Recent Updates

Mijin Malama 11


11

Cikin sauri Barrister Aliyu zaki ya shiga mota tare da bin bayan Abraham, His Excellency Abu-turab ya shiga zagayawa a wajan yana sauke numfashi a wahale jiri na neman É—aukan shi, ganin yadda yake shirin rasa

Jiddo a lokacin na biyu. Al'amarin na neman zame masa tamkar ta leƙo ta koma ne, ga ƙoshi ga kwanan yunwa. Wanda bashi da mara ba da inuwar giginya na nesa kasha daɗi.

Ya fesar da numfashi tare da juyawa ya kalli Uncle Isma'il wanda ya fito tare da tsayawa a harabar gidan nasa, gabaɗaya ya shanye mamakin da Abraham ya shayar da shi ta hanyar zubawa bakin gate idanu a tuninsa ko Abraham zai dawo da Malama Majeederh. Amma zaton shi ya saɓa tunaninsa.

"Uncle a É—aura auren kawai" Uncle Isma'il ya dubi His Excellency, duba na tsanaki. 

"Matsayin auren fa?" His Excellency ya ce "Zan sanya a rufe ko wacce tashar mota, data jirgin Æ™asa, zuwa na sama, dana ruwa, zan zuba jami'an tsaro a kama shi zuwa gidan yari, ita kuma sai a akai mini ita gidana" 

"Kada ka tsauwala, gaggawa aikin shaiÉ—an Your Excellency" ya Æ™ara girgiza kai ya ce "Majeederh ba auren sadaÆ™a za mu yi mata ba,  tana da daraja sosai Æ™addara ce kawai ta faÉ—a mata, yadda aka juya mata baya ni ba zan bari ba" cikin girmamawa His Excellency Abu-turab ya dubi Uncle Isma'il kamar zai rusuna ya ce

"Afuwan bana nufin haka, ka fahimci ni, ka dubi halin da nake ciki Uncle"

Mahaifin Aliyu Sufyan ya numfasa ya ce 

"Ita mace allura ce a cikin ruwa, mai rabo ka É—auka, ina tunanin abar maganar zuwa sanda wannan É—in zai dawo da ita" "Mahaukaci ne fa, zai iya aikata abinda ya furta" cewar Abuturab.

Murmushi kawai Uncle Bello ya yi, domin ya fahimci hutar son Majeederh a cikin idanun His Excellency.

Sun sha bamban da Abraham, shi a fili yake nuna maitar shi wanda yake sawa ayi tunani jikin Majeederh da kyanta ke fisgar shi tare da ingiza shi zuwa tubalin da bashi kenan ba. 

Shiru ya biyo bayan maganar ta su ko wanne akwai abinda yake saÆ™awa a ran shi. Abu-turab ya kasa jurewa hankalinsa yana can kan Jiddo, zuciya ke raya masa yanzu ga su can É—an iska yaron can mai idanu a tsakiyar kai yana yi mata tijara da keta mata haddi, ya samu damar da shi baya tunanin zai samu musamman da bai hango soyayyar shi a zuciyar Malama Majeederh ba. 

"No, i can't take it"

"Me za ka yi?" Inji Uncle Isma'il. "Zan nuna masa ni ke mulkarshi, zan yi amfani da ƙarfin iko, na manta waye ni, na ajjiya matsayina akan samun Malama Majeederh amma wani na can da ita" "Ba zai cutar da ita ba" cewar Uncle Isma'il.

"Zai aikata abinda ya ce, ai Mahaukaci ne"

"Depression ne"

"Ba su da mara ba, abin da ke gidan ƙaura shi ne a Goje, ka bani dama ka kuma share mini fage"

Sai a lokacin Haseenatou ta yi murmushi mai ciwo ta ce "Abin mamaki baya ƙarewa, raƙumin dawa ya ga na gida,ko a labaran Hikaya, da film da littafan hausa ban taɓa ji ko ganin yadda ake rurrumar auren mace mara tsafta wacce ta haihu ba aure ba sai yanzu" Daga Mama har Abu-turab kallon Haseenatou su ke. "Yes, duk soyayya ta rufe ku,kun makance kun kasa ganin gaskiya na tabbatar da a hayyacinku ku ke ko da kuɗi aka haɗaku ba zaku taɓa sha'awar aurenta ba, to yanzu baku da mara da wanda su ke turo" ta faɗa rai ɓace domin har ranta bata ƙaunar auren Abu-turab da Majeederh.

Ta yi ƙwafa ta ce

"Abin da sake an bawa mai kaza kai" Sona da ke tsaye ta riƙe ƙugu ta ce

"Abin nema ya samu,  matar dan doka ta haifi É“arawo, ka dai ki ce halin dangin miji ne ya motsa miki?" Kamar Sona na karantar zuciyar Haseenatou, bata da burin daya shige irin Abu-turab ya auri Æ´ar uwar shi Intisar ta gyara tsaiwa tana kallon Sona ta ce "Aikin banza talaka ya girmi sarki, ina abun yake? Ai da tsohuwar zuma ake magana"

"Hankaka mai da ɗan wani naka, na aza cewa kan ki ki kewa farauta, to ai ke kin yi kaɗan kuma Anti Jeederh dashen Allah ce, murucin kan dutse bai fito ba sai daya shirya, kuma ƙaddara bata bar kan kowa ba" har huci Sona ta ke don masifa ta ƙara watsawa Haseenatou harara ta ce

"Hannu É—aya baya É—aukan jinka, kin yi kaÉ—an a wannan wasan kina iya komawa ki samo nagartattun Æ´an wasa sai a fafata kuma....,"

"Stop it" Uncle Bello ya faɗa yana nunawa Sona hanyar shiga cikin gida ya ce "Ƴar banza uwar magana,ba ki ɗauka a ƙasa ba" murmushi kawai Uncle Isma'il ya yi domin surutun ƴar ta shi a yau ya yi rana.

Almustapha shi ma ya ji daɗin bayanin Haseenatou, Ubangiji ya sa Aliyu zaki ba zai taɓa samun Malama Majeederh ba har abada.

Musty ya kada baki ya ce 

"Idan kaga kare yana sunsuna takalmi É—auka zai, ba bu rami mai ya kawo rami Allah dai ya kyauta" Hajia ta watsa masa harara. Duk abinda ake Abbu yana ciki bai fito ba, baÆ™in ciki kamar zuciyarsa zata fito wai yau Æ´ar shi ta lalace? Take Æ™oÆ™arin lalata masa family?. 

Ganin yadda duk a kayi shiru kowa yana jimanta al'amarin a ran shi. Uncle Bello ya ce "Ina tunanin mu bar wannan maganar, zamu ƙara zama idan komai ya daidaita"

"Ba zai dawo da ita ba" cewar Abu-turab. Uncle Isma'il ya ce "Zai dawo da ita, da hannun daya ɗauketa ka sanya cewa wacce ta haifeka ba zata cutar da kai ba, to Abraham ba zai taɓa iya cutar da Maminsa ba"

His Excellency ya dubi Uncle Isma'il, ganin kamar shi ne babba kuma waliyyin Malama Majeederh, ya ce.

"Ka bani dama, ka yi mini alfarma a ɗaura auren nan" daga baƙin ƙofa Abbu dake fitowa ya ce

"Ni na ce ka auri Majeederh, kuma yanzu na ce kada ka aureta domin zata ɓata maka iri, kuma sam bata dace da kai ba" Abu-turab ya ce "Don't say that Abbu, kayiwa mata uzuri, kuma ka nasan ita alheri ce a gareni" murmushi kawai Abbu ya yi kana ya ce

"Allah ya taimaka, ko mene ya faru ka kuka da kan ka" yana faÉ—in haka ya nufi motarshi, Mami na bin bayansa suka shige ya ja ya rufe. Uncle ganin Abu-turab ya kafe ya ce "Ka je, zuwa dare sai ka zo mu yi magana"

"Thank you" "It's my pleasure Your Excellency sauka lafiya" Haseenatou kamar zuciyarta tayi bindiga haka ta shige fuuuu! Ta nufi mota shi na motarshi ya shiga ɗaya daga cikin motocinsa Chevrolet Silverado. Ash colour, dake tafiyar sirri ce ya sa baya buƙatar motar gidan Gwamnati hatta P.a ɗinsa Hammad bai taho da shi ba.

Hajia da Papi tare da Almustapha suka ta fi suma gidan ya rage daga Uncle Isma'il sai Uncle Bello da Yaran da suke cikin gidan.

Sosai Abraham ya take giyar motar gudu yake ba tare da ganin abin da yake gabansa ba, idanunsa sun yi jajur ta jikin madubin motar ya hango Aliyu dake biye da su. Ya cije leɓe yana girgiza kai a fili ya ce

"Fouk You, zan kashe ka" ya ƙara sanya giyar motar shi ma Aliyu ya ƙara gudu cikin sauri Abraham ya yi reverse kamar zai tsaya hakan ya sanya motar shi ta daki da Aliyu ya ƙara yin baya da motar ta sake hankaɗe ta Aliyu kamar zata kifa. Duk yadda ta so share shi ta kame kanta ta kasa ganin da gaske kisan kai ya ke son yi akan Idanunta a gabanta "Meke damunka, zaka kashe shi fa"

"And so f****** what?" Ya faɗa yana kallonta, sosai tayi mmkin ganin yadda idanunsa su ka yi bata taɓa ganin hakan ba sai ranar da haura cikin gidan su kowa na barci.

Gudu yake sosai tuni ya hankaɗe motar Aliyu,ta firgita ba kanta take ji ba ɗanta take ji ta runtse Idanunta cikin wata kalar murya ta ce "Stop the car, right there" ya yi mata banza. Hannu ɗaya ya sanya ya ɓalle bottle na rigar jininsa da ta yi masa nauyi bai saba saka kaya irin haka ba, yana cire rigar ya cilla ta gidan baya, ya rage sai singlet fara rabin faffaɗan ƙirjinsa a buɗe. Ga Brest ɗin shi kamar wata ma ce jikinsa duk a murmurɗe naman dake arms ɗin shi sai rawa yake. Ya kai giyar motar ƙarshe. "Stop, ka saurara"

Ya yi banza da ita, domin ya fara losing mind ɗinsa. Da ƙarfi tana ƙanƙame jikinta ganin sun nufi wani rami ta ce

"Don't, listen to me Little" Cak! Ya tsayar da motar dab da ramin tare da kifa kansa a kan sitiyarin motar ya shiga fitar da numfashi mai zafi yana dafe kansa da yake jin kamar zai rabe biyu.

Yadda zuciyarta ke harbawa haka ta shi take harbawa, ta rasa me zata ce masa, ta san kuma ba zai taɓa cewa komai ba. Sun ɗauki wasu daƙiƙo zuwa mintinu ni kafin ya ɗaga kan shi. ba tare daya kalleta ba cikin turanci ya ce

"Ki shirya mutuwa!" 

"Wait!" Ta faɗa ya harɗe hannu a ƙirji girman kai biyu sun haɗu, Majeederh ji da kai da nuna isa musamman da take ganin da auren wuri tayi da tuni ta haifi kamar Abraham. Ya sauke numfashi zuciyarsa tayi masa nauyi without looking at her ya ce

"Why!" "Shi ne tsarina"

"Liar" ya furta ya gyara zama sosai tare da juyawa ya kalleta ya ce

"Na ce ki jirani, na jima da bada saƙon haka, mene na cin mutumci haka?" Ta daure ta ce

"Na sha bamban da tsarin ka, You too young"

Kalmar daya tsana ta ce masa wai shi yaro ne. Ya jima yana kallonta.

"You're my Child, my little boy you're can be my husband har abada, bana son ka, bana ƙaunar ganinka zai dauma a haka ki babu aure, ka ruguza mini rayuwa"

"Child?" Ya yi murmushi kawai tare da sanya hannunsa ya ɗauki Khalil dake barci, ya yi ta kallon yaron cikin so da ƙauna idan ka ɗauke iyayensa da Majeederh babu abinda yake ƙauna sama da Ibrahimul-khalil. A hankali ya yi kissing na sa kana ya kwantar da shi a gidan baya. "Child?"

Ya sake maimaita kana ya ce  "Me zan yi wanda zaki daina kirana da haka?" "Babu har abada"

Cikin zafin nama ya sanya hannunsa tare da fincikota ta faɗa saman shi ya riƙe ta sosai hannunsa ta riƙe idanunta rufe sosai a hankali ya sunkuya ya manna kan shi a wuyanta cikin nutsuwa ya sauke mata laɓɓansa. Al'amarin da ta jisa har tsakiyar kanta, jikinta ya ɗauka gargasar jikin suka mimmiƙe, He just hug her so tight murya a rauna ce ya ce.

"I want you know that if can't be close to you. I settle for the ghost of you. I miss you more than life, And if you can't be next to me, your memory is ecstasy

I miss you more than life"

Shi kansa bai san kalaman na fito masa ba, kuma ya yi alƙawarin ba zai ƙara nuna yana son wani abu daga jikinta ba, yana son ta san ba jikinta ne ya dame shi ba.

"Let go of me"

"Promise me, ba zaki aure ban zan Governor can ba, na rantse da Jesus zan kashe shi" ya zameta daga jikinsa tare da tallafo fuskarta ya É—ora tasa akai ya ce

"I love you, i so much loves you Malumana, ki yafe mini na biki na tuba ban sakewa" ya ƙare maganar yana ƙara riƙe ta da kyau. Wani irin kunya ce ta kamata ranta ya ɓaci ganin yadda ƙaramin yaro ɗan cikinta yake ƙoƙarin sauya mata lissafi tare da kai duniyyarta zuwa inda ba tayi tsammani ba. Hakan baya rasa na saba da rashin sabo, ba wai yanzu ya fara ba amma a kullum sabo yake zame mata. Ta zisge jikinta tare da ɗaga hannu zata zabga masa mari ya yi sauri riƙe hannunta.

"Ya zama last time da zaki mareni, wancan na jure sbd you're my mother,and now zaki zaki matana i can't take it anymore" yana faɗin haka ya sake ta ransa ɓace tare da yiwa motar key, yanzu ne zai ɗauki mataki akan abubuwan da suke faruwa, yanzu ne zai koma ga mahaifinsa ƙilan hakan zai bashi damar mallakar Maluma. Kai tsaye gida ya koma, tunda suka ɗauki hanya babu wanda ya yi magana Malama Majeederh zuciyarta fal tunanin halin da Barrister Aliyu Sufyan Alhassan yake ciki.

Manyan motoci Majeederh ta gani a harabar gidan Uncle Isma'il, hakan bai ƙara bata mamaki ba sai da taga P.a ɗin Abu-turab Hammad kenan, ga kuma wani Dattijon mutum sai shugaban jam'iyya. Uncle Isma'il da Uncle Bello zuciyarta sai bugawa take ta buɗe ƙofa ta fito, Abraham Daniel David ya fito daga shi sai wandon kayan dake jikinsa, ya rungume Ibrahimul-khalil. A hankali P.a ya ɗago kai ya kalli Malama Majeederh tsoro ya kamata ganin yadda idanun Hammad suka kumbura tare da yin jaa alamar ya ci kuka son ran shi. Uncle Bello ya miƙe tsaye tare da ƙara sawa wajan Majeederh ya miƙa mata envelope da abu mai nauyi a ciki. Muryarsa na nuna zallar tausayi da kuma nuna nemon taimakon rai ya ce "Congratulations Majeederh,an ɗaura aurenki da Governor Abu-turab Alƙasim yanzu....

No comments