakar cikin  jin haushin tace.

"Yaseen bazan zauna a gidan nan ba, 

zan koma gida haka kawai a turoni dan inzo in taimaka miki tunda kin gurd'e kuma kina ganin jikanki ya rainani da yake kin fi sonshi bazaki mishi fad'aba."

cikin sababi irin na tsofaffi masu zafi tace.

"Ki tafi mana kada Allah yasa ki zauna dan ubanki! ai bani na kirakiba ni dama Zahira nace a turo min dan itace mai mutunci,

amman tunda kikace bazaki zaunan ba ni kuwa yanzu zan kira Babanku kina komawa zaki dawo kiyi asaran man motarki kawai."

bata bi ta kan magar tsohuwar ba ta fice abinta,

su kuwa duk bayanta sukabi,

suna fitawa tana figin motarta ta tana shirin barin harabar d'an k'aramin gidan,

Hayatuddeen ne yayi sauri d'aga murya tare da cewa. 

"Kadafa ki manta kinada tambarin *L* yaseen ki kula kada kije kiyi ta tambola a titi."

k'ura ta bud'esu dashi kana tayi ficewarta daga gidan.


Su kuwa nan sukayi ta sabgoginsu sai gab da magrib suka fito suka nufi gida duk da akwai 'yar tazara tsakaninsu amman haka suke tattakawa da k'afafunsu har zuwa gida a cewarsu Hayatuddeen yaga garin da kyau,

suna isa gab da gidansu Isma'il ne Imran ya tare machine ya tafi,

shi kuwa  Hayatuddeen jan hannun isma'il yayi a kan dole sai suje gidansu a dole  ya bishi.


Sannu-sannu su Ummi sun saba da bak'otansu da iyayen abokansu Saifuddeen da Hayatuddeen.


Yau jumma'a shiyasa Saifuddeen bai fita da wuriba, 

sai h'ar k'arfe tara ya tashi daga baccin daya koma bayan sallan asuba,

a hankali ya mik'e  mik'a yayi tare da yin salati a zuciyarshi,

bathroom ya nufa, 

wonka yayi mai rai da lfy kana yayi al'wala sannan ya fito d'aure da towel a k'ugunshi sai d'an k'aramin dake hannunshi bisa bakin gado ya zauna ya fara tsane ruwan jikinshi, 

mik'ewa ya kumayi bisa kujerar dressing mirror ya zauna mai ya fara shafawa sannan ya gyara suman kanshi,

mik'ewa yayi zuwa gaban durowar bud'ewa yayi ya zaro wani tattausan yadi mai taushi yadin bak'i ne mai shek'i yanada zanen gidan dara-dara,

sai kuma ya zaro boxer and vest farare k'al-k'al, 

a bakin gado ya ajiyesu, 

sannan ya kuma dawowa gefen durowar inda takalmanshi ke jere bisa wani kekyawan abin aje takalma wasu fararen takalma ya zaro, 

sai ya kuma   bud'e d'aya sashin na durowar inda hulunanshi ke jere,

hula zanna bukar ya zaro fara mai ratsin bak'i-bak'i,

kimtsawa yayi cikin kayan da ya fidda d'in, 

bayan ya gama sawane ya dawo gaban mirror yana dai'daita zaman hularshi a kanshi, 

murmushi yayi wanda har saida dimples nashi suka lotsa shida kanshi yasan yana kama da Abbansu, 

ya kuma san Abbansu kekyawane na nunawa sa'a  sosai bak'in kayan ya k'ara fito da farin fatarshi ras, 

in ka ganshi tamkar balarabe  suman kanshi a konce lib-lib a k'eyanshi da gefen sajenshi,

turare ya d'auka ya feshe jikinshi dashi lungu da sak'o,

ido ya lumshe a hankali tare da shak'an numfashi dan jin sassanyan k'amshin turaren dake ratsa mishi jiki da zuciya.

Towel d'in daya ciren ne ya d'auka ya shiga bathroom ya 

shanyashi sannan ya fito, 

ya nufi parlour.


Ummi kuwa da yaranta duk suna parlour suna tab'a hira,

Ummi na bisa 3 str Hayatuddeen kuma na konce kusa da ita yayi  !!! kan tv,

da sauri Ummi ta d'ago kanta  ido ta zubawa steps d'in sauk'owa k'asan dan jin takun d'an nata, 

murmushi tayi tare lumshe ido kana tana godewa Allah daya azurtata da wannan kekyawa halitta a matsayin d'anta cikin sanyin sauti  tace.

"Masha Allah, babana yayi kyau matuk'a gaya."

murmushi yayi shima dan idanunshi na kanta a hankali yaci gaba da tako steps d'in cikin takunshi mai d'arka hankali har ya sauk'o, 

gabab da ita yazo ya zauna cikin kurma-kurma ya gaidata.

"Lfy lau Babana ka tashi lfy ko?."

hannunta ya kamo ya manna a habarshi alamun lfy lau Alhamdulillahi.

cikin girmamawa Raliya ta kalleshi tare da cewa. 

"Ina kwana Hamma Saifuddeen."

kai ya jinjina mata ta lamun lfy lau, 

sai ya kuma kallin Hayatuddeen  dake kallonshi yana mirmushi cikin k'aunar d'an uwan nashi,  murya a sake yace.

"Barka da jumma'a Hamma." bai jira amsarshi ba yaci gaba da cewa.

"Kayi kyau sosai Hamma na."

murmushi yayi kana ya shafa fuskar k'anin nashi.

Ummi kuwa mik'ewa tayi ta nufi dinning table tare da yafitoshi tai mishi alamar yazo yayi breakfast."

mik'ewa yayi yabi bayanta, 


Zama yayi a kujerar dake dab da ita yana kallon yadda taken had'a mishi tea,

tana gamawa ta mik'a mishi sannan ta zubo mishi soyayyan dankali da kwai  sai kuma ta jawo wani filet d'in da alamun wani abun zata kuma zuba mishi, 

da sauri ya jujjuya mata kai, 

tare da mata alamun sauri yakeyi tea d'in kawai zaisha da d'ankalin,

sanin halinshi da halittarshi ta rashin cin abinci da yawane yasata meda filet d'in sannan ta zauna gefenshi yana d'anci suna kuma d'an tab'a hira sauri-sauri ya gama ya sallameta ya fita ya tafi.


Ita kuwa Ummi ta haura sama kai tsaye bedroom nashi ta nufa ita da kanta ta gyara mishi d'akinshi da bathroom da parlour nashi duka ta sassake mishi labuye sannan ta feffesa turaren d'aki mai suna touch me sannan ta rege mishi gudun AC kana ta fito.


Tana sauk'owa taci karo da Hayatuddeen a tsakiyar parlour yanata kiciniyar kwance bel d'in k'ugunshi,

ido ta zura mishi ba tare da ta k'arisa sauk'owanba hakama Raliya ido ta zura mishi,

shi kuwa baima san sunayi ba yana zare bel d'in yayi k'asa da dogon wondon Blue Jeans dake jikinshi ya rage dagashi sai d'an gajeren wondo dake jikinshi, sawunshi ya zare kana ya tsallake wondon inda ya sab'uleshi ya nufi hanyar d'akinshi tare da cilla bel d'in a tsakiyar parlour, 

sai kuma ya fara kiciniyar cire rigarshi tare da cewa. 

"Nima bari inje inyi wonka dan yau a masallacin fad'ar jiha zamuyi salla dasu Imran dasu Sulaiman Zakariyya shi yace yama je tun d'azu."

tsayawa yayi tare da juyawa da sauri jin Raliya na mishi mgna cikin tsawa take ce mishi.

"Wai kai kam Hayatuddeen wanne irin yarone mara kan gado, 

kalli yadda ka watsa mana parlour dan tsabar sakarci da sakalci inda ka cire wondonka nan kake bar mana shi wato kai gaka auta mai buhun sakalci uwar wa zata tattara maka kwamutsan naka to da ka barshi?."

wani dogon tsaki yaja tare da cewa.

"Uwata mana ce miki akayi bani da gatane banza kawai uwar sa ido."

yana fad'in haka yayi shigewarsa d'an k'aramin side inshi, 

ita kuwa Raliya taita zumbura baki dan Ummi ta sata tattaramishi kayanshi daya watsar.



Saifuddeen kuwa yana fita yaci karo da Salisu wanda shine ya d'aukeshi suka nufi hanyarsu da zata sadasu da titin tutun wada, 

mik'ewa sukayi direct har kusa da mashigar G.S.U cikin nitsuwa Salisu ke draving suna gab da shiga gate d'in. 

Jonapwd k'ungiyar nakasassu ta jihar kenan Salisu ya juyo cikin nitsuwa da kula ya kalli Saifuddeen tare da cewa.

"Motocin nan da mukayi mgnarsu last week sun iso jiya,

shiyasa nazo da nufin muje ka gansu ka zab'i kalan da kakeso a ciki,

dan gsky zamanka ba mota baiyiba, 

tunda ko bazaka yi tuk'iba zamu iya samar maka amintaccen direba da zai rink'a kaika duk inda kakeso da kai da Ummi kafin Hayatuddeen ya k'ara girma."

murmushi Saifuddeen yayi tare da gyara zamanshi duk da yaga Salisun yayi parking kai ya jinjina tare da rubuta mishi.

"Bank'i shawararku bafa sai dai kuda kanku kunsan cewa yanzu bani da kud'in a k'asa dan na yashe duk asusuna nayi hidimar k'aurannan  to kuma bani son abu da bashi."

a take fuskar Salisu ta sauya yanayi,

 cikin sanyin sauti yace.

"Bashi kuma! Saifuddeen yanzu ashe dama kayana ba naka bane, 

ashe dan ka d'auki mota d'aya rak cikin jerin motoci kusan takwas wanda kaine silar samar min jarinsu sai ya zama wani abu?."

Kai ya rink'a jujjuyawa cikin nuna alamun ba haka bane,

ganin haka yasa Salisu cewa. 

"To kada ka sake kiramin kalmar bashi a tsakaninmu kuma ko bakaje ka zab'i kalar da kake soba ni zan zab'a maka da kaina gobe zan kawo maka ita har gida,

kuma in ba matsala a cikin yaran da suke wonke mana motocin akwai wani yaro Sule yanada nitsuwa ya kuma iya tuk'i na mutunci sai ya dawo nan ya rink'a kaiku duk inda kuke buk'ata zai kuma iya kula da shuke-shuken gidan in yaso duk wata ka rink'a biyanshi abinda nake biyanshi, 

to dama kullum ina bashi kud'in abinci, 

to kaga kai ba sai kayi ta bashi kud'in abinciba sai Ummi ta rink'a zuba mishi shida baba maigadi ko?." ya k'arishe mgnar cikin yanayin tambaya.

kai ya jinjina mishi tare da rubuta mishi.

"To ba matsala kayi yadda kaga ya dace."

cikin jin dad'in amincewar Saifuddeen d'in yace.

"To ba matsala."


Daga nan suka fito suka shiga cikin harabar wurin,

kai tsaye office d'in Ishaq suka nufa, 

jin motsin bud'e k'ofarne yasa Ishaq juyawa da sauri sai ya kuma mik'e da sauri jin muryar Salisu, 

numfashi ya shak'a tare da cewa. 

"Lalle marhabin da manyan bak'i."

jin Saifuddeen ya rik'e hannunshi ya sashi juyawa gareshi tare da cewa. 

"Kai amman naji haushi wlh kaga da kazo awa uku da suka wuce da ka had'u da Zaleeha sabuwar ma'akaciyar gidan radio vision FM gombe wacce take gabatar da shirin *Babu nakasasshe sai rago* yau dani mukayi hira na d'an bata tarihin rayuwata ka ko san dole zaka shiga ciki."

shiru yayi jin Saifuddeen ya rufe mishi baki da hannu tare da zaro wayarshi da hannunshi d'aya kana ya rubuta mishi text.

"Kai dan Allah ka huta mana wai bakinka bai gajiya da surutune?  to ni ka bani ruwan sha tukun."

da sauri ya zaro wayarshi jin shigowar sak'o yasan Saifuddeen ne ya mishi mgn, 

dariya yayi sanda ya karanta kana yace.

"To sarkin k'warafi ga wuri ku zauna."

sai kuma ya d'anyi taku biyu zuwa uku ya isa gaban firiji ruwan sanyi ya d'auko musu sannan yazo kusa dasu, 

Salisu kam har yau bai dena mamakin yadda abota ta kasance tsakanin makaho da kurmaba suna kuma fahimtar juna over, 

amsar ruwan sukayi saida suka d'an sha sannan suka ci gaba da hira amman banda Saifuddeen dan TV yake kallon tashar Farin wata wanda duk had'e suke da vision sosai ya zubawa TV idanu yana karanta rubutun daya bayyana a fuskar tv inda aka rubuta Babu nakasasshe sai rago, sosai Saifuddeen ya maida hankalin shi kan tv ganin sun hasko fuskar wata kekyawar budurwa mai cikar haiba,

lips d'inta ya zubawa idanu dan yana son gane abinda zata fad'a da kyau, 

wani irin sassanyan ajiyan zuciya yayi jin wani abu na yana zirta cikin zuciyarshi har zuwa kwanyar kanshi ganin yadda take motso labb'anta wani sassanyar ajiyan zuciya ya kuma yaja a hankali ya sauk'e jin zuciyarshi na bugawa da sauri-sauri,

wani irin shauk'i ne mai cike da farin ciki ya ziyarci zuciyarshi da gangar jikinshi, 

ina ya kasa kauda idanunshi a kanta,

da kyar ya juyo a fizge ya kalli Ishaq da yake tab'ashi yana ce mishi.

"Yauwa Saifuddeen juya ka kalli tv kaga sun fara haska hirar da tayi damu yau da safen,

kaga wannan itace Zaleeha sabuwar mai gabatar da shirin babu nakasashe sai ragon."

da sauri ya maida kanshi ga tv ganin an d'auke fuskarta an haska fuskar Ishaq ya sashi jan dogon tsaki tare da yin mgnar zuci.

"Yauwa kaga wannan surutaccen ya janye min hankali da d'an banzai surutunshi kafin in juyo sukuma sarakan azarbab'i sun cire fuskarta sun hasko min sufkar wannan gardin,

sai ya kuma ja tsaki tare da buge k'eyar Ishaq da yaketa murmushin jin dad'in shirin.

sai kusan 4to5 minutes kafin suka sake nuno fuskarta inda take cewa. 

"Eh lallai kam na yarda Nakasa ba kasawa bace, tunda gashi kunayin komai kamar sauran masu cikekkiyar halitta."

tsaki ya kuma ja ganin an kuma nuno fuskar Ishaq, 

Salisu kuwa gaba d'aya hankalin shi na kan Saifuddeen d'in dan ya fahimci ya bawa kallon tv mahimmanci a ranshi yace. 

"Kamar yana jin me suke fad'i."

sai ya kuma yi murmushi ganin yadda Saifuddeen keta lumshe idanu da sauk'e sassanyar ajiyan zuciya."

a haka dai har aka gama shirin, 

sannan suka salami Ishaq suka tafi.



Washe gari kuwa kamar yadda Salisu ya fad'in haka yayi ya kawowa Saifuddeen motar da tayi matuk'ar bawa kowa mamki dan motace ta kud'i kimanin million uku da rabi,

ga kuma Sule direba.


Sosai darajar Salisu ta kuma k'aruwa a idanun makusanta Saifuddeen.



Daga ranar Ahmad kuwa ya kasa ya tsare akan ala dole Saifuddeen ya daina tallan leda,

ruwa da omo kuwa maiso yazo shagonsu ya saya, 

haka tasa dole Saifuddeen ya dena yawo a kasuwa yana gararamba,

sai dai ya ajiye yaro d'aya mai wul baro, 

wanda yake cika baronshi da leda ya rink'a kaiwa duk costumes d'in Saifuddeen shago-shago suna bashi kud'in ya kawowa Saifuddeen inda shi kuwa yake sallaman yaron da dubu biyu kullum, 

haka yayiwa Ado dad'i sosai dan cikin awa uku yake gama raba ledan sannan ya dawo yaci gaba da dakon kayan mutane.



A kwana a tashi asarar mai rai. 

Lokacin yaci gaba da tafiya, 

tuni Saifuddeen harkalla taci gaba ya gama biyan bashin daya amsa a shagonsu wanda ya cikata ya sayi gidanshi, 

ya kuma k'ara sayan wata dalleliyar mota mai d'an karen kyau da tsada.

Ya kuma jonawa Hayatuddeen da Faruq makarantar da suke son, 

ya sayawa Hayatuddeen mashin d'in U.D sabuwa dal a leda.

Hayatuddeen kuwa rawan kai sai abinda ya k'aru ya k'ara sabawa da abokanshi su Zakariyya sosai tunda yanzu makarantarsu d'aya kuma duk su hud'u sunada U.D


Sosai Sule direba ya saba da Saifuddeen yana gane body language d'inshi sosai, 

duk inda zaije Sule ke kaishi a sabuwar motarshi,

inda ya b'ar d'ayar kuma wa Ummi.


 Salisu da Warisu duk sunyi aure, 

Ahmad ma an aura mishi Raliya, 

kuma suna nan cikin gidan da yake Ahmad bai k'arisa ginin gidanshi ba shiyasa, 

Saifuddeen yace to yazo ya zauna a cikin d'aya daga cikin part d'in nan dake sashin daman gidan suna zamansu lami lafiya sai tsananin son haihuwa da Ahmad keyi musamman d'iya mace shiyasa yasa Raliya dole ta rink'a kiranshi Abban Farida kamar da wasa sai sunanshi ya koma haka dan sai ya zama su Ummi dasu Rahma duk haka suke kiranshi.


Salisu kuwa tuni ya d'auko kakarshi Iya shatu ta bar Dukku.


Mudassir kuwa bunsurune na Mamajo fir yak'i maida hankali kan batun aure sai tara buhun 'yan mata.


Ishaq kuwa shima har yau baiyi aureba da zaran an mishi mgnar aure sai yace wai baiga matar data mishi bane, 

duk sanda ya fad'i haka Saifuddeen kan ce mishi to wai da wanne idon zaiga matar da zata mishin, 

yakanyi dariya yace da idon zuciya zai ganta.


To uban gayya Saifuddeen kuwa tun randa ya fara ganin fuskar Zaleeha a tv Allah ya jarabci zuciyarshi da wata zazzafar k'aunarta mai kashe zuciya da jiki, 

Allah da ikonshi kuwa bai tab'a ganinta eyes to eyes ba duk da yanzu yana yawan zuwa k'ungiyar tasu wai ko Allah zaisa su had'u amman ina, 

ko dan yawanci Zaleeha k'auyuka takebi tana hira da nakasassunne shiyasa basu fiye had'uwa ba, 

amman fa duk ran jumma'a shabiyu da rabi nayi zai kunna tv tashar Farin wata ya kalli program d'inta da take gabatarwa.


Ya kuma ci gaba da sirranta soyayyarshi dagashi sai zuciyarshi. 

Duk da a wani sashi na zuciyarshi na tuna mishi irin wahala ko k'alubale da nakasassun kan fuskanta yayin neman aure, 

to amman shifa yanada yak'ini a kan kanshi.


Sai dai tun randa ya fara ganinta yanayin rayuwarshi ta canza, 

ya zama fitinenne da zaran ya tunata jikinshi ke harbawa shiyasa dole ya fara azumin Mondays and  Thursdays, dan rage k'arfin abinda ke addabarsa kamar yadda shariyarmu ta musulunci ta koyar mana.


Raihana Ta Haifi d'anta na miji suna kiranshi Affan.


Adda Rahma kuwa sai yanzu Allah ya bata ciki tun tsowon shekarun da tayi aure, 

tuni kuma Ya Adnan ya sayi wani gida a nan layin tudun wada kusa da babban titin da zai ratsa ta gaban babban pharmacy nan na A. A Aliyu pharmacy,

wanda gidan yake gab da gidan da Baba bello ya k'auro.


Ya Adnan kuwa ya k'arbi yar k'anwarshi ya had'a da Adam sun rik'e sun samu yara masu d'ebewa Mamasu kewa tunda dama can mahaifinsu baya raye.


Ganin aikin gidan zaiwa Raliya yawa tayi nata ta dawo tayi na Ummi ne yasa Saifuddeen yasa Adda Rahma ta nema musu mai aiki, 

tana taya Ummi aikace-aikacen gidan.


                 *****

Soisa kasuwancinsu yaci gaba yanzu Ahmad na yawan zuwa legos dasu Onitsha kalaba dan yanzu harda harkan manja sukeyi sosai, yamzu hakama baya garin Gombe tun last week ya tafi Lagos shida Salisu shi kuma ya wuce Cotonou dan dubo wasu sabbin motocin da aka tallata musu, 


Bappa Ali da Mudasssir da Warusu kuwa duk sun tafi umrah,

yanzu Bello da sabbin yaran shagon guda biyu da Ahmad ya nemane suke kula da shagon, duk da aiyukan shagon yana musu yawa, 

shiyasa time to time Saifuddeen na zuwa ya d'an zauna a shagon. 



Su Hayatuddeen kuwa sunata fama da karatun Waec sai gigi da rawan kan sun kusa shiga jami'a.


Raihana ma tazo da ziyara Affan d'inta dan tafi shekara bata zoba sai yanzu.


Yau Alhamis tunda safe Saifuddeen ya shirya ya taho office d'in Ishaq koda yaje lokacin ma Ishaqn baya nan ya shiga cikin G. S. U dan koyar da d'alibanshi, nan ya zauna shi d'aya dan Ishaq ya shaida mishi yau Zaleeha zata zo zatayi hira da masu matsalar spinal cord injury,

shiyasa ya bugo sammako, 

koda ya samu Ishaq baya nan bai damuba wayarshi da  tv suna d'ebe mishi kewa ganin zaman yayi yawane yasa ya mik'e ya ciro laptop d'inshi da yasa a carji tun zuwanshi, bisa kujerar ya dawo ya zauna ya jingina da jikin kujerar sannan ya mik'e k'afafunshi kan glass stoll dake ganshi, a hankali ya bud'e laptop d'in nashi ya fara duba sak'onnin da Ahmad ya turo mishi kasan cewar a rubuce suke komai ta yanar gizo-gizo tunda baya Magna shiyasa yafi gane yin harkar kasuwancinsa a na'ura sosai ya nitsu ya meda hankalin shi wurin tantance gamayyar kasuwancin shi.


Sai kusan azahar Ishaq ya shigo, 

bayan sunyi salla ne sukaci gaba da hira, 

ganin har sunyi la'asar bata zo bane yasa ya mik'e yacewa, 

Ishaq zaije ya duba baba bello da jiki, 

amman zai biyo ta nan wurinshi da haka suka sallami juna,

yana fita  Sule na isowa dan ya mishi text akan yazo ya kaishi gidan Baba Bellon.


Motarsu  na fita da kamar 5 minutes Zaleeha ta iso harabar wurin.


Direct gidan Adda Rahma ya fara shiga suka d'anyi hira har tana mishi batun aure dariya yayi yace mata auren ya kusa ta shirya. 


Daga gidanta gidan Baba Bello ya shiga ya jima suna hira sannan ya amshi takardar maganin da ya Adnan ya rubutawa Baba Bellon ya nufi Kemis d'in A. A Aliyu pharmacyn

yana isa bakin pharmacy d'in yaji an rik'e mishi hannu, 

da sauri ya sunkuyo ganin Zeenat ce d'iyar k'anwar Ya Adnan wacce take gaban Adda Rahma,

hannuta yaja suka shiga cikin kemis d'in,

bayan ya karb'in ledan magunguna ya basu kud'insu, 

sai yayiwa Zeenat alamun da ta kaiwa Baba Bello mgnin ta kira mishi Sule kuma yazo su tafi, 

da sauri ya rusuna gaban Zeenat ganin bata gane body language da ya mataba sai ya rubuta mata a wayarshi ya nuna mata, 

murmushi tayi tare da gyad'a mishi kai alamun ta gane.



Daga can bakin Gate d'in Gombe State University kuwa, 

a dai-dai lokacin mutanen dake bakin gate d'in duk suka fara kaucewa da sauri dan kauda kansu su tsira da ransu da lfyarsu daga sharrin Dalla...!



Wasa farin girki, wannan shine ma somin lbrin mun gama shimfid'an lbrin sai kuma shiga cikin ainin zaren lbrin kada ki/ka sake a baki/ka lbri, kada ayi babu ku!!






                                  By

                    *GARKUWAR FULANI*

8/18/20, 7:52 PM - Ummi Tandama: 26/2 2020...! 8:06 PM


📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


      *NAKASA BA KASAWA BACE*


                             *PAGE 13*


                            NA

         *AYSHA ALIYU GARKUWA*



🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇





 ~28 February 2020/ 9:10 Am~



*Godiya ta musammam ga k'ungiyar nakasasu ta Jihar GOMBE, (JONAPWD)  ina godiya da goyon bayanku*



         


                  _Gombawa d'iban fari ba'a kwana da kuba a tashi daku har cikin al'jannatul firdausi. Duk sammakonka to bagombe a tafe ya kwan,  Gombe hamadan sarki Sulaimanu Gombawa masu kyawawan shatale-shatale da tsabtattun tituna, wannan shafi nakune al'ummar gombe_



A  cikin babban birnin Gombe!. 


Yauwa  Monday da misalin 6:02 pm wannan lokaci yayi dai-dai da lokacin da mafi akasarin bani adam dake woje ke neman hanyar kowa gidanshi kama daga yan kasuwa da ma aikata maza da mata manya da yara da dai sairansu. 

Musamman maza da matan musulmai don kowa na k'ok'arin ganin ya yasamu yin sallanan magrib kan lokacinta kamar dai yadda Saifuddeen yake saurin ya samu Sule ya fito su wuce gida direct bazama su biya wurin Ishap ba dan ganin ana gab da kiran salla shiyasa yake son ya koma gida ya samu yayi bud'a baki yasha ruwa a nitse.


A irin ya wannan lokacin duk mazauna gombe sunsan yadda ababen hawa ke cika titinuna especially wuraren da fitilun bada hannu suke haka yakesa cunkoson ababen hawa ke yauwaita tamkar a birnin Lagos.


Hakan ce ta kasance a wannan babban titi daya ratsa daga gaban babban gate d'in Gombe State University (G.S.U) wanda titin zai ratsa gaban k'ofar babbar fadar masarautar jihar ta. Gombawa kana daga hannun dama kuwa Gate d'in babban ofishin k'ungiyar nakasassu ta jihar Gombe mai taken joint national association of persons with disabilities. (jonapwd) Gombe state chapter. All the best! ne wanda yake fuskantar ratsestsen ginin G.S.U kana daga gefen (jonopwd) d'in akwai wata yar kasuwar Tudu wato kasuwan mata, 

in ka mik'a titin kad'an kuwa akwai fitilar bada hannu, wacce gefen titin wurin akwai shaguna a cikin jerin shagunan kuwa a nan babban shago na saye da sayarwan magunguna wato A.A Aliyu pharmacy d'in yake wurinda Saifuddeen yake a yanzu haka kenan!.


Wasu jerin ayarin tsala-tsalan motocine suka ratso harabar gate d'in G.S.U  moto cin sun  sun kai guda 5 ,

kai da gani kasan yara ne suke jan motocin dan yadda suke tsula gudu tamkar zasu tashi sama, sai gilmawarsu kawai zakaji fiw-fiw suna gibtawa. Da sauri mutane suka rink'a kaucewa sanin rashin mutuncin shugaban ayarin, *Dalla* 

haka yasa akabi ayarin motocin da ido, 

dukansu kyawawan motocine amman,

 akwai guda d'aya daga cikinsu duk ta fisu tsada da sabunta, 

bisa dukkan alamu bugun 2019 ce motar dalliyace mai azabar kyau sai shek'i da k'elli takeyi, 

hatta tayoyinta tamkar ka lashe, koda yake haka baya rasa nasaba ne da yanayin tsabtace titunan birnin Gombe da akeyi ne a ko wanne safiya wannan yasa gombawa sukayiwa sauran jihohi zarra a fagen tsabta dan daga bakin gate din G.S.U. zaka iya cilla ganinka har kan shatale-talen dake k'ofar fadar jiha baza kaga koda tsinkeba a bisa titinunan ba,,

motar ruwan tokace sai gilashenta da suka kasance masu duhu, 

yadda na ciki na iya ganin na woje na woje kuwa bashi da damar ganin na ciki,

motoci biyu dake gaban wannan motar sun wuce kenan sai kuma ita motar da tafisu kyau d'in tana biye dasu, 

yayinda biyu ke bayanta gudu sukeyi tamkar titin dan su kad'ai akayishi . 


Sun zo dai-dai bakin gate d'in K'ungiyar nakasassu ta jihar Gombe, Joint national association of persons with disabilities, (jonapwd)  d'in kenan, sai kuma ga  ratsetsiyar motar Zaleehs ta fito daga cikin harabar (jonopwd) d'in kai tsaye ta danna hancin motarta bisa titin kana ta ratsa tsakiyar ayarin motocin nan, inda ta shiga tsakanin motar nan mai kalar toka da saura biyun nan masu biyoshi a baya,

Zaleeha kekyawar budurwace a cikin motar wacce da ka ganta kasan tana cikin ganiyar k'uruciyarta iska na kad'a  igiyar budurcinta,  tutarta na karkakad'a zuk'atan maza tauraronta na d'auke idon dukkan lafiyayya namiji ganin fuskarta kawai kansa duk lafiyayyan namiji yayita yayyafi,

taka motar takeyi tamkar zatabi takan motarnan dake gabanta, 

dole tasa saura biyun nan suka biyo bayanta, 

kasan cewa gudu sukeyi cikin abinda bai gaza 58 seconds ba suka isa madakatar fitilar bada hannun dake tsakiyar titin, dole tasa suka d'an tattaka birki tare da tsagaita tafiyar tasu, 

a hankali  ta lumshe idonta tare da bud'esu kana ta shak'i sassanyar iskar hunturu dake ratsa jikin mutane, 

kanta ta d'an juya ta kalli gefen gabas inda taga nanma cike yake mak'il da ababen hawa, wani d'an gajeren tsaki  taja tare da d'an juyawa ta kalli gefen yamma inda nanne dai-dai bakin babban kemis d'in A.A Aliyu pharmacy yake, 

ido ta kuma lumshewa kana ta kuma bud'esu a hankali, ido ta tsurawa fuskar Saifuddeen mai tsananin kyau dake  gefen pharmacy d'in,

a hankali ta fesar da sassanyar iska daga bakinta kana ta kuma bud'e kekyawan idanunta a hankali ta zubasu kan surar Saifuddeen da ya gama zama cikekken  matashi d'an 30 years kekyawa ne mai cikar zati da haiba wanda Allah yayi mishi cikar halitta, 

farine k'al tamkar balarabe sumar kanshi tamkar ba indiye, yanada tsawo dai-dai misali, kana yanada halittar gwanji duk da suturar dake jikinshi yana son b'oye asalin halittarsa ta k'ak'k'arfan namiji mai zarra, fuskarshi mai kyau da haiba ce gashin girarshi kad'ai abin ganine fuskar ras babu saje,

a hankali ta kai idonta kan yarinya dake tsaye a gabanshi wacce bazata wuce 7 years ba, da alamun tsantsar so da k'aunan yarinyar a fuskarshi, sunkuyowa yayi d'ai-dai tsawon yarinyar kanta ya shafa tare da mik'a mata ledar hannunshi cikin d'an yin d'igirgire yarinyar ta manna mishi kiss a kumatunshi murmushi yayi tare da juya yarinyar alamun ta tafi.


Matashin dake cikin motar nan kalar toka kuwa, 

shine ya d'an gyara zamanshi tare tsurawa motar dake bayanshi ido ta cikin madubi motarshi yaga sai matsoshi takeyi kuma yaga ba motocin shi bane, 

bai gama nazartar ya akayiba, 

sai kawai yaji gib-gib motarnan ta iso gareshi ta bugi wannan motar tashi da yakeji tamkar k'ok'on ranshi motar da aka binne miliyoyi aka saya mishi ita kuma du-du-du yau ya fara hawanta, 

idanunshi ya rumtse da k'arfi bala'i ji yakeyi ko uban waye ya tab'a mishi motar nan sai ya illatashi.

ita kuwa Zaleeha gaba d'aya ta shagala da kallon Saifuddeen  da babyn nan sam bata ankare da cewar motartafa na tafiyaba kuma sam ta mance cewa a madakata suke, bata dawo haiyacintaba saida taji motarta ta bugi motar dake gabanta, 

kana motarta ta d'anyi baya sannan ta kumayi gaba ta k'ara bugar motar dake gabantan, 

cikin tsananin firgici da razani ta taka birki da k'arfi ji kakeyi, k'uuuuh, ta caki motar ta tsaya. 

Sautin bugun da tayiwa motarnan da kuma sautin taka birki da tayi shiya jawo hankalin mutanen dake wurin gaba d'aya.

 Kai mutane suka rirrik'e tare da cewa.

"Innalillahi".

sabida motar ta kasa sarrafuwa har saida ta kuma bugan jikin motarnan  a karo na uku, 

sannan ta samu ta tsaya, gaba d'aya jikinta rawa yakeyi sabida tsananin tsoro da razani, 

yayinda duk mutanen dake sashin wurin suka zuba musu ido tare da sassauk'e numfashi da furta.

"Alhamdulillahi."

duk sautin nan da bugun motar ta   Saifuddeen  dake bakin kemis d'in nan shi baima juyoba, duk da hatta ma'aikatan cikin kemis d'in saida suka fiffito, 

idonshi ya zubawa bakin d'aya daga cikin maikatan kemis d'in yana ganin yadda lip's inshi ke motsawa hakan yasa ya gane abinda yake fad'i inda shi saurayin yake cewa.

"Innalillahi wannan wacce ce tsautsayi ya rubtawa rayuwarta ta bugi motar Dalla shi kenan zai illata rayuwarta gashi macece ya samu abinda zayita bibiyar rayuwarta."

d'aya dake gefenshi ne yayi saurin cewa.

"Kai subahallahi *Zaleeha  M. B.S. Dukku ce. 

da sauri Saifuddeen

ya juyo ya kalli inda yaga mutanen wurin gaba d'aya suna kallo, 

dai-dai lokacin kuma wanda aka kira da Dalla ya bud'e marfin motarshi gaba d'aya fuskarshi tayi jazir sabida tsananin bala'i fuskarnan tasa tamkar tayi aman jini, 

wani irin taku yakeyi wanda yafi kama dana azzalumai,

gaban motarta ya nufa gadan-gadan. Yayinda ita kuwa Zaleeha ta zazzaro ido tare da kame jikinta tanajin hanjin cikinta na bada sautin k'ululuku sabida tsananin tsoro da firgici.


Shi kuwa yana isa gaban motarta cikin rumtse ido ya wore tafin hannnshi kana ya mari glass d'in gaban motarta a take ya tarwatse yayi cikin motar, 

jin sautin tarwatsewan glass d'in  yasa gaba d'aya mutane sukayi cirko-cirko domin duk cikin fad'in gombe ansan waye Dalla domin yayi k'aurin suna, 

akan izaya da d'agawa da zalumcin Mace koda aurenta ko ba aure in dai ya ganta kuma ta mishi tofa zaisa yaranshi su d'auko mishi ita ya biya buk'atarshi da ita so yana cin karensa babu babbaka tunda yana ganin yanada manya gashi cikekken ɗan kalare mai girman daba. 

Bata dawo daga firgincin daya sataba taji ya bud'e marfin motar tata kana yasa hannunshi ya damk'i hannunta da azaban k'arfi wonda saida ta saki k'ara, 

fincikota yayi woje ya tsaidata gabanshi sannan ya ware tafin hanunshi ya yarfa mata wani gigitaccen mari mai azabar tsiya wanda saida taga taurari na gilmawa kana taji kunnenta yayi dummmm. 

A take sai ga jini ta hancinta, 

shi kuwa Dalla ba tare da yace mata komaiba ya juya ya shiga motarshi, dan ya sawa ranshi wannan jan kunne kawai ya mata yanke hukunci kuma na nan tafe a kanta haka yasa ya juya 

don fitilar bada hannu ta basu damar wucewa.


Shi kuwa Saifuddee ganin abinda Dalla yayi mata tun fasa mata glass da yayi ya nufo kansu da gudu so kasancewar akwai 'yar tazara tsakaninsu gashi sai ya ratsa gaban babura da keke napeps da motocin da suka cika titin yasa kafinma ya isa tuni Dalla ya shiga motarshi,

kana babura da napep da motoci duk sun fara shirin wucewa wonda dole suke ratsawa ta gefen motarta. Itako tunda ya mareta zafin marin da gigita yasa ta fad'in gaban motar tata ta kifu samanshi. 

Cikin gudu da sassarfa ya isa gareta, yana zuwa yasa hannunshi duka biyu ya kamo kafad'unta, kana ya d'agota ya tsaidata suna fuskantar juna yadda in tayi mgna zai iya ganewa, 

idonshi ya rumtse da k'arfi ganin jini na bin hancinta kana tuni fuskarta tayi jazir hatta shatin yatsunshi sun taso a fuskarta,

ga wasu zafafan hawaye dake kwaranya a idanunta sabida rad'ad'in marin da k'unar zuciya kan cimata zarafi da tozartata da akayi a tsakiyar gari. 

shi kuwa Saifuddeen tuni fuskarshi ta sauya launi daga fara ta koma jazir kana idanunshi tamkar su amayar da wuta tuni jijiyoyin kanshi suka taso, 

yayinda jijiyar kan goshinsa tayi ziwat har kan tsinin karan hancinsa a fili zaka gane zallan b'acin rai,  gaba d'aya jikinshi tsuma yakeyi, 

ido ya zubawa fuskarta kana itama ido ta zuba mishi cikin rauni da muryar kuka tace.

"Wlh ban saniba bada gaggan na buga mishi motarshi ba hankalina ya tafi wurin kallon wani ne."

lips enshi na k'asa ya taune da k'arfi tamkar zai hudashi, 

kana ya kama hannunta tare da yi mata nuni data shiga motarta, 

cikin rawan jiki ta nufi gefen direban, 

hannunta ya kamo da sauri, juyowa tayi tana kallonshi itama kai ya jujjuya mata alamar a a kana ya nuna mata gefen mai zaman banza, 

ba musu ta zagaya ta shiga ta zauna.  

Shi kuwa gefen driving sit ya shiga ya zauna, 

sit bell yaja ya sank'ala jikinshi, 

kana ya juyo ya kalleta tare da yi mata alamu da idonshi tasa nata sit bell d'in. 

ba musu ta saka, 

sai ta kuma d'ago kanta da sauri jin ya dannawa motar Key kana ya figi motar a guje, 

ido ta zazzaro ganin yadda yake tsula gudu tamkar zai tashi sama, 

gudu yakeyi da tsanani amman cikin bin k'a'ida da dokar tuk'i cikin abinda bai gaza 5 minutes ba ya cimma motocin su Dalla, yayinda su kuwa tuni sun mik'a hanyar data ratsa bakin kasuwa zata kuma wuce zata bi ta kaisu fantami daga nan su ratsa bayan gidan goje, 

binsu yakeyi kib da kib haka yasa suka gane binsu akeyi, 

tuni kuma an fara kiraye-kirayen sallan mangrib, 

murmushin mugunta Dalla yayi kana ya juya akalar motarshi ya shiga cikin  sitadiyon ,

shima binsu yayi a baya kusan a tare sukayi parking.

cikin azama da zafin nama ya bud'e ya fito kana ya zagoyo inda take ya bud'e mata tare da kamo hannunta ya juyo ya nufi inda motar Dalla take, 

shima Dalla wurinsu ya nufa, 

a tsakiyar sitadiyon d'in sukayi kicibus, 

cikin wani yanayi mai wuyar fassarawa Saifuddeen  yayiwa Dalla alama da hannu akan ya bata hak'uri. 

cikin izaya da tak'ama Dalla ya gyara tsayuwanshi tare da cewa.

"Baka da bakine ko iskanci ne zaka zo kana min mgnar kurame?."

cikin tsuke fuska Saifuddeen ya kuma yimishi alamu daya bata hak'uri, ganin haka Dalla ya kuma motsotsu kana yace.

"OK kyautarta ka kawo min kenan?, baka san waye Dalla bako?  shiyasa ka biyoni da mace kana nufin in bata hak'uri ne ko?."

cikin sauri da jin dad'in Dalla ya fahimci abinda yake nufi ya tsare fuska kana ya gyad'a mishi kai alamar eh ka bata hak'uri.

wani fatsik'in murmushi Dalla yayi tare da lashe manyan lip's enshi yace.

"Hmmm aini Dalla bana bada hak'uri sai dai in bata ciki tunda ka biyoni da ita, gata kuma zata iya kashe kishin dake addabata wunin yau gaba d'aya ban hutaba kaga yanzu na samu wurin hutawa gashi tanada lafiyayyun kayan marmari a jikinta, yanzu zan mata inkiyata Dalla-dalla da budurcinta zan rab'i jikinta." 

Ya k'arishe mgnar tare da kai hannunshi kan k'irjinta.

Wani irin wawan ihu da kururuwa Dalla ya kurma  jin wani irin damk'a da Saifuddeen yayiwa hannunshi ba tare da ya samu ya isar da hannun nashi kan k'irjintan ba,

ihu Dalla ya kuma kurmawa jin Saifuddeen ya kuma murd'a mishi hannunshi har saida ya bada sautin b'as alamun ya k'arya mishi hannun, ihun daya sane yasa tarin zugan matasan dake cikin sauran motoci hud'un  nan duk suka fito, 

wando gaba d'ayansu 'yan kalarene domin duk kansu da makamai a hannunsu wasu da sanduna wasu da kataki wasuma da wuk'ak'e. 

A guje suka nufin inda suke,  shi kuwa Saifuddeen ko kad'an bai karaya da ganinsu ba, 

asalima zagewa yayi ya fara dukan Dalla tamkar Allah ne ya aikoshi,

kunsan fad'an kurma babu sauk'i  shiyasa basa tsokana basa tada husuma sabida sun san zuk'atansu basa iya jurar suga ana raini ko zalumci bare fajirci.

sam Dalla ya gaza bawa kanshi kariya, 

shiko Saifuddeen  dukan ƙaton gargadi yakewa Dalla tare da dandatseshi ta yadda bazai sake sha'awar wata d'iya maceba a duniyar nan har gaban abadan, ita kuwa Zaleeha ganin yadda suka nufo kansu haik'an k'adaran ne yasata sakin ihu tare da bubuga tsalle tanayi tana yarfa hannu tana cewa.

"Zomu gudu zasuyi maka illa zasu kasheka fa, 

kazoo mugudu karsu isomu zasu illata ka."

ganin sam bai sararawa Dallanba yasa tayi sauri ta shiga tsakanin su kana ta rik'o hannayenshi tare da kallon fuskarshi tace.

"Mu gudu zafa su kashemu."

ido ya d'ago ya kalleta yadda jikinta ke rawa tamkar mazari tsoro da firgici k'arara a idanunta da ka ganta kasan cikekkiyar matsoraciya mai lasisi ce, haka yasa ya kamo hannunta kana ya juya da ita inda motarta take,

su kuwa zugan 'yan kalaren nan kansu suka nufo a guje ganin hakane yasa, 

yajata da k'arfi sannan ya bud'emata motartata wurin zaman direba ya ajiyeta kana ya meda marfin ya rufe sannan ya sunkuyo kanta tare da kad'a mata yatsunshi biyu kana yayi mata alama dataja motar ta gudu, gane abinda yake nufine yasa ta jujjuya kai tare da zubda hawaye cikin haki tace.

"Mutafi zasu kasheka fa 'yan kalarene fa yaranshi ne."

ganin zata b'ata lokaci har suzo su sameta suyi mata illane yasashi buga marfin motar da k'arfi tare dayi mata gurnani irin nasu na kurame wanda in bawai ka saniba sai kayi zaton tsawa ya buga mata hakance ta kasance ga Zaleeha dan jin sautinshi tayi a sama haka yasa ta figi motarta a guje, tana jan motar suna isowa inda yake, yayinda shi kuwa yake kallonta so yake yaga fitanta a wurin, su kuwa suna isa inda yake ba tare da ya juyoba don shi dai kurmane bazaiji sautin takun k'afafunsu ba,

suna isa d'aya daga cikinsu ya narka mishi k'aton katakon dake hannunshi a tsakiyar gadon bayanshi kafin, yayi wani yunk'urinma 

d'aya daga cikinsune ya dab'a mishi wuk'a a tsakiyar bayanshi kana ya zaro wuk'ar wanda tuni sun farka mishi rigarshi 

wani irin razanennen ihu Zaleeha tasaka tare da zubawa bayanshi ido sabida tana ganinshi ras dan hasken motoci dake haska wurin da hasken fitulun dake zagaye da farfajiyar wurin 

cikin tsananin tsoro da firgici taja motarta ta bar sitadiyon d'in, 

tana fita kai tsaye gombe division ta nufa.


Shi kuwa Saifuddin tuni sun mishi illa sun daddatsa mishi kataki a tsakiyan bayanshi.

yayinda duk da haka bai bar kare kanshiba sai dai ance sarkin yawa yafi sarkin k'arfi gashi sun zomishi ta bayanshi kuma sunzo tare da makamai yayinda shi kuwa babu ko allura a jikinshi, 

haka yasa sukayi mishi illah mafi muni a jikin d'an adam, haka suka rink'a hankad'ashi kan k'arafun wurin suna buga bayanshi a  kai 

saida sukaga yabar motsi kana suka dauki uban gidansu da Saifuddeen ya daddaga mishi jelershi sukaja motocinsu suka tafi, 

yayinda tuni mazauna wurin kuwa sun watse don kowa yasan rashin mutuncin Dalla.


Shiru cikin sitadiyon d'in ba ko tsuntsu sai Saifuddin dake yashe tamkar mamaci,.


Ita kuwa Zaleeha bayan ta sanarwa hukuma, ganin ita macece kuma sananniya kana yar babban Malamin da akeji dashi a fad'in jihar dama k'asar bak'i d'aya yasa aka had'ata da police officer d'aya ya rakata gidansu dake New G.R.A... 




A haka police officers na station d'in gombe division suka iso, 

yayinda aka had'a da sosojin Anty kalare, 

kana

 suna isowa ganin halin da yake ciki ne yasa suka d'aukeshi, 

kai tsaye general hospital Gombe suka nufa dashi, kai tsaye aka wuce dashi o,p,d. suna isa ma aikatan wannan sashin suka turo irin yan wannan gadaje na d'aukar marasa lfy, 

tare dasa hannun hukuma aka karb'eshi bayan an duddubashi ganin aikin babbane ya kuma ji rauni sosai ne sai aka basu takarda wacce zata sadasu da babban likitan dake Medical Center.


Kan hanyarsu ta zuwa Medical Center d'inne d'aya daga cikin police d'in yayi saurin zaro woyar dake al'jihun wondon   Saifuddin

ganin tanata kawo haske alamun shigowar sak'o, 

text ne aka turo kamar haka.

```"Babana Saifuddin Kana ina?  ka dawo kayi bud'a baki mana, ka sani duk muna jiranka kasan hankali na bazai kontaba in baka ci abinci ba."```

shiru police d'in yayi yana jujjuya kalaman, a ranshi yake cewa.

"Bawan Allah azumi ma yakeyi kenan."

sai kuma ga wani sak'on da yaga  suna no  daya turo text d'in Hayatuddin inda yake cewa. 

```"Slm Hamma Saifuddeen ka dawo gida muyi dinner yunwa nakeji kuma kasan bazamu iya cin abinci ba in baka nan please ka dawo da wurin shalelen Ummi kaga ta k'i kula kowa sai cekiyarka takeyi kamar kaine autanta."```

haka nan yaji tausayin ahlin wannan bawan Allah ya kamashi,

dai-dai lokacin suka shiga harabar Medical Center Gombe, 

kasan cewar da jami'an tsarone lokaci d'aya aka karb'eshi, aka fara bashi taimakon gaggawa

d'aya daga cikin doctors da sukayi kanshi ne domin bashi taimakon gaggawa don ceto rayuqarshi yayi saurin matsoshi ido ya zazzaro woje Cikin tsananin kad'uwa da tarin tsoro da tausayawa yace.

"Saifuddeen!."

sai kuma yayi maza ya fara had'a na'urar dai-daita nufashi wato oksijin kana yayiwa sauran doctors guda biyun alama dasu fara aikinsu, 

mazuk'in numfashin suka manna mishi, 

kana suka kunna wani wuta mai tsananin haske sannan suka matso da dukkan abin buk'atan aikin suka fara, duddubashi ciki da woje sam babu wani yanka ko karta a sauran sashin jikinshi sai na bayan nashi kawai, sai kuma alamun duka da katako dake tsakiyar k'ugunshi da bayanshi.

Kana sai suka koma duba kwokwon kanshi inda suka samu buguwar guda uku, amman iya karsu woje basu shiga ciki yadda zasu shafi hankalinshi da tunaninshi ba.


Sosai suka duk'ufa dan ganin numfashi sa ya dai-dai ta,

amman abin yaci tura, 

sosai suke aikinsu cikin iyawa da gwarewa da sanin makaman aikinsu, 

shiru kakeji ba motsi sai body language da sukeyi a tsakanin su.

Tsawon awa biyu sukayi a kanshi kafin suka samu nasarar dai-dai tuwar numfashi sa, 

canza mishi gado sukayi kana Doctor Adnan ya turo gadon da kanshi ya nufi I, C U inda nos guda biyu suke biye dasu, 

bayan ya dai-dai ta mishi komai sai ya fito kai tsaye office nashi ya nufa. 

Yana shiga ya zame bisa kujerar dake mazauninshi, idanunshi ya rumtse da azabar k'arfi yana jin wasu hawaye masu azabar zafi suna tsatsafo mishi cikin jijiyoyin idanunshi, 

sai ya kuma mik'ewa da sauri  kanshi ya kifa da jikin bongon office enshin yana mai zubda hawayen.

cikin rauni da tausayawa murya na rawa yake cewa.

"Astagfurillah Allah na tuna ya Allah nasan ka fini sanin waye Saifuddeen ya Allah nasan kafi ahlinshi sonshi, ya Allah ka sauk'ak'awa Ummi wannan jarrabawa dake shirin sauk'a gareta ya rabbil izzati ka duba larurar Saifuddeen ka yaye mishi ka bashi lfy."

sai ya kuma koma ya zauna kan kujerar kana ya kifa kanshi bisa babbn table dake gabanshi, 

dai-dai lokacin Doctor Arabi ya shigo tare da police officer biyu, 

da sauri ya matso wurin abokin aikin nashi ganin yana kuka cur-cur tamkar yaro, 

cikin kad'uwa yace.

"Doctor Adnan meke faruwa?."

kai ya jijjiga jikin son tsaida hawayenshi yace.

"Dr Arabi wannan da aka kawofa k'anin abokina Nuruddeen ne."

cikin firgici Arabi yace.

"Innalillahi Saifuddeen!  to kuma me yayi musu meya tsare musu, meyasa zasu cutar da bawan Allah shida baya mgna meyasa suke son sa ahlinshi a rana Allah sarki Ummi da Rahma wayyo Hayatuddeen wayyo Raliyya da Raihana."

cikin kad'uwa police d'in yace.

"Alhamdulillahi abu yazo da sauk'i tunda kun sanshi."

cikin rauni Arabi yace.

"officer  kun kama wad'an da sukayi mishi dukan ne su waye ne ina suke me ya musu?."

cikin kauda kai officer d'in yace.

"Ina bamu kamasu ba asalima bamu san su waye bane, 

domin kafin mujema shi kad'ai muka samu a wurin babu ko mutun d'aya, 

itama wacce ta sanar damu cewa tayi wucewa tazoyi ta gefen sitadiyon d'in ne so sai taji ihu shiyasa ta kawo rahoto, 

to ganin a firgice  take yasa muka had'ata da d'aya daga cikinmu ya rakata gida don ta gaza yin draving dan tace itama sun biyota ne ganin ta d'an tsaya shiyasa har suka samu daman fasa mata glass d'in gaban mota, so kunga bamu da hanyar samun wata shaida, abu mafi sauk'i a bashi taimakon gaggawa kana ga woyarshi ku nemi yan uwanahi ku sanar dasu."

cikin rauni Dr Adnan ya rink'a jujjuya kai tare da cewa.

"Innalillahiwainna'ilaihirajiun wayyo ni Adnan ta yaya zan tinkari ahlin Saifuddeen da wannan mummunan lbri da wanne baki zancewa Ummi Saifuddeen d'inta na asibiti cikin d'ayan biyu mutuwa ko rayuwa taya zan sanarwa Rahma halinda k'aninta ke ciki?."

ganin haka Dr Arabi yayi saurin cewa.

"Please  officer  ga adireshin gidansu kuje ku sanar dasu kana ku d'aukosu ku kawosu nan d'in."

da wannan shawarar police d'in suka nufi federal lowcost

babu wuya ya gane kwatancen da Dr Adnan yayi mishi, 

a k'ofar wani babban gida sukayi hon minti uku tsakani mai gadin ya lek'o, ganin motar jami'an tsarone ya sashi bud'e k'aramar k'ofar ya fito cikin hausarsa ta buzaye yace.

"Sannunku lfy kuwa?."

cikin saisaita fuska mai jan motar yace.

"Wurin masu gidan mukazo bud'e mana gate."

cikin sanyin jiki da d'an tsoro ya bud'e gate d'in kana ya rab'a gefe suka shigo, 

bayan sunyi parking ne biyu daga ciki suka fito, 

hannu suka bashi bayan sunyi musabaha ne police d'in yace.

"Kayi mana sallama da Hayatuddeen."

to yace jiki a mace har ya juya zai nufi cikin asalin gidan sai ya kuma juyowa tare da cewa.

"Dan Allah ku gaya min lfy dai ko?."

ganin alamun rashin gamsuwa a gareshi ya sasu ce mishi, 

"Saifuddeen ne tsautsayi ya ritsa dashi so ana neman danginshi."

cikin tsananin firgici da tsoro buzun nan ya kama kai tare da cewa.

"Innalillahi! Saifuddeen meya sameshi ina yake?."

cikin mmkin waye Saifuddeen menene nagartarshi shi wayene da Doctors ma suke kuka kan cutarshi kana kalli yadda ma'aikatan gidansu ma suka firgita jin yana cikin matsala,  jiki a mace yace.

"Kaga yi maza ka mana sallama da k'aninshi."

cikin rawan jiki ya kusa kai cikin gidan nan mai azabar kyau.

A cikin gidan kuwa Hayatuddeen ne da Ummi suke sauk'owa daga benen ,

cikin shek'iyanci Hayatuddeen ya zame ya zauna kan last step kana ya manna kanshi da k'afafun Ummi dake tsaye a gefenshi cikin shogwab'a ya kalli Raliyya kana yace.

 "Yaseen yau a bedroom d'in Hamma Saifuddeen zan kwana, nine auta amman anfiji dashi,  komai nashi na dabanne Ummi da kantafa take gyara mishi side nashi, ni kuma nawa ko oho."

cikin wasa sukayi mishi dariya, Ummi ce ta shafa kanshi tare da cewa.

 "Yoh kaida kake cewa ka fini sonshi ni uwar data haifeshi ma."

ido ya lumshe tare da cewa. "In banso Hamma Saifunaba to waye zanso a duniyarnan?, amman dai duk da haka nima ina son a gyara min d'akina yayi ta shek'i da zuba k'amshi koda rabin na Hamma na ne."

dariya Raliya tayi tare da cewa.. 

"Hayatuddeen waya isa ya medaka irin Hamma Saifuddeen ko Allah ma bai halicceku iri d'aya ba Hamma Saifuddeee mutun ne mai tsabta, kaikuma irin kune ake cewa kai dai kaga gaye a titi karkaga ma koncinsa, kaida inda ka tub'e wondonka nan kake tsallakeshi."

dariya sukayi baki d'aya  dan shima yasan halinshi kenan.

Raihana kuwa cikin dariya tace. 

"Karka damu autan Ummi shalelen Hamma Saifuddeen daga yau zan rink'a share maka side d'inka."

Dariya yayi cikin jin dadi kana yayiwa Raliya gwalo, 

cikin raha tace. 

"Au nanda yaushe zata koma ka dawo kana min k'aramar murya."

dariya sukayi baki d'ayansu banda Ummi da zuciyarta ke yawan tsinkewa yana fad'uwa ras-ras.


Shi kuwa buzun nan  

wata k'ofa ya bud'e tare da kusa kai cikin wannan corridor d'in, wucewa yayi ba tare daya tsayaba cikin wannan had'ed'd'en parlour mai azabar kyau ya kuma baiyana wanda yakeda tsananin girma da fad'i kana ga steps d'in da zai sadaka da sama, sallama yayi tare da duk'awa gefen Ummi kekkyawar mace wacce zata iya kai 49 years to 50 kekyawace wacce yawan shekarunta bai samu nasarar b'oye kyantaba, Ummi kenan sai wannan d'an matashi autan nata da banzai wuce 17  years da yan watanni ba, Hayatuddeen,

Raliyya  matashiya yar duma-duma wacce zata iya kai 23  years.

  Sai kuma Raihana da zata iya kai 26 year da d'anta Affan wanda bazai wuce shekara biyu ba.


Cikin maida hankali kan buzun Ummi ta juyo cikin wani yanayi da takeji tun da yammacin yau d'in tace.

"Baba ila ya akayi ne?."

cikin sanyin jiki yace.

"Wasune ke sallama da Hayatuddeen."

mik'ewa Hayatuddeen yayi tare da cewa.

"Muje wata k'il Zakariya ne."

kai ya jujjuya mishi cikin sanyi yace.

"A a bashi bane folisawa ne,  sunce Saituddeeen ne ya samu d'an hatsari yana asibiti shine akeson yan uwanshi suje."

wata iriyar zabura Ummi tayi kana ta rumtse idonta da azaban k'arfi  sabida wani irin duhu da jirin da ya rufe mata ido a take, 

wani irin rawa jikinta ya fara har cikin hanjinta takeji suna hautsinewa zuciyarta kuwa tamkar zata faso k'irjinta ta fito fili sabida tsananin razana da kad'uwa lokaci d'aya wata zazzafar zufa ta yanko mata 

hakama Raliyya da Raihana shi kuwa Hayatuddeen gaba d'aya idanunshi ya zazzaro woje.

kusan gaba d'aya a tare suka fito Ummi kam duk jikinta rawa yakeyi tamkar mazari.


Hayatuddin  ne yayi saurin isa garesu kana cikin tsananin kad'uwa da firgici yace.

"Ina Hamma Saifuddee ina yake meya sameshi ku kaimu wurinshi waya bugeshi?."

Raihana kuwa kuka takeyi mai cike da fargaba, 

ita kuwa Raliyya direbansu taketa rabkawa kira cikin firgici da d'aga murya take cewa.

"Sule taho mu tafi wurin Hamma Saifuddee."

a hamzarce Sule direban ya taso wanda yayi ta bai jima da dawowa ba dan shi yana ƙofan Baba bello lokacin da abin ya faru kuma yayi ta kiran Saifudddeen alamun yana nemanshi baiga amsaba, to sai yayo zaton ko yayi wani wurin ne shiyasa ya dawo shi ɗaya, 

Motarnda ke harabar gidan ya bud'e ya shiga tare da jawota zuwa gabansu, 

dai-dai lokacin kuma police officer d'in yake cewa Hayatuddeen . 

"Shiga mota muje yana asibitin Medical Center ne."

firgici da kad'uwan Ummi ya tsananta jin k'irjinta takeyi yana buguwa da azaban k'arfi wata fargaba da razani ya rufeta, 

jiki na rawa ta shiga motar da Sule ya kowa gabanta sam ta kasa furta ko k'ala domin harshenta ya mata nauyi jiki na tsuma ta shiga motar, wonda tuni Raliyya da Raihana sun shiga

shi kuwa Hayatuddeen cikin kaifin basira da zurfin tunani irin nasu na maza yace.

"Ummi kuje, bari in d'auko kud'i zan taho a U.D. d'ina."

jin haka yasa Sule jan motar yabi bayan motar police d'in kana suka fita suka nufi Medical Center Gombe.


Shi kuwa Hayatuddeen , a guje ya koma cikin gida sam bai lura da Affan ba d'an Raihana wacce itama Raihana ta mance da d'an nata sabida firgincin halin da d'an uwanta ke ciki, 

to bare kuma Hayatuddeen da Ummi,

 cikin sassarfa ya haura matakalan benen har yana take steps bibbiyu, 

direct d'akin Hamman nashi ya shiga bayan wasu yan mituna sai gashi ya fito, 

yana gyara zaman kud'i a cikin al'jihunshi still bai kula da Affan ba ya wuce  yana fitowa harabar gidan ya figi mashin nashi cikin azama ya nufi asibitin. 


Su Ummi kuwa bisa jagoran jami'an tsaron suka isa k'ofar d'akin da Saifuddeen yake, 

sai dai ba damar shiga kanshi.

suna isowa bakin k'ofar Ummi ta rumtse idonta da k'arfi cikin tsananin hargitsin rayuwa tace.

"B.......



Hmmmmmmm. Wasa farin girgi karfa ku manta na gaya muku labarin sashi-sashine, littafin yana tafe da ababe masu tarin yawa,

Salon Saifuddeenfa salone da zai sanyaku shauƙi bage farfaɗo da tsohuwar soyayya hmmmmmm dafa sauran rina a kaba, ku dai ku biyoni a baya.


                       By

              *GARKUWAR FULANI*

8/18/20, 7:52 PM - Ummi Tandama: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


               *NAKASA BA KASAWA BACE*


           

                                 *PAGE 14*

                    

                           NA

               *AYSHA ALIYU GARKUWA*


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇




~Har lau dai kuna samun garaɓsar free page ne kafin a tsaya ƙoƙarta ka/ki turo kuɗin karantar littafin har ƙarshe~


_Turo katin mtn na ɗari uku kacal ta wannan number 09097853276 ,ko kuma ka/ki turo ɗari ukun ta asusuna na 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo min shaidar biyanki_


Cikin tsananin firgici da kad'uwa jiki na tsuma murya cike da taraddadi Ummi tace.

"Bayida rai ko Raihana? Raliya baya numfashi ko!? yamutu ko shikenan Saifuddeen shima yatafi yabarmu inna'lillahi wa'inna'ilaihirraji'un,!sai ta kuma fashe da kuku mai matukar ban tausayi.

jiki a mace tasulale kasa ta ta zauna kan kujerar dake gefen k'ofar cikin muryar kuka mai cike da taradaddadi takefad'in.

 "Ya Allah karufamin asiri kakara rufamin, kad'aga kafad'ar wanna bawan naka,  Saifuddeen idan katafi kabarmu yazamuyi da rayuwar mu ina rayuwa zatata kaimu Saifuddeen kadawo garemu."

sai ta kuma kalli yadda Raliya ta kife kai jikin k'ofar tana wani irin narkekken kuka, 

cikin matsanancin tashin hankali Ummi tamike tsaye kamar anzabureta.

Da sauri su Raihana  suka rungumeta suma suka fashe dakuka mai sanyin sauti nan gurin yakacame da koke-koke duk wanda yagansu saisun bashi tausayi.


 Dr Adnan dake zaune acikin offece inshi kuwa shima sai sharar kwalla yake time to time sai kuma  yamike da sauri jin hayaniya a waje, dasauri yafito.

kana Dr Arabi yamara masa baya,

ganinsu Ummi ne yasa Dr Adnan saurin saida hawayenshi,  yanufi inda suke.

    A hankali yasa hannu ya Yajanye su Raihana ajikin Ummi,

dasauri Ummi tariko hannunsa tare da zuba mishi ido murya a raunace tace.

Adnan Saifuddeen yarasuko!? dan Allah ka kaini naganshi."

wasu zafafan hawayene yaji nakokarin zubo masa dasauri yamaidasu dan gudun kada takuma shiga wani tashin halin,dukda shima hankalinsa amatukar tashe yake sai dai ya fahimci bata cikin haiyacinta matar da take tsananin jin kunyarshi ko sunanshi bata fiye kira iya gaisuwa ke hadasu sabida fulakun fulanin gaske tunda ya zama surkinta suke kunyar juna, amman gashi yau ciwon Saifuddeen yasa ta mance komai har tana rik'e hannunshi cikin sama musu k'arfin guiwa yace.

 "Ummi ki kwantar da hankalin ki.

Saifuddeen yana raye, babu wani abunda yasame shi natashin hankali, illa d'an buguwa kadan kuma duk anyi settling d'in komai yanzu haka yasamu bacci.

Ummi addu'arki kadai Saifuddeen yake buk'ata, kidaina kukanna dan kinsan bazaiji dad'iba idan yatashi ya taddaki ahakan."

da sauri tasa tafin hannunta bisa fuskarta hawayenta tashiga sharewa cikin hanzari, dan tasan abinda yafada gaskiya ne.

 Dan a duniya idan dakwai abinda Saifuddeen yafi tsana arayuwarsa, baiwuce ganin bacin ran mahaifiyarsa ba in yaga tana zubda hawaye hankalinshi tashi yake ya birkice mata, tuno hakan yasa ta tsagaita kukan,

dai-dai lokacin kuma

Dr Arabi ya k'araso inda suke nan suka hadu sukayita k'arfafa wa Ummi guiwa, harsaida sukaga tad'an sami nutsuwa kafin, suka juya suka nufi office d'in Dr Adnan kasan cewar shi babban doctor daya ke kula da masu irin matsalar da Saifuddeen yake ciko.

          

Shi kuwa Hayatuddeen gudu yake akan U.D. d'inshi tamkar zai bar garin batareda  bata lokaciba ya'isa Medical Center, 

dasauri yafaka mashin d'insa acikin harabar asibitin, 

kana yanufi cikin asibitin inda Raliya ta kwatanta mishi.


A tsaye yataddasu Ummi ganinsu tsaye cirko-cirko yasa zuciyarshi bugawa da azaban k'anrfi ido ya tsura musu tare da sassarfa cikin kid'ima ya'isa inda suke,

jikinsa nab'ari ya kalli Umminsu cikin tsoro yace.

"Ummi ina Hamma Saifuddeen?."

kai ta sunkuyar cikin son samawa yaran nata nitsuwa tace.

"Ba matsala fa ka kontar da hankalin ka ya yana bacci ne."

sai ta kuma sa hannu ta share hawayenta kana ta nuna mishi inda su Dr Adnan sukayi tare da cewa.

"Kaje ka Adnan na son ganinka."

ba tare da yace komai ba yabi inda ta nuna mishi kasan cewar yasa ofishin Adnan d'in so kai tsaye ya shiga, 

in da ya samu Dr Arabi yana nunawa dr Adnan wasu takardu da sukafi kama da hoton k'ashin bayan mutun da jijiyoyin.

Da sauri ya k'arisa gabansu jiki na rawa yasanya hannunsa acikin aljuhu yaciro kud'ad'en daya d'ebu,ya mik'awa Dr Adnan tare da cewa. 

"Ya Adnan gashi dan Allah ayiwa Hamma Saifuddeen duk abinda yadace in bazasu isaba in k'aro wasu, mu dai lafiyarshi muke buk'ata in Allah yasa yanada sauran rayuwa."

cikin kulawa Dr Adnan yace. "Ay an mishi komai duk abinda yadace duk wani taimakon da ya kamata abashi anbashi yanzu dama numfashinsa mukeso ya dai-dai ta,

kuma Alhamdulillahi munsami nasarar ceto numfashinsa yanzu jira muke zuwa gobe muga abinda Allah zaiyi,"

Cikin sanyi Hayatudden yace.

"Ya Adnan ina tsoro, kar mu rasa Hamma Saifuddeen."

kafad'arshi Adnan ya d'an bubbuga kana yace.

"In sha Allah bazamu rasashi ba, 

sannan kacewa Ummi kada a gayawa Rahma abinda ya faru a bari in na koma zan san yadda zanyi in gaya mata."

Shiru Hayatuddeen yayi fuskarsa d'auke=da matsanancin  damuwa, saikuma yace.

"Ya  Adnan yanzu zamu'iya ganin sa?".

girgiza kai Dr Adnan yayi,

tareda fadin.

 "No yanzu yana buk'atar hutu so bazai yuwu kugansa yauba."

komawa dabaya Hayatudden yayi yajinginu da jikin garu

tareda dafe kansa da yayimasa nauyi, a hankali ya rumtse idonunsa yanajin zuciyarsa nayi masa kuna wasu zafafan hawaye na zubo mishi,

tausayin Hamman nasa dasu kansu yacike ilahirin zuciyarsa afili yafurta.

 "Ya Allah kabashi lfy ka d'aga mana kafad'unshi ka rufa mana asiri."


Tare suka fito wurinsu Ummi bayan sun isane.

Dr Adnan yadubi agogon dake daure a hannunsa, kana yadubi  Ummi cikin girmamawa yace.

 Ummi kuje gida dan dare ya fara nisa yanzu inyaso saimu zauna da Hayatuddeen kafin zuwa goben muga abinda Allah zaiyi,

dasauri Ummi tace.

"A a sudai sutafi ni subarni anand'in nakwana."

Raihana ce tace.

"Ummi muma bazamu iya tafiya ba tareda munga farkawarsa ba."

 kai ya jinjina dan yasan dama hakan bamai yuwuwa bane, dan yasan k'auna da shak'uwar da ke tsakanin ahalin,

dan haka saiya kyalesu yace su shiga office inshi, kana shi ya koma office d'in Dr Arabi. 

ya rasa meyasa tun d'azu Rahma keta kiranshi gaba d'aya sai ya rasa me zaice mata lokacin daya amsa kiran nata dan a zatonshi ko taji abinda ya farune, 

ita kuwa Rahma cikin sanyin jikin da takeji tunda yamma tace.

"Ya Adnan kana lafiya kuwa inata kiranka baka amsawa?."

numfashi ya d'an fidda kana yace lfya lau Rahma meya hanaki bacci har yanzu?."

gyara konciyarta tayi tare da cewa.

"Ji nake zuciyata nata tsinkewa gabana nata fad'uwa shine nace bari in kiraka inji lfyarka."

cikin son sama mata nitsuwa yace.

"Kiyi baccinki ni lafiyata lau, in kuma wani abu kikeso ki gaya min gsky Baby in dawo in miki kona 30 minutes ne in dawo bakin aikina."

cikin jin kunya tace.

"A a ni bance wlh."

da sauri yace. 

"Kin ce mana tunda du du du fa bayan sallan isha na baro gida kuma wuni mukayi tare amman yanzu har kwadayinki ya tashi ko?."

da sauri tace.

"A a wlh to  kayi zamanka, kaga saida safe."

kafinma yayi mgna ta katse kiran.



Ance bacci b'arawo ne mesace idon kowa,

to yaudai baisami damar sace idanun wanna ahalin ba.


Acan d'aya sashin kuwa cikin New G. R. A. 


Hargida police d'in da aka had'ashi da Zaliha yakaita, abakin makeken gate  d'in gidansu tatsaya, 

kana yafita amotar tayimasa godiya yatari abin hawa yatafi,

dasauri tafita takoma gefen driver tunkan takarasa zama tadanna horn dan har'alokacin amatukar tsorace take,

da gudu maigadi yataho dan jin yadda aketa danna hon ba sassauci da sauri ya wangale mata get d'in,

da sauri ta kutsa hancin motarta cikin farfajiyar gidan nasu da gudu,

asakar farfajiyar gidan tayi parking tafito, 

maigadi nakokarin rufe get

wata lafiyayyiyar mota mai azabar kyau da tsananin shek'i ta danno hancinta cikin gidan,

Zaliha kuwa har tajuya zata shige cikin gidan, 

ganin shigowar motar yasata tsayuwa, yayinda gaba d'aya zuciyarta da tunaninta ke can wurin kelyawan mutumin daya taimaketan

har aka faka motar tana nazari asannu akabude marfin motar  yazuro kafafunsa yafito,da murmushin sa yanufi inda  Zaliha take,

itako kwabe fuska tayi tareda langwab'ar dakai gefe,

yakaraso inda take waro idanu yayi ganin galashin motarta afashe cikin mamaki

yace.

"Hatsari ki kayine Zaliha?." cikin muryar shagwaba ta tura baki tare da yarfa hannu tace.

Ya Ahmed ba y'an kalare bane na taddasu a hanyata ta dawowa sunata fad'a shine suka fasamin gilashin mota, badon a mota nikeba nima da sun fasa min kai."

takarasa maganar kamar zatayi kuka dan tausayin Saifuddeen da ta baro suna shirin kashewa,

dasauri Ya Ahmed d'in nata yace.

 "Ina dai ke basu ji miki rauniba ko?."

kai tagyad'a masa tare da cewa.

 "Amman dai ai sunyiwa motata illa ai."

cikin kula da shak'uwa yace. "To Alhamdulillahi da Allah yasa akan motace ba kan 'yar kekyawar k'anwata aka fasaba,

gobe ida Allah yakaimu zamuji kizabi motar da kikeso.

 Amman fa mai sauk'in kud'i Hajia na sanki baki san zafin neman kud'iba sai son ayi ta kashesu ba sassauci."

bayanshi tabi tare da cewa. 

"To Ya Ahmed duk yadda kace hakan za'ayi."

shi kuwa Ahmed motar tata ya d'an kalla tare da cewa.

"Wannan d'in za'a gyara sai a saida ta  in cikata miki ki samu sabuwa koda wacce bata kai wannanba,

 ki samu ta zuwa aiki."

tsalle tarikayi tareda rike hannunsa,

tana fad'in.

 "Na gode Ya Ahmed Allah ya k'ara bud'i rabbi ya k'arawa Baba Malam daraja da lafiya da tsawon rai."

murmushi yayi cikin tsananin jin dad'in addu'arta ga mahaifin nasu ya rik'o hannunta suka shige cikin gida.

 Wani babban parlour suka shiga wanda yake  wadace da tsananin tsabta, wasu manyan kujerune na alfarma ke zagaye da fad'in parlour kana sai wani tattausan carpet mai tsananin taushi sai can gefen dama wasu manyan kanta guda biyu da suke cike da tarin Qura'anai da sauran littafai kama daga na addini dana boko harda su baibul wanda.

sai wani babban tv dake manne da jikin ginin, kana gefen hagu kuma dinning area wanda yasha gyara, 

sai kuwa wata kujera dake tsakiyar parlour wacce tafi kama data sarakuna sai wani stoll na glass dake gaban kujerar.

wani dottijone mai tsananin kyau fari k'al k'al dashi yake zaune bisa kujerar nan ta tsakiyar parlour, bisa dukkan alamu alwala yayi yanzu, duk da anyi sallan isha koda yake hakan baya rasa nasaba da kasan cewarshi baya zama ba tare da alwala ba.

zaune yake kana ya mik'e k'afafunshi bisa stoll d'in hannun shi had'e wuri d'aya yana murzasu kana yana d'an karkad'a k'afafun nashi, 

a hankali yake motsa labbanshi bisa dukkan alamu tasbihi yakeyi kasan cewa d'abi'arsa ce duk abinda yake bashi hanashi ambaton Allah.

can gefenshi kuwa wata kekyawar matace mai d'an ma dai-dai cin tsawo da jiki, bona ce ta jona jikin soket d'in wuta kana tasa wani turaren wuta mai dad'in k'amshi, 

labulayen parlour ta sassake sabida yanayin hazo, 

kana ta rage gudun fankan, sannan ta kashe A, C gaba d'aya. 

cikin nitsuwa dottijon ya juyo ya kalli k'ofar parlour inda yaji muryar yaran nashi, 

amsa musu sallamarsu yayi tare da basu izinin shiga. 

a tare suka shigo gabanshi suka zauna cikin cikar tarbiya sukace.

"Barka da dare Baba malam."

cikin son yaran nashi yace. 

"Allah ya muku Al'barka."

cikin tsananin jin dad'i Ahmed yace.

"Amin Amin Baba malam mun gode."

murmushi yayi dan yasan yadda Ahmed ke tsananin jin dad'i in ya mishi addu'a, 

ita kuwa Zaliha cikin nitsuwa sanin a gaban Baba malam suke ta kalli Hajia Aisha mahaifiyar Ahmed kenan wacce suke kiranta da  Mamy, cikin logob'ar da kai tace.

"Mamy yunwa nakeji."

cikin nitsuwarta ta matso inda suke kana tace.

"Ke kinada tsiya ne komai aka dafa kice bai mikiba, sai kije kitchen ki dafawa kanki dan ni dai tuwo nayi."

a hankali ta mik'a tare da cewa. 

"Baba malam saida safe."

ido ya d'an juyo ya kalleta kana yace. 

"Allah ya bamu Al'khairi kada ki konta bakiyi al'wala da adduba kada kiyita jin kid'e-kid'enan da kike sawa a gidan radionku."

cikin sanyi tace. 

"Toh". kana ta juya ta fita.

Ahmed kuwa murmushi yayi sanin an d'aureta tunda an hanata shan kid'a, 

nan sukayi ta hira da mahaifinshi da mahaifiyarshi, 

ita kuwa Zaliha kai tsaye parlour Mamanta ta nufa, 

gefen wata mata mai d'an k'iba da alamun rashin fara'a a fuskarta gefenta ta zauna da gani matar k'abilace ba hausa fulani bace sam bata da fara'a

cikin sauk'e numfashi tace.

"Mama barka da dare."

murya can k'asa a dak'ile tace.

"Sai yanzu kika dawo ko can d'akin uwar taki kika je."

konciyarta ta gyara bisa 2 str kana tace.

"Nida ya Ahmed ne kuma wurin Baba malam muke."

kai ta gyad'a kana tace.

"To tashi kije kici abinci Zulaihat ta muku awaran kuskus."

jin haka ta mik'e da sauri ta nufi dinning table, gefen washing hand baby ta nufa hannunta ta wonke sannan tazo ta zauna tanaci suna d'an hira da Mamansun.

Kad'an ta ci ta mik'e jiki a mace ta nufi d'akinta 

tazo gab da bakin k'ofarsu Zaheera taji Zulaihat nata hayaniya alamun tana tarfawa Zaheera rashin kunya,

kai ta kauda ta wuce d'akinta dan bata cikin yanayin jin dad'i bare konciyar hankali.


Tana shiga ta cilla woyoyinta bisa gadonta kana ta zame ta  durkusa a k'asa tare da kife k'irjinta bisa gadon pillow ta jawo tare da d'aurashin kanta a hankali ta rumtse idanunta sai kuma tayi saurin bud'esu da sauri sabida ganin tamkar yanzu ake sokawa Saifuddeen wuk'a a bayanshi kife kanta tayi cikin pillow ta saki wani irin zazzafan kuka mai sanyin sauti, ta jima tana kukan a hakan tayi baccin da baifi 45 minutes ba ta fara mafarki tana jujjuya kai da karfi ta saki ihu tare da cewa. 

"Mu gudu kada su kasheka kazo mu gudu wayyo ya Ahmed sun kashe minshi."

sai ta kuma mik'e da sauri sabida farkawan da tayi, 

kai ta kife bisa gadon tana wani irin kuka mai cike da tausayi da rauni, 

sai ta kuma mik'ewa da sauri kai tsaye bathroom ta nufa al, wala tayi kana ta fito nafilfili tayi tayi wanda duk cikin sujjadanta shi take yiwa addu'a ranar da a haka ta kwana batayi bacciba wonkan da yake al'adar rayuwarta ma kafin tayi bacci amman yau bata Toshiba. 


 Washegari damisalin karfe 6:00 Am, Dr Adnan yafito daga room d'inda Saifuddeen yake,dukda sanyin asuba irinta hunturu dakuma sanyin AC dake zagaye awurin saida Dr Adnan yahad'a zufa sharkaf sabida tashin hankali da fargabar dake tare dashi, 

kallo d'aya zaka yimasa kagane tsantsar tashin hankalin da ke shinfide akan fuskarsa cikin mutuwan jiki yayi isa office d'inshi, 

Cikin hanzari Ummi dake zaune akan sallaya tana jan jarbi,

tamik'e tsaye tana mai zuba mishi ido tare da fad'in.

 "Baban Adnan yafarka kuwa?."

saurin sai-sai ta nutsuwarsa yayi dan son boye tashin hankalin da yake ciki kana yace.

"Ehm Uhmm  ba..ba..bakomai fa Ummi in sha Allah  zai farka in Allah ya yarda ba wata matsala."

ita kam Ummi cikin rashin gamsuwa da maganarsa tafara magana cikin zubda kwalla tanafadin,

"Ka fad'amin halin da yake ciki in yamutune ma kada ka boye min dole inyi imani da k'addarata."

da sauri su Raliya dasuke zaune agefe suma bayan sun idar da sallah suka taso.

Hayatuddeen dayanzu dawowarsa daga masallacin dake cikin asibitin,shima ya'iso da sauri,

ganin haka yasa Dr Adnan cewa.

"Ummi baifa mutuba zo kuganshi ma."

kana ya juya yayi cikin room d'in dasauri suka rufamasa baya,can suka hangosa kwance ga na'urori sakale ajikinsa

da sauri suka nufi jikin gadon,idanunsa arufe ruf bayako motsi, abinda zainuna maka cewa yanada rai shine numfashin shi da yake ja tacikin na'uwar jan numfashi.

cikin rauni da fargaba jiki na rawa Ummi tariko hannunsa yayinda hawaye ke kwaranya a idanunta murya na rawa 

tace.

 "Saifuddeen wanene yayimaka wanna illa haka? waya zalincemu zalumci mafi muni arayuwar mu? memuka tare masa?."

a tare tajero tanbayar tareda kife kanta ajikin gadon ta saki sassanyan kuka.

Hayatuddeen,da shima kukan yake  ganin dan'uwansa acikin mawuyacin hali,

Raliya  Raihana duk kuku suke,

Dr Adnan ma shima kukan yake babu mai rarrashin wani a cikin su zuwa can Dr Adnan yashare hawayen sa cikin hanzari yamaso kusa da Ummi muryarsa narawa ya kwakulo murmushi dole yace.

 "Ummi bawata masalafa ku kwantar da hankalin ku in sha Allahu zamuyi duk abinda yadace."

 cikin muryar kuka Ummi tace.

"Adnan duba kaga halinda Saifuddeen yake cikifa sannan kace wai babu wata damuwa,

ka duba ka gani nice yau a gaban Saifuddeen amma yagaza d'aga ido yadubeni bare harya shiga farin ciki kamar kullum saboda ganina akusa dashi,

lallai Saifuddeen d'ina yana cikin  mawuyacin hali."

sai ta kuma rik'e hannunsa tamatse acikin nata tanamai cigaba da kukan,

da sauri Dr Arabi yaturo k'ofar da sauri dan duk abinda suke yanajinsu daga cikin offece insa,ya'isa ciki tareda d'aura wata na'urar dake rike a hannunsa asaman kirjin Saifuddeen dan da alamun bugun zuciyarshi ta tsananta da sauri 

yace.

"Ummi ku d'an je waje zamuyi aiki yanzu."

dakyar Ummi tasaki hannun Saifuddeen ta fita tana cigaba da sharar kwalla,

su Raliya ne sukabi bayanta.

Hayatuddeen ko wayar Saifuddeed ya d'auka wanda yagani agefensa sanna yafita,  sunafita Dr Arabi yahad'a na'urar daya d'aura kan kirjin Saifuddeen,

kana  ya juyo yana fuskantar Dr Adnan tare da cewa.

"Haba Dr Adnan a matsayin ka na Dr bai kamata karika kashewa majin yatanka guiwaba,

kamata yayi karika karfafa musu goiwa surika sawa aransu majinyacinsu zaisami lfy,

amma kaima kazauna agabansu kana zubda hawaye ai sai ka saka musu kokwanto azukatansu,

tabbas nasan shakuwar dake tsakanin ka da Saifuddeen,

so hakuri zakayi kabasu kwarin goiwa akan samun saukinsa sai kaga komai yatafi dai-dai."

a hankali Dr Adnan yashare hawaye kana yace.

 "Hakane amman kaima kasan dai akwai babbar masala,

bazan tab'a iya mik'ewa ya tsaya da kansa ba,bazai iya morar kansa ba,

saboda illar da suka yimasa agadon bayansa zuwa kugunsa,bansan tayanda zansanarwa Ummi wanna mummunar labarin ba"

 a hankali Dr Arabi yace. "Nasani,to amma ya zamuyi da ikon Allah, shi ya halicci Saifuddeen kuma ya fimu sonshi kuma insha Allah shi zai zama gatanshi,

 yanzu dai ya kamata musan menene mafita."

shiru Dr Adnan yayi saboda tunanin hanyar data fi dacewa don dole a wuce da Saifuddeen Abuja.


Koda Hayatudden yafita Gefe yakoma yazaro wayarsa a'al'juhu dan tun jiya yake akashe yakunna sanna yasaka wayar Saifuddeen acikin aljuhun,

bayan yakunna wayarsa saiya lalub'o number Ishaq wato babban abokin Saifuddeen, 

yana d'agawa yace. 

"Hello Hatuddeen yau kuma gaisuwar sassafene za'ayiwa Hamma Ishaq."

cikin raunin murya yace.

"Ina kwana Hamma Ishaq."

da sauri yace. 

"Lafiya lau, Hayatuddeen."

bayan sungaisanne Hayatuddeen yake ce masa. "Hamma ishaq muna asibiti Hamma Saifuddeen bashida lfy."

ba k'aramin tashin hankali Is'haq yashiga ba dajin cewa abokin sa na'asibiti wanda jiya da yamma suka rabu lafiya-lafiya sannan  kuma yanada tabbacin cewa bakaramin ciwo bane zaisa Saifuddeen yakwanta a asibiti.

shiko Hayatuddeen katse wayar yayi yakoma inda su Ummi suke, 

jugum-jugum sukayi kowa da abinda yake sakawa azuciyarsa.

sunan zaune har gari yayi haske.


Karan ababen hawane yacika cikin harabar asibitin motoci da  mashunan guragu irin masu tsada da kyau  wanda zasu iya kaiwa 23 kana  sai wasu motoci kusan guda 6 wanda sukeda tambarin (Jonapwd) Gombe state chapter all the best! bi ma'ana tambarin k'ungiyar nakassasu ta jihar wato Joint national association of persons with disabilities.

 kuma kowani mashin guda mutane biyu ne ke kansa,haka sukarika faka mashin d'in suna sauka akansa,abin mamaki mutanen duk nakasassune,

sai dai bazaka tab'a banbance makafin cikiba domin babu sanduna a hanunsu bare yan jagora kana suna cikin tsabtacecciyar shiga ta alfarma mafi akasarinsu sunfi kama da ma'aikata,  kuramen ciki kuwa bazama ka tab'a zaton sunada wata nakasa a jikinsu ba, guragu kuwa sai dai ka gane da sawun wasunsu da suke a shanye wasu kuma da sanduna suke dan tokarawa gaba d'aya sun cika  harabar asibitin kuma ba  hayaniya bare sowa suna komansu cikin tsari da wayewa  fiyema da masu ji da gani yayinda wasu ke ambaton.

 "Ya Allah! kabaiwa d'an uwanmu Garkuwarmu lfy,

idan kacire manashi a cikinmu  bamu san ya zamu k'are da rayuwaba dan munsan cewa zamu tagayyara mudawo abin kyama abin gudu acikin al'umma sunai mana kallon wasu hallitu na daban." makafin cikinsu  nata fad'in. "ku kaimu inda yake?."


Mutane sukarika fitowa daga cikin asibitin, wad'anda suke gefe da asibitin wato mazauna gefen asibitin suma suka shisshigo,danganin taron mutanen dasuka shigo cikin asibitin.

 Dan ganin abinda kefaruwa,jama'ar dasuka fito dan kallon mutanen sunsha mamakin jin kallama da ya kefita abakin wadanna nakasassun,sai ambaton Saifuddeen suke,

jama'a duk suka cika da alhinin jin sunan wanna bawan Allahn dasuke ammaba,to waye shi dahar wadanna mutanen zasu nuna damuwarsu da tashin hankalinsu akansa,lallai wanna mutumin komai akayi adaline,sosai a garesu domin wasuma sunyi zaton ko zanga-zangar lumana nakasassun keyi, 

gurin ya kacame da hayaniyar mutane dake tambayar meke faruwa. 

Hayatuddeen ne yamik'e tsaye da sauri yace.

"Ummi mutanen Hamma Saifuddeen ne sukazo dan naji sunata kiran sunansa bari naje wurinsu."

kai kawai Ummi ta'iya gyad'a masa alamar toh.


Hayatuddeen yafito farbajiyar asubitin suna ganinsa suka nufi inda yake suka zagayeshi,suna fadin.

"Ina Saifuddeenin d'inmu yake kanunama inda yake."

hannu sa yad'aga sama yana juyashi, tare da yin sauri ya isa gaban Ishaq cikin girmamawa yace.

"Ya ishaq barka da zuwa."

da sauri ishaq ya mik'o hannu ganin haka shima Hayatuddeen ya mik'o mishi hannu tare da cewa. 

"Gani nan Ya ishaq." 

da sauri ishaq yace.

"Yauwa Hayatuddeen ta ina Saifuddeen yake muje mu ganshi."

cikin d'an murmushi Hayatuddeen yace.

"Hmmm kai ishaq kullum lamarinka akwai k'arfin hali da iya ruggumar k'addara wai muje mu ganshi sai kace kana gani."

shima Ishaq murmushi k'arfin hali yayi tare da cewa. 

"ai ba idone gani ba, ku masu idone kuke d'auka da ido kawai ake gani,  mu kunnuwanmu ma tamkar idone kana da zuciyarmu da k'ok'wolwarmu, yayinda kuramenmu kuma idanunsu ne kunnuwansu,  ba gashi yanzu koda bana ganinka nasan kana zubda hawaye daga sautin muryarka."

cikin sanyi Hayatuddeen  yace.

 "Ku kwantar hankalinku,

ku dakata dan Allah kuyi hakuri yanzu bazaku sami ganin saba dan yasamu yin bacci saidai zuwa anjima."

cikin gamsuwa sukace.

 "To yajikin nasa?."

saida ya maida hawayensa dake kukarin zubo masa dagudun kada hankulansu yatashi,danyasan cewa basu kadai ahalinsa kebukatar Hamma Saifuddeen ba, hardasu wadanna nakasassun,dama  wasunsu baki d'aya,.

 "Da sauki". yace dasu atakaice,

dakyar shugabannin  nasu suka samu suka lallab'asu sukatafi,sanna shikuma Hayatuddeen yayiwa su ishaq d'in iso zuwa ciki inda su Ummi suke.

 

Suna shiga Dr Adnan nafitowa,

kana Dr Arabi nabiye dashi su Ummi naganinsu sukamike tsaye suka k'araso inda suke,Ummi kallonsu take fuska kunshe da tanbayoyi

Dr Arabi yakalli Dr Adnan wanda keta noke-noke yayi masa alama da ido,

jiki asanyaye Dr Adnan ya mik'awa Ummi wata doguwa takarda fara yace.

"Ummi wanna takardar ta transfer ce zuwa Abuja,

naturaku asibitin kimiya dake birnin tarayya Abuja National hospital Abuja

,idan kun isa saikiba su wanna takardar

da sauri Ummi  tace.

 "Abuja! Kuma?."

kai ya gyad'a mata alamar eh, 

a hankali tace. 

 "Lallai ciwon Saifuddeen babbane tunda har katuramu Abuja."

Kai Adnan ya girgiza  dasauri,dan bazai iya fad'a mata akwai masala ba, yafiso sai sunje can d'in  asanar musu.

tana karbar takardar yayi saurin juyawa dasauri dan gudun kada Ummi takuma jefo masa wat tanbayar,

yanafita yayi duk wani cuku-cukun dayadace natafiyarsu ba tareda bata lokaciba yakammala komai bank'arensu. 

Ishaq kuwa takardar ya amsa kana suka juya tare da Raihana, kai tsaye Federal low cos suka nufa, 

E passport d'in Ummi da Saifuddeen dana Hayatuddden yasa Raihana ta kawo mishi, 

daga nan direban k'ungiyar tasu yaja suka wuce  Airport, nan ya gama musu dukkan shirin tafiya hardashi d'in suka kuma yi sa'a akwai jirgin da zai tashi zuwa Abuja k'arfe  biyun rana zai tashi. 


1:53 pm  duk sun gama shirin komai, 

takofar baya Dr Adnan yashiga yaturo gadon yafita takofar bayan,

Dr Arabi natsaye ajikin motar da zai kaisu airport da taimakon sa suka tura gadon cikin motar suka dai-dai zaman gadon sosai acikin motar,

Kana Dr Adnan yakoma indasu Ummi suke yace.

"To Ummi  an gama shirya komai shirya komai ku akejira yanzu,

 sanna kuma tafiyar zai kasance dole damutun biyune sanna kuma... da sauri Raihana tace.

 "Ummi ku kutafi keda Hayatuddeen, mu zamu koma gida nida Raliya fatanmu  samun saukin Hamma Saifuddeen zan kira Abban Farida yayi k'ok'arin dawowa,."

cikin gamsuwa Ummi tace. "to".  

"kuyi maza kutafi nima zuwa gobe da yamma zan shigo Abujan." 

Dr Adnan ya fad'i tare da juyawa yayi gaba,

da sauri  suka bishi abaya.

koda suka'isa jikin motar, Ummi da Hayatuddeen suka shiga,driver yatada motar Raliya da Raihana nad'aga musu hannu dayimusu fatan samun nasara,yiyinda dukansu suke ta sharar kwalla,driver yaja sukabar harabar asibitin,

"Sukadau hanyar Airport, in da tuni ishaq na can su kawai yake jira. 

suna isa bada jimawa ba jirginsu ya tashi. 

3:00pm yamusu a cikin birnin taraiya Abuja direct National hospital suka nufa.

Kasancewar duk abinda yadace Dr Adnan yarigada ya'aiwatar dashi ta online , so ansan da zuwansu,basusha wani wahalaba,suna isa nurses suka taho jikin motar data d'aukosu daga airport nan suka fito dashi.

Kana Ummi 

 tamikawa d'aya dagacin nurse d'in takardar da Dr Adnan yabata,sanna suka turoshi sukashiga cikin asibitin, direct Emergence room aka shige dashi.

 Nan Doctors suka dukufa akanshi basu yi wata-wata ba suka fara bincike akan laluransa kamar yanda yazo musu arubuce,

cikin k'ank'anin lokaci S.....!








                            By

                   *GARKUWAR MARUBUTA*

8/18/20, 7:52 PM - Ummi Tandama: [3/30, 10:50 AM]

📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


           *NAKASA BA KASAWA BACE*


                           *PAGE 15*


                                     NA

                  *AYSHA ALIYU GARKUWA*


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇



                   ~Free page~



    Suka gano matsalar shi, kana suka dugufa kanshi dan samo numfashin sa ya dai-dai ta, domin babu wani aiki da zasuyi mishi har sai ya dawo haiyacinshi. 

Hakan yasa suka meda hankali ganin komai ya dai-dai ta, cikin ikon Allah a daren ranar ya farfad'o yana kuma cikin haiyacin sa, kasan cewar dare yayi nisa, yasa aka bar batun dubashi zuwa safiya. 


Bappa Ali da Warisu da Mudassir kuwa tunda Hayatuddeen ya sanar musu gaba d'aya hankalin su ya tashi sai dai sun meda hankali wurin yi mishi addu'ar samun lfy a cikin ka'aba. 


Ishaq kuwa, tunda aka shaida musu bazasu dubash yau ba sai gobei, sai ya kira babban yayanshi dake nan Abuja da iyalanshi ya shaida mishi, ba jimawa kuwa Ya Rabi'u yazo tare da direbanshi, domin dukkan sashin zuriya biyun sun san abotar Ishaq da Saifeddeen domin abotace tun na yarinta,  hakan yasa har iyaye su suke mutunci da zumunci mai k'arfi. 

Kasan cewar babban doctor uban gidane ga Dr Adnan hakan yasa tun kafin suzo an shirya komai, hatta da masu kula dashi, ya tanadar cikin ma aikatan nasu, 

ya kuwa kontarwa Ummi hankali ta tare da bata k'arfin guiwa. 

Haka yasa Ya Rabi'u ya tafi da su gidanshi, cikin sa'a ma kuwa asibitin ba tazara sosai da diganshi. 



Ummi kuwa da Hayatuddeen dugufa sukayi da Addu'a jigon nasu.

Deren ranar sam basu rumtsaba, shima Ishaqa bayi bacciba. 



A can gida Gombe kuwa, bayan su Raihana sun koma gida, kai tsaye falon Ummi suka wuce, 

cikin sanyin jiki Raihana ta zauna bisa kujera, 

idonta ta rumtse da k'arfi, a jere wasu zafafan hawaye suka zubo mata, 

ita kuwa Raliya wayarta ta d'auka, ta fara 'yan dube-dube bayan yan wasu dak'ik'u ta kara wayar a kunne, 

a hankali ta bud'e labbanta tare da cewa.

"Wa'alaikassalam, Abban Farida, yaushe zaka dawo?."

a can d'aya sashin Abban Farida yace.

"Lafiya dai ko?."

murya a sanyaya tace.

"Alhamdulillahi ala kulli halin."

jin haka yasan to tabbas akwai matsala sai dai iya sarrafa harshe na matar kwarai wacce tasan yadda zata isar da sak'o wa mijinta ba tare data firgitashi ba, 

cikin dakiya yace.

"Meke faruwa?." 

tallabe hab'arta tayi tare da cewa. 

"Abban Farida ka dawo gobe, please inda hali in zaka samu    jirgin yau dan Allah ka taho gida."

cikin kad'uwa yace.

"Raliya meke faruwa ki gaya min mana, zuciyata ta cika da zulumi."

"Hamma Saufudddeeen! Saifuddeeen!! Saifuddeen..!!!."

tai ta maimaita mishi murya na rawa. 

mik'ewa yayi tsaye cikin fargaba yace.

"Innalillahi wa Inna'illaihi rajiun. Meya sameshi? ina Hayatuddeen?  Ina Ummi?."

Cikin kuka tace. 

"Suna Abuja an tafi dashi asibiti."

daga nan ta sanar dashi dukkan abinda yake faruwa, 

ta k'ara da cewa.

"Ya Adnan ya turasu Abuja. Abban Farida ka dawo wlh Hamma Saifuddeen ko motsi baya yi sanda suka tafi dashi."

ta karishe maganar tana zubda hawaye. 

 Shi kuwa Abban Farida datse kiran yayi kana ya fara harhad'a yan abin buk'atunshi, kai tsaye Airport ya nufa cikin sa'a  ya samu jirgin Abuja, dama shi bai niyar zuwa Gombe ba. 


Kafin su isa abuja dare ya d'an fara nisa kuma yayi ta kiran number Hayatuddeen da Ummi duk basu d'agawa,  haka yasa ya nemi masauk'i inda ya kwana da nufin da safe zai nemesu. 



Dr Adnan kuwa, saida yaga tashin su Ummi sai da ya koma asibitin kafin ya koma gida. 

Shiru parlour nasu ba kowa haka yasa ya zauna bisa 1 str zuciyarshi da jikinshi na cike da fargaba da tsoron halinda martashi Rahma zata shiga in taji abinda ya samu d'an uwanta, 

ya rasa tudun dafawa, a fili yace.

"Ya ilahi ya mujubbat da'awati ko taya zan sanarwa Rahma."

sai kuma yayi sauri zaro woyarshi Ishaq ya kira, 

bayan sun gaisa yace.

"Kun isa lfy,?."

"Lafiya lau Alhamdulillahi."

gyara zamanshi yayi tare da kallon k'ofar corridor d'in part d'in Raihana sannan yace.

"Kun samu Dr Aliyu ko?."

"Eh to gsky mun samu tarba daga wurin Doctors har uku to gsky ban sanan wanne ne Dr Aliyun ba a cikinsu."

cikin sanyi yace. 

"Zakaga Dr Aliyu shima nakasasshene ai domin shima yanada matsalar spanal cord  kuma shine big doctor a k'asarnan in dai a wannan fannin ne, uban gida nane kuma wa nane d'an kawuna."

cikin jin dad'i Ishaqa yace. 

"Alhamdulillahi, hakan yayi kyau domin dama shi nakasa ai ba kasawa bace, kuma ya yi mana k'arin bayani kan mu kontar da hankalin mu, Alhamdulillahi kuwa tuni ya farfad'o kuma yana cikin haiyacin sa, so zuwa gobe da safe zasu fara bincikan adadin zurfin ciwon."

lumshe ido Dr Adnan yayi kana yace.

"To Allah ya kaimu, in sha Allah nima gobe zan taho please kuke kontarwa Ummi hankalinta."

"In sha Allah ba matsala." cewar Ishaq. 

Kana daga nan sukayi sallama, 

shi kuwa Dr Adnan Dr Aliyu ya kira bayan sun gaisa yake mishi godiya tare da tambayar ya mai jikin, so shima Adnan ya samu d'an nitsuwa duk da cewa Dr Aliyu ya tabbatar mishi cewa Saifuddeen ya samu nakasar lakkar bayanshi.

bayan sun gama woyar ne yana d'ago kanshi ya hangi Rahma tsaye bakin k'ofar kitchen ta kafeshi da ido gaba d'aya jikinta tsuma yakeyi tuni hawaye sun jik'a fuskarta, 

mutuwar zaune yayi domin tabbas yasan taji duk wayar da yayi dasu, dan sam hankalinshi bai bashi ko tana kitchen ba. 

Ita kuwa matsowa ta farayi a hankali take taku still jikinta na rawa, 

gabanshi ta tsaya tare da tirtsetsen cikinta, 

da sauri yasa hannu ya jawota jikinshi kan cinyarshi ya ajiyeta, suna fuskantar juna, murya na rawa tace. 

"Me kuma zaka boye min Ya Adnan me zaka boye min? gaya min me zaka boye min. wani abune kuma ke tinkarar rayuwarmu? meya samu d'an uwana? ina yake, waye zai nak'asa Saifuddeen ne ko Hayatuddeen gaya min wani hali Ummi ke ciki?."

gaba d'aya ta birkice ta gigitashi da tambayoyinta yama rasa wanne d'aya zai amsa mata kuma tana k'ara tuno mishi fargabar da Ummi ke ciki. 

Kawai sai ya had'eta da k'irjinshi ya ruggumeta da k'arfi kana ya fara magna cikin dakiya yace.

"Madadin kiyi mishi addu'a sai kiyi mishi kuka?  kin san halin da yake shiga duk sanda yaga hawaye a kwaranya a idanunki, meyasa rauninki yake yawaita, da can baya da juri na sanki to meyasa bazaki ruggumi k'addaraba, ki godewa Allah a cikin dukkan lamarinki."

tunda yace mata kin san baya son kukanki ta gane Saifuddeen ne, to wani zafin ya wuce inda hawaye yake fargabarta da nitsuwarta duk sun had'u sun hargitse sun danne hawayenta, 

sai tayi wani azabebben murmushi da yafi kuka zafi cikin sanyi tace. 

"Alhamdulillahi ala kulli halin, ya Allah ka fini sanin waye Saifuddeen ya Allah ka fini sani adadin mutanen da ya zame musu uwa uba yaya k'ana, ya Allah ka fini sanin rauninshi dana mahaifiyarmu ya haiyyu ya k'aiyyum ya zirjalali wal ikram ya Allah ka bashi lfy ka d'aga kafad'un shi."

da sauri Dr Adnan yace. "Amin Amin, Ameeen ya rabbil izzati."

daga nan yayi ta bata baki da nuna mata ciwon baiyi tsanani ba.

Amman duk da haka daren wannan ranar itama sam bata rumtsaba. 



Raihana kuwa har dare Allah baisa ta tuno da Affan ba domin tunda suka dawo data haura sama d'akin Saifuddeen kuka tayi tayi, 

sai bayan sallan isha da Amira 'yar Alhaji Kabiru ta dawo mata da shi itama haka ta kwana yiwa d'an uwanta addu'a.



 A can Abuja kuwa, tunda asuba matar ya Rabi'u Aunty Mami ta tasa yar aikinta gaba suka shiga kitchen, dan Ishaq ya gaya mata da sanyin safiya zasu koma asibitin. 

bayan ta gama komai ne ta d'auki na su Ishaq da yayanshi da Hayatudddeen ta kai musu bisa dinning table dake nan men parlour nasu, 

inda tunda suka dawo masallaci suna nan zaune suna tattauna matsalar inda shi Hayatuddeen yake cewa shi yafi son a fita woje da Hamma Saifuddeen nashi yaci gaba da cewa. 

"Ance Jermaine itace k'asar da tafi shahara da kwarewa ta fannin wannan ciwon, ni kam da zan samu mu fita dashi."

ya k'arishe mgnar yana mai kallon Ishaq da yanayin neman izini.

 Cikin tausayawa Ya Rabi'u yace.

"Ba matsala ! Hayatuddeen in sha Allah tun da Dr Aliyu yasa hannu kan lamarin so ko can Jermaine aka kaishi iya abinda yace zasu ce, kana nasan zaiyi duk abinda ya dace in kuma yaga fitar da shid'in nema maslaha to tabbas, nasan zai  bada dama a fitar dashi, kuma zai shige mana gaba yadda komai zaizo da sauk'i. 

Yanzu ku matso muyi breakfast saimu hanzarta zuwa, tunda ya shaida mana kwana zai a asibitin kana da safe zai dubashi kafin ya tafi gida."

cikin lumshe ido irin na marasa gani Ishaq ya d'an shafa kan Hayatuddeen tare da cewa. 

"Zo muje kaci abinci in sha Allah Saifuddeen zai samu lfy."

haka dai sukayi ta bawa juna k'arfin guiwa. 


Ummi kuwa sam ta gaza samun sukuni, abinda ta sanine bazata iya cin abinciba, amman ganin yadda Mami ta matsa akan dole taci abinci yasa tace.

"Bani tea kawai in sha."

cikin jin dad'i Mami tace.

"Yauwa Ummi gwara kici wani abu kafin ku tafi domin, bamu san yaushe zaku dawoba, kuma shima zama da yunwa cutane."

amsar cup d'in tayi tare da cewa. 

"Sannu Mami Allah ya saka."

Amin tace tare da mik'ewa ta fida dan ta bata wuri, tasan in tana nan ba sha zatayi zabida sabida poolaku irin na al'ummar Dukku.

ita kam Ummi ji take tea d'in tamkar da mad'aci aka tafashi ba sugar ba.

 Haka dai ta d'an sha rabi nai, kana ta kimtsa ta fito dan Hayatuddeen ya kirata akan tazo su tafi, tare da Ya Rabi'u da Aunty Mamin suka tafi, ita Ummi da Aunty Mami suna motar ya Rabi'u shiko Hayatuddeen key d'in mota ya Rabi'u ya bashi kana suka taho shida Ishaq.


Shi kuwa Ahmad Abban Farida kenan,

yana gama kimtsawa ya kira Hayatuddeen cikin sa'a ya d'aga bayan sun gaisa ne yake cewa.

"Hayatuddeen wanne asibiti kuke ne?."

cikin sanyi yace.

"Ya Ahmad kazo ne?."

da sauri yace.

"Eh nazo kuma ban san inda kukeba."

meda hankalinshi yayi bisa tuk'in da yake kana yace.

"Kana ina yanzu inzo in d'aukeka?."


masauk'in da yake ya gaya mishi hakan yasa ya juya akalar motarshi ya nufi Royal Hotel, 

a harabar hotel d'in suka sameshi, 

ba tare da b'ata lokaci ba ya shiga kana suka juya suka tafi.


Su Ummi kuwa suna isaya Ya Rabi'u ya nemi ganin Dr Aliyu  nurses en suka ce mishi ya d'an jira nanda 20 minutes. 

dan yanzu yana woyane, 

haka yasa suka zauna a yar farfajiyar gaban office enshi, 

bayan kamar 15 minutes su Hayatuddeen ma suka iso tare da Ahmad nan aka gaggaisa, kana suka zauna zaman jiran lokacin. 


Shi kuwa Dr Aliyu da Dr Adnan yake waya inda suka tattauna matsakar.


Bayan ya gamane ya kira nurses guda biyu.

bayan sun shigone ya d'an kallesu tare da kallon ta gefen damanshi yace.

"Amina kin shirya mana komai ko?."

cikin girmamawa da nitsuwa wacce a k'ira da Amina tace.

"Yes sir an gama komai ku ake jira."

sai ya kuma juya ya kalli ta gefen hagunshi tare da cewa. 

"Rebeka jeki kira min doctor Ayman."

"OK sir." tace tare da juyawa, wani office nan kusa da nashi ta nufa bayan an bata damar shiga, ta tsaya gaban Dr Ayman tare da cewa.

"Good morning sir."

ba tare daya kalleta ba yace. 

"Morning."

gyara nitsuwarta tayi tare da cewa. 

"Sir,  Dr Aliyu na kiranka ."

kanshi ya d'an d'ago tare da kallonta kana yace.

"OK ."

tana jin haka ta juya ta tafi, shi kuwa Dr Ayman ya fara tattara takardun gabanshi kana ya mik'e yabi bayanta.


 Yana shiga ya samu Dr Aliyu tare da Dr Batul, sai nurse guda biyun, 

bayan sun d'an tattauna ne, 

suka fito cikin shirinsu na aiki.

Cikin mamaki Hayatuddeen ya zubawa Dr Aliyu ido wanda yake cikin welchair bisa dukkam alamu bashi iya mik'ewa cikin sauri yace. 

"Ya Ishaq shima wannan gurgun likitane?."

A hankali Ya Rabi'u yace.

"Babba ma kuwa."

ganin sun isone yasa suka d'an matsosu kana suka gaisa ,

cikin kula Dr Aliyu ya kalli Ummi dake rik'e da carbi cikin fullanci yace.

"Ummi kiyi mana addu'ar samun nasara yanzu zamu shiga aiki."

ajiyan zuciya tayi tare da cewa.

"Allah ya baku sa'an aiki yasa ku fara lfy ku gama lfy, Allah ya bashi lfy dama dukkan Al'ummar annabi."

Amin Amin suka amsa baki d'aya, 

yayinda Dr Ayman ya kalli Amina tare da cewa.

"Jeki shirya shi kafin mu shigo."

da sauri tace to kana ta nufi room d'in da aka kontar da Saifuddeen. 


Suma har sun juya zasu bi bayanta Ummi ta d'anyi gyaran murya sabida muryarta data disashe sabida yawan kuka a hankali tace.

"Doctor Saifuddeen Nakasasshene, baya ji baya mgna, bazai iya ce muku ga abinda ke damunshi sabida shi kurmane."

sai kuma tayi shiru hawaye na zubomata, 

Ishaq kuwa cikin karsashi ya amshi mgnar da cewa, 

"Ummi kin mance nakasarshi ba kasawa bace,

Allah da yayishi a nakasashe ya kuma bashi basira da hikimar da mai ido baida shi."

sai ya kuma juyawa ya kalli Doctors d'in da suka zuba mishi ido, especially Dr Aliyu da dama burinshi kenan kada nakasa ta zama kasawa ga masu ita. 

Shi kuwa Ishaq gyara tsayuwarshi yayi tare da yin taku biyu zuwa uku tamkar ba makaho ba domin babu sanda a hannunshi bare d'an jagora, yana tafiya kamar ko wanne mai ji da gani cikin kula yace.

"Kuna ji ko Doctor's Saifuddeen kurmane, amman yanada hikimar da yake gane duk abinda mutane ke cewa matuk'ar yana ganin yadda bakin mutun ke motsawa, kana shi mai tarin ilimine fasihine ta yadda zakayi mgna dashi kamar kowa sai dai shi a rubuce zai baka amsar da duk kake buk'ata a gareshi yakan iya rubutama a phone ko laptop ko a fefa."

cikin Jin dadi Dr Aliyu yace. 

"Masha Allah. Alhamdulillahi komai yayi tsanani iya tare da sauk'i, 

yanzu bari muje muyi abinda ya dace."

fatan nasara sukayi musu kana, suka koma suka zauna a kujerun dake jere can gefe, 

sannan su kuma suka shige cikin d'akin. 



Tuni kafinma su shiga sun samu Nurse d'innan Amina ta gama kimtsa komai ta matso da dukkan abin buk'atarsu na yin aikin. 

Yayinda shi kuwa Saifuddeen yake konce rigingine yayi lib bisa gadon ida nunshi na lumshe dan sam baya jin dukkan motsin da takeyi kana zuciyarshi da ranshi na gaya mishi wani yanayi da yakeji a jikinshi, domin yafi sau biyar yana yunk'urin zai tashi zaune amman sai yaji jikinshi na b'ari kana sai yaji bayanshi tamkar ba nashi ba, yana jin jijiyoyinshi a sake, haka yasa ya koma yayi lub yana nazari nan take yake tuno abinda ya faru dashi kana ya gane ya samu wata matsalar. 

Ita kuwa  Amina, 

gaban gadon ta matso dan kimtsashi,

yayinda dai-dai lokacin su Dr Ayman Dr batulu da Dr Aliyu suka shigo, 

gab da gadon Dr Ayman ya turo welchair d'in dr Aliyu, kana ya d'an sunkuyo ya danna wasu abu guda biyu sai ga keken ya d'an baje kana ya mik'e yayi sama yadda har ya d'an d'ara gadon da Saifuddeen yake konce a kai, 

ta yadda tsowonshi ya kamo nasu Dr Ayman hakan yayi dai-dai yadda zai iya yin aikin tamkar ko wanne mai lfy. 

sai kuma Dr Batula data kasance abokiyar aikinsu kuma babbar macece dan zata haifi Amina da Rabeka Kana zata girmi Dr Ayman sosai shiko Dr Aliyu su iya zama sa'anni, 

ba mgna a tsakanin su sai nuniya kowa na shirya kanshi, ita Dr Batula taku tayi zuwa k'arshen gadon inda nan kan Saifuddeen  yake, kana shi kuwa Dr Ayman yana gefen hagu yayinda Amina ke kusa dashi, shi kuwa Dr Aliyu  yana gefen daman shi yayinda Rabeka ke gefenshi da wasu tarkace irin nasu na doctors bisa wani d'an abu mai kama da tire bayan ta ajiye kusa da gadon sannan ta juya ta fita ta bar d'akin. 

cikin nutsuwa Dr Aliyu yayiwa Amina nuni data d'an janye mayafin dake jikin Saifuddeen,

kai ta d'an juya ta d'an zuba mishi idanu tana kallon kyau da cikar haibar da ubangiji yayiwa wanan bawa nashi, haka nan taji tausayin shi na ratsata domin tasan matsalar  da ya samu a wannan yar jinyar, 

shi kuwa Saifuddeen cikin fidda numfashi ya bud'e ida nunshi dan jikinshi ya bashi ana kallonshi, a hankali ya bud'e idanunshi, kan fuskarta ya sauk'e idanunshi, 

da sauri tayi k'asa da kanta dan wani irin mashahurin kyau da korjini da ya mata fararen idanunshi da suka d'anyi lulu-lulu alamun sun dad'e a rufe suka k'ara k'awata kyawunshi.

A hankali ta kuma d'ago kanta ta d'an kalleshi cikin sanyin murya tace.

"Sannu ya jiki?."

sabida ita bata san kurma bane don kafin a gayawa su Dr Aliyu shi kurmane ta shigo ciki ta barsu a wojen. 

Shi kuwa Saifuddeen idanunshi ya d'an jujjuya kana ya lumshe tare da  gyad'a kanshi alamar yauwa, 

sosai hakan da yayi ya gamsar da ita a fahimtarta amsa ya bata da body language wanda normal ne sometimes akan samu mutane da wannan d'abi'ar. 

shi kuwa sai ya kuma bud'e idanunshi tare da kallon Dr Aliyu wanda yaketa mishi murmushi mai cike da tausayawa. 

Dr Batulu ce ta d'an kalli Amina tare da cewa.

"Gyarashi lokaci na tafiya."

kai Amina ta gyad'a tare dasa hannunta a hankali ta janye mayafin, ya rage doguwar rigar da anka zura mishi, 

wacce takeda mab'allan

 daga samanta har zuwa k'asanta, 

cikin sabo da k'warewa da sanin makaman aikinta ta fara b'alle boturan daga wuyanshi har zuwa k'irjinshi, 

tanayi tana bud'a rigar yayinda tuni Dr Batulu ta fara nata aikin na duba raunu kan dake kan yalwataccen k'irjinshi,

wanda yake faffad'a fari k'al sai tattausan suma bak'i mai sulbi da Shek'i dake konce lib-lib, 

batabi ta kan sumarba kasancewar raunu kan a gefe da gefe suke, 

Dr Aliyu kuwa hang gulp yake sawa, 

dan fara nashi aikin, 

yayinda tuni shi kuwa Dr Ayman yake had'a wata na'ura  mai k'ok'olwa.


Ita kuwa Amina a hankali take balla boturan har ta iso d'ai-dai kan mararahi, 

ba tare da damuwa ba ta b'alla botur d'in,

ido ta rumtse da k'arfi kana sabida ganin joystick inshi konce samar maranshi kasan cewar yayi rigingine ne shi yasa ta koma saman maranshi, 

wucewa tayi botur na gaba domin b'allesu gaba d'aya, 

wanda tuni jikinta karkarwa yakeyi domin bata tab'a ganin sururar namiji ziraran miraran hakaba gashi kuwa tayi katari da ingarman na miji,

bayan ta gama bud'a rigar ne, Dr Batulu ta kalleta tare da cewa. 

"Amina duba d'an buguwan dake kan mararshi nan ya yanayinshi."

kai ta gyada tare da dawo da hankalin ta kan mararshi, 

ido ta kuma rumtsewa jin zuciyarta na neman faso k'irjinta ta fito woje.

jin muryar Dr Ayman na ce mata.

"Duba mana in da matsala a a dubashi tun wuri."

kai ta rusunar kana ta dawo da idonta kan joystick nashi dake konce kan wurin buguwar da yake jazir alum fatar wurin ya kurje har ya mele. 

cikin tsuma tasa hannunta ta kamo joystick d'in nashi dan gyara zamanta don ta samu damar duba ciwon. 

shi kuwa Saifuddeen idanunshi ya rumtse da tsananin k'arfi dan wata iriyar zabura da harbawa da yaji gabanshi yayi a take mood nashi ya canza a fili yake ganin hoton fuskar Zaleeha, a take yaji tsikar jikinshi na tashi tuno, lokacin data koma bayanshi ta ruggumeshi tana kwakumeshi tare da lek'o fuskarshi tana ce mishi. 

"Kazo mu gudu, karsu ji maka ciwo, please kazo mu gudu zasu cutar da kai please mu gudu karsu kasheka dan Allah mugudu karsu cutar mana da kai."

 yam ya kumajin tsikar jikinshi  ya mik'e, 

numfashi  ya shak'a dan tuno wani irin assanyan k'amshi da jikinta yake, 

taushin tafin hannunta ya tuno lokacin data rik'e damtsenshi, 

a take lafiyarshi ta harba joystick inshi ta mik'e ta tsaya k'am tamkar zataci babu, bugu da k'ari ga fitsarin daya cika mishi mara, 

shiyasa taketa harbawa tana k'ara mik'ewa da cika.

Amina kuwa wata iriyar razana da tsoro da fargaba da kunya mai tarin tsananine ya farufeta.

Cikin azabar tsoro ta janye hannunta jiki na tsuma tamkar mazari murya a hargize tace.

"Innalillahi wa Inna'ilaihi rajiun, 

wayyo Allah na Wayyo Mommy."

ta k'arishe mgnar tana komawa bayan Dr Batulu, 

ihun da tayi da janye hannunta yasa Dr Aliyu da Dr Ayman suka juyo gareta ganin meya razanata, 

gaba d'aya jikinta tsuma da karkarwa yakeyi dan abun kamar a mafarki take ganinshi. 

Shi kuwa Saifuddeen janye hannunta da tayi daga jikinshi ne ya sashi bud'e idanun, 

sai ya kuma yi sauri yasa hannunshi na hagu ya janyo mayafin ya rufe  sirrin jikinshi sabida yadda yaga joystick nashi a tsaye gam, kana sai harbawa takeyi uwa uba yadda Dr Aliyu da Dr Ayman suka wani murmushin da yafi kama da na tsantsar farin ciki. 

Dr Batulu kuwa gaba d'aya yanayin Amina ya bata tsoro dan a fili ake gane firgitan da tayi, shiyasa ita bata ga sirrin jikin Saifuddeen ba dan hankalin na kan Amina dake bayanta,

janye kanta tayi daga rik'on da Amina tai mata, 

hakan yasa ita kuwa Amina ta k'ara buya a bayanta,

sabi still har yanzu ana iya ganin yadda lafiyarshi ke harbawa a ta cikin mayafin.

ganin fa da gske a firgice take yasa Dr Aliyu ce. 

"Amina fita."

kamar ace da ita ga qofar tsira a guje ta fice daga d'akin.

shi kuwa Saifuddeen gaba d'aya kunya ta mishi suture ji yake tamkar ya nitse cikin k'asa domin shi mutun ne mai tsananin Al'kunya dakawaici,

jin an kama hannunshi yasa shi bud'e ido,

 idon ya zubawa bakin Dr Aliyu da ke cewa. 

"Saifuddeen ka godewa Allah domin wannan alamace data nuna mana nakasarka bata shafi mazakuntanka ba, wannan mu a wurinmu wani sauk'i ne da alamun nasara da roggomi a cikin nakasarka, wannan alamace dake nuni da cewa har yanzu kana nan a cikekken na miji mai lfy wanda zai iya aure kana kuma zai iya haihuwa in Allah nufa."

sai ya kuma meda dubanshi ga Dr Ayman daya janye mayafin tare da cewa.

"Wannan yuna mana nakasarka ba mai zurfi bace, because zaka iya zama kana zaka iya tashi daga konce ka zauna da kanka ba tare da wani ya tallafa maka ba sannan zaka iya rayuwa ba tare da an sa maka ledar fitsari ba, hakan ya nuna mafitsararka lfya lau take haka kuma joystick naka ras yake zaka iya aure ka kuma sadu da mace ka kuma yi mata ciki matuk'ar tana da lfy, to amman fa sai in har ita matar ce zat.....!




        *GARKUWAR FULANI*

8/18/20, 7:52 PM - Ummi Tandama: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


              *NAKASA BA KASAWA BACE*



                          *PAGE 16*



                                  NA

               *AYSHA ALIYU GARKUWA*


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇



_Ga masu sha'awar biyan kuɗin karanta littafin ,turo katin Mtn na ɗari uku, kacal ta wannan number 09097853276 ko kuma ki turi ɗari ukun ta asusuna 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa kana ka/ki turo shaidai biyan naki_


          


         ~Free page~



"Zata ai watar da...!".

 Shiru yayi ba tare daya k'arishe mgnar tashi ba sabida, jin Dr Aliyu na cewa.

"Ya isa! in yasan hakan zai sa mishi fargaba."

sai ya kumo judo ya fuskanci Saifuddeen dan dama da zaiwa Dr Ayman mgna kauda kanshi yayi tunda yasan in Saifuddeen d'in yaga motsin lab'b'anshi zai gane me yake fad'in. 

shi kuwa Saifuddeen kai ya jujjuya tare da d'ago hannunshi a hankali ya d'aura kan mararshi, 

sai ya kuma janye hannun tare da kallon fuskar Dr Aliyu kana ya nuna mishi kan mararshi zuwa kan joystick inshi, 

sannan ya had'e girarshi wuri d'aya tare da tsuke jajayen lips enshi, kana ya fara mutsu-mutsu alamun Yana son tashi zaune, 

cikin saurin fahimta Dr Aliyu yace. 

"Mararka ta cika ne?." kai ya gyad'a mishi alamar eh, 

ganin haka Dr Ayman yayi saurin jawo wani d'an abu ya mik'a Dr Aliyu, amsa yayi tare da kamo joystick en nashi ya mana bakin robar. 

Ido ya rumtse tare da girgiza musu kai kana ya had'a yatsunshi biyu alamun a cire mishi, fahimtar haka yasa Dr Aliyu janye robar kana ya bud'a bakinta sannan ya zura kan kaciyarshi cikin bakin robar daya bud'a sannan ya kalleshi tare da cewa.

"Kayi."

ido ya lumshe cikin tarin kunya duk da yasan Dr Aliyu ya kai sa'an mahaifinshi hakama Dr Ayman zai girmeshi matuk'a kuma duk mazane yan uwanshi, sai kuma Dr Batulu da yasan tabbas zata haifi kamarshi, sannan kuma tama juya baya bata ganinshi,

amman duk da haka yana mai matuk'ar jin kunya duk da ya gane halin da ya ke ciki na kasantuwar wata sabuwar nakasa wani irin suya da maƙaƙi da ɗaci zuciyarshi ke mushi to amman ya yarda da wannan sabuwar ƙaddara tasa yasan tun ran gini tun ran zane. 

Su kuwa likitovin hakan ya sasu karsashi domin alamace ta nuna cutarsa batayi tsauri ba, alamace ta nuna bai samu damage sosai a jikin ba.


Bayan ya gama yin fitsarin Dr Ayman ya gyara mishi jikinshi ne, 

sannan suka fara shirin yi mishi aikin taimakon gaggawa, kafin asan matakin da za'a d'auka, yayinda Dr Aliyu ya fara mishi nasiha cikin taushin lafazi yace.

"Saifuddeen kayi addu'a da fatan Allah ya bamu sa'an aiki, kana kasa a ranka nakasa ba kasawa bace,  ka jajircewa zuciyarka, kasa a ranka wannan jarrabawace da ubangiji kan iya jarabtan dukkan bawanshi, 

kaga misali a kaina gani bana iya mik'ewa tsaye kuma rana tsaka larurar ta sameni sakamakon had'arin mota, 

wanda lokacin ina ganiyar k'uruciya ta, na gama karatu na kenan na fara aiki da mako biyu nayi hatsarin, wanda saida akayi tsawon shekaru biyu ana jinyata kafin na fara tashi zaune da kaina, kumani a lokacinma nakasata ta shafi lafiyata a matsayina na d'a namiji, koda na yarda da k'addara, nasan cewa jarrabawace bayan shekara 8 da faruwar abun lfyar mazan takana ya fara dawowa cikin ikon Allah kafin na cika 10 years da yin had'ari har nayi aure

sai da muka shekara 7 da ita kafin Allah ya bamu ciki a lokacin har na cire tsamnani, 

Allah da ikonshi ciki nada wata 5 ya bare.

Nayi matuk'ar shiga damuwa a lokacin ashe abinda bamu saniba, cikin tagwaye ne d'ayan nan bai bareba, 

bayan wata hud'u aka haifa min d'iya mace, daga kanta kuma Allah bai bamu waniba, 

to nima kenan da nakasata tafi taka in sha Allah kai muna sa ran zaka samu lfy kuma Alhamdulillahi kaga kai matsalar bata shafi mazantakan kaba.

kasa a ranka kana nan da lfyarka."

kai ya rausayar tare da lumshe ido kana ya gyad'a kanshi kai alamar. 

"To, ngd."

daga nan suka fara aikinsu ba kama hannun yaro, babu mgna sai nuneneniya, tuk'uru suka duk'ufa kanshi.


A can waje kuwa Ummi aje carbin hannunta tayi kana ta jawo wayarta ta fara karatun qura'an tanayi tana nemawa gudan jinin ta lfy a wurin mai rayawa mai kashewa mai badawa mai hanawa, Allahu wahidun k'ahharar.


Ya Rabi'u kuwa ya d'auki Aunty Mami sun tafi ya maidata gida, dan tayiwa bak'in nasu abinci, kana shi kuwa ya wuce ma'aikatansu.


Ishaq kuwa da Ahmad suna nan zaune suna dakon fitowan doctors dan suji menene matsalar Saifuddeen d'in.

 Kana Hayatunddeen kuwa ya tafi Airport dan tarbo Dr Adnan.


Bayan kamar awa biyu suka fito a jere, Dr Ayman yana turawa weelchair d'in da Dr Aliyu ke zaune, yayinda, Dr Batulu ke biye dasu a baya.

Suna fitowa Dr Adnan da suka ise bada jimawa ba, ya mik'e da sauri, ya nufi inda suke hakama Ahmad da Ishaq wanda kunnuwanshi ke mishi jagora duk inda sautin muryarsu da sautin takun Ahmad yake bi, kai baka tab'a cewa makaho bane, domin mutunne mai cikar zarrah da zati kekyawane mai tarin tsabta da yawa sukance suna ɗan kama da Saifuddeen.

cikin girmamawa Dr Adnan ya d'an rusuno ya bawa Dr Aliyu hannu tare da cewa. 

"Barka da hantsi sir."

cikin kula da dottaku Dr Aliyu yayi murmushi irin nasu na manyan doctors kana yace.

"Barka dai Adnan ashe har ka iso, ya hanya."

"Alhamdulillahi ya aiki?." Adnan yace yana bin bayansu shida Ishaq da Ahmad suka shiga tamfatsetsen office d'in Dr Aliyun. 


Ummi kuwa addu'a tayi kana ta kife wayar bisa cinyarta, 

ido ta zuwaba Hayatuddeen dake tsaye gaban Dr Batulu yana neman a barshi ya shiga yaga d'an uwan nashi. 

cikin kula tace.

"Kayi hak'uri bayan mun gama aikin bashi taimakon gaggawa an mishi allurar bacci so ana buk'atar ya huta."

sai ta kuma matso gaban Ummi da idanunta suka cika da hawaye, 

ganin tazo gabanta Ummi tace. 

"Dan Allah Dr ki gaya min halin da yake ciki? koda baya rayene kada ki boye min, tunda abinnnan ya farufa bangashi ba sai dai in haggoshi daga nesa, ke uwace kinsan abinda uwa kanji in makamancin wannan ya faru da d'anta please me ya sameshi?."

a hankali Dr Batulu ta zauna gefenta kana ta dafa kafad'arta tare da cewa.

"Abinda ma muke zaton zaiyi tsanani sai muka sameshi da sauk'i, 

Saifuddeen bai mutuba yana raye kuma insha Allah da yamma ni da kaina zan shigar dake inda yake, kafin nan ya farka zaki ganshi ya ganki kuyi mgna dashi, yanzu dai da ku koma gida domin nan akwai masu kula dashi. 

wadanda Dr Aliyu ya tanatar su zasu mishi komai, 

sannan batun abinci ma karku damu akwai d'iyar Dr d'in duk abinda za'a bashi damar ci ita zata shirya mishi komai.

 Yanzu kuje gida da yamma Ku dawo,zaku ganshi kuma Dr Aliyu zai gaya muku duk abinda ke damushi da matakin daya kamata ku dauka dama yadda zaku kula dashi."

sosai Ummi ta gamsu da bayananta kana taji sanyi a ranta, haka yasa tace. 

"To ba matsala ngd matuk'a Dr in sha zanyita addu'a zamu koma biyar na yamma zamu juyo."

cikin fara samun nitsuwa Hayatuddeen  yace, 

"Dr zai gane mu ko? numfashi sa ya dai ta ko?."

kai ta gyad'a mishi tare da cewa. 

"Sosai ma har magna fa yanayi mana da body language alamun yana gane duk abinda muke cewa."

a tare sukace Alhamdulillahi. 

sannan Dr Batulu ta bawa Ummi number ta kan in sun dawo da yamma su nemata.

 

Su Abban Farida kuwa, da Dr Adnan da Ishaq bayasu shiga sun so Dr Aliyu yayi musu bayanin matsalar Saifuddeen, so amman sai ya basu hak'uri sabida ya gaji yana buk'atan hutu ya dai ce suje da yamma su dawo dukansu yana son ganinsu dan zai musu cikekken bayanin matsalar Saifuddeen d'in da basu shawara da da gaya musu dabarun kula dashi.

dole suka hak'ura kan saida yamman in sun dawo.



Kai tsaye gidan Ya Rabi'u suka wuce dan Ishaq ya k'i su Ahmad da Adnan suje su kama hotel. 

A motar da Ya Rabi'u ya bari a hannun Hayatuddeen suka tafi,

 amman Ahmad ya karb'i tukin a cewarshi Hayatuddeen d'an koyone bazai yarda ya jasuba, 

Ummi na gaba kusa da Ahmad kana Ishaq da Adnan  da Hauatudeen suna baya a haka suka tafi. 


Aunty Mami kuwa tuni ta shirya musu abinci tasa an gyara BQ ensu.



                  *A garin Gombawa d'iban fari*



Yau tunda sanyin safiya Zaleeha ta shirya domin zata je kaltingo don zantawa da nakasassun wannan yankin.

 

Amman har zuwa ƙarfe taƙwas na safiyar ta gaza yin komai, ji takeyi tamkar tayi ta kurma ihu ta faɗi abinda folisawannan suka haneta faɗi tare dayi mata barazana da ranshi,

kukan da takeyi ya sanya ida nunta kumbura sukayi jazir ga wani fitinennen ciwon kai, ya zatayi a duniya ko wacw ƴa in tanada matsala uwarta take fara tinkara ,amman sam Mama itama bayan folisawan tabi.

tafin hannunta tasa ta share hawayenta a karo na barkatai, a hankali ta miƙe kana ta zari car key ɗinta, a falo ta samu Mama a hankali ta gaiseda da muryarta dake disashe, cikin haɗe fuska tace.

"Wato dai bazaki bar koke-koken nan ba ko, so kike sai an gane wani abu ya faru da ke ko?."

Kai ta jinjina cikin sanyi tace.

"Mama ai wani abu kam yama faru, sanadi nane fa akayi mishi komai, ban saniba yana raye ko ya mutu wani hali yake? tun randa abin ya faru da dare washegari naje asibitoci sunfi bakwai babushi ba dalilinshi, ni badan raina da sukayi min barazana da shiba, a a shida yake hannunsu nakeji kar su ƙara cutarmin dashi." ta ƙarishe maganar wasu zafafan hawaye na kwaranyo mata,

ita kuwa Mama kasake tayi tare da cewa.

"eyeh sannu uwarshi harda su wani kada su ƙara cutar miki dashi kamar kece  uwarsa ko ƙanwarsa ko matarsa lallai Zaleeha kifa kiyayeni tam!."

tana faɗin haka tayi cikin kitchen, ita kuwa Zaleeha rumtse ido tayi hawayen dake ciki suka silalo kana ta fita ta nufi falon Baba Malam ,bayan sun gaisane ta ɗan gyara zama ciin disashewar murya tace.

"Baba Malam bari in fita zanje gidan Adda Maryam daga nan zanje asibiti dubo wani mara lfy, Baba Malam a sashi a addu'a Allah ya bashi lfy ya kareshi da sharrin masu sharri."

murmushi dottijon yayi tare da cewa,

"To Mamana in sha Allah zan sashi a addu'a Allah ya bashi lfy, kuma in kinje asibitin bashi kaɗai zaki duba ki ɗan zazzagaya ki tuba wasuma dan ki samu ladan dake cikin hakan." kai ta gyaɗa kana tamiƙe tare da sallamanshi ta

tafi.


Tana isa gidan Maryam kaitsaye bedrrom ɗinta ta wuce,

Maryam dake zaune gaban mirror tana kwaliyya ganin Zaleehan ne ya sata juyowa da sauri sai kuma tayi shiru ganin ta zauna ta kife kanta bisa cinya tana kuka mai sanyin sauti,

da sauri ta dawo kusa da ita cikin kaɗuwa tace.

"Meya faru ? Meya saki kuka gaya min dan Allah hankalina ya tashi ,Baba malam ne ba lfy ko ya Ahmad."

kanta  ta ɗan nago ta kalli yayar tata cikin kuka tace.

"Ya Aminu yana nanne?."

kai ta jujjuya mata tare da cewa.

"A a ya fita ya kai su Abdul makaranta, amman zai dawo yanzu."

jin haka ta miƙe ta koma bakin ƙofa, rufe ƙofar tayi tare da gyara labulen sannan ta dawo ta zauna cikin kuka ta bawa Maryam labarin tun daga shagala da kallon Saifuddeen da tayi har ta kai ga buge motar Dalla da binsu da sukayi da dukansu da Saiddeen yayi da kuma dukan da suma sukayi mishi.

Gaba ɗaya jikin Maryam rawa da tsuma yakeyi tuni itama hawayen take zubdawa murya na rawa tace.

"Shike nan mun shiga uku Zaleeha Dalla kuma, shike nan sun kashe yaron nan, to ke me kikayi a kai?."

wasu sabbin hawaye ne suka kwaranyo mata kana taci gaba cewa.

"Daga wurin ban dawo gidaba  police station name wuce,  naje na shigar da  ƙara na faɗa musu komai, amman da yake basu da imani ƙasar nan ba'a bin gsky sai suka zagayeni a wurin babban cikin su yace min wai,

na kiyayi kai na na haɗiye wannan maganar kada na kuskura na bari wani yaji koda da wasane,

yace min wai yanzu dai yana ƙarƙashin kulawarsu in banbi umarninsu wallahi zasu kasheshi, kuma nima zasu bawa Dalla adireshina, kuma wai duk wanda yayi yunƙurin ɗaga zancen zasu kasheshi."

kuka sosai taci gaba dayi tare da cewa.

"Kuma sai da suka haɗoni da police ɗinsu guda ɗaya ya kawoni har ƙofar gidanmu, yace min.

Duk abinda zanyi suna bibiyata kada na yarda na kuskura na bar koda alama ɗaya da a gida za'a gane akwai wata matsalar har a kai ga tambayata, muddin nayi yunƙurin zuwa wani police station zasu  sanarwa Dalla komai ya tura yaranshi su kasheshi." ɗan zagaitawa tayi tare da cigaba da cewa.

"Wallahi ni ba don raina ba sai dan tseratar da ranshi yasa naketa boye abun a cikin raina har kwana biyu, ina tsiron kada su kasheshi, gashi naje asibitoci da dama na bincika babushi babu dalilinshi, na koma bakin sitadiyon ɗin ya kai sau biyar to wa zan tambaya ,jiya wuni nayi ina yawo, kuma ko yau da safe sun kirani sun gargaɗeni wai bani yar jaridaba in na kuskura maganar nan ta fito to wallahi kasheshk zasuyima suga ta zancen sunce min motata ince ƴan kalarene suka fasamin amman kada in kira sunan Dalla.

Adda Maryam ya zanyi ina zan shiga in ganoshi ina zan saka raina da nasa mu tsira daga sharrin Dalla da yan sandda ya zanyi in bashi kariya koda rabin yadda ya bani kariya ne! bani da konciyar hankali da nitsuwa bana iya bacci bana iya cin abinci, duk da sun gargaɗeni kada fa na sake damuta ta baiyana."

wannan al'amarifa ya firgita tunanin Maryam ya girgizata itama tuni hawayen takeyi sabida rauninta yama fi na Zaleeha cikin tausayawa tace.

"Kin gayawa Baba Malam ne?."

kai ta jijjiga tare da cewa.

"A a ban gaya mishiba kin san Baba Malam muddin na gaya mishi zai tada zancen zai sa Ya Aminu cikin mgnar  su kuma zasu iya kasheshi, ni kuma bana son su cutar dashi ina son rayuwarsa fiye da tawa sabida shi Garkuwane magarcine ya ahlinshi zasuji tunda ni da bai sani bama ya zamemin Garkuwa inaga ahlinshi." sai hawaye shar-shar na bin fuskarta a hankali taci gaba da mgna wai dan kar Ya Aminu ya dawo ya jisu.

"Amman dai na gayawa Baba Malam ɗin cewa akwai wani mara lfiya yana buƙatar addu'a,

yace kuma in sha Allah zai sashi a addu'a, Mama kuma dana gaya mata wai ita ni take jiyewa cewa tayi muddin na gayawa wani bata yafe ba,

ni kuma in ban gaya mikibs na damuwar zata iya fasa min zuciya."

cikin sanyi Maryam tace.

"Kinyi dai-dai karki gayawa kowa,

sabida bisa dukkan alamu yana asubiti kuma duk inda yake zasu sani, kinga muddin kika ɗaga mganar suna iya kasheshin,

gatan da zamuyi mishi itace addu'a domin annabi yace addu'a'u saiful muminin mu zama garkuwarshi da addu'o'i in sha Allah bazai basu damar cutar dashi ba, ki dena kuka ki yawaita mishi addu'a kuma kici gaba da zuwa asibitoci, ki kuma koma police station ɗin ki ce su gaya miki asubitin da suka kaishi."

sosai taji daɗin shawarwarin ƴar uwar tata haka anan tayi wonka ta shirya, ta fita daga nan fa tayi ta bin asibitoci duk da anata kiranta wurin aiki,

sai da tayi sallan azahar kafin ta tafi kaltingo domin yin hira da Nakasassun wannan yankin.


Tun k'arfe biyu na rana take cikin garin kaltingo, sai k'arfe hud'u na yamma ta gama tattara rahotanninta, 

kana ta kamo hanyar gombe, tana gab da shiga cikin garin taji wayarta na suwa,

ido ta d'an lumshe kana ta bud'e su tare da meda hankalinta kan draving d'in da takeyi, 

wanda sanyi A,C da k'amshi ya cika motar kana sautim wak'arnan ta. Soyayyar dake raina bazan sauya ra'ayiba, wacce akewa taken

 *Da ƙauna ta biki jiki an komawa wada ƙanwa*

hannu tasa ta k'ara volume d'in gaba d'aya Kasan cewar a gidan radio ensu na  vision FM Gombe aka saki wak'ar wanda nanne ma'aikatan da take aiki inda take gabatar da program d'in ta mai taken *Mushsƙata da kuma Babu nakasasshe sai rago*  wanda take hira da nakassu dan jin yanayin da suke rayuwa.

 Kamar yadda yanzuma aikin ne ya kaita kaltingo wata k'aramar hukumar jihar Gomben.

kai take d'an rausayawa tana bin sautin wak'ar, 

tamkar itace ta raira wak'ar, still kuma idanunta zubda zazzafan hawayen da duk sanda ta tuno Saifuddeen sai ta zubdasu, wanda kusan hakan yabi jikinta a cikin kwana biyun nan tayi kukan da itama da kanta batams san adadinshi ba, 

taje sitadiyon yafi k'afa takwas hakama taje asibitoci da dama dan ko zata samu lbrinshi, 

ganin ba lbri yasa yau da safe taje police station d'in nan amman sai suka nuna basuma san da wannan zancen da take musuba, 

kuma abun mmki da tsoro bata ga police officers d'in da ta samu a wannan ranarba ko guda ɗaya, shiyasa gaba ɗaya ta rasa tudun dafawa.


Gudu take tsulawa kamar mai tashi sama, a hankali take bin sautin wak'ar still kuma hawaye na kwaranya a fuskarta har yana d'iga bisa tudun brest d'inta, 

fuskarta d'auke da murmushi daya tunzura hawayenta tace.

"Ina kake wanne hali kake ciki me sunanka?."

sai kuma tace.

"Allah ya isanmin bazan yafe musuba, Allah zai saka maka zai taimaka maka fiye da yadda ka taimaka min."

 wayarta keta ringing tanaji tana gani bata kula kiranba, 

sai yanzu da taji an cire waqar daga can vision d'in ta d'an ja tsaki tare da d'ago woyarta ganin Abdussalam ke kiranta d'an minister, wanda yaketa nacin binta tun last week da suka had'u , Duwa plaza 

taje sayan burger,  

tsaki ta kuma ja tare da cewa. 

"Wannan wanne irin maye ne da baida zuciya, ko uwar me yakeso in mishi da bak'ar fuskarshi kamar an k'ona taya."

aje woyar tayi dai dai lokacin data isa, bakin gate din (Jonopwd)  d'in. 

tafiyar mai d'an tsawoce kafin ta isa gab da ofishin nasu, dan sai ka wuce farfajiyar court d'in, dake wurin, 

ido ta d'an lumshe kana tace kai.

 "Ya Habu ka cika naci dan kawai ka bani motarka kaketa nacin kirana kamar bazan dawo ba."

haka nan har yanzu hawayenta sunƙi tsayuwa

sai kuma ta amsa kiran tare da yin kasa da murya tace. "Ya Habu sai yanzu na dawo, kuma yanzu ma haka ina, jonapwd ne." 

sai ta kuma bud'e marfin motar kana ta zuro kyawawan k'afafunta woje, 

sannan ta kuma yi muryar shogoban da yanzu mai tushe takeyi dan cikin kwana biyun nan ta zama uwa wata lalatacciyar jiniya abi kaɗan tasa kukan da taketa son ɓoye,

to yanzunma hawayen takeyi tare da cewa. 

"Kuma sai naje Vision dan gabatar da program na."

A can gefen Ahmad ne ya amshi wayar Habu kana ya kara a kunne tare da gyara zamanshi kana ya rusunar da kai ya kalli mahaifin nasu kana yace.

"Baba malam ke nemanki, yace maza in kiraki ki taho gida."

fitowa tayi daga cikin motar, idanu ta lumshe still hawaye na tsiyaya jin wani sassanyan iska dake ratsa dukkan abin halitta dake wurin, a hankali ta bud'e idanun nata kana ta zuwaba jerin bishiyoyi da tsirran da sukayiwa harabar wurin k'awanya, 

a hankali ta fara taku ih zuwa cikin asalin harabar ofishin, 

kana cikin fargaba tace. 

"Dan Allah Ya Ahmad kace wayata bata shiga, nasan abinda Baba malam ke nemana dashi."

cikin nitsuwa da kamala Ahmad yace. 

"Yana ma jinki dan ina gabanshi."

ido ta zazzaro tare da dafe k'irjinta cikin kad'uwa tace. 

"Gani nan zuwa."

tana fad'in haka ta katse kiran kana ta k'arisa bakin k'ofar ta shiga danna door bell.

minti d'aya tsakani wani matashi yazo ya bud'e mata k'ofar, 

kana ta kusa kai ta shiga wani corridor tafiya kad'an ta bulla cikin wani tamfatsetsen office wanda aka k'awatashi da ababen buk'atar dan adam, 

wasu kujerenu ne masu kama da mazaunin lilo ke zagaye da wani babban table  na bak'in gilashi wanda yaketa shek'i

kana sai fankoki kusan guda biyar da sukabi layin tsawon table d'in, sai wani babbab firij dake can gefe kana, sai wani d'imemen TV sannan sai na'urar AC gudu biyu da suke fuskantar juna, 

sai kuma wasu k'ofofi d'aya k'ofar tana gab da k'ofar shigowa office d'in wanda bisa dukkan alamu bathroom ne, 

sai gefen dama da k'ofofi guda uku ke jere bisa dukkan alamu office din shugabannin k'ungiyar ce, 

kana gefen k'ofofin sai akayi wani dan steps guda biyar in ka haura wani d'an madaidaicin table ne na farin gilas mai ruwan garai-garai sai kujera d'aya rak a gaba kana sai d'aya a bayan table d'in sai tarin na'urai wanda sun kai bakwai. 

sai gefen hagu nanma haka tsarin yake sai dai shi sai ka d'an ratsa cikin wani corridor mai d'an fad'i.


Tana shiga wannan mutumin daya bude mata k'ofar yace. 

"Barka da zuwa Zalihan nakasassu."

murmushi tayi kana taja kujera ta zauna tare da cewa.

"Ya Ishaq fa baya nanne?." 

ba tare data jira amsarshi ba taci gaba da cewa.

"Ya naji ma'aikatan naku shiru yau ba mutane?."

bisa kujerar gefenta ya zauna tare da cewa.

"Ishaq yana Abuja, mutanen mu kuma duk suna fad'ar jiha sunje kai gaisuwa ga mai martaba."

mik'ewa tayi taku biyu zuwa uku ta nufi gaban firij, 

tsayawa ta yi jin abinda Sani ke fad'in.

"Ayyah kiyi hak'uri ban kawo miki abin shaba, sorry dawo ki zauna zan kawo miki."

cikin yanayin sabo dasu  tace. 

"Wai ku anya kuwa ku makafi ne? yanzu ya akayi kasan gaban firij na nufa?."

murmushi yayi tare da d'an kaikaice kunnenshi irin yadda makafi keyi kana yace.

"Motsinki da takun tafiyarki ne ya ganar dani inda kika nufa, 

ke har yau kin kasa barin mmki kan lamarinmu, abinda baku saniba ku.

 Mu nakasassun munada experience sama daku masu gadara da cikekkiyar halitta."

murmushi tayi bayan ta dawo ta zauna, 

robar faron ta bud'a bayan ta sha kana tayi hamdala dan ta ɗanji tafasar da zuciyarta keyi ya ɗan ragu aje goran tayi sannan tace. 

"Toh Ya Sani ni zan wuce tunda ciyaman bainan, 

wata k'il sai next week, zan shigo, dama zan tattauna da sune a shirin da za'a haska a tasharmu na Farin Wata, dan yace min wannan karon da kurame zan tattauna, to gashi  Malam Ishaq bai sanarmin bama a kan baya nan da ban zoba."

"To ba matsala, Allah ya kaimu lokacin, wannan karon kam hirar da kurame za'ayita?."

ya k'arishe mgnar cikin neman k'arin bayani  tare da 

mik'ewa yabi bayanta kana suka fito tare har gaban motarta, 

sannan tace mishi. 

"Eh shiyasa dole su sai a tasharmu ta TV za'ayi hira dasu. Yace min da wani babban abokinshi zamu zanta wanda shine Garkuwar asusunku, da nike ta cewa ku fasa ku bani in canza mota, kukak'i, saida kuka bari yan kalare suka fasa min glass, sannan Ya Ahmad na ya canzamin, kuma a kanku motata ke mutuwa kullum ina yawon binku da k'wak'ulo baiwarku."

dariya yayi sosai kana yace,

wannan asusun namune mu yamu."

itama murmushi tayi kana ta shiga mota sannan suka sallami Juna. 

Daga nan ya koma ciki.

 Ita kuma ta ja mota, 

kai tsaye hanyar Vision fm Gombe ta nufa, sanin ana jiranta yasa take sharara gudu kamar babu gobe kana dama d'abirta ne bawa mota wuta, 

tana isa harabar maikatar tasu tayi parking kana ta fito sauri-sauri gudu-gudu ta shiga cikin ainihin wurin kai tsaye d'akin tace murya ta nufa,

tana shiga  tazo dai-dai masauk'in bakinsu, 

taji abokin aikinta Rabeel na cewa.

"M.B. S Dukku, sai yanzu ne, ya mutanenki?."

bata kai ga amsa mishiba taji muryar d'aya daga cikin abokan aikin nata ta bayanta tana cewa.

"M.B Dukku, sai yanzu tun d'azu Abdulsalam da tawagarshi ke nan ya kasa ya tsare sai raba ido yake ta ina zaki fito bai saniba kina can cikin mutanen ki Nakasassu."

tsaki taja tare da cewa.

"Na damu dashi, in yayi ya haƙura ya bari d'an marasa zuciya kawai."

jin wani ya kuma kiranta yasa tace. 

"Kai dan Allah ku barni in huta ni dai ba dama ku barmin suna ya huta, daga mai cemin Zalee sai me cemin B M Dukku sai masu cewa M,B,S Dukku irin Rabeel har Dukkun kawaima zai kirani, 

sai yawan kiraye-kiraye kamar makaf.."

sai ta kuma yi shiru bata k'arisa ba.

su kuwa Dariya sukayi baki d'aya, kana Maigado tace. 

"Yoh meyasa kikayi shiru? ki k'arisa mana ai mutanenki ne, ga kuma Rabeel d'an had'i kina fad'i zai yad'aki a shirin *Mu daku* ya sanar musu."

ɗan wani guntun murmushi tayi tare da cewa.

"Ai duk had'inshi bazai ci nasara a kanmuba dan sun san Zaleeha tasuce."

dariya suka kumayi dan Zaleeha ta kowace ita kowa natane tanada fara'a da farfar da jama'a kana ga kaud'i da rakad'i awani sashin kuma tanada tausayi da mutunci, kana tana da white blood tanada kwarjini, da shiga rai shiyasa duk inda ta shiga sai tauraronta ya haska sai yawan tsiwa. tsoro kuma tamkar farar kura. sai dai Raveel ya kula kwana biyun nan bata cikin haiyacinta da nitsuwarta.

Zaleeha fara ce k'al irin farin fulanin Dukku.

Wanda  dukkan mazaunin gombe ko ince dukkan wanda yasan jamar Dukku yasa fulanine, kana fulanine da sukayiwa sauran tsashi na Gombawa zarrawa a fagen kyau ilimi wadata kiwo noma, 

duk wanda yasa mahaifin Zaleeha Malam Bashir Sulaiman Dukku muddin yaga Zaleeha to tabbas zai san ita d'in jininshi ce, haka yasa take tsananin kama da Ya Ahmad d'inta duk da ubane ya had'asu, 

Zaleeha kekyawace irin first  class d'innan Kana babbar yarinyace yar gidan babban mutun mai daraja, wanda k'asarmu ke al'fahari dashi

sannan taurarinta na haskawa tutarta na kad'awa kasancewarta ga ilimi ga asali ga haiba ga kyau uwa uba ga kud'i, sannan ga kwarjini bugu da k'ari yanayin aikinta yasa ta zama so popular 

ita ba doguwa bace kana ba gajeraba, irin dai tsaka-tsakin nance, 

tanada jikinta dai-dai da shekarunta yar sumul da ita, tana shek'i tamkar tarwad'a, kana tana da asalin gashi na fulanin asali, 

wanda babu surki gashinta har bisa kafad'unta bak'ine sitik kana yanada yauk'i da sulbi,

duniyar Gombawa da ma sauran inda aka santa sunanta na haskawa kasan cewarta maikaciyar gidan radio ne yasa muryarta ta sanu wa Al'ummar gari musamman matasa domin shirinta na mushaƙata yanada farin jini, kana fuskarta ta kasance sanenniya sabida aikinta daya shafi sashinsu na TV, 

Duk na miji mai rai da lfy in yaga Zaleeha sai yayi sha'awar ta zama matarshi kana in kasan gidan data fito dole kayi sha'awar had'a zuriya dasu sabida ko ba komai ana zatawa damuna sanyi, 

yayinda ita kuwa Zaleeha ta tarkace babin maza ta watsa a gefe, bana ce da ita ruwan idoba, to amman har yau mahaifinta da Ya Ahmad tare da Ya Aminu  sun gaza gane dalilin daya hanata tsaida gwaninta, duk da gashi k'anwarta mai bin k'aninta Zakariyya ma ta kai aure hakama mai bin mai binta itama ta fara girma uwa uba tayi karatunta har ta d'an kwana biyu da fara aiki. 

cikin Jerin masoyanta kuwa harda Manager d'insu duk da ya bar abin a ranshi ganin yadda wasuma ke neman shiga ta wurinshi kana ga abokin aikinta Raveel bar irinsu Abdussalam. 


Da sallama ta shiga cikin d'akin tace murya kafin a kai ga watsa shirin, 

tana shiga ta samu Manager nansu zaune bisa kujera yana aiki, 

zama tayi a kujerar gefenshi kana ta ajiye system enta sannan ta zaro woyarta, 

aikinta ta farayi bayan kamar 4 minutes ya dago ya kalleta ido ya lumshe tare da shak'an k'amshin turarenta murya can k'asa yace.

"Yau ba gaisuwa ne?."

Jawo ababen aikin tayi ganin alamun ya gama kana tace.

"Oga na gaidaka baka ji bane."

hannunshi yasa ya jawo system in nata kana yace.

"Kawo in tayaki aikin."

ba tare da ta kalleshi ba tace.

"Ngd."

shi kuwa Oga ido ya kuma lumshewa kana murya can k'asa yace. 

"Haram."

da sauri ta juyo ta kalleshi tare da cewa.

"Me d'in?."

mik'ewa yayi ya dawo gefenta kana ya fara harhad'a mata na'urorin sannan yace.

"Baliga tasa turare ta fita." shiru tayi sabida kunyar data rufeta daga nan shima bai kuma mgnaba, 

har suka gama aiki, 

sannan ya bata wani d'an k'aramin abu tare da turo mata laptop enta sannan ya kalli fuskar wayarshi yace.

"5:00 pm lokacin shirinki yayi,  jeki sashin asashin watsa labaran ki had'a kawai ki tafi gida dare ya farayi."

mik'ewa tayi tare da gyad'a mishi kai, har taje bakin k'ofa taji ya kuma cewa. 

"Ki dena sa turare in zaki taho kana da zakisa nik'ab da kin taimakawa wasu mazan daga fad'awa komar da baza'a kulasu ba."

kai ta gyad'a mishi kana ta fita, 

kai tsaye sashin watsa shirye-shiryen su ta nufa tana shiga ta had'a program nata kana ta fito, bata koma cikiba kai tsaye ta nufi parking lot nasu ta shiga mota ta tafi, 

a bakin Gate ta samu Raveel sarkin tsoka, cikin tsiya yace.

"Kiyi ta gudun masu k'afa  da idanu daji da gani dai wataran sai gurgu ya kwasheki."

Harara ta watsa mishi tare da cewa.

"To sai me?  mugu mai bak'in baki."

dariya ya kumayi kana yace.

"To ina ga dai Jinnul asheeq ne ya aure mana ke kowa yazo kice bakyaso sai na fara gulmataki a shirin Hasken Addini Baba malam ya taso min ke a gaba tunda kinƙi yin aure."

ganin zai b'ata mata lokaci ne yasa taja motarta ta tafi.

shi kuwa Rabeel murmushi yayi kana shiga motarshi. 


ita kuwa Zaleeha 

tana isa gida bayan tayi parking  kai tsaye parlour Baba malam ta wuce tana mai jin fargabawa dan tasan kwanan zancen. 




Abuja kuwa, k'arfe biyar dai-dai Amina ta shiga d'akin da aka meda Saifuddeen. 

Domin ta bashi magungunan shi dayi mishi allura,

tana shiga tayi k'asa da kanta, har ta isa bakin gadon, 

hannu tasa ta danna woni d'an abu sai kan gadon ya d'anyi sama yadda yana koncene amman kamar a jingine yake yake, 

shi kuwa Saifuddeen jin motsin an d'an tab'ashi ne ya sashi bud'e idanunshi a hankali, 

ido ya zuba mata ganin ta zubawa fuskarshi idanu, 

amman ita bazata gane idanunshi a bud'e sukeba dan ya regesu sosai zakama yi zaton bacci yake, 

shima kanshi ta tsakankanin gashin idanun nashi yake kallonta, 

ita kuwa d'an hararanshi tayi kana ta kalli saitin mararshi sannan ta juyo ta kalleshi tare da tura baki tace.

"To Ayu sarkin jaraba, wasu in sun samu larurar daka samu basu sak'e mik'ewa da wuriba wasu kuma har abadan bazama su sake miƙewaba, amman da yake kai Ayune ana tab'aka kad'an kake mik'ewa ka razanani, to wlh allura zan maka a hannunka in ka kuskura, kamin irin na d'azu wlh bazan sake zuwa inda kakeba, 

mutun baida lfy ma sai hegiyar fitina."

sai ta kuma kalleshi tare da cewa. 

"Gashi Aunty Batulu tace min wai kai kurmane, to ni Amina yanzu taya zanyi in tasheka, bayan kuma nasan wannan abun naka ana tab'aka zai tashi kamar wani maciji."

Takaici ne sosai ya cika Saifuddeen a ranshi yake cewa.

 "Kaji fitsarerriyar yarinya, tana k'are min tanadi, dan taga sirrina."

shiru yayi da tunanin nashi jin ta d'an zira mishi allura take a damtsen hannunshi 

rumtse ido yayi da  dan zafin allurar shigan ruwan allurar a jikinshi

saida yaji ta zare allurar sannan ya bud'e idanunshi dai-dai lokacin ita kuwa ta kalli fuskarshi.

ganin ya tsareta da idanune sai jikinta ya fara tsuma cikin yin k'asa da murya tace. 

"Wannan matarshi ta shiga uku, mutun ana tabashi sai ya canza yanayi."

Sai ta kuma kalleshi tare da tsuke fuska tace. 

"Gaka da jaraba gaka da k'aton joyst...!


                  A harabar asibitin kuwa, biyar dai-dai na yamma Su Ummi suka shigo asibitin, 

kai tsaye office d'in Dr Aliyu Abban Farida da Ishaq suka nufa bisa jagorancin Dr Adnan.


Kana Ummi kuma da Hayatuddeen kuwa haggo inda Dr Batula yasa suka nufi inda take da alamun itama yanzu ta shigo asibitin,

da sauri suka nufi inda take.


Sukuwa su ishaq suna shiga cikin tamfatsetsen office d'in Dr bayan sun gaggaisa kana sun tambayi mai jiki,

Dr Aliyu ne yayi gyaran murya tare da fuskantarsu cikin nitsuwa yace. 

"To Alhamdulillahi mun dai yiwa Saifuddeen iya abinda zamu iya mishi, sauran aiki kuwa yafi k'arfinmu tunda bamu da kayan aikin shi, so dole in dai anason yayi rayuwa cikin salama sai an fiddashi woje domin ceto rayuwanshi da mutuwar konce."

cikin tsananin kad'uwa da fargaba tare rashin gane me Dr yake son sanar dasu Ahmad ya zuba mishi idanu baki na rawa yace.

"Dr ban ganeba ban fahimci maganarka ba meya samu d'an uwana? me matsalar shi? yana raye kuwa? wani hali yake ciki? wani irin ciwone da babu kayan aikinshi anan k'asar tamu? , Dr zai worke kuwa!?."

gaba d'aya ya rude haka ya sashi jerowa Dr Aliyu tambayoyin a firgice.


Cikin taushin lafazi da iya magana tare da kwanatar da hankalin dangin mara lfy irin na sahihan doctors Dr Aliyu ya dafa kafad'an Abban Farida tare zuba mishi idanu kana a hankali yace.

"K.....! 



*Ohohoho muje zuwa dai wannan lamarin littafin da salo na ban mmki da tsuma zuciya yake tafe, shauƙi bege ƙauna mai ratsa jikin maranci hmmm abin dai sai wanda ya bi littafin zai gane*




                           By

             *GARKUWAR FULANI*

8/18/20, 7:52 PM - Ummi Tandama: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


              *NAKASA BA KASAWA BACE*


                       *PAGE 17*


                         NA


           *AYSHA ALIYU GARKUWA*


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇




  *Wannan shafi gaba ɗayanshi. Sadaukarwa ga Umar ibrahim Wambai, Allahu rabbi ta baka lfy dama dukkan al'ummar musulmai*



 _Kada dai ku mance har yanzu Free page kuke samu, wanda ana gab da rufeshi ga masu akwai da niyar biyan kuɗin karantawa, turo katin Mtn na ɗari uku rak ta wannan no 09097853276. Ko kuma ka/ki turo ta asusuna na 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, kana sai ka/koyi screenshot kids turo min shaidar kin biya ta wannan no 09097853276_



"Ka kwantar da hankalin ba komai, domin dukkan tsanani yana tare da sauk'i, kuma Allah ya sanar damu bai halicci ko wanni ciwoba saida ya halicci maganinshi, sai dai in har ba'a daceba ko kuma ba'a gano mgnin ba! amman ba ciwon da bashida mgnin."

gaba d'aya shiru sukayi domin kalaman Dr Aliyu ya sakarmusu fargabar da tasa jikinsu yin sanyi.

Shi kuwa Dr Aliyu juyawa yayi ya kalli Dr Adnan cikin kula yace.

"Naga alamun kamar wad'annan duk yayunshi neko, ina Mamanshi?."

a hankali Dr Adnan yace. 

"Ummi da k'aninshi Hayatuddeen suna  woje."

"Je ka shigo dasu."  cewar Dr Aliyu,

shiru sukayi baki d'aya, 

sai kuma Dr Adnan yace. 

"Sir har yanzu mahaifiyarshi bata san sahihin raunin daya samuba, 

muna tsoron ta sani kada ta shiga wani halin."

gyaran murya Dr Ayman yayi kana yace.

"Dole tasan matsalar d'anta dole ku  duka Dr yayi muku bayani da kanshi, domin ciwonshi ciwone mai buk'atar tallafi da kulawan yan uwa da  abokan arzik'i, ciwone da zai girgiza al'jihun ahlin shi, ciwone da d'ole sai an muku bayaninshi yadda za'asan hanyoyin kula dashi,

so kada ku damu jeku kirasu, Dr zaisan yadda zai musu bayani ba tare da ta firgitaba bare ta shiga wani mawuyacin hali."

jin haka yasa Ahmad mik'ewa jiki a sanyaye ya fita.

Jim kad'an suka kuma shigowa tare shi yana gaba Hayatuddeen na binshi a baya, kana Ummi na biye dasu. 

inda ya tashi ya nunawa Ummi ta zauna kana Hayatuddeen ya tsaya gefenta.

Ganin haka Dr Ayman ya jawo wasu yan kujeru guda biyu ya baiwa Ahmad da Hayatuddeen. Bayan duk sun gaggaisa, Dr Aliyu ya fuskanci Ummi da kyau, cikin bada k'arfin guiwa yace.

"Maman Saifuddeen, kin shiga kin ganshi kuwa?."

 cikin tsoron da tunda Ahmad ya kirata ta shigeshi cikin sanyin tace.

"Ban ganshi ba bai ganniba, bansan wani hali yake cikiba, dama akan Dr Batulu zata kaimu yanzu mu ganshi sai kuma akace kana kirana."

cikin bata k'arfin guiwa yace. 

"Ba matsala zuwa anjima zaki ganshi."

ajiyan zuciya ta sauk'e tare da gyad'a kai alamun gamsuwa, 

sai kuma tace.

"Dr me ya sameshi ne?."

gyaran murya yayi kana yace. 

"Ki kontar da hankalin ki, zan miki bayanin matsalarsa dan ku shawarta yadda za'ayi jinyarshi."

kusan a tare sukace. 

"Muna jinka Dr meke damunshi!?." 

kanshi ya d'an kauda daga garesu kana ya bud'i baki a hankali cikin nitsuwa da taushin lafazi irin nasu na Doctors ta yadda bazasu firgita yan uwan majin yaciba yace.


*"Spinal Cord Injury (cutar laka)."*

da sauri Ishaq da Ahmad suka rumtse ido da tsananin k'arfi,

yayinda Hayatuddeen kuma ya zazzaro idanunshi woje, zuciyarshi sai harbawa takeyi a 360.

Ummi kuwa da bata gane menene hakanba bata wani damuba,

sai cewa tayi.

"Menene hakan?."

Dr Adnan kam tuni ya sunkuyar da kanshi yana jin wasu zafafan hawaye na tsastsafo mishi, 

shiko Dr Aliyu fuskantansu yayi da kyau kana yaci gaba da cewa.

*"Spinal cord (Laka)* wani yanki ne na ci gaban k'wak'walwa da aka sauk'o da shi zuwa gadon bayan d'an adam domin sadar da sak'o daga k'wak'walwa zuwa ga sauran sassan gaggan jiki, da kuma daukar sak'o daga jiki zuwa k'wak'walwa."

numfashi ya fidda ganin duk sun nitsu suna sauraronshi kana yaci gaba da cewa. 

"Ciwon laka wanda ake cewa *"Spinal Cord Injury (SCI)*" a turance matsalace da ke faruwa sakamakon raunata ko katsewar laka da ke cikin kwaroron k'asusuwan gadon baya saboda dalilai da dama...


Alamomin ciwon laka sun dogara ne da inda rauni/ciwon ya faru.


Misali, idan raunin ya faru a wuya,(Cervical Injury) to daga wuya zuwa k'asa ne zai sami matsala, wannan ya had'a da hannaye, gangan jiki, k'afafuwa, da dai sauransu!... 


Haka nan idan raunin a dai-dai wani k'ashi daga k'asusuwan gadon baya ne, (Thoraxic) to daga nan har zuwa k'asa matsalar za ta faru."


Duk shiru sukayi kowa da irin fargabar dake ransa

Shiko Dr Aliyu cigaba yayi da musu cikkeken bayani cutar anitse yake cewa. 

"Idan raunin daga k'ashin k'ugu ne, (Lumbar) to daga k'ugun har zuwa k'asa da 'yan yatsun Mutum za su sami matsala.


Bugu da k'ari, matsalolin ciwon laka sun sake dogara da girman ciwon/ raunin da lakar ta samu. 

Gwargwadon raunin da lakar ta samu gwargwadon injury din da jikinsa zai sa mu.


Misali, a wani lokacin lakar tana tsinkewa gaba d'aya ne. A wannan yanayi za'a samu yankewa sak'onnin k'wak'walwa zuwa sauran sassan jiki mutum. 


A wani lokacin kuma in ta sami rauni ko ciwon da zai hana ta isar da sak'onni a wasu gab'ob'in yadda ya kamata.


Alamomin ciwon sun had'a da.


1 Kasa iya motsa hannaye ko k'afafuwa.


2 D'aukewar ji a fata, kamar tab'awa, jin sanyi ko zafi.


3 Kasa iya rik'e fitsari ko bahaya.

wanda Alhamdulillahi matsalar Saifudddeen bata kai wannan mata kinba domin yana iya rik'e buk'atunshi."

ajiyan zuciya suka ja dan sun d'an samu nitsuwa,

shiko Dr gyara hannun rigarshi yayi kana yaci gaba da cewa.

"4 Matsalar saduwa da iyali sex.


 Matsalar numfashi."


Sai ya kuma d'an kalli Ummi data ja wani dogon numfashi yayinda hawaye ke kwaranya a hab'arta, 

kai ya jujjuya mata alamun tausayawa kana yaci gaba da cewa.

" A Person Sensory messaging ya had'a da yadda Mutum ke jin abu, misali kamar jin

Zafi=hot

Sanyi=cold

Touching = tabawa

Pain=rad'ad'i &Pressure.

 K'wak'walwa ita ke regulating heart beat bugun zuciya, Blood pressure yanayin gudun jini da kuma dai-dai-ta zafin jiki Body Temperature."

Tsagai tawa yayi da bayanin da yake musu ya meda idonshi kan table d'in gabanshi ,

Remote d'in AC dake gabanshi ya jawo kana ya k'ara gudun AC ganin yadda wata zazzafar zufa ta ketowa Ummi da Hayatuddeen, 

goran ruwa dake gabanshi ya mik'awa Ummi, da nufin ta amsa ta sha amman ina ta gaza karba sai Ahmad ne ya amshi gorar, 

shiko Dr Aliyu k'ara tausasa muryarshi yayi tare da cewa.


 "Spinal Cord Injury ta wata fuskar ana raba shi gida biyu!.

Gasu kamar haka.

Complete & incomplete Spinal Cord Injury.


Complete Spinal Cord Injury shi ke kawo permanent damage a wuraren da aka sami matsala. Kamar misalin Hannaye ko k'afa za su iya zama paralyse, mai matsalar ba zai rinka feeling zafi, sanyi, ko bugu a wanan wuraren ba, 

saboda katsewar hanyoyin sada sak'onnin dake tsakanin k'wak'walwa da jiki. 

a irin wanna Mutum kan rasa sexual function.


Incomplete Spinal Cord Injury kuma wani sashi ne daga jikin laka ke samun matsala saboda haka matsalar tana shafar wasu ne daga cikin gabobin jiki ba duka jikiba!."

Numfashi yaja tare da jin wasu zafafan hawaye na ciko mishi ido murya a sanyaye yace.

 "Cutar Laka na addabar matasa da dama a duniya!.

Har yanzu ana ci gaba da fuskantar kalubale wajen warkar da cutar gaba d'aya, domin har yau kimiyya ba ta gano hakikanin maganinta ba."

share hawayenshi yayi gudun kada su Ummi su gani yasan hakan zai firgitasu, cikin danne rawan muryarshi yaci gaba da cewa. 


"Mu maza munfi kamuwa da cutar, idan an kwatanta da Mata.

Musamman wadanda suke ke  29-30 yrs. 

Duk da Akwai cutar laka wanda ake haihuwar mutum dashi.

Akwai kuma wadanda ke samu daga baya, kamar ta hanyar Accident Hatsarin Mota wanda shine yafi shahara a nan k'asarmu Nigeria.


Dalilin dake janyo wadanda suka yi hatsari kamuwa da cutar laka, mafi yawanci daga masu zuwa kawo taimako ne bayan had'ari ya auku.


Akwai bukatar wayar  wa Mutane kai sosai ta wannna bangaren,

kamar gayyatar doctors zuwa gidajen radio da TV kana wayarwa mutane kai da gaya musu abinda ya dace akeyi yayinda hatsari ya auku, domin shi wannan taimakon kowama yana iya riskar kanshi da yinshi ba lallai lokacin da akayi hatsarin ya kasance akwai doctors a wurin ba,

  domin a k'a'ida ba a so lkcn da had'ari ya faru, be kamata asa Mutum ya  tashi tsaye ko ya mike zaune ba. Ko da ko bai nuna wata alamar rauni ba a lokacin.


Wasu da yawa daga nan suke samun matsala, saboda wani zai iya yuwuwa incomplete Spinal Cord Injury ya samu a lokacin, amma dalilin yadda ake tasar da mara lafiyar, ko yanayin yadda ake ciccib'osu ba bisa ka'ida ba shi ke maida injury complete damage.

Akwai bukatar samar da kwararrun kayan aikin yayyanke mota idan hatsari ya faru yadda za a sami jawo Mutum ba tare da an tankwasa shi ba tankwashewar shi ke taba bayan su.

 Yawancin Mutane masu larurar laka basu da hali, saboda cuta ce mai matukar cin kud'i."

a nan kuma Dr Adnan ya kasa tsaida hawayenshi hakama Hayatuddeen tuni yaketa zubda hawaye, domin ya gano inda mgnar Dr ta nufa shi kenan Hammanshi ya k'ara samun nakasa, 

Ishaq ma tuni yake koka matsalar amininshi, 

Dr Aliyu kuwa a hankali yaci gaba da cewa.

"Ko kudad'en gwaje-gwajen da ake wa masu cutar aka bar Mutum dashi gagarumin aiki ne wanda dole in ya samu talaka ya gujewa asibiti, bare kuma a hada da maganar surgery da akeyi domin maida kasusuwan da suka sami matsala, da devices, abubuwan da suke supporting me larurar wajen kwanciya ko zama misali Kujerar zamansu wacce takeda tsananin tsada.


Sannan ga maganar Rehabilitation kulawar da taimakon da ake bawa wadanda suka sami nakasa wajen koyar dasu Aikin yi da za su dogara da Kansu kar su zama liability. 

Da yanayin yadda za su rinka kula da jikinsu don gujewa afkuwar wata matsala.

Wasu saboda rashin samun wadatacciyar kulawa babu treatment din da ya dace, haka za a koma dasu gida, wanda a karshe mutuwa suke yi!. sunkuyar da kanshi yayi dan b'oye hawayenshi dake zuba, a hankali yaci gaba da cewa.

 "Abubuwan da ke haddasa ciwon laka sunada yawa.


Hatsarin ababen hawa.


Faɗowa daga sama. Kamar masu hawa bishiya don dibowa dabbobi abinci ko kad'o 'yayan itatuwa.


Da kuma masu hak'e-hak'en ma adanan k'asa suma abu na ruftawa dasu a sami karyewar wuya.


Da kuma  masu tonon rijiya.


Harbin bindiga ko suka da makami.


kamar yadda ta faru ga Saifuddeen, sukan da makamin suka da makamin da aka mishi ya zama sanadi daya samu matsalar incomplete spinal cord injury. 


Sannan Cututtuka kamar sankara/daji, tarin fuka(tarinTB), da sauransu , suma suna iya jawowa mutun wannan larurar.


 FAƊAKARWA! Ga duk wanda hatsarin abun hawa ko fad'owa daga sama ya ritsa da shi ana k'addara cewa ya sami rauni a lakarsa har sai likita ya tabbatar da akasin hakan. 


Saboda haka akwai matuk'ar buk'atar d'aukarsu ta hanyar da ta dace, a garzaya da wad'anda irin wannan tsautsayi ya ritsa da su zuwa asibiti!.


Duk inda aka samu hadari ba a so a tayar da mutum zaune ko asa ya mike ko a janyo shi, hakan ke taimakawa wajen karasa yanke lakar jikin mutun!. 


Ba a so a tankwasar da Mutum In hatsari ya faru.


Yawan cin masu kawo taimako in anyi hatsari suke karasa sa Mutum wajen samun larurar.


A tak'aice, wasu masu wannan matsala na buk'atar a yi musu tiyata/aiki a gadon baya, yayin da wasu kuma basa buk'ata.

wasu kuwa basuma da damar da za'ayi musu aikin sabida cutar laka cuta ce me tsananin cin kudi.


Domin idan Mutum ya sameta rayuwar da yake bukata.

 Rayuwa ce mai tsananin tsada da cin kud'i.

Orthopaedic surgeons (likitocin da suka kware a fannin k'ashi) da

Neurosurgeon wanda suka kware a fannin k'wak'walwa suke kula da masu larurar. Wandada muna da karancin su a kasarmu nan Nigeria , shiyasa abin da ya shafi fannin ke dad'a tsada, uwa uba ga rashin wadatattun kayan aiki."

sai kuma ya kalli Dr Adnan kana yayi k'asa da murya tare da cewa.

"In dai da hali to a fiddashi woje yafi konciyar hankali."

kai Dr Adnan ya gyad'a mishi, 

shi kuwa fuskantarsu yayi kana yace.

"Karin inda matsalar take, da yawa wasu suna zama a gida sai daga baya suke zuwa Asibiti, wanda kafin aje condition din ya kara zama worst.

 Likitocin fisiyo (physiotherapists) ne ke k'ok'arin farfad'o da aikin lakar ga wad'anda akai musu tiyata/aiki da wad'anda ma bata kai ga a yi musuba.


Tabbatar akwai likitan fisiyo a cikin likitocin da ke kula da masu ciwon laka, dole yan uwan mara lfy su tabbatar da haka, dan kada suyi ta narka kudadensu a banza.

Saboda su fisiyo suke koyar dasu da tallafa musu wajen motsa jiki (movement) da kuma yin exercise(don a rinka strengthen muscles din) manual therapy, koyar dasu karatu game da shawarwarin da za su amfane su.

 To ga wadanda ba su da hali ina za su iya daukar nauyin wadan nan likitocin?.


 Kungiya Tabbatar da Ci gaban Rayuwar Masu Cutar Laka  (RHOWI) ta yi kira ga masu fama da wannan lalura da kada halin da suke ciki ya sa su karya da rayuwa kasancewar masu fama da wannan lalura za su iya ci gaba da karatu da samun guraben ayyuka a ma’aikatun gwamnati, domin ita. Nakasa ba kasawa bace, kana babu nakasasshe sai kasasshe.

suna k'arfafa gwiwar masu fama da wannan matsala, don su cimma muradin rayuwa ba tare da samun cikas ba, yana da matukar amfani kuma makusantan masu cutuar ma suke bawa mai cuter k'arfin guiwa kada suke nuna karayarsu.


Matsalar ciwon laka da shanyewar sassan jiki na da gagarumar illa ga gangan jiki, da kuma tattalin arzik'i da, tunanin Mutum, kwanciyar hankali, walwala, saduwa da iyali, da sauransu.

 Duk da mun san cewa wanda ya kamu da wannan cuta ba zai dawo kamar da ba, to amma hakan ba ya nufin Mutum ba zai ci gaba da harkokin rayuwarsa ba. Mutum zai iya yin karatu har ya yi aiki. Mutum zai yi aure har ya haihu da sauransu, duk da wasu ba za su iya haihuwa ba, ya dai danganta da yanayin damage din da Mutum ya samu.

 Ana son masu larurar su rinka kokarin kula da kansu, don guje wa aukuwar wasu cututtukan sakamakon rashin kulawa.


Ita wannan cuta tana haifar da wasu cututtuka ga mai lalurar sakamakon rashin kulawa.


Misali akan samu matsalar k'oda da shigar kwayoyin cuta a mafitsara sakamakon rashin shan isasshen ruwa, da kuma yiwuwar samun miki gyambo sakamakon rashin zagayawar jini a jikin mai lalurar.

 Don haka akwai bukatar kula da kai ta hanyar shan ruwa sosai kana akai-akai.

 Mafi yawan masu larurar marasa galihu ne, shi ke kara musu wahalar ciwon dan haka in dai kunada dama kada ku duba yawan kudin da zaku kashe, ku kula dashi da kudinku da jikinku haka zaisa mu tsammaci samun lafiyarshi cikin sauk'i. 


 Shekaru goma sha takwas baya ko aikin kashin ma ba a yinsa a Nigeria Amma yanzu anayi so duk da haka shawarata gareku in dai da hali ku fitar dashi woje.

kana muna mik'a kukanmu ga Al'umma masu hannu da shuni, sannan

 Ya kamata ace gwamnati ta dad'a sanya hannu wajen k'ara samar da wuraren da ake kula dasu a anan kasar tamu Nigeria.

Kamar irin makarantunsu, wajen motsa jiki, samar da ababen dake tallafa musu wajen zama, tsayuwa, kwnaciya ko saduwa da iyalin su, duk da wasu in bai tsananiba suna aiwatar da saduwar da kansu. 


Wasunsu na samun matsala ta Fitsari, ba su iya rike shi a duk sadda yazo, kunga irinsu na bukatar kulawa ta musamman!.


Suna da yawan jin zafi mai tsananin gaske saboda dalilin yankewar sakon dake tsakanin k'wak'walwa wajen regulating (daidaita) zafi na jikin Mutum shiyasa sukeda buk'atar wuri mai tsananin sanyi da wadaceccen tsabta.


 Bin hanyar rigakafin hana ciwon yayi worst ko da an kamu dashi a lokacin da aka samu hatsarin:


Ta hanyar daukar mara lafiyar bisa tsari ba tare da an sanyashi ya motsa ko juya jikinsa ba, har zuwa Asibiti.


Yin hoton kashi akan lokaci, da sauran binciken da ake gudanwar don gano idan mutum ya kamu da larurar (kamar irinsu X-ray, CT scan, MRI da sauransu).


Sannan gaggawar yin aiki da wuri ga wanda aka tabbatar yana da larurar (akwai wadanda kasusuwan ke danne lakan, har se anyi aiki an gyara kasusuwan) kamar irin aikin daya kamata ayiwa Saifuddeen dan haka yanada kyau a shirya fita dashi cikin gaggawa, duk da zamuyi mishi taimakon gaggawa. 


Samar da Facilities da wadatattun ma aikata da kayan aiki ta wannan fannin, munada rashinsu a k'asarmu nan, shiyasa ake buk'atar.

*Tallafawar gwamnati!* domin ya zama an agazawa marasa karfin dake fama da larurar, don maganar gaskiya ba kowa ze iya affording abubuwan ba,

 tun daga kan hotunan da ake wajen binciken gano ciwon, zuwa materials din da suke amfani dasu, da kudin aikinsu da dai sauransu.


Yawancin comment din masu ciwon, ko likitocin dake kula dasu shine, *Mutum baya taba iya fahimtar halin da suke ciki sai idan har ya tsinci kanshi a kwatankwancin larurar ko kuma d'an uwanshi* ko kuma idan ya kasance wanda ke kula dasu, su suka san irin wahalar rayuwa da suke sha.


MRI scanning alone is N85,000 to N95,000


Surgery is about N2.5 million wannan ina ga wajen shekaru 3 baya kenan bare kuma yanzu da komai ya k'ara tsada.

 Yawanci ana samun recovery within d first 6months bayan faruwar hadarin, duk inda ya ci gaba da samun loss of function sama da shekara guda wasu biyu, to yakan zama permanent damage shiyasa yana da kyau a kula da masu larurar da kyau.

Kana ana iya rasa muscle function 

loss of sensation daga saman kirji har kasa, 


loss of control of bowels and bladder, 


loss of normal sexual function. 


Spinal cord injuries a upper neck (saman wuya ) yana kawo difficulty in breathing har se ya zamana ana amfani da breathing machine, or ventilator.

 Treatment

Ana ba su Drugs domin rage symptoms din ciwon wanda Drugs en kawai ba k'ananan kud'i suke ciba.


Sai Surgery wanda shine sha k'undum mai yashe asusun yan uwan masu larurar, shiyasa muke neman tallafin gwamnati.



Then

Rehabilitation da kuma Samar da assistive devices kamar kekunansu, colar device na wuya da sauransu wanda sunada tsananin tsada

 95% na maza masu SCI suna fuskantar matsalar ejaculation


80% kuma suna fama da eractile dysfunction

 Wasu a wani lokacin suna samu motsawar sha'awar madadin semen ya fito daban kamar yadda aka sani, se ya rinka fitowa had'e da fitsari, wasu kuma sukan samu ya fito lfy lau, sai kaga har sun haihu.

 Maza sun fi kamuwa da cutar fiye da Mata.


Bangaren auratayya wasu za su yi iya saduwa da iyalinsu amma ba gamsuwa.

wasu kuma da sukeda cikar halitta sukan iya gamsar da matansu, domin a wasu lokutan sai kayi mmkin jarabar nakasashe sai ya zarta na masu tsayuwan


Wasu kuwa ko taba su akayi a bangaren ba za su ji komai ba, bare maganar jin dadi.


Wasu kuma sukan rasa karfin kuzarinsu, zai zamana ba sa iya tabukawa mace komai


Ya dai danganta da level of injury din.

wanda shine mukeso yau mu binciki na Saifuddeen yadda abin yake a jikinshi.

A gefen  mata kuma sukan sami karancin niima wanda takan kai har se anyi amfani da lubricant


Rashin jin feeling na sha'awa


Sannan suna samun Matsalar al'ada.


 Ga wadanda Kuma basu samu matsala gaba d'aya ba sukan iya hulda da iyalinsu sosai su samu gamsuwa da juna ras kai fiyema da wasu masu lfy, so ba mmki Saifuddeen inki yayi aure har yayi mata hud'u har kuma ki samu jikoki yan tagwaye."

ya k'arishe mgnar yana kallon Ummi dayi mata murmushi dan sama mata nitsuwa, 

kuma Alhamdulillahi ya lura ta d'anji sanyi dan har tayi d'an murmushi tare da goge hawayenta.

hakama Hayatuddeen ya d'an saki ajiyan zuciya, 

yayinda Ishaq ma yayi murmushi dan yasan mgnar Dr Aliyu gskyace tunda yana tare da masu matsalar a members en k'ungiyarsu ta Jonaqwd Gombe state chapter.


Cikin kula da farin cikinsu yaci gaba da yi musu bayanin yadda zasu kula da shi a matsayinsu na 'yan uwanshi cikin kauda kai yace.

Akwai dabaru da ake ba su musammn domin auratayyarsu, ga wadan da ba su iya mikewa sukan sadu da iyalan nasu a zaune wasu kuma suna iya dogaro da kafafunsu amma ba za su iya mikewa gaba daya ba sai dai hakan bazai hanasu sarrafa matansuba, mu samman in sun samu cikekkiyar kula da magunguna da allurai.


Jan hankalin ga drevars na gida dana haya, 

 domin a Nigeria an tabbatar da kiyasin cewa 70% na masu larurar a sanadiyyar hadarin mota ne suka samu matsalar

 Saboda rashin kyawun hanyoyi da kuma sakaci da gangancin su kansu masu tukin.

 Sannan da yawan masu larurar ba su da wadataccen hali shiyasa ake buk'atan tallafin gwamnati. 

 Wasu sukan samu cutar wajen wasanni irin na sports haka kwallon kafa, ko tseren Mota da masu irin tsalle-tsalle ko a shiga ruwa duka  dai da kuma yin galla yayin d'aukan aure da matasa keyi masu machine da keke napep da kuma motoci dan haka ni dai Aysha Aliyu Garkuwa ina kira ga matasanmu please ku kula domin zama lfy yafi zama d'an sarki,

 duk duniya babu abinda ya kai lfy dad'i da tsada.

 Mutum yakan daina feeling wadan nan gaba daya a daidai inda larurar ta same shi

 Ba ma idan aka ce ana zafi irin yanzu da zafin ke fara shigowa hunturu na fita

 Da yawansu ba  sa iya barci.

 Sai an rinka daukar ruwa ana kwara musu, in babu AC a inda suken.

 Idan anyi saurin d'aukar mataki *ana warkewa!* kamar yadda muke tsammanin Saifuddeen zai iya workewa.

 Amma complete injury shi ke kawo permanent damage.

 Saboda wasu kasusuwan spinal din ne ke danne ita lakar


To irin wadan nam abin da suke bukata ayi surgery na gwanaye doctors domin gyara zaman kasusuwan. Akwai wadanda Kuma wasu gabobin za su ci gaba da aiki wasu kuma ba za su ci gaba ba har abada

 sabida ita lakar had'e take da k'wak'walwa


A bangaren kimiyya kuma k'wak'walwa ita ce gaba da kowace organ na jikin dan Adam to idan ta sami matsala kusan kamar dukkan jikin Mutum ne ya samu.

 Musamman spinal cord injury din.

 Da k'wak'walwar ta taho se aka shigar da lakar shine yake zuwa har daf da mazaunan mutum ta baya, ana kiran wurin da *coccyx* wato kashin bindi nan ne inda ita lakar ta kare a jikin mutum tun daga k'wak'walwa, wanda kowa in ya danna tsakiyar mazaunen sa tasama k'adan zaiji wannan k'ashin bindin ko wanda ramarshi ta tsananta ana iya ganin alamarshi. 


To shiyasa ko duka! kamar yadda akayiwa Saifuddeen ko matsanan cin buguwa a wannn kashin bindin yakan iya haifar da matsalar.

 Kana a tare da ita lakar k'asan kasusuwa ne suka rufe ta domin ba da kariya a gareta wanda wanan hikima ce ta Ubangiji, 

domin duk abin da yake da matukar amfani da mahimmanci a jikin d'an Adam to bai barshi a waje a fili  dole sai ka ga an samar masa *Garkuwa* wato protection.

 Kamar ita k'wak'walwa d'in sai aka sanyata cikin kokon kai

 Saboda mahimmancin ta.

 Gashi abu k'iris ke iya damaging dinta in ace wai a sarari take

 Shiyasa za kuga an dage an bugi mutum akai amma sai dai a tab'a kokon.

 Shiyasa kuma idan aka samu buguwa mai tsananin kai ke samun matsala

 Sanan sauran organs din jikin mutum kmar irin su zuciya, koda, hanta, hunhu, ai idan kuka duba ko da a jikin dabba da aka yanka ne, za ka ga duk a boye suke ai?." 

ya karishe mgnar da zuba musu ido tare da lamun tambaya da son jin amsarsu da zata nuna tabbas hakane. 

Su kuwa a tare sukace. 

"Tabbas wannan haka yake."

murmushi yayi cikin jin dad'in suna fahimtar mgnarsa yaci gaba da cewa.

 "Bari in shaa Allah zan nuna muka wasu hotunan jikin Saifuddeen d'in da muka d'auka,

domin yadda za ku k'ara fahimtar  yadda case din spinal cord injury ke faruwa


Lamarin tsakanin k'wak'walwa ne da ita lakar sai kuma *nerves* kamar ace wasu nauin wayoyin lantarki, da suka zagaye dukkan sassan jikin d'an Adam to katsewar connection tsakannin nerves din da k'wak'walwa shi ke sanya har Mutum ya daina jin feeling a wasu gabobi na jikinsa."

sai ya kuma nisa alamun yazo k'arshen bayanin da zai musu, wanda zasu iya fahimta a matsayinsu na wata rana wani zai iya neman taimakonsu, 

mik'a ya d'anyi kana yace.

" Yauwa sai maganr kud'in keken hawansu wanda ya kamata ku sama mishi kana a sarrafa mishi abin magna a jikinshi.


Kana duk da kasancewarmu nan orthopedic hospital ne, amman zanfiso ku fitar dashi k'asar woje in har fa kunada damar fiddanshin. 

domin can sun fimu  kayan aiki daci gaban kimiya."

Cikin sauk'e ajiyan zuciya Ishaq ya gyara zamanshi fahimtar Dr ya gama bayanin da zai musu, 

cikin yak'ini da niyar tallafawa abokin nashi yace.

"To ba matsala Dr mun gode matuk'a  da kulawarka garemu da k'arin bayani da kayi mana, yanzu abinda muke son sani, wacce k'asace ta fi shahara da gwarewa da iya aikin masu larurar, muna son taimakonka domin in sha Allah zamu fitar dashi in Allah ya yarda zamuyi iya yinmu."

muskutawa Dr Aliyu yayi alamun ya d'an gaji da zaman kana yace.

 "Yauwa batun k'asar da ta fi shahara wajen aikinsu na san akwai kasar India akwai Singapore da U.S.

lokacin dana samu nawa hatsarin ni Singapore aka fiddani, 

kuma Alhamdulillahi gashi na samu sauk'i tunda ni kafin a kaini bana iya tashi zane, amman tunda akamin aiki na samu sauk'i har nayi aure har matata ta haihu."

cikin sauri Hayatuddeen da Ahmad suka had'a baki wurin cewa.

"To shima d'in a kaishi Singapore d'in kawai."

kai ya girgiza musu kana yace. 

"Shawara in kun amince a kaishi India, domin acan nayi karatu kana inada abokai biyu wadanda suna cikin manyan likitocin da duniya keji dasu a wannan fannin, so kuma zan iya muku hanyar ganisu a sauk'ak'e, sai daifa fiddashi india d'in zaifi tsada, amman kuma zaifi samun kulawa ya kuka gani?."

ya karishe mgnar yana kallon Ummi da Dr Adnan

cikin gamsuwa da k'arfin zuciya Ummi. 

Ta bud'i baki da nufin zatace a kaishi india, sai kuma tayi shiru tana kallon Ishaq da ya gyara zamanshi kana yace. 

"Ba matsala zamu kaishi india d'in ka fara yi mana hanyar had'uwa da Doctors d'in insha Allah kud'i bazai zama matsala ba."

hakama Ahmad yace shima, 

Dr Adnan ma kuwa yayi na'am da hakan, 

Ummi kuwa addu'a ta rinka yi musu tare da godiya da sanya musu al'barka. 

daga nan suka tattauna abinda duk ya dace kana suka tashi suka fit.

su kuwa Doctors d'in suka fara shirin bashi taimakon gaggawa kafin a gama cuku-cukun fitar dashi India d'in.



A can room d'in da Saifuddeen ke kwance kuwa, 

fuska ya tsuke tare watsawa Amina wani zazzafan kallon dayasa, ta had'iye regowar mgnar da tayi niyar ce mishi mai k'aton joysti...!







                                BY

         *GARKUWAR FULANI*

8/18/20, 7:52 PM - Ummi Tandama: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


              *NAKASA BA KASAWA BACE*



                          *PAGE 18*



                                  NA

               *AYSHA ALIYU GARKUWA*


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇




_Free page hmmm sunfa kusa ƙarewa yaseen gwara ka/ki biya yafi miki, kada kuyi shagala da free page wasan yanzu aka fara, somin taɓine. Daga yawan page ɗinma kunsan labarin mai tsawone shiyasa nake inƙanta yawan pages sabida rage muku zaƙuwa, biya ɗari uku kacal dan samun damar karantashi har ƙarshe._


*Turo katin mtn ta wannan no 09097853276. Ko ta asusuna 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ku turo shaidar biyan naku ta wannan no 09097853276*



 Sai ta kuma yi saurin sa hannu ta rufe bakinta dan ganin yadda ya had'e fuska kana ya tsareta da kyawan manyan idanun shi, had'iye mgnar tayi kana ta fara b'allo magungunanshi  tare da fara yi mishi nuni da wai zata bashi mgnani.

hannunshi ya mik'a mata ganin haka ta bashi maganin.

Bisimillah yayi a ranshi kana ya afasu cikin baki sannan, 

ya kuma mik'o mata hannu da sauri ta bashi goran ruwan mai sanyin dake hannunta, 

amsa yayi ba tare daya kuma kallontaba, ya had'iyi maganin, tare da shanye rabin ruwan dan bin shawarwarin da doctors suke bashi na ya yawaita shan ruwa, a ranshi yake cewa. 

"Fitsararriya kawai  mai kwaɗayin tsiya."

ita dai sai kallon saitin mararshi takeyi da alamun tsoro, 

ya fahimci tsoro ne yasa taketa mishi kallon kurillah. 

Tsuke fuska ya kumayi tare maganar zuciya,

"Ganta kamar mayya, wannan kallo kamar zata cinye min Saif ɗina, ja'ira to wannan dai nan gani nan bari." 

A zahiri kuwa,

hannunshi ya d'ago kana ya had'a yatsunshi biyu dogo na tsakiyar nan da babban yatsarshi ya murzasu suka bada sautin. Tab-tab!! da sauri ta juyo ta kalli fuskarshi.

dan tayi nisa da kallon haƙilo da takewa sashin lafiyarshi na inƙarman na miji mai cikar zarra, 

hannunshi ta zubawa idanu wanda yaketa yimata nuni data fita, 

ba musu ta kama hanyar fita baya ta ajiye magungunan har taje bakin ƙofa ta kuma juyowa ta kalleshi a hankali tace,

"Uhummmmmmm to wai wannan da yana lfy kuma ya yake?." sanin ba amsa yasa ta fice tanata zancen zuci.


Shi kuwa Hamma Saifuddeen tsaki ya ja tare da da had'e hak'oranshi,

duk duniya babu matar da ta tab'a ganin tsiraicinshi tunda akayi mishi kaciya ya worke lokacin yana d'an shekaru shida, koda Ummin shi da Aunty Rahma basu kuma ganin tsiraicinshi ba, 

sai wannan yarinya rana tsaka.

 Wani d'aci yakeji zuciyarshi na mishi tunowa ita gani tayi bai mance Zaleeha ba lokacin da ta lab'e bayanshi ta kama kugunshi lokacin da taga wadannan y'an daban sunyi kansu da makamai,

ido ya kuma rumtsewa jin yadda tsikar jikinshi ya mik'e tuno a lokacin tasa hannunshi ta zagaye konkosonshi tana k'ok'arin janshi garin zame hannunta ta shafa sirrinshi ta had'a da ƙugunshi ta riƙe abinda da babu wata d'iya mace data tab'a ko ganinshi bare ta shafa, 

tun daga wannan shafar da tayi mishine kuma wata azabebbiyar kasala ta rufeshi mood nashi ya canza yaji wata iriyar fitinar da bai tab'a jiba a iya tsawon rayuwarshi hakanne ya bawa yan kalaren daman yin nasara a kanshi. 

cikin ranshi yake cewa. 


Da a iya zatonshi shi baida cikekkiyar zarra tunda ko azumi yayi Saif ɗinshi koma yakeyi ya ɓuya, haka kuwa in yayi aikin wahala kaɗan abin kan noƙe, sai randa ya fara ganin laɓɓan Zaleeha a tv ne ya fahimci waye shi, sai kuma gashi daga taɓashi sau ɗaya da tayi har yau bai kuma konciya ba, a ranshi yace.

"Ya Allah ka sauk'ak'amin k'addarorina daga wannan ta tab'a sirrina sai wannan taga matsayina.

Yarinya har ta fara cemin jarabebbe, ko jarabar uwar mi na mata? alhalin ita keta kallona kamar ta cinyeni ɗanye."

sai ya kuma bud'e ido tare dayin mgnar zuciya.

"Zaleeha ce sila da bata tab'ani ba da bazan rink'a d'imaucewa ba duk sanda na tunota."

ido ya kuma rumtsewa yanaji bayanshi kamar ba'a jikinshi yakeba.


Ita kuwa Amina tana fita tayi kicibis dasu Ummi da Dr Batulu tayiyo musu jagora da suka fito office d'in Dr Aliyu, 

cikin girmamawa ta gaidasu kana ta wuce, su Kuma sukayi ciki.



 Zaleeha da Ya Ahmad d'inta da  Mamy da Mama dasu Habu wanda yayan Zaleeha ne kana sai maryam yayar Zaleeha wacce tazo da mijinta Aminu wanda d'an bappansu ne yayan Baba malam, duk sun nitsu sunyi shiru, 

shi kuwa Baba malam cikin cikar haiba da dottaku da nitsuwa da kamala irinta manyan mutane wadanda suka wadatu da ilimin addini, ya fara yi musu addu'a kana yayi musu nasiha mai ratsa jiki sannan ya d'aura da cewa.

"Alhamdulillahi duk kunsan sanadin zamannan namu tunda kukaga mun zauna zaman jiran Zaleeha."

gyad'a kai sukayi baki d'aya sai Aminu wanda da ka ganshi kasan irin mutanen nanne masu zafi da tsauri fuskarnan tashi tana had'e sai harara yake cillawa Zaleeha k'anwarshi d'iyar Bappanshi k'anin mahaifinshi wanda suke uwa d'aya uba d'aya, kana k'anwar salihar matarshi Maryam. 

Ya Ahmad kuwa tonk'oshe kafafu yayi cikin tsanin girmamawa yace.

"Na'am". Alamun suna jiran umarni ko shawara daga mahaufin nasu. 

Shi kuwa Baba Malam, Malam Bashir Sulaiman  Dukku kenan, 

gyara zama yayi tare da cewa.

"Dama ta k'arshe zan baiwa Zaleeha wanda zan ninka mata da damar dana bata, wata shida baya, nace ta fito da gwoninta, na bata dama tayi zab'inta duk da shariya ta bani dama in zab'a mata mijin danaga ya dace a matsayinta na budurwa ni kuwa mahaifinta, 

to amman na bata dama zan kuma k'ara bata dama na k'arshe kada ita da mahaifiyarta suyi zaton bani basu hak'k'insu,."

sai kuma ya tsagaita kana ya kalli Mamansu Zaleeha wacce fuskarta ke had'e kauda kai yayi tare da cewa.

"Halima ki shawarci d'iyarki data fidda goninta cikin masu sonta, 

nanda tsawon shekara guda, 

na bata wannan damarne sabida ina sane da k'orafin da kikayi tayi a auren Maryam cewa nayiwa yarki auren dole kika rink'a zugata data bijirewa zabin da ni nayi mata, 

sai nayi dacen Maryam salihace muminace mai biyeyya a gareni, tabi zabina ta watsar da mummunar shawarar da kike bata ta ruggume aurenta tayi biyeyya ga mijinta d'an uwanta."

sai ya kuma kalli Maryam wacce yasan duk yayanshi daga Ahmad sai ita basa son duk wani abu da zai bata mishi rai bare ya zubda mutuncinsa.

Cikin taushin lafazi yace.

"Allah ya miki Al'barka Maryama ubangiji ya sa yaranki su miki biyayya fiye da yadda kikayi min, Allah ya saka miki da jannatul firdausi."

"Amin Amin ya rabbil izzati ngd Baba Malam Allah ya kara nisan kwana". 

Cewar Maryam kana duk parlour suka amsa da Amin,

Ita kuwa Mama sai k'ara had'e fuska tayi, 

itako Zaleeha sai k'ara sunkuyar da kanta ta kumayi,

gyaran murya Baba malam ya kumayi sannan yaci gaba da cewa.

"Zaleeha ki fito da zab'inki cikin watanni goma sha biyun nan, ki fara lissafi tun daga yau d'in nan yanzun nan kuma, 

kinga dai a baya na baki wata shida, shiru baki fidda mijiba, 

to ki sani muddin kika cika wa'adin da na baki baki fidda mijiba, 

toh zab'i ya dawo gareni, duk wanda naga dama shi zan aura miki, domin nasan,

baki rasa ma nemaba, amman kinyi burus da zancen, 

kinasa ana nunani in na wuce ana cewa shine babanta, ai yar malami ne, 

wasu na tuhumar to meyasa ban aurar dake ba, 

na barki kinata gallafiri a gari sai kije gidan radio kiyi ta zuba kid'e-kid'e kina waƙe-waƙe kamar zabiya,

to na baki shekara guda."

cikin jin dad'i Zaleeha ta gyada kai dan ita a ganinta ai bata da matsala shekara guda aka bata so sai takega ai lokacin da tsawo lokacin ya isheta ta nemo inda yake tasan halin da yake ciki ta bashi tukuicin aurenta bisa kareta da yayi ya zame mata Garkuwa ya saida ranshi a kanta, to me take dashi da zata bashi a duniya in banda kanta ta hanyar haure tayi mishi biyayya ta faranta mushi ta haskaka mishi dararen rayuwarsu. 

Aminu kuwa tsawa ya daka mata tare da cewa.

"Baki da bakin amsawa ne sai mgna da kai?."

cikin tsoronshi tace.

"Na amsa fa Ya Aminu."

tsaki ya d'anja kana yace. "Wallahi Allah kenan, kada kiyi kuka da kowa kiyi kuka da kanki in har kika bari akaje matakin da Baba Malam zai miki zabi, kin sani muddin yace eh to eh d'ince har gaban abadan in kuma yace a a to a ance, dana gaba ake gane zurfin ruwa kin daiga Maryam gata a gidane tana kuma da yara har biyu dan haka kada kiyi wasa da damarki ki fito da zabinki in kin tsaida goni dai babu mai miki dole."

cikin sanyi tace. 

"To ngd Ya Aminu."

sai ta kuma kalli Mahaifin nasu cikin sanyi da tsantsar biyayya tace. 

"Ngd Baba Malam Allah ya k'ara girma, ya jik'a magabata."

"Amin Amin Allah ya muku al'barka ya tsareku da sharrin shaid'an da fitinar zamani."

ya fad'i yana gyara zamanshi, domin yana jin dad'in addu'ar da yaranshi kewa iyayenshi haka yana nuna mishin koda bayan ranshi zasu kasance mishi al'waladul saliha.

Ita kuwa Zaleeha 

sai ta kuma kalli Ya Habu tare da cewa. 

"Ya Habu ga car Key inka."

amsa yayi yana hararanta kana yace.

"Ni naso ace wata biyu za'a bata ai."

hannu Baban nasu ya d'aga mishi kana yace.

"Aminu yi mana addu'a."

Addu'a yayi musu kana suka tashi daga taron.


ita da Mamanta suka wuce side din Maman,

Maryam kuma tabi bayan Mamy, 

kana Aminu da Ahmad kuwa, suna zaune gaban Baba Malam suna tattauna kan lamarin Zaleehan,

ganin mangrib ta gabato yasa sukayi al'wala suka nufi masallacin dake cikin gidan nasu. 

A falo suka samu d'an wani matashi wanda bazai wuce sa'an Hayatuddeen ba, 

yana ganin Zaleeha yazo gabanta tare da cewa.

"Dan Allah Zaleeha sammin motarki mana."

hararanshi tayi tare da cewa, 

"Lallai kam Zakariyya ni zan baka motata wacce nima ko hawanta banba kai ko key d'intama Ya Ahmad bai banba nima yau da ta Ya  Habu naje wurin aiki, yanzune dana dawo ne naga motar a parking lot."

harara ya watsa mata cikin tsama irinta sak'o da sak'o yace.

"Kada Allah yasa ki bada, kawai dan na tambayeki sai kita min ihu a kai."

cikin huce haushinta a kanshi tace.

"Ni zaka cewa ina maka ihu a kai ni mahaukaciyace da zan maka ihu."

Gwalo ya mata tare da cewa..

"To da banne? Ba gashiba daga mgna kin fara zubda ƙolla."

juyawa tayi ta kalli Mamansu data zuba musu ido tana dariya dan yanzu in ta shiga zasu nuna mata itace bare inda sabo kowa yasan Zaleeha da Zakariyya, shida hatta abo kanshi sun medata abokiyar wasansu.

ganin Maman tana murmushi yasa tace. 

"Mama kina jinshi yana cemin mahaukaciya, kuma kina dariya."

cikin muryar rashin fara'a tace. 

"Kunfi kusa."

shi kuwa Zakariyya dariya yayi tare da cewa. 

"Ni barima in koma."

 zama tayi bisa stull din dake tsakiyar falon kana tace. 

"Da yafi maka kam, d'an ci rani kawai, gwara ka koma can wurin tsohuwar nan data sakaltaka kuyu fama da wannan tsukekken anguwar taku dake saman dutse."

zama yayi kusa da ita tare da cewa. 

"Tab kaji yarinya nida gidanmu harda cemin d'an cin rani, toma na fasa tafiya."

murmushi tayi tare da share hawayenta dake zuba duk sanda ta tunoshi kai ta sunkuyar kana tace, 

"Rainon kaka kawai".

Oho dai na fiki shanawa Baba malam yana ji dani tunda na girma gaban tsohuwarshi bakiji har cewa yake nine zan samu irin tarbiyarshi."

cewar Zakariyya, 

ita kuwa Zaleeha wayarta ta duba tare da cewa.

"Rainon sakalci ba, naga hatta abo kanka sakalallune."

dariya yayi kana yace.

"Oho dai na yarda ni goyon kakane, inje ƙasar da nakeso da ƴar tsohuwata."

baki ta tabe kana tace.

 "Yaro kai ke jiran wani ya biya maka ni in naga dama al'bashi na zai kaini ."

murmushi tayi tare da cewa. 

"Daga baya Keenan."

Gefenta ya zauna kana yace.

"Yauwa Adda Zaleeha kin tuna wannan abokin nawa Hayatuddeen wanda kwanaki kuka had'u a gidan kaka yaje wurina?."

jim ta d'anyi kana tace. 

"Yes na tunashi wani kekyawan yaro shima sakali irinka."

da sauri yace .

"Eh shi dai."

aje wayarta tayi tare da cewa. 

"Har yace min shine d'an auta a gidansu shiyasa akeji dashi."

Cikin sauri Zakariyya yace. "Yesss kin gane."

sai ya kuma yayi kalar tausayi tare da cewa.

"Ayyah to shine nakeso inje gidansu.

 Yayanshi ba lfy, suna Abuja yace ba mmki ma su wuce India,

to shine zanje in gaida wata yayarshi Raliyya irinki."

cikin sanyi tace. 

"Ayyah Allah ya bashi lfy, kaje wurin.

 Ya Ahmad ka amshi Key din."

tsalle yayi tare da manna mata kiss a goshinta tare da cewa.

"Yesss my lovely Aunty faratu."

ajiyan zuciya tai kana tace.

"Yayi kyau dan na bakane zaka cemin faratu ko?."

bazan sakeba yace yana mai fita, 

da sauri tabi bayanshi kana tace. 

"Yauwa Zakariyya ga kud'i in kana dawowa dan Allah ka saya min feesh roll."

ba musu ya amshi kudin kana yaje ya amshi key din sannan ya tafi. 


Ita kuwa saida ta wasa ruwa sannan ta nufi side d'in Mamy  inda ta samu Ya Ahmad da Maryam suna cin abinci.

Gefen Maryam ta zauna tare da cewa. 

"Ya tafi ko?."  Ahmad ne ya d'an kalleta tare da cewa.

"Waye d'in?."

jujjuya kai ta d'anyi tare da lek'a hanyar shiga sannan tace.

"Wannan masifeffen mijin nata mana. Shi komai in ansa dashi sai ya zak'e ya rink'a rabka over acting."

tab'e baki Maryam tayi kana tace. 

"Kamar a kunnenshi kika fad'i yaseen zan fad'a mishi."

 ido ta zazzaro tare da cewa.

"Dan Allah rufa min asiri, wannan saggamin yanzu zaice zai gwada gwanjinshi a kaina."

dariya sukayi sannan daga bisani Ahmad da Maryam sukayi ta bata shawarar kadafa ta bari ta k'ure Baba malam, 

suna nan sunata hira Zakariyya ya dawo nan akaci gaba da hira tare dashi, sai dai sam Zaleeha bata tare dasu har Ahmad ya fahimci hakan , so sai ya danganta abin da ko mgnar auren da akayi matane,

sai daga baya Maryam ta mik'e ta tafi side d'in mamansu nan suka d'an tab'a hira kana, suka fito dan tafiya gidan ganin Ahmad ya fito zai maida Zakariyya gidan kakar tasu da yake shi tun yaye yake hannunta, 

ganin dare ya d'anyi ne yasa Aminu cewa, Ahmad ya bari zasu biya su sauk'i Zakariyyan.


                          ***

           Asalin ahlin Zaleeha. 


Malam Bashir Suleiman Dukku asalin haifeffen garin Dukku ne gaba da baya, 

Malami ne wanda yakeda cikar haiba da kamala, 

Su uku ne a wurin iyayensu babban yayansu Malam Umur sai shi Malam Bashir sai k'anwarsu Goggo Maryam wacce itace akayiwa mai suna da Maryam yayar Zaleeha, 

Malam Umar yanada matashin hud'u reras Allah ya azirtashi da tarin yara sama da talatin, 

Malam Umar mutum ne mai tsananin zafi da fad'a yanada tsananin kafiya shi kaifi d'aya ne in yace eh tofa eh dince har gaban abadan babu wanda ya isa ya karya mishi doka muddin ya kafa dokarshi,

mutun ne wanda in yayi gyaran murya koda kajin gidanshi suke nitsuwa,

Allah ya shirya mishi yaranshi yayinda Aminu shine babban d'anshi kuma shine ya gado zafin zuciyar Malam Umar da kafiyarsa kab, 

sabanin Baba Malam shi kuma yanada tsananin nitsuwa da kauda kai da hak'uri ammanfa in aka k'ureshi yafi Malam Umar zafi da tsanani, 

Mahaifinsu ya rasu, shiyasa suka k'auro suka dawo Gombe sun dawo gombe ba juyama Allah yayiwa Malam Umar rasuwa daga nan komai na kula da gidan ya dawo hannun Aminu da baba malam da Ahmad.

Goggo Maryam kuwa tana dukku gidan mijinta.


Hajia Aisha Mamy kenan itace matar Malam Bashir ta forko wacce sukayi auren lalle da lalle, 

wacce Allah ya azurtasu da d'ansu Ahmad daga shi kuma bata sake samun haihuwaba.

Ahmad nada shekaru goma a duniya, 

lokacin su Malam bashir  suna shiga k'auyukan k'abilun gombe da kewaye suna da'awa, 

kuma Alhamdulillahi kafurai sunata musulunta suna shiga addinin musulunci sosai, 

a cikin hakane sukaje wani yanki kaltingo na k'abilun tangalu nan suka musuluntar da mutane da dama maza da mata a cikinsu akwai wacce ta musulunta da sunata Soro data musulunta ta zab'i a saka mata Halima,

sosai iyayen Halima suka tada hankalin kan musuluntar da tayi daga bisani sukayi mata barazar zasu kasheta, 

ganin ta kafe ne kuma bata tsorita ba sai suka koreta, 

to daga ranar tayi ta bibiyar malamai mata dasu Malam Bashir Sulaiman Dukku  ke zuwa dasu yin da'awa, 

dole suka d'auketa suka dawo da ita cikin Gombe suka ajiyeta cikin gidan da aka gina da isilamiya domin irinsu, 

nan ta zauna tayi ta karatunta daga bisani akazo batun aure nan ta kafa ta tsare tace ita Malam Bashir takeso.

Allah yayi da rabo a tsakani cikin k'ank'anin lokaci Malam bashir ya sanarwa iyayenshi da matarshi Hajia Aisha duk sai suka bashi k'arfin guiwa dan dama ita Mamy tana buk'atan ya k'ara aure. 

Nanfa akayi auren Baba Malam da  Halima Mama kenan, 

inda ya sai gida a ceceniya ya ajiyeta a nan sabida lokacin suna Dukku ya zama matanshi biyu, 

in yazo Gombe ga Halima amarya in ya koma dukku ga Mamy uwar gida mace mai tarin hak'uri da tawakkali.

Zuwan Halima gidan keda wuya Allah ya azurtasu da haihuwa yau da gobe jibi da gata.

saida ta haifi 'yara  shida Habu, Maryam, Zaleeha, Zakariyya, Ziyada , kana autarsu Zahira .

Zaleeha na yawan bin Baba Malam suje Dukku dan Mamy na matuk'ar sonta da kula da ita shiyass Zaleeha da Habu da Maryam sun zauna a Dukku sosai sun samu inƙantacciyar tarbiya a wurin Mamy kasan cewar haihuwar kunika Mama takeyi sai hakan ya zame mata kamar hutune da sauk'inta,

Mamy kuwa tasha wuyan yaran nan tamkar itace ta haifesu da cikinta dan ko Ahmad bata sha wuyan rainonshi ba kamarsu Habu Maryam Zaleeha kuma yaran suna masifar sonta hakan itama take matuƙar sonsu, 

Zakariyya nada wata biyu ta samu cikin Ziyads, 

so randa ta haifi Ziyada a ranar aka yaye Zakariyya daga nan Baba Malam ya d'auki Zakariyya ya kaiwa Innanshi, 

lokacin babansu ma na raye daga nan Zakariyya ya zama tamkar d'ansu gata da sakalci dai na goyon kaka yana shanshi, 

sai dai duk jikokinsu sunfi son Ahmad da Aminu sai Zakariyyan da Maryam .

Ziyada nada wata sha uku aka aihi Zahira auta

daga nan ita  itama haihuwar ta tsaya taci gaba da rainon Zahira da Ziyada wacce takeda nitsuwa irinta Maryam,

daga baya ta kafa nacin a dawo mata da su Maryam shi kuwa baba malam yace takau bazai d'aukosu ba, 

amman zai kawo mata Habu tunda ba d'a namiji a gabanta ko d'aya, 

to fa shine mafarin fara gane halin Halima dama inkiyarsu ce Halima hali dubu babu na zab'e.


bayan shekaru kad'an babansu Malam Bashir ya rasu daga nan Malam Umar ya k'auro ya dawo cikin gombe a gidanshi daya gina a Fantami yaso ya d'auko inna amman sai tak'i a cewarta bata son tayi nesa da d'iyarta Goggo Dada,

lokacin kuwa tuni Ahmad baya k'asar yana k'asar Italy inda nan yayi karatunshi har ya zama cikekken pilot Aminu kuwa kuwa zama babban soja, 

koda Baba malam ya sanarwa innansu cewa zai k'aura shima zai koma cikin gombe fir tak'i da kyar dai da sud'in goshi  ya lallab'ata suka k'auro suka dawo gombe nan suka zauna a nan gidanshi na ceceniyan bayan shekaru kamar biyar lokacin tuni Ahmad ya taka k'asa yayi kud'i sosai, 

Ahmad yana tsananin son mahaifinshi da k'annenshi baya son duk wani abu da zai tab'a mutuncin mahaifinshi yana tsananin tausayawa da son Mamynshi su Zaleeha kuwa jinsu yakeyi har cikin k'ok'on ranshi kusan shine yake musu komai na karatunsu.

 To sanadin hakane Halima ke d'an ragarwa Mamy kisan mummuk'en da takeyi mata, 

musamman da taga Ahmad ya sayi k'aton fili a New G. R. Aka tsantsara musu gida na gani na fad'a suka koma can kuma yana yiwa yaranta hidima.

Inna kuwa tace ita dai a barta a ceceniya ita da Zakariyyanta a kuma bata Ziyada acewar yanayin unguwar yana tuna mata k'auyensu badon Mama tasoba sai dan Dole Zoyada ta koma gaban fitinanniyar tsohuwar injita da faɗi. 


Ana cikin haka Baba Malam ya had'a auren Aminu da Maryam dan lokacin Malam Umar ya rasu to yana son k'ulla igiyar zumunci tofa anan Halima ta fito da asalin halinta. 

Gashi zuwa lokacin iyayenta duk suna ji da ita tunda yanzu tanada  wadata sanadin Ahmad kuma tana kasuwanci in zataje garinsu zai bata kud'i ta musu ihsani.


Sosai taso ta zuga Maryam sai kuma tayi rashin sa'a Maryam rainon Mamy ce sai tabi umarnin mahaifinta.


Daga nan kuma ta tsananta bak'in halinta


Yanzu su Zakariyya da Zahira da Ziyada ne suka rege suke karatu Habu da Maryam da Zaleeha duk har aiki sukeyi. 

kab cikin yaran kuma Zahira ce munafukar da ta gado bak'in halin uwartasu da k'abilancin ta.

to kuma Zaleeha na shiri da Zahiran fiye da Ziyada dan ita Ziyada irin masu shiru-shiru d'innan ne sosai,

kasan cewar duk yaran da gefen babansu suke kama shiyasa sukayi kyau mai d'aukar hankali.

Shiyasa kuma Halima take jin kanta da yaran take nunawa Mamy rashin d'a'a dan ma yaran basu biye mata.


To yanzu kuwa Zaleeha ce kan ganiyar budurci tana shawaginta son ranta, 

tana had'a gwara kan maza a cewarta sai ta duk mai nuna mata barazana da kuɗi ko wani matsayi baya ranta

duk kud'in na miji baya gabanta.

Tace ita soyayyar gsky zatayi duk wanda zata aura take kuma son ya mata tafi son miji jarumi mai tausayi da taumakon na ƙasa dashi kana har ranta tana son kekyawan miji bata son mummunan miji a ranta

Wannan kenan sune ahlin Zaleeha... 

                         ***

Ita kam Zaleeha sam bata wani damu da k'a'idar da aka bataba don ganin tsawon lokacin da aka bata takeyi kamar bazai zoba, 

so bata wani damuba asalima duk damuwarta da tunaninta a kan son gano ina wanda ya taimaketan yake.

 

Bayan ta gama shirin baccinta ne, 

tazo ta zauna bisa gadonta, ta ajiye system enta da wayarta a gefe, 

da niyar had'e muryoyin wadanda tayi hira dasu yau a kaltingo, 

kuma sai tayi shiru ta zuba fuskar System en idanu ko k'ibtawa batayi, 

ta kai tsawon 5 minutes a haka kana taja dogon numfashi tare da lumshe ido cikin sanyin murya tace. 

"Waya sani ma ko sun kasheshi ne?." sai kuma tayi maza ta girgiza kanta tare da cewa.

"Ya Allah ka kare minshi ka sake gaddara haɗuwata dashi."

sai kuma tace.

"To in ma yana raye ta ina zan ganoshi bare in mishi godiyar taimaka min da yayi, 

ba abinda na sani a kanshi suna ko anguwa ko aiki ko dangi ko abakanshi bare in mik'a godiyata a gareshi koda a gidan radionmu, 

ko menene sunanshi? ta yaya zanyi cekiyarshi ta ya zan ganoshi a faɗin duniyar nan?."

bud'e idanun tayi a hankali kana ta sharte hawayenta dan tabbas ta tuno lokacin da zata fito daga cikin sitadiyon d'in taga sun caka mishi wuk'a a bayanshi, da sauri ta kuma rumtse ido hawaye na zuba kana tace. 

"Allah ya isan mishi, Allah zai saka mishi, mugayen banza azzalumai Allah zai saka mana."

sai ta kuma ture system en kana ta zame ta konta, 

tana mai zubda hawaye a haka bacci ya saceta.


Dalla kuwa wani babban d'an kalarene wanda ya addabi birnin gombe da kewaye muddin yaga mace ko wacece ita inda ta mishi zaisa yaranshi su kamo mishi ita ya biya buk'atarsa da ita, 

Dalla ya addabi garin gombe yayinda duk naci da k'ok'arin hukuma basu tab'a kamashi ba, 

yana kuma da d'aurin gindin wani manya da suka medashi d'an bangar siyayasa shiyasa yake cin karensa babu babbaka babu wanda ya isa ya taka mishi birki.

To a yanzu dai babu 'yarinyar da yake cike da cikinta in ya kamata zaiyi mata Dalla-dalla sai Zaleeha, 

sai dai shima a sashinsa ana shirin fitar dashi woje dan yana jinyar raunin da Saifuddeen ya ji mishi a gabanshi wanda yake sashi firgita dan gaba d'aya alamu suna nunawa kamar joystick d'inshi zata mace,

shiko fatanshi koda zata mace tayi hak'uri har sai ya rarake Zaleeha a cewarshi...


                      ***

             A nan Abuja kuwa


Su Ummi kuwa suna shiga Hayatuddeen yayi saurin nufar gadon da Saifuddeen yake konce, 

yayinda shiko Saifuddeen ya mik'owa mishi hannu alamun yazo, 

da sauri ya ruggume k'anin nashi kana yasa hannu ya kamo hannun Umminshi dake tsaye tamkar ta d'agoshi, 

tuni hankalinta ya k'ara konciya ganinshi konce cikin haiyacin shi, 

Ahmad kuwa matsowa yayi gafenshi yana jan yatsun k'afanshi yayinda Ishaq kuwa yake mik'o mishi hannu ganin haka yasashi saurin sakin hannun Ummi ya kamo na Ishaq, 

wani sassanyan murmushi sukawa juna, 

ita kuwa Ummi kanshi ta fara shafawa tare da cewa.

"Alhamdulillahi Babana jiki da sauk'i ko?."

kai ya jinjina mata tare dasa hannu ya d'an ture Hayatuddeen wanda tuni yaketa zubda hawaye dan tuno bayanin da Dr Aliyu ya yi musu na nakasar da yayan nashi ya samu.

 Ita kuma Ummi  hawayenta take ta son medawa dan tasan in Saifuddeen yaga tana kuka hankilinshi zai tashi.

Shiko Saifuddeen hannu yasa yana sharewa Hayatuddeen hawaye fuskarshi kana yasa hannu ya zaro woyar shi dake aljihun Hayatuddeen in, 

juyota yayi gareshi, 

rubutu ya d'anyi kana ya mik'awa Ummi,  da sauri ta amsa dan tasan ta wannan hanyarce suke mgna dashi. 

Murmushi tayi gani abinda ya rubuta. 

"Ummi ki cewa Hayatuddeen ya bar kuka ya zama jarumi, ki tuna mishi yanzufa ya girma ya rage sakalci, ki sanar mishi jikin Hamma Saifunshi da sauk'i,  kice mishi in dai yana son in sai mishi mota to ya dena kuka."

cikin samin sauk'in fargabanta ta kalli Hayatuddeen tare da mishi bayanin Hamman nashi, da sauri yasa hannu ya goge hawayenshi tare da cewa. 

"Hamma nayi shiru na bar kuka kaji ko zaka saya min motar ko?."

 kai ya gyad'a mishi alamar yaji fuska d'auke da murmushin da yasa dimples  nashi duka huɗu suke lotsewa,  kana ya amshi wayar tashi ya shiga message ya kuma rubutu kana ya turawa ishaq ta inbox nashi, 

text d'in na shiga wayar ishaq tayi wani sautin mgna da sauri-sauri hakan yasa ya gane Saifuddeen ne ya turo mishi text alamun yana mishi Magna, 

Dr Batulu kam yar kallo ta zama sabida ganin yadda abota take tafiya tsakanin kurma da makaho kuma har suke Magna da juna kuma har kowa ya fahimci d'an uwanshi. 

shiko Ishaq lallatsa woyarshi yayi, jim kad'an ya karata a kunne sai ga wannan Magna sauri-sauri ya karanta mishi abinda Saifuddeen ya rubuta mishi kamar haka.

"Ishaq ya su Umma ya Amira da jiki?."

gyara tsayuwa Ishaq yayi tare da fuskantarshi yace.

"Alhamdulillahi suna lfy, sunce in gaidaka da jiki, kana Amira jiki yayi sauk'i har an sallamesu, kai yanzu ya jikin naka?."

rubutu ya kumayi kana ya turawa ishaq. 

"Alhamdulillahi jiki da sauk'i,  ina amsawa. ya an kai sak'on gidan marayun nan?."

Masha Allah ishaq yace tare da cewa.

"Eh an kai." 

daga nan sai kuma Ahmad yace. 

"Suifuddeen ya jikin?." murmushi yayi tare da rubuta mishi. 

"Alhamdulillahi jiki da sauk'i yaushe ka dawo daga Lagos?."

bayan ya karanta rubutun ne yace.

"Jiya na dawo."

sai ya kuma kalli Dr Batulu sai ya d'an dungula hannunshi ya mata irin gaisuwarsu sabida ya tabbatar ta haifi kaman shi.


Ummi kuwa cikin kula ta shafa kanshi tare da cewa.

"Kai Hayatuddeen bashi wuri ya tashi mana ya samu ya watsa ruwa."

shiru duk sukayi sabida ganin  kamar Ummi bata san menene ainihin matsalarshi spinal cord injury ba, ita a zatonta zai iya tashi da kanshi a yanzu haka a taken, 

shima Saifuddeen da yanada halin boy'e mata daya boye mata gskyar laturarshi sabida gudun tashin hankalinta. 

Itako Ummi sai juyawa tayi ga Ahmad kana tace.

"Ahmad tallefeshi ka kaishi bathroom kasan Saifuddeen da yawan son shiga ruwa."

Dr Batulu ce tayi saurin cewa.

"Ummin Saifuddeen kin mata bazai iya tsayuwa bane, kin mance ya nakasane kike ta cewa a tasheshi yaje yayi wonka, ai an mishi wonka d'azu kafin azo a bashi mgna, a yanzu haka bama zai iya tashi zaune bama sai mu zuba ido mu jira har lokacin da aka  mishi aiki ko Allah zaisa a dace, ya tashi ya.....!




Wasa farin girki Ana wata sai ga wata.




                                   By

                 *GARKUWAR FULANI*

8/18/20, 7:53 PM - Ummi Tandama: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


              *NAKASA BA KASAWA BACE*



                            *PAGE 19*



                                  NA

               *AYSHA ALIYU GARKUWA*


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇



~Wannan shafi nakune Nakasa ba kasawa bace fans 3 kuyi yadda kuke so dashi~


_Turn Katim mtn na ɗari   ukku rak ta wannan no 09097853276 ko kuma ta asusuna na 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa_



~Hmm Free page dai suna gab da ƙarewa saura ƙaɗan in rufe, hanzarta biyan ɗari uku kacal dan ka/kici da karantashi har ƙarshe~



Yauwa fa ba editing zakusa typing errors 



 "Ranan tashinsa tsaye sai dai muna tsammanin samun lfyarshi a ko wanne lokacin." 

tuni idanun Ummi ke kwaranyar da wasu zafafan hawaye masu tarin k'una zuciyarta tamkar zata faso k'irjinta ta fito woje dan tsananin firgita da tashin hankali uwa uba tsananin tausayi gudan jinin nata.

kukanta ya k'ara tsananta ne jin tafin hannunshi bisa hab'arta yana share mata hawayen tare da jujjuya mata kai kana yana wani irin sihirtaccen murmushi mai cike da zallan tawakkali da yarda da k'addara, 

Hayateddeen kuwa kanshi ya kife bisa pillow da kan Hamma Saifunshi ke konce goshinshi ya manna da hab'ar d'an uwan nashi kuka yakeyi mai cin rai da cushe farin ciki murya na rawa yake cewa.

"Dukkan jarrabobinmu sukan riskemu da tsananin zafi da tarin k'una,  ko yaushe ciwo ko mutuwa basa zabi duk inda Allah ya aikosu nan suke zuwa, mutuwa ta yashe mana jigonmu, yayinda kowa ya yanke k'auna sai ubangiji ya sauk'ar da k'udurarnsa bisa d'an uwana da duniya ke ganin bama zai amfanin kanshi bama bare ya amfane mu,  Hamma Saifuna ya karya zaton mutane da suke ganin nakasa kasawa ce, 

ya tashi ya tsaya kaida k'afa ya shiga rana dare zafi sanyi ya ratsa duhu da ruwa da iska na damuna dan tsaida hawayenmu ya zame mana Garkuwa kana bongo abin jingina jigonmu abin al'faharinmu."

sai ya kuma taso ya kalli Hamman nashi da yaketa juya musu kai murya na rawa yace. 

"Wallahi! Wallahi!! Wallahi!!! da ana canza ciwo da na canzashi ya dawo kaina, da ciwo bazai kuma rab'ar d'an uwana ba da ina da dama da na tsare maka dukkan wata cutar da zata kai ga tab'aka bare ta nakasa mana kai."

Ummi kam ta kasa cewa komai sai sunkuyar da kanta tayi k'asa tana zubda hawaye tare da ambaton Allah. 

Shiko Saifuddeen jawo Hayatuddeen yayi bisa k'irjinshi ya rink'a shafa kanshi cikin alamun lallashi kana ya d'auki woyarshi da d'aya hannun rubutu yayi mai yawa ya mik'a wayar ga Ummi. 

ba tare da ta kalleshi ba ta amshi woyar, 

sabida hawayen dake kwaranya a idanunta yasa take ganin rubutun bibbiyu d'ad'd'aya rumtse idonta tayi hawayen da suka cika mata idon suka zubo sannan ta fara ganin rubutun a dai-dai kana ta fara karanta abinda ya rubuta mata

"Ni kam Saifuddeeen bani da wani ciwo da zai firgitani koya tayarmin da hankalin a duniya, kamar yadda ganin hawayen Ummi na da k'annena zai sani d'imuwa, zuciyata na k'untatuwa in naga hawayenki,

Ya Nuruddeen ya bar komai a hannu na bisa ya k'inin zan hana idanunku zubda hawaye, 

ya Nuruddeen ya shaida min nakasa ba kasawa bace,  ya gina min zuciyata da rayuwata ta yadda zan iya zame muku Garkuwa duk da nakasata, 

Ya Nuruddeen ya haram tawa hannuwana rik'e k'ok'on bara ya damk'a min Al'k'alami da da jarumta. 

Ummi ya zanyi da raina? sai yaushe zanyi nasarar tsaida hawayenki?

 Sai yaushe zan saku farin ciki, 

Ummi bani da baki dana fad'i miki irin k'unar da zuciyata keyi in naga zubar hawayenki bana jin k'unci a kan larurata sai naga hawayenki na zuba. Ummi kalli yadda Hayatuddeen ke kuka tamkar zai shid'e wannan ya nuna min gazawata ce kenan, ni nasan Ya Nuruddeen bai tab'a barina na zubda kwallaba, to ya akayi ni na kasa hanaku zubda naku hawaye ko dai nakasa tace sila? yanzu Ummi kema kuka kikeyi su Rahma Raihana Raliyya kuwa ya zasuyi, 

Kalli kunsa  Ahmad ma kuka,  kalli ishaq bawan Allah da baya ganima kukanku ya sashi kuka, kalli Dr da kanta kun sata zubda hawaye,  shin Ummi kin mance imanin bawa baya cika har sai ya yarda da k'addararshi mai kyau ko akasin haka."

tuni wani azabebben kuka ya kwabcewa Ummi wanda yasa ta kife mishi woyar gefenshi tare dasa hannunta tsakiyar kanshi ta shafa sumanshi har zuwa kan goshinsa sai kuma ta juya ta fita da sauri, domin tasan in yaga tana kuka zai birkice, 

Abban Farida kuwa, hannu yasa ya kamo Hayatuddeen suka fita.

Yayinda tuni Dr Batulu kuwa tabi bayan Ummi,

shi kuwa Saifuddeen hannu ya mik'o ya kamo na Ishaq kamar yadda suka saba, shi kuwa Ishaq murmushin k'arfin hali yayi still kuma hawaye na kwaranya a idanunshi murya a raunace yace.

"Ya Rabi'u yace in gaidaka da jiki. Kana sak'on gskysuwa daga k'ungiyarmu sunayi maka fatan samun sauk'i."

hannunsu ya k'ara hadewa tare da jijjigawa alamun ya gode.

daga nan sukayi d'an hirarsu sannan Ishaq ya fito.


Nan ya samu Dr Batulu da Abban Farida sunata lallashinsu.

ganin lokacin salla ya kusa yasa suka, sallami Dr Batulu suka tafi ba tare da Dr Adnan ya fitoba. 


Shi kuwa Dr Adnan ya dad'e tare da Dr Aliyu yana mishi k'arin bayani, 

inda yace mai tunima an fara mishi alluran, 

sannan kada su damu zai rink'a taho mishi da abincin daya dace yaci, 

a nan asibitin Dr Adnan yayi sallan isha kana daga bisani suka shiga wurin Saifudddeen shida Dr Aliyu d'in.

suna shiga suka samu, nurse biyu maza masu gyara mishi jiki kamar taimaka mishi yayi wonka da al'wala da da juyashi ya fuskanci Al'k'ibllah yayi niya yayi sallanshi a koncen.


Suna shiga su kuma suka fita dan sun gama mishi shirin baccinsa, 

Yana ganin Dr Adnan yayi murmushi tare da lumshe ido kana ya bud'esu ya kalli Dr Aliyu dake zaune bisa welchair d'inshi,

a hankali ya mik'o mishi hannu sukayi musabaha, 

cikin kula Dr Aliyu yace.

"Ya jikin?." lips enshi ya motsa alamun da sauk'i kana ya jinjina kai, 

shi kuwa Dr Aliyu cikin tausayawa yace. 

"In sha Allah in an  fiddaka zuwa India nanda  wani d'an lokacin zaka fara tashi zaune da kanka."

da sauri Dr Adnan yace. 

"Allah yasa."

Amin Dr Aliyu yace kana ya duddubashi sannan suka d'an k'ara bashi k'arfin guiwa da sama mishi nutsuwa sannan suka fita, 

a bakin  harabar wurin Dr Aliyu da Dr Adnan suka had'u da Nurse d'innan Amina, 

da sauri ta iso inda suke, cikin shigarsu ta nurses wanda sunyi mata cib a jikinta sai d'an k'aramin hijabi,

hannunta na cikin haljihun gefe da gefen rigardata da iya karta guiwa,  rusunawa ta d'anyi tare da cewa. 

"Sir barka da dare."

"Barka dai Amina Usman Jada." 

murmushi tayi dan yadda ya kira cikekken sunanta, gaida Dr Adnan tayi kana tace. 

"Sir bari inje in bashi maganinshi, zan wuce gida."

jim ya d'anyi kana yace.

"To ba matsala amman dan Allah kiyi sammakon zuwa, kinga na damk'a amanar wannan aikin a hannunki, dan naga bafulatanine d'an uwanki."

cikin girmamawa tace, 

"In sha Allah ba matsala zan taho da wuri".

daga nan sukayi sallama ita tayi ciki su sukayi woje.


A hankali ta tura k'ofar ta shiga bakinta d'auke da sallama, 

kasan cewar idonshi biyu yana rubutawa Ummi text ne yasa yaga shigowarta, baibi ta kantaba yaci gaba da sarrafa woyar tashi, 

ita kuwa gefenshi ta tsaya, 

tana harhad'a alluran da zatayi mishi, 

bayan ta gama ne ta d'an matsoshi, tare da d'an zuba mishi idanu, 

kallonshi takeyi tamkar tauraro, 

gashin girarshi ta zubawa idanu wanda suke tamkar an zanasu da gazal sunyi lub lub dasu kana hancinshi zuwat har baki lips inshi jazir sai shek'ek'i sukeyi, 

ido ta lumshe tare da cewa. 

"Matarka taji dad'i koda ranta a bace yake in taga kekyawan fuskarnan taka farin cike zai kauda bak'in cikin."

lip's enshi ya d'an tsotsa ta ciki dan yana kallon motsin bakinta ta cikin fuskar woyarshi. So ya gane duk abinda tace. 

ita kuwa yatsunshi ta zurawa ido yadda yake sassarafa wayar tamkar shi ya halicceta, 

lips enshi ta kuma kalla kana tace. 

"Wannan labban da ganinsu zasuyi taushi, ji yadda suke shek'i."

still bai kulata ba, ganin ta shagala wurin kallonshi, 

ido ya lumshe yana tuno Zaleeha a ranshi sai yake jin inama itace kusa dashi,

a hankali taja numfashi kana tasa hannu bisa fuskarshi ta karkad'a mishi yatsunta, 

d'ago lumsasshun idanunshi yayi ya d'an kalleta.

ganin ta nuna mishi allurane yasashi, 

rumtse ido kana ya d'an mirgina tare da gyara zaman damtsen hannunshi na dama ya bata damar mishi allurar, 

a hankali ta zira mishi allurar kana ta fara tura ruwan, 

ido ya kuma rumtsewa kana yana sunkuyar da yatsun hannunshi har suna bada sautin k'aras-k'aras.

a hankali ta kalleshi cikin tausayawa tace. 

"Sannu."

bai nuna mata ya ganeba dan ya lura bata san yana gane mgnar mutaneba in yana ganin bakinsu, 

maganin ta babballa kana ta mik'a mishi.

 Hannun dama yasa ya amsa kana ya afasu a baki tare da amsar robar ruwan da ta mik'o mishi, 

sannan ya had'iyesu, bayan ta gama mishi komaine ta k'ara mishi gudun AC ganin tunda ta mishi allurar yake d'an had'a zufa, 

gaban gadon ta dawo ta gyara mushi mayafin sannan ta kalleshi tare da cewa.

"Zan tafi gida, dare yayi,  dan kai gobe da sassafe zan dawo Allah ya baka lfy, da masu kula da kai zasu ku kwana tare."

A ranshi yace. 

"Amin ngd." a zahiri kuma bai kuma kulataba, 

itako fita tayi, 

shi kuwa text yayiwa Rahma da Raliyya da Hayatuddeen kana yayi addu'a ya rufe ido dan allurar ta fara sashi gyangyad'i.



Rahma kam dama da Adnan zai taho cewa yayi ta koma Side d'in Mamanshi dan yana soron kartayi ta kuka, 

kuma Alhamdulillahi dake uwar mijintan na sonta suna kuma tausaya mata suna kula da ita shiyasa ta d'an sake bare yanzu da taga text d'in k'anin nata yana ce mata.

"Adda, yanzu Ya Adnan yazo, mukasha hira, yace min wai kince sai dai ku taho tare, 

ni kuwa gani garau na samu sauk'i itama Ummi da Hayatudden zasu dawo, an bar gida ba manya ga Ahmad ma yazo nan, duk sun tare a kaina sai kace basu da aikin yi."

murmushi tayi tare da cewa. 

"Zan zo kam in su Ummi sun dawo, in banzo na gankaba to wa zai zo ya ganka?."

murmushi yayi kana yace mata. 

"Budurwata mana zatazo."

dariya tayi cikin samun nitsuwa tace.

"Iye to me sunanta surkar tawa."

kai ya rausayar tare da cewa.

"Sai na dawo zan gaya miki." daga nanne ya rufe wayar tashi. 

Shiko Dr Adnan tare suka tafi da Dr Aliyu a can ya kwana.



Ummi kuwa tunda suka koma ta kasa samun sukuni duk da ta fawwala Allah lamarinta, 

Amman ta kasa cin abinci,

Hayatuddeen kuwa ya d'an sake sabida yadda Ya Rabi'u, da Ya ishaq da Ahmad suka rink'a yi mishi nasiha da bashi k'arfin guiwa da nuna mishi yarda da k'addara. 


Aunty Mami kuwa tausayin Ummi ya hanata sukuni sabida da ka ganta kasan tana cikin damuwa da fargaba, 

shiyasa data gama shirin baccinta ta kuma soya mata gwai da biredi kana ta had'a mata tea ta nufi d'akin da suka sauk'i Ummin inda suke sauk'e Mamansu Ishaq in tazo. 

bisa sallaya ta sameta tana rik'e da carbi, 

gefenta ta zauna tare da tank'oshe k'afafunta, ganin har yanzu Ummi hawaye take zubdawa cikin sanyi Aunty Mamin tace.

"Kiyi hak'uri Ummi ki dena kuka dan Allah kiyi ta mishi Addu'a, insha Allah zai samu lfy."

cikin sanyin murya tace, 

"Mami ya zanyi in banyi kukaba, me zanyi da hawayen nawa, ce minfa sukayi Saifuddeen na bazai sake tsayawa da k'afafunshi ba."

cikin tausasawa tace. 

"A a fa Ummi ana kyautata zaton wata rana zai iya mik'ewa."

kai ta jinjina kana tace, 

"Kayya ba dai boye min sukeyi ba, hakama sukayi min lokacin Nuruddeen da Abbansu."

Sai kuma ta share hawayenta cikin tarin damuwa taci gaba da cewa.

"Ina rasa nitsuwata da konciyar hankali na in naga Saifuddeen yana cikin wani hali, 

ina jin tausayinshi a raina ina rasa samun nitsuwata gaba d'aya a kanshi, 

ina tausayawa Saifuddeen in na tuna lfy lau na haifeshi, sai kuma abubuwa suketa biyu bayan rayuwarshi."

cikin tausayawa Aunty Mami tace. 

"Ummi. Wayene Nuruddeen d'in da Abbansu?."

a hankali Ummi ta nisa kana cikin sanyi ta fara bata lbrin asalinsu Saifuddeen dama yadda ya samu larurar rashin ji...

Cikin tsananin kuka da tausayawa Aunty Mami tayi saki wani nannauyan ajiyan zuciya.

Numfashi ta fudda a hankali sannan ta jingina da gadon tana mai sheshesk'an kuka har saida Ummi ta dawo tana bata hak'uri,

cikin rauni ta share hawayenta tare da cewa. 

"In sha Allah daga yanzu duk sanda nayi salla zansa Saifuddeen cikin addu'o'i na ya bani tausayi tun yana yaro k'arami yayita fuskantar k'alubalen rayuwa."

sai ta kuma gyara zamanta tare da cewa. 

"Dan Allah Ummi na rok'eki ki daina yawan kuka,

kiyi ta mishi addu'a in sha Allah Saifuddeen bazai tab'eba."

Sassanyan ajiyan zuciya Ummi ta sauk'e tare da cewa. 

"In sha zan daina yawan kukan zanyi ta mishi addu'a."

cikin jin dad'i ta mik'a mata kofin tea d'in, 

ba musu ta karb'a tare da cewa. 

"Ngd Allah ya miki al'barka."

Amin Amin tace sannan ta mik'e ta fita dan bata wuri. 


Washe gari kuwa tuni Doctor Aliyu ya harhad'a dukkan bayanan cutar Saifuddeen ya turawa Dr Acash prasat wanda yake aiki a wani babban asibiti dake New Delhi India, 

Ahmad kuwa E passport d'in Saifuddeen da Hayatuddeen da nashi ya tattara ya nufi Airport  tun da sanyin safiya ya fara musu cuku-cukun samun   visa, 

A nan ya samu Adnan ya taho dan tare zasu tafi dole yayi musu jagora a matsayinshi na likita da yaso ace da Dr Aliyu zasuje to shi aiyuka sun mishi yawa,

sai da suka gama duk abinda ya dace na zirganiyar samun tafiyar nasu cikin sauri cikin sa'a kuwa suka samu jirgin da zai tashi jibi nan zuwa India direct New Delhi Indira Gandhi Enternational Airport, saida suka gama komai na tafiyar sannan suka baro airport d'in.


Ummi kuwa da Ishaq da Saifuddeen Ya Rabi'u ne ya kaisu Asibitin.


Suna isa Dr Batulu tayi musu jagora har d'akin da Saifuddeen d'in yake, 

sosai Ummi taji dad'in samunshi cikin nitsuwa yana rik'e da wayarshi fuskarshi d'auke da murmushi, 

da sauri ta isa bakin gadon kujerar dake kusa dashi taja ta zauna, 

ishaq kuwa yana isa bakin gadon ya rik'e k'arfen gadon ya tsaya, 

Hayatudddeen kuwa gefen shi ya tsaya kusa da Umminsu, 

da sauri ya ajiye wayarshin tare da juyawa inda suke jin Ummi na shafa kanshi, 

murmushin ya kumayi tare d'ago hannunshi  ya shafa kan Hayatuddeen yayinda Ummi kuwa ke shafa kanshi, 

sai ya kuma mik'o hannunshi d'aya ya kamo hannun ishaq.

Ya Rabi'u ne ya d'anyi murmushi tare da cewa. 

"Masha Allah. Alhamdulillahi jiki da sauk'i ko?."

kai ya jinjina alamum eh. 

Dr Batulu kuwa sai binsu da idanu takeyi cikin shawar shak'uwar dake tsakaninsu.

Cikin kula Ummi tace.

"Sannu ko babana ya jikin?."

wayarshi ya d'auka da sauri ya rubuta mata. 

"Alhamdulillahi jiki da sauk'i."

cikin jin dad'i duk sukace. 

"Allah ya k'aro mana sauk'i."

Amin Amin ya amsa a saman lab'b'ansa. 



Dai-dai lokacin kuma su Ahmad da Adnan suka shigo,

bayan duk sun gaisa sun tabayi ya mai jikine sannan Ahmad ya kalli Ummi cikin nitsuwa yace. 

"In sha Allah jibi zamu tafi india, 

kuma Alhamdulillahi kafinma muje bayanan zuwanmu ya shiga hannun doctors d'insu."

cikin sauk'e numfashi Ummi tace. 

"To Allah ya kaimu lfy ya kuma bada sa'an aiki."

cikin son kontar mata da hankalin Dr Adnan yace. 

"Yanzu Ummi keda Ishaq zaku koma gombe gobe."

da sauri Ummi tace.

"In koma Gombe kuma?." Cikin nitsuwa Ya Rabi'u ya gyad'a mata kai tare da cewa. 

"Eh Ummi ba matsala ke da Ishaq ku koma gombe, 

Ahmad da Hayatuddeen kuwa dasu za'a tafi, 

tare da Dr Adnan kuma shima in yaje ba dad'ewa zaiba in yaga anyi aiki dai to zai dawo kiji labarin jikin Saifuddeen d'in  kuma, 

in ya dawo keda Ishaq da bappa Ali zakuje."

kai ta sunkuyar kana murya a sanyaye tace. 

"Yanzu sai in zauna a tafi dashi har wata k'asa ta daban."

Ahmad ne ya d'an kalleta tare cewa. 

"Ummi nida Hayatuddeen zamuyi duk abinda zakiyi mishi karki damu zamu kula dashi."

still dai kamar bata gamsuba ido ta zubawa Dr Batulu da ta dafa kafad'unta tare da cewa. 

"Ummin Saifuddeen ki kwantar da hankalinki shi jinyan namiji saida namiji d'an uwanshi hakama mace saida macce yar uwarta, 

kuma duk sanda kikeson zuwa zakije ki duboshi."

cikin gamsuwa tace. 

"To ba komai Allah ya shige mana gaba."

Sai ta kuma juyawa ta kalli Saifuddeen da yake kallonta fuska cike da bege murya can k'asa tace. 

"Allah ya baka lfy babana."

Amin Amin suka amsa baki d'aya, 

shi kuwa Hayatuddeen wayarshi daketa ringing ya d'aga ganin Salisu ne ya sashi mik'awa Ummi.

"Barka da safiya Ummi."


"Barka dai Salisu ya kasuwa?."


"Lfy lau Alhamdulillahi, ya Saifuddeen da jikin?."


Cikin rawan murya tace. 

"To Alhamdulillahi jiki sai dai ace da sauk'i.

Amman yanzuma fa shiri akeyi wai za'a fiddashi k'asar India."

sai ta kuma share hawayenta tare da ci gaba da cewa. 

"Kuma sunce wai baza'a je daniba."


Cikin k'arfin hali Salisu yace. 

"Ba komai Ummi in sha zai samu lfy ki kwantar da hankalin ki, 

nima daga nan in na gama abinda nakeyi bazan dawo Nigeria ba zan wuce can india inga jikinshi kafin in dawo,

ki kwantar da hankalinki ai yanzu duniya a had'e wuri d'aya take."

sosai ya bata k'arfin guiwa sannan yace ta bawa Ahmad nan ta bashi suka gaisa. 


Daga nan duk suka tafi dan ganin azahar tayi kuma doctor yace su fita su bashi wuri ya huta.



Koda suka koma gidan Ya Rabi'u,

 sosai Aunty Mami tayi ta karfafawa Ummi zuciya har dai ta nitsu akan washe gari zasuyi sammako diraban ya Rabi'u zai maidasu Gombe kana ya taho dasu Rahma suma su ganshi kafin ya tafi.


Washe gari bayan an idar da sallan asuba Ayuba ya d'auki Ummi da Ishaq dan zasuyi sammako, 

jin zasu biya asibiti ne yasa Hayatuddeen cewa to zai bisu a saukeshi a asibitin. 


K'arfe bakwai dai-dai suka isa cikin d'akin da Saifudden yake.

Konce suka sameshi kamar ko yaushe yana tsabtace dan masu gyarashi na fita ne su kuma suka shigo.


Hannu ya mik'o ya kama na Ishaq tare da rubuta mishi text. 

"Please Ishaq ga Ummi na dan Allah kake yawan zuwa gida kana kontar mata da hankalin, 

kaga tare da Hayatuddeen zamu tafi, 

Raihana kuma itama in sunzo kawai ta koma d'akinta kada tace zata koma gombe, 

dan Saminu yace min shima ya kusa dawowa,

sannan akwai system na a motar Sule da k'aramar wayata, 

duk a bawa su Raliya su kawo min su."

cikin nitsuwa Ishaq yace. 

"In sha Allah ba damuwa nima da Ummin zamu zo ai mu dubaka,

ba matsala zasu zo maka dasu."


Ita kuwa Ummi cikin sanyi ta shafa kan Saifuddeen har zuwa goshinsa, 

cikin sanyi tace. 

"Babana zan tafi yanzu zamu koma gombe sunce ku kuma gobe zaku tafi india,."

sai ta kuma share hawayenta tare da ci gaba da cewa. 

"Zan tafi badon na soba sai dai kada suce na raina musu ne,

Allah ya k'addara saduwarmu kan al'kairi Allah ya baka lfy babana Allah yasa da akwai sauran ganawa a tsaka ninmu, 

Allah ya baka lfy."

da sauri ya jawo tafin hannunta ya mannashi bisa hab'arshi yana mai zubda wasu zazzafan hawaye wanda ganin hawayen mahaifiyar tashi ne yasa nashi zubowa.

Hayatuddeen kuwa hannu yasa yana share mata hawayenta, 

dai-dai lokacin Nurse d'in nan Amina ta shigo,

gefensu can ta tsaya tare da kallon Ummi dake kuka cur-cur da hawaye, 

da sauri ta sunkuyar da kanta dan itama idanunta sun cicciko da hawaye cikin danne rawan muryarta ta kalli Ummi tare da cewa. 

"Kiyi hak'uri Mama ki daina kuka in sha Allah zai samu lfy."

kai ta gyad'a tare da kamo hannun Saifuddeen d'in tace. 

"Allah ya baka lfy."

sai kuma tasa hannunta ta share hawayen fuskarshi dana Hayatuddeen kana ta juya da sauri ta fita.

jin motsin ta fitane yasa Ishaq yabi bayanta, kai tsaye inda Ayuba yayi parking suka nufa, 

suna shiga yaja mota suka fita daga asibitin suka nufi kama hanyar gombe.


A cikin room d'in da Saifuddeen ke ciki kuwa Ummi na fita Hayatuddeen ya zauna kan kujerar data tashi, 

ya kife kanshi gefen pillow Saifuddeen yana mai shesshek'an kuka a hankali, 

shi kuwa Saifuddeen rumtse idanunshi yayi yayinda wasu hawayen ke zubo mishi, a hankali Amina ta matso kusa dasu cikin nitsuwa ta iso gabansu, 

ido ta zubawa fuskarshi Hayatuddeen tana kallonshi tamkar Aminu k'aninta mai binta kusan komansu dai-dai da Aminunsu.

a hankali tasa hannu ta tallabo fuskarshi, 

ido ya bud'e jin an d'ago kanshi, 

kai ta jujjuya mishi alamun ya bar kuka, 

sai ta kuma zaro hankicib d'inta dake cikin al'jihunta ta mik'a mishi, 

hannu yasa ya k'arba sannan ya shinfid'eshi bisa fuskarshi, 

ita kuwa Amina a hankali ta juyo kan Saifuddeen wanda idanshi ke lumshe hawayenshi na zubowa suna gangarowa har cikin kunnenshi kasan cewar  konce yake a rigingine.


K'ara matsowa tayi gab dashi, 

yayinda shi kuwa yake kallonta ta tsakankanin gashin idanunshi.

hannu tasa dai-dai bisa hab'arshi sai kuma tayi saurin janye hannun tare da zuba mishi idanu, 

ganin idanshi a rufene yasa ta sake kai hannunta duka biyu a hab'arshi na gefen dama da hagu,

manyan yatsunta tasa can k'asa idanshi sannan tasa sauran yatsunta hud'un ta tare tsakanin hab'arshi da kunnenshi sai ta jawo manyan yatsun tannan a hankali tana koro hawaye suna gangarowa tsakiyar tafin hannunta.


Shi kuwa Saifuddeen wani irin razanennen bugu heart beat nashi yakeyi so fast,

shiru yayi tamkar baya numfashi, 

hakan ya bata damar share mishi hawayen kab ta tarasu cikin tafin hannunta,

sai ta had'e hannunta wuri d'aya ta murza ruwan hawayen nashi tare da shafa hannun nata a fuskarta kamar mai shafa mai.


idonshi ya bud'e tare da tsareta dasu, 

ita kuwa da sauri ta juya ta fuskanci Hayatuddeen,

sai kuma tayi saurin kauda kanta ganin Hayatuddeen yana d'aga mata girarshi tare da cewa. 

"Kin yi sa'a kin samu tabarrakin hawayen hammana."

allura ta ciro ta had'a kana ta mishi allurar sannan tasa hannu zata b'allo mgnin ta bashi sai kuma ta tsaya jin Hayatuddeen na cewa. 

"Kada ki b'are mgnin bazai sha abin hannunkiba in ba wonke hannunki kikayi ba."

ba tare da tace komaiba ta juya ta d'au goran ruwan dake gefenshi sannan ta d'an matso jikin window ta d'an bud'e window ta wonke hannunta sannan  ta juyo tazo ta bashi mgnin sannan ta juya zata fita tare da cewa.

"Ka fito ka barshi yayi bacci."

jin haka Hayatuddeen yabi bayanta, 

suna fita sukayi kicibis dasu Dr Adnan da Ahmad. 

nan ya juya ya shiga dasu Ahmad d'in. 


Sama-sama suka gaisa sannan suka fito suka tafi gida.


Shida dai-dai Ayuba ya iso dasu Rahma cikin asibitin kai tsaye ya musu jagora d'akin da Saifuddeen ke ciki.


Suna shiga suka samu Ahmad da Adnan. 

da Sauri suka k'aroso gaban gadon cikin rauni fuska cike da hawaye Rahma ta kamo hannushi  tana cewa. 

"Allah sarki d'an uwana ciwo bai mana adalciba k'addarar ka tayi mana mugun bugu a rayuwarmu."

Raihana kuwa ta kasa mgna sai kuka, dan dama duk ta fisu rauni da sauri hawaye Rahma cema mai d'an k'arfin hali.

Ahmad kuwa da sauri ya kamo hannun Raliya da ta kife kanta bayanshi tana kuka tare da cewa.

"Ya Ahmad shikenan Hamma Saifuddeen ya k'ara samun wata nakasar wai bazai sake tashi tsayeba."

Jawota gabanshi yayi tare ruggumeta yana shafa bayanta,

Ya Adnan ma hannun Rahma ya kamo tare da cewa.

"Da nasan haka zakizo kisa k'annenki a gaba kina kuka kina karya musu zuk'ata da na hanaki zuwa,

kalli kafin ku shigo munata hira dashi daga zuwanku kun birkitashi."

a hankali ta rink'a jujjuya mishi kai tare da share hawayenta.

sai kuma duk suka juyo suka kalli bakin k'ofa Hayatuddeen ne da Amina suka shigo a tare,

ganin yayunshi yayi saurin isowa tsakiyarsu ganin yadda Raihana keta kuka ya sashi kamo hannunta cikin sanyi da yanayinshi yace.

"Allah sarki Adda Raihana kiyi shiru, 

kinga ya Adnan yana rarrashin matarshi Ya Ahmad ma yanata lallab'a matarshi ke kuma sun shareki dan sunga Ya Saminunki baya kusa, to kiyi hak'uri d'an uwanki zai rarrasheki kema ki daina kuka kinga zakusa Hammanmu tashin hankali."

duk da kuka sukeyi saida suka d'an murmusa, 

Amina kuwa da sauri ta iso hannu tasa ta d'auki Affan dake kan gado kusa da Saifuddeen.

sai kuma ta bisu da idanu a cikin ranta take cewa. 

"Allah kenan mai kyauta da k'ari su kuma duk ahlinsu kyawawane tamkar larabawa."

A zahiri kuwa cikin sanyi ta gaidasu ganin Rahma da tsohon ciki ne ya sata jawo kujerar kusa da ita sannan tace.

"Ga wurin zama ki zauna."

da sauri Adnan ya zaunar da ita sannan ya kalli Raihana da har yanzu ta gaza tsaida kukanta cikin kula yace. 

"Raihana kiyi hak'uri."

kai ta sunkuyar jin Saifuddeen ya kamo hannunta da sauri ta matso kusa dashi, 

hannunshi yasa ya share mata hawayenta sannan ya mata alamun tayi shiru.

kai ta gyad'a tare da cewa. 

"Hamma Saifuddeen Ya jikin?."

Hayatuddeen ne yace.

"Jiki kam Alhamdulillahi da sauk'i."

Raliya ce ta kalli mijinta cikin rauni tace.

"Ya Ahmad wai gobe zaku tafi?."

Kai ya gyad'a mata kana yaja hannunta suka fita harabar asibitin

taxi suka shiga kai tsaye hotel mafi kusa ya kama musu a cewarshi wai zai rarrashi matarsa ya sama mata nitsuwa.

hakama Ya Adnan ma ya d'auki Rahma suka tafi,

Raihana kuwa nan suka zauna ita da Hayatuddeen da Amina da take ruggume da Affan tana shafa suman kanshi, 

amman sai mutsu-mutsu yakeyi alamun gajiya

ganin haka sai ta shiga bathroom wonka ta mishi sannan ta fito inda ta samu, 

sunata hirarsu da body language, 

cikin kula tacewa Raihana, 

"Gashi a bashi nono."

hannu tasa ta karb'eshi tare da cewa.

"Sannu ngd matuk'a Allah ya saka."

murmushi tayi tare da cewa "Amin Amin."

ita kuwa Raihana Hayatudden ta kalla tare da cewa. 

"Autanmu mik'o min hand bag na in sa mishi pampers da kaya."

da sauri ya mik'o mata Jakarta d'in, 

pampers ta fara sa mishi sannan ta samishi kaya, 

tuni kuwa yana shan mama kafin ta gama sa mishi kayan ma yayi bacci.

ita kuwa Amina allura tayiwa Saifuddeen tare da bashi magungunanshi,

tana gamawa ta juyo ta kalli Raihana da taga Saifuddeen na mata mgnar kurame, 

sai kuma taji Raihana na cewa. 

"To."

sai ta kuma mik'o mata Affan tare da cewa. 

"Please sis mik'a mishi Affan."

karb'an yaron tayi sannan ta matso kusa dashi ta kontar da yaron kusa dashi.

murmushi tayi tare da cewa. 

"Tab amman suna kama kam kamar d'anshi."

Murmushi Raihana tayi tare da cewa. 

"Haka babanshi ma ke cewa wai kamar Hamma Saifuddeen ne ya haifeshi."

Hayatuddeen ne ya d'an sosa k'eya tare da cewa. 

"Da yayi k'aton kai kuma sai ace dani yake kama."

dariya Amina tayi tare da cewa. 

"Ai kaima ba k'aton kaine da kaiba gashinka ne ba irin nasuba sun fika gashi mai sulb'i naka nada d'an tauri gashi ka tarashi da yawa."

daga nan sukayi d'an hira sannan Amina tace.

"Ni zan tafi naga Dr Aliyu na kirana, saida safenmu."

mik'ewa Raihana tayi tare da cewa.

"Muma yanzu zamu tafi."

Hayatuddeen kuwa cikin d'an d'aga sauti yace.

"Gobe zakizo da wuri ko kafin mu tafi?."

juyawa Amina tayi ta kalleshi sannan tace.

 "Aikin dare ne dani ai anan cikin asibiti zan kwana gobenma sai bayan azahar zan koma gida dan akwai aikin da zamuyi."

sunkuyowa yayi ya ciccib'i Affan ya sab'a a kafad'unshi sannan ya kalli Hammanshi tare da cewa.

"To Hamma saida safe."

kai ya gyad'a mishi kana ya kalli Raihana da take gyara mishi mayafin jikinshi tana mishi sannu.

suna gab da fita masu kwana dashi suka shigo, 

dan haka suka fita da sauri dan sunce suyi maza su tafi dan ya kamata ace yayi bacci yanzu. 


Suna fitane Hayatudeen ya mik'awa Amina wayarshi tare da cewa. 

"Yauwa samin number ki."

karb'a tayi tasa mishi number ta sannan ta mik'a mishi wayar tasa, 

daga nan sukayi sallama ita tayi office d'in doctor Aliyu, 

su kuma Ayuba ya d'aukesu suka tafi gidan Ya Rabi'u.


Ya Adnan kuwa yana zaune shida Rahmanshi yaji shigowan sak'o a hankali ya jawo wayar tashi yana dubawa yaga alert ne cikin mmki ya zaro idanu ganin kud'in har naira million uku a hankali yace. 

"Jonapwd, k'ungiyarsu ishaq ne kenan fa to kud'in meye wannan?."

da sauri ya amsa kiran ishaq da ya shigo wayarshi yanzu cikin kad'uwa yace. 

"Salamu alaikum ishaq wannan kud'in fa?."

cikin nitsuwa yace.

"Tallafin k'ungiya ne kan jinyar cutar Saifuddeen, a wurin adda Rahma na samu account number ka, da zan tura a account d'in Saifuddeen to nasan ay yarda ayi amfani da kud'in in ya yardama nasan in ya dawo zaice zai maidawa k'ungiya kud'inta, Shiyasa nake neman al 

'farma kada ku gaya mushy,Ya Rabi'u ma  ya turawa Ahmad one million zaku d'an rik'esu dan hidimar da yawa shima Ahmad saida ya Rabi'u ya nuna b'acin kafin ya amince da kud'in."

sosai ya Adnan yayita godiya yayinda shi kuma da al'jihunshi ya biya kud'in jirgin shida su baki d'aya.

Rahma kam har kuka tayi tanayi musu godiya. 

 

 


Washe gari k'arfe tara dai-dai duk suna cikin asibitin dan k'arfe tara da rabi jirginsu zai tashi.


Suna cikin d'akin masu kula dashi sun canza mishi kaya sun gyarashi, 

Dr Adnan kuwa yana office d'in Dr Aliyu, 

yana bashi duk wasu takardun binciken lafiyar da sukayi mishi.


Rahma, Raihana, Raliya, Hayatuddeen,  Ahmad, Ya Rabi'u kuwa duk suna wurin Saifuddeen d'in 

Amina ce ta shigo cikin nitsuwa tazo ta bashi magungunanshi sannan ta had'a sauran ta kullesu a leda tare da mik'awa Dr Adnan daya shigo yanzu,

yana cewa. 

"Rahma ku fito ku tafi Ayuba na jiranku, 

zai fara biyawa kaduna ya sauk'i Raihana ku kuma zai wuce daku gombe,

Raliya ki kula da Ummi sosai."

Ahmad ne ya kalleta tare da cewa. 

"Goggo Dada ma taje tana can dan gaba d'aya Ummi bata cikin nitsuwa shiyasa nacewa Goggo Dadan taje ta d'an d'ebe mata kewa na kwana biyu."

kai ta jinjina tare da cewa. 

"Allah ya kaiku lfy ya bada sa'an aikin da za'ayi mishi."

Amin Amin sukace baki d'aya, 

sannan Adnan ya kalli Rahma cikin kula yace.

"Please ki kula da kanki kada kiyi ta kuka, 

kinga kinada larurar da ba'a son kina yawan shiga damuwa,

kiyi ta shan mgninki kan lokaci, 

nima Next two weeks zan dawo in Allah ya yarda."

kai ta gyad'a kana ta mik'awa Saifuddeen hannu sukayi musabaha tare da cewa. 

"Ka yafe min d'an uwana ban saniba ko in haihu lfy ko akasin haka, 

in Allah yasa da sauran ganawarmu to Allah ya had'amu kan Al'khairi in kuma baka dawo ka sameni a rayeba, 

amana da tarbiyar su Faruq tana gareka."

ina Raliya kam juyawa kawai tayi ta fita,

hakama Raihana sai dai ita tana kuka ta fita, 

ita kuwa Rahma shafa fuskarshi tayi tare da juyawa tabi bayan k'annenta,

tana isosu ta shiga mota Ayuba yaja suka tafi.


Su kuwa Hayatuddeen ne ya had'e woyoyin Hammanshi ya zurasu a jakar system d'in shi sannan yabi bayan Ya Ahmad da Dr Adnan dake biye da bayan Nurses guda biyu da suke rik'e da d'an k'aramin gadon da ake d'aukar masu irin larurarshi.


Cikin motar asibiti suka sashi, 

Ya Adnan ne ya shiga sannan driver ya shiga suka tafi Airport. 

Ahmad da Hayatuddeen kuwa Ya Rabi'u ne ya d'aukesu a motarshi sukabi bayansu, 

k'arfe tara dai-dai suka shiga cikin international airport Abuja.


Bayan duk matafiya sun shiga kowa ya zauna mazauninsa, 9:30 Am jirginsu ya d'aga zuwa k'asar India cikin babban birnin New Delhi.


Bayan lokaci mai tsawo suna ratsa gajimare jirginsu yayi sauk'an ank'ulu cikin Indara Gandhi international Airport Delhi.


Bayan duk an fito ma'aikatan lfy na cikin jirgin suka fito da Saifuddeen wanda yana bacci. Ahmad da Dr Adnan da Hayatuddeen suna biye dasu a baya har gaban wata motar asibiti, 

nan suka shiga kai tsaye driver yaja suka tafi, 

kusan tafiyar awa d'aya da rabi sukayi sannan suka isa cikin harabar wanni tamfatsetsen asibiti mai tsananin azabar kyau da d'aukar hankali,

suna fitowa Ahmad da kanshi ido ya zaro tare da cewa. 

"Tsarki ya tabbata ga ubangijin talikai mai sammai da k'assai."

Dr Adnan da kanshi kyawun asibitin yayi matuk'ar girgizashi,

Auta kuwa a hankali Hayatuddeen ya zuro k'afafunshi daga cikin motar,

fitowa yayi tare da d'aga kanshi ya zaro idanshi da k'arfi ya kalli can! can!! can!!! Saman bene na k'arshe inda ya zubawa rubutun sunan shahararran asibitin da duniyar New Delhi ke ji dashi. 

*SUPER SPECIALTY SAFDARJUNG HOSPITAL* da sauri ya dawo da kanshi k'asa a hankali yayi wani irin s...! 





                           BY

                   *GARKUWAR FULANI*

8/18/20, 7:53 PM - Ummi Tandama: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


        *NAKASA BA KASAWA BACE*


                               *PAGE 20*


                            NA

         *AYSHA ALIYU GARKUWA*



🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇





Sassanyan ajiyan zuciya yaja a hankali,

ido ya lumshe tare da bud'esu ya juya ya kalli gabas da yamma kudu da arewa, a fili yace. 

"Gari banban Allah d'aya." 

Ahmad ne ya juyo ya kalleshi tare da cewa. 

"Ko wanne wuri da irin kalar ni'imar da Allah yake musu."

da sauri suka juyo suka kalli ya Adnan dake ce musu.

"Ni zan shiga ciki zamu isa wurin Dr Acash prasat zan kama mana layi, 

duk dai Dr Aliyu ya mana hanyar ganinshi a watannan to dole sai munbi layi.

So kai Ahmad ga can taxi ku shiga sai ku duba mana hotel nan kusa mu samu masauk'i."

cikin gamsuwa da hakan Ahmad yace.

"To ba matsala bari mu d'auki kayan mu."

Shi kuwa Hayatuddeen da sauri yabi bayan nurses da suka fito da Saifuddeen dake kan gado, 

yana isa ya bawa Saifuddeen hannu tare da cewa.

"Zamuje nan kusa, ya Adnan zai shiga ciki da kai."

kai ya gyad'a mishi alamar sai sun dawo hakama Ahmad yazo ya salla meshi sannan Dr Adnan yabi bayansu, suka nufi cikin ainihin asibitin,

tafiya kad'an sukayi suka ratsa cikin wani babban corridor mai girma, 

tafiya yar kad'an suka isa bakin wata babbar k'ofa, 

suna bud'ewa wasu nurses d'in suka  karb'eshi, 

kana wad'an nan suka juya sukayi baya, 

su kuma wannan da suka k'arbeshi sai suka canza mishi gado suka d'auranshi kan irin k'ananun gadajen tura marasa lfyn,

sannan da sauri Dr Adnan kuwa ya mik'a d'aya daga cikinsu wata takarda,

bayan ya karb'a ya duba sai ya juyo ya kalli d'aya nurse dake tura gadon yayi mishi mgna cikin indiyancin.


Sai kuma suka canza hanya suka fuskanci wani ratsetsen gini mai azabar kyau amman shi ba benaye bane. 

suna isa harabar wannan wurin wasu nurses d'in suka karb'eshi kana suka basu wannan takardar da takeda tambarin National Hospital Abuja, 

a k'asa kuma ga sa hannun Dr Aliyu,

can gefe kuma ga shaidar transfer zuwansu wannan asibitin da.

shi dai Dr Adnan binsu yake a baya.

A hankali suka bud'e wata k'ofa mai girma suka shiga Dr Adnan na biye dasu a baya, 

yana sa k'afarsa cikin  Reception d'in nasu yayi wani irin ajiyan zuciya dan wani azabebben sanyi da ya cika wurin,

gaba d'aya reception d'in cike yake mak'il da mutane duk da girmanshi sai dai  duk ana zaune bisa tsari ba hayaniya, 

shi kuwa Saifuddeen kanshi ya d'an juya ya kalli gefen hagunshi da damanshi, 

jerin gadaje ne a gefen hagunshi mutane na konce a Kai,

d'aya gefen kuwa kekunan weelchair ne a jere wasu na zazzaune a ciki.

gefen gadajen aka tura gadon da Saifuddeen ke kwance, 

sannan nurse d'in ya yafito Adnan kana suka nufi gaban inda nurses ke zaune suna bada kati dama masu bud'e folda

suna isa suka mik'awa d'aya daga cikin matan dake wurin takardar,

mgna suka d'anyi cikin yarensu da Adnan baya ji ya dai ji suna kiran Nigeria,

sai kuma nurse d'in da aka kira da Divia ta juyo ta kalli Adnan tare da mishi tambayar ina fayel nasu na asibitin da aka turosu nan cikin  turanci.

Da sauri ya mik'a mata fayel d'in amsa tayi sannan ta had'a da takardar da wannan d'in ya bata, 

juyawa tayi ta d'auko polder sannan ta bud'e wanna fayel d'in kana ta d'auki biro ta fara rubutu a saman poldern sai kuma ta fara bud'a fayel d'in nan ta d'anyi 'yan rubuce-rubuce sannan ta mik'awa Adnan hand card data zaro cikin polder d'in, 

amsa yayi ya duba kasan cewarshi Dr ras ya gane rubutunsu na doctors da yafi kama da jagwalgwale, 

kai ya jinjina ganin bata saurari tambayarshi sunan mara lfy da shekaru ba duk ta samesu  cikin fayel d'in da suka zo dashi.

kai ta sunkuyar kana ta matso kusa da system d'in dake gabanta a hankali ta fara sassarafashi, 

daga bisani ta d'ago kai tace mishi yaje ya zauna za'a nemeshi. 


Gefen da Saifuddeen yake yaje, 

nan ya samu  yana bacci dan ya samu irin sanyin da jikinshi ke buk'ata, kasan cewar masu larurar cutar lakar jiki suna da yawan jin zafi, shiyasa suƙe matuƙar so da jin daɗin wurin dake wadace da tsabta da sanyi,

fita yayi daga cikin wurin  hanyar da suka bi sukazo ita yabi d'an suna wucewa yaga wani d'an k'aramin masallaci a hanyarsu, 

yana isa wurin yayi Al'wala kana yayi sallan azahar da la'asar da niyar k'asaru. 

yana idarwa ya mik'e da sauri ya koma.


Still har yanzu yana bacci hakan ne yasa ya koma gefe ya zauna, 

yana kallon yadda aketa shiga da fita. 


In an d'an jima wata nurse ta fito ta d'ebi wasu polder ta shiga dasu, 

hakama wata bisa dukkan alamu likitocin guda uku ne suke duba marasa lfyan, 

a hankali ya fara kallon rubutun dake saman k'ofofin office d'in na forko ansa Dr Biru Sahastara Dubbe, 

sai na tsakiyar da akasa Dr Acash prasat,

sai na k'arshen da aka saka Dr Abdul Malik Khan.

kai ya meda ya jingina da kujera dan ganin dare ya rufa, 

kuma da yawa sunata fita.


Da sauri ya d'ago kanshi jin motsin bud'e k'ofa ta tsakiyar nan, 

ido ya zubawa saman aljihun rigar mutumin inda aka rubuta Dr Biru S D,

ga kuma nurses guda biyu suna biye dashi a baya yayinda wani kuma yake rufe k'ofar office d'in.

Bai gama nazartan mutuminba ya kuma hango an bud'e d'aya k'ofar ido ya zubawa saman al'jihun rigarshi inda aka rubuta Dr Malik Khan.

tafiya yakeyi cikin nitsuwa kanshi d'auke da hular tab'a kaji hadis ɗin nan,

bisa dukkan alamu nurses dake binshi a baya ma, 

musulmaine, 

yana isowa tsakiyar Reception d'in sai ya d'aga hannunshi duka biyu ya fiskanci mutanen dake gefen damanshi yace.

"Assalamu laikum."

kad'an daga ciki da suka kasance musulmai ne suka amsa da. 

"Wa alaikassalam."

sai ya kuma d'an tsayawa tare da kallon marasa lafiyan kana yace. 

"Lah ba'as d'uhuru in sha Allah."

sai ya kuma juya gefen hagunshi in da ya kuma yi musu sallama, 

kasan cewar Adnan ne kad'ai musulmi a layin shiyasa shi kad'ai ne ya amsa da. 

"Wa alaikassalam."

cikin kula ya kalli Adnan tare da mishi murmishi ya tambashi shi d'an wacce k'asar ce. Cikin jin dad'i  Dr Adnan yace. 

"Nigeria."

sunanshi ya tambayeshi ya gaya mishi sanna ya kuma tambayarshi su sabbin zuwa ne ko,

dan duk wad'an nan sauran sun kai kwana huɗu zuwa biyar suna bin layi, 

kuma ba'a fara k'arb'an sabbin zuwa ba.

mik'ewa Dr Adnan yayi ya matso kusa dashi cikin nitsuwa da iya sarrafa harsher ya mishi bayanin da zai fahimta sosai a matsayinsu na doctors kuma kusan duk abu d'aya suka karanta, 

ya k'ara da mishi bayanin doctor daya turosu da kuma sani Dr Acash prasat.


Kai ya jinjina cikin gamsuwa sannan ya tamb'ayeshi ina mara lfyan,

da sauran ya nufi gadon Saifuddeen binshi yayi a baya cikin k'are mishi kallo yake tambayarshi wai Saifuddeen ba d'an Nigeria bane ko.

cikin sakin fuska Dr Adnan yace mishi cikekken d'an Nigeria ne.

kai ya rusunar ya shafa sumar kan Saifuddeen tare da tambayar Dr Adnan wai to shi wacce k'abilane.

sosai Dr Adnan yayi murmushi dan ya fahimci Dr malik irin mutannane masu raha da sauk'in kai jin suna k'abilar Saifuddeen Fulani sai yacewa Dr Adnan, 

to k'abilar tanada alak'a da indiyawa ko wai sabida Africa ba irin masu kamarsu?

dariya sukayi baki d'aya sannan yacewa Dr Adnan  ai tun d'azu Dr Acash ya bar cikin asibitin nan shi da zuwa kuma sai gobe da rana.

sai ya kuma k'ara da cewa. Tunda yau kukazo baku samu an dubashi bama ba,

ni zan d'an taimaka muku zan had'aku da Divia zata barku ku kwana a nan sashin, 

sannan zan bar wancan nurse d'in ya gyara mishi jikinshi da mishi abinda ya dace."

cikin jin dad'i Dr Adnan ya mishi godiya.


haka kuwa akayi, 

nan Divia ta nuna musu wurin da zasu fake sannan nurse d'in nan namijin nan ya gyarawa Saifuddeen jikinshi, sannan ya taimaka mishi yayi al'wala kana yayi niyar salla ya fara biyan sallolin da bai samu yayiba.

Shi kuwa Ya Adnan fita yayi ya tambayi inda zai samu abinda zai saya musu suci.

Wani k'aton Restaurant dake cikin asibitin wanda ana yin kalan abincin ko wanne k'asa, 

Snacks and drinks ya samo musu sannan ya koma ya tallafawa Saifuddeen ya d'anci sannan shima yaci kana ya koma gefe ya konta bisa kujerun silver dake wurin. 



Su Ahmad kuwa suna shiga taxi d'in suka cewa drivern ya kaisu hotel mafi kusa da asibitin,

to yace musu kana ya ja motar suka fita daga harabar adibitin tafiya kad'an sukayi sukaga ya ratsa cikin wani tamfatsetsen hotel mai azabar kyau da tsari na zamani,

suna fitowa Ahmad ya zubawa sunan hotel d'in idanu.

Hyatt regency Delhi, ido ya zubawa benayen da sukasha k'awanya da abubawan alatu na duniya, 

da sauri Ahmad ya koma cikin motar kana ya kalli Driver tare da cemishi. 

da ganin wannan hotel d'in zaiyi tsada, to in dai da akwai wani k'arami a nan kusa ya ka kaisu.

kai driver ya jujjuya mishi tare da mishi bayanin cewa babu wani hotel nan kusa in banda wannan sai wani dake gabanshi kad'an kuma duk tsadarsu d'aya, 

ya k'ara da ce musu gwara kuma su kama wannan d'in zasu huta da biyan kud'in texi na zirga-zirgan zuwansu da dawowa, 

ya shaida musu ko an bashi gado baza'a barsu su zauna dashi ba, dan akwai masu kula dasu. 

jin haka yasa dole suka fito, 

Direct reception d'in hotel d'in suka nufa, 

suna zuwa Ahmad ya k'arb'a musu d'aki d'aya tare da biyan kud'in sati biyu duk da yawan kud'in ya bashi tsoro to amman ya zaiyi.


Key aka basu bayan an rubuta sunayensu da time and date na zuwansu cikin littafin ajiyan shige da ficen mutane.


Hayatuddeen ne ya ciccibi 'yar ma dai-dai ciyar jakarsu, 

sannan yabi bayan Ahmad da d'aya daka cikin workers nasu da zai nuna musu d'akin da yake can saman bene na hud'u kasan cewar lifta ne cikin k'ank'anin lokaci suka isa, 

suna isa ya bud'e musu k'ofar tare da juyawa ya fita, 

suna shiga, 

Hayatuddeen ya ajiye jakar hannunshi tare da zuwa gaban TV, 

kunna tibin yayi sannan ya dawo ya zauna bisa lumtsuma-lumtsuman kujerun da sukayiwa parlour k'awanya, 

ido ya lumshe sannan ya bud'esu yabi bayan Ahmad da kallo, 

shi ko Ahmad bedroom ya wuce kai tsaye cikin bathroom ya nufa, 

wonka yayi mai rai da lfy sannan yayi al'wala kana ya d'aura towel d'in daya samu a ninke sabo dal cikin ledsnshi ys farkeshi, komai na wurin sabo.

yana fitowa ya koma parlour ya d'auko jakar kayan nasu yazo ya dawo bedroom d'in k'ananan kaya ya saka fitowa yayi ya koma parlour gefen Hayatuddeen ya zauna tare da cewa. 

"Je kayi wonka kazo muje mu samu abinda zamu ci, 

mu kuma sayi sim card na k'asar tasu."

da sauran Hayatuddeen ya mik'e tare da cewa. 

"To." shi kuwa Ahmad ido ya zuba mishi ganin yadda yake cilla kayanshi tsakiyar parlour, 

baki ya bud'e ganin ya tsallake wondenshi a inda ya cireshi, 

kuma ko a jikinshi ya nufi bedroom,

kai tsaye bathroom ya shiga bayan yayi wonka yayi al'wala sannan ya fito, 

gaba d'aya kayan cikin jakar saida ya fiddasu ya zubesu bisa gado sannan ya saka wani wondo 3 quarter pink color  sai rigarshi mai yankekken hannu  white Color,

sosai kayan sukayi mishi kyau.


Shi kuwa Ahmad a fili yace. 

"Wato haka Raliya ke fama da rigimar Autan Ummi."

dai-dai lokacin kuma ya fito tare da cewa.

"Na fito ya Ahmad muyi sallan muje muci abinci yunwa nakeyi."

cikin had'e fuska Ahmad yace. 

"To wa zai tattara maka kayan daka watsar d'in?."

kai ya d'an longob'ar tare da cewa. 

"Ni ban iya tattarewa ba ya Ahmad."

tsaki Ahmad yaja tare da cewa.

"Zaka ma koya ai, dan nima ban iyaba."

sai ya kuma fuskanci al'k'ibila ya tada kabbara ganin haka shima Hayatuddeen yabi bayanshi,

bayan sun idar da sallolin nasu ne suka sauk'a reception sukayi tambayar ta ina Restaurant yake nan aka kwatanta musu sannan, 

suka nufi wurin suna isa sashin. Restaurant ɗin.

Mathuramakrishna viswanathun.

Hayatuddeen ya isa gaban teburin da yaga an rubuta Africa food, gefe d'aya ya juya inda yaga ansa Nigerians food is ready,

sai kuma ya juyo jin Ahmad yana ce mishi, 

"Ni ka amso min feesh  roll,."

to yace sannan ya saya musu duk abinda suke buk'ata sannan suka juyo, 

suna dawowa reception d'in suka gayawa ma'aikatan wurin  cewa suna son sayan SIM card,

kud'in sukace su kawo zasu sayar musu dan suma suna saidawa, 

nan suka basu kud'in layukan da kuma kati sannan suka musu register tare da karb'an woyoyin suka saka musu layukan sannan suka saka musu katin, 

ganin tuni lokaci d'aya layin ya hau yasa suka haura d'akinsu.


Suna isa suka zauna a parlour sukaci suka sha, 

ganin ko kad'an Hayatuddeen bai damu da kanshi dake watseba yasa Ahmad  mik'ewa ya tattarusu ya shiga bedroom dasu, 

nan kuma  yayi arba da kayansu daya wancakalar 

hannunshi d'aya yasa ya tokare k'ugunshi kana yasa d'aya ya dafe goshinsa tare da cewa. 

"Wayyo ni Ahmad jikan Ahmad naga ta kaina da aka had'ani da wannan sangartaccen Ummin."

dole ya kimtsa komai. 


Shi kuwa Hayatuddeen a parlour ana ya konta tuni bacci ya fara d'ibanshi. 

Ahmad da ya gama tattara abinda ya watsanne ya dawo parlour ya tada Hayatuddeen tare da cewa.

"Ka tashi mu koma asibitin mana."

cikin gengyad'i yace.

"Ya Ahmad dare yayi sosai fa ka bari da asuba muje."

da wannan shawarar ya koma bedroom ya konta.

Dan akwai gajiyar tafiya tare dasu. 


Washe gari suna idar da sallan asuba,

suka fito suka kama hanyar da zata sadasu da asibitin, 

tafiya kad'an suka shiga cikin asibitin.


Daga bakin  harabar wurin, 

suka fara tambaya da tambayar suka samu suka isa har office d'in Dr Acash prasat dan dashi suke tambaya, 

suna shiga cikin wurin suka hango Adnan zaune bakin mashigar inda suka kwana, 

da sauri suka iso gunshi, 

Ahmad ne ya fara bashi hannu,

bayan sun gaisa ne, 

yace musu ana mishi wonka ne,

jin haka yasa Ahmad ya bashi SIM card d'in da suka saya mishi da key d'in d'akinsu ya kwatanta mishi yace.

"Kaje kayi wonka ka samu ka canza kaya ka kuma d'an ci abinci kafin ka dawo, wata k'il Dr yazo."

 haka kuwa akayi ya amsa ya tafi, 

su kuma suka zauna koda aka gama kimtsashi.

Hayatuddeen ne yaje ya samo mishi abinda zaici, 

daga nan sukayi ta hira dashi har zuwa  lokacin da Ya Adnan ya dawo, 

nan sukayi ta zaman jira sai bayan azahar Dr Acash yazo, 

haka sukayi ta bin layin ranar amman ina ranar basu samu damar ganinshi ba,


 the next day ma haka sukayi ta bin layi, har kusa k'arfe biyar na yammansu sannan suka samu damar shiga.


Suna shigar da Saifuddeen Dr Adnan yabi bayansu,

d'aya daga cikin nurses da suka shigar da Saifuddeen d'inne ya nunawa Dr Adnan wurin zama,

bisa wasu kujeru guda biyu dake gaban wani babban  table,

wanda d'aya sashin shi kuma kujera d'aya ce, 

wacce Doctor Acash prasat ke zaune,

kekyawan ba indiye ne,

fayel d'in da Saifuddeen da nurse ta bashi ne ya fara bubbud'ewa yana duddubawa, 

yayinda Dr Adnan kuwa ya zauna gabanshi,

sauran nurses d'in kuwa suke ta kiciniyar kontar da Saifuddeen bisa wani d'an gado dake gefen doctor.


Suna gamawa suka koma gefe suka zauna, 


Da sauri Dr Adnan ya d'ago kanshi cikin mmki yake kallon Dr Acash da yake mishi mgna cikin yaren hausa.

"Tun shekaran jiya Dr Aliyu yace min kun iso, 

kuyi hak'uri abin ne da yawa."

cikin nitsuwa Dr Adnan yace. 

"Ba matsala, d'azu mukayi mgna da Dr Aliyu ma."

juyawa yayi ya kalli Saifuddeen dake konce a rigingine, 

sai ya kuma meda dubanshi ga fayel d'in, 

kana ya bud'e poldernsu ya fara 'yan wasu rubuce-rubuce kusan tsawon 4 minutes sai ya kuma ture takardun sannan ya jawo system dake gabanshi still rubuce-rubucen yayi, sannan ya d'ago kanshi ya kalli Dr Adnan cikin bagwariyar hausarsa da zamanshi da Dr Aliyu ne yasa ya iya yace.

"Forko dai yanzu za'ayi mishi gwajin, X-ray CT scan MRI scanning  wanda ko wanne d'aya   N95,000. ne

sai kuma Surgery da ya kamata ayishi kan lokaci d'an yanzuma lokaci ya d'an fara ja,."

cikin gamsuwa da bayaninshi Dr Adnan yace. 

"Surgery d'in kuwa zai kai nawane?."

kai ya d'an rusunar sannan ya d'anyi dube-dube a system d'in sannan ya d'ago kanshi ya kalleshi kana yace.

"N2.5 million."

A hankali Dr Adnan yace. 

"Ba matsala a fara aiki."

mik'ewa yayi ya nufi gaban gadon da Saifuddeen yake a hankali yasa hannunshi ya fara jan 'yan yatsun Saifuddeen amman shiru bai kulaba a hankali ya fara bin k'afafunshi yana d'an lallatsawa still Saifuddeen baya ji bare ya bud'e idonshi, 

sai yaci gaba da tattab'ashi tare da juyawa ya kalli Dr Adnan dake tsaye bayanshi cikin kula yace.

"Naga kurmane shi ko?."

kai ya gyad'a mishi da sauri, 

cikin meda hankalin shi kan Saifuddeen yace. 

"In ba matsala in kunada hali musa doctor kunne a cikin aikinshi mana."

jim kad'an Dr Adnan yayi kana ya d'an matso doctor Acash d'in tare da cewa.

"Dr kanaga zai worke ne?."

da sauri ya jujjuya mishi kai tare da cewa. 

"Wannan ai sai Doctord ɗin kunnen ne zasu bamu amsar nan in sun dubashi,

sai dai muna zaton zai worke tunda ba haifarshi akayi da kuramtarba ko?."

da sauri Dr Adnan ya gyad'a mishi kai tare da mishi d'an k'arin bayanin yadda ya samu larurar kuramta, 

kamar yadda yayiwa Dr Aliyu a Abuja.

dawowa sukayi suka zauna bisa kujerun da suka tashi nan suka fara musanyan basira da shawara a matsayinsu na Doctors, 

sosai Doctor Adnan ya k'ara samun haske a lamarin sashin aikinshi dan zama da kwararran Dr da yayi na awa biyu.

da yawa suna kwarafin cewa shi Dr Acash in an aka shigar da mutun ba'a fitowa da wuri, 

shi kuwa k'a'idar aikinshi ne ya binciki marasa lfy da kyau a nitse ya kuma samu cikikken bayani daga bakin mara lfyar ko iyayenshi.

Shiyasa yake dad'ewa da mutane, 

shiyasa kuma mutane ke son ya dubasu,

anan take ya kira wani doctor da yake kula da sashin kunne.

Ba jimawa ya shigo nan sukayi 'yan  dube-dubensu,

daga bisani nan take aka fara aikin gudanar da gwoje-gwajensu.

Saida suka gama duba komai sannan aka fitar dasu,

aka kaisu room d'in da za'a kwantar dashi zuwa gobe in sun duba sakamakon awun nasu. 

nan ya bawa Dr Adnan number shi cewa gobe in sunzo ya shaida mishi. 


D'akin babba ne mai kyau gadaje biyu ne a cikin d'akin sai kujeru guda biyu ko wanne gado da kujera d'aya,

bayan sun gama komai nan suka zauna su dukan su uku Hayatuddeen yana gefen Saifuddeen,

Ahmad kuwa yana tsaye gaban Dr Adnan da yake musu bayanin yadda sukayi da Dr da kuma gwoje-gwojen da akayi da kud'ad'ensu.

ganin lokacin salla yayi ne sukayi al'wala sannan suka tafi masallaci, sukayi salla magrib nan suka d'an jira lokacin isha yayi, hankalin konce sukayi salla dan sun san akwai masu kula da Saifuddeen.


Bayan sun idar sun koma ne suka sameshi kwance amman an d'an d'aga kan gadon in ka ganshi zakace a zaune yake irin ya d'an jinginane,

da sauri Hayatuddeen ya zauna gefenshi tare da cewa. 

"Sannu Hamma Saifuddeen ya jiki?."

kanshi ya jinjina alamun da sauk'i sannan ya kuma mishi mgna cikin body language yake tambayarshi ya labarin Ummi.

da sauri Ahmad yace. 

"Ummi tana lfy tace a gaidaka."

murmushi yayi cikin jin dad'i sannan ya kalli Hayatuddeen dake cewa. 

"Bari in kira Raliya video call sai ku gaisa da Ummin."

matsowa yayi kusa dashi ya zauna gab dashi kana ya kira Raliya sannan ya kaikace woyar tashi ya matso da kanshi jikin Hamman nashi  duk suka fuskanci wayar.


A can gida Nigeria kuwa dai-dai lokacin Raliya na zaune gaban Ummi da take ce mata. 

"Tunda sukaje basu samu damar ganin Dr bama, ni gaba d'aya hankalin na a tashe yake."

da sauri Raliya tace. 

"Yauwa Ummi dama abinda ya kawoni kenan fa yanzu mukayi mgna da Ya Ahmad yace min yau sun samu ganin Dr kuma Alhamdulillahi duk gwajin da ake buk'ata anyi, zuwa gobe sakamakon zai fito."

ajiyan zuciya tayi tare da cewa.

"Alhamdulillahi."

sai kuma tayi shiru jin Raliya na cewa yauwa gama Auta na kirana."

da sauri tace amsa kiran."

Da sauri tayi picking call d'in murmushi tayi ganin fuskar yan uwanta duk suma suna mata murmushi da sauri ta yunk'ura ta dawo gefen Ummi ta saita fuskarsu da fuskare wayar,

suna kallon junansu,

wani irin faffad'an murmushi Ummi tayi ganin fuskokin yaranta cikin happy tace. 

"Alhamdulillahi babana ya jikin?."

kai ya d'an rausayar tare da yin yalwataccen murmushi,

Hayatuddeen kuwa cikin tankwara wuya yace. 

"To wai ni kam bakuyi missing na bako kallifa Ummi ko ki kulani ninefa autanki."

dariya tayi har saida wushiryanta ya baiyana sannan tace. 

"Nayi kewarka mana autana."

da sauri Raliya tace. 

"Ni dai banyi kewarka ba dad'i ma nakeji na huta da tattaren kayanka yanzu gidanmu baya hargitsewa tunda ka tafi."

dariya yayi sosai sannan yace. 

"Wayyo yarinya ai in ke kin huta mijinki bai hutaba yaseen watsar da komai nakeyi son raina Ya Ahmad ke tattaremin, 

Yau da safe harda boxer na ya wonke min da zai wonke nashi."

da sauri yayi shiru tare dasa hannu yana shafa k'eyarshi da Ahmad ya bugi yana mai cewa. 

"Wato kama maidamu bayinka nida matata."

cikin jin dad'i Raliya tace. 

"Yauwa ya Ahmad buge minshi da kyau, kuma ka dena tattare mishi komatsanshi."

Saifuddeen kuwa hannu yasa ya jawo kan Hayatuddeen ya manna da kafad'arshi sannan yasa tafin hannunshi yana shafa mishi inda Ahmad ya d'an buge mishi.

murmushi yayi tare da cewa. 

"Kada ya tattara mana ba sai muyi ta zama cikin dottiba."

cikin jin dad'i Ummi tace.

"Kai Autana ka fara girma fa ka rink'a womke guntayem wondunanka da kanka kaji ko?."

kai ya gyad'a mata sannan ya mik'awa Dr Adnan wayar cikin kauda kanshi yace.

"Barka da dare Ummi ya gida."

sunkuyar da kanta tayi cikin kunya irin ta surkai tace. 

"Lfy lau Baban Adam ya mai jikin?."

A mutunce yace.

"Alhamdulillahi Ummi jiki da sauk'i yau mun samu munga likita, 

nanda kwana biyu za'ayi aiki, ki kwantar da hankalin ki in sha Allah zai samu lfy."

cikin samun nitsuwa tace. 

"Allah yasa."

Amin Amin sukace baki d'aya sai kuma tace. 

"To ni kuma sai yaushe zan zo in dubashi?."

Da sauri Ahmad ya koma gefen Adnan d'in kana yace.

"Ummi ki kwantar da hankalin ki bari in an mishi aikin munga yanayin jikin sai kizo."

shiru tayi kamar dai bata gamsuba sai kuma Dr Adnan yace.

"Ki bari sai anyi aikin, dan nima in anyi aikin zan dawo, 

in yaso in na dawo sai ki zo ko?."

a hankali tace.

"To ba matsala Allah ya bada sa'an aiki."

Amin Amin yace sannan ya kalli Raliya tare da cewa. 

"Ina Faruq?." a hankali tace. 

"Yana d'aki wurin Goggo Dada wai sai ta mishi tatsuniya daga nan duk sukayi bacci."

"Ki gaida min shi, gobe asabar yaje gida mana yayi hutun sati a wurin Mamanshi."

cikin nitsuwa tace. 

"To ba matsala, ka gaida Hamma da jiki mun gode Allah ya saka ya bar zumunci."

Amin Amin yace sannan suka sallami juna. 


Sosai Ummi ta samu nitsuwa da sukayi hirar.


Su kuwa suna gama woyar Ahmad ya gyarawa Saifuddeen konciyarshi, 

dan ganin ya fara lumshe ido, 

a hankali Ahmad ya kalli Dr Adnan tare da cewa. 

"Ya Adnan kuje masauk'inmu kaida Hayatuddeen ku kwana bari ni in kwana dashi, kaje ka samu ka huta."

kasan cewar akwai gajiya a jikinshi yasa ya amince, 

tare suka tafi shida Hayatuddeen shi kuwa Ahmad ya kwana nan wurin Saifuddeen.


D'aya gadon ya hau ya kwanta yana kwanciya Bappa Ali na kiranshi wanda shi kuma kawunshi ne yayan mahaifiyarshi da sauri ya amsa kiran. 

"Salamu alaikum."


"Wa alaikassalam."


"Ina wuni Kawu Ali."


"Lfy lau Alhamdulillahi Ahmad ya jikin Saifuddeen?."


"Jiki da sauk'i Kawu yau mun samu munga Doctor."


"Eh haka dai Mudassir ke sanar min yanzu wai sunyi waya da Yayanshi Adnan."


gyara konciyarshi yayi tare da cewa.

"Na kira d'azu ai zan sanar maka to kuma sai naji layin naka baya tafiya."


"Eh lallai na rufe wayar ne, na tafi harami shiyasa."

Cikin nitsuwa yace. 

"Kawu Ali sai yaushe ne dawowarku?."

"Saura mako guda, kuma in sha Allah ni daga nan saudia zan taho india".


"To Allah ya kaimu lokacin ya dawo daku lfy.

Kawu Ali a tayamu da Addu'a fa."

"In sha Allah, Ahmad zamuyi ta addu'a."


Daga nan sukayi sallama, 

juyowar da zaiyi sai yaga Saifuddeen na rik'e da wayarshi,

a hankali ya tashi zaune kana ya mik'e ya taho gaban gadon, 

lek'a fuskarshi wayar tashi yayi, 

ido ya lumshe ganin karatun Qur'an  yakeyi, 

sai ya koma konta.


Shi kuwa Saifuddeen tunda Ahmad ya gyara mishi kinciyarshi, 

ya lumshe ido ya fara  bacci sai kuma  ya fara mafarki inda yake ganin Zaleeha 

tanata k'ok'arin son ganin fuskarshi daya rufe da tafin hannunshi, 

shima kanshi ta tsakanin yatsunshi yake gane fuskarta, 

ita kuwa sai tasa hannunta tana ta son ciro hannunshi daga fuskarshin amman ta kasa d'age hannun nashi, 

ganin haka sai ta koma gefe ta zauna tanata kuka,

daga nan ya farka daga baccin.

To shiyasa kawai ya d'auki wayarshi ya fara karatu.


Shi kuwa Ahmad Warisu ya kira suka gaisa sannan sukayi saida safe. 


Ya Adnan da Hayatuddeen kuwa da k'afa sukayi tattaki har cikin Hyatt kasan cewar ba nisa da asibitin.


Suna isa Ya Adnan yayi wonka,

yana fitowa Hayatudden ya mik'e ya shiga,

bayan sun gama shirin baccinsu ne, 

Ya Adnan ya koma parlour ganin Hayatuddeen baiyi bacci ba, yanata charting da abokanshi da yawanci jikin Hammanshi suke tambaya. 

Dan haka ya koma parlour dan yana son zaiyi waya da matarsa ya d'an kontar  mata hankalin.

Sosai ya kontar mata da hankalin, sannan yayi bacci.


Washe gari bayan sun karya suka sayawa su Ahmad abinda zasuci sannan suka nufi asibitin. 

Suna isa doctor na isowa, a tare suka d'anci abincin.

Tuni Dr Adnan kuwa ya kira Dr Acash prasat ya shaida musu suna kusa.


Suna gama woyar ya hangi Divia ta amsa kira sai kuma yaga ta nufi inda yake tare da ce mishi su shiga,

yana shiga suka tattauna da doctorn,

suna gamawa ya fita. 


Yana dawowa wurinsu  Ahmad yace.

"Har ka fito?."

"Eh na fito ya nuna min sakamakon gwajin da akayi ne, 

ya kuma cemin gobe ne zasuyi aiki."


"To Allah ya kaimu." Ahmad ya fad'i yana gyara wuyan rigarshi, 

Hayatuddeen kuwa Amin Amin yace tare da ajiye wayarshi kusa da kan Saifuddeen.


Washe gari kuwa k'arfe tara dai-dai na k'asar tasu.

Aka gama shirya Saifuddeen cikin shigar da akewa wad'anda za'ayiwa aiki,

tuni suma Doctors an gama shirya musu komai kayan aiki.


K'arfe goma dai-dai nurses suka shigo suka tura gadon Saifuddeen suka nufi wani corridor mai fad'i, a hankali Hayatuddeen ya bisu da ido da alamun karaya a idanunshi, 

ganin haka yasa Ahmad ya jawoshi suka zauna kana ya d'an kontar mishi da hankalin.

Ganin ya d'an nitsune ya kira Ummi yace mishi tofa an shiga aiki ta tayasu da addu'a yana katsewa ya kira bappa Ali ya gaya mishi hakama su Salisu da Warisu duk ya gaya musu.


Shi kuwa Dr Adnan yana tare dasu Dr Acash dan shi a wurinshi kamar samun k'arin ilimi ne ace a gabanshi akayi aikin.


Suna isa d'akin da za'ayi aikin Saifuddeen yayi murmushi ganin Ya Adnan da irin shigar doctors d'insu,

shima Dr Adnan murmushi yayi dan yana jin k'arfin guiwa da karsashi daga ganin lafiyayyun kayayyakin aikinsu,

bugu da k'ari ga Dr Malik Khan shima dashi za'ayi aikin dashi.


Allurar bacci ko ince cire haiyaci sukayiwa Saifuddeen,

bayan sunga yayi lib alamun alluran sunyi aikinsu.


Nanfa suka fara aikinsu baji ba gani,

shiru kakeji ba magana ko tari basayi sai sautin AC da kuma d'an sautin injuna da d'an k'aran ajiye ababen aiki da sukeyi.


Surgery ba sauk'i kusan tsawon awa hud'u sukayi a kanshi, 

sannan suka kammala komai, 

canza mishi kayan jikinshi sukayi sannan suka canza mushi gado, kana aka turoshi tamkar gawa aka fito dashi,

ta gabansu Ahmad akazo aka wuce dashi, 

mik'ewa sukayi suka fita daga wurin baki d'aya, 

yayinda tuni su Ahmad suna biye dasu a d'aya, 


Wani side dake can gefe suka shiga, 

suna shiga wurin suka shiga wani babban parlour dake cike da kekunana da kuma d'an ma dai-daicin pharmacy kuma ga ma'aikata a cike da wurin.

Suna shaga wasu suka taso suka karb'eshi a hannun wad'an nan d'in, 

wani d'aki suka shiga dashi dashi, 

kuma basu hana su Ahmad shigaba sai dai suna shiga sukaga sun zuge wani k'ofa na glass sun shiga cikin d'an keb'an taccen wurin dake cike da,

na'urori.

Kontar dashi sukayi bisa gadon dake ciki sannan suka k'ara gudun AC tare da gyara mishi konciyarshi,

suna mgna amman su Ahmad bazasu jisuba.

suna gama kimtsashi sukayi d'aura mishi ruwa tare dasa ruwan allurai a ciki,

daga nan suka fito suka zo inda su Ahmad suke, 

a nitse suka d'an musu bayanin cewar kada su yawaita hayaniya, kada kuma suce zasu shiga inda yake shida farkawa sai gobe iwar haka,

kada kuma su damu, su zauna na.

kai kawai suka gyad'a cikin gamsuwa da nitsuwa, 

kana suka zauna a kujerun dake jere a wurin, 

gaba d'aya Hayatuddeen ya kasa nitsuwa sai hawaye yaketa zubdawa da kyar dai Ahmad ke tausasa mishi zuciya.


A can kuwa ana fitar da Saifuddeen aka shigo da wani bature, 

shima awa hud'u sukayi suna aiki a kanshi daga nan kuma, 

suka firfito sai kuma gobe kasan cewar mutun biyu sukewa aiki kullum.


Suna fitowa Dr Malik da Dr Acash suka nufi can inda aka kontar da Saifuddeen

yayinda Dr Adnan ya bisu a baya, 

suna shiga suka k'ara duddubasu da kyau sannan suka fito, 

Nan Dr Acash ya kalli Dr Adnan cikin hausa yace. 

"Kuje masauk'inku kada ku damu akwai masu kula dashi. 

Dan koda kunza baza'a barku ku ganshiba ma'aikatanmu ne zasuyi mishi komai, 

sai bayan sati d'aya zaku ganshi."


"To ba matsala Dr."

cewar Adnan kenan,

dole tasa suka koma masauk'insu.


Sai dai kullum zasu zo safe da yamma su ganshi ta cikin glass d'in.


Sosai ma'aikatan wurin suke kula da majinyatansu cikin iyawa da sanin makamar aikinsu, 

tunda sun san irin mahaukatan kud'ad'en da suk'e karb'a a hannun 'yan uwan marasa lfy."


Yau kwana uku da yiwa Saifuddeen aiki Dr Acash ya nemi Dr Adnan ya bashi takardar daya rubuta wasu sabbin magunguna kala uku wanda zai shashu tsawon sati ɗaya rak.

Yana fita ya wuce pharmacy koda yaje ya basu takardar suka gaya mishi kud'in maganin kai ya kad'a dan daya lissafa da kud'in Nigeria dubu d'ari huɗu da sattin da biyar ne harda d'ari uku.


 Bayan ya saya ne ya bawa masu kula da shi d'in.

Ba b'ata lokaci suka fara bashi mgnin.


Tun randa aka fara bashi magungunan ya fara jin sauk'in nauyin da jikinshi ke mishi.


Randa aka cika sati da mishi aiki kuwa a ranar jirginsu bappa Ali ya iso India daga k'asar saudia.

kasan cewar da asuba suka iso, 

kai tsaye masauk'insu Ahmad ya nufa, 

saida sukayi breakfast sannan suka nufi asibitin.



Suna shiga Dr Adnan ya kira Dr Acash ya nema musu izinin shiga wurin Saifuddeen,

jin haka yace su jirashi yazo. 


Bayan awa biyu ya iso kana shida kanshi ya musu jagora har cikin d'an d'akin glass d'in nan. 


Suna shiga duk sukayi...!





                            By

               *GARKUWAR FULANI*

8/18/20, 7:53 PM - Ummi Tandama: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


              *NAKASA BA KASAWA BACE*



                            *PAGE 21*



                                  NA

               *AYSHA ALIYU GARKUWA*


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇




_09097853276 ta nan zaku turo katin mtn na300 kacal, ko kuma ku turo ta asusuna 0005388578  jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa sai ki turo shaidar biyanki ta wannan no 09097853276_


~Hmmm Daga gobene free page ya ƙare kun cinye alakoronku~



          Sukayi saurin k'arasawa gaban gadon da Saifuddeen ke kwance,

gaba d'aya fuskokinsu k'unshe da murmushi ganin yana musu murmushin.

Bappa Ali kuwa hannunshi yasa bisa kanshi yana shafawa tare da  fara jero mishi tambayoyi cikin kula yake cewa.

"Saifuddeen ya jikin? Da sauk'i ko? ina ke maka ciwo?."

ido ya lumshe mishi alamun da sauk'i, 

Ahmad da Hayatuddeen kuwa ido suka zura mishi ganin gaba d'aya ya rame sai wani fari mai d'aukar hankali da ya k'ara.

Dr Adnan kuwa ido ya zubawa na'urar dake gefen kan Saifuddeen d'in wanda Dr Acash prasat ke kimtsawa, 

Dr Malik kuwa hannunshi yasa yana jan yatsun k'afar Saifuddeen sannan ya juyo ya kalli Bappa Ali da ke cikin kid'ima cikin harshen larabci yacewa bappa Ali.

"Ba komai fa da yardar Allah zai samu lfy, 

adai tayamu da addu'a in sha Allah zai samu waraka, 

kuyi hak'uri komai zaiyi dai-dai amman sai mun hak'ura domin sauk'i a hankali yake samuwa."

kai bappa Ali ya jinjina alamun gamsuwa kana ya juyo da ganinshi kan Dr Adnan dake cewa. 

"Yauwa Bappa Ali yanzu mu fita, 

dan ba'a son yawanta surutu a kanshi."

Ahmad ne ya motso jikin gadon hannunshi yasa ya shafa fuskar Saifuddeen cikin sanyin lafazi yace.

"In sha Allah zaka samu lfy in Allah ya yarda zamu jure ko wanne wuya zamu kuma dage da addu'a in sha Allah zaka samu lfy."

sai kuma yayi sauri ya juya ya fita dan jin hawayenshi na zubowa.

Da sauri Bappa Ali yabi bayanshi, a wannan wurin suka zauna, shi kuwa 

Hayatuddeen a hankali ya bud'e baki cikin sanyi ya kamo hannun Hamman nashi murya can k'asa yace.

"Ummi tace in gaidaka da jiki, Adda Raihana ma tace in gaidaka."

sam baya iya motsa komai na jikinshi shiyasa sai da ido yake musu mgn, 

yana son ya d'ago tafin hannunshi ya sharewa Hayatuddeen hawayenshi dake kwaranyowa amman bazai iyaba, hakan ne ya sashi rumtse ido yana mai jin ciwo a duk wani sashi na jikinshi, 

ganin haka yasa Dr Adnan yaja Hayatuddeen suka fira.


Bayan fitarsu da kamar 23 minutes su Dr Acash suka fito suma.

 Dr Malik yace yana son ganin su da yamma. 

to sukace sannan duk suka nufi masauk'insu.


Zaune suke a parlour kowa da abinda ke ranshi, 

Dr Adnan ne yayi gyaran murya cikin sanyin sauti yace. 

"Bappa Ali munyi yawa anan dole wasunmu su hanzarta komawa gida Nigeria dan zamanmu zai k'ara tada hankalin Ummi, 

amman in wasu sun koma sun gaya mata jikin da sauk'i zatafi samun nitsuwa."

gyara zama Bappa Alin yayi tare da cewa. 

"Hankali na ya tashi da yanayin jikin Saifuddeen, bana son inyi nesa dashi."

sai dai ko in Ahmad da Hayatuddeen ne zasu koma."

cikin sauri fuska cike da rauni Hayatuddeen yace. 

"Bappa Ali in tafi in bar Hamma na kenan?."

shi kuwa Ahmad kai ya jujjuya tare da cewa. 

"Kayi hak'uri kawu Ali, komarka nada mahimmanci dan Ummi zatafi gamsuwa da kalamanka, sannan kasuwancinmu yafi buk'atarka akan ni, 

kuma kaga shima Ya Adnan ya kusa komawa, in mun tafi yazo shima ya tafi sauran kai d'aya, 

bazaka iya d'awainiyar ba, 

amman yanzu in kaje ka kwantar musu da hankalin bazai jimaba shima ya Adnan zai komo ya kuma kontar musu hankali ni da Hayatuddeen kuwa zamu kula da komai in munga sauk'in jiki sai nima in koma sai su Ummin suzo su dubashi."

shiru sukayi baki d'aya dan jin ta bakin bappa Ali.

Cikin gamsuwa yace to ba matsala in sha Allah cikin satin nan zan wuce. 

sosai Dr Adnan yaji dad'in hakan. 


Da yamma Dr Adnan da Bappa Ali suka shirya suka koma cikin asibitin kai tsaye office d'in Dr Malik Khan suka wuce. 

Nan suka samu Dr Acash ma a nan bayan sun gaisane Dr Acash ya gyara zamanshi tare da fuskantarsu da kyau cikin nitsuwa yace.

 "Jikin Saifuddeen dai da sauk'i sosai, amman akwai buk'atar k'arin kula da jinyarshi, 

in da hali nanda wata biyu zuwa uku akwai buk'atar canji asibiti daga nan New Delhi za'a maidaku Mumbai zuwa babban asibitin. 

Orthopedic hospital zanyi k'ok'arin hadaku da d'aya daga cikin manyan doctors d'in.

Physiotherapist domin sune suk'eda gwarewa da k'ok'arin farfad'o da aikin lakar jiki ga wad'anda akayiwa aiki dama wanda ba'a samu damar yi musu aikin ba. 

To shiyasa nake son turaku garesu in munyi sa'a zai samu sauk'i cikin k'ank'anin lokaci tunda an mishi surgery  sannan an sama mishi kular likitocin fisiyo to muna da k'arfin guiwar samun sauk'inshi."

cikin gamsuwa Dr Adnan yace. 

"Ba matsala in dai hakan ya kamata ayi duk abinda ya dace kawai."

shima bappa Ali cikin gamsuwa ya gyad'a kai, 

sai kuma suka nitsu jin Dr Malik Khan na cewa.

"Alhamdulillahi ko yanzu muna ganin alamun sauk'i sosai a jikinshi alamun aikin da akayi mishi yayi kyau to amman yana da kyau ku kaishi Mumbai d'in domin acan zai samu duk abinda ya dace a sauk'ak'e, likitocin zasu rink'a kula dashi sosai dan canma asibitin mune, munfi zama a canma nan duk wata sa huɗu muke zuwa muyi aiki, 

so a can akwai. 

Orthopedic surgeon likitocin da suka k'ware a fannin k'ashi, ga kuma neurosurgeon da suka kware fannin k'wak'walwa, to suke kula da masu larurar. So zai samu wadacecciyar kulawa da treatment mai kyau da ink'anci, da taimaka musu wurin movement motsa jiki da da kuma yin exercise a rink'a strengthen muscles d'in manual therapy. koyar dashi duk wani abinda ya dace tare da bashi shawarwari yadda zai kula da kanshi bayan an sallamesh.

 Sai dai kam akwai cin kud'i amman in sha Allah zai samu lfy."

cikin gamsuwa Bappa Ali ya kalli Doctors d'in tare da cewa.

"Ba matsala aiyi duk abinda ya dace fatana samun lafiyar d'an d'an uwan na."

murmushi Dr Malik Khan yayi tare da cewa.

"To Alhamdulillahi yanzu dai muna bashi Drugs masu rage mishi symptoms d'in ciwon sosai, kuma Alhamdulillahi yana jin dad'insu, so yana gama shansu zamu yi muku transfer zuwa can d'in."

sosai Dr Malik Khan ya musu cikekken bayanin da zai sama musu nitsuwa har saida yaga hankalin su ya kwanta sannan ya sallamesu suka fita suka tafi.


Daga ranar ba'a sake barinsu sun ganshiba sai bayan kwana hud'u wanda kuma a ranar ne Bappa Ali zai koma gida Nigeria. 

Da sanyin safiya suka nufi cikin asibitin bisa jagorancin Dr Malik Khan suka samu suka shiga suka ganshi, kuma Alhamdulillahi sosai suka samu nitsuwa dan sunga alamun d'an sauk'i a jikinshi, 

suna fitowa Bappa Ali ya shiga taxi ya nufi airport k'arfe sha d'aya dai-dai jirginsu ya tashi. 


Su kuma kai tsaye masauk'insu suka koma.


Bappa Ali kuwa komawarshi ya samawa Ummi nitsuwa sosai dan ya kontar mata hankali ya b'oye mata batun sauyin asibiti ya samu kuma ya hanata tafiyar yafi son sai sun koma Mumbai d'in taje.


Warisu da Mudassir da Bello kuwa suna kula da kasuwancinsu yadda ya kamata. 


Bappa Ali ya dawo da kwana biyar Salisu yaje India ya duba jikin abokin nashi kwana biyar yayi ya dawo gida Nigeria shima ya k'ara kontarwa Ummi hankalinta sosai.


Sai dai sunyiwa Ishaq bayanin komai, 

yaso yaje sai suka hanashi a kan ya bari sai sun koma Mumbai d'in sai yaje da  Ummin dan dole ya hak'ura.


                          ***

Yau watan su Saifuddeen d'aya da kwana goma kwanansu arba'in kenan a can, 

kuma yau ne zasu wuce Mumbai tare da jagorancin Dr Acash prasat. 


K'arfe biyar dai-dai jirginsu yayi sauk'an ank'ulu a babban  filin shige da ficen.

Hilton Mumbai international Airport.


 Daga nan Airport d'in kai tsaye asibiti suka wuce.

*Nanavati super speciality hospital*.   

Shine sunan dake liƙe asaman asibitin da akayiwa su Saifuddeen transfer. Asibitine da haɗuwarsa ya zarce misali don ya ƙawatu sosai, komai na cikinsa gwanin burgewa ne, ko ina kakai dubanka zakaganshi ya ƙawatar gwanin ban sha'awa, don sosai haɗuwarsa ya zarce na garin New Delhi.


 Mutane ne keta hada-hadan shiga da fice daga cikin asibitin.

 Koda suka ƙaraso cikin asibitin ɗaki na musamman aka samawa Saifuddeen tare da taimakon Dr Acash prasat,   Dr.Adnan da Ahmad ne suka ɗaga Saifuddeen daga kan weelchair ɗin da suka turosa akai, kan faffaɗan gadon dake cikin ɗakin wanda yaji lallausan katifa suka shimfiɗesa, ahankali ya maida kyawawan idanunsa ya rufe tare da ɗan sauƙe ajiyar zuciya.  Kafaɗansa Dr.Adnan ya ɗan dafa a hankali, jin an dafa kafaɗansa ya sanyashi buɗe idanunsa ya sauƙesu akan laɓɓan Dr.Adnan,

 Dr.Adnan kuwa ganin Saifuddeen na kallonsa ya sanyashi cewa.

 "Yajikin naka?"  

Kyakkyawan murmushine ya bayyana akan kyakkyawar fuskarsa, kansa yaɗan jinjina alamar da sauƙi, tare dakai dubansa ga Hayatuddeen dake tsaye ya kafesa da ido, murmushinsa me kyau yayiwa Hayatuddeen  tare da miƙo masa hannunsa, ganin haka yasa Hayatudden cikin tsananin ƙaunar da yake yiwa ɗan uwan nasa yataho garesa tare da miƙa masa hannu shima, damƙe hannun Hayatuddeen yayi acikin nasa hannunsa tare da lumshe idanunsa,  sosai yakejin son ƴan uwansa acikin rai da zuciyarsa, tabbas yasan Allah shine gatan kowani bawa, amma kuma yasan duk wani buri da fatan ƴan uwansa akanshi yake, shi musulmine da ya yarda da ƙaddara me kyau ko akasinta, haka kuma yayi imani cewa komai ya faru da bawa muƙaddarine daga Allah, 

Sake rufe idanunsa yayi kirif yayinda zara zaran eye lashes ɗinsa suka kwanta luf aƙasan idanunsa, gashin giransa kuwa sai shinning yake kamar wanda aka shafawa mai, uwa uba ga tohon sabon gashi na tattausan sajen da ya fara yiwa fuskarsa k'awanya, sosai fuskarsa tayi fayau da ita hasken fatarsa yasake bayyana, haƙiƙa Saifuddeen kyakkyawane sosai, sannan duk da nakasar dake tare dashi komai nasa abun burgewa ne da so,  ganin kamar yayi bacci ne yasanya Dr.Adnan duban Ahmad da Hayatuddeen cikin kulawa yace.

 "Yakamata ace kuje ku nemi masauƙi tunda Dr.Acash yayi mana komai ya kuma sama mana nurses ɗin da zasuna kula dashi, sannan gani ni zan zauna atare dashi."

Jinjina kai Ahmad yayi tare da duban hayatuddeen da har yanzun hanunsa ke cikin na Hamma Saifuddeen ɗinsa.  "Mutafi ko Hayatuddeen, naga idanunsa arufe inaga yasamu bacci".

 Ahmad yafaɗa yana me kallon Saifuddeen. 


Kallon Hamma Saifuddeen ɗin hayatuddeen yayi,cike da tausayin ɗan uwan nasa ya soma yunƙurin zare hannunsa dake cikin nasa,  har acikin ransa yakejin tausayin Hamman nasa, tabbas shikam da ace ana sauya ƙaddara, to da tuni ya sauya ta hammanshi daga mummuna izuwa kyakkyawa.

  Haka Hayatuddeen da Ahmad suka baro cikin asibitin don nemawa kansu masauƙin da zasu zauna,  taxi suka shiga inda suka ce yakaisu hotel wanda yake mafi kusa.


Tafiya kad'an sukayi kana motar ta ratsa cikin Ƙofar katafaren  hotel d'in.

Sahar International Mumbai,  mai taxi din ya sauƙesu, hotel ne ƙawatacce me kyaun gaske wanda yake ɗauke da dogon gine gine gwanin burgewa. 

Kallon Ahmad Hayatudden yayi bayan sun sauƙa daga taxi ɗin sun biya me taxi ɗin kuɗinsa, cikin yanayi naɗan damuwa yace.

 "Ya Ahmad baka ganin wannan hotel ɗin zaiyi tsada da yawa? ka duba kyawunsa fa". 

Ɗan jim Ahmad yayi tare da ɗaga kansa yana ƙarewa hotel ɗin kallo, asanyaye yace.

 "To Hayatuddeen ya zamuyi, dole haka zamu kama saboda shikaɗaine zai sauƙaƙa mana wahalan zuwa asibiti, kaga idan bashi ba ko ina muka kama sai munyi ta cacan kuɗin transport, kaga kuma wannan ma ƙarin ɗawainiya ne".  

Kai Hayatuddeen ya jinjina cike da gamsuwa da kalaman Ahmad, atare suka jera har zuwa cikin hotel ɗin inda suka tsaya a receiption.  saida sukayi duk wani abun daya dace kana suka biya kuɗi sannan aka basu makulli da kuma nomban ɗakin da suka kama,   tafiya suke suna me dudduba nambobin ɗakunan har suka iso ɗakin dayake da namba dai-dai da wanda aka basu, Ahmad ne  yasanya key ya buɗe ƙofar ɗakin, Hayatuddeen na biye dashi abaya haka suka shiga cikin ɗakin, amatuƙar gajiye hayatudden ya faɗa kan faffaɗan gadon dake cikin ɗakin, wanda ke ɗauke da wata luntsumemiyar katifa me laushin gaske, lumshe idanunsa yayi tare da sauƙe ajiyar zuciya, kallonsa Ahmad yayi tare da girgiza kai aransa yana me cewa .

"Allah Ya shirya mana kai Auntan Ummi".

  kasancewar agajiye suke su dukansu, yasanya Ahmad  soma ɗan rage kayan jikinsa kana ya wuce bathroom,  wanka yayi tare da ɗauro alwala don gabatar da sallan magriba wanda daf ake da cikar lokacinta, yana fitowa daga cikin bathroom ɗin yaci karo da wandon Hayatudden daya cire yayi wurgi dashi atsakiyan ɗakin, gefe kaɗan ma rigarsa ce wanda ya cire a yashe, cike da takaicin halin Hayatuddeen Ahmad ya girgiza kansa tare da ƙarasawa gaban mirror, don yasan idan yace da Hayatudden ya ɗauke kayan nasa daga ƙasan ma, wani sabon sakalci ne zai tashi, hakan yasa ya ƙyaleshi yashiga fito da kayansa dake cikin jaka don zaɓan wanda zai saka.

  Haka dai cike da sangarta Hayatuddeen ya wuce bathroom shima yayi wanka tare da ɗauro alwala,  koda ya fito awankan kamar yanda ya saba haka ya zazzage kayansu dake cikin jakan kaf akan gado, shidai Ahmad yana kallonsa bai kulasa ba, don yasan me hali baya taɓa fasa halinsa,  riga da wando na jeans Hayatuddeen yasanya cike da sakalci ya dubi Ahmad dake ƙoƙarin rufe kwalban turaren dake hannunsa, ɗan ɓata fuska yayi tare da shafa cikinsa cikin murya me ɗauke da gajiya yace.

"Yaya Ahmad nifa gaskiya yunwa nakeji, gashi bamu sayawa su Hamma Saifuddeen abinci ba!"


"To acici kai-dai baka da wani zance saina ci, yanzun idan mukayi sallah sai munemi waje mafi kusa musai abinci mukai musu, don tabbas nasan zuwa yanzu dole zasuji yunwa".

 Ahmad yafaɗa yana me ƙoƙarin saka takalmi aƙafarsa.

 Shi kuwa Hayatuddeen bai sake cewa komai ba har Ahmad yagama kimtsa kansa suka fice daga cikin ɗakin, cikin harshen turanci Ahmad ya tambayi ma'aikatan dake aiki a hotel ɗin inda zai samu abinci,  dayake babu wani nisa tsakanin hotel ɗin da kuma inda ake sai da abincin hakan yasa ɗaya daga cikin ma aikatan yayi musu kwatance,  saida suka fara zuwa wani masallaci da ke nan kusa suka gabatar da sallan Magriba, daga Hayatudden har Ahmad babu wanda daya kafa goshinsa aƙasa ba tare da yayiwa Saifuddeen addu'ar samun lafiya ba, 

 suna idar da addu'o'insu suka nufi inda zai sadasu da inda ake saida abinci. 

 Koda suka ƙarisa wajen cin abincin, waje ne me kyau da tsabta sannan babu irin abincin da babu awajen,  cimar Nigeria sukaci, inda Ahmad yaci Fish roll and gas meat, shikuwa Hayatuddeen yaci roasted fish da kuma damammiyar madara me kaurin gaske, daganan takeaway sukayiwa su Dr.Adnan da Saifuddeen, kasancewar tsakanin hotel ɗin da asibitin babu wani nisa sosai hakan yasa da ƙafansu suka shiga takawa har zuwa privet hospital ɗin.

 Kaitsaye inda su Hamma Saifuddeen din suke suka nufa,  abakin ƙofar ɗakin da Saifudden ɗin yake suka hango Dr.Adnan tare da Dr.Acash prasat, da alama magana suke mai mahimmanci, tsayawa sukayi daga gefe har saida suka kammala maganan kafun suka ƙaraso, kallon fuskan Dr. Adnan sukayi su duka, cikin yanayi naɗan damuwa Ahmad yace.

 "Akwai matsala ne?" 

Kai Dr.Adnan yagirgiza tare da cewa.

 "No babu wata matsala, sai-dai bayanzu zamu samu ganin doctors ɗinba aƙalla sai munshare kwana biyu  kafun mugansu,

  Dr.Anan Mehta, ƙwararren  likitane a ɓangaren  Orthopeadic surgeon, sai kuma  Dr.Mahesh Khurana, wanda shima ƙwararrene afannin neurosurgeon, muna da buƙatan ganin wad'annan likitotin don kuwa sune masu kula da irin lalurar Saifuddeen, fatanmu akullum dai shine Allah yabashi lafiya".

Da.

 "Amin Amin". suka amsa su dukansu, ko wanne zuciyarsa cike da tausayin Saifuddeen. 

 Ganin rauni nashirin bayyana akan fuskokinsu ne yasanya Dr.Adnan karɓan takeaway din hannunsu kana yace su koma masauƙinsu su huta sai kuma zuwa da safe idan Allah yakai rai,  bazasu musa masa ba domin dama agajiye suke, hakan yasa sukayi masa saida safe, koda Hayatuddeen ya buƙaci ganin Hamman nashi cewa dashi Dr.Adnan yayi yayi bacci sannan ba aso atasheshi, dole haka Hayatuddeen ya haƙura yabi Ahmad suka koma masauƙinsu.


Koda Dr.Adnan ya koma cikin ɗakin nan ya iske Saifuddeen kamar yanda yafita ya barshi wato idanunsa alumshe tamkar wanda yake bacci, shi kuwa Saifuddeen ba bacci yake ba, yayi nisa ne akan tunanin Zaliha, kyakkyawar fuskarta ne keyi masa gizo acikin ƙwayan idanunsa da zuciyarshi, tuno da yanda ta rungumesa ta baya tana me jansa akan su gudu alokacin da yaran Dalla suka kusa cimmasa  yasanya tsikar jikinsa  tashi, lokaci guda ya tuno da taushin hannuwanta da kuma yanda daddaɗan ƙamshin turarenta ya zautar dashi,  yanayin da yakejin kansa aciki, ya sanya shi jin tamkar alokacin abun ke faruwa, sake lumshe idanunsa yayi alokacin da ya tuna da yanda bakinta ke motsawa alokacin da take cewa yazo su gudu kada su cutar dashi, wani irin yawu ya haɗiya wanda tuntuni ya tsaya masa amaƙoshi, gaba ɗaya jiyayi jikinsa yayi wani iri, yayinda yakejin wani irin sassanyan yanayi shauƙin sha'awa na musamman suka rufeshi dangane da ita.     "Saifuddeen!".

 Dr Adnan yaƙira sunanshi yana me kamo hannunshi, tayanda zaiji ya buɗe ido,  jin sauƙan hannu akan nasa hannun yasanyashi buɗe idanunsa ahankali, murmushi Dr Adnan yayi masa tare da cewa.

 "Tashi kaci abinci, danajika shiru na ɗauka ma ai bacci kakeyi".

Ɗan murmusawa kawai Saifuddeen yayi, inda shi kuma Dr Adnan yaɗan ɗago saman gadon da Saifuddeen ɗin yake yayi sama, shida kansa ya gyara masa kwanciya inda yayi kamar azaune yake saidai kuma bayansa yana jingine ne  da gadon, abinci Dr Adnan ya miƙo masa kana ya koma gefe shima ya soma cin nasa,   cikin nutsuwa haka Saifuddeen ya shiga cin abincin ahankali yake ɗan lumshe kyawawan idanunsa masu matuƙar ɗaukar hankali, haryanzu tunaninta ne kwance aƙasan zuciyarsa, ahaka dai har ya ɗanci abincin kaɗan ya ture sauran gefe, don shi ba mutum bane me yawan cin abinci sosai... 



     Gombe Nigeria


Dawowarta daga wajen aiki kenan, 

aɗan gajiye ta shigo cikin  haɗaɗɗen ɗakin nata, jakar dake hannunta ta aje gefe tare da soma rage kayan jikinta,  saida ta cire komai na jikinta sannan ta sanya wata kekyawar rigan wanka baby pink colour, dogon gashinta ta ɗaure da ribbom sannan ta wuce kai tsaye zuwa toilet,  wanka tayi da sabulunta me daɗin ƙamshi kana ta ɗauro alwala, kasancewar ankusa ƙiran sallan Magriba,   zama tayi agaban tangamemen dressing mirror'n ta wanda gabansa ke cike maƙil da kayan shafa masu kyau da tsada, body lotion ɗinta tashafa wanda gaba ɗaya sanyin ƙamshinsa ya game ɗakin,  yanayin yanda takejin kanta agajiye yasanyata miƙewa tsaye, ahankali ta ƙarasa gaban drawer ɗinta wanda cikinsa ke shaƙe tam da kayan sawanta masu kyau da tsada, wanda ita kanta batasan iyaka yawan suturun sawanta ba,   wata ƴar doguwar riga marar nauyi ta zaro wanda yake daga ɓangaren kayanta marassa nauyi, rigar irin mai taushin nanne wanda takebin jikin mutum ta lafe, da fararen stones aka ƙawata wuya da hannayen rigan, wanda hakan kuma ba ƙaramin ƙarawa rigan kyau yayi ba,  sosai rigan ta amshi jikinta ta lafe, hakan yasa kyakkyawan body structure ɗinta bayyana, wanda da ace lafiyayyen Namiji zai gani to fa tabbas dasai ya rasa nutsuwarsa,  jin anata ƙiraye ƙirayen sallan Magriba ne yasanyata zura wani dogon hijab ajikinta tare da shumfuɗa sallaya,  koda ta idar da sallan magriba bata tashi akan sallayan ba har saida ta sallame sallan Isha, bayan ta tarin  addu'ointa wanda mafi yawansu akan Saifuddeen ne, cikin sanyin jiki  ta tashi daga kan sallayan tare da cire hijab ɗin ta ninkesa,  kana tayi taku uku zuwa biyar ta isa bakin gadonta kwanciya tayi akan lallausan gadonda tare da jawo pillow ta matse a ƙirjinta, rumtse idanunta tayi da tsananin k'arfi tare da fesar da wani zazzafan numfashi me ɗan karen zafi yayinda takejin wasu zazzafan hawaye sun tsastsafo mata cikin jijiyoyin idanunta, cusa kanta tayi cikin hannayenta tanajin akowani bugu na zuciyarta da tunaninsa yake wanzuwa, ina yake!? a ina zan ganshi? wani hali yake ciki? sun kasheshi ko yana da rai? tana da buƙatar sanin waƴannan amsan fiye da komai ayanzu, gyara kwanciyarta tayi tare da buɗe idanunta, kan zanen pop'n dake mamaye saman ɗakin ta tsaida idanunta sun kad'a sunyi jazir cikin raunin murya take cewa.

 "Ya Allah kasa ako ina yake yana cikin ƙoshin lafiya, in kuwa sun mishi rauni ya Allah ka bashi lfy!".

tafaɗi haka aɗan raunane, ahankali hawayen da suka cika idanunta suka samu daman gangarowa suka biyo ta gefen kumatunta,  haƙiƙa zuciyarta cike take da son jin wani abu daga garesa, yayinda idanuwanta kuwa ke ɗokin sake ganinsa, tunaninsa ya matuƙar tsaya mata azuciya babu dare ba rana ko yaushe bata da sukuni bata fahimtar komai domin duk nazarinta da tunaninta a kanshi yake k'arewa, 

 sake muskutawa tayi ta gyara kwanciyarta akaro na biyu, kana ta lumshe idanunta da har yanzu suke ɗigan hawaye,  da sauri ta buɗe idanunta tare da dafe ƙirjinta dake wani irin bugawa sakamakon tunowa datayi  yanda

Yaran Dalla suka caka masa wuƙa abayansa, da ƙarfi ta rumtse idanunta tare da sakin kuka me cin zuciya  cikin yanayi mai kama da sambatu tace.

 "Ya Allah Kasa ba mutuwa yayi ba, Ya Allah ko sau ɗayane ka ƙara nunamin shi, ya taimakeni alokacin danafi kowa buƙatar taimako, Ya Allah kasa yana cikin halin nutsuwa aduk inda yake ya Allah ka kaddara saduwa ta dashi koda godiya in mishi!!".

Da sauri ta d'ago kanta jin k'anwarta Zahira na cewa.

"Dan Allah Anty Zaleeha, ki bar irin wannan kukan, kici gaba da yimishi addu'a insha Allah addu'arki zata riskeshi."

cikin kuka ta kife kanta bisa cinyar k'anwar tata wacce ita kad'aine tasan da batun. Cikin kukan take cewa.

"Bai sanniba, bai tab'a ganinaba cikin taron maza dake wurin kab babu wanda ya kula da ni bare ya taimaka min dan tsoron Dalla da sukeyi, 

sai shi d'aya ya zame min Garkuwata, kuma sun mishi illa gashi ban san ina zan sake ganinshi ba."

shafa kanta Zahira tayi tayi tare da kwantar mata da hankalin. 

A haka tacigaba dayin kuka ƙasa-ƙasa tana me fidda shashsheƙa da haka har bacci ɓarawo ya ɗauketa.


                     ***


A gidansu Saifuddeen kuwa.

Ummi ce zaune afalo tayi jigum yayinda tunanin ɗanta kuma farin cikinta Saifuddeen ke kwance acikin ranta, dare da rana bata da wani addu'a sai na nema masa lafiya awajen mai duka,  Raliya ce da Adda Rahma da tazo musu tunda safe, 

sune suka tafito daga cikin kitchine, hannun Adda Rahma  ɗauke da goran ruwa me ɗan sanyi, jingina bayanta tayi da jikin ƙofar kitchine ɗin tare da kafe Ummin nasu da ido, wani irin tausayin kansune ke ƙara ɗarsuwa acikin ranta a kullum, haƙiƙa SAIFUDDEEEN shine komai nasu, Allah Ne gatansu amma Saifuddeen babban jigone agaresu wanda kuma shine gaba ɗaya farin cikinsu.

Raliya kuwa da sauri ta k'araso gefen Ummi ta zauna, ita kuwa Adda Rahma cikin sanyin jiki ta fara d'aga k'afafunda da suka kumbura sabida tsufan cikin jikinta da kyar take tafiya bisa dukkan alamu cikin ya cika wata bakwai ya shiga na takwas a hankali ta ƙaraso cikin falon tare da sanya hannu taɗan taɓa Ummi wanda tayi nisa acikin duniyar tunani.

  Ummi kuwa jin sauƙan hannu akan kafaɗanta ne yasanyata ɗagowa da sauri ta kalli wanda ya dafatan,  da fuska Raliya tayi arba wacce ta marairaice tuni idanunta sun tara k'walla.

A hankali ta kuma juya ganinta zuwaga Rahma wacce ta fara mgna cike da sanyin murya haɗi da tausayawa tace.

 "Dan Allah Ummi kidaina sa kanki adamuwa, Ummi idan kika kasance acikin damuwa akullum natabbata  Saifuddeen idan yasani bazai taɓa yafewa kansa ba,

 Ummi kinfi kowa sanin Saifuddeen sam bayason damuwarki, dan Allah Ummi kidaina sanya kanki adamuwa  Saifuddeen addu'a yake nema daga gareki damu baki d'aya , sannan Ummi kada kimanta addu'an uwa yana da matuƙar tasiri akan ƴaƴa, please ki tausaya mana ki dage da yi mishi addu'a!" 


Wani irin dogon Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe tare da ɗan rausayar da kanta gefe tana mai son maida hawayenta amman ina ta gaza tuni sun zubo mata bisa k'unshinta, haƙiƙa shiga damuwa yazame mata dole, tunda ɗanta mafi soyuwa agareta yana cikin wani irin mawuyacin yanayi a hankali tace.

  "Ina yimasa addu'a akullum akuma ko yaushe Rahma, sannan nakasa ɓoye damuwata akansa, ke uwace Rahma kinsan irin tsananin so da kuma ƙaunar dake tsakanin ɗa da uwa, wannan ƙaunar fiye da itace ke tsakanina da  Saifuddeen, kuma kisani ko ban nuna damuwata afili ba to tana nan kwance acikin zuciyata tana cina!".

 ta ƙare maganar murya araunane. 


Hawaye ne suka cika idanun Raliya har suna kwaranyowa kan fuskarta yayinda itama Rahma ida nunta suka cicciko da hawaye,

 tabbas idan  harsu da suke ƙannansa suna tsananin jin ciwonsa ajikinsu, sannan kuma suna tsananin tausaya masa, basu  da wani fata daya wuce samun sauƙinsa, to ya Ummi da take mahaifiyarsa zataji?  ƙoƙarin maida hawayen da suka cika idanunta tasomayi tare da sadda kanta ƙasa murya asanyaye tace.

 "Kiyi haƙuri Ummi In sha Allah Saifuddeen  zai samu lafiya, zai warke yazama cikakken mai lafiya, Saifuddeen d'inmu shine jigo kuma farin cikin mu, In sha Allah ko dan wannan Allah zai dubemu ya bashi lafiya, don bamu kaɗai keda buƙatarsa ba mutane dayawa daga waje suna da buƙatarsa!".


Murmushi Ummi tayi tare da cewa.

 "Allah Yasa!". 


Da "Ameen".

 Raliya ta amsa kana ta miƙe ta wuce ɗaki don duba Adam yaron Adda Rahma dake bacci koya tashi.




k'arfe biyar dai-dai na yamma Zaleeha ta shigo cikin gidan radio vision FM gombe. Driving takeyi cikin tsananin nitsuwa a hankali take tafiya, 

yayinda take sa hannunta tana goge sirarun hawayen dake zubo mata time to time.

parking tayi kana ta fito kai tsaye d'akin watsa shirye-shiryen su ta nufa, 

a bakin k'ofa tayi cikibis da Raveel wanda ya gama gabatar da shirinsa kenan ya fito da nufin zai kirata domin tazo ta gabatar da program d'inta.

Murmushi yayi tare cewa. 

"Yar halas kink'i ambato yanzu nake kiranki a raina."

sam hankalinta da nitsuwarta basa jikinta bare ta kulashi ratsawa gefenshi tayi a bakin k'ofar shiga ta cire takalmanta masu d'an karen tsini, 

kana ta zura silipas dake wurin sannan ta kutsa kai cikin d'akin.

Shi kuwa Raveel jingina yayi da jikin gini ya zuba mata idanu yana kallonta ko k'ebta idonshi bayayi koda ta shiga ta meda k'ofar ta rufe sai ya lik'a idanunshi kan takalmanta.


Ita kuwa Zaleeha tana shiga cikin d'akin watsa shirye-shiryen nasu wani azabebben bege da shauk'in son ganin fuskar da ta tab'a gani sau d'aya ya d'arsun mata a rai. 

A hankalin ta zauna kan kujerar zaman nasu, 

Kana ta ɗauki wannan ɗan abu da suke sawa a kai ta saka wanda  yake isa har zuwa kan kunnensu ta jawo ta sank'ala. 

Ji tayi zuciyarta na sarrafa gangar jikinta, 

madadin ta gabatar da program nata mai taken Babu nakasshe sai rago, 

kawai sai ta tsinci kanta dafuskantar na'urar tasu da kyau tare da zab'o wak'ar da take jijjiga sirrin zuciyarta. 

can cikin gidan Radio kuwa cikin mmki managernsu ya kasa kunne a na'urorinsu na tantance abinda suke watsa jin sautin sassanyar wak'ar da Zaleeha ta sake, dan ya hango shiganta, da sauri ya kalli agogon dake fuskar wayarshi ganin ai lokacin gabatar da shirinta har ya shiga da 3 minute.

Da sauri ya jingina jikin kujerar jin ta d'an rage sautin wak'ar. 

Yayinda mutanen cikin garin gombe da kewaye ke jinta dan shirinta yanada matuk'ar farin jini, 

musamman a wurin nakasassu, wanda yanzu hakama duk inda nakasasshe yake yana jinta sanin lokacin nasune.


A hankali take jin sautin wak'ar da tasa yana ratsa mata jiki da jini har zuwa cikin zuciyarta a hankali ta bud'e bakinta ta fara  bin wak'ar.

Yayinda akejin muryarta na gaurayewa da muryar mawak'an dan ta rage sautin hakan yasa abin ya had'e yake bada wani sok'o mai armashi wanda da zaran kajita kasan wani takewa baitukan,

lumshe ido tayi tare da bin sautin waƙar a hankali take cewa. 

"Soyayyar dake raina bazan sauya ra'ayi ba."

 sai kuma ta bud'esu tare daci gaba da cewa. 

 "Nayi lullubi kamar na ango da amarya."

sai kuma ta d'an d'aga sautinta kad'an taci gaba da rere wak'ar. 

 "So yanada dad'eeeee maso dashen wani ya shiga haushi."

sai ta kuma d'an k'ara volume  na radio kana taci gaba bin waƙar.

"Soyayya ta zahiri ba'ayi mata gudun barewa."

sai kuma wani sassanyan shesshek'a ya danne mata harshenta wanda kowa yaji salon yadda muryarta ke fita zai iya gane tana kuka da zubda hawaye take bin wak'ar cikin tsananin tausasa lafazi take cewa. 

 "In nayi rashin sautinka zan fad'a k'inshi ruwa.

Idan har na barka aban sona bani da kowa. 

Dana ganka sai na wadatu da k'oshi bani yunwa. 

Duba ka gani tsuntsun k'auna ya zana barewa.

Girgije samani tai lub-lub, lif tana zubar ruwa.

Ga itatuwa koraye d'orowa da sanwa."

sai kuma ta lumshe idanunta hayenta suka samu daman zubowa sannan taci gaba cewa.

"Munshiga ginin sha'awa ga iska tana kad'awa.

Da k'auna tabi jiki an komawa wa da k'anwa.

a hankali ta lumshe idanunta yayinda hawayenta sukaci gaba da kwaranyowa,

tana ganin wayarta nata kawo haske alamun ana kiranta amman bata da tunanin d'agawa, 

murya na rawa taci gaba da bin baitukan wak'ar a hankali take cewa. 

"Jikina yana jurar rab'ar wata soyayya.

sai kuma ta d'an d'aga murya da ɗan ƙarfi kana tace.

*"Nayi adanin soyayyata bani baiwa kowa!*

Barewa batayi gudu d'anta ya rarrafaba, 

*Soyayyar dake raina bazan mata kishiya ba.*

sai kuma ta lumshe ida nunta  kana ta buɗi baki a hankali ta taci gaba da raira wasu baitukan da yafi kama da amsa take bawa ƴan Nakasa ba kasawa bace fans 2, murya a tausashe take cewa.

*Mai sukar masoya bai san sirrin zuciya ba.*

_Idan na rasata jiki bazai daina bariba_

*baniwa masoyi rowar tattausan lafaziba.*

_K'auna ke gushe haushi so bazai canja wuriba

So in yayi kewar gani aso bazai tsayaba."_

Tana ganin ana danna mata danja alamun akwai matsala amman bata kulaba, 

saima ta k'ara d'aga muryarta  ta gaurayeta da muryar mawak'a har nata yana d'an d'ara na radio take cewa.

*"Bani bada rancen k'auna bazanyi aroba!.* 

*Na dad'e ina rarrafe cikin masu soyayya!.* 

*Gashi nayi fincinkawau misalin gudun barewa!.* 


Hakafa tayi ta sakin wak'ok'i masu jijjiga zuk'atan masoya wanda duk yaji yasan abin daga cikin zuciyarta ne. 

Koda akazo dan a shiga a ankarar da ita sai aka samu ta kulle k'ofar, a k'arshe dai saida tayi 35 minutes tana caccanza wak'ok'i wanda a zahiri ma program nata 30 minutes ne.

Saida taga kuka zaici k'arfinta ne ta mik'e da sauri ta fita. 

A bakin k'ofar ta samu Raveel da manager da Aminiyarta Bilkisu maigado dama wasu maikatan nasu. 

ido suka zuba mata ganin hawaye har kan habarta, 

sannan kuma ta wucesu da sassarfa, 

kai tsaye parking lot nasu ta nufa tana shiga motar a guje ta bar aharabar ma'aikan nasu. 


Maigadoce tayi sauri ta shiga cikin d'akin dan gabatar da shirinta. 

Raveel kuwa da sauri yabi bayanta, 

shi kuwa manager ko motsi ya gazayi.


Shida saura minti goma ta isa bakin gate d'in  gidansu, 

tana k'ok'arin danna hancin motarta cikin gidan taga wasu tsala-tsalan motoci guda uku suna fitowa a jere, bisa dukkan alamu manyan mutanene masu kamala, 

dan haka ta d'an tsagaita, 

Suka fita ido ta d'an zaro dai-dai lokacin da mota ta ukun ta iso inda take murya na rawa tace. 

"Abdussalam, kuma da iyayenshi a gidanmu." da sauri ta zaro ido...!



A can Mumbai babban birnin k'asar India kuwa. 

Hayatuddeen ke zaune gefen Saifuddeen, 

yana yanke mishi farcen kafafunshi ne ya d'an d'ago kanshi sannan ya zaro wayarshi daketa ringing a cikin al'jihunshi da sauri yayi  picking call d'in sabida ganin number k'asarshi Nigeria kuma video call ne, 

yana d'aga yayi murmushi tare da zazzaro ido ganin Amina ce nurse d'innan da take kula da Saifuddeen lokacin da suke Abuja, 

fuska a sake yace. 

"Amina kece?." hararanshi ta d'anyi tare tsuke fuska sannan tace. 

"Amina gatsal babu karanta min Aunty."

Dariya ya d'anyi tare da cewa. 

"Ke nafa fiki tsawo."

"To dai ai tsawon ka fini ba shekaru ba. "

ta bashi amsa cikin wasa. 

murmushi yayi sannan yace. 

"To idan dai kina son in ce miki Aunty to ki dage ki k'ara tsawo."

ido ta lumshe tare da fidda sassanyan nufashi kana tace.

"Ina Hamma Saifuddeen?  Ya jikinshi?  Da sauk'i sosai ko? yana tashi zaune da kanshi?."

kai ya liggob'ar tare da cewa. 

"Wayyo Allah na to wacce tambaya d'aya nasan zan amsa miki?." 

cikin zak'uwa tace. 

'"Duka zaka amsa min."

murmushi yayi kana yace. 

"A ina kika samu wannan number tawa?."

"Kai dai me ruwanka da inda na samu number kawai gaya min ya jikin Hamma."

cikin halinshi na tsokana yace. 

"In baki gaya min inda kika samu number taba yasee bazan baki amsoshinkiba."

Da sauri tace. 

"Dr Aliyu na tambaya shi ya bani dan Allah nuna min shi."

murmushi yayi tare da kallon Saifuddeen dake konce amman a jingine in ka ganshi kamar a zaune.

Da sauri ya dawo saitin Saifuddeen d'in dan ganin yana tambayarshi da waye yake mgn. 

Dai-daita fuskokinsu yayi da fuskantar wayar yadda zasuga juna da kyau, 

kana yace. 

"To gashi ina shine amsar tambayoyinki."

yana fad'in haka ya mik'e ya koma wurin kafafun Saifuddeen yaci gaba da yanke mishi k'ummarshi. 


Ita kuwa Amina cikin wani irin yanayi mai cike da farin cikin ganinshi  tayi mishi wani tattausan murmushi murya can k'asan mak'oshi tace. 

"Fatabarakallahu hasanil Kalil'in."

sai kuma ta lumshe ido tare sake bud'esu fuskarshi ta zubawa ido na tsawon 37 second a hankali tace. 

"Wallahi a duk iya tsawon rayuwata ban tab'a ganin wani mahluk'in da *Saje* yayi mishi kyau koda kwatankwacin rabin yadda Saje yayi maka kyauba."

sai ta kuma tonkoshe kanta bisa kafad'anta  na dama tare da cewa. 

"Darajar sajen wannan kekyawar fuskartaka yasa idanuna gaza barin kallonka, 

Hamma Saifuddeen kana kallon kanka a madubi kuwa, ? antaba ce maka kai kekyawa ne kuwa?. "

Shiru yayi ko numfashi a hankali yake fiddawa yayinda ya zubawa motsin bakinta ido yadda yana gane duk abinda take cewa, 

kana yayi dib ya nuna mata sam baya gane komai. 

ita kuwa a zatonta Hayatuddeen ya fitane gashi shi kuma kurmane hakan yasa taci gaba da fadin sirrin zuciyarta .

"Saje ya maka kyau in nace maka kyau ina nufin zazzafan kyawun da in dai mutun ba farin sani yayi makaba, in dai irin gani ɗaya zuwa biyu ne to wlh-wllhi bazai taɓa ganekaba duk yadda ya kai da rik'e kamanni!. in dai ba'ance mishi kai bane

Da kana jina da sai in ce maka. 

Dan Allah da darajar iyayenmu dan alfarman anabi da Qur'an kada ka sake aske sajen fuskarka ka barshi dan soyayyarka da manzonmu saje da gemu alamace ta nagarta, kaikuwa managarci ne please kada ka aske min sajen nan."

Cikin wani irin yanayi ya rumtse idanunshi da k'arfi jin tana cewa.

"Ina sonk...!





Hahahaha wasa farin girki


                           BY

                  *GARKUWAR FULANI*

8/18/20, 7:53 PM - Ummi Tandama: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


        *NAKASA BA KASAWA BACE*


        

                      *Page 22*


                              *NA*

   

               *AYSHA ALIYU GARKUWA*


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇



_FREEE PAGE SUN ƘARE DAGA PAGE 22 IN KA/KIN SAKE GANI PAGE ƊIN A WASU GROUPS ƊIN SUNA YAWO DAI TO BABU SHAKKA NA SATANE, ƁARAYI ZASU FITAR BANI BA_


*FREE PAGES DAI SUN ƘARE KAT DAGA YAU SHINE ƘARSHEN FREE PAGE DAGA WANNAN FAPE 22 ƊIN AN ƘARE FREE PAGE, BIYA ƊARINKI UKU KACAL DAN CI GABA DA KARANCE LITTAFIN DAGA FORKO HAR ƘARSHE, TURO KATIN MTN NA 300 KACAL TA WANNAN NUMBER 09097853276 KO KUMA KA/KIYI MIN TRANSFER TA ASUSUNA NA JAIZ 0005388578 JAIZ BANK AISHA ALIYU GARKUWA, SAI KA/KI TURO SHAIDAR BIYANKI TA WANNAN NO DAI 09097853276. IN KA/KINSAN BAKI BIYA ƘUƊIN KARANTA LITTAFINBA NA ROƘEKI DA ALLAH KADAMA KI NEMA BARE KI KARANTA*



_AKWAI KAYAN GYARA NA MUSAMMAN GA MASU BUƘATA AMARE DA UWAR GIDAYE, INA BADA SAYAN ƊAƊƊAYA KO SARI, akwai abubuwa masu zafi da inƙanci kamarsu. Sumin, tartai na ƙasar chadi, akwai tsumi mai riɗi na sokotawa, akwai zumar gembu membila, akwai garin daka na mallaka da garin maɗi mai haɗe mace daga ciki akwai sa buzu kuwa, akwai garin sakayawa da garin da ba'a baiwa mai kishiya akwai ɗan batta akwai gimbiyar mata da kwanon  ƙasaitacciyar mace akwai  garin carmazaƙwoi akwai na gyara nono da mgnin narkanwa akwai butar sirri, akwai  garin yaji na maza da kuma sabulan gyara jiki da mayuka akwai jigidar sirri kana akwai magungunan sanyi masu inƙanci, da dai sauransu.... sayan na gari maida kuɗi gida, duk inda kike ina aika kaya, inada reshena a Gombe Yola da kuma Sokoto da mai buƙata ka/ki tuntuɓeni ta wannan numɓer 09097853276,_





       Ina son kabar sajennan afuskar ka, saboda ya matuƙar yi maka kyau sosai. irin kyan da ban tab'a ganin saje yayiwa fuskar wani d'a namiji kyau ba. Lumshe ido tayi tare yin k'asa da murya tace. 

"Kayi kyau fuskarka ta zama mai cikekkiyar kyau da haiba."

Yanayin yanda ta faɗi maganar cikin  shauƙi shiya sanya Hayatuddeen dake gefe sakin dariya tare da cewa.

 "Dagaske ashe sajennan yayi masa kyau? karki damu bazamu bari ya aske ba! tunda kin yaba, dan da alamu dai kin ƙyatsa ko".

Wani irin tsananin kunyane ya rufe Amina don sam bata taɓa kawowa aranta cewa Hayatuddeen na nan ba duk zatonta ya fita ne.  Hannayenta tasanya ta rufe fuskarta da sauri tare da datse ƙiran tana murmushi mai cike da tsantsar nishadi da farin cikin gani Saifuddeen. 

Shima Hayatuddeen dariya yakeyi sosai musamman yanda yaga Hamman nashi yayi jigum yana kallon bakinta tamkar wani me ɗaukan karatu ko k'ibta idon bayayi, saidai ya rage girman idanun nashi,

 tabbas yayi imani cewa Amina batasan da cewa Hammanshi na fahimtar maganar mutunba idan yana kallon bakin me maganar ba, tabbas da batayi wannan katoɓarar ba.

 Shikuwa Saifuddeen idanunsa ya mayar ya rufe yana mejin yanda heart ɗinsa ke beating, sam yarasa ma tunanin me zaiyi hakan yasa yanemi ƙaƙalowa kansa bacci. 


                       ***

A nan Nigeria kuwa Zaliha jiki asaluɓe haka kuma zuciyarta ɗauke da mamakin ganin Abdussalam da iyayensa acikin gidansu ta tura hancin motar tata cikin gidan.

 Tana gama dai-dai-ta parking ta ɗauki ƴar jakanta me kyau tare da buɗe murfin motar ta fito.  

Kaitsaye ɓangaren Mamy Hajiyar Ya Ahmad ta nufa, da sallama ɗauke abakinta ta kutsa kanta cikin falon, Mamy dake zaune akan kujera ta amsa mata sallaman nata fuska ɗauke da murmushi.

"Mamy sannu da gida". tafaɗa tana me nufar inda makeken fridge ɗin dake cikin falon yake.

 "Yauwa Zaliha ya wajen aikin naku?".

 cewar Mamy data maida hankalinta ga tv. 

"Alhamdulillah". tabawa Mamy amsa tana me ƙoƙarin kafa bakinta ajikin goran ruwan data ɗauka acikin fridge, dawowa cikin falon tayi tare da kwantawa akan kujera kana ta lumshe gajiyayyun idanunta wandanda suke cike da zallar zazzafar soyayyan Saifuddeen, wanda kullum take k'ara narkar da zuciyarta.

 Zahira ce tashigo cikin falon daɗan sauri, ganin Zaliha kwance yasanya taɗan tsaya tare da cewa 

"Laaa Adda Zalee dama kina nan?". 

Harara Zaliha ta wurga mata tare dacewa.

 "Da bananan ai bazaki ganni ba!".

  dariya Zahira tayi tare da cewa. 

"Dama kina da baƙo a BQ yanajiran dawowarki".

 Idanu Zaliha ta ɗan zaro cike da mamaki tace.

 "Baƙo kuma wajena yazo?".  

Mamy dake jinsu ne tayi murmushi tare da cewa "Bak'ofa akace miki ba dodoba, kike wani zaro ido Abdussalam ne yazo". 

Jitayi gabanta ya faɗi don sai yanzune ma tatuno ganin da tayi musu shida iyayensa a lokacin da zata shigo cikin gidan, fuska ta kwaɓe tare da langwaɓar da kanta gefe,  murya asanyaye tace.

 "Ayya Mamy mekuma yazoyi?". 


"Me kuwa zaizo yi idan ba abun da bakyaso ba, kullum muna miki faɗa akan kifitar da tsayayye guda ɗaya amma kinƙi, to dai Abdussalam kam yagaji da wainasa da kikeyi yaturo iyayensa sun nema masa izinin zuwa zance awajen mahaifinki, ko tantama banayi kuma nasan ya amince musu!" 

Wani irin ƙululun baƙin ciki ne ya tsaya amaƙoshin Zaliha, take haushin Abdussalam ya cika ranta, meyasa zaiyi mata haka batare da ya tsaya yaji ta bakinta ba? ɗan ƙaramin bakinta ta turo gaba tare da komawa ta kwanta.

"Tashi kije ko bakiji Zahira tace nemanki akeyi ba,

Kije ki sameshi ku fuskanci juna, inafa gaya miki Zaleeha kada ki bari ki k'ure Malam kinfa sanshi kaifi d'aya ne zafa kiyi kuka a sanda babu mai lallashinki".

 Mamy tafaɗa cike da kulawa,

 cikin turo baki gaba Zaliha ta-tashi daga kwancen da take tare da ɗaukan hand bag ɗinta tafice, sashinsu ta nufa fuskarnan tata babu fara'a ko kaɗan,  harta kusa kaiwa ɗakinta taji muryar mahaifiyarta inda take cewa.

 "Da kika dawo tun ɗazu kika tsaya shashancinki bakisan cewa kina da baƙo bane?".    bakinta taƙara turowa gaba tare da cewa.

 "Ni agajiye nake yaje sai wani lokaci kawai".

  kallon bata da hankali Mahaifiyarta ta tayi mata tare da cewa

 "Zaki shirya kije ki samesa ne ko ko sai na ɓata miki rai yaro yazo yana son ganinki kice yaje sai wata rana shi bawan gidanku ne, ko kin mance shi d'an wanene?".   

ganin yanda mahaifiyarta ta ta haɗe fuska ne yasanya ta buɗe ɗakinta ta shige tana me guna-guni acikin ranta, kayan jikinta ta rage tare da faɗawa bathroom, haka tayi wanka ranta duk acushe, koda ta fito sama sama ta shafa lotion ajikinta, riga da sket na wani purpule ɗin material tasanya, sosai kayan suka amshi jikinta sukayi ɗas. kallon kanta tayi amadubi, tabbas ita kanta tasan cewa kyawunta ya zarce misali, sannan tanada diri irin wanda ke ɗaukan hankalin maza,  yanda takeji aranta yasanya bata jin zama ta iyayin kwalliya akan fuskarta, saidai kuma abun da batasani ba shine ko babu kwalliya akan fuskarta tauraron kyawunta haskawa yake, farfumed ta fesa ajikinta me daɗin ƙamshi kana ta ɗauki wani purpule ɗin mayafi tayafa ajikinta, normal flat shoe ta zura aƙafanta kana ta murɗa handle ɗin ƙofar tafice, BQ ta nufa inda tuni tasake sanja yanayin fuskarta.


  Sallama tayi can aƙasan maƙoshinta haka ta tura kofar katafaren falon tashiga.  

duk da cewa sautin sallaman nata baifito sosai ba amma yaji sautin acikin kunnuwansa, lumshe idanunsa yayi sakamakon wani daddaɗan ƙamshi daya kawowa hancinsa ziyara, ahankali ya amsa mata da "Wa'alaikissalam!"    Cikin takunta me ɗauke da nutsuwa taƙaraso cikin falon tare da zama akan wata kujera dake nesa da wanda yake kai.  

Murmushi Abdussalam yayi tare da cewa

 "Barka da dawowa gimbiyar mata, kiyi haƙuri kindawo kuma na hanaki hutawa".   ɗan satan kallon inda yake tayi tare da ɗauke kanta gefe, sanin cewa ba lallai tayi magana ba yasanyashi cigaba da cewa

 "Kiyi hakuri nima zazzafar soyayyarki ce take hanani hutawa, ita ke ingizani wurin kafa naci.

Haƙiƙa yau ina cikin farinciki kasancewar nasamu izinin zuwa wajenki daga wajen Malam.

 Ina sonki Zaliha ina miki so me tsanani, tabbas kina da wata irin baiwa ta musamman wanda duk wani ɗa namiji idan yaganki dole zaiji wani abu dangane dake, burina bazai wuce naga na sameki amatsayin mata ta ba, dan Allah Zaliha ki amincemin ki duba girman soyayyar danake miki!". yaƙare maganar cikin yanayi na kwantar da murya. 

wani murmushi Zaliha tayi wanda ya sake bayyana asalin kyawunta, bakomai yasata murmushin ba kuwa face jin ta tsuniyar da Abdussalam keyi mata akan wai yana fatan tazamowarta mata agaresa,  lumshe kyawawan idanunta wanda ke masifar jan hankalin maza tayi tare da jingina bayanta da jikin kujera,  hoton kyakkyawar fuskarsa ne ke yawo acikin idanunta koda yaushe, wani irin azababben so da shauƙin ganinsa ne suka dirar mata alokaci guda, take yanayinta ya sauya wani irin sanyi taji na shiga jikinta,  ƙwaƙwalwarta ne ta tuna no mata lokacin data kalli cikin idanunsa, tsikar jikinta ne taji yatashi yayinda taji zuciyarta na bugawa da sauri-sauri ji take kamar tayi ta shelanta duniya tana sonshi tana kuma  nemanshi da buƙatar ganinshi.  

Abdussalam kuwa ganin tayi shiru kamar ma bata cikin hayyacinta yasanyashi ƙiran sunanta murya asanyaye yace.

 "Zaliha!". 

Ƙiran sunanta dayayi shiyayi sanadiyar dawowarta cikin sense ɗinta, ahankali ta buɗe idanunta da suke  cike da shauƙin ganinsa, sam bataso Abdussalam ya katse mata tunaninta ba, kasancewar ayanzu tunaninsa shiya zame mata abincin ruhinta, miƙewa tsaye tayi tare da duban Abdussalam daya ƙafeta da ido. 

"Zanshiga gida!". ta faɗa ataƙaice. 

Murmushi yayi tare da cewa. "Idan muna tare banaso kiyi nesa dani". 

Bakinta taɗan taɓe tare da cewa.

 "Saida safe".

 Bata tsaya jin wani abu daga bakinsa ba tasakai tafice daga cikin falon, shiru Abdussalam yayi tare da bin bayanta da ido, jin soyayyarta yake tana ratsa ko ina na jikinsa, jiki asanyaye haka ya ɗauki makullin motarsa shima ya fice daga cikin falon.

  Itakuwa Zaliha tana kaiwa part ɗinsu kai tsaye ɗakinta ta wuce, kwanciya tayi luf akan gado tare da hugging pillow, idan da ace za a fasa zuciyarta to tabbas za'atarar da tarin begensa acikinta, wani irin abu takeji dangane dashi na musamman, sake rungume pillow'n tayi tare da sakin wata sassanyar ajiyar zuciya, a hankali take cewa. 

"Ina kake?  Me sunanka? Meyasa ka taimakane duk da ban sankaba baka sanniba?  wani hali kake ciki? Me sukayi maka? Kana ina?."  sai kuma ta kife kanta tare da sa kuka mai cike da rauni.



                    *Mumbai*

Yau tun safe su Hayatuddeen suke asibitin kasancewar yaune ranar da zasu gana da manya manyan likitotin guda hud'u da sukazo musamman dominsu.

 Alhamdulillah ƙarfe biyu dai- dai suka samu ganawa da Saifuddeen, sunyi masa  duk wani abun daya dace, sosai suka bincikesa suka kuma bashi duk wani iya taimakon da zasu iya, wanda kuma suke sa ran In sha Allah watara komai zai dai-dai-ta. 


Bayan wata ɗaya. 

Alhamdulillah acikin waƴannan kwanakin da suka gabata abubuwa da yawa sun faru ciki harda zuwan Mudassir, wanda ya shaidawa Ahmad kasuwarsu na buk'atarshi dan haka in jikin Saifuddeen da sauk'i to yayi k'ok'arin dawowa 9j.

kana sosai Saifuddeen ke samun sauƙin.

 Zuwa yanzu yakan iya juyawa da kansa ya kwanta ta ɓangaren damansa, in yana rigingine kuma yana iya juyawa hagunshi, sannan yana ɗan iya motsa wasu gaɓɓai dake jikinsa, kuma acikin kwanakin da suka gabata ne.

 Dr Akash prasat da Dr Malik khan sukazo har Mumbai ɗin suka duba jikinsa,yayinda agefe kuwa yake samun kyakkyawar kulawa daga wajen Dr Anan mehta da kuma Dr Mahesh khurana da kuma sauran nurses ɗin, sosai yakejin dadin zamansa a asbitin don suna ba sa kulawa ta musamman sosai yake jin canji a jikinshi,  duk da cewa jinya yake amma hakan baisanya kyawunsa  gushewa ba, saima wani hasken fata da ya ƙara sabida tsananin hutu da kula da zama wuri mai kyau da ya samu, yayinda wani irin kekyawan saje yasamu mazauni akan kyakkyawar fuskarsa, zaman sajen akan fuskarsa ba ƙaramin  ƙarawa fuskarsa kyau yayi ba, domin duk kyan namiji in dai fuskarsa ba saje tofa tsirara take bata da sutura.

    Ganin jikin nasa da sauƙi yasanya Dr Adnan da Ahmad suka shirya akan zasu dawo gida Nigeria. 


 Yau da ƙarfe uku na yamma jirginsu zai tashi hakan yasanya tun safe suka kammala shirya kayansu tsab inda zasu bar Hayatuddeen, dan kuwa zuwa yanzu jikin Saifuddeen sai dai ace Alhamdulillah.  Hayatuddeen ne yaturo ƙofar ɗakin ya shigo hannunsa ɗauke da wasu manya manyan leda guda biyu, wanda jikinsu ke ɗauke da tambarin *Inorbit mall malad west Mumbai* kasancewar nan yaje yayi musu sayayyan ƴan abubuwan buƙatansu dangin kayan sawa da duk wasu abubuwan da baza'a rasa ba shida Saifuddeen. 


 Aje ledodin yayi akan gado yana me duban Dr Adnan da Ahmad wanda yake ƙoƙarin zuge jakan kayansa. 

Murya asanyaye yace.

 "Ya Adnan lokacin tashin naku yakusa ko?". 

Murmushi Dr Adnan yayi tare da dafa shoulder ɗinsa cikin kulawa yace.

 "Badai kuka zakamana ba".  Ɗan murmushi yayi tare da son maida hawayenshi   tare da cewa

 "Sai kace ɗan ƙaramin yaro, kawai dai zanyi missing d'inku".

Dariya Ahmad da Adnan sukayi Ahmad ne yace.

 "Ehem dakai ɗin babbane? sakalallen Ummi kawai! Ba gashi har idonka ya ciko da ruwan hawaye ba".

 Dariya sukayi su dukansu kana suka nufi hanyar fita. Hayatuddeen ne ya riƙewa Dr Adnan jakansa, kana suka fice daga cikin ɗakin hotel ɗin.

  Kaitsaye asibiti suka nufa don yin sallama da Saifuddeen. 


Kamar koda yaushe kwance yake akan gadonsa yayinda kyawawan idanunsa ke rufe, ahankali Dr Adnan ya turo ƙofar ɗakin ya shigo kana su Ahmad suka biyo bayanshi,   Jikin gadon ya ƙarasa tare da sanya hannunsa yaɗan taɓa Saifuddeen. 

 Ahankali ya ware idanunsa wanda samansu ke ɗauke da zara-zaran eye lashes da suka matuƙar ƙarawa fuskarsa kyau, ganin Dr Adnan ya sanyashi sakin tattausan murmushi, shima Dr Adnan ɗin murmushi yayi tare da cewa.

 "Zamu wuce Saifuddeen lokacin tashin jirginmu yakusa."

Sai kuma ya d'an kalli sajenshi kana yaci gaba da cewa.

"Allah Ubangiji ya ƙara maka lafiya! Yasa nanda wata d'aya ka mik'e tsaye da k'afafunka".

  still murmushi Saifuddeen yayi tare da jinjina kansa kana yayi masa alamar godiya.

   Kallonsa ya maida kan Ahmad tare da miƙo masa hannu, hannunsa Ahmad ya kama idanunsa cike tab da ƙwallan tausayin abokinsa kuma d'an uwansa, ganin hawaye kwance a idanun Ahmad yasanya Saifuddeen girgiza kansa alaman kada ya bari hawayen idanunsa su zubo, da sauri Ahmad ya shanye hawayensa tare da juyawa da sauri yafita daga cikin ɗakin don bayajin zai iya jure tsayuwa agaban Saifuddeen batare daya zubda hawayensa ba.


  Cikin dakiya Dr Adnan yayiwa Saifuddeen bankwana don shima hawayenne cike a idanunsa kawai dai shanyewa yake dan kada ya raunata zuciyar Hayatuddeen. 

Tare da Hayatuddeen d'in suka fito kuma shi ya rakasu har airport saida yaga tashinsu sannan yadawo asibitin domin zuwa yanzu Hayatuddeen ya zama ɗan gari a india. 


               Nigeria k'asarmu ta gado.


Su Dr Adnan sun dawo gida cikin halin ƙoshin lafiya yayinda dawowarsu ya ɗan sanyaya zuƙatan masoyan Saifuddeen kasancewar sunji kyakkyawan labari daga garesu, inda hankalin Ummi ya ɗan daɗa kwanciya musamman da Dr Adnan da Ahmad suka shaida mata cewa ayanzu Saifuddeen har ɗan iya motsa jikinsa ya keyi, sannan kuma sauƙi yana samuwa sosai, inda kuma suka shaida musu cewa sun bar asibitin dake new delhi sun koma wanda ke garin Mumbai.

   Adda Rahama kuwa ganin mijinta da jin labarin jikin ɗan uwanta yasanya hankalinta ya ƙara kwanciya don dama takusa shiga watan haihuwarta gab take da fita a wata na takwas. 


Daren randa suka dawo bayan Ahmad ya gama kontarwa Ummi hankalin ganin dare ya tsala ne ya mik'e tare da kallon Raliya cikin sanyi da begen matarsa wata uku har an shiga na hud'u kenanfa.

"Tashi muje ki hada min ruwan wonka."

yace da ita, 

kai ta rausayar tare da mik'ewa tabi bayanshi dan tabbas ta hango wutar begenta da sha'awarta a idanunshi.

Suna shiga bedroom nata yasa hannu ya jawota suka fad'a kan gado blanket ya jawo ya rufesu tare da cewa. 

"Hak'uri nafa ya k'are ina gab da macewa in ban samu d'umin jikinki ba."

ido ta lumshe tare da shigewa jikinshi.


Hakama Ya Adnan sam ya kasa d'agawa Adda Rahma k'afa duk da tsohon cikinta.


Sati ɗaya da dawowan su Dr Adnan Ummi da Ishaq da kuma mahaifiyar Ishaq ɗin suka shirya tsab don zuwa India,

   wata ranan Asabar da sanyin safiya jirginsu ya ɗaga zuwa India. 


                  India. 


Hayatuddeen ne zaune akusa da gadon Hamma Saifuddeen d'inshi  wayarsa dake cikin aljihun wandonsa tasoma ƙara, ciro wayar yayi tare da duba sunan me ƙira "Zakari".

 shine sunan dake yawo akan screen ɗin wayar, murmushi yayi dan tuno kullum sai Zakariyya yayi ta musu fasifar su dena yanke mishi suna suna medashi sunan wani abu da ban dariya yayi tare da amsa ƙiran kana ya kara akan kunnensa tare da cewa.

"Zakari namu ina kake ne?."

Zakariyya dake jingine da jikin motar Zaliha yanajin Hayatuddeen ya ɗaga wayan yaja tsaki tare da cewa.

 "Yana cikin wondonka banzaye kawai, masu mgnar banza."

dariya sosai Hayatuddeen yayi kana yace.

"Yi hak'uri Ya'u namu."

tsakiya ya kuma ja kana yace.

 "Gwara dai ba indiye ya akayi ne? Don katashi daga ba gombe ka koma ba indiye mai katon z!".

Dariya Hayatuddeen yayi tare da ɗan gyara zamansa kana yace.

 "Amma Zakariyya baka da mutumci.

To Oho dai koma dai menene ina lafiya".

Dariya Zakariyya yayi tare da cewa.

 "Masha Allah to yajikin Hamma Saifuddeen Ina fatan da sauƙi sosai ko?". 

"Jiki Alhamdulillah da sauƙi sosai wlh,."

Masha Allah. Allah ya kara sauk'i."

"Amin Amin." yace cikin jin dad'i tare da ci gaba da cewa.

"Ya Nigeria?".

"Kai da kake ƙasar Indiyawa mene haɗinka dawani tambayar Nigeria?".

 Zakariyya yafaɗa cikin tsokana.

"Ko madai mene ae Nigeria ƙasatace kuma nanne tushena abin al'fahari na."

"To Nigeria tana lfy."

Gyara zamanshi yayi tare da cewa. 

"Ina hajia Zaleeha masifaffiyar yar jarida?".

 Hayatuddeen yatambaya cike da neman tsokana. 

Dariya sosai Zakariyya yayi tare da cewa.

 "Kana zancenta sai gata ta iso".

 Duban Zuleeha Zakariyya yayi wacce tasha ado cikin wani tsadadden pink shadda me kyaun gaske, cikin rausayar dakai gefe yace.

 "Adda Zaleeha Hayatuddeen ne please gashi ku gaisa".


Zaleeha wacce take ƙoƙarin buɗe murfin motarta kana ta tab'e baki ta amshi wayan batare da tayi masa musu ba dan tasan sai in zai tsokaneta yake ce mata Adda,

cikin zazzaƙan muryarta tace "Hello Hayatuddeen!".

Jin muryan Zaleeha yasanya Hayatuddeen sake gyara zama kana yace.

"Adda Zalees ina wuni ya aiki?".

Murmushi ta ɗanyi tare da cewa.

 "Alhamdulillah ya mai jiki?"

"Jiki da sauƙi sosai" Hayatuddeen ya bata amsa. 


"Allah yaƙara sauƙi".

 tafaɗa tare da miƙowa Zakariyya wayarsa. Nan Hayatuddeen da zakariyya suka ɗan taɓa hira daga bisani sukayi sallama. 


Jirginsu Ummi na dira aƙasar ta india taji wani irin faɗuwar gaba ya rusketa, take taji wani irin fargaba, tsoronta ɗaya kartaje tasamu Saifuddeen ɗinta awani hali, Ummun Ishaq ne ta tara musu taxi inda kae tsaye suka faɗa masa inda zai kaisu sabida kwatancen dasu Dr Adnan suka musu,  agaban katafaren asibitin mai taxi ɗin ya sauƙesu, batare da wani shan wahala ba suka isko ɗakin da Saifuddeen ke kwance.

Ɗaya daga cikin nurses ɗin dake kula dashi ne tayi musu jagora zuwa cikin ɗakin,   kwance yake flat akan gado kamar wani wanda yake bacci.

 Hayatuddeen dake zaune yana charting da Amina wayarsa ya ɗago da saurin jin muryar Umminsu, wani irin tsananin farinciki ne ya bayyana akan fuskan Hayatuddeen cike da tsananin kewarta ya mik'e da sauri ya ƙarasa gareta tare yana isa ya fad'a jikinta tare da cewa.

 "Oyoyo Ummi na!".

Murmushi Ummi tayi tare da sanya hannu ta shafa kansa, cikin ƙaunar ɗannata tace "Na'am Autan Umminshi". dariya yayi tare da duban Umman Ishaq cikin girmamawa yagaida ta, fuska asake ta amsa masa gaisuwan tare da tambayarsa ya mai jiki.

 "Da sauƙi, Umma ina Imran" ya bata amsa yana me duban Ishaq dake tsaye yana murmushi tamkar wanda yake kallon abun da sukeyi, ƙarasawa yayi ya kama duka hannayen Ishaq cikin son abokin hamman nashi yace "Ya Ishaq sannunku da zuwa".

  murmushin dake kan fuskar Ishaq ne ya faɗaɗa hannunsa yasanya ya dafa kan Hayatuddeen cike da kulawa yace.

 "Auntan Ummi Me jinya barkan ka dai, ya jikin Saifuddeen?!".

Ƴar dariya Hayatuddeen yayi cikin yanayin dayake ciki najin daɗin ganinsu da yayi yace.

 "Jikin Hammana da sauƙi sosai Ya Ishaq, don zuwa yanzu yana ƙoƙarin yin wasu abubuwa da kansa".

 cikin tsananin jin daɗi su dukansu sukace.

 "Masha Allah- Allah yaƙara mishi lafiya".

 Ummi ce taƙarasa jikin gadon da Saifuddeen ɗin ke kwance, idanu ta zuba masa tana mejin tausayi haɗi da ƙaunar ɗan nata na ratsa ko ina na jikinta. 

Ahankali ya buɗe manya manyan idanunsa, tarwal ya sauƙe ganinsa akan fuskar mace mafi soyuwa agaresa wato UMMI'n sa, cikin tsananin farin cikin ganinta ya sanya hannuwansa ya kamo nata hannun. 

Murmushine ya bayyana akan fuskar Ummi'n cikin jin daɗi tace.

 "Ashe ma ba bacci kake ba"

Gane abun data faɗa yasanyashi kaɗa mata kai, tare dayi mata alaman cewa. "Koda ma bacci nake indai kece kika tsaya akusa dani dole za  farka."

 murmushi Ummi tayi dan tana tsananin gane body language , dai-dai lokacin Ishaq ya ƙaraso jikin gadon, tamkar wanda yake gani haka ya ɗaura hannayensa adai dai saitin zuciyar Saifuddeen cikin kulawa yace "Ko wani bai faɗamin ba yanda naji zuciyarka na harbawa nasan kana samun sauƙi".

 murmushi Saifudden yayi tare da sakin hannun Ummi ya kamo na Ishaq ya riƙe cike da ƙaunar abokin nasa, mahaifiyar Ishaq ne taƙaraso tare da duban Saifuddeen cike da kulawa tace "Saifuddeen ya jikin naka?"  dayake yana kallon fuskarta ne hakan yasanyashi gane me take nufi,  kansa ya kaɗa mata tare da ɗan motsa laɓɓansa alaman da sauƙi,   sosai su UMMI da Ishaq suka jima awajen Saifuddeen har dare kafun Hayatuddeen yayi musu rakiya inda zasu kama hotel, anan hotel ɗin Sahar International Mumbai suka sauƙa inda Ummi da Ummun Ishaq suka kama ɗaki ɗaya, shikuwa Ishaq nan ɗakin Hayatuddeen ya sauk'a, ganin sun samu masauƙi ne sun ci abinci yasanya Hayatuddeen komawa asibiti wajen Hamman sa... 


               ***

A Nigeria kuwa Yanzu Adda Rahama ta shiga watan haihuwanta, yanzu ma zaune take akan kujera yayinda ƙaton cikinta ya cika mata gaba, aje kofin tea ɗin dake hannunta tayi tare da kai dubanta ga Dr Adnan wanda ke gefenta yana me aiki a laptop ɗinsa, cikin kwantar da murya tace.

 "Dan Allah Ya Adnan yaushe ne zanje naga Saifuddeen? koda yaushe idan nayi maka magana sai kace nayi haƙuri ba yanzu ba!".

 taƙare maganar tana me langwaɓar da kanta gefe. Murmushi Dr Adnan yayi tare da dubanta cikin son kwantar mata da hankali yace.

 "Kiyi haƙuri ba na hanaki zuwa bane, kinsan dai halin da kike ciki yanzuma haka kinsan kinshiga watan haihuwan ki haihuwa yau ko gobe, kiyi haƙuri idan kin haihu zamuje tare dukanmu!". 

Sake shagwaɓe fuska tayi tare da cewa.

 "Shikenan ai dai kullum haka kake cewa, Allah yasa na haihu lafiya ko sati bazan ƙara ba zanje na gansa!".

Dariya me kama da murmushi Dr Adnan yayi tare da kama hannunta ya shiga murzawa, cike da ƙaunar matar tashi yace.

 "Karki damu zamuje ki ga ɗan ƙaninki".

Murmushi tayi tare da ɗaukan cup ɗin tea ɗinta tacigaba da sha kaɗan kaɗan. 

Koda dare ya d'anyi nisa misalin ƙarfe 9 naƙuda ta tasowa Adda Rahama gadan gadan wanda har saida yakaisu ga zuwa asibiti, ƙarfe 10 dai-dai ta haifo kyakkyawan ɗanta na miji,me kama da ita sak,  farin ciki awajen Dr Adnan ba a magana, nantake yashiga ƙiran mutane yana sanar musu, koda ya sanarwa mahaifiyarsa baƙaramin murna tayi ba, nan ya bugawa mutanen India  yasanar dasu, daɗin dasu Ummi sukaji baya faɗuwa nan yabata waya suka gaisa, inda Saifuddeen kuwa ya ɗauki wayarsa ya tura mata saƙon murnar haihuwar da tayi lafiya tare dayin kyakkyawan addu'a ga yaron data haifa, koda takaranta saƙon sosai taji daɗi inda ta mayar masa da amsa tare da tambayar jikinsa. 


Alhamdulillah kulawa ta musamman Adda Rahama ke samu daga wajen mijinta da mahaifiyarshi Dr Adnan inda yaɗau soyayya da tarairaya ya ɗaura ga yaronsu da suka haifa.


 Ranan da ta cika kwana huɗu da haihuwa Raihana tazo daga Kaduna, sosai taji son yaron yana ratsata kyawun yaron  ba, don idan ma idanunta ba ƙarya sukai mata ba har kamannin Hamma Saifuddeen ɗinsu ta hango akan fuskar yaron. 


 Ranan da tacika kwana 7 da haihuwa arananne aka sha shagalin suna wanda yasamu halartar ƴan uwa da abokan arziki, inda yaro yaci sunan SAIFUDDEEN.  sosai bikin sunan ya ƙawatar don kuwa Dr Adnan ya buɗe bakin al'jihunsa inda ya gwadawa mai jego da ɗanta gata, anyi taron suna an watse lafiya sai- dai muce masha Allah, koda su Ummi sukaji sunan yaron Saifuddeen baƙaramin murna sukayi ba musamman Ummin nan tace ake kiranshi da Deen.


              India.

Yau su Ummi suka cika sati a India kuma yau ne suketa shirye shiryen dawowa Nigeria, sosai kuma suka aminta da sauƙin da Saifuddeen ke samu don ayanzu su kansu sun samu nutsuwa a zuciyoyinsu,  tsab suka gama shirya kayansu, inda suka wuce asibiti don yiwa Saifuddeen ban kwana,  sam Saifuddeen baiso tafiyansu ba saboda zuwansu sosai ya ɗebe masa kewa musamman daya kasance kullum suna tare da abokinsa Ishaq, haka su Ummi sukayiwa Saifuddeen sallama bayan Ishaq ya basa maƙudan kuɗaɗen da Ƙungiyansu ta *Joint National Association Of Persons With Desabilities. (Jonapwd) Gombe state chapter. All the best!👍🏻* suka bada abasa kamar yanda suke bawa kowani member ɗinsu wanda ke cikin hali na rashin lafiya, sam Saifuddeen ƙin karɓa yayi shikuwa Ishaq rufe idanunsa yayi ya dage dole saida Saifuddeen ya amsa bisa sanya bakin Ummi. 

Hayatuddeen ne ya rakasu airport inda suka hau jirgi daganan sai Nigeria. 


Koda suka dawo agidan Adda Rahama suka sauƙa inda suka duba yaro, daganan Ummi ta wuce gidanta Ummun Ishaq ma ta wuce nata gidan...


Yau Jummu'a ta kasance ranar da Zaleeha ke gabatar da program nata mai taken babu nakasasshe sai rago. 

Bayan ta gama gabatar da shirin natane ta shigo wurin masauk'i bakisu, 

a hankali ta zauna akan wata baƙar kujera dake cikin office ɗinsu  wanda ke cikin gidan radion vission FM. 

Sanye take da wata haɗaɗɗiyar doguwar rige me walwali yayinda tayi rollin kanta da mayafin rigar, sosai rigan ta bayyana tsananin kyawunta, wayarta ƙiran iphone 11 pro max ne riƙe ahannunta tana latsawa.  Manager da shigowarsa offie ɗin kenan cak ya tsaya yana kallonta, sosai take burgesa komai nata abun so ne ga ɗa Namiji, haƙiƙa yasan Zaleeha dabance acikin mata. 

Ahankali yatako zuwa inda take, Zaleeha da hankalinta gaba ɗaya ke kan wayarta ta ɗan ɗago kanta tare da dubansa, ganin Manager da kansa acikin office ɗin nasu yasanya ta sakin murmushin da ya sake bayyana kyawun fuskarta, cikin zazzaƙar muryarta tace.

"Barka da shigowa Manager!" 


Murmushi Manager yayi tare da ɗan lumshe idanunsa, dan sosai yakejin wani abu na musamman a dangane da ita. 


"Barkanki dai Sarauniya" Manager yafaɗa yana murmushi. 


Aɗan mamakance ta kalleshi  jin yaƙirata da sunan sarauniya.  


"Sarauniya kuma manager?" tafaɗa tana me ƙoƙarin rataya hand bag ɗinta don dama lokacin tashinta yayi. 


"Kin ma wuce haka Zaleeha, ke tamkar zara kike acikin dubbanin taurari! ko ince zinariya" 


Yanzu kam sosai maganganun Manager ɗin yabata mamaki don baitaɓa mata irin waƴannan maganganun ba. 

Murmushi kawai tayi tare da dubansa kamar zatace wani abu sai kuma taɗan raɓa ta gefensa zata wuce.  Da sauri yaƙira sunanta, inda yace.

 "Zaleeha!"

Jin yaƙira sunanta yasanya taɗan tsaya tare da juyowa ta fuskance sa. 

Gyara tsayuwa yayi tare da zura hannayensa cikin al'jihun wandonsa cikin tausasa murya yace.

 "Zaliha Ina sonki! Inada buri da fatan ki zamo matata uwar yarana na".

idanunta ta zazzaro da sauri sai kuma ta fara jan baya-baya ganin yana takowa zuwa gabanta, 

da sauri ta rumtse idanunta ganin ogan nata kuma babban mutun ya durk'usa gabanta da guiwowinshi duka biyu, 

hankalin ta ya kuma tashi jin yana cewa.

 "Na dad'e ina adana soyayyarki a zuciya ta, ina sonki irin so mai kauda nitsuwar mutun, kece fatana ki zame min matata ta biyu, shine cikar burina. 

Ina matuk'ar jin tsoro da fargabar kada na rasaki."

Wani azabebben ajiyan zuciya Zaheela taje tare da yin mgnar zuciya. 

"Meyasa? Meyasa ne?  mutane sukayi mata caaa a kanta, meyasa tun da can basu baiyana kansu gareta ba sai yanzu da Allah ya jarab ceta da son wanin namijin.

ido ta rumtse tare da bud'esu sannan tayi k'asa dai-dai gaban manager d'insu ta durkusa kamar yadda yayi cikin son yakice soyayyarta a zuciyarshi murya na rawa tace. 

"Kai matsayin yayane a gareni, koda zan boyewa kowa kai dai bazan boye maka ba Ya Abubakar.

Zuciyata ta cika ta batse tana zubda tururin zazzafar soyayyar da nake mishi, ina gab da rasa lfyar zuciyata muddin ban sameshi ba, ya shigemin zuciya  a lokacin da ni kaina ban Sabina, shine fatana, bani da mosoyi samadashi shine kad'ai mahaluk'in da zan iya mallakawa kaina,

shine abinda zuciyata keso. Tabbas da ka gabatarmin da kanka kafin had'uwata da shi to da na aminta da kai."

Idanu ya zuba mata yayinda yake gano wutar so da gskyar mgnarta cikin kwayar idanunta, 

cikin tsananin kad'uwa yace. 

"Waye ne shi?."

cikin zubda hawaye tace. 

"Oho shine abinda nima nake son in sani."

ido ya firfitar cikin azama yace. 

"Baki sanshi bane?."

Kai ta gyad'a mishi tare da yunk'urawa ta fita da sassarfa dan kukan dake taho mata.

wani mayataccen murmushi yayi tare da cewa. 

"Wannan ai shirmenki ne, dama kin sanshi ya sankine dole in hak'ura amman yanzu  dole in nace."


Ita kuwa tana fita ta nufi parking lot nasu, 

tana isa wurin tayi kicibus da Abokin aikinta Raveel, ganin yadda take saurine yasashi saurin sa hannunshi ya kamo nata cikin tsareta da ido yace.

"A haka zakiyi draving so kike ki kashe kanki ni ki illatamin rayuwa ne?."

fuzge hannunta tayi tare da cewa. 

"Ka sake min hannu."

cikin tsawa yace. 

"Ank'i a sake d'in, ni da kika rik'e min zuciyata bance ki sakemin itaba sai ke dana  rik'ewa hannu. 

Na gaji da ganinki cikin damuwa, yanzu tsawon wata hud'u kenan na fahimci kina cikin matsala ki gaya min make damunki?  meke faruwa da rayuwarki?."

tattaro sauran k'arfinta tayi ta fizge hannunta tare da wucewa ta shiga motarta ta figi motar da gudu ta nufi gidansu Bilku k'awarta da tasan sirrin soyayyar da take boyewa a ranta.


Ahmad ne da kawunshi Bappa Ali dasu Warusu da Mudassir da bello ke zaune a babban falon Ummi yayinda Ahmad ya tasa na'urar system a ganshi suna kallon Saifuddeen kana shima yana kallonsu.

Tattaunawa sukeyi kan kasuwancinsu da Allah ya sanya mishi al'barka.

Duk shiru sukayi suna sauraron bappa Ali da yake ware musu kud'in hakk'in aikinsu na cikon shekara.

Sannan ya hada lissafin da suka kawo baki d'aya, 

kana ya shiga cikin hatimin zakka, 

Kai ya d'ago ya kallesu tare da cewa. 

"Zakkarmu ta bana ta kama million hud'u da dubu dari biyu da hamsin da uku zamu fidda."

cikin gamsuwa sukace.

"Na'am."

cikin nitsuwa bappa Ali ya kalli fuskar Saifuddeen ta na'urar tare da cewa.

"Su waye kakeda niyar bawa zakkarka?."

gyara konciyarshi yayi tare da jawo system d'in nashi ya gyara zamanshi kan ruwan cikinsa kana ya fara rubutu musu mgnarshi. 

"Akwai bappa idi bappan Ummi dake garin Hashidu, a ware dubu dari biyar a bawa Ahmad da Ummi su kai mishi.

sai Goggo Abu Goggon Ummin a bata dubu dari biyu da hasin d'in.

Million d'ayan kuma Mudassir da Warisu su d'auka,

Bello kuma a bashi rabin million, 

Sannan million biyu daya range d'in a rabawa makotanmu na dukku."

cikin gamsuwa bappa Ali yace. 

"Hakan yayi Allah ya sanya al'khairi."

Amin Amin sukace baki d'aya, 

sai kuma Ahmad ya kalleshi tare da cewa. 

"Sai zakkar kasuwarka ta omo da kayan sanyi.

shi dubu dari takwas da hamsinne zakkar."

ya za'ayi dasu?."

Murmushi yayi wanda saida fararan hak'oransa suka baiyana cikin ratsin jajayen lips inshi. 

amsa ya rubuta mishi da cewa. 

"Wannan na goggo nane a bawa goggo Dada zakkan d'anta gaba d'aya."

Cikin shak'uwa Ahmad yace.

"A a kai malam wai ni bazaka bani zakkar bane?."

Kai ya gyad'a mishi tare da mishi alamun kaima mai badawa ne.

Dariya sukayi baki d'aya, 

kana Warisu yace. 

"Anfa gyara shagon da kasaya dinnan, sauran zuba kaya kawai."

Kai ya jinjina tare da rubuta. 

"next week Ahmad zai tafi Dubai shida Raliya da Anty Kubra zasuje suyi mana sarin, kayan yara da na yan mata da kamarsu dogayen riguna gyalluka zanuuwan gadaje kananun kaya da sarak'una."

Kai ya jinjina cikin gamsuwa shi kuwa Ahmad shafa kai yayi tare da cewa. 

"Jiya da Safe Jabeer d'in ya kirani yace ya gama yi mana shirin komai."

da yake da Jabeer d'in zasuje.

kai Saifuddeen ya rausayar tare da rubuta mishi. 

"Eh yama turomin hotunan sabbin kayyakin da ake hari, kai dai ka zama cikin shiri."

bappa Ali ne ya gyara zamanshi tare da cewa. 

"To batun sarinmu na kayyakin abinci duk dama kasuwannin sun tanadarmin dan na basu adaddin da nike buk'ata. 

Sannan kasuwar magi shi tuni Ahmad ya sara, saura ya tura musu kud'in."

Cikin gamsuwa ya rubuta musu.

"Bana kuma kamfanin k'ananan baturan radio sun tallata min hajarsu. Shiyasa na rage sarin magin zamu sari baturan koda kad'an ne."

Eh hakan yayi cewar Bella da Muddasir.

Daga nan suka tattauna yadda komai zai wakana sannan suka tashi taron.


Abuja birnin taraiya. Amina ce zaune gaban Mommo Hajia Salma kekkyawar bafillatanar jada. 

cikin kula tace. 

"Niko ya lbrin jikin Saifuddeen?."

ido ta d'an rufe cikin jin kunya tace. 

Mommo jikinshi da sauk'i yanzuma muka gama mgna da Hayatuddeen.

Yace min yanzu yana iya jujjuyawa da kanshi."

Cikin gamsuwa dan duk familynsu sun san Saifuddeen a sanadinta sabida yanzu dai a rayuwarta tafi son mgnarshi fiye da komai. 

Haka yasa iyayenta ke tsananin jin dad'i dan tunda Amir ya saketa bayan aurensu da sati d'aya bata kuma yin mgnar wani d'a namiji ba sai kan Saifuddeen ko dan haka baya rasa nasaba da rashin mutuncin  da Ya Amir ɗin nata ya  mata wanda suke ƴaƴan maza kuma a gidasu ya Amir ɗin a gaban mahaifiyarshi ta girma kasan cewar shi ɗaya suka haifa ita mahaifinta da mahaifiyarta suna Jadan Adamawa.

shekararta d'aya da rabuwa da Amir kafin ta had'u da Saifuddeen, 

cikin sanyin murya Mommo tace. 

"Kwanan Daddynku zaije India, in yaje zai isa ya dubashi da jiki."

murmushi tayi mai cike da Happy tace. 

"Badon aiki da yamin yawaba da munje tare."

itama Mommo murmushi tayi kana tace. 

"A a ki bari sai sun dawo Nigeria sai muje mu duboshi da jikin."

cikin gamsuwa tace.

"Allah ya dawo dasu lfyto."

Amin Amin tace kana sukaci gaba da hira.



                *************


A hankali fa rayuwa ke tafiya kwanaki na shud'ewa i zuwa makonni makkoni na juyawa i zuwa watanni. 

Abu da yawa ya faru cikin watannin nan kamar zuwan Daddyn Amina da zuwan Adda Rahma da Saminu da Raihana.

Da Mudassir da Warisu.


Kasuwancin Saifuddeen yanata habaka ga amintattun ma'aikata da ya samu  bisa jagorancin Ahmad da su Mudassir.

Yanzu Ahmad shi iya dukiyar Saifuddeen tashi ta kanshi yake jujjuyawa kuma Alhamdulillahi kasuwancinfa sai gaba-gaba.

  

Yau watansu Saifuddeen goma sha d'aya cib a k'asar India.


Hayatuddeen ne ke zaune gefen Saifuddeen dake kwance bisa dukkan alamu bacci yakeyi.

shi kuwa Hayatuddeen  waya yakeyi da Umminshi shiyasa bai lura da Saifuddeen da yayi mik'aba tare da bud'e idanunshi.

ido ya zubawa k'anin nashi da yake waya yanata zuba sakalci wa Ummin nasu.

wani nannauyan numfashi ya firzar tare motsa k'ugunshi, sai kuma yayi saurin juyawa rigingine. 

Wani sabon lamari ne yaji yana dirar mishi cikin k'ashin bayanshi wanda kusan wata d'aya kenan yake jin abun. 

ido ya rumtse tare da d'ago kafad'unshi, 

kamar al'mara sai gashi ya d'ago kafad'unshi har zuwa k'ugunshi wani irin zafi yaji yana ratsashi sai kuma ya tauna lips inshi duka biyu, 

sannan ya yunk'ura da k'arfi sai gashi a zaune da daɓas duwawunshi zama kuma na gam da gam.

Dai-dai lokacin Ummi ke cewa Hayatuddeen

"Har yanzu bacci yakeyi ne?."

a hankali ya juyo kanshi, dai-dai lokacin kuma Saifuddeen ya muskuta tare da gyara zamanshi daram bisa tsakiyar gadon.

Cikin tsananin kad'uwa da tarin farin ciki da al'ajabi Hayatuddeen ya cilla wayarshi gefe tare da kurma wani irin firgitaccen ihun da tsalle tare,

"Ummeeee Hamma Saifuddeen ya tashi ya zauna kanshi."

sai ya kuma sakin wani hargitsestsen ihun  da yasa Saifuddeen jin kunnuwanshi sun bada wani sassanyan sautin  keuuuuuuuuuhh cikin kunnuwanshi daga nan kuma sai kuma jin shuuh a hankali abin yakeyi a kunnuwan nashi.

 ido ya zuwa Hayatuddeen wanda ya kware baki da iya k'arfinshi yake rabkawa Dr Anan kira. 

"Dr Anan! Dr Anan!! Doctor Anan!!!...!."


A can gida Nigeria kuwa cikin New G.R.A Zaleeha ce ta fito cikin parlour Baba malam fuskarta cike da hawaye, 

kai tsaye parking lot nasu ta nufa tana zuwa wurin Raveel na sako kai cikin gidan nasu. 

Da sauri ta shiga cikin motarta da gudu ta fita daga cikin gidan. 

Ganin haka shima Raveel yabi bayanta. 


Babu inda suka tsaya sai cikin gidan M...!



Ka/ki biya ɗari uku kacal dan jun ƙarshen labarin, in baki da ƙuɗi ba dole bane sai kin karanta na sataba, gwara ki karance tsoffin littataimana baya kinga bakici da gumin daba nakiba.



                           By

              *GARKUWAR FULANI*

8/18/20, 7:53 PM - Ummi Tandama: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


              *NAKASA BA KASAWA BACE*



                            *PAGE 23*



                                  NA

               *AYSHA ALIYU GARKUWA*


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇






 Sai cikin gidan Maryam tana isa shima yana isa. 

Kusan a tare suka fito cikin motocin nasu.

Da sauri ya nufi inda take fuska cike da tsantsar kulawa murya a hargitse yace. 

"Me hakan? Wannan wanne irin ganganci kikeyi da ranki? So kike ki fasamin zuciyta ne?."

Hannu tasa ta sharte hawayenta, yayinda tuni wasu suka biyo layin wad'anda ta gogen cikin raunin murya tace. 

"Meyasa haka? Raveel meyasa zakayi min haka meyasa zaka tura iyayenka wurin Baba malam bayan kasan yadda nake fuskantar takura a gida, meyasa zakayi min haka ni nace ka tura iyayenka gidanmu ne?."

K'ara motsowa yayi gabanta cikin fidda sassanyan numfashi ya lumshe ido tare da bud'esu kana yace.

"Sabida ina sonki, kin kuma sani ina sonki, amman kika nuna kamar baki saniba, kin barni soyayyarki nata d'awainiya dani, na rasa sukuni, bani da zabin daya wuce dole in sanyan iyayenmu cikin zancenmu. 

Zaleeha kin sannifa kinsan halina kinsan tarbiyata kinsa komai nawa to meyasa kike gujemin meyasa kike son nasantamu."

Cikin tsananin k'unan rai tace. 

"Sabida bana sonka, bazan aureka ba, kai ba abokin rayuwata bane."

Idonshi ya rumtse da k'arfi tare da bud'esu kana yace. 

"Ni dai ina sonki kuma dole insa iyayenmu cikin mgnar in dai ba so kike in mutuba."

A hatsale tace. 

"Sai me? ka mutu d'in mana, na ce bana sonka na tsaneka bazan aureka ba." 

ta k'arishe mgnar hawayenta na ci gaba da zubowa. 

Jin wani azabebben fargabane ya sashi jingina da jikin motarta dan jin alamun zai iya fad'uwa a hankali yace.

"To meyasa? Me aibuna?."

Da sauri tace. 

"Auren ne bazanyi ba ko akwai dole ne."

tana fadin haka tayi cikin gida, 

da sauri yasha gabanta tare da cewa.

"Baki isaba in sha Allah sai na aureki, sai na zama mijinki."

wani irin zafi taji kalamanshi na gasa  zuciyarta cikin hatsala ta d'ago hannu ta yarfa mishi mari tare da tureshi gefe ta wuce tayi cikin gida. 


Ya Ameenu kuwa yana sama yanaji da ganin duk abinda sukeyi. 

Ganin ta zubawa Raveel marine ya sashi fitowa ya nufi parlour k'asa da tsananin sauri har yana take steps d'in bibbiyu uku-uku dan azabar zuciya da zafin raina, 

tabbas yanzu ya yarda muddin akabar Zaliha zatayi abinda taga dama.


Tana isowa parlour yana sauk'owa, 

Da sauri ta tsaya tare da zaro ido ganin ya nufeta gadan-gadan. 

Yana isa inda take ya ware tafin hannunshi cikin zafin rai ya fara yayyarfa mata wasu gigitattun tagwayen marukan da suka sata ganin start's suna yawo kana kunnenta ya bada sautin kauuuu. 

kafin ta dawo daga gigicewar data shiga ta kuma jin wasu tsinannun marukan da suka sata cilla wani irin zazzafan k'ara mai gigita duk wanda ya jita. 

"Wayyo Maryam Ya Ameenu zai kasheni."

shi kuwa Aminu cikin haki yake ci gaba da yayyarfa mata mari yana mai cewa. 

"Ae gwara ki mutu kowa ya huta, 

tunda fand'arewa kikeso kiyi, 

Yanzu kinfi k'arfin mata sai maza. 

Ashe har kin kai matsayin da zaki d'aga hannunki ki mari d'a namiji, dan yace yana sonki."


Raveel kuwa tunda ta kwad'a mishi mari ya sunkuyar da kanshi k'asa, 

saida yaji ta saki ihunne yayi sauri ya kutsa kai cikin gidan. 

Maryam kuwa tana isowa parlour sai ta koma gefe ta zuba musu ido. 

Raveel d'inne yayi k'arfin halin kamo hannun ya Ameenu tare da cewa. 

"Dan Allah dan darajar iyayenmu kayi hak'uri ya Ameenu mu bita a hankali please kada ka daketa."


Ita kam Zaliha tuni tayi bedroom d'in Maryam a guje tana shiga tayi fad'uwan 'yam bori bisa gadon kana ta saki wani marayan kuka.


Shi kuwa Ya Aminu bisa kujera ya zauna tare da nunawa Raveel kujera alamun ya zauna. 

Bayan sun zaunane ya kalli Raveel cikin sanyi da tafasan zuciya yace. 

"Raveel kayi hak'uri da abinda Zaleeha tayi maka, 

In sha Allah daga kanka bazata sake gigin marin wani d'a namiji ba."

Cikin sanyin Raveel yace. 

"Ba komai ya Aminu, Allah ya tabbatar mana da al'khairi."

Amin Amin yace kana yayiwa Raveel rakiya har bakin gate. 


Ita kuwa Maryam ganin mijin nata ya fitane yasa ta juya a hankali tabi bayan k'anwar tata, 

tana shiga ta maida k'ofar ta rufe.

Da sauri ta haura kan gadon cikin tausayawa tace. 

"Zaleeha, kiyi hak'uri kiyi shiru kukan ya isa haka please kinga ga Ayman  ma ya fara kuka, 

Gaya min make faruwa?."

A hankali ta mirgino tare da kife kanta bisa cinyar maryam cikin tsananin kuka tace. 

"Raveel ne ya tura iyayensa wurin Baba malam wai suna neman izinin zance. 

yau tunda safe ya aika ya Habu ya kirani ina shiga ya hauni da fada.

Wai zan maidashi mutumin banza ya za'ayi inyi ta turo mishi dattawan mutane.

A karshe yace dole cikin manema in fidda goni ko shi yamin zabi, yace min wai karfa inga yayi shiru yana sane k'a'idar da ya bani saura wata d'aya".

Numfashi ta sauk'e a hankali tace. 

"To ke Zaliha auren ne bakya so?."

cikin shesshek'a da miryar tausayi tace. 

"A a ni bance bana son aureba."

Cikin kula tace.

 "To bakida masoya ne?."

Still hawaye na zuba tace. 

"Ina dasu amman ni bana sonsu."

Gyara zamanta tayi tare da cewa. 

"To wa kike so?."

hannunta tasa duka biyu ta matse kanta da k'arfi cikin rauni da tashin hankalin dan a duniya tasan wannan amsar itace tafi komai wahal da ita cikin muryar kuka tace.

"Adda Maryam ya kike min tambaya kamar bakisan komai a kanshi ba?."

cikin sin cire mata wannan tunanu Maryam  tace.

"Shi waye ɗin kenan?."

Kai tajujjuya kana tace.

"Shi nakeso! Shine farin cikin rayuwata, in dai ba shine yace baya sonaba to bazan auri kowaba, ya sadaukar da rayuwarshi a kaina, ya kareni a lokacin da nafi tsananin buk'atar neman kariya, 

Ya zama garkuwata ya tsare min kimata ya bada ranshi da lfyarshi a kaina, ina sonshi."

Sai kuma ta tashi zaune ta rik'o hannayen yayar tata cikin zubda k'walla murya na rawa tace. 

"Ina sonshi, wlh ina sonshi bazan iya son wani d'an namiji ba in ba shiba."

Cikin kad'uwa maryam tace. 

"Wai waye ne?."

Da k'arfi tace. 

"Ban saniba."

Cikin mmki Maryam ta zaro ido woje kana tace. 

"Me sunanshi? Ina gidansu yake? Me sana'arsa?."

Nanma kuka tasa tare da cewa. 

"I don't know."

Zuwa yanzu abin ya fara bawa Maryam tsoro cikin tsoro tace. 

"To ina yake?."

Da k'arfi tasa hannunta tana dukan kanta tare da cewa.

"Ban sanshi ba, bai sanniba bansan ina yakeba bansan sunanshi ba.

daga sau d'ayan dai dana tab'a ganinshi nanma gabanin magriba ne, to ban sake ganinshi ba."

Nan ta k'ara bawa Maryam labarin had'uwarta da Dalla da yadda Saifuddeen ya taimaketa, dan ganin yadda Maryam ta nuna mata kamar bata gane waye take nufi ba, ta k'arishe mgnar cikin tsananin kuka tace.

"Bansan ina zan sake ganinshi ba, ina sonshi, shine nakeso ya zama mijina wlh in ban aureshi ba bazanyi aureba, 

wlh in ban sake ganinshi ba zan haukace."

Tsorone mai tsanani ya rufe Maryam, 

cikin zubda hawaye muryarta a sanyaye tace.

"Innalillahi wa Inna'ilaihi rajiun, Zaliha ko dai kinyi gamone, kodai al'janine ba mutun ba?."

da sauri ta durk'usa gaban yayartata cikin kid'ima da jujjuya Kai tace. 

"Mutum ne shi kamar ni, wlh ba al'jani bane shima d'an adam ne, 

na tabbata da al'janine da ya sake zuwamin koda a mafarki ne. 

Ni tsorona  bansan wani hali yake cikiba, yana lfy ko sun illatashi."

Wani nannauyan ajiyan zuciya Maryam ta sauk'e sannan tasa hannu ta share hawayenta kana ta sharewa Zaliha nata cikin fuskantarta da kyau a hankali tace. 

"Wannan zancen naki ba'ak'i ce dashi gaibuba,

domin tatsuniya ce mai zaman kanta, zancene da hankalin bazai kamaba, 

Zaliha ki yarda al'janine ya taimaka miki,  in ko mutunne to ya mutu."

Wani irin zabura tayi tare da rushewa da kuka tana jujjuya kai tare da yarfa hannu take cewa.

"Bai mutuba yana raye mutun ne ba aljanba ki gane mana ina jinshi a cikin duk wani bugun da zuciyata keyi."

Ganin yadda ta gigicene yasa Maryam cewa. 

"Na game mutum ne kuma yana raye."

Jin haka sai ta koma ta konta rubdaciki tana mai ci gaba da kuka. 


Ita kuwa Maryam da sauri ta d'iro daga kan gadon ganin Ya Ameenun yana tsaye a bakin k'ofa bisa dukkan alamu yaji duk batun da sukayi. 

tana isa inda yake kawai sai ta fad'a jikinshi tare da sakin sassanyan kuka. 

Da sauri ya tallabota dan a duniya Ameenu duk zafinsa baya son abinda zai tab'a mishi salihar matarshi mai tarin hak'uri da biyeyya. 

parlour ya fito da ita inda ya ruggumeta da kyau a jikinshi, 

jin haka yasa rauninta k'aruwa cikin rawar murya take cewa. 

"Shi kenan Ya Ameenu Zaleeha tayi gamo, al'jani ya shiga jikinta.

Zai haukata min k'anwata ya Ameenu kuyi mata Ruqyah kada ya haukatata."

ganin sosai take kukanne ya sashi d'ago kanta bakinsu ya had'e wuri d'aya wani irin zazzafan kiss yake mata wanda dole yasa tayi shiru, har saida yaga ta nitsu kana ya jawota suka zauna kan kujera, 

tafin hannunshi yasa yana share mata hawaye tare da cewa. 

"Am so sorry my happiness kiyi shiru ba abinda zai sameta sai al'khairi ki daina kuka, 

zan mata duk abinda kike so kinji ko Ummu Ayman?."

Kanta ta gyad'a mishi alamun gamsuwa, duk da haka bai bartaba har saida ya sama mata cikekkiyar nitsuwa. 


Ita kuwa Zaleeha tuni wani baccin kuka ya kwasheta.



Shi kuwa Raveel koda yaje office ya kasa samun sukuni.

Sai sak'onnin ban hak'uri yaketa tura mata. 



                       Abuja

Amina ce ke zaune bisa sallayarta, 

yayinda ta bud'e hannayenta sama Cikin sanyin lafazi take cewa. 

"Ya haiyu ya k'aiyum ya ubangijin sammai da k'asai ya rabbil izzati kaine mai rayawa mai kashewa ya Allah ka raya min wannan bawa naka Saifuddeen. 

Ya Allah ka bashi lfy, Allah ka jib'anci lamuranshi ka sanya salama da farin ciki a rayuwarshi ya Allah ka cika mishi dukkan buk'atunshi na al'khairi."

A hankali ta shafa addu'ar tare da zamewa ta kwanta a nan bisa sallayar, 

tare da jawo wayarta hotonshi dake bisa fuskar wayarta ta zubawa ido. murmushin da yake a hoton sai takega kamar ita yakeyiwa.



                    Indian Mumbai

A guje nurses da Doctors suka shigo d'akinda Saifuddeen ke ciki sabida ihu da kururuwan da Hayatuddeen keyi.

Ihu yakeyi yana tsalle tamkar yaro kana yana yarfa hannu yana cewa.

"Wayyo Allah na yau farin ciki zai kasheni, 

Wayyo ni Hayatuddeen waye zai tayani farin ciki, 

Wayyo Ummi na yau ga Hamma Saifuddeen d'ina a zaune da k'ugunshi, ya tashi ya zauna da kanshi ba tare da taimakon kowaba. 

Wayyo Adda Rahma Raihana, Raliya d'an uwanmu ya fara zama da kanshi.

Ya Adnan ya Ahmad Bappa Ali ina kuke?."

sai kuma yayi kan Hamman nashi wanda tuni likitoci sun zagayeshi, 

yayinda suma duk fuskokinsu ke cike da farin ciki. 

Wani Irin sassanyan rugguma yayiwa Saifuddeen sai kuma ya fashe da wani irin kuka wanda daga kaji kasan daga cikin zuciyarshi kukan ke fitowa. 

Ganin haka yasa Saifuddeen ruggumeshi da kyau tare da d'an bubbuga bayanshi kana ya d'agoshi ya share mishi hawayenshi tare da mishi alamun.

Shin irin godiyar daya dace yayi Allah kenan?.

gane hakan ya sashi yin sujhadar shukur da sauri, 

wanda kafin ya d'ago daga sujjadar tuni an tura gadon da Saifuddeen ke kai an shiga dashi wani d'aki na musamman. 


Ummi kuwa duk abinda Hayatuddeen keyi da fad'i tanaji, 

Lokaci d'aya hawayen farin ciki ya rufeta, 

cikin tsananin happy ta sanarwa Raliyya abinda taji, 

ruggume juna sukayi dan tsananin farin ciki, 

daga nan Raliya ta fita a guje side d'insu ta nufa, 

tana shiga ta samu ya Ahmad d'in baya parlour da gudu ta kutsa kai bedroom nanma baya ciki. 

Jin motsin ruwane yasa tayi saurin bud'e k'ofar bathroom d'in, 

hangoshi tayi k'asan shower yana tsaye ba komai a jikinshi, 

cikin wani irin tsalle ta fad'a jikinshi dan ta mance cewa wai gudunshi tayi.

Da sauri ya ruggumota ganin yadda taketa tsalle kawai sai yaga ta fara mammanna mishi kiss tako ina najikinshi.

Sam ta kasa cewa komai ganin haka sai ya fara zame mata kayan jikinta, 

bata bi ta kanshi ba bare ta hanashi sai ma k'ara mak'aleshi tayi cikin fizgo mgna tace. 

"Al'bishirinka Ya Ahmad."

cilla rigarta gefe yayi tare da had'e jikinsu wuri d'aya kana yace.

"Goro fari k'al."

kiss ta manna mishi a goshi sannan tace. 

"Jikin Hamma Saifuddeen da sauk'i ya shida kanshi ya tashi zaune ba taimakon kowa."

Wata iriyar amintacciyar rugguma Ahmad yayi mata tare da giggicewa gaba d'aya ya abka mata, 

bata da zabi dole ta karb'eshi a yadda ya zo mata, 

mgna d'aya sukayi ta maimaitawa juna, 

"Hamma Saifuddeen ya fara workewa yana zama da kanshi."

shi kuma sai yace. 

"Alhamdulillahi ya Allah mun gode maka ka nuna mana ranar da zai kuna tsayuwa da sawunshi."

A haka dai sukayi ta kabta nanayensu. 


Ummi kuwa wayarta ta d'auka ta gaya dukkan 'yan uwa da abokan arziki. 


Adda Rahma kam kawai sai taje gaban surkarta tana kuka tana sanar da ita, cikin kula tace.

"A a Rahma to ai wannan abin farin cikine bana kukaba Allah zamu godewa."


A gefen Raihana ma haka abin yake, 

dan ita cewa ma tayi dole Saminu ya kawota gida gombe.


Su Salisu, Mudassir, Warisu, da Bappa Ali kuwa duk Ahmad ya sanar dasu. 


Ummi da kanta ta kira Ishaq ta sanar mishi. 



Kai wannan rana wannan safiya tazowa da masoyan Saifuddeen da daddad'an labari da sanyin safiya.


Kafin zuwa shabiyu duk makota da 'yan uwa anata zuwa yiwa Ummi barka. 

Bappa Alima yazo da Aunty Nina da Goggo Dada maman Ahmad, 


Shi kuwa Hayatuddeen 

sanin bazasu barshi ya shiga bane ya sashi komawa ya d'auki wayarshi, 

aifa kusan a Jere a jere kiran abokan Hamma Saifuddeen da k'annenshi ke shigowa wayarshi, 

Haka ya zauna yana musu cikekken bayani yadda komai ya faru, 

sai ya k'ara da ce musu yanzu an shiga dashi wani d'akin. 


Haka dai yayi ta zaman jira, 

Abu wasa-wasa har azahar ba'a fito da Saifuddeen ba, 

Ganin haka ya kira Dr Aliyu ya sanar mishi abibda ke faruwa, 

sun gama mgna da Dr Aliyu kenan sai ga Dr Acash prasat ya shigo inda yake cikin tsananin jin dad'i ya ruggume Hayatuddeen kana ya jawoshi suka zauna cikin kula yace. 

"Hayatuddeen jinya tayi kyau komai yana tafiya yadda mukeso Alhamdulillahi yanzu alamomin samun sauk'i sunata k'ara baiya a wurin d'an uwanka, 

tun d'azu muna tare a kanshi duk wani bincikenmu yana bamu tabbacin kaso saba'in cikin kaso d'ari na cutar ya worke a koda yaushe Saifuddeen zai iya tashi tsaye da sawunshi.

Yanzu kuma Alhamdulillahi zai iya tashi zaune daga konce, 

kuma zai iya juyawa hagu da damanshi.

Sannan zai iya durk'usawa kan guiwowinshi, 

kai nan gaba kad'an ma zai iya sunkuyawa, 

shine zatonmu a binciken da muketa gudanarwa a kanshi. 

So yanzu ka kwanrar da hankalin ka koma masauk'inka dan sai gobe zaka kuma ganinshi."

Cikin gamsuwa da jin dad'i Hayatuddeen ya gyad'a mishi kai tare da cewa. 

"Thanks Doctor."

sai ya mik'e cikin jin dadi har zai fita sai Dr Acash ya jawo hannunshi gaban wani window ya kaishi tare da cewa ya lek'a.

Hammanshi ya hango cikin wata na'ura mai girma dan k'afafunshi kadaine a woje sai kanshi kad'an. 


Cikin bashi k'arfin guiwa Dr Acash yace, 

"Wannan shine taimako na k'arshe da akeyi masu irin larurarsa, 

Yanzu sai in an fiddashi sai bayan, wata shida za'a sake sashi, 

so nanda one month za'a sallameku, 

in zaku iya duk bayan 6 months sai yazo a dubashi, 

a k'ara canza mishi drugs d'inshi.

So ka kontarwa iyayenku hankalin kada wani yace zai zo."

Tofa wannan abu shine Noor ala noor haske kan haske, 

sosai bayanin ya kontarwa Hayatuddeen hankalin. 

Shiyasa cikin k'arfin guiwa ya koma masauk'inshi.


A ranar dai kam wannan family sunyi matuk'ar shiga farin ciki. 

Musammam Ummi da Hayatuddeen ya mata bayanin likita, kawai sai takeji kamar bata da wani sauran damuwa a duniya.


Hakama Dr Adnan da yaji bayani a bakin Dr Malik Khan sosai ya samu konciyar hankalin.


Ahmad kuwa a ranar ya nemo ma'aikata sukazo suka gyara side d'in Hayatuddeen dan Ummi tace anan Saifuddeen zai zauna, 

So an fasa duk wani wuri mai d'an tutu ko steps d'in da zai hana keken weelchair gangarawa da wucewa a sauk'ak'e.

Sosai aka gyara side d'in. 


A washe garin ranar Ahmad yasa aka kawo mishi gadon samfarin royal bed kana da kujeru suma royal d'in.

Aka canza mishi AC bedroom aka dawo dashi parlour kana aka sa sabon AC a bedroom d'in. 

Hatta labulaye da carpet da blanket da beshid sabbin Ahmad yasa aka saka komai na d'akin lemon green and white ne sosai kalan ya haska d'akin, 

Kayayyaki sabbi dal-dal Ahmad ya sayo yazo ya jera mishi kananu na d'inkawa kuma shida kanshi ya fito da kekken d'inkin Hayatuddeen ya fara yayyarɗa mishi ɗinkunan zamani d'inka mishi.


Sosai Ummi take cikin farin ciki.

Adda Rahma kuwa a kwanakin kullum sai tazo. 



Yau kwana biyar kenan da fara tashin Saifuddeen, 

suna zaune shida Hayatuddeen wanda ya kira Ummi video call sai hira da dariya suke, nan Raliya ta amshi wayar ta nuna mishi yadda aka gyara mishi side d'in da zai zauna. 

Murmushi yayi cikin jin dad'i da begen komawa gidan Cikin ahlinsa. 

Shiko Hayatuddeen kai ya jinjina kana yace. 

"Oho wato abinma son kaine, da yake Hamma ne zai zauna a nan kalli yadda kuka wani gyara d'akin tamkar makwancin shugaban k'asa.

Wato nine jaki in na ga dama in kwan a k'asa ko?."

Cikin kewar sangartarsa tace.

"Ohoho my autanmu kaima ai yanzu side naka tas yake in kana soma sama zaka koma, 

inda Hamma Saifuddeen yake da."

Cikin jin dadi yace. 

"Wayyo Allah kice na zama alhajin sama."

Dariya sukayi baki d'aya kana suka d'anci gaba da hira daga bisani suka salami juna.


Yau mako biyu kenan cib da fara tashin Saifuddeen zaune, 

Kuma Alhamdulillahi tuni an gama mishi duk wani abinda ya dace na sallamarsa da shared'in duk bayan wata shida zaizo a duba jikinshi.


Tuni Hayatuddeen ya gama musu dukkan shirin komawarsu da taimakon Dr Malik Khan.


Nanda kwana biyu jirginsu zai d'aga zuwa Nigeria. 


A cikin asibitin. 

Saifuddeen na konce shi kuwa Hayatuddeen yana harhad'a duk wani abu nasu domin gobe da asuba jirginsu zai tashi.

a hankali ya zubawa d'an uwan nashi idanu ganin yadda jikinshi ke rawa kar-kar- kar tamkar mazari idanunshi sunyi jazir, 

gaba d'aya jijiyoyin kanshi sunyi rud'u-rud'u wani irin zufane ya yanko mishi a take, da sauri ya matso gaban gadon cikin tsananin fargaba da tsoro murya a birkice Hayatuddeen yayi kanshi jiki na rawa. 

Sai ya kumayi dib ya tsaya wuri d'aya da yake ganin Hamman nashi na jujjuya mishi kai alamun karya matsoshi.

Idanu ya zuba mishi cikin kad'uwa sai kuma ya rink'a kame jikinshi ganin Hamman nashi so yake ya durkusa, 

cikin ikon Allah kuma sai gashi a durkushe bisa tsakiyar gadon. 

Kusan a tare suke sauk'e numfashi, 

Dai-dai lokacin kuma  Dr Anan da Dr Malik Khan suka shigo. 

Samunshi a haka yayi matuk'ar sasu farin ciki nan take suka k'ara gwadashi, 

kana suka dank'a mishi takardar sallama da sharad'in duk bayan watanni shida zaizo.

Nan Dr Anan ya kara ink'anta mishi durkuson nasa.

Washe gari bayan an idar da sallan Asuba Dr Malik Khan yazo ya d'aukesu, da kanshi ya Kaisu Hilton international Airport Mumbai.

Bai bar airport d'inba saida yaga tashin jirginsu.



             Abuja 

Amina kuwa yau satinta biyu kenan tana neman Hayatuddeen bata samunshi a waya, 

gaba d'aya abin ya dameta, 

gashi yanzuma ta kira layin baya tafiya,

kai ta rausayar kana tace. 

"Allah yasa dai lfy, sai anjima da yamma zan kuma gwadawa."



          Gombawa d'iban fari. 


Yau gidan Ummi a cike yake, 

Raihana mutanen kd ma tun jiya tazo da Affan d'inta. 

Adda Rahma kuwa itama yau sammako tayi.

Hakama goggo Dada da Aunty Mina.


Farop da Adam sai tsalle suke yau Uncles nasu zasu dawo. 

Salisu ma ya kawo Salimanshi.

Gida ya kacame da shirye-shiryen tarban Hamma Saifuddeen...!



To AL'amarin Zaleeha fa ya girmama, 

Domin har Ruqquya saida aka mata dan duk an d'auka gamo tayi. 

Shi kuwa Baba Malam ya sani sarai babu wani gamo,

ba iska a jikinta sai dai zallan iskanci inji Kakarsu da fad'i. 

Maryam Zahira kam su dai a dole Zaliha gamo tayi, 

Zeyada kuwa da Zakariyya da suke wurin Hajja Inna suma mgnar kakarsu suka bawa amanna Zaliha bata da wani iska sai zallan iskanci. 


Ya Ahmad d'inta kuwa wanda kwanan suka dawo Nigeria shida matarsa dan watansu bakwai a Istanbul. 

kasan cewarshi mai nitsuwa da hak'uri da k'aunar kannenshi suna dawowa da kwana d'aya ya taho gombe.


Shiyasa yau gaba d'aya Baba Malam ya tarasu, 

ya jaddada musu cewar Zaleeha fa tanada sauran dama na mako biyu ta fidda miji cikin tarin masoyanta, 

in kuwa ta sake mako biyun nan ya cika bata tsaida gwaniba to tabbas shi zai mata zabi kuma tayi kuka da kanta.

Koda aka tashi taron bayan Ya Ahmad d'in nata tabi suka shiga parlour Mamy gabanshi ta durk'usa cikin zubda k'walla tace. 

"Ya Ahmad ina sonshi, bayan shi babu wanda nakeso dan Allah ka bawa baba malam hak'uri ya rufa min asiri kada ya rabani dashi."

Hannunta ya jawo ya ajiyeta gefenshi cikin nitsuwarsa yace.

"Kin san a duniya bamu da kamar Baba Malam ko Zaleeha.?"

Kai ta gyada mishi alamar eh, 

shi kuwa cikin sanyin yanayinshi yaci gaba da cewa. 

"Kin san wayeshi a wurina nida Maryam da Ziyada da Habu, 

bama iya jurar ganin b'acin ransa, 

bama iya lamuntan duk wani abu da zai tab'a mana daraja da mutuncin mahaifinmu, 

Zaleeha koda nace miki ina tare dake namiki k'arya, 

zancen gsky bayan Baba malam da Ya Ameenu nake babu yadda za'ayi kiyi ta zaman jiran gaibu, 

abinda ni ganima nake Al'janine ,

to tayaya zamu lamunci ki zauna zaman jiranshi. 

Kawai dolenki dollen dolene ki Zab'i d'aya daga cikin masoyanki. 

Ko Abdussalam ko Managernku ko Raveel ko kuma wannan abokin nawa Al'amin wanda yayi ta nace miki zuwanki Abuja last year. In kuma kinki tsaida gwani da kanki to wllahi Allah kenan Baba malam zai zaba miki cikin su."

kife kanta tayi a kafadarshi tare da sakin nakasasshen kuka tare da cewa. 

"Na shiga uku ns, wlh ya Ahmad ina sonshi."

shigowan Ya Ameenu ne yasa ta mik'e da sauri ta wuce side d'insu kai tsaye bedroom d'in Mama ta wuce bisa gado ta fad'a tana kuka. 

Cikin takaici Maman ta harareta tare jan dogon tsaki kana tace. 

"Shirmen banza kawai ni dai ina gaya miki wallahi ko bakya son Abdussalam sai ya aureki yaro d'an manya jikan sarakuna har zakiyi ta wainashi da me kika fishi kyau ko asali ko gata, 

ni dai ina gargad'inki kada ki bari Malam ya miki zaben tumun dare yadda yayiwa Maryam auren dole to bazan lamunci a miki hakaba, 

shiyasa gwara ki bar batun wancan aljanin da ya taimakeki ki rik'e Abdussalam yafi miki." wannan shine rana zafi inuwa k'una jin kalaman Mamane yasa ta mike ta koma d'akinta taci ga da koke-kokenta... 



Tafiya tayi nisa cikin sararin samaniya,  kowa na harkan gabanshi, autan Ummu kuwa jinshi yake a takure.


Hayatuddeen ne ya d'an juyo ya kalli kekyawar matashiyar dake gefenshi. Wacce duniyar Khanywood keji da ita wacce tauraronta ke harbawa a fagen rawa da wak'a.

a hankali yace. 

"Asma'u Ahmad Matawalle,"

Sai ya kuma d'an juyawa ya kalleta a hankali yace. 

"Masha Allah.

 To Ashema tafi kyau a TV da nake ganinta akan a zahiri."

ita kuwa Asma'u tunda ta shigo hankalin ta na kan Saifuddeen dake rik'e da jarida.

kekyawan sajenshi ta zubawa idanu,

babu ko kebtawa, 

saida ta kai 2 minutes tana kallon sajen nashi sai ta kumayi wani tattausan murmushin tare da cewa. 

"Wannan kamar balarabe. Kuma kamar mara lfy ne dan taga lokacin da Hayatuddeen ya  bashi mgni yasha.


Ganin kamar suna Magna ne yasa ta d'an maida hankalin ta gefesu amman cikin hikima bazama suyi zaton su take kalloba, 

da k'arfi ta ajiye nannauyan ajiyan zuciya dai-dai lokaci da ta...!





                              By

                   *GARKUWAR FULANI*

8/18/20, 7:53 PM - Ummi Tandama: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


              *NAKASA BA KASAWA BACE*



                                 *PAGE 24*



                                  NA

               *AYSHA ALIYU GARKUWA*


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

           


 Da taga ya juyo fuskarsa ya fuskanci Hayatuddeen,

ba zato ba tsammani taji bakinta ya furta. 

"Masha Allah. Allah tsarki ya tabbata ga ubangijin talikai da yayi wannan hallitar kana ya wanzar da kwarjini a kanta."

gashin girarshi ta zubawa idanu ji takeyi tamkar ta kai yatsarta manuniya kan zirin girar nashi. 

Shi kuwa Hayatuddeen cikin sangarcin da yake zubawa d'an uwan nashi ya kwab'e fuska tare da cewa. 

"Hamma na gaji, wlh tafiyar nan tayi tsawo da yawa."

a hankali ya lumshe idanunshi wanda hakan ya basu damar hade gashinsu ya kwanta lib bisa kwarminsu, 

harshenshi ya d'an zaro a hankali ya lashi jajayen labbanshi, 

damshi yawun daya shafa musu ne ya basu damar Shek'i. 

Hannun shi yasa ya jawo Hayayuddeen ya mannashi da k'afad'arshi kana ya fara d'an bubbugawa alamun ya huta.

Duk abinda sukeyi idanunta na kansu.

sam bata luraba da wayarta dake zamewa sai da taji sautin fad'uwan wayar, 

wanda ya jawo hankali Hayatuddeen har ya rigata sunkuyowa ya d'auki wayar da ta fad'o a d'an zirin tsakiyar hanyar da ake wucewa.


Wanni lallausan murmushi tayiwa mishi lokacin daya mik'a mata wayar tare da cewa. 

"Kud'in ki million d'aya!."

amsar wayar tayi tare da cewa. 

"Kud'in me fa?".

Cikin yanayinshi na calikanci dayin wasa da kowa yace.

"Kud'in kalle min kekyawar fuskar Hamma na mana."

Itama dariya tayi cikin jin dad'i tace. 

"A a kune dai zaku biya kud'in darajar idanuna da suka kalleshi,

ladan jamin hankali da yayi da kekyawan sajenshi."

ta k'arishe mgnar da d'an k'arfi wai dan ya jita ya juyo.

murmushi Hayatuddeen yayi tare da cewa. 

"Hayatuddeen  Muhammad Ahmad Dukku."

kai ta jinjina tare da yin fari da ido kana tace. 

"Sunan babba ake fara gabatarwa."

gane nufinta ya sashi gyara zama tare da cewa. 

"Darajar mai sunan da sunan yafi k'arfin a badashi kyauta har sai in anyi baranshi, to nan muna badawa sadakanshi."

Sosai take matuk'ar jin dad'in hirarta da yaron mai d'an karen surutu da iya sarrafa harshe. 

Fuska ta kwabe tare da cewa. 

"To ina bara, duk da nasan shima da kanshi ai zai al'fahari da hakan."

cikin tab'e baki yace. 

"No shi ba kamar kowa bane, na tabbatar baki taba haduwa da irinshi ba kuma bazaki tab'aba ,

tsadar muryarshi yafi farashin tsadar ruwan sanyi a zazzafar sahara."

hannu tasa ta dake kanta tare da kai kallonta jikin windows d'in jirgin tana ganin yadda suke ratsa gajumare, 

a hankali tace. 

"Kana ji da Yayankan nan, ji yadda kake rowar sunanshi."

murmushi yayi mai kama da dariya kana yace. 

"Saifuddeen  Muhammad Ahmad  Dukku."

wata sassanyar ajiyar zuciya ta fesar tare da cewa. 

"Saifuddeeeeeeeeeeen sunan ya dace da kekyawar halitta."

kai ya gyad'a mata alamun yasan haka. 

juyawa tayi ta d'an kalleshi kana tace. 

"Asma'u Ahmad Matawalle."

gyad'a kai Hayatuddeen yayi tare da cewa. 

"Na sani,  ai ko ledan pure water yafi sunanki tsada da, da buya."

ido ta zuba mishi cikin wani yanayi mai wuyar fassara, 

sai kuma tace. 

"Yaushe kuka shiga India?."

ba tare da ya kalleta ba yace. 

"Last year."

da sauri tace. 

"Karatu kukeyi a can ne?."

Kai ya jujjuya mata tare da manna kanshi a kafad'an yayan nashi kana yace. 

"Jinya dai mukaje."

cikin sanyi tace.

"Ayyah waye mara lfyan."

da hannu ya nuna mata Saifuddeen wanda hankalin shi ke kan jaridar hannunshi.

ita kuwa cikin mmki ta tambayi meke damunshi, 

Hayatuddeen aku sarkin zance tuni ya fesa mata labarin ciwon Hamman nashi.

Tuni hawaye ke kwaranyowa bisa fuskarta, harda ɗan sheshesƙa

Da sauri Hayatuddeen ya d'ago kanshi tare da cewa. 

"Gsky dole kiyi tacin kud'i a fims  da wanna saurin hawayen naki haka."

ina Hayatuddeen fa bazai gane bane, bazai san ya taji Saifuddeen a rantaba. 

A hankali dai sukaci gaba da hira har sukayi musayen phone number, 

ta kafa ta tsare tana son ta kalli fuskar Saifudddeen Amman ina domin hankalinshi baya kansu.


                 Abuja

Amina kuwa bakin da tayine ya hanata damar sake kiran Hayatuddeen.


                    Gombe 

 Bayan ta tashi daga baccin, sai ta d'ora daga inda ta tsaya.

Tayi kukan mai isarta tanayi Maryam na tayata, 

Zahira kuwa itace ta shiga kitchen da Mamansu.

Bayan sun gama aikin lunch Zahira ta kai na Baba malam dasu Ya Ahmad da ya Aminu,

sai kuma tazo ta d'auki na Mamy ta kai mata. 


Ita kuwa Mama tana fitowa kitchen kai tsaye d'akin Zaleeha ta shiga.


A bakin gado ta zauna tare da juyawa ta fuskanci yaran nata cikin sanyi tace. 

"Zaleeha!." kanta ta d'ago kana ta zuba mata jajayen idanunta, 

hannunta ta kamo cikin yanayinta na fuskar bosawa tace. 

"Meyasa kika zabi ki azabtar da kanki a kan gaibu, abinda baki da tabbaci a kai?

Menene nak'asun Abdussalam? Meyasa bazaki zabi inda zakije ki hutaba Meyasa kike son tayarmin da hankalin? Kinfa san halin Babanku da kafiyar tsiya, 

kinga dai yadda ya min a auren Maryam? Kin kuwa sani bazan lamunci ayi miki auren doleba koda ko hakan na nufin zan rabu da mahaifinku,

meyasa zaki tasani gaba kina kuka?

kiga yadda kikasa Maryam shiga tashin hankali."

a hankali ta mik'e zaune kana ta share hawayenta sannan tace. 

"Please Mama kiyi wani abu mana, a barni in fito da zabina a hankali, 

ni bana son Abdussalam,

yana da k'afafa da al'fahari da kud'i yana jin kanshi shi wanine."

kai ta jinjina tare da cewa. 

"A a Zaleeha ki ma bar kushe Abdussalam, kadafa ki mance k'anin aminiyata ce."

A hankali Maryam tace. 

"To menene aibun Raveel?."

da sauri Mama ta had'e fuska tare da cewa. 

"Me kuma Raveel waye shi wannan yaro mai kama da gurgu yana tafiya yana d'ink'isa kafa, 

Surkina musaki ina ai Raveel bayama cikin layi,

Yaronda shine gatan danginsu babu wani ficeccen mai kud'i a ahlinsu."

cikin jin dad'i an yakice Raveel Zaleeha ta gyara zamanta, 

ita kuwa Maryam cikin sanyin sauti tace.

"Sanya getzner rik'e babbar waya, yin karatu a kasar waje, 

shiga manyan motoci. duk basu ake bincikawa a neman aureba a musulunce, 

Addininshi da asalinshi sana'arsa nasabarsa.

sune abin bincika Mama."

wani dogon tsaki taja tare da hararan Maryam kana tace. 

"Kin san ai ni tubebbiya ce, gwara kimin nasiha yar malamai."

Da sauri ta fara jujjuya kanta cikin tattausan lafazi da biyayya tace. 

"Afwan Mama ba haka nake nufiba ki gafarceni in furucina ya b'ata miki rai na tuba ki yafe min."

kai ta gyad'a tare da cewa. 

"Na yafe miki."

dan tabbas tasani Maryam d'iyace irin wanda ko wacce uwa ke fatan samu, 

matsalarta komai sai tace zata mata wa'azi shike had'asu.

Daga nan tasa Zahira ta kawo musu abinci suka ci.

suna zaune a wurin suka jiyo muryar Zakariyya yana cewa. 

"Mama! Mama!!."

bata kulashi ba har saida ya shigo cikin had'e fuska tace. 

"Sai shegen yawan kira kamar mafarauci ko tsohon makaho."

Murmushi yayi kana yasa hannu ya amshi spoon d'in hannun Zaleeha tare fara cikin abincin saida ya had'iyi lomar da yasa a baki sannan yace.

"Da Hajja Inna mukazo shine Baba malam yace inzo in gaya miki kije ku gaisa."

Tsaki ta d'an ja kana ta gyara zamanta tare da cewa. 

"Ziyada fa bada ita kuka zo bane?."

kai ya gyad'a mata alamar eh sannan ya kalli Zaleeha cikin tsokana yace. 

"Amaryar watan gobe har kin fara tunanin auren ne haka?."

duka ta kai mishi tare tura baki.

Shi kuwa ganin yadda Zahira ta zuba mishi idone ya sashi danna mata tsawa.

"Ke me haka kike ta kallona kamar tsohuwar mayya, muna fuka kawai."

tura baki tayi kana ta kauda kanta sam shi baya shiri da ita. 


Sunan zaune suka jiyo muryar ya Ameenu yana cewa. 

"Kai Zakariyya fito ku tafi."

Da sauri ya mik'e ya fita. 

Jin haka yasa Mama mik'ewa tabi bayanshi hakama, Maryam da Zaleeha.


Suna shiga parlour Baba malam suka sameshi zaune gaban mahaifiyar tashi tamkar yaro k'arami shi kuwa Ahmad na zaune a gabanshi, 

bisa dukkan alum farce yake yankewa kakar tasu 

Habu kuwa na gefensu. 


Suna shiga ta kalli Maryam cikin son jikar tata tace 

"Ah Maryama dama kina cikine?."

cikin nitsuwa tace. 

"Eh Hajja inna ina ciki salla nakeyi sanda Zakariyya yaje kiran Mama."

"Ayyah." tace da ita tare da kallon Zaleeha cikin yar tsamarsu tace. 

"Rasa kunya berar tanka uwar kid'e-kid'e, ke ba abinda kika iya sai rawa da wak'a da kid'a ko."

Baki ta murguda mata tare da watsa mata harara. 

cikin zaro ido tace. 

"Iye ni kikewa wannan kallo lallai wannan yarinya in ba'a aurar da keba to tabbas zaki tashi gari, 

hegiya mai zubin nasara."

Sai ta kuma juyo ta kalli Mama data tab'e fuska ko gaisheta batayi.

kwaffa tayi kana ta kalli d'an nata sannan tace. 

"Kai Bashiru wlh infa kana son tsira da mutuncinka to ka aurar da wannan fitinenniyar yarinyar.

In ba haka zataci gaba da worwore maka tubkar da kakeyi. 

Kullum kana kan hanyar zuwa gidan radio kana shirin tafarkin tsira al'ummar musulmai na k'aruwa da kai.

Abin takaici ana gama shirinka sai a sako shirin wannan dujaliyar yar taka wai mushak'ata, 

haka zatayi ta zubawa wak'ok'i ka jita tanabin waken tamkar zabiya."

duk shiru parlour sukayi sai Zakariyya dake cewa.

"Ni dai da zata amshi shawarata ta dena bin wak'ok'in tana hanamu jin abu d'aya. Mu jita ko muji radio."

Da sauri ta gyad'a kai tare da cewa. 

"Uhun ai dai kunji ko?."

shi kam Ahmad da Habu sai murmushin sukewa inna boris.

Ya Ameenu kuwa sai harara yake watsawa Zaleeha.

cikin muryar jin haushi Mama tace. 

"Inna an wuni lfy?."

A hatsale Inna tace.

"Lau na wuni! gsky ce dai sai na fad'i ehe!."

Dariya sosai Ahmad yayi yayinda Baba malam ya murmusa.

ita kam Zaleeha ficewa tayi abinta, 

ita kuwa inna sai cewa tayi. 

"Dama iyayen yara sunfi son marasaji, 

shiyasa take son Zaleeha kamar ranta bata son laifinta. 

Kuma dole in fad'i dan ba yadda za'ayi in haifi d'ana malami ke kuma kizo ki haifa mishi zabiya, amara k'irjin biki."

Su duk dai ba wanda ya kuma mgn, 

shigowa Mamy ne da kulan soyayyun kaji yasata washe baki tare da cewa. 

"Allah dai ya miki al'barka Mamyn Ahmad."

Cikin sanyi Mamy tace.

" Amin Amin ." dan ita dai bata fiye son abinda inna kewa Zaleeha ba, 

dan ita tana matuk'ar son Zaleeha kuma itama Zaleeha tana matuk'ar sonta. 

Ido suka zuba mata ganin ta mik'e tare da cewa Zakariyya. 

"Shalele na maza tashi mu tafi."

da sauri ya amshi kular sannan Suka fito, 

suna zuwa parking lot nasu Baba malam yace.

"Inna muje in maidaki."

da sauri tace. 

"Lalala bari a machine d'in Shalele na mukazo,

kuma a kanshi zamu koma."

Cikin tsoro baba malam yace. 

"Inna a machine kuwa, to Ahmad ya maidaki ko Ameenu."

Kama hannun Zakariyya tayi tare da cewa. 

"Muje ko Shalele yaro yana jin dad'in yau na hau machine d'insa kuma shine zaku hana."

Habu ne yayi dariya tare da cewa. 

"Allah sarki watarana sunan hak'oranta babu."

Mamy ne tayi mushi dak'uwa su kuwa jikoki suka k'elk'ele da dariya.


Koda suka koma cikin gida Baba Malam da Ameenu da Ahmad da Habu mgnar Zaleeha sukaci gaba da d'an tattaunawa inda shi Ahmad yaje jaddada musu wai al'janine.


Jirgunsu na sauk'a a Abuja. 

Ya Rabi'u da kanshi yazo ya d'aukeshi dan acan zasu kwana sai da safe zasu samu jirgin Gombe.


Sosai suka samu kulawa da karramawa ta musamman a wurin Aunty Mami.


Inda tayi tayiwa Hayatuddeen tsiya wai ya zama ba'indiye.


Washe gari k'arfe tara na safe jirginsu zai tashi.

So tun bakwai da rabi suka fito kai tsaye asibitin su Dr Aliyu sukaje.


Sosai fa Dr Aliyu yaji dad'in ganin Saifuddeen ya fara samun lfy,

Dr Batulu kuwa saida akayi mata kwatancenshi sannan ta tunoshi dan da fari tayi zaton ko ba indiye ne yazowa Dr Aliyu ziyara.


Karfe tara dai-dai jirginsu ya d'aga zuwa Gombe doma.


A hankali Hayatuddeen ke tura weelchair d'in da Saifuddeen ke zaune a kai, 

cikin shiga ta alfarma, 

wani dakekken yadine mai tsananin azabar kyau blue irin blue mai hasken nan sai ratsin d'igo-d'igo yellow irin yellow mai d'an duhun da za'a iya cemai ruwan k'asa.

Sai wata dakkeyar hukar damanga mai azabar kyau shina irin kalan kayanshin sai kuma takalminshi sau ciki  suma kalar yellow mai d'an duhuwa, 

sai agogon Gucci na fata shima kalan takalmansa, 

ya kafa hular tayi ras a kanshi, 

Sajenshi ya konta lib wanda hakan ya k'ara k'awata kekkyawar fuskarsa farar fatarshi ta k'ara baiyana red lips  ɗinsa suka kara yin kyau cikin zagayen saje da kota million dake fuskarshi. 

Shi kuwa Hayatuddeen wasu k'ananun kaya yasaka masu azabar kyau.

Tura weelchair d'in yakeyi a hankali da hannu d'aya, 

yayinda d'aya hannun kuma ke janye da trollinsu.

a d'aya sashi kuwa ma'aikatan jirginne ke turo sauran kayan nasu wanda yake hade da wani weelchair d'in a ciki da dai sauran abun buk'a tunsu.


A hankali iska mai sanyi ke ratsa jiki da zuciyar Saifuddeen. 

Tasbihi yakeyi ga ubangijin talikai daya sake nufarsa da dawowa k'asarsa jiharsa ta haihuwa wacce lokacin d'aya barta baisan inda yake bama tsawon shekara d'aya kenan dayawuce.

 

Isakar ya kuma shak'a tare da lumshe idanunshi yana maijin wani yanayi mai kashe jiki.


Suna isowa inda masu tarbarsu suke, 

Kamar daga sana Hayatuddeen yaji an ruggumeshi ta baya, 

da sauri ya juyo tare da sakin weelchair d'in ,

ganin Raliyya da Faruq ne ya sashi hadesu da jikinshi cikin tsananin jin dad'i, 

jin sun sakeshi ne yasashi binsu da ido ganin inda suka nufa, 

Adda Rahma ne sunkuye a gaban Saifuddeen dayi mishi wata iriyar rugguma ta yan uwa na jini, 

madadin tayi mgna ina sai murmushi takeyi ga kuma hawaye nata kwaranya a idanunta. 


Hakama Rainaha sarkin kuka tuni ta kasa isowa inda suke sai wani irin sark'ekk'en kuka da takeyi. 

Ahmad kuwa wayarshi ya zaro yanata yi musu hoto a cikin duk motsin da sukayi, 

ganin yadda Raihana ke kuka yasa Saifuddeen mik'o mata hannu, 

aifa da gudu ta iso inda yake kawai sai ta durkusa dirsham har k'asa ta kafa guiwowinta kana ta kifa kanta bisa cinyarshi tare da yin zazzafan kuka, 

kawai duk sai suka had'e kai a wurin.

Suna kukan farin ciki da tausayawa d'an uwansu. 


Salisu ne yayi saurin isa inda suke ya janye Hayatuddeen da Faruq, 

yayinda Ahmad kuwa ya janye Raliyya, 

Ya Adnan kuwa ya gaza ce musu komai, 

Ishaq kuwa,  yana zuwa ya ruggume abokin nashi, 

ganin airport d'in yayi musu kad'an wurin farin cikinsu yasa suka, 

shiga motocin suka tafi, 

Adda Rahma kam fir taki yin nesa da k'aninta a motar ya Adnan suke ita da Saifuddeen suna baya, 

Ishaq kuma na gaba.


Hayatuddeen kuwa da Faruq da Raliya motar ya Ahmad suka shiga. 

 

Salisu kuwa kuwa shi ya kwashi kayansu shida Raihana.



Daga airport zuwa cikin gombe akwai yar tazara, 

so tafe suke suna hirarsu ta yan uwa shak'ik'ai. 


Cikin tsananin mmki Hayatuddeen yake baza ido lokacin da suka shigo cikin gari sabida, 

Sosai yaga sauye-sauye a garin. 

Hakama da suka iso gida Saifuddeen da kanshi yayi mmkin ganin zubi da tsaruwar gidan, 

Komai yayi shar tsirran da shuke-shuke sunyi lip-lip gwanin sha'awa. 


Anayin parking  Hayatuddeen ya fita da sauri, kai tsaye cikin gidan ya nufa a guje.

Ya Adnan kuwa yana fitowa ya bud'ewa Saifuddeen k'ofa kana ya bude but d'in motar ya fito da weelchair d'in.

A gab da kofar motar ya ajiye kujerar, yayinda tuni Adda Rahma da da Ishaq suka fito. 

Hakama su Raihana ganin duk sun zagayeshi sun mishi zobene, 

yasashi lumshe ido kana ya zuro k'afafunshi wojen tare dasa hannunshi ya dafa gefen motar sannan ya yunk'ura ya taso cid'ak cikin azama da jarumta da zafin nama ya zauna bisa weelchair d'in.

Wani irin nannauyan ajiyan zuciya Adda Rahma ta sauk'e da tsananin k'arfi dan da gani take kamar bazai iyaba. 

Faruq kuwa da sauri ya tsuguna ya saita matakalar kujerar, 

wani lallausan murmushi Saifuddeen yayi kana da taimakon Ahmad ya d'aura fararen sawunshi kan abin takawan.

Salisu kuwa tuni ya firfito da kayayyakinsu ya nufi cikin gida dasu. 


Shiko Saifuddeen girarshi d'aya ya d'agawa Ahmad alamun tammayar ya dai ganin duk sun tsaya a kanshi. 

Cikin tsananin tausayi da k'aunar d'an uwan nashi yace.

"Ai kaine jagoran."

lip inshi na k'asa  ya d'an tauna ta gefe kana yasa hannunshi ya share hawayen dake bin fuskar Raihana sannan yasa d'aya hannunshi dai-dai wurin masarrafin weelchair d'in ya d'an daddana wasu madannai sai ga keken ya fara tafiya a hankali. 

da sauri sukabi bayanshi. 


Da sauri ya danna wani pin d'in sabida ganin Baba Ado mai gadinsu da Sule direbanshi sun rusuna gabanshi. 

Sam sule ya gaza tsaida ruwan hawayenshi dan kamar yau yana tuna randa sukayi fitarsu ta k'arshe in da uban gidan nashi ya taka da sawunshi, 

sai gashi cikin shekara d'aya ya zama bashi da damar tsayuwa. 

kai ya d'an jujjuya musu alamun suyi hak'uri su bar kuka.

da kyar suka iya tsaida hawayensu kana suka mushi sannu da hanya da fatan samun lfy. 


Hayatuddeen kuwa yana shiga parlour yayi tsalle ya fad'a kan kujera 3 str gefen Umminshi sai ya kuma ruggumota ta baya tare da cewa. 

"Wayyo dad'i yau gani ga Ummi na."

Sosai Ummi ta ruggume autan nata tana maijin son yaran da begenshi. 

Goggo Dada ce ta kalleshi cikin son yaran d'an uwan nata tace. 

"Wato Umminka kawai ka gani ko?."

Da sauri ya juya zuwa gareta.

Dai-dai lokacin kuwa su Saifuddeen suka shigo, 

wani irin farin cikine mara misaltuwa ya rufe Ummi wanda ta kasa koda motsa yar yatsarta, 

sai bugawa da zuciyarta keyi da k'arfi-k'arfi. 

Shikuwa Saifuddeen k'ara gudun weelchair d'inshi yayi ya saitata gaban Ummi. 


Yana isa inda take gab da ita tayi saurin mik'o mishi hannu, 

da sauri ya kamo hannun nata duka biyu kana ya tallabe fuskarshi dasu, 

haka nan rauni  zuciya suka rintsa mishi zuciya bai taba zubda k'walla akan wannan larura tashiba sai yau.

Kawai sai yaji wasu zafafan hawaye suna kwaranyo mishi, 

da sauri ta mik'e tsaye ta matso gab dashi hakan ya bashi damar sahannunshi duka biyu ya ruggumeta tare da manna kanshi a cikinta, 

wani sautin kuka mai cike da raunin d'a a gaban mahaifinshi ya sake.


Tuni itama Ummi kukan takeyi tamkar zata shid'e,

Raihana kuwa kife kai tayi bisa cinyar goggo dadansu tana kuka da majina. 

Yau Adda Rahama mai dauriyarma kuka takeyi wi-wi.

Raliya kuwa jikin mijinta ta fad'a cikin rauni take cewa. 

"Ya Ahmad kace suyi shiru, ya zamuyi da k'addararmu da munada dama da tuni mun canza k'addarar Hamma Saifuddeen."

ina shima kanshi Ahmad hawaye yakeyi. 

Ya Adnan ne yayi k'arfin hali cikin d'an d'aga sauti yace. 

"Kiyi hak'uri Ummi, addu'a shi ya dace da Saifuddeen ba kukaba, 

da ace kuka na mgni ai da tun kan yau Saifuddeen ya worke."

A hankali Ummi ta gyad'a kai kana tasa hannu ta d'ago kan Saifuddeen. 

murmushi tayi mai had'e da hawaye hannu tasa ta share mishi hawayenta. 

cikin rawan murya tace. 

"Baba kada ka mance furucin yayanku, koda ya mutu baya raye ai furucinsa bai mutuba."

rimtse idanunshi yayi da k'arfi kana ya bud'esu a hankali. 

kafad'unshi ta dafa cikin tausasa lafazi tace.

"Ae ita Nakasa ba kasawa bace.

Da nakasarma ka zame mana jigo garkuwa gata a garemu, ka meyewa k'annenka gurbin uba ni ka zame min uwa uba yaya k'ani d'a kuma abokin kukana."

kai ya jinjina mata alamun gamsuwa, 

Goggo Dada kuwa Raihana ta lallasa kana Ya Adnan yayi musu nasiha mai ratsa jiki, 

daga bisani yayi addu'ar samun lfy ga Saifuddeen sannan shida Salisu suka fita suka tafi. 



Ummi kuwa da kanta ta mik'e taje kawowa Saifuddeen  ruwan sanyi, 


Bayan yasha ruwan ne duk sun gaggaisa, 

tare da mishi sannu da hanya, 

sukaje Dinning table sukayi breakfast dan suma gidan duk babu wanda yayi karin kumallo.

Sosai suka cika musu gaba da abubuwan ci da sha namusammam.

Ummi da kanta ta zubawa Saifuddeen tuwon farar d'anyan shinkafa, 

miyar zogale wanda yasha man shanu da kifi da busasshen nama, 

cikin kula Ummi tace. 

"Nida kaina nayi maka girkin dan nasan kayi begen miyar da ita kafi so."

murmushi yayi tare mata alamun godiya da jin dadi kana ya fara cin abincin da yayi begenshi sosai. 


Hayatuddeen kuwa couscous da miyar hanta Adda Rahma ta sa mishi.


Ummi kam ji takeyi kamar ta bawa Saifuddeen abinci a baki sabida yadda yakeci wanda dama halittarsa kenan rabin malmalan yaci, 

kana ya cire hannunshi tare da jawo jug d'in damemmiyar fura da nono mai sanyi da zuma, 

da Sauri Goggo Dada ta tsiyaya mishi a kofi ta mik'a mishi. 

Hayatuddeen kuwa kular pepper chicken ya jawo kamar kura yayi ta yagan cinyoyin kaji saida yayi hanik'an sannan ya mik'e ya koma tsakar parlour. 


Su kuwa su Ummi babu wanda ya iya cin komai saida sukaga Saifuddeen ya k'oshi, 

sannan sukaci, 

suna gama duk suka dawo parlour akaci gaba da hira. 



Suna cikin hirar Bappa Ali da Malam Ashiru da Baba Hamisu suka iso.


Nan kuma aka gaggaisa tare da yiwa juna barka, 

karshe dai su Ummi d'akinta suka koma d'akinta. 

Dan Su Mudassir, Jabeer, Hisham,  Kabiru, Salisu, Ishaq, Ahmad. 

Kusan duk nan suka wuni yayinda Saifuddeen ke zaune a tsakiyarsu bisa weelchair d'inshi da system nashi a cinyarshi wanda dashi yake bawa kowa amsar mgnar da zai mishi. 


Sune basu tafiba saida akayi sallan azahar.


Bayan sallan la'asar Salisu da Ahmad suka meda Goggo Dada da Aunty Nina dasu Bappa har cikin Dukku sannan suka dawo. 


Suna isa ana kiran sallan margin.

 Bayan anyi sallane duk suka cika a parlour Ummi, 

nan sukayi dinner,

kana suka dawo tsakiyan parlour suna d'an tab'a hira, ganin isha ya kusa ne Salisu ya mik'e ya tafi da Salima kana Ahmad kuma ya maida Adda Rahma da yaranta. 


Koda kuwa suka tafi ci gaba da hira dasu Rahma, 

cikin kula Hayatuddeen ya kalli Hamman nashi a hankali yace.

"Hamma Saifuddeen lokacin baccinka yayi fa."

Kanshi ya gyad'a alamun to. 

Kana ya kalli Umminshi da k'annen nashi kana yace.

"Bari inje in d'anyi wonka kana inyi bacci."

Duk cikin body language yayi mgnar fahimtar hakanne yasa sukace to.

Ganin ya juya akalar weelchair d'inshi ya nufi side d'inshi da aka gyara mishi kuma aka nuna mishi tun kafin ya dawo.

Dan haka kai tsaye ya nufi parlour. 

Ummi ce ta kalli Hayatuddeen tare da cewa. 

"To kuma kana zaune?."

Gyara konciyarshi yayi tare da cewa. 

"Ummi ai da kanshi yakeyiwa kanshi komai ba, ruwan wonka kuma Adda Rahma ta had'a mishi."

kusan a tare sukace. 

"Har wonkan?."

Kai ya gyad'a musu tare da cewa. 

"Harda canza kaya da shirya kanshi da komi da komai yanawa kanshi."

wannan labarin yayi matuk'ar sasu cikin tsananin farin ciki. 


Shi kuwa Saifuddeeen yana shiga parlour nashi, 

wani sassanyan ajiyan zuciya ya dire dan daddad'an sanyi da k'amshin da yaji yana ratsashi. 

a tsakiyar parlour ya d'an tsaya ya karewa komai na parlour kallo,.

"Da kyau." yace a ransa kana ya wuce cikin bedroom yana shiga kai tsaye bakin gadon ya nufa, 

ido ya dan lumshe tare da yin luuu dasu,

 dan ya fara jin bacci, 

rigarshi ya fara cirewa iska ya fesar a hankali jin daddad'an sanyi da k'amshi, k'afafunshi ya dire bissa tattausan carpet dake gaban gadon, 

singlet d'inshi ya zare tare da ajeshi kan gadon a hankali ya ja ta zugen shi ya kunceshi soko-soko hannunshi d'aya yasa ya d'an danne bakin gadon yadda ya samu ya d'an d'aga mazaunanshi kana yasa d'aya hannun yayi kasa da dogon wondon saida ya kawoshi har guiwanshi sannan ya zauna, tare da sunkuyowa ya cire wondon baki d'aya. 

Ya rage boxer ne kadai a jikinshi, 

A hankali yayi mik'a mai cike da sak'onni a jikinshi, 

"Hoooohhh." ya bada sautin tare da sunkuyar da kanshi murmushi yayi ganin yadda bananarshi ta harba tayi sama sam b'al...!




To Gafa Saifuddeen ys dawo ga Zaleeha ga Amina ga Mama gasu Raveel da Abdussalam ƙaƙa tsara ƙaƙa wadin Zaleeha saura kaɗanfa hmmm



                            By

           *GARKUWAR FULANI*

8/18/20, 7:53 PM - Ummi Tandama: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


          *NAKASA BA KASAWA BACE*


                             *PAGE 25*


                          *NA*

             *AISHA  ALIYU GARKUWA*


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇




Ahankali weellchair ɗin nasa ke tafiya har zuwa bakin bathroom, hannayensa ya sanya ya tura ƙofar bathroom ɗin, tare da ɗan sake danna wani madanni dake jikin wellchair ɗin, take yaci gaba da tafiya.

   Saida ya ƙaraso har tsakiyan bathroom ɗin sannan ya tsaida  keken nasa, ahankali ya ɗaga idanunsa yana me ƙarewa cikin bathroom ɗin kallo, sosai aka ƙawata bathroom ɗin, komai tsab-tsab yayinda aka sauƙaƙa masa komai ta yanda zaiyi amfani da komai cikin sauƙi batare da ya sha wahala ba, inda akayi masa wani ɗan igiya kusa da toilet ɗinsa yanda koda zai zauna akai basai yasha wahala ba, haka wajen da zaiyi wanka ma anƙawata masa shi inda akayi masa komai asauƙaƙe,       Madannin kekensa ya danna tare da ƙarasawa wajen da zaiyi wanka inda aka kewaye wajen da wani haɗaɗɗen glass,  cikin nutsuwa ya zare boxer ɗin dake jikinsa tare da yunƙurawa ya sauƙa akan kekensa cikin tsananin  shauk'i ya zauna  acikin bathtube ɗin wanka, wanda cikinsa ke cike da tsabtataccen ruwa,  ahankali yazame yaɗan kwantar da jikinsa acikin bathtube ɗin yayinda gaba ɗaya ruwa ya haura saman jikinsa, iya kai da ƙirjinsa kawai ake gani,  kansa ya jingina da jikin bathtube ɗin tare da lumshe kyawawan idanunsa, wani irin abune yaji yana sauƙa ajikinsa mai kama da kasala,  sannu ahankali tunaninta ke ɗauke duk wata nutsuwarsa, idanunsa cike suke da ɗoki da kuma son sake ganin kyakkyawar fuskarta,  har yanzu yakasa manta yanda tattausan hannunta daya taɓa jikinsa, sannan kuma har yanzu  ya kasa manta kyakkyawan hug ɗin da ta bashi alokacin da take roƙonsa da yazo su gudu lokacin da yaran Dalla ke shirin cim musu,  wani irin abune yaji ya taso masa daga kansa har zuwa ƙasan ƙafarsa, ahankali yasake gyara kwanciyarsa acikin ruwan yana mejin wani irin fitinanniyar sha'awarta na taso masa, yayinda joystick ɗinsa dake cikin ruwa ta tashi tayi tsaye,  shikansa yana mamakin halitta irin nasa. 

Ido ya lumshe a hankali ya tuno, 

abinda yake faruwa dashi na sha'awa tun randa ta ruggumeshi.

Abinda bai tab'a jiba a tsawon rayuwarshi kafin had'uwa da ita lokacin Yanada shekaru 30  a duniya amman bai taba ji ko ganin gabanshi ya tashi ba, asalima in yaji wuya kad'an gaba d'aya ma gabanshi ke komawa ya lafe ya b'uya yayi lakwas,

musamman in yayi azumi. To amman tun randa suka had'u ya fuskanci cewa yana da wata irin fitinanniyar jaraba mai tada hankali,

  jikinsa ɗin ne yasake harbawa sakamakon tunowa da tausasan laɓɓanta da yayi wanda yaji tamkar alokacinne take motsasu, harshenshi ya d'an turo woje cike da shauƙi yaɗan lashi laɓɓan bakinsa kana ya ɗan buɗe idanunsa wanda suka ƙanƙance kuma sukayi ja, sakamakon wutar sha'awarta dake cinsa arai, 

coming ransa yace. 

"Name dawo gareki Zaleeha ina nan tafe, Allah yana sona tunda bai k'addara aurenki cikin shekara d'aya da nayi bana nan d'inba,  ya kuma bani damar sanin duk wani motsinki da shiga da fitanki ta sanadin aminine, shiyasa na rayu a india ba fargaba sabida ina jin labarinki wurin aminin da samun kamarshi ke wuya a duniya". Ishaq kensn.

Akasalance yashiga wanke jikinsa domin gaba ɗaya yayi weak, yayinda Saifuddeen ɗinsa kuwa har yanzun taƙi kwanciya, cikin nutsuwa yayi wankansa inda ya wanke jikinsa tsab, daddaɗan ƙamshin sabulun da yayi wankan da shine ke tashi ajikinsa.  Yana kammala wankan nasa yayi alwala, kamar yanda yasaka karsashi wajen shigar da kansa bathtube ɗin wankan haka yanzuma ya saka karsashin wajen ganin ya fito da kansa, wata farar rigan wanka irin ta maza dake rataye ajikin wani ɗan ƙarfe ya ɗauka tare da sanyawa ajikinsa, yana gama dai-dai-ta zamansa akan kekensa ya danna madannin da zai sanya keken tafiya batare daya wahalar da hannayensa ba,  koda yafito daga cikin bathroom ɗin  kaitsaye gaban dressing mirror ya nufa inda ke cike da tsadaddun mayukan jiki da kuma na gashi,  ɗan ƙaramin towel ya ɗauka tare da soma goge jiƙaƙƙen gashin kansa, yana gama tsane ruwan ya ɗauki handrayer tare da jonawa ajikin socket yashiga busar da gashin kansa, mintuna kaɗan kuwa gashin nasa ya bushe yayi wasar kamar ma ba'a samasa ruwa ba, wani body lotion ɗinsa me daɗin ƙamshi ya shafa tare da ɗaukan oil body spray me matuƙar ƙamshi ya kuma shafawa ajikinsa,  cumb ɗinsa ya ɗauka ahankali yashiga gyara haɗaɗɗiyar sajensa wanda tayi matuƙar ƙarawa fuskarsa kyau da kwarjini dan yadda ya cika yayi lip-lip a farar fatarshi tayiwa fuskar tasa k'awanya, yana kammalawa,

 yashafawa kansa wani hair oil me ƙamshi, kekensa ya tura har zuwa gaban tangamemen sif ɗinsa, inda aka jere masa gaba ɗaya kayan sawansa a hawa na ƙasa dana tsakiya wani long jeans black colour ya zaro tare da kai dubansa ɓangaren da t-shirt's ɗinsa ke jere reras, gaba ɗaya kayan sawansa sabine ƙal ƙal, wata white polo shirt ya ciro me kyau,  cikin dabara yasanya wandon ajikinsa tare da zura farar t-shirt ɗin ajikinsa, masha Allah sosai yayi kyau yayinda gashin kansa keta faman ƙyalli, rufe sif ɗinnasa yayi tare da sake tura kekensa ya ƙarasa gaban mirror, farfumed ya fesa ajikin kayan nasa tare da ɗaukan wayarsa,

  tura kekensa yayi ya ƙarasa gaban bedsite carbinate inda anan aka aje masa sallayan yin sallan sa, ɗaukan sallayan yayi tare da shimfuɗawa kasancewar lokacin har ansoma ƙiraye ƙirayen sallan Isha,  cikin hikima ya sauƙo daga kan kekennasa tare da zama akan sallayan,  azaune ya gabatar da sallan isha'ɗinsa yayinda daga ƙarshe ya haɗa da shafa'i da wuturi, akan ƙafafunsa ya zauna inda yajima  yana tasbihi,   hannunsa ya sanya ya ɗauko al'ƙur'anin dake aje kan bedsite,  ɗaura ƙur'anin yayi akan cinyansa tare da buɗe suratul Ma'idah ahankali cikin nutsuwa yashiga rera karatun yayinda zazzaƙar muryarsa ke ratsa mishi zuciyarshi,  aƙalla ya ɗauki wasu mintuna kafun ya kammala karatun addu'a yayi tare da shafawa kana ya rufe Al'Qur'anin, gadonsa yaɗan dafa tare da jawo wellchair ɗinsa ya yunƙura tare da komawa kai ya zauna, laptop ɗinsa ya ɗauka yashiga duba harkan kasuwancin su, daga nanne kuma yashiga duba labaran halin da duniya take ciki.

Hayatuddeen ne yaturo ƙofar ɗakin ya shigo bakinsa ɗauke da sallama yayinda hannunsa ke ɗauke da ɗan ƙaramin tray wanda samansa ke ɗauke da yankakkun fruits masu sanyi sai goran ruwa mai sanyi kana d'aya hannunshi rik'e da robar magunguna, 

ƙarasowa cikin ɗakin yayi tare da duban hamman nasa da gaba ɗaya hankalinsa ke kan laptop ɗinsa, cikin kulawa ya aje tray ɗin akan table d'in glasses  dake gaban gadon hamman nasa tare da cewa.

 "Hamma kasha fruit inji Ummi,

ga kuma magungunan ka" 

ido ya d'an lumshe   tare da ƙaɗa kansa alamar to, ɗaukan green apple wanda yake ba'a yanke ba yaɗan gutsura, lumshe idanunsa ya kuma yi tare da soma tauna apple ɗin ahankali,  ganin haka yasanya Hayatuddeen sakin murmushi tare da ɗan matsowa kusa da hamman nashi,  wayars ƙiran Samsung galaxy S10 ya ciro tare da shiga camera, hannayensa ya sanya akan kafaɗun Hamman nasa ya ɗaukesu  hoto selfie wanda dukansu murmushine ɗauke akan fuskarsu, sosai sukayi kyau a hoton bama kamar Saifuddeen,  komawa gefe Hayatuddeen yayi inda ya shiga Whatsapp ɗinsa ya ɗaura hoton nasu da sukayi a status ɗinshi. 

Shikuwa Saifuddeen sosai yasha kayan fruits dan shi yafi ta'ammali da yayan itatuwa fiye da abinci, bare kuma yanzu da likitocin suka umarceshi da yawanta cinsu. 

Maganinshi ya sha.

ya gamawa sauƙa yayi daga kan wellchair ɗin ya kwanta akan lallusan gadonsa wanda yaji tattausan katifa, luf yakwanta tare da ɗaura kansa akan pillow kana yaja blanket ya rufe rabin jikinsa, ganin haka yasanya Hayatuddeen ɗaukan ragowan kayan marmarin yafice daga cikin ɗakin, ganin fitan Hayatuddeen yasanya Saifuddeen yakai hanunsa saman gadonsa inda anan makunnin wutan ɗakin yake ya kashe, bedsite lamb wanda ke bata light blue ɗin haske ya kunna tare da sake gyara kwanciyarsa, wani irin sha'awane yasake taso masa wanda yasanya ya kasa bacci sai juyi yaketayi akan makeken gadonnasa. 


A hankalin Umminshi ta shigo, 

taku takeyi a hankali dan ganin alamun yayi bacci, 

kanshi ta iso tare da zuba mishi ido, 

sai kuma tayi saurin sunkoyowa kanshi jin ya kamo hannunta, 

murmushi tayi mishi mai cike da k'aunan gudan jinin nata, 

sannan tasa hannunta na dama ta shafa kanshi tare da cewa. 

"Ka gaji da yawa kayi bacci ka huta,  ko Babana."

kai ya gyad'a mata tare da sumbatar hannunta kana ya maida idanunshi ya lumshe a hankali. 

Ganin hakan yasa Ummi gyara mishi blanket d'in daya rife iya k'ugunshi sannan ta fita, 

tare da ja mishi k'ofa. 

A parlour ta samu Ahmad yanzu ya dawo daga meda Rahma gidanta, 

Ganin kamar yana buk'atar matarshi ne yasa Ummi cewa Raliya. 

"Ke Raliya dare yayi ni zanyi bacci tashi ku tafi."

cikin gajiya dan yau kusan wuni tayi hidima, 

mik'ewa tayi kana tabi bayan Ahmad da tuni ya fita cikin jin dad'i. 



Ita kuwa Ummi ita da Raihana ne sukaci gaba da hirar.


Hayatuddeen kuwa yana maida plate ɗin kayan marmarin kitchine direct sama ya haura inda ɗakinsa yake, yana shiga ya faɗa kan gado tare da shiga cikin Whatsapp ɗinsa don yaga anturo masa new messages da yawa, sunan Asma'u Ahmad Matawalle ce a sama tayi masa comment akan hoton nasu daya sanya a status ɗinsa inda tayi rubutu kamar haka.

 "Tsarki ya tabbata ga Ubangijin talikai da ya halicci Saifuddeen cikin wannan halitta mai d'aukan hankali"  murmushi mai kama da dariya Hayatuddeen yayi tare da yi mata reply inda yace. "Kuɗin ganin status yawane dashi ina fatan zaki iya biya?".

Itama dariya tayi kana tace "Zan iya bada gaba ɗaya dukiyata indai zanke ganin wannan kyakkyawar fuskar ɗan uwannaka ako da yaushe". 

Yanzu kam dariya Hayatuddeen yayi sosai yayinda ya rubuta cewa.

 "Sai kiyi ta addu'a dan samun Hammana  sai mai tsananin rabo, dan sai ya zaɓa kuma saiya darje, kuma shi mijin mace d'aya ne d'aya tak" 

Itama dariya tayi sosai don tasan Alhamdulillahi itama tana da nata kyaun yanda bakowani ɗa namiji bane zai ƙita, haka dai suka ɗan taɓa hira kaɗan da ita duk kuma zancennata akan Saifuddeen ne, don sosai ya tsaya mata arai. 


Saifuddeen kuwa yasha juyi kafun yasamu da ƙyar bacci ya ɗaukesa, ko acikin baccin nasa kyakkyawan fuskar Zaleeha itace keta zuwar masa, inda yayi bacci cikin wani irin shauƙi. 


Washegari.

Ƙarfe tara tuni yagama shirya kansa inda yayi kyau cikin riga da wandon jeans ɗin dake jikinsa, ahankali yake tafiya da keken nasa harya kawo bakin ƙofar fita daga ɗakin, hannunsa yakai jikin handle ɗin ƙofan ya buɗe,  yanzukam da kansa yake tuƙa keken nasa  cikin nitsuwa da salonsa na k'in wahala inda ya dumfaro babban falonnasu.

Ummi, Hayatuddeen, da kuma Raihana su ya tarar zaune acikin falon,yayinda Raliya ke ta kaikawo tsakanin dinning area da kitchine tana shirya musu breakfast, shigowarsa cikin falon shi yabayyana murmushi akan gaba ɗaya fuskokin ƴan uwan nasa, ƙarasowa tsakiyan falon yayi tare da kai dubansa ga mahaifiyarsa wanda takasa ɗauke idanunta akansa, murmushi zallan ƙaunarsa ne kwance akan fuskarta,  murmushin daya bayyana kyawunsa yayi tare dayi mata alaman.

 "Ina kwana" 

"Lafiya ƙalau Saifuddeen ya jikin naka?".

 Ummi tafaɗa cikin kulawa. 

Da body language yayi mata alaman.

 "Da sauƙi" nan Raihana ta gaidashi tare da tambayar jikinsa,  itama da body language ya amsa mata  fuskarsa ɗauke da murmushi tare da mik'o hannu ya shafan kan Affan dake kwance bisa jikin Ummi. Raliya da Hayatuddeen ne suka gaidashi, suɗinma amsa musu yayi cike da ƙaunar ƴan uwannasa.

 Raliya na gama shirya musu break fast shida kansa ya sarrafa kekensa har zuwa kan dinning table ɗin,  kujera ɗaya ya matsar gefe kana ya turo kekensa har wajen,  kasancewarsa bamai cin abinci da yawa bane hakan yasa tea kawai yasha sai kuma chips dayake ɗan tsakala yana sawa abakinsa kaɗan kaɗan, sosai zuciyar ƴan uwansa da Umminsa ke wanke fari ƙal, babu abun dake ɗawainiya dasu face farin ciki da jin daɗi, kasancewarsu da Saifuddeen awaje guda baƙaramin ƙara musu kuzari da karsashi yakeyi ba, basu jima da fara breakfast ɗinba Ahmad da  Saminu suka shigo, nan suma suka zauna aka shiga cin abincin tare dasu,  duk da cewa suɗin surukaine ga Ummi, amma su jin kansu suke matsayin ƴaƴa awajenta, don sunajin kamar yanda su Hayatuddeen ke ƴaƴa awajenta haka suma suke saboda haka babu batun wani nuƙu-nuƙu agabanta don mahaifiyace garesu a gabanta suka girma tun suna yara har zuwa samartansu sukanci abinci a gabanta a matsayinta na uwa a garesu shiyasa kuma, koda suka auri yaranta tafiyar bata sauya zani ba. 

Suna kammala cin abincin ne dukansu suka koma falo suka zauna,  hira sosai sukeyi yayinda Saifuddeen ke binsu da idanu yana me karantar abun da kowannensu ke cewa, idan na dariyane yakan ɗan murmusawa, ana haka ne Ishaq da tawagar ƙungiyarsu ta Joint National  association of persons with disabilities (Jonapwd) Gombe State Chapter. All the best! Suka ƙaraso, nanfa falon Ummi yacika tam da mutane, makafi, guragu, kurame, duk zuƙatansu suka cika da murnar ganin Saifuddeen,  Ishaq kam ji yake kamar yamaida abokin nasa ciki saboda daɗi, duk da cewa baya gani amma zuciyarsa ta gamsar masa da cewa Saifuddeen ɗinsa aboki kuma ɗan'uwansa ya samu lafiya, haka Ummi tasa su Raihana suka ajiye abunci da abunsha ga kowanne daga cikinsu, baƙaramin daɗi Saifuddeen yaji azuciyarsa na ganinsu da yayi ba, haka suka kwashe tsawon awanni suna tare da juna, saida akayi Azahar ne Ishaq ya tattarasu duk suka koma.

 Adda Rahama da Dr Adnan da  Baba Bello haɗi da goggo mahaifiyarsa ne suka zo,  suna zuwa babu jimawa kuwa saiga mutanen dukku wanda suka kusa cika mota suma sunzo don duba jikin Saifuddeen ɗin da kuma taya Ummi murnar dawowarsa,  nanfa gida ya ƙara ɗinkewa da jama'a.


  Da yamma kuwa Alhaji Sani da Alhaji Kabiru da kuma Alhaji Sulaiman mahaifin Hisham da Alhaji Adamu yayan Jabeer sukazo duba jikin Saifuddeen ɗin, sosai ƙwarai yaji daɗin ganinsu, suma sunji daɗi sosai da suka tararda jikin nasa da sauƙi, nan suka ɗan taɓa hira inda kowanni magana da body language sukeyi idan basu gane ba kuma yakan rubuta musu awayansa sai ya basu su karanta, sosai suka ɗansha hira kafun daga bisani sukayi masa sallama, koda sukazo tafiya al'khairi me yawa suka bawa Ummi don sunsan idan suka bawa Saifuddeen to ko sama da ƙasa zasu haɗe bazai amsa ba,  awajen Ummin ma kuwa ba tsira sukayi ba don kafewa tayi tace bazasu amsa ba, da ƙyar Alhaji Sani yasanya Ummi ta amsa, inda yayi mata tuni da cewa bakyau maida hannun kyauta baya.  Badon Ummi tasoba haka ta amsa kana tayi musu godiya.   


Wayar Hayatuddeen dake aje kan kujeran falonne kete tsuwa alaman shigowar ƙira saidai hartayi ta katse ba'a ɗauka ba, wani ƙiranne ya kuma shigowa, Hayatuddeen dake cikin kitchine ne yafito da gudu hannunsa ɗauke da wani dogon tsinke wanda jikinsa ke saƙale da gasashshen nama sai tiriri yake da'alama yanzu aka gasa naman,  saura ƙiris wayan ta tsinke ya ɗauka tare da karawa akan kunnensa, cikin yanayi na ɗan faɗa tace.

 "Saikuma kaga dama ne kafun ka amsa wayana?" 

Dariya Hayatuddeen yayi  tare da cewa.

 "Yi haƙuri Likita ina kitchine ne".


Murmushi Amina dake zaune akan kujera tayi tare da gyara zamanta cike da kulawa tace "Kwaɗayayye kawai, meya kaika kitchen?."

hyyy yayi dan zafin da yaji lokacin da ya kai bakinshi kan sokan nama daketa tiriri,

jin tana mishi dariya ne ya sashi cewa. 

"Nama ne Ummina ta gasa min, 

shine nake d'an tab'i."

Kwaffa tayi tare da cewa.

"Ni bawannan ba yajikin Hamma Saifuddeen?".


"Eh dai naji, jikin Hamma Saifuddeen da sauƙi sosai, don yanzu haka ma muna gida, da jiya kika ƙira ma wataƙila da kinzo kin dubashi don muna Abuja"  


Idanu Amina tazaro tare da cewa.

 "Wai kana nufin ya tabbata kun dawo Nigeria? kuma ma wai har jiya kun sauƙa Abuja shine baka ƙirani kasanar dani ba?"  


Dariya Hayatuddeen yayi tare da cewa.

 "Ga zahiri kuwa muna mgna da number ta na Nigeria."

Cikin jin haushi tace. 

"Tun shekaran jiyan can nake kiran number ka ta Indian bata shiga, 

sai kawai yanzu kamar da wasa nace bari in gwada mtn naka.

kuma sai ya shiga, gsky Hayatuddeen baka kyauta min ba wlh."

cikin tauna naman yace

"Tuba nake Likita, ai bansan kina da buƙatar ganin kyakkyawan Hamman nawa ba!" 

Cikin haushin rashin sanin dawowarsu da batayi ba tace "Harsai na faɗa mane sannan zaka sani, nidai ba wani nan munyi faɗa".

Dariya sosai Hayatuddeen yayi tare da cewa.

 "Kiyi haƙuri bokan turai!". 

"Nidai ai nace maka munyi faɗa ko".

 tana gama faɗan haka ta kashe wayarta, dariya sosai Hayatuddeen yayi, Ummi dake tsaye abayansa ne ta ƙaraso cikin falon, dubansa tayi tare da cewa.

 "Kai kuma kaida waye kake waya haka?"

Murmushi yayi tare da cewa "Amina ce fa Ummi wannan nurse ɗin da ta kula da Hamma Saifuddeen lokacin da muke Abuja, to shinefa yanzu da ta ƙira nake shaida mata dawowar mu shine wai ita tayi fushi da har jiya muka sauƙa a Abuja ban gaya mata ba taje ta duba jikinshi".

Murmushi tayi cikin tsananin jin dad'i tana matuk'ar son duk wani maison Saifuddeen d'inta,

murmushin kawai Ummi ta kumayi tare da zama akan kujera kana ta maida hankalinta ga TV inda sunna tv ke haska wa'azin Malam Isah Ali Pantami.  


Yau tunda tazo wajen aikin nasu fuskanta aɗaure yake tamau, sam takasa sakin fuska ga kowa wanda hakan ya matuƙar bawa abokan aikinta mamaki, don kuwa sunsan bahaka take ba ita takowace sannan itaɗin me yawan fara'a ce saɓanin yau da suka ga ta tsuke fuska,  fitowarta daga ɗakin gabatar da shirye-shirye kenan inda ta gabatar da shirinta na mushaƙata, kaitsaye ɗakin hutawansu ta nufa inda anan tabar jakarta harma da wayarta. 

Koda ta shiga cikin ɗakin kan wata kujera ta zauna tare da ɗaukan jakarta, zip ɗin ta zuge kana ta ciro wayarta, 4 missed call ta iske acikin wayar wanda kuma duk daga Abdussalam ne, tsuka tayi tare da kunna data'n wayarta ta shiga Instagram,   Raveel ne ya turo ƙofar ɗakin ya shigo bakinsa ɗauke da sallama,  can ƙasan maƙoshi ta amsa masa sallaman batare da ta ɗago kanta ta kalleshi ba,

 asanyaye ya tako ya ƙaraso zuwa inda take, kan wata baƙar kujera dake facing wanda take ya zauna murya asanyaye yaƙira sunanta "Zaleeha!" 


Bata amsashi ba haka kuma bata ɗago kai ta kalleshi ba, ganin haka yasanyashi sauƙe ajiyar zuciya, kansa ya ɗan langwaɓar gefe guda cike da tsananin shauƙin mayen soyayyarta yace.

 "Dan Allah M B S Dukku ki saurareni mana, ashe shikenan don zuciyata ta kamu da soyayyarki tayi laifi? Dan Allah Zaleeha  kiyi haƙuri ki fahimci irin sonda nake miki, wallahi inasonki ina miki son da nikaina bansan adadinsa ba, rasaki dai-dai yake da daiɗaicewar tunanina Inasonki Zaleeha, dan Allah ki Amshi soyayyata!!" 

Tsananin rauni da damuwar dayake cikine ya bayyana ƙarara akan muryarsa. 


Idanunta ta lumshe tare da cizon laɓɓanta wanda suka sha pink lipstick, jin kalaman nasa take tamkar sauƙan ruwan zafi afatar jikinta, waye zai fahimceta? wanene zai gane me takeji azuciyarta? tabbas da ace mazan dake kawo kansu gareta da sunan soyayya sun san metakeji acikin ranta tabbas da zuwa yanzu sun ƙyaleta hakanan ta huta,  tana matuƙar ganin ƙiman Raveel saboda koba komai abokin aikinta kuma suna shiri sosai dan yanada abin dariya tamkar abokin wasanta haka suke kodan kasan cewarshi babarbare ne, amma ayanzu furta mata kalman so da yayi yasanya taji gaba ɗaya batako son ganinsa, burinta ayanzu shine kowa yafahimci halin da take ciki na tsananin soyayyar dake cinta azuciya.  

Ganin yanda ta rumtse idanunta ne yasanya Raveel ƙiran sunanta murya atausashe yace.

 "Balaifina bane Zaleeha don Allah Karki tsaneni, laifin zuciya da ruhina ne da suka matuƙar kamuwa da soyayyarki, najima ina dakon soyayyarki araina Zaleeha, please and please ki amshi soyayyata ki amshi soyayyata kozan samu sauƙin abun danakeji azuciyata!!".

 tuni idanun Raveel suncika tab da ƙwalla, ji yake kamar yajawota jikinsa yayi hugging ɗinta sannan yasata ta amsa masa soyayyarsa. 

Idanunta da suka kaɗa sukai jajur ta buɗe tare da watsa masa su, saida yaji wani yaarr acikin jikinsa, cikin dakiya tare da ƙunan zuciya ta dube shi murya asarƙafe tace.

 "Please Raveel i say leave me alone!, dan Allah kabarni na huta, kana ta faɗin kana sona! kana sona! na tausaya maka, kai kasan ni me nakeji acikin tawa zuciyar kuwa! to ji nake tamkar zan mutu in bar duniya in ban sameshi ba? har yanzu ina mutuntaka amatsayinka na abokin aikina,saboda haka kana da sauran daman da zaka janye batun soyayya agareni, bana sonka Raveel bana kuma tunanin zan soka ko anan gaba!!".

  miƙewa tsaye tayi tare da ɗaukan jakarta ta nufi hanyar fita daga ɗakin, Sunanta Raveel yashiga ƙira amma sam bata tsayaba balle ta waiwayo ta kalleshi haka ta fice daga cikin ɗakin. 

Idanu Raveel ya rumtse take saiga hawaye sun biyo kan ƙuncinsa, ya zaiyi da matsanancin son Zaleeha da yakeyi? Tayaya zai soma rarrashin zuciyarsa akan ta haƙura da Zaleeha?   Kansa ya kifa akan ɗan madaidaicin table ɗin dake gabansa yana mejin wutar soyayyarta na ƙara kunnuwa acikin zuciyarsa. 


Itakuwa Zaleeha kai tsaye motarta ta nufa tana shiga tayi mata key tare dayin reverse, maigadi ne ya wangale mata gate ɗin fita daga cikin gidan redi'on nasu na vission FM.  gudu takeyi sosai akan titi gaba ɗaya komai ya cakuɗe mata waje ɗaya, ko ina tasanya kanta batajin daɗi, gida babu daɗi haka wajen aiki ma babu daɗi ko ina ta kutsa zancen aure akeyi mata kamar ita d'aya ce budurwa a duniya, hannunta tasanya ta bugi steering motar tata da ƙarfi tare da ɗan sake sautin kukanta,  kuka takeyi ƙasa-ƙasa hadda sheshsheƙa, kai tsaye unguwar sarki tanufa hanyar da zai sadata da  shagon A.A ALIYU PHARMACY  a dai-dai wajen a dai-dai lokacin kamar wannan ranan anan ta tsaida motarta tare da zubawa ƙofar shagon A.A ALIYU PHARMACY ɗin ido, dai-dai inda tafara ganinsa ta sauƙe idanunta, sannu ahankali tasoma ganin tamkar alokacinne abubuwan da suka wakana tsakaninsu ke faruwa,   lumshe idanunta tayi tare da sakin sautin kukanta ya fito fili, cikin magagin soyayyarsa da ta rufe mata ido tace.

 "Inakake? Inakatafi kabar zuciyata cikin tsananin kewa da begenka? Kaine mafarkina haka kuma Kaine Zahirina, Koba danni ba kodan zuciyar da ka dasawa soyayyarka acikinta dan Allah kabayyana agareni na ganka,  kowa yanamin kallon zautacciya wacce take son gaibu, wasu suna faɗin cewa kai ba mutum bane, kafito ka nuna musu cewa kai mutum ne kamar kowa, kazo gareni Ina Tsananin buƙatarka ayanzu fiye da wancan ranan, Dan Allah kazo gareni!!!".

 Kuka take sosai tare da kifa kanta ajikin steering motar, wani irin zogi zuciyarta keyi mata yayinda idanunta ke ƙoƙarin rufewa,  kuka tayi sosai harsaida wani irin azababben ciwon kai ya rufeta kafun ta zaro wani baby pink colour handkerchief daga cikin jakanta tashiga share fuskarta wacce tayi dama dama da hawaye, sake duban ƙofar shagon tayi, sai kuma ga wasu hawayen na sake sauƙowa daga cikin idanunta, dai-dai lokacinne wani matashin saurayi ya shiga kukkulle ƙofofin shagunan yana samusu kwaɗo kasancewar anata ƙiraye ƙirayen sallan magriba saboda haka zasuje sallah, ganin cewa sun rufe shagonnasu ne sannan da ɗai ɗai da ɗaiɗai jama'an dake wajen ke tafiya izuwa masallaci hakan yasa cikin rashin kuzari ta tada motar tata, ayanzukam ahankali take tafiya da motar kasancewar gaba ɗaya jikinta yayi weak ga wani irin zazzaɓi da ciwon kai da suka kawo mata cabka lokaci guda.  

Agaban tankamemen gate ɗin gidansu dake cikin New G.R.A ta tsaya da motartata tare da danna wani ɗan siririn horn, Malam Kalla me gadi ne ya wangale mata gate ɗin, yayinda ta tura hancin motar tata cikin gidan,  ko parking mai kyau yau batayi ba haka ta fito daga cikin motar, kai tsaye ɓangaren Mamy ta nufa, don acanne kaɗai take da yaƙinin samun nutsuwa,  cikin muryarta da ta dashe ta yi sallama, Unaisa da Unaid yaran Yaya Ahmad ne keta wasa acikin tsakiyar falon, suna ganinta suka taho da gudu cikin ƙaunarta su duka sukace.

 "Oyoyo Aunty Zaleeha!" 

cikin yanayin sanyi daya rusketa haɗi da rashin kuzari tashafa kayinsu kana ta zuge zip ɗin jakarta, kasancewarta uwar mak'ulashe da shan zaƙi hakan yasa sam bata rabo da abubuwan zaƙi dangin su chocolate's da sweet's, chocolate ta basu sannan ta nufi ɗakin Mamy nan tabarsu sunata murna. 


Sallama ɗauke abakinta tashiga ɗakin Mamy'n,

 Mamy dake zaune abakin gado tana ninke kaya ta amsa mata cike da kulawa tana me dubanta. 

"Sannu da hutawa Mamy!" tafaɗa tana me ajiye jakan hannunta kana ta sanya hannu ta zare mayafin dake jikinta.


"Yauwa Zaleeha sannu da dawowa ya aikin?".

 cewar Mamy tana mebinta da kallo. 


"Lafiya". tafaɗa ataƙaice kana ta faɗa kan gadon Mamyn blanket taja ta rufe jikinta dashi.

Cikin damuwa haɗi da kulawa Mamy tace .

"Yadai Zaleeha bakida lafiya ne?"

cikin muryarta dake neman sarƙewa tace.

 "Mamy kaina ke ciwo, sannan zazzaɓi na damuna!" 


"Subahannallah! kinsha magani kuwa?".

 Mamy tafaɗa aɗan rikice tana mai taɓa jikin Zaleeha'n, aikuwa nan taji jikin yaɗau zafi zau. 

Kai Zaleeha ta girgiza alaman batasha ba, tashi Mamy tayi tare da cewa.

 "Bari naje na kawo miki abinci da magani kisha inyaso idan yayanku Ahmad yashigo sai ya kaiki asibiti" 

Mamy na fita Aunty Lubna matar Ya Ahmad tafito daga cikin toilet ɗin dake ɗakin Mamyn, jikinta duk ruwa da'alama alwala tayi, ganin Zaleeha akwance lulluɓe da bargo yasanyata cewa.

"Lafiya kike kuwa Zaleeha duk wannan uban zafin shine ke hadda lulluɓuwa". 

Zaleeha da zazzaɓi yasake cin ƙarfinta ta ɗago idanunta ta kalli Aunty Lubna'n sai kuma ga hawaye shaaa sun kwaranyo daga cikin idanunta. 

Ganin hawaye na fita daga idon Zaleeha yasanya jikin Aunty Lubna yin sanyi, zama tayi akusa da Zaleehan tare da sanya hannu ta dafa kanta cikin kulawa tace.

 "Kuka kuma Zaleeha? share hawayenki kinji komai yayi tsanani yana tare da sauƙi ki sawa ranki jarumtar yadda zaki fuskanci k'addararki!" 

Kai Zaleeha ta girgiza mata tare da kife kanta akan cinyan Aunty Lubna'n cikin dasashshiyar muryarta tace "Menene laifina Aunty Lubna? meyasa kowa agidannan bazai yarda cewa inada wanda nakeso ba, sannan kuma ba aljani bane kamar yanda suke tunani, mutum ne shifa kamar kowa, Inasonsa! Aunty Lubna Inasonsa!, bansan meyasa kowa yaƙi fahimtan hakan ba hatta Ya Ahmad ɗina ma fa shima kallon bansan me nakeyi ba yakeyi mini gani yake wai ba mutum nake soba aljan ne!".

 shiru tayi da maganan tare da ƙara sautin kukanta. 

Cikin lallashi haɗi da tsananin tausayinta Aunty Lubna ta sanya hannunta ahankali take shafa bayan Zaleehan, cikin son kwantarwa da Zaleeha hankali tace.

 "Kiyi haƙuri Zaleeha ki kuma kwantar da hankalinki, nafahimci yanda kikeji kuma insha Allah zaki gansa harma kuyi aure dashi kidaina kukannan kinji shalelen Ya Ahmad ɗinta!". 

Wani irin sanyi kalaman Aunty Lubna suka sauƙarwa Zaleeha acikin zuciyarta, take taji son matar Yayan nata ya ƙara shiga ranta, nan tasoma ƙoƙarin share hawayenta harma da sakin murmushi, Mamy ce ta dawo cikin ɗakin hannunta ɗauke da plate ɗin abinci da kuma magani,  kasancewar taji sanyi acikin ranta bisa kalaman da Auntyn nata tayi mata hakan yasanya ta ci abincin saidai ba sosai ba magani tasha inda tayi alwala tayi sallah bata bar kan sallayan ba saida tayi sallan isha, anan ɗakin Mamy ta kwanta, mintuna kaɗan bacci ya ɗauketa,  ana idar da sallan Isha kuwa saiga Abdussalam yayiwa gidan dirar mikiya,  koda Mama taji zuwan Abdussalam nan tashiga zazzaga masifa wai Zaleeha batajin magana tayi baƙo me mahimmanci kuma taje ɗakin uwarta tabiyu tayi zamanta, koda akaje ɓangaren Mamy ƙiran Zaleeha nan aka iske tana bacci, inda Mamy ta shaida cewa bata da lafiya ne, haka Abdussalam ya koma gida batare daya samu ganin Zaleeha ba, Mama kuwa ba irin faɗa da maganganun da bata faɗa ba ita kaɗai taketa ɓaɓatun ta harda cewa wai Mamy ce ke zuga Zaleeha akan kada taso Abdussalam, haka tayita aikin baƙin ranta ita kaɗai awannan daren dai Zaliha aɗakin Mamy ta kwana.


                           ***


Alhamdulillahi yau kwanan su Saifuddeen uku da dawowa Nigeria, inda acikin kwanaki Ukunnan sauƙi kullum ƙara samuwa yake ga Saifuddeen yana mai ci gaba da shan sabbin magungunan da aka loda mishi.

sannan kuma acikin kwanakin kullum gidan nasu cikin karɓan baƙuncin mutanen dake zuwa gaisuwa yake,ciki kuwa hadda matar Alhji Sani, da kuma Matar Alhaji Kabiri da Mommyn Hisham.da kuma matar Alhaji Adamu Hajia Kingi damn k'anwarta Aunty Kubra yar kasuwa ce mai zuwa Dubai sari kayan k'awa na mata, time to time da ita Ahmad ke zuwa sari, suma sunzo sun duba jikin Saifuddeen inda Ummi taji daɗi sosai. 


Ranan yau takasance laraba kuma yaune ranan da Ishaq ya sanar da Saifuddeen cewa Zaleeha zatazo gidan nasu na nakasassu don gudanar da shirinta mai suna  BABU NAKASASHE SAI RAGO, hakan yasa tun safe yau Saifuddeen yatashi yanajin kansa cikin wani irin shauƙi yayinda yakejin zuciyarsa wasai. 


Ɓangaren Zaliha kuwa kwana biyu kenan yau bataje aiki ba sakamakon ɗan jinyan da tayi, amma yanzu Alhamdulillah jikin nata yayi sauƙi sosai, yayinda kullum Aunty Lubna ke ƙara kwantar mata da hankali,  hakanan yau tatashi tana mejin faɗuwar gaba yayinda takejin zuciyarta na tsinkewa akai akai haka dai ta kawar da duk wani abu da takeji ta shiga shirya kanta don zuwa gabatar da shirinta.


Fitowarsa daga wanka kenan lafiyayyar skin ɗinsa sai fidda daddaɗan ƙamshin  tsadadden sabulun wankansa, zaune yake agaban mirror yana shafawa jikinsa mai, yana kammalawa ya shiga gyara ƙawataccen sajen dake kwance akan fuskarsa, wanda ta sauya gaba ɗaya kamanninsa na da, taƙarawa fuskarsa kyau da kwarjini.   Wata dakakkiyar shadda me kyau da tsadan gaske wacce take da kalan skay blue ya sanya, sosai shaddar ta amshi jikinsa inda tayi bala'in da cewa da white skin ɗinsa,  wata haɗaɗɗiyar hulan zanna bukar wacce jikinta ke ɗauke da ratsin sky blue yasanya, yayinda aƙafansa kuwa yasanya lafiyayyun takalma sau ciki ƙiran kamfanin bally suma kalar sky blue garesu hakan yasanya haɗuwar tasa ta ƙara bayyana, bakaɗan ba Saifuddeen yayi kyau yayinda kyakkyawan sajensa keta ƙyalli, tsadadden turarensa me daɗin ƙamshi ya fesa ajikinsa take ɗakin ya gauraye da ƙamshinsa,  agogonsa ƙiran kamfanin rolex ya ɗaura akan tsintsiyar hannunsa na dama,  wayarsa ƙirar iphone ya tura acikin aljihunsa tare da sarrafa kekensa ya nufi hanyar fita daga cikin ɗakin.

Daddaɗan ƙamshin turarensa shiya ja hankalin su Ummi da Hayatuddeen da kuma Raihana dake falon suka dawo da kallonsu garesa,   "Wow Hamma Saifuddeen ka ganka kuwa? Wallahi Hamma na baka taɓa yin kyau irin na yau ba!!".

 Hayatuddeen yafaɗa cikin santin kyawun da yaga hamman nasa yayi. 

Murmushine ya bayyana akan fuskar Saifuddeen tare da duban Ummi cikin body language ɗinsa yayi mata alama akan wai maganan da Hayatuddeen yafaɗa gaskiya ne?

Dariya Ummi tayi tare da cewa.

"A kullum a koda yaushe kai kekyawa ne koda bakayi wonkaba bare kolliya. 

to ya kake zato idan kayi kwalliya to sai kayi kyau tamkar balarabe.

kaga kenan sharrin Hayatuddeen ne kawai dama tuncan kai kyakkyawane!" 

Dariya gaba ɗayansu suka sanya banda Saifuddeen wanda shidai saidai yayi murmushi. 

Cikin yabawa da kyawun da yayi Raihana tace.

 "Hammana wallahi kayi kyau sosai".

 murmushi yayi mata tare da yi mata alama kan cewa ya gode, Hayatuddeen kuwa cikin azarɓaɓi ya ciro wayarsa hoto yashiga ɗaukan Hammannasa yana me cewa ya samu na sawa a status da kuma Instagram.

jin haka Raihana ta amshi wayar tare da yi musu hoto shida Ummi da Raliya data shigo yanzu. Sunyi kyau matuk'a duk suna murmushi Ummi ta d'an roggofo kanshi. 


Cikin body language ɗinsa yayiwa Ummi bayanin inda zaije, fatan Alkhairi Ummi tayi masa tare da cewa.

 "Adawo lafiya".


Har bakin mota Hayatuddeen ya raka hamman nasa yayinda da kansa ya sauƙa akan kujeransa ya shiga cikin tsaleliyar motarsa ƙiran mercedes benz, agidan baya ya zauna sannan Hayatuddeen ya sa mishi weelchair d'insa a but yayinda  Sule driver ke tuƙasa...  


Tana gama shafa mai ta ɗauki tsadaddiyar hodan ta ta goga akan fuskarta,  tana gama shafa hodan ta ɗauki black eye pencil ɗinta ta goga acikin manya manyan idanunta dake matuƙar gigita masu kallonsu,   pink lipstick ta goga akan ƴan ƙananun laɓɓanta, yayinda tayi amfani da Mascara wajen miƙar da tulin eye lashes ɗinta,  ita ba mace bace wanda take da yawan cika meckup akan fuskarta hakan yasa bata ƙara komai akan fuskarta ba bayan wannan ɗan kwallian da tayi.

 Wani haɗaɗɗen lace wanda yaji dinkin riga da sket maroon colour wanda keda ratsin golding ash ta sanya, sosai kayan suka amshi jikinta inda sket ɗin ya bayyana haɗaɗɗiyar surar jikinta da kuma cikakkun hips ɗinta, parking dogon gashinta tayi atsakiyan kanta tare da zama akan stull ɗin mirror tashiga tsantsarawa kanta ɗaurin ɗan kwali, wani irin haɗaɗɗen ɗauri tayiwa kanta wanda yaƙara bayyana kyawun shigar nata,   wata ƴar siririyar sarƙa golding ash ta sanya awuyanta tare da liƙa ɗan kunnensa me kamar manne akunnenta,   wani takalmi me tsananin tsini da kyau wanda keda kalan lace ɗinta ta sanya aƙafafunta tare da ɗaukan wani vail shima maroon colour ta yafa ajikinta, baƙaramin kyau Zaleeha tayi ba ita kanta yau kyawunta ya ɗauki hankalinta, turarenta dake rikita maza ta fesa tare da ɗaukan haɗaɗɗiyar hand bag ɗinta me kalan kayanta ta riƙe ahannunta, wayarta tariƙe aɗayan hannun nata tare da car key ɗinta kana ta nufi hanyar fita daga cikin ɗakin, cikin nutsuwa take taku ƙwas-ƙwas hartakawo cikin falon mahaifiyartata, Mama dake zaune ta haɗe fuska tana ganin Zaleeha taji ranta ya sake, kallon Zaleehan tashigayi tana me godewa Allah daya bata wannan kyakkyawar yarinyar, lallai Zaleeha nada kyau irin nagaban kwatance,  cikin nutsuwa Zaleeha tadubi Maman nata tare da cewa "Mama ni zanje (Jonapwd) saina dawo". 

Tsuka Mama tayi tare da sake duban Zaleehan zata iya rantsuwa kyawun da Zaleeha tayi yau na dabanne amma abun haushin wai ba wajen wani hamshaƙin billionaire zataje ba wai gidan Nakasassu zata cike da ɓacin rai Mama tace.

 "Yanzu akan zuwa wajen waƴancan Makafi da guragunne zaki wani caɓa ado kamar wata mezuwa gasan kyau na duniya?". 

Baki Zaleeha taturo gaba tare da shagwaɓe fuska zatayi magana kenan Mama tace "Da halla ni ɓacemin da gani, ai dai indai wannan banzan aikin nakine kin kusa dainashi, don kuwa natabbata Abdussalam bazai bari kici gaba da wannan aikin ba don shi nasan awajensa aikinnan ƙasƙantacce ne".  

Murmushi kawai Zaleeha tayi tare da sakai ta fice daga cikin falon,  da kallo Maman nata ta bita aranta tana mejin wani sabon buri na ƙara ɗarsuwa acikin zuciyarta, don ayanzu tunaninta ya fara haurawa sama don kuwa har Abdussalam ɗinma tanaga Zaleeha ta zarce ajinsa.  


Ita kuwa Zaleeha tana fita, tayi kicibis da Ya Habu, 

cikin had'e fuska yace. 

"Kina dai sane haramunne in mace baliga zata fita ta zabga irin wanna turaren naki mai shegen k'amshi, na hanaki yafi a k'irga amman da yake kunnen k'ashi gareki kink'i ki bari ko?."

ya k'arishe mgnar cikin zaro mata ido.

cikin yin rau-rau da ido tace. 

"Ya Habu bazan sake ba."

kwaffa yayi kana ya wuce yayi cikin gida. 

Motarta ta shige, maigadi na buɗe mata gate ɗin gidan ta cilla motarta kan titi.  Cikin nutsuwa take murza steering motar tata yayinda daddaɗan ƙamshin turarenta ya cika gaba ɗaya motan.  


Hancin motartane ta kunno kai cikin gidan nakasassun inda ta tsaida motar a parking lot,  daga can wani babban falo kuwa nakasassune acike sun shirya tsab suna me jiran zuwanta.

  Cikin nutsuwa take takunta ƙwas-ƙwas yayinda takun takalminta ke bada wani sauti, saura bai wuce taku biyu ta samu kanta acikin babban falon ba taji wani irin faɗuwar gaba ya rusketa, take taji wani irin iska na shiga jikinta,  addu'a ɗauke abakinta ta sanya ƙafanta acikin falon,  mutanen dake zaune da waƴanda ke gani da waƴanda basa gani tuni sun shaida da zuwanta saboda jin sallamarta da sukayi, waƴanda basaji kuwa hancinsu ne yasanar musu da zuwanta tahanyar shaƙan daddaɗan ƙamshinta, cikin mutumtawa haɗi da rashin ƙyama Zaleeha ta gaishe da kowannensu, Ishaq ne yashigo cikin falon fuskarsa ɗauke da murmushi yace "Sannunki da zuwa Hajiya Zaleeha!".

Murmushine yafaɗaɗa akan fuskar Zaleeha cike da kulawa tace.

"Yauwa Malam Ishaq ya fama da jama'a?". 

Da. "Alhamdulillah ya amsa mata alokacin dayake ƙoƙarin zama akan kujera tare da gyara rik'on da yayiwa system d'inshi da wayarshi. Sosai ƙwazon Ishaq ke burgeta saboda yana aiwatar da komai nasa tamkar wanda yake gani.  


Yau da wani Gurgu zata gudanar da shirin nata don haka tuni ta tafara ƙoƙarin soma yi masa tambayoyi kamar yanda tsarin shirin nata yazo dashi, ko mintu 10 ba ayi da fara shirinba a hankali taji wani irin ni'imtaccen iska na ratsa ko ina dake jikinta yayinda bugun zuciyarta ya tsananta, 

 lumshe idanunta tayi sakamakon wani irin daddaɗan ƙamshi da taji ya ratsa cikin hancinta ya kuma cakuɗa da numfashinta, wani irin mimmiƙewa taji tsikar jikinta nayi, wani irin sanyi me daɗine taji yana kusanto ta tamkar wanda ake hurosa, hakan yasanya akasalance ta kai dubanta ga inda takejin kamar tanan sanyin ke fitowa, dai-dai lokacin shikuma ya shigo cikin wajen, zaune yake akan kekensa fuskarsa na fitar da annuri haɗi da ƙyallin kyau sajenshi yayiwa fuskar k'awanya mai jan hankali. 

Wani irin duka da harbawa zuciyar Zaleeha tayi, yayinda ta kafesa da idanunta masu rikita maza,  cikin nutsuwa yake sarrafa kekennasa wanda kuɗinta kaɗai ya isa yasai wani gida,  sam ya kasa ɗauke kyawawan idanunsa daga kan kyakkyawar fuskar da yajima yana bege dason gani,  wani irin yawu Zaleeha ta haɗiye wanda ya tsaya mata amaƙoshi, zata iya rantsewa bayan mutumin daya taimaketa bata taɓa ganin wani kyakkyawa aduniya ba bayan wannan mutumin dake zaune akan kekensa in dai ido da idone, cikin tsananin dauriya da kama ajinta bawai don ta ƙoshi da kallonsa ba ta kawar da idanunta gefe,  ƙarasowa cikin babban falon yayi tare da tsayawa adai dai inda Ishaq ke zaune, 

A fakaice ta D'angelo kalle fararen yatsun hannunshi da yaketa musabaha da mutanen nasu da suka kewayeshi tamkar sarki a fadarsa, 

ƙamshinsa kaɗai yasanya Ishaq ganesa, nan ya ɗauki wayarsa ya rubuta masa saƙo kamar haka.

 "Gafa Zaleeha nan tana gudanar da shirinta wani sati dakai za ayi".

Murmushi kawai Saifuddeen yayi tare da yiwa abokin nasa rubutu inda yace.

 "Allah ya kaimu," 

kana shiko Ishaq ya gyara zama tare da cewa. 

"Zaleeha ga aboki na kurman da na tab'a gaya miki naje Indian dubashi da jiki."

ba tare da ta kalleshi ba tace. 

"Ayyah."

Shiru yayi tare da kafeta da idanunsa kowani motsi da zatayi tare da bugun zuciyarsa yake tafiya amman da yake ya iya sarrafa kanshi babu mai ganewa sai ita da takejin kwayar kekyawan idanunshi na yawa a surar jikinta.  

Hakan yasa gaba ɗaya nutsuwarta ce tayi ƙaura daga jikinta, cikin rashin kuzarin dayazo ya lulluɓeta haka take gudanar da shirin, ɗan ɗago da mayan idanunta tayi  da niyar satan kallonshi karab idanunsu suka haɗe dana juna, da sauri tayi ƙasa da kanta, sakamakon wani irin shock da taji acikin jikinta, gaba d'aya taji wani abu na dark'efe kwayan idanunta, 

 bayan kamar minti 7 tasake ɗago da kanta don ta dubesa still idanunsu ne ya sake sarƙewa acikin najuna, sake yin ƙasa da kanta tayi aranta tana cewa.

 "Na shiga uku waye wannan kuma ne wai da yazo ya hanani sukuni, irin wannan kallo saikace maye hegen gurgu mai jajayen kunnuwa, dama ai ance gurgu yafi mai k'afa iya shege!". 

  bayan kamar 8 minutes a hankali tasake ɗago kanta, har yanzu dai kallonta yake baya ko ƙiftawa sai dai ya rage girman idanun nashi, ɗan jim tayi tare da yin mgnar zuci. 

"OK tsaurin ido ko tam zanyi mgninka yanzu".

kana itama ta tattaro tsaurin idonta da jarumta ta tsaida kwayar idanunta cikin nashi kwayar idanun, 

dib-dib taji zuciyarta na bugawa da k'arfi-k'arfi kuma da sauri, 

wani irin kwarjini da haibar fuskarsa da surarshi suka cika mata idani cikin one second ta janye idanunta cikin idanunshi da sauri ta maidasu akan surar kansa zuwa gefen sajenshi, ganin bai ɗauke nasa idanun daga cikin nata ba yasanya ta sakar masa harara tare da murguɗa masa baki, wani irin dariyane ya kama Saifuddeen don sosai hakan da tayi ya ƙarawa fuskarta kyau, lumshe idanunsa yayi yana mejin wani abu ya dark'afe ƙahon zuciyarsa.  

Adaddafe haka Zaleeha tagama gabatar da shirinta inda gaba d'aya kallon da Saifuddeen ke mata ya dagula mata lissafi, ita sam batason yawan kallo musamman ma shida ya kafeta da ido kamar zai cinyeta kuma idanun nashi wani haiba suke dashi na musammam.

a hankali taja gajeren tsaki tare, kallonshi a fakaice kana tace. 

"Maye kaci Kanka!."

ido ya lumshe a hankali dan ya gane me ta fad'i mishi, 

ita kuwa hararanshi ta kumayi kana taci gaba da aikinta.

Shi kuwa Saifuddeen cikin lumshe ido da shak'ar sassanyar iskar AC mai cike da k'amshi a ranshi yace. 

"Uhummmm bazan ci kaina ba in sha Allah ke d'in dai zan c...!





Duk fa masu bin labarin nan kunsan sashi sashi muke binshi, to da ganin yanzu kun san mun shigo wani sashi na musamman kuma. Wasan yanzu zai fara. 

Dan Allah da darajar iyayenmu da girman Al'arshi Kada ki fitarmin da littafi na, in kin fitarba ba sai nace Allah ya isaba ko inyi zagi da tashanci ba damn tijar maguzawa ba, No da Allah isasshene kuma shi yana sane daku in ni bana sane daku, kuma shine zai mana hisabi. Dan haka ni bazan zageku ba bare in zagi iyayenku, dan nasan darajar nawa iyayen ko k'abilata bana so a zaga bare iyayena shiyasa bazan zagi iyayen wasuba🤗🤗🤗


                        BY

       


       *GARKUWAR FULANI*

8/18/20, 7:56 PM - Ummi Tandama: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


         *NAKASA BA KASAWA BACE*



                            *Page 26*



                               *NA*


              *AISHA ALIYU GARKUWA*


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇



Lumshe ido yayi tare da yin magana a cikin zuciyarshi.

"Uhmmm bazanci kaina ba insha Allah keɗin dai zan ci!".

Sake ɗago idanunsa yayi ya watsa mata su, ita kuwa Zaleeha daketa  ƙoƙarin tattara kayan aikinta ta turo ɗan ƙaramin bakinta gaba, duk da cewa ba kallonsa takeyi ba amma tabbas tanajin idanunsa na yawo ajikinta,  tana gama haɗa kayan aikin nata taɗan ɗago da kanta,aikuwa idanunsu ne ya sake sarƙefe acikin na juna, 

 "Anya wannan ba maye bane!". 

ta kuma faɗa cikin ƙasa-ƙasa da murya tana me wurga masa harara da kyawawan idanunta. 

Lumshe idanunsa yayi tare da dafe saitin zuciyarsa dake beating, tabbas yau yasamu nutsuwa irin wacce yajima bai samu ba, bakomai ke tafiya da hankalinsa ba face yanda take kaɗa idanunta wajen hararansa,  harshe yasanya ya ɗan lashi red lips ɗinsa, yanaji ajikinsa inama da yana da damar da zai kusan tota garesa, tabbas daya jawota jikinsa yayiwa wannan bakin tsiwannanta shan tom-tom.

  hand bag ɗinta ta rayata abisa kafaɗanta tare dakai dubanta ga jama'an dake gabanta, sallama tayi musu akan cewa zata wuce, cikin takunta dake matuƙar ɗaukar hankalin maza ta tako harzuwa inda Ishaq yake,  ƙarasowanta garesu yayi dai-dai da kusan ɗaukewar numfashinsa sakamakon daddaɗan ƙamshinta daya samu cakuɗa da numfashinsa, cikin wani irin kasala ya lumshe beautyful eyes ɗinsa. 

Saura bai wuce taku huɗu ba ta ƙaraso garesu ta tsaya cak tare dayin ƙasa da kanta, sam batajin zata iya kallon cikin idanun Saifuddeen dan wata azababbiyar fitina take hangowa cikin kwayar idanshi mai kama da maganad'isu haiba da kwarjinshi yana sa zuciyarta cikin wani yanayi, hakanan ƙarasowarta garesu ya haifar mata da faɗuwar gaba yayinda ƙirjinta ke duka da sauri-sauri. 

Cikin tausasa murya ta dubi Ishaq daketa faman murmushi kamar yana ganinta,

  "Malam Ishaq nizan wuce sai kuma idan munsake haɗuwa wani sati Idan Allah yakaimu!"

Murmushin dake kan fuskar Ishaq ne ya faɗaɗa, inda ya sanya hannunsa ya dafa kafaɗan Saifuddeen cike da ƙaunar Saifuddeen ɗin yace "To  bari nai miki rakiya  Malama Zaleeha, amma fa wani sati kishirya don kuwa baƙonki na musammanne, abokina Saifuddeen kenan!". 

Wani irin ƙululun baƙin ciki ne ya daki zuciyar Zaleeha cike da haushinsa ta ɗago fararen idanunta ta watsa masa harara, inda still ta kamasa yana kallonta,  "Nasani ae dama kallona kake maye kawai!".

 tafaɗa cikin ƙasan maƙoshi tana me mulan-mulan da bakinta,  

Murmushin daya ƙara bayyana zallan kyau da kwarjininsa yayi, sarai ya fahimci me take faɗa cikin ransa yace.

 "Zakisan kuwa ni maye ne na gaske duk randa kika shigo hannuna!". 

Sake gayara zaman jakarta akan kafaɗarta tayi inda ta juya cikin takunta me ɗauke da nutsuwa ta nufi hanayar da zai fitar da ita daga cikin falon, tare da Ishaq suka jera suna tafiya, suna ɗan hira sam idan kaga Ishaq bazakayi tunanin makaho bane.

 Da wani irin kallon So, haɗi da shauƙi tare da zallan k'auna Saifuddeen ya bita, komai nata abun burgewane, idanunsa ne suka sauƙa akan tsararren hips ɗinta da cikin salo suke juyawa, saurin lumshe idanunsa yayi tare da cije laɓɓansa, don kuwa wani irin harbawa yaji jikinshi da zuciyarshi sa nayi,  wata irin sassanyar ajiyar zuciya ya sauƙe, tare da buɗe idanunsa, dai-dai lokacin ita da Ishaq suka fice daga cikin falon,   murmushi yayi tare da ɗan sanya hannu ya shafi lafiyayyen sajen dake kwance akan fuskarsa.


Sannu ahankali gaba ɗaya mutanen dake cikin falon suka soma watsewa kowa ya kama gabansa. 


Har bakin motarta Ishaq ya rakata, inda sosai taji daɗin rakiyar tasa, cikin muryarta dake nuna jin daɗin rakiyar tasa tace.

"Godiya dubu Malam Ishaq!".


Murmushi Ishaq yayi tare da cewa.

"To Malama Zaleeha kigaida mutanen gida!"


Da "To" ta amsa masa, kana ya juya yakoma inda yabar Abokinsa Saifuddeen.


Murfin motar  ta buɗe ta shiga  tare da murza mata key,  dai-dai-ta tsayuwar motar tata tayi, cikin tuƙinta me ɗauke da nutsuwa ta fice daga cikin harabar ofishin ƙungiyar ta (Jonapwd), cikin salo take murza kan steering motar tata,  tunaninsa ne ya faɗo cikin ranta, hakan yasa ta saki wata ƴar siririn tsuka tare dayin ƙwafa, cike da haushin irin kallon daya dinga yi mata ta murguɗa baki tare da yin guna-guni acikin ranta inda tace "Mutum gurgu sannan kurma amma sai shegen sa'ido, no wonder akace gurgu kafi me ƙafa iya shege!".

 tafaɗi haka adai-dai lokacin da take shan wata kwana. 


Ishaq na dawowa cikin falon, ya iske Saifuddeen wanda ke zaune cikin matsanancin shauƙinta.

Hannayen Saifuddeen ɗin Ishaq ya riƙo cikin nutsuwa yace.


"Saifuddeen kaga Zaleeha ko, tana da kirki sosai sannan akwai nutsuwa atattare da ita, sam kyawunta baisakata yin ɗagawa ba".

Murmushi Saifuddeen yayi tare da zaro wayarsa daga cikin aljihu, inda ya rubutawa Ishaq saƙo kamar haka.


"Nayaba da hankalinta matuƙa ishaq, saboda hakane ma  na zaɓeta a matsayi. Matar aurena uwar ƴaƴana in Allah ya yarda,

ba dama nace maka nasamu matar aure!".


Waro idanun Ishaq yayi bayan yagama sauraran wayarsa inda ta karanta masa gaba ɗaya abun da Saifuddeen ɗin ya rubuta, cikin tsananin mamaki yace.

"Wai kana nufin Zaleeha?"

Still murmushi Saifuddeen yayi inda ya rubata cewa.


"Inasonta Ishaq, haƙiƙa ina tsananin sonta, harma inajin kowani bugu na zuciyata tare da zallan soyayyarta yake tafiya, Inaso na Aureta! Ishaq tun randa na fara ganinta sonta ya zame min abokin rayuwa,

shiyasa kullum mukayi mgna da kai sai na tambayeka ita da lfyarta".


Koda Ishaq yagama sauraran batun wani irin tsananin farin ciki ne ya lulluɓesa, haƙiƙa baya gani da ido amma yana gani da zuciya, kuma tuni zuciyarsa ta gama karanta masa kyawawan halayya da kuma nagarta irin na Zaleeha, tabbas zaisowa abokinsa Saifuddeen samun mace irin Zaleeha amatsayin mata, cikin jin daɗi tare da son ƙarfafawa Saifuddeen ɗin guiwa Ishaq yace.


"Naji daɗi Saifuddeen, kuma zanfi kowa so da muradin kasantuwar aurenku da Zaleeha, saidai kuma baza muyi gaban kanmu ba, zaifi kyau mu fara sanar da manya don baza muje haka kawai ba sai da ƙarfin mu, ma'ana sai munsamu amincewar manyanta, tabbas ayanda nasan Zaleeha nasan tanada nagarta, kuma zata soka". 

Ya k'arishe mgnar cikin karsashi domin su basu sawa ransu cewa nakasarsu zata zame musu kasawa ba, bare ta hanasu neman duk wani abinda mai cikar halitta zai nema kuma ishaq bai san dakon son dake ran Zaleeha ba.


Wani irin ƙwarin guiwa kalaman Ishaq suka ƙarawa Saifuddeen, nan suka cigaba da tattauna hira atsakaninsu ta hanyar gudanar da text message.   


Zaleeha kuwa daga Jomapwd kai tsaye gidan redionsu na vission FM. ta nufa,  tundaga fitowarta acikin motarta gaba ɗaya kallo ya dawo kanta, haƙiƙa  Zaleeha cikakkiyar mace ce dake iya ɗaukar hankalin kowani ɗa na miji, cikin takunta me ɗauke da nutsuwa ta ƙarasa babban ɗakin da suke tantance shirye shiryensu kafun su turashi izuwa ɗakin watsa shirye-shirye,  saida aka tantance shirin nata na wannan rana kafun aka watsashi tayanda kowa zaijisa raɗau batare da wata matsala ba.

  Zama tayi akan wata kujera wanda keda ƙafafun taya, ahankali take jujjuyawa yayinda ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, wayarta ta ciro tare da saƙala earpiece acikin kunnenta, cool music na Edsheeran ne ke tashi acikin earpiece ɗin nata, ahankali take jujjuya kanta alaman waƙan na taɓa zuciyarta sosai, luf tayi ajikin kujeran tare da kwantar da bayanta kana ta lumshe kyawawan idanunta, tunaninsa ne yayi mata tsaye acikin ranta, wani irin ƙauna haɗi da begensa ne suka cika zuciyarta,  bazata taɓa cire rai da rabo ba akansa saba, haƙiƙa ita mai raunice hakanne ma yasanya soyayyarsa ke wahalar da zuciyarta, inama da ace wani zaiji abun da takeji, inama da ace ƴan uwanta zasu fuskanci mai takeji tabbas tasan da kowa sai ya jinjinawa girman soyayyar da takeyi masa, tanajin sonsa har cikin ƙashi da bargo, haka kuma tanajin soyayyarsa tamkar jinine dake gudana ajikinta ako yaushe, hawayene suka cika idanunta sakamakon rauni irin nata. 

Ajiyar zuciya Raveel yasauƙe, wanda tun ɗazun yake tsaye yana kallonta, ayayinda tayi nisa cikin begen masoyinta, shikuma alokacin yakejin kamar zuciyarsa zata tarwatse saboda ƙaunarta, son Zaleeha yake da duka zuciyarsa,  hawayene suka cika idanunsa, hango manager dake ƙoƙarin tahowa garesu da yayi yasanyashi saurin shanye hawayensa, tare da komawa cikin wani ɗan balcony ya tsaya don sam bayason manager ɗin ya gansa, saboda rauninsa ya bayyana sosai ta yanda bazai iya ɓoyewa ba.

Yana sako ƙafarsa cikin babban falon wanda yakasance kamar ɗakin hutu ga ma'aikata gidan radio'n vission FM ɗin wani irin walagigin ƙaunarta ne ya daki ƙahon zuciyarsa, yayinda ya lumshe idanunsa tare da shaƙan daddaɗan ƙamshin ta da ya cika ɗakin,  ahankali ya buɗe idanunsa tare da sauƙesu akanta,  sam batasan da zuwansa ba kasancewar haryanzu idanunta arufe suke, sannan zuciya da ƙwaƙwalwarta sunyi nisa wajen tunanin abincin ruhinta, ahankali yatako ya ƙaraso  gareta, cikin kulawa yaƙira sunanta,  sam bata jisaba don tayi nisa atunanin da takeyi, kujera yajawo tare da zama yana facing ɗinta,  hannunsa yakai ya zare earpice ɗin dake kunnenta, da sauri ta ware idanunta da sukayi ja ta sauƙesu akansa, cikin mamakin ganinsa da kuma yanda ya cire mata earpiece ɗin kunnenta taɗa kallesa kana tayi ƙasa da idanunta.

Murmushi Manager yayi tare da cewa.

 "Barkanki da hutawa gimbiyar mata". 


Cikin takura ta amsa masa da yauwa acan ƙasan maƙoshinta, hakanan ganinsa yasanya taji ba daɗi acikin ranta, itafa yanzu hakanan ta tsani duk wani mahluƙin da zaizo mata da zancen soyayya, ayanzu mutum ɗaya kawai take muradi kuma tana nan tana jira ya taho mata da soyayyarsa, 


"Zaleeha!" Manager yaƙira sunanta murya asanyaye.

Bata amsa masa ba bata kuma ɗago kanta ta kallesa ba, sam ayanzu batason damuwa, hutu da nutsuwa kawai take da buƙata. 

Ganin cewa bata amsa shibane yasanyashi cewa "Kiyi haƙuri Zaleeha, bansan da yaushene kuma tayaya bane nakamu da sonki, amma tabbas inasonki sosai, ina fatan zamo warki mata agareni Zaleeha, nasan kina ganin girma ƙima da kuma mutumci na, amma banda yanda  zanyi akan soyayyarki Zaleeha, inajin kaina tamkar ƙaramin yaro akan soyayyarki,  bazan gaji da fallasa miki sirrin zuciyata ba,  don ina fatan samun nasara agareki!". 

Sai alokacin Zaleeha ta ɗago idanunta ta kalleshi,  inama da ace shine zaune agabanta haka yake furta mata daɗaɗan kalaman soyayya? inama da ace zata kasance da masoyinta kasantuwa tahar abada, ajiyar zuciya ta sauƙe, tabbas tana ganin girman Manager acikin idanunta, saboda hakane ma batajin zata iya tafka masa yayyafin rashin mutumci, don ko bakomai shiɗin babban mutum ne,  kanta ta kawar gefe cikin dauriya tace. "Tabbas kamar yanda kafaɗa ina ganin girma da ƙimarka acikin idanuna, saidai dan Allah naroƙeka Manager daka janye soyayyar da kakemin, inada wanda nakeso araina, banajin dagashi zanso wani aduniyar nan, dan Allah karabu dani naji da damuwar dake raina!". taƙare maganar tana me haɗe hannayenta biyu waje guda alaman roƙo. 


Ajiyar zuciya manager ya sauƙe tare da ɗan rumtse idanunsa, idan yaji tana ambatan cewa tana da wanda takeso, ji yake tamkar kifiya take caka masa aƙahon zuciyarsa, cikin raunin daya bayyana akan fuskarsa yace. "Kamar yanda kike jinsa acikin zuciyarki haka nima nake jinki acikin tawa zuciyar, bansan taya zan fasalta miki irin tarin ƙaunar danakeyi miki ba Zaliha, dan Allah ki tausayawa zuciyar da ta jima tana dakon soyayyarki!" 


Idanunta ta rumtse tare da cije laɓɓanta tana mejin kanta na wani irin sarawa tamkar zai fashe, sam bazata iya jurewa ba hakan yasa ta ɗauki hand bag ɗinta, tare da wayarta, ko kallon inda Manager yake bata sakeyi ba ta nufi hanyar fita daga cikin falo, da sauri Raveel dake tsaye yanajin duk abun da suke faɗa ya koma jikin gini ya tsaya, don sam bayaso sugansa harsusan yaji abun da ya wakana atsakaninsu,  "Zaleeha! "Zaleeha!!"  haka manager keta ƙiran sunanta, ko tsayawa batayi ba balle yasa ran zata juyo ta kallesa, hannayensa ya sanya ya dafe kansa, yayinda soyayyarta ke ƙara ninkuwa acikin zuciyarsa, itakuwa Zaleeha tuni hawaye sun cika idanunta,  kaitsaye wajen motarta ta nufa, tanakai hannunta jikin murfin motar muryar Raveel ya daki dodon kunnenta. 

Inda yaƙira sunanta, ƙoƙarin shanye hawayen dake cikin idanunta tayi tare da tsayawa cak, saidai bata juyo ba,   ajiyar zuciya Raveel dake bayanta ya sauƙe tare da cewa.

 "Dan Allah kijuyo ki fuskanceni!"


"Kafaɗi abun da kakeson faɗa danni sauri nakeyi!" Zaleeha ta faɗa cikin ƙosawa, don gaba ɗaya komai bayayi mata daɗi. 


"Maganace akan SO Zaleeha, dan Allah Zaleeha ki bani dama, ashirye nake dana zama GARKUWA agareki, zan baki ingantaccen farin ciki me ɗorewa, sannan zan....."


"Ya isa haka Raveel, wai me kuka ɗaukenine kowa so! so!! So!!! maikuka maidani ne?  shin wai ni kaɗaice mace aduniya? Dan Allah Raveel kafita arayuwata, ka tsaya amatsayinka na abokin aikina kadaina wannan ƙoƙarin na tura kanka inda baka da muhalli awajen!!". Zaleeha ta katseshi tare da faɗin maganan aɗan tsawace. 

Bata jirayi me Raveel ɗin zai ƙara faɗi ba ta shige cikin motarta, azafafe ta murzawa motar key yayinda ta jata da wani irin speed,  ko gama wangale mata gate ɗin bata bari maigadi yayi ba ta danna hancin motar tata waje ranta amatuƙar ɓace. 


Raveel kuwa idanunsa da ke cike da hawaye ya rumtse tare da juyawa jiki asaluɓe shima yanufi wajen da motarsa take, don yanda yakejin ciwo azuciyarsa bayajin zai iya komawa cikin office ɗinnasu. 


Ahankali take rage gudun da takeyi, kantane ke mata wani irin ciwo, gaba ɗaya damuwa yayi mata yawa,   ɗan lumshe idanunta tayi tare da dafe saitin zuciyarta dakeyi mata zafi,  kaitsaye Havilla tanufa, don ayanda takejin zuciyarta dole tana da buƙatar abun da zai sanyaya mata rai,   tana shiga cikin wajen ta lumshe idanunta sakamakon wani irin daddaɗan sanyi daya ratsa jikinta,  wani irin ni'imtaccen ƙamshin korayen shuke shuke dake wajenne ke ratsa cikin hancinta, sosai yanayin wajen yayi mata,  cikin takunta mai ɗuke da nutsuwa taƙarasa can ciki,  ƴan mata da samari ne suka kusa cika wajen, waƴanda kallo ɗaya zakayi musu batare da sai anfaɗa maka ba zaka gane cewa masoya ne, don kowanne dake cikin wajen fuskarsa ɗauke take da shauƙi,  dayawan mazan dake wajen kallonsu ne ya dawo gareta, musamman wani kekyawan gaye dake zaune shi kaɗai akan table,   cikin ajinta da sanin darajar kanta ta ƙarasa ga ma'aikatan dake cikin Havilla'n,  nan ta basu order'n irin haɗin ice cream ɗin da takeso ayi mata,  mintuna kaɗan wani saurayi ya kawo mata ice cream ɗin,zip ɗin hand bag ɗinta ta zuge inda ta ciro kuɗi ta bashi kana ta karɓi ice cream ɗin, cikin takunta mai ɗauke da nutsuwa ta juya ta fice, da sauri wannan saurayin ya rufa mata baya, don bayajin zai iya jure kasa furta mata soyayyarta da ta kamasa alokaci guda.   


Harta kusa kai bakin motarta da sauri yasha gabanta,  cikin yanayi naɗan mamaki taja baya, tana me ƙare masa kallo,  murmushine ɗauke akan fuskar saurayin me suna Saleem, cikin da-ida-ita nutsuwarsa yace.

 "Amincin Allah ya tabbata agareki yake wannan ma'abocian kyakkyawar halitta" 

Idanunta taɗan juya tare da kafesa da ido. 

Ɗan lumshe idanunsa yayi ganin yanda kwawawan idanunta ke yawo ajikinsa, cikin nutsuwa yace. 

"Saleem Sa'ad Turaki, 

fatan banyi laifiba dana tsaida ki, naga kamar sauri kike".

Baki ta taɓe tare da buɗe murfin motarta ta shige, ƙoƙarin rufe murfin motar take, Saleem yayi saurin riƙewa, cikin sanya fuskar tausayi yace.

 "Nasan dacewa shawo kan kyakkyawar mace sarauniyar mata kamarki abune mai matuƙar wahala, amma please ko phone number ɗin kine ki bani hakan zai taimakamin sosai" 


Hannunta tasanya taɗan dafe goshinta, cike da ƙosawa ta ɗago ta dubesa,  shiɗinma kallonta yake wani murmushin k'eta tayi tare da bashi number Raveel kana ta gaya mishi sunanta,

murfin motarta ta rufe tare da data motar tatafi tabarshi tsaye awajen,  murmushi ɗauke akan fuskarsa yabi motarta da kallo, harta ɓacewa ganinsa, cike da fatan sake ganinta anan gaba ya juya yakoma cikin havilla.  Itakuwa Zaleeha tana tuƙi tanashan ice cream ɗinta, hakan kuwa sosai ya haifar mata da nutsuwa. 


Ransa fari ƙal fuskarsa ɗauke da farin ciki yake sarrafa keken nasa har yakawo cikin falon, Ummi da Hayatuddeen ne zaune, carbi ne riƙe ahannun Ummi yayinda Hayatuddeen kuma ke zaune akan sofa, yana riƙe da plate ɗin dambun nama  ahannunsa,  ahankali ya turo keken nasa zuwa gaban Ummi dake zaune akan kujera, wanda ganinsa da tayi yasanyata sakin murmushi, ƙarasowa gab da ita yayi tare da ɗaura kansa akan kafaɗanta, cikin tsananin ƙaunar da takeyi masa tasanya hannu ta shafa lallausan gashin kansa tare da cewa. 

  "Da'alama wannan fitar taka al'khairi zata haifar mana don naga kafita cikin farin ciki, ka kuma dawo cikin farin ciki". Murmushine ya faɗaɗa akan fuskarsa tare da sake gyara zaman kansa dake kafaɗanta, shikaɗai yasan irin farin cikin da yake ciki ayau ɗin.

   Hayatuddeen dake ta faman cin dambunsa yana jijjiga kai alaman daɗin dambun na ratsashi, dubansa ya kai ga Hammannsa cikin santin dambun nasa yace "Hamma nine fa auta kowa ya sani".

Hararansa Saifuddeen yayi cikin body language yayi masa alama da cewa.

 "Idan kaine auta saime, shikenan sai kada Ummina tanuna min ƙauna?" 

Dariya Hayatuddeen yayi tare da cewa.

 "Ai dai  ƙaunar dake tsakanina da Ummi na ta musammance, naɗan baka aronta ne naƴan wasu kwanaki" 

Murmushi Ummi dake jinsu tayi, shiɗin ma Saifuddeen murmushi kawai yayi don ya fuskanci cewa dambun naman da Hayatuddeen ɗin ke cine yasasa santi.  Dubansa Ummi tayi cike da kulawa tace.

 "Akawoma abinci ne?".

Cikin body language ɗinsa yayi mata alama da bayanzu ba, ahankali ya tura kekensa inda ya nufi ɗakinsa don so yake yayi wanka kana yaɗan huta,  


Shida kansa ya haɗawa kansa ruwan wanka acikin bathtube, inda yacika turaren wanka me daɗin ƙamshi aciki,  kwanciya yayi luf acikin bathtube ɗin tare da lumshe idanunsa, ba'a iya jikinsa kaɗai yakejin sanyin ruwan ba har acikin zuciyarsa,  wani irin ƙawataccen murmushine ya bayyana akan fuskarsa sakamakon tunowa da irin yanda take murguɗa masa baki dayayi,  tausasan lips ɗinsa yaɗan ciza tare da sanya hannunsa ya riƙe dai- dai saitin heart ɗinsa, wani irin tarin soyayyarta ne yasake ɗarsuwa acikin ransa,  sake gyara kwanciyarsa acikin bathtube ɗin yayi tare da sakin wani sabon murmushi, sannu ahankali yakejin sabon so da ƙaunarta na huda gaba ɗaya jijiyoyin dake jikinsa, aƙalla ya ɗauki kusan sama da 30 minute yana tunaninta yayinda wata irin ƙaƙƙarfan begenta ke neman zautar dashi, adaddafe haka yayi wanka,  koda yafito daga cikin toilet ɗin wata brown ɗin jallabiya me kyau yasanya ajikinsa inda ya feshe jikinsa da daddaɗan turarensa mai sanya nutsuwa,

 kwanciya yayi luf akan gadonsa tare da jawo laptop ɗinsa, ya kunna, kyakkyawan hoton fuskarsa ne ya bayyana akan screen na laptop ɗin,  cikin nutsuwa yake danna laptop ɗin inda ya kasa aiwatar da komai gaba ɗaya tunanin kyakkyawar fuskarta da zazzaƙan muryarta ya hana masa sukuni.

ya dade haka daga bisani ya turawa Ahmad text.

"Na samu matar aurefa yaro ka shirya shan biki."

Ahmad dake kwance bisa gado, yayi.da Raliya ke baccin gajiya a kan k'irjinshi.

dariya yayi tare rubuta mishi

"Eye-eye kace ka kusa shiga dausayin jin dad'in duniya yaro."

Tsaki ya tura mishi tare tura mishi nifa surkinka ne.

daga bisa ni dai yayiwa Ahmad d'an bayani, 

sosai Ahmad yaji dad'i. 


Washegari,  yau tunsafe yatashi da wani irin ƙwarin guiwa nason mallakarta, wayarsa ya ɗauka ya turawa Ishaq text message inda yace shirya zuwa ƙarfe  d'aya na gobe zai rakasa Dukku,   koda Ishaq yaga saƙon abokin nasa murmushi kawai yayi don yasan kwanan zancen har acikin ransa kuma yaji daɗin hakan. 


Zaune suke su dukansu akan dinning table suna break fast,  surutun Hayatuddeen da Raliya ne ke tashi inda suke ta musu, Ummi dai jinsu kawai take yayinda Saifuddeen ya zaro wayarsa dake cikin aljihunsa, saƙon tafiyarsa Dukku ya rubuta kana ya miƙawa Ummi, amsan wayan Ummi tayi tare da karanta saƙon, ajiyar zuciya ta sauƙe tare da duban Saifuddeen ɗin da kyau, tabbas taji daɗin cewa da yayi zaije dukku'n saboda hakanma wani ƙarin karsashi ne dake nuna samun lafiyarsa, saidai kuma tayi mamaki don yau kwata kwata-kwata kwana biyar ne da dawowarsa Nigeria, sanin da tayi cewa koma mene zaije yi a Dukku'n tana da yaƙinin cewa al'khairi ne hakan yasa, tayi masa fatan zuwa lafiya da kuma dawowa lafiya, Hayatuddeen ne ya dubi hamman nasa jin Ummi nayi masa fatan alkhairi yace "Hamma tafiya zakayine?"


Kai Saifuddeen ya jinjina masa alamar eh tare dayi masa alaman.

 "Ko zaka rakani?" 

Baki Hayatuddeen ya washe tare da kaɗa kansa cikin sauri yace.

 "Ƙafata ƙafarka ae Hammana!" 


Murmushi Ummi tayi tare da cewa.

 "To ɗan sarkin son yawo tunda dai kanason yawo ae sai kabisa Dukku zashi". 

Take Hayatuddeen ya kwaɓe fuska tare da girgiza kansa cikin halinsa na shagwaɓa yace.

 "Dukku kuma? chab wallahi na haƙura dama wasa nake ba binsa zanyi ba". 

Gaba ɗayansu suka sanya dariya don dama sunsan rashin sanin inda Saifuddeen ɗin yace zaije shiyasa cikin karaɗi yace zai bisa, suna kammala cin abincin, Saifuddeen ya wuce ɗakinsa, wanka ya ƙarayi inda ya shirya kansa cikin wata tsadaddiyar shadda Milk colour ɗinkin half jumper wanda taji coffee colour'n aiki a wuyanta,  sosai shaddan ta sake fidda sihirtaccen kyaunsa,  wata haɗaɗɗiyar hulan zanna bukar ya kafa akansa wanda gaba ɗayanta kalar coffee gareta saidai tana da ratsin milk colour ajikinta,  hatta takalman dake ƙafansa kalan coffee garesu, inda farar fatarsa tafito tayi ɗas acikinsu, tsadadden agogo ya ɗaura ahannunsa inda ya feshe gaba ɗaya jikinsa da turare, masha Allah Saifuddeen baƙaramin kyau yayi ba, sai ayanzune ma nake lura da cewa ba kayanne sukeyi masa kyau ba shine keyiwa kayan kyau, don kuwa kowani irin kaya yasaka sai yayi musu kyau, haƙiƙa Allah mabuwayine ayayin daya tauye Saifuddeen da tawaya irin ta rashin jin magana da takawa da k'afaffunshi sai ya basa wani irin ɗanɗareren kyau haɗi da kwarjini yakuma sa ya zamto abunso azuƙatan mafi yawancin mutane, haƙiƙa kyawun Saifuddeen madubi ne wanda ko wacce cikakkiyar ƴa mace zataso fuskanta don ganin kanta acikin sa.


falon ya fito cikin kamala ya zauna gefen Ummi yayinda Raliya da Hayatuddeen ke gefe sunata hirar zasuyi kewar Raihana da itama gobe zata koma KD da mijinta.

nan suka d'anci gaba da hira, cikin hirar Ummi tace. 

Raliya tare da cewa. 

"Rana tayifa tashi ki shiga kitchen ki hada mana lunch kinga yau Hammanku wunin gida zaiyi yace yau lokacinsa namu ne."

dato ta amsa kwana ta mik'e ta shiga kitchen. 

Raihana ce ta mik'e da sauri taje bakin k'ofar falon nasu jin ana d'an bubbugawa.

cikin fara'arta da sakin fuska ta kalli Mom d'in Amina tare da cewa. 

"Sannu da zuwa shigo ciki."

cikin mmki ta kalli Amina dake bayan Mom da sauri ta k'ara matsawa ta basu hanya tare da cewa. 

"La kamar na ganeki, ku ise."

murmushi sukayi baki d'aya kana suka kutsa kai cikin falon bakinsu d'auke da sallama.

Hayatuddeen ne ya mik'e da sauri tare d'an yin tsalle yayi gaban Amina tare da cewa. 

"La likita bokan turai? Yaushe kika zo gombe?  waya kwatanta miki gidanmu?."

Ummi ce ta mik'e cikin kamala take cewa Mom. 

"Lale marhabin maraba lale ga wurin zama."

cikin sakin fuska Mom tace. 

"Yauwa."

ita kuwa Ummi dak'uwa tayiwa Hayatuddeen tare da cewa. 

"Kai auta me haka zaka tsareta da tambayoyi?."

kanshi ya fasha tare da nuna mata kujera kana yace. 

"Kai naji dad'in zuwanki, zauna mana."

murmushi tayi tare d'an hararanshi k'asa-k'asa kana tace. 

"Ba nace maka munyi fad'aba?."

dariya yayi sosai kana yace. 

"Karki damu zan rarrasheki da dambun naman da Ummina tayimin."

Ummi kuwa cikin rashin saninsu ta gaisa da Mom. 

kana ta juyo ta kalli Amina dake durk'ushe a k'asan carpet kusa da k'afafun Ummi tare da cewa. 

"Ummi ina wuni."

cikin sakin fuska Ummi tace. 

"Lafiya lau Alhamdulillahi."

kanta ta d'an d'ago ta kalli Saifuddeen dake can gefe kan weelchair d'inshi da system nashi bisa cinyarshi yana sarrafa cikin gwarewa, a hankali tace.

"Ya jikin Hamma Saifuddeen?."

zuba mata ido Ummi tayi tare da cewa. 

"Alhamdulillahi jiki kam da sauk'i sosai."

a kunyace tace. 

"Allah ya k'ara sauk'i ya bashi lfy rabbi ya sa yanada rabon sake takawa da sawunshi."

cikin wani irin tsananin jin dad'in addu'arta ga Saifuddeeen Ummi da yaranta duka suka amsa da. "Amin Amin Ameeen ya rabbil izzati".

cikin nitsuwa Ummi ta kalli Mom daketa kallon Saifuddeeen kana tace. 

"Sai dai har yanzu ban ganeku ba?."

da sauri Hayatuddeen yace. 

"Ummi baki gane Amina ba itacefa wanna nurse d'in dake kula da Hamma a Abuja kafin mu tafi Indian."

cikin mmki Ummi tace. 

"Allah sarki Amina kai ngd ngd matuk'a Allah bar zumunci."

cikin tsananin jin dad'i Amina tace. 

"Amin."

Raihana ce tayi sauri cewa. 

"La wlh kuwa nima saida ka fad'a na tunata, yaudin tayi kyau da yawane shiyasa bamu ganeta ba."

dariya sukayi baki d'aya, 

yayinda Raliya kuwa take ta kawo musu ababen sha dana motsa baki.

ita kuwa Ummi da kanta ta kalli Saifuddeen lokacin da Amina ta kallonshi. 

tab'ashi tayi tare da nuna mishi Amina da mom sannan tace. 

"Nurse d'inka ta Abuja ne da mamanta ko?."

ta k'arishe mgnar da kallon Amina alamun tambaya, cikin nitsuwa ta gyad'a kanta alamun eh.

shi kuwa Saifuddeen cikin d'an sassauta had'e fuskarsa ya gaida Mom tare da mata godiya duk cikin body language. 

sosai Mom ke kallonshi, 

shi kuwa kauda kanshi yayi daga kallonsu sam yak'i yarda ya kalli Amina. 

shi kuwa Hayatuddeen sai jan Amina da hira yakeyi hakama Raihana. 

Ummi kuwa da Mom hirar ciwon Saifuddeen suke d'an tabawa. 

Raliya kuwa tuni ta koma kitchen. 

Mom ce ta kalli Amina tare da cewa. 

"Mu tafi ko Amina lokaci ya tafi."

cikin son bak'i Ummi tace. 

"A a ai kwa tsaya kuci abinci."

da sauri Mom ta girgiza kai tare da cewa.

"A a kai Alhamdulillahi ai a k'oshe muke, jiya muka shigo gombe bikin yar k'awata a nan unguwartaku, 

to shine fa Amina na zancen Saifuddeen sai aka samu wanda ta sanshi da gidan naku har ta kwatanta mana, 

shinefa fir Amina tace sai munzo, ashe ba nisama layi biyu tsakani."

cikin jin dad'i Ummi tace aiko na gode matuk'a wlh naji dad'i.

Amman dai kuyi salla kafin ku fita tunda an kira sallan azahar."

sam Mom bata soba amman dole Ummi tasata suka shiga bedroom ta nuna mata k'ofar bathroom kana ta shimfid'a mata sallaya. 

Hayatuddee  kuwa kitchen yabi Raliya tare da cewa Amina. 

"Bari inje in kawo miki abin dad'i."

murmushi tayi tare da kallon Raihana da ta nufi corridor d'in dasu Ummi suka shiga. 

ido ta juya kudu da arewa gabas da yamma, ganin ba kowa a falon daga ita sai Saifuddeen da yaketa saurin ya k'arisa aikinsa ya shiga side d'inshi. 

da sauri ta d'auki goran ruwan Faro ta garashi har zuwa gaban Saifuddeen d'in. Da sauri ya d'ago kanshi ya kalli ta inda yaga an turo goran, 

fuska ya kuma had'ewa ganin ta zuba mishi sosai ya haɗe girar sama data ƙasa. 

ita kuwa Amina, murmushi tayi tare da d'aga mishi gira kana tace. 

"Eye kayi kyau, k'asar Indian ta amsheka ji yadda kayi wani fresh da kai kamar ba kaiba."

baki ta tura ganin ya k'ara had'e fuska a hankali taci gaba da cewa. 

"Bafa zaginka nayiba kake wani had'emin kekyawar fuskarnan taka, 

ko dai baka son in kalli wannan kekyawan sajen nakane."

dib yayi dan baya son yayi abinda zata gane yana gane abinda take fad'an. 

ganin haka ita kuma ta lumshe ido kana ta bud'esu a kanshi a hankali tace. 

"Wai kai baka gane mai sonka ne? 

to in ma baka ganewa ni dai ina sonka, dan kana min kyau."

da sauri tasa tafin hannunta ta rufe ido dan ganin Raihana a tsaye a gefeta tanata dariya. 

dai-dai lokacin Hayatuddeen da Raliya suka fito kitchen,

wanda suma suke dariya dan sunji mgnarta ta k'arshe inda take cewa dan kana min kyau. 

wayyo ai ji tayi kamar ta nitse cikin k'asa ganin hakane Raliya ta jata suka tafi side d'inta inda acan tayi salla. 

shi kuwa Saifuddeen baibi ta kansuba ya wuce side d'inshi. 

Koda su Ummi sukayi salla suka fito ba yadda Ummi batayi akan suci abinci fir sukak'i, 

dole Ummi ta hak'uri kana sukayi musu rakiya har bakin motarsu inda dama direbansu na nan yana jiransu. 

saida suka tafi kafin su Ummi suka koma cikin gidan. 


Washe gari kuwa stab Saifuddeen ya shirya cikin shiga ta al'farma sai k'amshi yake zubawa cikin shirinshi na tafiya Dukku.

 Yana ƙoƙarin ɗaukar wayarsa dake aje kan gado, yaji anturo ƙofar ɗakin anshigo,  Ishaq ne yashigo bakinsa ɗauke da sallama yayinda shima yasha ado cikin yadin getzner me ruwan toka sosai shima yayi kyau.  

Tamkar wanda ke gani ya lumshe idanunsa tare da faɗin.

 "Kayi kyau sosai Saifuddeen!"

Murmushi Saifuddeen yayi yana me ƙoƙarin ɗaukar wayarsa don ya rubutawa Ishaq din saƙo, maganar Ishaq ta sake dakatar dashi inda yace.

 "Bama sai ka sha wahala wajen rubutu ba nasan me zaka tambaya, cewa zakayi dawani idon nasan kayi kyau, bayan kuma nasha faɗa maka cewa masu ido abu ƙalilan zasu nunamin donni ma inaganin komai da zuciyata, zuciyata itace idanuna!" 

Murmushi Saifuddeen yasakeyi aransa yana mejin ƙarin ƙaunar abokin nasa, cikin kulawa ya turawa Ishaq saƙo awayarsa kamar haka inda yace.

 "Nikam nagaji da wannan surutun naka ni yanzu burina shine naganni a Dukku inda zan faɗi abun dake raina". 

Ishaq na gama jin saƙon yasaki murmushi abayyane yace.

 "Lallai Zaleeha tacika mai sa'a dahar ta iya sace zuciyar mutum ɗaya wanda yazama tamkar da dubu, jajirtaccen Namiji wanda samun irinsa keda matuƙar wahala" 


Murmushi kawai Saifuddeen yayi inda ya danna madannin kekensa nan yafara tafiya, yana gaba Ishaq na biye dashi abaya haka suka fito daga cikin ɗakin, Ummi dake tsaye tana ganinsu ta saki murmushi cike da so da kuma tsananin tausayinsu tace.

 "Har kun fito, amma dai kafun kutafi ai dai zaku tsaya kuci abinci, musamman ma kai Ishaq musamman na aje maka ragowar dambun nama don nasan kanaso" 

Murmushi Ishaq yayi tare da cewa.

 "Shiyasa nake sonki Ummi na, yanzu dai abani dambun natafi dashi sai naci acikin mota don naga wannan abokin nawa sauri yake kamar wanda zai tashi sama burinsa kawai shine ya gansa a Dukku"


Murmushi Ummi tayi tare da cewa.

 "To bari kawo maka sai katafi dashi amma dai inkun dawo kabiyo tanan zanyi abincin dare harda kai!" 

Murmushin jin daɗi Ishaq yayi inda yace.

 "Insha Allah!" 

Nan Ummi ta kawo masa dambun naman, har bakin mota ta rakasu inda tayi musu adawo lafiya, Hayatuddeen kuwa ɗan kalen baki hadda cewa Hamma Saifuddeen ɗin nasa wai yakawo masa tsaraba. 


Ƙarfe Biyu daidai suka samu isowa cikin garin na Dukku, gari me ɗauke da tarin al'barka da shuke shuken tsirrai masu kyau da ƙawatarwa,   agidan Baffa Ali suka sauƙa inda yacika da tsananin mamakin ganinsu da yayi don sam Saifuddeen baisanar masa cewa yana zuwa ba. 

A falon Baffa Ali'n suka zauna inda Aunty Nina takawo musu ruwa tare daɗan abun motsa baki,   gyara zama Baffa Ali yayi tare da duban Saifuddeen cikin kulawa yace "Kashammace ni Saifuddeen nida jibi nake shirin tahowa Gombe'n sai kuma gashi kazo batare da kasanar dani ba, ai da kafaɗamin kanada buƙatar ganina to tabbas da har gida zanzo nasameka".


Murmushi Saifuddeen yayi tare da duban Baffan nasa, saƙo ya rubuta awayarsa kamar haka, kana ya miƙawa Baffa Ali'n.  

"Kagafarceni Baffa Ali, magana me mahimmanci ne ta kawoni, naƙi sanar dakai zuwana ne kuma saboda nasan idan kaji cewa zakayi nabari zaka zo". 


Ɗan murmusawa Baffa Ali yayi bayan yagama karanta saƙon inda yace.

 "Shikenan Saifuddeen ina sauraranka, tabbas nasan baƙaramar magana bace zata tasoka daga Gombe zuwa nan".


Ajiyar zuciya Saifuddeen yayi tare da sunkuyar da kansa ƙasa, Ishaq ne yaɗan gyara zamansa tare da yin gyaran murya cikin nutsuwa yace "Saifuddeen yaga mata kuma yana fatan aurenta wannan dalili shiyasa mukazo don musanar dakai, saboda yana da buƙatar anemamasa izinin fara zuwa zance daga wajen manyanta kamar yanda addini ya koyar!" 


Wani irin murmushin farin ciki ne ya bayyana akan fuskar Baffa Ali, cike da tsananin jin daɗi yace "Alhamdulillah masha Allah, Allah Abun godiya, haƙiƙa kun zomin da labari mai daɗi Ishaq, na kuma yi murna ƙwarai matuƙa, tabbas yanzu naƙara yarda dacewa NAKASA BA KASAWA BACE, haka kuma nakasar Saifuddeen bata tauye masa zamowa cikakken ɗa Namiji ba, Allah Abun godiya".

Duban Saifuddeen wanda kansa ke ƙasa Baffa Ali yayi cike dajin daɗi yace .

"To ita yarinyar a inane take sannan wanene mahaifinta?" 


Ishaq ne yace.

 "Anan Gombe take cikin G.R.A  sannan mahaifinta babban Malami ne wanda ƙasa gaba ɗaya ke alfahari dashi Malam Bashir!"


Cikin jin daɗi Baffa Ali yace "Alhamdulillah mungodewa Allah, Insha Allahu yau yau ɗinnan zan sanar da aminin mahaifinka Malam Ashiru, don kuwa gobe zamu dira acikin garin Gombe, bazamuyi k'asa a guiwaba don ba'a wasa a lamarin aure".


Sosai daɗi ya cika zuciyar Saifuddeen wani irin farin ciki yakeji, yayinda zuciyarsa ta cika da annuri, kasancewar tanaji ajikinta cewa takusa samun muradin ta.  

 Anan cikin Dukku su Saifuddeen suka wuni inda suka zazzaga ƴan uwa da kuma abokan arziki a gidan Goggo Dada ma sun dad'e. har gidan Malam Ashiru sukaje da Baffa Ali, nan Baffa Ali yayi masa bayani, sosai yaji daɗi shima kuma yayi na'am tare da nuna farin cikinsa, inda suka tsayar akan cewa gobe insha Allah zasu sauƙa acikin garin na Gombe.  Anan cikin Dukku su Saifuddeen sukayi sallan Magriba daganan suka kama hanyan dawowa cikin Gombe.  


Zaleeha ce zaune acikin falon Mahaifiyarta yayinda ta tanƙwashe ƙafafunta washe guda, kayan ciye ciyene zube agabanta dangin su snacks da chocolates, sanye take da wata ƴar riga marar nauyi wanda taɗan kama jikinta, idanunta ta lumshe akaro na barkatai tare da  jingina bayanta da jikin kujera, damuwane ke ƙoƙarin hallaka nutsuwarta, yayinda wutar ƙaunarsa ke tsananin ruruwa acikin zuciyarta, gaba ki ɗaya kwana biyunnan sam bata da nutsuwa, ko abinci bata wani ci sosai, sam batajin daɗin zaman gidan nasu ayanzu, don kuwa akowacce rana sake hura mata wuta ake akan fitarda gwaninta,  sam idanunta sun rufe, bataji bata gani akan soyayyarsa, akullum akuma koda yaushe, duk bayan shuɗewar wasu mintuna soyayyarsa ƙara ninkuwa take azuciyarta, yayinda abun ke ƙara girmama akowacce rana, don yanzu hartakai ta kawo hatta numfashin da zata shaƙa da Soyayyarsa yake tafiya, zuciyarta tuni ta narke akan tsantsar ƙaunarsa, takanyi kuka sosai akan soyayyarsa amma babu me rarrashi,, ahankali take fitar da numfashi tana mejin tsananin kewa da begensa. 

Zakariyya da tun ɗazu ke tsaye akanta batare da ta sani ba ya gyara tsayuwarsa, duk da cewa suna yawan faɗa atsakaninsu, amma duk da haka yana matuƙar son yayartasa, haka kuma yanajin duk wata damuwa tata shima damuwarsa ce, cikin tausayawa yace.

 "Adda Zaleeha!" 

Jin muryan Zakariyya acikin kunnuwanta yasanyata buɗe idanunta wanda sukayi ja. 


Ganin yanda idanunta sukai ja, yasanya Zakariyya zama akusa da'ita cike da kulawa ya kamo hannunta, cikin ƙaunar ƴar uwartasa kuma yayarsa yace.

 "Wace damuwace haka take neman rabaki da nutsuwarki? wace damuwace haka ta sauya gaba ɗaya yanayinki? Dan Allah Adda Zaleeha kidawo kamar yanda kike da, banason wannan damuwar taki, kiduba fa kiga yanzu ko ƴar faɗannan bamayi banajin daɗin hakan wlh nafi son muna fad'a abinmu a shiga tsakaninmu aji kunya!".


Idanunta ne sukayi rau rau, yayinda hawaye ya cika cikinsu, cikin sassanyar muryar dake bayyana zallan damuwan da take ciki tace "Yazanyi Zakariyya? Yazanyi da soyayyarsa? inajin zafi acikin ƙirji da zuciyata, inajin idan bansamesa ba bazan taɓa samun cikar farin ciki ba, Ina sonsa! Ina matuƙar son sa!!". Ta ƙare maganar hawaye suna me gangara akan ƙuncinta. 


Ajiyar zuciya Zakariyya ya sauƙe, duk da cewa shi yarone sannan baisan komai agame da soyayyaba, amma tabbas yaji ajikinsa cewa ƴar uwar tasa tana cikin wani hali, cikin son kwantar mata da hankali  yace.

 "Kiyi haƙuri Adda Zaleeha Insha Allah Zaki gansa, kuma shida kansa zai zo ya furta miki kalman Soyayya, nasan shima yanacan yanata tunaninki, yana kuma taso ya ganki, nasan shima yana can yana kuka akanki, yana cewa wayyo Zaleeha na, idan bake ba zan faɗa rijiya!".

Duk da cewa tana cikin halin damuwa sosai maganan Zakariyya ya bata dariya wanda har batasan sanda tayi ɗan murmushi ba, wani irin sanyi kalaman ƙanin nata suka sanya mata azuciya,   cikin jin daɗin ganin murmushin Yayartasa yace .  "Yauwa ko kefa Adda Zaleeha kinsan idan kina dariya ƙara kyau kike, sannan kuma idan kina dariya maza suna ganinki kamar tauraruwa ne, to waima wayeshi da zaice tunanin ƴar uwata bai kama masa zuciya ba? dagaske nake kiyarda dani shima yanacan yanata tunaninki, harma da inda zai sake ganinki, wataƙila ma yanacan soyayyarki ta kwantar dashi jinya, wata ƙilama baya iya bacci saboda ke, burinsa kawai shine ganinki, tabbas zaki ganshi zakuma ku haɗu nan bada jimawa ba, sannan har ƙasa zai tsugunna miki yace, wayyo Zaleeha na kibani soyayyarki dan Allah!!". 

Yanzu kam dariya sosai Zaliha keyi inda har fararen haƙwaranta saida suka bayyana, wani irin farin cikine ya lulluɓeta, jin kalaman ƙanin nata takeyi tamkar dagaske,  ganin tana dariya ne yasanya Zakariyya ɓare chocolate ɗaya yakai bakinta cikin kulawa yace.

 "Yauwa to kici chocolate ɗinki, kuma kiyi farin ciki yananan yana zuwa Insha Allah!".

Babu musu ta amshi chocolate ɗin taci, wani irin sanyin daɗi takeji azuciyarta.


 Wani dogon tsuka sukaji yafito daga bayansu hakan yasasu waiwayawa da sauri,  Mama dake tsaye tun ɗazu gaba ɗaya taji kome suka tattauna,  harara ta watso musu su duka biyun cikin takaici tace.

 "Ae dama batun yauba nasan cewa daga ke har Zakariyyan baƙananan shashashai bane, kina kuka harkina cewa bazakiyi farin ciki ba idan babu wani wanda baimasan kinayi ba, wataƙila ma yanacan duniyarsu ta aljanu, waya sani ma ko yashiga jikin wata anƙonesa da ayar Allah zuwa yanzu babuma labarinsa, Wallahi Zaleeha kidawo cikin hankali da nutsuwarki, nagama fahimtar cewa tunaninki ne ke neman gushewa, saboda haka ko kinaso ko bakyaso Abdussalam shine wanda zai zamo miji agareki, kai kuma kada ka sake nasake dawowa cikin falonnan na iske ka azaune, baka da aiki sai hauka, har wai kana kwaɗaita mata cewa zaizo gareta".

 Ƙwafa tayi tare da juyawa ta koma ɗaki. 


Fuska Zaliha ta kwaɓe tare da duban Zakariyya, murmushi Zakariyya yayi mata tare da yin ƙasa da murya cikin kulawa yace.

 "Kar maganan Mama ya dameki, ae dai bakyason Abdussalam ko?".


Kamar ƙaramar yarinya haka ta kaɗa masa kai alamar "Eh".

Murmushi yayi tare da cewa "Insha Allah Bazaki auresa ba, wanda kikeso shi zaki aura, kuma zaizo kamar yanda na faɗa miki, sannan baki dace da kowa ba saishi shi kaɗai!" 

Murmushi tayi tare da lumshe idanunta, sosai tasamu gamsuwa acikin kalaman ƙanin nata,  hannunta yakama tare da cewa takoma ɗakinta, anjima zaizo su buga game a laptop ɗinta,  bata musa shiba ta tattare kayan snacks ɗinta inda Zakariyya ya ɗauki cake guda ɗaya, haka ya fita yanaci itakuwa ɗakinta ta wuce tana mejin sauƙin damuwarta, don acikin kashi ɗari yanzu babu kashi 80.. 


Su Saifuddeen kuwa ƙarfe 7:30 pm dai-dai suka shigo cikin garin Gombe, kamar yanda Ummi ta buƙaci da Ishaq yadawo, baiyi ƙasa aguiwaba wajen biyo Saifuddeen suka dawo gidan,  Raliya ce ta cika musu gaba da kayan ciye ciye inda Ummi da kanta ta dafa musu fried rice mai rai da lafiya wanda yaji haɗin kayan lambu da hanta, gefe guda kuwa hadda haɗaɗɗen coslow wanda yaji madara da bama tayi musu,  dayake Saifuddeen bawani maicin abinci sosai bane hakan yasa baiwani ci da yawa ba, Ishaq ne kam yaci sosai, don dama yana matuƙar son fried rice sosai,  koda suka kammala hira ne ta ɓarke tsakanin Ishaq da Ummi inda sukayi hira sosai, har dare yayi sosai batare da sun ankara ba, ƙarfe 11 Ishaq yatashi daniyar tafiya, nan Saifuddeen yakafe kai da fata akan cewa dole lallai saidai ya kwana idan yaso gobe sai ya koma gida, Ummi ce tasa baki anan cewa Ishaq ɗin ya kwana kawai tunda dare yayi, hakan kuwa akayi ranan agidan Ishaq ya kwana tare da Saifuddeen,  haka yasha baccinsa yayinda yabar Saifuddeen nata faman juyi, sam yakasa bacci sakamakon wata irin fitinannennen tunaninta da ta addabesa, haka yayita faman juyi akan gadon da ƙyar bacci ɓarawo ya iya ɗaukarsa, ko acikin baccin haka yadinga mafarkai kala kala da Zaleeha, wacce gaba ɗaya ta riƙe masa zuciya. 


Washe gari. 


Kamar yanda su Baffa Ali suka alƙawarta masa hakance takasance don ƙarfe takwas dai-dai sai gasu acikin garin Gombe, tarba ta mutumci Ummi tayi musu, inda aranta take me mamakin ganinsu, bayan sun gama gaisawa ne Baffa Ali ya gyara zama tare da sanar da'ita abun al'khairin dake shirin tunkararsu. 

Wani irin tsananin farin ciki ne yakama Ummi har batasan sanda wasu ƙwalla suka gangaro daga cikin idanunta ba, cikin jin daɗi tace.

 "Alhamdulillah! Allah Abun godiya, naji daɗin wannan labarin matuƙa Allah kuma yasa matarsace!".

Da  "Ameen ya Allah ". Su Baffa Ali suka amsa, nan suka ɗan tattauna akan batun daga bisani Ishaq yazo tare da mahaifinsa, saboda tare zasuje, dan sosai mahaifin Ishaq ɗin yasan Baba Malam, mahaifin Zaleeha kenan, dan harma yaƙirasa yasanar dashi batun zuwansu, kai tsaye suka wuce G.R.A. 


Atare Raliya da Hayatuddeen sukayi Wani irin Tsalle, cikin tsananin farin cikin jin kalaman Ummin nasu suka rungume juna, cike da zumuɗi Hayatuddeen yace "Yesss! Allah Nagode maka Hammana zaiyi aure zan samu Aunty!!" 


Itama Raliya wani irin farin cikine ya lulluɓe mata zuciya cikin jin daɗi tace.

 "Insha Allah auren Hamman mu sai yazama abun kwatance aduk Nigeria, zamusha shagali irin wanda wasu basu taɓa yi ba!".

Hannu Hayatuddeen ya bata suka tafa cike da murna yace "Dan Allah Ummina asa lokacin bikin nan kusa!" 

Dariya Ummi tayi tare da cewa.

 "Amma kai dai Hayatuddeen Allah ya shiryeka, bafa sadaki nace maka ankai masa ba, neman izinin hirafa akaje nema masa!" 


Baki Hayatudden ya turo gaba tare da cewa.

 "Duk da haka dai, ai nasan Hammana JARUMI ne Insha Allah bazai taɓa zama LOSER ba, shi zaiyi nasara akan komai!". 

Murmushi kawai Ummi tayi tare da fita sha'aninsu, nan suka cigaba da murnarsu shida Raliya suna shewansu, Ummi kuwa Adda Rahama taƙira ta sanar mata,  sosai Adda Rahama taji daɗin zancen na Ummi, don itama tana da burin ganin auren ƙanin nata, haka Raihana ma tacika da murna alokacin da Ummi ta sanar da'ita. 


Acan G.R.A kuwa su Baffa Ali sun samu isa babban gidan na Baba Malam bisa jagorancin mahaifin Ishaq, suna isa cikin gidan, Wani matashi mai kamala Ya Aminu kenan ya ƙaraso garesu, cike da girmamawa ya basu hannu suka gaisa, nan yayi musu jagora zuwa babban falon Baba Malam ɗin, da sallama ɗauke abakinsu suka kutsa kansu cikin falon....!






                           By

                 *GARKUWAR FULANI*

8/19/20, 11:30 AM - Ummi Tandama: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


              *NAKASA BA KASAWA BACE*



                            *PAGE 27*



                                  NA

               *AYSHA ALIYU GARKUWA*


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇




 Cikin tsananin sakin fuska da cikar mutuntaka da 

martaba, Baba malam ya mik'e tare da cewa. 

"Ha Malam Ashiru kaine yau a gidan namu."

Sai kuma yayi saurin isowa inda suke tare da cewa. 

"Kai Alhamdulillahi yau inada manyan bak'i wa nake gani kamar Aliyu?"

cikin happy Baban Ishaq yace. 

"Ikon Allah kace dara taci gida kenan."

dariya Baba malam yayi irin tasu ta dattawa masu mutunci da cikar kamala haɗi da ilimi, 

hannu yasa ya jawo hannun bappa Ali tare da nunawa su malam Ashiru inda zasu zauna, 

kana ya kalli Baban ishaq da Aminu da kuma abokinshi malam Adam mukhtar kana sai Ahmad da yanzu ya shigo musu da ruwa cikin nuna sanaiyya Baba malam yace. 

"Wannan ai k'anin mune, 

Limamin masallacin fadar garinmu dukku ne. 

Kuma  mahaifinsu ne ya fara d'igamin Alifun akan allona, shine malamina a wurinshi nayi karatu har nayi sauk'a Al'qura'ani mai girma."

Sai ya kuma nuna malam Ashiru kana yace.

"Wannan kuma shine abokina tun na k'uruciya."


Sosai sukaji dad'in wanna abu, 

cikin dattaku Dirankad'i baban ishaq kenan yace. 

"Alhamdulillahi, wanna abu yayi kyau."

Cikin kamala malam Adam yace. 

    "Ainun kuwa."

Ya Ahmad ne yayi murmushi tare da gaidasu cikin nitsuwa,  murmushi Bappa Ali yayi kana yace. 

"Kaddai Ahmad ne ya girma haka?"

Murmushi Baba malam yayi tare da cewa. 

"Shine fa, shima yanzu harda yara gareshi."

"Ikon Allah  girman d'an adam babu wuya."

Cewar Malam Ashiru.


Shi kuwa malam Adam gyara zama yayi tare da cewa. 

"Bisa alamu dai bakuyi rik'o da zumuncinku bane, 

shiyasa har kuka gaza shaida yaran."

Dirankadi ne ya d'an k'urb'i ruwan da Ahmad ya zuzzuba musu cikin kofuna kana yace. 

"Ato yanzu dai igiyar zumuncin muka zo neman k'ullawa."

Murmushi mai kama da dariya sukayi baki d'aya, 

kana suka d'anyi gaishe-gaishe da tambayar bayan rabuwa sosai sukaji dad'in ganin juna, shiru suka d'anyi. 

Sai kuma Baba malam ya d'an kalli Bappa Ali tare da cewa. 

"Ina d'alibi na, Hamman Zaleeha?."

cikin murmushi bappa Ali yace. 

"Saifuddeen ne yana nan lafiya."


Jinjina kai baba malam yayi tare da cewa. 

"Shima yayi aureko?."

Malam Ashiru ne ya amshe zancen da cewa. 

"To yana dai da niya."


"Masha Allah. Allah Ya sanya al'khairi, Allah Ya jib'anci lamuranshi, yaji tausayin maraicinshi ya bashi mace ta gari."

cewar baba malam

"Amin Amin"    Suka amsa baki d'aya. 

Kana duk sai sukayi shiru tare da meda hankalin su kan Dirankadi, daya gyara zama tare da yin gyaran murya, kana ya kalli Baba malam da Malam Adam cikin nitsuwa yace. 

"To Alhamdulillahi, komai zaizo da sauk'i tunda sanaiya ya shigo cikin lamarin."

Kai suka gyad'a baki d'ayansu alamun gamsuwa,  shi kuwa cigaba yayi da cewa. 

"To wannan tafiya dai ko ince ziyara ta d'alibin naka ne."

cikin sakin fuska Baba malam yace. 

"Masha Allah Saifuddeen ko?."


"Na'am shi dai."

 Cewar Malam Ashiru. 

Aminu da Ahmad kuwa sunyi shiru kansu a k'asa domin girmama iyayen nasu.

Dirankadi ne yaci gaba da cewa. 

 "Shi dai Saifuddeen naka, shine yaga 'yar wojenka, to ya yaba da tsarin tarbiyan ta, 

har yayi sha'awar ta zamo mata gareshi kuma uwar yaranshi in Allah ya nufa."


Cikin tsananin farin ciki Baba malam yake jinjina kai, domin shi dai yasan su waye Baffa Ali, yasan tushensu ya kuma san tarbiyar Saifuddeen wacce kusan shima ya tarbiyantar dashi, 

dominko d'alibinshi ne,  a wurinsa Saifuddeen yayi hadda bayan sauk'an karatu da yayi a wurin kakanshi.

Yasan Saifuddeen farin sani, yasan sababin ciwon da ya jaza mushi kurumta, yana tsananin son d'alibin nashi sosai, irin soyayyar da malami keyiwa d'alibinshi mai gwazo da ilimi da basira,  nakasar da Saifuddeen ɗin ya samu ta k'ara samishi tausayinshi acikin ranshi,

shiyasa  koda yaji cewa Saifuddeen ne ke son d'iyar tashi, ya cika da tsananin farin ciki. Wanda ya kasa b'oyuwa akan fuskarshi. 

Haka kawai Ahmad yaji yana mugun son Saifuddeen,  saboda ganin yadda jin sunanshi kawai yasa mahaifinshi farin ciki.

Sai Kuma suka meda dubansu kan Bappa Ali da yayi gyaran murya kana yace.


"To koda ya shaida mana, yana sonta, ya nemi da muzo mu nema mishi izinin gabatar da kanshi a gareta, 

in ba'a tsaida mata mijiba, 

to shine dalilin zuwanmu dan sama mishi izini daga bakin iyayenta, kamar yadda shari'a ta tsara mana."


Malam Adam ne yayi murmushi kana yace. 

"To Alhamdulillahi ba'a rigada an tsaida mata mijiba, 

kana dama duk masu zuwa gareta bata tsaida gwaniba,

fatanmu in yazo ta ganshi su dai-dai ta tsakanin su."

Sosai Aminu ma kejin dad'i dan tabbas yasan wanna mutane ne masu mutunci wala Allah Zaleeha ta amince dashi, 

dan yana sane da shak'uwarta da Saifuddeen.

Shi kuwa baba malam kai ya jinjina musu alamun. 

"Eh abinda amininshi ya fad'a hakane a ranshi. 

Ajiyan zuciya mai nauyi bappa Ali ya sauk'e tare da gyara zamanshi, 

kana ya fuskancesu da kyau sannan yace. 

"To amman fa wani hamzari ba guduba, 

kasan Saifuddeen yanada larurar nakasa, 

kunaga hakan bazai zama matsala ba?."

Gyara zama baba malam yayi kana yace.

"Uhumm Aliyu kenan, to me a cikin nakasa?  ai ita NAKASA BA KASAWA BACE, 

kuma ai ko wanne d'an adam bai san k'arshensa ba."

Malam Adam ne ya karben zancen da cewa. 

"Hak'k'un don duk d'an adam ba'a gama mishi halittarsa ba har sai randa ya kwanta dama."


Cikin d'an jin dad'i, da kwarin guiwa bappa Ali yace. 

 "Malam Bashir, bayan kuramtanfa Saifuddeen ya kuma samun nakasar spinal cord injury! shekara d'aya daya gabata."

Da sauri Ahmad da Aminu suka d'ago kai suka zuba mishi idanu, cikin alamun tambaya, 

shi kuwa Malam Adam cikin son samun k'arin bayani yace. 

"To kuma zaiyi aure? Ya yanayi tsaurin cutar, kunfa san cutar lakar jiki ba k'aramar nakasa bace."

Baba Malam ne ya d'ago kanshi tare da girgizawa abokin nashi kai. 

tuni tausayin Saifuddeen ya cika mishi zuciya,  sai dai ya sani su Baffa Ali sun san abinda sukeyi, in har cutar ta Saifuddeen ta tsananta bazasuyi yunk'urin nema mishi aureba. 

Shi kuwa Baffa Ali wayarshi ya zaro kana ya shiga Gallery d'inshi, sashin pictures d'in Saifuddeen ya shiga, 

wanda sunfi hamsin kuma duk Hayatuddeen ke tura mishi su, 

Aminu ya mik'awa wayar tare da cewa. 

"Gashi nan zaune a kan wellchair d'inshi."

Da sauri Aminu ya amashi wayar ya fara kallon hotunan shida Ahmad. 

gaba d'aya jikinsu yayi sanyi ganin k'addara da k'udurar ubangiji a kan wanna kyakkyawan hallita, 

gashi da cikar haiba, 

tuni Ahmad baisan yana zubda hawayeba,  ganin wani hoton Saifuddeen dake zaune bisa sofa, Umminshi na zaune kan hannun kujerar ta rik'e mishi haba shi kuwa ya d'an raba jikinta duk suna dariya, 

Hayatuddeen kuwa na gefe bisa wellchair d'in Hamman nashi, yana kallonsu yana turb'una fuska waifa shine auta, 

Ahmad kuwa mijin Raliya, na tsaye kan Hayatuddeen d'in yana mishi dariya, 

Raliya ce ta d'aukesu hoton da yayi masifar kyau.

Hannu yasa ya sharte hawayenshi tare da mik'awa malam Adam wayar, bayan ya gama kallon hotunan ne wanda wasu Saifuddeen Yana kan sallaya, wasu kuwa yana tura welchair d'insa,wasu kuma yana konce kan gado ko 3 sitter,  sam bazaka tab'a yarda yanada matsalar spinal cord injury ba.

mik'awa Baffa Ali wayar yayi,  tare da maida hawayen tausayin Saifuddeen da suka cika masa idanu, kana a hankali yace.

"Shin zai iya aure har ya iya kusantar mace har in Allah ya nufa su samu haihuwa!?."

Wani sassanyar ajiyar zuciya Baffa Ali yayi kana ya, musu duk cikekken bayanan da doctors sukayi musu ya k'ara da cewa.

"Likitoci sun bamu tabbacin cewa zai iya aure harma da haihuwa, domin nakasarsa bata shafi jijiyoyin mazantakarsa ba.

Kuma ko jiya da sukaje suka sameni da batun saida na kuma tambayarshi batun lafiyarshi. 

Ya bani tabbacin shifa baida matsala ko kad'an."

Jin haka yasa Baba malam yin murmushi tare da cewa.

"Alhamdulillahi, na bawa Saifuddeen dama yazo ya gabatar da kanshi a wurin Zaleeha, in dai tayi mishi to in sha Allah Zan bashi ita."

Wani matsainacin farin cikine ya rufesu baki d'aya, 

Aminu da Ahmad ma sun aminta da Saifuddeen, domin suma ai basu san k'arshensu ba.

Malam Adam ne ya gyara zama tare da cewa. 

"An bashi dama yazo ya gabatar da kanshi, fatanmu Allah ya dai-dai-ta tsakaninsu."


"Amin Amin."  Sukace baki d'aya kana, 

daga nan suka ɗan taɓa  hira, daga bisani su Baffa Ali suka mik'e da niyar tafiya, 

Har bakin gate wurin motocinsu, Baba malam da abokinshi Malam Adam dasu Aminu sukayi musu rakiya. 


Kai tsaye gidansu Saifuddeen suka nufa, 

Wanda yake zaune a falon side ɗinshi shida Ahmad da kuma ishaq, 

hira suke amman gaba ɗaya hankalinshi baya kansu,  duk tunaninshi naga su Baffa Ali, 

tsoro yakeji kar suje ace musu anyi mata miji.

Ahmad ne ya kalleshi tare da cewa.

"Wai mene sai kayi wani shiru, in ma  an bada ita, ai akwai wasu matan."

Hararanshi yayi tare da girgiza mishi kai,  kana ya mishi alaman "Itace muradin zuciyarshi, kuma abincin ruhinshi."  

mik'ewa Ahmad yayi cikin yin dariya kana yace. 

"To nama jiyo muryar Baffa Ali a parlour ku taho muje muji dame suka dawo."

Kusan a tare suka fito, 

yayinda Saifuddeen yaketa musu kallon nazartar fuskokinsu. 

Murmushi yayi ganin Dirankadi na cewa Ummi. 

"Alhamdulillahi tafiya tayi kyau, abuma duk namune."

wani irin sassanyan ajiyan zuciya Ummi tayi tare da cewa.

"Gidan mutunci ne ko?."

Da sauri baffa Ali yace.


"D'iyar Bashiru nefa d'an abokin babanmu, 

kin tuna malamin su Saifuddeen na islamiya?."


Da sauri Ummi tace. 

"La Bashir kam ai bazan mantashi ba, 

lokacin da muke karatu su sunyi sauk'a, kusan sune manyanmu a wurinsu muke biyawa in kawu baya kusa."

Cikin dariya malam Ashiru yace. 


"Ato baki mance mu ba ashe."


Kai ta gyad'a cikin jin Kunya dan tuno k'uruciya. 

Dirankadi ne yace. 

"To Zaleeha d'iyarshi ce ai?."

Ahmad ne yace. 

"La Zaleehan Malam Bashir ce? D'alibar Saifuddeen lokacin in bashine zai bata haddaba sam bata tab'a iya kawoshi dai-dai."

Sai ya kuma juyawa ya kalli Saifuddeen da ya kauda kanshi kamar ba shiba.

Baffa Ali ne ya shafa kanshi, tare dayi mishi cikekken bayanin irin tarbar da suka samu,  da irin karra masu da akayi, da kuma basu izinin ya fara zuwa zance duk sanda ya shirya.

Wani irin tarin farin ciki yakeji a ransa, a fili kuwa sai hannu ya bawa Dirankadi da Malam Ashiru tare da yi musu alamun godiya da jinjina.

sosai Ummi ke lura da irin yadda fuskarsa ke cike da farin ciki, 

Amman kunyarsa ta boye hakan. 

Sosai sukaji daɗi daga nan Ahmad ya ɗauki su Baffa Ali ya maidasu Dukku, 

Ishaq kuwa yabi babanshi suka tafi. 


Bayan duk sun fitane, 

Saifuddeen ya sarrafa whellchair ɗinshi har zuwa gaban Ummi dake tsaye, 

yana isa inda take ya ruggumeta cikin farinciki da salama. 

Murmushi tayi itama tare da tallafo haɓarshi cikin son abinda ɗan nata keso tace. 

"Allah ya sanya al'khairi a cikin wannan lamarin naka, 

Allah ya shige maka gaba ya tabbatar maka da ingantaccen farin ciki!!."

A saman lips ɗinshi ya amsa da "Amin Amin my Ummi."

Sai ya kuma sarrafa whellchair ɗin nashi ya nufi falonsa.


Ummi kuwa da sauri ta haura sama, inda Hayatuddeen ya tasa Raliya a gaba ala dole sai ta share mishi d'akinshi. 

A parlour ta samesu ita tana shara, shi kuwa yanata zuba mata surutu,  hannunshi rik'e da pillet d'in kifin margi special yanaci yanata zuba mata zance, kana yana watsar da k'asusuwan a bayan inda ta share. 

Cikin gajiya tace. 

"Wlh na gaji Ummi autanki zai samin ciwon baya dana kunne,  duk inda na share yana b'atawa kuma ya cikamin kunne da surutu kamar kabari."


Baki ya turo gaba tare da cewa. 

"Ummi wai dan ina bata labarin wata mawaƙiya, Asma'u Ahmad Matawalle ce da take son Hammana kamar ta mutu,  ɗazu muka gama waya da ita wai in gaisheki."

Cikin mamaki Ummi tace. 

"Mawaƙiya kuma?."

"Eh" Yace yana lumshe ido tare da kurb'ar juice d'in dake hannunshi.

Kauda zancen Ummi tayi da cewa.

"Su Baffanku sun dawo harma sun koma."

Cikin tsalle Hayatuddeen ya diro daga kan firijin da yake zaune tare da wurga kwalin juice d'in yace. 

"An bawa Hamma na ita ko yaushe ne auren?."

Cikin dariya Ummi tace .

"Oh ya Allah ka kimtsa min autana ya zama nitsastse kamar Saifuddeen."

Jin Raliya na cewa. 

"Ummi an bashi izini zuwa zancen?."

Cikin gyad'a kai tace. 

"Eh an bashi sosaima suka samu karramawa, d'iyar Malaminshi nefa Malam bashir, wanda kuma yake shirin Hanyar tsira na gidan radion vission FM."

Tsalle Hayatuddeen ya kumayi tare da cewa. 

"Yanzu kuwa zan tafi gidan Adda Rahma inje musha hira."

Kafinma su ankara tuni ya fice abinsa. 

Nan Raliya ta samu daman gyara mishi ɗakin nashi. 


Ummi kuwa falonta ta dawo ta zauna taci gaba da karatun da takeyi.


Shi kuwa Saifuddeen dake zaune akan lumtsuma -lumtsuman sofan dake falonshi, gyara zamansa yeyi. 

Wayarshi ne a hannunshi da alamu hira yakeyi da ishaq. 

"Kai yaro kaji dai ko mun samu karɓuwa. 

Yanzu yaushe zamuje ne dan gabatar da kanmu?."

Cikin tsokana Ishaq yace.

"Sai next week ko?."

Da sauri ya rubuta mishi. 

"Kayi hauka ne, ai zuciyata zata narke kafin nan."

Dariya sosai Ishaq yayi kana yace. 

"To yaushe zamuje?."

Cikin gyara zamanshi yace.

"Anjima da yamma zamuje, kafin nan Ahmad ya dawo."

Dariya Ishaq ya kumayi kana yace. 

"A a sarkin sauri,  gsky ka bari sai gobe da yamma.

Dan yau zata gabatar da program ɗinta na mushaƙata."

Badan ya soba sai don dole haka ya haƙura.




6:00 pm.  Zaleeha ce ke cikin ɗakin watsa shirye-shiryen su. 

Zamanta ta gyara bisa kujerar da take kai, tare da ɗan rage sautin waƙar da tasa,  kana cikin irin muryarsu na ma'aikatan gidajen radio tace. 

"Assalamu alaikum, al'ummar jihar gombe da kewaye, barkanmu da war haka sannunmu da sake saduwa cikin shirin Mushaƙata,  tare dani Zaleeha Bashir Sulaiman Dukku."

Sai kuma ta ɗan dakata tare da ƙara sautin waƙar nan ta. Nura M Inuwa mai taken.

"Kaso a soka  yafi ƙawance cika taso a soka kanaso."

sai kuma ta ɗan range sautin tana mai bin waƙar, yadda ake iyajin muryarta dana mawaƙan na tafiya atare.


Raveel dake ɗakin kula da shirin dake fita, dariya yayi domin yasan dashi da manager akeyi.

Ita kuwa Zaleeha tuni shauƙin  sonshi ya rufeta, saboda zafafan waƙoƙin so da take sakawa. 

Cikin shauƙi ta katse wata waƙan Nura M Inuwa mai taken. 

"So makaho ne, kamar walƙiya ya kamani, gashi na zautu al'umma sunata nunani!."

Sai kuma ta yi magana a hankali, inda tace. 

"Da fatan dai kuna jin daɗin waɗan nan zafafan waƙoƙin da muke kawo muku daga tasharmu ta Vission FM.

Ku gyara zama domin jin waƙarmu ta ƙarshe sakamakon  ganin lokaci na hararanmu. 

Sai ta kuma saki wata zazzafar waƙa mai tsuma zuciya,  inda jarumar ciki ke cewa.

"Zo muyi zance masoyi na kajiya."

Sai ta kuma sai-sai-ta waƙar tare da dai-dai-ta muryarta data waƙar tana bin baitin.

"Karda ka kauce, kasa ai mini dariya.

Saida na tace na zaɓo ka guda ɗaya, babu irinka aduk faɗin duniya."

Sosai akejin muryarta na tafiya da sautin waƙar. 


Dai-dai lokacin kuma Baba malam da Ya Ahmad da Aminu,  suna gidan Inna wacce ya samu tana jin radio. 

Cikin kaɗa kai tace mishi. 

"Ka jiko Bashiru ka haifi zabiya mawaƙiya, 

Kaji da kunnen ka ko, 

Yanzu aka gama gabatar da shirinka na masu imani, Kajita ko ita kuma amara zabiya kantalla mai son kiɗe-kiɗe da raye-raye kamar jikar dujjal."

Shiru baba malam yayi cikin jin kiɗan da Zaleeha ta ƙure ta haɗe da muryarta yana hawa mishi kai. 

Kai ya jujjuya dai-dai lokacin da take bin waƙar inda ake cewa. 

"Kai d'aya gaiyya mazaje kubi baya. 

Babu irinka na duba duk nahiya!."

Cikin takaici Ahmad yasa hannu ya kashe radio'n, dan ya lura ran mahaifin nasu ya ɓaci sosai da sosai,  shi kuma sam  baya ƙaunar duk abinda zai ɓata mishi rai ko ya taɓa ƙimarshi. 


Ita kuwa Zaleeha cikin Shauƙi ta gama gabatar da shirinta kana ta fito. 

A bakin ƙofa suka haɗu da Bilkeesu mai gado, dan zata shiga gabatar da shirin labaran duniya. 

Cikin kula tace. 

"Kadafa ki manta Dukku,  gobe da yamma zamuzo gidanku nida Rashida zamuje gidan Adama ta haihu muyi mata barka."

Kai ta jinjina tare da cewa. 

"Ba matsala sai kunzo dama gobe ba inda zanje."

Daga nan sukayi sallama, 

a bakin motarta ta samu Raveel dariya ya mata tare da cewa. 

"Gani nazo muyi zance kar ai miki dariya,  ni d'aya gaiya na isheki a duniya,  dukka buƙatunki zanmiki ba inkiya."

Murmushi tayi dan dama ai Raveel natane yanada abin dariya dasa mutun Shauƙi.

Motarta ta shiga tare da cewa. 

"Kafi kyau a hakanka ka zauna matsayin abokina."

Murmushi yayi tare da rufe mata k'ofar motar. 


Kai tsaye gidan Addanta Maryam ta biya dan tace mata, 

Yau awaran couscous takeso tayi mata.

A dinning table suka zauna tana cin awaran da aka soya da ƙwai.

Sai miyan tarugu damn albasa da dusan kifi. 

Cikin kula Maryam tace. 

"Kina addu'o'in da na baki ko?."

Kai ta kaɗa mata tare da cewa. 

"Inayi Addana inata rok'on Allah ya baiyana minshi ya kawo minshi gareni in har shidin al'kairi ne a gareni."

Cikin sanyinta da haƙuri tace. 

"Yauwa yar uwata, ki kuma rage jin kiɗe-kiɗe ki yawaita jin karatun Al'Qur'ani.  Ƙinga inma aljanine kamar yadda mama ke faɗi zai rabu da ke."


Kunun ayan dake gefenta ta kurɓa tare da cewa. 

"Mutun nema my Adda na, ina sonshi, ina son abuna."


Murmushi maryam tayi kana tace. 

"Allah ya tabbatar miki da al'khairi!."


"Amin Amin."  Tace tare da miƙewa, ta ɗauki kular da Maryam ɗin ta cika da awaran tace a kaiwa Aunty Lubna da ya Ahmad.

cikin kula Maryam tace. 

"Ki tsaya kiyi salla mana."

Kai ta jujjuya tare da rataya hand bag ɗinta  kana tace.

"Kin san baba malam baya son in kaiwa dare a waje."

Kai ta gyaɗa mata kana ta rakata har wojen motarta.



Bayan anyi sallan ishane, Ya Habu ya shigo falon Mama inda ya samu Zaleeha da Zahira da Aunty Lubna suna hira, 

cikin yanayinshi na rashin sakin fuska dan shi ya gadi rashin fara'ar Mama amman shi yanada mutunci fuska a haɗe yace. 

"Ke Zaleeha kije Baba malam na ƙira."

Da sauri ta dafe ƙirjinta tare da cewa. 

"Ya Habu meya faru?."

  "In kinje ai zakiji."

ya bata amsa ataƙaice, 

jin hakane yasanya ta miƙe da sauri tare da zumbula hijabin sallanta, wanda yake har ƙasa ta nufi parlour'n  Baba malam ɗin. 

A bakin ƙofar parlour'n tayi kiciɓis da ya Ahmad, cikin sauri ta kamo hannunshi tare da cewa. 

"Please ya Ahmad muje ka rakani dan Allah!."

Murmushi yayi sannan yace. 

"To muje."


Shiru sukayi baki ɗayansu a gaban mahaifin nasu, 

yayinda Aminu ke gefe riƙe da wani littafi. 

Ganin shirun yayi yawane murya na rawa tace. 

"Baba malam gani."

tsareta yayi da ido kana yace. 

"Na ganki ai, ke nake jira inji ko kin fidda tsayeyye kamar yanda na umurceki."

Kai ta jujjuya a hankali kana tace. 

"A'a."

Murmushin girma yayi tare da cewa. 

"To ba matsala, ni na zaɓa miki, 

zai zo gobe ki ganshi, in ya miki shike nan, in kuma bai mikiba ba dole na baki kwana biyar daga goben sai ki kawo wanda kike so, 

In kuma har kwana biyar ya cika baki kawoba to tabbas zaɓina ya zama naki."

Da ƙarfi ƙirjinta ya wani irin wawan bugawa, take tsoro mai tsanani ya rufeta, 

da sauri ta rumtse ido jin Ya Aminu na cewa. 

"Gobe da yamma zaizo kuga juna kada kije ko ina."

Kai ta ɗago da nufin zatayi magana kenan. 

Baba Malam yace. 

"Tashi kije sai da safe, Allah ya muku al'barka."

Da kyar ta iya cewa. 

"Amin. " kana ta miƙe ta fita. 


Kafinma ta isa falon tuni hawaye sun ɓata mata fuska. 

kai tsaye ɗakinta ta nufa. 

Da sauri Aunty Lubna tabi bayanta tsaye ta sameta ta kifa kai jikin gini tana rera kuka. 

Kamota tayi suka zauna kan gado. 

Cikin sassauta lafazi tace.

"Meyasa bazaki zama jaruma ba wurin tinkarar matsalarki abu kad'an ki fara kuka."

Cikin zubda ƙwalla ta gaya mata abinda Baban nata ya gaya mata. 

Gyara zama tayi tare da share mata hawayenta kana tace. 

"To ai da sauƙi tunda har yanzu dai an baki damarki,

ki kuma dage da addu'ar Allah ya kawoshi gareki kafin kwanakin da Baba malam ya faɗan su cika. 

Kuka ba naki bane addu'ace ta kama ceki."

cikin jin ƙarfin guiwa ta gyaɗa kai. 

Haka dai tayi ta rarrashinta har ta sake.


Sannan ta fita ta koma side ɗin Mamy,  inda ta samu tuni Mamy ta tafi wurin Baba malam. 

Ɗakin da take sauƙa idan sunzo ta shiga, nan ta samu Ahmad ɗin na yiwa yaransu addu'a. 

yana gamawa suka dawo parlour'n Mamy nan yake bata labarin komai a kan Saifuddeen,  shiru tayi a ranta tana cewa nakasasshe kuma? a fili kuwa lafewa tayi jikin mijinta. 



A can wurin baba malam kuwa sosai yayiwa Mamy bayani sanin tanada nisuwa kuma Alhamdulillahi don ai ita tasan Saifuddeen farin sani.


Ita kuwa Mama Allah-Allah takeyi girkinta yazo,  ta shigar da batun Abdussalam a wurin baba malam,  akan zata ce mishi Zaleeha ta amince dashi.


Washe gari da yamma ƙawayen Zaliha Bilkisu da Rashida suka zo, 

inda tuni itama ta shirya, 

har zasu fita Ahmad yace

kada su fita su bari sai gobe in yaso suje, 

ya fake da yasan Rashida ta iya zana lalle yace ta zanawa Lubna. 

Sosai suke ganin daraja da girman Ya Ahmad ɗin,  dan haka ba musu suka amince. 

Nan Rashida ta fara zanawa Aunty Lubna lalle, 

ita kuwa Zaleeha kamar ta mutu dan baƙin ciki,  dan tasan abinda yasa Ya Ahmad ɗin nata yayi musu haka. 

Bilkeesu kuwa gyara kwanciyarta tayi tana kallon film d'in Sanam Teri Kasam da ake haskawa a tashar MBC Bollywood.



Biyar dai-dai Ahmad ya shigo tare da ishaq. 

  

Kai tsaye parlour'n  Saifuddeen suka nufa.

zaune suka sameshi bisa wellchair ɗinshi, mai kalan golding ash. 

Wani irin murmushi Ahmad yayi tare da cewa. 

"Fatabarakallahu fi hasanil Kaliƙin,  tsarki ya tabbata ga ubangijin sammai da ƙassai da yayi wannam kyakyawar halitta."

Ishaq ne ya amshi zancen da cewa. 

"Masha Allah!."

Murmushi Saifuddeen yayi wanda yake sanye da wata ɗanyen yadin getzner mai azabar kyau kalar dark green mai turuwa, irin dark mai shinng ɗinnan, yayinda aka zubawa kayan wani fitinennen ɗinkin half jumper and pencil trouser, daga wuyan rigar kuwa aka watsa mishi wani tattausan zaren surfani.

yayinda ya murza wata kyakyawar hular damanga mai ratsin dark green akansa, 

daga ƙafansa kuwa  wasu irin fitinannun toms mai kalan shaddarsa yasa, ƙiran company'n Gucci, me matuƙar tsada,

still kuma zazzafan agogon company'n Gucci ne ke ɗaure atsintsiyar hannunsa wanda kuɗinsa kaɗai ya haurawa 80k, 

sai wayarshi ƙiran iphone 11 pro max daya zura cikin al'jihun gaban rigarshi, wanda abayyane ta saman al'jihun rigartasa, kake iya hango kyawawan camera's ɗinta guda uku dake jere reras, biyu asama ɗaya aƙasa.

Yanayin shigar tasa ta matuƙar ƙara fito da farar fatarshi kai ka rantse da Allah cewa balarabe ne.

Sajen nan nashi yayi wani lub-lub yayiwa fuskarsa ƙawanya sai sheƙi da ƙamshi yake,

red colour lips ɗinshi sai shinning skeyi tamkar an shafa mishi mai a kansu. 


Shida kanshi ya sarrafa whellchair ɗinshi suka fito zuwa parlour. 

Ummi suka samu ita da Hayatuddeen azaune. 

gabanta suka tsaya

cikin shirinsu na fita,  murmushi tayi tare da godewa Allah daya bata wannan kyakkyawan ɗan,  cikin gane batun da ya mata tace. 

"Allah ya kaiku lafiya, ya dawo daku lafiya, Allah ya baku nasara da sa'a kan abinda zakuje nema. 

Allah ya sadaku da al'khairin dake cikin tafiyar ya rabaku da sharrin dake tare da tafiyar."


Da "Amin." Suka amsa baki ɗaya.

 

Shi kam Saifuddeen wani sanyi da farinciki ne suka rufeshi sabida addu'o'inta gareshi.

Shiko Hayatuddeen sai hotuna yaketa musu. 


Daga nan suka fita, 

har bakin gate Hayatuddeen ya rakasu,  saida yaga sun fita sannan shima ya ɗauki machine ɗinsa ƙirar UD, ya nufi gidan Inna dan zaije wurin Zakariyya.



Su Saifuddeen kuwa suna isa G.R.A.

 Ahmad ya rinƙa bin ƙwatancen da Baffa Ali yayi musu, 

suna isa bakin  gate ɗin suka danna horn, sunyi  biyu ana uku aka wangale musu makekem gate ɗin. 

Cikin nitsuwa Ahmad ya dai-daita parking ɗin motar,

a hankali ya buɗe marfin motar ya fito cikin shigarsa ta al'farma,

both ɗin motar ya buɗe tare da fiddo whellchair ɗin Saifuddeen,

ta inda yake yazo,  buɗe mishi murfin motar yayi kana ya gyara mishi keken.

Yayinda tuni Ishaq kam ya fito.


Yana gama gyara zamanshi kan whellchair ɗin sai ga Ahmad ya fito daga cikin gidan hannunshi riƙe da Unaisa

ganinsu yasa cikin sauri ya nufi inda suke, 

ganin haka Ahmad Abban farida ma ya saki fuska kana ya nufi inda suke hannu suka bawa juna, 

Abban Farida ne ya fara magana, inda yace.

"Assalamu alaikum."

"Ameen wa alaikassalam, barkanku da zuwa."

"Yauwa barka dai."

Murmushi yayi tare cewa. 

"Ahmad yayan Zaleeha."

cikin sakin fuska Abban Farida yace..

"Ni kuma Ahmad yayan Saifuddeeen."

Murmushi sukayi baki d'aya, 

sannan suka taho inda su Ishaq ke tsaye, 

cikin tsananin  son Saifuddeen ya sunkuyo ya bashi hannu sukayi musabaha, 

sannan suka gaisa da ishaq wanda shi sam bai gane cewa Ishaq makaho bane. 

Jagora yayi musu zuwa BQ  inda dama yasa Lubna ta gyarashi fes tunda safe. 


Bayan sun zauna ne yace. 

"Bari naje na turo muku ita ko."

cikin fara'a Abban Farida yace.

"Ayi haka babban yaya."

"Ai anyima." ya bashi amsa yana ɗan murmushi, kana yafice daga cikin babban falon BQ ɗin. 


Shiru sukayi kowa da abinda ke ransa, 

shi kuwa Saifuddeeen azkar yakeyi azuciyarsa cikin nutsuwa.


Zahira yasa ta kai musu abin sha, kana ya nufi side ɗin Mama. 

A Parlour Mama ya samesu suna hira sama-sama dan kowacce da abinda takeyi.

cikin tsare girar sama data ƙasa yace. 

"Ke Zaleeha tashi kije BQ kinyi baƙi."

wani irin tsuke fuska tayi tare da yamutsa fuskar kana tace. 

"Baƙi kuma ya Ahmad."

Ya Habune da yanzu ya fito ɗakin Mamansu yace. 

"Ke shi sa'anki ne yana miki Magana kina zaune, 

Zaleeha kifa kiyayeni nagafa baki da kunya ji kike kamar kin kamomu ko?."

Da sauri ta jujjuya mishi kai tare da miƙewa jiki na tsuma domin ita dai Allah ya sani tana tsoron ya Habu da Ya Aminu mugayene na bugawa a mujalla yazu zasuce zasu kai mutun mari.

"Maza ɗauko mayafinki ki ɓace mana daga nan."

Da sauri ta nufi ɗakinta, 

shi kuwa ya fice daga falon.

A zatonta yana nan shiyasa tayi maza ta fito tana mai yin rolling kanta da ɗan kwalin lafiyayyar Arabian gawn ɗin dake jikinta, 

ganin baya nanne ta zumbura baki tare da cewa. 

"Bilkisu muje ki rakani."

Kai bilkisu ta jujjuya tare da cewa. 

"Tab ina cikin kallon wannan film ɗin ai babu inda zani, 

Rashida ta rakaki mana tunda ta gama zanen da takewa Aunty Lubna."

Ahmad ɗinne ya kalli Rashida cikin bada umarni yace. 

"Rashida rakata ko."

"To"  tace tare da miƙewa ta ɗauki mayafinta. 

Suna gab da fita aka tafi talla, 

ganin haka Bilkeesu ta miƙe tare da cewa. 

"MBC Bollywood iyayen talla sun tafi, 

muje inga sahibin namu kafin in dawo sun gama tallarsu na tsiya."

dariyan mugunta Rashida tayi, kana suka nufi BQ. 


Shi kuwa Ya Ahmad parlour'n Baba Malam ya nufa.

Yana shiga ya samesu da Mamy da Mama da  kuma Baba Malam ɗin. 

Gefen da littatafan addini wanda suke jere ya nufa yana mai cewa. 

"Baba Malam su Saifuddeen sun zofa."

kai ya gyaɗa alamun to kana yace. 

"Ka tura mishi Zaleehan"

"ai tama tafi." 

ya bashi amsa yana  me zama kusa dashi, 

kai ya ɗan kwantar cikin sanyin sauti yace. 

"Naji tausayin Saifuddeen baba ya bani tausayi, mutun kyakkyawa matashi Allah ya jarabceshi da nakasa mai zafi, 

wlh Baba sai ka ganshi yama fi kyau a zahiri akan a hoto, 

in dai Zaleeha ta yarda dashi to haƙiƙa tayi dace da miji managarci, 

domin sam nakasarsa bata zame mishi kasawa ba, in ka ganshi kamar ba kurmaba, haka inba dan wellchair ɗin da yake zaune a kaiba bazaka taɓa cewa gurgu bane."

Cikin mamaki Mama ta ƙara haɗe fuska tare da cewa. 

"Wai maganar me kukeyi hakane ban gane inda kuka dosaba, 

Gurgu kurma wurin waye yazo!?."

Cikin isa da tsare fuska Baba Malam ya mata bayanin komai akan Saifuddeen ya ƙara da cewa. 

"Kuma ni yamin na yaba dashi muddin bata fidda waniba to niko zan aurawa Saifuddeen ita!."


Kaƙa ƙara ƙaƙa wayyo Mama ina wuta ta faɗa ciki, don baƙin ciki da takaici, 

cikin tsananin hatsala da takaici tace.

"Kurma! gurgu!? Yar tawa zaku haɗa baki kuce gurgu zaku aura mata? 

ai Wallahi bazata taɓa saɓuwa ba."

Mamy ne tayi saurin cewa. 

"Kiyi mata fata da addu'an abinda yafi al'khairi zaifi akan mugun furuci baki san inda rabonta yakeba."

Wani irin mugun kallo ta watsawa Mamy tare da cewa. 

"Mugun furuci?  Akwai wani mugun furucine daya wuce abinda kuka haɗa baki kuna cewa,

dan tsabar son k..".

Shiru tayi da bakinta sabida yadda taga Baba malam na watsa mata kallon ki shiga hankalinki kana ya nuna mata ƙofar fita.

Kamar kububuwa haka ta fice cikin zafin zuciya da takaici, 

tana isa parlour'nta ta rinƙa kai mari ta kai gwarzo cikin tarin takaici tace. 

"Shike nan ga irin ta nan, ni dama sam-sam ban taɓa yin farin ciki da wannan aiki na Zaleeha ba, 

ta ƙare lokutanta cikin waɗannan kurame da makafi da guragu, 

abinda nike tsoron shike bina, 

in banda tsinennen gurgu mai shegen tsaurin ido inashi ina ɗiyata da ƴaƴan ministers ma basu isheta kalloba, 

wayyo Allah ni Halima Allah ka dubeni da idon rahama wannan kurma kuma gurgu ya Allah tsole idonsa ya zama makaho inga ta inda zai sake kallarmin ƴa bare yace yana sonta."

zama tayi bisa sofa cikin zafin zuciya da tarin masifa, sai ta kuma miƙewa tamkar an tsikareta,  cikin ɗaga sauti tace. 

"Ina ai wlh muddin ina raye bazata taɓa saɓuwaba, ɗiyata ta zama matar gurgu kurma nakasasshe.

lallai shima Ahmad, wato ɗan ubanci zai nunawa Zaleeha dan ya gadi munafurcin uwarshi, a rinƙa musu kallon salihai kuma mugaye ne." haka dai tayi ta safa da marwa tana surfa bala'i.


A parlour kuwa tana fita sukaci gaba da abinda ya damesu, 

inda Ahmad ya matso mahaifin nashi yana karantar dashi. 



A can BQ kuwa suna shiga Zaleeha tayi mamakin ganin Ishaq so sai ta saki ranta a zatonta kawai ziyara ya kawo mata ba wanda Baba malam yace zai zo ɗin bane.


Cikin ɗan sakin fuska tace. 

"Malam Ishaq kaine yau a gidanmu kai lale marhaba."

cikin jin daɗin yanayin muryarta yace. 

"Yauwa ƙanwata yau kam dai gani na kawo miki ziyara."


"Ai kuwa ka kyauta naji daɗi sannunku da zuwa."

ta ƙarisa maganan tana mai kallon Ahmad. 

"Yauwa Amaryarmu." Ahmad ya faɗa cikin sakin fuska, 

da sauri ta ɗan waro idanunta wanda kuma sai lokacin ta kalli Saifuddeen dake gefen Ahmad, 

kamar abin tsafi idanunsu suka sarƙafe cikin na juna.  

wani irin azabebben faɗuwa taji gabanta yayi, wanda a take ta janye idanunta dan sam bata iya juran kallon cikin ƙwayan idanun wanna ɗan ruwan injita da faɗi. 

Wani dogon tsaki taja tare da cilla mishi wani zazzafan harara, kana ta janye idanunta da sauri.

wanda ganin haka yasa fara'ar Ahmad daƙushewa. 

Rashida ce ta kalli Ahmad cikin kamala tace. 

"Ina wuni."

jiki a sanyaye yace. 

"Lafiya lau ya gida."


"Alhamdulillahi"

Bilkisu tace dashi, 

ita kuwa Zaleeha juyawa tayi ta fuskanci Ishaq rai a ɗan ɓace tace. 

"Ya Ishaq ya mutane na?."

gyara zamanshi yayi tare da shafa cinyoyinshi irin yadda al'adar makafi take yace. 

"Duk suna lfy sunce in gaidaki."

Cikin ɗan sakin fuska ta kuma cewa.

"Ina ko amsawa."

sai kuma ta ɗan daure ta ɗan kalli Ahmad a fizge tare da cewa.

"Ina wuni."

A gajarce yace. "Lafiya!."


Juyawa sukayi kan Bilkeesu jin tana cewa.

 

"To waye ne angon namu a cikinku?."

Dan so take taje taci gaba da kallonta. 

Ahmad ne ya kalleta cikin cikar haiba ya nuna Saifuddeen da yake hukunta Zaleeha da ƙwayar idanunshi kana yace. 

"Gashi nan wannan shine angon naku mai jiran gado in Allah ya yarda."

Kusan a tare su duka uku suka zuba mishi ido.

ita Zaleeha wani irin mutuwar zaune furucin Ahmad ya jaza mata, 

hatta bakinta data buɗe dan cewa hahhhh Allah bai bata iko da damar rufeshi ba. 


Bilkeesu da Rashida kuwa wani irin kallo sukewa Saifuddeen tare da cewa. 

"Masha Allah. Kai angon nan da amaryarnan sune sirrin kyau."

sai kuma Rashida ta kalleshi cikin mutuntaka taka tace. 

"Ina wuni ango mai jiran gado."

shiru bai amsaba sai ta kuma yin murmushi tare da cewa. 

"Rowar murya ne angon zai mana?."

Ahmad ne ya d'an tab'ashi wanda sai yanzu suka lura cewa kan whellchair yake zaune. 

kusan a tare suka kalleshi suka kalli Zaleeha sai kuma suka kalli juna cikin tarin mmki.

Bilkeesu ce tayi ƙarfin halin cewa.

"Ina wuni angon Zaleeha."

Kai ya jinjina mata alamar lfy, 

tare da yi mata mgna cikin body language.

"Ya kuke."

tofa abin ya fara zarta zatonsu cikin son gano gaskiyar abin Bilkeesu tace. 

"Wai meyasa baya Magana ne?  Kodai zuwanmu tarene ya ɓata mishi rai?."

Ishaq ne ya ɗanyi Murmushi tare da cewa. 

"No, ai kurmane bayaji kuma baya Magana." 

Ya ƙarishe maganar cikin rashin damuwa dan shi a wurinshi sam nakasa ba kasawa bace. 

Da ƙarfi suka haɗa baki wurin cewa. 

"Toh kurma kuma gurgu a kan whelchair!." 

sai kuma Bilkeesu ta tuntsure da wata iriyar dariya mai cike da jin daɗi kana ta bugi ƙafar Zaleeha tare da cewa. 

"To Hajiar babu nakasashe sai rago. Lallai yau shirinki ya miki rana kin samo zankaɗeɗen saurayi kurma kuma gurgu."

ina ita ma Rashida tuni dariyarta da take dannewa ya subce mata.

Ahmad kuwa wani irin haɗe fuska yayi tamkar zaiyi ruwan jini. 

Ishaq kuwa cikin kaushin murya yace. 

"Ke Zaleeha waɗan nan ƙawayen naki wasu irin muta nene da basu san daraja da ƙimar ɗan adam ba?

me a jikinmu da zasuyi ta mana dariya."

cikin dariya Bilkisu tace. 

"Kai tafi daga nan makahon banza makahon wofi.

In banda iskanci ina wannan gurgun ina zankaɗeɗiyar baby kamar Zaleeha."

Cikin zafin rai da tsawa Ishaq yace. 

"Ke Zaleeha ki dakatar da wannan mahaukaciyar ƙawar taki da wanna hauk..".

Shiru yayi ba tare daya ƙarasa zancen nasa ba jin wani irin kuka mai cin rai da Zaleeha ta saki da ɗan ƙarfi cikin ɗaga murya tace. 

"Ya isa! Ya isa!! Ya isa!!! Haka malam Ishaq ka farka daga wanna wawan baccin da kakeyi har ya kaika dayin mummunan mafarki. 

Ƙawata ba mahaukaciya bace, 

sai dai ko wannan  dutsen da ka zo dashi shine mahaukaci."

Cikin tsananin fushi Ahmad ya yunƙura, 

sai ya kuma koma ya zauna jin wani irin zazzafan riƙo da Saifuddeen ya yi mishi wanda ya zubawa su Zaleeha da ƙawayenta ido yana gane duk abinda suke faɗin. 

Cikin zafin rai Ahmad yace. "Waye kike cewa dutsen?."

A zafafe ta kalleshi tace. 

"Shi wannan halittan ruwan da kuka zomin dashi.

Me marabarshi da dutse, kurma kuma gurgu, kalleshi kamar al'jani dan kyau.

Ginennen taɓo kawai."

Sai ta kuma juyo ta kalli ishaq cikin kuka ta haɗe hannayenta duka biyu wuri ɗaya alamun neman al'farma tamkar yana ganinta tace.


"Dan Allah Malam Ishaq kada ka sake min wanna haukan, kadai san ina ganin ƙimarka da darajar ka, so  please bana sonshi na tsaneshi!."

Sai kuma ta juyo ta kalli Saifuddeen tare da cewa. 

"Wallahi kurwata kurr ko kaine sarkin mayu to ni nan Zaleeha nafi ƙarfinka,  nan gani nan bari, ƙwalelen kare da hantar kura, mcheeww  banza kawai!! "

Hannu tasa ta jawo hannayensu Bilkisu daketa dariyar ƙeta tayi, fuuuuu suka fice daga cikin falon...


Ina Ahmad fa bazai iya magana ba,  dan tsananin ɓacin rai da jin tsanar Zaleeha  a ranshi. 

Miƙewa yayi a fusace ya koma bayan Saifuddeen tare da tura whelchair ɗin cikin ƙunan rai yacewa ishaq. 

"Mu tafi ishaq."

shima ishaq rai a ɓace ya miƙe yabi bayansu. 


Mota suka shiga, kana Ahmad ya figi motar ya bar harabar gidan. 


Suna isa gida ko Dai-dai ta parking baiyi ba  ya fito tare da kawowa Saifuddeen whelchair ɗinshi ya zauna kana suka nufi cikin gida. 

Kai tsaye parlour Ummi suka shiga, 

suna isa tsakiyar parlour'n Ahmad yayi wani irin z...! 



    

                             By

                *GARKUWAR FULANI*

8/19/20, 2:32 PM - Ummi Tandama: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


         *NAKASA BA KASAWA BACE*


                          *Page 28*


                              *NA*

              *AYSHA ALIYU GARKUWA*


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇




Zamewa  Ahmad  yayi ya zauna bisa kujerar dake bayanshi tare da sanya hannayensa duka biyu ya dafe kansa, dake bala'in sarawa, wani irin kukane ya ƙwace masa ransa cike yake da ƙuna haɗi da takaicin abun da Zaleeha tayi musu, yanda yakejin ƙuna acikin ransa harya zarce misali, wani  irin tafarfasa zuciyarsa keyi masa, harzuwa yanzu kalaman da su Zaleeha suka faɗa ga ɗan uwa kuma abokinsa basu daina yawo acikin kunnuwansa ba,  Ishaq ma zama yayi tare dayin shiru, tunda yake bai taɓa jin ɓacin rai irin na wannan ranan ba, sam shi bai ɗauki nakasarsu amatsayin kasawa ba, baitaɓa tunanin zasu fuskanci irin wannan tozarcin da cin fuska dalilin nakasarsu ba,  shin menene aibunsu? Menene aibun nakasarsu? Ashe Allah Bashine ke aiwatar da komai bisa abun daya so ba? haƙiƙa bawai don Allah Bayasonsu bane ya jarrabesu da nakasa, ƙaddara ce wacce yayi imani tanakan kowani bawa, babu wanda yafi ƙarfin nakasa kuma babu wanda ya isa ja da ikon Allah.

Shin ashe dama da gaskene Nakasassu na fuskantar iriren waɗan ƙalubalen yayin nemanaure da lafiyayyu, anya kuwa anayiwa nakassasu adalci? ace wai dole sai dai nakasasshe ya auri nakasasshiya ƴa uwarshi".

  Shi makoho ne bazai iyayin kukan cikin idanu ba, hakan yasa yakeyin na zuci wanda yafi na fili ciwo. 

A hankali Ahmad ya ɗago jajayen idanunsa, cikin wani irin tururi da zuciyarsa keyi masa, ya dubi Saifuddeen,  hawayene suka sake gangarowa daga cikin idanunsa sakamakon wani irin tsananin tausayin Saifuddeen ɗin daya kamasa. Cikin muryarsa dake rawa  yace.

  "Sam ba matar aure bace Saifuddeen, wannan bata dace dakai ba, kabarta Saifuddeen, dan Allah ka ƙyaleta kasayawa zuri'armu mutumci, sannan ka sayawa ƴaƴanka tarbiya, Kabarta Saifuddeen ba irinta ya dace ka aura ba, sam batasan menene Ƙaddara ba, batasan me ake nufi da ƙudurar Allah Ba!".  


Idanu Saifuddeen ya lumshe tare da cije laɓɓansa, shikaɗai yasan me yakeji acikin zuciyarsa, shikaɗai yasan yanda ƙirjinsa ke duka,   ahankali ya ware idanunsa wanda suka ɗan sanja launi, hannayensa yasanya ya dafe dai-dai inda zuciyarsa take,  cikin nuna alama yace.

 "Ina sonta Ahmad, Ina matuƙar sonta, sonta tamkar numfashi yake agareni, bazan iya rabuwa da ita ba, kasan so Ahmad!".

Hannayensa ya haɗe waje guda alaman ban haƙuri agaresu.


Tasowa Ahmad yayi tare da ƙarasowa har gaban keken Saifuddeen, cikin yanayi me ɗauke da tsananin tausayawa Ahmad ya rungume Saifuddeen, tare da sakin sabon kuka, tunda yake bai taɓajin zafi da ciwon Nakasar da ta samu Saifuddeen ɗinba sai yau. 

Ummi datun shigowarsu ke tsaye abakin kitchine tana jinsu batare dasun kula ba, wani irin karyewa zuciyarta tayi, yayinda tsananin rauni ya bayyana akan fuskarta, idanunta ne suka cika tab da ƙwalla, cikin sanyin jiki ta tako ta ƙaraso cikin falon,   jin motsinta yasanya Ahmad sakin Saifuddeen ya juyo tare da kallonta, ganin yanda hawaye ke gudana akan idanun Ahmad ɗin yasanya hawayen dake cikin idanunta samun daman gangarowa, murya araunane tace.

 "Kada ka ɓoyemin komai Ahmad, taƙisa ko? taƙisa saboda Nakasar dake tattare dashi ko?".

 Wani murmushi mai ciwo Ummi tayi tare da duban Ahmad cikin rawar murya tace.

 "Sanar dani gaskiya Ahmad kada ka ɓoyemin!". 

Kuka Ahmad ya fashe dashi tare da zama akan kujera, ayanda yakejin zafi da tsanar Zaleeha acikin zuciyarsa bayajin zai iya rufe cin mutumcin da tayi musu, cikin muryar kuka yasanar da Ummi duk abun daya faru inda ya ƙarishe maganan  yana kuka sosai, don sosai abun keci masa rai. 

Hawayene suka cigaba da fita daga cikin idanun Ummi.  Sosai hankalin Saifuddeen yakai ƙololuwa wajen tashi sakamakon ganin da yayi Umminsa na kuka, aduniya idan akwai abun da ya tsani gani to hawayen Umminsa ne, Yana matuƙar son mahaifiyarsa ta yanda bayason shiga damuwarta koda ta ƙwayar zarra ne, sam baiso ace sanadinsa Umminsa ke kuka ba, ahankali ya shiga murza kekansa har ya ƙaraso gareta, hannayensa yasanya yashiga share mata hawayen dake fuskarta, ɗago kai Ummi tayi tana kallonsa, Idanunsa wanda sukai ja ya lumshe tare da gigiza mata kansa,  wani irin sabon kukane ya zo mata, hakan yasa takawar da kanta gefe,  ji take kamar zuciyarta zata fashe saboda tsabar tsananin tausayin ɗan nata daya cika zuciyarta,  cikin dauriya haɗi da ƙoƙarin kauda rauninta ta juyo ta kallesa, hannunta tasanya ta shafi ƙuncinsa cikin son kwantar masa da hankali tace.

  "Kada  hakan yasanya rauni acikin zuciyarka Saifuddeen, idan ita taƙika balallai ne ace kowacce mace taƙi kaba, haƙiƙa nasan itama rashin sanin nagartan kace yasanyata ƙin amincewa, amma sam baƙinka take ba, babu macen da zata  ƙin Saifuddeen, saidai taƙi aminta dakai abisa rashin sani nagartarka." 

Lumshe kyawawan idanunsa yayi tare da ɗan sakin murmushi, haƙiƙa yaji daɗin ƙarfin guiwan da Ummin nasa ta basa, har acikin zuciyarsa yaɗanji sanyi. 

Ahmad dake kallonsu tsananin tausayinsu ne yasake rufesa, hannayensa yasanya ya sharce hawayen dake kan fuskarsa. 

 Ishaq kuwa kasa cewa komai yayi, raunin dake zuciyarsa yasanya gaba ɗaya jikinsa yayi weak, sosai kukan da Ummi tayi ya taɓa masa zuciya, sam baitaɓa tsammanin haka daga Zaleeha ba koda wasa, baitaɓa tunanin cewa ƙuruciyarta zai ruɗeta har takai gayi musu rashin mutumci ba, haƙiƙa zafafan kalaman da ta faɗamusu sun daki zuciyarsa sosai, sam bai damu da baƙaƙen maganganun da ƙawayenta suka faɗa musu ba, saboda koba komai sudama basaninsu sukayi ba, amma ita Zaleeha fa?."


Cikin son kwantar musu da hankali shida Ishaq Ummi tashiga basu baki, tare da yi musu nuni da cewa, ɗan Adam baya taɓa iya tsallake ƙaddaransa, ko ba gasu bama, mutanen da suke da cikakkiyar lafiya ma suna iya fuskantar irin haka, sannan taƙara da tausasa musu zuciya,  sam Ummi bata barsuba saida taga zuciyar kowannensu yayi sanyi, amatsayinta na Uwa ta gari, haka ta shanye gaba ɗaya damuwarta ta kwantar musu da ɓacin ransu, cikin ɗan nutsuwa da Ishaq ya samu, ya tashi tare dayiwa Ummi da Saifuddeen Sallama, Ahmad ne ya rakashi har waje, inda driver'n sa ke tsaye yana jiransa.  Koda Ahmad ya dawo daga rakiyan Ishaq kai tsaye ɓangarensu ya nufa.


 lura da Raliya tayi cewa mijin nata yana cikin yanayi marar daɗi, yasanyata kwantar da murya tare da lafewa ajikinsa, cikin salo irin nata na ƴa mace ta shiga kwantar masa da hankali tare da neman sama nutsuwa, lokaci guda ta fitar dashi acikin hayyacinsa, inda ya rungumi matar tasa tare da kawar da duk wata damuwa dake cikin ransa. 


Cikin son samawa zuciyarsa nutsuwa ya sarrafa kekensa, inda ya nufi hanyar ɗakinsa,  yana shiga ya turo ƙofar ɗakin ya rufe,  ahankali ya tuƙa keken nasa tare da ƙarasowa cikin tsakiyan ɗaki, cikin hikima ya cire kayan jikinsa, inda ya rage dagashi sai boxer,  kaitsaye bathroom ya wuce, nan ya haɗawa kansa ruwan wanka, kamar yanda ya saba, cikin hikima yayi wankansa,, bai wani jima acikin banɗakin ba yafito sanye da bathrobe ajikinsa,   sama-sama yashafa body lotion ɗinsa, tare da feshe gaba ɗaya jikinsa da daddaɗan turarensa, sif ɗinsa ya buɗe tare da ciro wata farar short sleeve da kuma wani combat 3 guater jeans ya sanya, sosai kayan suka amshi jikinsa,   kasancewar akwai alwala ajikinsa, yasanya ya shumfuɗa sallaya tare da sauƙa daga kan kekensa, kamar kullum kuma koda yaushe azaune ya gabatar da sallan Magrib ɗinsa, bai tashi akan sallayan ba harsaida yayi sallan Isha, koda ya gabatar da addu'o'insa kamar yanda ya saba, yunƙurawa yayi ya hau kan kekensa, cikin nutsuwa ya shiga tura keken nasa har izuwa bakin haɗaɗɗen gadonsa wanda aka lailaye samansa da tattausan bedshet mai kyau,  cikin hikima ya sauƙo daga kan keken nasa tare da kama jikin gadon nasa ya hau,    kwanciya yayi luf akan gadon tare dakai hannunsa gefen gadon inda anan makunnin wutan ɗakin yake ya kashe,  bedsite lamb ya kunna, sai yanayin ɗakin yayi daɗi shiba duhu ba shikuma ba wadataccen haske ba. 


Ɓangaren Zaleeha kuwa, ranta amatuƙar ɓace haka suka koma falon Mama, cikin rufewar ido Zaleeha na shiga cikin falon ta yaye mayafin kanta, saboda tsaban ɓacin rai da takeji, idanunta har rufewa suke, cikin ƙunan zuciya tace.

 "Ni! wai ni! Zaleeha Kurma kuma Gurgu zaizo yace yanaso, 

lallai mutanen nan sunfara ganin damata da yawa, chab lallaima nakasassunnan, wato shiga cikinsu da nakeyi ina murmushi shine abun dayasa harsuka rainani ko, waima wannan ɗan ruwan ni zaice yanaso na, ko nayi masa kama da kalan matar aurensa ne?, da sauri taƙarasa gaban ƙaton madubin dake jin k'ofar falon, tsayawa tayi tana me ƙarewa kekyawar surar jikinta kallo, wani irin kuka ta fashe dashi tare da kai dubanta ga su Balkisu waƴanda sukayi saƙare suna kallonta, cikin ƙunan rai da sheshsheƙan kuka tace. 

"Shin nima akwai wata nakasa ajikina ne dahar wani banzan nakasashshe zaizo yace yana sona?". 

Dariya Bilkisu ta kwashe dashi cikin tsananin shaƙiyaci tace.

 "Kawai ganin dama ne irin nasa, hmmm amma wallahi wannan mutumin ya raina miki hankali, tayaya ma in ban da rashin tunani irin nasa da tsaurin ido zai dubi ajibon yarinya kamarki yace wai yanaso".

  Dariya ta ƙara kwashewa dashi tare da tafa hannunta, cikin son ƙara cusawa Zaleeha tsanan Saifuddeen tace.

 "Kurma fa, kuma bayan haka ma wai gurgu, lallai kam aikuwa daki auri wannan gwara kin auri dutsi, donshi dama dutsi-dutsi ne bayako motsi, sai inke kika motsa shi, amma wannan kam banga dame zai amfaneki ba, saidai in kuma ko zaman jinyarsa zakiyi ba zaman aure ba!".


Rashida ce ta sauƙe ajiyar zuciya tare da duban Bilkisu dake ta dariyan mugunta, cikin ƙasa da murya tace "Haba Bilkisu dan Allah kibari hakanan, nifa Allah gayen yabani tausayi, sannan tsantsar kyawunsa ya tsoratani, koda farko Allah banso yin dariya ba kedaice kika sani, amma gaskia gayen sam bashida wata makusa, kunfasan wata nakasar bata zama kasawa, idan kikaga nakasashshe ya kasa, to tabbas ya kashe zuciyarsa ne, kuma kunsan nakasar zuciya tafi kowacce nakasa ciwo, sannan ayanda na fuskanci mutanen nan sam su awajensu.

Nakasarsu ba kasawa bace, don tabbas baƙaramin jahadi sukayi ba da sukazo miki da maganar Soyayya kuma ai komin yaya masoyi yafi mak'iyi". 


Wata uwar harara Bilkisu ta aunawa Rashida cike da baƙin ciki tace.

 "Tab amma dai Rashida baki da kai, me za'ayi da waƴannan nakasassun, kyawunsa na banza na wofi, idan kece suka zo gunki da batun soyayya na tabbata bazaki amince ba."   Tsagaitawa da maganan tayi tare da dafa duka kafaɗun Zaleeha cikin zugan hasada tace.

 "Wallahi kada kiyarda ki kashe rayuwarki wajen zama da nakasasshe, me wannan zai yi miki wanna ai dashi da mace duk d'aya, saidai baƙin cikinsa yayi ajalinki,  da kyaunki da ƙuruciyarki da komai ki cuci kanki ki auri nakasasshen da bazai iya kauda miki budurcinki bama, ae wallahi Zaleeha kinci baya!".


Wani irin kuka Zaleeha ta sake tare da faɗawa jikin Bilkisu cikin aminta da kalaman nata  tace. 

"Bazan taɓa sauraransa ba Wallahi, koda ace duk duniya zasu taru akaina don na soshi, na kuma zauna dashi, bazan taɓa aminta ba, Wallahi na tsaneshi tsana me tsanani, danayi rayuwar aure dashi gwara na mutu, don bazan iya ɗaukar baƙin cikinsa ba!!".

 Cikin kukan dayaci ƙarfinta ta juya da gudu ta wuce ɗakinta. 

Wani irin munafukin killer smile Bilkisu tayi tare da bin Zaleehan da kallo.

 Rashida kuwa ajiyar zuciya ta sauƙe tare da kwantar da kanta gefe, cikin sanyi tace "Amma Bilkisu dakin tausasa harshenki akan sa, saboda ƙaddara nakan kowa.....". 


"Dakata Rashida ai nima nasan ƙaddara nakan kowa, amma wannan nakasashshen gurgunne dai Insha Allah Zaleeha bazata aureshi ba". 


Ajiyar zucia Rashida ta sauƙe tare da ɗaukan jakarta, duban  Bilkisu tayi tare da cewa. "Natafi sai gobe saduwar al'khairi".


Da sauri itama Bilkisu ta ɗauki jakanta tabi bayan Rashidan, don sam bataso kowa yagane ainihin nufi dakuma abun dake ranta da zuciyarta, saboda ita tamkar mage take me kwanciyar ɗaukan rai...



          SAIFUDDEEN.


Gyara kwanciyarsa yayi tare da gyara zaman kansa dake bisa pillow, idanunsa ya lumshe tare da sauƙe ajiyar zuciya, filla-filla kalaman Zaleeha da ƙawayenta ke dawowa cikin idanunsa, inda idanunsa keyi masa imagine duk wani motsin bakinsu,  ƙam-ƙam haka ya kulle idanunsa tare da cije laɓɓansa, haƙiƙa yaji kalamanna Zaleeha har acikin zuciyarsa,  saidai kuma tsananin soyayyar da yakeyi mata yariga dayaci ƙarfinsa.

  Jin soyayyarta yake Tamkar zata zautar dashi, sake lumshe idanunsa wanda ke ɗauke da tsananin mayen sonta yayi, wani irin murmushi yayi wanda ya ƙawata fuskarsa,  cikin zuciyarsa yace. 

 "Dakin sani da baki nemi cin zarafinmu ba, domin hakan da kikayi bazai taɓa sanyawa na janye batun aurenki ba, ko yasa muradinki ya fita araina ba, kin ƙaramin sonki sannan kuma kin ƙara min kwaɗayi da burin aurenki, bazai taɓa yiwuwaba, kowacce ƙaddara da sanadinta, kuma ni dai nasan Allah ne ya d'ora min sai daifa duk abinda ya sameni arayuwa ta sanadiyarkine, kece kikajamin komai, sannan kuma dole ke zan aura, kamar yanda ƙaddarata akanki take to dole kema saikin ɗanɗani ƙaddaranki dake kaina, zan aureki koda bakyaso!, zankuma shayar dake mmaki da zazzafar soyayyata irin wanda zata zautar dake batare dakin shiryawa hakan ba!".

 sake muskutawa yayi tare da gyara kwanciyarsa,  tabbas ayanzu yaɗauki ɗamaran fuskantarta sam kuma bada wasa zaije mata ba, lallai al'ƙawarine sai ya shayar da ita ruwan mamaki, haka yadinga saƙa abubuwa da dama aransa har bacci ɓarawo ya ɗaukesa. 


Ɓangaren Zaleeha ma da ƙyar ta iya bacci, ita kaɗai tasan irin suyan da ƙirjinta keyi mata, haƙiƙa sosai zuwan kurma kuma gurgun da ko son jin sunansa batayi ya ɓata mata ranta, babuma abun dake hassalata kamar irin kallon da taga yanayi mata tamkar wani tsohon maye bugu da k'ari kwarjinshi na sata rud'ewa, sannan kuma ta lura duk irin rashin mutumcin data surfa masa sam bai ɓata ransa ba, don bata ga alaman ɓacin rai akan wannan munafukar farar kyakkyawar fuskartasa ba, yau ko tunanin abincin ruhinta batayi  sosai ba saboda baƙin ciki, haka tayi bacci cikin ƙuncin rai, wani abun mamaki kuwa fuskarsa ce tayita zuwa mata acikin baccinta. 


               Washegari. 


Saboda yanda ranta ke ɓace sam ko shirin fita wajen aikima batayi ba, don gaba ɗaya jinta take wani irin kamar wata marar lafiya. 


Saifuddeen kuwa yau da wani irin sabon tsarin plant ya wayi gari, harzuwa yau yanajin cewa shi nakasarsa ba kasawa bace agaresa, akan dinning table sukaci abinci su dukansu cike da ƙaunar juna,  inda Hayatuddeen keta damunsu da zancen Asma'u Ahmad Matawalle, zancen nasa ɗayane shine yanda yake faɗin takurawan da tayi masa da zancen hammansa, harma cewa tayi wai idan ayyuka sukai mata sauƙi zatazo Gombe'n ta dubashi. 


Ummi ce taɗago kai ta dubeshi cikin ɗan mamaki tace.

 "Au ma'aikaciya ce ma kenan to Allah ya taimaka." 


"Ameen, ma'aikaciyace amma bata gomnati kota kamfani ba, jarumace ƴar film kuma mawaƙiya".

 Hayatuddeen ya ƙare maganar yana mai sanya soyayyen chips abakinsa. 


Baki Ummi ta taɓe tare dayin murmushi kawai ta girgiza kanta, tabbas tasan da ace Saifuddeen ɗinta macece to fa da ankwashi ƴan kallo don ba makawa maza asuke musu layin zance aƙofar gida. 

  Haka suka kammala breakfast ɗin cikin lumana, inda Saifuddeen ya tura kekensa har zuwa tsakiyan falon, laptop ɗinsa ya ɗauka yashiga internet don ɗebewa kansa kewa. 


Sake muskutawa tayi tare da sauƙe ajiyar zuciya, duk da ɓacin ran dake shumfuɗe aƙasan zuciyarta amma hakan baihanata jin cewa abun da tayiwa  Ishaq bata kyauta ba, sai yanzu kalaman da ta faɗawa Ishaq din ke dawowa cikin brain ɗinta, haƙiƙa tasan Ishaq kamilin mutum ne sannan kuma jajirtacce ne, sam abun da tayi masa bai dace ba, saidai kuma koma me yafaru shi ya jawo, sannan abun da tayiwa abokinsa kuwa ko kaɗan bata dana sanin hakan, don ko ayauma yace zaizo zatayi masa wanda ya ninka na jiya. 

Wayarta ta ɗauka tare shiga contact ɗinta, number'n Ishaq ta zaƙalo, ɗan cije bakinta tayi cikin gamsuwa da zuciyarta ta dannawa number'n Ishaq ɗin ƙira, don tanaso taɗan bashi haƙuri akan abun daya faru, harsaida wayan ta kusa katsewa kafun akayi picking, cikin sassanyar muryarta tace.

 "Assalamu Alaikum, Malam Ishaq barka da safiya." 

Shiru taji anyi batare da anyi magana ba, hakan yasa taɗan ƙara duban screen ɗin wayar, ganin cewa eh da gaske an ɗaga wayanne yasanya cikin zazzaƙan muryarta tace. 

"Dama haƙuri nakeso na baka akan......".

    ƙit taji ankashe wayar, da sauri ta cire wayar daga kan kunnenta, tare da duban screen ɗin wayar, ajiyar zuciya ta sauƙe tare da sake dialing number'n.

Ishaq dake zaune akan table ɗinsa yanajin wayartasa na ringing amma ya share,  har yanzun baigama hucewa ba danko ɗaga wayar da yayi ɗazun ma rashin sanin cewa itace yasanyashi ɗagawa amma sam baida niyar ɗaga wayarta.  


Zaleeha kuwa jin wayar harta katse ba a ɗauka ba, yasanyata sake ƙiran number'n nanma har ya katse ba ayi picking ba, saida taƙira har sau uku amma no answer,  hakanne yasa tagane cewa Ishaq yayi fushi sosai, ɗan taƙaitaccen text message ta rubuta masa na bada haƙuri kana ta aje wayarta.. 


Cikin wata haɗaɗɗiyar boyel yellow colour wanda taji ɗinkin straight jumper ya shirya kansa, boyel ɗin irin mai tsadan nanne hakan yasa aka fesa haɗaɗɗen aikin ajikin wuyanta da coffee brown ɗin zare, sosai kayan yayi kyau, takalmine sau ciki mai kalan coffee brown sanye aƙafarsa yayinda ya ɗaura haɗaɗɗiyar hula akansa itama me kalan Coffe brown, sosai yayi kyau ba abun da jikinsa keyi sai tashin ƙamshi,    cikin nutsuwa yake tura whelchair ɗinsa har ya ƙaraso babban falon na Ummi. 

Ummi dake zaune hannunta riƙe da carbi tanaja, tana ganinsa ta saki murmushi cikin kulawa ta dubesa tare da cewa.

 "Sai ina kuma?." 


Murmushin daya ƙara bayyana cikar kwarjini da haibansa yayi, cikin nutsuwa yayi ƙasa da kansa, sam ƙarya ba al'adarsa bace bata kuma daga cikin ɗabi'arsa, hakan yasa yaɗanyi jim kafun ya ɗago kansa ya kalleta, cikin body language ɗinsa yayi mata alama akan cewa gidansu Zaleeha zashi,  shiru Ummi tayi tare daɗan yin murmushi, wani irin fargaba ne taji yacika zuciyarta,  hakanan taji tsoron zuwansa gidan su Zaleehan ya kamata, saboda batasan wannan karon kuma me Zaleehan zata faɗa masa ba, cikin son nuna rashin damuwarta tace.

  "Masha Allah, amma dai ae zaka ƙira Ishaq ko Ahmad don su rakaka ko?." 

Murmushi yayi tare daɗan lumshe idanunsa sarai ya fuskanci me Ummin ke gujemasa, amma dayake abun da zuciya ke so ne hakan yasa yayi mata alaman cewa.

 "Insha Allah.Ba abun dazai faru." 


Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe tare dayi masa fatan dawowa lafiya, cikin body language ɗinsa ya amsa mata da "Ameen." 

 Idanunta akansa harya fice daga cikin falon, ajiyar zuciya ta sauƙe, lokaci guda hawaye suka cika idanunta,  haƙiƙa tana tsananin jin tausayin ɗanta Saifuddeen, musamman ma yanzu da ta hango soyayyar Zaleeha kwance acikin ƙwayan idanunsa,  cikin dauriya ta maida hawayen nata tare da jingina bayanta da jikin kujera, ahankali take jan carbin tana me tasbihi ga Allah. 


Shikuwa Saifuddeen yana fitowa daga falon Ummin kaitsaye inda Sule driver ɗinsa yake ya nufa, Sule dakansa ya buɗewa Saifuddeen ɗin murfin motar, cikin hikima kamar koda yaushe haka ya shiga gidan baya ya zauna, both ɗin motar Sule ya buɗe inda ya aje keken Saifuddeen aciki,  cikin ɗan hanzari ya shige wajen zaman driver tare dayiwa motar key.  


Fitowanta awanka kenan, gaba ɗaya fatar jikinta ɗauke yake da danshin ruwa,  towel ne ajikinta wanda iya karsa guiwarta, zama tayi akan kujeran gaban mirror tare da ɗaukan handrayer'n ta ta jona ajikin socket,  dashi tayi amfani wajen busar da dogon gashin kanta wanda ke jiƙe da ruwa, tana kammala busar da gashinnata ta shafawa gashin nata olive hair oil mai tsananin ƙamshin zaitun,  cikin nutsuwa ta shiga taje dogon gashinnata wanda tsawonsa ke taɓa har tsakiyar bayanta,  wani baby yellow ribbom tasanya akannata tare da tattara gashin tayi farkin nasa agefen wuyanta,  body lotion ɗinta mai daɗin ƙamshi ta shafa agaba ɗaya jikinta,  powder'nta wanda aƙalla kuɗinsa zaikai 8k ta shafa akan fuskarta,  wani light mochka colour lipstick ta shafa akan siraran pink lips ɗinta,  sosai lipstick ɗin ya amshi ɗan ƙaramin bakinta,  black eye pencil taɗauka tare da buɗe idanunta ta goga acikinsu, da water proof mascara tayi amfani wajen miƙar da zara zaran gashin idanunta, wanda suke ga cika ga kuma tsawo, kallon kanta tayi acikin madubi'n, murmushine ya bayyana akan fuskarta don ita kanta tayi na'am da kyawun da tayi, haƙiƙa sau da dama takan godewa Allah agame da baiwan kyau daya bata.  

Miƙewa tayi ahankali tare da ƙarasawa gaban ƙaton drawwer'n ta,  buɗe drawwer'n tayi tare da zaro wani tsadadden yadi mai kallan yellow light, sosai yadin ya haɗu yayinda aka ƙawatasa da ɗinkin riga da sket pieces,   koda ta sanya kayan baƙaramin kyau sukayi mata ba, sket ɗin ɗas ya zauna ajikinta yayinda ya bayyana faffaɗan ƙugunta wanda ke ɗauke da wani irin tsareren hips mai jan hankali, kasancewar sket ɗin yakamata hakan yasa tsararren hips ɗinta bayyana, kamar yanda sket ɗin yayi mata ɗas ajiki haka ma ƴar fitted ɗin rigan ta amshi jikinta sosai saboda irin yanda rigar ta kamata yasanya har kana iya hango beautiful breast ɗinta ta saman wuyan rigar saidai ba sosai ba,  wani ɗan manne'n ɗan kunne mai kyau ta saƙala akunnenta tare da sanya wata ƴar siririyar sarƙa awuyanta,  zama tayi agaban dressing mirror tare da tsantsara ɗaurin turban akanta,  masha Allah kyau kam Zaleeha tayishi harta gaji. 


Tunda suka ɗauki hanyar G.R.A ɗin yakejin wani irin shauƙi aransa, babu abun da idanunsa ke ɗoki kamar ganin kyakkyawar fuskarta, baisan wani irin so yake mata ba, da tunani kala-kala acikin ransa harsuka iso gaban tangamemen gate ɗin gidan,  horn Sule driver yayi inda take maigadin gidansu Zaleehan ya wangale musu gate,  acikin compound ɗin gidan Sule driver yayi parking motar,  daidai lokacin Ya Aminu ya fito daga ɓangaren Mamy hango Saifuddeen dake ƙoƙarin fitowa amota da yayine yasanyashi ƙarasowa garesu. 


Da turarenta mai azababben ƙamshi ta feshe gaba ɗaya jikinta, wani ɗan siririn mayafi mai kalan kayanta ta yafa daga kan wuyanta zuwa ƙugunta, yanayin yanda dogon baƙin gashinta ya kwanto akan gefen wuyanta shi ya matuƙar ƙara ƙawata ado da kuma kyawunta, wani takalmi mai uban tsini ta sanya aƙafafunta, cikin takunta mai nuna tsantsar aji, ƙasaita, wayewa, da kuma jinkai tafito zuwa falo, nan ta iske Mama da kuma Zahira suna hira, duban tsab Mama tayi mata fuska shafe da toka tace.

 "Sai ina?."


Zama tayi akan hannun kujera tare da ɗan turo bakinta gaba murya acushe tace.

 "Makay zanjeni yin shooping".

Baki Mama ta taɓe tare da gyara zamanta ta fuskanci Zaleehan, fuskarnan tata sam babu alaman fara'a tace.

  "Ya kukayi da banzan gurgun da yazo wajenki jiyan?." 


Lokaci guda yanayin fuskar Zaleeha ta sauya kala domin tunowa da baƙin cikinsa da tayi, cikin bayyana tsantsar tsanarsa da tayi tace.

  "Na musu bana sonshi." 

 Ƙwafa tayi tare da ɗan gyara zamanta tacigaba da cewa.  "Wai harni wani banzan MUSAKI zaizo yace yana son ƴata hmm!." 

Murmushin jin daɗi Mama tayi tare da ci gaba cewa. 

 "Ae ni banga laifinsa bama, dama ni tuncan wannan ɗan iskan aikin naki na Babu maraya  ne, ko Nakasa ba kasawa bace ko mene yake da suna, sam ba ƙaunarsa nake ba, amma dayake ke uwar taurin kaine haka kike zuwa cikin nakasassu musakai kita washe haƙora kina naɗan muryarsu wai ke adole mai tausayi ƙaunarsu, to ai gashinan kin fara ganin sakamako tunda dai har Kurma kuma gurgu yasamu daman biyoki har gida da maganar soyayya. 


Hannu Ya Aminu ya bawa Saifuddeen suka gaisa amutumce, nan Ya Aminu dakansa yayiwa Saifuddeen jagora zuwa BQ, shikam har acikin ransa ya yaba da nutsuwa da kuma haiba haɗi da kwarjini irinta Saifuddeen, koda Ya Aminu yayi masa jagora zuwa BQ cewa yayi dashi bari ya ƙira masa Zaleehan, cikin body language Saifuddeen yace "To."

 Tare da yiwa Ya Aminu'n godiya.


Ɗan ƙaramin bakinta taƙara cunowa gaba, tare da gallawa Zahira dake ta dariya ƙasa ƙasa najin cewa wai kurma kuma gurgu yazo wajen yayartata da ƙoƙon barar soyayya, baki Zaleeha ta buɗe don kaftawa ƙanwartata rashin mutumci shigowan Ya Aminu ne yasanyata saurin haɗiye maganan dake ranta, dan da tayi niyan aunawa mayataccen gurgun zagine, kana daganan saita ci mutumcin Zahira dakeyi mata dariya. 

Duban Zaleeha Aminu yayi fuskarnan tasa sam babu alaman annuri akanta, cikin tsare gida yace.   

"Ke Zaleeha kije kina da baƙo a Boys Quaters." 


Wani irin faɗuwa gaban Zaleeha yayi, cikin sarƙewar murya tace. 

"Ni...Ni kuma Ya Aminu?." 

Harara Ya Aminu ya watsa mata cikin yanayinsa na rashin fara'a agaresu yace. "Da akwai wata Zaleehan agidannan ne bayan ke? ko kuma aduk gidannan akwai ƙatuwar gantsamemiyar budurwa sama dake? Maza tashi kije Saifuddeen ne yana jiranki banason shashanci!."  


Idanu Zaleeha ta zaro, lokaci guda jikinta yasoma ɓari kamar mai aljanu, sam ta manta da cewa Ya Aminu ne agabanta cikin tsananin ɓacin rai tace.

 "What! Mayataccen gurgun nanne yaƙara dawowa, aikuwa saidai ya shekara don babu inda zanje!!".

 Taƙirasa maganan cikin rufewar ido. 


Cike da mamaki Ya Aminu ya matso inda take azafafe, cikin tsananin ɓacin rai yace "Me kikace? Maimaita nasakeji don banji da kyauba!".


Shiru Zaleeha tayi tare da sunkuyar da kanta ƙasa, wani irin tafarfasa ranta keyi mata, ji take kamar ta kurma wani uban ihu ko zatasamu salama acikin rai da zuciyarta. 


Jin tayi shiru batace komai bane yasanya Ya Aminu daka mata tsawa cikin faɗa yace "Kintashi kinjene ko saina ɓaɓɓallaki anan wajen shashashar yarinya da batasan ciwon kanta ba!!." 


Jikin Zaleeha narawa ta-tashi da sauri har ƙafafunta na harɗewa haka ta nufi hanyar fita daga falon tuni wasu irin hawayen baƙin ciki sun cika idanunta, fuuuu haka Ya Aminu ya fice daga cikin falon,  tsuka mai ƙarfi Mama tayi cikin baƙin ciki da takaicin Mijin ƴartata Maryam wato Ya Aminu tace. "Wallahi indai akan Zaleeha ne babu wanda ya isa yayi mata dole, idan kuwa har dolennema za a mata tofa lallai saidai in akan Abdussalam, amma wallahi babu wani matsiyacin gurgu daya isa nahaifi ƴa kuma ya aure ta." 

ƙwafa Mama tayi tare da cewa. 

"Duk zanyi maganinku ne ae dani kuke zancen!." 


Zaleeha kuwa ko gabanta bata gani da kyau saboda tsabar hawayen da suka cika idanunta, wani irin ɗaci na ɓacin rai takeji a maƙoshinta,  cikin ranta wata irin wutar masifa ne ke cinta, yayinda wutan tsanarsa ke ƙara ruruwa acikin zuciyarta,  tana kawowa bakin ƙofan da zai sadata da babban falon BQ ɗin ta tsaya cak,  ƙoƙarin shanye hawayen dake cikin idanunta tayi,  da wani irin ƙarfi ta bugi ƙofan falon, cikin takunta mai ɗauke da isa da kuma tsantsar rashin mutumci ta kutso kanta cikin falon.

 Idanunsu ne suka sarƙe acikin najuna domin dama tuntuni idanunsa akan ƙofar shigowa falon suke. 

Wata uwar harara mai ɗauke da tsantsar tsana, Zaleeha ta watsa masa, cikin takunta dake nuna tsantsar rashin mutumcin da takeji dashi ta ƙaraso cikin falon, ƙwas-ƙwas haka sautin takun takalminta ke amsa gaba ɗaya ilahirin falon, sam idanunta ya rufe da tsana, haɗi da masifar dake cinta arai, cike da son ƙuntata masa ta tsaya kusa dashi tare da sanya hannayenta ta kama ƙugunta,  amasifance tace.

  "Waikai wani irin  maye ne? ina tunanin tun a jiya nasanar dakai cewa bana sonka na tsaneka!".

 ɗan shiru tayi tare da dubansa sama da ƙasa da sauri ta janye idanunta daga nashi dan wani irin bugu da zuciyarta keyi a duk sanda suka had'a ido,

tabbas yayi kyau sosai acikin idanunta amma masifane kawai ke ɗawainia da ita, cikin gatsali tace.

 "Oho wato kazone don ka nunamin naci da kafiya irintaku ta kurame ko?  to bari kaji duk bala'in nacinka bazan taɓa sonka ba, na tsaneka wallahi natsani ganin fuskarka, waima shin kai bakasan cewa kai nakasashshshe bane? gurgu, kurma, sannan kuma maye" ɗan numfasawa tayi tare da sake matsowa kusa dashi cikin son ƙunsa masa baƙinciki tace.

  "Kakalleni da kyau koda a iya fuskata aka tsaya kai kasan niba matar yara bace, bare kuma irinka wanda bazai taɓa amfanata da komai ba, ginannen taɓo mai kama da dutsi!".

 Taƙare maganar tana jujjuya masa idanu tare da murguɗa baki, wai ita ala dole hakan masifa takeyi.

Tunda tashigo cikin falon yake kallonta har kawo yanzu, wani irin sanyine yaji yana ratsa zuciyarsa, sosai abubuwan Zaleehan ke bashi dariya, duk acikin abubuwan da ta faɗa babu ɗaya wanda bai fahimci me tace ba sai dai ya gane tana tsoron kwayar idanunshi, acikin ransa yace.

 "Ginannen taɓo ko, hmmm zakisha mmki!." 

Ƙawataccen murmushine ya bayyana akan fuskarsa,  cikin tsananin takaici Zaleeha ke kallonsa, zuwa yanzu kam yakaita bango don yagama ƙureta ahatsale tace. 

 "Kayi dariya zama kayi kuka da waƴannan fitinannun idanun naka masu kama dana zuri'ar mayu, wallahi-wallahi, idan baka rabu dani ba nice nan ajalinka, me yasa bazaka gane cewa na tsaneka bane? Meyasa bazaka kalli wutar tsanarka dake ruruwa acikin idona ba? kaduba kaga na tsaneka nace, na tsaneka!!!".

 Cikin tsananin ƙaraji take maganan yayinda hawaye suka cika idanunta, jitake kamar taje ta ɗauko wuƙa ta caccaka masa. 

Dai-dai lokaci Sallaman Kaltume mai aikin gidan nasu ya ratsa kunnuwanta,  amatuƙar harzuƙe tajuyo tana kallon Kaltume,  ƙarasowa cikin falon Kaltume tayi hannunta ɗauke da wani babban tray wanda samansa ke ɗauke da bottle water dakuma kayan marmari dangin su Apple da Inibi, akan babban table ɗin dake tsakiyan ɗakin Kaltume ta ajiye tray ɗin, dubanta takai ga Saifuddeen wanda yake kallonta, aladafce tace dashi "Ina wuni ranka shi daɗe!". 

Murmushin daya bayyana cikar haiba da ƙwarjininsa yayi inda ya gyaɗa mata kai alamar.

 "Lafiya" 

Nan Kaltume ta miƙe tafice daga cikin falon aranta tana me mamakin tsananin kyau irin nasa take cewa.

 "Duk yanda akayi balarabe ne shiyasa banji ya amsa gaisuwata ba, dadukkan alama baisan ma menace ba, gsky Aunty Zaleeha tayi sa'an miji". 


Kaltume na fita Zaleeha tasaki wani mugun murmushi tare da cije laɓɓanta, ahankali ta ƙarasa gaban table ɗin da tray ɗin kayan marmarin yake, ɗaukan tray ɗin tayi tare da juyowa ta kalli Saifuddeen turamasa tiran kusa dashi tayi, ranta aɓace tace.

 "Dama nakasassu irinku sunfi buƙatar irin waƴannan abubuwan hala shiyasa kazo nan don kaci ko? Mayunwaci gasunan saikaci ae!".

 Tafaɗa tana me tura masa gaba ɗaya tray ɗin,

cikin wani irin yanayi ya rumtse idanunshi da azaban k'arfi, jin zuciyarsa na tafarfasa, 

sai kuma ya bud'esu da sauri. Juyawa tayi daniyar barin falon, cikin zafin nama da tafasan zuciya Saifuddeen ya damƙo hannunta tare da hankaɗata kan kujeran dake kusa dashi, 

mamaki ɗauke akan fuskar Zaleeha ta zaro idanu tana kallonsa cike da tsoro, domin sam ita batasan ya akayi ba sai jinta tayi akan kujera, cikin zafin nama ya ƙaraso dakekensa har gabanta, ƙafansa ɗaya yasanya ya tokare gefen kujeran yanda babu yanda za'ayi ta iya tashi. 

Wani irin horo yashiga yi mata da idanunsa wanda duk rashin kunyarta take kasa kallon cikinsu,

da sauri ta sunkuyar da kanta yayinda k'irjinta ke duka uku-uku,  ga wani iri abu da taji ajikinta, cikin haɗe fuska da tattaro d'an guntun jarumtarta da ragwowar tsiwartata tace.

 "Miye hakane dahalla Malam, ni ɗagamin ƙafanka na wuce idan ma maitan nakane yatashi kurwata kur kaci kanka!".

 Tafaɗa tana me ƙoƙarin miƙewa tsaye,  da sauri Saifuddeen yasanya ƙafarshi ya tokari guiwanta, da tashi guiwar da azaban k'arfi.

da sauri ta yarfa hannu tare da cewa. 

"Wayyo Allah na, mugu'azzalumi, karya min k'afa zakayi ka maidani gurguwa irinka ko?."

bai kulata ba sai k'ara datse mata guiwarta da yayi da tasa guiwar har takai suna iya jiyo hucin numfashin juna, yayinda daddaɗan ƙamshin turarensu ya cakuɗa waje ɗaya, ahankali yashiga yawo da idanunsa akan jikinta, wani irin yaaarrr haka yaji a jikinsa alokacin da idanunsa suka sauƙa kan tudun ƙirjinta, tuni tsikar jikinsa suka soma mimmiƙewa yayinda yaji wani irin feeling ya dirar masa alokaci guda,  idanunsa ya ɗauke daga kan ƙirjin nata tare da sauƙesu akan laɓɓanta, wani irin yawu ya haɗiya amaƙoshinsa tare da ɗan lumshe idanunsa, jiyake kamar ya jawota ta faɗa jikinsa,  yanajin kamar ya ladabtar da ita tahanyar bawa kyawawan laɓɓan  bakinta professional kiss, ahankali idanunsa suka ɗan sauya kala daga farare zuwa yanayin bacci, cikin wani irin salo yasanya hannayensa inda ya tallafo haɓarta, idanunsu ne suka dire acikin najuna da sauri tayi ƙasa da idanunta cikin faɗa tasanya hannunta ta buge hannun nasa daya taɓa haɓanta, cikin son koyan  rashin kunya murgud'a mishi baki tace. 

 "Ɗan iska kawai!, ai bama sai ka gwadamin a zahirance nagani ba.

 Duk wanda yaga waƴannan munafukan idanun naka yasan kai ɗan iskane!!". taƙare maganar tana murguɗa bakinta, wayarta dake hannunta ce takawo haske, cireta a key tayi tare da k'ok'arin duba waye mata flashing, 

sam ba zato ba tsammani taji Saifuddeen ya wafce wayar daga hannunta, rai aɓace ta ɗago ta dubesa cikin gatsali tace.

 "Bani wayata tunda bada kuɗin Nakasassun guragu na saya ba!". 

Ƙin bata wayar yayi gashi gaba ɗaya yayi mata ƙawanya da  jikinsa, sannan kwarjininsa ya cika mata ido. 


Saifuddeen kuwa number'nsa ya sanya acikin wayan inda ya danna dialing, take wayarsa dake cikin al'jihun gaban rigarsa ta soma ƙara, ganin numbern ta yafito acikin wayarsa ne yasanyashi katse ƙiran kaitsaye wajen text messages ya nufa,  sannu ahankali ya rubuta kalamai masu hikima inda yayi sending zuwa phone ɗinsa, saida ya tabbatar da cewa saƙon  yashiga wayarsa sannan ya maida idonshi kanta.


Itakuwa Zaleeha cikin ƙufula take binsa da harara, ganin yanda ya tsareta da idanune  yasanya a hatsale ta wafce wayarta dake hannunsa,  miƙewa tsaye tayi tare da watsa masa harara cikin yanayi na tsanarshi tace.

 "Kada ka taɓa manta cewa bana sonka, sannan kuma na tsaneka tsana mafi mufi, cigaba da kusantata tamkar kusantan ajalinka ne!".

 Tana kaiwa nan azancen nata ta tsallake ƙafarsa ta wuce. 

Da kallo Saifuddeen ya bita harta ɓacewa ganinsa, murmushi yayi tare da cije laɓɓansa, cikin zuciyarsa yace. 

"Kin gama naki daga yau ɗin saura nawa ƴan mata yanzu lokacina ya fara."

  cikin nutsuwa ya shiga tura kekensa har ya fice daga cikin falon,  koda ya kawo compound ɗin gidan nan ya iske Ya Aminu wanda fitowarsa kenan aɓangaren Baba Malam, ganin Saifuddeen yasanya Aminu cewa.

  "Har zaku tafi?" 

Kai Saifuddeen ya jinjina masa fuskarsa ɗauke da murmushi alaman.

"Eh". kana cikin body language ɗinsa yace "Yanason gaisawa da Baba Malam idan yana gida." 

Murmushi Aminu yayi don sam baigane me Saifuddeen ɗin ke nufi ba, kasancewar ba sosai yake gane body language ba. 

Ganin cewa Ya Aminun bai gane me yake nufi ba, yasanya shi zaro wayarsa daga al'jihu inda yayi rubutu ya miƙawa Ya Aminu'n,  amsan wayan Ya Aminu yayi, koda ya karanta saƙon murmushi yayi, cikin yabawa da hankalin Saifuddeen ɗin yace.  

"Masha Allah, aikuwa Baba Malam na ciki muje sai namaka jagora." 


Ya Aminu ne yayiwa Saifuddeen jagora har zuwa cikin haɗaɗɗen falon na Baba Malam. 


Ganin Saifuddeen yasanya fara'ar dake kan fuskar Baba Malam ƙara faɗaɗa, cikin farin ciki yace.

 "A'a ɗalibina Saifuddeen kaine ke tafe, Masha Allah sannunka da zuwa."  

Murmushi Saifuddeen yayi cikin hikima da ladabi yagaishe da Baba Malam ɗin,   fuska asake Baba Malam ya amsa tare da tambayansa ya bayan rabuwa, nan suka ɗan taɓa hira tsakanin Baba Malam da Saifuddeen, yayinda Ya Aminu ke sa musu baki, Ya Ahmad ne yashigo cikin falon na mahaifinsa, ganin Saifuddeen ya sanyashi faɗaɗa fara'arsa inda suka gaisa amutumce.  Nan suka sake ɗan taɓa hira wanda Saifuddeen ke ɗansa baki ta hanyar body language ɗinsa. 

Wayarsa yaciro inda ya miƙawa Ya Aminu, bayan yashiga text message saƙon da ya tura da kansa ta wayarta ya bayyana akan screen ɗin wayar tasa, koda Ya Aminu yakaranta saƙon murmushine ya faɗaɗa akan fuskarsa cikin jin daɗi ya miƙawa Ya Ahmad, Ya Ahmad ma yana karanta saƙon yasaki wata nannuyar ajiyar zuciya sosai hakan yayi masa daɗi, amincewa da auren Saifuddeen da Zaleeha tayi, abun farin ciki ne agaresu, domin samun nagartaccen namiji kamar Saifuddeen amatsayin suruki cikin zuri'arsu abun alfaharine sosai.

 Miƙawa Baba Malam wayar Ya Ahmad yayi, koda Baba Malam yakaranta saƙon da aka rubuta kamar haka. 

_"Ni ZALEEHA NA AMINCE DA AURENKA Hamma SAIFUDDEEN SABODA HAKA KATURO MAGABATANKA WAJEN BABANA DON ATSAIDA MAGANAR Aurenmu."_


Wani irin ingantaccen farin cikine ya cika zuciyar Baba Malam jin cewa Zaleeha ta amince da Saifuddeen takuma tsai dashi a matsayin gwaninta, cikin tsananin farin cikin daya kasa ɓoyuwa akan fuskar Baba Malam ya ɗago ya kalli Saifuddeen wanda ya sunkuyar da kansa ƙasa, cikin zuciyarsa yace.

  "Nawa wasan ya soma Zaleeha daga gobe idanunki zasu fara kuka kamar yadda kikasa Ummina kuka, kuma Insha Allah ni da kika ƙira Ginannen taɓo kuma dutse, niɗin nanne zan-zamo mijinki!." 


"Masha Allah, Haƙiƙa naji daɗin kasancewar haka sosai Saifuddeen, saboda haka ni mahaifin Zaleeha na baka Zaleeha sannan koda yaushe kashirya kana iya turo manyanka su kawo sadaki don atsaida ranar auren ku da ita!." 


Wani irin tsananin farin cikine suka cika zuƙatan Ya Ahmad da kuma Ya Aminu, shikuwa Saifuddeen faɗan farin cikinsa ma ɓata lokaci ne, domin kallon fuskarsa kaɗai da ƙwayoyin idanunsa sun isa sanardakai farin cikinsa.


Cikin aminci da salama Saifuddeen ya miƙa godiyarsa ga Baba Malam harma dasu Ya Ahmad, nan sukayi sallama cikin mutumta juna har bakin mota Ya Ahmad da Ya Aminu suka raka Saifuddeen saida sukaga ficewar motarsa acikin gidan kana suka juya suka koma wajen Baba Malam don su tattauna yanda bikin zai kasance...


A cikin mota kuwa wani irin murmushi Saifuddeen yayi tare da sake jingina bayansa ajikin kujeran motar,  lumshe idanunsa yayi yana me tunano haɗaɗɗiyar surar jikinta,  tabbas yaƙudurta aransa cewa zai shayar da ita ruwan mamaki, aduk sanda ya aureta kuwa saiya nuna mata cewa NAKASA BA KASAWA BACE...!






                         By

              *GARKUWAR FULANI*



             *NAKASA BA KASAWA BACE*


                            *PAGE 29*


                             *NA*

           *AYSHA ALIYU GARKUWA*


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇



Daga Gidansu Zaleeha kai tsaye unguwar tudun wada suka nufa wato gidan Baba Bello,  aƙofar ɗan madaidaicin gidan na Baba Bello Sule driver yayi parking motar, both ya buɗe inda ya cirowa Saifuddeen kekensa, buɗe murfin motar Saifuddeen yayi, inda dakansa  ya yunƙuro ya hau kan keken nasa. 

Yana gama dai-dai ta zamansa akan keken,  Jafar almajirin Baba bello yafito daga cikin gida, ganin Saifuddeen yasanya Jafar sakin murmushi cikin kulawa yaɗan rusuna tare da cewa. "Hamma Saifuddeen sannu da zuwa."

Murmushi Saifuddeen yayi masa tare da jinjina masa kai alaman.

"Yauwa." 

Cikin sauri Jafar yajuya ya koma cikin gida, nan ya iske Baba Bello dake zaune yasanar dashi zuwan Saifuddeen,  cikin hanzari Baba Bello yazura takalma aƙafansa,  inda kai tsaye yanufi hanyar fita daga cikin gidan. 

Fuska ɗauke da fara'a Baba Bello ya tarbi Saifuddeen,  nan yayiwa Saifudeen ɗin iso zuwa cikin ɗakinsa dake hanyar soro. 

Bayan sun zauna ne Jafar ya kawowa Saifuddeen ɗin ruwa acikin wani babban plastic jug,   kofin ruwan Saifudeen ya ɗauka tare da kaiwa bakinsa, tuno da yanda Zaleeha ta turs masa kayan fruits gabanshi ga kuma tsoronshi cikin ƙwayar idanunta tono hakan ne yasa yayi,  yasanyashi sakin murmushi, ɗan kaɗan yasha ruwan gudun kada Baba Bello yaji ba daɗi, cikin kulawa Baba Bello ya dubeshi kana yace.

  "Sam ban tsammaci zuwanka ba Saifuddeen, ai da nasanya Innar ku (Matar Baba Bello) tayi maka kwaɗon zogale da tumatur, gashi kuma yanzu batanan taje kitso." 

Murmushi Saifuddeen yayi tare  da sadda kansa ƙasa, cikin body language ɗinsa yayiwa Baba Bellon alamar cewa babu komai,  nan suka shiga ɗan taɓa hira da Baba Bellon, inda Baba Bellon ya nuna jin daɗin zuwan Saifuddeen ɗin, domin kuwa tun ranan da suka dawo daga zuwa dubasa da sukayi,  lokacin dawowarsa basu sake haɗuwa ba sai yau ɗin,  hira sukeyi tsakanin magana da kuma body language, inda sosai Baba Bello ke gane yaren Saifuddeen, wato body language, cikin girmamawa haɗi da kulawa Saifuddeen ya labartawa Baba Bello maganan aurensa, kama daga farkon tura masa tambaya har kawo yanzu, cikin hikima yanemi shawarar Baba Bello agame da bikin.

Cikin jin daɗin yanda Saifuddeen ɗin ya karramasa, yakuma maidashi uba, yasanya Baba Bello gyara zama, nan yashiga bawa Saifuddeen ɗin shawarwari masu kyau, sosai kuwa Saifuddeen ya aminta da shawaran, inda ya yanke cewa jibi jibinna za akai masa lefe da kuma sadaki,  sun ɗan jima suna hira daga bisani yayi wa Baba Bello sallama, kuɗi yaciro ƴan bandir ɗin ɗari biyar biyar sabbi ƙal ya ajewa Baba Bello agabansa, cikin dattako da halin kamala Baba Bello yace. 

"Dan Allah Saifuddeen kada kasa kanka awahala, bayan ɗaukemin nauyin gidana da kayi gaba ɗaya kuma saika ƙara da sakanka a wata wahalan? kabar kuɗinka Saifuddeen nagode sosai bani da abinda zance maka sai dai addu'a, domin kuwa koda baka da lfy baka ƙasarma baka daina kulawa damu ba." 

Fuska Saifuddeen ya kwaɓe cikin rashin jin daɗin dawo masa da kyautar tasa da Baba Bello yayi.

fuska  ya marairaice, cikin body language ɗinsa yace.

  

"Dan Allah Baba Bello ka karɓa, kaifa matsayin Uba kake agareni, kamar yanda zanyiwa mahaifina kaima haka zanyi maka.!" 

Jikin Baba Bello ne yayi sanyi, haƙiƙa Saifuddeen yaron ƙwarai ne, samun irinsa na da matuƙar wahala, tabbas Ummi tayi sa'ar haihuwa, domin samun Saifuddeen amatsayin ɗa babban nasara ce ga rayuwa,   haka Baba Bello ya amshi kuɗin nan batare daya soba saidai sanin halin Saifuddeen yasanyashi karɓan kuɗin dole, nan ya rako Saifuddeen ɗin har bakin motarsa, saida Baba Bello yaga tashin motar tasu Saifuddeen kafun ya juya yakoma cikin gida.


Daga gidan Baba Bello kuwa kaitsaye ƙaramar kasuwa suka nufa, abakin kasuwan sule driver yayi parking motar, shida kansa ya buɗewa Saifuddeen murfin motar tare da gyara masa zaman kekensa,  haka Saifuddeen da Sule driver suka kutsa cikin kasuwa,  cikin nutsuwa Saifuddeen ke sarrafa kekensa, duk inda suka wuce  ido ne ke binsu, yayinda mutane da yawa ke yaba tsantsar kyau irin na Saifuddeen, saidai ganinsa akan keken guragu shine abun dake ɗaure musu kai, kowa kallon cikakken balarabe yake yi masa, sam koda wasa babu wanda ya shaida kamannin Saifuddeen, duk acikin mutanen dake kallonsa babu wanda yakawo aransa cewa shine wannan matashin saurayin dake gararanban yawon raba leda, yake kuma yawon raba omo, kana harma da tallan fiyo wata (pure water),  babu wanda zai gansa ayanzu yace shine wannan yaron da yasha gwagwarmayar rayuwa, yayi ta zagaye kasuwa koro-koro luggu da saƙo.

 Fuskarsa ɗauke da annuri ya ƙarasa gaban wawakeken shagon wanda yake mallakinsu, Mudassir da Warisu naganinsa suka taso cikin tsananin farinciki suka tarbeshi,  sam basu tsammaci ganinsa ba don ya matuƙar shammace su,  yaɗan jima kaɗan ashagon nasu Warisu inda suka ɗan taɓa hira kaɗan,   duban Mudassir da Wareesu yayi cikin body language ɗinsa yace.

"Kufara shiri tun yanzu don nanda ƴan sati kaɗan zakusha biki."

Mamakine ya bayyana akan fuskar Wareesu,  daɗan ƙarfi yace.

"Biki kuma na waye?."

Murmushi Saifuddeen yayi tare da nuna kansa. 

Cikin alamun ban mamaki Wareesu yace. 

"Wow Surprise kenan!  Kai amma naji daɗi sosai Allah yasa ayi damu, koya Mudassir, yakamata ne ma ai mufara gagarumin shiri." 

Wareesu yafaɗa cike da farinciki. 

Shiru Ahmad da ya shigo yanzu yayi tare da kafe Saifuddeen da idanu, kallonshi shima Saifuddeen ɗin yayi, yanayin yanda yaga fuskar Ahmad kaɗai yasayashi gane abun dake cikin zuciyarsa,  murmushin daya bayyana kyawawan dimples ɗinsa yayi, cikin son ganar da Ahmad irin yanayin dayake ciki ya lumshe idanunsa, hannunsa yaɗaura adai-dai saitin zuciyarsa wacce ke beating. 

Ajiyar zuciya mai ƙarfi Ahmad ya sauƙe, tabbas ya gane hakan da Saufuddeen ɗin yayi me yake nufi, alamace dake nuna cewa Saifuddeen ɗin nasonta da duka zuciyarsa,  tabbas yana matuƙar jin tausayin Saifuddeen domin kuwa shi tuni yajima da gano cewa Zaleeha ba matar aure bace, ba irinta Saifuddeen ke buƙata ba, Saifuddeen yana buƙatar kamilalliyar mace, nutsatstsiya, wacce ta yarda da ƙaddara tayi imani mai kyau ko akasinsa daga Allah Ne, amma ya zaiyi dolensa zai haƙura da ƙin Zaleeha da yake, sahoda yaga gaba ɗaya soyayyarta ta rufe idanun Saifudeen, ya fahimci cewa Saifuddeen  Zaleeha kawai yake gani aciki da wajen idanunsa, saboda haka zaiyi ƙoƙari wajen manta abun da tayi musu, zai taya Saifuddeen ɗin ƙaunarta, nan yayiwa Saifuddeen ɗin Allah yasanya al'khairi, daga shagon nasu Warisu  kaitsaye Saifuddeen shagonsa ya nufa,  shida Ahmad masha Allah koda yaje yasamu nutane maƙil sun cika shagon, sayan kaya kawai suketayi, yayinda cikin shagon ke shaƙe da kaya tam na yara irin new designer ɗinnan masu kyau, Manyan Hajiyoyine keta business ɗinsu, wasu sayan dayawa sukazo wasu kuwa sayan ɗaɗɗaya , kasancewar shagon cike yake da mutane yasanya Saifuddeen baiwani zauna acikin shagon sosai ba ya tafi,  Kaitsaye shagon Ba mishkila ya nufa, nan ya iske Ba mishkila yau shida kansa ne acikin shagon, ba ƙaramin farin ciki ba mishkila ya yiba dayaga Saifuddeen, nan yashiga tambayarsa jikinsa,  inda ya amsa masa cewa "Dasauƙi sosai"

Daga shagon ba mishkila shagon Alhaji Ishaq baban abokinsa wato Ibrahim ya nufa, sosai Alhaji Ishaq yaji daɗin ganin Saifuddeen, shima sun ɗan taɓa hira inda yayi masa ƙarin ya jiki,  daga shagon Alhaji Ishaq shagon Alhaji Kabiru Saifuddeen ya nufa,  nan fa shima Alhaji Kabirun yacika da murnar ganin Saifuddeen, kasancewar hakan alamace dake nuna cewa sauƙi ya samu ga Saifuddeen ɗin.  Sosai Saifuddeen yaɗan jima acikin kasuwan yayinda ya tsaya yagabatar da sallan Magriba cikin masallacin dake gefen kasuwan, yana idarwa suka kama hanyar dawowa gida. 


Ahankali yake tuk'a kekensa haryakawo cikin falon na ummi inda ya iske Raliya, Hayatuddeen, da kuma Ummi wacce ke zaune akan kujera, Hayatuddeen na zaune aɗan gefe da ita yana latsa wayarsa, Raliya kuwa tsugune take agaban Ummin tana mammatsa mata ƙafa,  murmushin dake kan fukar Ummi ne ya faɗaɗa sakamakon ganin yanda fuskar ɗan nata ke ɗauke da farin ciki,  cikin kulawa tace.

"Saifuddeen kadawo?"

Kansa ya jinjina mata tare dayi mata alama,  cikin body language ya sanar mata cewa daga kasuwa yake.

Murmushin jin daɗi Ummi tayi tare da cewa.

"Allah ya taimaka." 

Duban Raliya tayi cikin kulawa tace. 

"Bar matsamin ƙafannan haka jeki kawowa hamman naku ruwa mai ɗan sanyi yasha."  

"To." 

Raliya tace tare da miƙewa tsaye ta nufi hanyar kitchine ɗin dake cikin falon. 

Hayatuddeen ne ya ɗago kansa, inda ya kalli Hamman nasa, cikin tausasawa yace. 

"Hamma barka da dawo, dama kamar kasan naƙosa ka dawo wallahi."


Murmushi Saifuddeen yayi tare dayi masa alaman meke faruwa?


Gyara zama Hayatuddeen yayi cikin zumuɗin labarin dake cinsa yace. 

"Ina wannan kyakkyawar mawaƙiyan da muka haɗu da ita a jirgi,  lokacin da zamu dawo Nigeria, Hamma ka tuna ta  Asma'u Ahmad Matawalle?." 

Yaƙare maganan yana me tsatstsare Hamman nasa da ido. 


Ɗan jim Saifuddeen yayi tare da ɗan lumshe idanunsa, in few second ya hasasho fuskarta, duban Hayatuddeen yayi tare da gyaɗa masa kai alamar eh ya tunota. 


Gyara zama Hayatuddeen yayi tare da cewa. 

"Yauwa Hamma, wai kasan mene? tun ranan da takarb'i phone number na, kullum sai munyi chart, bata da wani labari sai naka, kullum maganarka take, shine yau tace nafaɗa maka wai tanasonka, zaka aureta?." 


Baki Ummi ta buɗe tana kallon Hayatuddeen, shikuwa Saifuddeen fuska ya yamutsa tare da tab'e baki, wai harshi wata y'ar jagaliya mace mai rawa da wak'a data gama nunawa duniya sirrin jikinta babu hijabi zatace tanaso, bama wannan ba shi ayanda yakejinsa, ayanzu babu wata mace da zaiso, So d'ayane tak kuma Zaleeha yakeyiwa shi, sam bayajin cewa wata mace zata samu matsuguni ko muhallin zama, koda ko abaki-bakin zuciyarsa ne,   d'an madaidaicin glass cup ɗin da cikinsa ke d'auke da lemon exotic,  wanda Raihana ke mik'o masa ya amsa,   da kad'an-kad'an yake sipping exotic juice d'in,  saida yasha kusan rabin cup d'in kafun ya ajiye,  ahankali yatuƙa kekensa inda ya k'arasa har gaban Ummi, hannayensa ya d'aura akan nata tare da langwab'ar dakai.

Murmushi Ummi tayi don hakan da yayi yasa ta fahimci cewa magana me mahimmanci yakeso suyi. 

Cikin sakin fuska Ummi tace.

"Faɗi  duk abun dake ranka Saifuddeen ni me mara maka baya ce akoda yaushe." 

Murmushin jin daɗi yayi inda ya ciro wayarsa daga cikin al'jihun rigarsa,   duk wani abun dake cikin rai da zuciyarsa haɗi da duk wani ƙudirinsa saida ya rubuce shi cikin text message, miƙawa Ummi wayar yayi inda ya sunkuyar da kansa ƙasa, karɓan wayar Ummi tayi cikin nutsuwa ta shiga karanta abun da Saifuddeen ɗin ya rubuta,  wata irin sassanyar ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe alokacin da ta gama karanta saƙon nasa, murmushine ya bayyana akan fuskarta take kuma sai ga hawaye sun cika idanunta, sosai rauninta ke ƙoƙarin fallasa sirrin zuciyarta, hannayenta tasanya ta ɗago haɓarsa, cikin son ƙarfafa masa guiwa ta shafi gefen fuskarsa, cikin yanayi na tausasa murya tace. 

"Dama nasani ɗana bazai taɓa zama rago ba, haƙiƙa kai ɗin jarumine, haka kuma babu wata ƴa mace da zata so yin asararka." 

Ɗan numfasawa tayi tare da sauƙe ajiyar zuciya akaro na barkatai. 

"Nayi matuƙar farin ciki Saifuddeen, haƙiƙa ganin aurenka yana ɗaya daga cikin burukan rayuwata,  Allah Ubangiji yasanyawa tarayyarku albarka!."

Ummi tafaɗi haka cikin tsananin farin ciki, sosai takeson abun da Saifuddeen ɗin ke so, saboda farin cikinsa itama shine nata. 

Cikin samun nutsuwar zuciya Saifuddeen ya ɗaura kansa bisa kafaɗan mahaifiyar tasa, cike da ƙaunarta  yayi mata alaman godiya, ahankali tashiga shafa kansa, tana mejin farin ciki aranta, lallai dole ta-tayashi wajen ganin ta ƙawata bikin ɗan nata. 

Hayatuddeen da Raihana kuwa idanu kawai suka zuba musu,  aƙalla Saifududdeen yaɗauki kusan 4 minute kansa na bisa kafaɗan Ummi, kafun daga bisani ya janye, cikin nuna alamun gajiya ajikinsa yace da Ummin nasa zaije yaɗan watsa ruwa.  


"To." Ummi ta amsa inda tace dashi Hayatuddeen zai kawo masa abinci. 


Hayatuddeen naganin wucewar Hamman nasa ɗaki ya zaburo, cikin tsananin gulman dake cinsa yace.

"Ummi wani abu ya farune naga kunata farin ciki keda Hamma?".


Murmushi Ummi tayi tare da cewa.

"Banason gulma fa Hayatuddeen."

Baki Hayatuddeen ya turo gaba. 

Raliya ce ta gyara zama tare da cewa.

"Ummi ai ba Hayatuddeen kaɗai bama nima ina son ji, dan Allah Ummi menene, ko akan maganan aurensa ne?"


Dariyan yaran nata ne ya kamata, cikin kulawa tace. 

"Yarinyar da Hammanku yakeso ta amince dashi, harma ta bashi daman turo magabatansa don atsaida maganan aure,  yanzu haka mahaifinta ya amince, mu kawai ake jira mukai lefe da sadaki asaka ranar aure!." 


Wani irin ihun daɗi Hayatuddeen yayi tare da miƙewa tsaye, cikin tsananin farinciki yace. "Yessss!! Lokacin yazo!."


Raliya ma tashi tsaye tayi cike da murna tabawa Hayatuddeen hannu suka tafa, cikin jin daɗi da farin ciki tace. 

"Masha Allah, ae kuwa za ayi biki irin wanda ba'a taɓa yiban zaton mai nakasa zai yishiba acikin garin Gombe." 

Sake tafawa da Hayatuddeen sukayi cikin jin daɗi Hayatuddeen yace. 

"Yanzune jama'ar cikin garin Gombe zasu san cewa akwai manyan yara masu tasowa, na rantse Adda Raihana saina baku mamaki, saina nunawa Hammana cewa idan yana dani bashida damuwa a duniya!."  

Yaƙare maganar yana me jujjuyawa, tare da soma yin rawar shaku-shaku.

Dariya Ummi da Raihana suka saka, don abun na Hayatuddeen ya wuce tunaninsu, ganin hayaniyan su Hayatuddeen ɗin na ƙoƙarin damunta yasanya ta miƙewa ta koma ɗaki bayan tace da Hayatuddeen ya kaiwa Saifuddeen ɗin abincinsa,  tana shiga ɗaki ta dannawa number'n Adda Rahama ƙira, bugu biyu Adda Rahama dake kwance jikin Dr Adnan suna shan love ɗinsu ta ɗaga wayar, cikin son dai-dai-ta nutsuwarta tace. 

"Ummi barka da dare." 


Murmushi Ummi tayi tare da cewa.

"Barkanki dai, fatan kuna lafiya baki ɗayanku." 

Da "Lafiya ƙalau." Adda Rahama ta amsa mata. 

Gyara zama Ummi tayi,  take tashiga labartawa Adda Rahama maganan auren Saifuddeen ɗin da ta taso lokaci ɗaya.

Hmmm faɗar irin tsananin farin cikin da Adda Rahama tasamu kanta aciki ma ɓata lokaci ne, sosai taji daɗin labarin nan tace  zata tambayi Dr Adnan gobe idan yabarta zatazo gidan, da haka sukayi sallama ita da Ummin nata,  cikin ɗoki haɗi da marari ta rugume mijin nata ƙam-ƙam, fuskarta ɗauke da farin ciki tace. 

"Yaya Adnan Saifuddeen zaiyi aure,  ina cikin tsananin farin ciki wallahi, nasan shima zai samu salihar mace wacce zata kawar masa da duk wata damuwarsa!." 


Cikin jin daɗin labarin Dr. Adnan yasake hugging ɗinta,  dogon gashin kanta ya shafa, tare da sanya hannuwansa ya ɗago haɓanta,   ido cikin ido suke kallon juna cikin nuna jin daɗinsa yace. 

"Alhamdulillah lallai zamusha biki, masha Allah mun kusa zama surukai!."

Murmushi Adda Rahama tayi tare da cewa. 

"Farin cikina bazai faɗu ba Ya Adnan, akullum da tausayin Saifuddeen nake kwana nake tashi, raunin Saifuddeen raunina ne,  naji daɗi matuƙa saboda nasan shima ayanzu zai samu gamsuwa irinta aure!." 

Murmushi Dr Adnan yayi tare da jan dogon hancinta cikin salon tsokana yace. 


"Hmmm irin wato ke kinsan gamsuwar aure ɗinnan ko?" 


Dariya suka sanya atare, cikin yanayi najin kunya ta ɓoye kanta acikin ƙirjinsa,   sake matseta yayi cikin raɗa yace.

"Dama kuma nima gashi yau inada buƙatar wata gamsuwar, ke ma kinsani bana taɓa gajiya dake!."  yafaɗi maganar yana me haɗe bakinsu waje ɗaya. 


                      ***

Fitowarsa daga wanka kenan, wata brown jallabiya yasanya ajikinsa, tattausan darduman sallansa ya shumfuɗa inda ya gabatar da sallan Isha, kana kuma ya gabatar da sallan shafa'i da wuturi, yajima zaune akan sallayan yana addu'o'i har Hayatuddeen yakawo masa abinci ya fita, bai idar ba,  cikin nutsuwa yajawo kekensa, cikin  yanayi na ɗan dabara daya saba ya zauna akan lafiyayyar keken nasa,  food flask d'in da Hayatuddeen yakawo yashiga bubbud'ewa,  kulan farko daya bud'e yam balls ne aciki wanda yaji kayan ƙamshi da kuma ƙwai, sai kuma sauce ɗin egg and onion da akayi musamman don cin yam balls ɗin dashi, ɗayar kulan kuwa pepper chicken ne aciki wanda yaji curry da kayan ƙamshi,  gaba ɗaya ƙamshin abincin ya cika ɗakin,  pepper chicken ɗin yaɗan ɗiba kaɗan a plate,  wani ɗan madaidaicin flask ya jawo wanda ke ɗauke da tafashashshen coffee,   ruwan coffee ɗin wanda yaji kayan ƙamshi ya zuba acikin wani ɗan madaidaicin cup,   bawani sosai yaci naman ba saidai ace ba laifi, coffee ɗin nema yasha sosai, minti 10 da gamawa Hayatuddeen yazo ya kwashe kwanukan yafita dasu,  kekensa ya tura inda ya nufi bathroom,  kaitsaye gaban ɗan madaidaicin sink ɗin dake cikin toilet ɗin wanda yake dai-dai tsawonsa ya nufa,  yana daga zaune akan keken nasa yayi brush, yayinda ya sake ɗaura sabuwar al'wala ajikinsa, don sam hakanan yake baya wasa indai wajen zama da alwala ne shi gwanine awannan fannin, domin yawan zama da alwala ma wata babban kariyace ga bawa. 


Cikin hikima ya hau kan gadonsa tare da rage gudun AC'n dake ɗakin, luf yayi akan gadon nasa tare da fidda wani irin numfashi,    lumshe kyawawan idanunsa yayi yana me imagine kyakkyawar surarta acikin idanunsa,  kyakkyawan murmushine ya bayyana akan fuskarsa, sakamakon tunawa da yayi da yanda ɗan ƙaramin bakinta ke motsawa,  alokacin da take surfa masa ruwan masifa,  komai nata me kyau ne, haka kuma komai nata gwanin burgewa ne,  harshensa ya sanya yaɗan lashi laɓɓansa wanda suke cike da muradin jinsu akan nata laɓɓan, wani irin so yakewa Zaleeha wanda shikansa baisan iyakarsa ba,  yanason Zaleeha fiye da duk yanda wani zaiyi tunani,   sake gyara kwanciyarsa yayi tare da sakin wani killer smile, wani irin nishaɗine yakejin ya cika zuciyarsa,  kalmar

"Maye." da ta ƙirasa dashi shine abun daya dawo cikin brain ɗinsa. 

cikin ƙasan zuciyarsa yace.

"Am so sorry My Beautyful Wife, dama kin sani da bakicemin maye ba, don kuwa gashi yanzu kinjawo dole saina nunamiki cewa eh da gaske niɗin maye ne." 

Cikin wani irin azababben shauƙin sonta haka bacci ɓarawo ya ɗaukeshi.


Gaba ɗaya ko ina dake cikin gidan nasu ya ɗauki shiru,  a irin wannan lokacin mafi yawancin mutane kowa na kwance ne a makwancinsa, yayinda wasu ke gudanar da baccin nasu cikin yanayi mai daɗi, saɓanin wasu kuwa da sukeyinsa cikin rashin yanayi me daɗi, adai-dai wannan lokacin cikin waƴanda suke bacci cikin rashin jin daɗi hadda Zaleeha domin kuwa duk sanyin dake cikin ɗakin ita gumi ne ke fesowa daga jikinta. 


Binsa takeyi cikin sauri ayayinda ko takalma babu aƙafanta, ƙoƙarin cimmasa take amma yana ƙara yi mata nisa, bayansa kawai take iya hangowa kasancewar ya bata baya, cikin ƙosawa haɗi da gajiyawa ta tsaya tare da sanya hannuwan ta duka biyu ta kama ƙugunta, cikin tsananin gajiys muryar dake bayyana rauninta tace. 

"Dan  Allah katsaya, katsaya atare dani, barinka cikin rayuwata tamkar rabani da numfashina ne, tayaya zaka gane irin sonda nake maka? shin tayaya zaka gane cewa ina buƙatarka cikin rayuwata, Dan Allah kazo, katsaya nazo gareka!!." 


Cak ya tsaya daga tafiyan da yakeyi, amma saidai ko motsawa baiyi ba balle tasa ran cewa zai juyo ta kalli  fuskarsa. 

Ahankali tashiga takawa zuwa garesa, taku biyu kacal ya rage taƙarasa garesa,  ahankali yaɗan juyo gareta,  idanunta ne suka sauƙa akan kyawawan laɓɓansa wanda ke ɗauke da kalar red, yayinda wasu kwantattun gargasa sukayiwa bakinnasa ƙawanya, wani irin sheƙi da shinnig gashin dake kwance akan fuskar tasa keyi, idanunta taɗaga daniyar kallon full face ɗinsa, kafun ta sauƙe ganinta akansa wani irin haske wanda batasan daga ina yafito ba ya cika gaba ɗaya idanunta. 

Azabure ta-tashi daga baccin da takeyi, cikin ƙaraji tace "Dan Allah kada katafi pleaseee help me!!!." 

Buɗe idanunta wanda suka kaɗa sukai jajur tayi, lokaci guda wani irin gumi ya shiga keto mata,  ƙirjinta ne yashiga bugawa da sauri sauri,    aƙalla taɗauki kusan 3 minute kafun taɗan soma dawowa cikin hayyacinta gane cewa mafarki take yasanyata sakin kuka mai ciwo, jikinta ta takure waje ɗaya tare da cusa kanta tsakankanun cinyoyinta, kuka take rerawa sosai mai ɗauke da tsanin ciwon so, cikin rufewar ido haɗi da sambatu tace. 


"Shikenan  katafi kabarni? yazanyi? shin tayaya kake tunanin zan iya jure rashinka? nazautu akan sonka, nakai ƙololuwa,  nazama kurma, makauniya,  har wasu suna mini kallon zautacciya duk akan sonka,  Ina sonka! Ina sonka! Ina tsananin sonka!!!."  Taƙare maganar tana me rushewa da kuka, sosai Zaleeha tayi kuka awannan dare har da shiɗewa,  daƙyar ta iya jan jikinta ta wuce toilet, wanke fuskarta tayi kana ta ɗauro alwala, sosai wani irin zazzafan zazzaɓi da ciwon kai suka rufeta asakamakon kukan da tayi, wata zumbuleliyar hijab ta sanya ajikinta, inda ta hau kan shunfuɗaɗɗen dardumanta, cikin tsananin ciwon da kanta keyi mata tagabatar da sallan Nafila raka'a huɗu,  zama tayi akan praymad  tare da jingina bayanta da jikin bango, idanunta ta lumshe, ahankali wasu zafafan hawaye suka shiga kwaranyowa daga cikin idanun nata, ji take kamar zuciarta zata fashe saboda soyayyarsa, ashe dama haka so yake? ada taɗauki batun so wasa sai gashi kuma yanzu yana shirin yi mata ɓarin kwan makauniya, haƙiƙa gangar jiki da zuciyarta na azabtuwa, Inama da ace yin so baizama ɗaya daga cikin Ƙaddarorinta ba,  kuka tacigaba dayi sannu ahankali wani wahalallen bacci ya samu nasaran ɗaukarta..


Kamar yanda ya ƙudurta aransa hakance ta kasance, zuwa yanzu yasanar dasu Baffa Ali gaba ɗaya abun dake faruwa.


5 million ya ware daga cikin ribarsa,  ayau yau yake da buƙatar haɗa kayan lefe, inda Baffa Ali yace ya ɗauke masa nauyin biyan sadaki. 

Aunty  Kubra matar yayan Abokinsa Jabeer dakuma Adda Rahama sune suka shiga cikin babban kantin nan na San Hussain Super Market don haɗo masa kayan aure nagani na faɗa,  dayake Aunty Kubra cikakkiyar ƴar kasuwace kuma sana'anta kenan saida kayan mata, hakan yasanya sosai ta darje wajen zaɓo zafafan lesuka, atamfofi, shaddodi, materials,  dakuma tsadaddun yadukan boyels na mata, kaya sosai suka saya masu tsananin tsada don kuwa kaf cikin kayan nasu babu wanda kuɗinsa yayi ƙasa da dubu Hashirin talatin dai arba'in dai  kana hamsin, ɓangaren jakakkuna da takalma kuwa ba acewa komai domin kuwa kaya suka saya masu kyau da inganci.

sashin yan kunnaye da awarwaro haɗi da saraƙa kuwa komai na gwal suka saya,   ɓangaren takalma da jaka kuwa ko wani takalmi da mayafinsa, kana kuma da kalan kayansa, materials, lace, atamfa ko boyel,   sashin ƙananan kaya kuwa abun ba'acewa komai, ɓangaren dogin riguna kuwa saida suka cika akwatuna biyu tam da dogin riguna masu kyau da tsada, domin kaf cikin rigunan babu ta ƙasa da 30k, kaya kam dai sun haɗu sosai, musamman ɓangaren kayan meckup sun kashe kuɗi sosai, musamman suka sayi meckup kit har guda uku,   masha Allah kaya ya haɗu sosai inda aka shirya kayan cikin akwatuna, tsab kayan suka ɗauke gaba ɗaya akwatuna 24 dozin biyu kenan sai guda shida da akasa kayan uwa da uba a akwati sauran ukun kuma akasa na dangi shine ya bada akwati 30  da suka saya.   Koda suka dawo gida kowa saida ya yaba kayan domin anyi abu wanda sam babu ƙaranta aciki, ko ƴar Gwomna aka kaiwa ba laifi.   ya ware Million uku da rabi ya bawa Salisu, tare da cewa ya kawo mishi dan ƙareriyar mota mai kyau ta mata irin wacce ake yayi. 


Shima Salisu nan yayi tasa bajintar, inda ya kawo haɗaɗɗiyar mota har ta million huɗu.


Can cikin gida kuwa tuni su Adda Rahama, Aunty Mina, Aunty Kubra, matar yayan Jabeer, da Goggo Dada, da  Hajia Rabi matar Alhaji kabiru duk suna cike a parlour Ummi, musamman sukazo don kai lefen Saifuddeen. 


Hayatuddeen da abokanshi Imran da Sulaiman ne suka shigo da kayayyakin. 

Wanda Ahmad yake matuk'ar jin takaici da bak'in cikin yawan kuɗaɗen da aka ɓatar akan yarinyar da ba mutunci ne da itaba. 


Gaba ɗaya sun cika da mamakin irin Yanda Saifuddeen ya narka kuɗi wajen ƙawata kayan, 

Hajia Rabi ce tace. 

Sam baza'a kai kayan nan duka ba dole a rabashi biyu, ai wanna almobazzaranci ne. 

Ita dai Ummi shiru tayi tare da danne ainihin abinda ke ranta wanda babu mahaluk'in da zai gane meke cikin ranta. 

Aunty Kubra ce tace a a banda dai a raba biyu kam, 

dan ita bata son harkan ƙaranta, 

ita da tasoma a Dubai zasu haɗo lefen dan dai kawai abin yazo a ƙurarren lokaci ne, ta nace dole saida aka rarrage wasu abubuwan wasu kuma tama hana fir.


A gidan Baba malam kuwa tun jiya da yamma da Dirankadi ya shaida mishi gobe fa za'a kawo komai da komai kama daga gishiri goro da lefe da kayan rufi da sadaki, 

duk zasu kawo a tare sai ya gayawa Mamy. 

dan Mama yanzu ko Magana bata mishi, shiyasa shi kuma ya shareta dan ya bata iya matsayinta na uwa so yanzu dole ya nuna mata koda ita ko ba ita dole nefa zai aurar da yarsa ga wanda takeso, ya ga kuma ya dace da ita. 


Daga nan ya ƙira ƙanwarshi Goggo Maryama ta kwarar Maryam yayar Zaleeha kenan. 

Kana ya sanar da ita Maryam ɗin. 

sannan matar abokinshi Malam Adam itama tazo, 

sai Maman Ya Aminu matar yayanshi kenan, 

ga Lubna matar Ahmad nan fa Lubna da Maryam suka shiga kitchen tunda safe

suka fara shirya abin tarban baƙi, waƴanda za abawa ƴan kawo lefe da kuma abinda za'a basu su tafi dashi gida, kamar yanda al'adar Gombawa take. 

Mommy matar malam Adam ƙawar Mamy mace mai sauƙin kai gata ta iya girki da kala-kala kasancewar shuwa arab ce. Tana matuƙar son Zaleeha haka itama Zaleeha duk cikin matan abokan Baba malam  da suke ƙawayen Mamy tafi sonta. 


Sosai suka shirya komai cikin manya-manyan food flask masu azabar kyau, 

yayinda tuni sun cika fridge da ƙawatattun drinks. 


Mama kuwa dama yau tunda sanyin safiya ta tafi Doho gidan yayarta Ruda da takebi wacce itama arniya ce dan duk zuriyar Mama ita kaɗaice ta musulunta sai ƙanwarta mai binta, 

wacce ta sauya suna daga Rebeka ta dawo Aisha. 

tana nan cikin Gombe da mijinta da yaranta Aisha macece mai nitsuwa da kamala sau da dama tana dakatar da yayar tata daga aikata wasu mugayen ɗabi'u da sukafi dacewa da masu aljihun baya.

Yayinda Ruda kuwa ke ingizata. 


Ƙarfe uku da rabi  na yammaci dai-dai,

Salisu yazo da Matarsa Sadiya da zazzafar motarsa,

Kana Ahmad ya d'auki motar Saifuddeen, 

sai kuma Aunty Kubra da Jabeer yazo ya amshi tuk'in haɗaɗɗiyar motarta ƙiran babbar vibe, 

sai kuma Motar Ishaq da direbanshi. sai Motar ya Adnan. Sai dalleliyar mota kirar kia samfurin bugun 2019, wacce take baƙa mai Shek'i dan har an kawo fara Saifuddeen yace, 

ai ita farar macece dan haka baƙa za'a kawo mata, don haka dole aka canzo aka kawo mata kalar da yake so ɗin.

Nan duk suka kwashi kayan suka shirgeshi cikin motar kana aka bawa Muddasir Key ɗinta yaja.


A jere-a Jere suke tafiya yayinda, 

Hayatuddeen ke cikin motar Aunty Kubra, 

yana gaba gefen Ya Jabeer. Ita kuwa Aunty Kubra ita da Aunty Mina suna baya. 

Imran kuwa motar ya Adnan ya shiga yana gaba kusa dashi baya kuma Adda Rahma ce da Goggo Dada.

Sai motar Saifudddeen da Ahmad ne  aciki,Raliyanshi na gefenshi, 

tana ta son sama mishi farin ciki dan ta lura sam shi baya wani farin ciki da abun. 


Sai Hajia Rabi dage gefenshi wacce itama sam bata farin ciki da abin sabida Hayatuddeen yana gaya mata komai. 

sai motar ishaq wacce ba komai a ciki shiyasa shida Saifuddeen suka shiga baya direbanshi yaja, 

suka nufi can k'ungiyar tasu. 


Shima Ahmad sam baiso zuwaba to ya zaiyi dole yaje.


Su kuwa masu kai lefen.

Suna isa bakin Gate ɗin gidan mai gadi ya wangale musu gate inda suka kutsa cikin gidan cikin nutsuwa, 

bayan sun gama yin parking ne. 

Ahmad ya fito ya nufi wurin mai gadin, 

hannu ya bashi suka gaisa sannan yace mishi ya shiga cikin gida yace bak'in sun iso. 

Cikin mutuntawa mai gadin yace to tare da juyawa ya shiga cikin gidan. 


Jim kaɗan ya fito yace.

Ance su isa.


Nan duk matan suka shiga su kuma mazan duk suka zauna cikin motocin. 


Suna shiga cikin gidan Maryam tayi musu jagora har babban parlour Mama duk da bata nan dole a bata matsayinta na uwa. 

Bayan sun zazzauna, an gaisa cikin mutun taka, an kawo musu drinks da snacks, sun ɗan taɓa abin sha. 

Hajia Rabi ce ta gyara zama tare da cewa. 

"Raliya je kice Imran Suleiman da Hayatudeen su shigo da kayan."

A hankali ta mik'e tare da cewa.

"To."


A tare suka shigo duk suna riƙe da akwatuna harda ma'aikatan gidan, 

haka suka dinga shigowa da haɗaɗɗun akwatunan cikin falon, saida suka ƙare 

sannan suka juya suka fiti suna haki,  dan sosai akwatunan suke da nauyi kasancewar kowanne ashaƙe yake da kaya. 

Aunty Kubra ce ta kalli Raliya dake riƙe da ɗan Maryam tana mishi wasa, 

tace. 

"Ke ƙanwar ango ai bakici ta zama tashi ki nuna musu kayan."

murmushi tayi tare da cewa. 

"To Aunty Kubra amman dai a tayani."

Murmushi sukayi baki ɗaya ganin yadda taketa kiciniyar bubbude akwatunan, 

tare da cewa. 

"Wannan turamene a ciki wannan laces, wannan shadda wanna boyel."

sai kuma ta fara jawo na ƙananun kaya dana kayan shafa wanda ta buɗe akwatuna biyu wanda suke cike maƙil da ababen shafawa na kwalliyar jiki irin na mata.

Da sauri Mommy matar Malam Adam tace.

"Masha Allah. Gsky ki huta kawai, wannan ai yafi ƙarfinki muma masu gani har mun gaji, 

wani abun ai bazai ganuba, 

sai dai muce Allah ya sanya al'khairi yasa al'barka a ciki."

Aunty Lubna kuwa kai kawai take jinjinawa domin idonta ya raina fata, 

nakasasshen da ake zatawa riƙe ƙoƙon bara da bin kwararo lungu da saƙo yana allazi wahidin, 

shine da wannan kayan lefe wanda ita dai a iya ganinta lefen Zahra buhari ne kawai ta taɓa gani wanda zatace yafi wannan, a dai gani da idonta. 

Goggo Maryama kuwa tausayi suka bata ganin irin ruwan dukiya da suka binne a kan yarinyar da ta sani tabbas uwarta bazata barta ta zauna a gidan Saifuddeen ba.

Mamy ma tabbas tausayinsu taji ganin yadda sukayi ɓarin naira. 

Maryam kuwa sai addu'a takeyi a ranta tana cewa.

"Ya Allah ka rufa mana asiri, 

ka hana mahaifinmu jin kunya da tozarta,  ya Allah ka tausasa mana zuciyar wannan baiwar taka Zaleeha kasa tayiwa mahaifinmu biyayya ta zauna lfy da mijinta da yan uwanshi."

sosai Maryam ke jin tsoron abinda zai zubarwa mahaifinsu darajarsa da mutuncinsa.

Adda Rahamace ta ɗanyi dariya kana ta jawo ɗan kit ɗin  da saraƙuna suke ciki, ta buɗe  babban gwal ɗin da Saifuddeen ya saya  a India ta zaro ta miƙawa Mommy dake kusa da ita cikin sanyi tace.

"To ga wannan ko za'a adanashi da ban, duk da cewa sauran ma gwala gwalaine amma shi tsadansa dabanne."

sosai Mommy ta girgiza da girma da darajan gwal ɗin, mai surki da ruwan farin zinari.

amsa tayi tare da miƙawa Mamy, 

mamakinsu ya ƙaru ne lokacin da Aunty Kubra ta miƙawa Aunty Lubna car key ɗin kia d'innan tare da cewa. 

"Ga wannan Key d'in motar amaryarmun ce, 

motar tana nan waje.

zuwa yanzu fa Mamy abin ya fara zarta zatonta cikin dattaku da nitsuwarta da iliminta tace. 

"Anya kuwa, gsky Malam zaiyi faɗa in muka karɓi abubuwan nan, ko lefen ma in ya gani zaiyi faɗa."

Da sauri Goggo Dada da Aunty Kubra sukace. 

"Dan Allah da manzonsa kar muyi haka daku,

Saifuddeen bazaiji daɗiba tunda shi ya gani zai iya yiwa matarsa komai, 

kuma abinda nanda wani ɗan lokaci ta zama matarsa."

Murmushi Aunty Lubna tayi tare da cewa. 

"Kuma shi za'ayiwa kolliyar ba."

Ta ƙarishe mgnar tana kallon Aunty Kubra wacce bazata wuce sa'arta ba. 

da sauri Aunty Kubra tace.

"Ato kunga ai kanshi yayiwa tanadi, mutun da matarsa."

Goggo Maryama ne tace. 

"To mu dai tunda kunce dan Allah da manzonsa to zamu amshi kayan, 

saura mgna kuma tana wurin Yaya Malam."

Hajia Rabi ce tace. 

"Shima anjima da dare za'a kawo sadaki fatanmu Allah yasa, 

a saka bikin nanda mako ɗaya."

Amin Amin sukace baki ɗaya.

Maryam ce tace. 

"ai kam naga alaman Saifuddeen ya zaƙu yana son matarsa nan kusa tunda gashi harda kayan rufi kuka kawo."

Cikin sakin fuska Adda Rahma tace. 

"Sosai makuwa ,ai shi ko yau ya sameta yana so."

Daga nan suka ɗan taɓa hira sannan suma miƙe tare da cewa. 

"To mu zamu tafi sai kuma in munzo ɗaukan amaryarmu."

Da sauri Mommy ta kalli Maryam da Lubna ta musu alamun su ɗauko food flasks ɗin dake cike da ababen mƙulashe. 


Ganin sunata cika musu kulolin a gabansu yasa, 

Goggo Dada cewa.

"wannan abu yayi yawa ku barshi."

da Saudi Goggo Maryama tace. 

"A a ai yaba kyauta tukuici, ku barmu muma muyi iya iyawarmu."

Hajia Rabi ce ta kalli Mommy matar Malam Adam dake miƙa mata damin kuɗin tukuicinsu rafa guda shida yan dubu daddaya. 

A hankali tace. 

"Hajia wannan kuɗin kuma na menene duka?."

Cikin salon girma ba batun ƙaramta Mommy tace. 

"Yaba kyauta tukuici, ba ku muka bawa ba yaran da suka shigo da kayan muka bawa."

Akan dole su,suka karɓa, nan Aunty Lubna taƙira biyu daga cikin masu aikin gidan Baba Malam ɗin suka shiga jidan food flask ɗin suna kaiwa cikin motocin da su Adda Rahama suka zo dashi.


Har bakin gate suka rakosu baki d'ayan su, 

aka rabu cikin mutunci da jin dadi.


Bayan sun koma cikin gida ne,

Aunty Lubna ta kalli Maryam tare da cewa. 

"Ke zo muga kayannan da kyau,".

Dariya Maryam tayi kana ta matso ta fara bubbud'e akwatunan, Mommy, Mamy, goggo Dada kuwa suma zama sukayi suna kallon kayan d'aya bayan d'aya. 

yayinda tuni Aunty Lubna keta viewing tana d'aukan komai a zazzafar wayarta. 


Sune basu gama ba har aka kira sallan magrib, dole suka hak'ura suka k'arisa kallon a gaggauce kana suka rufe komai, 

suka shirgeshi a cikin d'akin Mama, 

kana duk sukayi al'wala dan gabatar da salla.


Bayan sunyi sallah harda na isha, 

sukaci abinci, 

sukaci gaba da hira, 

dan Maryam jira take mijinta ne zaizo ya d'auketa hakama Mommy Malam Adam ne zaizo ya d'auketa,

Goggo Maryama kuwa Ya Ahmad ne zai maidata gida. 


Baba Malam kuwa, tunda yamma yake gidan Malam  Adam, 

dan amaryarshi bata zoba. 

Ya Ahmad kuwa da Ya Aminu tunda safe suka tafi dukku kai ziyara dan Ya Ahmad ya kusa komawa  Abuja.


Saida akayi sallan magriba suka dawo, 

Kai tsaye parlour'n Baba Malam suka nufa, 

nan Maryam ta kawo musu abinci, 

bayan sun gama cine sukayi al'wala suka nufi masallaci a nan suka samu Baba malam da Malam Adam. 

Koda aka idar da salla tare suka shigo cikin gida.


Suna shiga bada dad'ewa ba, 

Dirankadi da Bappa Ali da Malam Ashiru suka iso harabar gidan. 

Dirankadi ne ya kira Baba malam ya shaida masa isowarsu, 

jin haka ya kalli Ahmad tare da cewa. 

"Ahmad tashi kaje ka shigo da iyayen Saifuddeen."

Cikin tsananin girmamawa da sanin darajar mahaifa Ahmad yace. 

"To." sannan ya miƙe tsaye ya fita.

Yana zuwa yayi musu jagora har zuwa parlour'n Baba Malam ɗin, sunyi farin cikin ganin juna sosai. 


Bayan sun gaisa ne tare da ɗan taɓa hira, 

sai Bappa Ali ya ɗan gyara zamanshi tare da yin gyaran murya kana ya fito da damin kuɗi kimanin dubu ɗari cas, 

daga cikin aljihun babbar rigarshi, 

miƙa kuɗin yayi wa Malam Adam tare da cewa. 

"To ga aiken ɗana Saifuddeen ga sadakinshi."

cikin sakin fuska Malam Adam ya karɓa tare da cewa. 

"Masha Allah. Allah ya sanya al'khairi. Yasa ayi damu."

"Amin Amin."  suka amsa baki ɗaya,

sai kuma suka kalli Dirankadi da yace. 

"Tofa ɗalibin naka yace yanzu sauran a saka masa rana kawai."

Murmushi mai kama da dariya sukayi baki ɗayansu, sannan

Malam Adam ya kalli amininshi Baba malam da yaketa murmushin jin daɗi yace. 

"To Malam Bashir me kace kan batun saka ranan?."

Kanshi ya ɗan rausayar ya kalli babban ɗanshi mafi soyuwa a zuciyarshi, kana kuma ɗansa mai tsananin biyayya da kare mutuncinsa,

sannan ya kalli ɗan ɗan uwanshi kuma surkinshi mai kare daraja da martabar ahalinshi wato Ameenu kenan, yace.

"To ga yayun Zaleeha nan mu basu dama muga irin dattakunsu mana."

da sauri Ahmad ya ɗago kanshi ya kalli mahaifin nashi sai kuma yayi sauri yayi ƙasa da kannasa tare da cewa. 

"Baba malam in dai kuna raye ai mu bamu da bakin mgn, sai abunda kukace."

sosai Ahmad ke burge su Bappa Ali yanayin biyayyarsa tamkar Saifuddeen.

malam Adam ne ya ɗan kishin giɗa kana ya kalli Ahmad da Aminu yace. 

"To Ahmad mu ɗin tabbata zamuyi ne?."

A hankali ya jujjuya kanshi yana mai jin tsoron randa zai rasa iyayenshi. 

Shikuwa Malam Adam cigaba yayi da cewa. 

"To kaga shiyasa muke jawoku a jiki dan mu nuna muku yadda ake aiwatar da komai na jagoranci, 

a matsayinku na manya wanda dole wata rana kune a madadinmu,

yanzu dole zamu so muga yanayin dattakunku,  tunda dai kusan komai kuma kunga an kawo ko wani abu na al'ada kama daga gishiri da goro da lefe da kayan rufi, kana yanzu kuma kunga sun gabatar da abinda shariya ta zantar sun kuma buƙaci a saka ranar biki, 

to yanzu dattakunku muke son gani,

kai Aminu kaine Babba kan Ahmad yaushe nene kakega za'ayi bikin?."

A hankali Ya Aminu ya ɗan rusunar da kanshi sai kuma ya kalli Ahmad, 

kusan a tare suka haɗa baki wurin cewa.

"Ashirin da bakwai ga wata mai kamawa. Yayi ko?."

A hankali Baba malam ya fidda sassauƙan numfashi tare da cewa.

"Yayi kyau,  to Amman meyasa har wata ɗaya, baku shirya bane?."

Cikin nitsuwa Ahmad ya kalli mahaifin nashi tare da cewa. 

"Eh to Baba malam mun shirya amman bamu gama shirin ba. 

Nanda kwana biyar zan koma Abuja, 

sannan inada zirga-zirga tsakanin ƙasashe da dama Dubai, India, US,  Korea, Egypt. Yanzu dai in na fita zan ɗan kwana biyu kafin in karkato Nigeria, kuma inaso inyiwa Zaleeha kayan ɗaki mai kyau zan bata zabi kayan ƙasar da takeso,

zan gama saya mata komai a online sannan nasan cikin sati biyu jirgi zai iso dasu nan, 

to shiyasa nake son ya kai wata ɗaya."

murmushi Dirankadi yayi tare da cewa. 

"Yaran zamani ku dai kunfi yarda da kayayyakin ƙasashen turawa, sam kun Kasa tsayuwa ku inganta mana na ƙasarmu yadda zamuci gaba muma, yanzu jihar gombe wanne irin kayane babu?.

Duk fa arewacin ƙasarnan babu jihar da ta kai jihar Gombawa yawan kafintoci da ci gaban kafintoci. Babu irin samfurin kayan ƙasar waje da basa iya sarrafawa,yanzu konan cikin Sahaja Ventures kuka shiga ae akwai kaya masu kyau da inganci, wasu ma harsun ɗarawa kayan waje kyau."

Malam Ashiru ne ya amshi zancen da cewa. 

"Ahmad wannan zirga-zirga duk na menene?."

Aminu ne ya ɗan kalleshi tare da cewa.

"Ai  driver ne shiɗin shiyasa yana nan kamar farin wata yana ko ina."

Cikin mamaki Bappa Ali yace. 

"Driver kuwa?."

Murmushi Malam Adam yayi tare da cewa. 

"Eh shi pilot ne driver' n jirgin sama. Yana aiki da kamfanin Azman Air Land."

kai bappa Ali ya jinjina jin suna kamfanin ma aikatar Ahmad ɗin.

Nan dai suka gama tsara komai da shirya komai na bikin yadda ya dace, 

an dai bar batun ɗaurin aure nan da wata ɗaya mai zuwa.


Wai to ina Zaleeha ne, mun dai san Mama da Zahira kan suna Doho, 

Ziyada da Zakariyya kuma mun san su dama gidan Hajja inna suke da zama tsohuwa mai boris. 


A gidan su Saifuddeen kuwa su Adda Rahma suna dawowa, 

duk suka zauna parlour'n Ummi suna hirar mutunci da karramawar mutanen, Hajia Rabi ce ta kalli Ummi cikin nitsuwa tace. 

"Na ɗan samu nitsuwa da naga gidansu yarinyar gidan mutunci ne, duk mutanen gidan sunada mutunci."

Kai Ummi ta jinjina tare da cewa. 

"Masha Allah."

Aunty kubra ce tace, 

"A gsky ba laifi sunada dattaku, sai godiya suketayi kamar kyauta muka basu kayan."

Hayatuddeen ne yayi dariya tare da cewa. 

"Nan kuma wayo zamuyi musuba mu ɗauke musu ƴarsu kayan kuma gidanmu zai dawo da dalelliyar amaryar Hamma na."

Dariya sukayi baki ɗaya, Imran ne ya ɗan sosa ƙeya tare da cewa. 

"Aunty Kubra zamu tafi fa."

cikin dariya tace. 

"Yo to ku tafi mana."

Sulaiman ne ya ɗan zaro ido tare da cewa. 

"To kuɗin namufa da aka bamu?."

da sauri suka juyo suka kalli Isma'il da yayi dariyar ras Kamar ba kurma ba.

Hajia Rabi ce tace.

"Ohoho ni Rabi'atu wlh wata rana kuɗi zaisa Isma'il ɗina yayi magana, ji shewar da yake jin ance kuɗin nasu ne."

Hayatuddeen ne ya kece da dariya tare da cewa. 

"Yaseen kuwa Mom Isma'il in yaga kuɗi har harshenshi zakiga yana rawa."

Dariya yayi tare da kaucewa dukan da Isma'il ya kai mishi, 

Ita kuwa Hajia Rabi kuɗin ta fidda cikin Jakarta irgasu tayi ganin dubu hamsin ne a rafar forko kuma duk girmansu ɗaya, 

shiyasa suka gane cewa dubu ɗari uku ne suka basu tukuici, 

wanda a al'adan gombawa in an kai kayan lefe anasa kuɗi a ƙasan turame, 

in dubu goma akasa to dangin amarya zasu ƙaro wasu dubu goman su ɗaura kan goman dake ƙasan turame sai su bawa wanda suka kawo kayan wannan nasune tukuicinsu kenan so su yasu zasu raba, 

in dubu biyar akasa to biyar ɗin dangin amarya zasu ƙara,

In 20k nema to dole  zasu ƙara in 30k ne ko 50k Ko 80k 100k nema dole su ninka, 

to su dama dubu ɗari suka saka a ƙasan turamen, 

su kuwa madadin su ƙara dubu ɗarin sai suka ƙara dubu ɗari biyu, 

shiyasa suka samu dubu ɗari uku. 

Rafan dubu hamsin Hajia Rabi ta miƙawa Hayatuddeen tare da cewa. 

"To gashi ku karɓi wannan."

Da sauri suka amsa tare da ɗaukan tiren da Adda Rahama ta cika musu pepper chicken dasu drinks akai, tace kuci abinci kafin ku raba kuɗin. 

to sukace kana suka haura sama a parlour'n Hayatuddeen suka baje kolinsu, 

Imran ne ya ɗauki kuɗin ya irga 10k ya bawa Sulaiman kana ya bawa Isma'il ma 10k shima ya ɗauki 10k kana ya bawa Hayatuddeen 10k, 40k kenan, 

sai ya ɗago sauran 10k ɗin kuma yace. 

"To wannan 10k ɗin kuma na Zakariyya ne.

kun san Zakari namu yaseen in mukaci kuɗin nan bamu bashi ba sai ya tsigemu.

dan baya nanne shiyasa bai samu zuwa ba."

dariya sukayi baki ɗaya, 

Hayatuddeen ne ya figi lallausan tsokan cinyar kaza tare  da taunawa ido ya lumshe jin harshenshi na motsi dan daɗi,  buɗe idon yayi tare da cewa.

"Yanzu ma yamin text wai wlh mu ajiye mishi naman rabonshi."

dariya Suleiman yayi tare da cewa. 

"Wai ina yaje ne?  Ni tun jiya bamuyi mgna da shiba?."

Hayatuddeen ne yayi gyatsa tare da cewa.

"Dad'in kowa sukaje da Hajja inna tamu, da wannan fitinenniyar yayar tashi wai sunje gidan ƙanin Hajja inna tamun sai gobe zasu dawo."

dariya sukayi ganin Isma'il fa baya tare dasu sai harraƙawa yakeyi.

Nan sukayi ta hirarsu irinta sabbin matasa masu jin da rawan kan gigin balaga.


A parlour kuwa Adda Rahma da Raliyya sam ƙin karɓan kuɗin sukayi. 

Ummi ta kalli Hajia Rabi tace. 

"Ku rabasu, ki ɗauki dubu hamsin Kubra hamsin sai Goggo Dada itama a bata hamsin Aunty Mina ku bata hamsin Sadiyan Salisu hamsin.

Su kuma Rahma da Raliya angon zaizo ya basu tukuicin."

Dariya sukayi duka ganin karamci da kima da dottakun Ummi sannan tasa Aunty Mina ta raba musu kayan ciye-ciyen da suka dawo dasu.


Ganin magriba ta karato yasa  duk suka miƙe suka sallami juna suka tafi. 


Hakama abokan Hayatuddeen duk sun tafi. 


Bayan an idar da sallan magriba ya Adnan ya shigo har parlour'n Ummi in da ya samu suna zaune gaba ɗayansu ga Aunty Mina da Goggo Dada, 

cikin sakin fuska ya kalli Hayatuddeen tare da cewa. 

"Eye ƙanin ango me ka samu hakane naga sai murna kakeyi?."

kai ya jinjina tare da cewa.

"Ji nake kamar dai na jawo bikin nan."

kafaɗanshi ya ɗan buga tare da cewa. 

"kamar yau ne."

Sai ya kuma kalli su Ummi tare da cewa.

"To Ummi mu zamu wuce gida, 

tun ɗazu Faroq keta kirana wai muyi sauri mu koma."

kai ta jinjina tare da cewa. 

"To Allah ya kiyaye hanya."

"Amin Amin".

yace tare da miƙewa ya amshi Akih dake hannun Raliya, 

sannan ya juya ga matar tasa tare da cewa. 

"Rahma taso mu tafi ko."

to tace kana ta miƙe ta zari hijabinta tabi bayanshi.


Ƙarfe tara na dare dai-dai su bappa Ali suna parlour'n Ummi. 

suna shiga da kamar 15 minutes Saifuddeen ya shigo bisa wani zazzafan wheelchair ɗinsa red colour da gani kasan sabone.

ganinshi ne yasa su murmusawa gaba ɗayansu,

Ahmad dake biye dashi a baya wanda shine daya maida Imran sai ya ɗaukoshi dan shi tunda yamma yana gidansu Ishaq . 

Cikin girmamawa ya gaidasu, 

kana shima Ahmad yazo ya zauna gefen kawun nashi tare yin gyaran murya yace.

"Kawu Ali kun jene?."


"Eh munje yanzu ma daga can muke?."


"Masha Allah, to ya batun saka ranan?."


Malam Ashiru ne ya amshi zancen da cewa. 

"Alhamdulillah an tsaida ranar ɗaurin auren."

Cikin zumuɗi Hayatuddeen yace.

"Yaushe ne auren?."

murmushi bappa Ali yayi tare da cewa. 

"Yau saura kwana ashirin da takwas  yadda lissafi ya nuna."

Wani irin zabura Hayatuddeen yayi tare da sakin sauti, 

sai kuma yasa hannu ya rufe bakinshi tare da komawa ya zauna ganin wani irin kallon da Saifuddeen ke mishi alamun ya nitsu. 

Zumbura baki yayi tare da  karkaɗa kai. 

Shi kuwa Saifuddeen wani irin yalwataccen murmushi yayi a cikin zuciyarshi yana mai jin wani irin zazzafan farin ciki na ratsa mishi jiki jini jijiya harma da ɓargo, 

a fakaice ya kalli Hayatuddeen tare da yin mganar zuciya. 

"Hmmmm am so sorry Hayatuddeen, duk farin cikin da kakeji baka kai niba, da kunsan yadda nakeji tabbas da kunsha mamaki,.

lumshe idanunsa yayi tare da ci gaba da batun zuci.

"Badan kunya da nakasar da Allah ya minba da nashayar daku mamaki, Wallahi ina ɗagowa daga sujjadar godiya ga mahaliccina sai inyi ta tsalle ina kurma ihu da kururuwa duniya tasan cewa ban taba samun irin farin cikin dana samu a yau ba."

a hankali ya buɗe idanunshi ya kalli, 

Ahmad da fuskarsa ba yabo ba fallasa inda yace.

"Masha Allah, Allah ya kaimu lokacin bisa rai da lafiya."

Amin Amin suka amsa baki ɗaya.

Shi kuwa Saifuddeen sai godiya yayi musu kana ya kalli Umminshi da yake hango abubuwa biyu a kwayar idanunta farin ciki da fargaba mai tattare da tsoro, 

ita kuwa Ummi zallan farin ciki dake cikin kwayar idanun gudan jinin nata take hangowa hakane yasa kaso 50 cikin 100 na fargabanta ya gushe.

kauda idonta tayi daga gareshi ganin alamun yana son keɓewa da ita, 

cikin kula ta miƙawa Hayayuddeen Key ɗin BQ ɗinsu tare da cewa. 

"Tashi kaje ka buɗewa su bappa Ali masauƙinsu kazo ka kai musu abinci."

Amsa yayi ya fita kana suma su bappa Ali dake son hutawa sukabi bayanshi. 


Goggo Dada da Aunty Mina kuwa ɗakin budurcin su Raihana suka shiga dan duk sun gaji, 

Ahmad ma miƙewa yayi tare da kamo hannun Raliya yace. 

"Ke mu tafi bacci nakeji."

cikin jin kunya ta miƙe tabi bayanshi,

shi kuwa Saifuddeen ko inda suke bai kuma kallo ba.

Kai tsaye side ɗinshi ya nufa.


Yana shiga ratsetsen parlour'n shi yayi wani irin sassanyan a jiyan zuciya,

tare da lumshe manyan idanunshi, 

murza masarrafin wheelchair d'in nashi yayi tare zaro harshen sa ya karkad'a a rashi yace. 

"Kaddararki ce aurena Zaleeha, insha Allah sai kin amsa sunan matar wanna gurgun kurma nakasasshe ginennen tabon nan zai shayar dake zallan ruwan madarar da zata tsastsafo daka gareshi, 

sai kin zama inuwar ni'imata, 

wannan ginennen tabon sai ya zautar da kwanyarki."

A hankali ya fara zare rigar jikinshi yanayi yana shiga bedroom ɗinshi, 

cire kayan jikinshi yayi can ya rage dagashi sai boxer d'inshi mai zanen fari da ja, 

Bathroom ya shige cikin tsananin shauk'i da farin cikin cin nasara yake komai da kuzarinshi.

yana cikin bathtube ɗin wankan shi ya kalli surarshi tare da lumshe ido kana ya fara zancen zuci. 

"Am sorry Baby zakisha bulalar nan da kika tab'o lafiyarta tsawon shekaru talin bata tab'a tashi tsayeba bare ta harba saida kika tab'a sashinta,

kuma daga ranar duk sanda zuciyata ta tunaki sai ta harba, 

wannan shine yak'inin gidanta a jikinki yake."

A hankali dai yayi wanka yana fitowa yayi shirin baccinsa.


Bakin gadonshi ya zauna tare da mik'e k'afafunshi sannan ya d'aura system d'inshi a kan cinyoyinshi bisa dukkan alamu, 

aiki mai mahimmanci yakeyi, wanda kuma fuskarsa cike take da farin ciki,


Yana cikin haka yaga Umminshi ta shigo bisa dukkan alamu itama ta gama shirin baccinta, 

ganinta ya sashi muskutawa ya ɗan bata wuri,

ganin haka ta zauna gefenshi, 

cikin tsananin jin daɗi ya ture system ɗin kana ya matsota a hankali ya raba jikinta kanshi ya kontar a kafaɗunta,

ganin haka alamune na yana cikin tsantsar farin ciki, ko tarin gajiya, 

sabida Saifuddeen baya da juriyar hawala ko kaɗan in dai Umminshi na kusa to tana gane rauninshi shiyasa baya ma boye mata.

hannunta tasa ta shafa kanshi, 

sannan ta matso da system ɗin cikin rashin kwarewa tayi rubutu a hankali. 

"Gajiya ne ko farin ciki?."

ganin abinda ta rubutane ya sashi lumshe ido tare narkewa jikinta a hankali ya rubuta mata. 

"Daɗi farin ciki kwanciyar hankali salama da annashuwa, Ummi yau ina cikin farin cikin da ban taɓa jin irinsa ba."

ya ƙarishe rubutun yana kallonta dan sam bai iya mata ƙarya."

murmushi tayi tare da cewa.

"Allah ya cika rayuwar auren naku da farin ciki."

A saman lips inshi ya amsa da Amin. 

Sai kuma tasa hannu bisa bedside ta ɗauko cup mai ɗauke da zazzafan tea mai ganyen Na'a-na'a, ta miƙa masa.

karɓa yayi tare da ɗan zuƙa a hankali, 

idonshi ya lumshe dan jin ƙamshin da tea ɗin keyi.

Ita kuwa Ummi a hankali tace. 

"Sai da safe ko."

Kai ya gyadɗa mata alamun "To."

tana fita ta wuce bedroom d'inta, 

kwanciya tayi amman baccinta yak'i zuwa nazari sosai takeyi tana tsoron duk wani abu da zaizo ya cutar mata da ɗanta. 


Hayatuddeen kuwa a d'akinshi yana konce yayi ɗai-ɗai yana shan dadɗan sanyin A.C  kana yana chatting da yan uwa da abokan arziki inda yaketa sanar musu date ɗin auren Hammanshi. 

musamman  a dandalinshi na Instagram wanda yakeda mabiya sama da dubu 9 wanda kuma yawanci sabida pictures ɗin Saifuddeen ne da yake sawa, da kuma son jin ainihin waye shi, 

tarin tambayoyin da ake mishi bazai iya amsarsu ba, 

sabida da yawama a zatonsu Saifuddeen bazai iya aureba. 


Ganin tambayoyin sun mishi yawane ya rufe datan Instagram yana niyar buɗe  WhatsApp sai ga kiran Amina ya shigo wayarshi video call. 

yana ɗagawa yayi dariya ganin yadda ta haɗe fuska, 

A ƙufule tace. 

"Dariya ma na baka kenan?."

Cikin dariyar yace. 

"Hmmm to ni me nayi miki naga sai hararata kikeyi?."

ajiyan zuciya ta ɗanyi tare da cewa. 

"Yau kwana biyar kenan ina kiranka baka ɗaga waya meyasa."

da sauri yace. 

"Sabida nasan zakice in bawa Hamma Saifuddeen wayar, 

kuma duk sanda kike kira baya kusa shiyasa bana ɗagawa."

baki ta ɗan taɓe tare da cewa.

"Ai dai yanzu kam yana gida ko?."

Miƙewa zaune yayi tare da cewa. 

"To amman ya shiga fa."

Da sauri tace. 

"Please karkace komai ka kai mishi wayar. Dan Allah karkace a a."

jin haka ya miƙe tsaye ya nufi ƙasa. 


Kai tsaye Side ɗinshi ya nufa inda Ummi ta rufeshi ta baya dan haka a sauƙaƙe ya shiga parlourn, 

a hankali yace. 

"Ni dai duk in da akace nawane sai ya koma kamar tirken doki, 

kalli yanzu parlour nan ko sarkin makka zai zauna a nan komai tsab-tsab sai ƙamshi tamkar da turare ake mishi mopping, 

kalli can kuma sama yadda banzayen nan su Imran suka wancakalarmin da parlour haka aka barminshi kamar wani maraya, 

to yaseen yau a nan zan kwana."

Ya k'arishe mgnar lokacin da yake shiga bedroom d'in. 


Ita kuwa Amina sai dariya takeyi dan duk taji me yake faɗin. 

Yana shiga kai tsaye ya nufi kan gadon inda ya hango Hamman nashi na zaune wayar ya miƙa mishi cikin zumbura baki ya haura kan gadon ya konta gefen ɗan uwan nashi tare da rufe idanunshi wai shi yayi bacci.

Murmushi Saifuddeen yayi tare da gyara mushi rufuwan da yayi dan yasan bazai iya jure kwana cikin sanyin dashi yake kwana ba, 

sai ya kuma juyo ya kalli fuskar wayar tashi daya miƙa mishi,

da sauri ya rage idanun nashi ganin fuskar Amina ita kuwa, 

girarta ɗaya ta ɗaga mishi alamun ya dai.

sai ta kuma kalleshi cikin lunshe ido tace. 

"Ya jikin ka?." bata tsumayi amsaba dan tasan ba samu zatayi ba shiyasa taci gaba da cewa. 

"In zo har garinku har gidanku in dubaka da jiki, 

in dawo Amman ko ka kira kaji mun dawo lfy ko?."

a hankali ya zaro harshenshi ya lashi jajayan labbanshi hakan yasa suka ƙara  fitar da sheƙi,

Lumshe idonshi yayi tare ds longoɓar da kanshi bisa kafaɗarshi tare da narke fuska, haka nan yaji wani guntun murmushi ya suɓuce mishi,

ido ta lumshe tare da cewa. 

"Bakinka yana min kyau, gashin girarka mai kyau, idanunka masu  tarin   kyau,  sajenka yana min  kyau sosai Hamma, ina son komai naka surarka, yan uwanka, abokanka ina son duk wani abu naka, 

bayan Ya Amir kaine mutun na forko da nake bege da so."

shiru yayi ya zuba mata idanu, yana karantar lafuzanta, 

ita kuwa cikin zazzafar soyayyarshi dake sarƙe mata zuciya da ruhi tace. 

"Ina sonka Hamma Saifuddeen zaka aureni?  Kayi haƙuri kunya nakeji bazan iya rubuta makaba, kuma inajin kunyan in gayawa Hayatuddeen, gashi kai kuma baka jina to ta yaya zan shaida maka soyayyata, 

ina sonka ka zamo mijina uban ƴaƴana, ina addu'ar Allah ya azurtamu da samun yara masu kama da kai."

sai kuma ta kalleshi ganin ya tsareta da ido haka nan yake jin kalaman nata har cikin zuciyarsa, 

to amman wai meyasa ita bata kunyan faɗi mishi wasu abin ne, ita kuwa ganin yayi shiru ya kuma rage girmam idanunshi ne ya sata cewa. 

"Ka gaji ko? bacci kakeji ko?, naga idonka yayi limshi, bari in kashe wayar sai da safe."

Tana kaiwa nan ta katse kiran, 

shi kuwa Saifudddeen dariya yayi a ranshi yace. 

"Sokuwa kawai mai tunanin yara wato kina sona, hmmm ke dai faɗi gsky bani kike wani soba, kinada dai abinda kikeso daga gareni."

daga nan yayi ta aikinshi.

sai kusan ƙarfe ɗaya, 

ya sauƙo ya shimfid'a sallaya kana yaje yayi al'wala sannan yazo yayi nafilfilinshi sai d'aya da rabi ya konta.


Washe gari ranar Jummu'a tun da safe su Zaleeha suka dawo, 

daga gidan Hajja inna tayi wanka ta wuce Billiri dan hira da nakassusun wancan yankin wanda k'arfe biyar na yammacin ranar jumma'ar ne zata gabatar da shirin, tun randa ta had'u da Saifudden a Jonapwd, bata sake zuwa canba, 

kuma tunda ta turawa ishaq text ɗin ban haƙuri bai kulataba itama bata sake bin ta kanshi ba, 

shi kuwa Ishaq shida Saifuddeen bakinsu a had'e a cewarshi ita da kanshi zata nemeshi har mazauninshi...


K'arfe uku ta dawo daga billiri kai tsaye gidan radio nasu ta nufa, 

a nan tayi sallan la'asar, sannan ta zauna jiran lokacinta, 

tana zaune anan Bilkisu ta shigo ita da Manager d'insu tana ganin Zaleeha ta kwashe da dariyar shak'iyanci cikin ingizarwa tace. 

"Hajiyar nakasassu ina mutanen naki ne? Koda yake amaryar nakasashen gurgu kurma zance ko."

cikin tsananin takaici Zaleeha ta watsa mata harara tare da cewa. 

"A a uwar nakasashe zakice ba amryar nakasashe ba wlh mai gado bana so ki daina had'ani da wannan musakin."

cikin Shek'iyanci bilkisu ta iso gareta tare da cewa. 

"Sorry baza k'araba,  amman mutanen nakine da abin dariya."

juyawa tayi ta fita tabi bayan Manager ita kuwa Zaleeha Raveel ta kalla wanda yake mik'o mata sweet amsa tayi tare da cewa. 

"Ngd."

kai ya gyad'a mata tare da cewa.

"Kada ki sake aibata nakasassu dan duk wanda bai mutuba ba'a gama mishi halittaba.

da kullum haka kike gaya min to meyasa kawai dan nakasasshe yace yana sonki sai ki juye daga Mai kakkyawar alaƙa i zuwa mummunar ɗabi'a, kada ki bari imaninki ya samu rauni."

kai ta gyaɗa mishi sannan ta juya ta nufi ɗakin gabatar da shirin nata ganin lokacinta yayi. 


Mama kuwa da Zahira sosai zugar Ruda yayi tasiri a kwanyarsu da yake dama zuciyar ba inganci. 


Ƙarfe huɗu dai-dai suka dawo daga doho,

suna shiga gidan kai tsaye side d'in Baba malam suka nupa, 

a parlour suka sameshi shida Ya Ahmad da Ya Habu, sai Mamy dake haɗa musu tea a kofuna.

sannu da hanya sukayi musu, fuskarnan kamar zatayi ruwan jini Mama ta amsa musu kana ta gaida Baba malam, 

sannan Ahmad da Habu suka gaidata, 

Zahira kuma duk ta gaidasu sannan ta wuce cikin gidan tayi shashin maman.

Ita kuwa Mama a hankali ta mik'e ta fita ganin duk basubi ta kantaba, 

to wazai kulata yadda taketa harare-harare,

tana fita ta nufi Side d'inta da yake tsab   Maryam da Aunty Lubna sun gyarashi jiya da dare. 

A parlour ta zauna, 

dai-dai lokacin kuma Zahira ta fito daga bedroom d'in Maman a guje, 

ganin Maman a parlour yasata tsayuwa cikin rawan jiki da halin fitina tace.

"Mama zo zo zo kiga wani abu a bedroom naki."

tsaki ta d'an ja tare da cewa. 

"Menene kike wani zaro idanu haka?."

hannun uwar ta kamo tare da cewa. 

"Mama zo ki gani mana an cika miki d'aki da akwatuna dasu buhunan gishiri dasu goro."

ido ta zaro gaba d'aya tare da cewa. 

"Akwa tuna kuma to na meye."

cikin hatsabibanci tace. 

"To waya sani ko lefen Anty Zaleeha aka kawo."

ai kafin ta rufe bakima Mama ta kutsa kai cikin bedroom ɗin. 

wani irin wawan birki taja tare da cewa.

"To wanna kuma daga ina, to ko Abdussalam ne da tace mishi a turo komanshi Zaleeha ta yarda dashi, tuni ya turo ɗin, 

sai kuma ta girgiza kai ina sam ba shi bane ai in shine zai gaya mata, shida kuma ɗazu suka gama mgna, 

cikin tafasan bala'i tace to waye. 

Sai kuma ta dawo parlour da sauri cikin karad'i da kware murya baki d'aya ta fara rabkawa Habu kira.

"Habu! Habu!! Habu!!! Habuuuu!."

da sauri ya iso cikin parlourn a tsorace yace. 

"Na'am Mama ganifa nazo."

A hatsale tace. 

"To dan ubanka meyasa bazaka amsa da kyau ba."

cikin had'e fuska yace, "Na'am." cikin yamutsa fuska tace.

"Wancan kayan fa na meye ne."

Kai tsaye yace. 

"Lefen Zaleeha aka kawo jiya."

cikin ɗaga sauti tace waye kawo lefen?."

A dake yace. 

"Wasu mata ne."

zaburowa tayi kanshi tare da cewa. 

"Dan ubanka ba wanda suka kawo nake tambaya ba wanda aka kawowa nake nufi."

cikin kauda kai yace.

"Zaleeha aka kawowa."

wani dogon tsaki taja tare da jawo hannunshi tace. 

"Kai mahaukacin inane wanne saurayin ne ya aiko lefen."

Cikin dakiya da rashin tsoro yace.

"Saifuddeen."

wani irin zabura tayi tare da buga tsalle tace. 

"Inji uban waye ya basu damar kawo banzayen lefen wanna musakin d'an nasu?."

Yana fita yace. 

"Inji Baba Malam mana Baban Zaleeha shine ya basu dama."

wani irin kware murya tayi tare da yin sauri ta nufi parlour Baba malam tana shiga parlour tare da masifa murya a hargitse tace. 

"Lallai yau  za'a sabunta yaƙin duniya....!




*Dan Allah da manzonsa ku dena fitarmin da littafi,*


                                  By

                     *GARKUWAR FULANI*

8/


              *NAKASA BA KASAWA BACE*


                            *PAGE 30*


                                  NA

               *AYSHA ALIYU GARKUWA*


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇



"Lallai yau za'a sabunta yaƙin duniya na biyu".

 Fuska ta ƙara haɗewa tamkar wacce akayiwa bushara da mummunan al'kaba'in rayuwar duniya.

Ido suka zuba mata baki ɗayansu, tare da maida hankalinsu gareta. 

Cikin takaici da tashin hankali tace. 

"Meyasa!  Meyasa haka ne malam? Ina dalilin kullum sai an sani baƙin ciki kan aurar da ƴaƴana?." 

Kauda kanshi yayi daga kallon mummunar fuskarta tare da maida dubanshi ga al'ƙiblah, a hankali yaci gaba da tasbihi da yakeyi.

"Subahallahi, walhamdulillahi, wa la'ilahalillahu, wallahu akhbar."

haka yaketa mai-maitawa tare da motsa yatsun hannunshi na dama, kana yana ɗan karkaɗa ƙafafunshi dake miƙe bisa table ɗin dake gabanshi a hankali a hankali.

idonshi ya rumtse da ƙarfi jin Mama na cewa. 

"Wallahi-Wallahi bazan taɓa yarda a zalumunci Zaleeha irin yadda aka zalumci Maryam ba, akan wani dalili zai sa baza'a sakarmin rayuwar yarana ba, suma su auri wanda sukeso sai ayi ta musu cushe da auren dole ina dalili? to Wallahi  muddin ina raye, Wallahi bazan taɓa lamunta Zaleeha ta zauna da wannan banzan nakasasshen kurma kuma gurgun, da kuka yayibo zaku liƙa mata ku kashe mata rayuwa ba, 

haka kawai dan an iya min kisan mummuƙe, shine za'a nunamin wariyar launin fata, a nuna min ni bare ce to Wallahi ban amince ba!."

Cikin gajiya da ihu da hayagagar da take musu Ya Ahmad ya ɗan tanƙwashe sawunshi tare da cewa.

"Mama ai Zaleeha ita ta kawo shi, zaɓinta ne ita ta amince dashi babu wanda ya mata dole, 

itace ta amince tasa ya turo iyayenshi."

Cikin tsawa tace. 

"Rufe min baki, kaima ae munafuki ne, ban nemi jin ta bakinka ba, da ubanka nake magana,

karka wani karkace kace zaka meda laifin kan Zaleeha, munafurcin banza kawai."

Rumtse idanu Ya Ahmad yayi, cikin takaicin abinda Mama'n kewa mahaifin nashi yace.

"Allah ya huci zuciyarki."

A hasale tace. 

"Wannan karon dai zuciyar tawa ba zata huce ba, Wallahi bazan taɓa lamunta da batun ƴata ta auri musakiba,

dan rainin hankalin yarinya da kyawunta da ƙimarta tanada masoya gabas da yamma kudu da arewa amman a rasa wanda za'a zaɓa mata sai nakasasshe, wulaƙantacce wanda ko magana bayaji!."

 Tafaɗa ranta amatuƙar ɓace domin sosai zuciyarta ke tafasa. 


Duk ihu da hargowan da takeyi Baba Malam bai sake ɗaga  ido ya kalleta ba, sai ma tasbihi da yakeyi ga mahaliccinsa da ya jarabceshi da auran wanna mata mai munanan al'adu.

Mamy kuwa wayarta ta jawo kana ta fara karanta  Dua Azkar.

Ganin haka shima Ahmad sai yasa hannu ya ɗauki ɗan madai-daicin Qur'Ani'n  dake gefenshi ya buɗe ya fara karatu ahankali cikin suratul. Kahf kasan cewar yammacin Jummu'a ne.


Habu ne ya shigo parlour'n a hankali ya nufi gefen mahaifin nasu ya zauna kusa da ɗan uwan shi Ahmad,

ido ya rumtse da ƙarfi yana mai jin takaicin hali irin na mahaifiyar tashi,

cikin sanyin sauti yace. 

"Ya salam! Dan Allah Mama kiyi haƙuri ki bar yin ihun nan, kowa yanayin abinda zai samar mishi lada ke kuma kinzo kina tarawa kanki zunubi kina ɗaga harshenki sama dana mijink..." 

Da sauri ya haɗiye rogowar maganar tashi, sakamakon jin Maman ta kai mishi wani uban bugu kan bakinshi.

"Habu kayi asara Wallahi, kai dai ka banunka da baka da kishin mahaifiyarka!." Takuma faɗa a hasale.


Baba Malam ne ya miƙe tsaye, tare da kallon yaran nashi cikin kamala da cikar haiba yace.

"Kuyi al'awala mu tafi masalaci lokacin sallah ya gabato."

Da sauri suka mimmiƙe tare da cewa.

 "To."

Haka duk sukaje suka sabunta al'wala kana suka tafi zuwa masallaci. 


Mamy ma tuni tayi side ɗinta,  inda ta samu Aunty Lubna a parlour tana sawa ƴarta hijabi alamun zatayi salla ne.

"Barka da shigowa Mamy."

cikin nitsuwa da mutuntaka Mamy tace.

"Barka dai Lubna ya gajiyar kitchen? na tafi na barki ke ɗaya da aiki niƙi niƙi ko."

Kai ta rausayar tare da cewa.

"Tun ɗazu na gama ai Mamy aikin ba yawa."

"Masha Allah!  Allah Ya saka da al'khairi, ya baki surkai masu miki fiye da abinda kike min."

"Amin Amin"  Aunty Lubna  ta amsa cikin jin daɗi, kana tayi side ɗin da nanne masauƙinsu duk lokacin da sukazo Gombe dan ita da Mamy tamkar uwa da ƴarta haka  suke.


Ita kuwa Mama ta cika tayi tam sai ihu da haushi takeyi ita kaɗai kamar karya. 


"Watoma mahaukaciya suka medani? sun watse sun barni wato inyi ta haushi ni ɗaya ko, tam zanyi maganinku, Wallahi gaba ɗaya saikunji aranku cewa inama da ace bakuyi ganganci ƙulla wannan haɗin ba, saina sanya baƙinciki acikin zuciyoyinku, kuma sannan saina saku danasani marar yankewa, badai dani kuke wasan ba, hmmm Wallahi zakusan kun taɓo cikakkiyar ƙaɓila Batangali da surkin bateriya, akan auren nan babu wanda zan ɗagawa ƙafa!!."

Tana gama faɗin haka ta juya fuuuuu kamar kububuwa tafice daga cikin falon na Baba Malam. 


Tana shigowa falonta ta soma afkawa Zahira ƙira, 

da sauri Zahira ta fito daga cikin ɗakinsu tana cewa. 

"Na'am Mama."


A harzuƙe tace. 

"Zo zonan mu kwashi ƴan iskan kayayyakin nan mu watsasu waje, Wallahi bazasu kwanar min a ɗaki ba gayyar tsiya!."


Da sauri Zahira  tace "To."


Nan suka shiga cikin ɗakin, haka suka dinga ibo akwatunan nan masu kyaun gaske,  suna watsasu a tsakiyar farfajiyar gidan, 

wai don ma kasancewar Mama ƙaƙƙarfar  mace ce shiyasa kab ta iya jidon manyan akwatunan, tanayin waje dasu harda su gishiri da goron bata bari ba, ranta yakai ƙololuwa wajen tafasa, jin kanta take dai-dai da uban kowa, jira take wani yace mata cass tuni zata sullesa tas.


Saida ta gama watsasu a tsakiyar gidan, sannan ta koma cikin ɗakinta tana haki tamkar wacce tayi dambe ta gaji. 

Al'wala tayi sannan tazo ta kabbara niyar sallan magriba, wanda tuni lokaci ya ƙure mata, don  har an riga da anƙirayi sallan isha.


Zaleeha kuwa daga ma'aikatan nasu gidan kakar tasu ta koma, 

don dama kwana uku ta roƙi Baba Malam  daya barta tayi, kuma da yake gidan mahaifiyarshi ce sai bai hanata ba.


Kafin ma ta dawo tuni Ziyada ta gama haɗa musu komai na girki, 

tuwon ɗanyar shinkafa da miyar kase,

tana ganin haka tace.

"Ziyada ina Zakariyya kuma da tsohuwar nan sukaje, suka barki ke ɗaya a gida?."

Cikin yanayin nutsuwarta irin na Maryam sak tace. 

"Sun tafi gidansu abokinshi Hayatuddeen."


Tana warware naɗin gyalen hijabin dake jikinta tace.

"Sun daɗe da tafiya ne?."

Kai ta gyaɗa mata  tare da cewa.

"Eh tun da akayi sallan la'asar suka tafi."

kai ta jinjina kana ta zaro wayarta ta danna ƙiran number'n Zakariyya.


Shi kuwa Zakariyya lokacin suna parlour'n Ummi shida Hayatuddeen da Raliya, sunata tsiya wa Hajja Inna, ita kuwa Hajja inna 

sai surfa musu boris takeyi, 

Ummi kuwa sai nan-nan takeyi da hajja Inna dan taji dad'in zuwan kakar abokin autan nata, sosai takejin son tsohuwar a ranta, musamman yadda ta nuna tana masifar son Saifuddeen ɗinta.

Ta tasashi gaba tana yabo harda kukanta tana. 

"Allah sarki bawan Allah, yaro kyakkyawa, Allah ya jarabceshi da nakasa, 

ganshi kuwa kamar balarabe."

Sai kuma ta juyo ta kalli Ummy tare da cewa. 

"Wannan yaron naki abin sone da tausayawa ga ko wanne mutum ɗan Adam me imani, ki godewa Allah daya azurtaki da samunsa a matsayin ɗa,

wasu suna can sun haifi lafi yayyun yara amman sai ki samu yaran munanane kamar kashin dare, 

kinga ko gwara miki kyakkyawa fari ƙal nakasasshen."

Hayatuddeen ne yayi dariya sosai tare da cewa. 

"Kai tsohuwar nan munana sun boni a wajenki."

Zakariyya ne ya zaro wayarshi dake suwa, wacce take cikin aljihun wondonshi yana cewa. 

"Itafa sam bata son mummunan mutum, in taga kyakkyawan mutun kuma wai ji take kamar ta dawo dashi ɗanta."

Dariya sukayi baki ɗaya, 

kana shiko Zakariyya ya amsa kiran Zaleeha tare da cewa. 

"Hello Adda Zalees ya akayi ne?."

Sai ya kuma yafito Hayatuddeen tare da mishi alamun ga mutuniyarshi fa. 

amsar wayar yayi ya kara a kunne tare da cewa. 

"Adda Zalees nayi fushi dake muka dawo ko kizo ki duba kyakkyawan hammana da jiki ko."


Murmushi tayi tare da cewa. 

"Afwan autan gidansu."

da sauri yace.

"No autan Ummi dai zakice, gidanmu kam ai kwanannan ma Hamma na zai fara ƙenƙesa mana yara sabbin zubi, ƴan yayi kuma kyawawa, irin yaran da Hajja inna ke masifar so."

Ƴar dariya tayi tare da cewa. 

"To aku sarkin zance, please ka cewa Zakariyya su biya Abba bakery ya saya min  pizza dan Allah."

Da sauri yace. 

"To ba matsala karki damu zan bashi abin daɗi ma ya kawo miki, cikin na Hamma na zan ɗiba miki."

Da sauri tace.

"A a ni dai pizza kawai nake so."

Bai kulataba ya katse ƙiran.

sannan ya amshi kular da Raliya ta haɗa musu tsarabar Kai kayan lefen jiya."

Daga nan suka miƙe  zasu tafi,  har sun kusa fita daga parlour Hajja Inna ta juyo ta kalli Saifuddeen murmushi ya mata, haka itama murmushin tayi mishi sannan ta kalli Ummi cikin halin tsufa tace. 

"Kin ga ƴata kada ki yarda ki bari wannan kyakkyawan ɗan naki ya auro miki mummunar surka,

in kuwa kika bari ya auro miki mummunar surka,  to shike nan ya ɓata miki wannan kyakkyawar zuriyar taki,  dan tabbas dole wata rana sai ta haifo muku mai kama da ita, 

dan ni dai anmin na gani, yanzu in kika kalli Zahira zakice ba jinin ahlina bane dan ita kamannin dangin uwarsu tayi yo."

Zakariyya ne ya tura baki tare da cewa. 

"Kefa kince baki da goni a duniya sai mai kyau, to sam gigin tsufarki baya gaya miki gsk,  ya zaki rinƙa sarata ina ji, aikin kawai."

Dariya sukayi dukansu ganin yadda ta kamo hannun Zakariyya tana cewa. 

"A a kada kaji haushi shalelena, ai kai sak da kakanka baban babanka kakeyi,  shiyasa kai da Ahmad kuke tsananin kama, 

Zaleeha da Ziyada kuwa dani suke kama, bakaga Zaleeha ko gashi irin nawa ta gado ba?."

Janye hannunshi yayi tare da kunna machine ɗinsa, kana ya amshi kular da Hayatuddeen ke miƙo mishi ya saka a cikin ɗan kondon dake gaban machine ɗin. 

Sai ya kuma kallon Hayatuddeen dake miƙo mishi 10k kana yace.

"Ga tukuicinmu na jiya."

Dariya Zakariyya yayi tare da cewa. 

"Kace abin namu ne babu ƙaranci, ashe ko zamuyi casu a bikinga."

Sosai Ummi ke murmushi dan Zakariyya sak autan tane da shirmensa.

Sosai hajja Inna ta ɗale saman machine ɗin na Zakariyya,  kamar ba tsohuwa ba, 

da sauri Ummi ta riƙe kai ganin yadda Zakariyya ya figi machine ɗin ya fita a guje. 

Hayatuddeen ne ya kece da dariya tare da cewa. 

"Hege Zakary namu, wata rana zai ɓarar da hagwaran tsohuwar nan a titi yaseen."

Dariya Raliya tayi tare da cewa. 

"Ai harda karya mata ƙafa."

Daƙuwa Ummi tayi musu tare da juyawa tayi cikin gida sannan suma sukabita a baya.


Su kuwa Zakariyya na isa ya miƙawa Zaleeha kular da Hayatuddeen yabasa yayi,  dan tuni shi yaci a can yayi haniƙan,

ita kuwa Zaleeha kamar bazata buɗe kularba sai ta kuma buɗe,  ganin abinda ke cikine ya sata yin murmushi sannan ta miƙe tsaye, lemon exotic ta ɗauko acikin fridge kana ta dawo ta zauna, haka  ta fara cin pepper chicken ɗin dayaji onion,  tanaci tana latsa wayarta, 

Ziyada kuwa tuni tabi bayan Hajja inna da ta kirata wai tazo ta cire mata sarkan da ta sanya awuyanta, kasancewar idanun tsufa gareta bazata iya cirewa kanta ba.


Ƙarfe tara dai-dai Zaliha Ziyada da Zakariyya dukansu suna zaune parlour'n  Hajja ina sunata hirarsu irin ta ƴan uwan juna, 

yayinda kakarsu ke tsakiyarsu, 

tana kallon kyawawan jikokinta da take matuƙar so arayuwa, dan  

duk cikin  jikokinta tafi son Ahmad da kuma Zakariyya. 

Sam bata shiri da Habu a cewarta wai shi baya dariya.


A can New G.R.A kuwa kasan cewar yau girkin Mamane dan Mamy yau ta ƙare kwana biyunta. 


Suna dawowa sallan isha Ahmad da Habu sukayi cikin gida.

Da sauri Habu ya tsaya, cikin mamaki yace. 

"Ya Ahmad kalli can."

Da sauri Ahmad ya isa wurin da Habu ke nuna mishi, ganin 

kayan  lefen Zaleeha ne da aka kawo jiya watse aƙasa, setin gaba ɗaya akwatuna 30  dasu  tarkacen gishiri da goro duk an watsosu waje,  

cikin tsananin Al'ajabin halin Mama da tsaurin ido irin nata yace. 

"Innalillahi! Habu tayani mu kwashesu, tunkan Baba Malam yazo yagani, nasan bazaiji daɗi ba aransa ba."

Da sauri suka fara tattara kayan, sai kuma duk suka tsaya tare dayin shiru, sakamakon jin muryar mahaifinsu ta window parlour'n shi.


"Ku barsu a wurin ko tsinke kada ku ɗaga, ku wuce ku bar wurin."


Shiru sukayi cikin tsananin tarin damuwa dan dagajin muryar Baba malam yana cikin tsananin baƙin ciki, muryarshin ce ta katse musu tunanin da sukeyi. 

"Ku bar wurin ko nace!." ya ƙarishe maganar cikin bada umarni irin na fusata. 

Da sauri sukace. 

"Toh".

sannan suka juya, kowa ya nufi ɗakin mahaifiyarshi. 


Gefen Mamy Ahmad ya zauna cikin ƙunan rai yace.

"Please Mamy kije ki bawa Baba malam haƙuri, naga ranshi ya matuƙar ɓaci, kice  yayi haƙuri ya barmu mu kwashi kayan, in yaso mushigo dashi nan ɗakinki."


Murmushi Mamy tayi tare da cewa.

"Hmmm Ahmad ai wannan ba hurumi na bane, 

ku bar kayan kamar yadda ya umarceku, 

Mamanku ta zauna da Malam kusan tsawon shekaru 30 kenan yau, amman har yau bata san waye Malam ba, bata taɓa ƙureshi ba, 

amman da dukkan alama yau zata san kaɗan daga cikin halaiyarsa,  idan ransa ya ɓaci, 

shi acikin ruwan sanyi zai dafata."


Jin haka yasanya Ahmad cewa. 

"Hmmm kai Mama tanada matsala Wallahi, mutum duk haƙurinshi sai ta ƙureshi."


"Kaje kaci abinci ka dena zama da yunwa."

Mamy ta umarceshi cikin son kauda zancen, kasancewar bata son tayi mgnar kishiyarta, dan wannan shi ke ɓata alaƙar zuciyar yaro da matar ubanshi.


Ƙarfe tara dai-dai Mama ta shiga parlour'n  Baba Malam,  tare da yin sallama can ƙasan maƙoshi, ta yadda shi baima jitaba.

A kan kujera ta sameshi zaune ya zubawa TV idanu yana kallon BBC News. 

Kan dinning table ta kai dubanta, gani tayi  yanda ta ajiye abinci, yana nan ayanda yake, da alama babu wanda ya taɓa ko food flask ɗin bare akai ga ci, 

juyowa tayi ta maida kallonta kan fuskarshi da ta ɓoye ɓacin ransa, 

ta sani koda bazaici abinciba to tabbas zaisha tea, 

dan haka  taku uku zuwa biyar ne yakaita gaban dinning area,  

cup ta ɗauka sannan ta haɗa mishi tea kamar yadda ta saba, 

a hankali tazo ta ajiye mishi cup ɗin a kan table ɗin dake gabanshi, wanda yawanci nan yake miƙe sawunshi idan yana zaune akan kujera.

danne ɓacin ranta tayi dan yanzu so take ta gwada kirsa tunda taga hayagagar bata kamashi, 

gefenshi ta zauna tare da cewa. 

"Ga tea ɗinka nan nahaɗa ma kada yayi sanyi."

shiru yayi  baice ƙala ba, ganin yadda yayi kamar babu wani mahaluƙin dake kusa dashi, yasanya 

cikin tsareshi da ido taƙira sunanshi.

"Malam!."

Baima juyo ya kalleta ba bare tayi zaton ko zai amsa mata, 

saima kaɗa ƙafafunshi da ya farayi a hankali. 

shi kuwa wani irin tafarfasa zuciyarsa keyi, 

yadda tazo tayi ta mishi ihu da haushi a kanshi gaban yaranshi da uwar gidanshi, shine ke ƙara ɓata masa rai, sam bata sa hankali da nutsuwa cikin lamuranta.

Kusa dashi ta kuma matsowa tare da cewa. 

"Malam magana nake so muyi da kai fa."

Bai bi ta kantaba bare ya saurareta saima ƙara volume ɗin TV da yayi.

Cikin takaicin abin tace. 

"Ya kamata muyi magana ta fahimtar juna, 

a bani matsayina da damata a matsayina na uwar yarinya, 

ni nasan Zaleeha bata son wannan nakasasshen, ta tsaida gwaninta, harma ta bashi daman ya turo komai na aure, tunda dama iyayenshi kam sun zo kuma ka sansu ba baƙin fuska bane, 

d'an manya ne gaba da bayansa."


Gum yayi mata tamkar dutse, 

ita kuwa sai surutai takeyi uwa aku, 

ganin an gama labaran ne ya sashi, 

miƙewa tare da kashe TV sannan ya nufi bedroom ɗinsa, 

da sauri tabi bayanshi tana Magana, bai kulata ba, haka ya shiga bathroom,

ruwa ya watsa sannan yayi al'wala kana ya fito.

A bakin gado ya sameta tana zaune, 

shi kuwa shirin bacci yayi kana yazo ya tsaya gefenta, da  hannu ya nuna mata hanyar fita alamun ta fice mishi daga ɗaki, 

fuska a tsuke tace. 

"Muyi maganar tukun!."

Fuska ya kuma tsukewa wanda saida taji gabanta ya ɗan faɗi, yayinda zuciyarta kuwa ta buga da ƙarfi, 

hanyar fita ya kuma nuna mata, 

da sauri tace. 

"Dan Allah, dan darajar ma'aiki kayi haƙuri ka buɗi baki muyi magana."

Ido ya rumtse dan ya rigada ta haɗashi da Allah.

Itama sanin in dai ta haɗashi da Allah zai saurareta ne ya sata yin hakan. 

cikin kaushin murya da haɗe fuska zuciya na tafasa murya a zafafe yace.

"Kije ki kwashi kayan da kika watsar ɗin ki maidasu ɗakinki ki ajiyesu yadda kika samesu."

da sauri tace.

"Dare yayi fa."

A kausashe yace. 

"Baza kuma su kwana a waje ba."

Cikin sanyin jiki tace. 

"To bari in ƙira Habu yazo ya kwashesu."

A ƙufule yace.

"Waya fito dasu?."

Kai ta juya tare da cewa. 

"Ni ce."

Cikin bada umarni yace.

"To kije ki maidasu kizo muyi maganar."

Bata da zaɓi dan ta san kaɗan kenan daga halinshi dole taje a daren ta kwashi kayan, 

ta maidasu cikin ɗakinta, 

tana gamawa a gajiye ta koma ɗakin nashi,  a kwance ta sameshi cikin maida numfashi tace. 

"Na maidasu. Ka tashi muyi maganar."

Kai ya jujjuya tare cikar haiba da isa da gidanshi yace. 

"Maganar ai na gamata babu wani wanda zan aurawa ɗiyata Zaleeha sai Saifuddeen,  kuma babu wani mahaluƙin da ya isa  hanani sai ubangijin daya halicceni!."

Yana faɗin haka ya gyara kwanciyarshi tare da rufe ido alamun bacci zaiyi. 


Cikin tsananin takaici haɗi da ƙunci tace. 

"Ni kuwa Wallahi ƴata bazata auri gurgu kuma kurma ba, ɗiyata bazataje ta zama majinyaciya ina kallo da idona ba, sannan bazan taɓa bari takashe rayuwarta wajen kula da nakasasshe ƙaskantacce ba, Allah ya sauwaƙa ma, ni dai ajinina ban haifawa nakasashshe matar da zai aura ba ehe!!." 

Tana gama faɗin haka ta juya ta fita a fusace.

Gyara kwanciya Baba Malam yayi tare da rufe idanunsa, sunayen Allah Kawai yake ambata acikin ransa.  

***


Washe gari kuwa Zaleeha daga gidan hajja Inna ma'aikatarsu ta nufa, bayan ta gabatar da shirinta na mushaƙata kai tsaye gidansu kuma ta nufa.


A harabar gidan tayi kiciɓis  da ya Ahmad, 

cikin shaƙuwarsu ta nufi inda yake, da alamun cewa shima yanzu shigowarsa cikin gidan. 

hannunshi ta kamo tare da cewa. 

"Ya Ahmad nayi kewarku kwana biyu bana nan ko kuyi cikiyata."

murmushi yayi tare da cewa. 

"Muma munyi kewarki, kin san inata shirin tafiyarmu ne, 

naso in wuce da Lubna amman Mamy tace wai in bar miki ita."

tsalle tayi cikin jin daɗi tace. 

"Yessss! My mamy kai amman ko naji daɗi sosai!!."

Murmushi yayi tare da cewa. 

"Ato ai dama amare yan jin daɗine."

Sam bata kawo komai a rantaba da jin furucinsa, 

sai sakin hannunshi da tayi lokacin da sukazo dab da ƙofar Mama,  cikin alamun gajiya da kuma yunwa dake damunta tace. 

"Yauwa Ya Ahmad bari inje inyi wanka sai inzo muyi hira,  ka cewa Aunty Lubna ta gasa min abin daɗi yunwa nakeji, please  ko roasted fish nema nasamu idan nazo."


"To." Kawai yace tare da juyawa yayi side ɗin Mamy.


Ita kuwa Zaleeha da sallama ta shiga, 

da sauri ta kutsa kanta cikin parlour'n,  saboda hango Mamanta na zaune fuskar nan a kumbure alamun tsananin fushi, 

da sauri ta durƙusa agabanta cikin tsoro tace. 

"Lafiya kuwa Mama? Meya sameki? baki da lfy ne?." Duk tayi mata tambayar cikin kulawa, irin wacce ke tsakanin Ƴa da Uwa.


Cikin tsananin takaici Mama ta watsa mata harara tare da cewa. 

"Ae naji ke har dariya ma kike ko? yayinda ni kika barni ina nan baƙin ciki da ɓacin ranki zasu haɗu su kasheni!."


Cikin zaro ido haɗi da tsoro tace. 


"Na shiga uku Mama me nayi miki?."


A hasale Mama tace.

" kikamin ko kikayiwa kanki."

Sai kuma ta miƙe tsaye tare da watsawa Zaleeha wani  irin mugun kallo.

Sannan tayi cikin bedroom ɗinta, wanda idan  ba doleba, sam  bata son shigarsa, saboda idan taga wannan kayan ji takeyi kamar ta faɗi ta mutu, tsabar baƙincikin dake cika zuciyarta.


Da sauri Zaleeha ta bita,

a gaban Maman  ta tsaya, cikin raunin murya tace. 

"Mama kiyi haƙuri in na miki laifine ki gaya min Wallahi bazan sakeba!."


Azafafe ta nuna mata tarin akwatunan wanda ita sam bata gansuba sai yanzu cikin kakkausan murya tace. 

"Kinyi asara Zaleeha, Wallahi kinyiwa kanki sakiyar da ba ruwa, ki rasa wanda zaki zaɓa duk cikin masoyanki sai wannan banzan nakasasshen da baya ji baya magana, uwa uba kuma baya tafiya, ki zaɓeshi matsayin miji har zaki bashi dama ya turo iyayenshi su kawo tarkacensu harda su sadaki,

wato kin maidani shasha naje inata haushi ashema ban saniba kece kika amince mishi sai ɗazu Habu yake sanar min."

Mama fa bata tsagaita da masifaba bare tasan halin da Zaleeha ke ciki.

sai Zahira ne ta zaro ido da ƙarfi ganin yadda Zaleeha tasa hannu da tsananin ƙarfi ta kama kanta, 

yayinda tuni kunnuwanta sun toshe tun lokacin da Mama tace mata an kawo sadakinta kuma wai ga kayan aurenta a gabanta, 

sannan wai da yardarta uwa uba kuma wai da wancan ginannen taɓon ne da Allah ya ƙawatashi da kyan sura, 

daga nan bata kuma jin zancen Mama ba, sai rumtse idanunta da tayi tare da  cilla wani irin gigitaccen ƙara mai tsananin ƙarfi, haɗe  da cewa. 

"Ƙarya ne banice na turo shiba, bana sonshi! bazanyi aureba Wallahi, bazan zauna da kowaba sai wanda ya taimakeni!!."  

Sai ta kuma buɗe idanunta, wanda sukayi jazir ta kalli tarin akwatunan, wani irin gigitaccen ƙara ta saki wanda yasa, 

Ahmad, Habu,Aunty Lubna da suka nufo parlour'n  maman tun ihunta da sukaji na  forko  ya sasu shigowa a guje, 

suna shiga ita kuwa zaliha ta yanki jiki ta faɗi sumemmiya.


Da sauri Ahmad ya tarota ta faɗa jikinshi, 

cikin rawan jiki murya a hargitse yake ɗan jijjigata tare da marin kumatunta yana faɗin.

"Zaleeha!  Zaleeha!! Ki tashi Zaleehaaa!!!."

Sai ya kuma kalli Zahira daketa kuka tana cewa. 

"Shike nan ta mutu, tace muku bata son auren ba wanda take so ku barta ta jira wanda takeso anƙi gashi yanzu baƙin ciki zai kasheta.

Mama kuwa da sauri ta juya ta nufi falon Baba malam tana shiga tasa kuka tare da cewa. 

"Shike nan baƙin ciki zai kashe min ƴata, 

in ta mutu ai kowa ya huta sai a kaiwa shashashan musakin gawanta."


Shiru Baba malam yayi sai murmushin da yakeyi, Mamy kuwa da sauri ta miƙe zata nufi side ɗin Maman, 

dan da fari da suka jiyo ihun Zaleeha sunyi zaton ko uwarce ke dukanta, shiyasa data yunƙura zata je Baba malam ya dakatar da ita.


A can ɗakin Mama kuwa a kiɗime Lubna ke cewa Ahmad. 

"Hubby a sume take fa,  ko dai da gaske al'jani ne ya taima keta shine yau zasu baiyana kansu? Hubby mu kaita wurin Baba Malam!." Tafaɗi maganan cikin tsananin ruɗewa.


Yunƙurawa  Ahmad yayi da ita a jikinshi,  fita yayi da matsanancin sauri ya nufi parlour'n Baba Malam, 

a bakin ƙofa sukayi karo da Mamy.

Cikin tsoro da firgitan ganin Zaleeha kamar gawa Mamy tace. 

"Malam da gaske Zaleeha ba lfy."

Shi kuwa Ahmad a gaban mahaifin nasu ya direta tare da cewa. 

"Baba malam al'janine fa a jikin Zaleeha da gaske danfa kawai taji batun auren ne yasa ta suma."

Habu ne yaja wani dogon tsaki tare da cewa. 

"Ya Ahmad meyasa kake yarda wai Zaleeha iska gareta?."

Cikin tsawa yace da Habu. 

"To in ban yarda tanada iskaba meya sumar da ita? 

please Baba malam ayi mata ruƙiyya ko al'janin zaiyi magana."


Cikin takaici Habu ya juya gaban fridge ɗin dake gefenshi, buɗewa yayi tare da ɗaukan goran bottle water  mai ɗan karen sanyi, 

kana ya juyo marfin gorar ya murɗa kana ya ziraro da bakin gorar dai-dai saitin fuskar Zaleeha ya fara tsula mata ruwan sanyin. 

Wani irin wawan ajiyan zuciya taja, me ɗauke da azaban ƙarfi kana ta fizgo numfashinta da wani zazzafan kuka, 

cikin kuka mai cin rai ƙuna da kuma tsananin tsoro take cewa. 

"Bana sonshi Ya Ahmad ka gayawa Baba malam wallahi bana sonshi na tsaneshi!."

Sai ta kuma kamo hannun Ya Ahmad ɗinta da tuni ya fara zubda hawaye, cikin kuka taci gaba da cewa. 

"Ya Ahmad ka gayawa Baba malam mana, 

ka faɗa mishi cewa gurgu nefa haka kuma kurma ne, kace mishi bana sonshi na tsaneshi, 

wallahi in aka aura min shi zan mutu wlh ya Ahmad mutuwa zanyi!!!." Taƙare maganar cikin wani irin kukan fitar hayyaci.


Habu ne ya watsa mata wani zazzafan harara tare da cewa.

"To ki mutu mana! In kin mutun sai me? Ko kina zaton mutuwarki zaisa muma mu mutu ne?."

Faɗawa  jikin Aunty Lubna dake raɓe agefe  tana zubda hawaye tayi, cikin kuka da raunin murya tace. 

"Wayyo Allah na Aunty Lubna ki taimaka min ki faɗa musu inada wanda nake so, kice musu wlh bana son musakin can."

Cikin rauni Ahmad ya kalleta murya  a tausashe yace. 

"To meyasa kika ce mishi kin amince dashi ya turo iyayenshi tunda kin san bakya sonshi?."

cikin kiɗima da gigita tace. 

"Wallahi ban faɗaba wlh ƙarya yake min, to shida kurmane ta inama zaiji abinda zance mishi?."

cikin hatsala Habu yace. 

"Ba text messages kika tura mishi ba, da wayarki."

Miƙewa tayi a hargitse ta kalli Mahaifinsu da ya zuba musu ido, yana murmushin ganin ƙuruciyar yaran nashi, ba abinda ke sashi murmushi kamar yadda Ahmad yake taya Zaleeha kuka kamar yaro, 

yana jin daɗin zafin Habu dan yasan Habu Baban ya Aminu ya gado yayan Baba malam kenan, 

cikin kuka Zaleeha tace. 

"Wallahi ƙarya yake min ni bani da number shi ma."

Mama ce tayi kaffa tare da jan dogon tsuka. 

Habu kuwa falon Mama ya koma, 

jim kaɗan sai gashi da wayar Zaleeha riƙe a hannunshi, 

cikin takaici ya cire wayar a key dan yasan komai na wayar,  hakan kuma tsarinshine dan bincikar woyoyin ƙannenshi yasa su duk yasan komai na wayarsu. 

kai tsaye inbox nata ya shiga ai kuwa text biyar ya duba, ana shida sai ga text ɗin gama number shi da Saifuddeen yayi seven da My happiness.

Cikin zafin rai ya nuna mata wayar tare da cewa.

"Meye wannan?".

Ido ta zaro gaba ɗaya, ganin abinda ke rubuce da kuma haƙiƙa ita ta rubuta, kuma ta turawa number da aka sawa suna da my happiness, sai kawai ta miƙe ta koma can gefe nesa da mahaifin nasu ta fara buga tsalle tare da yarfa hannu tare da kurma ihu kana tana cewa. 

"Sharri! Sharri!! Sharri!!! Sharrine yayi min wallahi ƙarya ne ni bana sonshi!!!."


Ganin yanda takeyifa yasa Baba malam yin wani murmushi mai kama da dariya. 

Saura kuma gaba ɗaya ido suka zuba mata. 

Habu kuwa belt ɗin ƙugunshi ya zaro tare da yin kanta. 

ai fa tana ganin haka ta juya a guje tayi cikin gidan, shi kuma ya mara mata baya a guje, 

radadada kake jinsu a guje.

ganin yadda Habu ya bita yasa Ahmad binsu da gudu hakama Aunty Lubna da Zahira.


Zaleeha kuwa gudu take da iya ƙarfinta dan tasan Habu ba mutunci ne dashi ba. In ya kama duka kamar mara imani. 

Kai tsaye ɗakinta ta shiga cikin sa'a ta samu ta maida ƙofar garam ta rufe, 

tun kafin ya iso, 

ganin haka yayi kwaffa ya juya tare da cewa. 

"Yar iska kawai da ki tsaya mana."

Ita kuwa a cikin ɗakin wani irin fitininan nen kuka tasa da iya ƙarfinta, tana kuka da surutai cewa. 

Ita dai bata sonshi ta tsaneshi zata mutu in an aura mata shi.

Ahmad kuwa da Lubna rarrashinta sukayi tayi da bata baki amman ina. 

ranar haka ta kwana a rufe tana kuka da al'washin ciwa Saifuddeen zarafi.


Mama kuwa sosai taji daɗin abinda Zaleeha tayi, 

ta kuma yi niyar yaƙi da wannan auren.


Ƙarfe takwas dai-dai na safiyar ranar asabar Zaleeha fito cikin d'akinta inanun ta a kumbure tayi ja alamu tayi kukan  mai yawa.

gefen Mamanta ta zauna cikin sanyi tace. 

"Ina kwana Mama".

"Lfy."

ta bata amsa a tak'aice.

kai ta d'an sunkuyar ida nunta cike da hawaye tace. 

"Mama wlh k'arya yake min sharri ne, ni bance ina sonshi ba." kai Mama ta gyad'a mata cikin alamun gamsuwa tace. 

"To yanzu ya zakiyi?."

cikin k'arifin hali tace.

"Zan yi mgnin abun in sha Allah shida kanshi zai dawo yace ya fasa."

Cikin jin dad'in Mama tace. 

"Ke dai ki kafa ki tsare cewa bakya sonshi ni kuwa zan san abinda zanyi a kai."

To tace kana ta kira Zahira tare da cewa. 

"Je parlour Baba Malam ki d'auko min wayata".

Juyawa tayi ta nufi bedroom d'in Mama tare da cewa. 

"Gashi nan na d'aukoshi tun jiyan ai."

Amsar wayar tayi kana ta koma d'aakinta. 

Ita kuwa Mama murmushin jin k'arfin guiwa tayi tare da cewa. 

"Bazaki auri gurgu ba kam ko kina sonshi zan hana kuma wlh bazan bari kiyababanki boyayya kan arennamba dole zanyiwa boka bayanin yadda nake son yasa ki bijirewa wannaɓin da BAban naki ya miki, don   ko sama zata had'e da k'asa zaki auri Abdussalam dan shine dai-dai dake."

Tana kaiwa nan ta kira wayar Abdussalam yana d'agawa suka gaisa kana tace mishi, 

ya had'o komi da komai na aure ya turo iyayenshi Zaleeha ta yarda dashi. 


Jin haka yasa Abdussalam jin k'arfin guiwa nanfa yaci gaba da shirya lefenshi dai-dai da matsayinshi.


Ita kuwa Zaleeha konciya tayi kan gadonta sannan ta fara rubuta text kamar haka.


```Kai baka cancanci inyi makasa sallama ba, domin ita sallama ta masu amincine ba mak'aryata azzalumai irinka ba. nace maka bana sonka na tsaneka bazan soka ba har abadan, 

dan haka kayi maza ka turo wad'anda ka aiko suka kawo wannan tarkacen suyi maza su zo su kwashe gaiyar dukiyarka```

murmushi tayi lokacin da ta tura text d'in a ganinta ta k'unsa mishi bak'ak'en maganganu.


Saifuddeen kuwa yana zaune bisa kujerar wheelchair d'inshi Amman a dinning table, 

Ummi na had'a mishi tea yayinda yake cin soyayyan doya da kwai, 

jin wayarshi dake cikin al'jihunshi ta bashi wani alamun sak'o ya shigo kamar bazai duba ba, 

sai ya kuma zaro wayar ganin number tane ya sashi yin murmushin mugunta dan yasan, 

Kwanan zancen. 

ganin yanata murmushi Ummi yin murmushi dan farin cikinsa shine nata.

Raliya kuwa da Hayatuddeen suma murmushin suke tayasu. 


Bai bud'e text d'inba saida ya koma side d'inshi sannan ya bud'e ganin abinda ta rubuta ne yasashi yin maganar zuci. 

"Hmmmm wasa farin girki, yarinya kinga ta kanki." a zahiri kuwa yi yayi kamar baiga text d'inta ba bare ya bata amsa. 


Ita kuwa ganin shiru-shuru bai maida mata martini bane yasa da azahar ta sake tura mishi wani text d'in wanda yafi na safe zafi. 


Shiru ba amsa har dare, ganin haka ta kuma tura mishi wani text d'in. 


Har kusan k'arfe d'ayan dare tana jiran amsa amman cib ba amsa. 


Washe gari haka da asuban fari ta kuma tura mishi wani zazzafan text ,

Still ba amsa.


Abu fa ya isha Zaleeha yau kusan kwana uku kenan ba amsa, 

kuma bata fasa tura mishi bak'ak'en maganganu ba.


A gidan kuwa babu wanda ya sake mgnar auren Baba malam kuwa duk nacin Mama bata jin ta bakinsa. 


Habu kuwa shida Zaleeha hararace a tsakaninsu.


Zahira kuwa munafuka yar koren Mama ce.


Aunty Lubna kuwa ita ke hillace Zaleeha, 

har take mantar da ita batun wani aure. 


Ita kam Zaleeha ta fara sakewa dan ganin baya maida mata amsa sai take zaton yayi mubaya'a ne, 

koda wasa bata shiga d'akin Mama dan bata son ganin jerin akwatunan.


Ya Ahmad yanata shirin gobe zai tafi. 


Suna cikin hira ya kalli Zaleeha da ta d'an sake a hankali yace. 

"Ke Zaleeha kayan d'aki dana kitchen na wanne k'asane kikafi so kikega sunada ink'anci. 

cikin rashin fahimtar mgnar tashi tace. 

Gada je dai da kujeru Dubai komansu nada ink'anci da tsari.

Kayan kitchen kuwa na Chaina sunfi kyau." murmushi yayi tare da salonta yadda gaba d'aya hankalin ta na kan wak'ar da takeji a wayar Lubna, har tana cewa. 

"Yauwa Aunty Lubna tura min wannan wak'ar mana ina sonta tamin dad'i."

To Lubna tace tare da yiwa mijinta signal alamun sam fa Zaleeha bata gane komai ba.


Mama kuwa a sashinta ta kira yayarta Ruda ta shaida mata abinda ke faruwa, 

Jin haka yasa Ruda cewa cikin satin nan zata shigo gombe.


Maryam kuwa duk abinda akeyi bata saniba. 

shiyasa har ta kira Anty Aisha k'anwar mama ta shaida mata an kawo lefen Zaleeha biki kuma 27 next month.

Itama tace zata zo ganin lefe.


Saifuddeen kuwa Ishaq kadai ya gayawa abinda Zaleeha ke rubuto mishi nan Ishaq yace mishi ya barta sai tazo har inda suke, 

dan yasan zata zo.


Ya  Ahmad ya tafi harkan aikinsa, tunima ya bar k'asar.

in da ya bud'a bakin aljihunshi yake kashewa Zaleeha mahaukatan kud'ad'e na ban mmki wurin saya mata dukkan abin buk'atan amare.


Tafiya dai ta mik'a a lissafin yau saura mako d'aya ne auren.

tuni shirye-shirye sun kankama ta gefen ango da amarya.


Da hantsi misalin k'arfe 11:15 Am Zaleeha ta shigo d'akin Mama wanda lokacin kenan ta fito daga d'akinta da shirin zata wuce wurin aikita, jin

muryar Yayarta Maryam da Anty Aisha da Ruda yasa ta nufi d'akin a hankali ta shiga bakinta d'auke da sallama. 

sai kuma tayi turus a baki k'ofar ta tanya cikin tsananin kad'uwa da firgita, 

ido ta zubawa Maryam dake tsakiyar akwatunan ta bubbud'esu gaba d'aya tana nunawa Any Aisha kayan, 

Yayinda Mama kuwa da yayarta Ruda suke kan gado fuskokin nan nasu tamkar suyi ruwan jini kuma tuni sun barbaɗe ƙofar falon Mama da maganin da Ruda ta kawo wanda aka basu tabbacin in dai Zaleeha ta tsallakashi tofa bazata lamunci zaɓin mahaifin nataba zata tashi hankalin kowa har sai an janye batun auren. 

cikin sanyin murya Anty Aisha take cewa. 

"Allah ya sanya al'khairi yasa gidan zamanta kenan iya rai da mutuwa."

Maryam ce tace Amin Amin. 

sai kuma suka juyo suka kalli Ruda dake cewa. 

"Tir da addu'arki Aisha bakinki ya sari guntun kashi, 

kifa kalli wannan zuk'ek'iyar budurwa ki fasalta zamanta da gurgu kuma kurma musaki mara amfani kice Allah yasa gidan zaman tane. 

Ke kuma Maryam da yake baki da hankalin da kishin yar uwarki harda wani cewa Amin."

ita kam Zaleeha tamkar an dasa tane a wurin ta kasa tantance abinda kunnuwanta ke jiye mata daga bakin Maryam dake cewa. 

"Addu'a ita ta dace da Zaleeha tunda dai wannan abun yin Allah ne, 

ko ana so ko ba'a so in Allah yayi ita matar Saifuddeen ne dole taje gidanshi, 

kuma ke Mama kin san halin Baba malam me amfanin bad'i babu rai, 

yak'in da babu nasara ai gwara yin mubaya'a du du dufa auren nan saura sati d'aya ne rak."

Da sauri Zaleeha tasa tafin hannunta ta dafe k'ahon zuciyarta dake gab da tarwatsewa, 

idanunta ta rumtse da azabar k'arfi kanta ta fara jujjuyawa tare da zamewa ta durk'usa gaban Mamansu murya a hargitse tace. 

"Bana sonshi, bazan zauna da shiba, wlh mutuwa zanyi in aka had'ani dashi please Mama kiyi wani abu a kai."

Maryam ce ta d'an kalleta a tausashe dan tasan irin abinda Zaleeha keji a ranta tunda itama a dole aka had'ata da Ya Aminu amman gashi yanzu da tayi biyayya tabi umarnin iyayenta tana ganin ribar haka, 

duk da zafin zuciya irin na ya Aminu zama yake kamar bawa a gareta, 

baya son duk wani abinda zai sata zubda hawaye. 

shiyasa a hankali tace.

"Zaleeha kiji tsoron Allah kiyi biyayya ga mahaifinmu zakiga ribar hakan kada ki bari rud'in duniya ya Kaiki ya baroki. 

Ku dena yakice Saifuddeen dan nakasarsa dan babu wanda yasan k'arshensa, kuma in baka mutuba to ba'a k'are maka halitta ba,

shimafa bada larurarnan aka haifeshi ba, kaso 95 cikin 100 ba haihuwarsu ake da nakasaba a duniya suke samu. Kaso 5 ne na cikin 100 ake haifarsu da nakasa, 

because muma bamu da yak'inin a haka zamu k'are rayuwarmu."

Cikin tsawa da masifa Mama tace.

"Rufe min baki hegiya mara zuciya, 

mai mugun fata mu nan in sha Allah lfy lau zamu k'are rayuwarmu. 

Kuma wlh wlh muddin ina raye Zaleeha bazata zauna da wannan gurgunba. 

Dan ke kinada macecciyar zuciya sun tankwaraki kin zauna a dole to banda Zaleeha."

Cikin sanyi Maryam tace. 

"Kiyi hak'uri Mama ki gafarceni in furucina ya sosa miki zuciya."

ita kuwa Zaleeha mik'ewa tayi ganin sunk'i su sarara bare su saurareta, 

ficewa tayi daga gidan a guje.


A Cikin gidan kuwa, Anty Aisha ce ta kalli yayun nata cikin kafiya da fad'in gsky tacewa Mama. 

"Da hankalinki da tunaninki kike biyewa zugar wacce kin san batayi imani da Allah da manzonsa ba, bare ta yarda da k'addara mai kyau ko sab'aninta."

A zafafe Ruda tace. 

"Ke Rebeka ni kike gayawa haka?."

cikin tsuke fuska da tsawa tace. 

"An gaya mikin! K'arya nayi ne, imanin gareki tunda har yanzu baki samu tsarkin zuciyaba, kina kafura, 

mara lissafi zata zauna tana bin zugarki, 

lallai ke yar uwata ce kuma yayata Amman baki da hurimin kirana da Rebeka call me Aisha in bazaki iya ki bari."

A zafafe tace.

"don't call me Rebeka again."

Sai kuma ta juya ta kalli Maryam tace. 

"Maryam tashi mu tafi, ni dai ina bayan Baba Malam daga yau kuma zamu fara shirye-shiryen auren nan."

A hankali Maryam ta maida akwatunan duk wurin zamansu, 

sannan ta mik'e tabi bayan Anty Shatu kamar yadda suke kiranta kenan...


Mama kuwa da kafurar Yayarta Ruda, 

nan sukaci gaba da tubka da warwara, 

suna tubke yadda auren Zaleeha da Abdussalam, kana suna warware auren Saifuddeen.


Ita kuwa Zaleeha tana fita kai tsaye (Jonapwd)  ta nufa tuk'in takeyi tamkar wacce zata bar garin.

tana shiga harabar wurin tayi parking, cikin sauri ta fito gaba d'aya ida nunta dishi-dishi suke mata, 

kai tsaye office d'in Ishaq ta kutsa kanta sam bata iya amsawa mutanen nata gaisuwar da suke mata. 

shi kuwa Ishaq tun tana babban parlour yajiyo mgnar Sani na mata sannu da zuwa so koda aka turo k'ofar office nashi aka shiga yasan itane. 

Tana ganinshi kawai sai rauni ya rufe masifarta dan iya tsawon zamanta da ishaq a matsayin yayanta Ahmad take kallonshi ishaq yanada mutunci a ida nunta gashi last time ta surfa musu rashin ɗa'a kuma daga nan yake fushi da ita, 

a hankali taja kujerar dake fuskantar wacce yake zaune a kai ta zauna. 

sunkuyowa tayi ta kifa kanta bisa glass table dake tsakiyarsu kawai sai ta saki wani irin mawuyacin kuka mai cike da rauni da tarin k'uncin rayuwa.

cikin tsananin mmki Ishaq ya zubawa saitin inda yakejin kukan idanu tamkar yana ganinta. 

sai kuma yayi shiru kamar baya wurin yana jin sautin kukanta na ratsa kunnuwanshi. 

Kusan tsawon 10 minutes tana kuka, 

bai kulata ba, ita kuma bata bariba, 

har 20 minutes har ta zarta rabin awa tana kukan bil hak'k'i da gsky. 

daga jin kukan kasan daga cikin zuciyarta yake fitowa kukane mai tattare da k'una da tsoro,

sosai Ishaq ya fara jin tausayinta na kamashi ai ko ba komai ita macece kuma mai rauni.

cikin sanyin sauti yace. 

"Ya isa, ya isa haka Zaleeha kada ki cutar da kanki."

jin haka sai kukanta ya k'aru cikin kukan murya a raunace tace. 

"Malam Ishaq bana sonshi, wlh bana sonshi, na tsaneshi, inada wanda nakeso wanda ya bada ranshi da lfyarshi domin kare mutun cina pleaseeee Ya Ishaq kace mishi ya janye batun aure a tsaka ninmu, wlh muddin akayi auren nan cikin mu biyu dole d'aya zai rasu."

Sosai ya nitsu yana jin kala manta sai ya kuma ji alamun tazo tana durk'ushe a gabanshi a hankali tace. 

"Dan Allah Ya Ishaq ka zame min Garkuwa na mana a karo d'aya dai a rayuwa ta, 

dana rok'eka abu dan Allah dan annabi kaji tausayi na mana ka rabani dashi kar in rasa raina please ya Ishaq kada ka bari ayi min auren dole."

Sai ta kuma kife kanta bisa d'aya kujerar taci gaba da kuka. 

Sosai raunin ishaq ya halarto kan zuciyarshi, 

me zai hana ya taimaketa, to amman bari yaji meyasa bata son Saifuddeen, a hankali yace. 

"To waye kike son?." murya a raunane tace. 

"Ban sanshi ba?."

fuska cike da mmki yace. 

"Ina yake to me sunanshi?."

A hankali tace. 

"Duk ban saniba sau d'aya muka tab'a had'uwa shiyasa a gidanmu ake cewa wai ba mutun bane al'janine."

Da sauri yace.

"Yes al'janine mana nima haka zance, tunda shi gaibune."

kuka ta kuma sakewa, sai kuwa ta d'ago kanta jin yana cewa.

"To meyasa baki son Saifuddeen?. "

Rashin sani yafi dare duhu shiyasa Zaleeha tacewa Ishaq.

"Nakasasshe nefa shi gurgune kurma ne ta yaya zan aureshi da lfyata gurgunefa ananfa kuke cemin irinsu basa aure."

da sauri ta mik'e tsaye jiki na rawa ta koma gefe dan jin yadda ishaq ya buga table dake gabanshi tare da buga mata tsawa.

"To sai me!? Shi nakasasshe ba mutun bane!? Ko shi nakasasshe baida ikon auran lafiyayyiyar mace!? To wlh Zaleeha kinyi ganganci wannan furucin naki, ni babu taimakonki da zanyi in sha Allah sai Saifuddeen ya aureki ko zaki mutu ne.

Get out of my office!."

Ya k'areshe mgnar da k'arfi tare da mik'ewa tsaye. 

wanda saida mutanen cikin babban parlour nan suka jiyosu. 

Ita kuwa Zaleeha cikin tafasan zuciya ta juya ta fita dan yanayinshi ya bata tsoro.


Daga nan gidansu Rashida ta nufa, 

nan ta tasa Rashida a gaba tana kuka.

Murmushi Rashida tayi tare da cewa. 

"Hmmmm Zaleeha kenan to ni mai zance miki, 

kin dai san bazan baki goyon bayan ki bijirewa iyayeki ba, in dai k'awancenmu na gsky ne, 

sannan da kiketa mai-maita shi nakasasshe ne ke kinada tabbacin a haka zaki k'arene.

Zaleeha kifa farga ki dawo nitsuwarki kin gani ko wlh wlh dani Saifuddeen yace yana so na rantse miki da zatin Allah da hannu bibbiyu zan amshi soyayyarsa, 

Zaleeha inafa gaya miki kada kiyiwa kanki sakiyar da babu ruwa, kibi umarnin iyayemu ki samu rabauta duniya da k'iyama in zaki farga ki farga Ki daina wanna yarintar."

Cikin tsananin takaici ta ture Rashida da tasa hannunta tana share mata hawayenta a hatsale tace. 

"Sai yau na gane asalinki Rashida, ke farin cikima kikeyi da wannan abun har dariya kikeyi ko?."

Da sauri Rashida tace. 

"Tabbas farin ciki nakeyi abinda baki saniba, 

ko jiya muna tare da abokan ango, d'azuma na dawo daga can anguwar tasu federal law cos, layin Sabana hospital, wurin shagon Bash wani tela ne. 

Can suka kai kayayyakin d'inkinmu na biki naki da namu na k'awaye kuma komai yayi kyau, 

anjima kuma zasu zo batun shagulgulan da za'ayi."

Cikin mmki da tarin takaici Zaleeha tace. 

"Shegiya yar iska a ina kika sansu?."

Dariya Rashida tayi tare da cewa. 

"A wayar wani ɗan kawuna Jabeer naga hoton Saifuddeen sai yake cemin abokinshi, 

harma an kai lefe.

to nan nake ce mishi ai mune k'awayen amarya,

kinga daga nan komai yazo da sauk'i mu yanzu shirin bikin mukeyi babu kama hannun yaro. 

nice nan na kaiwa telan kayanki yadda zai d'inka komai dai-dai dake."

bazata fa juri jin tatsuniyar Rashida da ɗan kawunta Jabeer da sauran abokan Saifuddeen ba don haka ta zari car key d'inta ta bar gidan. 


Ita ko Rashida murmushi tayi tare da cewa. 

"Ayyah Zaleeha zuk'ar zuciya da rud'in shaid'an na d'awainiya da ke sun hanaki ganin nagartan Saifuddeen. 

Fatana Allah ya sanya al'khairi a aurenku."


Ishaq kuwa Zaleeha na fita ya biyo bayanta ranshi a matuk'ar b'ace, 

parking lot ya nufa ganin haka Ado drivarnshi ya biyu bayanshi bud'e mishi marfin motar yayi.

Bayan ya shiga ya maida marfin ya rufe, 

sannan ya shiga yaja motar suka fita, 

suna hawa kan titin da kyau Ado ya juyo ya kalli uban gidan nashi cikin girmamawa yace. 

"Ina zamu je?."

A takaice yace. 

"Gidan Saufuddeen."


A parlour'n Ummi ya samu Saifuddeen shi kad'ai, 

kamar babu kowa a gidan. 

bayan sun gaisa ne da salon yadda suke mgna, 

Ishaq ya rubutawa Saifuddeen duk yadda sukayi da Zaleeha yanzu,

yana gama karanta text d'in ya gyara zamanshi kana ya fuskanci abokin nashi cikin lumshe ido yayi wani tattausan murmushi tare da rubuta mishi. 

"Cool down my friend.

kada ka damu da duk abinda zatayi."

cikin jin haushi Ishaq fuskaci abokin nashi da kyau kana yace. 

"Saifuddeen ka hak'ura da Zaleeha mana tunda ba ita kad'ai bace d'iya mace, 

ita mafa macece kamar kowa ya za'ayi wasu na binka kai kana binta tana ci maka zarafi, na gaji Ka rabu da yarinyar nan, 

yarinyar da ikirari zata mutu in ka aureta kayi zuciya ka barta mana."

A hankali Ummi ta zame ta zauna a kujerar da Saifuddeen ya baiwa baya, ishaq kuma ba ganinta zaiba. 

Gaba d'aya jikinta rawa yakeyi. 

Tsoronto d'aya kada k'iyayya tasa Zaleeha ta cutar mata da d'anta, ya zatayi in wani abu ya kuma samun Saifuddeen d'inta d'a mafi soyuwa a zuciyarta d'an da yake k'arar da lokutanshi wurin sama mata farin ciki da kare martabarsu. tuni hawaye na zirya a kumatunta dan tana tausayawa zuciyar d'an nata da Allah ya jarbaceshi da son matar da bata sonshi.


Shi kuwa Saifuddeen kanshi ya jujjuya kana ya fara rubutawa ishaq mgna kamar haka. 

"Uhmmm Ishaq ai duk cikekken masoyi zai jure karan tsana. 

Zai jure kai kawo da zirga-zirga ako ina.

Kuma bazai nufi masoyinshi da hatsala ba.

Kuma ai ba'a son fushi a so sai dai hak'uri da juriya

domin yin fushi a so alamun rashin nasara ne, in sha Allah 

dole ne fa sai Zaleeha ta shigo gidane dolen-dolenta sai taga aikin ginennen tab'on nan da tace sai na shayar da ita ruwan mmki, barni da ita zata gane kurenta!."

cikin mmki Ummi ta zuba musu ido ganin sun tafa kuma ishaq ya saki wani irin shak'iyin dariya. 

"Saifuddeen kenan ya iya sarrafa harshe gashi daga fushi yasa ishaq dariya ko meye ya rubuta mishi sai Allah."

Ummi Ke fad'i a ranta lokacin data mik'e ta nufi bedroom nata dan bata son Saifuddeen ya gane taji zancensu.


Ita kuwa Zaleeha daga gidansu Rashida  gidan Hajja inna nufa, 

tana shiga kawai ta tasa hajja inna a gaba ta bud'e wani sabon shafin kuka.

Zakariyya ne dake gugun kayanshi dana Ziyada ya ajiye dutsen gugan tare da cewa.

"To yau kuma me aka miki?."

cikin kuka take cewa hajja inna. 

"Wallahi bana sonshi dan Allah ki cewa Baba malam yayi hak'uri kada ya min auren dole."

shiru tayi jin hajja Inna ta ja wani dogon tsaki,

kana ta b'alli tsallin goro ta afa a bakinta tare da taunashi, 

kai ta karkace tare da cewa. 

"To me ruwana a ciki, aure ne dai dole fa sai an aurar dake, 

na gaji da zamanki a gidan d'ana."

Dariya sosai Zakariyya da Ziyada keyi sabida abin na hajja Inna ba mutunci. 

suna cikin dariyar suka jiyo muryar Hayatuddeen da sauri Zakariyya ya tarbeshi cikin murna suka ruggume juna irin yar ruggumarnan ta gefe. 

kana suka zauna bisa 2 sitter.

Bayan sun gaisa da Hajja Inna ne Ziyada ta gaida Hayatuddeen cikin mmki Hayatuddeen yake tambayar meyasa Zaleeha kuka,

Zakariyya ne yayi dariya tare da cewa. 

"Wai kuka take dan za'a mata aure."

Dariyar shak'iyanci sukayi mata cikin dariyar Hayatuddeen yace. 

"Ato yarinya da kin san kina tsoron auren mai yasa zakisa gaye ya turo iyayenshi."

Ziyada ce ta d'an kalleshi cikin yanayin d'an sabonta dashi tace. 

"Ya Hayatuddeen ai bata son mijin ne shiyasa take kuka auren dole za'ayi mata."

da sauri ya matso kusa da Zaleeha wacce keta kuka hajja Inna kuwa nata aikin auna mata harara, cikin sanyi yace. 

"Allah sarki Adda Zalee gsky ba'ayi miki adalciba a dai wannan zamanin mace kekyawa big girl kamarki ace an miki auren dole, 

gsky dole kiyi kuka."

jin haka yasa Zaleeha fuskantarshi cikin kukan tace. 

"Kuma ina da wanda nakeso sannan su had'ani da wani can banza ginennen tab'o."

kai ya jinjina mata tare da cewa. 

"To meyasa bazakuyi mgna ta fahimtar junaba keda shi, 

ki gaya mishi kinada wanda kikeso, kice mishi koda ya aureki bazai ji dad'in zama da keba,

in ya amince ya hak'ura shine nan kin huta in ya kafe ya nace kuma kiyi hak'uri kibi umarnin iyayenki."

Cikin kuka tace. 

"Na tsaneshi bana sonshi ta yaya zan auri nakasasshe alhalin da lfyta."

shiru tayi ganin yadda a take fuskar Hayatuddeen ta canza launi da yanayi cikin had'e girar sama da k'asa mik'ewa yayi ya matsa gefenta tare da cewa. 

"Zancen banza kenan, ashema baki da hujja, shi nakasasshe ba halittar Allah bane, ko a zatonki Nakasa kasawa ce, 

aikin banza d'an adam da bai san k'arshenshiba yace yana kyaran larurar wani."

Gaba d'aya ran Hayatuddeen ya b'aci sosai sai yake tuno wata k'ilfa wata ran ayiwa Hamma Saifuddeen d'inshi irin wannan cin zarafin, haka kawai kalamanta sukayi masifar tayar mishi da hankali,

Hajja Inna ce tayi dariya tare da cewa. 

"Ato ai duk mai bin bayan Zaleeha zai shak'i takaici, yo wani nakasasshen ma ai yafi mai cikar halitta haiba."

Ita kuwa Zaleeha cikin kuka tace. 

"Bazaku gane bane. Gurgu nefa akan wheelchair yake rayuwa, kuma kurmane bayaji baya mgna."

Dam-dam zuciyar Hayatuddeen ya bada wasu tagwayen tarnaki mai cike da fargaba cikin zargin kai anya kuwa wannan bada Hammanshi take ba, cikin tsananin fargaba baki na rawa yace.

"Uhmmm me sunan shi ne!?."

cikin tarin tsanar tsuna taja wani dogon tsaki tare da mik'ewa kana tace.

"Wai Saifuddeen n!!!."

da sauri Zakariyya ya mik'e tsaye tare da cewa. 

"Hamma Saifuddeen.

Shi kuwa Hayatuddeen cikin k'arfi ya fizgo hannunta tare da zaro idanunshi da sukayi jazir tuni hawaye na shatata a kumatunshi har kan gemunshi cikin rawan murya yace. 

"K'arya ne wallahi Hamma na ba nakasasshe bane, domin nakasarsa bata zame mishi kasawa ba, 

Ke da kike zagin nakasarsa kinada tabbacin naki lafiyar ne, da har kike inkarin ke da lafiyarki, to wlh yanzu kika fara kuka ko zaki mutu sai kin zama matar kurma kuma gurgun nan, 

D'an uwane shine jigon rayuwar ahlinmu."

Sai kuma ya sake mata hannu ya koma ya zauna, Zakariyya ma tuni hawaye yake zubdawa, dan sai yanzu ya gane ashe Hamma Saifuddeen ne wanda yayarshi Zaleeha keta ƙi. 

hakama Ziyada hawaye take zubdawa, 

Hajja Inna kuwa cikin mmki tace. 

"Hayatu, ashe ma Saifuddeen kyakkyawa ne ta samu har take rigima.

Wlh ni ban saniba."

Cikin zubda kwalla shima Hayatuddeen yace. 

"Wlh Hajja Inna nima sai yanzu na gane data kira sunanshi da yanayin nakasarsa kuma,

na tuna ance min sunan matar da aka bashi Zaleeha ne."

ita kam Zaleeha juyawa tayi ta fita jin ƙaninta Zakariyya na cewa. 

"Wlh nima ban san akan Hamma Saifuddeen bane take wannan haukan da ko inda take bazanma kallaba."


Hajja Inna ce ta katsesu da cewa. 

"Ai kuwa ko mutuwa zatayi sai ta aureshi."

Sai ta kuma kalli Hayatuddeen cikin rarrashi tace. 

"Kayi haƙuri kaji ko Hayatu, dan Allah kada ka gayawa Umminku da yayunka wannan batun in sha Allah Zaleeha zata tanƙwaru."

Kai ya gyaɗa mata alamar to, 

sai ya kuma Kalli Zakariyya tare da cewa. 

"Dama nazo nefa muje gidansu Imran muyi batun dinner ɗin da za'ayi a bikin ne, ina son mu tsara fita ta musamman a wurin," cikin bada ƙarfin guiwa Zakariyya yace. 

"To muje, danko abu namune maganin a kwaɓemu."


Daga nan suka tafi gidansu Imran ƙanin ishaq.


Ita kuwa Zaleeha abu ya cakuɗe mata komai ya birkice mata, 

Yanzu ba mai bin ta kanta ta lura Aunty Lubna da Zakariyya basu damu da dmuwar tata ba 


Haka yasa dole ta ƙudurci son haɗuwa dashi ido da ido ayita ta ƙare. 


A lissafi dai yau saura kwana biyar ne auren. 

ganin har danginsu na Dukku sun fara zuwane ya ƙara tayar mata da hankalin. 

Gashi haka nan take jin kamar ana ingzata da zugata kan tayi wani mummunan abu.

 Shiyasa yau tunda safe taketa tura mishi text akan yazo gidansu zasuyi mgna mai mahimmanci ganin har yamma ba amsa ne yasa ta kira Ishaq bayan ta tuttura mishi saƙo dan Allah ya amsa kiranta, 

Yana d'agawa cikin rawan murya alamun zata fara kuka tace. 

"Dan Allah Malam Ishaq na rok'eka da manzon rahma kace yazo gidanmu inada mgna dashi."

cikin danne dariyarshi da sai yanzu kalamanta na wai sun ce mata irin larrarshi basa iya aure dariyar ya ɗan danne kana yace.

"Yaushe kike son yazo?."

Da sauri tace .

"Dan Allah yazo yau. Ban san in da zan sameshi ba da naje na sameshi."

wani munafukin murmushi ishaq yayi sannan yace.

"Ki duba hanyarshi zuwa bayan sallan isha."

Da sauri tace to kana ta katse kiran, 

a take ta kira Bilkisu dan tasan itace zata tayata ci musu zarafi ta yadda sai sun tsani kawunansu ma, aiko Bilkisu najin shirin Zaleeha tace gata nan zuwa.


Bayan sallan isha, Saifuddeen ne zaune bisa wheelchair ɗin shi kalar ruwan toka mai azabar kyau da sheƙi, a zahiri yadda yake caccanza sutura da ɗaukan wanka to hakama mota da wheelchair ɗinshi suma masu kyau da tsada ajin forko yake hawa hakama huluna da takalma, 

Sanye yake cikin wani d'anyen yadin voyel mai kalar shud'in sararin samaniya,  sai kuma ratsin fari fari tamkar gajumare, 

an ƙyanƙyasawa rigar aiki da surfani mai ruwan garai-garai, 

hannun rigar guntu ne masu zagayen zaren garai-garai d'in daga bakinsu, hannun yayi cib damatsan hannunsa da suke farare k'al-k'al masu yalwar gargasa mai tsawo da shek'in bak'i mai d'aukar hankalin duk wanda ya gansu sun zauna cib, 

hular damanga ya kafa a kanshi irin kafin nan da ake cewa baruwanka da duniya bi ma'ana ya d'an tura hular tayi baya, 

hular farace sai ratsin shud'in zare, sajen nan nashi ya kwanta lib-lib a kyakkyawar fuskarshi mai suturce da farar fata da kan sura jajayen labbansa sai Sheƙi sukeyi a cikin zagayen gashin bakinsa. 

hakama takalmanshi farare ne k'al sai layi biyu da akaja mai kalar shuɗin daga samansu, 

sai wani zazzafan agogon fata na Gucci mai kalar garai da manna a tsintsiyar hannunshi na dama, 

sai farin ring ɗin azurfa dake ɗauke da ɗigon diamond a tsakiyarshi daketa wal-wal,

wayarshi samfarin iPhone daya zura cikin al'jihun gaban rigarsa, wanda  kana iya ganin kusan rabin wayar ma a sarari.

Hayatuddeen ne ya lumshe ido tare da ƙara zuƙan numfashi dan shaƙan ƙamshin turaren Hamman nashi. 

Ummi kuwa ido ta zuba mishi cikin yin hamdala da godiya wa ubangijinta da azurtata da wannan kyakkyawan matashi a matsayin ɗanta.

Murmushi yayi tare da mishi fatan a dawo lfy bayan ya mata alamun zai fita. 

Hayatuddeen kuwa har bakin mota ya rakashi inda suka samu Ishaq da Sule direba suna jiran fitowarshi. 

Mota suka shiga sannan suka nufi New G.R.A.


Suna isa cikin gidan kuwa sukayi kicibis da Ya Aminu shi yayi musu jagora har cikin parlourn BQ kana yaje ya turo Zaleeha wacce, 

take tare da bilkeesu.

kusan a tare suka fito yana gabansu.

suna bayanshi suna tafe zuƙatansu fal farin cikin zasuci zarafinsu 


A harabar wajen suka samu  Ya Aminun da Ishaq suna mgna da alamun mai mahimmanci ce.


Suna shiga cikin parlour'n. Zaleeha tayi wani irin taku  me tattare da  izza ta isa gabanshi kujerar dake gefenshi ta zauna tare da ɗaura ƙafanta ɗaya kan ɗaya, a hankali take karkaɗa ƙafafun nata cikin tsaurin ido ta ɗago fuska tare da harba mishi ida nunta cikin nashi idanun. 

A hankali ya muskuta ya gyara zamanshi tare da sarƙe manyan idanunshi cikin nata idanun, kana yayi wani irin makirin murmushi tare da ɗaga mata girarshi ɗaya, alamun. 

"Baby ya dai ya akayi ne?."

Wani irin yam taji tsikar jikinta duka na amsawa, hatta gashin kanta saida taji ya amsa, 

wani irin azabebben kwarjini fuskarshi tayi mata tsoronshi da shakkarshi suka cika mata idanu. 

A gigice ta janye ƙwayar idanunta daga nasa,  tare da rumtse idanun Nata,  jiki na rawa murya a sarƙafe cikin zato da yaƙinin wannan ba mutun bane tace.

"WA innahu Sulaiman...!".




Yau dai ba editing


                             By

                 *GARKUWAR FULANI*

8/22/20, 5:15 PM - Ummi Tandama: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


          *NAKASA BAKASAWA BACE*


                              *PAGE 31*


                       ~End of part one~


                                *NA*

              *AYSHA ALIYU GARKUWA*



🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇



*WANNAN SHAFI GABA ƊAYANSHI NAKANE KYAUTA NA BAKA SHI Babana ALIYU IBRAHIM WAMMABI, inayi maka fatan al'khairi a rayuwarka Allah ya kauda mugun ido da mugun kunne daga kanka rabbi ya Al'barkaci rayuwarka yasa ka zamo al'waladdussaliha ga iyayenka. Allah dai ya raya mana mai sunan babana ka rage mishi rawan kai, ke kuma Zaleeha in na sake jin kin cewa babana A cici kazar birni nidake bibbiyu..*


_Fatan al'khairi ga WambaiFamly_


"Innahu Sulaimanu wa'innahu bismillahirrahamanirrahim!." 

Tafaɗa ƙasa-ƙasa  tana me watsa masa harara da manyan fararen idanunta, yayinda kuma idanun nata suke fallatsa tsantsar tsoron dake wanzuwa daga zuciyarta zuwa jikinta. 

Wani irin ƙawataccen murmushine ya bayyana akan fuskar Saifuddeen, sosai maganan nata ya bashi dariya, wato ma matsayin Aljani ta ɗaukeshi?.

Sake jawo wheelchair ɗinsa yayi ya ƙaraso gaf da ita,  wani irin killer smile ne ɗauke akan fuskarsa,  ƙasa yayi da kyawawan idanunsa masu matuƙar kyau sannu ahankali yake ƙarewa kekyawar surarta kallo,  jin yamatso kusa da ita ne yasanyata ɗago da kanta da nufin tasake watsa masa wata hararan, amman sai tayi maza tayi ƙasa da kanta dan kwarjininshi yi yawaita gareta, ɗan ƙaramin bakinta taturo gaba cikin son ƙuntata ransa tace.

"Amma dai kasan cewa bana son ka aureni, nafaɗa maka ni bazanyi aureba, aduniya babu wani abinda  na tsana kamar ayi min mgnar aure,  meyasa bazaka gane hakan ba? kada fa ka taɓa tunanin cewa wai aurena zai sama maka farin ciki,  wallahi bazan taɓa bari kasamu farin ciki a dalilina ba, zama dani tamkar kana kusanto da ajalinna  zuwa gareni ne, wallahi idan ka bari aka ɗaura aurena aka kaini gidanka zan mutu!."  

Taƙare maganar murya na rawa, domin kuwa wani irin tuƙuƙin baƙinciki ne, takejin na game gaba ɗaya zuciarta da jikinta. 

Sam ko sau ɗaya munanan kalaman nata basu shiga kansa ba dan shi yasa a ranshi bata da abinda zatayi mishi ta b'ata mishi rai, kana har yanzu killer smile ɗin dake kwance akan fuskarsa na nan bai kau ba, komai tayi  sai yayi gmagar zuci cewa.

"Uhumm kinci bashi, zaki biya, dan ni ba-bawan gidanku bane da xakiyi ta soka min baƙaƙen mganganu son ranki."

a fili kuwa yanda ƙananan laɓɓanta ke motsawa ya ɗan zubawa ido a fakaic,  jiyake kamar ya jawota jikinsa ya bata wani irin professional kissing,  lumshe idanunsa yayi tare da ɗan jingina bayansa da jikin kujeransa,  hannunsa ya ɗaura adai dai saitin zuciyarsa wacce ke beating da sauri-sauri, ɗan buɗe idanunsa yayi tare da watsa mata su, idanunsu ne suka sarƙe ajikin na juna da sauri tayi ƙasa da kanta, domin sam bata iya jure ganin idanun nan nasa masu birkita mata lissafi, wani irin malolon baƙinciki ne ya zo ya tsaya mata amaƙoshinta,  sosai tafito daniyar cin zarafinsu, tayanda gaba koda kuɗi akace suyi zancenta bazasuyi ba, amma kuma sai gashi ganinsa yasanya tanemi wutar bala'in dake cinta arai ta rasa,  tarasa shi wani irin mutum ne, mai tsananin kwarjini da haiba mai firgita zuk'atan magautanshi.

Zuwa yanzu kam tagama gamsuwa da cewa shiɗin al'janine, idan ba aljani bane to kuwa maye ne!.  

Kallon-kallo sukayi ita da Balkeesu, cikin salon ƙarin zuga Balkeesu tasaki wani ɗan iskan murmushi mai ɗauke da ma'anoni kala-kala, cikin yanayi na gatse haɗi da muzantawa, tace. 

"Musakan angwayenmu ina wuni ku!." 

Kafun ma sukai ga cewa komai tayi saurin cewa.

"Au ashema na manta cewa ginannen taɓon angon namu dutse ne, bayaji baya tashi gani kawai yake iyawa." Taƙare maganan cikin nishaɗi da son ƙufular da Ishaq, domin atunaninta shi Saifuddeen bajinta yake ba, itakuwa dama tunda idanunta ya sauƙa akan Ishaq takejin wani irin tsanansa acikin ranta, domin acewarta shine wanda yafara kawo Saifuddeen cikin rayuwar Zaleeha.

Shikuwa Saifuddeen duk abun data faɗa yajita sarai domin tun fara maganan nata yake kallonta.

 To amman shi ganinta yake kamar akuya aka shafawa jambaki asalima dariya take bashi, sai dai miskilancin ya danne sirrin zuciyarshi ta yadda sam Zaleeha da bilkeesu suka gane me yakeji game da kalamansu. 

Wani irin murmushi Ishaq yayi, tare da cije laɓɓansa, tabbas bazaice baiji zafin maganganun da Balkeesun ta faɗa musu ba, saidai kuma shima akwai wani tunanin dake yawo acikin ransa, saboda haka baya tunanin ayanzu zai tanka mata, saidai zai bari nan gaba kaɗan  zaisa tagane kurenta itama dan sai ya sata cikin komar nakasassu sai ya ganar da ita *Babu nakasasshe sai kasasshe.*


Rumste idanunta tayi sakamakon wani irin ɗaci da takeji amaƙoshinta, sam batason kallon dayakeyi mata, rai da zuciyarta tafasa suke, ayanzu aduniya bata da wani maƙiyi irinsa arayuwa taso taga zallan tashin hankali da tsoronta a ida Saifuddeen, amman ina Namijin duniya ya nuna mata bata da wani kalamin da zata gaya mishi wanda zai razanashi.

Sosai tayarda da abun da zuciyarta ke gaya mata hakan yasa ta miƙe tsaye, kallonsa tayi sama da ƙasa, kana ayangance ta watsa mishi k'ask'antaccen kallo, cikin yanayi dake nuna tsananin shakkar kwayar idanunshi taɗan ranƙwafo da kanta  kusa dashi, cikin son ƙuntata masa tace.

"Sam bakayi kama da namijin aure ba, saboda haka zaifi dacewa kabar cikakkun maza masu lafiya su tinkareni bawai kai nakasashshe ba,  baka da abun da zaka bani koda kuwa ka aureni bazaka iya zame min miji ba, kaiba Namiji bane, kai wani halittane dayakasance marar kumfa a saman ruwa  dana zauna dakai gwamma na tabbata ba aure tunda dai nasan da aurenka da tabbata ba auren duk d'aya ne."

Sai ta kuma fesar da zazzafan numfashi kana taci gaba da cewa.

"Naji shikenan tunda kanace lallai cewa dolen-dole wai kai saika aureni to daga yau kuma daga yanzu kafara ƙirga kwanakin mutuwarta!, saboda nasan zan dan rashin abinda rai kene zaiyi ajalina!,   mai wahalalliyar zuciya!.".

ta k'arishe mgnar tare zare mishi ido wai ita zata bashi tsoro.

Wani mugun kallo ta watsa masa kana ta juya cikin azama zata bar wajen domin kallon fuskarsama yana sata mata ɗimaucewa.

Azafafe Saifuddeen yasanya k'afarshi ya d'an tad'eta, lokaci guda tayi taga-taga tayi su zata faɗo.

Cikin tsananin tsoro da figita ta rumtse idanunta da azaban k'arfi tare rik'e numfashinta kana ta sakin k'ara mai cike da tsoro, dan tasan kan table dake gefenta zata dad'i kuma na glass ne, hannunshi ya mik'a daga zaune ya jawo mayafinta-ta fad'o  jikinsa, al'amarin daya girgiza Balkeesu kenan, shikuwa Ishaq dama ba gani yake ba hakan yasanya baisan nenene ya faru ba.


Manyan idanunta ta zaro waje, cikin tsananin takaicin haɗewar da jikinsu yayi waje ɗaya, 

a gigice tasoma kiciniyar ƙwace kanta, amma ina ƙarfin musakin da ta raina ya wuce tunaninta, don kuwa riƙo yayi mata bana wasa ba.

Yanayin idanunsa ne suka sauya daga farare zuwa ɗan garai-garai sai k'ank'ancewa da suka d'anyi kad'an, take jijiyoyin jikinsa suka mimmiƙe, yayinda lokaci guda yanayin fuskarsa ya sauya,  cikin zaƙuwa haɗi da takaici ta ɗago kanta daniyar auna masa wata mummunar baƙar magana, tuni maganar ta maƙale amaƙoshinta sakamakon yanda jikinta gaba ɗaya yashiga shock,  sosai ganin yanayin idanunsa ya tsorata ta, da sauri ta ɗauke idanunta daga garesa, cikin wani sabon fargaba haɗi da ɓacin rai da suka ziyartota ta tasanya hannunta ta bugi chest ɗinsa da ɗan ƙarfi, atunaninta idan yaji zafi dole zai sake ta, saidai amma ko motsi bataga yayi ba, jikintane gaba ɗaya ya ɗauki rawa sakamakon  yanda yake ladabtar da ita da wani irin kallonsa da idanunshi masu sata shayinshi da shakkarsa,   shikuwa Saifuddeen da gangan ya tsareta da idanunsa,  bakomai ya ɓata ransa cikin maganganunta ba kamar cewa da tayi waishi ba namiji bane, hmmm wai harshi Saifuddeen ne za aƙirasa da sunan  bacikakken Namiji ba, ahankali yake matso da fuskarsa gab da tata, wanda hakan yasanya gaba ɗaya ta ruɗe,  ahankali yake ƙara kusanto da fuskarsa gaf da nata, hartakai takawo numfashinsu ya cakuɗa dana juna, haɗuwar numfashinsu waje ɗaya, baƙaramin bugun zuciya ya haifar musu ba suduka biyun,  sosai zuciyar Zaleeha ke bugu kamar zata faso kirjinta tafito, akaron farko dataji wani matsanancin tsoronsa ya shigeta, don kuwa matsowarsa gareta baƙaramin zautar da tunaninta yayi ba, sosai yayi mata wani irin kwarjini a idanunta, sam batasan cewa haɗuwa da kyawunsa yakai har haka ba sai ayau ɗin daya kusanto da fuskarsa gareta, daga gefe kuwa fitinannen ƙamshin turarensa ne yacika hancinta,  lokaci guda jikinta yafara fitar da wani irin gumi da kerma da karkarwa, dake nuna tashin hankalin dake bunne cikin zuciyarta.

Haka Saifuddeen ya cigaba da kawo fuskarsa gab da nata, ahankali yake matsowa kamar zai haɗe bakinsu waje ɗaya, tuni Zaleeha ta rumtse idanunta jikinta kuwa rawa yake sosai, ta sadakar aranta cewa wannan musakin na sauƙe bakinsa akan nata, babu makawa saitayi kuka!,  Allah ma yasauwaƙe ita Zaleeha tasha yawun shi. 

Kawar da fuskarsa yayi zuwa gefen wuyanta, ahankali ya fesa mata wani irin numfashi mai tsananin ɗumi, wanda take yasanya tsikar jikinta mimmiƙewa,  hannunsa dake kan waist ɗinta ya janye tare daɗan matsar dakansa baya, jin ya sake ta yasanya ta sauƙe wata ɓoyayyar ajiyar zuciya, buɗe idanunta wanda suka kaɗa sukai ja saboda tsananin tsoritan da tayi, wani ɗan guntun tsuka taja tare da ƙwace jikinta daga cikin nasa, batare da tunanin komai ba haka Zaleeha ta tattaro yawun bakinta da tunanin zata tofar had'e tsukakkun lips d'inta tayi da niyar zata tofar da yawun. 

Sai kuma ta zazzaro idanunta woje tare yarfa hannu jin yadda Saifuddeen yasa yatsunshi biyu ya had'e lips d'inta da yaga tanada niyar yimishi tijarar da bazai lamunta ba, 

matse lips d'in nata yayi da k'arfi har saida taji fitsari na son kwabce mata. 

Ida nunshi ya jujjuya mata tare da k'ada mata kai kana ya d'an kamo gefen lip d'inshi na k'asa ya d'an ciza alamar. 

"Ko mafarki kikayi in kin farka kiyi sadaka."

kana ya sake mata lips d'inta da tuni sunyi jazir,

a tsoroce ta had'iye yawun nata tare da juya da sauri 

cikin tsoro da ƙunan da zafin da lips ɗinta keyi tace.

"Ɗan is kawai, Allah ya haneni ranan da zaka ƙara taɓani, mugu! Allah ya isana!! 

Kuwa wlh, koda wasa kada ka taɓa tunanin sake haɗa jiki dani, balle har  tunaninka yabaka daman kawo bakinka kusa da nawa, wlh dana sha yawun bakinka gwamma ace nasha tom-tom, saboda ko bakomai nasan tom-tom yafi ɗanɗanon yawun bakinka daɗi.

Ganin ya ɗan taɓa masarrafin  kekenshine ya nufi gareta, yasa ta juya da gudu-gudu

  

 tafice daga cikin falon kamar wace aka koro

Da sauri Balkeesu tatashi ta rufa mata baya bayan tagama watsawa Ishaq wani matsiyacin kallo.


Murmushi Saifuddeen yayi tare da sanya hannu ya shafo yawun bakinta dake  bisa kan yan yatsunshi  harshensa yasanya yaɗan lashi saliva ɗin, lumshe idanunsa yayi tare da sauƙe wani irin ajiyar zuciya, tunowa da magananta nacewa da tayi da tasha yawunsa gwara tasha tom-tom, yasanyashi sake sakin wani shak'iyin murmushi, cikin zuciyarsa yace.

"Am so sorry Zaleeha wannan al'ƙawarina ne insha Allah saina shayar dake  duk  wani abun dazai fito daga jikina, dazaran na aureki ba iya yawuna ba ma kaɗai harta spe... ɗinama saina shayardake." 


Dubansa yakai ga Ishaq wanda ke zaune shima murmushi ne ɗauke akan fuskarsa, don kuwa shima zuwa yanzu abubuwan Zaleeha da ƙawayenta sun soma bashi dariya, wani zubin kuwa idan Zaleeha tafaɗi wata maganar tsantsar yarintarta kawae yake gani. 

Zuciyarsu wasai batare da wani ƙunci ba haka suka baro gidan su Zaleehan.


Zaleeha kuwa koda suka bar BQ ɗin kai tsaye ɓangaren Mama suka nufa, afalon Mama Balkeesu ta zauna yayinda Zaleeha kuwa ta wuce ɗakinta kai tsaye ranta na bala'in tafasa, tarasa maiyasa bayajin haushi ko ciwon duk wata magana da zata faɗa masa.

Sosai al'amuransa ke bata takaici, duk da cewa shiɗin kurmane yakamata ace ae yana da zafin zuciya irin na kurame amma wani abu da ta lura dashi shine, shi kamar dutse yake ko bugunsa zakayi to sai kashirya kakuma saka duka ƙarfinka.

Hmmm Zaleeha taka a sannu zuciyar irinsu Saifuddeen bata tankwaruwa in ta hatsalo kada ki k'ureshi, wani sashi na zuciyarta ke rad'a mata a hatsale tace zaiko ci ƙaniyarsa a wurina. Ta fad'i kamar tana mgna da wani.


Balkeesuce ta kalli Mama wanda take zaune akan kujera 1 sitter fuskarnan tata aɗaure take tamau, ɗigon fara'a babu akanta.

Cikin iyayi da kisisina haɗi da zallan munafurci irin na Balkeesu ta gyara zama,  tare da fuskantar Mama murya kamar wacce zatayi kuka tace.

"Yanzu Mama haka zamu zubawa Zaleeha idanu takasance kullum cikin kuka? amatsayina na ƙawarta sam bazanso cutuwarta ba,  dan Allah Mama kiƙara sa baki akan maganar Saifuddeen ɗinnan wallahi Zaleeha bata sonshi, hasali ma babu wanda Zaleeha ta tsana sama dashi, Zaleeha kyakkyawace son kowa ƙin wanda yarasa, ni aganina tauye haƙƙine idan har aka haɗata zama da nakasashshe, wanda bashi da banbanci da dutse." 


Cikin tsananin baƙin ciki da takaici Mama ta watsawa Balkeesu jajayen idanunta, duk yanda kowa a duniya yakai ga ƙin son auren Zaleeha da wannan musakin to abayanta yake, domin ko tunowa da batun auren tayi saitaji wani abu kamar jiri na ƙoƙarin kada ita. 

Wani abu daya tsaya amaƙoshinta ta haɗiya,  ranta adagule cikin cushewar murya tace.

"Da ace zanbuɗe miki zuciyata ki gani Balkeesu da tuni kinsha mamaki, duk yanda wani yakai ga tsanar auren Zaleeha da wannan banzan musakin ninafishi,  duk da cewa ban taɓa ganinsa ba amma tsanar danayi mishi babu wani wanda na taɓa yiwa irinta!." Mama taƙare maganan cikin ƙunan zuciya. 

Ɗan jim tayi tare dayin ƙwafa, abayyane tace. 

"Badai dani suke wasan ba, Insha Allahu zasusha ruwan mamaki, in -dai-da-raina da lafiyata bazan taɓa bari ƴata Zaleeha dana haifa acikina ta auri wannan shashashan nakasashshen ba,  bazan taɓa bari wannan banzan auren da suke shirin ƙullawa ya tabbata ba, Ni nan nayi al'ƙawari ƴata Zaleeha ba zata taɓa auren MUSAKI ba!!.".

  Murya  akausashe Mama taƙare maganan domin kuwa ji take kamar zatayi aman wuta don bala'i,  alwashi ne bazata taɓa bari Zaleeha ta auri Matsiyacin gurgu kuma mayataccen kurma ba, tayi al'ƙawarin saita tashi hankalin kowa dake gidan, sannan kuma sai takau da duk wani zaman lafiya dake cikin gidan matuƙar akaƙi bin zaɓinta. 

Cikin jin daɗin kalaman Mama Balkeesu ta saki wani ɓoyayyen killer smile, tabbas so take Mama ta jajirce wajen ganin Zaleeha bata auri Nagartaccen Namiji kamar Saifuddeen ba, tasan cewa Saifuddeen nakasashshene, amma sam ita bata hango nakasartasa, don kuwa babu wata nakasa da ta nuna ajikinsa, hasalima ita bata taɓa ganin wani nagartaccen Namiji kamar Saifuddeen ɗin ba, tahango abubuwa da yawa dangane da Saifuddeen ɗin wanda maza da yawa basu dashi, irin Saifuddeen sune mazan da suka fi ƙaranci aduniya, haka kuma irin sa mata da yawa ke fata da burin samu matsayin abokin rayuwa. Kullum haushinta d'aya kada Zaleeha ta rigata aure, kuma kada ta fita samun miji na nunawa sa'a shiyasa ta dage ta raba Manager da son Zaleeha tana ta son cusa kanta gareshi, dan Raveel dai ya nuna mata baya tare da ita, A wani sashi na ranta kuwa dadi takeji dan in zaliha ta auri nakasasshe ta samu abin nunawa mutane tawayarsa.

Miƙewa tsaye tayi yayinda ta nufi ɗakin Zaleeha. 


Zaleeha kuwa tana shiga cikin ɗakinta, kai tsaye kan lallausan gadonta ta faɗa, cikin tsananin baƙin ciki da takaici haɗi da tsanar Saifuddeen tashiga rera kuka, tayaya zai fuskanci cewa ta tsanesa? mai yasa bazai gane irin tarin tsanar da tayi masa ba ya rabu da ita? meyasa shi baida zuciya? ta tsanesa tsana irin ta wuce misali, sam batason duk wani abu da ya shafesa, ganin fuskarsa na sawa tanajin kamar takashe kanta, meyasa har yanzu kowa ya kasa fahimtar irin raɗaɗi da kuma zafin da takeji? meyasa kowa yakasa sanin zafin ƙiyayya irin wanda takeji, mutum ɗaya takeso aduniya shi ɗaya za kuma taci gaba da so, har iya ƙarshen rayuwarta,  batajin zata so wani koda kuwa kwatan kwacin rabin yanda takeson wanda yakasance mai taimako agareta,  abu ɗaya tasani shine, ko duka mutanen duniya zasu taru suyi mata kallon mahaukaciya akan son da takeyi masa to bazata taɓa fasawa ba, koda kowa zai yi mata kallon shashasha, tayarda zata amince za kuma ta jure matuƙar akan soyyayarsa ne, tariga tasa aranta cewa komai wahala komai daɗi,  komai kusa komai nesa zata bada kai da ƙarfinta wajen zaman jiransa, sau dayawa zuciyarta na gaya mata cewa watarana zaizo gareta, ta kuma aminta da hakan, saboda haka tasa aranta cewa, har abada bazata taɓa daina so da ƙaunarsa ba.


Balkeesu ce ta turo ƙofar ɗakin ta shigo, ganin Zaleeha kwance na kuka, yasanyata taɓe baki, cikin ranta tace.

"Bakiyi komai bama Zaleeha, sai alokacin da idanunki suka buɗe ki ka gane cewa kinrasa nagartaccen namiji  kamarsa, daga wannan lokacin zakiyi kuka irin wanda ake ƙiransa da sunan kuka bawannan sharan fage ba, wanda ni kuwa dama hakan shine burina." 

Afili kuwa ƙarasawa gaban gadon tayi tare da zama abaki bakin gadon, cikin son  zuga tasanya hannu ta dafa kafaɗan Zaleeahan, cikin ƙoƙarin ɓoye manufarta tace. 

  "Kuka baya maganin damuwa Zaleeha, sam kuka bai kamaceki ba ba kuka yakamata ace kinyi ba." 

Afusace Zaleeha ta tashi zaune, fuska caɓa-caɓa da hawaye tace. 

"Bakuka yakamata nayi ba? dariya kenan kikeso nayi mai gado? okay nagane saboda ke bakisan zafin ƙiyayya dana soyayya ba ko shiyasa zakice haka, da ace kinsan yanda nakejin zafi a zuciyata wallahi da ke ce zaki fara cewa naƙara sautin kukana tayanda gaba ɗaya Nigeria zasu jiyoni bama iyaka Gombe kaɗai ba, Natsaneshi Mai gado, Natsaneshi, banason koda ganin fuskarsa, aurensa dai-dai yake da tarwatsewan zuciya da rayuwata gaba ɗaya, da ace na buɗi idona naganni matsayin matarsa gwara ace na wayi gari bana numfashi.!"


Wani irin ƙatuwar ajiyar zuciya Balkeesu ta sauƙe, tabbas haƙanta gaf yake da cimma ruwa, saidai kuma har yanzu bata hango irin zazzafar  tsanar da takeson Zaleeha tayiwa Saifuddeen ba, haƙiƙa komai na Zaleeha na bayyanar da tsanar Saifuddeen saidai ita har yanzu akwai abun da bata gamsu dashi ba. 

Cikin yin ƙasa da murya tace.

  "Bance kiyi dariya ba Zaleeha, ni ƙawarkice maison duk wani abun da kikeso, saboda haka burina shine ki samu wanda kikeso,  kishare hawayenki Zaleeha, saikin cire tsoro haɗi da kunya kin fuskanci kowa sannanne zaki samu cikar burinki, saikin dage kin kuma ɗaga hankalin kowa dake gidannan, sannan zasu fuskanci cewa babu soyayyar Saifuddeen aranki."


Ɗago jajayen idanunta wanda suke cike da ƙwalla tayi ta kalli Balkeesu, murmushi Balkeesu tayi tare da dafa shoulder ɗinta, cikin son tarwatsa nutsuwar Zaleehan tace.

   "Nasan kin fahimci abunda nake nufi, dole ne ki tashi tsaye wajen ganin kin samawa kanki ƴanci,  wani irin kallo kike tunanin mutane zasuyi miki aduk sanda sukaji cewa da kyawunki da komai  kin kashe ƙuruciyarki wajen auren nakasashshe? ki dubeki Zaleeha, kyau, ilimi, diri, hutu, wayewa, aji, sanin darajar kai, duk fa kin mallakesu, babu wani ɗa namiji da zaki gifta ta gaban idanunsa matuƙar ya amsa sunansa namiji ace baiji komai game da ke ba, sam bakiyi kama da matar nakasashshe ba, zama da nakasashshe kuwa agareki tamkar tarwatsa rayuwarki ne!." 

Ɗan tsagaitawa da maganan tayi tare da miƙewa tsaye, duban Zaleeha tayi da kyau, tare da sakin wani ɗan guntun murmushi, ahankali tashiga takawa harta ƙarasa jikin ƙofar fita daga ɗakin, juyowa tayi still fake smile ne ɗauke akan fuskarta, cikin son tausasa zance tace. "Nabarki lafiya ƙawata, ina fata zakiyi tunani me kyau akan maganata, idan kuma kin amince nakasashshen kurma yazamanto ango agareki am fine, mudai always zamu tayaki murna." Tana kaiwa nan azancennata ta murɗa handle ɗin ƙofar ta fice, tana sakin wani dariya mai ɗauke da tsananin mugunta. 

Lumshe idanu Zaleeha tayi saiga wasu sabin hawaye shaaaa sun kwaranyo daga cikin idanunta, wani zafi-zafi ɗaci-ɗaci haka takeji acikin maƙoshinta, cikin ɗaya daga cikin trow pillows ɗin dake watse bisa kan gadon ta jawo ɗaya, tare dayin hugging ɗinsa a ƙirjinta, kanta ta jingina da saman gadon tare da sake sakin wani sabon kuka, sosai shawaran Balkeesu yasamu mazauni acikin zuciyarta, don ta ƙudurta aranta cewa daga yau babu wani wanda zai ƙara bacci cikin daɗin rai acikin gidan, saita ɗaga hankalin kowa, bazata nutsa ba kuwa harsai taga ta samu abunda takeso...


Ɓangaren su Saifuddeen kuwa daga gidan su Zaleeha kai tsaye wani babban Cafe dake cikin unguwar federal lowcost suka nufa, wanda ananne suka narka kuɗi don buga musu ƙawataccen katin auren nasu wanda yanzu kwana biyar ne kacal ya rage,  koda sukaje tuni suka samu an gama kammala musu komai, nanfa suka amsa,  daganan gidansu Ishaq suka wuce, domin kuwa musamman Ummu'n Ishaq taturowa Saifuddeen ɗin  saƙon text message akan cewar tayi masa tuwon semovita miyar moringa (zogale) sanin cewa yana matuƙar son miyar, koda sukaje gidansu Ishaq ɗin nan sukaci abinci suka ƙoshi, domin kuwa harda wani irin daddaɗan coconut drinks da kuma zoɓo Ummun ta haɗa musu,  anan gidansu Ishaq ɗin Ahmad da Salisu da Jabeer sukatarar dasu, suka  karɓi kusan rabin katin,  daga  gidansu Ishaq ɗin kaitsaye Ahamd wajen ƴan uwa da abokan arziki ya nufa inda yadinga raba musu katin auren nan kowa yake cika da murna da kuma fatan al'khairi.

                  ***


Ƙarfe 6 dai-dai jirgin Azman Air Land ya sauƙa ababban airport ɗin dake cikin garin Gombe, wato Gombe International Airport,   mutanene da dama cike a airport ɗin, dagani kowa da wanda yazo tarba, can nesa kaɗan na hango wasu matasan samari wanda aƙalla zasu kai su 10 sunyi gungu guda, gabaki ɗayansu hankalinsu naga ƙofar fita daga cikin jirgin.

Sannu ahankali mutane keta sauƙowa daga cikin jirgin,  shine wanda yayi kusan na ƙarshen fitowa.

 Cikin isa, izzza, haɗi da zallan iskanci da kuma tsageranci, haka yake sauƙowa daga kan matattakalan  jirgin, kallo ɗaya zakayi masa kafuskanci cewa riƙaƙƙen ɗan iskane irin wanda babu wanda ya isa sashi babu kuma wanda ya isa hanashi,  ko daga nesa ka hangosa saiya baka tsoro balle kuma ka kai gayin face to face dashi, *Dalla* kenan, riƙaƙƙen ɗan iskan da ya riƙa a iskanci, sannan kuma sunansa ya buwayi ko ina na cikin gombe, babban tashin hankalin ko wacce ƴa mace shine wani ya ambato mata sunan Dalla, musamman ga waƴanda suka sansa, sam baya ragawa mace wajen yi mata Dalla-Dalla da virginity ɗinta. 

Cikin yanayinsa  dake nuna nutsewarsa acikin daba yaƙarasa sauƙowa daga kan matakalan jirgin.

  Da wani irin ihu haɗi da shewa yaransa sukayo kansa, cikin tsananin jin daɗin ganinsa da kuma murnar samun lafiyansa,  suka shiga yi masa ƙirari da yi masa take irin nasu, take kan Dalla ya ƙara huruwa har takai ha yanajin kansa kamar wani sarki, nan yasoma ɗaga kai yana hura hanci,      cikin nuna isa da halinsa wanda sama da shekara ɗaya yakasa sanjawa ya dubi yaran nasa, hannayensa ya zura acikin aljihun wandonsa, tare da ɗage kansa sama, cikin murya da yanayin magana irin tasu ta riƙaƙƙun ƴan daba yace.

"Allah yayi dawowana yau, bayan nashafe sama da shekara ɗaya ina jinya a k'asar Jermany,  Wallahi Na rantse da  sarkin dake busan numfashi, babu wani mahaluƙi aduniya daya isa ya hanani yiwa yarinyar da a sanadinta na haɗu da lalurar da takaini.shafe sama da shekara ina jinyan kaina Dalla dalla, ni Dalla al'ƙawari naɗaukarwa kaina cewa duk inda tashiga tafita saina nemota, zan banƙarata kamar kaza, sannan zanyi mata dalla-dalla irin wanda ban taɓayiwa wata mace ba, zan keta mata haddi irin ketawar cin zarafi, sannan zanyi watsi da duk wani mutumcinta, wallahi saina yaga rigar budurcinta na tarwatsa shi tayanda bazata ƙara numfashi ba bare takai ga yin motsi, idan kuwa har hakan bata kasance ba Ni Dalla ban haifu acikin uwata da ubana ta hanyar sunna ba, sannan kuma al'ƙawarine akanta zan fara gwada lafiyar dana shafe tsawon lokuta ina nema!!!." 


Ihu haɗi da kirari yaran nasa suka yi masa, haka suka cigaba da masa kirari suna ƙara fasa masa kai, shikuwa Dalla tuni kansa ya ƙara girma, ayanzu burinsa ɗayane a duniya shine ya damƙi tsinaniyar yarinyar nan da sanadinta ya fita daga sahun mazaje tsawon wasu lokuta, haka suka cika mota shida yaransa ƴan daba, kaitsaye babban gidan na Dalla wanda acanne yake hutawa idan yazo suka nufa, inda nan cikin unguwar shango estate gidan yake. 

 

    ***

Ummi ce zaune akan makeken gadonta, yayinda gaba ɗaya hankalinta sam baya jikinta, sosai tayi nisa cikin tunani,  zuwa yanzu kwata-kwata takasa jure rauni, damuwa, fargaba, haɗi da tsoron dake kwance cikin ranta,  sam kwana biyunnan bata tare da nutsuwarta, wani irin tsoro haɗi da fargaba suke cika zuciyarta, har yakai ga ko bacci take fargaban baya barinta, sosai al'amarin auren na Saifuddeen ke mugun ɗaga mata hankali,  kwata kwata bata da nutsuwa akan maganan auren, musamman yanda labarin irin tsanar da Zaleeha keyiwa Saifuddeen dayazo kunnenta,  ko acikin ƴaƴanta son da takeyiwa Saifuddeen daban yake, har acikin jininta takejin soyayyar ɗan nata, sam koda wasa bata ƙaunar abun da zai cutar mata da Saifuddeen ɗinta, haka ko kaɗan batajin son wanda bayason Saifuddeen ɗinta, sosai takejjn tsoron abun da zaije yazo idan Saifuddeen ɗin ya auri Zaleeha,  daga gefe guda kuwa tsananin tausayin Saifuddeen ɗin ne kullum ke ƙara cika zuciyarta,  musamman yanda ta lura da irin sonda Saifuddeen ɗin keyiwa Zaleehan kamar ransa, aduk sanda ta so tunkarar Saifuddeen da maganar son fasa auren nasa da Zaleeha, takansamu kanta cikin rashin ƙarfin guiwa domin kuwa da ta kallesa zata hango tsantsar soyayyar da yakewa Zaleehan kwance acikin idanunsa, wannan shine abun da yake karya garkuwanta ako da yaushe,  ɗan numfasawa Ummin tayi tare da sauƙe ajiyar zuciya, a hankali tace. 

"Lallai yanzun kam bazan iya jurewa ba, dan dole zan aiwatar da abun dake zuciyata, sam bazan taɓa yarda in zuba idanu inga Saifuddeen yakai kansa inda za'a halakar min dashi ba, shiɗin garkuwa ne agaremu, muna tsananin buƙatarsa, daga ini har ƴan uwa da abokansa bazamu taɓa son abun da zai cutar dashi ba, saboda haka na gama yanke shawara tabbas zan ƙira Baffa Ali da Malam Ashiru kamar yanda sukaje suka nemawa Saifuddeen ɗin auren Zaleeha, to ayanzu ma zasu koma suce Saifuddeen ɗin ya janye, saboda kwata kwata babu wani alfano wajen auren matar da bata sonsa, babu komai cikinsa sai, danasani, baƙin ciki, da kuma tashin hankali, sam kuma bana fatan Saifuddeen ɗinna yaji koda ɗaya daga cikin waƴannan ne, burinna shine yayi aure yaji daɗi, ya kuma samu kwanciyar hankali, da nutsuwa, sam bana fatan akasin ɗaya daga cikinsu ya samesa, saboda haka na aminta da shawaran da zuciyarta ta yanke min, dole ne za'a  fasa auren Saifuddeen da Zaleeha." ta k'arishe maganar tare da kwanciya. 


Hayatuddeen da abokansa kuwa, tuni suke ta murnar bikin, inda suka shirya partyn da zasuyi a bikin nasu na musamman,  tuni Hayatuddeen ya watsa hotunan katin auren ashafinsa na Instagram da kuma WhatsApp status ɗinsa,   tuni Ameena ta haukace masa da tayi tozali da invitation card ɗin, nan tafara kuka yayinda zuciyarta tacika da kishi haɗi da raɗaɗin auren na Saifuddeen da zaiyi, wasa-wasa fa Ameena harda kwanciya zazzaɓi.

Asma'u ma sosai tayi takaici domin bata da wani buri daya wuce kasancewarta da Saifuddeen, ita kanta batasan soyayyarsa tashigeta sosai ba saida taga katin na aurensa da Zaleeha kuma dai hakan baisa ta sauya k'udirinta ba.



Ɓangaren Zaleeha kuwa tun jiya da ta sa kanta aɗaki ta kulle bata ƙara ko leƙowa ba, gaba ɗaya haka ta wuni cikin ɗaki, zuciyarta cike da ƙunci, haɗi da takaici,  tuni tagama shirya duk wani plant ɗinta na yanda zata fitowa da ƴan gidannasu sabon tsarin takunta, na yanda zata rufe idanunta ta shumfuɗa taɓaran ƙin auren Saifuddeen da ake ƙoƙarin laƙaba mata. Hakanan ta-tashi yau da son zuwa gidan yayarta Maryam, don haka tun safe ta kammala shirye shiryenta,  wanka tayi inda ta shirya kanta cikin wata haɗaɗɗiyar doguwar riga navy blue colour mai kyaun gaske,  sosai rigan tabi shape ɗin jikinta ta ƙafe, yayinda adon stones ɗin rigarta keta shinning yana ɗauke ido, parking dogon gashinta tayi atsakiyar kanta, kana tayi rolling ɗan maidaidaicin vail ɗin rigan  akanta, wanda ya sauƙo har zuwa kan  ƙirjinta, wani ɗan maidaidaicin hand bag ɗinta shima me kalar navy ta riƙe ahannunta tare da ɗaukan wayoyinta, ƙiran iphone da kuma samsung, wani navy blue toms masu kyau da taushin gaske ta sanya aƙafafunta, wanka tayiwa jikinta da daddaɗan turarenta mai daɗin ƙamshi, sosai tayi kyau duk da kasancewar ƴar rama ta bayyana ajikinta amma tayi kyau sosai, raman ma saiya kasance yaƙara mata kyau da burgewa. 

Cikin takunta mai ɗauke da burgewa tafito daga cikin ɗakin nata, bata samu kowa acikin falon ba hakan yasa kai tsaye ta nufi compound ɗin gidan,  cikin nutsuwa taƙarasa jikin motarta, buɗe murfin motar tayi tare da shigewa ciki, maigadi ne ya wangale mata gate sannu ahankali tatura hancin motar tata waje, cikin nutsuwa haka take murza steering motar, azahiri idan kaganta bazaka taɓa tunanin cewa wani abu na damunta ba, amma abaɗini tanajin kusan ma tafi kowa yawan damuwa, sosai takejin kamar zuciyarta zata fashe saboda damuwa,  batayi wani tafiya sosai ba taƙaraso gaban gidan na Maryam wanda yake madaidaici mai kyaun gaske,  maigadi ne ya wangale mata gate ɗin gidan ta cilla hancin motar ciki. 

Da mamaki take kallon  motar Yaya Ahmad dake fake cikin compound ɗin gidan na Maryam, sam batasan ma da zuwansa cikin garin na Gombe ba, da ɗan sauri ta bude murfin motar tafito, direct ta nufi cikin gidan, ahankali ta murɗa handle ɗin ƙofar tashiga, bakinta ɗauke da sallama,  Ya Ahmad, Maryam, sune zaune acikin falon yayinda suka juyo da kallonsu gareta,  idanunta ne suka sauƙa acikin na Ya Ahmad,  saurin ɗauke idanunta tayi tare da turo bakin nata gaba, lokaci guda hawaye suka cika idanunta, sai kawai ta kawar da kanta gefe, cak kuma ta tsaya batare da ta ƙaraso tsakiyar falon inda suke zaune ba.

"Zaleeha!." Maryam taƙira sunanta murya asanyaye, domin tuni ta hango ƙyallin hawaye acikin idanun Zaleehan.

Ɗan juyowa Zaleeha tayi ta kalli yayarta ta,  sai kuma ga hawaye zirrr sun ziraro daga cikin idanunta,  rumtse idanu Ya Ahmad yayi tare da ɗan cije laɓɓansa, sam baya ƙaunar ganin hawaye a idon ƙannensa, musamman ma ita Zaleeha dayakejinta matsayin shalelensa,  cikin son sama mata nutsuwa yace.

"Bansan ƴan matan Yaya Ahmad da saurin kuka haka ba, nasan dai tana da juriya sosai, calm down my lovely sister, zo kigayamin menene damuwar da har tasanyaki hawaye!". 

Ae tuni kafun ma yaƙare maganar tasa ta rugu da gudu zuwa cikin falon, faɗawa jikinsa tayi tare da sakin wani irin kuka mai taɓa zuciya, ƙwarai tajima bata samu wanda zata shiga jikinsa tayi kuka haka ba sai yau, hakan yasa ta ƙara riƙe Ya Ahmad ɗin nata tana kuka sosai, shiru Yaya Ahmad da Maryam sukayi, sam sun kasa hanata kukan, domin sunyi imani cewa kuka ma rahamane, sannan wani lokaci yana gusar da damuwa,  kana kuma duk cikinsu babu wanda baisan kukan me Zaleehan keyi ba, domin dama ansan tatsuniyar gizo bata wuce ta ƙoƙi, tayi kuka sosai, aƙalla ta share sama da mintuna 15 tana kuka, sannu ahankali kukannata ya tsagaita, ajiyar zuciya kawai take sauƙewa akai-akai,   ɗagota daga jikinsa Ya Ahmad yayi tare da kai dubansa gareta,  hannu yasa ya goge hawayen da gaba ɗaya suka dame fuskarta, cikin tausasa murya yace.

"Akullum tun kina ƙarama nakasance ina me horanki da ki-kasance mai haƙuri, Domin shi haƙuri yana maganin abubuwa da yawa Zaleeha, sannan Addu'a tafi kuka don itace babban jigo akan komai, ke ƴar uwata ce kuma jinina, bazan taɓa son ganinki cikin damuwa ba, amma yazamuyi Zaleeha? yarda da ƙaddara mai kyau ko akasinta alamace dake nuna ƙarfin imanin mutum, sannan kada ki manta kowani bawa a duniya da irin jarabawar da Allah yake ɗaura masa, wani mai kyau wani akasinta, shin meyasa bazaki sa aranki cewa aurenki da ake ƙoƙarin yi  da Saifuddeen haɗi ne na Allah Ba? babu fa wani bawa aduniya daya isa sauyawa kansa Ƙaddararsa!." 

ɗan tsagaitawa da maganan yayi kana ya sanya hannunsa ya shafi kanta, cikin son kwantar mata da hankali yace.

"Kaf cikin ƙannena nafi ƙaunarki Zaleeha, inason duk wani abu da kikeso, banason ɓacin ranki ko kaɗan, dan Allah Zaleeha, kada ki watsawa mahaifinmu ƙasa a ido, kizama mai biyayya agaresa koda yaushe, ita al'barkan iyaye tana da tasiri akan ƴaƴa, har abada Baba Malam bazai taɓayin danasanin zamantowarki ƴa agaresa ba matuƙar kikayi masa biyayya,  zai tabbata yana me alfahari dake,  ki yi dubi ga ƴar uwarki".

 Ya nuna Maryma wanda take zaune itama idanunta sunyi rau rau, kana sun cika da ƙwalla.


"Maryam takasance abun al'faharin Baba Malam, tayi masa biyayya, bata bijiremasa ba, tayarda da zaɓinsa duk da cewa bata so, amma ayanzu ki dubeta, tana zaune cikin jin daɗi, farin ciki, annushuwa haɗi da salama,   hakan yafarune kuma duk saboda biyayyan da tayi ga mahaifinmu, sam bata bijire masa ba duk da kuwa bataso, haka yasa muke tsananin sonta kema ki daure ki masa wannan biyayyar." 

Hannayen Zaleeha ya kamo cike da kula yace.

"Dan Allah Zaleeha kimin al'ƙawarin zaki yiwa Baban mu biyayya, Insha Allah aurenki da Saifuddeen al'khairi ne, sannan Baba Malam bazai taɓa kaiki inda za'a cutar dake ba!." 

Sabon kuka Zaleeha tasanya wiwi kamar wanda aka faɗawa ranar muruwarta, sam kalaman Ya Ahmad basu shigeta ba, inama dazai gane cewa ayanzu idanunta sun rufe, bataji bata gani, inama dabai ɓata lokacin sa ya faɗi waƴannan maganganun ba, zuciyarta tajima dayin nisa wajen tsanan Saifuddeen, bata sonsa, ba kuma ta son aurensa. Haka Zaleeha ta dinga yi musu kuka wiwi, Ya Ahmad da Maryam kuwa sai nasiha sukeyi mata tare da ban baki, saidai kuma ko ɗaya bata ɗaukar nasiharsu, aduk ma sanda sukace da ita tayi haƙuri ta ɗauki Ƙaddara, takuma yiwa mahaifinsu biyayya, saitaji kamar wuƙa suke caka mata agadon bayanta, idan kuwa suka yaba  Saifuddeen, suka kuma ce ta rungumi aurensa hannu bibbiyu sai taji kamar narkakken dalma suke watsa mata cikin kunnuwanta. 

Haka dai tasha kukanta ta ƙoshi har saida idanunta suka kumbura, daga ƙarshe dai Ya Ahmad ne dayaji yanda jikinta ya ɗau zafi yasakata amotarsa suka dawo gida, yayinda tabar motar ta agidan Maryam ɗin. 

Tunda ta dawo daga gidan Maryam tasa kanta aɗaki ta kulle, wani zazzafan zazzaɓi kuwa take yakawo mata ziyara, domin irin kukan da tayi yauɗin nadabanne.


Haka Zaleeha ta kwashe kwana d'ayan cur bata fitowa ko ina, banda kuka ba abun da ta sa agaba, washe garin nema da taji zaman kaɗaici naneman takurata yasanya ta shirya don zuwa aiki ko kewan da takeji zai ɗan ragu, ko wani wadataccen kwalliya yau ɗin batayi akan fuskarta ba, wata bubu gown red colour da red vail kawai ta yafa ajikinta, amma dayake itaɗin ce mai kyau bawai kwalliyan da takeyiwa kanta ba duk da haka saida tayi kyau, cikin ƙunci haka ta nufi gidan redion nasu na Vission FM.  

Koda taje banda Rabeel da suka gaisa babu wanda ta kula, kai tsaye tatafi gabatar da shirinta na Mushaƙata.

A kasalance ta gyara zamanta tare dacewa. 

"Barkanmu da war haka sannunmu da sake saduwa cikin shirinmu mai taken mu shak'ata.

sai kuma ta d'anyi shiru tare da sakin wak'ar,. 

Tattausan lafazi mai dad'i jinshi ya ratsa raina, hadarin so yayi had'owa.

Sai ta kuma d'an rage volume tare da cewa. 

"Taken na masoya ne, gareku masoya."

A hankali ta dinga sake zafafan waƙoƙi na soyayya masu taɓa zuciya,  wani waƙan idan tasaka har ƙwalla ne ke bin ƙuncinta, domin sosai suke ratsa mata zuciya.

kai ta jinjina tare dacewa. 

"Ganin lokaci na hararanmu a gurguje ga zazzafan sak'o na masoyo, wanda shine na kusa da k'arshe. 

sai kuma ta saki wak'ar  K'anina Hamisu Breaker tare da k'ara volume. 

A hankali Wak'ar ke tashi. 

Tun forkona duniya an dasa so bisa zuciyar mutun biyu.

kuma har abadan bazai yankeba dan yanada armashi. 

sai ta kuma d'an rage volume d'in tare da d'aga muryarta tana bin wakar yadda sautin ke fitowa tare cikin rauni take bin baitukan.

"Soyyyy ruwan zuma inji wasu, 

wasuko sukace ruwan gubane." haka tai tabin wak'ar har k'arshe kana tasa hannu ta share hawayenta tare da cewa. 

"Ganin lokacin da aka d'ibar mana ya k'are ga wak'armu ta k'arshe."  wak'ar isa ayagi.

Duk masoyi zai jure karan tsan." sai kuma ta d'an k'ara sautin muryarta tare da bin mawak'in inda yake cewa.

"Zaya jure kai kawo ko ina,  zai nufin masoyinsa da hassada. Ba'ason fushi sai dai dangana."

sai kuma ta dai-daita muryarta da mawak'in suka had'a baki wurin cewa. 

"Yin fushi a so tono fittina, wanda ya fara so baishiga yak'i na kanganba."

sai kuma tayi maza ta katse wak'ar dan sai taji kamar Saifuddeen take bawa k'arfin guiwa,

 tana ƙare shirin nata ta fito.

Balkeesu ce ta karɓa don itace zata gudanar da labaran duniya, bayan tagama gabatar da labaranne ta gyara zama, cikin isgilanci tace.

"Kanun Labaran duniya da ɗumi ɗuminsu.mun samu wani labarin mai cike da al'ajabi daga wata majiyarmu mai taken Babu nakasasshe sai rago,  cewa soyayya ta ɓarke tsakanin masu lafiya da kuma nakasassu, inda shahararriyar matashiyar budurwa maiji da kyau, ilimi, wayewa, haɗi da aji tayi gamdakatar da wani nakasashshen kurma, kana gurgu,  inda yazo ya bayyana mata soyayyarsa hartakai ga suna ƙoƙarin yin aure, mudai fatan mu anan shine Allah yaƙara danƙon ƙauna da soyayya, domin ai Nasaka ba kasawa bace, kuma babu nakasasshe sai kasasshe!." taƙare maganar tana me ƙoƙarin gimtse dariyarta.


Zaleeha dake zaune aɗakin watsa shirye shirye tanajin abun da Balkeesun ta faɗa, taji ranta yayi wani irin ƙuna, take ɓacin rai ya cika mata zuciya, sam bata tsammaci haka daga Balkeesu ba abinda taketa boye shine take son sanarwa duniya. 

Jakarta ta ɗauka  tare da miƙewa tsaye batajin zata iya jure zama awajen aikin, saboda haka tafiyarta gida shine kawai zaifi.

 Tana fitowa, tayi kiciɓus da Balkeesu, tare da wani Hamza wanda yake shima abokin aikinsu ne, Hamza irin mutanen nanne masu gulman tsiya da kuma shishshigi, gason shiga abun dabai shafesa ba, shiyasa ma sam basa shiri da Zaleeha.

Yana ganin Zaleehan yasaki dariya tare da dubanta da kyau, cikin son ƙarin jin gulma don wanda Balkeesu ta gulmata masa bai ishesa ba yace.

"Zalees fashion amaryar nakasasu, anguji masu lafiya an ƙare a nakasassu." 

Cak ta tsaya da tafiyan da takeyi tare da juyowa ta watsa masa wata uwar harara, bata da lokacin tanka masa hakan yasa ta juya taci gaba da tafiyarta. 

Dariya suka ci gaba dayi shida Balkeesu, ita kuwa ko sake waiwayosu batayi ba.

Kaitsaye wajen motarta ta nufa, tana shiga ta murza wa motar key tare da cillata kan titi,  kanta ne ke mata ciwo sosai, gaba ɗaya damuwa ya cika zuciyarta, har wani ɗaci takeji aranta.


Baba malam ne zaune a falonshi bayan tafiyan iyayen Abdussalam wai sun kawo sadakinsu wa Zaleeha kuma wai masu kawo kayan aurenma suna kan hanya, 

Malam Adam ne ke tausarsa da cewa. 

"Malam Bashir ka kwantar da hankalinka domin al'amarin yaran yanzu sai du'a'i." cikin tsananin b'acin rai da tarin bak'in ciki murya a hargitee Baba Malam yace.

"Me Zaleeha take son maidani da zatayi ta turomin manyan mutane masu daraja a kanta ita d'aya, da kaifa muka amshi sadakin Saifuddeen a hannun mutane masu kima da daraja, sannan yanzu ta kuma turo min wasu, biyu za'a rabata ne? ga uwarta ita ma sai tayar min da hankali takeyi."

cikin tausasawa Malam Adam yace.

"Kada ka damu tunda su iyayen Abdussalam mun basu hak'uri mun kuma ce musu kada su bari a kawo kayan lefensu ai inaga sun fahimcemu."

kai ya jujjuya tare da cewa.

"Banga alamun hakaba a fuskokinsu, bakaji cewa suke ai dai da fari nine na bawa d'ansu damar zuwa zance wurinta, kanaji har cewa sukeyi wai in dai daure inyi dottaku kaji fa abinda Zaleeha ta jaza min zubewar mutunci da kima da dottaku a idanun mutane."

"Ba komai in sha Allah, bari inje gida anjima zan dawo inyi mgna da ita Zaleeha ka kwantar da hankalinka."

Da haka Malam Adam ya sallami Baba Malam ya tafi ya barshi cikin tarin bak'in cikin abinda Zaleeha da Mama keyi mishi... 


Ita kuwa Zaleeha kaitsaye  ta fara zuwa Makay ice cream and chocolate ta saya,  daganan ta ɗauki hanyar komawa gida.

 Tun daga shawo kwananta ta hango wata ƙatuwar mota tirela fake aƙofar gidansu sai ya Habu dake kusa da masu motar alamun suna mgna dashi kamar dai umarni yake basu kan su dena fidda kayan bisa dukkan alamu jagoranci ko kwatancen wani wuri yake musu inda zasu kai kayan. 


 Abakin tangamemen gate ɗin gidannasu tayi parking, buɗe murfin motar nata tayi ta fito nan tashiga bin kayayyakin furnitures ɗin da ake shigarwa cikin gidannasu da kallo, mamakine bayyane akan fuskarta haka ta wuce zuwa cikin gidan.

Kai tsaye ɓangaren Mamy ta nufa, nan ta iske su Zahira da Ziyada zaune gefensu kuwa Mamyne hannunta riƙe da littafin hisnul muslim.

Wurga jakanta tayi kan kujera cikin gajiya ta dubi Mamy ashagwaɓe tace.

 "Barka da gida Mamy." 

Dubanta Mamy tayi tare da cewa.

"Yauwa Zaleeha ya aikin." 

"Alhamdulillah". 

tafaɗa tana me ƙoƙarin buɗe ledar ice cream ɗinta,

zaro roban ice cream ɗin tayi tare da buɗewa, harta sanya ɗan ƙaramin cokali cikin ice cream ɗin sai kuma ta ɗago kanta duban Mamy tayi cikin son ƙarin bayani tace.

"Mamy naga anata shigo da kayan furnitures gidannan, Baba ne zai sanja kayan part ɗinsa ko?" 

ta k'arishe maganar tare da cika bakinta da daddad'an sassanyan ice cream d'in

Kafun Mamy tayi magana tuni Zahira tayi carab ta cabke maganan inda tace.

"Kayan furnitures ɗinki ne na aure wanda Ya Ahmad yayi miki order daga Dubai shine suka iso." 

Tuni ta ƙware da ice cream ɗin dake cikin bakinta, wani irin tari me ƙarfi ne ya sarƙafemata wuya da numfashi, take idanunta sukayi jajur, tari take sosai, har saida su Mamy suka tsorata, Ziyada ne tatafi kitchine da gudu inda ta dawo hannunta ɗauke da bootle water, Mamy ne  ta karɓi ruwan tare da ɓalle murfin goran ta kai bakin Zaleehan, sosai tasha ruwan, saida taji ta rin nata ya tsaya sannan ta kawar da goran daga bakinta,   zamowa ƙasa tayi daga kan kujeran tare da fashewa da wani irin kuka, kuka take sosai kamar wacce aka faɗawa ranan mutuwarta,

Mamy da su Zahira baki kawai suka sake suna kallonta.

Cikin kuka ta mirgino tare da kama ƙafafun Mamy, cikin matsanancin kuka tace.

"Mamy dan Allah Kifaɗawa Baba Malam cewa banason wannan auren, wallahi na tsaneshi, matuƙar aka aura mini shi kashe kaina zanyi, wallahi dana aureshi na gwammace mutuwata!" 

Ajiyar zuciya Mamy ta sauƙe tare da kamo kafaɗun Zaleehan cikin son bata baki tace. 

"Ki kwantar da hankalinki Zaleeha, babu wani bawa da ya isa kaucewa ƙaddaransa, ki amshi auren nan amatsayin ƙaddaranki..." 

Ihun da Zaleeha tasanya ne yasanya Mamy yin shiru ta zuba mata ido, kuka sosai Zaleeha takeyi, afujajan ta nufi hanyar fita daga cikin falon sambatu kawai takeyi tana cewa.

"Wallahi Bazan aureshi ba, na tsaneshi saina kashesa sannan kuma nakashe kaina!."

Da kallo suka bita su dukansu harta fice.


Kaitsaye part ɗin Mama ta nufa, da kuka sosai ta shiga cikin falon, kaitsaye ɗakinta ta wuce,  Mama da Yayarta dake zaune afalon suka bita da kallo.

Tana shiga cikin ɗakinta ta murzawa kofar key, nanfa tashiga buge 'uge da fashe fashe, tanayi tana ihu da kururwawa akan cewa ita lallai batason Saifuddeen.


Motocine jere reras kusan guda goma ke shigowa cikin gidan a dai-dai lokacin da tuni Habu yayiwa tirelar nan jagora sun tafi bayan yasa sun kwaso kayan yaje ya gayawa Baba Malam uzurinshi, 

suna gama dai'dai-ta parking, wasu mata suka soma fitowa daga cikin motacin nan aka soma fito da wasu haɗaɗɗun akwatuna kai tsaye matannan ɓangaren Mama suka nufa, koda suka ƙarasa falon na Mama cike da farinciki Mama da Yayarta suka karɓesu, nan fa matan suka baje waƴannan akwatunan nan guda 35 agaban su Mama, haka suka dinga fito da tsadaddun kayayyaki suna nunawa su Mama, Mama kuwa da Yayarta tuni zuciarsu sun cika da farinciki, Mama dai burinta na son ƴarta Zaleeha ta auri Abdussalam ya kusa cika, yanzu ma aka soma wasan tunda dai ga kayan aure nan dangin Abdussalam sun kawo,   haka Mama suka cika dangin Abdussalam da kayan tarban baƙi, cikin girmama juna sukayi sallama inda suka rakasu har bakin motocinsu  saida sukaga tafiyarsu kafun suka dawo cikin gida.


Afujanan Zaleeha tafito daga cikin ɗakinta aniyarta nason zuwa falon Baba Malam don sanar dashi cewa batason auren, fitowarta yayi dai-dai da shigowan Maryam cikin falon wanda yanzun zuwanta gidan.

Baki buɗe Zaleeha ke kallon tarin akwatunan dake zube gabansu Mama,   kamar zatace dasu wani abu kuma saita fasa, hartakai ƙofar fita daga cikin ɗakin, Muryar Ruda ya daki dodon kunnenta inda take cewa.

"Kee! Zaleeha bakiga kayan aurenki da Abdussalam ya kawo bane?".

Dummmmm dammmmmm haka zuciyar Zaleeha ya buga, a firgice ta juyo cikin tsananin damuwa haɗe da tashin hankali murya can sama da k'arfi tace.

"Kayan aurena kuma again?".

Cikin son lallaɓata Mama tace.

 "Eh mana Zaleeha ko bakyaso afasa aurenki da wancan bazan musakin ne?".


Wani irin tsalle ta daka tare da kururuwa haɗi da ihu Zaleeha tayi da k'arfi nan fa ta shiga kuka tare danufar kayan auren, cikin fitar hayyaci tashiga ɗiban kayan tana watsi dasu acikin falon, babu abun da take sai sambatu masu nuni da cewa bata cikin hankalinta sam.

Ganin watsi da kayan basu mata ba yasa ta shiga ɗaukan kayan tana watsawa can waje, cikin zaucewa take ihu kana tana buge-buge da ife-ife kamar wanda aljanu suka shafa,

Dai-dai lokacin Ya Ahmad da Mamy suka ƙaraso don tun daga part ɗin na Mamy sukejiyo ihu da kururwan Zaleeha.

Ganin Zaleeha na watsi da kaya yasa Ya Ahmad ƙarasowa da sauri ya nufi inda Zaleehan take,  ƙoƙarin kamo ta yake da sauri taja da baya, wata ƴar knife ɗin da ke aje bisa wani table ta ɗauka, saita knife ɗin tayi akan cikinta, cikin zaucewa haɗi da fitar hayyaci ta zazzaro jajayen idanunta murya a hargitse tace.

"Zan kashe kaina, wallahi idan aka auramin ɗaya daga cikinsu saina kashe kaina, kada ka matsoni Ya Ahmad kana matsowa wallahi saina kashe kaina ayanzu nan!.." taƙare maganan tana sakin wani matsanancin kuka mai nuna tsantsar tashin hankali.


Iya tashin hankali babu wanda bai shigesaba acikinsu, tuni Maryam ta saki kuka mai taɓa zuciya, Ya Ahmad ma hawayene suka cika cikin idanunsa.


Duk abun dake faruwa akan idanun Baba Malam, da ya taho tun ihun Zaleeha na forko wanda a zatonshi wani mugun abune ya farmata, jin kalamanta da ganin abinda takeyi ne yasashi bud'e labulen ƙarasowa cikin falon yayi tare da duban Zaleeha dake kuka harda shiɗewa still knife ɗin na hannnunta da alama ƙiris take jira ta cakawa kanta. 

Cikin tsananin takaici haɗi da ɓacin rai da tsantsar tashin hankali da bak'in ciki ya bud'e bakinshi cikin tsananin cushewar sauti muryarsa cike  da amon ɓacin rai yace.

"Kin nunamin ban isa dake ba, kin nunamin cewa baki ɗaukeni matsayin uba agareki ba, haƙiƙa kin nunamin cewa ke bakizama ƴa ta gari mai biyayya ba, shikenan zan barki keda mahaifiyarki kuyi duk abun da kukeso, zama daku sam bashida amfani awajena saboda haka yau zan tafi zanyi nesa daku, Zaleeha yau zanbar miki gidan idan yaso kiyi duk wani abun da kikeso, duniyace ae ta isheki riga harma da zanin ɗaurawa, zan tafi inyi nesa daku tun kafin ku kasheni da bak'in ciki." Yana kaiwa nan azance nasa ya juya yanufi ƙofar fita daga ɗakin.

Cikin tashin hankali da fargaba Ahmad da Maryam  suka zube aƙasa tare da kamo ƙafan Baban nasu cikin matsanancin kuka suka shiga basa haƙuri.

 Rumtse ido Baba Malam yayi har cikin ransa yanajin wani matsanancin ɓacin rai,  saidai suyi haƙuri amma tabbas tafiya zaiyi zaiyi nesa dasu domin bazai iya jurar haɗiye baƙinciki da ɓacin ran da Zaleeha da kuma Mama ke ƙunsa masa ba.  

Hawayene ke zuba a idanun Mamy yayinda zuciyarta tayi wani irin mummunan karyewa tabbas idan Baba Malam yatafi itama bazata zauna ba, saboda dama danshi kawai take zaune agidan.

idan babushi kuwa me zata zauna tayi agidan. 


A kid'ime Maryam  ta dawo kusa da Zaleeha cikin muryar kuka tace.

"Dan Allah Zaleeha kice kin amince kada kice a a, Baba fa tafiya zaiyi Zaleeha, kiji tausayinmu! Zaleeha kiji tausayinmu!! dan Allah kada ki bari bak'in cikinki yasa mahaifinmu yayi nesa damu." cikin matsanancin kuka Maryam takare maganan.

Kai Zaleeha ta girgiza cikin bushewar zuciya tace.

"Wallahi Bazan auresu ba, natsanesu dukansu biyu ba wanda nakeso, wlh xan kashe kaina matuƙar aka matsamin kan aurensu."

Cikin ƙaraji tace.

 "Natsanesu Bana sonshi!" 

Wani irin gigitaccen ihu tasa tare da sanya knife ta yanka wuya..............!


               Alhamdulillah...


Mu had'u a kashi na biyu,  dan jin yadda wasan zai kaya. K'ak'a-tsara-k'ak'a?."  Shin Dalla me zai aikatawa Zaleeha? 1  towai ina Baba malam zai tafi? 2 Ya cire hannunshi cikin auren ne? 3 wa zai auri Zaleeha!? 4 Anya kuwa Saifuddeen zai iya ratsa budurcin budurwa?. 5 Wacece Amina me nufinta kan Saifuddeen? 6  Shin Asma'u zata hak'ura da wannan zazzafan matashi mai suran laraban  kuwa? 7 Ummi dai tace dolefa a fasa wannan auren  na Zaleeha da kekyawan d'anta! 8 Me nufin Ishaq akan Bilkeesu? 9  Me gskyar zuciyar bilkeesu akan Zaleeha? 10 Shin Saifuddeen  kuwa zai iya yin sex kamar ko wanne  lafiyayyan namiji? 11  ina Habu zaisa akai kayan da akace na Zaleeha ne? 12  Me Raveel zai iya yi a rayuwar Zaleeha?. 13. Me nufin Mama me zata aikata?  14 Ya Aminu da Ya Habu me zasu aikatawa Zaleeha shalelen Ya Ahmad in sunji tasa Baba malam Kuka? 15  Amsoshin tambayoyin nan duk suna cikin littafin Nakasa ba kasawa bace part two kada ku sake a barku a baya, dan yanzu muka shiga cikin ainihin  gundarin labarin. Zazzafar soyayya mai kashe jiki da ratsa zuk'ata, al'ajabi, tausayi, mamaki, dariya, Shauk'i mai girgiza zuk'atan makaranta duk abubuwan suna cikin part two. Saifuddeen zaiyi abunda babu jarumin da ya tabayi cikin jaruman books na, zai shayar daku mmki zai saku Shauk'i mai tunzuro k'uruciyar amarci...!






                             *BY*

                *GARKUWAR FULANI*

No comments