Mijin Malama 34
https://arewabooks.com/chapter?id=64ac50ef324ef73a495e70b9"This is the first and last da za ki yi pointing nawa da finger, Dog!" Guy É—in ya furta hakan a tsawa ce, mai da police É—in ma ce ta hanyar faÉ—in “Za Ki yi” Saboda rashin cikakkiyar hausa maganar ta shi ma a gurÉ“ace take. Sosai Police yake jin azaba nan take hannun ya kumbura zufa na yanko masa ya ce "This is not fair, su waye ku? You came and blocked the road and prevented the vehicles from entering"....“Your Father” Guy É—in ya faÉ—a. Yana ware kuma dara-daren idanunsa akan ÆŠan sandan, Kyakkyawan saurayi ne mai Æ™arancin shekaru domin baifi 16yrs ba, kulawa da kwanciyar da jin daÉ—in rayuwa haÉ—i da samun duk wani abun da yake so ya sanya jikinsa wani irin mahaukacin buÉ—ewa, domin gabaÉ—aya cikin Gang team É—in yafi kowa girman jiki, tsayi da kauri jikinsa a murÉ—e yake ga wasu six-pack da suka bayyana musamman saman Æ™irjinsa, baÆ™i ne shi sosai irin baÆ™in Æ´an America É—in kana ganinsa kaga Ba'amurke baÆ™ar fatarshi mai kyau da sheÆ™i irin baÆ™in da yafi farar fata kyau da É—an kan idanu. GabaÉ—aya jikinsa zanen tattoo ne daga wuya har zuwa Æ™irjinsa da hannaye ga wata Æ™atuwar sarÆ™a mai tabon Cross a jiki. Sumar kansa a murmurÉ—e kamar indomie wacce ta Æ™ara fito da kayan fuskarsa da jajeyen laÉ“É“ansa.... he is outstandingly handsome and robust, very masculine. Cikakken namiji mai iko da tsayawa akan ra'ayinsa. Police É—in ya nuna kansa ya ce "Ni ka ke zagi?"
"An zage ka titin na ubanka ne?" Taj ya faÉ—a yana nufar kan Police É—in ganin haka yasa ya yi saurin yin baya tare da barin wajan. Taj ya ja tsaki ya juya ya kalli Guy É—in daya karyawa police É—in Hannu ya ce
"Abraham let's go" Da wani irin kallo wanda aka kira da Abraham ɗin yake bin Taj da shi cikin warning ya ce "Sai na ci Babarka, duk sanda ka sake ce mini Abraham" Ya faɗa cikin harshen turanci. Da sauri drivern Abbu ya juya zuwa wajan mota yana isa jiki na rawa ya ce "Yallaɓai wallahi ƴan fashi ne, mun shiga uku" Abbu ya ɗago kai ya dubi driver a hankali ya ce "No! Ba ƴan fashi ne, ƴan fashi da rana??" Driver ya ce "Kwarankwatsa su ne, hadda bindiga irin ta film na gani fa? Innalillahi mun shiga uku" Abbu ya ajjiye Jaridar hannunsa domin meeting ne da shi na gaggawa akan wata contract da zai yi signing akan papers ɗin. Ganin haka ya sa Driver buɗewa Abbu ƙofa ya fito yana tattare babbar riga cikin sauri kana ganinsa kaga manyan Alhazawan nan masu tashe da kuɗi, ya dinga ratsa mototci yana shigewa har ya isa tsakiyar Gang team ɗin. Abraham na tsaye hannunsa riƙe da Cigarette yana busawa tare fitar da yaƙinta zuwa sama. Taj ya ce
"Guy's let's go, go go" Abraham na ƙoƙarin shiga mota ya ji an damƙi wuyansa ta baya, abinda tunda uwarsa da haife shi ba a taɓa yi masa ba, kasa juyawa ya yi saboda tsananin mamaki kafin a ankare ya ji an fizgoshi tare da sauke masa wasu tagwayen maruka. Gabaɗaya Gang team ɗin, Taj, Joshua, John... Da sauran sukai kan Abbu kowa yana fito da bindiga Jikin Abraham har wani tsuma yake naman wajan na wata kakkarwa idanunsa sukai jajur Yatsun Abbu suka fito raɗau a saman kyakkyawar fatarsa. Da wata murya ya daka musu tsawa ya ce "Noo!!!!! Don't shoot him" John ya ce "But why? Marinka ya yi, He slapped you, waye shi a Kano? Ubansa ma ubansa zamu ci dan kaza kazanshi" Abraham dai kallon Abbu yake without blinking his eyes. "Ni ne zan hukunta shi, Ba a taɓa mini haka ba in my whole life" Abraham ya basu amsa. Cikin sauri kuma ya ƙwaci bindiga a hannun Taj zai bugawa Abbu kan bindigar ya ji Abbu ya ce "Wato kune irin gagararrun da muke da su a kano ko? Haihuwar kan titi wanda baku san girma da darajar kowa ba? Shegu gayyar tsiya, gayyar na ayya" Cak Abraham ya tsayar da hannunsa dab da fuskar Abbu ya runtse rinannun idanunsa. Ganin ya tsaya Gang team ɗin suka haɗa baki wajan faɗin "Bad boy Shoot, Shoottt him" Ko motsawa bai yi ba balle ya yi ƙoƙarin harbin Abbu, murmushi Abbu ya yi ya ce "Idan kai ɗan halak ne harbeni, ɗan daba masu kwacan wayoyi sisi babu a aljihu maimakonsa ku nemi aikin yi kun bige da sata da bashi da makami, me ake da talauci shi yake saku irin wannan Allah wadaran naka ya lalace" Wani acikin jama'ar wajan ya ce "A'a Alhaji ɗa ai na kowa ne, ka yi musu fatan shirya idan da rabo watarana sai kaga sun zama wasu a Nigeria bana jihar nan ba" Abbu ya girgiza kai ya ce "Goodness! Ai basu da rabon shiriya irinsu da haihuwar su gwara ɓarin su, basu da wani muhimmaci talakawan banza, maybe na shan wiwi da sigari basu da shi" Yadda jikin Abraham ke ɓari kaɗai zai bawa mutum tabbacin maganganun sun shige su, duk da ba komai yake fahimta ba cikin yaren Hausar.
"Useless" Abbu ya ƙara furtawa yana tofar da yawu. Kafin su Taj su lura Abraham ya shigo dukan kansa da ƙasan bindigar nan nan da nan jini ya fara zubar masa. Ganin hakan ya sa John nufar Abbu Gadan-gadan zai harbe shi kafin ya ƙarasa Abraham ya cimmasa yana zuwa ya dunƙule ya naushi John a ciki yana huci kamar zaki ko kumurcin maciji cikin ƙara ji ya ce "I said no!"
"Bad boy akan wannan tsohon ka ke cutar da kan ka?" A fusace ya sake juyawa kan Taj ya ce "Abu ɗaya ka ƙara cewa zan kashe ka, I'll kill you Taj" Yana faɗin haka ya ƙwaci key ɗin motar shi hannun Joshua motar da tafi ko wacce mugun kyau ya nufa yana zuwa ya buɗe tare da shiga ya jata da wani irin sauri kamar zai tashi sama haka yabar wajan, ganin irin gudun da yake saka Gang team ɗin suka shiga mota tare da marawa Bad boy baya, Abbu ya ja tsaki tare komawa a hankali masu tsaron kan hanyar suka dinga bawa mutane hannu suna shigewa "Ƴan iskan yara gantalallu" Abbu ya faɗa bayan driver ya shige da shi zuwa hanyar su da Murtala Muhd way.... Gudu kawai Abraham yake idanunsa yana zuwa kan corner da zai You-turn danja ta tsayar da shi, a hankali ya ɗora kansa akan string motar zuciyarsa kamar tayi tsalle ta fito sbd wani irin baƙin ciki da takaici da yake ji, This is the second time he finds himself in this situation, bai damu da jinin da yake zuba daga kansa ba burinsa kawai ya tuna inda ya taɓa jin muryar, tabbas ya san muryar Abbu but where? Ba a taɓa riƙe wuyan rigarsa ba balle wani ya yi attempting marinsa, bai kuma san dalilin daya sanya ya kasa yin komai akan Dattijon ba, da alama he's special da wani da wallahi sai ya kuntile hannu idanunsa har wani ruwa ne ke kwanciya sbd tsabar zuciya da taurin rai.... Knocking Glasses ɗin motarshi ya ji ana yi a fusace ya ɗago zai zabga ashar idanunsa ya sauka akan wata yarinyar wacce take duƙun-duƙun ya ja siririn tsaki ganin yadda fuskar yarinyar take duk majina, idanunsa ya ɗauke tare da rufe shi yana jin komai ya duniyar ya fice masa a rai, ya yi dana sanin dawowa ƙasar bakiɗaya. Ci-gaba da knocking kawai tayi ya zuge Glasses ɗin zuwa ƙasa da sauri ta ce "Ka taimaka mini dana abinci saboda Allah Yallaɓai" Bai san meta ce ba, amma ya ji sunan Allah sarai sai ya ci gaba da kallonta, nan da nan zuciyar tausayin sa ta motsa musamman akan ɗiya mace yana da tausayin mata ƙwarai tashin hankalinsa yaga mace na kuka, ya ɗauke yana kwaso kuɗi ya watsa mata ta ƙofa da sauri kuma ya ja motar ya yi gaba... Tun daga ƙofar gate ɗin gidan yake danna horn kafin gatekeeper ya fito ya yi saurin fitowa kansa a ƙasa domin baya jira bai yarda kuma a jira shi ba, ya nufi ƙaramar ƙofar shiga tare barin motar a buɗe a waje, cikin sassarfa cike da kuzari duk da jiri na ɗaukarsa haka ya nufi cikin gidan ya tsaya a ƙofar farko yana danna password ƙofar ya buɗe, a Main parlour ya tsaya cikin zafin nama kamar Mahaukaci ya shiga ɗaukan duk abinda hannunsa ya je kai yana doka shi da ƙasa... Daga saman upstairs aka ce "Grandson!" Abraham bai tsaya daga abinda yake ba, ganin zai jiwa kansa ciwo ya sa David ya shiga sakkowa daga steps ɗin benen da sauri yana zuwa ya kama hannun Abraham ya ce "Waye? Kai da wa?" Yaƙi cewa komai sai huci da yake jikinsa na rawa David ya san Abraham ba zai taɓa magana ba, hakan yasa ya ja hannunsa zuwa saman kujera ya damƙa masa wani cup ya ce "Drink"
Bai tsaya tantance mene ba ya amsa tare da kafawa a baki ya shanye tas, David ya ƙara zuba masa wata ya shanye daga nan ya miƙe ya nufi wani part not too ya dawo hannunsa riƙe da first-aid box ya gyara masa wajan.
"Who is he?" David ya tambaya, cikin mayen daya fara ɗaukar shi ya ce "I don't know, but i knw him na san muryar" David ya ce "Where?" Ya yi shiru... Ganin yana cikin maye kuma zai fi ɗaukar magana ya sa ya ce "Look Grandson, na ce ko da wasa bana son ganin jini a jikinka gwara ka fitarwa da wani jini da a fitar maka, ka ci mutuncin wanda ya ci naka, ka taka wanda ka ke so, kai ɗaya nake da shi a gefena You're my grandson exit? Babanka yabarka, baka da Mother baka da kowa a duniya sai ni, ni ne Grandfather naka, idan kuɗi na maganin komai a duniya to duk irin bala'in daka ɗauko zan ji da shi, ni ne shugaban church ni ne Pasto bayan haka kafi kowa sanin matsayina a ƙasar nan bana country ba, ina da kuɗi mai kuɗi shi ke da magana, a top 5 na masu kuɗin Nigeria zan shiga ciki, Mahaifinka Daniel zai shiga.....," "Stop calling his name, i hate him he's not my father" Abraham ya faɗi hakan idanunsa na lumshewa ya shiga surutan maye yana faɗin
"She left me, Mamina Grandpa, Mamina Mamina" Sai kuma jikinsa ya shiga jijjiga. Grandpa ya yi shiru kafin ya ce "Mamin nan taka maybe she's no more bata ra....," Tasss! Ya ji saukar Glasses ya miÆ™e da sauri yana riÆ™e Abraham ya ce "Am so sorry Dear, Maminka na nan I'll find out where she's hiding to" Da Æ™yar bacci ya É—auke Abraham bakinsa É—auke da sunan “Mamin, JEENA" Ganin ya yi bacci yasa Grandpa kiran Taj a waya ta prvt line nasa yana É—agawa ya ce "What's happened?" In brief Taj ya faÉ—a masa komai Ya ce "Ka nemi mai Zane ya yi drawing na mutumin ka kawo mini nan gida" Taj ya ce "Bad boy fa? Ai zai fi yin zanen yadda ake so" Grandpa ya ce "It's secret"....
Saudiya. Majeederh na zaune saman kujera gabanta ɗauke da laptop tana duba abubuwan da zatai a B.u.k idan ta koma Nigeria, komai nata maturel ne nutsuwa ga wani irin jan aji da kamon kai bata sakewa kowa fuska, har office ya buɗe wanda za a dinga samunta kai tsaye a ranakun weekend, ba ruwanta da batun tama sakawa ranta ba zatai ba tunda babu wanda ya ƙara tunkararta tana jin surutai na yawo a unguwa harda Social media ba ga family taƙi yin aure sai yawo... Door bell ta ji ta yi ƙara a hankali ta ɗan zame hannunta daga keyboard ɗin laptop ɗin, tare da ɗan yi shiru tana tunanin who is there by this time? Bata da appointment da kowa amma waye kuma? A hankali ta miƙe tana saka sunglasses ɗin ta na medical kana ta ƙarasa jikin ƙofar ta ce "Who's there?" Aka amsa da "Messenger" "Ok came in" Ta faɗa a gajarce, tana kowa tayi saurin saka hijabi da liƙab kana ta buɗe ƙofar, da mamaki ta dinga kallon mutumin ganin uniform ɗin masarauta a jikinsa da alamar Bafade ne shi yana ganinta ya zube a ƙasa yana kwarara mata gaisuwa, ita dai bata ce komai ba ya miƙe mata wata envelope ya ce "Saƙo ne daga Palace ranki ya daɗe Gwarzuwar Nigeria" Da hannu ta nuna masa ya ajjiye nan ƙasa ya ajjiye bayan ya tafi ta durƙosa ta ɗauka envelope ɗin tana komawa cikin bedroom ɗin, a hankali ta ware iya haɗuwa Envelope ta haɗu wani irin zaibar rubutu ne manne a jiki an rubuta.
_Your Highness Ajlaal Sultaan_
Invite
_Malama Majeederh Abdul'aziz Khan_
Ta duba date yau kenan sai kuma time 4 na yamma, ta dinga juya Envelope ɗin Ajlaal mijin Ƙhulud Arzaan kenan? za taga Ƙhulud farin ciki ya wanzu a zuciyarta duk da fargabar kiran ya ɗarso a zuciyarta.... 3:45 Daidai ta fito cikin wata Abaya dark blue tayi rolling kanta da vail sai liƙab da wani sirrin Glasses a Idanunta hannunta riƙe da hand bag da wayarta, tafiya take cikin tarin nutsuwarta kamala da sanin ya kamata, harta isa motar da ake jiranta tana zuwa driver ya buɗe zata shiga gaba ya ce "Ranki ya daɗe baya, ni driver ne" Ta ɗan girgiza masa kai kamar ba za tayi magana ba sai ta ce "Ina so gaban" Ta shiga ta zauna cikin sauri taja motar sai Palace.... Ƙhulud Arzaan na tsaye cikin shigar larabawa ga tsohon ciki a jikinta wanda shi ne karo na farko da zata haihu, fuskarta ɗauke da murmushi Majeederh na yin sallamawa Ƙhulud ta fasa ihu tare da nufar Majeederh, cak ta tsaya idanunta na gizo mata wani abu sai kuma ta nufeta suka rungume juna sosai sukai farin ciki bayan shekaru nawa sun sake haɗuwa, Ƙhulud ta ce "Ina mijinki fa?" Majeederh ta ɗan yi shiru sai kuma ta ce "Ban yi aure ba" Cikin wasa Ƙhulud ta ce "Kina jiran haɗaɗɗan namiji ko?" Murmushi kawai ta yi sai kuma ta ce "Kamar labari littafi? Kawai Allah bai kawo ba" Ƙhulud ta ce "Ubangiji ya kawo na gaban kwatance amma na yi mamaki na ɗauka ma kin haihu wlh" Majeederh ta yi shiru Ƙhulud ta ce "Mu je wajan Granny Zaytoon" Suka miƙe wani plat suka nufa mai kyau da tsari. Zaytoon na zaune saman ladduma gabanta cike da kayan itatuwa ana mata firfita suna shiga Zaytoon ta sauke wani irin kyakkyawan murmushi tana tafa hannu ta ce "Lale lale da babbar Malama" Gabaɗaya Hadiman suka fita Majeederh ta zube gaban Granny tana gaisheta ta amsa da "Ma sha Allah, Allahamdulillah Sannu kin ji ina sake tayaki murna" Ita dai kanta a ƙasa, Granny ta dinga kallonta ko zata cire liƙab ɗin fuskarta amma taƙi itama kuma bata ce ta cire ba sbd she don't want interfere a rayuwar Majeederh. Majeederh ta ɗago kai idanunta ya sauka akan wata matashiyar mata mai wani kyau kamar ba mutum ba, ta dinga kallon matar sai kuma ta ce "Ina yini?" Granny ta juya ta kalli matar da Majeederh ke gaisarwa wacce take zaune saman wheelchair Granny ta ce "Wai Gimbiya kike gaidawa? Allah sarki Hawwa'u ai bata da lafiya bata magana bata tafiya hannunta kawai ke motsawa" Cikin tausayawa Majeederh ta ce "Allah sarki, Allah ya bata lafiya" Granny ta ce "Ƙarasa wajanta mana, takwararki ce sunanta Hawwa'u yadda take kallon naki kamar ta sanki bayan ko Nigeria bata taɓa zuwa ba" Majeederh ta ƙarasa gaban matar ta durƙosa ta ce "Sannu Allah ya baki lafiya" Ga mamakinsu sai su kaga tayi murmushi harda hawaye ta riƙe hannun Majeederh ƙam! Sun jima kafin ta ce "Naga saƙon kira" Ƙhulud ta ce "Ohh Takawa ke kiranki" Gabanta ya faɗi ta ce "Mai martaba Sultaan?" Ƙhulud ta ce "Tsohon zance tuni muka ture shi mijina ke kan karaga ai, Mai martaba Ajlaal Sultaan ke kiranki" Ta yi shiru bata ce komai ba Granny ta ce "Fulani rakata mana, yana part ɗinsa ai ya bar fada tuni sai miskilanci yake ji jiya da yau" Ƙhulud ta ce "A'a jinin sarauta ke yawo a jikinsa fa, ba wani miskilanci" Tana faɗin hakan ta miƙe tsaye Majeederh ta miƙe ƙirjinta sai bugawa yake a haka suka ƙarasa wani irin ƙyakƙyawan plat mai ɗaukar kyau ga matso tsaran ƙofa nan birjik suna ganin Fulani suka zube Ƙhulud ta yi murmushi tare shigewa Majeederh ta bi bayanta, suna shiga Ƙhulud ta yi sallamawa yana zaune hakimce idanunsa rufe yana cikin wata Jallabiya mai kama da Alkyabba, ya ɗora hirami a saman kansa ga gefensa fuskarsa suma ta sakko kamar ka taɓa shi jini ya fito, bai amsa gaisuwar Ƙhulud ba, bai kuma buɗe idanunsa ba, Ƙhulud ta miƙe ta ce "Ina zuwa Majeederh" Majeederh kamar ta saka kuka ta cikin liƙab ɗin, amma ta kasa ko motsi. Wajan ya yi shiru ita ba tayi magana ba shi ma bai ce komai ba, bashi da niyyar cewa komai ɗin, shafewar seconds kafin Majeederh ta ce "Barka da hutawa Takawa" muryarta na rawa domin ba ƙaramin kwarjini ya yi mata ba, tana jin kanta Uncomfortable a gabansa musamman da taga kamar bai taɓa sanin wani Abu Annuri ba a saman fuskarsa. Ta ɗauka bai ji ba ta ƙara maimaita gaisuwar nan ma shiru tana ɗago idanunta da niyyar ganin ko baya wajan cikin rashin sa a idanunsu ya sarke cikin na juna, Ajlaal Sultaan ya kafeta da narkakkun idanunsa can kuma ya taɓe baki kana ya janye idanunsa a hankali ta ce "Gani" Ya jima kafin ya ce "Ke wa?" Tama ɗauka ba zai magana ba sai ta ji ya ce hakan. "Ance kana kirana" Bai ce komai ba ganin tana ƙoƙarin wulaƙanta kanta gabansa duk da tarin nata kimar ya sa ta miƙe tare nufar hanyar fita, sai da ta je bakin ƙofa ta ji an ce "Wait" Bata ɗauka da ita yake ba duka jikinta rawa yake Allah ya gani bata taɓa ganin mutum nai haibar Ajlaal ba zata fita ta ji an ɗora hannu akan hannunta dake jikin Handle da sauri ta juya ta ganshi tsaye kamar ya haɗiyeta gabaɗaya ya yi mata rumfa da ƙaton jikinsa rawar jikinta ya tsananta haka ma bakinta ƙirjinta na ɗagawa tunda uwarta ta haifeta bata taɓa yin kusanci da namiji kamar yadda sukai da Ajlaal ba, hannunsa ya murza akan nata kana jata zuwa cikin bedroom ɗinsa ba parlour ba......
No comments