Kana Naka Book 3 Complete Hausa Novel
[7/20, 7:55 AM] U.M Collection ZMFR CM: *KNKB2020*
*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*
*09069067488*
Ko yaran ban bari sun fahimci Halin da nake ciki ba,daki na shige ina kokuwa da
yanayina.Nace kada su dameni da Hayaniya Hafsah bata nan daman tun jiya ta wuce karofi daganan Abba zai turo mota a Dauketa zuwa kaduna.
Yaran ne kad'ai da babansu ke ta Budurin su da murnan gobe zasu hau jirgi,sannan zasu koma Lagos da zama,kayan su dai masu muhimmanci na hada musu saboda tafiyar jirgi ce yace ko shi daga baya zai saka a taho mana da komai gabadaya,Badariya tana kano sun kusa gama Hidimar kasa bata da Lokaci sai dai zata taho daga baya.
Kwana nayi ina kuka Sai dai ban kwanta ba ina sallah hawayena sun kasa tsayawa sai kuma naji kamar abunda nake shirin yi bai kyautu ba.?kamar in nayi haka na karya raunin zukata da dama ciki har da ta yarana. da suka fi kowa shakuwa dani ammh sai wata zuciyar ta tunasar da ni Babban Dalilina da yasa naji na kara samun karfin zuciya.
Sai dai a komai in zan yi ba ma yin gaban kaina Allah nake fara sawa cikin Duka al'umarana,Shi na daga hannu na roka da kyawawan sunayensa sannan na yi masa magiya na yi masa naci ina kuka ina fadim"Ya Allah kasan damuwar dake damuna acikin zuciyata, sannan kasan wahalwahalun da nayi ta fama da su yayin biyayyan auran da kai ka Umarcemu da yin sa.
Sannan kasan komai da ya faru tunda kai mai ji ne kuma mai gani ne na yanke wani Kuduri a raina ya Allah in har ba alheri acikin Tunanina, Allah ka hanani aikata wannan kudurin nawa in kuma Hakan shine alheri a gareni da Duniyata gabad'aya Allah ya bani Hakuri ka sanyamin juriya kada kuma ka barni ni kad'ai kayi Riko da Hannayena sannan ka yimin Jagoranci a duka al'murana,sannan ya'yana Allah ka tallafe su, kayi musu albarka, ka kara shiryamin su cikin addininka"
Ina addu'an kukana yaki Tsayawa sai na kife kaina a kan hannayena ina ta rafzan kuka,ni da barci sai wajen hud'u na asuba shiyasa na makara sallar asuba sai da naji sa a kaina yana Tab'a kafafuna na bude idanuwana jajir da suka kumbura saboda kuka,na sauke a kansa cikin mitsike ido na ce"An yi sallah ne..?
Kai Tsaye yace"Har mun dawo masallaci ni da yara kina kwance ashe baki tashi ba..?
Jin haka yasa na yunkura Dakyar na mike ina fadin"Ban yi barci da wuri ba ne"
Kai tsaye na wucewa zuwa Tiolet sai ya bini da kallo yaga idanuwana sun tasa ammh ganina a kan darduma sai yayi tunanin sallar Dare nayi,Ficewa yayi falon wajen yaran har Anum ta kunna gas ta Dora ruwan zafi saboda wanka,Amir kuma ya saka a Heater tunda akwai wuta.
Sai da idar da sallah na fito falon ina ganin an saka ruwan zafi nasan Anum ce uwar zumud'i ban dora abun kari ba sai da duk sukayi wanka har da Baban nasu,sannan na fere dankalin Turawa na soya musu sai ruwan Tea muna da sauran kayan ciki sai nayi mana Ferfesu da yawa saboda Mama da Anty Hure,su Anty Nasara suna Karofi sai yau zasu taho ammh ina Tunanin zan Dakatar dasu.
Saboda tafiyar dake gaban mu yasa suna gama karyawa suka fara shiri ni dayake ban iya saka komai aciki na ba gabad'aya komai baya min dadi.
Yaya Ishaq yana dakin mama shi da yaran zainab ta kirani bayan na Dauka mu gaisa tace"Maman Amir yau sai kwanan Lagos ko?
Sai nayi yake kafin nace"Uhm ke bakin k'i mu je mu gyara gidanmu tare ba.?tana dariya tace"Wlh ba haka ba ne zan tsaya shirye shirye ne Daddy wannan karon bai bani matsala ba,da Full yes din sa zan koma ai ko Sati biyu baza'ayi ba zan same ku achan in sha Allahu"Jin haka yasa nace"To Allah yasa"
Ta amsa da Ameen mun taba Hira sama sama na tambayeta yara tace suna makaranta,mun yi sallama cikin girmama juna kamar yadda muka saba,har ta kashe sai na sake kiranta tana dauka nace"Maman Fadil ga amanan yaran nan. Don Allah ki kula da su sannan kiyi hakuri da su,Amir da Anum sun girma nasan zasu yi miki kokarin kula da sauran kannensu. In sun yi ba daidai ba ki tsawarta musu ki yi musu fad'a ki Tsaya kan tarbiyan su don Allah, in sun fi karfin ki ki had'a su da Babansu shi sai ya yi musu hukumci"
Bata gane kan mganata ba yasa tace"yaran da duka nakin da nawan kike hadawa ki rike Maman Amir..?kinsan bani da juriyan kwarammiya yara fa..?kina ma wata mgana muna komawa ai su Farhan daman ya'yan ki ne"Sai nayi mirmishi kafin nace"Ki rike mganata zaki tuna da abunda na gayamiki watarana"ban tsaya sauraran mganarta ba na katse wayata ina maida numfashi anya zan iya kuwa.?sai wata zuciyar tace min zaki iya in sha Allahu Fa'iza.
Anty Nasara na kira tana Dauka sai tace min gasu nan gidan Goggo yanzu zasu taho kai tsaye nace"Ku yi zaman ku nima ganinan tafe"
Cikin mamaki Anty nasara tace"Ga ki nan zuwa..?ban gane ba.?kun fasa tafiyar ne..?
Kai Tsaye nace"Aa.."
Anty nasara tace cikin mamaki"Bangane a'a ba ki bude baki ki yi min mgana Fa'iza"Bana son mgana alokacin sai kawai nace"Sai dai nazo"
Da sauri na katse kiran,ina jin kaina yana saramin ban zauna ba na mike na rika fito da jakunkunan kayana na zuwa falo,Sai ledan kayan da ba cikin kayana zan hada shi ba.
Ina cikin aikin ne sai ga shi ya shigo yana ganin haka sai yace"Yauwa daman mganar da na shigo nayi miki ne,bari naje tasha na yo tashar Ko Sharon ne yadda zasu daukemu da kayanmu duka"
Kai na gyad'a mai kafin nace"ni ma ka yo min tashar Ko karamar Golf ne don Allah"
Cikin mamaki ya juyo yana kallona lokaci d'aya yana fadin"bangane ba..?sharon fa zata ishemu in na yo tashar ta"
Kai tsaye nace"Aa ina so zan aika ma Goggo wannnan Frezer din karofi ne, in na barsa anan ba'a amfani da shi zai lalace. shiyasa nayi mgana da ita zan aika mata da shi"
Kamar zai yi mgana sai ya fasa ganin zai fita yasa nace"Kayi ma su Amir mgana su zo su fitar da kayan su"
Ya amsa min da toh ina ji ya leka Dakin Mama yana musu mgana,sai da suka zo nace su fito da kayan su tsakar gida daman tun jiya nagama duka kaye kaye muka kwashe komai muka adana cikin rawan jiki suka fara fito da kayan suna murna suna jin Dadi kallon su kawai nake yi ina zaune ko wanka ban yi ba Anum ce tace"Umma ke bazaki shirya ba ne..?
Sai na Rausayar da kai ina fadin"Zan yi wanka yanzu Anum"
Nan suka fice suka barni,ina sake sake ganin zaman bazai amfaneni ba yasa na mike na shiga daki,tubewa nayi na shiga wanka,kokarin daidaita kaina nake yi saboda in na rasa kwarin gwiwa bazan iya aiwatar da kudurina ba.
Na fito wankan kenan ina Shafa mai,naji dawowar Yaya Ishaq da maganan su Mama sai hayaniyar yara kamar suna fita da kayan ne waje da Sauri na Zura Doguwar rigar leshi,daman kwalliya ba aikina ba ne,Dankwali kawai na dora na zura Hijabi,na fito da sauri duk suna Tsakar gida har su Mama yana ganina yace"Ga motar chan a waje."
Nasan wanda nayi masa mgana ne kai Tsaye nace"akwai yara a waje ne..?
Juyawa yayi yana fadin"Bari na duba"
Ba jimawa ya Dawo,da wani Saurayi tare suka kama suka fita da Babban Frezer din da Starplezer,Anty Binta da ta shigo kenan ta ci karo da su suna fita da shi shine ta shigo tana fadin"Ina za'a je da wannan frezer din.?ba dai Lagos ba..?
Dayake na gayama su Mama karofi zan kaisa sai itace ta bama Anty Bintan amsa ni dai muna gaisawa na koma daki na shirya a gurguje saboda kada na bata Lokaci,hijabina na saka Dogo har kasa ni na kulle sauran Dakunan gabad'aya na fito da jakar hannuna na,karama na duba duk sun gama fita da kayan suna jidan sauran zuwa waje ne, har da Baban nasu ina kulle dakin na juyo ina kallon Amir da zai Dauki karamar ledar da na fito da ita da Sauri nace"Kai bani ledan nan"
Ba musu ya mikamin na karba ina fadin"ina kayana.?kun kai waje ne..?
Cikin natsuwarsa yace"Daada ya saka a mota"ina shirin mgana sai ga shi ya shigo yana fadin"Ku hanzarta fa Goma ta wuce mu isa kano akan Lokaci,ke kuma ga mai motar nan yana mganar lambar wanda zai kira in ya isa karofin..?
Anty Binta har ta fice,Mama ce da Anty Hure ban damu ba nayi karfin halin yi masa mgana ganin zai sake fita cikin Dakiya nace"Ina son mgana dakai"
Ba shi kad'ai ba har Mama sai da tayi mamaki gabad'ayan su suka kuramin ido,Sai nayi saurin Kauda kai ina juyawa na koma na bude dakin na shige daidai Lokacin da yake fadin"Fa'iza zamu makara fa kinsan jirgi ba jiranmu zai yi ba"
Ina kokarim daidaita yanayina nace"In sha Allahu bazaku makara ba"
Biyo bayana yayi muka Tsaya a Tsakiyar falon,na juya bayana ina maida hawayena a bayana ya tsaya yana fadin"Kin kuma juya.?wata mgana ce..?
Sai na juyo cikin karfin hali,idona yake son kallo saboda ya Fahimci yanayina ni kuma sai naki basa Dama,jikina ne ya kara yin sanyi Sabida ba jimawa mun yi mgana da Anty Fadila tace ita da mijinta zasu zo Filin jirgi daukan mu sai min je gidanta mun huta sannan su rakamu Sabon muhallin mu,da ita taje jiya ta kara gyara shi bayan kamfani yazo ya saka kayan Furnitures.
Har muka gama waya ban samu abunda na gayamatabba, ina jin kunyar gayamata cikin masu sauka a Lagos ba Fa'iza a ciki.
Ledan hannuna na mika masa sai ya saki baki yana kallona cikin sanyin jiki yace"Meye wannan kuma..?
Kai Tsaye nace"Duba ka gani mana"
Sai ya amsa ya bude yana gani Lokaci d'aya yana kallona da mamaki da alamun karin bayani da sauri nace"Kayan ka ne. Tun daga lokacin da ka jingine aurena da kai na daina amfani da duk wani abu naka,Abinci dai naci sannan ka bani wajen kwana Darajan ya'yana nagode kwarai Ishaq."
Na fad'a ina kallonsa ido cikin ido yadda ya kafeni da ido ne yasa nasan karin bayani yake so sai na yi ta Mazan cewa"Kayi hakuri Ishaq. Bazan iya binka Lagos ba."
Cikin Daga murya yace"What..?wannan wata irin mgana ce Fa'iza don Allah ki bar wannan wasan bana so.."
Ya fad'a har yana d'agamin hannu,sai nayi mirmishin takaici kafin nace"Ba wasa nake yi ba. Da gaske nake yi, daman na fad'a maka ka bani Lokaci naga ko zan iya bama auran mu wata Dama ko ba haka ba..?
Kamar gaula haka ya gyad'amin kai sai ya bani Damar cigaba da mgana ina fadin"To abunda na Dad'e da yankewa kenan,rasa aikin ka da abunda ya faru yasa na dakatar da kudirina,ammh yanzu tunda ka samu aiki komai ya wuce zama na dakai ya kare daman auran ka jingina ne, shine nake rokom ka ka karisa ballesa daga wannan jinginan ma'ana ka Furta min SAKI da kan ka"
Na gama fad'a ina maida hawayena lokaci daya ina jin karfin gwiwa na shigata shi ko ledan hannunsa ne ta kubce ta fadi kasa cikin Tsananin Firgita kamar kiftawan ido na ji sa ya Damki kafaduna duka Biyu yana fadin"Fa'iza ki daina irin wasaan. Wani irin saki.?ki yi tunani mana kina tunanin zan iya sakin ki ne.?so kike na rabu dake wai Fa'iza..?
Kai Tsaye na gyad'a masa kai cikin idonsa nace"Kwarai haka nake nufi ka Sauwake mun auran ka domin bazan so ka cigaba da zama da matar da baka so ba. Ka auri zab'inka a wanchan Lokacin kace nayi maka adalci in barka ka yi rayuwa mai Dad'i da matarka. ni ma a wannan karon ina neman wannan adalci nima a wajenka kayi hakuri ka sakeni, daman a jingine nake kamar yadda ka fad'a"
Ban ko gama mgana ba kawai naga ya sakeni da karfi yana fadin"Ina. Wasa kike Fa'iza har fa mun shirya jirgi na jiranmu fa ?kowa yasan yau zamu tafi sai yanzu ki sauya mgana..?ga yara chan na murna sai na fita nace musu me..?su Mama na Tsakar gida me zan gaya musu..?to wai kina nufin na tafi ni kad'ai dagani sai yara.?wa zai kula damu Fa'iza rayuwar mu ta fara tare dake kuma Dole mu karisa tare Fa'iza har Abada babu saki ko yaji Tsakanin aurena da ke"
Nima cikin Tsawa da Daga murya na taresa da fadin"Ammh akwai jingina acikin auran namu ko..?sannan akwai Tozarci da wulankanci duk aciki ko.?kayi hakuri na riga na yanke hukunci bazan iya cigaba da zama dakai ba.."
Sai ya juyo yana kallona cikin Fitan hayyaci yana fadin"In sake ki na Lalace Fa'iza?kin manta abunda Baba ya fad'amin?yace in na rabu dake na rasa mata tagari sannan bazai taba yafemin ba in na barki,don girman Allah ki bar wannan mganar ki bari in muka isa chan na yarda mu zauna da Mama ki fad'a mata komai tayi mana Sulhu, ammh zuciyata bazata iya Daukan wannan mganar ba. plz ki bari don Allah"
Ya fad'a har yana hada hannayensa alamun roko gabadaya tsoro da firgici sun bayyana a saman fuskarsa gabadaya,jikinsa kuma sai rawa yake yi,ina kallonsa kamar zan yi rauni sai kawai na tuna da irin zaman Tozarcin da nayi da shi na Tsawon shekarun auran mu,kuka ya kwace min na juya baya na ina fad'in"Kayi hakuri ba zan iya ba.."
Sai kuka shabe shabe,Ban sani ba ashe duk'amin yayi sai ji nayi yana jan Hijabina Lokaci d'aya yana fadin"Ki yi ma girman Allah Fa'iza ki yi hakiri ki bar mganar nan. Hankalina tashi yake yi in naji kina fadin saki da kuma cewa bazaki bimu ba.?Ta yaya kike so na fara rayuwa a in da baki..?
Bansan Lokacin da na juyo,har ina bangajesa cikin daga muryan da bansan ina da shi ba nace"Zaka iya. Nace Ishaq zaka iya.."
A baya ka zauna da wata macen inda bani kuma baka mutu ba. Na fuskanci Kaskantattaciyar rayuwa a gidan auranka,na fuskanci tozarci a wajen ka da wajen dangin ka a karkashin auran ka,ka rabani da kowa nawa ciki har da mahaifiyata ka rabani da yan'uwana duk wani mai so na baka kaunarsa,baka son ganin Dariyata sai kuka na Ba a macen aure ka Daukeni ba,ka Daukeni a baiwa,mara gata,jahila wacce bata da ilimin zamani,sannan mummuna baka wacce ka ke zaune da ita Saboda alfarma,wacce tayi ma rayuwarka karan Tsaye Fa'izar dai da tayi ma mafarkin ka kutse, Fa'izar da ka zaunar da ita kana rokonta da ta taimaka tayi maka adalci ka zama na mace Daya,Matar da ka fifita a kan Amaryan ka,Fa'izar da baka san ciwon ta ba,baka san cikin ta ba,baka san zafin nagudar haihuwar ya'yanka da ta dinga yi ba, itace dai wacce ahaka ake kiranta kamar akuya ta cika Haihuwa Fa'izar da ka nemi datse mata Haihuwa saboda baka kara kaunar Zuru'a da ita,Ni ce dai Fa'izan da kasa nuna ma duniya ni matsayin matarka kana jin kunya,Nice Fa'izan da ka ke barina wata da wattani Saboda wata mace ni ce Fa'izan da na dauki dukkan Tozarcin yan'uwan ka har da na Dangin matarka saboda Fa'iza bata da gata,Fa'iza ba kyakyawa bace. Sannan bata da ilimin zamani ba wayayyiya bace ba kuma yar gayu ba ce,sannan ita ba fara bace bata kuma iya haihuwan Fararan ya'ya ba,ni ce Fa'izan da kake kirana mara amfani Fa'izan da auran ta bai amfana maka komai ba ni ce dai Fa'iza nan wannan mai raunin jin,wacce ka ce ka tsani mgana da ita saboda tana saka ka ihu ko ka manta ne..?
nice fa nice fa kake kiran bazaka iya Rayuwa a inda bani ba..?karya ka ke yi..Wlh karya ka ke yi.."
Na karishe fad'a cikin Tsawa Lokaci daya da kuka sai kawai na zube saman Cafet din ina wani irin kuka mai cin rai ban sani ba ihu na da mganata yasa su Mama rugowa Dakin,duk a gabansu na rika amayar da abunda ke cikina.
Su kansu jikinsu yayi sanyi sannan sun kasa gane wasu abubuwan
Shi bai ma gansu ba sai ya rarrafa cikin Fitan hayyaci ya na kokarin rikoni nayi maza nayi baya da jajayen idanuwana ina fad'in"Kar ka kara tabani. Kar ka kara in ba haka ba wlh zan sharara maka mari"
Na fad'a ina nuna sa da yatsa cikin bacin rai da bai taba ganina aciki ba
Sai ya kasa karisowa gabana,cikin rawan baki da na murya yace"Fa'iza ba kin ce kin yafemin ba..?
Me ya sa..?
Kai Tsaye nace"Eh da gaske na yafe maka,.ammh ba shi zai goge tabon da kayi ma rayuwata ba.
Dalilinka aure ya fita kaina na Tsani duka maza sannan nake Tausaya mata ire ire na da Tunanin wata irin Rayuwa su kuma suke fuskanta a gidan nasu auran..?ka taba Tunanin ko sau d'aya kayi min adalci?
Nace ka taba wannan tunanin.?
Sai kawai na kara fashewa da kuka ina fadin"A gabana ka kori yar'uwata uwa d'aya uba d'aya,Har kana ikirarin in ka kara ganinta a gidanka zaka had'a ta da Hukuma?ashe ko bata ci darajan aurena da kake yi ba, bazata ci Darajan zumunci ba Ishaq..?
Mahaifiyata ta rasu bata san Dadina ba. Har ta koma ga Allah ban taba zama da ita na yini d'aya ba.
Ranar da zata rasu ma baku barni na kwana da ita ba,ta rasu ban sani ba.
Na rasa uwata ammh ko gaisuwa baka zo min ba, kana wajen wacce ta fini muhimmanci a wajenka.Sai da ka dawo baka iya ce min Fa'iza ya hakuri ba sai Duba na kayi kana ce min ashe wai kuma babarku ta rasu..? Wai ne ma baka Tabbatar ba.?shine kake so na manta..?ko kuwa yadda ka ware ni daga cikin sauran mata a dalilin auranka yasa nayi shekaru ina fama da Gulit din mata masu kyau da gata ne suka chanchanci ado da kwalliya,a gidan ka na fuskanci mata ire irena basu dace da samun soyayyar miji irin Ishaq kabir karofi ba. Shiyasa na yanke shawaran karshen zama na dakai yazo daga yau.Na rantse da Allah bazan bika ko'ina ba. Daganan karofi zan koma daman ranar da Baba yace zai had'a aurena dakai Mama ta koreni sannan tayi alkawarin bazan koma mata gida ba,Karofi na koma wajen Goggo kuma chan aka daukoni nan duniya bani da gatan da ya fi gaban Goggo gabanta zan koma na zauna Domin Fuskarta Sabuwar rayuwata"
Na karishe Fad'a ina share hawayena lokaci Daya na mike da Sauri ina fadin"Zainab zata iya kula da kai. Yara kuma Amir da Anum sun yi girman da zasu iya kula da kansu. Ahmad da mutsy ba su da matsala zasu kula da su.
Ba lalle ba ne don na faro rayuwata dasu na karishe ta da su ba..Haka Allah ya kaddara Labarin ya kare daga wannan Lokacin"
Na fad'a Lokaci daya ina Daukan karamar jakata,Mama na gefe sai sharan kwallah take Anty Hure ta sha gabana tana fadin"Haba Fa'iza ku ba yara bane. yi hakuri mu tafi in mun je chan sai a zauna a fahimci juna'
Kallonta nayi kafin nayi mirmishin takaici na tuna har da ita a masu biye ma Mama suna cin zarafina,sai kawai na kad'a kai ina fadin"Bakin alkalami ya riga ya bushe Anty Hure.."
Na kad'a kai na zan fita waje,Ishaq ya yi kukan kuran shan gabana yana rike Hijabina na balla masa harara ina fadin"Cikani kafin raina ya baci"
Yaki ko sakina fad'i yake yi"Fa'iza ina zaki.?Fa'iza kada ki yi min haka..?me zan ce ma yaran chan..?
Fa'iza..Fa'iza"
Sharr sai kuka abunda ban taba gani ba,kai na kauda abubuwan suna dawomin kamar yanzu komai ke faruwa,kwace hijabina nayi ina fadin"Na fada maka kuma zan kara fad'a maka na gama zaman aure da kai. Na tsani aure na tsani kowani zamantakewa,Ka sauwak'e min Ko kuma ka k'ara Turgud'e shi daman jinginanne ne"
Na turesa zan wuce sai ya makale kafafuwana yana fad'in"Kada ki yi min haka Fa'iza,Kada ki yi min haka"
Kasa kwace jikina nayi sai kawai na juya ga Mama tana kuka nima ina Hawaye nace"Mama ki fad'a masa ya cikani don Allah"
Sai Mama ta sunkuyar dakai shi ko,sai alokacin yaga su Maman sai ya sakeni ya Rumtuma wajenta ni kuma sai na kwashi Sauri na fita Daga Falon ina Fitowa sai nayi Turus ganin yaran duk Tsaye suna jin abunda ke faruwa ga Anty Binta itama.
Cikin mamaki tace"Fa'iza meke faruwa ne har kofar gida ana jin Hayaniyar ku..?
Ban bata amsa ba Ishaq ya fito rike da Hannun Mama ya kawota gabana yana fadin"Mama ki gaya mata wlh nayi nadama.bKi gayamata abunda Baba ya sha fada'min,Yace in na rabu dake zan lalace Fa'iza ko so kike kada nayi albarka..?
Komai ban ce ba kaina na kallon kasa ina Digar kwallah,Mama ma sai sharan hawaye take yi Anty Binta ta kalli Anty Hure tana fadin"Anty meke faruwa ne..?
Anty Hure cikin Damuwa tace"Fa'iza ce tace bazata bisa lagos ba. Tana neman saki ne da wasu mganganun da ban gane ba.."
Sai ta waro ido kamar yadda yaran suka yi cikin wani yanayi tace"Fa'iza yanzu kuma?kika ma zauna dashi a bai da shi sai kuma yanzu da Dadi yazo sai kice haka.?aa ku bari muje chan sai mu zauna mu tattauna kin ji ko..?tafad'a gabanta na fadi domin bata san ya wannan al'amarim zai kare ba.
Jallonata nayi ina tuna Yadda tayi Tsawon shekaru tana Tozartani har da ita masu saka bakin na zauna sai kawai na share hawayena ina fadin"lokacin da bai da aiki wannan yanayin da mata ire iren Fa'iza ya Dace shiyasa ban tafi ba tun a wanchan Lokacin,sai yanzu kuma da komai nasa ya dawo sai nayi Tunanin Lokacina ya kare daman kema kin sha Fad'a jin dadi bai dace da mata ire irena ba,wahala ce da bauta ta Dace dani kamar yadda Mama ta sha fada. Shiyasa zan tafi zainab itace ta Chanchanci zama da shi Tunda ita ta tako kashin arziki sannan bata yi kama da matan bauta ko wahala ba.."
Dukkansu Tsaye suka yi an kasa mai mgana ina gani Anty Binta na zaran ido sai kawai nayi Dariyan takaici kafin nace"Na kwashe fin shekara goma ina bautar aure kuna ganin komai ammh baku taba zaunar da shi kin fad'amasa bai kyauta ba..?sai ni yau don a shekaru goma sha Biyar da auran mu na yunkuro sai ku nemi Danne ni.?wannan karon ba wanda ya isa ya hana Fa'iza tafiya.
Zan tafi kuma tafiya ta har abada"
Ina gama fad'in haka na ratsa Mama zan wuce sai ta riko Hijabina tana kallona,yanayinta zai sakani rauni sai na daga kaina sama cikin wata murya tace"kiyi hakuri Fa'iza.
Ba domin na isa ba..Ki yi hakuri ki Duba yara nan kada ki bar su yi maraicin uwa"
Ta fad'a tana nuna su Amir,Anum har ta fara kuka da su Ahmad zuciyata ta karye ammh ban damu ba Hawayena na Shatata saman fuskata nace"Ke kan ki shaida ce Fa'iza bata dace da D'anki ba.,yaran nan kuma rabo ne Allah ya sa na same su,maraici kuma baza su yi maraici ba Mama kina nan ga Zainab,sannan shi ma babansa zai kula da su tunda ya'yansa ne sune Dolensu bazan ce a zama da shi bai Tabamin wani abun alheri ba,yayi min Tunda dalilin sa yasa yau nake amsan sunan uwa,ammh mganar na Duba yaran nan bai taso ba. Nima a lokacin da yake tozartani ko sau d'aya bai tab'a Duba darajan ya'yana ba.."
Na fad'a ina kallon su, bana so na cigaba da mgana a gabansu kada su ji,kamar ma Amun da Amir tunda suna da wayan su.
Na tuna Lokacin da Anty Binta tazo ita da Mama suna min watsi da kaya akan sai na bar gidan,meyasa yau don nace zan tafi sai su damu..?
Wani tukuki ya taso min dayasa har jiri na fara gani cikin Duhun ido na juyo ina fadi'n"daman kuna so na tafi,Aurena ba alheri ba ne ko ba haka kuka fad'a ba..?meyasa don yau nace zan tafi kuke magiyan kada na tafi..?Wlh kaina tuni ya Dauki Dumi kuka na kara Fashewa dashi na juya ga ya'yana da suke kallona cikin rauni hatta Amir da ba kasafai ake ganin kukan ba yau har da majina,Ahmad kuwa da gudu ya nufeni ya rumgume ni yana fadin"Umma zan biki ni dai"
Musty ma ya kariso yana kuka ya rikemin Hijabi gam yana fadin"Nima Umma ke zan bi na fasa zuwa Lagos din"suna mgana kukana na karuwa Anum ma ta rugo ta makalemin jiki ta fashe da kuka tana fadin"Umma nima ke zan bi"
Ina Kuka suna kuka Amir na Tsaye shi bai zo ba na dago ina kallonsa cikin kuka nace"Amir ku yi hakuri ka zo ka taimaka min ka lallashi kannen ka"
Sai kawai shima ya rugo da gudu ya Rumgumeni yana fadin"Umma zaki tafi ki barmu?don Allah kada ki tafi Umma kada ki tafi ki barmu"
Sai kuka yadda suke kukan ne yasa naji gabbaina sun yi sanyi in na tafi na barsu yaya rayuwarsu zata kasance?sai na juya ina kallon Ishaq da idanuwansa suka kad'a jajir,sai kawai naji Duhu ya rufeni da Hanzari na yakice su a jikina na duka Bisa gwiyoyina dukkansu na rike hannayensu cikin nawa sannan na Dauki na Amir na rike ina fad'in"ba inda zan je ina karofi gidan Goggo zan koma,In ina bukatar ganin ku zan zo ko ku kuzo wajena,sannan zan rika kiran ku a wayar Anynku muna gaisawa kun ji ko?
Ahmad ya makale kafada yana Fadin"ni dai umma zan biki"
Musty ma yace haka Anum Sarkin kuka tace"Umma ki tafi damu chan gidan goggon mana"
Ina girgiza kai hawaye na zubomin nace"Bazai yuyu ba Anum. ku kuna da Baba sannan ga kakar ku nan bazai yuyu ku bini ba,ni kuma bani da uwa ba ni da uba,Goggo itace gata na shiyasa zan koma wajenta ku kuma Babanku na da mata Antynku ga kannen ku su Farhan,ku zauna lafiya da junan ku ku zama masu jin mgana Amir kai ne Babba ka rike kannen ka Amana ka ja su ajikinka a matsayinka na Babban Yaya,ku zama masu jin mgana da Tarbiya Anum ki kula da Ahmad kin ga shine karamin cikin ku kada ku takurama Antynku komai tace ku yi kuyi kun ji ko..?.sai suka kasa dagamin kai ina kokarin Dauriya na saki Hannayensu na rika bin su daya bayan d'aya ina share musu hawaye ina fad'in"kada ku ce zaku rika saka Anynku mgana,Amir karatu ka rika duba na kannenka,Karatun Qur'ani ku rika bita kada ku manta da azkar din safe da maraice,ban da abokan banza sabon waje ne bakusan kowa ba,kada ku manta da Tarbiyan da na baku Anum kece mace ki rika taimaka ma Antynku da ayyukan gida kuna ji ko..?
Sai gabadayansu suka bare min baki Amir jikina ya fad'a yana fadin"Umma mu ba ma a son Antynmu ke muke so.."
Hawaye suka kwaranyomin na kamkamesa ina kuka Anum ta ruga wajen Babansu tana fadin"Daada kaje ka ce Umma kada ta tafi.."
Tana fada tana jan Hannunsa,sai ya biyota har gabana shima dukawar yayi,yana fadin"Don Allah Fa'iza ki duba yara nan"
Ban ko amsa mai ba na hada ya'yana na Rumgume gabad'ayanmu muka saka kuka,Mama na gefe sai ta juya kawai ta fice tana kuka Anty Binta ma duk jikinta yayi sanyi in Fa'iza ta tafi ya kuma abubuwa zasu tafi?Zainab wannan yar son jikin da bata iya komai ba, ta ina zata yi da Dawainiyar yara?akwai matsala babba kuwa.
Suna kuka ina kuka da na ga bazai Fissheni ba na rarrashi kaina na koma ina ba su hakura suka makaleni suna kukan sai sun bini Hon din masu mota ne ya ankarar damu suna jiranmu,Ishaq ya marairaice yana fadin"Na siya mana Ticket Fa'iza asaran kudina kike so nayi..?
Kai tsaye nace"Ai ban ce ka siya har dani ba. Tunda ban ce maka zan bika ba"
Cikin wani yanayi yace"To dukkanmu mun fasa bazamu tafi ba, mu tattara muje karofi a warware komai"
Cikin yak'e nace"Kada ka biyoni Karofi Ishaq ka lallaba ya'yanka ku tafi,kada ka manta aikin. ka fara ba jimawa rashinka a office zai iya zame maka matsala sannan meyasa bayan ka kashe kudin jirgi zaka fasa?
Na fad'a ina kuramai ido gani yayi kamar na fara saukowa yasa da Sauri ya rikeni yana fadin"Fa'iza zuwan bashi da amfani idan baki kin sani ko?
Kai tsaye nace"Bazan bude baki nayi mgana ba.ka lallashi yaran nan ku tafi in kuma kace zaka bini karofi zaka Fallasa kanka da kanka. Daman na Fada maka da bakina bazan fad'i komai ba,sai dai in kai ka fad'a da kanka"
Shuru yayi yana ajiyar zuciya a Firgice kamar wanda yayi karya,Ban damu ba naja hannun su Ahmad da Musty,su Amir suka biyo bayana muna zuwa kofar gida masu motoci na jiran mu sawa nayi aka Fitomin da akwatina da jakunkuna na,nace a sakamin a karamar Golf din nan,Mama na gefe tana sharan kwallah,su Ahmad nata kuka har Lokacin sai na Daure saboda bazan bari su hanani Tafiya ba,key din gidan na isa gaban Ishaq na Damka masa ina Fadin"Key din gidan nan, ne Sauran kayana in ka sauwakemin zan zo na kwashe"
Makullin fad'i ya yi a kasa,ya kasa amsa ni kuma na juya ina goge kwallah na bude bayan mota na shige,Su Amir sun yinkuro zasu shiga na rufe kofar da karfi ina kuka ina ganinsu suna kuka suna dukan jikin mota ammh na kasa motsi,Direba ya shigo yana fadin"Hajiya yaran nan zasu hanamu tafiya fa"
Kai tsaye ina kuka nace"Glass.! d'agamin"
Ba musu ya d'agamin na Leko da kaina da sauri suka nufeni Ahmad sai fadi yake Umma nima zan biki shi da Musty,Amir na share ma Hawaye Na rike hannun Anum ina fadin"ba na ce ku lallashi kannen ku ba..? To in dai kuna kuka bazan dawo na Dauke ku ba"jin haka yasa suka daina kukan Amir yace"Umma to kizo mu tafi tare"kai tsaye nace"Aa ku fara yin gaba, ni zan zo daga baya..Ka kula da kannen ka kaji ko Amir"
Sai ya gyad'amin kai dukkansu na Shafa kansu ina fadin"Allah ya yi muku albarka"Sai kuka yaci karfina cikin kukan nace"Direba muje"
Lokaci daya na maida glass din na zuge,mun fara tafiya na juyo ina daga musu hannu Ahmad ya kwace yabi motarmu yana kiran sunana har yana Fad'i ina gani Baban yaje ya daukesa,Anum kuma Mutsy ta rike tana kuka Anty Binta ta rike Amir kasa Daurewa nayi na juya ina kuka kamar in ce Direba ya Tsaya sai kuma wata zuciyar tace"Fa'iza ki sani ko kin koma baki da wata daraja. Ishaq Zainab kadai yake so ke alfarma yake miki"
Ammh ya'yana fa..?basu saba da kowa ba sai ni wazai kula da su..?zasu fara sabuwar rayuwa a inda bani ya ya zasu tafiyar da rayuwar su.?Zainab bazata kulamin da yarana ba bazata iya ba,yar gatace bata saba da wahala ba ,yaranta ma yan aiki ke daukan mata su,Tarbiyan su da na dauk'i shekaru ina ginawa in ta rushe fa..?
Kuka nake yi da karfina har sai da Direba ya juyo yana fadin"Hajiya ki yi hakuri,In bazaki iya tafiya ba sai mu koma ko kuma ki taho da su naga yaran basu son tafiyarki hala rabuwa kuka yi da Baban nasu,duk da shima naga kamar bai so tafiyar ta ki ba..?
Irin dirobobin nan ne masu fad'i ba''a tambaye su ba.
murya shake nace"Karofi..Karofi zaka kai ni"
Na katse mganarsa lokaci d'aya ina cigaba da kuka zuciyata na Zafi kaina ya fara Dif Dif ga jirin danake ji. alama ce ta jinina ya haye sama.
Har mun yi nisa sai naji bazan iya wannan jarumtar ba ya'ya na,ya'yana kawai nake tunani.
Sai kawai na ce ma Direba"Tsaya mallam.."
Sai ya juyo yanaa fad'in"In tsaya..?
Sai kawai na gyad'a mai kai da sauri ina fad'in"Mu juya mu koma..! mai dani da sauri'
Ina haki na fad'a,Tunani na da zullumi na,kada kafin mu koma mun iske sun tafi.
Na fasa bazan iya nesa da yarana ba. tunda na iya kwashe tsawon shekaru goma sha, cikin tozarci na jure me zai hana yanzu bazan jure ba..?kuma yayi nadama zan karbi Tubansa zan bisa naje na zauna tare da yarana.
Muna tafe ina fadin"Kayi gudu don Allah ka yi sauri."
Yadda nake mganar zaka san bana cikin Hayyacina.
*K'arshen littafi na Biyu,Littafi na uku zai zo in na samu natsuwa insha Allahu,Ammh ba gabadaya zai zo ba,zai zo kamar yadda muka fara daga farko.*
*Nagode..Nagode da Soyayyarku Allah ya bar zumunci Ameen*
*Janafty*
*19/17/2023*
[7/24, 7:47 PM] U.M Collection ZMFR CM: *KNKB3001*
*Madallah da ku,Nagode da soyayyarku gareni.*
*Nagani kuma na yaba,Ubangiji ya saka da alheri. Ina gaida masoyana gabadaya Allah ya had'amu a Aljannah Ameen*
*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*
*09069067488*
Lokacin da nace Direba ya juya dani,fita daga hayyacina nayi.
ya'yana kawai nake tunawa,ina tuna kukan da suke yi sanda zan tafi a raina nake jin kirjina ya matse waje d'aya,na kasa Sarrafa kaina abu d'aya zuciyata da gangar jikina suke fad'amin. Fa'iza Zaki iya ba ma auran ki wata dama Fa'iza zaki iya ko saboda ya'yanki.
Bansan Lokacin da na furta a fili ba"Zan bashi wata dama. Zan bashi ko Saboda ya'yana"
Ina fada ina shara hawayena ina kokarin bama kaina karfin gwiwa,Sai dai sai me?muna shiga layin sai naji gabbaina sun karayin sanyi kalau,zuciyata ta fara sakewa kirjina ya fara nauyi,gabana kuma na fad'i Ras! cikin wani yanayi a acikin zuciyata nake jin kamar ana min mgana da cewa Haba Fa'iza ashe kin manta irin zaman da kika kwashe shekaru sama da goma kina yi tare da Ishaq.?Ashe kin manta bai taba sonki ba?Mama bata kaunar ki ba,ko ya'yanki Rabo ne ya shiga Tsakani,kin manta da cewa wanda yace baya sonka har abada baya sonka? Sai alfarma yake yi maka kamar yadda ya fad'a"
Ya'ya ba kanki farau barin su ba Fa'iza, bazasu mutu ba in kikaga sun mutu Lokacin su ne ya yi,in kuma suka rayu Allah ne ya rayasu ko kina Tare da su,ko bakya tare da su ta Allah in yaso zata kasance tare da su,kada ki bari Tausayin ya'yanki ya hanaki cika Muradinki.
Kamar wacce aka bugi kaina,cikin kiftawan ido na dawo cikin hayyacina na fahimci shirmen da na kusa yi ma kaina da rayuwata,kamar yadda na saba a baya.
Da sauri nace"Direba. Direba juya mu koma,Mu koma kawai"
Na fada ina kokarin danne kukana,cikin mamaki Direba yaja ya tsaya sannan ya juyo yana kallona Cikin wani yanayi ganin yadda nake kuka,sai kawai ya koma ya gyara zama yana fadin"Hajiya ki tsaida Shawara d'aya in tafiya tafiyar in kuma komawa to komawar"
Sai kawai na shiga Sharan kwallah da Bayan hannuna cikin Dashewar murya nace"Muje kawai.."
Cikin jadaddawa yace"kin tabbata Hajiya?
Cikin Tabbatarwa na gyad'a masa kaina lokaci d'aya ina kokarin bama kaina karfin gwiwa.
Acikin zuciyata kuma ina maimaita Hasbunallahu wani'imal wakeel domin samun karfin gwiwa,Nan take Direba ya juya muka koma.
Ban kara yadda na zauna haka ba saboda kada zuciyata ta kara raunana muna tafe ina salati da Hailala acikin raina,sai dai kuma kukana ya kasa tsayawa ina na zucci sannan hawaye sun kasa daina ambaliya a saman fuskata muna tafe ina yi ina saka hannu ina sharewa sannan ina faman jan Hanci da majina.
Wlh bansan mun iso Karofi ba sai da naji yana tambayana inda zamu je sannan na daga ido na ga inda muke,sannan nayi masa kwatance,Ina jin wayata acikin jaka tana zuzu alamun ana kira ammh bana cikin yanayin da zan iya duba wayar ma.
Bamu jima ba sai gamu a kofar gidan Goggo,muna isowa na bude mota na fito karamar pos din dake hannuna na Laluba dubu hudu ne yan Dubu Dubu Sabbi na cire na bama Direba ya karba yana godiya Yaran da basa rabo da kofar gidan Goggo,su suka yayyameni ana fara sauke kayan suka rika jida suna shiga cikin gidan Goggo da shi,Nima bayansu nabi cikin wani yanayi har ga Allah ko gani bana yi jiri ke dibana ga ciwon kai mai Tsanani,ina ji muryan Direban na fadin"Allah ya kawo miki mafita"
Ko amsa shi ban yi ba. na shige gidan goggo,a tsakar gida na isketa tana tambayan yara kayan waye ?ina Sawo kaina Tsakar gidan nace"Nawa ne Goggo"
Muryata a shake,na bata amsa baki sake Goggo ke kallona cikin mamakin ganina bata rufe baki ba. taga ana shigowa da freezer,suna kiciniyar inda za'a sauke Goggo ta nuna musu dakin da ta ke sauke karikitaanta suka shiga da su,sallaman ma Goggo ce ta sallame su ni ko ban iya tsayawa a ko'ina ba sai akan Daya daga cikin kujerun falon Goggo na zauna Dabas ina Numfarfashi kamar wacce tayi gudun Tsere,Goggo ta shigo ta tsaya a saman kaina,Hijabin jikina na cire kan kujeran ma sai naji sama sama nake jin kaina. kasa na koma na zauna,ina Kokarin tare kukan dake neman tasomin.
Cikin mamaki da al'ajabi Goggo tace"Fa'iza daga ina?kun fasa tafiyar ne..?yanzu nan su Nasara suka fita suna shirin tafiya tace kin kira kince su Dakata ga kinan zuwa lafiya.?ina yaran ina shi Megidan naki..?
A jere Goggo ta rika jefomin Tambayoyin,ammh na kasa amsamata ko d'aya daga ciki sai na koma na Dafe kaina ina kokarin daidaita yanayina,Goggo bata hakura ba ta cigaba da kallona tana Nazari na sai ta Fahimci na fita daga hayyacina Idanuwana sun kumbura alamun nasha kuka sai ta Firgita cikin jimami da Fargaba tace"Fa'iza ki yi min mgana mana naganki da uban kaya sannan ke kadai kika zo ina su Amir..?ina shi Ishaq din..?
Ambaton su Amir yasa na fashe da wani marayan kuka zargin Goggo sai ya tabbata ta ji jikinta yayi sanyi sai ta koma ta Durkushe a gefe na tana fadin"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un Fa'iza ba dai Ishaq din ne ya sake ki ba?
Ban bata amsa ba na cigaba da Dirzan kukana Goggo na tayani da Sallalami fadi take"Haka Allah ya kaddara. Fa'iza ki yi hakuri"
Ta kasa zama ma mikewa tayi tana fita tana Dawowa cikin wani yanayin da na kasa Fassarawa,sai da nayi kukana ya isheni sannan na lallashi kaina Lokacin Goggo ta kawo min Ruwa da abinci tana fadin"Wannan wata irin kaddara ne..?bai rabu dake tun kuna samun matsala ba sai yanzu da kowa ke ganin abubuwa sun daidaita?
Sai da na sha ruwa naji na samu natsuwa sannan na Dago jajayen Idanuwana na sauke a kan Goggo ganin yadda ta rud'e ne hankalinta a tashe yasa na bude baki nace"Ba sakina ya yi ba Goggo.."
Sai da naji ajiyar ran Goggo na samun Salama. cikin mganarta tace"Har na samu salama Fa'iza to me ya faru.?na ganki da uban kaya ko kun fasa tafiya Lagos din ne"
Kai tsaye nace"Aa ni ce dai na fasa binsu chan ne,ammh su inaga suna Hanya ma Goggo"
Cikin mamaki Goggo tace"To saboda mene Fa'iza..?
Kaina na kasa ina kokarin Danne abunda ya tasomin nace"Na GAMA AURAN ne Goggo."
Cikin Razana Goggo tace"Wata irin mgana ce wannan Fa'iza.?Daman ana gama ibadar Ubangiji ne ko a gaji da ita..?
Ina tsiyayan hawaye na dago ina fadin"Wlh Goggo na gama aure tsakanina da Ishaq. Bama shi ba na gama auren ko wani Namiji a duniyan nan,ba komai acikin aure sai kaskanci da zalunci da Tozarci Goggo"
Na karishe fad'a cikin Kuka mai Tsanani,sai Goggo ta saka salati Tana fadin"Haba Fa'iza wannan wata irin mgana ne..?aure fa Ibada ne mai yinsa bai taba Tabewa ba. Me akayi miki Fa'iza?meyasa tun a baya baki yi wannan Borin ba sai yanzu da naga komai ya daidaita har ita Saudatun kuna zaune lafiya da ita.?shi kan shi Ishaq din ya sauko Fa'iza sannan Meyasa kika yanke hukunci batare da kin tuna da ya'yanki ba.?wazai rike miki su Fa'iza?
Cikin Kuka da karfi nace"Zainab da Mama zasu rike su Goggo. bazasu mutu ba..chan ne dolen su tunda gidan Ubansu ne,ni kuma ba gidanmu ba ne nan ne Dole na Goggo"
Goggo ta tsorata da yanayina da bata taba gani ba cikin wata irin murya tace"Fa'iza bautar auran kika gaji da shi?Saki kika nema?
Kin san yadda al'arshin Allah ke girgiza saboda Sakin aure..?
Nima cikin kuka na bata amsa da cewa"To Goggo ibadan aure ai ba Bauta mutum ba ne..?sannan ba laifi ba ne in nace na gaji da auran ina da Dalili na Goggo"
Sai Goggo ta fara fad'a tana fadin"Dalilin menene..?wani Dalilin ne zai sa ki bar auran ki da ya'yanki Fa'iza abunda baki yi ba a baya ba sai yanzu..?anya kin yi tunani kuwa..?
Mikewa nayi ina ganin jiri na Dafe kujera ina fadin"Bazan fadi Dalilin ba Goggo ,ammh shi ya sani in ya fada muku zan kara muku bayani in kuma bai fada muku ba shikenan domin alkwari ne nayi masa baza'a ji wannan mganar a bakina ba"
Hijabina na kwasa da Karamar jakana na wuce dakin Goggo ina jinta tana fadin"Fa'iza zo ki bi mijinki..Bazan zama goggon banza ba"
Da karfi nace"Wlh tallahi ba inda zani Goggo. In kuma kika matsamin na fita Daga gidan nan to ba lalle ki kara ganina ba"
Jin abunda nace ne yasa Goggo ta saka Salati tana fadin"Ai shikenan tunda kin raina ni kina da uba,Bari Isa ko Salisu su shigo zan sa su kirasa,shi in yazo zaki fadamai Dalili sannan in yace ki koma gidan mijinki shi bazaki yi mai gaddama ba"
Ina jin haka na shige Dakin Goggo na Rufo kofar na fada kan gadonta na saki kuka,tun ina yi a Hankali har na fara yi da karfi,da dukkan zuciyata ya'yana nake tunawa ina tuna tun Tsawon Rayuwata in ba makaranta sukaje ba bamu taba awa daya bama tare da juna ba,sai yau da nake jin Nisa zasu yi dani na har abada,ina kwance ina tuna zama da nasu da yanayin yadda rayuwata da yarana ta kasance wlh sune duniyata ni ce tasu duniyar ina Tausayinsu na yadda Rayuwarsu zata kasance a bakon waje batare da ni ba,basu saba da kowa ba sai ni,nima ban saba da kowa ba,sai ya'yana bansan nima ta yadda Rayuwata zata fara tafiya daidai ba batare da su ba.
Tuna hakan yasa nake ta rafzan kuka,kukan da ya rikitani yasa naji zazzabi na rufeni,daman na shigo da jiri da ciwon kaina sai kuma abun ya yi min yawa,ina jin hayaniyar su Goggo a falo da mganganun mata da maza ban iya motsi ba,har ta kai ga suna ta buga kofar dakin Goggo Lokaci daya da kiran sunana ba amsa ba.
Naji muryan Yaya Mariya,naji na Hafsah da ta Yaya Isa ammh na kasa budewa saboda bazan karbi kalmar hakuri ba wannan karon sannan bazan yi mgana ba kuma bazan iya gaddama da su ba. gwara nayi nesa da Tambayoyinsu a wannan Lokacin,ni abu daya nake son ji ko gani ya',yana ina so naji Halin da suke ciki,ina cikin Dakin nan har Dare sai da aka kira mangariba na iya jan kafana na shiga Toilet nayi alwala na fito na rama Salollin dake kaina duka a zaune nayi su,wayata na ciro daga cikin pos dina,da naji ana kira Anty Fadila ce ina gani har ta gama ringing ban dauka ba kawai na ijiye wayar a gabana ana cigaba da Kira.
Ba wanda bai kirani ba acikin su har da Yaya Abdul'Ahad,Abba ne ya kirani a karshe sai naji kuka ya kara kwace min Cikin kukan nake fadin"Kayi hakuri Abba..Kayi hakuri"
Domin bansan me zan ce mai ba in na Daga wayarsa ina da Tabbacin Tuni Labari ya kai musu shiyasa suke ta kirana ni kuma bani da amsar Tambobyinsu a lokacinm
Kaina na Hada da gwiwa na cigaba da Kuka,gabadaya duniyar tamun zafin da bata tabamin ba. Lokaci daya rayuwata ta baya na sake dawowamin kamar yanzu abun ke faruwa, an yi an gama. na gama Daukan Tozarcin da na Dauka baya ina Bukatar Rayuwar yanci nima.
A chan Falo kowa Goggo ta kasa zama gabadaya Hankalinta a tashe yake,Har da su Yaya Isa ita kanta Yaya mariya ta kasa komawa gidanta Tunda Hafsah tazo ta gayamata Fa'iza tazo ammh ta rufe kanta adaki tana ta kuka.
Goggo ita ta saka Yaya isa ya kira mata Abba tamai bayani yace yana warri baya gari ammh zai kirani a waya yaji meke faruwa?
Ammh kafin nan bari ya kira Ishaq din yaji to yace yayi ta kiransa bai same shi ba,Zuwa yammah kuma Anty Fadila ta kira Abba tace Mijin Fa'iza da yaranta sun sauka a lagos ban da ita shi yake mata bayanin da Goggo tayi masa shine fa suke ta kiran wayoyina ban Dauka ba.
Jin har dare ban Bude kofa ba Abba yace gobe zai biyo jirgi zuwa Kano Daganan zai dauko tashar Mota zuwa Karofi domin yaji abunda ke faruwa.
Ba bugun kofar da basu yi ba tare da magiyan na bude kofa ammh ban bude ba,Zazzabi ne mai zafi ya rufeni da bazan iya tashi ba,ga yunwa ga rashin kwnciyar Hankali ga kuma karin kuka,su suka taimaka wajen kwantar dani cikin Halin ciwo,da har asuba ina ji ana kiran salla na kasa tashi ina kokarin mikewa wani jiri da ya Debeni Allah ne ya taimakeni na koma na zube bisa gado da a Kasa ne da Tuni zence ya sha bambam.
Ina kwance ina kuka ina tuna da su Amir yau mun kwana a mabambamta waje,abunda bai taba Faruwa ba sai zuwa na kano bikin Halisa sai kuma yau,Duniyar ma a sama sama nake jinta,tun ina iya jin abunda ke faruwa kad'an kadan daga Falon Goggo har duniyar ta Daukemin gabadaya.
Na gama Sadakarwa mutuwa zan yi, ni kadai acikin daki ba wanda ya sani.
****
Abba tun goma ya baro warri ta jirgi ya sauka a kano Direban gidan su Ammi yazo ya Daukesa bai zarto da shi ko'ina ba sai karofi ba kuma wai don ya gama abunda ya kaisa ba ne matsalan data kunno kai ne yasa ya yanke komai ya taho.
Yau da safe Ishaq ya kirasa bayan sun gaisa yadda yaji muryansa yasan shima a rikice yake tun kafin ya yi mai mganar Fa'iza ya tsinke da Fadin"Abba Fa'iza zata barni. Ta ki yarda ta biyoni Lagos Abba. Kayi ma girman Allah kada ka bari Fa'iza ta bar gidana"
Daga jin yadda yake mgana ba cikin natsuwa ba ne Abba nata ya saurareshi yayi mgana ya kasa sai ma ya cigaba da fad'in"Abba jiya har mun shirya Fa'iza tace bazata bimu ba.Yara suna ta kuka Abba,Na kasa lallashin su,Mama da su Anty Binta ma sun kasa lallashinsu Abba wlh tallahi ba domin ajiyan sun kirani suna Bukatar ganina affice karfe bakwai na Safen yau bacda karofi zamu bi Fa'iza Abba,bazan iya tafiya Lagos batare da Fa'iza ba,Abba su Amir sun ki yarda su kwana wajena sai Anty Fadila ne ta koma da su gidanta suka kwana har kuma da Safen nan mun yi mgana tace Amir da Anum sun bar kuka ammh Ahmad kwana yayi yana kuka yana kiran sunan Umma. Abba ya Fa'iza take so nayi..?zata kasheni ni ne kwana na bai kare ba.? ka ganni nan ina Office ne ammh wlh Abba bani da Natsuwa kamar zararre nake ji na,ni dai ka taimakamin in na gama abunda nake yi zan sake biyo jirgi Abba ni dai Fa'iza tayi hakuri ta janye kudurinta"
A yadda yake mgana ba tsayawa yasa Tausayinsa ya kama Abba shi kanshi yayi mamakin abunda akace daga bangaran Fa'iza yarinyar da yake mata so na Dabam duk cikin su Mariya,tana da sanyin Hali ga Hankali da natsuwa sai dai shi sha'anin aure baka katsalandan in ka shiga ka zakewa sai kaji kunya in sulhu ne to zai nemi a zauna a samu Fahimtar juna ko don zuru'ar dake tsakani.
Dakyar ya Lallashi Ishaq da cewa ga shi yana Hanyar Karofin,kuma ya hanasa tahowa, da alkwarin da kansa zai kawo masa Fa'iza har Lagos da haka suka yi sallama yana cigaba da masa a magiya shuru yayi ya na tunanin a mganganunsa kamar shi ne bai da gaakiya domin yana ta nanata a bama Fa'iza Hakuri ta duba ya'yansu kada tace zata barshi.
Sannan kuma yana auna mganganun Ammi a jiya da Daddare da suka yi mgana shi dai bai kirasu ya fad'a musu komai ba,sai dai yana tunanin a wajen su Nana Fadila taji abunda ke faruwa,shi yace kada ta sanar da su Inno tukunah yaje ya gani ko zai iya Daidaita lamarin Kalaman Ammi alokacin sun saka ya fara nazari.
Ce mai tayi"Baban Nanah tsakani ga Allah kada ku zake kan sai Fa'iza ta koma Allah kad'ai yasan bakincikin da yarinyar ta Hadiya.
Nifa tun ganina na farko da ita na Fahimci tana da Damuwa,kuma duk sauran sun fita kama mai kyau da sakin jiki cikin mutane Nana Fatima ta fadamin tana da abokiyar zama tana chan Abujan"
Abba ya fadamata diyar abokin karatunsa ne Dr.Lawal bako abokiyar zaman Ita Fa'izan.
Ammi ta cigaba da fadin"Ku saurareta ta fad'a muku dalilinta kuyi ma kowani bangare adalci kada kuce zaku Tursasata"
Shi dai bai yi wani mgana ba,saboda bai je ya gani ba ammh mganganun Ishaq yasa ya fara auna maganganun Ammi sannan yana jin Tausayin yaran shima ai sun yi mgana da Fadilan shi ya ce ta dauke yaran zuwa gidanta har komai ya Daidaita. har ya isa Karofi yana fatan komai ya Daidaita
Sai dai me? koda yaje su Goggo na Cikin Tashin hankalin tun jiya ban bude kofa ba sannan ana ta Bugamin naki Budewa suna Tunanin ba Lafiya.
Cikin Tashin Hankali Abba yace"Tun jiyan data shiga bata fito ba..?
Goggo na sharan kwallah tace"Tun jiyan nan Alhaji. Ni na fara jin tsoron ko lafiya yanzu da ka ganmu Tsaye mariya nace ta kiramin Isa ya kira mai balle kofa yazo balle kofar nan muga Halin da take ciki,daman tun jiya da tazo take ta faman koke koke"
Abba ya fito da waya yana fadin"Bazai yu yu mai rai acikin Daki tun jiya ba'asan halin da ta ke ciki ba, akwai ciwo akwai yunwa dole a san yadda za'ayi a balle kofar nan bari na Kira Isan da kaina"
Ya daga waya yana kokarin daidaita yanayinsa,Yaya mariya da Hafsah sun yi tsuru tsuru Yaya Asiya sai kiran mariya take yi domin tunda suka fada mata itama Hankalinta ke matukar tashe.
Abba ya samu Yaya isa ya fad'amai Halin da ake ciki yace ga shi nan zuwa da mai balle kofar suna zaune Jugum Jugum sai ga su sun shigo.
Hankalin tashe gabada'ya a kabi bayansu mai balle kofa na aikinsa su Abba na tsaye cikin Zullumi.
Kofar tayi gaddama Saboda Sakata na sakata ta ciki Sai da aka warwareta sannan akayi iya budeta,chan bakin gado suka ganni ina Numfashi sama sama daga kirjina baya sauka a cikina iyakarsa nan yana sama da kasa Goggo da su Yaya Mariya suka yi kaina suna kiran sunana ina ko jin su bana yi lokacin ina kokuwa da numfashina ne ga jikina ya Dauki zafi kamar wuta.
Goggo ta tattaba jikina tana Fadin"Jikinta zafi."
Abba a rud'e yana daga kofaar Dakin yace"Muje asibiti..Isa daukota muje Asibiti"
Yana fada yayi waje a binsa Yaya isa ya Fada dakin cak ya Daukeni su Goggo suka biyo bayansa har waje suna fitowa sai ga su Anty Nasara Goggo ba takalmi ba Hijabi sai da Yaya mariya ta bata na jikinta tare da ita da Yaya Isa sai Abba suka Daukeni zuwa asibiti a halin Rayuwa da mutuwa.
Wani asibitin kudi dake cikin garin Dutsenmah suka kaini nan da nan suka karbeni suka shigar dani Likitoci suka Rufo kaina Saboda Numfashina Dake neman kwacewa sai da suka sakamin Oxygen,sannan suka min allurai da Drip,numfashina ya fara Daidaita Likitan dake on Duty haka ya rika yin fad'a yana fadin ina da Hawan jini meyasa ake tadamin Hankali..?ga jinina nan ya haye sama ina neman mutuwa Abba ya shaki mamaki yana kallon Goggo Lokaci daya yana Fadin"Fa'izar ke da hawan jini..?
Goggo ta dagamai kai tana fadin"Tana da shi shekarun wajen hudu muma bamu sani ba,domin bata gayama kowa ba ta mgangun da aka bata a asibiti yara suka gani suka gane"
Mamaki ya kara kama Abba duk da Hawan jini ya zama ruwan Dare a wannan rayuwar,ammh Fa'iza tayi kankanta a shekarunta ko shi da ya Haura Hamsin wlh ba shi da wannan mugun ciwon.
Gefe ya koma kawai yana kara nazarin wasu abubuwan,sai dai yayi mgana da likitan yace a kula dani komai zai iya kashewa saboda na samu lafiya,suna asibitin nan har Yammah sai sallah ke fitar da su Abba ko ruwa bai isa sha ba sai dai yana amsa wayoyin dake shigomai ciki har da na Ishaq Abba na Daukan wayansa yace"Kayi hakuri Ishaq mu bi komai a sannu. Yanzu haka nazo na iske Fa'iza ba yadda take gata ma a asibiti likitoci na kokarin ceto numfashinta"
Shima cikin karaya yace"Wlh nima Abba in naje asibiti na kwanta nima zasu kwantar dani. Nima bani da lafiya bani kuma da natsuwa"
Abba ya rintse ido kafin ya bude cikin Dattakonsa yace"To kai ma ka natsu kasan satin ka na farko kenan da Fara aiki plz ka tsaya kayi abunda ya kamata. Fa'iza na bukatar addu'anka, in ta ji sauki sai a zauna ayi sulhu a Fahimci juna insha Allahu komai zai Daidaita"
Da haka jikinsa yayi sanyi yana fadin"Allah ya bata lafiya Abba meke damunta..?
Kai Tsaye Abba yace"Hawan jininta ne Likita sukace ya tashi,Damuwa ne yasa jinin ya Daga sama sosai sannan ga maleria"
Cikin mamaki Ishaq yace"Hawan jini Abba?Fa'iza ke da Hawan jini?
Cikin mamaki Abba yace"Eh baka sani ba?Goggon su tace an yi shekaru fa"
Sai ya kasa mgana kunya ya kamasa,To yaushe ya san Laluran Fa'iza ballatana yasan Halin data ke ciki Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un bazai raba dayan biyu ba,Dalilinsa Fa'iza ta kamu da wannan cutar nauyi da yadda ya fara fallasa kansa yasa bai kara ce ma Abba komai ba suka yi sallama Ya bar Abba da kara auna Tambayarsa kan mizani girgiza kai yayi a fili ya furta"Allah yasa ba abunda nake zargi ba ne. Domin in zargina ya tabbata bazan ragama kowa a kan wanda ya nemi kashemin y'a ba"
Abba ya fada yana kokarin daidaita kansa shi mutum ne mai zafi baya son ka wulakantasa ko kaci zarafinsa alhalin shi bai ci naka zarafin ba,Sannan ya'yansa ba abun wulakantarwa ba ne,shiyasa yake tsaya musu tsayin daka ga duk wanda ya nemi tozartasu ta kowacce siga.
Sai Dare na Farfado kuma Alhamdulillah na farfado cikin Hankalina sai dai tun da naga Abba sai kuka,alluran barci akayi min na koma barci kamar mattaciya sannan har da rashin samun hutu da bana yi sukace. shiyasa sukace zasu rikeni na Tsawon kwanaki anan.
Sai da su Anty Nasara da su Yaya Mariya sukazo Yaya isa ya tafi da Abba gida yaje ya huta yaci abinci,Goggo kuma bata koma gida ba su Hafsatu suka zo mata da abubuwan da zata bukata,nan ta kwana tare dani kafin kuma wayewar gari ciwo na ya shiga kunne kowa ana ta kiran wayata bata hannuna tana wajen Yaya mariya,da Safe na tashi Lafiya sai dai idanuwana sun yi luhu luhu sai ciwon kai da bai sakeni ba,ammh bana ma kowa mgana in an gaisheni sai na amsa dakai.
Zuwan Abba ya rikitani yana cemin"Fa'i ya jikin naki.?
Sai kawai na Fashe mai da kuka sai ya zauna gefen gadon yana Lallashina fadi yake yi"Kinga bar wannan kukan kin ji ko..?ba mai kara takura miki Fa'iza har sai kin samu lafiya"
Jin haka yasa na tsaigaita da kukana Daman Fargabata kada Abba ya ce na koma ma Ishaq abu na farko da zai Umarceni naji na kasa cika umarninsa ammh jin haka yasa sai naji nauyin kirjina ya kwanta,Kaina kawai na Dafe nayi kasa da kaina ina ji Abba nata waya ciki har da Nana Fadila na kasa kunnena sai naji ana mganar su Amir da sauri na Dago ina kallon Abba tun kafin in yi mgana yace"In ta kara jin sauki zuwa yammah sai a had'ata da yaran su ji muryanta ko zasu samu natsuwa"
Sai na kurama Abba ido har ya gama wayar ya kariso gareni yana kallon yadda na rame da bai taba Lura ba sai yau cikin son kwantar min da Hankali yace"Kada ki damu su Amir na wajen Nana Fadila tace suna ta kiran sunanki ne, sai nace ta bari in kin kara jin sauki zaki yi mgana da su ko..?
Kai tsaye na girgizama Abba kai karo na farko da nayi mgana nace"Ku kyalesu Abba. gwara su saba da rashina"
Na karishe fada muryata a shake,Gabadaya sai suka bi ni da kallo ganin haka yasa na koma na kwanta na kauda kai ina tsiyayan Hawaye ni kadai nasan yadda nake azbatuwa da rashin su Amir ammh bani da mafita kila tamu kaddaran kenan dagani har su.
Wasa wasa sai da na Shafe kwana Biyar kwance a gadon asibiti,ranar da na kwana Biyu Ammi ta zo Dubani ita Nana khadija da Yaya Abdul'Ahad da Raliya,aranar kuma Abba ya koma tare da su da Hafsah da zata fara karatunta a Kasu Kaduna State University,Abba ya tafi da Dokar kada wanda ya karamin wata mgana a kyaleni sai nasamu lafiya tunda likita yace jinina ya yi sama a guji tadomin da abunda zai rika tadamin Hankali. da wannan Abba yace a rabu dani mganar Ishaq ko ta yarana kada a sake Daukomin ita,a kyaleni sanda na samu Cikakkiyar Lafiya sai a zauna a samu mafita shi kuma Ishaq din Abba ya masa mgana da kakkausan murya akan kada ya baro aikinsa ya taho in yana so ya shiga mganar in kuma baya so shikenan ya taho Dole ya Hakura ya zauna su Anty Binta kwana Hudu sukayi suka biyo mota ita da Anty Hure,suka bar Mama agida ita kad'ai tunda yaran sunki zama kamar ma basu san su ba har Shi kanshi Baban ya kasa Lallashin su,Anty Binta ita kanta tasan rabuwar Fa'iza da Ishaq wani abu ne wanda kowa ba zai so faruwansa ba,Da ka gansa kasan yana cikin damuwa duk ya fita Hayyacinsa,Abinci siya yake yi Mama bazata iya wani girki ba. Anty Binta a ranta ta saka cewa in suka koma zata je ta samu Fa'iza ta mata mgana ta roketa ko zata koma ko saboda yaran dake tsakanin su.
Zainab kuma daman tace sai ta gama shirinta,Ishaq din tun a washegarin tahowarsu Lagos ya fada mata Halin da ake ciki itama hankalinta ya tashi tace zata kirani to kuma tun ranar take kirana bana Dauka bata san ina Gadon asibiti ba,sai daga baya Yaya Mariya ta Dauka ta fadamata ga Halin da nake ciki, sai jikinta ya karayin sanyi itama ta kuduri niyar cewa kafin ta wuce Lagos zata zo ta sameni mu yi mgana domin har ga Allah kamar yadda na bata gummuwa a auranta da Honey itama bazata zo aurammu ya samu matsala ba.
Tunda ya fad'amata cikin damuwa cewa Saki nake nema batayi mamaki ba,tunda ai zuwanta tasan wasu abubuwan dake faruwa tsakani ga Allah abunda Honey da su Mama suka aikata,ma Maman Amir bai kyautu ba.
*Janafty*
*24/07/2023*
[7/25, 8:13 AM] U.M Collection ZMFR CM: *KNKB3002*
Kimanin kwanaki takwas kenan da sallamoni daga asibiti bayan na shafe kwana bakwai sati d'aya kenan karkashin kulaawar likitoci.
Na dawo gida da Tud'in mganguna tare da Dokokin likita kan na kiyaye shiga Damuwa da tsananta ma kaina Dogon Tunani,duk jinsu kawai nake yi ana iya raba bawa da Tunani ne..?ballata ni da tunani ya zame min dole ba ma sai na gayyace shi ba.
Tun ina asibiti ina amsa wayoyin yan'uwa masu min sannu sama sama,da kuma muka dawo gida na karajin sauki Tiryan tiryan nake mgana da mutane,sai dai kamar yadda Abba yayi gargad'i ba wanda ya karamin mganar Ishaq dasu Amir duk da suna raina nima nayi kokarin yakice tunanin acikin raina,Kud'in da aka kashe a asibiti na Dawainiyata duk Abba ya dauki nauyin komai da komai bayan na koma gida kuma Goggo ta mike tsaye ta cigaba da kula dani kamar yadda ta saba itama kamar yadda Abba yace bata kara tada wata mganar ba.
Mun yi waya da Anty Fadila ta gaisheni bata min mganar komai ba nima ban mata ba,Haka zalika Badariya ma ta kirani tamin sannu itama a bakinta nake jin jamal sun gama Jarabawa zasu yi graduation dinsu sannan ya taho gida,to shima a daran ranar da ta fadamin haka ya kirani ya gaisheni da farko na zata ba su san ina Karofi ba sai da naji yana tambayata ya su Goggo? sannan nasan sun ji Labari ammh yadda basu nuna min komai ba nima ban nuna musu ba.
Abun mamaki hatta da Mama sai da ta kirani kuma ina da tabbacin shi gogan ya fad'a musu banda Lafiya ta,ni banganeta da farko ba saboda ban da lambarta,sai da tamin bayani sannan na gane bayan mun gaisa tamin sannu,sai naji tana ta kame kamen mgana ammh ta kasa fad:a sai kawai ta bige da fadin"Kiyi hakuri Fa'iza ki yi hakuri don Allah"
Toh kawai nace mata saboda na kashe mganar,Kuma muna mgana da mama yau gobe Ishaq ya dosa kirana a waya na ki dauka Saboda so nake na yanke alaqa da shi a yanzu tukunnah ko zam samu natsuwa inaga shine sai ya kira Abba ya fad'amai ya kirani ya gaisheni ban amsa ba,Damn kuma Abba a rana mukan yi waya sau uku sau hud'u shi da Ammi da sauran yan'uwana Hatta Hajiyar su raliya ta kirani ta gaisheni ita da sauran yayyin su Raliya tace a bakin Raliya taji bani da lafiya,Abba ne ya yi fadan meyasa ban Dauki wayar Ishaq ba..?
Sai na kasa mgana cikin Umarni Abba yace in ya kira na dauka mu gaisa Dalilin da yasa daya sake kira na Dauka muka gaisa kenan bazan taba iyama Abba gardama ba daman ba Halina ba ne.
Mun gaisa kamar bakin juna ya gaisheni na amsa a Tunkushe,kamar bana so,ina jinsa ya dade yana Auna mganganunsa kafin ya fara fadin"Fa"iza kin gani ko.?Dukkanmu bamu da natsuwa yaranmu ma basu da natsuwa basa tare dani suna wajen Fadila,ki dawo Fa'iza mu rumgumi ya'yan mu kamar yadda muka saba"
Ina jinsa yana kuma kai aya na katse kiran ina,jin wani takaici ya kara kumeni.
na kara tabbatarma kaina Ishaq bazai taba sona ba, zai yi kokarin maidani ne Saboda inganta gidansa da wani Muradinsa,Zainab ai mun yi mgana da ita ammh itama ban bata damar min wata mgana ba,Ranar ina tare da baki Yaya Asiya da yan gidan su Ammi Mota guda suka zo dubani sai nace mata ta bari zan kirata nayi baki Daganan kuma na manta ban nemeta ba.
Nana Fatima duk ta waya muke mgana da su ammh ta min alkawarin zata zo har karofi ta Dubani,ina Dakin Goggo bana aikin komai daga ci sai shan mgani sai kwanciya,na rame sosai duk nayi zuru zuru in na kwanta ban da tunanin su Amir ba abunda nake yi ina sharan kwallah Ko Goggo ta ganni ina kuka ci kanki bata cemin Ita da Yaya Mariya ke Dawainiya dani tunda koda yaushe tana gidan,haka ma su Anty Nasara Suma gidan suke yini da matan su Yaya isa wani Lokacin sai in Dare yayi ne,Mallam mijin Goggo ya tarkata kowacce zuwa gidan mijinta,Ni daman ina Daki daidai da Falon Goggo bana lekewa.
Na maida kaina wata Shuru shurun karfi da yaji lura da yanayina yasa suke kyaleni kawai da kuma dokar Abba.
Kabarin komawata Karofi ya shiga kunnen dangi da Dadama,har Hajiyar Dala ita kuma daman iyalan Anty Binta zasu fad'a mata tunda ga ma Halisa a kusa da su,bata zo ba sai dai ta kira Goggo ni ban ma sani ba sai da Yaya mariya ta shigo dubani Goggo na dakin tana bani mgani suke mganar naji ashe bayan ta kira Goggo sun gaisa sai ce mata tayi"Aisha yanzu da girmanki da komai zaki yarda yarinyar nan Fa'iza ta ce zata kashe auranta ta zauna a gidan ki..?
To in ta kashe auran uban wa zai rike mata ya'yan..?ya kamata fa kuyi Tunani shima dan'uwan mahaifiyar nasu naji ance mganar na hannunsa bai ce komai ba. gwara dai ku maida ta bata da inda yafi nan Ishaq ne Rufin asirinta,kuma ya rufa mata tun a baya bama yanzu ba"
Inajin sun manta ina Dakin ne sai da sukaji nace"In har Ishaq ne Rufin asirina, to na yarda na rabu da shi. In yaso sai asirina ya fallasu a duniya gabad'aya"
Na fad'a ina kokarin maida hawayen da suka cikomin ido ko don ganin Aurena da Ishaq alfarma ne ya zama Dole na nuna musu Allah ne kadai ya isa ya yi ma bayinsa alfarma ba Mutum ba,Goggo da yaya mariya suka kalli juna ganin haka ma yasa na tashi na shige Tiolet na rufe na fashe da kuka,Ina jin su Goggo na mgana a Cikin Dakin ban jin dai me suke fadi daga karshe suka fice sai da nayi kuka na ya isheni sannan na wanke fuskata na Fito ina kara ma kaina karfin gwiwa ba kaina Farau mutuwar aure ba, Sannan ba a kaina aka fara zama zawarci ba kuma ba kaina za'a kareta ba,sai dai nayi alkwarin zawarcina ba irin na kowa ba ne.
ban rabu da Ishaq Saboda na koma makaranta domin na samu Ilimin da yake min gori ba a'a na yanke rabuwa da shi ne,saboda baya sona sannan yana zama dani ne Saboda Kalaman Baba da kuma alfarma. tunda ya auri zabinsa sannan ya Jingine aurena da shi addini ya bani Damar iyayena ko shari'a ta shiga ciki ta raba auranmu.
Ranar kamar an yi min fami Yini nayi ina kuka,ni ko sai na nuna ma masu Tunanin Ishaq rufin asiri na ne da cewa ba shi ya Rufamin asiri ba. Allah ne sannan shi ke rufama bayinsa asirin su na Duniya har da na Lahira. naji kwata kwata ko ina da burin komawa Saboda ya'yana na cire wannan Tunanin ina da yakinin tunda ga Zainab ga Anty Fadila yarana baza su yi maraici a Lagos ba.
*****
Ina da Kwana ashirin da Biyu da jinya a asibiti ranar wata asabar Nana Fatima ta Diro,bata zo da yaram ba. daga ita sai Direba tace kuma zata kwana min Daya sannan ta koma,tazo min da katan katan din lemuka da kayan karin jini,sai pepe Chicken da yawan shi,gefe daya ga Yam ball,sai Faten wake da yaji hanta da allayahu,Naji dadin zuwanta sosai daman kuma ni na fada mata bakina bayamin dad'i sosai ba kasafai nake son cin abinci ba,kuma naci Faten waken sosai ya kuma saka bakina yayi dadi.
Mun kule a daki muna ta Hira na saki jiki da ita saboda Nana Fatima ta Dabam ce gaskiya ina kaunarta don Alah kamar yadda take kaunata,Ba ta sako min mganar Ishaq ba kwata kwata. sai dai tana ja na da Labaran da suka saka na saki jiki muna ta Hira kowa yazo dubani Ranar sai yayi mganar sakin jikina sai an ga Nana Fatima sai ace Lalle jinina ya hadu da ita.
Mun tsinke da hira ko kiran wayata ban ji ba,muna ta hiran ginin Abba da aka gama komai Fenti kadai ya rage Nana fatima ke cemin"Kila har da Inno zata dawo nan"
Ni kuma sai nace mata"Anya..?Abba ban ji yana mganar ba"
Sai tace min"To ai naga Inno ta saba da Baba Ati ne dakyar ta yarda Abba ya Dauketa zuwa nan sai dai su dawo tare"Kai tsaye nace"Ita kuma Ammi ai bazata ji dadi ba in dai Inno ta dawo nan da zama"
Muna cikin Hiran ne Abba ya kira wayar Nana Fatima bayan ta Dauka sun gaisa tace gata ta ga Fa'inzan sa Cikin Dariya yace"Au madallah ashe ke Fa'iza ta samu yau ba'a ji kiran Abba ba"Dayake ta saka ta a amsa kuwwa ina ji.
Cikin Dariya na karbi wayar ina gaisheshi ya amsa yana fadin"Fa'in Fatima shikenan yau ina ta kira baki Dauka ba ashe Fati ce tazo ta sha gaban Abba"bakina na rufe da Hannuwana ina yar Dariya nace"Abba wayar na nesa ne ban ji kiran ka ba kayi hakuri"
Da Sauri yace"Bakomai Fa'iza daman naji ya jikin ki ne..?na kuma jiki Lafiya lau ga Nana nan ta wakileni ki kula da shan mganin ki kin ji ko..?
Na gyada mai kai Lokaci daya ina fadin"Toh Abba"
Sallama muka yi gabadaya ya kashe wayarsa bayan yace min zai zo da zaran aiki yayi masa sauki.
Mun cigaba da Hirarmu da Nana Fatima sai taba kashin wuyana take yi tana Fadin"Haba Fa'in mu wad'anan kasusuwan fa..?
Ina Dariya nace"Daman ina da kashin wuya. Bani da kiba tun asalina"
Nana Fatima tace"Har da ta damuwa da kuma yanayin rayuwa Fa'i"
Kai Tsaye nace mata"To bawa ai ba'a rabasa da Tunani ballatana mata ire irena da suka samu nakasu ta bangarori da dama"
Sai a alokacin ta kalleni cikin wani yanayi kafin tace"Fa'iza daman fa zuwana ba na duba ki ba ne. Harda cire miki wannan tunanin a ranki"
Sai nayi dariya ina kokarin mantar da ita mganar nace"Shine kika k'i zuwa da su Jalil.."?
Hararata tayi kafin tayi mgana mukaji Goggo na faman maraba da bakuwa afalo,Muna dakin bamu fito ba Goggo ta lekomu tana fadin"Ke fa kin yi bakuwa. abokiyar zaman ki ce ta zo yanzu"
Ido na zaro kafin nace"Zainab..?
Ban gama rufe baki ba sai gata ta shigo,da cikinta na fara cin karo har ya Fito dayake mayafi ta sanya ta kara Kiba ta zama katuwa,cikin Mirmishinta na yan gayu tace"Ni ce Maman Amir kin yi mamaki ko..?
Ni da Nana Fatima muka kalli juna kafin ni na yunkura na mike naje na Tarbota rumgumeni tayi tana fadin"Sannu Maman Amir kin sha jinya"
Na amsa mata ina kokarin karban karamin akwatin hannunta da jaka na jata gefen gado ta zauna ina fadin"Sannu..ai sannu na wajen ki maman yan uku da nauyin jiki haka kika Dauko hanya..?
Kai Tsaye tace"Ya zama Dole tunda kin Hana Honey sukuni dole nazo nayi masa biko"
Ban ce mata komai ba na fita falo na barsu suna gaisawa da Nana Fatima Ruwa na Dauko mata da lemu na kawo mata,ruwan kawai tasha tace min tana so tayi wanka sai na nuna mata Tiolet ta shiga ni da Nana Fatima sai muka fita falo mu bata waje ta natsa kan kujerun falon Goggo muka yada zango nan Goggo ta same mu ta kallemu tana fadin"Daman kinsan zaki yi bakuwa baki yi mgana ba Fa'iza..?
Cikin girgiza kai nace"Wlh ban sani ba Goggo ni bamu yi mgana da ita ba"
Goggo ta kada kai tana fadin"To me za'a dafa mata..?
Kai tsaye nace"Abunda ya sauwaka Goggo kada ki matsa ma kanki".
Goggo ta wuce tana fadin"Ke dai bari. ai bakon ka Annabin ka Fa'iza"
Sai da ta bar falon Nana Fatima ta kalleni tana fadin"Wannan ita ce abokiyar zaman naki..?
Na gyada mata kai sai kawai itama ta tabemin baki tana fadin"Lalle to me tazo yi..?daga Lagos din take kenan..?
Da sauri nace"A'a ita bata bisa ba..Tace sai ta gama kintsawa inajin bata riga ta tafin ba ne"
Daganan Nana Fatima bata kara mgana ba,sai muka sauya hirar muka Shiga wata mganan muna nan zaune sai ga Anty Nasara tazo sai muka hade muna Hirar gabadaya,Abinci da tazo da shi aka dibar ma zainab Farar shinkafa da miyar allayahu,da Nama taci kadan sai ta kishigida hutawa sai da aka kira mangariba na tada ita tayi sallah muma muka yi.
Sai bayan mun idar muka zauna muna kara gaisawa ina tambayanta yara tace suna gida wahala ce tazo dasu tana fama da kanta.
Na gabatar mata da Nana Fatima sai ta kalleni kafin tace"Ok..nagane Daddy ya bani Labarin Kanin mamanku friend dinsa ne yarsa ce ko..?
Sai na gyada mata kai itama Nana Fatima na gabatar mata da Zainab suka gaisa sama sama na wayayyin yan Boko daganan kowacce ta Dauke kanta.
Ni ce muka cigaba da mgana da ita,ban tambayeta ba tace min"Gobe zan wuce lagos fa Maman Amir"
Cikin murnata nace"Allah sarki..Kin gama shirin naki kenan..?.
Da kai tamin mgana kafin tace"Eh nagama gobe jirgin yammah zan bi zuwa lagos shiyasa da wuri zan bar nan"
Da jinjina kai na bita kafin nace"ammh tare da yaran gabad'aya ko..?
Cikin muskutawa tace"Da Farhan kadai Daddy ya roki Honey ya bar masa Fadil ban san ko ya amince ba tukunnah"
Da kamar bazan yi mgana ba sai nace"Naso da Fadil su Amir zasu ji dadin in kannen su na tare da su"
Sai ta juya ta kalli Nana Fatima taga tana ta latsa wayarta cikin Sauke murya tace"Maman Amir wajen ki nazo..Ina so mu yi mgana ne"
Ta fad'a tana kallona ni kuma kai Tsaye na gyara zama ina fadin"To ina sauraranki"
Sai ta juya tana kallon Nana fatima Fahimtar da nayi na abunda take nufu yasa da sauri nace"Kada ki damu Nana Fatima yar'uwata ce ta jini zaki iya yin mganarki bata da matsala"
Jin abunda nace yasa ta gyara zama tana fadin"Maman Amir sai naji mgana a bakin Honey mara dad'i"
Cikin son basar da zencen nace"Mganar me..?
Bude ido tayi kafin tace"Kin ki binsa Lagos sannan kin ce ya sake ki.
Haba Maman Amir"
Zan yi mgana kenan Nana Fatima ta katseni da fadin"Baiwar Allah kinsan fa tana kan dokar Likita ne ba'a so ana mata mganar da zata tada mata Hankali.
duba da Condition dinta, da zaki yi hakuri da mganar nan sai next time da yafi"
Sai naga Zainab ta mata wani Kallo kafin ma tayi mgana itama sai na tareta da fadin"Nana kyaleta ai na samu sauki"
Cikin tsareni da ido tace"Dokar Abba fa..?Shi yace kada a kara miki mganar mijinki har sai lokacin da yace"
Idanuwana na Lumshe kafin na bude Lokaci daya ina fadin"Fatin mu kyaleta ai mgana ce kadai ko..?
Ganin nace haka yasa ta koma gefe tana cigaba da danna wayarta Zainab kuma sai tayi wani iri ta Lura dai yar'uwata bata yinta kwata kwata.
Kallonta nayi ina fadin"Uhm ina jinki maman fadil"
Da Sauri ta rike hannayena tana Fadin"Nazo ne tattakiya daga Abuja na baki Hakuri maman Amir wlh Honey duk ya susuce ya kasa ma natsuwa kan aikinsa yara kuma kinga sun ki zama tare da shi,Mama ita kadai ce a gida tunda Badariya na kano,Kuma kinsan sun saba dake bai kamata ki yanke hukunci cikin Fushi ba. A madadinsa ina baki Hakuri gobe ki shirya sai mu tafi tare bazan ji Dadin zama agidan nan baki ba Maman Amir"
Ta karishe fada cikin marairaicewa,Sai na yi mirmishin yske kafin nace"Ba ga ki ba maman Fadil. Bani da Haufi kan su Amir zasu samu kulawarki kamar yadda suke samun nawa,mganar kuma ya susuce akan in koma ba gaskiya ba ne. Ke kanki shaida ce farkon zamanki dani kinsan wasu abubuwan kin kuma san Mijinki baya sona kece zabinsa to ki barni nima na sauwake ma kaina mana,da zama fa inda ba'a sonka gwara ka zauna inda ake sonka sau dubu Zainab"
Taran Numfashina tayi tana fadin"Wlh Honey na sonki ni Shaida ce"
Kai tsayen nima nace mata"Aa ban yarda ba,so d'aya ne yana wajen ki. Ke yake so kuma ke ce ki ka yi daidai da Ra'yinsa da Burinsa ni kawai na Haifa masa ya'yavne sannan na zauna na Kula da su,ko a yanzu ya damu ne Saboda haka ba domin ni din yake son zama na da shi ba,duka al'amarin na alfarma ne Maman Fadil kema fa kinsani kina so ki take gaskiya ne ki bi bayan karya"
Na fad'a mata kai tsaye ina kallonta ganin na cije sai ta kara rike hannuwana tana fadin"Don Allah ki yi hakuri nasani abaya ammh a yanzu ai ya sauya ko..?
Cikin jinjina kai nace"Ba kamar yadda kike Tunani ba,ke kad'ai yake so to meyaasa zai zama laifi don na bashi Dama ya zauna da abunda yake so ita kad'ai"
Ajiyar rai ta sauke kafin tace"Naji ni yake so..kema ai yana sonki da bai sonki bazai zauna dake shekarun nan ha har ku yayyafa ba Maman Amir"
Tunamin da yadda aka samu rabon ya'yana yasa Hawaye sun cikamim kwarmin idanuwa na, kai tsaye nace"Bai gayamiki duka rabon su ne ya rantse ba?
Sai ta kasa mgana ni kuma sai Hawaye suka samu Damar gangaromin na kwace hannunawana cikin nata ina fadin"Kinsan akwai ya'yan da ba'a so haifarsu ba,rabo ne kawai in Allah ya rantse yasa suke Fitowa duniya.
Ki yi hakuri Maman Fadil bazan iya komawa ba,ina rokin ki da kiyi hakuri,amanar duka yarana yana Hannunki ne"
Na fada ina share hawayena,Cikin jimani tace"Nima ba zama zan yi ba Maman Amir Daddy na kokarin nema min aiki in na samu aiki zan rika fita wazai zauna da yaran sannan wazai kula da mama..?
Aikin ki ne fa..Kema kinsan bazan iya duka wannan ba"
Ba ni kadai na kalleta da mamaki ba. har da Nana Fatima daman ranta nata baci da mganganun Zainab din,Kalamanta na karshe sun fassara inda ta dosa wato Fa'iza ce yar wahala ana so ta koma ne saboda kula da yara da megidan ita yar boko aiki zata rika fita,ni ko mamakina kad'an ne daman nasan aikina ne kuma don shi ake min bikon na dawo.
Sai kawai nayi wata karamar Dariya kafin nace"Hakanan zaki koya,ammh ni kam ba inda zani"
Itama kai tsaye tace"To in hakane nima na fasa komawar shikenan"
Tafad'a tana bata rai sai na maida abun dariya ina yar dariya nace"Kada ma ki fara. Dolen ki ki bisa chan In kika komawa wazai kula da shi da yaran mu da na baki Amana..?
Sai ta kasa mgana ganin haka yasa na Dafa kafadarta ina fadin"Kiyi hakuri Maman Fadil..Ban zan iya miki wannan alfarman ba,da zan iya da tuni na yi miki.."
Ki bi mijinki a duk inda yake hakki ne akanki ni kuma kada ki damu dani daman a Dofane nake tuntuni"
Duk sai na kashe mata jiki ta kasa mgana cikin wani yanayi tace"Kin dai ki jin mganata Maman Amir a yadda na sanki mai hakuri..?
Sai kawai nayi dariya ban yi mgana ba,Haka ta cigaba da kawo min mganganu ina kauce mata,Sai da aka kira sallar isha'i muka saki mganar muka mike mukayi sallah Nana fatima ficewa tayi ta barni da ita na Lura takaici ya isheta tayi tayi na rantse mata bazan koma ba.
Sai ta kyaleni ammh jikinta yayi sanyi sai fadi take yi daman haka kike Maman Amir ni dai sai dai nayi mata Mirmishi.
Da daddare tea kadai Zainab ta sha tace ya isheta,Nana Fatima bata ci komai ba sai ruwa tace batacin abinci da Daddare,Dakin da nake ciki muka bar ma Zainab sai muka koma Dakin da Hafsah ke zaune a baya da katifa a kasan Dakin a kanta nayi mana Shimfida,Sai da muka yi shirin kwanciya sannan Nana Fatima ta kalleni tana fadin"Ba dai kishiya zaki bar mijinki ba Fa'i?
Kai tsaye nace mata"Eh mana in mijin ya fi son zama da kishiyar ba laifi bane, ne in na bar mata shi"
daman nata ne ita Kad'ai"
Sai ta saki baki tana kallona,ni kuma sai na basar da mganar,itama bata karamin min ba ammh ta tabbatar ma da kanta akwai mtsala a mganganuna ta Fahimci cewa da akwai lauje cikin nadi,da muka tashi da Safe sai kawai tace min"Gaskiya zan gayama Abba. Bazaki bar ma kishiya mijinki ba"
Kai tsaye nace"Tuni na bar mata ma, kune baku sani ba.."
"Bamu sani ba..?
Ta maimaita kai tsaye nace"Eh mana baku sani ba,ammh lokaci zai fada ma kowa komai"
Daganan ban kara mgana ba itama sai ta kauce ma mganar,Zainab ta fara wucewa Tunda Direbanta nan ya kwana,Kafin tafiyarta har Goggo ta tuntuba goggo tace mgana na Hannuna da Hannun Abba sai an zauna,ganin ba sa'a yasa ta tafi da magiyan don Allah na dawo mu zauna tare sai kawai nace mata insha Allahu daga haka muka rabu lafiya bayan na kara jadadda mata amanar su Amir a hannunta.
Tafiyan ta ba jimawa Direban Nana Fatima yazo daukanta itama mun rabu cikin kewa karfe sha biyu da wani abu ta mika Hanya suka barni ni kadai ina Tunanin makomar rayuwata..
Mun yi waya da Nana Fatima da yammah ta isa gida lafiya,Zainab dai sai washegari muka yi mgana ta tabbatar min ta sauka a lagos,sai tamin korafin gida shuru ba yara,dariya kawai nayi ban ce komai ba sai tace in Honey ya dawo zasu je su Daukosu nace Allah yasa,daganan muka yi sallama,hankalina sai naji ya kwanta tunda Zainab ta koma ina mata kyakyawan zato zata kula da su Amir dai dai kulawan ta.
Su Zainab sun tafi da kwana hudu sai ga Anty Binta da Anty mahma tunda nagansu nazata gaisheni suka zo yi sai da Anty Binta tace tana son mgana dani muka kebe. shine take bani Hakuri da bakinta da bakin Mama kan nayi hakuri na janye kudurina na koma Dariya ma ta bani sai dai ban yi mata rashin kunya ba, na bita da toh zan koma,Har da Anty Mahma a bani Hakuri mganar su kuma duk na koma Saboda yara ne a raina nace nima ai bai Darajani Saboda yaran ba.
Bayan Anty Binta ma Badariya ta sauka a Karofi daga kano itama haka ta tasani tana fadin"Haba Anty Fa'iza tun a baya baki nuna haka ba sai yanzu..?ai yanzu kin wuce wannan wajen da naji labari hankalina ya tashi bansan ya zan koma Lagos a gidan nan naga baki nan ba"
Ni dai ban ce mata komai ba sai dai na bita da toh zan yi tunani zan koma kwana Daya tayi ta koma kano tace zata bi mota zuwa Lagos tunda bata da kudin jirgi,ammh sai taje ma Jamal graduation dinsa tukunna.
Bayan sati daya sai tayo min Taron Dangi ta Dauko min harda Jamal suka sake zubewa gabana suna magiya,daman ranar a raunane nake mun yi mgana da Zainab sun dauko su Amir ammh Ahmad da Musty sun ki sakin jiki suna ta rigima su dai Umman su,har kukan nasu ta karamin ta waya naji sai hankalina ya tashi tace Ishaq ma basa yarda da shi ballatana ita har gwara su Amir suna yarda da su,makaranta ma an saka su wacce ya'yan Anty Fadila ke yi ammh Ahmah da Musty ranar da kuka aka kaisu, su dai wajen Ummansu zasu hankalina duk ya tashi ga magiyan su jamal wanda fadi yake yi"Matar yaya ki yi hakuri. Ki godema Allah kin zama giwar mata Mama da kanta tace nazo na baki hakuri ki dawo su Ahmad sun ki zama suna ta rigima"
Sai naji zuciyata ta karye,har suka tafi ban basu amsa ba,da asuba ranar ishaq ya kirani sanda naga kiransa sai da Gabana ya yanke ya fadi kamar bazan dauka ba har ta katse ganin ya sake kira yasa na Dauka ina Dauka naji sa cikin wani yanayi yana fadin"Fa'iza kin kyauta taurin kan ki zai yi silar kashe mana Ahmad gamu nan a asibiti, tun jiya yaron nan ke kakkafewa yana suma saboda ke"
Sai na Rud'e hankalina ya tashi na Fashe da kuka cikin kukan nake fadin"Innalillahi wa'inna ilaihirraju"un"
Salati na ya shigo da Goggo tana tambayan Lafiya sai na gayamata jikina na rawa na mike ina had'a kayana Lokaci daya ina fadin"Goggo Lagos zan tafi..kada Ahmad ya mutu Goggo.."
Sai ta saki baki tana kallona cikin mamaki tace"Lagos ke kad'ai Fa'iza?
Ban ko Saurareta ba na cigaba da Had'a kayana ina kuka ganin bana cikin Hayyacina, yasa ta fita zuwa Dakin mallam ta gayamai Halin da ake ciki kai tsaye ya fiddo wayarsa yana Fadin"Aa bazai yu yu mu barta ta fita cikin wannan Halin ita kad'ai ba, bari na kira baban nata na fad'amai"
Sai goggo ta aminta da mganarsa kai Tsaye ya kira Abba shima ganin kiran safe sai hankalinsa ya tashi.
Ya na jin jawabin abunda ke faruwa yace maza su Dakatar dani. bari ya fara kiran Ishaq din yaji abunda ke faruwa.
*Janafty*
[7/25, 2:50 PM] U.M Collection ZMFR CM: *KNKB3003*
*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*
*09069067488*
*TASTED & TRUSTED*
*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATUN SAIWOWIN MUTANAN CHADI DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZAR AMARE, MASU JEGO DA WADDA TAKE SON GYARA KANTA*.
*AN GWADA ANGA INGANCINSA SHIYASA NA KE TALLATA MUKU DA K'ARFIN GUIWATA*.
*ABIN BIRGEWA DA WANNAN SAIWOWINRL ZAKI YI AMFANI DA SU SAMA DA SAU DAYA.*
*AKWAI FULL PACKAGE, AKWAI RABI, TA YADDA KOWA ZAI IYA SIYA*.
*SANNAN BABU BAURI NA TASHIN HANKALI.*
*DA KANKI ZAKI DAFA ABAR KI, KOMAI ANA SAKA WA A CIKI*.
*SHIN KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR, KO KUWA KE CE KIKE SON GYARA KANKI?*.
*KAYANA NATURAL NE DOMIN SAIWOWI NE DA AKE HAKOSU A DAJIKAN CHADI. BAYAN SAUKAR DA GAMSUWA HAR YAQI SUKE YI DA DRYNESS DA KUMA INFECTIONS.*
*AKWAI NA TSUGGUNO DA YAKE HA'DE MACE TA MATSE.*
*AKWAI HADADDUN DAKA NA SHA DA MADARA KO NONO WANDA BABU ALGUS*.
*SANNAN AKWIA GADALIN MATA NA ASALI, WANDA SHA YANZU NE MAGANIN YANZU DA IKON ALLAH*
*DUKKANSU TESTED & TRUSTED NE*.
*TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU*
*08032773332*
*DOMIN KARIN BAYANI, SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*.
*NATION WIDE DELIVERY*
Lokacin da Mallam mijin Goggo ya kirasa yana shashen Inno ya shiga gaishe su da kwana ita da Baba Ati,shiyasa yana gama wayar Inno ta jefamai tambayar me ya faru..?ba shi da mafita illah na gyara zama ya fayyacemusu abunda ke faruwa.
Inno ta rike baki kafin tace"Ikon Allah. Shi aure fa daman rai garesa Usman duk yadda ka so ka san al'amarin sai kaga daga baya komai ya Sauya, ya kamata a zauna da ita da shi din domin yi musu sulhu, ba saboda komai ba sai domin yaranta"
Abba yace"Daman akwai niyyar haka Inno. rashin Lafiyar da tayi ne yasa na Dakatar da komai sannan ga Dokokin Likita a kanta"
Inno ta jinjina kai tana fadin"Allah Sarki wlh duk cikin ya'yan Hafsah tafi bani Tausayi sai ka ganta shuru shuru bata da Hayaniya Allah kad'ai yasan bakin cikin data Had'iya, sai dai bazamu yanke ma barayin mu Hukunci ba har sai shima yazo an zauna da shi, an ji Daga ina aka Haihu a Ragaya"
Baba Ati na gefe tayi karaf tace"Fad'i ki kara Inno yarinyar nan Fa'iza ta Had'iye Bakincikin wannan mijin nata da danginsa"
Daga Inno har Abba Hankalinsu suka maida kan Baba Ati na neman karin bayani sai ko ta gyara zama ta cigaba da Fadin"Mganar gaskiya sauran yan'uwanta sun fita sa'ar gidajen mazaje,Nasan wasu abubuwan tun Tamadina nada rai sannan ita Hajiyar Fatiman Goggo nasu na fad'amin wasu abubuwan"
Da Sauri Abba yace"Don Allah Baba ki fadamin abunda kika sani kan auran Fa'iza da Ishaq"
Ya fad'a Lokaci daya yana jin ransa na kuna,Baba Ati tayi shuru taki mgana Inno ta kalleta Lokaci daya tana Fadin"Atine ki fadamasa komai Uba yake gareta kuma domin a samu gyara in zai gyarun kenan fa"
Baba Ati tace"Da dai ban so nayi mgana ba. ammh Tunda takai suka Kure Hakurin yarinyar nan nasan komai ya zo karshe.
Duk cikin ya'yan Tamadina ita ta Dauko hakurinta da Zurfin cikinta Wlh ni nasan ko yan'uwanta ba kasafai take zuwa Inda suke ba,mijin ya hana sannan Karofin ma sai ta shekara bata zo ba sai wani babban sha'ani,ance Mahaifiyarsa da yan'uwansa basa Son Fa'izar ne ta sha wahalan su,Uwa uba kuma yazo yayi aure,Goggon su ke fad'amin sai yafi wata uku a chan inda yake aiki wajen Amarya bai waiwayi Fa'iza ba. sai itace ke mata sako akai akai Saboda yaranan,kuma nima na gani Rasuwar ta madina wlh sau d'aya Surukarta tazo ranar uku daganan bata dawo ba. mijin nata kuma ni dai har muka watse wlh bai zo ba,kuma har Ciwo Fa'izar tayi Goggon su ta wuce da ita gidanta ta yi jiyya har ta warke ta koma bai zo ba, ammh mazajen su Asiya sun zo wlh da su aka Sallaci tamadina sannan da su aka zauna akayi karban zaman gaisuwa,wannan mijin na Fa'iza yanzu ne ya yi sanyi daga shi har uwarsa da Rayuwa ta koya musu Hankali Saboda d'an rashin da Shi Yaron yayi Fama da shi"
Baba Ati ta karishe fad'a tana gyada kai Inno ta kalli Abba shima ya kalleta Cikin takaici da wani bacin rai,Inno na son mgana sai ya rigata da Fadin"Tabbas biri ya yi kama da Mutum.."
Sai yama kasa mgana Saboda bacin rai,Inno ta jinjina kai Lokaci da'ya tana Fadin"Gaskiya Yarinyar akwai zurfin ciki ga sanyin Hali"
Baba Ati tace"Irin uwarta ce. Har tamadina ta bar duniya bata da abokin Fad'a haka Mijinta da abokan zamanta suke fadin Tarin alheranta Ita kan ta Dace wlh ta samu shedar Duniya Saura ta Lahira"
Inno tace"Allah ya jikanta ta. Lahirar ma muna mata Fatan Dacewa in sha Allahu"
Kamar Daga sama sukaji Abba na fadin"Shi Ishaq din baya son Fa'izan ne..?
Baba Ati tace"To ni kam ban sani ba ammh ai auran zumunci ne. mahaifinsa Alhaji Kabiru mutum mai son zumumci shi ya had'a auran,zai iya yuyuwa Saboda kaga ita Fa'izar na da Lalura,ammh dai kam ta yi zaman Hakuri da shi da kuma iyayensa"
Cikin kaushin Muryan Abba yace"Shi ne an san wannan ba'a raba auran ba.?ta yaya za'a bar yarinya tana kunsan bakin ciki haka..?oh na gane Hawan jinin da ta samu ma Dalilin sa ne da Danginsa kenan..?
Baba Ati tace"To wa suke da shi da zai tsaya musu?Goggon su ce kad'ai da ya'yanta,kuma kasan sha'anin aure yadda yake, sannan zurfin cikin yarinyar ba'a jin kamai a bakinta sai dai in an Fahimta fa,To ta ina zasu fara sai mutum ya shiga mganar kuma ita tazo taki mgana shiyasa aka saka mata ido ake binta da addu'a. baga shi yanzu da tagaji don kanta ta nema ma kanta Mafita ba Usmanu..?
Abba sai sakin Huci yake yi yana auna wasu abubuwa kowa zai bude baki sai yace Fa'iza sai a Hankali Ashe sa'ar Gidan miji ne batayi ba.
Ya na ji su Inno na mgana baya Sauraransu sai ma mikewa da yayi yana Fadin"Cikin Satin nan za'ayi ta kare In sha Allahu"
Inno tace"Gwara hakan dai gaskiya. Nima ina son zuwa na Dubata in zaka tafi sai na bika muje tare"
Da Sauri Baba Ati tace"Ni kuma sai ki bar ni ni kadai..?ai kafata kafarki"
Abba duk da bacin ran da yake ciki sai da ya Dara kafin yace"Shikenan duk sai muje Direba ya tukamu.
Gidan nan daman an gama komai Funitures,kadai suka rage ban samu zama ba ne,ammh zamu yi mgana da Maman Nana,saboda mu samu wajen sauka in munje garin"
Inno da Baba Ati suka hada baki wajen Fadin Allah ya taimaka ganin yadda Abba ke yi ne yasa Inno ta kira sunansa ya amsa sai ta kallesa tana Fadin"Kada ka yanke hukunci cikin Fushi Usman, mu bi komai a sannu kaji ko"
Kai Tsaye yace"In sha Allahu Inno"
Daga shashem Inno Dakinsa ya wuce yana neman Fadila a waya bayan ya sameta ta Dauka sun gaisa cikin Dakushewar murya yace"Fadila ki kira mijin Fa'iza ki tambayesa asibitin da suke kije ki Dubamin Ahmad dan wajen Fa'iza. in da yuyuwa ki saka ayi masa Transfer zuwa in da kike aiki "
Cikin Ladabi tace"To shikenan Abba"
Daganan ya katse wayar saboda Haushin Ishaq din yasa bai kirasa ba,ransa kawai yaji yana Tafasa a Fili ya furta"in dai ko hakane Zan tabbatar masa da Fa'iza na da Gata"
Ko Ammi da taga yanayinsa ta tambayesa,sai yace mata bakomai gajiyan aiki ne kawai shi kadai ya zauna yana auna wasu abubuwa sai yaji ya zaku a zauna ma domin yaji inda bakin zaren ya fara
Ya kira wayar Fa'iza bata Dauka ba,sai ya kyaleta Tunda Sun sake mgana da su Goggo sun tabbatar masa sun hanata tafiya ta shige Daki tana ta kuka,sai ya bari sai zuwa anjuma zai sake kira ya lallasheta.
Har ma ya fita yana Office Nana Fadila ta kirasa ta fadamai jikin Ahmad da Sauki,zazzabi ne ya rikita jikin yaron,sannan kuma ta maida shi asibitin da take aiki Abba yaji Dadin jin haka cikin Murna yace"Dakyau Allah ya yi miki albarka Nana Fadila"
Ta amsa da Ameen Abba kafin tacigaba da fadin"Ammh Abba Laluran Ahmad har da rashin Uwa a kusa. Sai kuka yake yana kiran sunan Umma sai da muka saka alluran barci cikin Drip dinsa sannan muka samu ya kwanta yana barci"
Shuru Abba ya yi kafin yace"Bakomai Fadila ina shi Ishaaq din..?
Fadila tace"Yatafi wajen aiki sai dai Mahaifiyarsa na nan,tare da amaryansa suka tafi inaga ita gida ta koma tazo da wasu kayan"
Abba ya jinjina kai yana fadin"Bari zan kiraki ina office ne"
Daga haka suka yi sallama Ranar gabadaya ransa a bace ya yini a office duk wanda ya gansa sai yace yau waya bata ma Eng,rai an riga an san shi Mutum ne,mai barkwanci da Wasa da Dariya shi ko Bacin ransa irin Labarin da ya samu ne Ishaq ya basa,kunya sosai shiyasa yaga kiransa yaki Dauka sai dare da ya koma gida yayi wanka ya na Hutawa ya kira Fa'iza domin yaga kiranta Daga baya.
Sanda wayar Abba ta shigomin na Idar da Sallar isha'i kenan,ina ta kuka tun Safe da Mallam ya hanani Tafiya nake kuka sannan ban ko kara lekawa ko Falo ba, da Farko Kin amincewa nayi da Goggo taso tsaidani sai da Mallam ya fito da kansa ya rika lallashina sannan na Hakura bayan yace Abba yace kada na tafi na Dakata,Tunanina Ya'yana sai a lokacin na Fahimci nayi Wauta,kada na zo na rasa ya'yana Saboda su na zauna shekaru ina kunsan bakinciki yanzu in na rasasu wake da asara? kamar an rufe zuciyata na daina Hango duk abunda ya Shude a baya ya'yana kawai nake tunawa da kuma Halin da Ahmad yake ciki nayi ta kiran Ishaq naji ya jikin nasa Ammh bai Dauki wayata ba, sai na sakama raina na rasa Ahmad shikenan ya rasu Goggo kuma banza dani tayi bata kara kulani ba Har Yaya Mariya tazo tayi ta aikin Lallashina ban saurareta ba.
Sanda naga kiran Abba kukana sai yaci karfina a raina nace rasuwar ya kirani ya fad'amin Shiyasa sai da ta kusa katsewa Sannan na Daga ina kuka nace"Ahmad ya rasu ko Abba..?
Cikin Muryan Lallashi yace"In ji wa..?Ahmad na nan da ransa kuma jikinsa da Sauki, yana asibitin da Fadila ke aiki Ita ke kula da shi"
Fadin haka yasa ajiyar rai ya kwacemin har sai da Abba yaji cikin Dariya da kuka nace"Da gaske Abba..?Da gaske Ahmad yaji sauki"?
Kamar yana ganina ya gyad'a min kai kafin yace"In sha Allahu ki kirata kiji yanayin jikin nasa. in baki yarda dani ba"
Da Sauri nace"Na yarda Abba wlh na yarda"
Sai yace"To ki daina kuka mana Fa'i Share hawayen ki kin ji ko..?Ahmad ya samu sauki sosai har yana mganarsa ma"
Kamar yana ganina na ko share Hawayena Hankalina ya kwanta Cikin Sanyin murya nace"Na share Abba. Na bar kukan wlh"
Abba ya gyara zama yana fadin"Dazu ni nace Goggon ku su tsaidake saboda barinki ki tafi Lagos ke kadai Fa'i hatsari ne ga shi baki da ishashen Lafiya,kuma baki san waje ba wahala zaki sha ki bari in kina son zuwa zan zo sai mu tafi ta jirgi yadda bazaki wahala ba"
Da Sauri nace"Na hakura Abba daman da naji jikin Ahmad din ne ammh tunda ga Anty Fadila ga su Zainab basai naje ba"
Abba yayi mirmishin su na manya kafin yace"Shikenan to ki kwantar da Hankali ki kira Fadilan sai ta baki Ahmad din kiji muryansa ko..?.
Kunya ta kamani na noke fuska ina yar Dariya mun dade muna Hira da Abba yana ta jana da wasa domin ya kwantar min da Hankali,daga karshe ya bama Ammi itama ta rika Lallashina nan da man naji zuciyata tayi sanyi Hankalina ya fara kwanciya kunya da nauyi yasa na kasa kiran Anty Fadila kamar na kira zainab sai na rasa me zan ce mata ganin itama bata nemeni ba.
Zama na gyara waya a hannuna ina jiran kiran Anty Fadila har goma ta gota bata kira ba,Duk kuma sai na Damu kamar na kira wata zuciyar sai ta Hanani,goma da minti shidda sai ga Kiranta da Rawan jiki na Daga,cikin sanyin murya na gaisheta ta amsa Lokaci daya tana fadin"Ya jikin ki Fa'in mu..?
Kai tsaye nace"Naji sauki Anty Fadila"
Ina so na tamnayeta jikin Ahmad kunya ta hanani kamar ta sani sai tace"Ina asibiti,dayake aikin Dare gareni ga Ahmad yau ya kira Umma yafi sau dubu"
Murna ta kwace min na kasa mgana har sai da naji Muryan Ahmad yana Fadin"Umma."Umma..ni zan dawo wajen ki"
Sai kuka na rud'e na mike har hijabin jikina na neman kadani Cikin rawan murya nace"Ahmad din Umma..Daina kuka kaji ko..?
Kamar yana ganina ya fara goge hawayensa yana fadin"Umma ina ta kuka ina kiran sunan ki baki zo ba Umma yaushe zaki dawo..?
Ina sharan hawaye nima nace"Kayi hakuri Ahmad din Umma zan zo in dai ka sake kirana ya jikin ka..?ka warke ko..?
Da kai ya amsa min cikin muryan Kuka yace"na ji sauki Umma Anty Fadila tamin allura,Anty Zainab da Daada sun kawo min nama Umma"
Cikin jin dadi nace"Sun kyauta kaci abinci sosai sannan ka rika shan mgani kaji ko Ahmad di'n Umma..?
Da sauri yace"Umma yaushe zaki zo..?mu kadai ne a gida daga Daada sai Anty sai Mama ke baki zo ba"
Cikin karfin hali nace"Ka rika shan mgani ka warke da wuri in dai kana so nazo na ganka"
Da Sauri yace"To Umma zan warke da wuri"
Cikin jin dadi nace"Yauwa Yaro na ina sauran yan'uwan ka..?
Ina yaya Amir ina Yaya Anum?
Bai yi mgana ba sai naji ana mgana kafin naji muryan Zainab tana Fadin"Maman Amir"
Nima sai na maida mata da fadin"Maman Fadil mutanen ikko"
Ajiyar rai ta sauke kafin tace"Ba kin ki mu ba Maman Amir..? Ga Ahmad rigima duk ya rikitamu baya yarda da kowa sai Amir ko Anum har Honey baya yarda da shi yanzu shi dai Umma Umma. Don Allah Umma ta Dawo wlh gidan ba Dadi da baki nan"
Sai nayi mirmishi Lokaci d'aya ina sharan kwallah kafin nace"Daman gidan bai taba karban bakuncina ba to bakomai ba ne in bana nan Maman Fadil ba ga ki ba?nasan zaki kula da su"
Cikin Jimami tace"Nima kinsan ba iyawa zan yi ba.
Allah yasa ma nazo da Yarinyar nan dake min Reno. ita ke tayani Dawainiya da yara"
Cikin Tausayawa nace"Wlh ga shi kin yi nauyi,Allah dai ya raba lafiya"
Ta amsa min da Ameem kafin tace min ga Amir ta mikamai wayar ban san ko Ishaq na dakin ba,Domin banji Ko Tarin sa ba
Amir bai yi kuka ba sai dai shima Muryansa a sanyaye ya gaisheni na amsa ina fadin"Amir kana kula da Sauran kannen ka ko..?
Kai Tsaye yace"Eh Umma. Ahmad ke kuka kullum Mutsy ma nayi. Umma yaushe zaki zo ki Daukemu mu wajen ki zan koma?
Tausayin yaran ya kamani Cikin Dauriya nace"Zan zo watarana Amir..Ya mganar makarantar Boko kun fara zuwa?
Cikin sanyin murya yace"Sai Ranar Monday zamu fara zuwa makarantar su Fahad din Anty Fadila Daada ya sakamu"
Cikin murna ta nace"Eyee yan gatan Daada islamiya fa..?
Kai tsaye yace"Ba'a sakamu ba Umma"
Sai na jinjina kai kafin nace"To kace ma Daadan ku ya saka ku kaji ko..?.ya amsamin da toh sannan na sake gyara zama ina fadin"Amir kai ne Babba ka Kula da sauran kannen ka,Ka rika musu Bitar karatun Qur'ani kai da Anum Tunda kin yi nisa ku rika karanta azkar Safe da yammah,ban da abokan banza Amir ban da wasa na rashin gan gado,ka rika taimakon kannenka bangaran karatun Boko da na islamiya,kuma ku zama yaran kirki ban da damun su Daada kada ku ki jin mganar Antyn ku,duk abunda tace ku yi ko ku bari ku ji mganarta,kun samu bambamcin Muhalli ba kamar katsina bace Lagos Amir don Allah ka kula da kanka da kannenka, ku rika sallah akan Lokaci kuna yimin addu'a kuna yi ma kan ku kaji ko.?
Cikin Sanyinsa yace"In sha Allahu Umma"
Cikin jin dadi na sakamai albarka sai ya bama Anum wayar itako kuka ta sakamin tana cewa itama waje na zata Dawo sai da na Lallasheta da zan zo sannan tayi shuru itama fad'a na rika mata ina Fadin"Anum ke macece kin sani ban da waasa da maza a makaranta ban da kawayen banza Anum,azkar Safe da maraici kun iya karatun Qur'ani ku rika yi in da kika karkare yayan ku ya Tadake,ki kula da kannen ki gabad'ayan su Anum ban da rashin ji ko Rashin kunya ku ji mganar Daada Data Antyn ku in wani abu ya shige miki Dubu ga Antynku ga Mama ga Babanku duk zaki iya tambayan su kin ji ko?
Ta amsa min da naji Umma,mganarta tasa jikina yin sanyi da nace ta mika ma Musty wayar kafin ta basa sai tace"Shikenan Umma bazaki dawo nan da zama ba..?
Sai na kasa mgana na Dauke Hawayena ina fadin"In Allah ya yi zan dawo Anum"
Daga haka bata kara mgana ba ta bama Musty wayar shima duk yan Rigiman ne sai da nace zan zo gobe sannan ya koma yana bani Labarin agidan Anty Fadila an siya musu wannan an siya musu wannan yana gayamin Ahmad bai da lafiya suna ta kuka,Sai da Fadil ya kwace wayar shima duk labarin kuruciyar ne,Mun jima muna mgana da su wayar daga kunnen wannan zuwa wannan sai da naji kamar Muryan Yaya ishaq na Fad'in tafiya za su yi sai naji mgana dai sama sama kafin wayar ta katse na samu natsuwa da nayi mgana da ya'yana sannan na kuma Tabbatar da Ahmad na nan da ransa bai mutu, kamar yadda nake Hashashe ba.
Sai alokacin naji yunwa ta taso min na zare Hijabin jikina na fita Falo ba kowa kila Goggo na Dakin mallam Kitchen na shiga ina neman abinci sai ga Goggo ta shige muna Had'a ido tace"Kin gama kukan ne kuma kika Fito neman abinci..?
Sai na kasa mgana itama bata kara mgana ba sai da ta Dauki abunda zata Dauka sannan ta fice tana Fadin"Ki duba flalks din nan akwai ruwan zafi ki sha sai ya warware miki ciki yadda kika yini baki ci komai ba"
Naji dadin shawaran Goggo tea na Hada mai kauri na sha sai zufa nan da nan naji na fara dawowa Daidai sannan na Dora da doya da miyan da Goggo ta Dafa a cikin kitchen din naci na koshi na kora da ruwa sannan naji ni na dawo cikim Hayyacina.
Ranar barci nayi har da makara Washegari tunda Goggo taga na tashi Garas ina walwalata sai ta kalleni tace"Hala kun yi mgana da yaran ne..?.
Kai tsaye nace"Eh Umma jiya nayi mgana da su har Ahmad din yaji ma Sauki"
Sai Goggo ta gyada,kai kafin tace"Dakyau! Allah ya kara lafiya"
Ta Fahimci farinciki a Fuskata.
A ranar aka sallame su suka koma gida Anty Fadila na kira ta fad'amin sai na Kira wayar Zainab bayan mun gaisa da Tambayam mai jiki sai ta bani Ahmad da Sauran yaran muka yi mgana suma na Lura sun fara walwala da jin muryata.
Da nace bazan nemesu ba sai sun saba da Rashina ammh ban san nayi Fatali da wannan Tunanin ba sai da naga kullum Safiya sai na kira mun yi mgana da su,Ranar da zasu fara zuwa makaranta Zainab ta kira da Safe ta fad'amin harda Ahmad Tunda ya warware tace babansu zai rika kaisu tunda ya siya mota in an tashi Direban gidan Anty Fadila in ya Dauko su Fahad zai rika sauke su agida an basu waya,mun yi mgana nayi ta musu nasihan kada su manta da karanta addu'an fita gida da azkar tare da natsuwa suka tabbatarmin da bazasu manta ba.
Naji dadi hankalina ya kwanta Tunda Ahmad ya samu sauki sannan ya Daina Rigima,kuma Yaran hankalinsu ya kwanta tunda suna mgana dani,Jamal ashe sanda Ahmad yayi ciwo yana kano yazo kamallah Takardunsa sai daga baya ya koma sai naji Dadi da Amir ya fadamin yana yi musu Lesson agida kafin ya samu Tafiya bautar kasa ko bakomai shi yana gidan zai kula da wasu abubuwan sai na samu natsuwa Hankalina ya kwanta ammh fa ko ban kira su ba zasu dauki wayar Antynsu ko ta Mama su kirani Amir da Anum tuni sun haddace Lambata.
Sati uku Tsakani Abba ya yi min waya cewa gobe suna tafe shi da su Inno yadda bai cemin komai ba nima ban kawo ba sai a daran Anum ta saci Wayar Mama ta kirani tana murna tana Fadamin gobe zasu zo wajena In ji Daada, sai Hankalina ya tashi na rasa ta ina zan kama mganar Cikin Tashin Hankali nace"Ke Saudatu bana son karya"
Da Sauri tace"Wlh Tallahi Umma har da ma Mama fa zamu zo Anty kad'ai zamu bari a gida"
Sai na yarda da ita domin tasan ai rantsuwa in kayi karya na shafa Fada musu ba kyau,Da Sauri na katse wayar sai na rasa wazan tambaya tuna Goggo yasa na kwashi gudu na Fita bata afalo tana Dakinta ina shiga na isketa tana zaune tana jan Cashaba ina Tsaye a kanta nace"Goggo Abba yace min zasu zo gobe..?akwai abunda zasu zo yi ne"
Kallomta tayi da mamaki kafin tace"Eh nima mun yi mgana da shi Inno ne da Baba ati zaso zo dubaki wani abu ne?
Kai Tsaye nace"Anum ta kirani da wayar Mama tace gobe Babansu yace zasu zo wajena, har da Mama itama"
Goggo tace"To ni ban san wannan ba kira Baban naki kiji"
Goggo ta fad'a tana kauda kai ni ko hankalima ne ya tashi bana so ya kwasomin yaran nan ban kuma san yadda zan yi da su ba.
Sai na kada kai na koma Daki Goggo ta bini da kallo kafin tace a fili"Ya Allah in da sauran zama Tsakanin yaranan Allah ya Daidaita su. in babu kuma Allah ya warware mana al'amuran"
Taki fad'amin abunda zai kawo su Abba saboda jin nima bai Fadamin ba,Abunda bata sani ba ina komawa Daki na kasa Hakuri sai na Kira Yaya Ishaq har sau uku bai Dauka ba,Dare ne nasan yana gida sai na Kira Zainab tana Dauka ta fara fad'in"Maman Amir"
Muryata a shake nace"Yana kusa..?basa wayar"
Tasan wanda nake nufi tunda ai a gabanta nake kira yaki Dagawa so yake yayi amfani da yarana ya sake Cutar dani tana bashi ko mganarsa ban jira ba na fara fadi'n"Kada kace zaka yi amfani da yarana domin ka sake Kuntatama rayuwata Ishaq.."
Kada mu yi haka dakai.
Ka bar su, su zauna in da ya zame musu Dole.
Naji Labarin kana shirin kwaso su ka kawomin su nasan manufarka wlh karka fara na riga nayi rantsuwan Wallahi Tallahi NAGAMA aure dakai. ya rage naka ka kyalesu ko kazo da su, ka kara Rikita su yadda kaima din zasu Gagareka"
Ina gama fad'in haka na yanke kiran ina Huci duk da Abba bai Fito Fili ya fad'amin ba ammh na Fahimci zama Abba ya Shiryamana kamar yadda yaso yayi tun farko na tuna mganar mu da Nana Fatima jiya har ce min tayi in Abba yazo yana tambayata kada naji nauyin gayamasa komai Abba zai kwatar min yancina to sai yanzu na Fahimci mganar ta gefen gado na zauna gabana na Faduwa ni bazan taba iya mgana ba. sai in har Ishaq ya warware mafarin komai da bakinsa.
Washegari ma yadda Goggo ta tashi da Shirye shirye na tabbatar da Zargina sannan da Safe mun yi mgana da Hafsah tace Har da Ammi da Yaya Abdul'Ahad a babbar Jeep din Abba zasu taho,Kuma naji Goggo na waya da Yaya mariya ita zatayi girkin bakin,Tunda Tafi kusa akan Anty Nasara ina Daki sai na Lafe wanka kawai nayi na koma na kwanta Ina Tunanin yadda komai zai gudana yau sai dai na samu mutuwar jiki da Faduwar gaba Ishaq da Mama suka Fara isowa tunda su tafiyar Jirgi ce,Ina Daki naji muryoyinsu suna gaisawa da su Goggo,naki Fitowa nima kuma ban ji an yi mganata ba Duk da Raunin jina nima na Koyi na kasa raunanun kunnuwana ina Jiyo mgana daga Falon Goggo.
Su Abba sai wajen sha Biyu suka iso,zuwan su yasa na fito bazan ji zuwan Abba da su Inno naki Fitowa ba,sanda na fito su Abba na kofar gida sai su Inno na duka na gaishesu Inno tace"Yar nan haka kika sha jinya..?jiki sai kashi..?
Baba Ati tace"Daman ai duk sauran sun fita kumari sannan ga rashin Lafiya kuma"
Sai mamakin Ramata suke yi wajen Mama na isa tana Falo na gaisheta sai naga bata son kallona kanta na kasa ni dai ban bi ta kanta ba. araina nace yaji barazana kenan bai Daukomin yaran ba wajen Ammi naje muka gaisa ita kan sai da ta taba wuyana Tana Fadin"Na shige su ni Aziza..Fa"i kin ji kasusuwa..?bari Baban Nana yazo tafiya dake zan yi na cike miki wannan kasusuwa da ba su da kyan gani"
Inno tace"ke ana shirin Daidaita komai tabi megidanta kina wata mgana"
Sai Ammi tayi shuru batayi mgana ba,Abba basu shigo gidan ba sai bayan azahar yaje duba ginin gida sai da kuma suka Tsaya suka yi sallar azahar sannan suka shigo nan ma cikin gida su Ammi sun yi salla sun ci abinci Inno da Baba Ati da Goggo sun kule sai Tattaunawa suke ni ko muna tare da Ammi tana ta ja na da Hirarta na barkwanci,su dai sun ci abimci ammh Su Abba ko da suka shigo akace ga abinci yace sai an gama zaman muna Daki ni da Ammi ya kirata yace tazo dani.
Ina jin haka sai na Rude ganin haka yasa Ammi ta mike ta Dafa kafad'ana tana Fadin"Kada kii damu Fa'i ba wanda zai miki Dole. sai dai kada ki yi shuru ki Cutar da kanki ki yi mgana domin nema miki yancinki aure Ibadan Allah ne ba Cutarwa ko bautan Mutum ba ne, kin ji ko?
Sai na gyada mata Kai Lokaci d'aya ina maimaita sunan Allah a raina yadda zan samu natsuwa Hijabi na saka ta riko Hannuna har Falon Goggo kaina na kasa har gaban Abba.
Ina zama na dago kaina karaf ana Yaya Ishaq ya rame yayi baki yana Sanye da shadda navy blue daga bangaran Hagun Abba ni kuma ina Bangaran Dama mun saka shi a Tsakiya, sai na dauke idona ina zagayen mutanen falon da kallo.
Dukkamu muna saman Cafet ne Inno da Baba Ati ne suke kan kujera,Naga Mallam mijin goggo sai Ammi sai Mama sai ni sai Abba, sai Uban gayyar Ina jin Yaya Abdul'Ahad yana waje shi da su Yaya isa.
Kaina na maida kasa ina kokarin Daidaita kaina. domin sai naji kamar bazan iya mgana a yanayin da na samu kaina a gaban Abba ba.
*Janafty*
[7/25, 2:50 PM] U.M Collection ZMFR CM: *KNKB3004*
*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*
*09069067488*
*TASTED & TRUSTED*
*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATUN SAIWOWIN MUTANAN CHADI DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZAR AMARE, MASU JEGO DA WADDA TAKE SON GYARA KANTA*.
*AN GWADA ANGA INGANCINSA SHIYASA NA KE TALLATA MUKU DA K'ARFIN GUIWATA*.
*ABIN BIRGEWA DA WANNAN SAIWOWINRL ZAKI YI AMFANI DA SU SAMA DA SAU DAYA.*
*AKWAI FULL PACKAGE, AKWAI RABI, TA YADDA KOWA ZAI IYA SIYA*.
*SANNAN BABU BAURI NA TASHIN HANKALI.*
*DA KANKI ZAKI DAFA ABAR KI, KOMAI ANA SAKA WA A CIKI*.
*SHIN KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR, KO KUWA KE CE KIKE SON GYARA KANKI?*.
*KAYANA NATURAL NE DOMIN SAIWOWI NE DA AKE HAKOSU A DAJIKAN CHADI. BAYAN SAUKAR DA GAMSUWA HAR YAQI SUKE YI DA DRYNESS DA KUMA INFECTIONS.*
*AKWAI NA TSUGGUNO DA YAKE HA'DE MACE TA MATSE.*
*AKWAI HADADDUN DAKA NA SHA DA MADARA KO NONO WANDA BABU ALGUS*.
*SANNAN AKWIA GADALIN MATA NA ASALI, WANDA SHA YANZU NE MAGANIN YANZU DA IKON ALLAH*
*DUKKANSU TESTED & TRUSTED NE*.
*TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU*
*08032773332*
*DOMIN KARIN BAYANI, SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*.
*NATION WIDE DELIVERY*
Abba ne ya fara bude taron da addu'a sannan ya gyara zama ya yi gyaran murya kafin ya fara da fad'in"Alhamdulillah dukkanmu nan mun san abunda ya taramu Magana ce akan ya'yan mu Fa'iza da Ishaq,"
Ya na gama fad'in haka sai ya karkato ya kalleni kaina na kasa ya kira sunana na amsa bakina na rawa na Dago ina kallonsa,Sai ya karkata kansa zuwa ga Uban gayyar shima ya kira sunansa abun mamaki da kwarin gwiwa ya amsa har yana wani gyara zama.
Abba ya sauke numfashi yana Fadin"Zaman nan naku ne. Tun tuni ya kamata mu yi sa sai bamu yi ba. Saboda Rashin Lafiyan Fa'iza da wasu uzurirrikan da suka sha kan mu, ammh yanzu Alhandulillah ga shi lokaci ya bamu dama mun zauna ke Fa'iza dake zan fara mganata"
Ina jin haka naji na fara rasa karfin gwiwana bai damu ba ya kalleni ya kara kiran sunana Idanuwana cike da kwallah na Dago ina fadin"Na'am Abba"
Cikin kaushinsa yace"Mijin ki ya rasa aikinsa a baya kin zauna da shi acikin Halin babu kuma da bakinsa ya fad'a min kin Tallafa masa da sana'o'in ki,bamu taba jin kan ku ba,Sannan Daga Baya Allah ya wankesa aka dawo masa da aikinsa da karin girma. kowa yasan Dake aka yi shirin komawa Lagos sai kuma Daga baya zence ya sha bambam,ina so ki bud'e baki ki Fad'amana me ya faru kika bin mijin ki Sabon Muhallinsa? sannan meyasa kike neman Saki a wajensa..?
Yana Dire mganarsa nima na Dire kukana saboda yana mgana zuciyata na bud'ewa da wani kunci sai na kasa mgana gabad'aya suka zubamin ido suna kallona.
Ammi dake gefe ta kalleni ta kalli Ishaq taga sai kifta ido yake yi alamun rashin gaskiya karaf ta taso tazo gabana ta rike min hannu tana Fadin"Yanzu ba Lokacin kuka ba ne Fa'iza. bude baki ki fad'i Abunda ke faruwa dukkan mu nan mun zauna me domin yi ma kowanni bangare adalci"
Wani irin kallo Abba ya watsa mata da ban taba ganin yayi mata irin shi ba. Da Sauri ta sakeni tun kafin yayi mgana ta koma wajen zamanta tana Fadin"Kayi hakuri Baban Nana"
Kai ya jinjina cikin bacin rai yace"Baki da Hurumi a kan wannan mganar ki yi shuru da bakin ki"
Jin haka yasa ta hade rai ta kama bakinta,Abba ya dawo da kalllonsa kaina yana Fadin"Umh muna jin ki Fa'iza ki juya ki ga wad'anda ke zaune gabadaya iyayen ki ne da kakaninki, zaki iya fad'amana duk abunda ke Faruwa Domin neman masalaha"
Hannayena na saka na kare bakina ina kuka,kamar a wani Lokacin kalamansa suke min duka acikin raina Dakyar na iya bude Idanuwana cike Taf da hawaye na sauke kan na Ishaq na wani Lokaci ina kallonsa ina kallo ya sunkuyar da kai yana zufa ni kuma kai tsaye cikin muryata da kuka Ya taimaka wajen Dasashe su nace"Ku tambayesa shi ke da duka amshoshin tambayoyin ku Abba. Ammh ni bazan iya cewa komai ba matukar bai yi mgana ba"
Na fad'a ina kuka na da Sauri ya Dago yana kallona gabansa na fad'i bai Dauka zan iya Dawo da wannan mganar ba Tunda nace na yafe masa cikin rawan baki yace"Haba Fa'iza na dauka mun gama da wannan mganar Tunda na roke ki gafara,kuma kika yafemin"
Ina Sharan hawayena da bayan Hannuna nace"Da gaske nake yi na Yafe maka yaya ishaq duniya da Lahira,sai dai ka sani ba hurumina ba ne Tun a wata Hudun Farko addini ya bani Damar haka. Mganar nan kuma Wlh kamar yadda nayi alkwarin baza'a ji ta daga bakina ba. Ka sahale min auran ka,kamar yadda na Bukata sai mganar nan ta mutu har Gaban Abada ba wanda zai jita"
Sai ya Rude kamar zai ta shi Daga inda yake Abba da suka zama yan kallo yace ya koma ya zauna ammh ya kasa zama Daidai Cikin sigar Lallashi yace"Bazan iya ba. ai na fada miki bazan iya sakin ki ba Fa'iza Baba yana kabarinsa wlh zai yi fushi dani Sannan me zan fad'ama su Anum da suke jiran na dawo musu da Umman su..?Sannan Zainab na fad'amin bazata zauna ba indai bakya gidan don Allah ki yi Hakuri Fa'iza ki janye wannan mganar ki had'a kayanki mu tafi"
Yadda yake mgana zaki san bai da gaskiya duk ya rasa natsuwa sai kowa ya koma yana kallonsa ni kuma Sai naji duk wani Fargaba na fita daga rainaa.
Naga kamar yama raina min wayau yana so na koma saboda ya'yansa da Muradin matarsa ba domin muradin kansa ba. sai na samu kaina da yin Wata karamar Dariyar da babu Nishad'i ko kadan acikinta sai zallar bakinciki sannan nace"In dai Saboda kalaman Baba ne kada ka damu Bazai kamaka da Laifi ba ko da yana raye domin ba'a so dole, sannan ba'a aure Dole.
Maganar yara kuma Kai ne Uban su kuma Dolen su. ni kuma nan ne ya Dace dani kayi hakuri ka rike su domin bazan bika ba,mganar matarka kuma ta zauna mana ai daman bani na aurota ba, kai ne mijinta kuma kana Tare da ita daman kuma bamu taba zama waje d'aya da ita ba. ballatana Domin bani ya zama abun damuwa,masu kular muku da yara kuma akwai ma'aikata a gari in kuka nema zaku samu in sha Allahu"
Na fad'a ina kokarin maida kwallan dake neman ziraromin,kowa sai mamaki ya cikasu na mganganun mu daga wannan ya kalleni sai wannan ya kalleshi Inno ta gyara zama ganin Abba ya kasa mgana cikin muryan data kwana Biyu tace"Kai mu duk bamu gane kan mganganin ku ba .Ku Bude baki kuyi mana mgana yadda zamu gano bakin zaren kai Usman ka yi musu mgana mana"
Abba ya sauke Numfashi kafin ya kalleni yana bude baki yace"Fa'iza..".
Ban bari ya cigaba da mgana ba ina kallon Ishaq nace"Abba shi zaka tambaya in dai bai yi mgana ba nima bazan yi ba. Saboda ina so na cigaba da yimasa adalci da ya rokeni nayi masa Tun a baya"
Ina mgana ina kuka muryata na Sauyawa sai Abba ya maida kallon kansa sai zufa yake yi duk da Fanka sama data kasa dake aiki a Falon da ka gansa kasan ba gaskiya, bai taba zaton zan iya dawo da wannan mganar ba na Shammacesa.
Abba ya kira sunansa ya amsa yana Rawan baki Abba mamaki ya kamasa sai dai bai nuna ba cikin Sanyi yace"Kaji abunda Fa'iza tace..?shin zaka iya yi mana bayani ne yadda zamu gane? Ko kuwa zaku cigaba da wasa da Hankalin mu ne..?
Sai Ishaq ya fara share zufa da Farin Hanky din dake hannunsa ya Juya yana zare ido suka Had'a ido da Mama wacce ta kauda kai da Sauri ta kasa kallonsa ya dawo da kallonsa kaina ya kasa zama kansa na kan kafafunsa Cikin rawan murya yace"Plz Fa'iza ki bar wannan mganar mana"
Nima kai tsaye nace"Zan bar ta kad'ai ne in ka sahalemin auran ka Ishaq"
Marairewa ya kara yi kafin ya kalli Abba yana Fadin"Abba ka bani minti goma kacal mu yi mgana ni da Fa'iza"
Har zai yi mgana Goggo tace"A baya da baku fallasa mana abunda ke Faruwa ba,ba wanda yaso yaji ammh yanzu tunda kuka fallasa a gaban kowa da kowa zaku yi mganar daga yau koma menene muna so mu ji kuma mu sani"
Tafad'a tana kallona ina Kuka haka kurum taji duk abunda yasa Fa'iza mgana abu ne mai taurin da jinsa sai ya Girgiza zukata,kuma ta fi kowa sanin zaman hakurin da Fa'iza tayi a gidan Ishaq mganar ta yasa Inno da Baba Ati suka ce ya yi mganar nan kowa yaji ai Sulhu ake nema
Abba ya kalli Ishaq ganin yadda yake rawan jiki yasa ya Dafa kafad'ansa yana Fadin"Kada ka damu ni ba Uba kad'ai nake ga Fa'iza ba.
Har da kai,in ita ke da Laifi wlh da kaina zan tasata sai Dakinta bazata kara kwana a garin nan ba"
Jin kalaman Abba yasa sai ya fara samun natsuwa yana Hango adalci a mganar Abba Cikin ajiyar rai ya koma ya zauna yana Fadin"Abba ku yafemin kuskure ne na aikata cikin Rashin Sani ammh wlh nayi nadama Tuni kuma naba Fa'iza Hakuri tace ta yafemin ban san me yasa ta kuma Dawo da mganar data wuce ba"
Da sauri nace"Saboda itace mafarin duka al'amura. mganar yafiya kuma na Jima da fad'amaka na yafe maka Duniya da Lahira"
Abba sai ya koma ya kalleni ya kallesa kansa ya Daure,da yasa ya kasa mgana Shuru falon ya Dauka Kafin Inno tace"Muna jin ka Isiyaku"
Ya dago yana kallon Inno ga Tsoro ga Takaicin sunan da ta kirasa da shi ya Tabbata in bai yi mgana ba,ba mafita ammh kuma yana ji ajikinsa Abba zai Fahimcesa Mama ko Jikinta nata rawa,kunya duk ya kamata bata Fatan Fa'iza ta fad'i musgunawanta gareta duk da taga irin kallon da Goggo ke jifanta da shi ji take kamar ta tashi ta Fita sai dai ba Dama.
Kamar Daga sama taji Ishaq na Fadin"Wato Abba..Lokacin da zan kara aure ne..Sai sai na ce ma Fa'iza..Mu mu.."
Ya kasa karisawa Saboda kunya da nauyin mganar Abba ya kuramai ido yana Fadin"Uhm ina jin ka"
Ishaq ya Runtse ido kafin yayi gundinbalan fad'in"Nace ma Fa'iza zamu jingine auran mu ni da ita"
Gabad'aya sai Falon ya Dau shuru kamar Mutuwa ta gifta ni ko kamar a Lokacin yake min mgana Hawaye wasu na korar wani a saman Fuskata.
Goggo cikin mamaki tace"Wani irin jingina kuma..?
Inno ta karb'e da Fadin"Ni kaina na kasa ganewa fa"
Mallam mijin goggo da sai a lokacin yayi mgana cikin kallon Ishaq yace"jinginar aure kala kala ne Ishaq, kayi mana bayanin wata irin jingina ce ka nemi ku yi ma auran ku kai da Fa'iza?
Ishaq kansa na kasa ya Dago yana kallon Mama itama shi take kallo Cikin mamakin kalamansa kafin ya Sadda kansa domin ya kasa kallon Abba cikin rawam murya yace"na nemi alfarman Fa'iza kan mu jingine auran mu, ba mu'amalan miji da mata a tsakanin mu ,ba wani hulda ta ma'aurata Tsakanina da ita,sai dai kawai ta zauna ta cigaba da kularmin da ya'yana"
Yana Dire mganarsa sai gabad'aya su Inno suka Dauki Salati suka Dire Baba Ati tace"Lalle lamarin Babba ne"
Ni ko hawaye kawai na bari suna zobomin da mirmishin da ke saman Fuska sai dai a alokacin in za'a tona Zuciyata kamar zata fashe saboda bakinciki da kunci.
Abba ya kasa mgana Saboda Takaici Goggo tace"Wannan mganar sharia"a ce ta ila'i dole muna bukatar malaman da zasu yi mana fashin baki kan wannan al'amarin"
Da Sauri Mallam ya jefomasa tambaya da cewa"Har na tsawon wata nawa ka di'bar ma wannan jinginar?
Ba zato kawai sukaji Muryata a Kausashe ina Fadin"Har na Tsawon Shekaru bakwai. Shekaru bakwai da Doriya Mallam"
Gabad'aya sai suka had'a bakin wajen Fadin"Shekaru bakwai fa kika ce Fa'iza..?
Ina kuka na jinjina kai kafin nace"Iya shekarun da nagaji ne na nemi mafita ammh Jinginarsa gareni ta har Abada
Ne.
Saboda baya kaunar kara Had'a zuru'a dani bana haifa masa ya'ya Daidai da Burinsa,tunda bazai iya sakina Saboda kalaman Baba akansa ba,sai ya Zabi ya jingine ni tunda zai auro wacce tayi daidai da Ra'ayin sa kuma wacce zata Haifa masa ya'ya farare kyawawa daidai da ra'ayin sa Shekaru sama da bakwai na kwashe Cikin kunci da bakinciki bayan wad'anda na kwashe a baya Abba ka gayamin nayi Laifi domin na nemi da ya Sauwakemin..?ba aikin da ya fara na nemi ya karishe ba..?
Na fad'a ina kallon Abba Hawaye kamar ana tunkudo su haka suke zubomin Abba yaji jijiyoyin kansa na tashi,Saboda bacin rai ya kalli Ishaq yafi sau uku shi kuma kansa na kasa su Inno jikinsu duk yayi sanyi Ammi ko har tana tayani kuka.
Abba ya kalleni ina kuka Tsausayina ya kamashi,ya rikoni gefen kafadarsa yana Lallashina jina acikin jikinsa yasa na barke da kukan da shekaru sama da goma ina neman Kafad'an da zan kwanta nayi wannan kukan ban samu ba sai yau sai kawai suka ji muryanta na saki kukana da Dukkan Karfin zuciyata sai Ran Abba ya kara baci ya Dago Cikin Fushi yana kallon Mama cikin Tsawa yace"Da Sanin ki D'anki ya jingine auran yata shine baki yi komai a kai ba..?
Jikin Mama na rawa zatayi mgana da Sauri nayi Wuf na tashi daga kafad'an Abba cikin kuka nace"Bata sani ba Abba. Dagani sai shi ne muka sani.."
Abba ya dakamin Tsawa nima kafin yace"Meyasa baki fad'ama kowa ba..?
Tunda Lokacin bana nan meyasa baki zo kin Fad'ama Goggon ku ba..?
Kuka na kara sawa ina Fadin"Ya zan yi Abba..?yace nayi masa adalci da ya shekara takwas yana min na aurena a yadda nake ya zauna dani. to nima ya Roki da nayi masa adalci na barsa yayi Rayuwarsa da amaryansa Abba ina son na zauna da ya'yana Wlh Sabo da su ne. Sannan alokacin bana so na Dorama kowa nauyina Abba Shiyasa ban taba Fad'ama kowa ba"
Na karishe Fad'a ina kuka gaban Hijabina ya jike da kuka.
Abba sai sakin Huci yake yi yana kallon Ishaq da ya gama Tsurewa Mallam ya yi gyaram murya kafin yayi mgana Goggo ta rigasa da Fadin"Tabbas nasan Fa'iza bata ji dadin zama da Ishaq ba .bata da mutumci a idon sa da shi da Mahaifiyarsa da yayarsa, ni shaida ce ba irin cin kashin da basa mata Har ni kaina da ya'yana bamu Tsira ba Saboda ina kaunar Fa'iza"
Abba kamar zai dagi Goggo yace"Kuma kuka kasa Raba auran dake cike da Zalunci Goggon su.?
Sai Goggo ta saka kuka tana Fadin"Ya zamu yi Alhaji..?ina tausaya ma Fa'iza ina Tausaya yaran nan nata
Sannan ita bata mgana ko yan'uwanta su yi tambayan duniyan nan bata Fad'a musu komai, sai dai tayi shuru bakincikin na cinta,sai dai muga tana ta rama da kamjamewa"
Ta karishe fad'a cikin kuka,Abba ransa ya kara baci ya mike a fusace cikin Fusata yace"To ana aure Dole ne..?meyasa aka bashi auranta tunda baya sonta..?
Mallam ne yayi mgana cikin lallashi yana fadin"Alhaji koma ka zauna ayi mganar nan a tsanake"
Sai da inno ta kara mgana sannan ya zauna yana Huci,Kukan Fa'iza na soya masa rai Mama ma kukan datake yi ya sa kowa ya maida Hankalin kanta.
Cikin kuka tace"Alhaji ku yi hakuri wlh ban san da wannan mganar ba,Ishaq bai gayamin ba sannan ita kanta Fa'iza bata gayamin ba. abu daya na sani a baya na musguna ma Fa'iza ina kuma neman afuwarta data yafemin"
Ta fad'a tana share kwallah da Haban zaninta Abba kyafci yayi kawai ransa na Cigaba da kuna sai kiran wayarsa ake yi yana Kashewa baya son mgana ma alokacin Saboda yadda ransa ke kuna Ishaq ko motsi ya kasa Saboda Fargaba da yadda yaji muryan Abba cikin zafi da kaushi.
Mallam ya gyara zama yana Fadin"Duk ba wannan ba ne Alhaji. A kokacrin Alhaji kabiru shine namiji babba ga su Fatima da Aisha shi kuma ya rike Fa'iza a hannunsa har ga Allah bai had'a auran nan da wata manufa ba. ya hada shi ne Saboda yana Tunanin Ishaq zai iya Rike Fa'iza da maraicinta har bayan Ransa bai taba sanin zai yi haka ba,In da ya sani Alhaji kabiru yana kabarinsa Allah yaji kansa bazai aura mata shi ba sannan inda yana Raye wlh shi da kansa zai raba auran nan indai ya ga Fa'iza na cutuwa"
Falon sai ya yi shuru kowa na Sauke Numfashi Inno ta gyara zama tace"Duk mun ji,Daman yaran yanzu ai ka haife su ne,baka Haifi Halin su ba mu yanzu matsayin wannan auran zamu fara nema domin a shari'a ina jin Tuni auran nan ba shi"
Baba Ati tace"Gaskiya shekaru bakwai ba kwana bakwai ba ne. Inno wannan Cutarwan ya yi yawa gaskiya"
Abba ya yi saurin taransu da Fadin"Ban damu da wannan ba ko da aure ko ba aure sai ya sakar min y'ata tunda ba'a aure dole"
Ya fad'a a kausashe Ishaq ya Dago Fuskarsa ta jike da zufa saboda Fargaba,cikin rawam murya yace"Don Allah Abba..!
Hannu ya daga masa kafin yace"Ai baka sonta ko.?to ka saketa bazan yi maka Dole ka zauna da wacce baka so"
Yafad'a cikin bacin rai sai kuma kowa ya kasa mgana Ammi nata jin Dadi a ranta ni Abba ya kallah ina sharan kwallah Cikin Fada yace"Ni ba sakarai ba ne ban kuma Haifi sakaran d'iya ba.Meyasa,kika zauna Tsawon wannan Lokacin da wanda baya sonki..?wanda ya zabi wata matar sama dake..?
Yafad'a yana kallona Zuciyarsa har Dagawa take yi ran yan maza ya baci Tsawa ya dakamin yana Fadin"Tunda kinsan baya son ki meyasa kika yi masa afarman zama dashi..?
Ina kuka jikina na rawa nace"Abba ya'yana.."
Abba kamar zai Dageni ya tasomin yana Fadin"Ya'yan banza..Nace ya'yan banza kan ya'ya ne zaki zauna ya na wulakantaki Shi da yan"uwansa..?ki bar ya'yaan su mutu mana ai ba ke kika Haifesu ke kad'ai ba shima Uban su ne. Kada ki kara zama Saboda wasu ya'ya ana wulakantaki Jariri ma yazo duniya bai ga uwarsa ba. kuma ya Rayu ballatana yaran da suka girma"
Yadda yake mgana yasa Inno saurin cewa"Usmanu kayi mata a Hankali"
Sai a lokacin ya Saussauta mganarsa yana Fadin"Ki bude baki ki Fad'amin Tundaga farko har karshe in kika boyemin wani abu sai naci Mutumcin ki Fa'iza"
Kaina naji ya sara na kasa mgana Tsawa ya sake dakamin Cikin Hargagi yace"Ki fad'amin Hujja nake nema yadda zan ci uban duk wanda ya ci zarafin y'ata wlh"
Jin haka yasa da Sauri nace"Abba ba niyyata in tona masa asiri ba don Allah ka bar mganar nan"
Marina ne kad'ai Abba bai yi ba,Ammh sai da na samu Tsaraban kallo kafin yace"Shi ai bai Rufa miki naki asirin ba shine ke kike neman ki Rufa masa.?Tona masa kowa yasan Abunda ke Boye"
Kuka na kara Fashewa da shi har ga Allah na riga na yafe masa bana son Dawo da abun da ya wuce shima kallona yake yi alamun roko cikin lokaci daya duk ya zabge sai Zufa yake yi har Shadda jikinsa sai da ta jike da Zufa.
Mama ce tayi mgana cikin Dashewar murya tana Fadin"Gwara ki Fad'a Fa'iza ki fad'a musu komai duk da nima nasan da Laifina tunda ina gani yana wasu abubuwan ban taba Hanasa ba,sai ma kokarin Dora shi kan Hanyar banza da laifina nima"
Kukan da take yi baisa kowa yaji Tausayinta ba.
Kamar daga sama sukaji ance"Ai bazata taba mgana ba Abba.
Da zata yi mgana da ta fad'a muku ishaq ya yi ikirarin zai Daukomin yan Sanda in ya kara ganina a gidansa"
Gabad'aya muka jiya bakin kofa in da muke jin mganar Yaya mariya ne ke Tsaye tana Hawaye Gabana ya fad'i shikenan Yaya mariya zata fad'i wannan sirrin da na zata ta manta da shi.
Da sauri Abba yace"Taho nan Mariya ki fad'amin abunda kika sani kan zaman Fa'iza da yaron nan"
Da Dauri ta kariso ta zauna agabansa kafin tace"Abba ban taba fadin ma kowa abunda ya faru ba sai yau. Saboda Fa'iza Saboda ita ammh yau bazan iya shuru ba!
Ta kalleni kafin tace"Kiyi hakuri Fa'iza..'"
Kafin tamaida kanta wajen Abba bayan ta gama kare ma mutanen Falon kallo ta wani sakarma Ishaq wani kallo kafin tace"Abba ban san mganar da kuke yi ba na shigo na dade Tsaye ina jin wasu mganganu.
Wlh Abba Fa'iza ta sha wahalan rayuwar kaskanci da wulakanci a gidan wannan mutumin,Fa'iza bata da daraja ko Kima a wajensa da wajen uwarsa gata nan da Yayarsa Abba ni fa uwa d'aya uba Daya muke da Fa'iza ishaq ya bata Sakon ta gayamin kada na kara zuwa Gidansa da bata gayamin ba ranar da ya iskeni Abba koran kare ya yi min Fa'iza na kuka tana rokonsa ammh ya rantse in ban fita ba sai ya Had'ani da yan Sanda Abba"
Gabadaya suka saka Salati Abba yace"Good..'
Yaya mariya na Hawaye ta kalli Goggo tana Fadin"ai kin tuna Lokacin goggo. Lokacin da kuka barni wajen Fa'iza sanda tayi ciwon nan kikace nayi mata kwana Biyu to kwana D'aya nayi yayi min tozarcin da har na Mutu bazan manta ba dalilin da yasa har yau ban kara taka inda Fa'iza take ba. sannan ban kuma taba gayama kowa ba,sai yau shima din naga in nayi shuru Fa'iza zata iya koma ma Wannan rayuwar data bari"
Da Sauri Abba yace"Bazata koma ba. Bazata taba komawa ba indai ina Raye mari"
Yafad'a idanuwansa jajir Goggo na Sharan kwallah tace"Nasan dai daga Lokacin indai zamu gidan Fa'iza sai ki zille na Dauki Saunan wani abu sai dai yadda baki ce min komai ba, Fa'iza ma ban ji tayi mgana shiyasa sai na dauka tsiyar ki ne ya tashi kika dauke kafa."
Baba Ati tace"Ko ba domin Darajan Fa'iza ba,ai ya Duba zumunci"
Yaya Mariya tayi mirmishi kafin tace"Ke kika san wannan Baba Ati, tunda Fa'iza ta zama banza a wajen su zaki san ba su damu da wannan zumuncin ba"
Kai Tsaye Abba yace"Ki fara sanar dani abunda kika sani"
Ina kuka ina girgizama Yaya Mariya kai bata Saurareni ba ta fara zayyana ma Abba abubuwan data sani akan zamana agidan Ishaq da yadda ya rabani da su da auran sa da wulakanci da Anty Binta tayi mana. da yadda na kara zama banza bayan auransa da Zainab Saboda ita mai kyau ce kuma yar gata ce,da yadda har mahaifiyarmu ta rasu bamu gana ba,kunci rayuwar da na cigaba da Fuakata kafin samun sana'ata da duk irin cin kashin da Mama da Anty Binta suke min ta fadi iya abunda ta sani kafin ta gama gabadaya su Inno sun fara kuka saboda Tausayina.
Ammi tace"innalillahi lalle Fa'iza ta ga Kunci rayuwa"
Abba ko Ishaq da Mama yake kallo ji yake kamar ya saka a kulle masa su har sai sun daina Numfashi,shuru falon ya Dauka sai mganganun su Baba Ati cikin Tausayawa ni ko kuka kawai nake yi cikin kunar rai abubuwan da suka faru suna Dawo min Daki Daki.
A fusace Abba ya mike yana fadin"Ba anfanin wannan zaman. Ka rubuta ma y'ata takardan saki tunda ba'a Dole. kuma kwatankwancin yadda ka Wulakantamin Fa'iza wlh nima sai na wulakantaka"
Kokarin Fito da wayarsa yake yi ganin haka nayi wuf na rike kafafun Abba ina kuka nace"Abba kada kayi mai komai don Allah nice daman baya so to ya sakar maka y'a
Abba da gaskiyansa ni Nakashashiya ce ina da Raunin ji,sannan ni ba Fara bace bani da kyau Abba sannan ni bani da ilimin Boko kuma ban iya Turanci ba,sannan ni bani da gata bani da kowa ni ba yar kowa bace sai Diyar Bebiya,Abba da gaske ne ni nayi kutse cikin mafarkin sa ni ban Dace da Mutum irin sa ba,Abba ka Dubeni baka mara kyan Fuska wacce batajin Turanci bata kuma da gata Abba dole yaji kunyar nuna ma Duniya ni a matasayin matarsa in kuma yaji kunyar nuna ya'yansa shima bai yi Laifi ba ,Abba bai so a haife su ba Karfin Rabo ne ya samar da su na fi shi sanin zafinsu shiyasa na zauna Domin na kare su Abba.
Abba ka kyalesa yana da gaskiyansa ni Fa'iza bani da wani amfani Abba ni ba macen data dace da namiji kamar Ishaq ba ne,ba ya so na ne Abba Kuma gaskiyan Mama data sha Fad'in bauta ya Dace da Mata irina. Abba na zauna na wahala da ya'yana Tunda ya zabi wata matar sama dani Abba sai mu kwana mu yini ni da yara bamu ci abinci ba Abba,Abba ba tun yau ba Mama da tab'a so ta koreni Anty Binta ta taba zuwa har gidana ta min watsi da kayana akan sai na bar gidan kaninta Abba..!
Sai kuka yaci karfina na rika rusa kuka sai jikin kowa ya karayin sanyi Abba ya Duka ya rikeni jin hannayensa yasa na cigaba da Basu labarin irin zaman da nayi da ishaq irin yadda na fuskanci tozarci da wulakanci a wajensa da wajen mama yadda suke zuwa da Zainab ina musu wahala kamar jaka yadda yake tafiyar ya barmu da yunwa ni da ya'yansa,Yadda mahaifin matarsa da shi kanshi suka taru suka wulakantani Saboda bani da gata ni kaina ban san ina mgana ba Idanuwana a Runtse nake maida musu komai ina ganin shi a idona yana wucewa kamar a majigi.
Ina basu labarin taimakon Hajiyar su Raliya gareni tare da taimakon Badariya da kudin da Kungiyarsu tabani kafin fara koyan san'ata da yadda muka yi da ishaq da zaman mu da shi bayan haka.
Na Damke hannunwan Abba ina Fadin"Bani da abunda zai so Abba. Shiyasa na yi zaman ya'yana Lokacin da na yanke shawaran barinsa sai ya rasa aikinsa sai na janye kudirina Abba har zuwa wannan Lokacin"
Kuka yaci karfina ammh ban yi shuru ba na cigaba da gaya musu yadda muka fara Sabuwar Rayuwa da duk abubuwan da suka Faru da Lokacin da ya nemi na bama aurammu wata Dama.
D
Da sauri Abba yace"Allah yasa baki bashi wannn damar ba Fa'iza..?
Ina kuka nace"Na kasa Abba..Na kasa dalilin Ishaq yasa na Tsani aure da maza Gabadaya auren ya fita a raina. Don girma Allah Abba ka saka shi ya Sakeni ina jin kamar zam mutu in na Tuna da auren sa a kaina"
Na karishe Fada ina wata jijjiga Saboda kuka Inno na sharan kwallah tace"Tabbas ya wajaba a raba wannan auran Usman zaluncin ya yi yawa"
Abba yaji gabadaya bai son ganin Ishaq da mahaifiyarsa dake kuka shi ko Uban gayyar kansa na kasa jiki na rawa.
Cikin Daga murya Abba yace"Sai ya saketa..?ai wannan auran ba shi..Duk da ban da zurfi a sanin wasu hukunce hukuncen addini,nasan matsayin ka jingine auran ka a musuluci wata Hudu ne in baka Waiwiyo ba, ta nemi manya su Raba auran ita ko ta haura shekaru mganar ma yayi saki ko kar ya yi ya Rage nasa mgana D'ayace daga ita na gama Bilhil azim ko kusa da Y'ata Ya sake kusantowa sai na saka an Dauremin shi"
Ya fad'a cikin bacin rai yana kokarin mikewa da Sauri Mallam yace"AlhaJi don Allah ka koma ka zauna ina da karin bayani kan wannan al'amarin"
Girman Mallam yasa Abba ya koma ya zauna ina jikinsa ina kuka Yaya Mariya ma sai sharan kwallah.
Kowa ka gani jikin ya yi sanyi Ishaq ko bakinsa ya yi nauyi ya kasa ma mgana.
Mallam ya gyara zama yana fadin"Matsalace ta Ila'i wannan mganar ma'ana rantsuwa a shari'a,kamar kace kayi ramtsuwa ka iyakan cewa bazaka kara kusantar matarka ba har na tsawon Lokacin da ka Dib'a ma kanka.
A shari'ance Wata Hudu ya bama mace dama ta zauna in bai Sauya ra'ayi ya Dawo ba ta saka manya Cikin mganar, ko ta kai kara Alkali ya raba auran,ita kuma Fa'iza ta Shafe wasu shekaru tana jingine bi masala ta addini auran su bai saku ba, sai in har shi da kansa mijin ya Saketa ko kuma ya bayyana mana matsayin jinginarsa gareta na saki ne ko ba na saki ba ne. Ammh Shari'a ta bata damar ta Nemi Saki in har bazata iya zama da shi ba"
A fusace Abba ya ce"Ai ko yanzu zai sakarmin y'a don mai garin su.."
Kai Tsaye ya maida kallonsa kan ishaq kafin yace"Zaka sakar min y'a ko sai na gwada ma ka nima d'an tasha ne?
Abba ya fad'a yana Zare mai ido Lokaci daya kamar D'an tashan daya ambata.
*Janafty*
[7/26, 11:56 AM] U.M Collection ZMFR CM: *Al'bishirunku Ma'aurata, GA GARKUWAR KU nan tafe muku da tsarabobi na musamman gareku ma'aurata daga cibiyar mgnin mata mai taken GARKUWAR MA'AURATA*
NI DAI AYSHA ALIYU GARKUWA.
Ina matukar mamakin wani irin lokaci da ya riske mu mai wahalallan fassara. Kullum dai magana daya ce, akan ma’aurata, fada, rashin jituwa, mutuwar aure, akan kuskure kalilan, rashin kula, rashin yi wa juna uziri. Toh wai duk me ya janyo hakan? Na zurfafa a tsananin tunani hakan ya tilasta min bincike mai tarin yawa wanda ya kai ni ga gano inda matsalar take? Shin yar’uwa ke macece amma kin san wacece mace ku? Kin san me ake kira mace kuwa? Mace ita ce matar da take zama iyali a wajan namiji ta zame masa bango, sanyin idaniyarsa, ta zame masa gata da farin cikin rayuwarsa ta zame masa ruwa abar kore ƙishinsa ta zame masa mayafi mai karesa daga gigitar kadaice, ta kuma dorar da mijinta kan turbar gaskiya, ta kashe masa jiki da salonta ta rikita shi da baiwa da ni’imar da Allah ya bata idan har ta san hanyar mayar da kanta sabuwa dal awajanta, wato kullun takasance masa tamkar amarya har ya kasa tantance daren amarcinsu da sauran dararen rakun rayuwar su.
Wannan ita ce mace. Ina da wata saukakkar hanyar da zaki zama abar so da kulawa da soyayya a wajan mijinki ta hanya mafi sauki, 09097853276 hanyar ita ce ki gwada amfani da kayana na gyara ki gani, ina mai tabbatar miki da in sha Allahu sai kin dara da murna sai kuma kin gode min. Kayana kaya ne da aka yi shi da zallan itacanmu na gado marasa illa a cikin jikin dan adam musamman mace, kaya ne da suke taimakawa (sex hormones 😍) dinki.
Misali kina kallon India😘, hollywood, Asian film🥰 kina ganin yanda mazansu ke nunawa matansu tsananin soyayya kamar su ba su kyautar ransu!?
Saboda me hakan? Saboda suna sadaukar da lokacinsu wajan gyara jikinsu da kayan da ke tsattsafo da ni’ima cike da tsukewa, kayan nan kuma ana yinsu ne zallar magungunan gargajiya wanda ba su da illa domin haɗine na ingantattun itatuwa da yayansu.
Ina baiwar Allahn da miji ke daure mata fuska babu hirar arziki?
Zo ki ji yar’uwa zan baki gumbata da zallar gari wanda aka yi su da nagartattun itacen da ke da matukar amfani a jikin mace. Gubar ciko, gumbar tsalle dole, gubar da ba'a baiwa mai kishiya, garin maɗi, garin mallaka, tsumin goron tula, tsumin tsartai, tsumin maratsi, pala-pala butar sirri, kwanon k’asaitacciyar mace, furar mata madararta gareki Hajia takenta sha yanzu mgni yanzu,
Ina mata masu fama da sanyi? Sanyin mara ki zo na hadaki da magani na na sanyi wanda yake wanke mara ya fitar da duk wata cuta da ke samun mazauni a wajan.
Ina da ciccibi mai kyau. Ina da hadin amare mai kyau wanda zai gyara yarinya ya kankaro mata kimarta akwai hadin mai jego wanda muke yinsa na asali inada kekkyawan Hadi maida tsohuwa yarinya.
Akwai daya bangaren wato *KAMSHI*
Kimarki gyaranki da kamshinki. Matan da suka gane suka san yanda za su kankaro da mutunci su ne masu amfani da kayan gyara da kuma sanyaya jikinsu da kamshi, ina da turaren wanka da na bandaki na daki na jiki da na kaya dana tsuguno kamshin turarena na dabam ne mai sanyaya zuciyar wanda ya shaka ina da kayan kamshi na amarya da na maijego da na uwargida da dukkan macen da take kokarin mayar da kanta mai daraja a idon kowa ta zamo sarauni a idon mijinta, akwai shu'umar humra, sayan na gari maida kuɗi gida, banda karanta yayin gyara Hajia.
Zaku iya samun kayyakina a duk garin da kike, zakiyi min mgn ta whatsApp number na 09097853276 domin yin zaɓinki, ko karin bayani, zaki tura kuɗin ta account na 0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU in mun gama mgna zan sa miki kaya a mota yazo duk garin da kike, in baki shirya saya yanzuba Please kada mu wahal da juna ki bari sai kin shirya kafin kiyi min mgn.
🤝🏻🥰😘 Daga taku AYSHA ALIYU GARKUWA
*(GARKUWAR MA'AURATA)*
Isrehjɗɗ. Acan Falon Moddibo kuwa zaune yake akan 2sitter hannunsa riƙe da Kofin Tea yana sha time to time zai ɗaga kansa tare da kallon agogon dake manne abango ahankali ya gyara zamansa tare da kurɓan tea dake tiriri ya lumshe idanunsa tare da buɗe su akan agogon cinyarsa ya matse da ƙarfi har saida yaji jikinsa na rawa, ƙara matse jikinsa yayi sabida yadda yake jin M ɗinsa na miƙewa yana harbawa cike da zalama, ɗan gajeren tsakiya yaja, cikin sanyin murya a fili yace.
“J har yanzu baka dawo ba”.
Yayi mgnar kamar Jameel ɗin na gabansa.
Sai kuma ahankali yasa hannunsa tare da laluɓar wayarsa a aljihun sa na hagu da dama jin babu yasa yaja siririn tsaki tare da miƙewa cikin wani irin masifeffen kasala da sanyin jiki mai kashe ilahirin gaɓɓai ya nufi bedroom ɗinsa a kuma lokaci ɗaya zuciyarsa ta buga tare da tsinkewa da masifaffen ƙarfi, da ƙyar ya iya ɗaga ƙafarsa na dama kana ya taka ya shiga Bedroom tare da furta.
“Hasbunallahu wani'imal wakin”.
Jin yanda zuciyarsa ke cigaba da bugawa cikin yanayin tsinkewar zuciya da sanyin jiki ya ɗauki ƙaramar wayar tasa, kana ya dawo falon ya zauna tare da shiga Call log zai kira M Jameel sai kuma kiran Malam Arɗo yashigo wayar sa.
Zubawa screen ɗin wayar ido yayi tare da jan siririn tsaki kamar ba zai ɗaga ba sai wata zuciyar tace ka ɗaga mana kasan menene Uzirinsa ajiyar zuciya ya sauƙe tare da picking.
Acan ɓangaren Ummi kuwa zaune take a falonta kan kujera 3sitter tayi ta tagumi da duka hannunta biyu, kana ta tsirawa waje ɗaya Idanu yayin da ƙirjinta ke bugawa da masifar ƙarfi zuciyarta na tsinkewa yana bada sautin dif-dif-dif lokaci ɗaya taji wata muguwar kasala na rufe mata jiki haka nan take jin zuciyarta na tsinkewa.
Jiki a mace Asma'u ta fito daga kichen hannunta riƙe da Plate ƙara sawa falon tayi Idanunta akan Ummi data zabga tagumi ta zauna akan 1sitter tare da cewa.
“Ummi har yanzu baki kwanta ba?”.
Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe tare da fesar da numfashi kana ta gyaɗa mata kai tare da cewa.
“Eh Asma'u ban kwanta ba”.
Cike da kulawa Asma'u ta ɗaga kanta tare da kalli agogo, tare da cewa.
“Ummi kalli fa har sha ɗaya ta wuce me kikeyi afalo ke kaɗai shiru ga Abban mu yashiga tun ɗazu”.
Lumshe Idanu Ummi tayi still zuciyarta na tsinkewa kana tace.
“Babu”.
Numfashi Asma'u ta fesar tare da ajiye cokalin dake hannunta tace.
“Toh Ummi ko dai baki da lafiya ne?”.
Kallonta Ummi tayi tare da girgiza kai.
“Lafiyata ƙalau Asma'u”.
“Ayyah Ummi am to mai yasa baki kwanta ba kin zauna shiru ke kaɗai dubi yanda kika yi tagumi da hannu duka bibbiyu”.
Cewar Asma'u.
“Ban sani ba Asma'u ba wai bani da lafiya ba amma ina jin jikina wani iri bai min daɗi ba ina jin zuciyata na tsinkewa sannan ga wata kasala data rufe ni”.
Ido Asma'u ta zuba mata kamar mai son gane wani abu sai kuma tace.
“Toh Ummi ki riƙa maimaita Hasbunallahu wani'imal wakin mana kuma may be rashin bacci ne kinga jiya kwana mukayi muna hira ba kisamu kinyi wadataccen bacci ba, sannan yau da safe ma baki samu kinyi wani ishesshen bacci ba”.
Gyara riƙon da taiwa plate ɗin tayi kana taci gaba da cewa.
“Har yanzu ma baki samu kinyi Ummi, kiyi ƙoƙari kije ki kwanta Insha Allah zakiji dama dama”.
Kai Ummi ta jinjina tare da cewa.
“Toh ki maida Plate ɗin kichen idan kin gama sannan ki rufe ƙofar kichen ɗin kana kizo ki rufe mana ƙofan falon”.
Kai Asma'u ta gyaɗa tare da cewa.
“Toh”.
Ta mike tare da ajiye Plate din ta kife Sauran abincin sannan ta rufe ƙofar tare da murza mukulli ta dawo.
Still zaune ta samu Ummi tayi tagumi.
Cike da kulawa tace.
“Ummi kije ki kwanta dan Allah kiyi baccin”.
Ahankali Ummi ta ɗago ta kalleta tare da sauƙe ajiyar zuciya kana tace.
“Toh kije Insha Allah yanzu zan kwanta”.
Kai Asma'u ta gyaɗa kana ta wuce Bedroom ɗin ta Ummi kuwa kasa tashi tayi ahankali ta lumshe Idanunta tare da komawa ta kwanta akan kujeran still zuciyarta na cigaba da tsinkewa tana mai maimaita kalmar Hasbunallahu wani'imal wakin aƙasan ranta.
Acan ɓangaren Moddibo kuwa yana Picking call ɗin yakai kunnensa tare da cewa.
“Assalamu Alaikum”. cikin sanyin murya M Arɗo ya gyara zaman wayar akunnensa tare da cewa.
“Wai yanzu yaran nan tsakanin ku da Allah kun bar batun karantarwa Amakarantar nan kenan?”.
Anutse Moddibo ya lumshe Idanunsa kana ya buɗe su cikin yanayin kasala da tsinkewar zuciyar da yake ji ya gyara zamansa tare da cije lips ɗinsa na ƙasa yace.
“Toh ka asamsa Sallamar da nayi maka mana Before ka fara ƙorafi da zakayi”.
Girgiza kai Malam Arɗo yayi tare da cewa.
“Toh Wa'ailaikum salam kune ai baki ɗaya kuke son caza min kai, baki ɗaya satin nan yashiga har ya fita amma baku zoba toh gashi yau jumma'a gobe Asabar za akoma shiyasa nace bari na kira ku kada ace baku zoba”.
Iska mai zafi Moddibo ya fesar daga bakinsa tare da shafa sajensa kana ya lumshe idanunsa tare da cewa.
“Gaskiya baza mu zoba”.
Asanyaye Malam Arɗo yace.
“Toh meyesa”.
Muskutawa Moddibo yayi tare da gyara zaman wayar akunnensa kana yace.
“Ai mun riga da mun gama yi maka magana kayi haƙuri kawai ”.
“Amma kunsan ina son koyar wanku Amakarantar nan ina jin dadin zama daku sannan ɗaliban ma suna jin daɗin koyarwanku, makaranta na ya cigaba adalilin kune kada kuyi min haka”.
“Malam kayi haƙuri da akwai Uzurin da yake gaban mu, wanda yafi wannan na tabbata badan wannan Uzurin ba babu dalilin da zaisa mubar koyar wa Amakarantar”.
Cikin sanyi murya Malam Arɗo ya sauƙe Ajiyar zuciya kana yace.
“Toh shikenan tunda abin ya zama haka dole in sawa zuciyata haƙuri amma kusa marmin wasu Malamai masu Hazaƙa, duk da nasan da wuya asamu kamar ku tabbas nasan nayi rashin zaƙaƙuran Malamai kamar ku”.
Kai Moddibo ya gyaɗa kana cikin sanyin murya yace.
“Toh ba matsala zamu yi kokarin hakan”.
Cikin sanyi Malam Arɗo yace.
“Toh Nagode saida safe”.
kana ya katse wayar.
Moddibo kuwa cikin sauri zuciyarsa ya cigaba da bugawa yana bada sautin dif-dab-dif-daf ahankali ya ɗago wayar da niyyar kiran M Jameel cikin wani Irin yanayi ya dafe saitin ƙahon zuciyarsa jin yanda yake bugawa da azabebben ƙarfi yana cigaba da bada sautin dif-dif-dif rintse idanunsa yayi still hannunsa na dafe da saitin ƙahon zuciyarsa.
Acan ɓangaren Gimbiya Bunayya kuwa har Misalin ƙarfe sha biyu da minti biyu na dare Uncle Naseer da Amina na zaune akan 2sitter suna hira.
Yayin da ita kuma ke kwance a Bedroom ɗin ta kunneta maƙale da waya tana Magana da Hajiya Lami.
Murmushi Hajiya Bunayya tayi tare da cewa.
“Hajiya Lami ni dai yanzu Alhamdulillah buƙata ta biya hankalina ya kwanta, yanzu batun soyayyar Amina da Naseer ya kankama yayi zurfi”.
Atake fara'ar dake fuskanta ya gushe ta mike ta zauna tare da cewa.
“Yanzu kuma hankalina ya koma kan ƴaƴan wannan shegiyar matar mai kama da Mayyar wannan yaro mai ƙwala-ƙwalan ido daya karye nake son kawar dashi tun da shi wancan mai kama da Brolas ɗin Uwarsa ta shayar dashi saɓani, tunda kinga wannan hatsarin ma shi na shiryawa abi takansa amma, ba'a samu babban ba akabi takan ƙaramin”.
Sai kuma ta sauƙe numfashi tare da jan dogon tsaki kana tace.
“Dole saina koma na samu boka Kar'uzu da maganar ayi duk abinda za ayi nikam Haiydar shine babban matsala ta tunda shi Ramadan shine ƙarami akan Aminu, babu yanda za ayi Aminu na raye aɗauki Sarauta abawa Ramadan dole dai sai ɗana ɗin dai”.
Cikin sauri Hajiya Lami ta katseta tare da cewa.
“Kul-Kul Hajiya Bunayya kada kiyi la'akari da wannan ƙaramin tunanin naki, ba kiji Malam Bahaushe na cewa ɗan hakin daka raina shike tsole maka Ido ba?.
To ki rufa wa kanki asiri ki kawar dasu duka biyun hankalinki ya kwanta ki samu nutsuwa da salama aranki”.
Kana ta saki wani murmushi tare da cewa.
“Kinga idan kika gama dasu ɗaya ce zaki samu nutsuwa akanta itace Raudat da kuma Khausar.
Kinga Khausar kuwa ba ƴar gidan bace babu yanda za ayi agola tavi gadon Sarauta koda na mijine bare kuma mace. Raudat kuwa ƙarama ce kuma mace.
Amman Haiydar da Ramadan dai kaudasu, da kike batun Ramadan shine ƙarami a kan sulaiman, sau nawa manyan Yayu ke zaune ake bawa ƙannen su Sarautar, ni dai shawarar da zan baki yanda zaki gama da Haiydar haka zaki gama da Ramadan”.
Jinjina kai Hajiya Bunayya tayi tare da gyara zaman wayar akunnenta kana tace.
“Haka ne fa kuma aini duk wannan tunanin bai zo min ba, atunanina idan na kawar da Haiydar shikenan”.
Girgiza kai Hajiya Lami tayi tare da faɗin.
“A'a tsaya kallon ruwa kwaɗo ya miki ƙafa, har kina wani batun shine ƙaramin akan Aminu ai ba'a wannan zancen kima rufawa kanki asiri, kigama dasu gaba ɗaya to asannan hankalin zai kwanta, ki samu nutsuwa anan ne zaki tabbatar sarauta ahannun Aminu take, ke kuma kin zama Gimbiyar Gembulan Matar sarki Uwar sarki amma muddin ƴaƴan wancan koɗaɗɗiyar matar na nan keda Saurauta saidai hange daga naisa”.
Jinjina kai Hajiya Bunayya tayi cike da gamsuwa kana tace.
“Aikuwa hakane Nifa duk wannan tunanin bai zomin ba shiyasa nake alfahari dake ƙawata.
Insha Allah zanje muyi magana da boka Kar'uzu asan yanda za'a ɓullowa lamarin”.
Kai Hajiya Lami ta gyaɗa tare da cewa.
“Eh nima Insha Allah gobe idan muka je zan faɗa masa ya tsaida rana da Samira zata fara zuwa wajensa suyi satin, tunda dai yace idan ya kusance tama zai mayar mata da budurcinta ai shikenan”.
Atare suka sheƙe da dariyamai cike da farin ciki da annushawa kana Hajiya Bunayya tace.
“Ai dai haka yafi shiyasa na yarda da aikin Boka Kar'uzu kamar yankan wuƙa dan sha yanzu magani yanzu ne tun yaushe muke bin boka bursunu tsawon shekaru ba biyan buƙata sai asaran kuɗi”.
Jinjina kai Hajiya Lami tayi kana tayi mata Sallama suka katse wayar.
Aɓangaren Abban M Jameel kuwa tsaye yake ajikin window falonsa ya tsirawa harabar gidan Ido tun bayan fitar Motar M Jameel ya kasa motsa wa daga wajen.
Hajiya Karima data fito daga Bedroom ɗin sa ta dubesa cike da kulawa tace.
“Ya dai Alhj tun tuni kana tsaye ana ka gaza motsa sama da awa biyu kenan tun bayan fitar motar Jameel kake tsaye lafiya kuwa?”.
Cikin wani irin yanayi ya lumshe idonsa.
Haka nan yaji ruwan hawaye na tsats-tsafo masa a hankali ya sauƙe ajiyar zuciya tare da furzar da iska kana yace.
“Haka nan dai narasa me nake tunawa awajen nan”.
Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da dafa bayansa kana tace.
“Toh kazo ka zauna mana”.
Girgiza kai yayi tare da fesar da numfashi kana cikin sanyi murya yace.
“Ina ga ko dan garin dana gani da alamun hadari ne ko yaya ne ban sani ba”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Toh kadawo ka zauna dan Allah tsayuwar tayi yawa”.
Kai ya gyaɗa lokaci ɗaya yaji wani irin masifaffen rauni mai haɗe da bugun zuciya ya rufe sa Atake yaji Idanunsa na tsats-tsafo da ruwan hawaye masu ɗumi yayin da zuciyarsa ya cigaba da tsinkewa jikinsa na mutuwa tamkar ana zare masa laka cikin sanyi jiki yaja ƙafafunsa da yaji sunyi masa mugun nauyi ya zauna akan kujera tare da kwanciya akan 3sitter kana ya lumshe Idanunsa.
Cike da kulawa tace.
“Ya dai lafiya kuwa kashiga ciki mana?”.
Girgiza kai yayi still zuciyarsa na cigaba da bugawa yayinda muryarsa ke ɗauke da rauni yace.
“Please Karima ki barni in kwanta inaji kamar kaina na ciwo”.
Cikin sauri tace.
“Alhj kad dai BP kane?”.
Girgiza kai yayi still Idanunsa na lumshe yace.
“A'a ba BP na bane bari dai mu gani”.
Zama tayi daga hannun kujeran kana tace.
“Toh kasha maganin ka kuwa?”.
Kai ya gyaɗa tare da cewa.
“Eh sosai ma yan zun nan kafin Jameelu ya fita ya bani nasha”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Eh ƙwarai kuwa hakane toh Allah ya sawwaƙa”.
Ahankali yace.
“Ameen”, Miƙewa tayi tare da shiga Bedroom ɗin sa ta kwanta.
Ɓangaren Moddibo kuwa har Misalin sha biyu da kwata yana zaune dafe da ƙirjinsa dake cigaba da bugawa ahankali ya ɗago kansa tare da shafa gefen wayarsa haske ya bayyana tare da nuna masa ƙarfe 12:15 afili ya furta.
“Har yanzu J bai zoba”.
Yayi mgnar tare da shiga Call log yayi dearling number M Jameel amma ga mamakinsa sai yaji Swich off.
Cikin yanayin damuwa ya dafe kansa tare da cewa.
“Ikon Allah lafiya kuwa wayar J arufe?”.
Kallonsa ya mayar kan babbar wayarsa tare da ɗauka kana ya fito da ɗaya number M Jameel ya kira Shima still Swich off.
Miƙewa tsaye yayi ido a lumshe yace.
“Ha'a ya wayar J akashe kuma dai J baya kashe wayarsa, to amma mai yafaru yau wayarsa akashe toh me yake faruwa bayan ya faɗa min yau zai dawo!?”,l.
Yayi maganar cikin zulumi
“Ya ilahi ya mujabat da'awati, to kuma ko kafin J ya fito sai da ya kirni yace zaije wajen Abba ya sallame sa sannan yazo amma kuma har yanzu bai zoba”.
Atake wata zuciyar tace kasani ko yazo suna tare da Innayi suna can suna ƙus-ƙus atake ya amince da abinda zuciyarsa ya raya masa cikin mutuwar jiki ya nufi ƙofan falonsa tare da buɗewa.
Wani sanyayyan iska ya hurasa ahankali ya ɗaga kansa sama gani yayi hadari ya fara haduwa sai walƙiya dake haskawa can ƙasa alamun yanzu hadarin ya fara, garin ya danyu duhu sakamakon rashin wuta ga kuma hadarin,
ahankali yabi sararin samaniyar da kallo ganin yanda hadarin yayiwa garin zobe kana aƙasan ransa yace to kodai wannan hadarin ne ya hana J zuwa sai kuma yace to kodai yana ɗakin Innayi ya faɗa yana taka step ɗin ahankali.
Cikin sauri Innayi ta haske masa ido da touch light mai masifar haske cikin han zari ya Janye hannuunsa dake danne da J ɗinsa ya tare Idanunsa dashi saboda hasken touchlight daya haska masa ido.
Cike da kulawa Innayi tace.
“Moddibo ya dai lafiya ina zuwa Atsakiyar adaren nan?”.
Ahankali ya sake sakƙowa daga kan step ɗin tare da jingina bayansa da jikin filan barandarsa, kana hannunsa na dama na kan flowes dake gefe yace.
“Kece fa kike ganinsa tsakiyar dare ne, dudu shabiyu da rabi ne fa yanzu”.
Kallonsa tayi tare da cewa.
“Tsakiyar dare ne mana Moddibo yanzu fa ƙarfe shabiyu harda rabi ai tsakiyar dare ne, to amma me kafito yi lafiya dai ko?”.
Cikin sanyin murya yace.
“J ne har yanzu bai zo ba kuma ya fito akan zai zo ma ya kirani awaya kan cewa yanzu zai shiga wajen Abbansa ya masa saida safe ya fito, kuma har yanzu bai iso ba sannan nata kiran layukan sa basa shiga”.
Ya ida maganar akasalance.
Ajiyar zuciya Innayi ta sauƙe tare da cewa.
“Toh dan bai zoba Moddibo ai ba abin tashin hankali bane, kaga yanayin wannan hadarin daya haɗu zai iya hanasa zuwa wataƙil daya shiga wajen Abban nasa zaice dare yayi kuma ga hadari ya bari sai gobe”.
Da sauri ya katseta da cewa.
“To ai Innayi wayarsa bata shiga fa”.
Saurin Kallonsa Innayi tayi tare da cewa.
“Ka kira layinsa duka?”.
Kai ya jinjina mata.
“Eh na kira layukansa duka fa basa shiga”.
Cikin yanayin bacci ta kalli Moddibo tare da sakin hamma kana ta aro Jarumtaka tare da cewa.
“To ko dai network ne?”.
Lumshe Idanunsa yayi tare da Girgiza mata kai kana yace.
“A'a ba network bane cemin akeyi akashe kuma fa Innayi J baya kashe wayarsa, ko zai kwanta komai yaya kuma nasan wayar J baya rasa caji”.
A hankali Innayi ta rufe idonta jin kamar tsinkewar zuciya ya ziyarci ta.
Amma sai ta daure kana tace.
“To amma kaga jiya ma kace min wajen Umminsa ya kwana to ko dai yauma yaje canne ne ya kashe wayarsa dan kada kayi ta kiransa?”.
Jinjina kai yayi tare da faɗin.
“Ok ba mamaki fa bari na kira Ummi”.
Cikin sauri Innayi ta kallesa tare da cewa.
“Aƙarfe ɗaya saura zaka kirasu?”
Kai ya gyaɗa kana yace.
“Eh Innayi in dai har wurin Ummi yake nasan yanzu zasu ganshi kamar takwas na dare ne, saboda nasan yanzu suna hira ba suyi bacci ba.
Kai Innayi ta gyaɗa tare da gyara tsayuwar ta kana tace.
“Toh shikenan ka kira”.
Dearling number Ummi yayu.
Acan ɓangaren Ummi kuwa kwance take yayin da idanunta ke lumshe cikin tsananin tsinkewar zuciya da kasala jin rurin wayarta yasa ta miƙe firgice cikin yanayi sanyi sanya hannunta na dama ta janyo wayar tare da ƙurawa screen ɗin Ido sunan Moddibo ke yawo.
Cikin sauri tare da rawan jiki tayi Picking call ɗin tare da kaiwa Kunnenta batare data amsa Sallamar daya mata ba tace.
“Babana Lafiya?”.
Cikin ƙoƙarin danne damuwarsa yace.
“Ummi lafiya ya naji kamar kin razana?”.
Ahankali ta koma ta jingina bayanta da jikin kushin ɗin tare da lumshe idanunta kana cikin wata raunan'niyar murya mai cike da kasala da tsoro ta fesar da numfashi tare da cewa.
“Gaba ɗaya ma ai. Arazanen nake Babana”.
Moddibo kuwa cikin kasala da mutuwar jiki ya yaja numfashi tare da fesar wa kana yace.
“To Ummi me yafaru?”.
Buɗe Idanunta dake lumshe tayi tare da dafe ƙirjinta da still yake bugawa kana tace.
“Ban saniba amma gaba ɗaya ina jina wani irin gani nan dai kamar mara lfy, kuma ba zance ga abinda yake damuna kai tsaye ba”.
Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe kana yace.
“Toh amma Ummi lafiyar ki lau?”.
Kai ta gyaɗa masa kamar yana gabanta kana tace.
“Lafiya ta ƙalau,Amma Babana lafiya ka kira yanzu?”.
Numfashi ya sauke tare da lumshe idanunsa kana ya sake jingina bayansa da jikin step ɗin tare da cewa.
“Eh lafiya lau babu komai dama zan tambayeki ne ko dai J yazo yana wurinki ne munyi dashi tun ɗazu akan zai zo har yace min gashi ya fito amma zai sallami Abbansa ne kawai ya taho”.
Sai kuma ya lumshe idanunsa tare da cijan lip ɗin sa na ƙasa kana yace.
“Amma har yanzu be taho ba, inata jiran sa ko ƙofar gida bamu rufe ba, shiyasa nace bari na kira koya biya wajenki, da yake jiya ma nan ya kwana!?”.
Rumtse ida nunta tayi da masifar ƙarfi k cikin wani azabebben tsinkewar zuciya da faɗuwar gaba ta buga hannunta na dama aƙirji tare da cewa.
_“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n. Allahumma Ajirni fii musibati wa'ahlifli khairan min_
bai zo ba kuma yace maka zai zo?
Abbansa kaɗai zai Sallama?”.
Gyaɗa kai Moddibo yayi tamkar yana gabanta kana cikin raunan'niyar murya mai cike da sanyi yace.
“Eh Ummi”.
Cikin wani irin yanayi na taraddadin zuciya da rauni Ummi tace.
“Ya Ubangiji Allah ka dubeni da Idon Rahma. Ya Allah ka tsare wannan bawan naka, aduk inda yake Alfarman Annabi da Alkur'ani”.
Jin salatin da kuma yanayin da Ummi tayi Magana cikin firgici ya farkar da Asma'u, Bashir da Malam Ahmad Aruɗe Asma'u ta miƙe tare da dafe kanta da taji yayi masifar sarawa ta sauƙa daga kan gadon.
Acan ɗakin Bashir kuwa Hasbunallahu wani'imal wakin ya furta tare da sauƙa ƙasa kusan atare suka fito falon ko wannensu zuciyarsa na bugawa da kaso tamanin cikin ɗari.
Moddibo kuwa cikin sanyu da ruɗu yace.
“Ameen ya Allah Ummi ameen ya rabbil Izzati”.
Cikin zulumi Ummi ta runtse Idanunta kana tace.
“Amma Babana ka kira Abbansa mana”.
Numfashi Moddibo ya fesar tare da kallon Innayi data tsaresa da ido cikin yanayin razani yace.
“Eh Ummi nayi tunanin kiran Abbansa amma sai nace bari na fara kiranki tunda jiya yazo na, sannan Ummi nasan J baya kashe wayarsa rashin shigar wayarsa nema yafi damuna!”.
Girgiza kai Ummi tayi yayinda ruwan hawaye masu masifar ɗumi suka cika kwarmin Idanunta kana cikin raunan'niyar murya tace.
“Tabbas baya kashewa ka kira Abbansa kaji”.
Kai ya gyaɗa kana yace.
“Eh dama zan kirasa amma Innayi tace ko Abbansa ne ya hanasa zuwa ganin hadari”.
A hankali tace.
“Anya?,Ka kira sa dai”.
“Amma yanzu dare baiyi ba Ummi”.
Cikin sauri tace.
“A'a ka kira Babana ka kira Abbansa ɗin duk yanda kukayi ka kirani ka sanar min”.
“Toh”.
Moddibo yace kana ya katse kiran.
Asma'u da Bashir kuwa zuru-zuru sukayi da ido domin suna iya jiyo sautin muryar Modibbo.
Durƙusa wa Asma'u tayi tare da toshe bakinta kana tashiga.
Girgiza kanta tare da cewa.
“Ya Allah kada ka jarabcemu da abinda baza mu iyaba ɗaukaba Allah ka tsare Yaya Jameel aduk inda yake ya Allah kada ka bari wani abu na cutarwa ya sameshi”.
Cikin raunin murya Ummi ta kalleta Atake taji wasu hawaye masu masifar ɗumi sun zubo kuncinta.
Ahankali Malam Ahmad da jikinsa yayi masifar sanyi ya ƙarasa kusa da Ummi.
Moddibo kuwa yana katse kiran ya shiga contact tare da fito da Number Abban M Jameel.
Kana ya Kalli Innayi cikin sanyin murya mai cike da tashin hankali yace.
“Kin gani ko Innayi baya can. J baije gidan Ummi ba. Innayi ina J ya tafi bayan yasanar dani cewa zai taho”.
Lokaci ɗaya wani masifaffen tsoro da tashin hankali ya ziyarci Innayi wanda ta kasa ɓoyewa har hakan ya bayyana asaman fuskarta dake nuni da tsantsar ruɗu.
Cikin dakiya da kuma nuna masa babu komai insha Allah ta gyara tochligt dake hannunta kana tace.
“Ka dai kira Abbansa muji wataƙil yana can tare dashi hadarin ne ya hanasa fitowa”.
Kai ya gyaɗa mata tare da dearling number Abban M Jameel yana jin yanda zuciyarsa ke cigaba da bugawa da masifar ƙarfi yana bada sautin dif-dumm-dif dumm.
Abba dake kwance kan 3sitter Idanunsa arufe bacci ya fara fusgarsa yaji suwwan wayarsa Atsakiyar kansa afirgice ya miƙe tare da zama kana ya duba screen ɗin wayar nan yaga sunan Moddibo na yawo cikin rawan jiki yayi Picking.
Atare Abba da Moddibo sukayi Sallama.
Ahankali Moddibo ya sauƙe numfashin tare da ƙoƙarin dai-dai-ta nutsuwarsa kana yace.
“Wa'alaikum Salam Abba”.
Cikin yanayin firgici da ruɗu Abba ya sauƙe ajiyar zuciya tare da cewa.
“Na'am Aliyu ya akayi?”.
Numfashi Moddibo ya fesar kana yace.
“Lafiya Abba”.
Kai Abba ya gyaɗa tare da jingina bayansa da jikin kushin kana yace.
“Ya gida kowa lafiya dai?
Jameelun yaƙara so yana lafiya ko?”.
Lokaci ɗaya zuciyar Moddibo ya buga da masifar ƙarfi kana yayi saurin dafe ƙirjinsa tare da cewa.
“Abba baya gidane”.
Wani irin azabebben bugawa zuciyar Abba yayi kana yace.
“A'a bakwa tare ne tun 10:15 ai ya sallameni yace min zai taho wurinka”.
Moddibo kuwa da sauri ya rumtse idanunsa tare da dafe jikin step ɗin yana mai jin kansa na masifar sarawa tamkar zai rabe gida biyu cikin raunin murya yace.
“Abba tun ƙarfe 10:15 ya fita kuma yace wajena zai zo? Abba tun ɗazu fa nake jiransa ko ƙofar gida bamu rufe ba har yanzu J bai zoba sannan fa nata kiran layukan basa shiga”.
Cikin tsananin razani da tsinkewar zuciya Abba ya miƙe tsaye kana yace.
“Aliyu mai kace?”.
Araunane Moddibo da Idanunsa ke juyawa ya dafe kansa kana cikin sanyin murya yace.
“Abba na yita kiran layinsa baya shiga”.
A ruɗe Abba ya miƙa tsaye tare da cewa.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n to lafiya Aliyu?”.
Girgiza kai Moddibo yayi tare da gyara tsayuwar sa kana yace.
“Toh Abba kuma yace waje na ɗin zai taho?Abba J bai zoba bafa”.
ya ida maganar cikin raunin murya mai cike da tsantsar tashin hankali.
Atake zufa ya wanke wa Abba jiki duk da iskar dake kaɗawa d ƙarfi ya haɗiye wani abu mai ɗaci kana yace.
“Ko dai gidan Ummin sa yaje”.
Da sauri Moddibo ya girgiza kansa muryarsa na rawa yace.
“Um-um Abba baya can yanzu nayi waya da Ummi itace ma tace in Kira ka Dan ni Ina tunanin dare ma yayi bazan kira ba”.
Cikin tsinkewar zuciya Abba ya nufi ƙofar falon Hajiya Karima da sautin muryansa ya farkar da ita tayi saurin fitowa daga Bedroom ɗin Aruɗe ta kallesa kana tace.
“Lafiya Alhj?”.
Girgiza kai Abba yayi tare da cewa.
“Jameelu ba agansa ba wai baije wajen Moddibo ba sannan baije wajen Umminsa ba”.
Da sauri ta dafe ƙirjinta kana tace.
“Ba agansa ba kuma gashi yanzu ƙarfe ɗaya”.
Kasa cewa komai Abba yayi ya nufi ƙofa da sauri.
Tare da cewa.
“Miƙo min key mota”.
Cikin sauru tabi bayansa tare da Kallonsa ganin Gajeren wando da single ne kaɗai ajikinsa yasa tace.
“Toh yanzu ina zaka je adaren nan??”.
Cikin raunin murya yace.
“Karima ina zanje kike tambaya ta? Jameelu na fa baya gidansu Aliyu sannan baya gidan Umminsa to ina Jameelu yaje kinsan waye Jameelu da in dai baya nan yana gidansu Aliyu ko gidan Umminsa tabbas da akwai abinda yake faruwa”.
Cikin sauri ta juya tare da komawa Bedroom ta dauƙa Masa Jallabiya da key mota kana ta sanya hijabinta ta fito tare da miƙa masa.
Karba yayi yana tafiya yana saka jallabiyar kana ya nufi inda Motarsa yake ya shiga cikin sassarfa tabi bayansa yana shiga mazaunin Driver itama tayi saurin buɗe gefen mai zaman banza ta Zauna.
Kallonta yayi tare da cewa.
“A'a ki koma”.
Girgiza kai tayi tare da cewa.
“A'a Alh ya za'ayi in barka ka tafi kai kaɗai muje dai”.
Kai ya gyaɗa batare da yace komai ba ya figi motar.
Suka tafi bayan mai gadi ya buɗe masa ahankali ya fara bin hanyar Yana dudduba gefen titin kana cikin sanyin murya yace.
“To ko dai motarsa ta samu matsale ne?”.
Girgiza kai Hajiya Karima tayi kana tace.
“Idan ma motarsa ta samu matsala Alh ai saidai ya kira akawo masa wata”.
Kai ya jinjina still Yana cigaba da Driving ɗin yayin da zuciyarsa ke cigaba da bugawa da kaso Cassa'in cikin ɗari suna cikin tafiya har suka isa gidan su Moddibo.
Moddibo dake tsaye coumpund ɗin har zuwa lokacin ya gagara koda ƙoƙƙwaran motsi yayi saurin kallon gate ɗin ganin hasken mota Itama Innayi dake tsaye tayi saurin bin wajen da kallo zuciyarta na cigaba da bugawa.
Cikin sauri tare da rauni yace.
“Toh waye wannan ko dai motar J ne?”.
Ya faɗa tare da nufar gate ɗin Innayi kuwa ido ta zuba masa har ya buɗe gate.
Moddibo kuwa yana buɗe gate din idanunsa suka sauƙa akan motar Abba.
Cikin sauri ya ƙarasa jikin motar tare da cewa.
“Abba kaine?”.
Jinjina kai Abba yayi asanda ya ƙarasa fita daga motar kana cikin raunin murya yace.
“Eh Nine Aliyu ina tsammanin Jameelu yana nan to idan ba nan ba ina Jameelu zai je adaren nan.
Amma anya ka bin cika baya gidan Umminsa ba wasa take mana ba?”.
Girgiza kai Moddibo yayi cikin mutuwar da jiki da rauni yace.
“A'a Abba baya can tunda nayi magana da Ummi kuma yanzu da muka gama waya da kai ma na kirata nace baya can itama kuka fa takeyi”.
Cikin ruɗu da rashin sanin madafa Abba yace.
“Toh kazo muje can ɗin mu duba may be ko motarsa ta ɓaci ahanya can ya nufa”.
Kai Moddibo ya gyaɗa tare da faɗin.
“To bari in ɗauki motata dan nasan Innayi ma bazata zauna ita kaɗai agida ba”.
Ya faɗa tare da shigewa cikin gida kai tsaye falonsa ya nufa ya ɗauki key sannan suka fito da Innayi acikin motar.
Motar Modibbo ce ta shiga gaba na Abba na biye da ita tuƙi kawai Moddibo yake amma baki ɗaya baya cikin nutsuwarsa.
Acan gidan Ummi kuwa tunda Moddibo ya sanar mata M Jameel baya gidan Abba hankalinta yayi masifar tashi ta fito coumpund ta tsaya tana kuka yayinda Asma'u da Bashir ke taya ta cikin tsanananin kaɗuwa.
Cikin rarrashi da nasiyya Malam Ahmad ke tausanta dasu Asma'u.
Cikin sauri Ummi ta ɗaga kanta ganin hasken motoci abakin gate ɗin gidan su.
Aruɗe ta kallesa tare da cewa.
“Ka kalli hasken mota Malam ko dai Jameelu ne?”.
Cikin sanyin murya yace.
“Ki kwantar da hankalin ki Fatima dan Allah ki nutsu Insha Allah babu komai, ba abinda zai samu Jameelu”.
Kai ta girgiza kana tace.
“A'a to ai naga hasken mota ne”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da riƙe hannunta ganin yanda ta firgice kana yace.
“Toh bari naje na duba naga ko waye ne”.
Kai ta girgiza kana cikin raunin murya tace.
“A'a to muje dai”.
Kai ya gyaɗa tare da yin gaba kana tabi bayansa Malam Ahmad na buɗe ƙaramar ƙofa yaga motar Moddibo daf da bakin gate Dai-dai lokacin Moddibo ya buɗe Murfin motar ya fito.
Cikin sauri Ummi ta kallesa tare da leƙa motar dake bayansa kana tace.
“Babana”.
Cikin sanyin murya yace.
“Na'am Ummi J bai zo nan ba dagaske?”.
Cikin muryan kuka ta girgiza kai kana tace.
“A'a bai zo bafa Babana idan yazo ya za ayi in ɓoye muku”.
Cikin mutuwar jiki Abba ya buɗe Murfin motar tare da fita kana ya kalli Ummi da hawaye ke bin kuncinta yace.
“Fatima”.
Saurin Kallonsa Ummi tayi tare da cewa.
“Abban Jameel”.
Cikin yanayin tashin hankali yace.
“Da gaske Jameelu bai zoba?”.
Kai ta gyaɗa Masa still Hawaye na bin kun cinta tace.
“Bai zoba kuma nata kiran wayoyinsa basa shiga”.
Cikintashin hankali da ruɗu suka haɗa baki wajen furta.
_“Innalillahi Wa'inna Ilahi rajiu'n Allahumma Ajirni fii musibati wa'ahlifli khairan minha”_.
Cikin sanyi Moddibo ya kalli Abba da idanunsa suka sauya launi saboda tashin hankali kana yace.
“Abba mu koma ta hanyar gidaku mu duba ko dai motarsa ta samu matsala ne ko kuma yayi hatsari ne?”.
Kai suka gyaɗa cikin sauri Ummi ta juya tare da kallon Moddibo kana tace.
“Bari na ɗauko hijabina muje tare”.
Bata jira jin abinda zasu ce ba ta juya da sauri ta koma tare da ɗaukan hijabinta ta fito coumpund ɗin kallon Asma'u da Bashir tayi wanda har zuwa lokacin suna cikin ruɗani, cikin Muryan kuka tace.
“Asma'u ku kula da kanku zamu duba hanya ko Allah zaisa mu gansa”.
Cikin sauri Asma'u tace.
“Ummi zamu biku”.
Girgiza kai Ummi tayi tana tafiya tace.
“A'a ku zauna kada ku fito”.
Daga haka ta fice Malam Ahmad na ƙoƙarin ɗauko mota Moddibo yace.
“Ummi kuzo ku shiga motata kawai”,
Kai ta gyaɗa kana tashiga bayan motar kusa da Innayi.
Malam Ahmad kuwa a gaba, kana suka fara tafiya koda da irin tunanin da yake Aransa duk wani inda suke tunanin mota zai iya maƙalewa ko kuma hatsari sun duba amma babu M Jameel da motarsa babu dalilinsa har unguwar su Abba suka koma amma still Babu shi babu dalilinsa.
Cikin yanayin gajiyawa da ɗimuwa Abba ya buɗe Murfin motar ya fito kana Moddibo da sauran ma duk suka fito.
Cikin raunin murya me nuni da razani Abba yace.
“Gashi mun biyo har nan ma amma baya nan, to mu gwada zuwa asibiti mu duba ko dai yayi hatsari ne ko yaya”.
Cikin raunin murya Moddibo ya Girgiza kai kana yace.
“Abba hatsari kuma? Ai da hatsari ne da munga mota kuma da ankira mu”.
Kafin Abba yace wani abu Innayi ta kalli Moddibo tare da cewa.
“Eh muje dai asibitin saboda Kore shakku”.
Jinjina kai sukayi tare da shiga motar kana suka nufi Asibitin.
Ahankali Moddibo ya kalli Innayi kana yace.
“Toh wani asibitin zamuje kin san dai bawasu manyan asibiti muke dasu ba”.
Cikin sanyi malam Ahmad yace.
“Mu fara zuwa babban asibitin idan yaso sai mu duba sauran daga baya”.
Kai Moddibo ya gyaɗa tare da nufar babban asibitin Abba na biye dasu.
Suna isa suka tarar da gate din asibitin arufe kasancewar har biyu tayi,sauran asibitin suka shiga zagayawa amma ko wanne arufe in sun buga an buɗe musuma in sun shiga bashi ba lbrinsa.
Cikin han zari Abba ya cewa Moddibo su nufi Private hospital ɗin Abba haka kuwa akayi.
Suna isa Moddibo ya sauƙa tare da nufar cikin Hospital kana ya tambayi Norse dake aiki ko M Jameel yazo suka ce a'a juyawa yayi ya shiga motar kana suka ci-gaba da nemansa.
Wasa gaske fa babu Jameel ba dililinsa ba motarsa, gaba ɗaya sun shiga ruɗu da zulumi gamida tsoro.
Misalin ƙarfe uku hankalin su ya kai ƙololuwa wajen tashi baki ɗaya sun cika da damuwa zuwa wannan lokacin sun tabbatar ba lafiya domin M Jameel baya yawo sannan Gembulan ba wani babban gari ne da keda charking point ba bare su kai report.
Moddibo kuwa banda tasbihi da kiran sunan Allah babu abinda yake Aransa yayin da kasala da mutuwar jikinsa ke ƙaruwa fiye da farko kana ga hadarin da zuwa yanzu yayi gangami asama da alamar ruwa na gab da sakƙowa, dan tuni aka fara yayyafi.
Abba kuwa tunda suka fito a asibiti ya kifa kansa ajikin motar zuciyarsa na bugawa da masifaffen ƙarfi cikin raunin murya yace.
“Acikin wannan daren ga hadari na kira layukan Jameeluna duka basa shiga a wannan yanayin ina Jamilu na ya shiga”.
Cikin raunin murya mai cike da karaya Modibbo ya fesar da numfashi mai zafi kana yace.
“Yanzu acikin daren nan ina J yake?.
Wani hali yake ciki?.
Wani irin yanayi yake cikin a wannan daren da kuma hadarin da yake tasowa ina J ɗina yake!?”.
Cikin ƙarfin hali Malam Ahmad ya numfasa kana yace.
“Insha Allah ba komai mu bari muga zuwa safiya abinda Ubangiji zai yi”.
Cikin tsanananin rauni Ummi ta kife kanta da jikin kujeran Motar kana ta fashe da wani Marayan kuka mai gunji”.
Cikin damuwa da kuma tausayawa Abba ya juya tare da kallon Malam Ahmad kana yace.
“Malam ku tafi gida kaima Moddibo ku koma gida da Innayi kada ruwan nan ya saƙƙo muna nan duk inda ya kamata mu duba mun duba baya nan bari mu gani zuwa safiya”.
Girgiza kai Moddibo yayi Araunane yace.
“Abba ya za ayi mu koma mu shiga cikin gida mu samu mafaka bayan bamu san halin da J yake ciki ba. Abba ina kake tunanin zamu koma mu samu nutsuwa acikin wannan yanayin bayan bamu san ina J yake ba!?”.
Kallonsa Abba yayi cike da rauni yace.
“Toh Aliyu ina zamuje mu duba?, Duk inda ya kamata mu duba mun duba sannan wayoyinsa basa shiga wannan shine babban tashin hankalina mu koma gida muyi alwala mu sanar wa Ubangiji halin da muke ciki Aliyu”.
Jinjina kai sukayi atare cike da gamsuwa da abinda yace sam tashin hankali da ruɗanin da suke ciki yasa sun kasa samun nutsuwar da zasuyi addu'a.
Kai Moddibo ya gyaɗa kana yace.
“Toh Abba”.
Sannan suka shiga mota Abba yaja ya nufi gidansu cikin tashin hankali da ɗimuwa yayin da Hajiya Karima ke kuka Abba kuwa ko da kallonta ya gagara yi bare kuma ya iya lallashin ta.
Ya yinda Moddibo ya nufi gidan Ummi babu abinda ke tashi acikin motar banda sheshsheƙan Kukan Ummi ta rasa shin wani irin tunani zata yi shin ina Jameelunta yake awannan tsohon daren Akuma irin wannan lokacin.
Moddibo kuwa cikin tsananin damuwa da zulumi da macewar jiki ya cigaba da Driving har ya isa kofar gidan yayi Parking.
Fita Malam Ahmad yayi Ummi ma ta sauƙa suka nufi cikin gidan.
Ganin hasken mota yasa Bashir miƙewa da sauri tare da buɗe ƙaramin gate ɗin.
Cikin sauri Asma'u da har zuwa lokacin take zaune ta ɗago kanta tare da miƙewa ta riƙe hannun Ummi kana tace.
“Ummi Ina Yaya Jameel Ummi kunga Yah Jameel?".
Cikin sanyi Ummu ke jujjuya mata kai.
Ita kuwa a ɗimauce tace. “Ummi to ina yashiga awannan daren dubi hadari fa wani hali yake ciki?”.
Girgiza kai Ummi tayi tare da fashewa da kuka kana tace.
“Ban saniba Asma'u Bansan inda Jameelu na yake ba, bansan halin da yake ciki ba Asma'u zuciyata zafi take jinake tamkar kaina zai rabe gida biyu!”.
Aruɗe Asma'u tace.
_“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n Allahumma Ajirni fii musibati wa'ahlifli khairan minha_, nashiga uku Yah Jameel”.
Cikin sauri Malam Ahmad ya riƙe hannun Asma'u ganin kamar bata hayyacinta kana yace.
“Subhanallah Asma'u da iliminki kike kirawa kanki shiga uku kada ki sake haka Addu'a ya kamata mu masa kunji ko?”.
Kallonsa ya mayar kan Bashir kana yace.
“Kuzo mushiga muyi masa addu'a ayanzu ba kuka Jameelu yake da buƙata daga wajen muba face adduoi”.
Kai suka gyaɗa sannan ya sake hannun Asma'u ya riƙe na Ummi Bashir kuma yarike hannun Asma'u suka shiga ciki kai tsaye ko wannensu toilet yashiga ya ɗaura Al'wala kana ya fito suka shimfiɗa Sallaya tare da fara jera nafillah suna roƙon Allah daya fitar da M Jameel aduk halin da yake ciki.
Moddibo kuwa suna isa gida yayi Parking tare da rufe ƙofar kana ya wuce falonsa yayin da Innayi ma tashige sashen ta yana shiga kai tsaye toilet dake falon ya shiga ya ɗaura alwala kana ya fito ya shimfida Sallaya cike da nutsuwa ya fara Sallah kana duk sujjadar da zaiyi sai ya roƙi Ubangiji ya kare J ɗin sa aduk inda yake”.
Baki ɗaya su haka suka raya wannan daren cike da bautar Ubangiji tare kuma da rokon Allah daya bayyanar da M Jameel kana Allah yaraba sa da duk kan sharrin Mutum da Aljan.
Bayan an kira Assalatu Moddibo ya fito ya nufi masallaci ana idar da sallah kai tsaye gidan Abba ya nufa.
Yana isa kiran Ummi na shiga wayarsa ciki. Sanyin jiki ya ɗaga wayar tare da kaiwa kunnensa kana yayi Sallama.
Cikin dashashshiyar murya Ummi ta amsa Sallamar sa kana tace.
“Babana ya labarin Jameelu na?”.
Cikin sanyin murya yace.
“Ummi nima gashi yanzu nazo wajen Abba naji ko ya dawo gida”.
Dai-dai lokacin Abba ya buɗe gate ya fito ganin Moddibo tsaye yasa ya isa wajensa ahankali Moddibo ya zare wayar daga kunnensa bayan yace anjina zai kirata.
“Aliyu dama yanzu zanje wajenka”.
A hankali Modibbo yace.
“Abba to yanzu ya zamuyi”.
Numfashi Abba ya fesar tare da cewa.
“To mu tafi police station Jiya Baki ɗaya ba muyi tunanin zuwa can ba”.
Kai Moddibo ya gyaɗa kana suka shiga motarsa yaja Abba kuwa jingina da jikin kujera yayi baki ɗaya zuciyarsa ta tushe ya rasa wani irin tunani zaiyi yayin da Idanunsa suka tsats-tsafo da ruwan hawaye.
Moddibo kuwa Driving yake amma baki ɗaya baya fahimtar komai ko gilmawar mutum ya gani sai yaga kamar J ɗin sane.
Suna isa yayi Parking atare suka fito daga motar tare da shiga station din Dpo dake ƙoƙarin fita yayi Murmushi tare da cewa.
“Alh Bashiru maidala Barka da zuwa kaine da kan ka?”.
Jinjina kai Abba yayi kana cikin sanyin murya yace.
“Na kawo report ne ɗana Jameelu ne bamu ganiba”.
Cike da mamaki da kuma al'ajabi Dpo da sauran folisawan suka ce.
“Ɗan ka Jameelu kuma?”.
Kai Abba ya gyaɗa kana yace.
“Eh tun jiya ba agansa ba kuma babu motarsa sannan akira layukan sa basa shiga”.
Cike da jimami Dpo yace.
“Subhanallah Alhj mai yasa baku kawo report tun dare ba!?”.
Numfashi Abba ya fesar kana yace.
“Yanayin hadari ne sannan baki daya hankalin mu baya Jikin mu sai mukayi tunanin bari muyi addu'a mu kaiwa Ubangiji kukan mu”.
Daga nan yayi miki bayanin dukkan abinda ke tafiya.
Kai Dpo ya gyaɗa tare da cewa.
“Toh shikenan Alhj insha Allah yanzu zamu kira hedquater mu na cikin Taraba afaɗa musu halin da ake ciki”.
Kai Abba ya gyaɗa kana yace.
“Toh shikenan mun gode”.
Moddibo kuwa tun da suka shiga ya jingina da jikin bango Ya Lumshe Idanunsa yana motsa laɓɓansa alamar tasbihi bai ce komai.
Wunin wannan ranan baki ɗaya haka gidaje uku sukayi sa cikin zullumi,fargaba da kuma tsantsar tashin hankali Moddibo kuwa duk bayan minti biyu sai ya kira Number M Jameel aƙalla daga Jiya da daddare zuwa yau ya kira wayarsa yafi sau ɗari.
Acan ɓangaren Ummi ma haka yakasance bini-bini zata kira layin sa amma amsar ɗaya ake basu shine Switch off.
Haka zalika Abba time to time zaiyi try number M Jameel amma akashe Wunin wannan ranan baki ɗaya sunyi zuru-zuru dasu kallo ɗaya zaka musu kasancewa suna cikin tsananin tashin hankali da ɗimuwa duk inda ya kamata su nema ko su bincika duk sun nema sun bincika amman ba lbri.
Abba kuwa zama yayi afalonsa tare da kira duk wani danginsa ko kuma abokin arziki ko zaiji Jameelu yaje amma kowa amsa ɗaya yake basa baije ba.
Haka zalika Ummi baki ɗaya ta kira danginta ko M Jameel yaje amma suma dai amsar ɗaya ce baije ba.
Wunin wannan ranan har dare babu M Jameel babu labarin sa zuwa wannan lokacin tsananin tashin hankali da ruɗun da suke ciki ba zai misaltuba.
Da daddare Misalin ƙarfe goma Moddibo ne zaune a falon Abba kansa aƙasa yayinda idanunsa suka kaɗa sukayi ja jawur kana jijiyoyin kansa sun tashi sunyi ruɗu ruɗu rabonsa da bacci tun daren shekaran jiya haka zalika yauma koda runtsawa ne yakasa kana ya sanya duka hannunsa biyu ya dafe kansa dashi zuwa lokacin baki ɗaya ya kasa control ɗin kansa kife kansa yayi ajikin kujera tare da fashewa da kuka mai gunji.
Cikin wata raunan'niyar murya mai cike da karkarwa yace.
“Abba ina J yake? Abba ina J ya tafi ya barni Abba wani hali J yake ciki?”.
Hajiya Karima ce tashigo falon bakinta ɗauke da Sallama tare da kallon Moddibo dake kuka tamkar ƙaramin yaro lumshe Idanunta tayi tare da cewa.
“Haba Aliyu kuka kuma kai da ya kamata ka tausashi Mahaifinsa sannan kuma ka zauna zakuyi ta kuka atare kenan?”.
Karo na farko kenan arayuwar data yi masa magana cikin taushin lafazi.
Ahankali Moddibo ya ɗago kai ya kalleta still yana kuka yace.
“Aunty Karima ina J yake Ina J ɗina yashiga ya barni?”.
Cikin rauni Abba ya ɗago idanunsa da hawaye ke zuba Akuma dai-dai lokacin wayar Abba ta ɗauki ruri yana ɗagawa yaga number ce ba suna sai ya mayar ya ajiye.
Kallonsa Moddibo yayi tare da faɗin.
“Abba waye ne?".
Ciki Sanyin Abba ya kalli wayar kana yace.
“Numbar ce ba suna”.
Cikin muryan kuka Moddibo yace.
“Toh Abba ka ɗaga mana ko za'a faɗa mana anga J ne”.
Cikin sauri Abba yayi Picking call ɗin tare da cewa.
“Assalamu Alaikum”.
Daga ɗaya ɓangaren cikin wata bauɗaɗɗiyar murya aka amsa da.
“Wa'alaikum Salam kaine Alhaji Bashiru Maidala mahaifin Malam Jameelu?”.
Cikin sauri Abba ya gyaɗa kai tare da miƙewa tsaye kana yace.
“Eh nine mahaifin Jameelu”.
Cikin sauri Moddibo ya miƙe tsaye,
itama Hajiya Karima cikin sauri ta miƙe tsaye.
Gyaran murya yayi kana yace.
“Toh Jameelu yana wajen mu”.
Cikin rawan baki Abba yace.
“Jameelu yana wajen ku yana cikin halin lafiya? To a ina kuke?”.
Kai tsaye yace.
“Eh gashi ma kaji muryarsa”.
Ya faɗa tare da miƙawa M Jameel wayar.
Cikin sauri Abba yace.
“Jameelu”.
M Jameel kuwa cikin wata raunan'niyar murya me cike da galabaita da tashin hankali kamar wanda yayi kuka yana sauƙe ajiyar zuciya yace.
“Abbana”.
Cikin rawan jiki da rauni Abba yace.
“Na'am Jameelu Meye sameka?,Aina kake?”.
Ajiyar zuciya mai nauyi M Jameel ya sauƙe cikin rauni da yanayi wahala yace.
“Abba nima ban sani ba bansan inda nake ba Abba ina A.J”.
Cikin muryan kuka Abba ya kalli Moddibo da jikinsa ke rawa kana yace.
“Gashinan".
Ahankali M Jameel dake sakin ajiyar zuciya yace.
“Abba ka bashi wayar”.
Miƙawa Moddibo wayar Abba yayi cikin sauri Moddibo ya amsa tare da mannawa akunnensa kana Yace.
“Jyyyyyy”,yaja sunan cike da taraddadi.
Fesar da numfashi M Jameel Yayi tare da cewa.
“AJ”.
Cikin yanayin rauni da tausayawa ya lumshe idanunsa tare da cewa.
“J ina kake?”.
Girgiza kai M Jameel Yayi kana yace.
“AJ ban sani ba bansan inda nake ba, ban san ida suka kawoni ba”.
Cikin sauri aka Fisge wayar daga hannun M Jameel kana cikin wannan bauɗaɗɗiyar murya akace.
“Ka bawa mahaifinsa waya”.
Ahankali kuma cikin sanyi Moddibo yace.
“Waye kai ina J yake?”.
Cikin wata razananniyar tsawa yace.
“Kabawa mahaifinsa waya ba da kai muke son magana ba?".
Moddibo kuwa Girgiza kai yayi kana yace.
“Toh me kuke so ku faɗa min ko mameye”.
Cikin sauri Abba ya janye wayar daga kunnensa tare da sa wayar a handsfree kana yace.
“Gani mahaifin Jameelu".
Daga ɗaya ɓangaren mutumin yace.
“Jameelu yana hannunmu bawai mun sace sa dan mu kashe sa ko wani abu bane amma idan kuka yi mana taurin kai zamu iya kash”...
*Littafin SAKAYYAH na kuɗine ƴar uwa 1k ne kacal ki biya ki karanta cikin Aminci ba haƙƙin wani a kanki 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA. Sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276*
*By*
*GARKUWAR MARUBUTA*
[7/26, 11:56 AM] U.M Collection ZMFR CM: *Littafin SAKAYYAH na kuɗine ki biya ki karanta cikin Aminci da salama babu haƙƙin kowa a kanki littafin 1k kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276, sai in saki a Group ɗin*
“Idan har kana son rayuwar ɗanka to.
Kabi sharaɗin mu kabi tsarinmu, sannan kabi dukkan dokokin, muddin kana so Jameel ya rayu idan kuma ka kuskura kayi mana taurin kai kayi mana gardama kan sharuɗan da muka ginda ya maka to zakaga abinda zai biyo bayan gardama”.
Cikin tsanananin kaɗuwa Abba ke girgiza kai yayin da bakinsa ke rawa ya gaza furta komai.
Cikin wannan bauɗaɗɗiyar murya mutumin ya cigaba da cewa.
“Dama kai tsaye mu aikin kashe sa aka bamu. Toj amma saboda nagartansa da mutuncinsa yasa mukaji bama buƙatar kashe Malam Jameelu munfi ɓuƙatar abada kuɗi musakeshi domin shi Jameelu na kowane, kauda irinsu a doron kasa asarace data shafi, dukkan al'umma, dan haka kabi sharuɗanmu mu sakeshi salamun-salaman ya dawo hannunku hankali kwance, idan kuma ka kuskura kayi mana gardama duk da na gartan Jameel zamuyi abinda muma ranmu bai soba!”.
Cikin tsanananin tsoro da tashin hankali Abba ya dafe ƙirjinsa da hannu ɗaya kana yace.
“Innalillahi.
Dan Allah ku faɗa min koma me kukeso zan baku bazan muku gardama ba da Izinin Ubangiji”.
Cikin wata kakkausar murya mutumin yace.
“Bayan kai wanda mu kejin sa agefenka kada ya mana gardama domin shine Amininsa Moddibo”.
Girgiza kai Abba yayi still jikinsa na rawa kana muryarsa cike da rauni yace.
“Ba zaiyi gardama ba”.
Gyaran murya Mutumin yayi kana yace.
“Kasa amsa kuwwa shima Moddibo yaji abinda ake magana akai”.
Kai Abba ya gyaɗa still muryarsa na rawa yace.
“Nasa, nasa, nasa”.
Cikin bada umarni mutumin yace.
“Ku nutsu ku zauna ku jini”.
Kai Abba ya gyaɗa kana yace.
“Toh”.
Gyara murya mutumin yayi cike da isa yace.
“Baku zauna ba nasan atsaye kuke”.
Atare Abba, Moddibo da Hajiya Karima suka zauna Araunane Abba yace.
“Toh mun zauna wallahi”.
Kai Mutumin ya gyaɗa tare da faɗin.
“Yayi kyau sharaɗin mu na farko da zamu ƙidanya muku idan ka bishi Jameel ya rayu idan kuwa baka bishi ba Jameel ya mutu wannan shine sharaɗi na farko kuma shine mafi tsauri”.
Ajiyar zuciya kawai Moddibo ke sauƙewa zuciyarsa na cigaba da bugawa da masifar ƙarfi.
Mutumin ya cigaba da cewa.
“Sannan yanzu rayuwar Jameel yana hannunka da kai da Amininsa da kuma mahaifiyarsa da ma sauran Makusantan ku, idan kuka mana gardama kamar kuna wasa da rayuwar Jameel ne”.
Atare Moddibo da Abba suka haɗa baki wajen cewa.
“Meye kuke buƙata menene sharaɗin naku?”.
Kai Mutumin ya gyaɗa kana yace.
“Sharaɗin namu shine wannan maganar kada ku yarda kada ku kuskura koda agigin bacci koda amafarki kusa hukuma acikinta!”.
Moddibo kuwa ƙirjinsa ne ya buga cikin sauri ya dafe kansa da hannunsa biyu tare da kifa fuskarsa ajikin kushin kana ya furta.
“Innalillahi wa'inna Ilahi rajiu'n”.
Cikin ƙasa da murya Abba ya runtse Idanunsa tare da cewa.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n La'ilaha Illah anta subhanaka Inni kuntu Minal Zhalimin”.
Cikin tsawa mutumin yace.
“Zaku faɗa kenan!?”.
Da sauri Moddibo ya girgiza masa kai dake kife akan kushin kamar yana gabansa kana yace.
“Ba zamu faɗa ba wa kowa ba, mudai fatan mu J ya kasance cikin ƙoshin lafiya, kada ku cutar dashi”.
Taɓe baki Mutumin yayi kana yace.
“Kada ku yarda kada ku kuskura ku sanya hukuma aciki”.
Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe tare da fesar da numfashi kana yace.
“Ba zamu faɗa ba da izinin Ubangiji zamu bi sharaɗin ku.
Amma sai dai kafin ma ku kiramu mun kaiwa hukuma maganar amatsayin Jameel ya ɓata tunda mun kwana babu shi sannan mun wuni babu shi toh munje wajen hukuma amma bawai munje amatsayin mun kai ƙorafi akan ku bane”.
Jinjina kai Mutumin yayi tare da taɓe baki kana yace.
“Toh wannan sharaɗine Idan hukuma sun dawo dan suna nan kamar Mayu, daga sunji babu mutum idan sun sake kawo kansu kada kuce mun nemi kuɗi awajenku”.
Yarfe hannu Hajiya Karima tayi tare da girgiza kai ta ƙurawa Abba Ido tamkar shike maganar.
Cikin bauɗaɗɗiyar murya Mutumin ya cigaba da cewa.
“Muddin kana son ran Jameel to.
Kayi shiru da bakin ka idan mun kafa maka sharaɗi na biyu ko kuma mun faɗi abinda mukeso kun bayar to Jameel zai dawo amatsayin ɓata yayi sannan ba sace sa akayi ya dawo ba”.
Abba kuwa buɗe idanunsa dake lumshe yayi kana yace.
“Insha Allah zamu bi sharaɗin ku amma yanzu mai kuke so ku faɗa min”.
Cikin sauri ya janyo wayar tare da kallon screen ɗin jin ɗit-ɗit-ɗit alamar an kashe.
Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe tare da rintse idanunsa da karfi kana yace.
“Innalilahi wa'inna ilahi rajiu'n Hasbunallahu wani'imal wakin”.
Moddibo kuwa da still hannunsa ke dafe akansa yana taune lip ɗin sa na ƙasa babu abinda ke fita abakinsa face kalmar Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n.
Hajiya Karima kuwa Girgiza kai kawai take tare da yarfe hannu kana tana mai maimaita kalmar Hasbunallahu wani'imal wakin ta juya tare da kallon Abba da idanunsa suka kaɗa suka yi jawur sannan tace.
“Innalillahi wa'inna Ilahi rajiu'n wannan wani irin zamani Allah ya kawo mu kenan ƴan Kidnapping ne suka ɗauke Jameelu”.
Lokaci ɗaya Moddibo ya sake dafe kansa da karfin yana cigaba da taune lip ɗin sa na ƙasa.
Girgiza kai Hajiya Karima tayi kana ta cigaba da cewa.
“Amma Alhj wannan sharaɗin nasu zancene na banza ina muke da yaƙinin zasu iya kare Jameelu ba zasu cutar da shiba ba gwara mu faɗawa hukuma ta shiga cikin maganar nan ba”.
Cikin sauri Moddibo ya ɗago kansa daga jikin kushin wanda sai alokacin ya samu damar hakan hannunsa biyu ya haɗe waje ɗaya alamun roƙo kana ya runtse Idanunsa da ƙarfi ya shiga.
Girgiza kansa muryarsa na rawa yace.
“A'a,a'a,a'a Aunty Karima kiyi wa Allah da Manzonsa kada ki sako hukuma acikin maganar nan Wallahi kina sa hukuma zasu iya yiwa J komai kiyiwa Allah kada kisa hukuma aciki kiji abinda suka faɗa mana”.
Abba kuwa jujjuya kai ya shiga yi kana idanunsa akan Hajiya Karima yace.
“Karima ban yarda ba ban yafe ba wannan maganar ya fita muddin kinaso Jameelu na ya dawo kada ki faɗawa hukuma wannan maganar”.
Kai ta gyaɗa cike da damuwa.
Kallon wayarsa Abba yayi tare da cewa.
“Yanzu bari na sake kiransu naji me suke buƙata”.
Ya faɗa tare da dearling number amma swich off”.
Ɗagowa Abba yayi tare da kallon Moddibo kana yace.
“Aliyu Wayar akashe”.
Cikin sauri Hajiya Karima tace.
“Ai dama zaiyi wuya yashiga ya za ayi ya shiga ai ba zai taɓa shiga ba”.
Daga Abba har Moddibo babu wanda yace komai Allah ne kaɗai yasan abinda suke ji aransu.
Dai-dai lokacin Hajiya Turai ta shigo bakinta ɗauke da Sallama kusa da Hajiya Karima ta zauna Idanunta sun kaɗa sunyi jawur har sun kumbura alamar tayi kuka ta gaji Idanunta akan Abba tace.
“Alhj har yanzu babu labarin Jameelu”.
Kafin Abba yace wani abu Hajiya Karima tayi saurin cewa.
“Yan zun nan ƴan Kidnapping sun Kira su suka ɗauke sa!”.
Cikin sauri Hajiya Turai ta dafe ƙirjinta tare da cewa.
“Hasbunallahu wa niimal wakil Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n,Ƴan Kidnapping kuma Alhj!?”.
Girgiza kai Abba yayi sai kuma ya riƙe tafin hannunta kana yace.
“Ki zauna”.
Ba musu ta tazauna jikinta na rawa saboda tashin hankali da take ciki.
Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe kana ya maida kallonsa kan Hajiya Karima tare da cewa.
“Wannan maganar daga mu sai mu iya mu nan kada ku kuskura maganar nan ta fita iya mu nan ban amince ba kuma ban yafe ba daga ke har Karima ban amince ku kai maganar nan kunnen hukuma ba, duk wacce takai abakin igiyoyin auren ta duka saboda sun sa sharaɗin idan na yarda hukuma ta shiga zasu kashe min Jameelu”.
Ya ida maganar cikin raunin murya.
Kai Hajiya Turai ta girgiza cikin Muryan kuka tace.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n in sha Allah ba zamu faɗa ba Alhj yama za ayi mu faɗa ai wannan ba abin faɗa bane!”.
Hajiya Karima ma cikin sauri ta girgiza kai kana tace.
“Insha Allah ba zamu faɗa ba, zamu kiyaye”.
Moddibo kuwa har zuwa yanzu yana dafe da kansa da hannu biyu still Idanunsa aruntse.
Ahankali Abba ya kira sunan sa tare da cewa.
“Aliyu”.
Araunane Moddibo ya ɗago idanunsa da sukayi Jawur kana sun kumbura ga lip ɗin sa na ƙasa sunyi ja kana ya ɗan kumbura.
Cikin rauni ya kalli Abba tare da cewa.
“Na'am Abba”.
Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe kana yace.
“Aliyu ya zamuyi?”.
Zazzafafar ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe tare da cewa.
“Abba sai dai mu jira kiran su na biyu muji mai suke buƙata magana ce dai na kuɗi atanadi abinda suke bukata a ajiye tun wuri”.
Kai Abba ya gyaɗa tare da cewa.
“Toh Aliyu amma yanzu ya zamuyi da mahaifiyarsa inaga kada ka faɗa mata halin da ake ciki”.
Moddibo kuwa kallon Abba yayi kana ya girgiza kansa tare da cewa.
“Abba kar afaɗa mata kuma? Ai gwara tasan cewa J yana raye, domin zuciyar Ummi zata iya bugawa da idan ba afaɗa mata ba gwara in Faɗa mata tasan cewa J yana raye tasan cewa munyi magana da shi naji muryansa, kaima kaji muryan J fa yanda muka yi magana dashi ƙilan sun dake shi!”.
Ya faɗa cikin raunin murya.
Runtse Idanu Abba yayi da ƙarfi hawaye masu zafin gaske suka shiga bin kuncinsa Shar-shar-shar.
Moddibo kuwa still Idanunsa na runtse ya gagara buɗewa har zuwa yanzu yana jin muryan M Jameel na cewa A.J bansan inda nake ba ban san ina nake ba.
Cikin rauni ya ɗago kansa muryarsa na rawa yace.
“Abba kaji fa J cewa yake baisan inda yake ba Abba ina suka kaisa ina suka cusa sa”.
Dafa kansa Abba yayi kana yace.
“Aliyu duk yanda za ayi idan ka faɗawa Fatima kada ta faɗawa kowa, sannan ka kiyaye yanda zaka faɗa mata kada hankalinta ya tashi!”.
Girgiza kai Moddibo yayi kana yace.
“Abba ba zata faɗawa kowa ba idan na faɗa mata halin da ake ciki”.
Jinjina kai Abba yayi tare da cewa.
“Toh shikenan Aliyu ka kula”.
Kai Moddibo ya gyaɗa dai-dai lokacin kiran Ummi ya shigo wayar Moddibo kallon Abba yayi kana yace.
“Abba ka gani ko kirana ma take yi yanzu kafin na wuce gida ma saina biya wajenta”.
Cike da rauni Abba yace.
“Toh shikenan tashi kaje Aliyu gashi kaima har ƙarfe goma na dare yayi tsoro nakeji, jiya a irin ya wannan lokacin suka ɗauki Jameelu”.
Runtse Idanu Moddibo yayi tare da miƙewa kana ya yiwa su Hajiya Turai sallama ya fita har kofar gida Abba ya rakasa sai da yaga tashin motarsa kafin ya koma cikin gida zuciyarsa na zafi.
Cikin sanyin jiki yayi parking kana ya fita ƙaramin ƙofar ya tura ya shiga A baranda ya hango Ummi, Asma'u da Bashir Idanun Ummi da Asma'u sun kaɗa sunyi Jawur dasu kana sun kumbura.
Bashir kuwa cikin dauriya kasancewar sa namiji yasa ya riƙe hannun Asma'u dake kuka tare da cewa.
“Ummi ki kwantar da hankalin ki da izinin Ubangiji ba abinda zai samu Yah Jameel Allah zai tsaresa aduk inda yake Asmey ki daina kuka dan Allah”.
Girgiza kai Asma'u tayi cikin Muryan kuka tace.
“Bashir taya zamu iya tsaida hawayen mu bayan bamu san halin da Yah Jameel ke ciki ba!?”.
Cikin rauni Ummi ta ɗago kanta Idanunta ya sauƙa akan Moddibo dake shigowa Iska na kaɗa sa duk yayi sauya cikin sauri Ummi ta miƙe jikinta na rawa ta nufesa tare da cewa.
“Babana”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da fesar da numfashi kana ya zuba mata Ido cike da tausayawa ganin kamar bata cikin nutsuwarta ƙarasawa kusa da ita yayi tare riƙe hannunta kana suka zauna agefen barandar cikin sanyin yace.
“Ummi”.
Kallonsa tayi tare da cewa.
“Na'am Babana ya labarin Jameelu na”.
Sunkuyar da kansa yayi tare da cije labɓansa na ƙasa wanda zuwa lokacin sunyi masifar ja kana sun kumbura yayin da Idanunsa ke tsats-tsafo da ruwan hawaye sai dai sun gagara zubo wa.
Ahankali ya ɗago kansa tare da damƙe hannun Ummi na dama acikin nasa kana yace.
“Ummi munyi waya da J”.
Cikin sauri Ummi ta zaro Idanunta duka waje kana tace.
“Kayi waya da Jameelu”.
Kai ya gyaɗa mata hawaye masu zafi suka zubo akuncinsa.
Kallonsa Ummi tayi tare da faɗin.
“Kayi waya da Jameelu Babana kuma kana kuka!?”.
Moddibo kuwa kallonta yayi cikin ƙoƙarin tsaida hawayen sa yace.
“Ummi anyi Garkuwa Da shine”.
Cikin matsanancin tashin hankali Asma'u ta ɗaura hannunta akai tare da cewa.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n”.
Ta dire addu'ar tare da komawa ta zaun.
Ita kuwa Ummu wani irin zazzafan numfashi ta fesar tare runtse idanu kana ta buɗe su akan Moddibo cikin dan sassaucin tashin hankali da take ciki tace.
“Toh ai ba komai Babana kawai Abbansa yayi ƙoƙarin haɗa kuɗi da suke buƙata a basu, su sako mana shi.
Alhamdulillah tunda yana raye, domin ai wannan abune da ya zama ruwan dare, tunda su dai in an basu abinda suke so basa kisa.”
Sai kuma ta lumshe idanunta wasu sirran hawaye suka gangaro mata cikin raunatacciyar murya tace.
“Waya sace min Jameelu na!? Waya sacemin farin ciki na!?
Waya ɗauke min jin daɗina!?
Waya ɗauke min Garkuwana da gatana!?
Wayake son yimin shamaƙi da bangona majinginata!?”.
Moddibo kuwa hannunta ya riƙe acikin nasa kana yace.
“Ummi dan Allah ki daina kuka addu'a zakiyi masa kamar yadda kikace abinda suke so kawai za'ayi musu, sun kuma gargaɗemu kada asa hukuma a cikin mgnar, sai muyi ƙoƙarin kiyayewa”.
Kai Ummi ta gyaɗa tare da share hawayen ta amma still wasu na zubowa.
Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe tare da zayyane mata duk yanda sukayi.
Atare Asma'u, Ummi,da Bashir suka sauƙe nannauyan numfashi.
Kallon Moddibo Ummi tayi kana tace.
“Babana basu faɗi nawa suke so bane?”.
Kai ya girgiza tare da cewa.
“Ummi basu faɗa ba tukunna sharaɗin su na farko suka bamu kada ayarda a faɗawa hukuma”.
Ajiyar zuciya mai haɗe da jan zuciya Ummi ta sauƙe still tana hawaye tace.
“Ba zan faɗa ba Insha Allah bazan faɗa ba Babana.
Ba zan faɗa ba”.
Kai Moddibo ya gyaɗa tare da cewa.
“Ummi ki cigaba da addu'a Insha Allah babu abinda ya gagari Ubangiji kuma Insha Allah tunda suka fara kira zasu sake kira su faɗi abinda suke so sai ayi ƙoƙari amusu abinda suke so”.
Jinjina kai tayi kana tace.
“Insha Allah gobe zanje gidan su muyi magana da Abbansa idan Malam ya bari”.
Dai-dai lokacin Malam Ahmad ya shigo cike da tausayawa yake Kallonsu kana yace.
“Nama bari Fatima na bari Allah ya tsaresa ya kuma bayyana sa aduk inda yake”.
Atare suka amsa da Ameen.
Miƙewa Moddibo yayi kana yace.
“Ummi zan tafi gida”.
Kai ta gyaɗa kana tace.
“Toh Babana Allah ya kiyaye”.
Ameen ya amsa sannan ya juya ya fice cikin mutuwar jiki.
Yana isa gida yayi Parking tare da fitowa ya rufe ƙofar kana ya shiga falon baki ɗaya abubuwan sun ca kuɗe masa ga rashin bacci rabonsa da bacci tun daren shekaran jiya ga tashin hankali da damuwa baki ɗaya zulumi sun mishi rubdugu ya fita hayyacinsa sai alokacin ya tuna baki ɗaya wayewar garin yau baiyi wanka ba cikin kasala ya nufi toilet din sai dai baya tunanin zai iya yin wanka, al'wala ya ɗaura kana ya fito tare da shimfiɗa darduma ya fuskanci alƙibla cike da nutsuwa ya shiga gabatar da nafillah aduk lokacin da ya kai goshinsa kasa (Sujjada)Sai ambaci J dinsa, raka'a huɗu yayi bayan ya idar ya ɗauki Alkur'ani mai girma kana ya fara karantawa Acikin Suratul An-Nisa'i har Misalin ƙarfe 2:00am yana karatun idan ya karanta wani aya sai M Jameel ya faɗo Masa arai kana ya tuna da wasu lokutan idan yana karatu yazo wajen Ayar azaba saiya rufe Kur'anin ya Rungume kana yaita kuka idan kuma yazo wajen Ayar Rahma sai yaita sakin murmushi kana yana cigaba da karatun.
Ahankali Moddibo ya runtse Idanunsa tare da Rungume Kur'anin aƙirjinsa idanunsa sun kaɗa sunyi jawur dasu kana sun kumbura saboda tashin hankali da yake ciki har aka kira Assalatu Moddibo bai rintsa ba.
Haka zalika ɓangaren Abba ma ya kwana ba tare daya rintsa ba acikin kwana ɗaya da yini duk ya canza yayi zuru-zuru dashi.
Washe gari da safe:Misalin ƙarfe 8:00am Abba ne zaune afalonsa ya ƙurawa wayoyinsa Idanu koda motsin kirki ya gagara baki daya hankalin sa nakan wayarsa.
Cike da ladabi mai gadi yayi Sallama ɗagowa Abba yayi ya kallesa kana ya amsa masa Sallamar.
Cike da tausayawa mai gadin yace.
“Alhj ga baƙi awaje”.
Numfashi Abba ya fesar kana yace.
“Su waye ne?”.
Tsayuwa mai gadin ya gyara kana yace.
“Hukumar ƴan sanda ne wai daga Taraba suka zo”.
Kai Abba ya gyaɗa tare da cewa.
“Toh ka shigo dasu”.
Kai mai gadin ya gyaɗa kana ya fice yace su shiga.
Dai-dai lokacin Moddibo yazo Parking motarsa Yayi kusan atare suka shiga ƴan sandan mutum biyar na gaba shi Kuma yana bayansu.
Bakinsu ɗauke da Sallama suka shiga wajen zama Abba ya nuna musu bayan ya amsa Sallamar su.
Moddibo kuwa gefensa ya nufa ya zauna cikin mutuwar jiki da damuwa.
Gyaran murya ɗaya daga cikin ƴan sanda yayi kana Idanunsa akan Abba yace.
“Sunana Asp Mahmud Adam Shani daga rundunar ƴan sandan jahan Taraba masu bincike akan abinda ya shafi ɓatan mutane da kuma kisan kai kana da fashi da makami ina fatan zaku bamu haɗin kai.
Mun samu kirane daga nan ƙaramin Headquarter din mu”,'.
Sai kuma ya sauƙe numfashi tare da kallon Moddibo da yayi ƙasa da kansa kana yana motsa laɓɓansa alamar tasbihi yake.
Kana ya cigaba da cewa.
“Mun samu masaniya Kan cewa Jameel ɗan Alhj Bashiru Maidala ya ɓata shiyasa nazo da kaina inji ba'asin maganar sannan muga ta inda ya kamata mu fara da taimakon Allah da kuma baya nan da zaku bamu zamuyi nasara wajen gano inda yake”.
Jinjina kai Abba yayi tare da rintse idanunsa kana ya fesar da numfashi tare da sunkuyar da kansa ƙasa hawaye masu zafi suka zubo masa.
Cike da tausayawa Asp Mahmud Adam Shani yace.
“Alhj ka kwantar da hankalin ka kayi min duk kan bayanin da zan gane saboda yanda zamu kula da aikin da kuma abinda ya kamata ayi akai”.
Jinjina kai Abba yayi tare da ƙoƙarin hana hawayensa zuba kana ya daure yace.
“Jameelu nine mutum na ƙarshe da yayi sallama dani ya fita ina tsaye ajikin window har ya fita bayan fitarsa na kai kimanin awa ɗaya da rabi ina tsaye ajikin window, Bayan nan kuma duk cikin mu babu wanda yayi magana da Jameelu domin ya fita akan zaije wajen Abokinsa amma bai isa ba”.
A hankali ya fesar da zazzafan iska tare da taune lip ɗin sa na ƙasa tare da kallon Asp Mahmud Adam Shani kana yace.
“Adaren Abokinsa yazo domin rashin samun layinsa da bai yiba”.
Jinjina kai Asp Yayi kana yace.
“Eh anyi min wannan bayanin daga Headquarter din mu na Nan Inspector Ayuba Garba kumo ya sanar dani komai to amma daga ɓatansa zuwa yanzu babu wanda ya kira ka!?”.
Cikin sauri Abba ya Girgiza masa kai kana yace.
“A'a babu".
Ido Asp ya zuba masa kana yace.
“A'a Alhj Bashir dan Allah kada kuce zaku bi sharuddan ire-iren mutane masu garkuwa da mutane, idan har akwai wanda ya kira ka ya maka barazana ko kuma ya nemi wani abu ka faɗa mana ko kuma ka bami number da suka kira Insha Allahu Jameelu zai kuɓuta sannan zai rayu da izinin Ubangiji zamu tsera tar dashi”.
Moddibo kuwa cikin sauri ya kalli Asp zuciyarsa na bugawa da masifar ƙarfi ya Girgiza kai tare da cewa.
“Babu wanda ya kira ai da akwai wanda ya kira zamu sanar daku sannan mu ma da hankalin mu zaifi kwanciya ma, mun san cewa yana raye”.
Ido Asp ya tsira musu kana yace.
“Anya kuwa anya babu wanda ya kira ku!?”.
Cikin sauri Moddibo ya gyaɗa kai kana cikin ƙoƙarin dai-dai-ta nutsuwarsa yace.
“Babu wanda ya kira tashin hankalin mu kenan”.
Abba ya karɓi maganar da cewa.
“Da har ankira Asp Mahmud da ace ankira kamar yanda kake zaton ƴan Kidnapping ne kuma sun buƙaci kuɗin ai da tuntuni nayi muku bayani sannan idan yakama da in basu kuɗi zasu dawo min da Jameelu na da tuni na bayar an dawo min da Jameelu na!”.
Anutse Asp ya gyara zamansa kana cikin sauri yace.
“Alhj na roƙe ka dan Allah koda ankira ance kuɗi ake buƙata kada ka basu, kawai ka bamu Number sannan kayi mana bayani shine abinda muke bukata amma ana temakamu sune sannan ana ƙara basu ƙarfin gwiwa dayi musu abinda suke so shiyasa suke ƙara yin abinda suke su ɗin”.
Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe tare da jingina bayansa da jikin kujeran kana yace.
“Insha Allahu zanyi ƙoƙari duk abinda ake ciki zan sanar muku Nagode sosai musamman tattakin da kayi daga Taraba zuwa nan”.
Dai-dai lokacin Hajiya Karima tazo Idanunta akan Asp Mahmud Adam Shani da sauran Folisawan Kallonta ta mayar kan Abba kana tace.
“A baƙi mukayi ne sannun ku da zuwa”.
Asp dake rubutu awata ƙaramar takarda yace.
“Yawwa”.
Kana ya cigaba da rubuce-rubucen sa.
Kallon Abba Hajiya Karima tayi tare da kallon Moddibo da idanunsa ke lumshe haƙoransa uku na sama na kan laɓɓansa na ƙasa numfashi ta fesar kana ta ƙara sa kusa da Abba da har zuwa lokacin bayansa ke jingine ajikin kujera tace.
“Alh ga Hajiya Fatima mahaifiyar Jameel ta iso”.
Ahankali Abba ya ɗago kansa kana cikin sanyin murya yace.
“Kice ta iso”.
Kai ta gyaɗa tare da juyawa ta fita ba jimawa ta shigo Ummi na biye da ita Ahankali Ummi ta ƙara sa kusa da Moddibo ta zauna Hajiya Karima ta juya ta fice cike da tausayawa Moddibo da Abba ke kallonta ganin yanda Idanunta suka kumbura sukayi jawur sun ƙanƙance.
Anutse Asp ya ɗago kansa tare da kallon Ummi kana yace.
“Wannan ce mahaifiyarsa?”.
Kai Abba ya gyaɗa tare da faɗin.
“Eh itace”.
Atausashe Asp ya gyara zamansa tare da cewa.
“Sannu Mmn Jameel Ubangiji Allah ya bayyana sa ya kuma tsaresa aduk inda yake, ki kwantar da hankalinki in sha Allah zamuyi iyakar iyawarmu zamu samoshi a duk inda yake”.
Kai ta gyaɗa cikin muryanta daya dishe da kuka tace.
“Ameen ya Allah”.
Miƙewa Asp Yayi kana yace.
“Alhj to bari mu tafi amma dan Allah duk abinda ake ciki a faɗa mana”.
Kai Abba ya jinjina tare da cewa.
“Toh Insha Allah”.
Bayan tafiyarsu Ummi ta juya tare da kallon Abba cikin raunin murya tace.
“Alhj har yanzu basu sake kira ba!?”.
Kai Abba ya gyaɗa kana yace.
“Fatima har yanzu basu kira ba”.
A raunace ta sanya gefen hijabinta tare da share hawayen da suka zubo mata kana tace.
“To idan sun sake kira duk abinda suke so dan girman Allah kataima keni kaceci rayuwar Jameel kayi musu”.
Girgiza kai Abba yayi idanunsa na tara ƙwalla yace.
“Fatima ba sai kin roƙeni kin haɗa Ni da Allah ba, idan har banyi musu abinda suke so andawo min da Jameel ba menene amfanin dukiyata?”.
Sai kuma ya runtse Idanunsa kana ya cigaba da cewa.
“Jameel yafi min komai aduniyar nan zan iya sadaukar da duk dukiyata domin ceton rayuwar Jameel insha Allah zanyi iya bakin ƙoƙarina wajen ganin ya dawo”.
Ajiyar zuciya ta sauƙe kana tace.
“Toh shikenan Nagode Ubangiji Allah ya kuɓutar dashi Allah yasa su faɗi abu mai sauƙi kada su faɗi abinda yafi ƙarfin mu Allah ya tsaresa Allah yasa yana cikin ƙoshin lafiya”.
Atare Moddibo da Abba ke Amsawa da Ameen cike da tausayawa.
Kallon Abba tayi kana tace.
“Bari na tafi gida”.
Kai Abba ya gyaɗa kana yace.
“Toh shikenan”.
Cikin sanyin murya Moddibo yace.
“Ummi muje in kaiki gida”.
Kai ta gyaɗa kana ta miƙe.
Suka fita da kallo Abba ya bisu cike da tausayawa.
Moddibo kuwa yana ajiye Ummi agida kai tsaye makarantar Malam Arɗo ya nufa yana isa yayi Parking tare da fita ya nufi harabar makarantar iska na kaɗa shi kai tsaye Office din malam Arɗo ya Murɗa handle din ya shiga bakinsa ɗauke da Sallama.
Anutse Malam Arɗo dake duba wani littafi ya ɗago kansa tare da sauƙe Idanunsa akan Moddibo ganinsa cikin wani irin yanayi yasa yayi saurin miƙewa tare da riƙe hannun sa kana yace.
“Moddibo ya dai?”.
Kai Moddibo ya Girgiza cikin sanyin murya yace.
“Bakomai”.
Kujera Malam Arɗo yaja masa ya zauna kana shima ya koma mazauninsa.
Cike da kulawa Malam Arɗo yace.
“To ina ƴan biyun naka?”.
ƙasa yayi da kansa tare da runtse Idanunsa kasancewar sa ba mai saurin kuka ba ya tabbata da ace yana da saurin kuka da zaran an ambaci sunan J ɗin sa zaiyi kuka ko hakan zaisa ya samu sassaucin abinda yake ji Aransa ya sake damƙe lip ɗin sa da ƙarfi wanda zuwa lokacin ya sake kumbura kana yayi ja sai sheƙi yake.
Ido Malam Arɗo ya tsira masa kana yace.
“Ya dai Aliyu mai yake faruwa da Jameelu tun jiya da yamma naji ana raɗe-raɗin wai ba agansa ba nayi ta kiran wayarka baka ɗauka sannan shi kuma idan na kirasa akashe ina Jameelu da gaske ne babu shi!??”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da ɗago kansa still yana taune da lip ɗinsa kana cikin raunin murya yace.
“Babu J”.
Kai Malam Arɗo ya gyaɗa kana yace.
“Na sani Aliyu ka nutsu ka dawo hayyacinka Aliyu na sani babu Jameelu sannan na gaskata tunda har naga kai kaɗai kazo nan na tabbata do min idan anganka tamkar anga wata ne dole za'aga zara”.
Ya faɗa tare da miƙewa ya dafa kafaɗar sa.
Runtse Idanu Moddibo yayi
“Yanzu ya ake ciki?”.
Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe tare da shafa ƙirjinsa dake bugawa da ƙarfi kana yace.
“Nima kaina ya kulle a duniya bansan me zanyi ba bansan ya zanyi na ganni da J ba?”.
Dafa kafaɗar sa Malam Arɗo yayi cike da tausayawa yace.
“Toh yanzu wani mataki aka ɗauka akan lamarin!?”.
Cikin raunin murya yace.
“Babban matakin da aka ɗauka shine addu'a da faɗawa Ubangiji abinda yake faruwa”.
Jinjina kai Malam Arɗo yayi tare da faɗin.
“An ɗauki mataki mai kyau, da girma wanda ya dace da dukkan Musulmi yanzu mu shiga cikin makaranta mu faɗawa yara su tayamu da addu'a Ubangiji Allah ya tsare malam Jameelu ya kuma bayyana sa aduk inda yake”.
Kai Moddibo ya gyaɗa tare da miƙewa kana yace.
“Toh Nagode Allah ya saka da alkhairi”.
Hannunsa Malam Arɗo ya riƙe bayan ya mike suka fita kai tsaye bangaren ƴan primary suka fara shiga Ajinsu Ramadan da Raudat yaran na ganinsa suka miƙe cike da farin ciki suna cewa Moddibo Moddibo Kusan a tare Raudat Ramadan da wasu ɗalibai uku suka ce Moddibo ina Malam Jameel munyi kewar ku bakwa zuwa.
Lumshe Idanunsa da yaji suna masa zafi da zaran an ambaci sunan J ɗin sa zuciyarsa zata buga da masifar ƙarfi tsayuwar sa ya gyara agaban ajin tare da cewa.
“Ina ɗaliban Malam Jameel?”.
Baki ɗaya yaran suka ɗaga hannu suna tsalle tare da cewa gamu nan Moddibo ina yake munyi kewarsa bakwa zuwa yanzu, dan Allah kace yazo muna san ganinsa.
Kasa furta komai Moddibo yayi hakan yasa ya jingina bayansa da jikin bango yayi ƙasa da kansa yasan yanda J ɗin sa ke son Yara da kuma wasa da su wanda a ra'ayinsa baison koyar da yara amma saboda yanda J ɗin sa ke son Yara Yasa yake shiga koyar musu ganin haka yasa Malam Arɗo yayi gyaran murya Atake duk yaran suka nutsu tare da tsirawa Malam Arɗo ido.
A hankali Malam Arɗo ya sauƙe tare da faɗin.
“Kuna jina?”.
Kai suka gyaɗa masa.
Ya sauƙe numfashi tare da cewa.
“To zaku yiwa Malam Jameel din ku addu'a Allah ya bayyana shi?”.
Aruɗe yaran suka ce Malam Jameel ya ɓata ne?."
Kai Modibbo ya gyaɗa musu cike da damuwa.
Cikin zare ido Raudat tace.
“Malam Jameel din mu ya ɓata kuma to ina yaje?”.
Ramadan kuwa miƙewa yayi tare da zuwa gaban blackboard ɗin cikin yanayin damuwa sosai ya riƙe hannun Moddibo da har zuwa lokacin Idanunsa ke lumshe yace.
“Moddibo ina Malam Jameel ɗin mu yaje dan Allah ka kira wayansa kace ya dawo Muna so sa”.
Kasa cewa komai Moddibo yayi sabida zulumi.
Gyaran murya Malam Arɗo yayi tare da cewa.
“Kuyi masa addu'a Allah ya bayyana shi idan kunyi sallah kuyi addu'a Allah ya bayyana Malam Jameel sannan ku faɗawa iyayenku suma suyi masa addu'a Allah ya karesa ya kuma dawo dashi cikin aminci da salama”.
Hawaye Ramadan ya fara zubdawa tare da cewa.
“Toh Malam zamuyi masa addu'a zan faɗawa Mommy da Addah Khausina suma zasuyi masa addu'a Allah zai dawo dashi”.
Ahankali Moddibo ya shafa kansa tare da cewa.
“Yawwa Ramadan kuyi masa addu'a ayanzu babu abinda Malam Jameel yake buƙata awajen mu face addu'a”
Cikin rauni sosai yaran suka ce zamu yi masa.
Cikin sanyin jiki Malam Arɗo da Moddibo suka fita zuwa bangaren Secondary bayan sun fita anan suka shiga ɓangaren na naziri saida suka gama zagaye ko wani aji suna sanarwa Ayiwa Malam Jameel addu'a Ubangiji Allah ya bayyana shi cikin tashin hankali ɗalibai suka shiga masa addu'a.
Bayan sun fito Moddibo ya nufi hanyar gate
Cikin kula malam Arɗo yace.
“Moddibo baza ka shiga office din ku ba?”.
Kai ya girgiza tare da cewa.
“Um-um bazan shiga ba zan tafi bazan iya zama babu J ba”.
Ya faɗa tare da ficewa yashiga motarsa kai tsaye gidan Abban M Jameel ya nufa bayan yayi Parking ya fito tare da shiga falon bakinsa ɗauke da Sallama A inda ya fita yabar Abba anan ya dawo ya sameshi zaune still wayarsa na gabansa ya zubanusu Ido da alama tun bayan fitarsa ko motsawa baiyi ba.
Ahankali Abba ya ɗago kai tare da zuba masa ido cike da tausayinsa baki ɗaya ya rame ya canza idanunsa sun sake girma da ja kana idanunsa sun faɗa, Ahankali Moddibo ya ƙaraso ya zauna agefensa aƙasan Capet Cike da tausayawa Abba yace.
“Aliyu ba kayi wanka ka sauya kaya ba”.
Siririn tsaki Moddibo yaja tare da yin ƙasa da kansa kana yace.
“Abba har yanzu basu sake kira ba!?”.
Kai Abba ya Girgiza tare da cewa.
“Har yanzu basu sake kira ba gani nan ina zaune tamkar gadin waya nake sai tsumayin kiransu nake amma basu kira ba, amma yanzu ka samu kaje kayi wanka ka samu kaci abinci”.
“Abba banajin yuwa”.
“Ya zamuyi Aliyu idan kaima baka ci abinci ba ai faduwa zakayi. Insha Allah addu'ar mu bazai bar Jameelu ya ta gayyara ba”.
Sai ya kuma maida kallonsa kan Hajiya Karima data shigo wacce ita ma baki ɗaya tayi sanyi ahankali yace.
“Ki zubawa Aliyu sbinci”.
Kai ta gyaɗa tare da nufar dining ta ɗauki Plate ta zuba masa jollof fice da yaji bushesh-shen kifi da namar kaza ta kawo masa.
Moddibo kuwa hannu ya daga mata alamar kada ta ajiye masa ganin ta ajiye yasa ya maida kansa jikin kushin ɗin ya jingina tare da lumshe idanunsa yace.
“Ina ma ace tare suka ɗauke Ni da J da yafi min farin ciki ina rayu dashi aduk inda yake duk halin da yake ciki ace muna tare wallahi da yafi min farin ciki akan rabani da Jameel da sukayi”.
Kallonsa Abba yayi cike da tausayawa wannan shine karo na farko arayuwar sa da yaji Moddibo ya kira Complete sunan M Jameel cikin raunin murya yace.
“Toh ya zamuyi Aliyu ka daure kaci abinci”.
“Abba ba zan iya cin abinci ba”.
Cikin rarrashi Abba yace.
“Haba Aliyu ka naso kasake sa kamu cikin damuwa ne rashin cin abinka dai dai yake da yiwa kan ka illah, wanda bazan so hakan ba dan Allah ka daure kasa wani abu acikin ka”.
Kai Moddibo ya gyaɗa kana yace.
“Toh Abba abani tea”.
Miƙewa Hajiya Karima tayi ta nufi dining kana ta haɗa masa tea cup ɗaya ta kawo masa ahankali ya karba tare da kaiwa bakinsa da ƙyar ya iya shan rabi ya ajiye Cup ɗin.
Abba bai tilasta shiba dan shima akaran kansa yasan ba zai iya saka komai acikin sa ba baya ga tea ɗin da yake sha dan raya kai, cikin sanyin murya yace.
“Aliyu kaje ɗakin Jameelu kayi wanka ka sauya kaya”.
Girgiza kai yayi cikin rawan murya yace.
“Abba bari in je gida saboda nabar Innayi ita kaɗai tun safe sannan na barta cikin damuwa”.
Kai Abba ya gyaɗa tare da cewa.
“Toh Aliyu ka gaisheta”.
Yana isa gida yayi Parking tare da wucewa Bedroom ɗin sa, kai tsaye toilet ya shiga tare da sakarwa kansa ruwan sanyi sai alokacin ya lura da Dick ɗin sa daya kwanta luƙui tamkar bai taɓa tashi ba tsanananin fargaba da tashin hankali da yake ciki yasa ya kasa tantance shin shi ɗin wani irin halitta ko kuma wanne irin jinsi ne shin shi ɗin namiji ne ko mace baisan matsayin da yake ba bare kuma ace sha'awa baki daya Dick ɗin sa ya kwanta tamkar babu wani abu mai suna sha'awa daya taɓa ji cikin sanyi Jiki ya gama wankan tare da fitowa ya shirya cikin Jallabiya kana ya fesa turare kai tsaye sashen Innayi ya nufa.
Misalin ƙarfe 5:00pm da wasu Mintuna bayan antaso Amakaranta motarsu Ramadan na shiga harabar gidan tayi Parking Ramadan ya ɓude tare da ficewa da gudu.
Acan falo kuwa Mommy da Khausar ce zaune suna kallon TV cikin tashar Nat geo well Suna kallon namomin daji Ramadan ya shigo tare da zama gefen Khausar kana ya langwaɓar da kansa tare da cewa.
“Addah Khausi”.
Hankalinta na kan wasu irin halittun ruwa tace.
“Na'am Ramadan”.
Cikin muryan rauni yace.
“Addah Khausi wai Malam Jameel ya ɓata”.
Cikin sauri ta kallesa tare da riƙe hannunsa kana cike da mamaki tace.
“Malam Jameel ya ɓata kuma!?”.
Kai ya gyaɗa mata kana yace.
“Eh Addah Khausi Moddibo da Malam Arɗo su suka shiga ajinmu suka faɗa mana Malam Jameel ya ɓata ba asan inda yake ba”.
Cike da mamaki da kuma al'ajabi Khausar tace.
“Ha'a wace iriyar magana ce wannan Malam Jameel ya ɓata ba'a san inda yake ba!?”.
Mommy kuwa cike da mamaki take kallon Ramadan kana tace.
“Ramadan ka tabbatar kuwa?”.
Kafin yace wani abu Raudat ta shigo da kuka fuskarta jage-jage da hawaye kana ta zauna kusa da Mommy tare da cewa.
“Wallahi Mommy wai ya ɓata!”.
Da sauri Mommy ta ɗauki wayarta dake hannun kujera kana tace.
“Gashi kiramin Umminsa”.
Amsar wayar Khausar tayi still da mamaki atare da ita tace.
“Eyyy aikuwa Jiya naga miss call ɗin Asma'u bana wajen daga baya kuma da nazo ina ta kiranta bata ɗaga ba”.
Dai-dai lokacin Hajiya Bunayya ta shigo sanye da hijabi har ƙasa kana ta zauna kusa da Khausar dake laluɓo number Ummi ya zama na sun sa Ramadan Atsakiya kasancewar kujeran 2sitter ne.
Bayan Mommy ta amsa Sallamar ta tace.
“Hajiya wai kinji abinda yaran nan suke faɗa wai Malam Jameel ya ɓata!”.
Kai Hajiya Bunayya ta gyaɗa tare da cewa.
“Eh dama baki ji bane aini tun jiya da yamma Aminu ke faɗa min wai yaji Amasallaci ana cewa ayi addu'a Allah ya bayyana ya kuma tsaresa ashe dama ba kiji ba?”.
Kai Mommy ta.
Girgiza fuska cike da damuwa tace.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n Wallahi ban jiba Subhanallah ya Salam Ubangiji Allah ya tsaresa”.
Hajiya Bunayya kuwa ahankali ta saci kallon Mommy sai taga idanunta nakan Khausar data maƙala waya akunnenta cike da dabara ta sake murza turaren dake hannunta kana ta fito dashi ta ɗaura akan Ramadan tana shafa masa aranta kuwa fari fess tana cewa Alhamdulillah wannan turaren dai na samu na shafa masa saura kuma gobe in faɗawa Boka Kar'uzu na shafa masa turaren.
Khausar kuwa jin Asma'u tayi Picking call ɗin yasa cikin sauri tace.
“Asma'u”.
Cikin wata dashash-shiyar murya mai cike da rauni Asma'u tace.
“Na'am Khausar”.
Cikin alamun damuwa Khausar tace.
“Asma'u wai me nake ji?”.
Cikin muryan kuka Asma'u tace.
“Khausar an sace Yah Jameel yau kwana biyu kenan kusan na uku ba Yaya Jameel ba labarinsa”.
Atsorace Khausar ta dafe hannunta aƙirji kana tace.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n ansace Yah Jameel Kuma?”.
Kai Asma'u ta gyaɗa hawaye na bin kuncinta tace.
“Eh”,
Cikin sanyin murya tace.
“Ubangiji Allah ya bayyana shi aduk inda yake Allah ya fito mana dashi”.
Ameen Asma'u ta amsa tare da katse kiran.
Kallon Mommy Khausar cikin tashin hankali tace.
“Mommy wallahi da gaske an sace sa”.
Girgiza kai Mommy tayi tare da cewa.
“Ya Salam wallahi bamu sani ba barin idan Abbanku ya shigo zan tambaye sa muje muyi wa Umminsa jaje Ubangiji Allah ya bayyana shi Allah ya tsaresa aduk inda yake”.
Khausar kuwa kasa tsaida hawayen ta tayi cikin Muryan kuka tace.
“Ameen Mommy Ameen ya hayyu ya ƙayyum Allah ya bayyana Malam Jameel har kwana biyu kuma!?”.
Ta gumi Hajiya Bunayya tayi tare da marairaice fuska kana tace.
“Hakane kam wannan duniyar ta zama abin tsoro idan kana fama da talauci ka banu idan kayi wadata ɓarayi da ƴan Kidnapping su hanaka kwanciyar hankali da nutsuwa Allah dai ya kyauta”.
Ta faɗa tare da miƙewa ta fice ranta fess.
Baki ɗaya Wunin wannan ranan haka Mommy da Khausar suka yita cikin jimami da fargaba musamman Khausar ta gagara tsaida hawayen ta.
Moddibo kuwa yana fita daga sashen Innayi mota ya shiga tare da nufar gidan Abba yana isa ana kiran maghariba tare da Abba suka shiga Masallaci suka gabatar da sallah.
Acan ɓangaren Mommy kuwa bayan an idar da sallar Isha'i ta sanarwa da Lamiɗo suna san zuwa yiwa Ummi jaje nan yace ba damuwa ta kira Khausar da Hajiya Bunayya su fito bayan sun fito da kansa yayi Driving ɗinsu zuwa gidan Ummi.
Bayan sun isa.
Mommy ce agaba sai Khausar sai kuma Hajiya Bunayya bakinsa ɗauke da Sallama suka shiga dai-dai lokacin kuma maƙotansu suka fito.
Zaune suka samu Ummi kan 2sitter tana riƙe da Kur'ani Idanunta sun kumbura sun ƙanƙance yayin da Asma'u ke zaune gefenta hannunta riƙe da Carbi.
Cikin sauri Khausar ta ƙarasa kusa da Asma'u tare da riƙe hannun ta kana tace.
“Asma'u da gaske wai dagaske ansace Yah Jameel!?”.
Cikin zubda hawaye Asma'u ta gyaɗa mata kai kana tace.
“Khausar da gaske ansace Yah Jameel tun randa kikazo ya maida kin nan, har yanzu babu labarin sa yanzu kusan dare na uku kenan za ashiga”.
Khausar ma cikin zubda hawaye ta damƙe hannun Asma'u tare da cewa.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n”.
Kallon Ummi Hajiya Bunayya tayi tare da cewa.
“Ayyah Ummin Jameel Ashe abinda ya faru kenan toh Ubangiji Allah ya tsare Allah ya bayyana shi”.
Kai Ummi ta gyaɗa tare da faɗin.
“Ameen ya Allah Nagode”.
Mommy kuwa kafaɗar ta ta dafa kana tace.
“Ba komai Ummin Jameel kiyi haƙuri ki daina kukan nan ki riƙa yi masa addu'a Insha Allah Ubangijin zai bayyana shi”.
Cikin sauri Ummi ta share hawayenta kana tace.
“Nagode Mommyn Khausar Nagode³”.
Cike da tausayawa Mommy ke sake ƙarfafa mata guiwa.
Ahankali Khausar ta juya tare da kallon Ummi cikin Muryan kuka tace.
“Ummi Allah ya bayyanar da Yah Jameel insha Allah ba zasu samu nasarar cutar da shiba zamu tayi masa addu'a Allah ya karesa”.
Miƙewa Hajiya Bunayya tayi kana tace.
“Bari mutafi Alhj na jiran mu awaje yace a gaidaki".
Kai Ummi ta gyaɗa tare da cewa.
“Nogeda Allah ya saka”.
Sannan suka fita a coumpund suka haɗu da wasu matan sun shigo yiwa Ummi jaje bayan sun koma gida.
Baki ɗaya Khausar ta kasa nutsuwa kafin ta kwanta taje tayi alwala kana ta ɗauki Kur'ani tana ta karatu tare da tawassali dashi da niyyan Ubangiji ya bayyana M Jameel aduk inda yake.
Misalin ƙarfe goma na dare kamar lokacin da aka dauke M Jameel Moddibo dake gefen Abba ya miƙe da niyyar tafiya Akuma dai-dai lokacin wayar Abba dake gabansa ta hau ruri.
Atare Abba da Moddibo suka kalli wayar cikin sauri Abba yayi Picking call ɗin tare da kaiwa Kunnensa.
Daga ɗaya ɓangaren akace Alhj Bashiru mahaifin Jameel ko!?”.
Cikin sauri Abba ya gyaɗa kai tare da cewa.
“Eh nine nayi ta kiran layinku baya shiga”.
Cikin fusatacciyar murya Mutumin yace.
“Dama ce maka mukayi idan ka kira zai shiga?”.
Girgiza kai Abba yayi tare da faɗin.
“A'a to menene sharaɗin ku na biyu kaga ban faɗawa kowa ba!”.
Cikin bauɗaɗɗiyar murya Mutumin yace.
“Kuɗin fansa zaka biya shine sharaɗin mu na biyu”.
Kai Abba ya gyaɗa tare da cewa.
“To nawa kuke buƙata?”.
Kai tsaye mutumin yace.
“Milion ɗari biyu”.
Atsorace Abba ya dafe hannunsa aƙirji kana ya zare ido cikin tsanananin firgici yace.
“Milion ɗari biyu!?”.
Atare Hajiya Bunayya da Moddibo da maganar ya dakesu suka haɗa baki atare wajen cewa.
“Milion ɗari biyu?”.
Cike da gadara Mutumin yace.
“Toh idan ba zaka bada ba sai ka shirya karɓan gawar ɗan ka!”.
Cikin sauri Abba ya Girgiza kai tare da cewa.
“Kuyi hakuri dan Allah dan darajar Annabi kada ku kashe wayar”.
Cikin Yanayin ɓacin rai Mutumin yace.
“To ai mun riga mun faɗa muku abinda ake buƙata idan ka shirya gobe zamu sake kiran ka muji ko ka shirya”.
Yana gama fadar haka ya katse kiran...!
By
*GARKUWAR MARUBUTA*[7/26, 12:46 PM] U.M Collection ZMFR CM: *KNKB3005*
*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*
*09069067488*
*TASTED & TRUSTED*
*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATUN SAIWOWIN MUTANAN CHADI DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZAR AMARE, MASU JEGO DA WADDA TAKE SON GYARA KANTA*.
*AN GWADA ANGA INGANCINSA SHIYASA NA KE TALLATA MUKU DA K'ARFIN GUIWATA*.
*ABIN BIRGEWA DA WANNAN SAIWOWINRL ZAKI YI AMFANI DA SU SAMA DA SAU DAYA.*
*AKWAI FULL PACKAGE, AKWAI RABI, TA YADDA KOWA ZAI IYA SIYA*.
*SANNAN BABU BAURI NA TASHIN HANKALI.*
*DA KANKI ZAKI DAFA ABAR KI, KOMAI ANA SAKA WA A CIKI*.
*SHIN KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR, KO KUWA KE CE KIKE SON GYARA KANKI?*.
*KAYANA NATURAL NE DOMIN SAIWOWI NE DA AKE HAKOSU A DAJIKAN CHADI. BAYAN SAUKAR DA GAMSUWA HAR YAQI SUKE YI DA DRYNESS DA KUMA INFECTIONS.*
*AKWAI NA TSUGGUNO DA YAKE HA'DE MACE TA MATSE.*
*AKWAI HADADDUN DAKA NA SHA DA MADARA KO NONO WANDA BABU ALGUS*.
*SANNAN AKWIA GADALIN MATA NA ASALI, WANDA SHA YANZU NE MAGANIN YANZU DA IKON ALLAH*
*DUKKANSU TESTED & TRUSTED NE*.
*TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU*
*08032773332*
*DOMIN KARIN BAYANI, SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*.
*NATION WIDE DELIVERY*
Ba domin halin da ake ciki ba, da abunda zai hana mutanen Falon Darawa da kalaman Abba.
Ammh yadda zukata ba sukuni yasa ba wanda ya bi ta kan mganar ni dai kuka kawai nake faman yi gabad'aya ji nayi zuciyata ta rufe ba sarari ko kad'an shi ko Ishaq sai da Abba ya kara Dakamai Tsawa sannan ya Dago a Firgice yana rawan bakin fadi'n"Don Allah Abba kayi hakuri. kace zakayi min adalci wlh nasan nayi kuskure ammah na dade da yin nadama ita Fa'iza ta sani na nemi afuwarta da amincewar ta bama auran mu wata Dama Abba.."
Abba ya katseshi a Fusace Lokaci Daya yana Fadi:n"ai baka sonta. ko ba haka ba ne..?
Rantsuwa ya kwaso kamar ya yi kuka Cikin rawan murya yace"Da ne Abba ban da yanzu wlh ina son Fa'iza ita ta sani ina Sonta.."
Ina jikin Abba na rika girgiza kai ina Fadin"Bani kake so ba. Bazaka taba sona ba saboda ba'a sauya Fa'iza ba,ni ce dai Fa'iza bakar nan mummuna, mai raunin ji mara gata yar talakawa wacce bata jin Turanci ba ni kake so ba.
So kake na koma saboda ya'yanka da kuma yi maka gadin gida kamar yadda na Saba, tunda daga kai har matanka ba masu zaman gida ba ne kuna fita aiki"
Na karishe fad'a hawayena suna shata shata kamar an Bude Famfo Goggo tace"Kibar kuka haka Fa'iza wannan ai sai hawayen naki ya kare"
Inno tace"Na yaushe kuma?ku barta tayi kukanta na samun salama ne yarinya ta jima cikin kuncin rayuwa ba'a sani ba irin shi ke sa jini ya haye yayi sama kaji an ce mutum ya Fad'i ya mutu,kayi ta mamaki to shi kadai yasan irin bakincikin da ya rika Hadiya shi kadai"
Kalaman Inno suka kara Tunzura Abba ya kara dagama Ishaq murya yana Fadin"Da baki zaka Fad'a ko sai an kawo maka takarda..?
Rawan muryansa ya kara Daukowa Abba ya Dakatar da shi cikin Kaushin murya yace"Kada ka sake kirana da sunan Abba kirani Usman karaye na. Ishaq ni uban Fa'iza ne kad'ai"
Ya karishe fad'a cikin kaushin Murya har ya nuna sa da yatsa Yaya mariya na gefe ta gyad'a kai cikin jin Dadi Ammi ma ranta fes,Daman tasan Baban Nana bashi da wasa.
Cikin kankantar da kai yace"Kayi hakuri Abba ammh bazan iya sakin Fa'iza ba"
Abba ya kallesa a wulankance Baba Ati tayi karaf tace"Tunda har baka sonta ka saketa mana..?fiye da shekara goma kana cutar da yarinyar nan bata taba mgana ba sai yau kayi mata adalci kaima mana"
Inno ta karbe da Fadin"Ahto mganar Sulhu ai batama taso ba. Mganace fa ta Shari'a Atika haba ai ya cutar da ita abun sam ba adalci aciki."
Mita dai suka fara yi nasu na Tsoffi,Goggo dai tama kasa mgana Domin bata da abun cewa mganar gaskiya auren Fa'iza da Ishaq akwai tarin zalunci in akace Fa'iza tayi hakuri matuka an danne mata Hakkinta da shari'a ta bata.
Mama ce tayi karfin Halin matsowa tana Fadin"Alhaji don Allh ku yi hakuri. Ku yi hakuri ku yafe mana gabadayan mu.
In sha Allahu hakan bazai kara faruwa ba,Alhaji a Duba ko domin yaran nan a bama Fa'iza Hakuri tabi mijinta"
Abba ba domin girman shekarun Mama ba,Tuna baya yaso yayi wato ya mulmulamata ashariya,ammh girman shekarunta yasa bai zageta ba. ammh fa sai da ya auno wata mganar cikin bacin rai yana fadin"Su ya'yaan sun ci kaza kazan su. shekarun ki nake dubawa Hajiya shiyasa na raga miki,Shi ai ba duba Darajan ya'yan ba ya Tozartata kema ai baki duba yaran ba sanda kike Cin mutumcinta,sannan ki saka D'anki shima yayi,yaran ai ba son da ranshi suka zo Duniya ba Tunda ba zabinsa ba ne .Bani da damuwa da yara in suma bai kaunar su ya had'o min duk zan iya Hada su da uwar su na rike in sha Allahu bazan gagara ba ammh Wlh tallahi ba mai maida ma Ishaq Fa'iza ko tace zata kuma. ni Usman karaye sai nayi shari'a da d'an ki wajen karban ma Y'ata Hakkinta.
gwara tun muna ganin darajan juna ki sa kashi ya saketa kafin mu yi mara kyau ni da shi"
Ya fad'a yana Huci ransa gabadaya ya gama baci da wannan renin wayau na uwa da D'anta.
Mama ta kasa mgana sai matsar kwallah yau ga ranar nadama bata taba zaton akawai wannan Ranar ba ta dago tana kallon Goggo wacce ta kauda kanta alamun bani da ta cewa sai ta kalli Ishaq kafin tayi mgana yayi saurin ta shi yana cewa"A'a mama kada ma ki rokeni bazan iya sakin Fa'iza ba. Wlh bazan iya ba..!
Fa'iza! Don Allah ki saurareni"
Ya fada yana kokarin Tunkaro ni Abba ya mike ya taresa cikin wani Kallo na gargadi yace"Kada ka fara. Kada kuskura"
Kaina na Tusa cikin gwiwata ina Cigaba da kuka sai ga Ishaq ya Duka gaban Abba ya rike kafafunsa yana Rokonsa Abba ya kwace kafarsa ya matsa gefe yana Fadin"Ka riga ka bata komai da kanka Ishaq. shi kan shi Dr.Laawal din da yazo har gida ya wulakantamin y'a sai naji Dalilinsa ka bani Takardan Fa'iza kaje ka zauna da wacce ka zaba ya'ya ko zan kara maimaita maka in bazaka rikesu ba ka dawo ma da uwar da su, ita zata rike su tunda tasan Darajan su"
Abba ya fad'a yana kauda kai Ammi Daga gefe tace"Shikenan kuwa Baban Nana mgana ta kare masu cewa ayi Hakuri saboda ya'yaa an kashe bakin su"
Ta fada tana kallon Mama tana Hararanta,duk sai ta zama kamar Mujiya acikin mutane,Ina kuka nayi Saurin Tsaigaitar da kukana na Dago ina Fadin"Abba ba ruwan Zainab da Mahaifinta wanda ya ijiyeni ne ya nuna musu matsayina. In da ace ya nuna musu ina da Daraja abunda ya Faru bazai Faru ba,Mganar gaskiya Zainab bata taba kyamatata ba ta rikeni ni da ya'yana tsakani ga Allah kuma ta kaunace ni shiyasa nima na kaunaceta domin Allah,Wlh ba ruwanta nayi zaman amana da ita da Daraja fiye da yadda mijinta ya Darajani taga kimata fiye da yadda wanda ya ijiyeni ya gani, ka kyalesu Abba mahaifin Zainab ba shi da Laifi kwata kwata.
Abba sai faman Huci yake yi Falon ya yi Shuru Ishaq ya Dake yana ma Abba magiya shi kuma yace ya gama mgana ganin Haka yasa ishaq ya mike ya kalleni nima na kallesa da ruwan Hawayena kafin ya gyada,kai yana Fadin"In kina tsammanin zan sake ki ne to gwara ki sake Tunani Fa'iza.."
Aurena dake har Abada babu Saki"
Mama muje.."
Yafada Lokaci daya yana Saurin barin Falon Abba ya bisa da kiran sunansa ammah yaki juyowa Mama ta mike jiki a sanyaye tana Fadin"Kuyi hakuri. Fa'iza Allah ya baki Hakuri"
Daga haka itana tabi bayansa Abba ya kada kai cikkn takaici kafin yace"Wlh ko auren zobe ne sai ka saketa ishaq. mutumin banza da wofi kawai"
Ina kuka Abba ya Durkusa gabana ya Rumgumeni yana Lallashina fad'i yake"Zai sake ki Dolen shi ma,nayi miki wannan alkwarin"
Ki daina kuka Ba raina ki yayi saboda baki yi boko ba..?makaranta ba'a Nageria ba har kasashen waje duk inda kike so nan zan kai ki samu Ilimi Fa'iza"
Nasan karamci da kauna yasa Abba ya ce min haka ammh ni ba shi ba ne Burina shiyasa na Dago ina kallon Abba kafin nace"Aa Abba bani da sha'awan yin karatun Boko. Har kuma yau bana Nadamar rashin jin Turanci da ba na yi ai nasan Allah kuma ina jin yaransa wato Larabci, sannan ni ba Jahila bace Abba ina da ilimin addini nasan Qur'ani nasan hadisai da Hukunce hukunce Tsarki Abba nasan yadda zan gyara Sallata da Ibadata, Abba ka fad'amin akwai wani Ilimi ne bayan ilimin da Manzon Rahma yazo mana da shi..?
Cikin girgiza kai Abba yace"Babu Fa'iza sai dai zamani ne yazo mana da komai. An ce mu nemu Duniya kamar bazamu barta ba sannan mu nemi Lahira kamar bazamu je ba. kuma ana so kowani Mutum ya Had'a Fukafukai guda biyu saboda zaman Duniya da Lahira"
Duk na aminta da mganar Abba kawai Ra'ayin karatun bokon ne bana so shiyasa nace"Abba ni ba ni da ra'ayi ne kwata kwata ku bar ni kawai"
Da Sauri Abba yace"An barki Fa'iza ki Fada'min abunda kike Bukata ni kuma nan duniya in dai bai fi karfina ba zan yi miki shi"
Cikin jin dadi ganin Abba ya bar mganar Karatu nace"Abba ka karb'omin Shaidar sakina wajen Ishaq"
Da Sauri Abba yace"Nayi miki alkwari"
Sai me kuma..?
Kaina na kasa tace"Ina so na bunkasa kasuwancina Abba shiyasa nake neman alfarman ka barni wajen Goggo kada kace zaka tafi dani Kaduna"
Shuru yayi kafin kuma yace"Na amince zan baki jarin da zaki bunkasa kasuwancin ki Fa'iza. sannan zan barki wajen Goggo har sai ranar ke da kanki kika so dawo wa wajen mu da zama"
Ina Sharan hawaye da bayan Hannuna nace"Zan shiga islamiyan matan aure sannan ina so zan koma Hadda. Ina so na Haddace Qur'ani tunda Sauka nayi a baya ba Hadda ba".
Kai tsaye Abba yace"Nawa zai isheki Hidimar karatun naki..?
Sai hawaye ina sharban su ina zuba ma Abba Godiya sai ya Dafa kaina yana Fadin"Bakomai ki daina kuka Daga yau nayi miki alkwarin Farinciki a rayuwarki har Abada kin ji ko..?.
Na gyada mai kai sai ya Sakeni ya mike yana Duba agogon Rado baki dake Hannunsa Lokaci daya yana Fadin"An yi la'asar ma bari muje mu yi sallah mu yi harama Goggon su da mallam ga amanar Fa'iza nan ban amince Ishaq yazo kusa da ita ba ni da kaina zan karbo mata takardan Sakinta"
Goggo tace"ba kwana zaku yi ba..?
Kai Tsaye yace"Inno da Baba Ati suna nan.
Ni da maman Nana da Abdul'ahad kaduna zamu kwana yau in sha Allahu"
Yadda ransa ke bace yasa bama wanda ya basa baki har Inno shi da Mallam suka fita aka bar ni da Ammi nata faman Lallashina da su Inno Yaya mariya na Fadin"Fa'iza fa ta Dade cikin wannan bakincikin, Allah ne ya kawo karshen abun har kuka ga Haka ta faru"
Ni dai ina jinta ban yi mgan ba. Dakyar na daina kuka na koma Daki nayi sallah ina yi ina kuka,kawai ni yanzu abu daya nake so Ishaq ya Sakeni da gaske nake yi nagaji da auransa
Abba kuwa suna Dawowa masallaci sama sama suka yi mgana da yaya Isa kan in ya koma gida ya natsu zasu yi mgana da Ammi kan kayan da za'a zuba a gidan su kansu sun gansa a Zafafe sun sam zaman bai yi Dadi ba Balle daman suna kofar gidan Ishaq ya Fito shi da Mama cikin wani yanayi Yaya isa bai damu ba a Fidi sai da ya Furta ma Yaya Abdul'ahad cewa Baya so Abba ya Daidaita Fa'iza tabi ishaq Lagos da ya nemi sanin Dalilinsa sai ya Fara fadamasa iya abunda ya sani kan zaman Fa'iza da Ishaq Shima nan take yaji ya Tsani Ishaq din haka kamar wani Dabba shiyasa suna zaune ya fito suna kallonsu yana kallonsu suka ki mai mgana shima baya cikin yanayi mai Dadi..
Katsina suka koma Mama tace ita ya barta gidan Binta kamar yaso yaki Saboda yara yasan Zainab bazata iya kula da su ita kadai ba,ammh sai ya Tuna Badariya zata bi Jirgin Jibi da Rana shi ya biya mata ma kudin jirgin sai Direban da suka yi tasha Daga karofi ya sauketa gidan Anty Binta shi kuma ya karisa dashi kano ya samu jirgin karfe 5pm zuwa Lagos bai yi wata wata ba ya siya Ticket suka tashi sai birnin Ikko.
Anty Binta ita kanta ta tsorata da Lamarin da Mama take maida mata abunda ya faru Rike baki tayi kafin tace"Shi ko Ishaq meyasa yayi haka..?gaskiya bai kyauta ba wannan zalunci ne"
Mama ta ja majina kafin tace"Wlh ban sani ba Binta bai taba Fad'amin ba"
Anty Binta tace"Allah ya kyauta ya bari in Abban Fa'iza ya huce yaje har gida ya kara bashi Hakuri ammh Sakin Fa'iza yanzu ai akwai matsala ni kaina Sai daga baya na Fahimci mganar Baba, da yace Fa'iza ce Matar rufin asiri ga Ishaq Mama"
Mama na sharan kwallah tace"Ni zan Fada miki haka ni da na zauna tare da ita.Ta ci damu ta sha Damu da Guminta,tayi mana suturra bata Duba abunda ya faru a baya ba Zainab din daya ke so bazata iya wannan Rayuwar tare da shi ba.."
Anty Binta ta sauke Numfaahi kafin tace"Sai muje har ni mu bama Abban Fa'izan hakuri. ko don yaran nan Mama"
Mama tace"Anya?bana jin zai yarda ya Dauki fushi daga shi har su Goggon bana jin zai iya Sauke gudurin sa"
Anty Binta sai ta kasa mgana saboda Lamarin ya fi karfinta kafin tace"Yanzu ina shi Ishaq din..?
Mama tace"Ya wuce kano jirgi yace min zai hawo ya koma lagos"
Anty Binta tace"Allah ya kaisa lafiya"
Daganan suka cigaba Tattauna Lamarin.
*****
Kamar yadda Abba ya fada basu kwana a karofi ba Inno dai da Baba Ati suna nan zasu kwana Biyu,Sai Dare suka isa gida,Ranar Abba barci ma rabi da rabi yayi washegari da yaje Office idanuwansa yayi ja matuka alamun baya cikin natsuwarsa,Kansa sai ya fara ciwo shiyasa ya Dawo gida ya kwanta Ammi tasan Baban Nana bai iya Fushi ba ballatana abunda ya shafi yaransa,Dakyar ta Lallashesa yaci abinci ya sha mgani ya kwanta sai bayan La'asar ya tashi ya yi wanka ya Sauya kaya Ammi sun yi waya da su Nana Fatima ammh bata fada musu yadda zaman ya kaya ba.
Nana Fatima sai taji Hankalinta ya kwanta da Ammi tace Fa'i na Karofi har alokacin.
Abba ko Dariya ya Daina yi yana Sakawa da warwaran yadda zai karb'an ma Fa'iza Takardan Sakinta ko Hiran Daran da sukan taba da Hafsah da Nana khadija ranar bai samu ba,Daman kuma Ammi tace bai jin Dadi daga gaisuwa da Tambayan ya jiki ya koma ya kwanta ya Lumshe ido shiyasa suka fice suka koma Shashen Ammi suna Tunanin kila ciwon kan ne ya matsa ma Abba.
Yayi nisa cikin tunanin sa har baisan sanda Maman Nana ta shigo ba itama gajiya tayi da kiran sunansa ta matso kusa da shi tana Taba kafarsa Lokaci daya da kiran sunansa"Baban Nana"
Firgigit yayi kamar wanda ya farka Daga barci sai yaci karo da sanyin Idaniyarsa,Azizat.
Ajiyar rai ya sauke cikin wani yanayi ya kasa mgana Maman Nana ta zauna gefensa,Sai ya matsa ya bata wajen zama ya mike dakyau ya gyara zama kafadunsu na dukan juna.
Cikin wani yanayi Ammi ta kallesa tana Fadin"Haba Baban Nana meyasa..?wannan tunanin da kake yi fa ba mafita ba ne"
Numfashi ya sauke kafin yace"Alkwarin da nayi ma Fa'iza ke damuna Maman Nana na rasa ta hanyar da zan karban mata takardan Sakinta Ishaq bazai yi sakin nan cikin Sauki ba"
Ko na kai shi kara kotu ne..?
Da Sauri ta girgiza kai kafin tace"A'a duk bata kai haka ba Baban Nana. akwai ya'ya tsakani sannan ga zumunci a bi dai komai a sannu. Kowa ya shaida zalunci da Kuntatawa a zaman auren Fa'iza da shi mganar ma yaki sakinta bai taso ba".
Abba yayi shuru ya kasa mgana Ammi ta cigaba da bashi mgana cikin kwantar da Hankali har ya samu natsuwa cikin Sauke ajiyar rai yace"Bakomai nasan ta inda zan Bullo masa"
Ammi tace"kabi a sannu Baban Nana nasan ka sarai"
Mirmishi yayi mata kafin yace"In sha Allahu"
Daganan shi da kanshi ya Rufe mganar bayan ya bude mganar kayan Funitures din da yake so a saka a sabon gininsa na karofi Ammi tace"Ga inda muke siyan kaya kano.
Har gida zasu kai komai su kuma gyara wajen"
Kai tsaye yace"Ki yi lissafin kudin zan Tura miki ta asusun ki"
Da kai ta gyada masa kafin su cigaba da Hiran su sama sama na mata da Miji masu kaunar juna da Fahimtar juna.
A cikin Hiran ne Ammi ta kallesa tana Fadin"Wai ina labarin Engr ne Baban Nana..?kwana Biyu ban ji kuna waya ba hala bai shigo kaduna ba ne..?
Abba yayi hamma kafin yace"Gaskiya satin nan kaf bamu yi waya. Mgana ta dashi ta karshe yace zai je London ina kyautata zaton ya tafi ayyuka ne suka masa yawa kinsan Engr da Sabgogi da yawa fa"
Ammi tace"Sosai fa,ya jikin Hajiya Kudirat kwanaki na kira Hajiya Shukran bata Dauka ba,Azima ta fadamin kwanaki ta shigo ta gaida Hajiya Jikin Hajiya tafisu ne ya matsa tazo Dubata"
Abba yace"Haba tuni ta warware kamar ma Engr yace min ta saka rigima sai ta koma Benue ,Lokacin muna Warri tare da shi naji an kirasa ana fadin ya Lallasheta yace rigimmiyar Tsohuwa a barta tatafi mana"
Ammi tayi Dariya kafin tace"Kai a wannan matar akwai rigima wlh,ka tuna da mukaje dubata sai Yarbanci take tana masifa saboda za'a bata mgani sai da D'anta yazo ya lallasheta ta yarda fa"
Abba na mirmishi yace"Engr na yawan Fadin rigimarta tana matukar son mahaifinsa da su kansu tunda shi kadai take da shi ance Haihuwanta Goma tara duk sun yi wabi ne shi kadai ya tsaya"
Ammi tace"Allah sarki.."
Nan ya cigaba da bata wasu labaran itama tana bashi wanda ta sani Dalilin Hajiya Tafisu,Suna ta yabon kirkin Engr da iyayensa.
Abba yace"Muna da Seminar a Abuja sai dai ban sani ba ko zai samu zuwa"
Ammi tace"To kila in yana gari"
Abba yace"Ba lalle ba gaskiya"
Da haka suka rufe wannan Hiran suka Fara shirin kwanciyaa
*******
Tunda ga ranar da Abba ya bar Karofi, Rana bazata tab'a fitowa ta fad'i Abba bai kirani mun gaisa yaji Lafiyata ba.
sannan ya turamin 100k na bunkasa kasuwancina mganar makaranta kuma Mallam yace a jira sakin ya tabbata nayi iddata in nagama ina da Damar fita duk inda naga Dama,Da haka sai na Dakata ammh na samu natsuwa da kwanciyar Hankali,sannan na fara maida jikina,Goggo na da almajirai masu Dibo ruwa da sharan Tsakar gida gyaran Daki kawai nake yi sai Girki,Yarana kuma muna mgana da su ta wayar Zainab ammh ba ko da yaushe ba,Goggo da kanta ta shiga kasuwa ta min siyayyan kayan zobo da Kunin Aya,aka sauke a dayan Dakin inda na saka Freezer dina sana'ata zata dawo gadan gadan tunda zaman bazai min Dadi ba.
Goggo ta aikamin makota yaya mariya ma haka tunda nan kusa da su suna siya Lokacin da ta kan sara a wajena shiyasa da na fara Zobo ba laifi ana samun ciniki matsala D'aya na samu Rashin wuta in nayi kunin aya sai ya fara Lalacewa kafin ya kare Tunda ba ciniki ba kamar Lokacin ina katsina ba.
Da na fad'ama Abba ana matsalan wuta batare da sanina ba Sai ga Yaya Isa da katon Generator in ji Abba sai dai na kira nayi Godiya Baba Ati na nan bata koma ba,Inno dai Abba ya Turo Direba ya Dauketa zataje ganin Likitan ido.
Gida kuma Tuni ma'aikata sun zo sun kawata gidan da kayan Furnitures masu kyau muma mun je mun gani mun kara gyara gidan nan Su Abba zasu rika sauka Tunda Baba Ati tace bazata iya zama ita kadai ba.
Muna waya da Anty Fadila kuma tana zuwa duk weekend tana Duba su Amir suma Baban nasu na kawo su Tunda yaga sun shaku da yaranta.
Mama bata koma Lagos ba tana katsina wajen Anty Binta sai dai Badariya da Jamal suna chan Zainab ga Tsohon ciki ammh haka ta fara zuwa aikin da Mahaifinta ya samar mata sannan kuma ya siya mata Motar da zata rika zirga zirga aciki ta Riga ta sadakar maman Amir bazata Dawo ba.
Shi kan shi Uban gayyar tun bayan Tafiyarsa sai kirana yake yi ban taba Dauka ba,in dai naga shine ammh ina Daukan kiran Zainab Saboda nasan ko ita ko yara ko kuma Badariya,Har Jamal ma yana kirana duk korafin su Daya na dawo sai dai na bisu da toh ammh su kan su sun tabbatar da bazan Dawo ba.
Dad'ina Daya da su Amir suka fadamin sai la'asar suke tashi daga makarantar Boko,gidan Anty Fadila suke zama saboda yaranta suna da Malamin islamiya in suka yi karatun Tare babansu in ya tashi aiki sai ya Biya ya Dauke su,Zaman su sai asabar da Lahadi shima gidan Anty Fadila suke yin shi Zainab fama take da kanta Ko nata ya'yan su Amir ke kula da su sai mai renon da ta zo da'ita.
Ashe bani kadai Ishaq ke kira ba Harda Abba shima bai kara Saurarensa ba domin yace in yana son mgana da shi ya rubutamin Takardan Sakina,Tun bayan Lokacin Abba bai zo Karofi ba sai dai Hafsah da Nana Khadija sun zo sun yi Sati Daya suka koma Hafsah ta zama katuwa tayi jajir da ita ta samu Waddatccen hutu da jin Dadi.
Ba Laifi sana'ata ta Dawo kuma Tunda aka ganeni ana ciniki sannan Goggo tasan almajiranta na Dauka su tafin da shi wata makarantar maza ta secondary sai kudina suma da suka gane har gida suke zuwa siya in ba Wuta sai na Tada in ji na,Ganin aikin namin yawa yasa Goggo ta ce na Dauki wacce zata rika taimakamin nan makotan su Goggo na samu wata Jummala Mijinta ya rasu tana da marayin ya'ya ita mukayi ciniki da ita zan rika bata 5k duk wata ta amince da Murnan ita ke Dafamin zobo ta kuma wanke aya ta kai nika nawa kawai Dubawa da zaman Had'awa sai aikin ya Ragemin Kuma Alhamudulillah sai Hankalina ya Dauke Damuwa ta rage samun Muhalli a zuciyata,Saboda ayyukan dake gabana.
Yaya Asiya duk abunda ya Faru Labari taji mun yi mgana ta waya abu daya tace min"Fa'iza ki zauna ki yi Tunanin makomar rayuwarki in rabuwa da Ishaq mafita ce gareki zamu baki Goyon baya,in kuma komawarki itace Mafita Fa'iza ki koma Dakin ki ki Rumgumi ya'yan ki''
Da toh kawai na amsa mata Saboda bani da abun ce mata komai zan Fad'a bazata gane ba Makotana ma muna waya da su barin ma Sa'adatu sai dai ban taba Fada musu ina Karofi ba na barsu a ina Lagos ne Haka ma Hajiya sai dai ita nasan Kila Raliya zata Fadamata ammh har Lokacin batamin mgana ba,Sai nima na share ban mata ba,na maida jikina duk da ramar kasusuwan wuyana basu shige ba,Sai dai sun fara shigewa din
Koda yaushe Nasiha ne tsakanina da yan'uwa suna Lallab'ani Saboda na samu kwanciyar Hankali kuma na samu matuka.
Anty Binta ta kirani sau biyu tana min Daidaiciyar mgana na bita da Toh,ta kuma saka har Anty Mahma da Halisa suka kirani duka mganan su kan ya'ya ne na koma Saboda su,ni ko bana cewa komai sai dai toh, sai yanzu suka san da yaran..? Bazan kara bari Saboda ya'yana a cutar dani ba.
Suna ta so na koma ne na cigaba da Bautar da na saba ina bakin Alkalami ya Riga ya bushe ba Ishaq ba gabad'aya maza ne da aure ya fita kaina kwata kwata.
*******
Ranar litini da Safe mukayi mgana da Abba zai je Abuja suna da Seminar,kwata kwata Abba bai Fad'amin niyyarsa ta zuwa Lagos ba ashe haka ya kudurta a ransa,sun je sun yi seminar na kwana Hudu ma'aikatansu uku kaduna,Edo,da Warri suka hadu a wajen,Tattaunawa ta musamman kan bunkasa mai a Nageria,Engr bai zo ba yana London shiyasa ranar da suka gama Seminar din Washegari jirgin Safe yabi zuwa Lagos yana sauka a Tashar Saukan Jirage na Murtala muhammad ya samu Taxi har Headquater tattara Haraji na reshen jahar Lagos.
Yana zuwa sunan Ishaq kadai ya Fad'a aka masa jagora har Office dinsa misalin karfe 11am na Safiyar Ranar jumma'a. Ishaq sai dai kawai yaga Abba cikin Shigar Suit bakake ya shigo office dinsa.
Cikin Rawan jiki ya mike yana rawan bakin Fadin"Abba.."
Abba bai damu ba shi da kansa ya samar ma kansa wajen zama Ishaq ya kasa zama Jikinsa ya fara rawa sai zufa Duk da sanyi A.c din dake Office d'in ya san mganar data kawo Abba. shi kuma Rabuwa da Fa'iza daidai yake da Lalacewar rayuwarsa gashi nan yanzu ko cikakken abinci baya ci,Badariya ta gama Hutunta ta koma kano,Zainab bata zaman gidan koma tana nan ba iya girki tayi ba Sai dai fa ya rika siya,me renon ne ma kan yi ma yara abinci da daddare in sun dawo makaranta shi kuma bazai iya cin abincinta ba,Kudinsu duk a Restaurant yake karewa wajen siyan abinci.
Sanda ya dawo din nan dakyar ya Lallashi su Anum da karyan Umman su zata dawo in ta gama karatun data fara,rigima suka yi masa sosai sai da yakai su gidan Anty Fadila suka yi weekend yace ta lallashesu sannan suka Daina rigima Allah ya taimakesa makaranta ya Dauke musu Hankali da kiran Umma,ammh Tabbas yasan Fa'iza ce ginshikinsa yau in da ta nan da da shi da yaransa basu taggyara ba.
Abba ya gaji da ganin Ishaq a tsaye sai ya karkace ya dauko karamar Jakar Briefcase dinsa ya zaro wata Farar Takarda, da Biro ya Sauke a gaban Ishaq Lokaci daya yana Fadin"Ka zauna mana"
Ya fada yana nuna masa wajen zama Jiki ba kwari ya koma ya zauna a Dofane,Zufa har tana gangaro masa ta saman Goshinsa Abba ya Daure Fuska ya gyara zaman Tie dinsa cikin kaushin murya ya tura ma Ishaq Takardan zuwa gabansa yana Fadin"Ka da ka batamin Lokaci ina kan Hanya ne"
Ishaq yaji kamar zuciyarsa zata bar Jikinsa Cikin rawan jiki yace"Abba.."
Hannu Abba ya Dagamai murya a kausashe kafin yace"In har ka yi abunda nake so shine kake da Hurumin kirana Abba"
Daga haka ya koma ya Hade ransa kamar bai taba Dariya ba Ishaq ya Kallesa Yaga ba wajen da zai yi wargi sai yaja Takardan ya Dauki Biron Jikinsa na rawa da Hannunsa ya kasa Rubutawa ya sake Dagowa yana kallon Abba kafin yace"Abba Baba ya ce min duk ranar da na saki Fa'iza bai yafemin ba.."
Abba ya daga murya a Kausashe yace"Zai yafe maka mana aure ai rai garesa ya mutu ne, Kuma kada ka manta a jingine auran yake karisa ballasa kawai zakayi"
Ishaq ya bude baki zai yi mgana Abba ya Dagamasa hannu yana fadin"Zaka rubuta ne ko sai kaji sammanci..?
Yadda Abba yayi ne yasa Ishaq yasan bai da zabi.
Sai ya sunkuyar da kansa kasa ya Fara Rubutu zufan goshin sa na Diga Bisa Farar Takardan gabansa.
*Janafty*
[7/26, 6:26 PM] U.M Collection ZMFR CM: *KNKB3006*
*TASTED & TRUSTED*
*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATUN SAIWOWIN MUTANAN CHADI DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZAR AMARE, MASU JEGO DA WADDA TAKE SON GYARA KANTA*.
*AN GWADA ANGA INGANCINSA SHIYASA NA KE TALLATA MUKU DA K'ARFIN GUIWATA*.
*ABIN BIRGEWA DA WANNAN SAIWOWINRL ZAKI YI AMFANI DA SU SAMA DA SAU DAYA.*
*AKWAI FULL PACKAGE, AKWAI RABI, TA YADDA KOWA ZAI IYA SIYA*.
*SANNAN BABU BAURI NA TASHIN HANKALI.*
*DA KANKI ZAKI DAFA ABAR KI, KOMAI ANA SAKA WA A CIKI*.
*SHIN KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR, KO KUWA KE CE KIKE SON GYARA KANKI?*.
*KAYANA NATURAL NE DOMIN SAIWOWI NE DA AKE HAKOSU A DAJIKAN CHADI. BAYAN SAUKAR DA GAMSUWA HAR YAQI SUKE YI DA DRYNESS DA KUMA INFECTIONS.*
*AKWAI NA TSUGGUNO DA YAKE HA'DE MACE TA MATSE.*
*AKWAI HADADDUN DAKA NA SHA DA MADARA KO NONO WANDA BABU ALGUS*.
*SANNAN AKWIA GADALIN MATA NA ASALI, WANDA SHA YANZU NE MAGANIN YANZU DA IKON ALLAH*
*DUKKANSU TESTED & TRUSTED NE*.
*TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU*
*08032773332*
*DOMIN KARIN BAYANI, SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*.
*NATION WIDE DELIVERY*
*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*
*09069067488*
Hannunsa na rawa zufan goshinsa bai bar Diga saman Farar takardan gabansa ba.
Abba ya had'e rai ko kad'an bai yi fara'an da zai fuskanci saussauci ba sai da yaga ya jima yana rubutun sannan ya mika hannu yana Fadin"Sakin kawai na bukata in ka Rubuta bani takardan kawai"
Kansa na kasa ya turama Abba Takardan ya saka hannu ya Dauka bayan sallama sai Saki d'aya da yayi ma Fa'iza,daganan sai ya dora kalamai Lausassu zuwa ga Fa'iza.
Abba bai gama karantawa ba ya ninke Takardan ya maida cikin jakarsa sannan ya Dago yana kallon Ishaq Lokaci d'aya da sakin Fuska yana kare ma Office kallo kafin yace"Masha Allah Office yayi kyau sosai.."
Shi dai yana zaune ya kasa mgana ji yake yi kamar an zare mai jijiyon kuzari a jikinsa,wani irin sanyi jikinsa ya yi sanyin da bai taba yi ba mamakin Abba ya kamashi yadda ya raba shi da Fa'iza sannan ya zauna yanata jansa da Hira.
Ko kwakwaran mgana ya kasa sai dai ya rika bin Abba da ido da suka fad'a kamar wani Mara lakka ajikinsa.
Abba kuma yaki tafiya sai ma gyara zama da yayi yana fadin"Ya yanayin aikin naka? fata dai ba wata matsala ko..?
Ishaq kansa na kasa ya gyad'a masa kansa kamar wani Tsohon kadangare,Abba bai damu ba ya cigaba da fadin"Allah ya taimaka ka maida Hankali in kana da wata matsala ka kirani kai Tsaye ka fad'amin har gobe har Jibi ni Uba nake gareka kaji ko..?
Nan ma kai ya gyad'a kamar kadangare. Ishaq aransa yana fad'in kaji Cuta ka rabani da matata kuma kana cemin kai Uba na ne"
Abba kamar bai Fahimci yanayin da Ishaq ke ciki na son kadaici ba, ya gyara zama yana bashi Labarin Seminar da sukayi a Abuja ta kwana Hudu Ishaq takaici da bakinciki suka yunkuro masa, ammh ya kasa mgana Abba kwarjini yake masa sannan duk Rashin kunyarsa Abba yafi karfi nan a wajensa.
Abba sai ya kallesa ganin sai mutsu mutsu yake yi ya kasa zama waje d'aya a saman kujera cikin kulawa yace"Fitsari ka ke ji ne..?
Nan ma ya girgiza kai kawai sai Abba yace"To ina ga Basir ke damunka ka nemi mganguna naga baka iya zama waje D'aya, sai Faman muskutawa kake yi kamar mai kurga"
Sai a alokacin ya Dago yana kallon Abba kamar almajirin da ya yini yana yawo bai samu abinci ba haka ya lamgwabe kai ya kasa mgana. Ga takaicin mganar Abba ga Sakin da ya yi ma Fa'iza sai daga baya yaji meyasa yayi Saurin barin Hargagin Abba ya yi Tasiri a kansa..?
Yana wannan Tunanin yaji Abba ya katseshi da Fadin"Ina su Amir da Amaryata Anum..?
Duk suna makaranta kenan..?
Sai alokacin ya iya bude baki murya kamar wanda aka shake yace"Eh suna makaranta sai 1pm zasu tashi tunda yau Friday"
Abba yace"Allah sarki da suna gida da naje na Duba su ammh bakomai akwai Next time bari na zo na wuce Daman sakon nan nazo karb'a ,sannan naga Sabon Office dinka kuma nagani Allah yasa albarka kaji ko..?
Yafada Lokaci d'aya yana mikewa,Jakarsa ya Dauka ya rataya Dakyar Ishaq ya iya mikewa kamar ma Jiri yake gani bakinsa na rawa yace"Gidan Anty Fadila zaka biya Abba..?
Kai Tsaye Abba yace"Daganan sai Filin Jirgi daman abunda ya kawoni Lagos kenan"
Har Abba ya yi masa sallama ya fice ya kasa Daga kafa ya Bisa Saboda yadda suka yi masa sanyi da nauyin Dagawa ko da ya samu ya Turasu dakyar ya fita har taxi din data kawo Abba ta mika da shi sai ya yi Tsaye Sototo na rashin mafita yana jin Tsigar jikinsa na tashi kowani Kofofin Fatarsa iska ya samu sararin shiga yana Hurasa da jan kafa ya juya ya koma Office dinsa cikin mummunan yanayin da bai taba tsammanin zai shiga ba.
Abba kuwa yana filin jirgi ya yanke shawaran kiran Mallam mijin Goggo yaji salama da ya cikama Fa'iza alkawarinta,bayan ya samu mallam a waya sun gaisa kai tsaye yace masa"Mallam ka fad'a ma Fa'iza ta fara kirga iddanta daga yau, na karbo mata Takardan Sakinta a wajen Ishaq"
Sai mallam ya yi shuru kafin yace"Allah yasa haka shine mafi Alheri. zan gayamata in sha Allahu Alhaji"
Da haka suka yi sallama,Daganan ko minti Talatin bai yi ba jirgi ya sake Daukansa zuwa Abuja dagachan zai samu Mota zuwa kaduna.
Mallam kuwa Suna gama waya da Abba ya kira Goggo dakinsa ya fad'amata yadda suka yi da Abba. Goggo itama sai da tayi jim kafin ta Sauke Numfashi tace"Mutuwar aure bai da Dadi ko kad'an mallam"
Kai tsaye yace mata"Umarnin Allah ne. ammh an ce duk sanda akayi saki sai al'arshin Allah ya girgiza"
Goggo ta jinjina kai cikin wani yanayi kafin tace"Allah ya zaba mafi alheri. Allah yasa hakan shine alherinta su kuma yaran Allah ya raya mata su ya shirya su"
Ya amsa da Ameen Ameen kafin ya Dora da Fadin"sai ki fad'amata da wuri Saboda ta fara Lissafin iddarta"
Goggo tace"Sai tayi idda mallam..?Naga shekaru bakwai basu had'a Shimfida ba"
Mallam yace"Ai da ba su taba Had'awa ba ne sai kice haka,ammh har da zuru'a tsakani fa ba tantama ya Dora mata Iddarsa"
Sai Goggo ta jinjina kai kafin ta fita tana Fadi'n zata shaida min.
Lokacin da Goggo ta fito Daga Dakin mallam muna Tsakar gida ni da Jummala muna had'a zobo muna yar Hira sama sama sai Goggo bata katsemu ba sai da muka gama muka jera su cikin Frezer na kira Almajirin Goggo ya tadamin min inji Tunda ba Wuta.
Na koma Daki nayi wanka nayi sallar azahar ina zaune ina Salatin Annabi Goggo ta shigo itama sanye da Hijabin da alamun itama sallar ta Idar gefen katifar gadon ta zauna sai da na Shafa na Dago ina fadin"Goggo yau me zamu ci..?
Kai tsaye tace"duk abunda kika Dafa"
Bata bari na sake wata mganar ba tace"Yau nawa ga wata..?
Na kalleta kafin nace"Sha hud'u ga watan jumada ula Goggo"
Sai goggo ta dora da Fadin"Daga yau ki fara lissafin iddarki"
A bazata mganar tazomin sai na Kurama Goggo ido cikin wani yanayi ganin ta mike tana shirin barin Dakin yasa nace"Goggo.."
Ban karisa ba ta juyo tana Fadin"Ishaaq ya sake ki. Baban ki ya karbo miki Takardan ki"
Daga haka ta fice sai naji wani irin Sanyi ya ratsani tundaga sama ta har kasan kafata sanyin da kamar ina cikin kankara na kasa Fassara irin yanayin da nake ciki.
Sai naji na koma na gyara zama Dabas yanzu shikenan ba zan kara zama tare da yara na ba..?
Sai kuka ya tasomin hawaye wani na korar wani,Ammh kuma zuciyata dake cikin kunci naji tana Bud'ewa wani iska mai Dadi na kadani kamar an Saukemin wani kaya mai nauyi a saman kaina.
Sai na Daga hannuwana sama ina Fadin"Ya Allah ga baiwarka nan Fa'iza Mafitan alheri na rokeka kan aurena da Ishaq Tunda ka zab'amin wannan mafitan nasan itace alherina na kuma Karbeta da Hannayena Biyu, Allah ya shiryamin yarana Allah ka kare su da kariyar ka ka jikansu da jikan ka ya Allah'"
Haka nayi ta maimaitawa kafin na Shafa,na Dauka zan ji na Damu sai kuma Lokaci d'aya na watsake na cigaba da Harkokina,Dambun Shinkafa nayi mana na zogale.
Goggo nata mamakin walwalata ita da mallam,Anty Nasara da Yaya mariya suka zo gidan ni dai ban fad'a musu ba sai Goggo ce ta fada musu suka kalleni da mamaki ina wasa da Abul dan wajen Anty Nasara.
Goggo tace"Hakika da an matsama Fa'iza ta koma auran Ishaq da an cutar da ita, kalli yadda take fara'a yau kadai da akace ba auransa a kanta"
Yaya Mariya tace"Alhandulillah yau Allah ya raba Fa'iza da wannan kaddareren auran"
Anty Nasara ta Dora da Fadin"Yadda bataji dadin auren ba ne auren gabadaya ya fita a kanta. Allah yasa hakan shine alheri"
Nan dai suka cigaba da mganar ina zuwa wajen kuma suka yi shuru,ban nuna wani abu ammh nasan mganata suke yi.
Sai dare Abba ya kirani ya kara Jaddamin shima yayi mamaki da bai ji ni cikin Damuwa ba,sai Hankalinsa ya kwanta ya kara tabbatar ma kansa da gaske nake nagaji da aure da Ishaq rabasa shine alheri,shima a bangaransa Ammi kada'i ya fad'amawa ta ko rangada guda,Abba ya kalleta cikin mamaki kafin yace"Sakin auren kike ma Gud'a Aziza..?
Ammi tace"Baban Nana aure dai irin na Fa'iza a tayata Barka da arziki".
Mirmishi kawai yayi bai yi mgana ba aransa yana jin farinciki ganin yadda nima Farincikina ya soma dawowa.
****
LAGOS.
*9:30pm*
Da wuri yau Ishaq ya tashi daga Office kamar zazzabi yaji zai rufe shi bayan tafiyar Abba,ba kowa a gidan sai Jamal sai shema'u mai renon yara.
Mama na katsina bata dawo ba sannan Zainab na wajen aiki.
Anty Fadila ya kira yace in Direba yaje daukan yara ya kawosu gidanta sai yammah Jamal zai zo daukansu taji muryansa ba Dad'i ta tambayeshi sai yace mata bai jin dadi tayi masa sannu da haka suka yi sallama.
Sa ni yayi ko sun dawo abinci da zasu ci ma aiki ne,yarinyar nan kuma bata iya komai ba sannan ma ai girkin gidan ya yi mata yawa yaushe zata iya.
Shima ranar kwance ya yini salla ma agida ya dinga yi ruwa ko a cokali bai sakama cikinsa ba.
Gabadaya yadda ya tafiyar da zamantakewarsa da Fa'iza ya ke hassowa ta wani Fanni bai ga Laifinta ba, ya zauna da ita cikin Kaskancin Rayuwa da zalunci da mugunta bai taba mu'amalatan Fa'iza da kyakyawan zamantakewa ba.
Ammh ai ya gane kuskuransa ya nemi gafaranta yasan Tunda Fa'iza ta iya bude baki tayi mgana ko duniya zata hade bazata Dawo ba. shiyasa kawai ya Rubuta takardan sakin nan ammh ji yake yi kamar an zaremai wani lakka mai amfani a jikinsa.
Zainab ya yi ta jira sai 6pm ta Dawo gidan har Jamal yaje ya Dauko su Amir, Anty Fadila tace ya barsu su kwana Tunda sun sake suna ta wasa sannan suna Haddan Qur'ani gobe asabar, sai jamal yace bari ya tafi dasu goben sai su dawo.
Shema'u ke taimaka ma yaran sun dawo basu da yunwa ammh yasha takaici da ya fito falo sai yaran ke Budurin su Zainab bata dawo ba.
Kuma shidda na yammahn data shigo wai ta gaji Dakinta ta shige ta kira shema'u D'akinta ta na matsa mata kafafunta da sunan sun kumbura.
sannan bayan ta gama ta saka ta Had'a mata ruwan wanka ta shiga ta gasa jikinta, basu hadu ba sai wajen takwas da Rabi na Dare ya dawo daga sallar Isha'i ya iske yaran na kallon Cartoon a Falo Farhan ne yazo wajensa yana Fadin"Daada yunwa nake ji"
Anum ya kallah Dake zane a Takarda ya Kira sunanta ta taso fuskarsa ba Annuri yace"baku ci wani abu ba ne..?
Anum tace"Eh Daada naso na Dafa mana Indomie Yaya, yace ka hana mu kunna gas"
Yaya suna nufin Amir tunda shine Babban su,Ba shi ma a Falon yana Dakinsu yana karatu yana kaunar yaron Sanyin Halinsa kamar na Fa'iza ne
Ya sani shi ya hana su kunna gas a farko dawowar su Anum na karambani Tunda duk ta iya wasu ayyukan wajen Fa'iza kai ya kad'a kafin yace"Ina Antyn ku..?
Anum tace"Tana Dakinta tun dazu"
Tsaki yaja a fili Zainab bata da wani amfani ko zama da yaran fa batayi taji matsalan su,Bai ga shema'u ba ya tabbata ita ta sakata wani aikin illai Anum tace wanki take yi ma Anty a bayan Compound ko Tsayawa bai yi ba ya Sauke Farhan Jamal ya kwalama kira ya fito da jallabiya a jikinsa shuru dai har yanzu sunansa bai Fito har yan Batch b sun tafi camp.
Kudi ya basa yace ya yo takeaway din abinci yadda zai isa duka gidan Jamal ya karba yana jin Tausayin ya'yansa da kuma kara kyamatar aure irin auran yayan nasa ta wani Bangare bai jin Hauahi Anty Fa'iza ba. yasan hakan ma wani Darasi ne Allah ya fara nuna ma yayan nasa
Key din motar daman na Hannunsa daganan ya fice sauran yaran su Ahmad Hankalin su na wajen kallo basu bi ta kansa ba,sai yace Anum ta kula da su ya shige Dakinsa shima wanka yayi ya watsa ruwa ya saka Gajerun wando ya kwanta Ruf da Cikin kansa ke saramai sannan makogaransa ya Bushe ammh kuma bai jin shan komai.
ko cin wani abu shi dai ga shi nan yana jinsa kamar wanda ya Tafka wata mumnunan asara.
Zainab bata nemesa ba shima yaki nemanta ta kansa yake yi,Bayan jamal ya Dawo ne ya shigo Dakinsa ya kawo masa key din mota da chanji yana daga kwance ya ce ya ijiye key din saman dirowa kudin kuma ya rike ya yi masa godiya ya fice.
Shi da yaran suka rika Budurin abincin Jamal ya kira Anum yace ta samu Filet da Ruwa da lemu ta kai ma Daada nasa tunda Zainab bata fito ba. Nata ma A kitchen suka barta mata basu san tayo takeway a Hanya ba taci ta koshi abunta.
Yana kwance Anum ta shigo da abinci Farar shinkafa Miyar kaza sai maltina da ruwa.
Ijiye wa tayi a saman Cafet tana Fadin"Daada ka tashi kaci abinci"
Yana daga kwancen ya Dago yana kallon Diyar tasa kwallah ta cika masa ido Fa'iza da ya'yanta sune sanyin Idanuwansa ko yaki ko ya so.
Saurin daidaita yanayinsa yayi da Fadin"Anun maida abincin nan ban ji Dadi. bazan iya ci ba"
Sai ta Rude ta fara fadin"Meke damun ka Daada..?in kawo maka panadol..?
Da Sauri yace"Ina da shi in na tashi zan sha ki barmin ruwa ki je ki kula da kannen ki,ku kashe kallo ku yi karatu Gobe akwai karatu a gidan Anty Fadila"
Da toh ta amsa mai ta fice da abinci bayan ta ijiye mai ruwan har ta fice tana waigensa,Shifa sai da yaransa su kula da shi ban da Zainab,Musamman Amir da Anum suna da karancin shekaru ammh Tarbiyan da suka samu yasa suna abu kamar manya,Da farko in yaga Fa'iza na matsa musu kan karatu da sauran su,sai yayi ta ganin iyayin ta nw sai yanzu yaga amfanin shi,Ko da bata nan yaran basu yada Tarbiyanta ba. barin ma Amir yana kokarin taimaka ma kannensa kan karatu musamman ma Da yanzu yake ganin ba Umman su dukkan girman ya hau kanshi,sai ya kama kanshi yaran suna girmama shi ko mgana yayi yanzu zasu shiga taitayinsu,Shima ganin haka yasa in dai ya Dawo yana tare da su ga Jamal ma yana shiga cikin su shima yana kokari wajen nuna musu abunda basu gane ba.
Zainab dai ya'yanta ma bata san yadda zata kula da su ba ballatana ya'yan wasu,Dalilin haka yasa yaso Fa'iza ta dawo lamarin fin karfinsa yayi.
Anum na fitowa Daga Dakin Ishaq suka ci karo da Zainab da Cikinta a gaba tana tafiya Dakyar sannu Anum tayi mata ta amsa tana fadin"Ya kika Dawo da abincin Anum..?
Anum tace"Anty Daada yace bayajin Dadi bazai ci ba"
Bata yi mgana ba ta raba ta gefenta ta wuce Dakin yana kwance yadda Anum,ta barsa yaji shigowarta da mganarta"Honey whta wrong with u Anum tace kace a maida abinci baka da Lafiya..?.
Tafada Lokaci d'aya tana zama wajen kafafunsa sai ya janye ya yunkura ya mike zaune ya Dafe kansa,matsowa kusa da shi tayi tana fadin"Honey..Honey..!
Saurin Dagowa yayi ido jajir yace"Lafiya na kalau,na Rabu da Fa'iza yau na saketa"
Zainab ta zaro ido kafin tace"Ka sake ta fa Honey..?Maman Amir din..?
Da kai ya gyad'a mata yana jin wani Rauni na saukar masa.
Zainab sai ta shiga Tafa Hannu kafin tace"Kayi wauta honey why..?
Wani irin banzan kallo ya jefeta da shi,kamar ya daketa sai yaji duk Haushin Abba ya huce a kanta cikin Fad'a ya mike yana Fadin"Naji ni wawane ko Zainab?nasan haka dole zaki ce nayi wauta mana duk ba ke kika jamin ba. Sanadin auran ki yasa na jinginee aurena da Fa'iza na kuma zabe ki a kanta Dole yanzu kice na zama wawa mana"
Ya karishe fad'a cikin bacin rai idonsa ya Rufe kamar ya kama Zainab da Duka haka yake ji kamar duk itace Silan komai,Zainab ta saki baki galala tana kallonsa ta mike dakyar da Cikinta a gaba tana Fadin"A'a Honey kada ka doramin Laifi what i do..?
Abunda ka shuka ne kake girba ni ba ruwana"
Tafad'a Lokaci daya tana dagamai kafad'a irin bata damu ba. ransa ya kara baci ya nuna kansa yana fadin"Ni ne kike fad'ama haka..?
Zainab ta fara tafiya tana tura cikinta gaba tace"ban fad'i karya ba. Honey ka sani kaima abunda ka yi ma Maman Amir baka kyauta ba"
Har ta fice ya kasa motsi,saboda kalamanta gaskiya ta fad'a duk abunda ya faru shine sila,ga shi yanzu abunda ya faru Allah ya barsa da zabinsa ya ga yadda zai yi kansa ya kara Dafewa kafin yace"Allah na Tuba. Allah ka dawo min da Fa'iza"
Aransa yaji bazai karaya ba Kafin Fa'iza ta fita idda zai kara gwada sa'arsa.
Ranar haka kowa ya kwana ad'akinsa yaran kawai ya fita ya Duba sai da ya Tabbatar sun kwanta da Safe kuma Shema'u ta dafa ruwan zafi suka sha Tea,wanka kuma Anum da Amir ke yi musu suna taya kananan shiryawa. Jamal ya kwashesu zuwa gidan Anty Fadila dayake bai da Fita Office sai ya koma Daki yayi kwanciyarsa yana jinyar zuciyarsa Zainab bata kara nemansa ba shima bai nemeta bala'in Haushin ta yake ji.
Ita kuma aranta tana fadin meye nata da zai zargeta..?tun adaran ta kira Daddy ta sanar da shi abunda Ya faru Tsakaninta da Ishaq,Dr.Lawal ya yi Tsaki kafin yace"Ki kyalesa dota in ya matsa miki ki biyo jirgi ki Dawo gida. ni ina sonki na kuma san Darajan y'ata.."
Aransa daman yasan Engr Usman bazai kyale Ishaq ba. su ina ruwan su basu sukace yak'i Daraja matarsa ba.
Wannan shine in da ka raina inda zaka na ran maka"
*******
Bayan Sati biyu.
Kimanin Sati biyu ina cikin Iddata zuwa Lokacin tuni Labari ya bazu a ko'ina wanda ma ba'ayi Tunani ba duk sun samu Labari,su Nana Fatima bakin Ammi sukaji duka sun kirani suna min nasiha sai na nuna musu ba komai,Anty Binta ko kunya kirana tayi a waya tana cemin yanzu sai da na kashe wannan auran..?ni kuma sai na bata amsa da cewa daman Tuntuni ya kamata ya mutu Bai mutu bane Daganan bata kara mgana ba Yaya Asiya kuma duk sai jikinta ya yi sanyi tace"Fa'iza zawarci ba Dadi"
Kai Tsaye nace"Ni ba zawarci zan yi ba makaranta zan koma, na karo ilimi sannan zan bunkasa kasuwancina ke dai kiyi min fatan alheri"
Jin haka yasa sai ta bini da addu'a kawai ganin Nima ban damu ba.
Hankalina kwance abuna har yar kiba nayi ina mgana da su Anum ta wayar Zainab tunda itama ta kirani tana Fadin"Yanzu shikenan mamam Amir..?ina mirmishi nace"Ba shikenan ba Maman Fadil zumunci Allah ne ya had'a sannan akwai ya'ya tsakani ke ce kuma uwar su ko Auran su ya tashi ni yar kallo ce"
Ban bata Damar da zata rokeni ba na cikata da mgana sai ta kasa mgana Sannan yaran kuma ko da yaushe sukace Umma yaushe zaki zo..?Sai nace ina nan zuwa to sun ma Fahimci ina Fade ne kawai sun daina Damuna ammh ban yi wasa ba duk sanda mukayi waya zan ce su kula da salla da Azkar ban da kawayen banza su taimaki kannensu sannan na roki Anty Fadila dom Allah ga amanar ya'ya na nan ne tace Haba kada na Damu kamar suna gidanta ne tunda nan suke weekend.
Har Badariya sai da ta kirani tana jimami nace mata tayi min Fatan alheri a bakinta nake jin Hajiyar Dala nata Fad'an wai da na kashe aurena ina da wanda yafi Ishaq din ne.?taga mai kwasata wato ina Takama muna da Uba mai arziki.
Ban ce komai ba sai mirmishi kawai da nayi, na jima da sanin Hajiyar Dala bata kaunarmu kuma bazata taba ba shiyasa nima na shata mata Layi,ranar da Badariya ta Fad'amin ta kira Goggo tana fad'a ta kuma ce a bani waya ta maimaita min abunda Badariya tafad'amin ni ko ban yi mata shuru ba nace"Bani da shi Goggo,kuma bana Fatan samu ma. saboda sha'awan aure da Namiji dalilin ishaq yasa ya fita a raina"
Sai mgana ta yasa jikinta yayi sanyi bata kara mgana ba sai cewa tayi"To su yaran fa wa kika bar ma su.?
Nace Mata Allah sai ta kashe wayarta a raina naji Fes,duk da Ishaq din na Damuna da kira ban taba Dauka ba. Text din ban hakuri safe da yammah har da na Turanci in nagani Dariya nake yi na goge a raina nakan ce ya manta Fa'iza ba Turanci ne Sulhu yake nema ni ko Har Abada Ishaq ya fita raina sannan yayi sanadiyar da Sauran maza suma suka fita a raina.
Rayuwata nake yi cikin Farinciki bani da matsalan komai ina sana'ata ban nemi komai na rasa ba, duk wata Abba na sakamin kudi bayan riban da nake samu,yan'uwana dukkansu yanzu Tallalina suke yi kamar kwai Goggo da mallam sai abunda nace duk kuma abunda bana so wlh suma sun bar shi kenan.
Ni da kaina na kira Hajiya na fadamata Mutuwar aurena Hajiya bataji Dadi ba ammh sai tamin Fatan alheri da kuma Fatan kada na bar sana'a ta shi zai taimakeni sannan a Satin har karofi tazo mun jima tana mgana dani shawarwarim da uwa zata bama yarta shi ta bani ta nemi na koma makaranta nace mata bani da Ra'ayi sai ta kyaleni ta kawo min kayan kwalliya sannan ta kawo ma Goggo atamfa,ni dai duk kyautar da su nayi ga su Anty Nasara har da Hafsah da Khadija na ijiyemawa,sun yi mganar har sun gaji sun san ba ruwana da kwalliya balle ina cikin iddata.
Sa'adatu ma da na fad'amata Har Karofi tazo ta jajantamin sai yammah tatafi bayan ta fadamin Haruna ya samu aikin Bijilanti,nayi mata Murna da na Rakota zaure zata tafi sai ta kalleni kafin tace"Kai Maman Amir kinga yadda kika yi kiba kika sauya kuwa..?
Ina Dariya ban yi mgana ba sai tace"Allah ya kawo bazawari nagari"
Da Sauri na Tareta ina Fadin"A'a ni yanzu namiji baya bani sha'awa kasuwancina zan bunkasa domin goben ya'yana"
Kai tsaye tace"An ya..?da kuruciyarki fa wadanda suka fiki ma ai sun yi aure"
Dariya nayi kafin nace"Bani da Ra'ayi kwata kwata kuma ina kuruciya anan Shekarata 34 fa"
Sa'adatu tace"Uhm ko dai da Baban Amir din za'a daidaita?
Mganarta yasa sai da gabana ya fadi araina nace ba Ameen ba Daganan na Sauya mganar sai itama ta barta. Dubu Biyar na bata tana ta godiya sannan na bata garin Danwake da yawa na kuma bata na ce ta kaima Habiba sun yi min abunda bazan manta da su ba.
Ina gida bana fita ko'ina ina kuma lissafin iddata ko alama ban taba mgana da wani nace masa Ishaq na damuna da kira da sako ba,gogewa ma nake yi saboda kada wani ya gani Ranar wata Jumma'a da Daddare aranar ina da kwana talatin da Hudu da Iddata,misalin karfe takwas da wani abu na Dare naga Ishaq nata kirana ban Dauka ba,Kiran ne naga yayi yawa yasa na daga sai naki mgana maimakon naji muryansa sai naji Karadin Anum tana fadin"Umma Umma"
Da Sauri nace"Na'am Anum din Umma"
Cikin zumudi tace"Umma Yaya Amir ya yi na 1st postion a makaranta. yau aka bamu Hutu an basa kyauta Umma"
Farinciki ya rufeni Cikin Dariya nacr"kai masha Allah..Amir din Umma yayi kokari ke fa nawa kika yi..?
Da zumudi tace"Umma na 8th nayi fa kinsan bamu jima da fara zuwa ba aka fara Exams"
Cikin nuna jinjinata nace"Dakyau Anun din Umma Ahmad da Musty fa..?
nan ta rika zayyanomin abunda sukaci ina saka albarka Amir bai karbi wayar ba sai Musty daga shi Sai Farhan,yana ta min hiran an bama Yaya Amir kyauta nace dakyau ina tambayan Fadil suka bashi yana min Hira da gauranci ina Dariya wayar tsakanin yaran ta fara zagayawa wani har sau biyu ma irin su Ahmad da Farhan da basa gajiya daga karshe Anum ta kwace wayar sai nake tambayata ina Amir..?tace yana Daki ta kai masa ne sai nace ta kyalesa Antynsu na tambaya tace min Tana Daki ko da yaushe daman in na Tambayeta zasu ce tana ciki na Fahimci zainab bata son yara kwata kwata.
Mamakin jimawar mu muna mgana nayi yasa nace ma Anum"Waya baki waya haka Anum..?
Kai tsaye tace"Ta Daada ce fa shiya ce bari ya kiraki mu fad'a miki"
Ba'a sirri da yaro ina ji ana mgana ban dai jin me ake fadi naji Anum tace"Me kace Daada..?
Sai araina nasan wata mganar zai ce ta fadamin kamar ina wajen sai ji nayi tace"Umma Daada yace yaushe zaki zo..?
Ban bata amsa ba na fara Hamman karya ina fadin"Oya sai da Safe barci nake ji"Ba ason ranta ba na katse wayar a fili na yi mirmishi ina mamakin Rashin kunya a wajen Ishaq sai yanzu yasan ya'yana suna da Rana.
Nasan kunya ce ta hanasa zuwa garin nan ammh a juri zuwa rafi tunda bai da kunya zai iya zuwa.
Kwana Biyu Tsakani Zainab ta Haihu aiki akayi mata An cire mata yarta mace kyakyawa nima Anty Fadila ta fadamin Tunda ita Ishaq ya taso cikin Dare sai tace ya kawota asibitin datake aiki a bakinta nake jin zainab din ta wahala karfinta ne ya kare sannan yarinyar ta karkace acikinta shiyasa akayi mata aiki.
Dole Mama ta koma Lagos itama Zainab din daga Adamawa yayar Hajiyar Halima aka tura mata ta kula da ita,aikin yayi kwana biyar suka sallameta suka koma gida,na kirata nayi mata barka tace tana jirana sai nazo barka ina Dariya nace zan bata mamaki kuwa.
Ba suna suka yi ba tunda ga nisa ga kuma kashe kudi,Sai dai Dr.Lawal da Hajiya Halima sun je sun ga yarsu da jikarsu sai kanwarta zuzu da ta gama karatu ta je aka barta achan sai Anty Fadila da yaranta,yarinya taci sunan FA'IZA.
Da Anty Fadila ta fad'amin sunan yarinyar sai da Dariya ya kamani shima yayi ta kirana ban Dauka ba.
Zainab ta kirani tace sun yi min takwara in dawo ko saboda little Fa'iza,yara kuma suna ta murna an haifa musu bby,Anty Fadila tayi bajinta kamar ni ce na Haihu, kayan alfarma tayi ma Zainab da Little Fa'iza har Abba da yaji sunan Bby sai da yayi Dariya Tausayin Ishaq kad'an ya tsirga masa.
Sai dai kuma ina! bakin alkalami ya riga da ya bushe.
*Janafty*
[7/27, 9:27 AM] U.M Collection ZMFR CM: *KNKB3007*
*TASTED & TRUSTED*
*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATUN SAIWOWIN MUTANAN CHADI DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZAR AMARE, MASU JEGO DA WADDA TAKE SON GYARA KANTA*.
*AN GWADA ANGA INGANCINSA SHIYASA NA KE TALLATA MUKU DA K'ARFIN GUIWATA*.
*ABIN BIRGEWA DA WANNAN SAIWOWINRL ZAKI YI AMFANI DA SU SAMA DA SAU DAYA.*
*AKWAI FULL PACKAGE, AKWAI RABI, TA YADDA KOWA ZAI IYA SIYA*.
*SANNAN BABU BAURI NA TASHIN HANKALI.*
*DA KANKI ZAKI DAFA ABAR KI, KOMAI ANA SAKA WA A CIKI*.
*SHIN KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR, KO KUWA KE CE KIKE SON GYARA KANKI?*.
*KAYANA NATURAL NE DOMIN SAIWOWI NE DA AKE HAKOSU A DAJIKAN CHADI. BAYAN SAUKAR DA GAMSUWA HAR YAQI SUKE YI DA DRYNESS DA KUMA INFECTIONS.*
*AKWAI NA TSUGGUNO DA YAKE HA'DE MACE TA MATSE.*
*AKWAI HADADDUN DAKA NA SHA DA MADARA KO NONO WANDA BABU ALGUS*.
*SANNAN AKWIA GADALIN MATA NA ASALI, WANDA SHA YANZU NE MAGANIN YANZU DA IKON ALLAH*
*DUKKANSU TESTED & TRUSTED NE*.
*TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU*
*08032773332*
*DOMIN KARIN BAYANI, SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*.
*NATION WIDE DELIVERY*
*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*
*09069067488*
Zainab tayi tayi dani nazo naga Little Fa'iza naki ce mata zan zo,Har da yaran suka had'a baki suna ta kirana suna magiyan Umma kizo don Allah.
Zuwa Lokacin Anum da Amir sun Fahimci yanzu Umma da Daada basa tare Anty ce kadai ko da ba'ayi musu bayani ba.
Nii kadai na kudura araina zan bada Sako a kai ma Zainab da yaran sai na kira Badariya nace yaushe zataje..?sai tace min da tare da Anty Binta da Anty mahma zasu bi jirgi ammh daga baya su zasu rigata tafiya zata tsaya sai ta gama karban takardunta gabadaya tunda ta kamallah bautar kasarta in tatafi bazata dawo ba,har ina mata tsiyan ta zauna a kanon ta kawai wajen Hajiyar Dala.
Kai tsaye tace min Allah ya kyauta zaman hakuri da ba yadda zatayi ne yasa ta zauna a baya.
Gwara ta koma inda tafi wayau,mun rabu cikin Raha nace kafin tatafi ta biyo ta Karofi na bata Sako Tunda tace min doguwar Mota zata bi tana da kaya da yawa.
Ko Goggo ban yi shawara da ita ba sai dai taga ina ta shiri Zainab Less na siya mata ita kuma takwara kayan kanti masu kyau da Huluna da Dan kunne da abun hannu har da lalle mai kyau,sai takalma na yara masu kyau da yarari.
Sai na siya shadda Mai ruwan kasa na bama Yaya isa ya kai dinki aka dinka ma duka mazan har da su Farhan Anun kuma na mata dinkin Atamfa da less,sai hijabai kala Uku,sannan na fansar musu kananun Qur'anai sai azkar dukkan su kowa Daya Daya Amir kuma sai na karamai da karamar Mp na saka aka cikata da Complete Qur'an kyautar na yin na D'aya da yayi,na kuma zage nayi musu Dambun nama kaza,daman na iya bana yi ne to yanzu kuma ina so na Dawo da shi na rika karban aikin ana Biyana sannan daman na Dawo da sana'ar Turaren wuta dilka ce ban fara ba Tukunnah
A na gobe Badariya tazo ta kirani ta fadamin ranar jummala na bar ma Hada zobo da kunin aya na Dukufa Hada Tururika sai da na cika Dan Botiki da na icce,sai wani gora da kwallacha na ruwa ne ban yi ba,kwallacha kuma nayi ma Anum nata ita da Amir sun girma suna Bukatar kamshi suma Goggo taga na kasa zama ta tambayeni sai na Fada mata rike baki tayi kafin tace"Duk wannan kayan na mutanen ikkon ne..?ko dai ko dai fa'i..?
Nagane nufinta yasa nayi Saurin Dagowa ina Fadin"Haba Goggo..Ko ba komai ai tana rikon ya'yana sannan akwai kauna Tsakanina da Zainab wlh ba domin Ishaq ba, domin kaunar da ta nuna min ni da ya'yana tun farkon auran su da Ishaq"
Zan iyi ma zainab komai in dai bai gagareni ba"
Goggo ta jinjina kai kafin tace"Na Fahimta nima zolayarki nake yi"
Sai nayi Dariya ban kara mgana ba sai da naga har Dinkin nasu An karbo na hada kayan waje daya kowa kuma na saka sunan shi jikin nasa gudun rigima.
Washegari karfe Tara da wani na Safe tayi ma Badariya a karofi Daki muka kulle muna ta Hira,Daman kuma tace tana son ganina sai nima naga duk ta rame kamar ba Badariya ba.
Kayan na fara nuna mata tagani ta saka albarka kafin tace"Anty Fa'iza kina da kyakyawan zuciya matar da sanadinta kika rasa mijin ki kika yi ma wannan Hidimar haka..?
Kai Tsaye nace"Ko daya. Zainab ba ita tayi sanadiyar mutuwar aurena ba,Ita me ta sani.?abunda ta gani ko taji gayamata akayi badar..Ni nayi mata don Allah ne domin Sanadin kaunar datagwadamin ni da ya'yana abaya nima fa tana min alherin nan Bazan manta da ita ba"
Badariya ta yi jim kafin tace"Eh gaskiya tana da kirki sai dai ba matar Aure ba ce.
Bata fa ta aikin komai sai fita aiki Jamal yace wannan yar renon ke Jagwalgwala abinci ko Kuma ya ishaq ya siya,bata aikin fari ballatana na baki yaran ma Anum ce da Amir masu kula da su da kuma yayarki dake chan"
Kai tsaye nace"Daman ai bata aiki ko suna Abuja ma'aikata garesu"
Badariya ta tabe baki kafin tace"Ai yanzu daga shi har Maman sa gane amfaninki Anty Fa'iza Mama yanzu ita ke girki ban da Lalacewa ina mama ina wani girki"
Ido na zaro kafin nace"Subhanallah garin yaya..?to su dauki yar aiki mana"
Badariya ta gyara zama tana Fadin"Basu samu ba daga nan ba'a samu wacce zataje chan ta zauna ba,Sai Dole yar chan kuma wa suka sani..?Anty Zainab kuma bata saba ba tace bata ma zata iya ba,Mama kuma tana Tausayin Yaya ishaq da yara nan Dole yanzu ita ke yi shiyasa na kosa na koma naje na amsheta tunda abunda suka shuka ne suke girbansa Daidai gwargwado"
Ta fada idanuwanta sun tara Hawaye kai tsaye na nuna jimami na har acikin zuciyata kafin nace"Gaskiya kan gwara ki koma,kuma ammh Anum ta iya Dafa Saukakkun abinci ita da Amir.
Badariya tace"Yaya Ishaq yace bazasu rika girki ba, sun yi kankanta ita kuma Gimbiyar tace bazatayi ba"
Kai na jinjina ban sake mgana ba,araina nace Rariyan da ya siya kenan ita ke zubar ruwan.
Badariya sai ta nemi min kuka na kalleta cikin wani yanayi kafin nayi mgana ta rigani da fadin"Anty Fa'iza wlh hakkin ki ne yake bibiyata"
Sai na tsorata da Sauri na zaro ido kafin nace"Hakki kuma..?ni me kika min..?
Har ga Allah na tsorata na tuna muna waya da ita sosai har Raliya suna kirana ita da Laila su gaisheni bayan an kwana Biyu zuciya ta zargesu ko sun ce nace wani abu ne akan Badariya
Ammh sai naji ta rike Hannayena tana Fadin'"Abubuwan da su mama suka rika yi miki ne ita da Anty Binta da Yaya ishaq wlh hakkin ki ne ke Bibiyana Anty Fa'iza, ba mashinshini Wlh bani da Saurayi rabon da ma wani yace yana sona na manta wannan ba hakki ba ne Anty Fa'iza..?
Ta fad'a sai kuka sai Tausayinta ya kamani har ga Allah ina sakata cikin addu'ata
Na rumgumota ina Lallashinta har abada bazan manta da karamcin Badariya a gareni ba ta kaunace ni lokacin rayuwa ta juyamin baya har kuma gobe tana kaunata ita Fa'iza ta kaunata tun Fa'iza na Fa'izarta,Sai da naga ta daina kuka sannan na Dagota na share mata hawaye Lokaci d'aya ina Fadin"Ki daina Fadin haka Badar. Ni fa ban ta rike su a raina ba har shi Yaya ishaq din na yafe masa Darajan ya'yan mu aure lokaci ne in Lokacin ki yayi zaki yi. Mu masoyan ki muna yi miki addu'a in sha Allahu Nagarin na nan tafe"
Kai ta girgizamin cikin Raunin murya kafin tace"Ban ki mganarki ba Anty Fa'iza ammh ki sani sharri dan aike ne inda ka aikasa zai dawo maka komai Daran Dadewa. Mama ta aikata miki ba Daidai ba. yafewarki bazai hana Allah ya nuna mata Ishara a kaina ba shi Yaya Ishaq ya fara gani Anty Binta ma tunda itama Halisan yar Mijinta ta hanata zama Lafiya kwanaki har gida taje ita da ya'yanta, suka mata duka har ciki dan Sati uku ya fita ajikinta sai da tayi yaji tayi kwanaki a gida kafin manya suka ciki aka Sulhunta"
Ido na zaro cikin Firgici domin ni ban ji Labari ba,Ganin haka yasa Badariya ta cigaba da fadin"Wlh kwanakin baya akayi,Anty Binta na bala'in zata kai kara kotu Anty Mahma ta bata amsa da cewa ba zencen kai kotu duk abunda kayi shi zaka girba walau khairan walau sharri kamar yadda ta hana Fa'iza zaman lafiya itama kwatankwacin haka za'a hana yarta ai sai tayi shuru tasan gaskiya"
Tagumi nayi har araina ban ji dadi ba nace"Allah ya kyauta"
Badariya tace"Amin ga miji dan iska manenim mata chan naji Suwaiban Hajiyar Dala na gulmar, suna ta zagin Halisa araina nace Allah ya kara"
Ajiyar rai na sauke nace"Allah ya kawo mata mafita"
Ta amsa da amin kafin tace"Har da ita amasu yawo dani ban yi aure ba ido cikin ido na fada'mata da aure irin nata gwara babban mace agida muka yi kaca kaca da ita naso Anty Binta tamin mganar. har ita ban so na kyale ba sai kuma batamin ba"
Nasan Badariya da Fad'a sai na Shiga bata hakuri ina fadin"Sai hakuri badar..Ki rika banza da irin su. aure Lokaci ne kuma in sha Allahu Lokacin ya kusa"
Tana mirmishin yake tace"Allah yasa"hira muka cigaba da yi a bakinta ma nake jin wasu labaran,mun gangara Hirar Raliya tace min tana da ciki taje ma kwanaki ta mata kwana Biyu tana fadin alherin Raliya gareta da basu had'a komai ba ina bata Hakuri,nasan irin zafin datake ji acikin ranta,muna tare da ita har Bayan La'asar sannan tayi shirin Tafiya,tace min gobe da asuba zasu dau hanya har ta siya ticket din motar,su Anty binta suna chan basu dawo ba,Na nuna mata kayan duka da na kowa da kowa tace ta gani ina da wata atamfa da Anty Nasara ta bani ban ko Dinkata ba,sai na hada mata da kayan kwalliya da Hajiya ta kawomin wanda na ijiye ma su Hafsat basu zo ba na bada kudi 5k nace tayi Hakuri zan yi mata sako tana ta Godiya.
Da zata tafi Goggo ta hadamata su zogale kubewa,kuka tace ta kai ma Mama,har zaure na rakata kamar kar mu rabu bayan tafiyanta abun ya Dameni har na fadama Goggo Abunda Badariya tace itama tayi shuru kafin tace"Allah ya kyauta ammh ai fadar Allah ne ya hana kansa zalunci kuma muna bayinsa ya hanemu da shi"
Daga haka bata kara mgana ba,a raina na kuduri zan kara Dagewa da addu'an Allah ya kawo ma Badariya miji na gari na nuna sa'a.
Bata kirani ba sai da aka kwana tunda kwana suka yi tafiya ta hadani da yaran suna ta murna,sannan itama Zainab din ta kirani tamin godiya daga karshe tace"Naga sako Little tace bata Hakura ba,sai Takwaranta tazo ta ganta"
Dariya kawai nayi ban yi mgana Domin na saba jin korafin Zainab kan rashin zuwana.
Wannan kayan da Ishaq ya gani suka zaburar da shi yana son zuwa kuma yana Tsoro,ammh yana ta kamun kafa wajen Abba ko da yaushe yana kiransa shi ko Abba in ya kirasa sai ya bige da masa Hiran aiki da Duniya in kuma Ishaq yaso sako wata mgana sai Abba ya shanshantar da mganar,shi kuma nauyi da kunya yasa ya kasa neman ma kansa mafita ammh yasan Yana Bukatar fa'iza.
Mama kuma ya yi mata magiyan ta shiga Lamarin kai tsaye tace"Ishaq ba ruwana bazan kara saka baki a zalunci Fa'iza dani ba.
kaje ka sameta kafin ta gama Iddanta ka kara bata Hakiri in ta Hakura zata dawo don kantaina murna in kuma bazata Dawo ba Ishaq bazan saka baki ba sai kayi Hakuri ka rumgumi zainab din tunda ita ka zaba"
Tunda ta fadi haka yasan bazata kara mgana ba,Anty Binta ma haka tace yaje ya samu Fa'iza tunda baban nata baya tare da ita ya Lallasheta Anty Mahma dai bata ce komai ba amnh a ranta tana Fatam Fa'iza kada ta amince.
Ga su ga Zainab din nan ko su basu ci albarkacin ta zauna da su ba,Mama ce take yi da suka zo ne suka karbeta,Ammh tana jin sauki ta koma aiki wai basu bata hutu ba,sannan tareda Shema'u take tafiya saboda Renon Little,Allah yasa yaran na gida an yi Hutu da Mama ta shiga uku.
Jamal kuma an kira su yana Gombe ya tafi Camp abunsa.
Da shawarwarin su ya yanke shawaran tahowa karofi ya sameni bayan ya gama shirya yadda zai yi amfani da kalaman bakinsa ya shawo kaina.
*****
Bani da masaniyar zuwansa ko abunda ya shirya a ransa,Ranar asabar da nake da kwana hamsin da shidda cikin idda ne ranar na tashi da jini na Biyu,Da aranar Abba da Ammi za su Karofi sai suka fasa An kira su Abba taro a Parthercourt sai ya tafi ajiyan. har Goggo ta saka su Yaya mariya sun je sun gyara gidan an saka Turare sai kuma zuwan nasu bai yuyu ba.
Da Safe bayan na tashi nayi wanka nayi mana abun karyawa jummala bata zo ba sai karfe goma,sai na gyara Falon Goggo na zauna ina karyawa ita taje kaima Mallam nashi ta dawo ta zauna kusa dani tana shan koko da kosai shi nayi mana lokaci d'aya kuma muna taba Hira sama sama acikin Hiran ne nace"Goggo bayan na gama Iddata na ina so na dawo da girke girke na tunda kuna da Fili a nan"
Goggo tace"Sosai ko Tunkuya goma ce za'a dorata a gidan nan kuwa. Sai ki Dauki ma'aikata su rika tayaki ayyukan"
Ina tusa kosai bakina nace"Haka nake Tunani da na bari sai Abba yazo ne sai nayi masa mganar"
Goggo tace"Eh ki yi mganar da shi hakan yana da kyau sana'a nada Dadi zaman haka bazai dameki ba"
Mun dan saurara da Hirar sai chan nace"Goggo yaushe za'a je katsina a kwasomin kayana..?ina so a kwasomin wasu ina so nayi amfani da su. wasu kuma sai na kyautar da su kada su lalace" Goggo tayi shuru kafin tace"Kin ga mun Sha'afa da wannan mganar to yanzu ya za'ayi?Dole sai an kira Ishaq din tunda kila key din gidan na Hannunsa"
Kai tsaye nace"Nima ina da shi Goggo"
Domin kamar na sani na cire na kofar gida guda daya da na Dakina.
Goggo tace"To shikenan zan saka mallam ya kira Baban naku a gayamasa abunda yace shikenan"
Da haka muka Rufe Hirar Goggo tace min zata shiga ciki ta kwanta kanta na saramata nace toh.
Kafin jummala tazo na hada wuta na Daura zobon da tazo karisawa ne kawai muna yi da yawa sosai kafin yammah ya kare,tunda duk barayin ni kadai ke yi har barayin su Yaya Mariya ma,kuma ina samun alheri in ina da Hadin Turaren wuta shima Tana tayani mun saba ita kan je kasuwa tamin siyayya har katsina nasha aikenta.
Bayan mun gama hada zobon mun dura a gorina muka zuba cikin Frerzer akwai wuta ba'a tada in ji ba,Sai ita kuma jummala ta wanke Aya ta hada shi ta fita kai nika
Sai na koma Daki na cire kaya zan shiga wanka Nana Fatima ta kirani a waya na zauna gefen dago muna ta shan Hira da ita fiye da Minti talatin sannan muka yi sallama.
Kwata kwata ban san da Mutum a bakin kofar dakin da nake ciki ba,Na ijiye wayar kenan saman gado na mike sai naji kaina ya daki kirjin mutum,A tsorace nayi baya ido na rufe garin yin baya na ci Tuntunbe da Matashi sai na kusa tintsirawa sai ji nayi an rikoni har da karfin Halin Rumgumeni bai yi mgana ba ammh kamshin Turarensa da Yanayin rikonsa yasa na gane ko waye ba kowa ba ne sai ISHAQ KABIR KAROFI.!
Har yana d'ora kansa a saman kaina Lokaci daya yana sauke ajiyar zuciya,Haushi ya kamani sai na Daddage na saka hannuwana na Turesa baya har zanina na kwancewa nayi Saurin taresa da hannuna.
Kai tsaye na ke kallonsa kamar yadda yake kallona sanye yake da Kaftani Riga da wando kalan Sararin Samaniya har da Hula ya rame ammh ya sake Fari da hutun jin dadi
Nima cikin wani yanayi yake karemin kallo,ganin haka yasa na juya na Rarumi Hijabina na zura jikina na rawa nace"Mallam lafiya?
Sai naga yayi mirmishi kafin yace"Lafiyar kenan. wajen matata Fa'iza nazo"
Idanuwana kamar zasu fad'o na hararesa kafin nace"Baka da wata mata mai suna Fa'iza in Zainab kake nufi tana inda ka barota"
Na fada ina matsawa baya ganin yana Tunkaroni,tsoro ya kamani kada Ya min akuyanci.
Ai ko naga rashin ta ido sai da ya matseni a jikin bango sannan ya Takore bamgon da Hannayensa yana bina da wani kallo kafin yace"In gama gudun..?ina bakin tsiwar..?
Na bude baki nayi mgana ya Hade bakin mu waje d'aya yana sumbatata yana Hadawa da taba jikina da iya karfina nake turesa ammh ko gizau,abun ka ga Namiji,gajiya nayi na koma ina Tsiyayan hawaye sai da ya gaji don kansa ya saki bakina yana maida numfashi Cikin sanyin murya yace"Fa"iza ki yi min afuwa ki kuma yafe min kura kuraina ki Dawo rayuwata mu daidaita kanmu, in muka Daidaita kan mu ba wanda zai ce kada ki koma Don Allah Fa'iza"
Ya fada yana kallo na a narke ni kuma ina kallonsa ina tsiyayan hawayen takaici yadda Ishaq ya raina ni.
Hannayena ya sake Rikewa ya jani gefen gado muka zauna yana wasa da yatsuna yake fadin"Fa'iza yaran mu. Sun saba da ganin mu tare basa jin Dadi in suka wayi gari baki a gidan nan. Komai ya daina min Dadi wlh tallahi na Fahimci ke ce gata na ni da ya'yana ki taimakemu ki dawo garemu Fa'iza I so much Love u.."
Ya fad'a Lokaci d'aya yana sa ke hannuna bakin sa ya yi kissing,na kasa wani motsi kukan takaici yaki Tsayamin ina jinsa yana ta mganganunsa cikin taushin murya ganin ban daina kuka ba yasa sunkuyo ya fito da harshensa yana Lashe hawayena har ya gama yaga ban yi wani motsi sai ya tallafi Fuskata yana Fadin"Kin amimce Fa'iza..?
Kaikayi ne ya tasomin a idona sai na Kifta kamar kiftawan ido ya Rumgumeni Lokaci daya yana Fadin"Nagode Fa'iza nayi miki alkawarin bazaki kara kuka saboda ni ba,zamu reni ya'yan mu ni da ke,saboda Farincikin su"
Hawaye sharr suka zobomin na wani Turiri a kasan raina,a kaf kalamansa da Nadamansa bai taba cemin zamu inganta sabuwar rayuwar,bai taba ce min Fa'iza zan baki farincikin da ban baki a baya ba,Shi dai tunaninsa ya'yan mu ya'yan mu kawai.
Saboda rainin da ya yi min sai kawai ya shiga Budurinsa a jikina ni ko kamar an Saremin kuzarin jikina ina ji ina gani ya rabani da Hijabi na, ya kwantar dani kan gado yana kokarin janyemin zanin jikina sai a lokacin na Dawo Hayyacina sanda na Fahimci zai yi wasa da Hankalina da na iyayena.
Da karfi na turesa bayan ya saki jiki,sai da ya fadi kasa na mike a gigice kamar zakanya na gyara Daurin zanina yana Dagowa ni kuma na juya na Dauki Hijabi na,ya sake riko hannuna yana Fadin"Fa'izaaa!
Tas..! Na daukesa da mari Lokaci d'aya ina juyowa idanuwana jajir na nunasa da yatsa ina huci kafin nace"kada ka kuskura"
Kada ka kuskura ka fara wannan tunanin Ishaq"
Na fad&a lokaci daya ina kara kankance idanuwana ga huci ina Fitarwa kamar wata zakanya.
Sai ya Dafe kuncinsa cikin mamaki kafin yace"Yau ni kika mara Fa'iza..?
Sai da na juya na zura Hijabina kafin nace"Na mareka din. kuma ka bari hannunka ya sake taba jikina kaga ni,marin makauniya zan yi maka ma.
Ka daina Tunanin ni Fa'izan zan koma ga auran ka. Har gaban Abada ni da kai Ishaq Karbi karofi ta kare, Fa'iza ba Turanci ba ajinka bace na barka da zabin ka meyasa bazaka kyaleni ba.?
Meyasa bazaka daina damuna ba..?
Na karishe cikin tsawa kamar mahaukciya sannan ina Fitar da Hawaye,Idanuwana jajir ya Tako zai iso gabana na Dakatar da shi da Hannu ina fadin"Wlh ka kara matsowa kusa dani zan maka ihun kwarto"
Jin kalamai na yasa ya Dakata kuka na Fashe da shi kafin na hada hannayena ina fadin"Don girman Allah ka kyaleni ka ce baka sona na barka ka zauna da wacce kake so,Na roki ka barni na samu salama Dalilinka aure ya fita kaina da dukkan wani namiji Ba domin ni ba domin Darajan Mama ka Rabu dani don Allah"
Sai kawai na saka fuskata a cikin Tafukan Hannayena ina kuka ban san yanayin da yake ciki ba ammh naji motsi da Tafiya sai da na Dago naga bashi a dakin kenan ya fice. wankan da ban yi ba kenan na kwanta nan ina ta Rusan kuka jummala ta shigo da Sauri tana Fadin"Maman Amir waye ta fita yanzu..?na hadu da shi a zaure kadan ya rage bai tureni ba"
Ina kukana ko sauraranta ban yi ba,Sai ta juya taje ta kira Goggo,Sai ga su sun dawo tare har Goggon tayi mganan duniyan nan ban ce komai ba sai kuka karshe ma na shige Bayi na kulle kaina.
Abun sai ya basu mamaki,Shigowar Mallam yasa sukan sa bakin zaren,Yace ya hadu da Ishaq din a gabansa mota ta sauke sa Goggo najin haka tace"Ko da naji Nasan shi kadai ke saka Fa'iza kuka haka"
Jummalla dai duk ta rude ranar kunin Ayan ne sai dai jummala tayi shi ita kadai ban kara fitowa ba.
Abba na kira domin nasan shi kadai zai iya takama Ishaq Burki ina ko gayamasa abunda ya faru ina kuka na Boye taba jikina da yayi ba, illah cema nayi yazo ya na ta min magiyan na koma.
Ran Abba a bace ya katse wayar ya kira Ishaq ya masa gargadi da kakkausan murya kada ya kara zuwa inda nake ya kashe wayarsa,Ishaq ranar yayi kuka kukan nadaman da bai Taba yi ba,Hotel ya kama ranar bai iya komawa Lagos ba. A katsina ya kwana sai washegari ya koma sannan ya kuma kara jin Tsoron Rasa Fa'iza har Abada.
Goggo ganin zuwan Ishaq ya sauya ni gabadaya yasa ta kira Abba tamai mganar kwaso min kayana yace su Yaya Mariya suje su kwasomin a Da'u tashar Mota zai biya kudin komai da komai,Haka ko akayi Yaya mariya da Anty Nasara sai Aminan Yaya isa suka je katsina da Katuwar mota mai Budadden baya.
Goggo ta min mgana na basu key din suka Bude gidan suka kwasomin duka kayana Mutanen anguwan su suka kira megidan suka Fadamai an shiga gidan shi kuma yazo da kansa ya zata ko barayi ne. Anty Nasara tamai bayani sun dawo suna bada Labarin sai da ya jinjina kafin yace"Lalle Ishaq ya tafka asaran Rabuwa da mace tagari in matarsa"
Yana gaya musu bai sanni ba ammh ya basu labarin irin yadda na rika rokonsa da yazo kan mganar kudin haya,Sai jimami yake har suka gama kwashe kayan yana wajen ya kuma bada sakon gaisuwa gareni.
To shi ya kira Ishaq ya fada masa an kwashe kayana ya kara da fadin"Kai ko bawan Allah me ya kai ka..?ka yi waauta ko nace kayi asara..!
Saboda Takaici bai bari ya karisa ji ba. ya Katse kiran kamar ya zagesa haka yaji Lalle ya yarda Fa'iza da gaske take malkulin gidan daman megidan suka mikamawa tunda ba wani abu kuma zan yi da shi ba, A dayan dakin dake tsakar gida aka jibge kayan na fito na gani kayan amfani kawai na kitchen na cire gadon da kujerun basu komai ba Yaya Mariya na baa,tare da Dirowowin yaran nace ta gyara,cafet ma duk ita na bamawa,Tv kuma nace Goggo ta Dauka,Kayan su Amir kuma daman har da su aka kwaso na ce Goggo ta kyautar nasan ba kara waiwayan su kuma za'ayi ba.
Goggo ta ga duka na kyautar da kayan har Jumnmala na bama kololi da Tukwane,Sai ko tamin mgana da cewa ta ga na rabar da kaya nifa..?
Sai nace ba abunda zan yi da su.
Goggo tace"In kika tashi wani auran fa..?kai tsaye nace''Wa tab..Ni kasuwancna zan cigaba yi da karatuna"
Sai Goggo tamin shuru bata kara mgana ba,sanin Halina tunda na cije bamai sauke ni kan ra'ayina.
Tun faruwar abun da ya faru Ishaq bai kara min waya ko sako ba,sai na samu zaman lafiya cikin ikon Allah na gama iddata Abba sun zo garin sun yi Sati da kudin sa ya yi min Hidiman shiga Haddan al'hamis da jumma'a
Da karfe hudu zuwa bayan isha'i sai Islamiyan matan aure da Safe karfe 9am zuwa Goma da rabi na safe,Duka na hada na shiga zuwa Lokacin tuni yan gari sun san aurena ya Mutu,na samu salama yanzu da kwanciyar Hankali ina zuwa makaranta na maida Hankalina a karatuna ya'yana kuma ina mgana da su bani da wata damuwa.
Jummala ta samo min wata yarinya Laure ta na tayata aikin zobon da kunin aya in bana gida,ko kuma aikin su Tarare,na riga mun yi mgana da Abba zan fara kwangilar girke girken sha'ani a gida zai siyamin manyan Tukwane da murahu da Kololi,daman alokacin na kara siyan wata Frezeer guda d'aya ta daina isa ta tuni kuma mata su gane bangaran kayan kamshi da Gyaran jiki tunda ina tallata kasuwancina a makaranta.
Sai gidan Goggo ya zama wajen shiga da Fice gefe d'aya kuma ina kokari wajen karatuna ban yarda wani abu ya Daukemin Hankali ba.
Sauka nake so nayi na zama Mahaddaciyar Alqur'ani mai girma.
*Janafty*
[7/27, 9:27 AM] U.M Collection ZMFR CM: *KNKB3008*
*TASTED & TRUSTED*
*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATUN SAIWOWIN MUTANAN CHADI DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZAR AMARE, MASU JEGO DA WADDA TAKE SON GYARA KANTA*.
*AN GWADA ANGA INGANCINSA SHIYASA NA KE TALLATA MUKU DA K'ARFIN GUIWATA*.
*ABIN BIRGEWA DA WANNAN SAIWOWINRL ZAKI YI AMFANI DA SU SAMA DA SAU DAYA.*
*AKWAI FULL PACKAGE, AKWAI RABI, TA YADDA KOWA ZAI IYA SIYA*.
*SANNAN BABU BAURI NA TASHIN HANKALI.*
*DA KANKI ZAKI DAFA ABAR KI, KOMAI ANA SAKA WA A CIKI*.
*SHIN KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR, KO KUWA KE CE KIKE SON GYARA KANKI?*.
*KAYANA NATURAL NE DOMIN SAIWOWI NE DA AKE HAKOSU A DAJIKAN CHADI. BAYAN SAUKAR DA GAMSUWA HAR YAQI SUKE YI DA DRYNESS DA KUMA INFECTIONS.*
*AKWAI NA TSUGGUNO DA YAKE HA'DE MACE TA MATSE.*
*AKWAI HADADDUN DAKA NA SHA DA MADARA KO NONO WANDA BABU ALGUS*.
*SANNAN AKWIA GADALIN MATA NA ASALI, WANDA SHA YANZU NE MAGANIN YANZU DA IKON ALLAH*
*DUKKANSU TESTED & TRUSTED NE*.
*TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU*
*08032773332*
*DOMIN KARIN BAYANI, SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*.
*NATION WIDE DELIVERY*
*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*
*09069067488*
*BAYAN SHEKARA D'AYA DA WATTANI*
*KAROFI*
Ko daga tsakar gidan Goggo in ka shigo Dariyata zaka fara jiyowa. saboda yadda nake faman kyalkyata Dariyan ba kakkautawa har ina Dukawa rike ciki na jin ya fara kullewa.
Goggo ce ta dago labule ta Leko Dakin Lokaci daya tana Fadin"Ke kuma ke da wa kike ta Dariya haka har waje fa ana jiyoki"?
Ina Dariya ido na har ya tara kwallah na Dago ina fadin"Goggo ni da Badariya da Anum ne. ina Dariyan sun je ziyara karnukan sun biyo su uwa da y'a sun ware kafa suna gudu"
Na fad'a har ina kara Dukawa ga waya rike a gefen Kunnena na Hagu karamin Tsaki Goggo taja ta sakarmin Labule tana fadin"Shine abun dariya..?Allah ya shirya ki Fa'i"
Ina jinta ammh na kasa daina Dariyan da nake yi ina jin Anum na fadin"Umma bafa abun dariya ba ne Anty Badariya har fad'uwa tayi ta gurje Gwiwa"
Ina so na bar Dariyan na kasa cikin Dariyan nace"Garin ya kika bar uwar taki a baya..?
Cikin sauri tace"Umma ni ban san ta fadi ba ina ta gudu ban juyo ba sai da na kawo kofar gida"
Dariyan na cigaba da yi domin ta kasa tsayawa,Badariya ta karbe wayar cikin muryan Tausayi tace"Kai Anty Fa'iza ina fada miki duk na kurje kafa kina Dariyan mugunta..?
Ina Danne bakina nace"Waya aike ki..?ai sai da mijinki ya hanaki nima kuma da kika fad'amin sai da nace karki je"
Kamar tayi kuka tace"Wlh don Allah naje mata barka ko Anum?
Bansan me Anum tace mata ba ganin yadda take mgana kiris tayi kuka yasa na danne dariyata ina Fadin"Hakane ammh dai da kin ji mganarmu da haka bata faru ba,ba sani nayi ba ammh nasan da gangan ta saka a sakar muku karnukan nan"
Badariya na ta jinjina kai kafin tace"Tayi ma kanta Anty Fa'iza ni dai Allah yaga niyyata"
Jin haka yasa nace"Allah ya baki lada
Sannu .Anum ta Dafa miki ruwan zafi ki gasa kafar in taki sai kuje ko Chemist a duba miki.
Da haka muka yi sallama ina cin dariyata a raina.
Wattani biyar baya muka sha bikin Badariya tare da mijinta Alhaji Yusuf mai kudi ne shaharareen dan kasuwa mai harkan Safaran motoci daga kasashen waje zuwa Nageria,asalinsa Haifaffan Azare ne dake Bauchi uba da uba ammh kasuwanci yasa suna zaune a cikin garin Bauchi sai wasu dangin dake azaren.
Ganin Farko soyayyar Badariya ta shige sa mai zafi a Lagos ya ganta yaje ganin motocinsa da suka sauka ta Jirgin ruwa ita kuma ta fito daga kasuwa suka had'u,Yana da mata d'aya ya'yansa Biyar kuma cousin dinsa yake aure,Badariya ta karbi Yusuf ganin yadda yake kaunarta Saboda Allah sai dai kafin auran su an sha Fama Tunda fafur mahaifiyarsa da Danginsa suka ki amincewa da har mganar ta sha ruwa, sai daga baya Babban yayansu da Dangin Mahaifinsa na azare suka zo har Karofi nema ma Yusuf auran Badariya.
Shagalin Bikin da komai a katsina aka yi shi Tunda Ishaq ya siya gida ya gyara shi an zuba komai lokacin Bikin aka fara amfani da shi,na daki kirji na nuna ma Duniya ni yayar Amaryace ko da aure na ya kare tsakani na da Ishaq na shiga sha'anin sosai ba Domin kowa ba sai domin Badariya,ba kuma don taimakon da tayimin ba a'a ta kaunace ni saboda Allah,ni na siya mata Fridge,sai tv da Tv Stand sai cafet d'an Italiyan sannan nayi mata Turaran wuta na itace kwallacha da Humra,na kashe mata kudi ban san iyakaba sannan nayi mana Dinki ranar Bikin muka saka ni da ita Kowa ya ganni a wannan Lokacin da rayuwa ta sauyamin Gababadaya ya san ba waccen Fa'izan daya sani ba ce
Fa'izan yanzu ta kama kudad'e a hannunta sosai ban sauya ba ina nan a Fa'iza ta y'ar gargajiyata ta. su Nana Fatima har sun gaji da magiyan na rika kwalliya sun kyaleni kayan kwalliya kuwa ko an bani sai dai su Hafsah su mora,bayan Shigata makaranta yanzu haka muna matakin Haddan Izifi Hamsin sauran mu izifi goma mu sauke,Tunda daman nayi sauka haddan ina wani bangaren sai ya kasance kamar tishi nake yi.
bangaran islamiya kuwa mun yi nisa tuni mun gama wasu littafan mun Dora wasu,Sana'o'i na na rike sune suka zame min kashin takawana bayan Abba ya kasance bango gareni. Bayan girke girken da nake yi yanzu na suna ko biki ko walima ko wani Taro a biyani ina aikin Dambun nama ko na kaji Dari ne a biyani ladana,ga Dilkar amare da Halawa,ga aikin Turareka na amare da matan aure ga Zobo da kunin aya domin ban daina ba Sai dai bayan ma'aikatana jummala da Laure a kallah yanzu mata masu min aiki ina Biyan su sun yi goma sannan ga almajirai masu Hidimam wanke wanke na manyan tukwanen abinci da kuloli,kaf Karofi ,Dutsemah,katsina kano,kaduna da kewayanta sun san Fa'iza mai Turaren kamshi ko SAFMA,tunda har lokacin ina Buga Sticker kuma ina amfani da ita a Kwallaben Turaruka na.
Ina da karfin jari a hannuna wanda Abba ya bani sannan ga Ribata shiyasa kafin Lokaci na sha kwana na mallaki kudad'en da ban san adadin su ba,Ni mutum ce mai kyauta hannayena suna Bude ne sannan ina yawan Sadaka da kyautata ma mutane ko matan da na Dauka ko da yaushe cikin min godiya suke yi na taimake su wasu mazajen su ba sana'ar sai wahala ni ko ba iya albashin ki ba in aka samu babban aiki aka biya da tsoka nima nakan yi musu ihisani.
Kuma ban bari hakan ya taba karatuna ba in ba na gida aka kawo aiki duk sun iya jummala da Laure suke jagorantan komai, in na Dawo sai dai na Duba kawai na dan gyara wani waje a ajin Haddamu ni kadai ce babba sauran duka matasan yara ne,Ammh kwakwalwata naja tunda na saka abun a raina gwara ma ajin islamiya tunda ta matan aure ne akwai sa'i'o na da ma wad'anda suka girmeni ana ta gungurawa tare,Duk da ban yi karatun boko ba ammh yanzu ina jin kananun kalmomin Turanci sai dai in turancin yayi tsawo sannan na iya Lissafi ba Dole ma na iya ba Tunda na kama kudi a hannuna.
Hatta su Yaya Asiya Abba ya basu manyan jari a hannunsu,sannan mazajen su ma bai barsu haka ba Mijin Yaya Asiya yayi mai hanya yanzu Vice principal aka basa ita kuma mijin Anty mariya aka kara ma kasuwancinsa jari Hafsatu kuwa ta zama yan kaduna wayayyiyar mace mai ilimi da gata sai kace ba ita ba. ita da Karofi sai dai da Hutu ko wani sha'ani.
Ba wani abu tsakanina da Ishaq tun abun da ya faru tsakanin mu lokacin da yazo inaga ya Hakura ne,sai dai ina waya da ya'yana ko da yaushe,tun kuma daga Lokacin bamu kara haduwa ba sai a bikin Badariya bai min mgana ba ni kuma sai na gaishesa Darajan zumunci ammh bai amsani ba araina nace kan ka akeji,a sha'anin nan ko Zainab Mama bata rika sakata cikin lamarin bikin kamar ni ba, komai sai tace a yi ma Fa'iza mgana,Hatta da Anty Binta rayuwa ta saka tayi sanyi yanzu mijinta yayi Ritire ba wani arzikin yanzu Halisa kuma kannen miji da yayyinsa sun hanata zaman Lafiya. sau biyu tana samun ciki suna barar mata da shi,Duka sau biyu ga na miji ga na Danginsa igiyar aure saura d'aya kuma yaki ya saki duka Halisa ta rame ta Lalace kamar ba ita ba,Duk kushen Hajiyar Dala da Kallon renin ya'yanta yanzu sun san a inda suke yi,Sun kuma gane muma mun sha kwana Fiye da yadda suka sha barin ma ni shigar alfarma da kaya masu Tsada sai dai su nuna min kwalliya da gayu, yar wayewar nan ma ai muna da ita daidai gwargwardo.
Kafin bikin Badariya su Amir sun zo min sun min hutun azumi har salla tare dani suka yi naji dadi matuka,har da su Farhan tunda ko'ina daman tare suke zuwa har yau ban taka kafata Lagos ba har kuma karin girma mijin Anty Fadila ya samu aka had'a walima ban je ba su Ammi sun je tare da su Nana Fatima. har da Hafsah sun kuma Biya sun ga su Amir suka dawo da labarin kyakyawan rayuwar da yaran ke ciki.
Mama na tsaye kan su ita da Ishaq zainab kuma ba'a sakata a lissafi Fa'iza ma da suke kira islam gida take barinta Mama da Shema'u na jigilan wahala da ita.
Yanzu haka Amir he is now 16yr kuma ya gama Jss zai shiga SS section ne ita kuma Anum she is now 14yrs Tana bauchi wajen Badariya ta roki yayan nata yasa an kaimata ita hutu da sun koma zata shiga Jss3 ne Musty kuma he is now 12,da wani abu kuma ya gama primary zai shiga Jss1 Ahmad ne ke matakin aji shidda a primary yana da shekara goma a duniya yara tuni sun biyo tsawon kafan Ubansu, sun zama manya barin ma Amir wlh in mukajera sai ace kanina ne to an fada ma Lokacin da suka zo min Hutu kowa ya shiga ya gan su in Goggo tace ya'yan Fa'iza ne sai an tsaya kallona barin ma Amir da ya fini Tsawo Anum haka ni ko yar karama jikina ba Kiba sai murjewa,Amir yana kara girma Hallayansa na bayyana shuru Shuru marason Hayaniya sai dai baya Daukan Reni yadda yaran ke tsoron sa ko Babansu basa tsoro haka, tsawa kawai zai Daka musu yanzu nan zasu shiga Taitayin su duk rashin jin Farhan da Ahmad kuwa basa rawan kai a gaban Amir hatta ko da Anum da suke sako baya mata da wasa ni ko sai Hakan ya yi min dadi na tabbata watan watarana Amir ne duka Uban ya'yana zai iya karesu a duk inda rayuwa ta kaisu addu'ata kullim Allah ya raya su ya shiryamin su.
Da bikin Badariya ne naga Anum har ta fara kirgen Dangi da na gani sai da gabana ya fadi,araina ina fatan Tsarewar Allah a kan y'ata sai dai Hankalina ya kwanta da Badariya ta tabbrtamin da bata fara Jini ba.
Sannan karin salama ta weekeed gidan Anty Fadila suke saboda Hadda idonta na kansu a gida daman basa Fita suna gida,Mama kuma na lura da su ga Amir sannan ga Jamal duk da shima ya koma kano da zama da taimakon Abba ya samu aiki da Hukumar Wutar Lantarki na jahar kano chan yake zaune yanzu har ya siya motar hawa sai dai in ya samu hutu yana chan Lagos din yayi achan.
Tsakanina da Zainab har yau bata sauya ba,Muna zumumci mu ko nace kawancen mu har gobe ko fad'a suka yi da Ishaq sai ta nemi shawarata ni ko da zuciya daya nake bata shawara duk da sai a Hankali tana son mijinta shi kuma ya riga ya gama Sarewa da ita ana dai lallabawa kawai,Ko shi bata Fad'ama ta saka Tsarin iyali ba ammh ni ta fadamin saboda tace bazata iya wahala ba ga fita aiki ga yara sai kace ita ke kula da su yaran da ko cikakken minti goma bata zama da su in ta Dawo aiki d'aki take shigewa ta kwanta, Mama ce kan yaran Don ma Allah yasa ta Dauko Diyar Anty Hure daga yamai tana taimaka mata da girki da gyaran gida shema'u kuma taji da Hidiman yara.
Har yau kuma Badariya bata daina Fadin hakkina ne ke bibiyanta ba, Saboda tun auranta itama bata Huta ba Uwar miji ta sakata gaba da Farko gidanta ya gina mata ita kadai ta tare ni kuma har Bauchi sai da na raka Badariya ni da Raliya dake fama da Laulayi Lokacin ammh tace sai taje Badar ce fa,Dayake wanchan cikin fita yayi sai a lokacin Allah ya bata wani haka muka dawo muna santin gidan Badariya sai ga shi ba'a rufe wata ba ta kirani tana kuka tace uwarsa tace zata dawo gidan da zama bazai yuyu a bar ma Badariya katon gida ita kadai ba, ada tana gidan yayan sa a zaune ne ammh Saboda Jaraba ta dawo gidan Badariya ta shiga takura mata,Ahalin ga uwargidan chan a katon gidan da yafi na Badariya tana watayawa.
Saukin Badariya daya Yusuf na sonta ammh fa basu samun sakewa kuma daman ba mazauni ba ne yana yawan Tafiye tafiye,Badariya na yawan kuka da abunda Mama ta min ne itama ake yi mata na yarda da Haka ni kaina nasan Mama ta zalunceni ta kuntatamin fiye da Tunani sai dai na yafe mata har ga Allah ita kuma Badariya koda yaushe ina gayamata tayi Hakuri jarabawarta kenan
Wannan hutun da Anum taje mata ne Uwargidan ta Haihu zataje barka mijin yace ta bari ya dawo taki jin maganarsa.
Ta Saka Anum a gaba sukaje suna zuwa ta saka aka sakar musu karnuka suka Dawo gida a jigace.
Badariya ta fadi ta Kurje gwiwa shine Anum ta kirani tana bani Labari ina Dariya,Dariya ta yadda Anum ta fi uwarta gudu Naga kuma Badariya bata da wani jiki sai dai in itama aure ya Bud'ata ne.
*****
Yau ina da aikin Dambun kaji guda ashirin,Shiyasa na fito duk da ma'aikatan sun zo har sun tafasa kajin,Da Goggo naci karo a falo tana Faman tsinke zogale sannu nayi mata ta amsa tana Fadin"Kin gama Dariyan kin fito kenan?
Mirmishi nayi ban yi mgana ba Goggo tace"Gwara da kika fito,.Duk da sun iya ammh ki fita ki Duba musu"
Da toh na amsa mata sannan na fita suna Tsakar gida suna cire naman suna rabasa da kashi suna ta Hiran su ina fitowa suka dago suna gaisheni. duk da mun gaisa da wasu daazu Jummala ce ke nuna min abunda suka yi na jinjina kai kafin nace"Indo da Zainabu su yi daka yau,Maman Jamilu da Laure su yi Suya matsewan kuma su Auwalu sai su tayaku ni da jummala Zamu hada kwallacha ne"
Da toh suka amsanin ranar yini muka yi wannan aikin daga karshe sai da nazo na kama musu wajen matsewa yana da wahala ne sai dare na samu kaina nayi wanka nayi sallar Isha'i girki ma Goggo tayi ranar.
Badariya na kira naji ya jikin nata sai take cemin sai da taje chemist yanzu kuma uwar mijin tace sai ta koma gobe karya take makirci ne bata son zuwa ammh karnuka basa komai,ganin tana neman yin kuka yasa nace"To kin gayama Yusuf din..?
Kai tsaye tace"Na fadamai komai shima ya kirata ya ce mata bana jin Dadi ta bari ya dawo, ammh ta kafe sai yace nayi hakuri naje in na isa gidan agoben kada na shiga na kirasa zaisa azo a shiga dani"
Jin haka yasa na shiga Lallashinta ina nuna mata tayi addu'a Allah zai kawo mata mafita domin naga ranar addu'a Allah na rike shi kuma ya taimakeni.
Kafin mu gama waya na tambayi Anum ban ji karadinta ba tace min tayi barci a raina nace su Anum an ji maza yau dole ayi barcin wuri.
Washegari Aikin abincin biki garemu na Gidan Alhaji Sabo Dutsenmah wani mai kudi ne Tunkunya lamba Talatin talatin hudu muka yi biyu Jalop din shinkafa da kayan lambu Daya Priderice ce.
Da wuri muka gama suka zo suka Dauka na saba musu daman girki kudina ta banki suke turomin,Shiyasa ban damu ba da yake ma sunana suka sani da gidan mu ba ni ba,ba fita nake yi ba in nayi nisan fita gidan Yaya Mariya ko gidan Anty Nasara ko gidan su Yaya isa doguwar tafiya sai ko kasuwa katsina dai ina shiganta Tunda Ga sa'adatu ga Habiba,Frezer dina da na siya sabuwa tsohuwar ita na bamawa suna ta godiya ita da Haruna ni ko kaf yanzu ban da wata kawa kamar Sa'adatu kano ma ina shiga siyan kayan hadin turaruka in ban samu wani abun a katsina ba.
Shima bana kwana Saboda karatu da ayyuka na ko Dutse sau daya naje wajen Nana Fatima na kwana Biyu kaduna kuma B'arin Raliya mukaje muka Dubata muka dawo aranar Ammi ce ke korafin bana zuwa ammh Abba ba ruwansa tunda yace ya yi min alfarman na zauna a karofi bai kara tada mganar ba.
Goggo ma tayi ta k'orafin naki zuwa kaduna nayi ko sati ne,Sai tace in aiki ne ga su jummala ai sun iya komai ga waya ko ba na nan za'ayi komai ni ko sai nace mata"Karatuna fa kin fa san Hadda baya son yawo goggo. Ki bari ai mun kusa gamawa in muka gama zan je sai su Ammi sun gaji da ganina"
Kyaleni Goggo take yi Tunda tasan ni da Kafiya ko kan zawaran dake sintiri a kaina ban taba Fita ba kuma fa da Likaf nake yawo da dogon Hijabi ammh har ake zuwa kirana Mallam ko maza sun fi biyar da suka mai mgana masu tarin mata da yara ni. Har a ga Allah a cikin raina ban dauka bayan mutuwar aure akwai mazan da zasu fito su ce suna sona ba. In ban manta a yadda Ishaq ya sha kusheni ba. ban dauka ina da sauran amfanin da wani namiji zai ganni ya yaba ba,ammh duk da haka ban yarda na ba ma kowa fuska ba.
Goggo tayi ta fad'an ba kyau abunda nake yi. ni dai na kyaleta har k'arata takai wajen Abba wai haka zan zauna nufina bazan kara aure ba Abba ko yace ta kyaleni yanzu Hurumin su tursasamin nayi aure ba na su ba ne,
Su barni na samu natsuwa Daganan ne Goggo ta shafamin Lafiya ammh Har Baba Ati da Inno da suka zo sai da na kosa su tafi Saboda yadda suka Dameni kamar ina kan su ne.
Ni aure yanzu ko sha'awa baya bani mazan ma sun fita raina kuma nasan har da kudin da na ke kamawa a Hannun yasa suke Kara kaina akaina Tsabar ma renin wayau har da mijin Ma'aikaciyata Zainabu da Farko Godiya yace yazomin kan daukan matansa da nayi ashe ba haka bane. sai naga ya zake abun ma sai ya bani Dariya wai me maza suka maida mata ne..?na lura gabad'aya maza Halinsu daya shiyasa nayi musu kullin Goro na tattara su na ijiye na cigaba da kasuwancina.
Anum ta gama Hutunta a Bauchi,Daga chan Badariya da Mijinta Suka sakata a jirgi suka maidata da kansu,da kuma godiya da farko sun so su turata ita kad'ai ne Ishaq yace kada su fara yi mai wannan ganganci su saki kamar Anum ita kadai a jirgi daga Bauchi zuwa Lagos.
Dole suka shirya tafiya suka kaita,kwana Daya suka yi suka dawo duk da yaso su tsaya su huta mahaifiyarsa ta hana dole dai suka Dawo kuma bai jima ba ya sake wata Tafiyar ya bar Badariya cikin Takura da Tsamgwaman uwar miji da yan'uwanta.
Haka dai rayuwar ta cigaba da gangarawa da dadi ba dadi,Koda yaushe muna waya da Badariya tana Fadin Halin da mahaifiyar yusuf ta sakata aciki ni kuma ina bata baki Shudewar wattani biyu mun yi nisa a Haddamu mun shafe izifi Hamsin da Takwas,sauran mu izifi biyu,Mu uku ne muka fara saukewa ni kadai ce Wacce ta Haura talatin sai wata yar shekara ashirin da takwas,sai namiji iyakarsa da Biyar,sauran suna bayan mu hadda nake yi ta sosai daman ina Saurin Dauke abu a kaina ko malaman suna matukar jinjina ma kokarina,ko Goggo tayi tamin Fad'a kwata kwata bana samun hutu saboda karatun hadda ga aiki,kada hawan jinina ya tashi nace mata ai ba cikin damuwa nake ba ba abunda zai faru da izinin Allah.
Ina dake ma karatun nan ne domin amfanin kaina da kuma al'ummata da ya'yana duk da basa tare dani,sannan na nuna ma duniya nakasa ba kasawa bace,kuma Samun fiffike daya na ilimi ba tawaya bane,ba kuma ina ja da karatun boko ba ne a'a ina so mutane su sani bazai zama tawaya ko Wariya don bakayi boko ba,sannan bazaka zaman abun wulakantawa ba domin baka iya Turanci ba.
Zan nuna ma Mutane cewa shima Haddan Qur'ani ilimi ne kuma mai girma. rashin karatun Boko ba tawaya ba ne ammh rashin ilimin addini shine babban Tawaya da koma baya. domin shine Ilimin Da Annabi yazo mana da shi,shiyasa na Dage kuma ni kaina nasan ina kokari matuka ko don kada na bama yan'uwana da Abba kunya.
A lokacin ne Yaya Abdul'Ahad ya daga zuwa kasar Calfonia karo karatu bai tafi da Raliya ba.Tunda tana da ciki Tsoho sai bayan ta Haihu daga baya sai ta bishi Abba da Ammi suka rakasa har chan sai da aka gama komai sannan suka Dawo kaduna.
Ya tafi ba jimawa ko wata bai rufe ba Raliya ta haihu haihuwar kuma tazo da gaddama C.S akayi mata Sai da ta kusa sati a asibiti sannan aka sallameta kanwar Hajiya Aisha taje ta zauna da ita sannan ga Ammi itama tana Tsaye a kanta shiyasa ma da akace ko zata koma gida ne tace nan zatayi zamanta haka suka yi da mijinta.
A ka shirya suna Sati biyu tsakani Yaro daman yaci sunan Abba wato Usman,kuma abun jin dadi sunan yazo min a daidai na had'a Haddata izifi sittin ni na fara hadawa sai akace na bari sauran su hada mu kai goma sai a yi mana Sauka da karban shahada,Islamiya kuma daman da Sauki Sauki tunda wasu littafan maimaici muke yi shiyasa na shirya zuwa kaduna ga shi daman Hajiya ta sakani gaba kan girkin suna da Turarukan Amarya shiyasa ana gobe suna muka tafi da Yaya mariya da Anty Nasara sai Aminan ya isa da Goggo aiki kuma na bar ma su jummala nace mu rika mgana ta waya.
Ya Asiya ma tazo Badariya kuma sai ranar suna ta iso,gida ya cika da yayyin Raliya ana ta Hidima,Ammi ma tayi taronta a gida walima ta shirya na Usman Abdul'ahad Usman karaye(Walid),ita da Abba soyayyar Abdul'ahad ya shafi walid har su Nana Fatima na fadin suna kishi. suma dukkansu duk sun zo akayi suna Lafiya aka ci aka sha akayi Hotuna,kusan dukkansu sun koma sai ni kadai Ammi tace sai nayi wata zan koma ina Dariya nace daman nazo da niyar nayi musu hutu.
Wajen kwana biyar nayi gidan Raliya Tafiyar Badariya yasa na koma gidan Abba,yayi murna sosai kuma yana son zuwana kawai dai bai taba mgana ba ne,Muka samu Lokaci mai tsawo muna Hira ni da shi na fad,'amasa na had'a Haddata saura karban Shahada kawai sai saka albarka yake yi har mganan Ishaq sai da mukayi yana Fadamin duk bayan kwana biyu sai ya kirasa sun gaisa na Fahimci Abba yana Fad'amin yadda Ishaq yayi Laushi ne kila ko zan koma ne,ni ko baisan komai ya fita raina ba. ganin nima ban bada Fuska ba shiyasa shima bai Takuramin ba.
Tunda naje kaduna shikenan su Abba suka rikeni musamman Ammi daga wata sai ga shi na share wata biyu,ina nace zan tafi sai Ammi tace ban isa ba in nace aiki sai tace ga shi nan ina waya da su komai na tafiya daidai,sai nayi Shuru sannan tunda ga Goggo ban damu ba,nasan zata kula da komai kuma ko aiki ne ya samu in aka kirani sai na kira jummala ko goggo mu yi mgana komai zasu kamallah kudin kuma in a hannu ne Goggo ta karba ta sallame su in kuma ta banki ne Yaya isa nake turamawa ya kai ma Goggo to anan din ma ban zauna ba ina taba Hada Taruruka,har zaria mun je da Ammi siyan kayan hadi'n su kawayenta kaf daman sun sanni ta fanni kayan kamshi zamana kuma a garin sai kowa yace yana so. nan din ma harka samun kudice ta Bud'emin sai godiyar Allah sannan tunda nazo ni nake yin girki Ammi ta sakarmin komai su Hafsah suna zuwa makaranta har weekend wani Lokacin.
Abba kuma na Office in kuma tafiya ta kamasa sai kiga yafi sati baya garin,suna yawan zuwa abuja da Parthercourt,to wannan karon dai naji Ammi na tad'in zasu yi warkshop gabadaya ma'aikansu na warri da porthercourt a nan Kaduna na tsawon wata daya har ma'aikatan su na Edo.
Kuma naji Ammi na ambatan har da Ogan Abba wato Engr shima yana cikin Warkshop din.
*Janafty*
[7/28, 11:26 AM] U.M Collection ZMFR CM: *KNKB3009*
*TASTED & TRUSTED*
*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATUN SAIWOWIN MUTANAN CHADI DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZAR AMARE, MASU JEGO DA WADDA TAKE SON GYARA KANTA*.
*AN GWADA ANGA INGANCINSA SHIYASA NA KE TALLATA MUKU DA K'ARFIN GUIWATA*.
*ABIN BIRGEWA DA WANNAN SAIWOWINRL ZAKI YI AMFANI DA SU SAMA DA SAU DAYA.*
*AKWAI FULL PACKAGE, AKWAI RABI, TA YADDA KOWA ZAI IYA SIYA*.
*SANNAN BABU BAURI NA TASHIN HANKALI.*
*DA KANKI ZAKI DAFA ABAR KI, KOMAI ANA SAKA WA A CIKI*.
*SHIN KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR, KO KUWA KE CE KIKE SON GYARA KANKI?*.
*KAYANA NATURAL NE DOMIN SAIWOWI NE DA AKE HAKOSU A DAJIKAN CHADI. BAYAN SAUKAR DA GAMSUWA HAR YAQI SUKE YI DA DRYNESS DA KUMA INFECTIONS.*
*AKWAI NA TSUGGUNO DA YAKE HA'DE MACE TA MATSE.*
*AKWAI HADADDUN DAKA NA SHA DA MADARA KO NONO WANDA BABU ALGUS*.
*SANNAN AKWIA GADALIN MATA NA ASALI, WANDA SHA YANZU NE MAGANIN YANZU DA IKON ALLAH*
*DUKKANSU TESTED & TRUSTED NE*.
*TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU*
*08032773332*
*DOMIN KARIN BAYANI, SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*.
*NATION WIDE DELIVERY*
*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*
*09069067488*
A satin suka fara workshop din,
A nan babban ma'aikantansu na NNPC da ke kaduna. in Abba ya fita tun safe sai dare Direba ke dawo da shi gida a gajiye. wanka kawai yake yi yaci abinci ya kwanta,kwana uku da Farawarsu ranar da daddare bayan ya dawo yana cin abincin da na Dafa na shigo ni kuma mu gaisa.
Ina zaune gefensa na Hagu Ammi na barayin Dama ganin ya share Mulmulen tuwon shinkafa guda uku da Ammi ta sakamai ammh kuma yana mganar ta karamai,jin haka yasa muka kallesa a tare ni da ita cikin mamaki tace"Na hudu fa kenan Baban Nana.."
Cikin ka'da kai yace"yunwa nake ji ne Maman Nana. rabo na da abinci tun karin da nayi na Safe fa."
Cikin mamaki tace"Tun Safe fa Baban Nana?baka ce min akwai restaurant guda da aka dauko suna baku abinci a wajen ba..?
Kai tsaye Abba ya kalleni kafin yace"D'iyata k'aramin tuwon nan kin ji,in na biye ta tambayoyin wannan uwar taku yunwar sai ta kara jigatani"
Ina Dariya kafin nayi mgana,Ammi ta zubamai ta karamai hade da miyar Ogun din da nayi wacce taji Bushasshen kifi da Kashin Rago.
Sai da ya fara ci sannan ya Dago yana Fadin"Wato maman Nana Allah ya yi ma Diyar nan taki albarka ta shagwabani da girke girkenta duk inda naje naci abinci in ba Dandanon Abincin ki ko nata ba,wlh baya kosar dani sam ga masu abincin sai ma abunda ka zaba ni dai wlh kada'n nake ci sai naji duk ba Dadi na gwammace in na dawo sai naci gabad'aya"
Ammi tace"Gaskiya to bari ka Hakuri kana ci zama da yunwa ina yaga amfani in wani cutar ta kama ka fa..?
Abun wanke hannu yace ta tara masa sai da ya wanke hannu da bakinsa sannan ya koma ya kishingida yana Hamdala ni na kwashe kayan zuwa Kitchen ban koma Falon Abba ba,sai na wuce dakin da na sauka nayi shirin kwanciya ban san kuma ya Abba suka karkare mganar ba da Ammi sai washegari Ammi ke kara min mganar cikin wasa tace"Jiya kin ji Baban ku da rigima. Kamar wani yaro yana zama da yunwa sai kaci abunda ke hannunka in ya dawo sai yaci na gida ba shikenan ba"
Nima cikin Dariyan nace"Ba matsala fa Ammi za'a iya yi masa abincin sai Direba ya rika zuwa yana karban masa'"
Ammi ta kalleni kafin tace"Ko..?duk wahala ce Fa'i bar rigiman Baban ku kin ji"
Ni kuma na Dage sai a rika yin haka Ammi ta tabe baki tana fadin"Ke mai Uba ko..?Allah ya ba da sa"a
Abba na dawowa ta fad'amai sai ya Daga waya ya kirani Lokacin ina waya da Badariya sai da muka gama naga kiransa sai na saka Hijabi zuwa Falonsa,a chan na iske Hafsah da Nana khadija suna ganina suka fara Rige rigen tashi Ammi ta kallesu tana Fadin"Daga gani baku da gaskiya ko..?
Ina Dariya nace"Ammi Wainar Fulawa na soya nafa saka musu nasu. daga shigata wanka suka zagayo suka Kwashe wanda na bari zan ci"
Ammi tace"mugaye shiyasa zasu gudu"
Dariya suka saka Nana Khadija tace"Bani bace fa Hafsi ce"
Hafsatu tayi saurin cewa"Wlh bani ba ce ni da bana cin wainar fulawa ma"
Hararanta nayi kafin nayi mgana ta kama kanta Abba waya yake yi shiyasa bai sakamana baki ba sai da ya gama su kuma Lokacin sun fice suna Dariya su san abunda suka aikata.
Zama nayi gefen Abba muka gaisa ya amsa cikin Sakewa kafin yace"Mamarku ta fad'amin kin ce bazaki bar babanki da yunwa ba ko.?
Ina mirmishi na Daga kaina kafin nace"To Abba kana damu meyasa zaka zauna da yunwa?
Abunda kake so shi za'ayi maka."
Jinjina kai ya yi Lokaci daya yana fadin"Nagode sosai Allah ya yi miki albarka yasa ya'yanki su rama miki.
Ammi ta amsa da Ameen kafin tace"Ba ka ce Allah ya bata miji nagari ba..?
Ina jin Haka na mike ina fadin"Abba mu kwana lafiya"
Ammi ta bini da Dariya tana Fadin"Diyar taka Baban Nana sai kayi da gaske ko wani gwaskan muka samu sai ta bamu kunya na lura da take takenta"
Abba ya murmusa kafin yace"kyaleta ba mai yi mata Dole. in ma bazata kara yin auren ba ina bayanta"
Ammi ta karkace baki kafin tace"Haba da kuruciyarta Baban Nana..?Allah zai kawo mata wani wanda zai kaunace ta saboda Allah ya rud'ata ta zo da kanta tana fadin Abba na amince masa"
Ta karishe fad'a tana Dariya Abba ya jinjina kai yana Fadin"Allah yasa ni dai a nawa shawaran ta daidaita da Baban yaran nan ishaq ya yi nadama sosai wlh in da zata koma da ni kaina naso hakan'"
Yana mgana Ammi na tabe baki sai da ya gama sannan tace"Nafi yi ma Fa'iza sha'awar sabuwar rayuwa akan ta koma Rayuwarta ta baya kwata kwata ishaq bai chanchanci a basa wani Dama ba, gwara haka dai kowa da nashi Kaddaran"
Kai kawai Abba ya kada kafin yace"Tunda baki son sa ai komai zaki ce, ammh duk in da zata je bai kai inda ta fara gina Zuru'arta ba azizat. da sabon yabe duk lalacewar tsoho wlh gwara tsohon yaben nan ni a ganina"
Ammi ta kada kai kafin tace"Wlh wani Sabon Yaben yafi tsohon sau Duhu"
Kyaleta yayi sanin Halinta ita ko taki Hakura tacigaba da fadin"kuma in kana mganar ya'ya ne ai sun saba da Rashinta,suna zaune gidan uban su in da ya dace da su ita kuma Allah ya bata wani mijin taje tayi auranta ta Huta taji dadinta"
Abba ya gyara zama yana fadin"Allah ya bata Azizat"
Dariya tayi kafin tace"Ameen Baban Nanas d'ina"
Girgiza kai yayi yana mirmishi kafin yace"'Allah ya shirya Maman Abdul'ahad'
Da Ameen ta amsa mai tana Dariya mganar Fa'iza suka rufe su ka kama na Raliya da mganar sai Walid ya yi kwari za'a shiryamata tafiya wajen mijinta.
******
Kamar yadda nayi alkwari ban sauya ba tunda ina nan ba ranar Tafiya. Goggo ma bata damu ba tasan daman Ammi nata korafin rashin zuwana,aranta daman tasan sai an ganni kawai,daman ni nake yin girkin Rana sai nake dib'arma Abba Ammi ta kirasa ya turo Direba ya Daukan masa ya kai masa watarana ma in ya makara sai dai a basket yake tafiya da abun karin nasa ya yi achan ba'a Rufe Sati ba Ranar Abba ya dawo yace yunwa yake ji sosai.
Ammi ta kallesa yana ragema Tie din wuyansa tsukewa tace"a'ah ina abincin da direba yakai maka..?
Kai ya girgiza kafin yace"Wani abinci..?ai ina gaya miki tun rana na biyu da Ashuru ya fara karbo'min abincin su Engr Bashir suka sakamin ido. wlh tun suna su biyu har sukamin gayya suna min tsiyan ina musu wayau ina barin su da abincin kedaran maza ga mai dadi da Dadin dand'ano,da nakan samu naci ko ba da yawa ba,ai yau ko a bakina ina gaya miki Engr ya ga Shigar Ashiru Office d'i na da kwandon abincin bai yi mgana ba sai da aka tashi sallah da cin abinci yaga mun zame jiki mun shige Office dina ya Rutsamu Maman nana"
Ammi ta zaro ido tana Fadin"Allah yasa ba laifi kuka yi ba?
Abba yace"Wani laifi..?ai shima cewa yayi an munafuncensa barin ma ni ban taba gayyatansa shima yazo aci abincin da shi ba,karshen ta dai wanda zan ci na bar mai ni da yunwa na yini wlh sai santi suke suna fadin muna jiran na gobe Engr Usman"
Ammi na Dariya tace"To sai kace musu me..?
Abba yace"Nace ba mai gajiyarmin da D'iya kunyar Engr naji domin da kansa yace a fada miki a sawo da nashi Gobe ba Baban Nana kadai ke kaduna ba"
Ya karishe fada yana Dariya Ammi ma Mirmishinta take yi kafin tace"Allah Sarki kada ya damu zan fad'ama Fa'i ta kara sanwa Hannunta ya yi albarka"
Abba yace"Ban so a rika wahalar da ita ba domin Engr ya yi mgana ba, har ni hakura zan yi mu rika cin wanda ma'aikata ta bamu"
Ammi tace"A'a bazai ayi haka ba. bazai gagara ba in sha Allahu"
Da farko Abba bai amimce ba Darajan Engr da ba abunda bazai iya masa ba yasa ya amince,ammh sai da ya kirani yamin mgana har da bani Hakuri ina Son Halin Abba mutum nagari mai sanin Darajan dan Adam
Ni ko nace masa bakomai na saba ba aikin da zai gagareni nan duniya.
Abba nata min godiya kamar bai isa dani ba.
Tunda ga ranar na kara sanwa a babban Tukunya nake yin girkin,a cika manyan kololi direba ya kai musu bayan abinci kullum da kalan lenukan da nake hada musu kala kala wadanda muka koya a katsina da kuma daman wadanda na iya tun a baya abinci ko kala kala nau'ika Dabam Dabam,ko wata rana da kalan Godiyan da Abba zai ce sun ce ayi min in ya dawo da farko sun zata Ammi ce ke yin girki daga baya ya fada musu Diyarsa ce to sun zata ko cikin ma yaran da ya Haifa ne.
Abba da kansa ya fad'amin wani cikin abokan aikinsa yace a jinjina min tabbas a gaisheni bai taba cin girki mai Dadin girki ma ba har ko na matarsa Ranar ma Dubu Ashirin Abba ya kawo min Sabbin yan Dubu Dubu yace gashi in ji Engr yace a kai ma yar Baiwa.
Ammi nata Dariya da naki karban Abba ya min tsawa yace maza na karba ai kyauta suka bani na wahalan da nake yi sai na karba,Itama Ammi da nace ta ciri wani abu ki tayi haka takemin ko Aikin Hada Turare na samu in na bata wani abu bata karba,Sai dai na bama su Hafsah kowacce dubu uku suna ta Murna.
Inno ma na bata Dubu ukun ta karba tana ta saka albarka tana nan idonta ya tashi tana ta fama da shi Baba Ati na Korafi bata dawo ba.
Yau da gobe bata bar komai ba,Har ga shi su Abba sun kamallah warkshop din su cikin nasara,Ranar da suka gama washegari bayan Abba ya fita ya kira Ammi a waya yace ayi girki na Mutum goma haka su Engr sun ce zasu zo godiya anjuma da Daddare.
Bana gida ma Lokacin ina gidan Raliya ni da su Hafsah Ammi tamin waya,daga gidan Raliya Ashiru Direba ya wuce damu kasuwa nayo cefane,a hanya ma muna ta waya da su Anum sun samu wayar Mama,Amir ne kadai bamu yi mgana ba shi bai cika karamniya ba. sai mu yi waya da sauran yaran sau nawa shi bamu yi ba ko yana daki ko yana karatu baya son damuwa sai dai mun yi waya da shi ta wayar Jamal in yana gari zai saki jiki mu sha Hira da shi na lura Shirgin yaran ne baya son shiga gudun reni.
Tare da su Hafsah muka yi aikin Tuwon Shinkafa mukayi da miyar Allayahu wacce taji kashin Rago da manshanu sai Ferfesun kayan ciki da priderice,sai Fruit salat sai nayi musu kunin Aya ga zobo,sai lemun kankana,sai yammah muka gama muna gamawa ana kiran sallar mangariba Ammi bata da ko yar aiki komai ita ke yi da kanta,su hafsah na bar ma gyaran kitchen din ni kuma na tafi yin wanka nayi sallah ba Karya nagaji sosai shiyasa ina fitowa daga wanka nayi sallah na kishigida ina azkar barci barawo nata son sace ni karar wayata yasa na zabura Jummala ce ta kirani kan mganar gidan Alhaji Bukar na cikin gari sun turo da kaji talatin za'ayi musu Dambun kaji na girgiza kai ina fadin"Kai aikin ya yi yawa jummala..?zaku iya kuwa..?
Jummala tace"Zamu iya maman Amir ga Zainabu ta dawo ma, sai nayi ma su laure mgana su Auwalu sai su tayamu Matsewa"
Kai na jinjina kafin nace"Sun hado da kayan yi ne..?
Kai tsaye tace"Ban duba ba tukunna"
Ban damu ba nace"Duba bari na kira Goggo mu yi mgana"
Goggo na kira bayan mun gaisa na fadamata yadda muka yi da jummala Goggo tace"Sai su yi ga su Auwalu ba komai zasu iya, da kina nan ai kun sha yin masu yawan su"
Jin haka yasa sai nace to shikenan bayam gama wayarmu da Goggo ashe ma matan gidan Alhaji Bukar ta kirani sai na kirata daga baya mukayi mgana tace an ce bana nan,ammh sun kai ma Jummala nace ta fadamin kada su damu za'ayi ammh sai nan da kwana Biyar zasu samu tace bakomai sun san ka'ida na ko wacce kaza daya Dari takwas ce nake yi tace zasu hada su Turomin kudin aikina ta banki da haka muka rabu cikin Karrama juna.
Sai daga baya na kira jummala na fad'amata yadda zasu yi tunda tace sun kawo komai da komai harda kayan kamshi,wayar ne ta Daukemin Hankali har akayi isha'i na tashi nayi salla barci ne malale a idona shiyasa na koma na kwanta saman gado sama sama naji mganar su Hafsah kamar wacce ta sha wani abu na kasa tashi,sai asuba shima sai da Ammi ta shigo ta tasheni na tashi ina jin kaina yamin nauyi.
Ban ko san yadda bakin Abba suka kare ba sai da safe na shiga gaishesa ya Turomin tulin kudi gabana na kallesa da mamaki ina fadin"Kudin miye wannan Abba..?
Kai Tsaye Ammi dake kusa tace"Kudin ki ne jiya bakin Abban ku suka ce a baki Tukwici da godiya"
Ido na kwalalo,cikin mamaki kafin na samu bakin mgana Abba ya yi dariya yace"To rufe bakin mana Fa'i"
Ganin yadda na bude baki cike da mamaki,da sauri na rufe bakin ina fadin"Abba naga kudin ne da yawa..?ni fa yarsu ce Abba don ma nayi ma abokan aikin ka girki bai kamata su biyani ba wannan kudin ai kamar biyana suka yi"
Abba yace"Wlh haka na fad'a musu suki jin mganata sun so ma kizo ku gaisa akaje kin riga kin yi barci. nace a kyaleki sunce kema yarsu ce ba Kyauta ba ne Tukwaici ne"
Sai naji na kasa mgana Ammi tace"Dubu Dari ce cif Fa'iza sai a kara jarin Turaruka.."
Ina mirmishi nace"Allah ya biya su da aljannah kamin godiya sosai Abba"
Abba yace'In sha Allahu"
Ammi na daukan bandir daya na kudin take fadin"Kowanne goma ya bata kenan..?
Abba yace"Ban sani ba fa. ni naga dai suna tarawa waje d'aya"
Ammi tace"Tab..don ma ba babban Gwaska kenan Engr da kila sai a takarda check"
Abba na Dariya yace"Maman Nana ke dai kina kaunar Engr din nan"
Ammi tace"To dole na kaunaci Engr da zuru'arsa mana Baban Nana suna da kirki da Dattako ga harkan girma. karon farko fa kyautar dubu Dari ya yi min Baban Nana ina zan manta da wannan kyautar,nayi takaicin rashin zuwansa jiyan nan wlh"
Abba ya girgiza kai yana kallo na kafin yace"Fa'i kina jin maman ku ko..?
Ni ma mirmishin nayi ban ce komai ba Ammi tace"Wlh da yazo da Fa'i taga kyautar girma"
Abba yace"Kila yana da abu mai muhimmanci ne shiyasa. ni dai yace min ayi mai afuwa ammh na bisa bashi zai zo har gida ya gaida Maman nana da Diyarta da gajiya"
Ammi tace"Allah yasa dai yazo rabonsa da gidan nan tun murnan auran Nana fatima da ya zo maka Bayan ya dawo kasar na Abdul'ahad a waya kuka yi abun ku bai zo ba"
Abba yace"Yana da ayyuka da yawa ne kinsan Babban mutum irin haka Allah yasa kada tafiya kuma ta kamasa zuwa wani wajen"
Ammi ta amsa da Ameen suna ta Tattaunawar su ni dai sallama nayi musu Abba yasa na kwashi kudina zuwa shashen Inno nan nake zuwa mu sha hirarmu in su Hafsah sun shiga makaranta.
Na nuna mata kudin ta yi ta saka albarka da na matsa ta Dauka sai ta kalleni tana Fadin"Shikenan komai sai kin bani Fa'iza..?
Ban ce komai ba ta saka Hannu ta dauki Dubu biyu tana fadin"Na dauka Allah yasa albarka ni da ba abunda na rasa baban ku da mamanku tun kafin nace ina bukatar abu suke min. kuma ga ku kuna iya bakin kokarin ku Allah yadda kuka ji kanmu Allah yasa kuma naku ya'yan su ji kan ku'
Na amsa mata da Ameen Ameen muka ci gaba da Hira,ina jin dadin zaman kaduna alherin da na samu na kudi ban san iyaka ba sana'a nada dadi da amfami mu tashi mu nemi sana'a sannan mu kuma gayama Allah
Cikin Hirar ne take tambaya na ya wajen yarana nace duk suna Lafiya cikin mganar su na manya tace"Fa'iza kina ganin bazaki ba ma baban yaran nan wata dama ba..?ya yi nadama zuwan sa gidan nan ba adadi yana zuwa gaishemu kuma cikin neman ki koma ne Fa'iza"
Ina jin nauyin Inno sai na kasa mata musu,Ishaq ya riga ya samu kan Abba da Inno harda anty Fadila ko da yaushe muka yi waya sai ta fara korafin na dawo gidan mijina na zauna da ya'yana Abba dai bai taba min mgana ba sai dai a yanayinsa na Fahimta,ga Inno ma tagaji ta furta kaina na kasa na kasa mgana sai ta jinjina kai kafin tace"Ki yi Tunani ko Saboda yaran nan Fa"iza. ko wani aure da na shi kalubalen yanzu bama shi ba ko Ahalinsa bamai kara takaki kina da komai da bazai saka namiji ya rainaki ba. ga yaranki sun kawo girma ki yi tunani a matsayinki na uwa ko Saboda ya'yan ki"
Tafada cikin wani yanayi na lallashi,kafin ta gama mganarta hawaye sun kawo ido na,Inno ta Cigaba da fadin"kuma in ki duba kina da kuruciyarki bai kamata ki kare rayuwarki ba aure ba, ko ki yi Tunanin koma ma uban ya'yanki ko kuma ki fitar da wani mijin ki aura ammh a shawarata da hangenmu na manya gwara ka koma inda ka saba ka kuma sani da ka koma inda baka sani ba Fa'iza, sannan ko bakomai akwai zumumci tsakaninku ko ba'a duba komai ba a duba zumumcin Tunda Allah ne ya Umarcemu da mu yi zumunci kuma mu rike zumunci wlh wutar Allah zataji wanda bai rike zumunci bai kuma taimaki zumunci ba"
Ni dai na baro shashen Inno ina Hawaye yinin ranar a kwance na yi sa ya tadomin wani tsohon ciwo ne daga abunda ya shafi rayuwata ina neman in binne mganar Ishaq,ammh sainaga kamar yanzu ne ma suke neman tadomin da ita Tsausayi yake bama kowa yanzu har Yaya Mariya da a baya take adawa da shi yanzu ta dawo itama tana min mgana komawa gidansa,Harta ko Da goggo itama abunda take fadamin kenan,su Anty Binta da su badariya sun gaji da rokona na koma har sun gaji Zainab ma har gobe bata Hakura ba ni Uban gayyar bana jinsa sai dai gabada'ya ya Nannade dangina da Nadamarsa da kirkinsa,A satin kaf naji kaduna ta fita raina saboda matsawar Inno kan mganar Ishaq,Sai na dai zuwa na zauna a shashenta ita kuma in dai naje sai ta Tsaidani da nasiha da tunasarwanta.
Ranar ma gaban Abba tamin mgana shima kuma ta kallesa tana fadin"Usman kada fa ka zama uban banza. Wajibinka ne ka shiga rayuwar yarinyar nan in bazata koma ma tsohon mijinta ba,to ka bata dama ta fitar da wani mijin zama haka ba shi da wata Fa'ida"
Abba sai yaji nauyi na har ya kasa mgana ni kuma ganin haka sai na tashi na fita sai da na ficen sannan yace"Inno Fa'iza tayi girman da ta san daidai da akasa sin sa.
Bazawar ce sharia'ta bata damar ta zaba ma kanta mijin aure, bazan mata Dole ba Inno ta sha wahalan rayuwa in ta nuna tana son komawar shikenan muna son hakan ammh in bata so Inno bazan iya mata Dole ba"
Inno ta kasa mgana sai ma kai data jinjina kai tana fadin"Duk da haka dai mace ce tana karkacewa. ka tunasar da ita tare da nuniya"
Sai ya tabbatar mata da cewa in sha Allahu zai yi min mgana da haka suka rabu shi kuma bai min mganar ba. balle Ammi da yasan bata son ma mganar Ishaq sai ya bar abun a ransa ammh har ga Allah mganganun Inno sun sakashi Tunani da Ganin cewa abunda ta fada din gaskiya ne.
Ni ko na tsorata bana so Abba yace na koma domin bazan iya masa musu ba sai dai har a cikin raina bana sha'awan aure a wannan Lokacin. ballatana koma ma wanda ya taimaka wajen fitar da aure da jin dadinsa a raina. shiyasa ko Abba ya kirani nake jin Fargaban mganarsa a kaina ammh har lokaci ya tafi Abba bai ce min komai ba sai nima Hankalina ya kwanta sai dai duk wanda yamin mganar komawa gidan Ishaq cewa nake yi ba shi ba auran ma gabadaya bazan yi ba kasuwancina zan cigaba da yi. sai bakin su ya mutu basu kara mgana ba,Inno kuma da ta lura ina gudunta sai tace min"dai na guduna Fa'iza in dai mganar aure ne nayi shuru bazan kara mgana ba,ki rika zuwa muna Hira kina Debemin kewa"
Sai naji kunya ashe har ta gane ina Gudunta,jin haka yasa sai na saki jikina Tunda itama ta daina Damuna da wata mganar aure
*****
Sati uku da gama warkshop din su Abba ranar tun Safe cikin wani yanayi na tashi gabana haka kurum yake ta fadi ranar litini ne ina azumin Lada,har kuma da su Anum mun yi mgana suna Lafiya ba abunda ya same su sai na rika addu'a ina fatan koma me zai sameni ya zama na alheri. Azumin da nayi ya bani wahala saboda na kwanta ban ci abincin dare ba,sannan ban yi sahur ba kuma ranar na hada Turaren Humra na Laila,aikinta ya jima a Hannuna ban hada mata ba,Girki ma na kasa yi.
Kunin tsamiya kawai na Dama nayi mana yam ball,Dakyar na iya yin wanka na sauka wata doguwar riga ta Roba mai ruwan kasa kunin kawai na sha na kasa cin komai haka kawai nake jin bakina ba Dadi da yanayin gabadaya sai na kwashi yam ball din da Pepe chicken din da tun jiya na yisa yau dumamasa kawai nayi zuwa Shashen Inno,tamin barka da shan ruwa muna taba Hira sama sama.
Ina Shashenta har akayi isha'i sai nayi salla na anan kawai na kwanta saman Dardumanta sai ga Ammi ta shigo ta yi ma Inno sannu da gidana tana kallo na kafin tace"Inno fa'i ta fara barci ne..?
Inno tace"anya..?naganta dai yau duk ba kamar yadda na saba ganinta ba. abinci ma bata wani ci ba.Ke Fa'iza Fa'iza."
Sama sama na jita na mike ina Hamma Naci karo da Ammi da sauri nace"Ammi yaushe kika shigo..?
Ammi tace"Yanzu mana. Daman babanku ne ya yo waya Megidansa Engr din nan Inno shi ya kirasa yace ya shigo kaduna yau kuma yana azumi zai samu abincin shan ruwa ya shigo an juma..?sai nace bari na Duba Fa'iza nagani"
Inno tace"To ke Fa'iza kin ji babban bako ne wajem babanki in zaki iya tashi ki sama masa wani abun"
Daman tuni na mike jin wanda ke tafe Engr fa mai girma ne a wajen Abba da su Ammi duk da yanayin jikina,Ammi ta kalleni tana fadin"Naga kin sha wahalan azunin nan Fa'i in bazaki iya ba bari na saka su Hafsah"
Da sauri nace"laa zan iya fa Ammi. gajiyan azumi ne,kawai zai sakeni in na kwanta"
Sai ta jinjina kai tare muka fita da ita,ina tambayanta me zan dafa masa sai tace nayi mai sauki suna tafe yanzu kila shi da Abba ko kuma shi Abba ya rigasa zuwa.
jin haka yasa sai na bar masa sauran kunin Tsamiyar da na Dama da Ragowar yam ball,akwai nama sai na yi masa Ferfesun naman,sai jallop din shikafa colour da kayan lambu ban ko gama ba Abba ya dawo naji yana fad'ama Ammi a falo Engr na hanya zai kariso yanzu sai nayi hanzarin karisawa na had'a komai zuwa falon Abba yana ta sakamin albarka.
Falon Ammi na koma wajen su Hafsatu suna ta aikin makaranta suna Hira sai na koma na lafe kan kujera muna zaune da yake falon Ammi na ta wajen Haraban parking space ne. sai muka ji karan shigowar mota Nana Khadija,ta mike ta Daga labulen Window ina daga kwancen nima sai da na mike na leka kamar an tadani Tsaye wata bakar BMW,ta shigo cikin parking space din gidan Abba.
An dad'e kafin Abba ya fito daga cikin gida ya bude kofar baya kafa ce ta fara fitowa Fara cikin Takalmi baki rufaffe na fatar Damisa,kafin kansa ya fito gabadaya ni ban ga fuskarsa ba. saboda Abba ya karesa naga dai dogo ne har yafi Abba Tsayi sannan sanye yake da Suit masu ruwan toka.
Baya nayi na koma inda na tashi. ina jin Nana Khadija na fadin"Engr ne fa megidan Abba."
Sunan kawai yau da Nana Khadija ta ambata sai da gabana ya fadi ras!
Abunda bai taba faruwa dani ba. tunda nasan Abba nake jin sunan Engr a bakin su, amnh yau kawai sai naji sunansa ya tafi da Faduwar gaba na.
*Janafty*
[7/28, 11:26 AM] U.M Collection ZMFR CM: *KNKB3010*
*TASTED & TRUSTED*
*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATUN SAIWOWIN MUTANAN CHADI DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZAR AMARE, MASU JEGO DA WADDA TAKE SON GYARA KANTA*.
*AN GWADA ANGA INGANCINSA SHIYASA NA KE TALLATA MUKU DA K'ARFIN GUIWATA*.
*ABIN BIRGEWA DA WANNAN SAIWOWINRL ZAKI YI AMFANI DA SU SAMA DA SAU DAYA.*
*AKWAI FULL PACKAGE, AKWAI RABI, TA YADDA KOWA ZAI IYA SIYA*.
*SANNAN BABU BAURI NA TASHIN HANKALI.*
*DA KANKI ZAKI DAFA ABAR KI, KOMAI ANA SAKA WA A CIKI*.
*SHIN KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR, KO KUWA KE CE KIKE SON GYARA KANKI?*.
*KAYANA NATURAL NE DOMIN SAIWOWI NE DA AKE HAKOSU A DAJIKAN CHADI. BAYAN SAUKAR DA GAMSUWA HAR YAQI SUKE YI DA DRYNESS DA KUMA INFECTIONS.*
*AKWAI NA TSUGGUNO DA YAKE HA'DE MACE TA MATSE.*
*AKWAI HADADDUN DAKA NA SHA DA MADARA KO NONO WANDA BABU ALGUS*.
*SANNAN AKWIA GADALIN MATA NA ASALI, WANDA SHA YANZU NE MAGANIN YANZU DA IKON ALLAH*
*DUKKANSU TESTED & TRUSTED NE*.
*TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU*
*08032773332*
*DOMIN KARIN BAYANI, SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*.
*NATION WIDE DELIVERY*
*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*
*09069067488*
Duk wanda yasan Abba yasan waye Engr duk da ban san ko cikakken sunansa ba nadai san yana da babban matsayi a wajen Abba,da Ahalinsa gabadaya.
Ban san komai a kansa ba,illah sanin shine sanadin Samun aikin Abba. kuma megida yake garesa, yana gabansa da babban matsayi a wajen aikin su.
Sannan sun zauna makota ka da kakaninsa na bangaran uwa da su Ammi,tunda Ammi daman diyar yayan Inno ne Baffa yake ga Abba Allah ya yi mai rasuwa tun Abdul'ahad na karami. kafin a haifi su Nana Fadila bayan wannan bazan iya Dora komai a kan sunan da naji yau kadai an kira yasakani fad'uwar gaba ba.
Daman kuma bana cikin yanayi mai Dadi sai kuma abun ya sake rikicewa har wani sanyi sanyi naji yana shiga kashina sai na kara lafewa saman kujeran in ba ka duba dakyau ba bazaka ma lura dani ba.
Ina jin mganganun su Hafsah na kasa tashi ballatana nayi mgana Daga baya sai naji kamar suna hawa min kai ma hirar tasu na yanke shawaran tashi na shiga ciki ne,sai ga Ammi ta shigo Falon Cikin mayafinta daga gani Daga Falon Abba take cikin fara'arta data karu na lokacin tace"Kuzo falon Abban ku ku gaida Engr.
Ina Fa'i..?ko ta kwanta ne..?
Ina jin ta ambaci sunana sai na yi kamar ina barci haka kurum naji ko tashi ma bana son yi Nana khadija ne ta Dago tana kallona ganin idanuwana a rufe yasa tace"Ina ga tayi barci Ammi"
Sai ta juya tana fadin"ok ku kyaleta tunda tayi barci daman tun dazu naga kamar bata jin dadi"
Hafsatu tace"Ammi bari mu karisa assigment din mu"
Ammi ta wuce tana fadin"Ku bari ku gama shima yana cin abinci ne"
Da toh suka amsa mata ta fice ta bar Falon,ina jin fitar ta su kuma suka cigaba da hirarsu kan abunda ya shafi karatunsu kara lafewa nayi zuciyata na tsalle waje daya kamar zata faso kirjina ta fito na kasa gane meke damuna,ammh ina ji ajikina wani abu zai faru dani ko mai kyau ko mara kyau,tun ina karyan barci har ban san Lokacin da na gasken ya yi awon gaba dani ba.
Sai farkawa nayi na ganni ni kad'ai a falo ba su hafsatu sai tarin littafansu dakyar kasala ta sakeni na mike ina Dafa kaina nayi Daki ina sauke Tawagayen ajiyar zuciya ina jin Hiran Abba a falonsa kenan har zuwa Lokacin bakon na Abba bai tafi ba.
Achan Falon Abba kuwa su Nana khadija da Hafsatu na zuwa gaishe da Engr yana zaune a saman kujera bayan ya gama cin abinci Abba na gefensa suna hira suka shigo suka Durkusa cikin Ladabi suka gaishe shi
ya amsa cikin Fara'a yana tambayan su sunayensu suka fad'amai sai ya tambayesu matakin karatu shima suka fadamai sai ya jinjina kansa Lokaci daya yana fadin"That very good. Allah ya bada sa'a a maida Hankali da karatu ban da wasa kun ji ko..?suka amsa mai da toh duk a Lokaci daya har sun yi musu sallama sun tashi zasu tafi Engr ya kalli Abba yana fadin"Baka nuna min wacce ta rika dawainiya damu ba Karaye,ina so nayi mata godiya"
Abba na mirmishi yace"FA'IZAA.."
Bata cikin su wadanan ai kannenta ne "
Sunan kawai da Abba ya ambata sai da yaji gabansa ya fadi a saman labbansa ya maimaita sunan da "FAA'IZAA.."
shi kadai kawai ya murmusa kafin yace"Nice name.."
Kafin ma hankalinsa ya dawo su Nana khadija sun fice ba Dabi'arsa ba ne yawan tambaya ammh sai ya samu kansa da kallon Abba yana fadin"To ita ta na ina..?
Abba yace"Bansani ba kila ko ta kwanta ne,kuma ita ma tayi maka kayan bude baki da yake itama ma'abociya azumin litini da Alhamis ne. in naga tana azumi kai kawai kake fadomin a rai Engr'"
Kansa na kasa yana Duba wani sako da aka turomai bai dago ba. ammh sai ya samu kansa da son ganin Fa'izar nan da Baban Nana ke yawan mgana a kanta. yasan yar baiwa ce ta karshe ta hada komai a rayuwarta.
Shuru kuma ya biyo bayan mganar Abba shi Engr na duba wayarsa shi kuma Abba ya Dauko tasa ya lalubo Ammi sai gatama ta shigo da Fara'arta sai ya sauke wayar yana Fadin"Ke nake kokarin kira"
Kai tsaye tace"Gani nan na shigo kuna Bukatar wani abu ne..?
Abba yace"A'a Engr ke tambayan Diyarki wai yana son yi mata godiyan Dawainiya"
Ammi na Dariya tace"Haba dai bakomai wani kuma Dawainiya an zama Daya ranka ya Dade"
Tafada tana kallon Engr wanda ke karkad'a kafarsa Daya dake kan Daya bawai girman kai ko reni ba,ya riga ya saba in dai ya zauna sai ya Dora kafa d'aya kan dayan nan ya karkad'a.
Da mirmishi a saman fuskarsa ya dago yana kallon Ammi kafin yace"Duk da haka Maman Nana a kiramin ita na gode mata."
Sai Ammi ta juya tana fadin"Bari to na dubata na gani"
Tafada Lokaci daya tana ficewa falon ta,ta koma sai su hafsatu da ta tambayeni sukace kila na shiga ciki nan dai suka barni sai ta shiga Dakina ta iske har nayi barci kuma har ga Allah nayi barci domin ina shiga kaya kawai na sauya na kwanta.
Tana ganin nayi barci sai ta koma Falon Abba tana fadin"Engr ta yi barci Fa'izan"
Kai tsaye yace"Is ok..ma gaisa wani Lokacin"
Har Ammi zata fita ta barsu su yi hira tunda daman sun gaisa da ya shigo sai ya yi gyaran murya ta juyo cikin yanayin mganarsa yace"Ammh yaran ku ba duka sun yi aure ba..?in ban manta ba,Baban Nana ka fad'amin Autan ka kadai ta rage ko..?
Abba na mirmishi yace"Yes mun taba mganar dakai"
Ya fad'a yana kallon Ammi itama Mirmishi tayi kafin tace"Oh Na gane. yan mata biyu da suka zo suka gaisheka Doguwar ciki ita ce Hafsatu diyar kanwar Baban Nana ce mai rasuwa, d'ayar kuma Nana khadija itace Auta mu"
Kai ya jinjina kafin yace"Good. Allah ya raya su"
Suka amsa mai da Ameen Ammi ce ta fara tambayan sa ya gida ya su Hajiya yace duk suna lafiya.
Ammi tace"Ya jikin kakan naka ta warware ko..?
Kafada ya zakuda kafin yace"She is fine now, tana Benue granny ai akwai rigima taki zaman Abuja"
Ammi na yar dariya tace"Nagani fa haka tsofaffin suke Allah dai ya kara tsawon rai"
Ya amsa da Ameen Hajiya Tafeesu ta tambayeshi yace sai jibi kila zai sauka ta kano kafin ya wuce Abuja ya Dubata ta,sun yi hira da Ammi kan itama Rigiman Hajiya Tafeesu na Tsufa,Abba na taya su da dariya tun da zuwan nasa ma na rigiman nata ne na sai an kawo mata D'anta Bukar. kuma fa ya rasu ammh duk sanda abunta ya tashi sai tayi sati tana kuka tana kiran sunansa.
Ya jima a gidan sai wajen goma ya tafi bayan ya shiga ya gaida Inno dubu ashirin ya zube mata tace ya Dawo ya Dauka yana duke gabanta yace"Haba Hajiya in Baban Nana ya yi miki alheri kina cewa ya dawo ya Dauka..?
Sai bakin Inno ya mutu ta bisa da saka albarka Ammi ma kudi ya zube mata ita da yara Sai dai bai ce ga na Fa'iza ba aran Ammi nata tunanin ko ya manta sanin Halinsa mai Hannun Alheri.
Abba har bakin bakar motarsa ya rakasa inda Direbansa ke jiransa wannan karon tafiyar mota ya yi Daga Abuja yake shiyasa wani aikin gaggawa ne ya dawo da shi ,sun yi sallama ya wuce Abba ya Dawo cikin gida Ammi ta taresa da fadin"Baban Nana nace Engr ya manta da Fa'iza ne..? Naga bai bar mata nata Sakon ba.."
Abba sai ya kalli Ammi kafin yace"Sakon me..?
Sai da ya fad'a ya gane manufarta kai ya girgiza kafin yace"Allah ya shirya ki Maman nana,abun bin bashi ne"
Dariya tayi batace komai ba.
Bansan duk wainar da suka toya ba sai da Safe Ammi ke fad:amin Engr yaso ya ganni yamin godiya na yi barci da wuri cikin mganata nace"Wlh Ammi kaina ne jiya ya yi ta ciwo shiyasa na kwanta da wuri"
Ammi tace"Ayya sannu.in bai yi sauki ba sai muje asibiti"
Da haka muka rufe hiran bayan Ammi ta bani labarin kudin da Engr ya bata na tayata godiya,Ammi macece dake son kayi mata kyauta komai kankantarta tana jin dadin haka Nana Fatima ta fadamin sannan nima zama na da ita yasa na Fahimci wasu hallayan nata.
Panadol na sha sai ciwon kan ya fad'a ranar na yini ina harkokina har kasuwa naje siyo kamshin Turare saboda zan hada ma wata kawar Ammi,tare da na Nana Fatima tace min nata ya kare zan hada mata,za'a saka a mota a kai mata,da na dawo sai na hada Humra na itacen kuma na bari sai zuwa da Safe zan gama hadasa.
Maganriba ma Dakin Inno na yi shi su Hafsatu daga makaranta suna gidan Raliya,sun je ganin Walid,na idar da salla kenan bayan na gama azkar na Dauki wayata ina Dubawa,Sai ga kiran Abba mamaki ya kamani sai kuma nayi tunanin kila bai samu wayar Ammi ba ne sai na daga kiran bayan mun gaisa Abba yace"Ya ciwon kan..?ya fada kuwa.?
Kai tsaye nace"Eh Abba na warware yau har kasuwa na shiga"
Dagachan bangaran yace"Masha Allah Allah ya kara sauki..Daman Engr ne ya kirani ya roki alfarman Dinner sai gobe zai wuce kano, na kira maman taku ban sameta ba shiyasa na kiraki"
Da sauri nace"bari na tashi Abba daman Doya da miya muka yi da rana,kuma ta kare bari sai a dora da shi"
Abba yace"Shikenan Allah ya yi miki albarka after isha'i yace zai shigo"
Da haka muka rabu da Abba,na mike da sauri ina fadama Inno sai tace nayi hanzari,sai da na Shiga Bedroom din Ammi na fadamata washe baki tayi tana Fadin"To maza hanzarta"
Kitchen na fad'a kamar na sani daman da rana nayi nikan Ayan zan yi kunin aya sai nayi amfani da shi yanzu,Na fara tunanin abunda zan dafa masa,kawai sai nace bari nayi Cousscouss da Souces din kwai,da yaji albasa,Ban yi fruit salat ba,sai da na yayyaka lemu da abarba da apple sai kankana,Nama kuma daman muna da Soyayyen Nama sai nayi dubara na yi masa pepe yaji kayan kamshi Gabadaya nayi na gidan. Inno Daman bata cika cin wannan cimar ba kunu na Dama mata da rana shi take sha har Dare tayi Farau Farau,dashi ta sha ta kwanta.
Ina gamawa na hada na su Abba na kai falon shi,namu kuma na barsa a kitchen tunda su Hafsah basa gida Ammi kuma sai Dare ya raba take cin abinci ni kuma daman in na sha su kankana ko Fruit salt shikenan ya isheni.
Wanka nayi na saka Riga da wando na barci masu taushi,Sabbi ne Ammi ta siyamin su da muka shiga kasuwa,Na fesa turare na zura Hijabi na tada sallah,bayan na idar ina azkar Zainab ta kirani bayan mun gaisa nace ina Takwarata ta karamin ita tana min gwaranci.
Mun dan taba Hira da ita kan yaran ne nace ina suke tace suna falo tare da Babansu ambaton sa ma da tayi yasa gabana sai da ya fadi,sai nayi shuru jin haka yasa ta samu damar ce min"Maman Amir muna ta biko dai don Allah"
Mirmishi kawai nayi ban yi mgana ba,tacigaba da fadin"Honey na son ki Maman Amir kin sani nima na sani"
Da sauri nace"Yaushe kika sani..?
Daga baya kenan ya fara so na..?
Zainab tace"ko a bayan yana sonki Maman Amir bai bayyana ba ne sai yanzu. Wlh baki ga yadda yaran nan suka koma ba ba sa jin dadi baki nan. shi kan shi duk ya rame damuwa ta masa yawa jininsa ya hau fa wanchan Satin asibiti ya yini ana karamai ruwa"
Kai tsaye nace"Nima ai ya sakamin hawan jini da karancin shekaruna Zainab"
Sai ta marairaice tana fadin"Baki mantuwa..?don Allah ki yi hakuri ki dawo wlh ya yi nadama ki zo mu zauna tare kamar yadda muka saba a farko Har Mama abun na Damunta tace min kunyarki take ji bazata iya miki mgana ba ne"
Sai kawai nayi dariya ban ce komai ba ta cigaba da masa kamfe tana fadamin yadda Ishaq ya sauya duk da tasan an batamin daga farko ammh na yafe don Allah na kara basu wata damar kowa yana so na dawo na duba yaran nan saboda Farincikin su.
Sai naji ta fara jan ra'ayina da mganganunta ga kuma daman mganar Inno sai wata zuciya ta fara rinjayata kan sa. Sai nace mata ta bari zan yi tunani cikin wani yanayi murna tace"da gaske Maman Amir..?zaki dawo..?
Cikin yar dariya nace"Kila ina saka ran haka"
ihun data min yasa nayi saurin kashe wayata ina Dariya sai ga hawaye ina tuna mganarta da tace wai Abba ya sauko yan'uwa kuma sun ce matsalan daga wajena ne in na amince kowa bai da matsala.
Ji nayi araina zan iya bama Ishaq dama ko saboda ya'yana na Tabbata ya Hori sannan daga shi har Mama da Anty Binta baza su kara yi min abunda suka min daga farko ba domin Dan zaki ya riga ya girma.
Kiran sallar isha'i yasa na watsar da wannan Tunanin nayi salla ko azkar ban yi ba nace nayi in na tashi kwanciya sai dai a raina ina ta addu''a na kudurta nan da kwana uku zan yi istikara in Allah ya nuna min komawata ga Ishaq alheri ne zan basa wani Dama,in kuma ba Alheri bane Allah ya zabamin mafi alheri a rayuwata ba domin aure na raina ba har abada sai dai darajan ya'ya kawai.
Ban son tunani ya addabeni sai na Kira Nana Fatima muna mgana da ita,ban ma san Bakon Abba da shi kan shi Abba sun shigo gidan ba, sai da Nana Khadija ta leko tana fadin naje Abba na kirana afalo.
Sai na kashe wayar nace mata zan kara kiranta in na dawo.
Hijabin sallah na saka Kato,har kasa Fuskata kadahan kadaran ko kwalli ban saka ba,baki duk ya bushe haka na fita zuwa falon Abba sam na manta da Abba na da bako kai na Tsaye na zurma ciki da sallama cikin yanayin muryata.
Abba baya Falon sai wani mutum Dake zaune a kasan cafet ga kololin abincin nan alamun anci an gama da su,ya tamkwashe kafa ne kafarsa sanye da bakar safa,Sanye da wani yadi mai ruwan kasa shara shara domin har Farar vest dinsa ana gani kansa na sunkuye yana Danna wayarsa,kansa cikin hula mai ruwan kasa na zanna bukar hannunsa Sanye da bakin agogon rado na fata baki,ban ga fuskarsa ba sosai,tunda ya duke kuma kamar da alamu bai ji sallamata ba waige na farayi ganin Abba baya falon,har zan juya sai na ga bai kamata ba sai na kara yin sallama da Sanyin muryata.
Hankalinsa na kan abunda Engr Bala ya turo masa yaji wata murya cikin sanyi da gardi tayi sallama,bai san sanda ya Dago da sauri ba
Daidai Lokacin da nima na dago Sai ga shi mun Hada ido Hudu da shi.
Dam!
Ras!
Gabana ya fadi ashe tare da nashi ya amsa,ni kunya ce ta kamani ganin wani Kamilalliyar fuska mai cike da Haiba da kwarjini,kuma kallon namiji baya cikin Dabi'ata sai na Sadda kai na kasa shi ko tunda ga sama har kasa yake kallona acikin ransa yana mamakin wacece wannan.?
Yana Shirin mgana Abba ya fito Daga Bedroom dinsa yana Fadin"Engr na bar..!
Bai karisa ba ya ganni Tsaye sai ya saki mganar yana Fadin"A'ah Fa'i yaushe kika shigo..?
Ni ko a raina nace au wannan ne Engr..?
Sai na kara satan kallonsa a raina ina fadin ashe ma ba tsoho ba ne.
Kasa na duka daga inda nake tsaye ina Fadin"Abba ina yini..?
Ina yini..?
Na fada ina kallon kasa Abba kadai ya amsa yana zama gefen bakonsa kafin yace"Engr ne yace a kiraki ku gaisa jiya yazo kin kwanta.
Engr meet my Fav.Dota Fa'iza itace mai wad'anan Girke girken masu dadi da kake ci kana yabawa.."
Kyar idonsa da kallonsa a kaina daman ya yi tunanin haka ya yi Tunanin FA'IZAA ce!
Ni ko kaina na kasa ina kallon kwalliyar Cafet din falon Abba.
Abba da bai ji na gaishesa ba sai ya kalleni yana Fadin"Fa'i ga Engr da kike jin Labarinsa ki gaishesa"
Sai alokacin na Dago karaf ko muka kara Had:a ido cikin yanayin mgana ta nace"Ina yini..?
Ya aiki..?
Cikin Muryansa mai laushi yace"Lafiya lau Faa'izaaa.."
Yadda yaja sunan sai da na kallesa sai kawai ya kasheni da wani mirmishi mai Tsada da ya tsayamin arai,kafafuwana naji sun fara sanyi ban san ma'anar wannan kallon ba. ammh Tabbas kallon ya shiga jikina ya fara kassarani domin ya kasa Dauke idonsa a kaina
Cikin mganarsa d'aya bayan Daya yace"Sannu da kokari Fa'izaa. Mungode sosai Allah ya biya ki da aljannah"
Kasa kasa na amsa da Ameen,Ina shirin mikewa naji Abba na ce masa"Ai Fa'i yar baiwa ce ga girke girke sannan tana sana'ar saida kunin aya da zobo,Turaren kamshin nan duk aikin ta ne ba abunda bata iya ba"
Naji dai yana mgana banji me yace ba Saboda nayi musu sallama na fice kuma har alokacin naji idanuwam Engr a kaina.
Jikina da Dumi na kai Dakina haka kurum nake ji kamar zafin zazzabi ya Rufeni. sai na samu gefen gado na zauna ina maida numfashi kamar wace tayi wasan tsere,wlh a cikin jikina nake jin mirmishim Engr nayi min yawo yam!
Yam!kamar wacce aka yi ma asiri. Haka nake ganin Fuskarsa acikin Idanuwana kai na Dafe da Sauri ina Fadin"Wai meke shirin faruwa da ni ne ni Fa'iza?
Kiran wayata da Nana Fatima ta yi shi ya fitar dani acikin Halin da na fad'a,ammh ita kanta da muka fara mgana taga bana cikin natsuwata sai da tace"Lafiya Fa'i?
Sai naji daman ta kira sunana Fa'izaa naji ko ta iya fad'in irin na Engr bakon Abba.?
To wai me ke damuna ne..?
Murya shake nace mata bakomai
******
Achan falon Abba kuwa tun fitan Fa'iza Engr ya rasa natsuwarsa. Abunda yake dubawa a wayarsa ma sai yaji ya daina gane komai da komai Abba na masa hiran aiki shima kwata kwata bai gane me yake fad'a ba. in da Fa'iza ta tashi ya kurama ido cikin yanayin da bai gane ma kansa ba yanzu yanzu nan.
Shi Abba duk bai gane ba,ya cigaba da Hira da Engr,shi kuma ganin ya daina Fahimta yasa ya yi ma Abba sallama da godiya yace zai wuce yana Sauri ne gobe tun safe Kano zai wuce abun ya bama Abba mamaki ko zuwa gaida Inno bai yi ba yace a kyalesa da yace bari ya Kira Ammi su yi sallama sai yace itama ya rabu da ita.
Har ya rakasa bakin mota ya dawo cikin gida hankalinsa ya kasu na abunda ya sauya fara'ar Engr yanzu yanzu Ammi ko da ta shigo ta iske ya tafi cikin mamaki tace"kiran sa akayi hala..?
Abba yace"Ko daya muna hira kawai naga ya sauya, sai kuma yace min zai wuce ban san abunda ya faru ba."
Ammi ta zauna gefensa tana fadin"Topha Allah yasa dai lafiya"
Ya amsa da Ameen.
Abunda basu sani ba shi kanshi bai san meke damunsa ba sai da ya isa inda yayi masauki bayan ya yi wanka ya kwanta barci ya gagara yana da gida a kaduna ammh in dai ba tare da su Sweetheart suka zo ba, baya zama a wannan gidan shi kadai kowa ya san shi mai jama'a ne mai harkokin Rayuwa da yawa ammh yau wayoyin sa ma duka kashe su ya yi baya so a Damesa. abun kamar almara bai Taba jin wata mace ta tsaya masa arai ba tun bayan rasuwar Tauhidat,yasani ba auran soyayya ya yi da ita ba rigiman Granny ce ta hada shi da ita,ya ga mata kala kala yare yare dabam dabam na'i dabam dabam tsayin shekaru ashirin da wani abu bai taba ganin macen da ta hanashi Sukuni irin Faa'izaa ba..!
Da ya runtse ido domin yayi barci ita yake gani,Dakyar a Daddafe ya kai asuba ko da ya tashi ya tabbatar ma kansa Fa'iza ce ta hana shi sukuni abunda bai faru da shi da kananun shekarunsa ba ne yanzu da girma ya kamasa zai faru da shi. bai son So ba amnh ko kaffara bazai yi ba SON Faa'iza ya kamasa daga kallon Farko da ya yi mata.
Ko wanka bai tsaya ya yi ba, ya taso Direbansa daga shi sai farar Jallabiya da Dogon bakin wando ya nufi gidan Abba karfe shidda da yan mintina na safe.
Abba ya dawo masallaci kenan sun gama waya da Abdul'ahad sai ga kiran Engr,domin jiyan ma yayi ta kiransa bayan ya tafi wayarsa a kashe.
Ya dauka da kwarin gwiwarsa sai yaji ya Rude jin yace masa yana haraban gidan shi Abba ya mike yana Fadin"Cikin gidana dai..?
Yafada cikin mamaki Ammi da ta fito daga cikin bedroom Da hijabinta na sallah taga Abba ya Sauke waya cikin mamaki da sauri tace"Baban Nana lafiya..?
Kai tsaye yace"Wai yanzu Engr ya kirani yace yana Haraban gidan nan yana son ganina"
Ammi ta zaro ido kafin tace"Yanzu..?
Kawai sai Abba ya wuce bai mata mgana Ammi kuma sai ta fara Tunanin anya lafiya..?
Abba dai bai kara shiga Rudani ba sai da ya fita yaga Engr da Jallabiya da takalmin wanka. ya firgita yana mika masa hannu ma su yi musabaha Engr bai karbesa ba, cikin wani yanayi da bai taba ganinsa aciki ba. ga idanuwansa sun yi ja alamun bai samu barci ba.
Cikin dishewar murya Engr yace"FA'IZAA tana da aure ne..?
Kai tsaye mganar tazo masa domin bayan ya Fahimci abunda ke faruwa da shi, zullumin ko matar aure ne yasa jininsa ke barazanan hayewa sama bai sani ba gwara ya farajin Tabbaci sannan.
Abba ya kallesa yana mamakin kalamansa shi fa har mantawa yake yi da Engr ya hada jini da yarbawa Saboda komai na sa na Hausawa ne hatta Dabi'unsa,ammh yau sai yaga kamar ya juyo masa yau ya fito a bayarben nasa shiyasa ma cikin mamaki yace"Wata Fa'izan kuma Ranka ya Dade?
Engr ya sauke lumsassun idanuwansa kafin yace"Fa'izaa dai..Ur Daughter."
Sai Abba ya ware ido kafin yace"A'a bata da aure wani abu ne ya faru..?
Yana jin sanda Engr ya sauke karfaffan ajiyan zuciya mai karfin da sai da ya kara kallon sa daga sama har kasa cikin Dafe kirjinsa saitin zuciyarsa yace"Alhamdulillah..!
Mu shiga ciki mu karisa mganar"
Abba kamar gaula haka ya bisa ammh yana tunanin to lafiya..?Me ya hada Engr da tambayan Fa'iza nada aure ko a'a..?
Wata zuciyar ta hasaso masa Dalili a razane ya kallesa lokacin sun shiga Falonsa yana shirin mgana kawai yaga ya zube a kasa yana fadin"Ina kwana Abba"
Abba ga mamaki ga Dariya cikin Dauriya yace"Ranka ya Dad'e..Ni ne fa Baban Nana sai na koma kuma Abba.."
Engr na shafa kansa yace"Ka zama Abba daga yau tunda zaka bani auran y'arka"
Abba ya zaro ido cikin mamaki kafin yace"Y'ata wata y'ar tawa..?
Kai Tsaye Engr yace"FAA'IZAA.."
FAaa'izaa zaka bani Abba. I love her ganin Farko da nayi mata jiya, daga dare zuwa Safe na Fahimci ina sonta kuma auran ta zan yi, ni ba yaro ba ne kai ma haka bazan zo na zauna ina maka wasa ko karamar mgana ba, duk abunda nace maka i mean it form my Heart.
Ya fada yana Dafe saitin zuciyarsa,Abba kamar ya kwashe da Dariya mutane suna kallonsa yana da barkwanci ammh yasan in da sun zauna da Engr sai sun san shi a barkwanci bai iya komai ba.
Mutum ne free ba ruwansa mgana fadinta yake daya bayan d'aya a muhallinta.
Ganin Abba ya tsaya yana kallonsa yasa ya gyara zama yana Fadin"Abba da gaske nake ina son Fa'iza.
Zaka iya bama tsoho kamata auranta..?
Abba ya bude baki ya rufe yafi a kirga,Zama ma Dakyar ya iya yi saboda mamakin wannan al'amarin
Ganin haka yasa Engr yace"Kana mamaki ko..?
Ka daina mamaki nima jiya haka na kwana mamaki ammh daga baya sai na Fahimci Hadin Allah ne shi ne mai Tsara abunda yaaso alokacin da yaso kuma ya faru a sanda yaso"
Abba ya jinjina kai kafin yace"Hakane. Sai dai ka sani Fa'iza ba D'iyata ta cikina ba ne..D'iyar kanwata ce mai rasuwa da muka taba zencen ka da ita ta garin mu Karofi"
Engr ya gyara zama kafin yace"Allah Sarki Allah ya jikanta na tuna wacce kace baka san kana da kanwa ba sai daga baya..?
Abba ya gyada kai yana fadin"Mganar gaskiya Fa'iza auranta shari'a ita ya bama wannan damar, sannan ta rabu da mijinta ba domin shi baya sonta ba sai kaddara"
Engr ya yi karaf yace"Kaddaran aure na ne Abba.."
Shima sai ya mayar masa da cewa"Ya'yanta Hudu fa Engr"
Shima cikin kwarin gwiwa yace"Masha Allah daman dagani sai su Taye Sweatheart Ta haifa. Ka fara fada musu ma sun samu wani Baban din bayan na su Baban"
Abba ya murmusa sanin Halin Engr kafin yace"Fa'iza ba tayi boko ba fa Engr.."
Shima mirmishin yayi kafin yace"A na addini a ina ta tsaya..?
Abba yace"ta wannan fannin Mahaddaciya ce sannan ta sauke wasu littafan"
Cikin Annushuwa yace"Good. Karatun boko! da nake da shi ya ishemu ni da ita har gaban Abada"
Sai Abba ya kasa mgana Abba yasan waye Engr da naci kan abunda yake so.
Shima kuma yasan ya san shi din Shiyasa ya yi mirmishin nasara kafin yace"Ka gama min gwajin tambayoyin..?zaka iya bani amanar rayuwar Yarka Fa'iza..?
Abba ya girgiza kai kafin yace"Fa'iza ba kamar ko wacce mace ba ce,Tana da lalura.."
Sai ya kalli Engr ya tsaya yaga yadda zai yi sai yaga yace"Lalura ai ta Allah ce Abba ko da lalura ko ba lalura ni Fa'izar nake so,kaga kenan da duk abunda ya danganceta ina son shi"
Abba ya karbe da fadin"ko da laluran kurmanta ne..? Bata iya jin mgana sai an yi mata da karfi."
Da sauri Engr yace"Alhamdulillah naji dadin haka. daman ni kadai ya Dace tarika jin muryata saboda ina da kishi kan abunda nake so"
Jaruntar Engr sai ta bama Abba Dariya sai ya kanne kafin yace"Fa'iza ba yar kowa ba ce bata da komai bata ijiye ba kuma bata bama wani ajiya ba. Ba yar kwalliya bace ba yar kyale kyalen yanmatan zamani ba ne,Ba ta da wayewar yan matan zamani balle ka yi tunanin samun soyayyar da kake Fata Engr Fa'iza yar zuhuda ce duniya da abunda ke cikinta baya gabanta ba lalle ka iya zama da ita ba,kuma Fa'iza ba fara ba ce sannan bata cikin Sahun manyan mata kyawawa burin kowani namiji"
Engr ya kura ma Abba ido har sai da ya tsargu kafin ya yi mirmishi yace"Na dauka kafi kowa sanin irin zab'ina. Kyau ko fata bai taba zama Dalilina ba."
Engr zai cigaba da mgana Abba ya taresa da fadin"bazan taba ma Fa'iza dole ba Engr ammh ina ganin kai ba sa'an auranta ba ne.."
Sai mganar ma ta basa dariya ya yi mirmishi kafin yace"Tafi karfina ko..?
Abba yace"Kai ne kafi karfinta.."
Sai kawai ya mike ya hau kan kujera ya zauna yana fadin"Naji dadi da ba ita bace ta fi karfina ba. in har ka aminta dani zan shiga layin zawaran Fa'izaa..'"
Abba ya saki baki kafin yace"Engr.."
Hannu ya dagamai kafin yace" *ENGR.ABDULBASIT ABDULGHAFFAR OLOWATOSIN..*"
Lokaci daya yana Dora kafa d'aya kan d'aya yana girgizawa.
Abba sai kwarjinin Engr ya dakesa ya kasa mgana kai Tsaye yacigaba da fadin"Engr Usman Karaye ka amince na shiga layin bazawaran Fa'iza..?
Abba sai kawai yayi kayattacen mirmishi mirmishin hango Salama da aminci in har Fa'iza ta samu miji kamar Engr.
Batare da fargaban da yaso yayi tasiri a ransa da farko ba yace"Na amince"
Cikin karfin gwiwan da yakinin cewa Engr zai karkato hankalin Fa'iza garesa.
Yana wannan tunanin ya tsinkayesa yana fadin"Ayi min mgana da ita,Daga yau zan fara zaawarci na"
*Janafty*
[7/29, 10:07 AM] U.M Collection ZMFR CM: *KNKB3011*
*Goron Tula*
*Ingantaccen maganine dake saukarda niimar mace sannan dadin dadawa fruit ne ga dadi abaki zakine dashi chakwai sannan bashi da wata illa yadda kikasan fruit haka yake*
*yana da matukar kyau da tasiri ga ma aurata daga mace harna mijin Kuma munada Syrup nasa da akataceshi sannan aka hada da ingantattun magunguna dasuke temakawa ma aurata kwarai don inganta lafiyarsu dakuma maganin matsalarsu ta auratayya yana saukar da niima sosai yana karawa mace dadi fiye dazatanku sai kingwada zak ibada labari insha Allah*
*Sannan akwai zumar kiba*
*Duk macen dake son ta murmure tayi kyau taciko tatada komad'a sosai shaf dinta yafito sosai da sosai to tasha wannan zumar insha Allah zaki gode min*
*Zumar gyara nono*
*Zasu yi kyau suciko ammanfa bawai su tsaya ba😄 zadai suciko suyi kyau sosai insha Allah*
*Zumar hips*
*Indai kinsha zumar nan to hips dinki zai bude zasu yi kyau suciko sosai zaki godemin nina fadamiki insha Allah*
*Note magungunan mu ingantattune basu da side effects kokad'an anyisu da ingantattun*
*magunguna sosai*
*Location Gombe munaturawa ko ina 08030861857*
*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*
*09069067488*
ABBA.."
yaji muryan Engr ya kira sunansa cikin taushin murya. ya riga ya yi nisa cikin Tunaninsa yana juyowa yaci karo da Engr gurfane a gabansa ya sadda kai kamar me neman gafara cikin mamaki yace"Engr..!"
Kallonsa yayi kafin ya yi mgana ya cigaba da fadin"Haba ranka ya Dad'e.."
"ABDULBASIT.."
Eh ka kirani da sunana Abdulbasit Abba ni ai surukin ka ne,nema nake a wajen ka y'arka zaka auramin fa"
Yafad'a har yana sosa kai alamun kunya Abba baisan sanda kyattacen mirmishi ya kubce masa ba.
Duk da bai san Engr tun yana matashinsa ba. ammh yasan shi Lokaci mai tsawo shine zai iya ba da Labari da shedar nagartan sa.
Yana kallonsa zuciyarsa na bud'ewa da wani farinciki yana kuma fatan Fa'iza ta karbi tayin Engr.
Mganarsa ne ta katsesa cikin gyara zama yana fadin"Nagode Abba na yi maka alkawarin in sha Allahu bazaka yi nadaman bani amanar Faa'izaa ba.."
Zan rike maka ita amana bisa gaskiya da aldalci"
Abba ya murmusa kafin yace"Na fad'a maka tun farko bani da Hurumin yi ma Fa'iza zabi duk da ina matsayin Uba gareta, bazawara ce Shari'a ta bata Damar yi ma kanta wani zabin a karo na biyu"
Ya fad'a yana dan dakatawa yana nazarin fuskar Engr da tayi wani haske da Haiba,wanda yaga ya karu na yau kada'i.
Maimakon yaga sarewa a tare da shi sai yaga Jarumta da Kwarin gwiwa daman ya sani Engr ba shi da Tsoro ko Fargaba. ko karaya kan abunda ya saka ma gaba.
Cikin irin Taushin lazafinsa yace"Ai nima ban ce ka yi mata Dole a kaina ba. Ina son Fa'iza kuma zan nemi soyayyarta ina fatan ta bani Dama har takai mu ga aure, in kuma hakan bai Faru ba ni musulmi ne na yarda da Allah zan rumgumi kaddara a madadin Allah ne bai yi ba."
Yana mgana Abba najin yana kara Burgesa ko daman yasan shi mutum ne mai hankali da Takwalli yana ma Fa'iza fatan samun Engr a matsayin abokin Rayuwa.
Mikewa Abba ya yi yana Fadin"Shikenan bari naje na saka Maman Nana tayi mata mgana."
Da sauri Engr yace"Allah ya saka da alheri Abba"
Abba ya kara kallonsa yaga ya ma gyara zama ne cikin gyaran murya yace"Ammh nake ga da kaje ka shirya ka dawo ko..?lokacin itama an fad'a mata ta shirya..?
Kai tsaye yace"kirawota kawai kaji ni da zamu gina auran gaskiya ina ruwan mu da wani kyale kyale..?
Ya fad'a yana kara tankwashe kafa sai kawai Abba ya girgiza kai ya fice Daga Falon shashen Ammi ya shiga su Hafsah na Falon suna kallo kowacce da Hijabinta alamun bayan sun idar da sallah ne suka fito gabadayan su suka Duka suka gaishe shi ya amsa yana tambayan su yau ba makaranta ne sukace sai 9am zasu tafi.
Bedroom din Ammi ya shiga tana zaune tana duba wasu kayanta da aka karbo wajen dinki,Abba ya shigo daman tana ta zencen zucci na zuwan Engr sai ta mike ta tare shi tana Fadin"Baban Nana lafiya..?ina Engr din..?Abba ya riko hannunta zuwa bakin gado suka zauna yadda taga ya yi ne sai da gabanta ya fadi daman Ammi akwai rudewa cikin Rudanin ta Dafe kirji tace"Ba dai wani abun ne ya faru wajen aikin naku ba Baban ko Nana..?
Mirmishi ya yi kafin yaace"Kwantar da Hankalinki abun alheri ne zan ce ya faru"
Ammi ta sauke ajiyar zuciya kafin tace"Har na samu salama me ke faruwa ne..?ya tafi ne..?
Abba yace"yana nan..Ina Fa'iza..?
Ta tashi.?
Ammi cikin mamaki tace"Eh yanzu ta bar nan tazo mun gaisa ka sakani a duhu meke faruwa ne Baban Nana. ?
Ganin ta fara rud'ewanta ne yasa ya rike hannayenta yana Fadin''Ki natsu mana..Bafa wani abu ba ne Engr ne jiya da yaga Fa'iza.."
"Eh sai yace Fa'izan ta masa me..?
Ammi ta katseshi cikin Firgici har acikin Idanuwanta.
Yanayinta yasa sai da ya yi Dariya kafin yace"Ba abunda yace ta yi masa sai abu d'aya"
Ammi taji wani ras! fad'a da masu gwammati da yarbawa ai bala'i ne Cikin Kara rudewa tace"Mun shiga uku me yace ta yi masa..?
Abba na kanne Dariyan sa yace"To laifin D'iyarki daya da ta sace mai zuciya"
Kyam Ammi ta tsaya da kifta idanuwan da take yi tana auna mganarsa kafin kwakwalwarta ta hasaso mata zencen Abba ai sai ta ware ido kafin tace"Wai kana nufin Yana son Fa'i?
Sai Abba ya jinjina kai yana Fadin"Haka yace"
Nan ya shiga bata Labarin abunda ya faru Tsakaninsa da Engr a falo yanzu ai Ammi bata jira komai ba ta kwace hannunta cikin na Abba ta mike ta rike Hanci ta Rangada kyakyawan guda,Sai da Abba ya saki baki yana kallonta kafin yace"Aziza me ye haka kuma..?
Juyi tayi a gabansa kafin tace"Bar ni nayi gud'a babban gwaska fa Irin Engr yaga d'iyata yana so..ah ban ga ta zama ba kai Allahu akbar,wani Hanin ga Allah baiwa ne sannan KANA NAKA Allah ya riga ya gama nasa Baban Nana kaji Rabo ko..?
Take fad'a bakinta kamar ya tsage tsaki yaja yana kokarin yi mata bayanin yadda suka yi taki Tsayawa ta Fahimta tunda taji Engr na Falo yana Jiran Fa'iza ta fice tana Fadin"Bari naje na sakata ta kimtsa taje ta same sa"
Yana kiranta ammh bata dawo ba sai dai Fadi take yi"Ina zuwa Baban Nana"
Kai kawai ya Dafe a fili ya furta"Yaushe Aziza zata girma ne..?
Bai ga ranar ba, tunda takai ga jika bata Sauya ba,kila sai cuta mai Tsanani da ba'a fata shi kanshi a hakan yake tsananin kaunarta mace ce tagari son kowani namiji mai kima.
Ammi na shewa ta fito falon su Hafsah ganin yanayin ta yasa Nana Khadija tace"Ammi hala Abba ya biya miki Umra ne..?
Ammi na Dariya tace"A'a Abban ku ai ya gama kaini Umara yanzu fanni na Surukai ne. in da rai da rabo bana ai dani za'a keta Hazon hajji ya'yan nan haihuwa mai Dadi"
Take fada tana Dariya sun san Halinta yasa suka saka Dariya Hafsatu na fadin"Ammi mijin Anty Fadila ko Anty Fatima ne zai biya miki..?
Ta wuce tana fadin"Kash kuna da gajen hakuri ku jira mana Lokaci ya gaya muku"
Murnan da take yi ya isa yasa su san wani abu na faruwa. Abba kuma kin fitowa ya yi saboda ya bama Fa'iza daman sakewa kada ya koma ya takura musu yana suruki guda duk da yar kunya Tsakaninsa da Engr ammh ya Lura daga yau da Safe ya sauya mai matsayi da suna daga baban Nana engr ya koma Abba,baban Fa'iza.
*****
Ni ko ban san wainar da ake toyawa ba,Tsakani har ga Allah nima cikin wani yanayi na kwana abun mamaki da Haushi mafarki na yi ta yi masu cike da Engr a cikin su,sannan ko yaya na yi zurfi a tunani sai na hango kamilalliyar Fuskarsa na min mirmishi gabad'aya sai na tashi a jagule na rasa gane kaina Na tambayi kaina Fa'iza daga ganin mutum baki san komai a kansa ba sai Tunanin sa..?
Abunda ban taba yi ba ko zamanin Ishaq wlh tallahi bana zama nayi Tunanin sa to basai da kwanciyar Hankali da so da kauna kake tuna mutum ba..?ba auran soyayyah nayi ba shiyasa ban san kallon so ko mirmishin soyayyah ba,ni bani da sani ta wannan bangaran a bangaran auran ma akwai ta bangaran da ni Fa'zan ban san komai ba.
Na idar da sallar asuba ban d'aga daga kan Darduman ba ina ta azkar dina daman kuma jiya da daddare sai uku na kwanta nayi istikara,sai kuma na ga akasin haka maimakon naji na samu natsuwar Komawa gidan Ishaq a'a sai mafarkan Engr nake yi acikin barcina.
Kuma in bude baki in fad'ama wani wannan iftila'in daya sameni abun kunya ne to abun kunya mana Daga ganin Sarkin fawa ni Fa'iza sai miya taki zaki...? Da hannu bibbiyu nayi Taguni ga Uban Hijabi ga carbi ina ja har bata lissafi nake yi saboda Tsabar Tunani ana ta ma kiran wayata ban ji ba sai daga baya ina Dauka Zainab ce sai dai ba muryanta ba ne na Anum ne na Tsorata ganin bakwai saura.
Cikin tashin hankalin daya bayyana har amuryata nace"Ke Anum lafiya kuwa..?ina Antyn naku..?
Sai naji ta saka Tsalle da Ihu tana Fadi"Eyee Umma wai da gaske zaki Dawo gidan Daada gabadaya ki zauna tare damu da Daada da Anty..?
Sai da gabana ya fadi Zainab ta gama dani daga ce mata zan yi Tunani har ta Yadani na kuma san gabadaya yaran ta fad'a musu har da uban gayyan.
Kafin na bata amsa naji hayaniyan sauran yaran suna ihu suna kiran sunana dakyar na iya tambayanta su Ahmad ne tace min"Eh Umma kowa nata Murna zaki dawo har da Yaya Amir baki ga Daada ba,yace yau zamu fita shopping gabadayan mu zamu gyara miki daki Umma don Allah ki Dawo.."
Miyau na naji ya kafe nama kasa hadiyewa,saboda rudani ni yaushe nace zan dawo..?
Ina jin hayaniyar yara kamar zan kashe wayata ammh Anun taki bari fadi take"Umma don Allah ki dawo kawayen mu fa kowa gidan su Umman su daadan su na waje d'aya sai mu ne Umman mu bata nan,Sannan Umma Daada yace shi ya yi miki laifi mu tayasa bashi hakuri don Allah ki yafe masa.."
Tafada cikin wani yanayin da yasa sai da Hawaye suka kawo cikin Idanuwana,Anum da iya zencen Amir ne daman mara Hayaniya.
Damuna tayi da fadin"Kin ji Umma ki yafe ma Daada don Allah ki dawo"
Sai na samu kaina da fadin"Na yafe masa tuntuni Anum"
Sai ta saka Ihun murna tana fadin"To Umma zaki dawo din.?
Da gaske ne..?
Kasa ba ta amsa nayi ina fadin"Yau ba makaranta ne..?
Da sauri tace"Umma muna shiri ne..Ni ki fad'amin zaki dawo..?
Da kai na daga mata kamar wacce aka zare ma lakka naji jikina ya yi min nauyi kafin nace"Ehh.."
Kamar ashe a amsa kuwwa a ka sakani ina jin ihun yaran gabadaya Da mganar Anum tana fadin"Umma Umma yaushe..?gobe..?
Don Allah ki dawo gobe.?
Kaina na Dafe da naji yana Saramin kafin na samu damar mgana naji sallamar Ammi da shigowarta yadda naga tana hanzari ne yasa na katse wayar na mike da sauri kafin ma nayi mgana tajani gefen gado muka zauna tana Fadin"Fa'i albishirin ki..?
Cikin kallonta nace"Goro Fari kal Ammi"
Tana Dariya tace"Sauya Hijabi kije falon Baban ku ki dawo sai na baki albishir din"
Cikin mamaki na kalleta zan yi mgana ta dora yatsa a bakina tana fadin"Ba yanzu ba sai kin dawo"
Da kanta ta mike ta zabo min wani hijabi sea green cikin kayana Sabo ne ban ko taba sakashi ba.
Ta bani na cire na jikina na saka bayan ta sakani na sauya kayan barcin jikina na saka wata bakar Abaya,ta kuma saka na goga Turaren Humra cikin mamaki nace"Ammi bana son kamshin turare,kuma fita zan yi fa"
Ammi tamin dakuwa tana Fadin"Kuma kike had'awa kina Saida mana amnh ke kice baki so..?ai ko baki isa ba yarinya ba turare yanzu kika fara son shi da saka shi"
Dariya nayi ban yi mgana ba,haka ta sakani gaba muka fita ina tafiya ta shiga gabana tana nuna min wai irin Salon Tafiyar da zan yi in na Shiga Falon Abba baki na bude kafin nace"Ammi waye ya zo wajena..?
Ko baki Abba ya yi.?
Fadin haka yasa sai da gabana ya amsa ko dai ko dai Engr ne..?
Na juya nayi ma Ammi mgana naga Tuni ma ashe ta koma Shashenta ta barni nan tsaye sai na fara waige ina jin wani yam acikin jikina.
Kamar najuya zuwa shahshen Inno daman ban shiga mun gaisa ba da Safe,Sai kuma na kasa bazan iya komawa ba tunda Ammi ce da kanta ammah jikina ya bani wani abu.
To ko dai ishaq ne..?in shi ne kuma da Anun ta fad'amin.."
Ni dai kafafuwana suke ja na zuwa Falon Abba ga yanayin mganata ga Sanyin murya shiyasa da nayi sallama ban sani ba ko yaji,ni kuma sai naji kamar gyaran murya shiyasa na shiga falon kaina na kasa.
Kafafunsa na fara gani zuwa kansa yana tsaye ya juyamin baya yana waya ammh kuma abun mamaki wani yare yake yi kamar yarbanci yarbanci na kasa dai ganewa saboda ina Rude ne.
Dagowa nayi in kallesa dakyau karaf ko kamar juyin waina naga ya juyo muka hada ido hud'u da shi jiri ne yaso ya kwasheni na kame kaina da jikina ammh a wannan karon ma jikina da gabana sai da suka amsa wannan kamilaliyar Fuskar da wannan mirmishin da yaki b'acemin yau ma da su ya jefeni kafin ya yi mgana ashe wayar na makale a kunnensa bai kashe ba naji yana Fadin"Is ok Papa i will call u later"
Daga haka ya katse kiran kacokan kuma ya maida Hankalinsa kaina ni ko ban saba ganin irin wannan kallon ba, kaina na kasa ina rawan jiki Lokaci daya ina faman cikwikwiye hijabina ta gaba.
Ina ga fahintar haka ya yi yasa ya yi mirmishin sa dake dimautani kafin ya matsa yana nuna min saman d'aya daga cikin kujerun falon Abba yana fadin"Barka da shigowa sarauniyar mata Hv a sit.."
Sai kuma daya fada haka yayi yayi sauri gyarawa da fad'in"Ki zauna bismillah"
Yafad'a duka a tare ai da sauri na samu gefen kujera na zauna ina kara Dukar da kaina sai kawai naji yace"Kada mu fara haka dake Fa'izaa kan kujera zaki hau a matsayin ki na Sarauniyar mata,ni kuma na zauna a kasa a gabanki tunda nine zan mika kokon barata."
Da sauri na dago muka hada ido sai na Dirirince zan yi mgana ya yi saurin cewa"Kada ki fara da min gaddama Faa'izaa ni mutun mai son ya yi mgana Daya ajisa. kuma a Sauraresa"
Yafada kai Tsaye cikin taushin murya mamakin kalamansa yasa na dago ina kallonsa kwarjinsa yasa na kasa mai gaddama sanda ya sake nuna min kujera yana fadin"Ga inda ya dace dake nan"
A kunyace na mike na zauna kamar zan yi kashi,saboda yanayin zaman nawa sai ya yi dariya kafin na ankara sai ganinsa nayi a gabana ya zauna har da tankwashe kafa baki na bude ina kallonsa da Sauri yace"To Rufe bakin mana kada ya makale a haka na shiga uku"
Mganarsa ta bani Dariya har sai da na kannen fuskata cikin Hijabi Saboda kunya shima yar Dariyan ya yi kafin kuma yadan ci Serious yace"Da farko dai ni sunana Abdulbasit Abdulghaffar Alowatosin.."
Da sauri na d'ago ina kallonsa in naji dakyau sunan yarbawa naji ya fad'a shi kan shi yasan yanayin kallon nawa kenan yasa yayi dariya kafin yace"Yes ni bayarbe ne mahaifina Haifaffan garin Beneu ne,mahaifiya ce Bahaushiya haifaffiyar garin kano ni ruwa Biyu ne Hausa_Yoruba"
Yafada kai tsaye bai kuma bani Damar mgana ba ya cigaba da fadin"Ni Engr ne ina aiki da matatan mai na Edo state,ni ba yaro ba ne ba Wasa ko bata Lokaci ko Doguwar mgana yasa nace ayi miki mgana ba. jiya ne da kika zo gaisheni na ganki to mganar gaskiya tun daga jiya zuwa yau baki bari zuciyata ta Huta ba Faa'izaa.."
Ya fad'a yana kallona nima abun mamaki shi nake kallo ina auna daman akwai yarbawa masu kyau haka..?Na san maza masu kyau da gayu tunda na zauna da Ishaq ammh sai naga kamar wannan na gabana ya hada wasu abubuwa masu tarin yawan da Ishaq bai da su.
Sai dai tunanani ya tsinke ne da nganarsa na karshe gabana ya fad'i kada dai shima jiya tunani ne ya kamasa kamar yadda ya kamani..?
Sai dai ganin yadda na bada Hankalina a kansa ne ina jin yadda yake kiran sunana na shiga duka sassan jikina FAA'IZAA..!
Gyara zama ya yi yana fadin"Kai tsaye ba tare da kwana kwana ko zagaye zagayen samarin zamani ba, na ganki kuma naji ina son ki Faa'iza kuma so irin na aure"
Ido na waro a firgice kafin nace"Ni..?
Sai ya gyadamin kai kafin yace"Yes..Ko ban kai ki soni ba ne..?nayi miki tsufa ko..?Shekarata arba"in da Biyar kiyi hakuri ban fara Furfura ba, a kai ne kuma bata wuce guda Biyar ba in baki so sai na aske su Faa'iza.."
Dariya ce take neman kamani sai na kanne na juyar da kaina ganin yadda ya marairaicemin a gabana cikin yanayin muryata nace"A'a ko d'aya ai kai ba tsoho ba ne"
Ajiyar rai yayi har ina jin saukanta kafin yace"To mene laifina ne..?ko so na ne kawai ba'ayi..?
Kai na girgiza kafin nace"Ba haka ba ne"
Da Sauri ya katse ni da fadin"To ya ya ne Faa"izaa..?
Yadda ya kiran sunana sai da tsikar jikina ya tashi kai na girgizamai kafin nayi mgana yayi saurin fadin"Bana son mgana da kai. Ina son ko da wani Lokaci na rika jin muryan ki mai Dadi"
Sai na saki hanci kawai ina jin abunda ban taba ji ba,ni daman ashe muryata na da dadi...?muryan da Yaya ishq yace yana jin haushi ina mgana ina rabeta kamar yar koyo.
Sai idanuwana suka ciko kwallah kaina na kasa nace"Ni ba ajinka ba ce kafi karfina bani da dukkan abunda mata masu kyau da wayewa suke da shi..ni bazawara ce"
"Ya'yan ki kuma hud'u ko..?
Yafad'a da sauri bayan katseni cikin mamaki na kallesa shi kuma cikin kwarin gwiwa yace"Nasan ke bazawara ce na kuma san muna da ya'ya yaushe kika shirya kaini na gan su? ko kuma ki bani lambobin su New papa din su zai kira su ya gaishe su"
Sai na kasa mgana kiris ya rage in yi kuka kai tsaye yace"Sai kuma me ma kika ce..?
Yauwa ke ba ajina ba ce sannan baki da abunda da mata masu kyau da wayewa suke da shi ko..?
Yafada cikin sigar tambaya sai na kasa bashi amsa yanayin Fuskarsa sai ta sauya cikin Sautin maza jarumai yace"Kafin na baki amsar ki meyasa kika yi min wannan mganar..?
A ransa yana tunanin meyasa suke da wannan tunanin Baban Nana ma ya fad'a masa
Ni ko kaina na kasa nace"Saboda mazan wannan mazanin basa auran mace in bata da abubuwan kamar kyau,nasaba,gata,karatun boko wayewa,in kuma suka samu akasin haka sai kuke
ganin kamar ba ku auri macen da ta dace da su ba kuma haka naga kuna yi shiyasa"
Katsaneni ya yi da fadin"Kika ga suna yi dai Fa'azza..!
Ni ba haka nake ba ni Abdulbasit kyan mace bai taba Damuna ba"
Wlh tallahi billahil azim in kyau nake nema ba a Nageria zan yi aure ba akwai kasashen larabawa,ina ne bamu shiga ba wasu matane bamu gani ba..?
Ammh ba wacce ta kwantamin arai sai ke Faa'iza ina sonki da zuciya d'aya ba domin wani abu naki ba ke din kawai nake so.."
Yafad'a yana bina da wani kallo kaina na kasa sai hawaye cikin Tagumi yace"Ya illahi ni Tosin saboda rashin so na har da kuka Faa'izaa..?
Sunan da ya fad'a yasa bansan sanda na kwashe da Dariya ba ina Tare bakina kallona yayi yana mirmishi kafin ya cire tagumin yana Fadin"Eh Alowatosin Yoruba name dina ne shine a gida su papa ke kirana Tosin in ba a bangaran aiki ba, achan Benue Da tosin suka sanni ammh yanzu a gabanki Abdulbasit ne"
Ina dariya nace"Ko dai Tosin..?
Sai kawai ya sake tagumi yana kallon bakina kafin yace"Tosin din FAA'IZAA ammh"
Dariya ta shakeni na fara tari da sauri ya mike ya isa frige din Abba ya Daukomin ruwa jiki na rawa ya budemin ya mikamin na karba na sha kadan na mika masa ya karba yana min Sannu sai da yaga tarin ya Tsaya sannan yace"Oh ni Tosin zan ma kaina Tsiya tun kafin na gama na kafa gwamnatina.."
Dariya naji ta kara kamani sai da ya sauke ruwan hannunsa sannan ya zauna yana fadin"Ni dai ki bar Dariyan nan ki fara ji da Tosin bawan Allah"
Ya fad'a kamar ya yi kuka ni yanayin yadda yake fadin Tosin din ne yasa Naji na kasa daina Dariya ai sai ya Hade rai yana Fadin"Kin san Allah? kika kara shakewa ko ruwa bazan miko miki ba"
Sai na natsu ina Sadda kai na kasa mgana sai dai ina ta mirmishi leken Fuskata yake yi yana Fadin"Cute"
Nasan ma'anar cute da Sauri nace"Nasan zagina ka yi"
Ido ya waro kafin yace"Ni tosin yaushe..?
Kai tsaye nace"kace cute ni nasan ba Cute ba ce..Nasan ni mummuna ce sannan ana yawan fad'amin ni mummuna ne"
Rai ya hade kafin yace"su waye..?
Gaskiya ba gaskiya suke fad'a ba..To ni dai koma menene haka naji kuma nagani"
Kai tsaye nace"Baka ce ni. ga shi ban da ilimin boko ban iya turanci ba"
Shima kai tsayen yace"Ni bakin ki ya yi min daidai ma,nima baki ga bakin ba ne, mu taru mu ta haihuwan ya'ya dunaye balakai."
Hausarsa ta saka dariya ta kamani bai damu ba ya cigaba da fadin"Mganar Turanci kuma ina ruwan Tosin. Ni ai ba da Turanci muke mgana ba sannan ni kaina in fad'a miki gaskiya ba Turancin nakeji ba, duk barazana ce wlh asaran kudin tara Papa ya yi gabadaya kaina nan a Duhu yake"
Yafad'a yana Buga kansa Dariyata har tana fitowa cikin dariyan nace"To ya akayi ka samu aiki..?
Kai tsaye yana mirmishi yace"To wannan kuma su Papa ne suka shiga suka fita ammh ban chanchanta ba"
Fuskarsa fa ba wasa ya cigaba da fadin"kinga kenan dukkan mu bamu iya ba an had'u da an dace kenan"
Ina Rufe bakina nace"Kuma ka zama megidan Abba..?
Da Sauri yace"ai na fada miki Papa ne ammh ina Tosin ina zaman Ogan Abban ki..?
Dariya ya yi shikan shi da mganarsa nasan yana yi ne saboda na amince masa ni ko dan barkwancinsa yasa na saki jikina da shi ban sani ba.
Dariya ya rika bani ni ko nama manta inda nake har ina kyakyatawa.
Ganin na shashantar da zencen yasa ya marairaice yana Fadin"Har yanzu dai Fa'iza bata ce tana Tosin ba..?
Fuskata na rufe kafin nace"Sai na fad'ama Abba"
Kai tsaye yace"Da izininsa ma na neni ganinki. Ba ruwan Abba a wannan mganar domin ya fadamin na nemi yarda a wajen ki tunda shari'a ta baki damar zaban miji a karo na biyu.
Faa'iza ni ma ba kowa ba ne mahaifina ma'aikacin gwammati ne nima haka muna zaune a garin Abuja tare da mahaifiyata da Sisters d'ina guda Biyu,sai granny kakarmu wacce ta haifi Papa,Shekaru takwas da suka wuce na taba aure sunan matata Tauhidat satin mu hudu da aure wutar gas ya kona ta Allah ya yimata rasuwa ,tun daga Lokacin ban kara mganar aure ba sai yau a kuma kan ki Faa'iza shiyasa na fada miki ni ba yaro ba ne kalleni nan bazawari ne ni ki bani dama bana son na bata Lokaci mu wuce wajen ina sonki nasan Sauran Fahintar junan zamu yi shi idan muka zama mata da miji"
Karfin Halinsa ke bani mamaki in yana mganar aure farawa da iyawa alokacin sam na manta da wani Ishaq,sai kawai nace masa zan yi Tunani kara marairaicewa yayi yana Fadin"Tunanin minti daya Faa'iza..?
Ina zaro ido nace"Aa nan da wata biyu"
Sai kawai ya gyara zama yana Fadin"Abba zai bani Masauki ko..?
Nayi dariya kafin nace"Da gaske nake yi"
Shima kai tsaye yace"Baki isa ba fa. Sai kuma chan yace Allaha sarki Tosin bawan Allah Fa'iza ki Tausayama Abdulbasit mana kin gani kano zani. ammh saboda ke na fasa sanda kika yi tunanin kika fad'amin Abdulbasit na amince ka zama miji na sai na tafi inda zani"
Ganin yadda ya zauna yasa nasan ba wasa a mganarsa da sauri nace"Kayi hakuri ka tafi bazai d'au Lokaci ba.
Shuru yayi kafin yace"To kwana daya Faa'izaa."
Zan yi mgana ya tareni da kallonsa Dskyar nace"Sati daya dai don Allah"
Kamar yana jira yace"Aa kwana Biyu Faa'iza bazan iya jiran Sati ba zaki kashe Tosin da Tunani fa"
Kina so in na mutu ki biya Diyya ne..?
Da Sauri na girgiza kai sai yayi Mirmishi kafin ya zaro wayarsa a Aljihu yana fadamin"Sakamin lamabarki anan Faa'iza"
Yanayin mganarsa yasa ban yi masa musu ba na karba na saka masa ya amsa ya kira da bai ji ringing din ba da Sauri nace"Tana Daki"
Sai ya gyada kai kafin yace"Ki rika barinta kusa dake. bana so na kiraki ban ji ki ba"
Ina kallomsa kafin nayi mgana yace"Abba ya fad'amin an haifeki da Hearing problem ni kuma nace Daidai kenan daman ai ni kadai ya Dace ki rika jin muryata sosai ko..?
Sai ya bani dariya na Lura in muka kai wani Lokaci cikina zai kulle.
Wayar mikamin yana cemin na sakamai lambar ya'yan shi.
Cikin mamaki nace masa"Basu fa da waya. Yara ne babba ne Amir(Kabir)16yr yana Ss1 sai mai bi masa 14 Anum(Saudatu)tana Jss3 sai Mustapah dake jSs1 Ahmad ne karamin su yana primary 5 ne"cikin gansuwa yace"Masha Allah suna ina yanzu..?
Kai tsaye nace"Suna wajen Baban su a lagos"
Kai tsaye yace"Ana Daura mana aure zamu karbo su damu zasu zauna in sha Allahu"mamakinsa ya kamani kawai sai nace"In babansu ya baka ba..?
Yana kallon cikin idona yace"Zai bani mana nima ai ya'ya na ne"
Kamar wacce ta samu abunda ta jima tana nema haka na saki jiki da Engr muna Hira,na manta da kowa da komai sai da Nana khadija ta kawo abun kari naganta da shirin makaranta sannan na Duba agogo tara saura nayi salati ina sallalami shi kuma yana Dariya fadi yake"Kinsan Tosin akawai hira Abdulbasit ma ba baya ba"
Ina Dariya na fice ina ji yana kiran sunana naki dawowa dakina na koma na kwanta kan gado ina mirmishi ni kadai kamar wacce tayi gamo ina ji Ammi tana kirana nayi saurin Shigewa Tiolet na tube na fara wanka saboda Kamar zai tafi ne,aka kirani ai ko sai da yabar gidan na fito,nako ga tarin missedcall a wayata har da bakuwar lamba kuma nasan shi ne sai da naga na Zainab kusan guda biyar na Tuna da wayar mu ta dazu sai gabana ya amsa gabadaya jikina ya wani mutu kamar bani da Lakka.
Ga Engr ya yi min bake bake a zucci da baki,ko tunasa nayi sai nayi Dariya sai naji mirmishi ya kamani sannan ta wani bangaran ga mganar da na Fad'ama yara na.?
Gefen gado na koma na zauna ina jin Hajijiya ni Fa'iza ya zan yi..?
Engr ko Ishaq..?
Ko da ban ga Abba ba nasan bazai ki ba. sanin Darajan da Engr ke da shi a wajensa, Ammi daman sai tafi kowa murna ammh Ishaq fa..?ba shi kan shi ba, saboda yara na.."
Tabbas ina cikin Tsaka mai wuya.
*Tosin..#*
*Ishaq..#*
*FAA'IZAA...#*
*Janafty*
[7/29, 10:07 AM] U.M Collection ZMFR CM: *KNKB3012*
*Goron Tula*
*Ingantaccen maganine dake saukarda niimar mace sannan dadin dadawa fruit ne ga dadi abaki zakine dashi chakwai sannan bashi da wata illa yadda kikasan fruit haka yake*
*yana da matukar kyau da tasiri ga ma aurata daga mace harna mijin Kuma munada Syrup nasa da akataceshi sannan aka hada da ingantattun magunguna dasuke temakawa ma aurata kwarai don inganta lafiyarsu dakuma maganin matsalarsu ta auratayya yana saukar da niima sosai yana karawa mace dadi fiye dazatanku sai kingwada zak ibada labari insha Allah*
*Sannan akwai zumar kiba*
*Duk macen dake son ta murmure tayi kyau taciko tatada komad'a sosai shaf dinta yafito sosai da sosai to tasha wannan zumar insha Allah zaki gode min*
*Zumar gyara nono*
*Zasu yi kyau suciko ammanfa bawai su tsaya ba😄 zadai suciko suyi kyau sosai insha Allah*
*Zumar hips*
*Indai kinsha zumar nan to hips dinki zai bude zasu yi kyau suciko sosai zaki godemin nina fadamiki insha Allah*
*Note magungunan mu ingantattune basu da side effects kokad'an anyisu da ingantattun*
*magunguna sosai*
*Location Gombe munaturawa ko ina 08030861857*
*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*
*09069067488*
Gabadaya sai naji yar natsuwar da na fara samu kamar an kwace min ita,jikina ya yi sanyi.
Gabbaina sun rusuna,ina kaunar yarana sannan zan iya yin komai saboda naga sun dauwama cikin farinciki sai dai ya zan yi da Engr..?wata zuciyar tace min Sannu Fa'iza riga mallam masallaci Daga had'uwa yau har kin fara tunanin ya zaki yi da shi..?
Sai kaina ya fara wani Dum! eh yau kawai muka na hadu da shi ammh ya yi nasara dawo min da natsuwan da tayi shekaru da kwacemin,sai dai kuma kamar natsuwar ta wucin gadi ce tunda yanzu tana neman ta kwace daga gangan jikina.
Kasa ma fita nayi gabadaya kunya da nauyi tare da sanyin jiki sun haifarmin da kasala ban karya ba ina jin cikina na kukan yunwa ammh Bakina bazai iya karban wani abinci ba.
Ammi ce ta gaji da jiran fitowata ta Biyoni har dakina ta sameni kunsan dai Ammi ba ruwanta Turkeni take yi sai da na fad'amata yadda muka yi da Engr ai sai ta kama Hanci ta saki Guda kafin tace"Wlh kin yi miji Fa'iza ba domin Engr me kudi ba ne, nake fada miki haka ba,sai domin kyakyawan Hallayansa mutun ne nagari mai kima da sanin Darajan d'an adam ina miki albishir da cewa kin yi miji. mijin da acikin maza Dubu babu kamarsa kada ki tsaya wasa haske ne Allah ya kawo miki ki karbesa hannu Bibbiyu ki yi kuma addu'a muna zamu tayaki. muna nan dake watarana da bakin ki sai kin ce Engr mijin Nuna ma duniya da Tsara ne Fa'i"
Haka ta zauna tana karantomin Hallayar Engr tana kara fito da shi a idanuwana ni ko na kasa ce mata komai har ta fice daga Dakin na shiga wani yanayin da mata ire ire na suke shiga to ni me nake da shi da ya ganni yaji yana sona..?
Amsar da na kasa bama kaina kenan. Ranar ko inno ban je na gaisar ba sai da yammah abinci ma Ammi tayi bata nemeni ba ta barni nayi tunani Abba kuma ban yarda ma mun had'u ba kunyarsa nake ji.
Ammh fa Tunanin Engr bai bar zuciyata ba motsi kadan sai ya fadomin arai sai naji Farinciki ya kamani,ya kirani da rana lambarsa na gani na gane kunya da nauyi suka hanani Dauka sai ga Sakon shi.
"Bamu yi haka da ke ba Fa'iza,a sharadin ki ba bu rowar jin muryan ki mai dadi. Ki taimaka ma Bawan Allah Tosin yaji muryan Matarsa"
Sakon sa ya bani Dariya wai matarsa mutumin nan fa yana da karfin Hali,sai Dare ya kara kirana na Dauka ina Dauka ya sauke ajiyar rai yana Fadin"Har kin sa naji d'adi, zuciya ta tayi Sanyi"
Cikin alamun waka ya fad'a da bansan Lokacin da na kwashe da Dariya ba Shima sai ya yi Dariyan kafin yace"Tosin din Fa'izaa ne ke mgana ina Fatan kin gane..?
Ina mirmishi nace"Na gane mana ammh ni ba Tosin dina ba ne"
Da Sauri yace"Naki ne mana. Wlh Tosin din nan naki ne Engr Abdulbasit ne na mutane"
Sai naji na kasa musa mai bakinsa ne ya Bude ya cigaba da min Hira yana Fad'amin yana kano gidan Granny din sa tun dazu ta hana shi tafiya zai kwana sai gobe zai wuce Edo yana da Meeting da rana.
Ayyah kawai na iya ce masa kawai sai ya karya wuya yana Fadin"Gaskiya Faa'izaa ba haka ake yi ba. Sai nayi ta kiran waya baki dauka ba. Sannan Dazu kin yi min laifi kika gudu bamu yi sallama ba"
Sai nima naji ban kyauta ba cikin yanayin mganata nace"Kayi hakuri"
Da sauri yace"An yafe miki. ai amarya bata laifi ko ta kashe dan masu gida"
Ni ko nace bata dai kashen ba ne shi kuma sai ya gyara murya yana Fadin"To ki bari ki zo zan jawo miki Taye da kahinde ki kashe su ki gani ai Godiya zan miki ma duk cikin so ne"
Ina mamakin sunayen da ya kira cikin sigar tambaya nace"Taye da kahinde..?
Sai ya yi mirmishi kafin yace"na manta ke baki iya yarenmu ba ko..?kamar kin koya kin gama in dai muna tare.
Taye and Kahinde Twins name ne da Yaroba,Sister na Twins ne ammh asalin sunayen su Kafayatu Abdulghaffar BIMFE,and Sharifatu Abdulghaffar ERIMIPE."
Cikin jinjina kai nace'Tab kowa sai an sakamai sunan yaren naku ne.?
Yana dariya yace"Sosai ke ma ai zan saka miki naki"
Ina rike bakina nace"Fada mu ji"
Sai yayi shuru kamar yana tunani kafin kuma yace"Naki wayan sai nazo,Gani ga ki sai na fad'a miki naki sunan"
Dariya nayi ina hasaso ni da sunan yarbawa wayaga diskindarid'i,hira muka cigaba da yi yawan hiran daman nasane na barkwanci da ban Dariya sai 11pm yace naje na kwanta zamu yi mgana da Safe,ni ina ma na san Dare ya yi haka kai Fa'iza kam na zake da yawa haka na kwana mafarkin Engr da Safe da naje gaida Inno,bayan mun gaisa ta kalleni tana Fadin"Naji abun alheri wajen Aziza..Bawan Allah ne mai halin kirki ne matuka Baban ku yasan karamcin sa in kika amince masa bazaki yi nadama ba Fa'iza, sai dai bamai yi miki Dole kamar yadda Baban ki ya fada duk abunda kika zabama kanki daidai ne Allah ya sanya Alheri"
Na kasa amsawa a fili sai acikin zuciyata haka na koma daki jikina a sanyaye,ina ko daukan wayata nagama ya kirani har sau uku ina shirin kiransa sai ga shi ya sake kirana ina Dauka yace"Gaskiya ni dai ba'a kyautamin ba gaskiya"
Ina mirmishi nace"Da aka yi me ne..?
Sai ya basar yana fadin"Kin ta shi lafiya?nace lafiya lau muka gaisa nan yake fadamin zai bar kano Jirgi zai bi zuwa chan Edo din ba zato fa tsammani naji yana mgana sama sama sai naji wata yar tsohuwa na kwalamin sallama na amsa na gaisheta cikin girmamawa da ta fara kwarara mana addu'o"i sai da naji kwallah ta zuromin tsohuwar nan akwai addu'a a bakinta.
Sai da ya karbi wayar ne kafin nayi mgana ya rigani da cewa"Hajiya ce kakata ta bangaran uwa. na bata labarin ki ne sai kuma taji muna waya sai tace na bata ku gaisa,sai na bata ai kin ga yawan gaisuwa yafi yawan Fada ko Faa'izaa..?
Sai nayi Dariya kafin nace"Hakane Engr"
Yana kada Harshe yace''Laalaa aiko zamu bata ke ma Engr ne a bakin ki..?
Sai da na rufe bakina kafin nace"To Ko Tosin zan ce...?
Yanayin mganata yasa yadda na fadin Tosin sai da naji kyatatan Dariyan sa kai kawai yake girgizawa yana Fadin"Zan rama ne zan rama Faa'iza"
Da wannan hiran muka yi sallama yace zamu yi mgana bayan ya sauka,ammh yana Filin jirgi sai da ya Kirani daman ina Daki waya a kirjina kamar yasan Tunaninsa nake ina Mirmushi ni kadai.
Da rawan jiki na dauka ko sallama ban gama yace"Sharadin mu gobe ne ko Faa'izaa..?
Cikin mamaki nace'Sharad'in me..?
Sai kawai ya yi mirmishi kafin yace"Ashe zan dawo kaduna yau kuwa..?har kin manta..?
Ina jin haka na fara dariya sai shi kuma ya kanne yana Fadin"Kwana uku zan yi a Edo zan shiga gida Benue dagachan zan je Abuja, wlh bakin nan nawa bai Haila sai na gama yadaki a Dangi gabadaya"
Da Sauri nace"Kai don Allah kamar wata yarinya..'"
Shima kai tsayen yace"Yarinya ce mana shekaran ki nawa..?
Kai tsaye nace"35..ban karisa ba ma sai watan jibi"
Irin Dariyan da ya yi ta nishadi kafin yace"Ashe ma da yarinya nake mgana. Ni ai ban ga baban mace ba yarinya danya Sharaf zan dauka nima ta jikani da yarintarta na dawo Dan Saurayi shar dani"
Dariya ta kamani kafin nace"da Furfuran zaka dawo yaro.?ni kuma da ya'yan hudun zan zama yarinya sharaf.?
Yana shafa kansa kamar ina kallonsa yace"Ke bar wannan mganar muma fa Tsiffon nan mun iya romancewan nan ko wasu matasan albarka,bar ganina haka Tsab zan dawo dake yarinya Dayan sharaf dake abun da duk mun san komai"
Ya karishe fad'a yana Dariya kunya ta saka na kashe wayar yana ta kira ban Dauka ba kawai sai ga sakon shi.
"Karya nayi Tosin da Faa'izaa basu san komai ba..?
Lalle Engr yafi karfina haka na fad'a a cikin raina ina mirmishi in akace zan iya sakin ma wani namiji fuskata da zuciyata sai nace karya ne,yadda Ishaq ya karya duk wani kwanjina ashe ban sanu jarumin maza ba ne sai ga shi kwana Daya da yini Daya Engr na neman Sauya rayuwata daga Duhu zuwa Haske,sai ga shi ni mai ijiye waya sai ayi ta kira ban ji ba sai ga shi ina yawo da waya a hannuna Saboda kada Engr ya kirani bana kusa ransa ya baci.
A rana ban san adadin sau nawa yake kirana ba,ranar dai har sai da nace masa"Kana kirana kamar kana kiran wata budurwa..?
Kai tsaye yace"Budurwa ce mana ni kuma Saurayin ki ba"
Ina Dariya nace"A ina na zama Budurwa ya'ya hudu fa suka fito daga jikina"
Cikin Shakiyan cinsa yace"Allah..?ni ko kin ga da na ganki ban ga ta inda suka fito ba..?ta ina ne..?
Ko sai nazo zaki nuna min.?
Ai ranar yini muka yi bamu mgana ba ya kira har ya gaji ban Dauka ta bakin sa Tosin bakinsai ai ba Saiti.
Sai dare na dauka muka yi mgana shi bai san ya yi wata mgana ba cikin Hade murya yace"Ni dai bana son wannan Horon Faa'iza.
Ko aure muka yi ko laifi nayi miki kada kice zaki Daukemin zaki sakani cikin wani Hali, da kiyi gaba dani ai gwara ki ce Tosin Saka gwiwoyin ka a kasa ki saka Bulala ki zaneni zai fimin kwanciyar Hankali da ki horani da rashin jin muryan ki na yini d'aya"
Jin yanayinsa yasa na basa Hakuri nan da nan ko ya saki yace an yafe min ammh next time in na kara to basan kuma wani mataki zai Dauka a kaina ba.
Ikon Allah akace sai kallo sai ga shi na saki jiki na da zuciyata na bama Engr duka amanar rayuwata batare da Tunamin komai ba tunda da kwana Biyun da na dibar masa ya cika ya rika Damuna da naci mganar. kwanan sa Biyu a Edo ya koma Abuja ya kirani a waya ya Hadani da mahaifiyarsa da yake kira Sweetheart.
Ce mata ya yi ga Faa'iza na son su gaisa cikin kunya muka gaisa yana karban wayar tun kafin nayi mgana yace"Ko ki bani amsata ko kuma wlh mu yi miki gayya har da Papa ga shi nan zaune"
Nasan hali fa zai aika sai nace zan fad'ama sa gobe shima bai barni ba sai da na fadi Time nace da Daddare,ai ni nama manta da kowa da komai Tunanina da mafarkina Engr ne ciki da bayana,Ammi daman ta rigani ta fad'ama su Nana Fatima sun kirani Anty Fadila ce ma bamu yi mgana ba,ta kirani ban gani ba sannan nace zan kirata daga baya ni kuma sai na manta tunda na zama bani da wani Tunani sai na Engr.
Nana fatima kuma ta nuna min goyon bayanta sosai kan al'amarin,Abba ne dai bai ce min komai ba har ranar ni kuma naga rashin kyautarwa na yanke ma kaina hukunci batare da saninsa ba har ga Allah na Ture ishaq da komai a gefe yaran ma bamu kara mgana da ba,su ni kuma ban kira su ba.
Ganin Lokaci na ta tafiya ga Engr bazai bar ni nayi sukuni ba yasa Abba na dawowa naje har falon sa na samesa.
Kunya da nauyi suka lullubeni na kasa mgana shi kuma sai ya gane me ya kawo ni cikin mirmishi yace"Fa'iza mganar Engr ne ko..?.
Sai na gyad'amai ammh na kasa hada ido da shi nauyi nake ji yaushe nasan Engr..?Sai nake ganin kamar Abba zai ce nayi gaggawa kuma ni dai bansan me yake fizgata ba nasan dai ina adddu'a ammh duka mafarkaina na Engr ne bana ganin kowa sai shi.
Kamar Abba ya karanta abunda ke raina ya gyara zama yana kiran sunana sai da na amsa sannan ya cigaba da fadin"Fa'aiza kamar yadda na fad'a a farko yanzu zan kara maimatawa bazan yi miki Dole ba. kamar yadda shari'a ta baki Dama nima na baki. Engr mutumin kirki ne mai Halin Dattako in nace zan fada miki Tarin hallayansa sai kice ina yabonsa ne ammh ni nasan kin fara gani Saboda shi mutum ne Free da kowa ya zauna da shi ko na yini Daya ne sai ya tafi da halinsa masu kyau a baki. Bazan ce ki amince masa domin yana Tare dani ba sai domin zabin ki. Ki natsu kada ki yi gaggawa Fa'iza abunda duk kika yanke ni ina Tare dake har Abada"
Sai naji kalaman Abba sun sakamin natsuwa cikin gyada kai na amsa mai Tare da godiya Abba yace"Allah ya sanya alheri Fa'iza.'
Na kasa amsawa da Ameen sallama nayi masa na fice ya bini da kallo ko da ban fad'a ba labarin zuciya ai a tambayi fuska yasan Engr ya gama Siye zuciyar Fa'iza da Halinsa shifa Dan baiwa ne yana ma siye zukatam maza ba ma mata ba.
Tabbas in Fa'iza ta amince ma Engr sai yafi kowa murna ba saboda komai ba sai saboda Halin nagartansa,ammh kuma yaji matsanancin Tausayin Ishaq ya kamasa ko dazu yana Office ya kirasa sun gaisa suka yi ta Hiran aiki,sannan ya jisa cikin farincikin da har sai da ya tambayesa ko ya samu karin girma ne sai ya yi dariya yace"Abunda na samu yafi karin girma Abba.wani abu ne mai muhimmanci da ya kubcemin har na Fidda rai yanzu zai dawo gareni"
Kwata kwata tunanin Abba bai basa mganar Fa'iza yake yi ba, sai yayi masa Fatan alheri shi kuma Ishaq bai fara ma Abba mganar ba yana jin kunya da nauyi yana Tunanin da Sanin sa Faa'iza ta yanke komawa gidansa.
Abunda kowa bai sani ba tuni labarin zan koma gidan Ishaq ya Zaga Dangi har Karofi bakin su Goggo,Itama Yaya mariya tazo tana fada musu itama a bakin Anty Binta taji tunda Anty Mahma ta haihu sun je suna sukaji ana ta maida zencen Yaya mariya abun ya bata mamaki tazo ta samu Goggo ita kuma tace anya.?
Bata sani ba ammh bari Mallan ya dawo taji ko Abba ya kirasa sun yi zencen to shima abakin Goggo yace yaji bai sani ba jin haka yasa Goggo sai ta Dauka shirme ne jin ko ni ban gayamata ba ballatana shi Baban namu.
Labari har Bauchi Mama ta fad'ama Badariya ba wanda ya kaita Murna ita da Jamal,Anty Fadila ko har gida Ishaq yaje ya sameta da mganar kan zasu je tare ta zabamin Furnitures din da za"a sakamin a dakina,abun itama ya bata mamakin zan dawo ammh bataji ko a bakin Abba ba,sannan ta kirani bata Sameni ba Abba kuma data kirasa sai yace yana meeting ne zai kirata Daga baya.
Ayyuka suka sha kanta bata ko yi zencen da kowa ba. a tunaninta ai za'a sake Daura aure tasan Dole za'a fadamata sai bata kara neman wani da mganar ba ammh da ita akaje aka siya min komai na kayan Daki masu kyau da yarari har ga Allah taji dadi ganin ma yaran nata Murna har da ita Zainab din da Mama yasan ta san gabadayan su suna maraban da dawowata a ranta tace nayi hankali da zan dawo saboda ya'yana mganar Engr kuma Ammi ta fad'amata ammh jin wannan mganar sai ta Dauka Abba ya basa Hakuri shiyasa ma bata Damu ba.
Bani da masaniyar mganata ta zama zarar buni gabad'aya tunanina da komai nawa yana kan Engr,Sanda na fadamasa na amince masa kai tsaye a inda yake ya duka ya daidaici gabas ya yi sujudul shukur ta godiya ga Allaj sai da ya dago sannan yace min"Alhamdulillah nagode sosai Faa'izaa.ban yi miki alkwarin Farinciki har abada a tare dani ba.
Sai dai nayi miki alkawarin zan yi iya kokarina wajen hana Faruwar bacin rai ko damuwa a kan fuskarki."
Yadda kika amince dani kika bani amanar Ragamar rayuwarki ni kuma ina rokon Allah ya bani ikon rike ki bisa gaskiya da amana kada ya barni na zama silar zubar hawayen ki watarana"
Kalamansa sun saka sai da nayi hawaye na tuna ban fa sauya ba ina nan a Fa'izata baka,mummuna mara gata da galihu,mai raunin ji mara ilimin boko wacce batajin Turanci bazawara mai ya'ya hudu ammh mutum kamar Engr da ya mallaki komai na matakin rayuwa ya ce yaji ya gani sai nima na sallama wata irin Soyayya yake gwadamin kulawa ko kamar tsoka daya a miya,Engr duk yadda zai sakani Dariya ya sani in muna wayar har hawaye ina yi Saboda Dariya ba shi da girman kai kamar sauran maza a baya na Dauka maza ire iren su suna da Dagawa sai da na hadu da Engr na karyata haka sannan na kuma gane me ake kira soyayyah ina jinsa a raina Fiye da yadda nake jin Ishaq a baya acikin Raina. kada ku ga laifina na yi shekaru Cikin bautar aure da Tozarci bansan ace ana sona ko na Burge ba yanzu kuma na samu mai sona wanda yake nuna ma duniya ba kamar ni sai na Zama kamar wata sauna kira mana shashasha zuciyata da gangan jikina ta fara bin Umarnin Engr da duka Bukatansa.
Duk da bai gayamin komai akansa duka ba ammh a Hankali na fara Fahimta,Nayi waya da mahaifiyarsa Hajiya Shukra matar nan tun bata ganni ba ta kaunaceni,cikin muryanta mai sanyi da muka yi waya ta rika min Godiya tana sakamin albarka sannan mun yi mgana da Sisters dinsa duk da Hausan su bata fita sun fi iya Yarbanci da turanci ni kuma ba Turanci sai Hausa kawai ahakan ma nagodema Allah,Mahaifinsa ne bamu taba mgana ba yace sai na zama amarya zamu je ya yi mana Nasiha Benue ko sai nagaji da zama cikin yarbawa akaso ne da kilose sai nagaji da ji,in ya fad'i haka sai dai nayi ta Dariya,ga shi ko da wani Lokaci muka yi waya sai yace ina yara..?
In nace suna lafiya sai yace ina Fatan kin fara basu labarina saboda ina so ranar da zasu fara ganina na bude hannuwana su zo da gudu suna rige rigen kiran sunana da Baba..Baba..!
Ina Dariya nace"Ba Baba Tosin ba..?
Daure fuska ya yi kamar yana gabana kafin yace"Ni ai tosin din Faa'iza ne a wajen Ya'yana sunana Baba Abdulbasit'
Kai Engr abun dariyansa basa karewa.
Dakyar a Daddafe ya yi sati biyu yazo ya ganni ni kawai na kawosa kaduna yazo yayi awa biyu,Abuja ya koma Tunda a daran zai bi jirgi zuwa Lagos,A ranar hirar sa duk ta mganan auren mu ne yace zai je America next month,yana so kafin ya tafi a Daura mana aure,ni kuma sai nace ya Tuntubi Abba da haka muka rabu,ni in ana fadin Engr nada kyauta bana gani domin bai taba bani ko Biyar ba. sai da yana samun kati yace na kira Yara bayan haka bazan dora komai ba. nima ba wannan ne a gabana ba shiyasa ban damu ba.
Ranar da yazo Ammi har kwalliya tasa nayi nace mata a hakan yace yana sona baya bukatar wani kyale kyale da Katon Hijabina har yana sharan kasa naje masa ko kayan jikina bai gani ba ammh haka ya rika zuzuta nayi kyau Allah sarki Rayuwa ashe akwai ranar da ni Fa'iza zan iya Burge wani..?
Tabbas ko ban auri Engr ba ya yi sanadiyar kafa aya mai girma a Rayuwata.
Kowa ya ganni yasan ina cikin Farinciki da Annushuwa sanadin Tarayyata da Engr,sannan na samu natsuwa tunda su Anum basu karamin mgana ba itama Zainab din sai dai mu gaisa,ashe ban sani ba shi Gogan ya hana su karamin mgana Tunda acewarsa yasan Halina da Taurin kai yanzu sai na iya Sauya ra'ayi.
Kuma har alokacin bai nemeni ba ammh yana ta shirin dawowata Alhalin ni da shi bamu yi wata mgana ba.
******
Watan mu daya da Haduwa da Engr,Makarantar Haddanmu ta kiramu akan Karban shahada, mu goma Cif zamu karbi shahadar Haddan Qur'ani izifi Sitti,Dole zan koma karofi,Har ga Allah har zuwa Lokacin Abba baisan Halin da ake ciki ba ta bangaran Ishaq ba,ammh sun yi mgana da Engr sosai ta waya akan aurena yace masa ba shi kadai ke da ni ba ina da yan'uwa da iyaye achan karofi zai je ya same su,abunda suka yanke zai Fada masa da haka ma suka rabu.
Sai dai kuma bayan ya samu Inno sun Tattauna itama ta goyo bayan yaje ya samu Goggo da Mallam su tattauna,Ya shirya tafiya ma karofi sai kuma Ishaq ya kirasa da wata mganar data sa ya kasa gane ina aka nufa.
Abunda ya faru shine Mama ta yi ma Ishaq maganar yaushe za'a maida auran..?
Har ga Allah ya ma manta da sai an kara Daura mana aure,ya dauka kawai zan dawo ne ita ta ankar da shi,Sai alokacin ya tuna da sai fa an kara daura wani auran shine Dalilinsa na kiran Abba bayan sun gaisa da Tambayan aiki Ishaq cikin jin nauyi ya yi kasa da Murya cikin Ladabi kafin yace"Abba nace ba..yaushe kuka saka ranar Daurin auran..?
Sai abun ya bama Abba mamaki cikin mamakin yace"Daurin aure kuma..?
Auran wa..?
Ishaq na jin kunya yace"Ko bata fad'a maka ba ne Abba..?
Abba da ya fara hasaso abunda ke faruwa yace da sauri'"Ita wace ce bata fad'amin ba? kuma me zata fad'amin"
Sai ishaq ya yi tunanin kila Fa'iza bata fad'ama Abba ba tana jin nauyi sai yace"Fa'iza mana Abba.
kan mganar maida auran mu ni da ita"
Sai Abba yaji zufa na ketomai cikin mamaki yace"Topaha..Fa'iza bata fad'amin ba ban ma san da wannan mganar ba"
Ishaq yace"To ban san meyasa bata fada maka ba,ammh ta sanar da yara da Zeey cewa zata dawo har ma ina mata shirin dawowa Abba"
Sai Abba ya jinjina kai kafin yace"Ba shakka. to ka bani Lokaci zan yi mgana da ita abunda muka yanke zan nemeka a waya"
Da haka suka rabu da Abba da ransa ya baci a fili ya furta"Meyasa Fa'iza zata min haka..?domin na bata dama bai kamata tayi wasa da Hankalin mutane haka ba"
Shi kunyarsa Daya Engr ya zai yi da shi..?da tasan tun farko ga inda zata koma meyasa ta amsa masa ai da ta basa Hakuri gabadaya ya shiga Tunani Saboda wlh tallahi yana ganin girman Engr baya so ya yi abunda kuma rai zai zo ya baci ta turo sa sannan kuma ga Ishaq da wata mgana a gefe.
Da bacin ran ya koma gida sai kuma Ammi ta tare shi da mganar Fa'iza zata koma karofi Saboda walimar Saukar su,Da farko ya so ya kirata ne ya tambayeta ammh sai kuma ya Sauya shawara yana so yagani ko zan nemesa da mganar ammh har akayi kwana Biyu bai ji komai daga bangarena ba, sannan Engr ma ya kirasa akan ko yaje karofin yace bai je ba sai weekend sai ya Fahimci shi kan shi bai san abunda ke faruwa ba in ma ni na sani to ban Fad'a masa ba.
Ranar alhamis da Daddare bayan ya Dawo gida yana shirin kirana sai ga shi na shigo Falon,da rana ya Kira Nana Fadila sun yi mgana itama yaji mganar komen a bakinta sai bai nuna mata yaji wani batu ba,Abunda kuma ya kara Dauremai kai da suka yi mgana da Mallam mijin Goggo yace masa zai zo akwai mganar da zasu yi Bude bakin Mallam sai cewa ya yi"Masha Allah Allah ya kaddara da Sauran zama Tsakanin Fa'iza da Yaron nan ai gwara ta koma Saboda ya'yan Dake Tsakani"
Sai ya tabbatar da ba shi kadai yaji wannan mganar ba mutane da Dama sun sani,da ya dawo yau ya tambayi Ammi kan yanayin alakata da Engr Ammi cikin Fara'a ta labartamasa yanayin Farincikin da nake ciki sai ya gano shi Ishaq bai yi mgana dani ba abaki yaran yaji mgana ya hau ya zauna kuma ya yad'a labarin batare da ni na sani ba lalle ko in hakane akwai kura ya zama Dole nasan Halin da ake ciki na kuma yi gaggawan fidda Guda daya in Engr na bama Dama zai bama Ishaq hakuri in kuma Ishaq ne zai san yadda zai lallabi Engr yasan shi da Takwalli da yakana.
Ni daman nazo sanar da Abba ranar asabar zan tafi Karofi ne saboda walimar mu,sai kuma naji yace yana son mgana dani ni yanzu nauyin Abba nake ji saboda Engr,naji Abba na mgana ammh har ga Allah ban ji da kyau ba ina chan ina tunanin hirarmu da Engr na rigiman sai yazo walimarmu har karofi daganan ma sai na nunasa wajen Dangi.
Kamar daga sama naji Abba na ambaton Ishaq da mganar ya kirasa yana tambayansa Lokacin da da suka sanya na auran mu.
Sai na kalli Abba cikin wani yanayi kamar ban ji da kyau ba nace"me kace Abba..?
Sai da Abba ya kara maimaitamin sannan na gane in da aka dosa gabana ya fadi cikin rawan murya nace"Abba..Ni kuma..?
Daman ka ba shi dama ne..?
Abba ya girgiza kai kafin yace"Ke yace kin basa dama kin fad'ama yaran da Antynsu"
Sai na tuna mganar muka yi da Anum,Da mganar mu da Zainab sai naji hankalina ya yi bala'n tashi cikin tashin hankali da rawan murya nace"Ni na fad'a ne wasa nake musu Abba.."
Kai tsaye Abba yace"Zabi naki ne har yanzu Fa'iza ki yi tunani in Ishaq din kika zaba falillahil hamdu sai na sallami Engr, in kuma Engr kika zaba sai na bama Ishaq hakuri ki yanke hukunci daga yanzu zuwa ranar da zan zo Karofi yaushe ne Walimar taku..?
Cikin rawan murya nace"Sati mai zuwa"
Abba ya jinjina kai kafin yace"To kiyi tunani a tsanake kafin lokacin aranar zamu tsaida mgana in sha Allahu.
Tashi ki je, jibin Direba zai kai ki zan barma mamanku Sako ta baki."
Daga haka ya sallameni na mike jikina na wani girgiza zuciyata na rawa.
Allah ne ya kaini d'aki lafiya ko gani bana yi,gabadaya idanuwana sun yi Duhu kamar yadda zuciyata ke cikin Duhu da Sarkakiya.
*Janafty*[7/30, 6:24 PM] U.M Collection ZMFR CM: *KNKB3013*
*Goron Tula*
*Ingantaccen maganine dake saukarda niimar mace sannan dadin dadawa fruit ne ga dadi abaki zakine dashi chakwai sannan bashi da wata illa yadda kikasan fruit haka yake*
*yana da matukar kyau da tasiri ga ma aurata daga mace harna mijin Kuma munada Syrup nasa da akataceshi sannan aka hada da ingantattun magunguna dasuke temakawa ma aurata kwarai don inganta lafiyarsu dakuma maganin matsalarsu ta auratayya yana saukar da niima sosai yana karawa mace dadi fiye dazatanku sai kingwada zak ibada labari insha Allah*
*Sannan akwai zumar kiba*
*Duk macen dake son ta murmure tayi kyau taciko tatada komad'a sosai shaf dinta yafito sosai da sosai to tasha wannan zumar insha Allah zaki gode min*
*Zumar gyara nono*
*Zasu yi kyau suciko ammanfa bawai su tsaya ba😄 zadai suciko suyi kyau sosai insha Allah*
*Zumar hips*
*Indai kinsha zumar nan to hips dinki zai bude zasu yi kyau suciko sosai zaki godemin nina fadamiki insha Allah*
*Note magungunan mu ingantattune basu da side effects kokad'an anyisu da ingantattun*
*magunguna sosai*
*Location Gombe munaturawa ko ina 08030861857*
*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*
*09069067488*
Ko gani bana yi haka na fad'a kan gado yaraf kamar kayan wanki. tunanina ba shi a tare dani ya tafi wani waje mai nisa na tunanin yadda zan iya kara zaman aure da Ishaq..?tuna Engr kawai in nayi sai naji gabana ya amsa kaina da zuciyata suna amsa kuwwar Rugugi a lokaci daya.
Tsakani ga Allah ina son Engr a lokacin da ban sani ba,na fara son shi batare da na sani ba,Sai dai na amince da kyawawan hallayarsa da barkwancinsa da kuma yadda yake sona batare da shi ya yi tunanin alfarma ya yi min ba,shiyasa na ba shi amanar duka rayuwata gabadaya.
Saboda Tsabar Rudanin da na shiga har bansan ana ta kiran wayata ba sai da Hafsatu ta shigo ta kawo min nata wayar tana fadin"Yaya Asiya ce tace tana ta kiran wayarki baki dauka ba"
Idanuwana har sun yi ciki ciki Tsabar Tashin Hankali na mike a kasalance zaune kan gado ko Hijabin jikina ban nemi cirewa ba, na karbi wayar ina gani tana kallo na kasa kasa nazarina take yi ganin yanayina,ammh bata ce komai ba ta juya ta fice ta bar min Daki.
A amsa kuwwa na saka wayar kamar yadda na saba,Sallama nayi Yaya Asiya ta amsa muka gaisa kamar yadda muka saba jin muryata a chunkushe yasa tace"Ya na ji muryan ki ta yi ciki ne ko Mura kike yi..?
Na rasa amsar da zan bata sai nace"Uhm'
Sai ta min fatan samun sauki kafin ta zarce da fadin"Ashe kuma zaki koma gidan mijin ki Fa'iza naji dad'i wlh.
Gwara ki koma ko Saboda yaranki"
Wani irin Dum!naji a tsakar kaina nama kasa mgana saboda bakina ya yi nauyi sosai kamar ma miyau ya kasa tsirgamin saboda yadda naji harshe na ya nad'e waje daya.
Ina jinta tacigaba da fad'in"Gwara da kika yi wannan tunanin Fa'i komai lalacewar Ishaq dan'uwanki ne kuma akwai zuru'a a tsakanin ku,tunda kuma yayi nadama kema ai kin kwatarma kanki yanci na tabbata kika koma kina da Darajan ki"
Ni da yake ma ko Goggo bata fadamin ba Gidan Halisa naje jiya kinsan ta kara samun bari Anty Binta ta kirani tace naje na dubata, ita ke min zencen daga gani suma sun ji dadin komawar da zaki yi,Da farko mamaki nayi tunda ban san mganar ba sai da na Kira Mariya tace itama haka taji baku yi mgana a waya ba dai gaskiya"
"Uhm"
kawai na samu kaina da Fadi Saboda yadda harshe na ya Nad'e waje daya,mgana ta cigaba yi tana tunamin manufa da alherin komawa gidan Ishaq jin yanayina yasa bata neme ni da wata mgana ba. muka yi sallama na rude zufa kawai nake yi kenan mgana ma ta shiga bakin yan'uwa ban sani ba..?
Zufa ya jikamin jiki tunda ga Hijabi na har jikina, Tsabar shiga wani yanayi,kenan har su Goggo suma sun ji labari ni ina nan bansani ba..?
Dole na zare Hijabin jikina ina Fifita da shi zufa har kasan wuyana,sai lokacin na tashi na Dauko wayata kira ne ba adadi kuma nasan duk na Engr ne domin tun safe da shi nake fara mgana.
Wayar na hannuna ina Tunanin kiransa ammh kuma kamar an hanani saboda ina ganin ban kyauta ba in na cigaba da yaudaransa,kila ni tawa kaddaran kenan yin aure har Abada batare da naji dadin auran ba.
Zama nayi na tasa wayar a gabana ina gani Engr na kira ammh na kasa Dauka Idanuwana suka cika da kwallah Hirarmu na dawomin a cikin kaina bansan Lokacin da naji hawaye sun cikamin ido ba a fili na Furta"Allah Sarki Tosin"
Kiransa na katsewa sai ga kiran Badariya sai da gabana ya fadi daman mun kwana Biyu bamu yi mgana ba. kamar bazan dauka ba saboda nima bana cikin yanayi mai Dad'i sai dai na Daga kiran Tuna fa Badariya ce.
Ina Dauka sai jin guda nayi a cikin kunnuwana sai da na matsar da wayar Cikin Ihun murna tace"Lalle Anty Fa'iza irin wannan kome na ban mamaki ba Labari.?
Wayata ta lalace tun last week Mama ta fad'amin da muka yi waya sai yanzu nan Yusuf ya kawo min sabuwa ina saka layi ke na fara kira. Ina murna Anty Fa'iza yayan dai nawa In sha Allahu"
Salati na saki a raina kafin naji na tsinke da al'amarin itama kenan taji Labari,ni dai bayan Badariya na amsa wayoyin mutane da dama ciki har da Anty Fadila a bakinta nake jin har kayan dakina da ita akaje aka siyo an gama shiri dawowata kawai ake jira naji ina kuka ne batare da nasan hawaye na fitomin ba
Anty Fadila na fad'amin irin murnan da su Anum suke yi zan dawo har a makaranta sun gayama yan ajinsu, suma Umman su zata dawo hatta da Zainab da Mama suna farinciki da dawowata,har muka gama waya hawaye nake ina sharewa a matsayina na uwa ban isa na Karya ma ya'yana zuciya ba.
Zan koma ma Yaya Ishaq ba domin ina son shi ba sai domin Ya'yana da Farincikin su,bazan iya karya musu zuciya a karo na biyu ba,barin ma da Na kira jamal saboda shima naga kiransa shima zencen yake yi min,jikina bai kara saki ba sai da yace a wayar wani dan ajin su Amir shi Amir din ya ara ya kirasa ya fad'amai haka na zauna na hada kai da gwiwa ina ta kuka kamar raina zai fita,kukan rasa wani abu da nake so kuma ya yi min nisa.
Kamar kuma yan gidan sun sani ba wanda ya nemeni da Hafsatu tazo karban wayata baya na juya bata ma ga Halin da nake ciki ba,bakin kowa sai dai yace na koma ma Ishaq Saboda yarana ba wanda ke tunanin shin in na koma zan samu Farinciki ko bazan samu ba..?meyasa mata da dama ake kokarin Danne musu hakki Saboda yara da an yi mgana sai ace ki koma Saboda yaran ki babu wanda ke tunanin ya mace zata yi in ta koma..?Shin zata yi farinciki..?ko zata Dauwama cikin kunci Allah Sarki Uwa uwa itace wacce zata Sadaukar da Duka Farincikinta Saboda Farincikin ya'yanta.
in dai ko hakane naji zan Sadaukar da farincikina saboda Farincikin ya'yana na. Na Tsaida mgana zan koma gidan Yaya Ishaq saboda yarana Engr kuma bansan ya zan yi da shi ba,Sai dai ko sunan shi na tuna sai naji kuka yazo min na san yana sona ya zai yi in nace na fasa auran sa..?wlh da nasan hakane da tun farko ban basa Dama ba da tun farko ban karya masa zuciya ba.
Ammi bata a gida diyar kawarta ta haihu sun je barka,shiyasa na yini a Daki ina kuka Engr ya kira har ya gaji yayi sakonnin ammh saboda na riga na yanke hukunci yasa ban bude Sakon ba,Ina son na bama kaina karfun gwiwa abincin ranar bai shiga Cikina ba sai ruwan Tea sai yammah Nana Khadija ta lekoni tace Inno na Cigiyata,sai nace tace mata bana jin Dadi ne zan shigo da Daddare.
Bayan sallar mangriba Abba ya Dawo gidan tare da Ammi kila sun biya ne sun D'auketa,ina daki Hafsatu tazo ta kirani In ji Abba sai da gabana ya fadi amnh sai ban razana ba na riga na yi zabi kuma bazan sauya ra'ayi na ba.
Cike da kwarin gwiwa na tafi falon Abba ammh duk wanda ya ganni yasan bana cikin natsuwata.
Suna tare da Ammi Lokaci duka na duka na gaishesu.
Ammi ta kalleni idanuwana sun kumbura tace"lafiya naga idon ki sun tasa..?
Cikin Dishewar muryata da yanayina nace"Lafiya kalau Ammi inaga ciwo suke"
Sai ta faramin fad'an meyasa ban yi mgana ba da sai aje asibiti Abba na gefe yana jin mu bai ce komai ba.
Ni nace ma Ammi idon fa ba sosai ba ne duk Abba na jin mu bai yi mgana ba sai da aka kira wayarsa bai Dauka ba Ammi ta kallesa tana fadin"Ba kiran ka ake yi ba Baban Naana..?
Kai tsaye ni ya kallah kafin yace"Engr ne yau ban san adadin sau nawa ya kirani akan Fa'iza ba"
Ammi sai ta zaro ido kafin tace"Topha lafiya ba su yi waya da Fa'in ba ne..?
Abba yace"Gata nan kiran da nayi mata kenan ya kirani a rude baki ji sa ba, yace tun safe bata daukan wayansa kuma ya tura mata sakonni bata bude ko Daya ba,yanzu ma kiran da kika ga ya yi min nace mai ne ina Office ya bari na koma gida"
Ammi mamaki ya kamata ni ko sai sharan kwallah Abba ta kallah kafin tace"To me ya faru.?
Ke Fa'i meyasa baki daukan wayansa kada fa ki rikita bawan Allah kinga yana son ki"
Sai kawai na Fashe da kuka Abba Da Ammi suka tasani suna kallona cikin mamaki yi nake yi harda shessheka daganan Ammi tasan akwai matsala.
Cikin Sausauta Murya tace"Fa'iza bar kukan nan fadamin meke faruwa..?
Ko kun samu Sabani ne..?
Abba na gefe yaki cewa komai ammh Tabbas ya fahimci wani abu.
Fa'iza na son Engr ammh Ishaq ya sakata cikin Tsaka mai wuya.
Wayar Abba aka sake kira sai ya Turo wayar gabana yana fadin"Ina jin nauyin Engr Fa'iza ki dauka ku yi mgana kada yaga kamar ina masa yawo da Hankali ne"
Kaina na kara shigarwa cikin Hijabi ina kuka Abba bai nuna ya damu da kukana ba,ya cigaba da fad'in"Dauki mana Fa'iza"
Sai na dago kaina cikin kuka nace"Abba bazan iya ba. Bazan iya mgana da shi ba"
Na fada ina rufe bakina saboda ji nayi zuciyata na wani harbawa saboda yanayin da nake ciki.
Ammi ta kalleni a tsorace kafin tace"Wai ban gane ba..?
Mgana da Engr ne bazaki iya ba ko mene..?
Abba kuma shuru yayi bai yi mgana ba ammh kukan fa'iza ya gama tadamai Hankali Cikin kukan na cigaba da fadin"Abba ka bama Engr Hakuri.."
Gabadaya da shi da Ammi suka kafeni da ido shi yana min kallon Tausayi ita kuma Ammi na Rudani da mamaki.
Kafin tayi mgana Abba ya rigata da fadin"Hakurin me..?
Kai tsaye ina kokuwa da Numfashina nace"Na zabi Ishaq. Zan koma gidansa Saboda ya'yana Abba ka tayani ba ma Engr hakuri wlh ba da son raina ba ne
Bansan haka zai faru ba Wlh bansani ba"
Na karishe fad'a cikin gunjin kuka Abba yaji jikinsa ya yi sanyi Tausayin Fa'iza da Engr ya gama kassara Sauran kuzarinsa kaunar da Engr ke yi ma Fa'iza daga Allah ne, Ubangijine ya hada wannan soyayyar ba ta mutum ba ce.
Ya tuna kalamansa dazu da ya kirasa kan bata amsa wayarsa fad'i yake yi"Baban Nana ina son Fa'iza ina jin ta a raina yadda ban taba jin wata y'a mace ba, ka fad'amata tayi hakuri in Laifi nayi mata ta bari in nazo sai ta Hukuntani ammh ta yi ma Girman Allah kada ta hanani jin muryanta"
A yanayin yadda yake mganar zaka Fahimcin yanayin da yake ciki sannan zaka san mganar daga karkashin zuciyarsa suke fitowa.
Ammi kuwa mgana ma kasawa tayi baki ta bude kafin tace"Bangane ba..?
Baban Nana meke faruwa ne..?
Ta fada tana kallon Abba na neman karin bayani.
Shi ko Abba ni ya ke kallo na wani Lokaci kafin yace"Kin tabbata..?
Bana so ki yanke hukunci cikin gaggawa kina da Sauran Lokaci"
Kai Tsaye nace"Ban yi gaggawa ba Abba. Na yanke shawaran zan koma gidan Yaya ishaq"
Na fada ina kokarin danne yanayina ammh fa hawaye bai bar idanuwana ba.
Ammi fadi take yi"Ke baki da Hankali ne..?Engr din fa..?
Ina Abba bai bi ta kanta ba zama ya gyara yana fadin"To Alhamdulillah. Allah yasa hakan shine mafi alheri zan yi mgana da Engr zan basa hakuri goben zaki tafi karofin.?.
Ina kokarin Dauke hawayena na daga mai kai sai yace"Allah ya kaimu lafiya tashi kije kin ji ko..?Allah na tare da ke Fa'iza"
Jikina na rawa na mike na fice ina Kare Fuskata Saboda kukan daya tasomin,haka na koma Daki na kulle kaina ina ta kuka wayata ma kasheta nayi gabadaya..
Sai bayan fitar Fa'iza Abba ya yi ma Ammi bayani ashar ta zuba kafin tace"Wlh wannan mugunta ce ya za'ayi bai yi mgana da Fa'iza ba sai ya kama yad'a mgana haka ake yi baban Nana..?Saboda yasan Fa'iza kan ya'yanta shiyasa yayi mata haka Engr fa ya zaka yi da shi..?
Abba ya lumshe ido kafin ya bude yace"Muna namu ne Allah na nashi kuma na Allah shine Daidai. Komawarta gidan Ishaq ba laifi ba ne Aziza,Duk kyan Sabon gini gwara Tsohon yabe"
Ammi ta karkace kai kafin tace"Wlh da Tsohon yaben nan na Ishaq gwara Sabon gini irin na Engr ko baka lura itama Fa'izan na son shi ba..?Fin karfi yayi mata kuma kana gani kai bazaka yi mgana ba"
Abba ya girgiza kai kafin yace"Ai zabi na bata kuma ta zaba ni bani da wani abu zan yi mata. Ba Hurumina ba ne"
Ammi ranta ya baci tace"Sai kayi shuru yarinya ta cutu Baban Nana..?
Wannan ba zalunci ba ne"
Abba yace"Komama Uban ya'yan nata ne Zalunci..?
Ammi ta mike ranta ya gana baci kafin tace"Eh Saboda bai dace da Fa'iza ba"
Fuu kamar iska haka ta bar masa Falon kai tsaye shashen Inno ta wuce su Hafsah na wajenta idanuwanta sun rufe ta shiga karanta ma Inno Abunda ke faruwa sai Inno tayi shuru kafin tace"Kin san shi aure rai garesa Azizatu..Gwara da Usman bai saka baki ba,in har Fa'iza ta amince da komawa gidan Uban ya'yanta shikenan Aziza abu ne mai kyau hakan suna da ya'ya a tsakani,sannan ga zumunci kuma ko Allah ma muna masa laifi ya yafe mana ballatana mu d'an adam..?mganar wannan bawan Allah kuma ai ba nisa yayi ba sai Usman ya bashi Hakuri haka Allah ya tsara kuma mu bamu isa muja da hukuncinsa ba"
Sai bakin Ammi ya mutu ganin Inno ma bata goyo bayanta ba ammh tasan wannan komen na zalunci ne,Sai ta yi fushi da Abba ta shige dakinta tana kunci tasan da Baffa na da rai shi kadai ne zai gayama Abba yaji,Ga tafiyar Fa'iza ga abunda ya faru ko siyayyan komai ma bata samu yi ma Fa'izan ba. sai da Safe da ta shigo gaisheta ta bata kudin da Abba yace ta bata ita kuma ta hada mata kayan kwaliya da atamfa da less da Hijabai wadanda bata dinka ba.
In ta tuna Fa'iza zata rasa mutun kamar Engr sai taji ma Fa'iza takaici har sai da ta mata mgana da cewa"Ke yanzu gidan wanda baisan Darajan ki ba zaki koma Fa'iza..?kada fa ki yi gaggawa kizo ki yi da kin sani"
Sai na fashe mata da kuka shiyasa ta kyaleni tare da Nana khadija da Hafsatu zamu tafi zasu weekend achan Abba na gida bai fita da wuri ba Direban sa zai kai mu har karofi.
Naje yi ma Inno Sallama ta rika yimin nasihan hakuri da rayuwa Daga karshe tace"Ki yi hakuri ki kuma barma Allah, Zabin nan da kika yi in sha Allahu Hairan ne"
Mganganunta suka d'an sanyayamin rai ammh muna mota na makure kaina a gefe ina kuka Hafsah na gaba Nana khadija na baya sai na sanya Nikab ina ta kuka na ba wanda ya sani wayata ko tana kashe ban kunna ba na so ma Enge ya same ni.
Nayi niyyar zuwa nayi ma Raliya sallama,ammh bana cikin yanayi mai Dadi shiyasa ma na sha'afa kwana nayi kuka saboda haka da ciwon kai na tashi da shi kuma na isa Karofi.
Muna mota amai na dinga yi ni da bana amai a mota ammh Ranar nayi duk na bata jikina,Lagai lagai muka isa gidan Goggo sai ga shi nice kwance da Daddare har da karin ruwa Ulcer ta tashi sai jini da yayi sama Abba nata Fad'an nasan ban ji dadi na shirya Tafiya, ita kuma Ammi ta ce Wlh bana son komawa gidan baban su Amir ne, in aka kyaaleni zan cutar da kaina.
Abba kuma yaki biye ma mganarta Domin ya kira Engr tun a daran jiya ya ba shi hakuri tare da yi mishi bayanin Halin da ake ciki ya yi shuru na wani Lokaci kafin yace"Ita Faa'izan ta ce ta zabi komawa gidan Uban ya'yanta..?
Abba kunya da nauyi dakyar ya amsa masa sai yayi mirmishi kafin yace"Shikenan hakan nada kyau. Allah yasa hakan shine mafi alheri na so ni na sameta domin na cike mata wani gurbin da ta rasa, ammh ko a yanzu bazan cire rai ba sannan bazan mata bakinciki ba,ina yi mata fatan alheri Allah ya sa tayi farinciki fiye da in ni ta aura."
Sai Abba yaji ya kara jin girma da wani Darajan Engr ya karu acikin Idanuwansa,abun mamaki kuma sai suka cigaba da mganar aikin su ko alama bai nuna masa wani Damuwa ba duk da yasan tabbas akwai damuwan.
Shi kan shi abun ya kamasa ammh kuma Fa'iza yake so ta yi ma kanta da Rayuwarta zabi shiyasa bai shiga mganar ba kuma a ranar da Fa'iza ta koma karofi ya kira Ishaq yace sati mai zuwa za'a maida auran sa da Fa'iza ranar asabar kenan in an yi walima jumma'a asabar daurin aure. Ishaq farinciki kamar an yi masa Bushara da gidan aljannah,Haka ya Dawo gida yana fad'ama Mama ta washe baki tana fadin"Masha Allah. Allah ya sa albarka"
Zainab ma tun tana wajen aiki ya kirata ya fad'amata itama tana ta Murna yaran na Gidan Anty Fadila yaje ya Daukosu a daran Sukaje shan I.cream da kayan kwalama saboda Murnan dawowar Fa'iza hatta Amir ranar an ga walwalansa ya shige cikin kannensa yana ta wasa da su.
Akwai wani Farinciki da annushuwa a fuskokin yaran.
Ishaq har kati na waya ya saka an buga masa gayya yake so ya yi sosai,ita kanta Zainab tace zasu yi walima in Fa'iza ta iso Lagos.
Abba shi da kanshi ya kira Mallam mijin goggo ya fad'amasa ranar maida auran, shi kuma ya fad'ama Goggo ina kwance tunda na dawo ina fama da kaina da zuciyata wayata ko ban kunnata ba har a lokacin tana kashe ne ga,shi tunda aka san na dawo ana ta kawo ayyuka ai bani ma da wani guzari su jummala ke yi kunin aya da zobo daman Goggo ke yi yanzu.
A bakin Yaya Mariya nake jin ranar asabar za'a maida aurena da Ishaq ranar sai a asibiti na kwana,Haki na farayi sama sama numfashi na sama sai kuka,kuma na kasa fitowa nayi mgana Abba kuma yayi bakam domin shima ya yi katin daurin aure, ya gayyaci abokan aikinsa.
Labari ya kai ma Ishaq bani da lafiya shima Yaya isa ya fad'amai kwana na Biyu a asibiti aka sallamoni da gargadin na rika cin abinci sannan na daina yawan Tunani to ai tunani a wajena ya zama Dole.
Sai dai sun ta kirana wayata a kashe shi da Zainab,Badariya ma tana son mgana dani ammh na Toshe duk wata hanya,sun yi sun yi su ji Tsarina na Biki naki mgana sai shirin walimarmu kawai nake yi dubu ashirin ashirin muka bada sai Hijaban da muka dinka iri Daya.
sai ni a gida zamu yi abincin Sadaka,Sai kuma na baki Tunda Abba da Ammi da Inno suna tafe ga su Hafsah suna nan basu koma ba.
Nana Fatima ma mun yi mgana ta wayar Goggo tace ranar jumma'a zata zo da safe tun da walimar sai la'asar ne, bana yarda ayi min mganan Daurin aure yanzu sai na saka kuka duk wannan Dauriyar da nake yi Engr na makale a raina bai fita ba kowani Bugawar Numfashina tare da shi acikinta ammh Farincikina ya'yana ne ya yi min katanga da shi har Abada.
Tun ranar alhamis Abba da Ammi da Inno sai Raliya da walid suka Dira a Korafi daman na fad'ama Hajiya zencen walimar ammh ban gayamata na Daurin auren ba sai Raliya ne ta gayamata sannan na kira sa'adatu da Habiba na gayamusu sun kuma min alkwarin suma zasu zo min in sha Allahu.
Su Ammi a gidan da Abba ya gina suka sauka,tunda Daman Baba Ati na cikin gida ita da ya'yan makota ta kama ta rike,ranar jumm'a da Safe sai ga Badariya abun bai wani bani mamaki ba nasan abunda ya kawota ko murnan ganinta ban yi ba, itama ta ga hakan don da tace min tayi ta kiran wayata a kashe yake kawai nayi mata sai kuma ta kalleni tana fadin"Amaryan tamu ba kunshi ba gyaran kai ba na jiki..?me kike nufi..?
Ko amsa ta ma ban yi ba a raina sai da na Zageta in da ace yau Engr zan aura da sai nayi masa abun yafi haka ma sanin shi zai aureni ne ba domin ya yi min alfarma ba sai domin yana sona.
Baki duk sun hallara har da Yaya Asiya su Anty Binta dai ance suna katsina wai Mama sun zo ita da Ishaq da Yaran nima a bakin Yaya Asiya nake ji tunda tace tare suke da Halisa ta sauka katsina Hajiyar Dala ko cewa tayi nasan zan koma uban meyasa na matsa sai da aka kashe auran..?
Bata zo ba kuma wani nata bai zo ba ,ni dai gidan su Yaya isa na koma da shirin walimata na tsani naji ana ambaton sunana da na Ishaq,sai dai na ji sanyi da akace da yaran yazo garin ko banza zan ga ya'yana naji dadi.
Ko kafin karfe hudu an gama komai na walimar ni a gida ma na barsu mun isa makarantan tun biyu na rana,an shirya taro tunda dukkanmu iyayanmu zasu zo,su zasu shaida karban Shahadar.
Sai bayan la'asar aka fara a babban masallacin makarantar za'ayi abun,dukkanmu mun sanya Hijabai Sea greeen har kasa da Safa da bakaken likabai ni kadai ce bazawara mai ya'yan sauran matan duk yan mata ne sai maza uku.
Ahalina kaf sun zo,abun mamaki har da Anty Binta, Mama,Anty mahma,Halisa,Da Ishaq,sai Amir da nagani banga Sauran ba tunda mu muna chan gaba ne,Nima din waige nake yi,Nana Fatima tazo duka ita da ya'yanta sai Sa'adatu da Habiba Allah sarki tare da su Anty Nasara suka iso masallacin,Hajiyar Raliya ma tazo ita da yayar Raliya Salima,Yaya mariya da ya'yanta su Hafsah har da su jummala laure da makotan Goggo.
Naji dadi matuka har sai da nayi hawaye Amir ina cikin nikab ammh sai da ya gane ni yazo wajena na Rumgumesa ina tambayansa sauran yan'uwansa yace"Suna gida Umma Tare da Anty"
Cikin mamaki nace"Katsina suka zo"
Kai tsaye yace"Lagos dai ai Daada yace tare zamu koma dake ko Umma..?
Sai na kasa mgana illah kai da na Dagamai,an fara gabatar da walimar jawaban manyan baki da kuma mai makaranta sai na malamai sai kuma jawaban iyayen yara har Mallam mijin Goggi yayi jawabi Abba ya yi amatsayin Babban bako. Sannan Ya muhallin d'in mu an basa dama yayi jawabi na samu lambar yabo na Hazikar mace ta farko da shekaruna na Hankali na Haddace Qur'ani ya yi kira da sauran mata su koyi dani kada su duba shekaru su tashi su nemi ilimi,Sannan ya yi mganar Lalurata ammh yace hakan nan na Dage har na riga masu lafiyan Haddace Qur'ani,mu sani Allah baya maka hallita batare da yana da manufar hakan ba ina kallon su Abba suna ta mirmishi Allah Sarki tamadina da Baba nayi musu addu'an Aljannah da na tuna da su.
An fara kiranmu d'aya bayan Daya Domin karban rantsuwa naga Fitan Abba ina ta Allah Allah ya Dawo kafin a kirani sai dai addu'ata bata amsu ba nice ta Biyu,tunda in zaka karbi shahadar sai da Hannayen iyayenka da yan'uwanka gabadaya.
Sanda sunana ya karade lasifikan hankalina na baya ina leken Abba domin bazan amsa ba sai hannunsa na kan Hannuna.
Kira sunana ake yi"Fa'iza Sidi karofi"
Ammh ban ta shi ba sai da Yaya Mariya da su Nana Fatima suka zo suka tadani ina kamkame da Hannun Amir,Sai waige nake yi Yaya mariya tace"Wai wa kike nema ne..?
Kai tsaye nace"Ina Abba..?
Sai alokacin suma suka san baya masallaci Nana Fatima ta matsa gefe tace bari ta kirasa kuma ta kira bai Dauka ba ganin ana ta kirana yasa na tafi,ina zuwa akace ina Dangin Fa'iza Gabadaya sai su Goggo suka taso abun mamaki har da Ishaq su mama daman tare da su Goggo suka taso zuwa inda nake tsaye.
Ni dai hankalina na wajen kofar shigowa,ina jin ana jawabai wlh ban Fahimci komai ba, gabana ke fad'uwa fat Fat!
Mallam ya juya bai ga Abba ba cikin wani yanayi yace"Ina Alhaji ko fitan sa din nan bai dawo ba..?
Ina shirin nayi mgana sai ga Abba ya shigo masallacin ina ganinsa sai naji sanyi araina ban tsaya ma kallon bayansa ba na juya ina kallon Ishaq dake ta bayana,taka hijabi na yake kamar zan fad'i sai na juyo sai ya kauda kai yana Dariya yayi fari ammh bai yi kiba ba,sai kasumba daya tara kamar wani kumurci.
Ni ko harara na ballamai ta cikin nikab dina na sauya waje zuwa kusa da Goggo Amir kuma ya Biyo ni.
Sai ji nayi Yaya Mariya na fadin"Abba ashe bako ya yi"
Dago kaina kenan naji Nana Fatima na fadin"Ammi kamar Engr..?
Dum!
Gabana ya amsa ina Dago kaina sai a na Engr yana sanye da Fararen kaya shadda ce tana maiko da yarari,Daga sama har kasa shigansa ta manyan mutane fuskarsa ma'abociyar Haiba da mirmishi tana nan har alokacin Abba na gaba yana bayansa da Takunsa na Cikakkun maza yan kwalisa.
Ni dai naji Abba na gabatar da shi abun mamaki Ishaq har yana bashi Hannu harda rankwafan girmamawa Abba dai bai ce komai ba kansa ya kulle shi kuma Ishaq yasan sunan Engr a bakin Abba ammh bai taba ganinsa ba. yana jin Abba yace ga Megidansa Engr dole yakai gaisuwa tunda da taimakon Engr Aka wankesa daga Zargi.
Abba kuwa mamakin Engr ne ya kamasa duk da yasan Halin nagartansa bai taba fad'amasa yasan Fa'iza zatayi walima ba,sai kiransa kawai suna masallacin nan yace gashi sun shigo Karofi ya bashi address din wajen walimar.
Sai da ya fita suka had'u ya gasgasta wannan kauna da Engr ke yi ma Fa'iza,kai tsaye ma yace masa"Nan da kwana hudu tafiyata America ban manta gobe ne Daurin Fa'iza ba. sannan na rike date din walimar su ina daga cikin masoyan Fa'iza dole zan bar duk abunda ke gabana Saboda nazo na tayata murna"
Daganan yasan Fa'iza ta rasa masoyi,masoyin kwarai da nagarta irin Engr Abdulbasit.
Ni ko jikina sai naji ya saki ammh kuma Farinciki ya lullubeni ina kallonsa yana wurga idon nema na,karaf ko ya ganni ta idona inaga ya gane sai naga ya yi min wani kayattacen mirmishin da ya shiga har cikin tsokar jikina sai na kara Damke hannun Amir ina makyarkyata.
Kafin a ba ni Shahadar sai da nayi karatu cikin suratul Yusuf farko da Tsakiya da karshe aka yi min kabbara,sannan akace yan'uwana su matso su tayani karban shahadan.
Duka muka had'a hannayen mu,Engr na gefe bai saka hannunsa ba sai da Abba yaja hannunsa ya hada da nashi suka mika a tare nima na rike na Amir na mika nawa sauran ma suka miko nasu hannayen muka karba Tare sai kabbara ni ko sai ruwan hawaye.
Ya muhallin d'in mu ya karbi abun mgana yace"yau na karbi shahadan haddan Qur'ani mai girma gobe kuma a wannan masallaci zan karbi nauyin igiya uku na aure, yana tayani murna Allah ya sanya alheri"
Sai aka kara Daukan kabbara,Mallam ya bada sanarwan Ammi jikinta duk yayi sanyi ganin Engr,Mallam shi ya nuna Ishaq yana fadin"Ga mijin nata nan ga kuma d'an su"
Yafada yana riko Ishaq kusa dani da Amir sai masallaci ya Dau kabbara sai fatan alheri ke tashi ni ko kaina na kasa ina jin nauyin idanuwan Engr a kaina
Ina ko dago kaina muka hada ido sai naga ya sakarmin mirmishi ammh wannan mirmishin ba so acikinsa sai zallar kewa da tunanin ka rasa wani abu mai daraja,mirmishin nasa babu karsashi a cikinsa sai karfin hali kawai.
Ido na suka kawo kwallah bansan lokaci da suka fara shatata ba har suna jika nikad di'na.
Ga dai ishaq ga kuma Amir a gefena ammh,Engr dake nesa da ni shi zuciyata ke bugawa da amsa kuwwa a kansa anya ni Fa'iza zan iya kuwa..?
Maida aurena da Ishaq kamar na koma gidan jiya ne."
Amince ma Engr kuma bawa raina da zuciyata abunda suke so da muradi ne..!
Farincikina ko farinciki ya'ya na..?
Wanne ne kan gaba..?
Wanne zan zaba..?
*Janafty*
[7/30, 6:24 PM] U.M Collection ZMFR CM: *KNKB30014*
*TASTED & TRUSTED*
*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATUN SAIWOWIN MUTANAN CHADI DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZAR AMARE, MASU JEGO DA WADDA TAKE SON GYARA KANTA*.
*AN GWADA ANGA INGANCINSA SHIYASA NA KE TALLATA MUKU DA K'ARFIN GUIWATA*.
*ABIN BIRGEWA DA WANNAN SAIWOWINRL ZAKI YI AMFANI DA SU SAMA DA SAU DAYA.*
*AKWAI FULL PACKAGE, AKWAI RABI, TA YADDA KOWA ZAI IYA SIYA*.
*SANNAN BABU BAURI NA TASHIN HANKALI.*
*DA KANKI ZAKI DAFA ABAR KI, KOMAI ANA SAKA WA A CIKI*.
*SHIN KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR, KO KUWA KE CE KIKE SON GYARA KANKI?*.
*KAYANA NATURAL NE DOMIN SAIWOWI NE DA AKE HAKOSU A DAJIKAN CHADI. BAYAN SAUKAR DA GAMSUWA HAR YAQI SUKE YI DA DRYNESS DA KUMA INFECTIONS.*
*AKWAI NA TSUGGUNO DA YAKE HA'DE MACE TA MATSE.*
*AKWAI HADADDUN DAKA NA SHA DA MADARA KO NONO WANDA BABU ALGUS*.
*SANNAN AKWIA GADALIN MATA NA ASALI, WANDA SHA YANZU NE MAGANIN YANZU DA IKON ALLAH*
*DUKKANSU TESTED & TRUSTED NE*.
*TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU*
*08032773332*
*DOMIN KARIN BAYANI, SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*.
*NATION WIDE DELIVERY*
*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*
*09069067488*
Bayan ni an cigaba da kiran sunayen sauran,har aka kai na goma sai bayan an gama bama kowa shahadarsa ne aka fara rabon abinci da kayan makulashe daga bangarorinmu mu masu saukan,ni dai su Goggo sun yi shinkafa da wake,da nama sai Cake da Donot,sai tsire sai drink kuma duka Abba ya bada kudi akayi komai,ni dubu ashirin din makaranta kawai nasan na bada kuma Goggo tayi waina itama na Sadaka.
Ni dai duk bana cikin natsuwata,Dakyar na dan tsaya mukayi Hotuna,Sai waigen Engr nake yi shi kuma ana gama bada rantsuwar suka fice da Abba abun haushi duk inda na juya sai na samu mayattun Idanuwan Ishaq a kaina, a baya ina ganinsa mai kyau gayen da yafi kowa kyau,ammh Daga baya da na hadu da Engr sai na tabbatar ma da kaina Yaya Ishaq ba kowa ba ne a iya Daukan wanka da Tsari akwai iyayen gidansa.
Ko tsayawa ban yi ba na koma gidan Goggo ni da Badariya Amir na kamkame da Hannayena,bayan na sallami bakina Sa'adatu da Habiba,Hajiyar su Raliya ma bata jima ba ta bani gift dina suka koma.
Naje na iske Gift dina da yan'uwa suka taramin Nana Fatima ta kawo min Dan kunnen azurfa mai kyau,Sai Ammi kuma daman nata kayan kwalliya ne sai takalma Badariya kuna kananun kaya tazo min da shi wai na zaman Falo da tsaraban harara ta samu Tsabar yadda kayan suka bani Haushi.
Hajiyar su Raliya ta kawomin Turamen atamfofi masu kyau da mayafai sai sabulun Shower gel na gyaran fata,Hijabai da littafan Addini ba wanda ban samu ba kaya aka taramin kamar wacce ta haihu ko wani Biki,Abba dai yace nasa Gift din sai daga baya zai bani,Abba da Engr da Ishaq gida Abba ya sauke su nan aka kai musu abinci ni dai tun da naga Engr shikenan na rasa yar natsuwan da ta fara zama a tare dani.
Nayi kamar na kunna wayana sai kuma na fasa saboda ko na kunna bani da abunda zan fad'amai.
Bayan mangariba gabadaya ana falon Goggo ana ta Hira har da su Mama da Anty Binta tunda suna gidan,Inno ce kadai ke cikin Daki gajiya yasa ta kwanta Ammi sai da ta bari gabadaya an hadu daman kuma abun na cin ranta ta kalli Goggo tana fadin"Goggon nace kin ko gane wani Engr ne yazo Walimar Fa'iza dazu.?
Sai hankula suka koma kanta Nima ina daga gefe ni da Nana Fatima hira take min ammh bana Fahimtar ta,Amir yabi Yaya isa daya shigo zai kaisa wajen babansa.
Goggo da ta maida Hankalinta wajen Ammi lokaci daya tana fad'in"A'a ban gane sa ba. ina ce abokin aikinsa ne..?
Ammi tayi mirmishi sai da ta kallo Fuskokin su Mama sannan tace"Megidan Baban Nana ne fa. Ina Engr wanda sanadinsa aka wanke Ishaq Daga zargi a EFCC..?
Da sauri Goggo tace"Oh na gane daman shine..?
Ammi tace"Eh wlh shine ai mahaifinsa ne Chairman na EFCC din da taimakonsa ne aka wanke ishaq din har suka maida masa da aikinsa"
Sai gabadaya har da su Mama suka hada baki wajen fadin"'Allah ya saka mai da alheri"
Acikin raina sai da na amsa da Ameen,ko alama ban da masaniyar Ammi zata iya fad'an Engr na sona ba sai kawai da naji tana fadin"Ai shima ya so Fa'iza sosai, sai kuma ga mganar komawarta gidan tsohon mijinta"
Sai gabadaya kallo ya koma kan Ammi ni kuma gabana ya fadi a raunane na dago ina kallonta,Yaya Mariya da Yaya Asiya aka hau kallon kallo kafin su kalleni ganin yadda na Sadda kaina kasa ne yasa suka san Gaskiya Ammi ta fad'a.
Goggo ce tace"Topha mu kuma bamu ji labari ba..?
Ammi tace"Ai Baban Nana na shirin zuwa ya gabatar da mganarsa sai kuma muma mukaji na komen daga sama"
Cikin mamaki Goggo tace"Bangane ba..?Ba Fa'izan ta amince masa ba? sannan shi Baban nata yasa lokacin maida auran ba..?
Sai da Ammi taga yadda su Mama suka yi wani Fiki fiki da ido sannan ta gyara zama tana fadin"Wlh muna daga sama mukaji mganar bayan tagama Zaga dangi. Gatan nan ita kanta Fa'izan tace basu mgana da shi ba shi ya shirya mganarsa,Sanda ya kira Baban Nana ya yi ta fad'an meyasa tasan da shi kuma ta bama Engr dama sai ya kirata gatanan zaune ya bata zabi to kusan Fa'iza kan yaran nata yasa ta amince ammh mganar gaskiya Engr Fa'iza ke so kuma shi din ta bama Dama da Farko"
Sai falon ya yi shuru aka rasa mai mgana,Mama da Anty Binta suka hada ido suna kallon juna kunya da nauyi duk ya kamasu.
Ammi ko ajikinta ta cigaba da bada Labarin irin soyayyar Engr da Fa'iza ta karishe da fadin"Wlh yana ganinta haka din ta yadda take yaji duk duniya ba wacce yake so sai ita, ku duba dai matakin abunda ya taka a rayuwarsa ammh Fa'iza ce ta masa,Daga karshe da ta zabi koma ma uban ya,yanta sai Baban Nana ya bashi Hakuri da yake shi Mutum ne mai takwalli Yace bakomai Haka Allah ya kaddara kuma Daurin auranta ya kawosa Jibi yake da Tafiya zuwa America"
Sai falon ya dau Allah Sarki Yaya Mariya tace"Tab..'
Tama kasa mgana Nana fatima tace tana kallona"Daman ke kika zabi ki koma Fa'in mu..?
Sai na kasa mgana Idanuwana sun kawo kwallah,Goggo dai sai jinjina kai take yi ta dauki saunar mganar yadda taji mganar a gari batare da Abba ya kira su ba, sannan nima ban mata mgana ba kenan Ishaq da yaran Fa'iza ya yi amfani.
Goggo sai ta Bude baki tace"Bai ko kyauta ba in dai hakane da sai ya yi mgana da ita yaji ra'ayin ta ko.?
Da Sauri Mama tace"Kar ku ga laifinsa ita Fa'izan tayi mgana da Anum ta fada'mata zata dawo,sannan ta fadama Zainab su kuma suka fadamasa to shi rudewa ya yi yasa bai nemi jin ta bakinta ba kuskuran da ya yi kenan"
Tafada cikin fargaba da abunda taji,Yaya Asiya tace"Allah dai yasa hakan ya zama alheri"
A ka amsa da Ameen ni kan ina zaune kirs ya rage ban yi kuka ba Badariya na chan gefe sai auna wasu abubuwan take yi tsakani ga Allah wannan Engr ta lura da daman irin kallon da yake bin Anty Fa'iza da shi sai da akayi mganar ta Fahinci komai.
Tana hasaso yanayinsa a Fuskarsa Tabbas babban gwaska ne,taji matukar Dadi da Fa'iza ta samu wani mai kaunar ta bayan Yaya Ishaq sai dai an ce so so ne ammh son kai yafi, bazata zabi bare a kan yayanta ba ammh da ace wani ne bazata yarda Fa'iza ta koma ba, da sai ta bata shawaran ta auri wanda ke son ta ba domin komai ba sai domin kauna Daga Allah ba wanda zai ce zai yi mata alfarma ba.
A na cikin mganar sai ga Amir ya shigo da sallama sai falon ya yi shuru,Gaishe da su Goggo ya yi suka amsa cikin Fara'a Ammi tace"Ina ka baro abokin naka..?
Cikin yanayin sanyin sa yace"suna chan gida ni an aiko ni wajen Umma ne"
Sai alokacin aka lura da abunda ke Hannunsa,wani dan karamin kwali ne mai kyau yana kyalkyali wajena ya Nufa ya mikamin kwalin na karba ina kallonsa kafin nace"Waye ya baka wannan Amir..?
Kai tsaye yace"abokin Abba ne..yace sunansa Baba shima wai baba na ne"
Yana fadin haka gabana ya fad'i nasan waye ya bashi Engr ne.
Da sauri na kara rike abun na kasa mgana shi kuma ya cigaba da fadin"Shi ne yace na kawo miki"
Kai na gyada ina kokarin maida hawayena ban damu da yadda ido ya Dawo kaina ba na tashi na shige Daki har da turo kofa..
Na zauna a saman gado na bude kwalin wani irin agogon Silba ne mai kyau da yarari daga ganinsa kamar na Diomod,yana kyalli irin na mata da na gwada shi daidai ni a hannuna kamar an gwadani.
Sai wata karamar Takarda na gani a gefe na dauko na warwareta ga abunda ya Rubuta.
"Congratulation Faa'izaa. Allah ya sa ma abunda kika karanta albarka"
Ina miki Fatan alheri a sabuwar rayuwarki da zaki fara"
"Engr Abdulbasit Abdulghaffar Aluwatosin"
Haka na kamkame takardan ina kuka wannan wani irin shiga tsaka mai wuya ne..?bana duba ban kuma san wani irin zama zan yi da Engr ba, ammh ina masa kyakyawan zaton zan samun farimciki ko da ba duka ba a tare da shi Fiye da yadda na samu a tare da Ishaq sai dai ya'yana su nake tunawa bana so a wannan karon ma na kara karya musu zuciya, shiyasa na yanke shawaran komawa in dai su zasu yi farinciki na amince ko da nawa Farincikin zai samu tawaya.
Kwata kwata bana jin Farinciki ko annushuwa kan maida aurena da Ishaq,sai ma wani kunci da nake jin yana mamaye ruhina ina ji ajikina kamar zan koma gidan Jiya ne,wanda fa yace baya sonka to har abada baya sonka sai dai kila Daga baya ya Fahimci kana da wani Muhimmanci a Rayuwarsa ne shiyasa ya Damu ya kai.
Ammh nasan waye Ishaq ni ba Zabinsa ba ne bazan kuma taba samun Farinciki daga garesa ba..
Gobe ne za'a maida auran mu ammh mgana ta Fatar baki bata had'amu ba,koma ya tambayeni wani shiri nayi..?hakane soyayyar..?na fi Tunanin shima Saboda ya'yan mu ne sannan kuma da Tasirin zama tare da shi ba Domin muna da Fahimtar juna a tsakanin mu ba.
Na yarda da wani tunanin masana Soyayya,ita soyayya tana ginuwa ne tare da Fahintar juna,ban dad'e da Haduwa da Engr ba ammh ya fahinceni nima na Fahincesa fiye da yadda Ishaq ya Fahinceni shekaru kusan goma sha da auren mu nima yadda na Fahimci Engr wlh ban Fahimci waye ishaq ba. Saboda bai bani Damar haka ba abu daya kawai ya bani wanda zan Daki kirji na nuna shi shine ya maidani uwa ya bani Ya'ya bayan su a zama da shi ban san komai ba, sai Tozarci da wulakanci sai kuncin zuciya da ciremin dukkan sha'awan aure acikin raina.
A Daran ranar nayi kuka sosai kukan da bansan iyaka ba,Ina kuma kamkame da agogo da yar takarda a Hannuna ina ji ana kwankwasa kofar naki Budewa,inaga ganin halin da nake ciki yasa suka kyaleni.
har Biyu na Dare idanuwana Biyu,gajiya nayi da kukan na tashi na Dauro alwala na shiga Sallah bayan na Idar na Daga Hannuwana sama ina fadin"Ya Allah ga baiwarka nan Fa'iza kaga zuciya ka ga zabina sai dai na baka zabi. Sai ka zabamin Ishaq a karo na biyu..Ya Allah ina rokon ka da ka tabbatarmin da alheri ka bani natsuwar zuciya da kwarin gwiwa shi kuma Engr yadda ya kaunace don Allah,ka basa wacce zata kaunace sa shima domin ka,ka cire masa damuwan rashi na,ka yi masa kyakyawan Sakamako irin sakamakon da kake yi ma bayin ka Salihai masu Hakuri"
Ina addu'a ina kuka Sauran Daran da karatun Qur'ani na raya su kuma na Bude muryata har ma karatun ya tada wasu da asuba sauran kuma Dakunan su na Bisu na buga musu sannan na koma na tada sallar Raka'atul Fijir.
Ina sallamewa na Dora da Sallar asuba bayan na idar ina azkar barci ya rika Fizgata nan saman Darduma na bingire da barci ban ta shi ba sai tara na Safe kuma Daurin auran karfe Daya ne ina ta shi ba kowa a dakin, sai ni a firgice na tashi da ganin rana har ta fito,hayaniya na rika ji a tsakar gida ina lekawa naga suna ta ayyuka kamar ma sun gama abincin share share suke yi.
Nana Fatima ce ta shigo falon Goggo tana ganina tace"Amarsu kin tashi..?
Ina tura baki nace"Shine baku tasheni ba..?
Tana Dariya tace"Mu tashe ki mu yi laifi..?
Ban ce mata komai ba na juya na koma Daki har ga Allah naji zuciyata ta samu natsuwa kuma na samu saukin Al'amura naji na samu natsuwa Dari bisa Dari,wanka nayi tunanin na fara yi na shirya kafin mutane su fara taruwa duk da ni ban yi gayya ba ammh nasan Goggo tayi gayya kuma wasu mutanen arxukan ko ba gayya sai sun shigo.
Bani da wani zabi sai na Ubangiji kuma Tunda ya zabanin Ishaq to bazan yi Butulci ba na karba Hannu Bibbiyu.
Ina wanka Abba ya shigo gidan saboda ta bayin ne tsakar gida ina jin mganarsa,har yana tambayana shiyasa da na fito na shirya a gurguje cikin,less riga da zani ko kallabi ban saka ba na zumbuda hijabi na fita Falo muka gaisa da Abba da Mallam Sai Amir da ya taho wajena yana Fadin"Umma ina kwana"
Ina shafa kansa na amsa masa chan ya kwana wajen babansa.
Zama na yi a kasa Mallam ya bamu waje tunda kamar Abba na son mgana dani ne.
Cikin dattakonsa ya kalleni yana Fadin"Ya kuka yi da shi Ishaq din kan mganar tafiyarki..?
Kaina na kasa Amir na gefena nace"Ni bamu yi wata mgana ba Abba"
jinjina kai Abba ya yi kafin yace"Shikenan in an Daura auren sai ku yi mgana in zai wuce dake ne sai na baki kudin kayan Dakin ki yar'uwanki ta rakaki ki siya abunda kike so. ina Tunanin kila tare zaku koma"
Gabana na fadi ammh na cije sai kiran sunan Allah nake yi acikin raina,Abba ya yi ta min nasihan da suka kara sanyayamin jiki,haka Inno da Baba ati suna ta bani Hakuri da Nasihan zamantakewar aure.
har Abba zai fita ya tuna ya Dawo da baya yana fadin"Kin ga na manta ki kira Engr ki yi masa godiya 300thousand ya turomin yace a baki,ko kuma ma kije chan gidan ku gaisa ki yi masa Godiya,Engr mutum ne mai kirki har ga Allah a zuciyarsa komai ya wuce, yace ke ba Rabonsa ba ne"
Kai na kasa na Daga ma Abba kai,ina son tashi ammh na kasa bani da kwarin gwiwan Fuskantarsa yasa nayi zama na Badariya da Nana Fatima ne suka jani Daki suka tasani gaba da tsiyan sai nayi kwalliya
Gajiya nayi na kyalesu suna min kwalliyar a waje kuma Yaya Asiya ke fadin ko kayan gyara ban sha ba, Ammi naji batace komai ba saboda Ishaq ne yasa bata bani komai na shafa ba, ammh da Engr ne da an ga Ruwan gyara kuwa.
Yaya mariya ne tace tana da wasu sai a bani na sha Goggo kuma tace kwanaki ai ta bani na tsumi na sha da tace na mganin sanyi ne achan Daki kuma sai da sukamin kwalliya suka min Dauri sai ga shi na fito ras dani Allah yasa daman kaina ya Tsefe yake Kunshi ne ban yi ba.
Badariya sai fadi take"Kina gyara wasu amaran ammh ko yar Dilkar nan bazaki kwama kan ki ba..?
Nana Fatima tace"Ba kuma turarren kamshi ta kuma iya had'a ma wasu ammh ita ko na goga ma jiki bata da shi"
Duk ina jin su ban ce musu kala ba ina da Turaruka suna cikin kayana ne ban fito da su ba, Tunda ba amfani zan yi da shi ba kuma ma ina da Zallar madaran Turaren ban dai hada ba ne.
Tunawa nayi da mganar Abba yasa nace musu zan fita Amir ya fice tun dazu kila yana wajen babansa.
Sai kuma na rasa yadda zan yi na fita sai na ari wayar Hafsah na kira Abba na tambayeshi suna tare da Engr ne..?
Abba yace basa tare sun fita da mallam Shi Engr na gida naje nayi masa godiya.
Kunyar zuwa ni kadai yasa naja Nana Khadija nace ta rakani,na saka Dogon Sabon Hijabina mai ruwan madara da takalmi,goggo kawai na fadama inda zani ta kalleni cikin wani yanayi kafin tace"Yakamata kam sai kin dawo"
Suna ta faman tambayana ina zani nayi musu banza domin haushin su nake ji suma.
Muna fita waje muka hadu da Yaya isa da su Yaya Salisu muka gaisa suna ta zolayata mun wuce kenan sai ga Yaya Ishaq da Amir,har ga Allah ni ban gan su ba ance hankali ke gani ni kuma ina chan tunanin haduwata da Engr suna ta mana mgana ban ji ba hatta Nana khadija bata gan su ba tunda suna ta gefen hanya ne.
Shi kuma yana ganin mu mun nufi gidan Abba sai yayi tunanin ko shi nake nema sai suka biyo bayan mu.
Tunda tun safe suna tare da Engr suna ta Hira mutum ne mai ilimi ba ruwansa ga sakewa da mutane. tun a jiya Abba ya yi masa bayanin shine Ishaq din da ya kirasa kan mganarsa da EFCC har yasa mahaifinsa ya shiga ciki,Engr na ta mamakin daman shine mijin Fa'iza kenan..?
Ko a fuska bai nuna masa komai ba suka cigaba da tattauna mganar aiki Sai Ishaq ya Fahimci Engr mutum ne da yake da ilimin rayuwa da wayewa ga shi bai da girman kai duk ko da matakin Rayuwar da ya samu ya yi mamakin da yaji sunansa ashe bayarbe ne..?ko a kama ko a mgana ba shi da kama da yarbawa Allah mai hikima kenan..
Dayake gidan shashe biyu ne shashin da aka bude na Abba sai nayi Tunanin yana ciki muna kokarin shiga Nana Khadija tace min wai fitsari take ji nace mu shiga tayi tace a'a bari ta koma gida tayi ba'a son raina ba ta koma tana fita suka hade da Ishaq a Hanya shine yake ce mata ya gansu yana ta mgana basu ji ba..
Nana khadija tace"Laa bamu lura dakai ba dayake muna ta sauri Anty Fa'iza tace na raka zata je wajen Engr"
Gaban Ishaq ya fadi bai gane zata je wajen Engr ba..?
Bai gama tunaninsa ba Nana Khadija yace"Tana chan ni zan koma gida ne na Dauki wani abu"
Fitsarin ne ya matseta sai ta wuce da Sauri bayan tace Amir yazo ya rakata sai ya noke wajen Babansa.
Ishaq kasa gaba ya yi ballatana baya haka kurum yaji shakku a ransa.
Sai da Amir yaja hannunsa yana Fadin"Muje Daada Umma na chan na jiran mu"
Kamar an jasa haka ya shiga Binsa har gidan.
Suna bakin kofar falon sukaji Muryan Engr na fadin"Faa'izaa..Son da nayi miki daga Allah ne. Don kuma na rasaki sai na butulce masa..?
Sai kafafun Ishaq suka fara rawa jin kalaman Engr,sai dai kuma bai jin mganar Fa'iza ba, abun mamaki sai Amir shima ya Tsaya cak kamar ubansa.
Ji sukayi cikin tattausan murya ya Cigaba da fadin"Ni daman bana so nayi miki Dole wajen aurena. Tunda kika zabi komawa gidan mijin ki i will Support u Faa'iza ni masoyin ki ne masoyi na Hakika"
Sai a lokacin yaji muryata cikin sanyi ina Fadin"Duk da haka nagode Abba ya fadamin abun alheri Allah ya biya da Aljannah"
Kai tsaye ya amsa da Ameen Ameem.
Duk kokarinsa na kada ya kalleni ya kasaa sai da ya kuramin ido yana daga zaune kan kujera ni kuma ina zaune a kasa ne sa da shi, daman sanda na shigo anan na samesa.
Sanye da Farar shadda har da babban Riga sai kwarjinsa ya karu a cikin Idanuwana mirmishin nan nasa bai bace ba.
Cikin kauda shurun yace"1pm ne Daurin auran ko..?
Kaina na kasa saboda kallon Engr Daidai yake da Ruguza duk wani kwarin gwiwata.
Ban ba shi amsa ba sai ya yi mirmishi kafin yace"Abuja zan wuce ana gama Daurin aure nan, sanadin ki yasa cikin wattanin nan ina ta tafiyan Mota Faa'iza"
Muryata a shake nace"Allah ya kiyaye hanya'
Ya amsa da Ameen kafin yace"Tafiya ta a America ranar Tuesday ne fa,sai nayi wajen 1month achan kafin na dawo tunda aikin daga nan Ma'aikatarmu ta Edo ne suka turani"
Ni dai ina jin bayaninsa na ko kasa motsi kamar yadda Shima Ishaq ya kasa motsi Amir kuma tunani yake Umma zata auri Daada na biyu ammh me take yi da wannan mutumin kuma ..?
Gani nayi na kusa rasa jarumta ta ga Khadija taki dawowa yasa na mike ina fadin"Zan tafi"
Shima sai ya mike yana fadin"Tun yanzu Faa'izaa..?
Yadda yaja sunan Faa'izan ne ya karyamin Lago na sai da na Dago ina kallonsa sai ya wani sakarmin mirmishinsa mai kassarani lokaci daya yana Lumshe idanuwansa..
Ji nayi kamar zan fadi ammh bai lura da haka ba kai tsaye yace"Kin yi kyau Faa'izaa.."
Yau dai kad'ai Ki bari Tosin ya yaba faa'izarsa"
Yanayin mganarsa yasa na kwashi Saurin zan fice Tsautsayi yasa na ci tuntube da Cafet din dake Tsakar Falon sai nayi gaba zan fad'i da azama da wani karfin gwiwa ya rikoni sai gani na Dawo baya Dumu Dumu a acikin kirjin Engr.
Sai na ganni yar karama dani a saman hammatansa tsabar yadda bani da Tsawo da girma
Cikin Sanyin muryansa yace"Subhanallah sannu baki dai ji ciwo ba ko..?
Kamshin Turaransa ne ya cikamin Hanci yasa na kasa mgana ina shirin kwace jikina daga rikon da yayi min, kamar daga sama mukaji an bankad'o labulen Falon an shigo.
Gabadayan mu a tare muka juya sai idon mu ana Ishaq.
Gabana ya yi kwance kwance yace Ras!
Ban ga Amir tare da shi ba ashe shi kuma sai yaki shigowa. ya tsaya daga bakin kofa bai so ya shigo yaga wani abu da zai saka yaga bakin Umma.
Engr bai damu ba sai ma sakina da yayi bayan ya tabbatar da na Tsaya Daidai har yana fadin"kin tabbata kina Lafiya..?
Kai na d'agamai jikina na rawa ganin irin wulalakantattacen kallo da Ishaq ke bin mu da shi kamar wand'anda ya kama suna wani abun assha.
Engr ko Ishaq ya kallah yana Fadin"ko ka biyota ne kaji ta shuru..?
Sallama ma muke yi zata tafi"
Cikin kallon reni ya ke kallonsa duk da ya gani bai damu ba, ni ko jikina na rawa na kama Hanya zan fice sum sum sai ji nayi Ishaq yaja hijabi na ya Dawo dani ta baya kee da karfi ya yi jifa dani har na kusa fad'i wannan karon ma Engr ne ya rikeni yana Fadin"Sannu"
Lokaci daya yana kallon Ishaq kafin yace"Ka yi mata a hankali mana..?
Ai cikin tsawa da Fusata yace"Kace nayi mata a hankali mana tunda abokiyar shashancin ka ne.."
Dagani haar Engr a rude muka kallesa baki bude shiko kishi da rashin sanin Daraja yasa idanuwansa ya Rufe gani yake yi raina masa wayau nayi ina tare da wani zan kuma koma gidansa.
Cikin Dariyan renin wayau yace"Ku ke kallona kamar baku gane manufa ta ba ko..?karya nayi ba shashancin kuke yi ba..?Abun naku ma bai isa ba har sai a ranar da za'a Daura mana aure shine kika lallabo kikazo a yi abunda aka saba, achan kaduna duk watsewar da kuka yi bai isheku ba ya sake biyo ki nan. Anan din ma a filin Allah na kamaku rike da juna saboda Lalacewa Fa'iza me kike nema.?
Me kika rasa..?
Oh na gane kudi ko..?yana sakar miki kudi ke da iyayen shi shiyasa kike sakar masa jikin ki Tir dake Fa'izaa. wlh kin yi asara idan har kin san kin Fara watsewar ki a waje tun wuri ki yi min bayani domin duk yadda nake so ki koma gidana bazan kwashi datti na kai gidana ba,ki gurbatamin Tarbiyan yarana ba Faa'iza ba zai yuyu ba,Ki Fad'amin gaskiya nawa yake Biyan ki kina bashi jiki..."
Mganarsa tasa bata gama Fita ba na Sauke masa tagwayen maruka har guda Biyu dama da Hauni. kafin na Fashe da wani irin kuka wanda daga ji shi kasan na tsatsananin bakinciki ne da bacin rai.
Cikin kuka na nunasa da hannuna cikin ihu da Tsawa nace"Kul..Karka kuskura ka kara dangantani da barna ko datti Ishaq kada ka kuskura"
Na fad'a ina zubar kwallah shi ko duk da Mamakin marinsa da nayi haka ya watsake idanuwansa sun rufe Engr ko Daskarewa ya yi a Tsaye yana kokuwa da bacin ransa.
Dariyan wulakanci ya saka yana nunani sama da kasa daga karfi yace"Don na fad'i gaskiya shine kika mareni..?
Karya nayi nace karya nayi..?
Ba rike da juna na same ku ba..?
In ba iskanci ba ina ruwansa da cewa kin yi kyau kuma meyasa kuka kebe a gida daga ke sai shi nace Muharraman juna kuke..?
Ya karishe fad'a yana min ihu kawai sai na kasa tsaida hawayena cikin dauriya da wani Turiri dake taso min daga kasan raina nace"Gaskiya ka fad'a. Tabbas ka fadi gaskiya bai kamata a yi maka rufa rufa a kai maka Datti agidan ka ba,ballatana ta gurbata maka tarbiyan da ka kwashe shekaru kana yi ma ya'yan ka.".
In sha Allahu baza'a kai maka Datti gidan ka ba".
Na karishe fad'a cikin kuka hawaye wani na korar wani na kama Hanya zan fice Engr ya yi saurin kiran sunana"Faa'izaa.."
Ban juyo ba sai da na tsaya cikin kukan dake tasomin ina Dannewa nace"Kayi min alfarman bazaka je ko'ina ba sai an gama Daurin auran nan..?
Ina jin muryansa cikin jarumta yace"In sha Allahu"
Ban tsaya ba na fice da Sauri ina jinsa ko kunya wai yana kiran sunana ashe da na koma ma auran Ishaq haka zan cigaba da Fuskantar wulakanci..?
Ashe a shekarun da na kwashe tare da shi bazai iya shaida ta ba?
Ina fita naci karo da Amir na tsaya ina kallonsa sai raunina ya karu na fashe da kuka da Sauri ya kariso zai rikeni na kauce na fita da gudu shima sai ya Biyo ni yana Kiran" Umma Umma"
Ina tafiya ina kuka kamar mahaukaciya ban je gidan Goggo ba. sai na wuce gidan su Yaya isa Dakin matar Yaya salisu ke bude ciki na shiga ina ta rafzan kuka sai ga Amir ya biyo bayana.
ba kowa a falon sai wayar yaya Salisun kila yana ciki ne,ita na Rarumi na shige uwar Dakin matarsa da ita na rufe kofa.
Ina ji Amir na kiran sunana Daga baya har da muryan Yaya Salisu suna kiran sunana cikin kuka da Ihu nace"Ku tafi kyaleni. lafiyata kalau bana son ganin kowa.."
Sun jini shiyasa Yaya Salisu yaja Amir suka fita daga gidan nan.
Ni kuma nan na sulale ina kuka kamar karamar yarinya.
******
Karfe Daya na ranar asabar din karshen mako,Dubban mutane suka Shaida Daurin auran *ENGR ABDULBASIT ABDULGHAFFAR ALUWATOSIN*
Tare da Amaryan sa *FA'IZA SIDI KAROFI* sauyin da aka same shi batare da kowa ya sani ba.
Abba shi ya yi ma Engr walicci Ya yin da Mallam ya zama waliyyina,Akan Sadaki Dubu Dari,kuma Engr ya biya da Cheque din banki tunda ba shi da Cash a hannunsa.
sannan Direban Engr ne kadai ya shaida Daurin auran sai shi Engr d'in cikin mutanensa, sai dai ya saka an Dauki komai Live ta Vedio call ga su Papa da Sweetheart da Sisters dinsa.
Daurin auran da ya faranta Zuciyar Engr sannan ya Kusa tafiya da Bugawar zuciyar Ishaq kabir karofi.
Engr gaban mutane acikin masallaci ya yi sujudul shukru kafin ya Daga ya hannayensa sama yana Fadin"Allah na gode maka. ba wayau na ba ne kuma Dubarata ba ne da ka bani Faa'iza amatsayin mata ba,Allah karka barni ni kad'ai ka yi min jagora wajen tafiyar da rikon Amanarta a tare dani"
Ba su Abba ba kowa dake masallacin nan Engr ya Burgesu ciki har da Jamal da yazo Daurin auran yayansa da ma wasu daga cikin abokansa sai sukaji Labari ya sha bambam.
Kallonsa kawai ake yi duk yayi zufa sai uban zare ido yake jamal ya taso yazo wajensa yana fadin"Yaya Ishaq ya haka..?
Sai a lokacin ya fara Nadaman abunda ya aikata duk da yayi nadaman tun ad'azu din ammh bai Taba Tunanin zai iya rasa Faa'iza a wannan gabar ba.
Ya dauka bata da wani zabi sai zabin shi da ya'yan su.
Idanuwansa sun tara kwallah dishi dishi yake hango Amir tare da Abba tun bayan da ya barsa nan bakin kofa bai kara ganinsa ba sai yanzu.
Kamar in ya gane manufar abun Amir ya fara Gudunsa kenan..?
Kenan yaji abunda ya faru tsakaninsa da Fa'iza..?
Innalillahi wani"inna ilaihirraju'un
Ya fadi a zucci da Sarari kamar yadda ya saki wannan salatin haka suma acikin gidan Goggo,Mama da su Anty Binta ke salatin lamarin.
Har Labari yazo cewa ba da Ishaq aka Daura aure ba da Engr ne.
*Janafty*
[7/31, 3:09 PM] U.M Collection ZMFR CM: *KNKB3015*
*Na gaida ke,My Anty. Anty Sis♥️Kyakyawan sharhin ki yasa kin gama fad'in komai game da wannan labarin,Madallah da ke,Allah ya raya Zuru'a*
*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*
*09069067488*
*AWANNI BIYU KAFIN DAURIN AURAN*.
A lokacin da na shige dakin Matar Yaya Salisu Zulaihat,bana cikin hayyacina zuciyata gabadaya tayi Duhu tare da wani irin kuncin da na jima ban jini cikin yanayin ba.
Kuka nake yi da hawaye da sautin muryata ina tuna kalaman Ishaq gareni da ya kirani Datti gaban Mutum mai karamci irin Engr.
Tunani nayi cewa har abada bazan yi kima a idon Ishaq ba,baya sona kuma bazai taba sona ba,ba abunda zai iya sauya wannan abun kawai dai akwai wani gibi ko bangaran da ni zan cike masa ne shiyasa yaso komawata garesa.
Ammh daga yanzu na fahimci komai kuma bazan kara bari rayuwata ta kara shiga wani hali ba,ya'yana na wa ne har kuma gaban Abada ba su da uwar da ta fini a wajen su,ko da sun Raunana na dan Lokaci ne zasu dawo daidai da yardan Allah.
Da wayar Yaya Salisu nayi amfani na kira Abba ina kuka daman na Haddace lambarsa sai da na saka naga shima ashe yana da lambarsa.
Jina cikin kuka da Damuwa yasa Abba yace na zauna a inda nake ga su nan zuwa shi da mallam bayan na fad'a musu ina gidan su Yaya isa.
Sai da naji muryan Abba na bude kofa ina kuka gabansu na zube na had'a Hannayena Biyu ina fadin"Abba in nace na fasa komawa gidan Ishaq ran ka zai baci..?ba zaka kalleni a wacce ta maida kai karamin mutum ba..?
Sai Abba ya saka Hannu ya Dago ni Cikin wani yanayi muka isa har falo kan Daya daga cikin kujerun falon ya zaunar dani su ma duka suka samu gefena suka zauna cikin Tausasawa Abba yace"Bazan taba cewa ba Fa'iza daman ai zabin naki ne ba namu ba ko ba haka ba Mallam..?
Sai ya jinjina kai yana fadin"kwarai da gaske"
Cikin kuka na zayyane ma Abba komai da ya faru tsakanina da Ishaq na karishe da fadin"Abba ko waye ka auramin shi ni dai ka taimaka kada ka auramin Ishaq Saboda yace ni Datti ce bazan je ce na gurbata masa Tarbiyan ya'ya ba'
Na karishe fad'a cikin gunjin kuka Abba ya yi shuru ransa ya baci ya kasa mgana Mallam ne yace"Subhanallah shi kuma ya zai yi haka..?Ana mganar aure kuma zargi na shigowa ciki"
Abba ya yi huci kafin yace"Ai shikenan bakomai daman zabin na baki da kaina ban miki katsalandan ba ne, saboda watarana ko bani ki iya sanin abunda ya dace dake. tunda yace haka ya gama mgana ba kwantai kika yi ba Fa'iza ke yar baiwa ce in yace ke Datti ce wani a Dattin zan bashi auranki kuma ya karba tashi ki je ki wanke Fuskarki ki kwantar da Hankalin ki insha Allahu bazaki ji kunya ba Allah zai nuna miki Ribar Hakurin ki tun a duniya."
Kalaman Abba suka sanyayamin rai duk da ban kawo ma Engr a lokacin ba, na riga na yanke hukunci gwara na auri koma waye da na koma ma Waye da auran Ishaq,bayan tafiyar su Abba ba jimawa sai ga Ammi ashe Abba ya yi mata waya yace tazo ta zauna dani.
Alokacin su kan su su Goggo ba su san abunda ya faru ba, ita kanta Abba bai yi mata bayani ba yace dai ina gidan su Isa taje ta zauna dani bayan tazo ne na zayyane mata komai..
Kyafci ta fara kafin tace"Uhm komai akayi da jaki daman sai ya ci kara mutum mai kima irin Engr ya yi ma wannan cin zarafin..?
Ina hawaye na kasa mgana saboda ni kaina kunyar kaina da abunda Ishaq ya yi ma Engr duk ya kamani,Ammi ta rika fada kamar zata ari baki tana fadin"Daman wata Daraja naki ya sani..?dan renin wayau ne fa Jaka ya maidake wacce bata da yanci ki koma ki cigaba da gadin gida da kula da mahaifiyarsa da ya'yansa da matarsa. to ai kuma yaci taliyar karshe ya'ya in bazai rike ba ya baki zaki hada ki rike abinku kuma na tabbatar da Engr wlh ko duka duniya kika haifa bazai gaza ba wajen rike miki su ba'
Ina tsiyayan hawaye nace"Ammi ni fa ban ce Abba ya auramin Engr ba. Cewa nayi ya bani duk wanda yaga Dama"
Ammi ta min dakuwa kafin tace"Kaji min sakarci in ya je ya aura miki wanda baki sani ba fa..?an rabu da bukar kuma sai a haifi Habu"
Ina kuka ne ammh sai da nayi dariya a raina nasan Abba uba ne na gari bazai taba min zabin da zai zama Cutarwa gareni ba, shiyasa ma ban damu ba ni dai tunda na sahale ma kaina Ishaq sai naji kamar an saukemin wani katon dutse mai nauyi daya tokaremin zuciya.
Cigiyata suka fara yi dagachan Gidan Goggo,tunda an ce ina ko tare da Abba ne sai aka kira Ammi tace tana tare dani,Yaya Salisu kuma na tare da Amir yana lallashinsa Domin yaga yaron ya shiga damuwa shi ko Amir kalaman Daada ne ke masa yawo a kwakwalwa tare da Kukan Umma sai yaji ya tsani Daada ta ya zai kira Umma da wannan sunan mara kyau..?
Kuma ya sakata kuka.?
Kawai don yana Da dauriya ne yasa bai yi kuka ba ammh duk yayi zuru zuru.
Abba da Mallam suka tattauna mafita batare da sun yi zencen da kowa ba. Engr na gidan inda Ishaq ya Fice ya barsa cikin kogin nadama,Hankalinsa ya tashi Tunanin abunda ya aikata kuskure ne bai zo mai ba sai da ya aikata wani kishin Fa'iza ne ya taso masa da yasa ya kasa iya Sarrafa kansa. kishin ta samu wanda ya fisa komai yace yana sonta shi ya Dauka bayan shi ba kuma wani namijin da Fa'iza zata Burgesa,yana da yakinin in ba shi ba,Fa'iza ba ta da kowa kuma yana takamar cewa shi da ta gujen ma wa bata da kamarsa sai ga shi Allah ya nuna masa Isharan sa da cewa ita Daukakan Allah ba ta zaba ba ne, Daukakarsa ta kowa da kowa ne koda kai ba kowan kowa ba ne in ya tashi zai Daukaka domin nuna izina ga maza ire iren su ishaq masu Tunani irin nasa.
Har ga Allah shi kan shi Engr bai san da Sauyin mganar ba sai da suka shiga masallaci Abba ya karkata ya ce masa ya kawo sadakin Fa'iza ya bashi auranta Engr sai yaji kamar bai ji da kyau ba, sai da Abba ya maimaita masa bashi da Cash sai cheque ya rubuta ya bada sannan ya kira Sister dinsa kafayatu Vedio call Papa na gida tunda Weekend ne ya bama Direbansa ya Daukan musu Daurin auran Live suka kallah duka duka Lamarin ya faru gaza da mintina talatin ne. sai akalan Fatan alherin ya koma ga Engr a madadin Ishaq da aka barsa baki Bude.
Engr bakinsa kamar zai Tsage daman ga shi ma'aboci mirmishi da Fara'a haka jama'a ke ta ba shi Hannu cikin masu hannu da shi har da Dr.Lawal bako. yazo Daurin auran Abba ya fad'amai Ishaq ma haka shi kan shi da yaga Engr sai da ya rankwafa Aiko a gidan giya akwai babba shi kan shi yasan yanzu ko yarsa zainab bata isa ta Dagama Fa'za kai ba,Tafita komai na Duniya Tunda ta samu miji a gefenta kamar Engr da ya taka matakan Rayuwa masu girma.
*******
Tsakanin Mama ko Anty Binta an rasa mai iya mgana ballatana su fahimci yadda aka samu wannan Sauyin haka bangaran su Goggo ma suna ta jimamin garin yaya aka samu Sauyi ba tare da kowa ya sani ba..?Sai dai ba amsa tunda mazan duk ba su dawo ba,ni kuma ina gidan su Yaya isa Nana Fatima ta kira Ammi tana fad'a mata Halin da ake ciki da sauyin da aka samu.
Ammi ta rangada guda ta yi rawa tayi juyi ina zaune ina kallonta Sai da ta katse wayar Fatima sannan ta kalleni tana fadin"Aure ya Dauru murna muke ta yi. Kin Zama Amaryan Engr igiya uku har Abada"
Kamar an zaremin wani mutuwar jiki haka naji,sannan na ji gabbaina da suka yi sanyi sun tashi daga suman da suka yi,Naji dai yanayina ya sauya kadan ammh kuma bana bakincikin sai ma wani boyayen ajiyan zuciya da na saki batare da na sani ba,Ina da yakinin zan samu farinciki ko ba duka ba ammh zan samu ko da kad'an Daga cikin farincikin da Sauran mata suke samu a gidan auran su.
Sai da mukayi sallar Azahar Ammi ta sani gaba muka koma gidan Goggo ba wasu jama'a sosai sai na gida,Muna shigowa Yaya Mariya ta saka gud'a tana fadin"Shi daman alkawarin Allah baya tashi"
Daman ita bata wani so Yaya ishaq ba,tun da farko da bata yi da shi yasa har yanzu sama sama sama ne,ni dai daki na wuce,Su Mama na falo duk jiki ba Dadi,Badariya ce kadai ta biyo su Nana Fatima zuwa dakin wajena ita kuma Ammi ta tafi wajen Goggo Abba ya kirata suna bukatar abinci da abun sha.
Duk da Jikin Badariya ya yi sanyi bayan Nana Fatima ta rumgumo ni tana fadin"Ina tayaki murna yar'uwata. Allah ya sanya alheri"
Na amsa mata da Ameen kasa kasa Sai Badariya itama ta kariso tana Fadin"Ina murna Anty Fa'iza Allah yasa gwara da akayi"
Na amsa mata ina kallonta tana so mu yi mgana ammh sai taga idanuwan mutane shiyasa ta juya ta fice Su Raliya ne da su Yaya Asiya tare dani suna ta tattauna yadda lamarin ya sauya ni dai ina jin su ban ce komai ba zan yi mgana ammh ba yanzu ba.
Abinci su Abba Nana khadija da Hafsatu suka kai musu,Sai wajen uku na rana muka samu kebewa da Badariya shima din tazo fad'amin su Mama na shirin zasu koma katsina ne..
Cikin mamaki nace"Yau kuma..?Na sha sai gobe..?
Cikin damuwa tace"Mama tace kunyarku take ji bazata iya zama ba. taji abunda yaya ishaq ya aikata Jamal ya kirani a waya duk ya fad'amin yace Yaya ishaq nata kuka yana bama Abba hakuri, shi kuma yace bakomai tunda dai kin auri wani shi ba da shi za ayi masa rufa rufa akai masa Datti ba.."
Kai na sadda kasa ban yi mgana ba sai ta Dafani tana fadin"Don Allah ki yi hakuri Anty Fa'iza"
Ina kokarin maida hawayen da suka kawomin nace"Bakomai rayuwa ce Badariya"
Nama kasa mgana sai kawai na saka kuka,sai ta rumgumeni tana Lallashina itama tana cikin damuwa ammh kuma bazata iya gayamin ba ganin yanayin da nake ciki.
Tare da ita mukaje wajen su Mama,Anty Binta dai ta kasa mgana Mama ce ke ta bani Hakuri nace bakomai Anty mahma tace"Shi ma dai Ishaq kamar wani yaro..?
Ai ba haka ake nuna kishi ba"
Yake kawai nayi ban yi mgana ba Halisa nake kallo duk ta rame ta lalace kamar ba Halisa ba Daga gani dai tana ji ajikinta a raina nace Allah ya kyauta.
Anty Binta ke tambayan ina shi Ishaq din.?Badariya tace"Jamal yace ya wuce kano ta chan zai siyi ticket na komawa Lagos. tunda yasan tsiyar da yayi"
Mama tace"To ina shi Amir.?
Sai da akayi mgana na Tuna da Amir cikin Damuwa nace"Ko dashi ya tafi ne..?
Badariya na shirin mgana sai ga Jamal da Amir sun shigo tare,yana ganina ya Rugo ya rumgumeni yana kiran"Umma."
Mu kadai ne afalon su Goggo suna ciki,Ammi ta gama warware musu komai kowa yaji sai yace gwara da ya rasa Fa'iza bai chanchanta ba.
Mama har ciki ta shiga tana basu hakuri tana sharan kwallah Goggo tace bakomai kansa yayi mawa ga shi ya rasa Fa'iza ita kuma Allah yasa gidan arzikinta ne.
Ganin yanayin sa yasa nasan Amir na cikin damuwa sai najashi Daki bayan mun gaisa da Jamal shima hakurin yake bani nayi yake,nace bakomai a raina ko nace shi ke da Hakuri kuma yanzu ammh har abada bazan taba yafe masa da kazafin da ya kullamin ba sai mun yi Hisabi a gaban Ubangiji ranar gobe kiyama.
Tambayan Amir na yi da yaci abinci sai ya dagamin kai kafin yace"Naci ai ina tare da su Abba ne a sabon gida"
Sai nayi shuru na kasa mgana saboda nasan yaji mganganuna da na Babansa kuma wasu kalmomin masu nauyi ne a Tunanin yaro karami kamar Amir.
Ba zato kawai naji ya riko hannuna kafin yace"Umma ki yi hakuri"
Sai hawaye sharr da sauri na rikosa ina fadin"Kai Amir menene yasa kake kuka..?
Sai na rumgumesa ina Lallashinsa cikin shesshekan kuka yace"Umma ki yi hakuri kin ji ko.?
Sai naji kaunar d'ana ta kara ratsani na Dago fuskarsa ina share masa hawaye,ina fadin"To shikenan na hakura kai ma ka daina kuka"
Mirmishi nayi masa shims ya maidamin kafin yace"Umma gwara da kika auri Baba baki auri Daada ba. Tunda yace miki ke datti ce"
Cike da mamaki nake kallonsa kafin na samu bakin mgana yace"Baba yace yana son ki Umma. Muna yace yana son mu"
Sai ga hawaye sharr sun zubomin rike hannayensa nayi ina fadin"Nima ina son ku ya'yana ka kula da kannen ka Amir kuma kada ka kuskura ka fada musu abunda ya faru kaji ko..?
Sai ya gyad'amin kai alamun bazai fada ba,kansa na dafa ina fadin"Yauwa Sannan ka lallashesu in zasu yi kuka saboda ban dawo ba kaji ko..?
Nan ma kai ya gyadamin nima sai na jinjina kaina kafin nace"Allah ya yi muku albarka gabadaya"
Ya amsa da Ameen,mun dade muna Hira da shi yawancin labarin rayuwar su a lagos ne ina jin sa ina mirmishi gefe daya ina sharan kwallah Haka Allah ya kaddara bazan zauna da ya'yana har abada ba. domin nasan Ishaq bazai bani ko daya Daga ciki ba.
Sai bayan La'asar su Mama suka wuce katsina an rabu zukata ba Dadi,kamar kada mu rabu da Amir da yaga ma Ina Damuwa sai yace"Umma ki daina damuwa fa zan lallashi su Anum kuma ma ai Baba yace zai rika kawo ki,kina ganin mu muma yace zamu rika zuwa muna ganin ki"
Sai na rumgumesa ina kuka Kaunar Engr da ta boye acikin raina ta sake Fitowa a cikin zuciyata,ance mai d'a wawa daman ya Fad'amin shi baya son ya'yansa su kirasa wani Daddy yafi son Baba na gargajiya.
Nasan Engr na da kirki ammh sai da Amir ya kalleni yace"Umma ki daina Damuwa shi Baba na da kirki bazai rika sakaki kuka kamar Daada ba"
Har suka tafi da na tuna da mganarsa sai naji hawaye sun kawo min Allah Sarki ya'ya Rahma ne Allah ya bama wadanda ba su da ya'ya masu albarka mu kuma da muke da su Allah ya tsare mana su sannan ya kara shiryawa,katsina zasu kwana Gobe su tafi kano Jamal Dole zai siya musu Tiket zuwa lagos tunda Uban gayyar ya watsar da su ya yi gaba.
Tunda dai na tabbatar da cewa Engr na aura sai duk wani Fargaba na ya kare na saki jikina da yammah Nana Fatima na cewa na sake wanka ba Gaddama na Sake yin wanka na sauya kaya zuwa atamfa Doguwar riga.
Da naga bata ce zatamin kwalliya ba kai Tsaye nace"Fatin mu kwalliyar fa..?
Cikin shagwaba na fada ai sai ta rike baki tana fadin"Eyee lalle na yarda ana son Engr ammh ai dazu har kina mana Boren baki so"
Ina Dariya nace"Dazu kika ce. yanzu ai komai ya sauya".
Duka ta D'akamin tana fadin"Zaki sani ne bazan yi kwalliyar ba".
Dariya na fara ina bata Hakuri sai ta rumgumeni tana fadin"Naji dadin ganin ki cikin farinciki Fa'in mu Allah ya saka ki yi farinciki fiye da yadda kike Tsammani, Allah yasa Engr ya juyar dake Dadin da sai kin manta sunan ki"
Tsungulinta nayi ina fadin"Ba'a gasa bakin nan naki ba"
Na fad'a ina dariya ni da ita ina tuna Dazu da Yaya Mariya tace gwara da Ishaq ya furta haka akansa wasu hallayansa tasa Inno ta mata dakuwa tana fadin bakin ki kamar bai ji gashi ba Mariya, muna ta dariya shine na tuna na fad'ama Nana Fatima"
Sai da mukayi sallar mangariba sannan Nana Fatima ta min kwalliya mai sauki sai tunani nake yi ko Engr yayi Fushi ne bai nemeni ba.
Abunda ban sani ba suna tare da su Abba har Dr.Lawal sai washegari zai koma Abuja,bazai iya barin su ba,kuma wayata ban kunna ba amnh yafi kowa son ganina da jin muryata.
Abincin har sai da aka bama almajirai tunda ba wasu jama'a ni ko su Sa'adatu hana su dawowa yau nayi alokacin bansan lamarin zai sauya ba Ammi ko bakinta har kunne ammh da Safe ko Fara'a batayi.
Taruwa suka yi Nana Fatima da Raliya suna min tsiya Badariya na taremin daman tana nan bata koma ba,Yusuf din zai turo Direba yazo ya Dauketa jibi.
Muna cikin hakane Abba ya kira wayar Nana Fatima akace a bani ina karba yace"Fa'i ki kunna wayarki Engr na son mgana da ke"
Cikin sanyin jiki na amsa mai da toh wayar na cikin karamar jakata ta hannu na fiddota na kunna,naga tarin sakonnin Engr ban bude ba sai na goge su nasan ma magiyane tun a baya yanzu kuma mun taka wani mataki basai mun koma baya ba.
Ina kunna wayar kamar yana jira sai ga kiransa gabana ya fadi ga su Badariya sai na lallaba na fice ashe suna Lura dani sai suka kwashi shewa na fice ina girgiza kai kawai.
Tsakar gida na fita sai naji akwai sanyi sai na shige dakin Karikitan goggo da nawa ni kaina,na samu saman Freezer na haye har kiran ya katse sai ya kara kira ina Dagawa bai jira nayi mgana ba yace"Alhamdulillah Faa'iza ta zama ta Tosin har Abada"
Mirmishi nayi ban yi mgana ba sai ya cigaba da fad'in "Ki ce wani abu mana karo na farko da aurane na akan ki Faa'iza"
Dakyar na iya fadin"Ina mana Fatan alheri"
Ina jin Sautin mirmishinsa kafin yace"Kin gama mgana gabadaya..?
To Ameen ykk..?kin ci abinci kuwa..?kin daina kuka..?
Ina dariya nace"Duk ni kadai wanne zan fara amsa maka..?
Kai tsaye yace"Duka nake bukata"
Cikin karya murya da bansan na iya ba nace"ina lafiya kamar yadda kake. abinci kuma ban ci ba kila sai an jima kuka kuma na daina tun daga Lokacin da naji Labarin na zama matarka"
Ni kaina in ina tare da Engr bana sanin ma ina sakin baki ina mgana.
Sai da naji yace"Da gaske Faa'iza..?
Ni kaina bansan adadin Halin da na shiga ba nayi ma Allah godiya Sosai har Umra zamu Faa'iza domin mu kara godema Allah"
Jin nayi shuru yasa ya cigaba da fadin"Papa da sweetheart sun ce na gaishe ki sosai tare da Sister dina. Suna ta min magiyan gobe na taho dake Abuja"
Da sauri nace"Ni kuma..?
Sai ya marairaice kafin yace"Eh suna so su ganki ne. Ni dayake ma kinga jibi zan yi tafiyata bama ganina zaki rika yi ba"
Dariya ya bani kafin nace"Ai sai jibi ne Tafiyar goben bazan ganka ba ne..?
Sai ya yi saurin fadin"Nufina daga goben nake so nace"
Yafad'a yana sosa keya kamar ina ganinsa yana jina ina yar Dariya wani irin farinciki ya mamayesa kafin yace"Wlh da na son da auran nan Visa zan yi miki kafata kafarki zuwa America Faa'izaa"
Ina mirmishi nace"Ayya sai kuma ga shi kafarka kafarka zaka tafi"
Kai ya kada kafin yace"Kin ci ba shi. Zakuma ki sha wahala wajen biya'
Ni dai dariya nayi masa hira ya dinga min yana bani labarin granny din su ta kirashi tana fadan meyasa aure cikin gaggawa haka? bai fad'ama kowa ba yana cemin"Kinsan me na gayamata..?
Sai na girgiza kai cikin Danne Dariyansa yace"Ce mata nayi gaggawan na rabo ne,gwara ayi ayi auran kada na haifa mata yaran da take son gani a titi"
Sai na rufe baki ina salati shi kuma yana Dariya kafin yace"To karya nayi..?haka tsohon mijin ki yace nawa na biyaki kika bani jikin ki..?
Ni wlh ban ji haushinsa ba ga shi Sanadin mganarsa ya sa jikin ya zama nawa har Abada, in a baya ina biya ne yanzu a kyauta ma za'a bani sai ma ina yanga"
Kasa mgana nayi ina toshe bakina kada nayi dariya shi ko ajikinsa cikin Kada harshe yace"Wayyo na tausaya masa sosai"
Kai kawai na girgiza kafin nace"Ba kai kayi masa kwacen mata ba"
Da sauri yace"A'a daman ai Faa'iza ta Abdulbasit ne shi kadai ban cika neman abu na rasa ba Faa'iza,ni da kika ganni nan ina da sa'a duk abunda na nema ban Samu ba to ki tabbatar da ba Alherina ba ne"
Cigaba ya yi da bani labarin sa kad'an da wasu abubuwa na shi,ya yi mganar yana dawowa zan tare na zabi in da nake so na zauna kaduna ko Abuja,ko Edo
Saboda na Zolayesa nace"Lagos nake so"Da sauri yace"Ban da nan. Ni bana zuwa Lagos"
Yafada har da hade rai sai na kyakyalce da dariya shima tayani yayi kafin yace"In domin yaran mu ne kada ki damu tare zamu rika zuwa ganin su bazan lamunta da barin ki ke kad'ai ba. gwara ki zabi kusa dani wlh kika zabi nesa korata za'ayi a aiki Tunda wajen ki zan tare kinsan makale mata manne mata'?
Ina Dariya nace"Eh.."
Shi kuma sai yace"To ai irina kenan so gwara ki neman mana masalaha"
Hiran ce tayi dadi cikin wasa da Dariya da barkwanci har bansan Dare ya yi ba,sai da wayata ta dauke,ashe ba Chaji na fito naga duhu ya yi sosai har mallan ya dawo dukkanmu bamu yi sallar isha'i da wuri ba.
Koda na koma Daki ina Sadda kai Badariya batayi barci ba Nana Fatima kuma na wanka Raliya na Dayan dakin Goggo.
Kallona tayi kafin tace"Uhm za'a kwashi kallon kauna agidan ki Anty Fa'iza.."
Kai na Sadda kasa sai naji ina jin kunyarta dariyanta naji tana Fadin"ni ce fa.
Badariya ce Anty Fa'iza.
Wlh ina miki murna na jima ina addu'aan Allah ya baki miji mai sonki wanda zai kasheki da Soyayya kuma Daga gani Allah ya baki"
Sai na kwashe da Dariya a raina ina Tuna Engr duk da ba'a son maci Tuwo ba sai miya ta kare,ammh alaman karfi yana ga mai kiba Engr karshe ne a sanin kan mace to ya shiga ko'ina meye bai gani ba..?
Nasan ba domin wayar ta mutu ba bazai kyaleni ba chaji na sakata da Nana Fatima ta fito nashiga nima nayi wanka na Dauro alwala nazo nayi sallah ranar raba Dare muka yi muna Hira suna ta bani sharwari Badariya tace"Yaushe ne tarewar.?
Ina kauda Fuskata nace"Wai fa yace da ya dawo"
Nafada kamar zan yi kuka suka kwashe da Dariya har da tafawa.
Nan fa suka fara min mganar gyara nace bazan yi ba Nana Fatima tace"Zaku gamu da Ammi"
Ina jin haka na zaro ido nasan Halin Ammi mutumcina zata ci.
Sai wajen uku na Dare suka kwanta ni dai sai da nayi raka'a biyu nayi ma Allah Godiya sannan na kwanta,shiyasa muka makara sallar asuba sai da aka rika bugamana kofa da karfi.
Da safe ma daganan akayi abun karyawa aka kaima su Abba,kuma sai da Safen na kunna Wayata da Sakon Engr na fara cin karo.
"Fatan kin tashi lafiya Amaryan Abdulbasit?
"I love u"
Na lura baya son yana yi min Turanci Saboda kada na rika jin kamar zai kureni Allah Sarki Engr sai ya koma Daidai dani mun taba mganar karatu da shi nace masa bana ra'ayi kai Tsaye yace"Bokon banza Bokon wofi kin burgeni wlh meye a bokon ban da wahala.?ke ce mai ilimin duk duniya Tunda kinsan Qur',ani da Hadisai ni kaina kamar na kwashe bokon kaina na Kona haka nake ji"
Alokacin bansan Dariyan da nayi ba,Shi komai nawa ya gama yi masa ba shi da wata matsala.
Tun Safe nayi wanka na cakare da Wani materil Doguwar riga ya kuma yi min cif mayafi dai suka yi sukayi na saka nace Hijabina zan saka.
Yace min daman kafin ya tafi zamu yi mgana,bamu yi waya da Safe ba na dai yi kokari na tura masa amsar da cewa"Lau na tashi Ya Tosin din Faa'iza shima ya tashi.?
Sai bai bani amsa ba kuma bai kirani ba nafi Tunanin ko yana waya ko kuma wanu uzuri ya rikesa.
Wayar tana hannuna ina jiran kiransa sai naji kira na dauka jikina na rawa na zata shine sai naga bashi ba ne Zainab.
Sai da jikina ya yi sanyi ina Dauka ko sallamata bata amsa ba tace"Shikenan sai ki yi mana haka Maman Amir..?
Ta fada a sanyaye cikin wani yanayi nace"Ba haka ba ne Zainab shi bai fad'amiki yace baya son Datti a gidansa ba..?kinga kuwa tunda ni Datti ce ya kamani da kwarto bai kamata kuma na koma masa ba"
Cikin damuwa tace"Duk ya fad'amin komai wlh yace kishin ki ne ya rufaimai ido ammh ba har zuciyarsa ba haka ba ne,ga shi nan da zazzabi ya Dawo sai rawan sanyi yake yi yana kuka yana Kiran sunan ki"
Sai naji dadi ko banza shima zai ji abunda naji acikin raina.
Cikin Mirmishi nace"Allah ya ba shi lafiya bani da abunda zan yi masa bakin Alkalami ya riga da ya Bushe zainab.."
Cikiin wani irin sanyu tace"Yanzu shikenan Maman Amir..?
Sai naji nima Tausayin ta ya kamani Cikin karfin hali nace"Shikenan ba shikenan ba. akwai amanar ya'yana a wajen ki zainab ki kularmun da su ki yi kuma Hakuri da su ki yi musu Gyara a inda suka yi kuskure, Allah me ya had'amu ba Ishaq ba saboda haka bai isa ya rabamu ba zamu cigaba da waya da zumuncin mu in sha Allah"
Cikin Tausaawa tace"Hakane ina yi miki Fatan Alheri Allah ya bada zaman Lafiya"
Na amsa mata da Ameen ina so na tambayeta yaran sai kuma na kasa haka muka rabu zukata ba Dadi.
Ita kanta Zainab tasan Alhakina ke Bibiyan Ishaq,daman tun kafin dawowarsa Daddy ya kirata ya fad'amata ga yadda abun ya kaya ta sani har ga Allah bata bakinciki da Dawowar Fa'iza ammh tayi farinciki da ya rasa ta, ko domin haka ya zame masa izina gobe ko kashi ya aura sai ya san yadda zai iya Daraja shi.
Ni ko muna gama waya na bama Nana Fatima Labari daman tana Dakin cikin Tausayawa tace"Allah sarki. Sai ta bani Tausayi,ai yaran suna gidan Anty Fadila tace jiya tana gidan Baban zainab din ya kira yake fadin abunda ke Faruwa, sai ta tafi da su kada su ji labari su fara kuka tunda suna ta Murnan Umman zata dawo"
A raina nace"Ai ko Umma bazata Dawo ba har Abada"
Naji ma damu ammh jin suna tare da Anty Fadila sai naji na samu natsuwa.
Sai wajen sha Daya su Abba suka shigo muna daki Badariya tazo tana Fadin ga su Abba chan har da Engr sun zo gai da su Inno da su Goggo.
Ni dai leke nayi ta yi ta Labule har da Dr.Lawal mahaifin Zainab ko kunya.
Ni dai gwanina na rika d'age ina son gani a chan na hangosa kasa gaban su Inno kansa duke ya sanya Shadda mai ruwan kasa hular kansa na hango duk da yana Duke ne ammh duk yafi su Abba tsawo shiyasa na hangosa.
Sun jima ana ta dai yan nasihu kafin Naji ana cigiyata kamar an jefoni haka na fito daman na saka Hijabina har kasa,nasan idanuwansa na kaina shiyasa ban yarda na Dago mun hada ido ba. har kasa na duka na gaida su Abba.
Inno ce ta kalli Engr tana fadin"To kai Ango an ce kuma zaka yi tafiya kasashen Turawa wa zaka bar ma amanar amaryan taka..?
Tafada cikin zolaya kai tsaye yace"Nan zan bar muku ita Hajiya har sai na dawo sai ayi shirin tarewar nata in sha Allahu"
Sai inno tace"Au to na zata ai wayau zakayi mana ka dauketa kai kaita cikin yan'uwan ku yarbawa"
Gabadaya aka saka dariya tunda cikin Sigar wasa tayi mganar shi ko sai so yake mu hada ido naki yarda ina zan yarda ya bani kunya gaban su Abba.
Sallama ya yi musu bayan ya sauke ma su Inno kudi suna ta saka albarka Abba ya gabatar da Dr.lawal sai kika ji Allah Sarki na tashi.
Da suka fice kasa fita nayi ina kunyar Abba sai da Ammi tace naje mu yi sallama da mijina,ko alokacin kasa bin shi nayi sai da ya kirani a waya yana Fadin"Kuna shikenan zan tafi ban yi sallama da iyalina ba Faa'iza.?
Dole na fita yana zaure su Abba kuma na waje jikina ke kyarma na zata zai rikeni ammh wlh ko Tafin hannuna bai Taba ba,sallama kawai mukayi ana ta kiransa a waya yace zamu tattauna in ya samu natsuwa haka ya tafi yana Dagamin hannu ina Dagamai kamar kada ya tafi.
Koda na dawo cikin gida sai naji kewa sai dai fa har suka isa Abuja muna waya kamar ta bakinsa manne mata makale mata kenan..
Washegari Litini su Abba suka koma Kaduna Yaya Asiya ma ta koma kano,Badariya ma Direba yazo ya Dauketa ta Dau Hanya Gida ya rage dagani sai Nana Fatima sai baba Ati,Inno an tafi da ita Saboda zuwa asibiti.
Nana Fatima sai talata ta tafi Ammi taso na bisu nace mata zan taho Daga baya tace gyara zatamin na sosai,Nima ina son na gyara din Domin Farincikin Engr shi kadai nake so tunda nima yake sakani Farinciki shima ina son saka shi,100k ya turomin yace kada na kara tambayan Abba komi shi zai yi min yanzu sannan bai ce nacigaba da wannan sana'ar na wahala ba, sai mun tare sannan zamu zauna mu zamanantar da al'amarin yadda bazan rika wahala ba., Yana chan fa bai barni ba daya samu Sarari sai ya taboni,sai dai ko in aiki ya yi masa yawa na rasa wani irin so Engr ke yi min haka Mamansa da Yan'uwansa ya basu lambata haka zasu kirani suna gaisheni Mamanshi kuwa ba dai kirki ba in ta kirani haka zata rika ce min"Ba dai matsalan komai ko..?
In nace mata babu sai tace Allah ya yi muku albarka dukkan ku Allah ya baku zaman lafiya"
In na fad'amai sai yace"Sweetheart haka take bata da damuwa Faa'izaa"
Yana chan mun yi mganar Lefe sau daya yace dai sai ya Dawo mganar in da zan zauna ma yace ya fasa bani Zabi yaga in ya Biyemin zan cuceshi ne.
Saboda zan zabi nesa da shi, shikuma wlh kara'in Holewa zai yi ba ruwansa.
Engr. Uhmm sai da na had'u da shi na farajin ashe nima macece kamar sauran mata..?
Shi d'in ya wuce namiji,gwarzo ne ta kowani Fanni.
*Janafty*
[7/31, 3:09 PM] U.M Collection ZMFR CM: *KNKB3016*
*TASTED & TRUSTED*
*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATUN SAIWOWIN MUTANAN CHADI DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZAR AMARE, MASU JEGO DA WADDA TAKE SON GYARA KANTA*.
*AN GWADA ANGA INGANCINSA SHIYASA NA KE TALLATA MUKU DA K'ARFIN GUIWATA*.
*ABIN BIRGEWA DA WANNAN SAIWOWINRL ZAKI YI AMFANI DA SU SAMA DA SAU DAYA.*
*AKWAI FULL PACKAGE, AKWAI RABI, TA YADDA KOWA ZAI IYA SIYA*.
*SANNAN BABU BAURI NA TASHIN HANKALI.*
*DA KANKI ZAKI DAFA ABAR KI, KOMAI ANA SAKA WA A CIKI*.
*SHIN KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR, KO KUWA KE CE KIKE SON GYARA KANKI?*.
*KAYANA NATURAL NE DOMIN SAIWOWI NE DA AKE HAKOSU A DAJIKAN CHADI. BAYAN SAUKAR DA GAMSUWA HAR YAQI SUKE YI DA DRYNESS DA KUMA INFECTIONS.*
*AKWAI NA TSUGGUNO DA YAKE HA'DE MACE TA MATSE.*
*AKWAI HADADDUN DAKA NA SHA DA MADARA KO NONO WANDA BABU ALGUS*.
*SANNAN AKWIA GADALIN MATA NA ASALI, WANDA SHA YANZU NE MAGANIN YANZU DA IKON ALLAH*
*DUKKANSU TESTED & TRUSTED NE*.
*TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU*
*08032773332*
*DOMIN KARIN BAYANI, SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*.
*NATION WIDE DELIVERY*
*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*
*09069067488*
*ENGINEAR ABDULBASIT ABDULGHAFFAR OLUWATOSIN*
Sheik Abdulbasit Abdulfattah Oluwatosin shine asalin sunan kakan Engr wanda ya haifi mahaifinsa.
Su asalin su tun tale talen kakan kakannin su yarbawan Ilorin ne, ammh aiki da kasuwanci ya sa suka tashi garin Benue ,ammh ba Haifafun nan ba ne, nan dai suka girma suke kuma gudanar da Rayuwarsu a tsakiyar Birnin Beneu State.
Sai dai aiki da karatu na fidda wasu Daga garin ammh kusan dukkan su ba su da tushe ko asalin daya wuce garin,Ilorin kuma shine Tushen su.
Sheik Abdulbasit Abdulfattah ba bahaushe ba ne iyaye da kakkaninsa duka yarbawa ne,ammh sun fito daga Tsatson gidan malamai ahalin sunna Shiyasa ba sa kyamtar Hausawa ko wasu yarukan, suna auran junan su sannan sukan yarje ma mutum ya auro dukkan yaren da ya yi masa ma'ana babu tursasawa ko takura da lalle sai ka auri yar'uwan ka bayarbiya.
Kuma hakan ya samo asali ne ga ilimin zamani da na addinin da ya lullube su kuma ko a garin Benue gindom din su na malamanta ne. shiyasa kaf zuru'an Abdulfattah a garin Benue ba wanda bai san su ba.
Daga cikin ya'yansa sai aka samu wanda ya yi gadon sa shine kakan Engr wanda ya haifi mahaifinsa Sheik Abdulbasit Abdulfattah Oluwatosin wanda sunan shine Engr ya ci, Ma'anar Oluwatosin da yarbanci shine God is worthy to be Saved,tunda su a al'adan su ko da an saka maka sunan yanka wannan al'adace za'a rika kiran ka da sunan ka da yaren su ko da na ranar da aka haifeka ne.
Mahaifin Engr, Mr AbdulGhaffar Abdulbasir Babatunde,shi kuma ma'anar Babatunde da yaren yarbanci shine The Father return,shi ne kusan manyan ya'yan Sheik Abdulfattah,yana da yayye maza da kanne mata,kusan dukkan su sunyi ilimin zamani da na addini matan suna Gidajen mazajen su suna aiki wasu kuma suna kasuwanci mazan kuma kowanne ya kai mataki mai girma na karatu kuma suna aikin gwammati. suna garuruwan da aiki ya ijiyesu duk da wasu har a yanzu suna garin Benue da zama su da iyalansu.
Hajiya Kudurat Olaminde,itace kad'ai matarsa da tayi masa takaba sauran matan sa guda biyu duk sun rigasa mutuwa kuma Hajiya Kudirat Abdulghaffar kad'ai ta haifa ya tsaya sai da ta binne tara reras a kasa suna rasuwa sannan shi ne na goma Allah ya raya mata shi,shiyasa ya samu dukkan gatan duniya da kowani d'a kan samu a wajen iyayensa.
Mr Abdulghaffar Abdulbasit a london ya hado Degree dinsa na farko kafin ya zo Usman dan fodiyo University Sokoto ya yi mastering Degree dinsa. ya zama Cadet na EFCC Officers tun wanchan Lokacin.
Ya fara aiki da EFCC a matsayin Assistance Detective superintendent(ADS) kafin jajircewan sa a aiki yasa ya samu karin girma zuwa Deputy cheif Detective superindent (DCDS),Mr Abdughaffar ya yi gwargwamaya sosai a aikin sa Saboda yana da ilimin matakin Kwalin Degree hudu garesa a mabambata kwasakwasai,Sannan kuma ya yi anragama da masu cin hanci da rashawa da masu d'iban kudin gwammati kama daga yan siyasa ma'aikatun gwammati dabam Dabam kuma ya yi nasara shiyasa tsawon shekaru Tara yana nan a matsayinsa na Chairman na EFCC gabadaya.
Mr Abdulghaffar da yaransa ke kiransa Papa yana da mata aure guda Daya Hajiya Shukra wacce ta kasance bahaushiya ce gaba da baya mazauniyar kano, kuma haifaffiyar kano din ce sun hadu ne a sokoto inda yaje degree dinsa na biyu itakuma taje hada Degree dinta na farko a kan Economis.
An yi soyayya kamar me,Itana ganin D'an mutan Beneu ta rude shima yana ganin asalin bakanuwa yaji duk duniya ba wata sai ita,kuma da yake yasan Family dinsa basu da matsala Sai ya saki jiki ta bangaranta ne aka so a samu matsala Tunda tun a baya mahaifiyarta Hajiya Tafeesu mafadaciya ce ta dinga fad'an yarta bazata auri yarbawa masu kashi a leda ba, sai da lokacin dangin mahaifinta da suka yi binciken gidan su Mr Abdulbasit suka kuma suka ga cancantan suka bashi auran Hajiya Shukra sai ga shi ko gidan da take ciki yanzu a kano shi ya gyara shi ya zuba mata ma'aikata sannan babu abunda ta nema ta rasa,sai gashi Hajiya Tafeesu tafi kowa jin dadin Yaron yarbawa masu kashi a leda, a cewarta ko banufe ne in dai nagari yazo zata bashi aure ta fahimci a kowani yare akwai na banza kuma akwai na kirki.
Sun yi aure lokacin Hajiya Shukra ta gama karatunta a Benue suka fara zama tare da mahaifiyarsa Hajiya Kudurat,dalilin haka yasa ita bata cigaba ba,Saboda aikin mijinta ba na zama waje daya ba ne.
Suna zaune lafiya cikin soyayya da kaunar juna ba su da matsalan komai,matsalan su ma farko shine sai da Hajiya Shukra ta shekara biyar da aure sannan ta haifo d'anta namiji mai kama da mahaifinsa sai dai ya Dauko hasken mahaifiyarsa.
Bayan haihuwan Abdulbasit da yaci sunan kakansa Suna kiransa Oluwatosin sai da hajiya shukra ta shekara ashirin bata yi ko batan wata ba har sun fidda rai da kara haihuwa Allah mai kyauta da kari ya kawo Rabon Cikin yan biyu,cikin da ya wahalar da ita kamar bazatayi rai ba aiki akayi mata a wani asibiti dake India sannan aka ciro mata santalan santalan ya'yanta guda Biyu.
Wadanda suka ci sunan Kafayatu da Sharifatu.
To a yaren su yan biyu ana musu lakabi da Taye da kahinde bayan kuma haka suna da yarouba name din su,Bimpe da Erimipe,koda suka taso sun iske su Abdulbasit ya riga ya girma ammh duk da haka akwai shakuwa mai girma a tsakanin su sannan iyayensu sun yi kokarin basu Tarbiya,in ka gansu bazaka taba cewa sun sirka da wani yare ba sai dai ta Harshen su,kuma sai ma sun juya harshen ake ganewa.
Gwara ma su kayafatu ana gane suna da jini da yarbawa saboda suna yawan zuwa Beneu hutu da kuma sanin kan wasu al'adunsu nasu kamar yanayin Shigar su da sauran su. sabanin Engr da makaranta kwana ya yi sannan shima University of Ibadan ya yi Degree dinsa na farko sannan ya tafi London shima ya hado Degree dinsa na biyu akan Chemical Engineraring, bayan haka ya hallaci manyan manyan kwasa kwasai a kashashe ketare akan abunda ya karanta ya fara da aiki kamfanin Narka karfe a garin Lagos na shekara Hudu kafin wani Uncle dinsa Uncle Tobi ya sama masa aiki a Edo Refinary and petrochemical Limited na karkashin Jahar Edo_Ekiti.
Engr mutum ne na gari mai dattako da sanin ya kamata, duk wanda ya zauna da shi ko na kwana Daya sai ya tafi da Labarin karamcinsa.
Yana da barkwanci da Dad'in zama Mutum ne da yasan abunda yake yi,Ta dalilin Hajiya Shukra da ya ke kira Sweetheart su kuma su kafayatu suna kiranta Mah,ita kuma Hajiya Kudurit Granny ya san Engr Usman karaye saboda suna makota a gidan su dake kano, Dalilin haka har yasan abunda ya karanta ya kuma karbi Takardunsa ya nema masa aiki a NNPC dake kaduna da kuma matsayi mai girma kafin Abba ma ya nema ma mutane aiki da suka zama wani abu sun fi Dubu,haka ma bayan Haka kowa aka kira sunansa sai dai kaji ana fadin nagartansa da irin kyawawan Hallayansa,sannan in ba shi ya fad'i cewa shi ba bahaushe ba ne, yaroba ne,ba mai ganewa ko kuma in anji karshen sunansa tunda tun yana karami har girmansa bai cire Oluwatosin a sunansa ba,yace a san mutum asan Dabi'arsa da Rayuwarsa da inda ya fito ya fi asan ka batare da an san ko waye kai ba.
Engr ya je kasashen ketaren da baza su kirgu ba,tunda aiki na yawan Fitar da su waje to karshen wayewa yana da shi,sai dai mata basa gabansa ko a cikin Danginsa akwai masu son shi ammh baya maida kai.
A chan family din su kowa da Tosin yake kiransa Papa kuma yace Oluwatosin,Maa tace Babatunde Saboda sunan surukinta ne kannensa kuma suna kiransa Brother Tosin,a wajen aiki da mu'amalansa da mutane kuma Engr Abdulbasit ne,yana da kyakyawan shaida wajen mutane da wad'anda suka san shi daman wad'anda basu san shi ba.
Engr mata basa gabansa ya jima bai yi aure ba, sai da ya shekara talatin da Tara har kannen sa su kafayatu sun shiga jami'ar Abuja,Maa ce ta ke damuwa shi Papa ba ruwansa Oluwatosin kamar abokinsa yake haka zasu zauna su yi ta hira ba ruwan shi haka da Uncle's dinsa kamar wani kanninsu haka zasu riga hira suna Dariya shi mutum ne mai Sakewa mai al'amarinsa ba kumbiya kumbiya mutum ne simple,ba kowani Lokaci ake iya ganin Rauninsa ba. yana dakiya da juriya mai naci kan abunda ya sakama gaba mai kyauta da Alheri.
Sister's dinsa kuwa in kaji suna Brorhers Tosin kaza kaza,ya riga ya nuna musi bayan yaya shi din dan'uwan su ne da basu da kamar shi kamar wani kaninsu haka yake shigewa cikin su ana hira har da Shewa Maa ita bata da Hayaniya sosai ammh fa duk abunta in Tosin na gida sai ta saki jiki an sha hira sai dai bata yin irin yadda Papa ke yi ki ga har suna tafawa da Tosin ko suna mgana ta kunne ko su hada kafada ga shi tsawon su d'aya sai dai shi Tosin har yafi Papa budewa na jaruman maza.
Abdulbasit Abdulghaffar Oluwatosin Dogon namiji ne ingarma kalarsa kalan Chaculate ne kalan yan maroco ne,sannan yana da karan hancin Paapa,kuma ya Dauko Doguwar Fuskar Maa,sai idanuwansa masu girma kamar na mace,yana da bakinsa mai Fadi kadan sai ya tsuke yayi Tudu kamar na mata,hakoransa masu haske da walwali yana da cikar gashin ido da na gira ba ma'abocin tara suma ba ne shiyasa duk sati sai ya yi aski,Mutum mai Fara'a da mirmishi cikin kowani Hali wannan mirmishin baya Bacewa daga Fuskar Engr.
Matarsa Tauhidat da ya aura ta rasu Diyar yayan Papa ne Abdulwasiyu,Hajiya Kudirat ta matsa sai da akayi auran asali ita ke son shi Tana zuwa Hutun gidan su na Abuja kawar su Kafayace,shi kuma baya sonta ammh Yanayin yadda granny ta rikice ne kuna ga shi Lokacin an gano tana da matslan koda,saboda ya faranta mata yasa ya amince ashe auran ba mai dadewa ba ne,A chan Benue duka aka yi shagalin bikin su daganan suka wuce Edo gidansa dake chan duka duka Sati uku ne yana wajen aiki ta kunna gas ya tashi da ita duka gidan ya kone ko Tsinke ba'a Fitar ba gawarta ma duk ta kone sai k'ashii.
Bazai ce bai shiga damuwa ba. tunda Tauhida na son shi,shi kuma mutum ne daya san Darajan dan adam barin ma mace,sai yake biye mata kuma dai bai yi wasa ba ya haikemusu yar yarinya yana ma tsaka da moran auren ne ta rasu to shiyasa ya shiga Damuwa kuma dalilin haka ne aure ya fita ransa,Lokacin da za'a cire ma hajiya Kudirat koda a yi mata dashen na siya da akayi har rigima ta tada akan sai Tosin yayi aure yako ce gaskiya sai dai in yanzu zata karisa mutuwa ammh matukar ko aurensa take jira ba yanzu ba,Dole ta shafamai Lafiya.
Lokacin da yaje ma da Maa da papa da mganar Fa'iza duka fatan alheri suka yi masa suna jin dadin Tosin zai kara wani auren,basu zata abun zai zama cikin gaggawa ba shiyasa achan Benue ba wanda yaji sai labarin auran sukaji Daga sama Dayake mutane ne masu Fahinta paapa na musu bayani suka gane sukace in za'a tare nan benue zai kawota ayi shagalin al'ada.
Farinciki ya cika su kayafatu Shiyasa suka amshi lambar Fa'iza suna kiranta Domin duk abunda Brother Tosin yake so suma a wajen su abun so ne da Girmamashi.
Gidan Papa dankarare ne yana nan a Gwarinpa,Shi ma kuma Engr yana da Dankareren gidan a Apo dake garin Abuja sannan yana da wani Edo bayan gobara ya bata wanchan sai ya Saida ya siya wani a anguwan Benin City,a garin Benue ma suna da gida inda suke sauka inda sun zo kato mai bangarori da dama. kaf ahalin su ba alfahari ba,babu talaka suna da kudi suna da ilimi sannan suna kasuwanci.
Suna kuma da kowani yare acikin su ba kyama da tamgwama,har balarabiya Kanin papa ya auro daga sudan,wani kawun su ma na auran baturiya,acikin yaran su matasa irin su Tosin akwai wanda ya auro Bafullatana acikin Ruggar jigawa. shiyasa nace suna da hausawan suna kuma da turawa da larabawa da kuma Yarbawan, shiyasa basa ka ma da ya'yan su sun fita daman kamar ba su hada jini da yarbawa ba.
Ammh ba su bar gida ba,yara da manya sun yi kokarin koya musu yaren su saboda duk inda suka shiga a gane su ko ba ta kammani ba.
*******
Na dauka yara na za su yi rigima ko kuma zasu raunana kamar yadda na zata a farko sai dai kuma Alhamdulillah da sukaji bazan dawo ba basu yi rigima ba,Ahmad ne kadai yayi kuka shima din Amir da Anum sun lallashe sa,Hatta Anum bata yi kuka ba inaga Amir me ya yi mata mgana da suka kirani ta wayar Jamal Anum kamar Babba sai ce min tayi"Umma Yaya Amir yace sabon Babanmu shima mai kirki ne yace zai rika kawo ki kina ganin mu, muma zamu rika zuwa muna ganin ki"
Mirmishi kawai nayi cikin jin dadi kafin nace"In sha Allahu. Anum ki kula da kanki sannan ki kula da sauran kannen ki Karatun Qur'ani da azkar salla akan Lokaci Anum ban da rashin,jin mgana komai Antyn ku ta sakaki kiyi kin ji ko..?
Ta amsa min da Toh Umma sannan muka rabu sai hankalina ya kwanta,da jin yarana suna lafiya,Sai dai ance shi Ishaq din bashi da lafiya har da su kwanciya a gadon asibiti,
Abakin yaran na fara ji sannan da muka yi waya da Badariya take kara fada'min jiki yaki dadi.
Likitoci sun ce jininsa ne ya hau da kuma Damuwa a raina nace"Dakyau! Shi sai yanzu ya samu nashi hawan jini..?kafin shi ni ya fara sakama hawan jinin"
Ban fad'a a fili ba saboda ina jin nauyin Badariya har ga Allah ban ji tausayin shi ba,Itama matsaloli duk sun sha mata kai uwar mijin ta kara matsa lamba tunda bata samu ciki ba,tana mganar sai Yusuf ya kara aure,Kullum Badariya ta kirani ko tana kuka ko tana cikin damuwa,Ni ce ma ke tausanta da Hakuri tunda mijinta na sonta kuma yana kaunarta kawai matsalan uwarsa ne da matarsa.
Ni dai ba ni da matsalan komai a rayuwata ko da yaushe muna makale a waya ni da Engr mun kara wata irin shakuwa kamar mun shekara da Haduwa,tunda yace kada na sake yin wani abu ban kara ba iyaka dai ina Taya Goggo dafa zobo tunda ita na barma sana'an tun tafiyata Kaduna,Aikin Dambun nama su jummala na barmawa ko an kawo sai dai nace akai musu hatta da Hadin Turaruka sai dai in An matsamin ni zan yi tuni na samu Hutu nayi kiba nayi haske kamar bani ba.
Ina cin mai kyau ina shan mai kyau,kuma ina shafa mai kyau tunda ni da kaina nayi ma kaina fada ina Shafa mayuka masu tsada saboda gyaran jiki.
mun yi mgana da shi na kayan lefe yace in ya dawo kudin kawai zai bani na siya abunda nake so mganar gida kuma a Abuja zamu zauna bayan mun Dawo daga benue sannan yana Tashi komawa wajen aiki Edo state kafarsa kafata ln nace to tosin ranka ya Dade sai shi kuma yace yauwa yar matata Bolawatifenisola(Tife) sunan da ya samu kenan da yarbanci ni sai dai nayi ta dariya na ma saba har amsawa ma nake domin daya kirani ina Dauka zai ce"yar matata Tife kina lafiya..?
Sai nayi mirmishi in ce"Ina lafiya mijina Tosin"
Rayuwa muke gudanwar cikin aminta da juna ba gundura ba kosawa,Sannan in nayi abu baya so kai tsaye zai ce min"Gaskiya Faa'izaa ba na son abu kaza..kaza nake so"
Shi dan Afadi mgana ce ko yaya zaka Dauka shikenan shidai ya fad'amaka iya gaskiyansa,Mutum ne free da bai da kwana kwana acikin lamarinsa kuma in ya fad'i mgana hakan take daga karkashin zuciyarsa.
Labarin aure na da Engr har ya kai kunnen Hajiyar Dala ba kira tayi ba har Karofi tazo,ta same mu ni da Goggo tana ta kananun mganganu tun suna daki ita da goggo da ta fito zata tafi ina falo ina yanken kumba ta kalleni sama da kasa kafin tace"Yanzu ke Faa'iza ki ka k'i dan'uwanki. saboda Bayarbe ko..?
Mganarta tamin ciwo sai dai ban tanka ba kuma kaina na kasa ban dago ba sai ta tabe baki kafin tace"Ko da yake an ce yana da kudi masu gidan rana baza'a damu da Yarensa ba. Ammh wannan abun kam ba tsari ki ki' bahaushe dan'uwan ki ki auri bayarbe asalin yarbawan ma na garin Benue"
Na kasa juran wannan cin zarafin nata Goggo ce ke fadin"Fatan alheri zaki yi mata kuma kada ki manta wani baya auran matar wani"
Kamar an goggo ta watsa mata ruwan zafi haka ta yarfa hannu tana fadin"Wannan karatun ki ne .Ammh ni ba kudi ba ko duniya ya tara in dai bayarbe ne bazan bashi auran y'ta ba. ai gwara banufe da bayarbe."
Dagowa nayi ina kallon Hajiyar Dala kafin nace"Shi Bayarben ba musulmi ba ne..?
Na fada idanuwana suna kallon nata kawai sai tace"Musuluncin su bai cika cika Daidai ba.
sunan dai suna musulmai ne"
Nima yadda bataji kunyar gayamin mgana ba nima ban ji ba sai kawai na mike ina fad'in"Kamar yadda a muma Hausawan ana samun b'ata garin addinin musulunci da wad'anda basu cika daidai ba da kuma wadanda suka cika shi daidai suma kamar hakane,Daya muke da su bamu da bambamci musulmai ne su kamar yadda muke musulmai masu imani kuma shi Addinin Ubangiji ba ruwansa da bambamcin yare duk Daya muke a wajensa bai bambamta ba sai wanda yafi jin tsoronsa, ya fi so kuma ban ga Nafsin ko aya da Hadisin da yace kada mu auri wani yare sai namu ba.
In kuma da Aya ko hadisin da ya Haramta aurena da Engr ki fada'min Goggo kila su Abba sun samu makuwa ammh yanzu in kika Tunasar damu sai kila mu gyara kuskuran mu?
Daga ita har Goggon sun yi mamakin kalamai na ita ko kasa mgana tayi saboda bata da abun cewar ganin haka yasa na kakkabe jikina na wuce daki ai sai ta fara tafa hannu tana fadin"Kina gani ko..?ni yarinyar nan zata yi ma rashin kunyar don na fadi gaskiyata.?
Ni dai naji Goggo da ke biye mata tana bata hakuri ko kara sauraran su ban yi ba araina nace ai na bar kara yin shuru a rika raina min wayau ana Dannen min hakki shi bahaushen da na aura dan'uwan nawa me ya tsinanimin..?ban da bakin ciki da takaici, Allah na tuba da wani Bahaushen ai gwara wasu yaren sun fi sanin Darajan mata da sanin amfanin su.
Ba irin wasu mazan mu na Hausawa ba. da suka maida mata jakuna ababen biyan bukata masu cikin haihuwa,da wahalhalun duniya Allah dai ya sa mu dace a kowani yare akwai nagari akwai na banza sai fatan mu dace da had'uwa da na garin.
*****
Ba iya ni kadai ba hatta Abba,Engr ya fad'amasa da zarar ya dawo zan tare sai Abba ya kirani a waya akan nazo yana son mgana dani,daman kuma ina son zuwa,tsaikon ma da na samu Anty nasara ne suka dawo sun yi tafiya zuwa kasar Ghana inda dangin mijinta suke wajen watanta uku duk bata nan ma akayi aurena dayake kuma na tayata gyara gida da sauran su.
itama da taji abunda ya faru tamin murna balle da taga yadda bini bini muna manne da Tosin di'na a waya yana min hira ina Dariya sai ta tsinke da lamarin balle kuma wajen kwana uku nayi a gidanta yana ta magiyan kada nayi aiki duk nagaji so yake kafin ya ganni na zama Tife, din gaske ina jin haka na mika ma Anty nasara wayar suka gaisa kai tsaye yace"Gaskiya Anty ki yi hakuri anemi wacce zatayi aikin zan biya. ke kinga ya kyautu ango na wata duniya yana kuma son in ya dawo yaga amaryansa tayi bulbul tayi kyau sai kuma ya ganta duk a jime..?
A yankwane..?
Anty Nasara na dariya tace"Ina fa mu kanmu bazamu so haka ba. zamu fi son ka ganta shar da ita ai mu a dad'in mu ne"
Yana yar dariya yace"To ina godiya Anty daga gani kina so kanin naki ya zuba shagalin sa"
Haka ya saki jiki suna ta Hira sai da suka yi sallama ta bani wayar kawai sai yace"Gaskiya Anty nasara dagani yar kara'i ce ita"
Dariya na tsintsire masa sai kuma ya rage murya yana fadin"Ke kuma saura ki fad'amata sirri ne dai tsakanin amarya da ango"
Aiko muna gama waya na gayamata ta sha dariya kafin tace''Ya ko fad'i gaskiya yar kara'i ce ni kuma zan mara masa baya ya yi kara'i"
"Masha Allah Fa'iza Wlh nayi miki murna kin samu miji irin wanda kowacce ke fata,ina miki fatan wannan kaunar da yake miki har tsufan ku"
Na amsa mata da Ameen ina bata labarin irin halin Engr da kuma inda yace zan zauna da garin su da zamu je su yi nasu shagalin.
Cikin sanyi na nace"Ni fa ina so na zille wani irin shagali Anty nasara kamar wasu yara..?
Anty nasara ta ballamin harara kafin tace"Ke dallah ja chan daman nasan sai kin taba halin wlh sai mun yi shagali zuwa Benue ba fashi muma mu ci zani da alaku mu saje cikin yarbawa sai kiji akaro na tashi bazaki ganemu ba"
Tana dariya ina Dariya ta cigaba da fadin"Kuma wlh gyara zaki yi malama na jiki da chan kasa gwara dai a gyara mai yaji dadi.ttunda shima yace yana son ya yi shagalinsa"
Ina rufe ido nace"Anty Nasara kada ki lalatani"
Duka ta dakamin tana fadin"Shegiya ki gwale kafa ki haifi ya'ya har hudu kike kiran zan lalataki. ?
Kaji min wani iskanci wajen Fa'iza..?
Ina dariya ban ce komai ba nasan ko na bude baki na shekara ina mgana ba wanda zai yarda cewa ban san komai a harkan auratayya tsakanin miji da mata ba. shiyasa nake mamakin yadda su Anty Mariya suke rawan jikin gyara Saboda maza ina mamakin me suke ji..?domin mganar gaskiyan bansan dadin da suke mganar ana ji ba.
Shiyasa ni wlh ban damu ba. shima Engr sai dai yayi mganar zai yi kara'i ammh wani mganar daya danganci haka bai taba hadamu ba.
Anty Nasara tayi ta bani shawarwari tana ta nanata mganar gyara nace mata Ammi nachan na jira tayi dariya kafin tace"Shikenan ma nasan Ammi bata da wasa mu in kin raina mu ita kaniyarki zata ci"
Kamar ko ta sani Ammi akwai wasa da Dariya ammh in taci Serious kowa shiga taitayinsa yake yi.
Engr na da saura kwana goma ya Dawo Abba ya turo Direba ya Daukeni zuwa kaduna ina zuwa Ammi Daman na jira na turarukan wuta da Humra da kwallacha tace ni zan yi ma kaina Dilka da Halawa kuma tace na hada ruwan yin sa akwai wacce zata zo tamin har gida.
Abba kuma mun zauna da shi kan mganar kayan daki nace Engr bai min mgana ba sai yace na tuntubesa saboda aje a jeramin komai a muhallinsa da na yi masa mgana sai yace"Matas rabu da Abban naki kawai duka gidajena ba abunda babu ina kuma zai yi tunanin saka wani kaya ban da rigima..?
Alamun dai baya bukata ina fadama Abba yace"A'a kamar kowacce y'a kema haka zan yi miki ya ware cikin gidajensa ya fadi in za'ayi miki jere ni zan ma kirasa da kaina"
Ai ko an sha muharawa kafin yace ayi amfani da gidansa na malali,duk da shima bangare daya akwai Furnutures,Bangare dayan ne ba komai aciki za'a gyaramim.
Shima yana korafin wai Abba ya ki ya Fahimcesa ni dai na samu na lallashesa ya hakura.
Kudin kayan lefe kuma 500k ya fara turomin tun yana chan ni da Ammi mukaje kano muka yo siyayya,kaya ba ni da kaya ba aakwatina biyar ta siyamin,muka siya kayan da zan fita tarewa da shi da duk abunda bukata Gidan su Ammi muka kwana washegari mukaje gidan Yaya Asiya muka gaisheta taga kayan tana ta saka albarka sannan muka dawo kaduna.
Engr an ce yana da kudi ammh har ga Allah ni baya nuna min yana da shi,in zai min abu daidai misali yake yi min.
Domin Ammi ma da nace mata Dubu Dari biyar ya turomin sai da tayi mamaki har tana fadin"Ko dai yace sai ya dawo zai cikamiki..?nace bansani ba,ni kuma ba kudinsa nake so ban damu ba wlh.
Muna ta shirye shiryen mu Tunda su Goggo sun ce sun barma Abba azo nan a Dauke ni,Anty Fadila tace sai tazo itama sai na roketa akan ta yi ma Baban su Anum mgana ko zai barta ta tahomin da ita.
Tace min zata tuntubesa taji a bakinta nake karajin yasha jinya kwanciyarsa asibiti biyu bayan wanda na sani,duk ya rame ya lalace a kaina tace min har ita yasha fad'amata cewa rashina gibi ne babban ne a rayuwarsa.
Ni ko sai dai fatan Allah ya sauwake domin bani da abunda zan yi masa.
Fatana Daya Allah yasa ya bar Anum din tazo domin zan ji dadin zuwanta.
Kayan Furnitures kuma Abba ya ba ma Ammi kudi anan kaduna ta siyamin komai da komai,masu kayan sukaje har gidan suka shirya komai Tare da Raliya da su Nana khadija ni dai ban je ba ina gida an faramin Dilkar matar na zuwa tamin na rana ni na goga ma kaina na Dare.
Kayan mata kuwa musamman Ammi ta saka aka kawomin kayan sokkoto na tsumi na tsugunne ga gumba ga garin aya da ake sha da madara.
Sannan ga saiwar Gudayo ta hannun Surayya marubuciyar Halin yau.
Ina ta sha wani yana da dadi wani kuma daci sai na Daure nake iya shansu.
Sun dawo suna santin gidan mai kyau Falo biyu Bedroom hudu sai Kichen sannan kowani daki da Tiolet,kuma ko'ina yaji kaya Abba ya kashemin kudi domin kayan alfarma ya yi min kayan kitchen kuma Ammi ta siya sauran su zannuwan gado kuma Nana Fatima tayi su cafets kuma da sauran kayan kamshin girki abubuwa Anty Fadila zata yi.
Hajiyar su Raliya ma ta aikomin da su Dinner sets masu kyau da kofunan shan Tea sai Kayan adon mata na kwalliya kala kala da kayan gyaran fata da na gashi.
Ina da kudi ammh basu barni nayi amfani da kudina ba komai su suka yi min yan'uwana kuma kudi suka hada suka siyamin katon Showglss na Turare sannan suka siyamin Turaren da kwalaben batare da sun fadamin ba,bayan wanda ni na hada da kaina Har hawaye sai da nayi Goggo kuma kayan dake dake tayi min irin su Kuka,daddawa kubewa kayan kamshi,sai kuma suka yi min kayan gara ita da mallam hatta Yaya Abdul'ahad dake chan sai da ya Turo kudi Ammi ta siyamin Dan kunnayen zinare masu kyau aka yi ci ko da sadaki na aka siyamin masu sarka har da awarwaro.
Badariya ma da mijinta ba'a bar su a baya Tv suka siyamin da Freezer babba,Sai frem masu kyau na kwaliyar Daki,Mama ma ni da kaina na kirata na fad'amata ta rika sakamin albarka da fatan zaman lafiya Anty Binta ma ta kirani tamin Fatan alheri har da Halisa rayuwa kenan.
Jamal kuma har kaduna yazo ya yi min murna ya kuma bani Dubu ashirin gudumuwa yana ta bani hakuri nace masa bakomai nagode da farko kin amsa nayi sai da ya nuna bacin ransa sannan na amsa.
Engr na da wata daya da kwana Biyu ya sauka Nageria ta lagos dagachan ya hayo jirgin Abuja.
Kwana daya yayi yazo kaduna ganina Karo na farko da jikin mu ya hadu waje daya domin ina shigowa falon Abba a bazata ya tashi ya Rumgumeni wata irin Rumgumar da ban taba sanin ana yin ta ba.
Rumgumar da har ya tafi ban daina jinta ajikina ba.
Mun fi minti goma ahaka kafin ya sakeni ya dago kaina yayi min kiss a saman goshi kafin yace"Kin yi kyau'"
Kuma ba kwalliya nayi ba,Nadai sha gyaran fata da jiki nayi walwal ina tahin kamshi.
Bai jima ba daman tsaraban America ya kawomin sai mganar wad'anda zasu bi ni zuwa Benue daganan su rakani Abuja,Sai nace zan musu mgana abincin ma da nayi masa kadan yaci kamar yana sauri ashe kada ya yi kara'i ne tun agidan Abba sai da ya tafi ne ya kirani yana Fadin"Kamshin ki ya yi min Dadi Faa'iza. na kusa na turmusheki a falon babanki wlh"
Kunya duk ta kamani bai damu ba ya cigaba da fadin"Wlh na kosa na ganki gani ga ki, na kosa Tife na"
Ni kaina na kosan duk da bansan yanayin abun ba ammh ina son sani ko ba duka ba sai dai kunya yasa ban furtamai ba.
Ammi na fada'ma yadda muka yi ita kuma ta kira su Goggo suka Tattauna an Tsara tafiya da Yaya mariya da Yaya Asiya tunda yace akwai motoci ba matsala,sai Ammi su Nana khadija na gida suna jarabawa Anty Fadila zata zo sai Nana Fatima,Anty Nasara,Anty Amina matar Yaya isa,Badariya sai Raliya da Hajiyar su itama tace har Benue zata rakani. sannan na kira Sa'adatu na fad'amata tace min zataje itama sai ni mu sha Biyu kenan Goggo tace ta wakilta Ammi itama ai uwace sai Halisa da itama Daga baya tace zataje har ma na fad'amasa yawan Mutanen sai kuma Goggo ta kira tace Hajiyar Dala zata je.
ina ji nace gwara taje taga komai duk da nasan abunda zai kaita kenan.
Kai duniyan nan akwai mutanen da duk Daukakan da zaka samu bazasu ji suna sonka ba.
kuma bazasu bar adawa dakai ba, to irin su Hajiyar Dala ce.
*Janafty*
[8/1, 8:55 PM] U.M Collection ZMFR CM: *KNKB3018*
*TASTED & TRUSTED*
*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATUN SAIWOWIN MUTANAN CHADI DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZAR AMARE, MASU JEGO DA WADDA TAKE SON GYARA KANTA*.
*AN GWADA ANGA INGANCINSA SHIYASA NA KE TALLATA MUKU DA K'ARFIN GUIWATA*.
*ABIN BIRGEWA DA WANNAN SAIWOWINRL ZAKI YI AMFANI DA SU SAMA DA SAU DAYA.*
*AKWAI FULL PACKAGE, AKWAI RABI, TA YADDA KOWA ZAI IYA SIYA*.
*SANNAN BABU BAURI NA TASHIN HANKALI.*
*DA KANKI ZAKI DAFA ABAR KI, KOMAI ANA SAKA WA A CIKI*.
*SHIN KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR, KO KUWA KE CE KIKE SON GYARA KANKI?*.
*KAYANA NATURAL NE DOMIN SAIWOWI NE DA AKE HAKOSU A DAJIKAN CHADI. BAYAN SAUKAR DA GAMSUWA HAR YAQI SUKE YI DA DRYNESS DA KUMA INFECTIONS.*
*AKWAI NA TSUGGUNO DA YAKE HA'DE MACE TA MATSE.*
*AKWAI HADADDUN DAKA NA SHA DA MADARA KO NONO WANDA BABU ALGUS*.
*SANNAN AKWIA GADALIN MATA NA ASALI, WANDA SHA YANZU NE MAGANIN YANZU DA IKON ALLAH*
*DUKKANSU TESTED & TRUSTED NE*.
*TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU*
*08032773332*
*DOMIN KARIN BAYANI, SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*.
*NATION WIDE DELIVERY*
*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*
*09069067488*
Sai Dare muka isa garin Edo,gidan Engr na garin karamin gida ne gaskiya.
Saboda Falo d'aya ne sai bedroom guda biyu sai Kitchen haraban gidan ma karami ne bai wuce wajen ajiyan motoci biyu ba.
Sai Dakin megadi sai daga ciki kad'an D'akin waje muhallin da Direba kan kwana in suna gari.
Mun iso da daddare sannan ga gajiya a tare damu tunda tun da muka zo Benue ban yi wani barcin kirki ba,Shi ya sake fita ya siyo mana abincin kayana ma duka shiya shigomin da shi,ni ko sallalolin dake kaina na fara saukewa bayan ya nuna min Tiolet shi kuma da ya fita ina ga ya yi nasa a chan.
Koda ya dawo har na fara barci shi ya tasheni muka ci abinci rabin ma abincin a baki ya bani,muna gama ci na bingire sai barci ko kayan jikina na kasa ragewa shi ya kwashe sauran abincin yakai kitchen ya dawo ina jinsa yana tashina, na bude ido a kasalance ina kallonsa cikin yanayin mganarsa yace"Ki tashi ki yi wanka ko zaki ji dad'in jikin ki"
Luu nayi da ido na zan koma saboda na jini ne gabadaya gabbaina sun saki kamar wacce akayi ma dukan tsiya.
Ganin na sake komawa yasa ya kyaleni ya shiga tiolet din ya yi wanka Saboda baya so ya takuramin.
Nidai bansan yadda akayi ba naji ya gyaramin kwanciya sannan ya yi ta matsamin kafa alamun Tausa naji yana mgana ammh barci yaci idona, bansan me yake fad'i ba ammh dai nasan ya jima ya na min Tausa da ya yi sanadiyar sawa na kara lafewa samman makeken gadonsa ina kara jin Dadin barcina.
Hankalina kwance Allah sarki bawan Allah shima fa a gajiyan yake ammh bai duba kansa ba yafi ji dani tukunnah
Ckin Dare na farka na ganni nannade acikin kirjinsa ba haske acikin Dakin ammh ta window labulen na dagawa Hasken wata daran goma sha Biyar ya haskemin Fuskar sa. ko yana barci Mirmishinsa bai barin Fuskarsa yana Sanye da kayan barci ruwan toka masu Taushi,yana rumgume dani kamar wani zai kwace masa ni sai na shiga wani yanayi yanayin da ban taba sanin akwai sa ba, na miji ya Rungume matarsa su yi barci tunda na auri Ishaq bamu taba kwana waje daya daga farkon Dare har karshe ba. koma wani abu yake bukata yana samun natsuwa zai tsallakeni ya barni wani lokacin ko na koma Daki ko kuma shi ya koma Falo ya kwana ammh sai ga shi bingiren rayuwata ya kawoni inda ban sani ba.
Ina yin motsi ya kara saurin rikoni ya maida kaina saman kirjinsa yana Fadin"Nima nagaji Faa'izaa ki barmu mu yi barci"
Yafad'a cikin wata irin murya ashe yaji motsin tashina,sai kawai na bi Umarninsa na koma na lafe saman kirjinsa ina sauke numfashi nayi barci cikin salama barcin da na jima ban yi kamarsa ba.
Da asuba shi ya jamana jam'i bayan mun idar muka zauna ya yi ta mana addu'an zaman lafiya,bayan nan kuma yace na dauko Qur'ani daman nazo da shi,shima yana da nashi ya fito da shi,shi ya fara jawomin aya daga cikin suratul bakara na dauka sai da na karanta masa shafi biyar sannan ya yi kabbara yace na Dakata yayi min tambayoyi kan abunda ya shafi sallah,alwala da Tsarki ba domin ban iya ba yasan na iya domin cike wani bangaran sunnan ma'aiki.
Muna gamawa shi ya karbi Qur'ani ya ijiye saman Side drower din gadon yana juyowa nayi saurin cewa"Ina kwana"
Mirmishi ya yi min irin mirmishinsa mai narkan da zuciyata.
Kafad'a ya noke min kamar karamin yaro kafin yace"Bana son wannan kalan gaisuwan Tife bana so.
kada mu fara haka da ke"
Cikin kallonsa nace"To wata iri kake so..?
Tsam ya mike ya iso gabana ya saka Hannuwannsa ya Dagoni ya rumgumeni kam na wani Lokaci kafin ya sakeni ya dago kaina ya sumbaci Goshina kafin ya tsaya yana kallona nima ina kallonsa gira ya dagamin kafin yace"Ki rama ma kura aniyarta mana"
Kunya ta kamani na Sadda kaina saman kirjinsa da sauri ya Dagoni yana Fadin"A'ah Faa'iza ni bana son haka sam kunyar me..?ni fa mijin ki me Sirrin ki wanda iyayen ki da yan'uwanki suka damka amanarki a Hannuna ni kuma na karb'a da alkawarin zan iya yi na wajen ganin na rike wannan amanar sai ki bari kunya ta shigo zamantakewar mu ta Cutar dani..?A'ah Faa'izaa..!
Bana so..bana son kunyar nan fa"
Ya fad'a har cikin zuciyarsa sai naji jikina ya yi sanyi na Dago ina kallonsa sai ya lakuci hancina yana Fadin"Nayi miki afuwa na yau ammh daga gobe zaki fara Duty"
Sai na gyada masa kai sake Rumgumeni ya yi ina jin wata natsuwa acikin raina da gangar jikina.
Hijabin da nayi sallah ya ciremin yana Fadin"Jiya kika yi min wayau kika yi barci kika barni ko..?
Ina sunne kaina nace"Nagaji ne"
Shima kai tsayen yace"Nima ai na gajin Faa'izaa sati nawa nayi ina bin Hanya ba kuma tafiyar Jirgi ba"
Sai na kasa mgana Tabbas gaskiya ya fada ya fini gajiya da Sauri nace"To kayi hakuri"
Ina rufe baki ya amsani da fadin"Waya fad'a miki laifi kika yi..?
Sai na rausayar da kaina kafin nace"Nayi laifi mana. muje ka kwanta nayi maka Tausa"
Dariya ya saka lokaci daya yana rike hannuwana ja na yayi muka koma kan gado muka kwanta ya Dora kaina saman kirjinsa yana shafawa kafin yace"Menene na sauri..?
Tausa ai sai kin gaji da yi yanzu dai ki gama Hutawa ni zan kula dake ammh ki sani bashi ne zaki biyani kayana"
Ina mirmishi nace"Kada ka damu Tife zata biya Tosin bashin sa"
Dariya ya saka yana kara rikeni a jikinsa da karfi har sai naji zafi nayi yar kara sai ya sausasauta rikon da yayi min yana Fadin"Ina ji kamar in nayi miki karamin riko zaki iya kubcemin ni kuma bana so nayi rauni wajen rike amanarki Tife na"
Kai tsaye nace"Nasan ai zaka iya.Zaka iya"
Shuru ya yi na wani lokaci ammh bai sakeni ba,har sai na dago kaina ina kalllonsa sai naga shima ni yake kallo maida kaina yayi saman kirjinsa kafin ya kira sunana.
"Faa'izaa..'"
Cikin wata kasalalliyar murya nima a kasalancen na amsa masa,da Na'am sai kuma ya yi shuru har sai da nace"Umh menene..?
Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace"Wata alfarma zan roke ki Faa'izaa..?
Kai tsaye nace"Wata irin alfarma ce wannan..?
Kai tsaye yace"Rokon ki zan yi. Don Allah Faa'izan a zaman da zamu yi in nayi miki wani abu wanda ba daidai ba ki yi gaggawan sanar da ni na baki Hakuri,kada kice zaki yi fushi da ni ko ki yi min horan kusantar in da kike,Zan fi jin zafin hakan fiye da Laifin da na aikata miki.
Ina so komai nayi miki ki tareni ki fad'amin ba kunya ba tsoro ni mijin ki mai sonki da kaunarki ba bautar juna zamu yi ba,bautar Ubangiji zamu yi
Ni dake ladan mu na wajen Ubangiji,kada mu zama bakin juna mu dora zamantakewarmu kan tafarkin koyarwa sunna da addini. nima in kika min ba daidai ba zan fad'a miki Domin ki gyara nima don Allah ki ankarar dani a inda na kuskure ba iya amanar kan ki ba Faa'iza Amanar junan mu dukkanmu zamu rike don Allah"
Ko kafin ya gama mgana Hawaye sun cika idona yana gama mganarsa suka kwaranyomin ashe akwai ranar da wani namiji zai daukeni nima kamar Sauran mata masu daraja da kima..?
Yana ji na fashe da kuka,kukan dake fitowa daga kasan raina jikinsa na rawa ya mike zaune ya tarairayoni ya Rumgume yana fadin"Kuka kuma..?
Ko na fadi mganar da bata yi miki Dad'i ba ne..?
Yafad'a yana kara rikeni acikin jikinsa ammh na kasa daina kuka saboda abun daga kasan zuciyata yake fitowa,gani nayi ya rude yasa na kara rumgumesa kamkam cikin shesshekan kuka nace"Kukana na farinciki ne. Ina kukan samun abokin rayuwa irin ka,sannan ina kukan da na rasaka ni ko wani irin asara na Tafka a rayuwata..?
Sai da ya Dagoni muna kallon cikin Idanuwan juna sannan yace"Ni ne da na rasaki da nayi babban asara Faa'iza ina sonki. Soyayya ta gaskiya"
Runtse ido nayi sai ga hawaye sharr,kafin na bude su akansa yana kallona da kaunata acikin idanuwansa sannan ga mirmishin nan nasa mai tsuma zuciyata.
Cikin muryan kuka nace"Me ka gani a tare dani..? Kyau.?kudi.?ilimi..?
Bani da komai fa. Bani da komai anya na chanchanci wannan kaunar daga gareka..?kana da komai,ko ta ko'ina bamu dace da juna ba..ban chanchanta ba..ban.."
Bai barni na karisa ba ya kariso ya hade space din dake tsakanin mu lokaci daya yana sumbar bakina na bude baki zan yi mgana ya tura harshensa cikin bakina da ya yi sanadiyar Daukewar mganata Lokaci daya da wani yanayi da ya zirgamin.
Tun ina rawan jiki sai ga shi na saki jikina har ina rumgumesa cikin samun natsuwa da na samu tun a ranar da auren Engr ya sauka akaina.
Sai da ya yi har ya gaji yana ganin zai rasa control dinsa ya sakeni ni kuma na koma na lafe ina runtse idanuwana Saboda kunyar data Lullubeni.
Rumgumeni ya karayi kam kafin yace"Na rufe wannan mganar. Kada na karajin kin ce baki chanchanta ba. Bana so, raina na kuna,in kuma kina so raina ya rika kuna ne shikenan ki cigaba da fad'a"
Yafad'a har a muryansa ina jin ransa na kuna nasan na ji kalmar bana so din da yasa nayi saurin cewa"Na bari bazan kara ba"
Saman kaina ya sumbata idanuwansa na lumshe yace"Yauwa Tife na"
Mun jima rumgume da juna yana zayyanamin kalaman kauna da Soyayya,yana kuma rarrashi na domin yana yi yana shafa kaina zuwa bayana bansan Lokacin da barci ya kwasheni ba shima dai kusa dani ya koma ya kwanta muka kamkame juna sai Sha d'aya na rana muka tashi ina ta mamakin barcin da na sha.
Yana dariya yace"To kin samu jikin Tosin mana ga Taushi dole ki yi barci baki sani ba"
Dariya nayi masa ban ce komai ba Tunda nasan gaskiya ya fada,Wanka muka fara yi dagani har shi sannan ya fita ya siyo mana abinci nikan sai da nace"Ka siyo cefane na fara girki baka yi ta siyan abinci a waje ba"
Yana dariya yace"Sai yadda kika ce Hajiyata. Siyan abinci kuma daman an saba ganina."
Kai tsaye nima nace"Eh lokacin baka da mata yanzu kuma kana da mata"
Cikin dagemin gira yace"Ehyee! ya sunan matar tawa..?
Nasan zolayarsa yasa na masa fari kafin nace"Tife mana. Tife sunanta"
Dariya ya kwashemin dashi kafin yace"Ah'a su Tife an waye an zama yan gari"
Dariya nayi masa ban biye masa ba tare muka ci abincin yana bani a baki ni da naji kunya nace zan basa sai yace'"Miye na sauri kuma..?
Ai har wanka zaki yi min gama zama dai yar gari. duk ina yi ne na bashi zaki rama ma kura aniyarta"
Ban ce masa komai ba sai dai na sunne kai nayi mirmishi.
Ranar yini ya yi bai fita ba sai da yammah ya fita siyo mana abinci bayan ya tayani mun gyara gidan mun gogesa na saka turaran wuta na da na had'a mai kamshi tunda duk Ammi ta sako min su kamar tasan ko zasu yi amfani.
A burner na saka turaran tunda nazo da kananun abubuwan da nasan zan nema da Engr ya shaki kamshin sai da yayi mgana cikin yanayin mganarsa yace"Kai Turaren nan akwai kamshi"
Ina gyada kai ban ce komai ba sai shine yace"Ke kika had'a..?
Na kara gyadamai kai sai yace"Tab. Masha Allah Zuwa zamu yi mu bud'e gidan Turarukan wuta nan da wani Lokaci sai kiji mun fi Dangote kudi"
Kai kawai na girgiza ina dariya nasan Halin Engr in ya fara zolayarsa sai cikina ya nemi ya kulle saboda Dariya.
Ranar ma tare muka kwana,bai nemi wani abu ba,Sannan shi ya karamin Tausa har nayi barci,abinci ma in ya siyo a baki yake bani gatan duniya dai ba wanda bana gani tun ina Tunanin zai nemi wani abu ina jin kunya har na saki jikina da shi na koya irin gaisuwansa komai kuma yace yana so shi nake yi masa,Sai da muka kwana uku da zuwa na bude wayata na kira su Ammi muka gaisa nayi musu bangajiya nan take gayamin a Abuja suka kwana gidan surukaina sai washegari suka koma kaduna.
Bayan Ammi na kira su Badariya,Anty Fadila da tace min jiya suka dawo Lagos ga Anum ma bata riga ta koma ba har ta bani muka yi mgana.
Dukkansu ba wanda ban kira nayi musu bangajiya ba. Nana fatima sai shakiyanci take min,wai ina cin amarci na kashe waya.
Na kira Abba mun gaisa yanata tambayana ya bakon waje..?
Nace lafiya lau,Tunda dai ba fita nake yi ba ina gida Engr yace duk makotan mu yare ne da wad'anda ba musulmai ba,Har Goggo na kira mun gaisa da Sauran yan'uwa kowa mukayi mgana sai yace na dace sai fatan zaman Hakuri da juna.
Engr bai koma aiki ba yace sai ya yi sati zai koma,ranar da muka kwana Biyar nace ya bar siyan abinci yayo cefane zan rika Dafawa sai da ya kalleni yace"Kin tabbata..?bana so ki na wahala fa"
Kai tsaye nace"Hakki na ne fa na girka na baka ko wanda kaga ina barin ka kana siya na bakunta ne,ni dai kayo cefane zan fara girki"
To kasuwan ma tare muka je muka siyo komai na cefane da kayan abinci naga garin Edo cike da yaruka kala kala da mabambantan al'ummah.
Da muka dawo tare muka shirya kitchen din nayi nayi ya tafi yaje ya Huta sai ya noke kafada har ce min ya yi "Kin manta nace miki sunana makale mata manne mata"
Ai ko naga makale mata girkin ma da nayi na Doya da miyar kwai tare muka yi yana mikomin abubuwa sannan yana tayani Hirarrakinsa masu dadi da ban Dariya.
Da na gama girkin nace masa megadi da Direba kai tsaye yace"Ni kad'ai ne Dolen ki Faa'iza su ko ba Dolen ki ba ne ki kyalesu ina basu kudin abinci"
Tunda ya nuna haka sai ban ja ba,aammh nace masa in ya ragu gudun kada ya lalace zan rika basu sai yace shikenan in ba Takura.
Tundaga ranar na nake yi mana abincin yaci kuma yana Santi yana sakamin albarka wani lokacin har hawaye nake Daukewa a boye ashe ashe nima zanga wannan ranar..?.
Ranar da zakayi ma miji abun alheri yaci da godiya yana saka maka albarka.
Cakarewa ta nake yi a gida ina cin gayuna ban cika dai kwalliya ba tunda ban saba ba,ammh ina saka kaya masu kyau ina gyara kaina.
Tunda Engr yana yabamin ko wani irin shiga nayi ko na burgeshi ko ban burgeshi ba,sai yace"Tife na kin yi kyau"
Wannan yabawar tasa ke karamin kaimi ina jin wani karsashi a kasan raina.
kuma Engr bai taba min korafin rashin kwalliyata ta yan matan zamani ba,zai gani kuma zai yabamin shiyasa ban ma san Lokacin da nake cin masa gayun ba saboda bakinsa da idanuwansa suna nuna Darajata sannan suna yabamin shiyasa nima nake yin wasu abubuwan ban sani ba.
Zuciya tana son mai sonta sannan tana Daraja mai yaba mata.
Ranar da muka cika sati na kira Maa muka gaisa na tambayi Kafaya tace suna makaranta tunda University of Abuja suke yi,bayan mun gaisa sai tace"Kuna nan dai lafiya dai ko..?
Ba wata matsala shi Babatunden d'in bai yi miki komai ba ko..?
Sai nace mata lafiya lau muke haka fa da mukayi waya da Paapa shima haka yace min ko oluwatosin din na bani matsala nace musu komai lafiya muka rabu suna sakamin albarka.
Yafara zuwa aiki ranar yana ta kirana ina waya sai da na gama na kirasa da ya tambayeni da wa nake waya nace ma su Paapa ne.
Kai tsaye yace"Uhm lalle kin kwace gwammati na. Nifa basu kirani ba yau kwata kwata."
Ya fad'a kamar zai yi kuka.
Ina Dariya nace"ko kana kishi dani ne..?
Da sauri yace"Name..?zan famshe a wajenki ni dai in dai zaki gatan tani ai shikenan''Dariya nayi masa ban ce komai ba sai da ya dawo muna cin abinci ya kalleni kafin yace"Wai Hajiya baki gama Hutun naki ba ne..?
Ban gane mganarsa ba nace"Hutun me..?
Sai da ya kashemin ido kafin yace"To ina so na fara kara'i na da shagali mana"
Kunya ta kamani na sunkuyar da kaina ina hararansa shi ko sai ya saka Dariya kafin yace"Ji min yarinya daga na Daga miki kafa sai ki saki jiki..?
Tab shagali zai fara soon"
Na lura daman ya riga ya gama Dagamin kafa,tunda naji abunda ya fada nima sai na shirya duk da ina jin Fargaba da faduwar gaba.
Bayan mun idar da sallar isha'i tunda in dai yana gida shi yake jan mu jam"i ya fita ya dawo da leda a hannunsa ashe Zabbi ne gassasu da Yan shilla,sai madaran youghourt mai kauri da sanyi,ya sani na kara Dauro alwala muka yi sallah raka'a hudu tare addu'o'i sannan ya jani kan cinyarsa ya ciyar dani zabbin nan tare madara duk da ina kaucewa ammh bai damu ba.
Bayan mun gama shi ya kwashe komai ya kai kitchen ni kuma sai na shiga wanka,shima dayan bedroom din ya shiga domin ya kimtsa kansa.
Rigar barcin da Zainab ta aikomin da shi na saka rudewa iya rudewa Engr ya yi ya kamkameni yana shinshinar kamshin Turarena lokaci daya yana Fadin"Ke ma kin amimce in fara shagalina Tife na"
Kasa amsa masa nayi ina sunne kaina a kirjinsa tun ina ganin al'amarin kamar wasa kamar yadda ni na saba jinsa,sai dai ina lamarin ya sha bambam wanda na sani dabam ne da wanda Engr ya jani zai sanar dani. kusan shidewa nayi lokacin da naji yana kaima kowacce gaba dake jikina Sumbata kafin na dawo hayyacina yabi duk inda ya sumbata yana Tsotsa abunda ya kara rikitani har Tafin kafana sai da Engr ya lashe.
Ya bi dani ta wata hanya ce siririya mai wuyar isa ammh fa babu gargada ballatana kwalabai .
Kwalbati ne a shimfid'e cikin natsuwa da kwanciyar hankali ya kaini bakin Bodar inda labarin ya sha bambam.
In nace ban ji tarin bambamce ba nayi karya,na saba jin shigar abun kamar agaggauce,ammh wannan karon a sannu sannu ne cikin Fitar hayyacin sambatun kalamai masu dadi da sanyaya zuciya,naji ni na kame tunda Ammi batayi min wasa ba Shiyasa Engr ya Rude nima ya Rudar dani da Farko naji Zafi gaskiya Daga baya kuma sai ya yi sauki zafin ammh mganar gaskiya Engr ya famshe Bashinsa na tsawon sati Dayan da yayi yana min hidima.
Ya fita hayyacinsa sai sambatu yake yi yana faman kirana da sunaye mabambamta,har da yarensu ya juya yana ta yi bana Fahimta.
Ni dai na mika masa Jikina da zuciyata gabadaya kamar yadda nima ya bani komai nasa,dakyar ya iya kyaleni bayan ya samu natsuwa ya wani Saukemin nauyin shi a kan jikina Lokaci daya yana sakin Numfarfashi a jere kamar wanda yayi gudun Tsere sai kuma chan naji kamar baya numfashi jikinsa ya saki na rude ga shi ya yi min nauyi a jikina haka na rika Shafa Fuskarsa ina fadin"Tosi...Tosin..Engr.."
"Engr..engr.."
Gabana ya yanke ya fadi ras,gabadaya sai naji na rude da nayi wani tunani ko dai ya rasu ne Fa'iza..?
Ganin yadda na rude ne yasa ya yunkura daga kan jikina ya mulmula gefe chan sannan ya rikoni,ya dawo dani samansa ya kamkameni yana ji yadda na sauke ajiyar zuciya na salamu jin ashe yana lafiya.
Yana kamkame dani,ya na sauke numfashi,cikin wata irin murya a shake yace"Ban mutu ba. Tife na ban mutu ba kawai dad'i ne ya yi min yawa"
Yana fad'a yana tusa kansa a tsakanin wuyana kamar zai yi kuka ya cigaba da fadin"Anya ke ce kika haifi Amir da Anum..?
Ina Danne dariyata nace"Harda Mutsy da Ahmad ma ka manta"
Girgiza kai yayi lokaci daya yana Fadin"Anya daga nan suka fito..?
Yafada yana kai hannunsa wajen na Turesa ina yar Dariya wata rumgumar ya karamai kafin yace"Allah ya yi miki albarka. Allah ya yi miki albarka Nagode sosai Tanque Very Musch Faa'izaa Tife na"
Albarka bansan adadin da na sha ba har muka je muka yi wanka muka Tsarkake jikin mu..
Muka koma muka kwanta mun Dade bamu yi barci muna ta Hira har mamakin kaina nake yi ni ce kan gado daya da wani namijim..?har muna Hira cikin so da kauna haka..?.
Allah ne abun godiya domin shi yake baka abunda baka taba tunanin zaka samu ba".
Da asuba ma muna idar da sallah daga gaisuwan Safe ya nane min har da shagwaba yana fadin"Kinga dai jiya na fara ko..?
Dariya kawai nayi na biye masa ya yi kara'insa nan ma fad'i yake"Ni dai ina tamtama anya su Amir ya'yan ki ne..? ko dai ya'yan Yaya Asiya ne?saboda naji wajen gam. Tsam da shi wlh kamar ni na fara shiga"
Filo na dauka ina makamai Lokaci daya ina fadin"To kuma wayace ka fada..?ba sai ka yi shuru ba"
Filon ya rike yana fadin"To kuma bakin Tosin ke rufuwa.?ni fa d'an Free duniya ne komai na gani sai nayi mgana haka kurum na rika shuru ana Cutata"
Nasan daman bazai yi shurun ba shiyasa na kyalesa,ranar makara ya yi zuwa wajen aiki sai da rana ta take ya fita shima din domin suna da Meeting ne. da bazai je ba kuma yace min da an yi mgana zai ce to sai jiya ya fara kara'in sa Tife na hutawa ne shiyasa nasan zai aika yasa na rike bakina ina kallonsa shi kuma yana min dariya.
Ranar yana dawowa ya fad'amin yan Office din su sun shiryamana Liyafan aure,ya kuma ce in dai bana ra'ayi bazamu ba nace meyasa..?zamu je mana tunda don mu suka had'a walimar.
Ai ko mun je yar liyafan ta Dare ce,Shi Suit baki da Fari yasa ka ni kuma sai na nuna mai wani less d'ina mai baki da blue sai yace na saka shi Riga da zani ne na saka takalmina baki mai saukakkan Tudu sai Dan kunnena zinare da aka siyamin da Sadakina harda zobba.
Ban yi kwalliya ba amnh nayi kyau Tunda kusan shigar alfarma tana ma mata kyau,mayafi na saka mai girma kalan kayana na rufe jikina da farko ma sai da na tambayesa ko mayafin ya yi..?Sai yace min ko Hijabi na so sawa na saka abuna bakomai ra'ayina ne. abunda zai fi min daidai a jikina.
Sai ni kuma na kada baki nace"Kai dai ka dubamin ko ya yi. kasan abun ka da ba yar boko ba kada su ganni su ce Engr ya auro bakidajiya"
Kallona kawai ya yi bai yi mgana ba ni kuma ban lura da yayi fushi ba. Tunda ban taba ganin Fushinsa ba sai da mukaje wajen liyafar naga ya rage Fara'a ko hirar da ya sabamin sai sama sama.
Ko a wajen duk wanda yazo yi mana murnan aure in da Turanci ne shi zai amsa in yaganka bakajin Hausa sai ya kyaleka in kuma kai bahaushe ne sai yace maka"Ka yi mgana da Hausa Matata bata jin Turanci"
Ba da wulakanci ba, da Mutuntatawa Saboda kada naji kamar an wareni,Liyafar mazan kowannen da matan su da ya'yan su,gaskiya yare da Wad'anda ba musulmai ba sun fi yawa Hausawan mu ba su da yawa sosai
Bamu jima ba awa biyu ne an ci an sha an kuma yi Hotuna sannan mun samu kyattukan kudi da Flowers na masoya sai greeting card na fatan alheri.
A gajiye muka dawo gida Engr har kayan barci shi ya sakamin bayan nayi wanka sannan ya yi min Tausa sai dai baya min hira,ni kum sai naji ban ji dadi ba daya kwanta bai rikoni ajikinsa kamar yadda ya saba ba,duk sai naji ban ji dadi ba na fara batama mutumin da ke min hidima da jikinsa da aljihunsa mutumin dake kaunata Saboda Allah.
Sai na matsa kusa da shi na Rungumosa ta baya ina fadin"Kayi hakuri bazan kara ba. "
Shuru yayi bai yi mgana ba sai da yaji na kara rumgumesa ina fadin"Kaji bazan kara ba"
Sannan ya juyo yana kallona kafin ya sakani ajikinsa gabadaya yana Fadin"Bana so Fa'iza.
bana son irin wad'anan mganganun suna fitowa daga bakin ki, ni na ganki nace ina sonki ba gayyata ta kika yi ba,kuma ba tallarki aka kawomin ba. ni na ganki nace naji na gani ina sonki a haka so a i don't care da mganar kowa kin gane"
Dole na gyad'a masa kai jikina a sanyaye kafin nace"Kayi hakuri"
Kai tsaye yace"Na yafe miki ma tun kafin ki nemi afuwata"
Sai na kara lafewa saman kirjinsa ina ajiyar zuciya.
Ranar dai ba'ayi shagali ba sai da asuba da safe ma kafin ya tafi wajen aiki sai da ya kara,lalubata ni ko fad'i nake"Baka gajiya..?
Sai kawai yace min"Zan fara Zagayowa ma ina karb'an na rana"
Duka na d'agakamai a baya ina Fadin"A'a wlh..".
Saboda nasan Halinsa wlh zai aikata abunda ya fad'a.
Zaman mu cikin kwanciyar Hankali da Fahintar juna gaskiyan Engr ne da yace me na sani akan Abdulbasit sai da na zama ya fara gudana Tsakanin mu na ke Fahimta waye na aura..?
Engr mutum ne mai dad'in zama,mai addini da cika Lokacin sallah,mai gaskiya da rikon Amana shi mutum ne dan free bashi da kumbiya kumbiya duk abunda ke ransa zai fad'a maka sai dai kaji Haushi,sannan mutum ne mai girmama ra'ayin wanda yake tare da shi,komai nake so wlh shi yake min bai taba cewa nabi na shi ra:ayin ba. sai dai ma shi ya bar na shi yabi nawa ra'ayin a koda yaushe mganarsa shi ne yana girmama Ra'ayin mutane shine zaman lafiyan ka da su.
Ya fahimceni nima na Fahimcesa,abunda nasan yace min baya so ina nesa da aikata shi,shima Duk abunda yasan bana so wlh tallahi ko kusa da shi bazai Kusanta ba .ban taba tunanin watarana ni Faa'iza zan zama haka ba.
Ban taba tunanin yau ni Fa'iza zan samu abokin rayuwa irin Engr ba. koda yaushe na kallesa kara godema Allah nake yi,duk weekend muna Fita wayo ni da shi sannan ranar a waje muke cin abinci,kamar yadda yace duk inda ya saka kafarsa nan nake maidaa nawa kuma bai taba jin kunyar nunani a matsayin matarsa ba.
Mun sha had'uwa da abokan aikinsa Cikin Fariya zai nuna ni yana fadi'n"Meet my Wife Fa'izaa.."
Ban taba ganin mutum irin sa ba,shi dai kawai na kasance cikin Farinciki shine Burinsa,yana da tarin ilimi in yana Turanci kamar bature,sannan wani abun da ya kara Burgeni da shi ko waya zai yi da yan'uwansu na benue sai yace min"Zamu yi fa yaren mu kada kiji wani iri Faa'iza.."
Ko kuma in yana waya da su Kafayatu da yake su ba su cikamai mgana da Hausa ko Turanci ba, sai ya nemi izinina kan zasu yi mgana da yaren su da nace meyasa yake neman izinina sai yace"Kada ya shigga hakkina naji kamar suna yi da ni"
Daga ranar na kara ganin kimarsa da Darajansa sannan ya samu babban matsayi a rayuwata.
Iyayensa kuwa tsakanina da su sai Godiya bayan kwana biyu sai sun kirani suna tambayata lafiya ta Papa da Maaa kamar diyar su suka Daukemi. haka suma su kayafatu nima kuma na saki jiki da su kamar yan'uwa na,nima ina kiran su tunda kudi yake sakamin kamar bai san zafin su ba. koda yaushe nima cikin waya nake yi da yan'uwana.
Su Anum kuma bai wuce a sati mu yi mgana sai biyu ta wayar zainab ba. Engr har mgana yayi zai siya musu waya nace Babansu bazai bari ba Daganan bai kara mgana ba illah cewa da yayi wannan tunani ne shima mai kyau.
Sannan bai taba Tursasani akan na sauya ra'ayi kan karatun Boko ba. sai ma supporting dina da yake kan ra'ayi na ba ruwansa yace ni ya ke so kuma Dole ne ya girmama Ra'ayi na. karatu nace ba na so. wlh bazai taba min Dole ba ranar da nake da sha'awa ko na furta masa ko wata makaranta ne zai kai ni nayi karatu har sai nagaji.
Watan mu biyu da zuwa Edo Engr yace na shirya zamu je Lagos na zata zan rakasa wani aiki ne,ashe Hutu zamu tafi tafiya ce mai mikakkiya.
Tafiyar mota muka yi kuma bai sa na Dauki kaya masu yawa ba a hotel muka kwana ranar sai da safen yake fad'amin London zamu je ya dauki Hutunsa na karshen shekara zamu sha Honeymoon yadda zai ji dadin yin kara'in sa sosai.
Da nace ban fad:a kowa ba sai yace shi ya sanar da Abba baki na bude kafin nace"Kace mai me..?
Kai tsaye yace"Nace masa zamu je Honneymoon mana sannan na fad'amasa kila ma sai kin samo ma su Amir kani ko kanwa zamu dawo"
Nasan fa zai fad'a hakan din yasa kunya kamar Abba na gabana da yasa ma na kasa kiran shi wlh.
Zuwana Lagos sai ya tasomin da kwad'ayin ganin ya'yana da na yi ma Engr mgana sai yace min na bari in muka dawo ta nan zamu sauka zamu je mu gansu. sai na bar mganan Saboda zama da shi na Fahimci yadda yake Daraja kowata mgana ko shawara da ta fito daga bakina, na kuma san tunda yace to haka din zai kasance.
Kwanan mu biyu a lagos kafin jirgin mu ya tashi zuwa London Ranar an ga rawan banjo da rawan jiki a gurina haka na rike Engr da jirgi zai karta tashinsa sai da jikina ya juya,kamar zan yi fitsari karshenta dai har da zawo sai da Engr ya rakani Tiolet din Jirgin nayi,Allah yasa ma muna Vip ne,Kunya duk ta kamani sai daga baya bayan na dawo hayyacina na kalli Engr ina fadin"Kayi hakuri ban taba hawa jirgi ba ne"
Sai hawaye sharr sai ya kamani ya Rungumeni yana fadin"To meye aciki..?
Ai jirgi yanzu kika fara hawa Hajiya ta"
Ai ko dai domin kwana goma muka yi a london mun yawata sannan ta bakin Engr ya gwangwanji amarcinsa nima ai na yi amarcin nayi kiba nayi Fari kamar bani ba na samu hutu,Hutun da ban taba Tunanin zan samu ba. Daga London Dubai muka je muka yi sati Biyu shima mun yawata naga manyan Dogayen gine gine sai da na zama yar kauye daman chan yar kauyen ce munje mun yi siyayya katin bankin Engr na Hannuna yace na daukan ma ya'yansa tsaraba tunda zamu sauka a wajen su kafin mu koma Edo.
Daga Dubai sai Mumbai India shi kam garin ya yi min dadi mune har Cinema kallo, tsukewa cikin Riga da wando yanzu tuni na kware akai,sai dai bana yadda na bayyana jikina Tunda nasan Halin mijina.
Duk inda muke muna tare da juna hannayena na makale cikin nasa Hotuna ko ban san adadin da muka Dauka ba da ni da shi,ina kallo kaina ina kara tuna ni ce dai Fa'izan nan da bani da komai ban mallaki komai ba. nice yau ke zagaye kasashen ketare a haka a yadda nake din nan, Allah shi bakayi masa Dubara sannan ka sani abunda ka raina watarana shi zai tsole maka ido.
Duka yawon mu da muka gama a Saudiya muka yada zango Lokacin an fara Umra sai muka yi ta Ibada a Masallaci muke yini sai dare muke haduwa mu tafi masauki.
Wata daya muka kwashe a Saudiya kafin mu fara shirin tafiya Lokacin da naganni gani ga ka'aba sai kuka nayi ma yan'uwa na Addu'a tare da yara na da Mijina,sannan na rikor ma kasata zaman lafiya tare da Allah ya bama iyayena aljannah,tare da sauran musulmai gabadaya.
Ta Lagos din muka sake sauka kamar yadda yace,kuma tare da kayan mu muka taho Tunda Engr ya saki kudi ni kaina Sauran kayan nawa duk achan ya siya mana wasu na sawan,ba wanda ban yi ma Tsaraba ba Paapa maa,su kafayatu har da Hajiya Kudurat sai su Amir da Abba da sauran yan'uwana Tunda in ban Siya ba Engr zai ce kin ko yi ma wance Tsaraba..?in nace A'a sai yace to nayi ma kowa da kowa shi ya bani Dama.
Sai da muka Huta na kwana Hud'u sannan Engr yace na kira Anty Fadila Tunda gidanta zamu fara zuwa kamar yadda na bukata Daman wayata kasheta nayi,lokacin da taji ina Lagos zamu zo ni da Injiniya ta saka ihun murna tana jin dadi.
Tace tana asibiti ne ammh zata dawo sai ta turomi lambar babansu Falaq Engr ya kirasa shi ya bashi address din,Tashar Taxi muka yi tunda Direba da mota chan Edo muka barsa. ya ma ce Kano zamu je daga Lagos mu gaida Hajiya Tafeesu tana ta korafin bai kai mata ni ta ganni ba.
Riga da wando na saka Baki da Fari sai na Dora wata riga mai zif ta gaba kamar aftar dreess na yane kaina da mayafi fari,sai na saka takalmi mai tsini yana da igiya jaka bata Dameni ba,bana Daukanta Engr kuma ya saka Farar shadda harda babban riga daman yazo da su ina ta mamaki ma na daga bai saka ba har muka dawo.
Ashe ya ijiyesu saboda zai je ganin ya'yansa kada su gansa da kananun kaya su ga Uban banza"
Muna Taxi yake fad'amin haka ina Dariya duka Tsaraban na kwaso,hatta su Falaq din nayi musu nasu Tsaraban. Hannuna na cikin nasa yana murzawa muna Hira sama sama.
In ka sanni a baya a yanzu akace maka ni ce sai ka kara juyowa ka kalleni Dakyau kafin ka iya ganeni na sauya na zama burtuka,nayi kumatu nayi Fari kamar ina Shafa mai kirjina da mazaunena sun kara cika na zama mai kyau dani kamar a sace ni a gudu ni kaina nasan Engr ya zama wani Bangarena irin madaran soyayya da kaunar da yake bani Dole ma na Sauya gabadaya. sannan ya Bud'emin ido irin budewar da a baya ban san shi ba ya zagaya dani kasashen da ko a mafarki ban taba tunanin takawa ba.
Wannan duka yana cikin ikon Allah kada ka raina mutum domin wata Halitta da Allah ya yi masa saboda shi ya hallicesa kuma shi kad'ai yasan baiwar da yayi masa.
kamar yadda Lokaci daya ya Daukaka Fa'iza baka,mummuna,mai fama da raunin ji, mara gata wacce bata kai namiji mai kyau ya sota ba.
Sai ga shi yanzu ba abunda Allah bai mallaka mata ba. Sai dai godiya da Hamdala.
*Janafty*
[8/1, 8:56 PM] U.M Collection ZMFR CM: *KNKB3017*
*TASTED & TRUSTED*
*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATUN SAIWOWIN MUTANAN CHADI DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZAR AMARE, MASU JEGO DA WADDA TAKE SON GYARA KANTA*.
*AN GWADA ANGA INGANCINSA SHIYASA NA KE TALLATA MUKU DA K'ARFIN GUIWATA*.
*ABIN BIRGEWA DA WANNAN SAIWOWINRL ZAKI YI AMFANI DA SU SAMA DA SAU DAYA.*
*AKWAI FULL PACKAGE, AKWAI RABI, TA YADDA KOWA ZAI IYA SIYA*.
*SANNAN BABU BAURI NA TASHIN HANKALI.*
*DA KANKI ZAKI DAFA ABAR KI, KOMAI ANA SAKA WA A CIKI*.
*SHIN KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR, KO KUWA KE CE KIKE SON GYARA KANKI?*.
*KAYANA NATURAL NE DOMIN SAIWOWI NE DA AKE HAKOSU A DAJIKAN CHADI. BAYAN SAUKAR DA GAMSUWA HAR YAQI SUKE YI DA DRYNESS DA KUMA INFECTIONS.*
*AKWAI NA TSUGGUNO DA YAKE HA'DE MACE TA MATSE.*
*AKWAI HADADDUN DAKA NA SHA DA MADARA KO NONO WANDA BABU ALGUS*.
*SANNAN AKWIA GADALIN MATA NA ASALI, WANDA SHA YANZU NE MAGANIN YANZU DA IKON ALLAH*
*DUKKANSU TESTED & TRUSTED NE*.
*TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU*
*08032773332*
*DOMIN KARIN BAYANI, SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*.
*NATION WIDE DELIVERY*
*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*
*09069067488*
Dole akwai wasu kayan da za'a bar su a gidana na kaduna,shiyasa Ammi da rakiyar su Nana khadija suka kara komawa suka kai tunda akwai key din gidan a hannun su Ammi.
Kaya kad'an suka ragemin wad'anda zan sassaka in mukaje chan sai turaruka da kayan kwalliya sai kayan gumbar mata na tsimi da Saiwar kazan da na siya wajen Surayya Halin yau,ta kuma yi min alherin turrukan wutan ta masu kyau da kamshi,Sannan har da garin daka na sha madara ko nono.
Gaskiya Surayya ta na da kirki da iya mu'amala sosai na ji dad'in huld'a da ita,kayan ta kuma masu Inganci ne.
Kazan saiwar nan ina fada muku duniya ce.
Tun zuwan nan da Engr ya yi bai sake dawowa ba. aiki ya yi masa yawa yana Edo sai dai mu yi waya ni da shi duk tsaren tsaren ta waya muke yi.
Ranar alhamis ya kama tafiyarmu Abuja tunda yaso mu fara ta chan Benue din ne ammh sai Sweetheart tace tare zamu tafi saboda haka mu fara sauka ta nan sai a wuce gabadaya.
Ni kuma ranar Talata da Safe naje nayi gyaran kai Steaming akayi min tunda ban saka mai ba.
Mai kitson su Ammi tazo ta yarfamin shi 2step kanana masu kyau,Ranar laraba kuma nayi kunshi Baki da Ja,a baya ina Dauka kunshi bai dace dani ba tunda ina baka ammh sai ga shi an yi min kuma ya fito ras har ya fi ma na Bikin Yaya Abdul'ahad kyau da fitowa ko don yanzu na kara haske ne sannan Fatata ta Murje tayi kyau. kamar bani bace Fa'iza nan ba sannan kuma nayi Dilka da Halawa,sai yanzu na kara yarda da mganar Hausawa da sukace in kana da kyau to ka kara da wanka to in baka da kyau in ka kara da wanka sai kayi kyau din.
Engr sai min santi yake yi,yana jadaddamin ayi min zanen kunshi mai kyau in ya gani zai ba da tukwaici,shi a chan Benue zamu hadu tunda shi yana Edo Bazamu had'u da shi a Abuja ba Motoci kuma daga ma'aikan su Abba aka bamu manyan motocin su mai cin mutane sha takwas guda daya,Tare da Direban su shi zai kaimu har Abuja.
Naso naje karofi nayi ma su Goggo sallama ammh ban samu dama ba, sai dai mun yi mgana ta waya kuma nasan Daga baya in nace Engr ya kaini bazai ki kaini ba.
Tun ana gobe tafiyar masu harama suka zo,har da Hajiyan Dala tunda ta kwallafa rai sai tazo,Su hafsatu suna ta bakin rai bazasu samu zuwa ba. Yaya Mariya nayi musu dariya har ga Allah na cire rai da zuwan Anum tunda ban ji Anty Fadila tace min komai ba,Sai dare ta iso Lokacin an gamin min lalli har na cire nayi sallah ashe jirgin yammah suka shigo abun mamaki sai gata da Anum,sai D'iyarta Falaq sa'an Anum din sauran suna gida saboda makaranta.
Sai gani ga Anum baki har kunne muka Rumgume juna tana Dariya tace"Umma.."
Irin cikin mamakin nan nima sai na Dago kanta ina kare ma girmanta kallo yarinya ta kusa ma kereni a Tsawo Cikin Dariyan jin dadin ganinta Tsab cikin kamala na ja kumatunta ina fadin"Anum d'in Umma"
Hannayena ta kama ta kallo sai kuma ta kara kallona kafin tace"Umma kin yi kyau kamar ba ke"
Sai na kara Rumgumota ina jin wani farinciki na ratsani ba wamda ya nemi takura mana muka shige daki ina ta faman tambayanta ya sauran yan'uwanta ina su Mama da Antyn su..?
Tace min duk suna Lafiya Anty ma ta bada sako ta kawomin yana cikin akwatin Anty Fadila Allah Sarki daman tace min zan ga sako,bazan mata da alherinta ba taso zuwa ammh awajen aiki ba'a bata dama ba. har ina mata tsiyan ko megidan ne ya hana cikin Dariya tace"Wlh ya barni maman Amir daga wajen aikin ne. Ai yanzu Honey ya sauya sosai wlh,Karin ma barina da yayi yace in mun had'u na kara roka masa gafaran ki"
Ni ko kai tsaye nace"Bai min komai ba na yafe masa"
To ashe sai da ya kara aiko Anum,Takarda ce karama fara ya bata ta tura cikin sikat dinta rubutun Hausa ne layi biyu yayi aciki.
"Ki yafemin Fa'iza. Daga karshe ina yi miki fatan Alheri da rayuwa mai inganci. fiye da yadda kika samu a zama na tare dake"
"Ishaq sidi karofi"
Sai naji Tausayinsa kad'an ya kamani yaga Takardan nayi ban ce komai ba Anum tace"Umma ya ki ka ga yaga..?
Sai na kalleta kafin nace"Bata da amfani Anum. na yafe ma Daadan ku ko Saboda ku! Allah ya yafe mana Gabadaya"
Sai ta rumgumeni tana fadin"Yauwa Umma daman ai Allah na son mai yafiya ko..?
Sai na daga mata kai ranar dai uwa da y'a tare suka kwana har abinci tare mukaci bini bini tace Umma kaza tana kuma nane dani ranar ma ko waya bamu yi sosai da Engr ba jin Anum tazo kai tsaye yace"Ah'a muna da babban bakuwa to bari Baba ya daga ma yarsa kafa. na ara miki kanki ki kularmin da Diyata Sosai"
Bai kuma hakura ba sai da na bashi Anum suka gaisa cikin sakewarsa kamar yadda ya Saba Radam ya rike sunayen su Amir yana ta tambayanta su Daya bayan Daya sannan ya tambayeta karatu tana bashi amsa daga karshe yace sai sun hadu a Benue.
Bayan sun yi sallama ta bani wayar nima bamu jima ba muka yi sallamar ina sauke wayar Anum tace"Umma Sabon Baban mu yana da kirki"
Kai na daga mata ban yi mgana ba,Sai da Safe ne Anty Fadila ta kawo min Sakon Zainab a wani kwali ne ashe Sleeping dress ne kala uku masu kyau da Tsada sexy na rike baki ina mamaki da na kirata in yi mata godiya sai tace"A sa ayi ma Yallabai kwalliya da shi. Don Allah white din nan ranar First nigt zaki saka shi"
Kunya ma ta bani ina yar Dariya nace"First Night sai kace wasu yara"
Shewa ta saki kafin tacr"ke kika san wannan, namiji baya tsufa ko shekara Dari yayi zai yi shagalinsa ni dai don Allah ki saka maman Amir ni fa a yar'uwa na Daukeki kin sani"
Sanin Halin nacinta yasa nace mata zan saka mun jima muna taba hira kafin tayi mana fatan isa Abuja Lafiya sannan muka yi sallama.
Duka shiri ake ta yi,su Ya Mariya da Anty Nasara sun fi kowa zumud'i tun asuba suka shirya karyawa ma sama sama suka yi nima nayi wanka cikin kayan lefena na saka Abaya doguwar Riga sukayi suka yi na yana mayafinsa naki na zuba Hijabina fari har kasa,sannan na fesa turare duk inda na Gifta ina tashin kamshi.
Anum ma da Falaq sun yi wanka sun saka kaya iri d'aya na wani leshi sun saka mayafai sun kyau kamar yan Biyu.
Mota bata zo ba sai karfe sha daya na Safe tun safe da muka yi waya da Engr ban sake jinsa ba. nima da zamu tashi na kirasa bata shiga sai nayi Tunanin network ne.
Motar nan gabadaya ta Daukemu mu da kayan mu har da rara ma su Hafsatu kamar zasu yi kuka suna Dagamana Hannu Hajiyar su Raliya tace sai gobe zata taho Abujan tana taro yau Abba har da shi a masu rakiya ya yi min kuma dukkan nasihan da Uba zai yi ma yarsa.
Shi da su Baba Ati da Inno tunda tun Daurin auren suke min har kuma da zamu tafi sai ga shi ina sharan kwallah Rayuwa kenan kana naka Allah na nashi kuma na shi Tsarin shine daidai.
Da yake motar Sabuwa ne ga Lafiya karfe biyu muna garin Abuja,Direban baisan wajen ba,na kuma ta kara kiran Engr lambarsa bata shiga muna cikin Tararradi ne sai Kafaya ta kirani ita ta agaza tayi ma Direba kwatancen gidan su na gwarimpa tunda daman nan zamu fara sauka kafin Su rakamu gidansa na Abuja mu kwana kafin gobe mu wuce Benue din.
Gidan su Engr wani katon gida ne Aljannar Duniya har ta Hajiyar Dala mai takama da suna da shi sai ta ce"Kai kun ga gida kamar a turai"
Komai ba hayaniya cikin aji da kudi,Gida ne mai girma daga su sai ma'aikata acikin wannan wargajejen gidan Hajiya Shukra da kannenta mata su suka tarbemu tare da su kafayatu,munga karamci irin karamcin da bamu taba zaton suma sun iya ba,ko don ita Hajiya Shukran Bahaushiya ce..?
Wani shashe mai falo biyu suka saukemu ashe shashen Engr ne Sharifatu ke fad'a,babu abunda babu a shashen na kayan more rayuwa,abinci ko kala kala da ababen sha ga su nan nama ko harda na Dawisu sai wanda kake jin ci.
Sallah muka farayi kafin zaman cin abinci ni dai na kasa ci saboda rashin jin Engr,nasan kuma nasan shima bai Sameni ba ne shiyasa ban jisa ba.
Direban da ya kawomu shima an sauke shi a daki na musamman an bashi abinci da abun sha ya huta zuwa Gobe tunda Har Benue da shi zamu je.
Dakyar na iya tsakuran abinci shima sai da Ammi ta matsamin sai bayan mun gama cin abincin sannan Hajiya Shukra ta shigo sanye cikin wata shadda Doguwar riga taji aiki,ta ci Daurinta daga ganinta kinga bahaushiya mai ilimi da wayewa da sanin ya kamata ga ta da fara'a,haka hakoranta duk a waje ita da Sister dinta suna mana maraba da zuwa da tambayan Hanya.
Su kafayatu ma basa kama da Engr sai dai kama ta jini ammh yanayin Fatan su iri daya ne,tsawon kuma ma Hajiya Shukra suka Dauko dukkansu zabga zabga ne masha Allah.
Tana ganin su Anum ta kirasu tana tambayan su sunayen su dayake sun san juna da Ammi suna ta Hira tace"Wannan jikata ce ko..?
Tafad'a tana kallona ni daman Tunda ta shigo kaina ma kasa tun kafin ma Anmi tayi mgana Hajiyar Dala tayi karaf tace"Eh ita ce ma ta biyu. ai akwai ma yayanta da kannensu biyu,Kunsan ai auran zumunci ne da shi tsohon mijin nata"
Ammi sai hararanta take yi fadi ba'a tambayeta ba sai Hajiya Shukra ta bata mamaki da cewa"Ai Babatunde ya fad'amin Allah Sarki ya sunanki..?
Ta tambayi Anun ni kuma ina jin tace Babatunde nasan Engr take nufi tunda shi ya fad'amin sunan datake kiransa.
Anum da Falaq suka fada mata sunanyensu cikin Mirmishin ta tace zasu zo mata hutu sai suka juya suna kallon mu tayi dariya kafin tace"Suna tambayan ku ne ku ce eh"
Gababaya sai akayi dariya,ni kuma har inda nake ta kariso ta dagoni ta Rumgumeni kafin ta dago kaina Tana Fadin"'Sannu da zuwa Faa'iza.."
Allah ya sanya alheri ya baku zaman lafiya"
Gabadaya aka amsa da Ameen cikin yanayin fara'arta tace"Papa din su na hanya. bari ya kariso ku gaisa sai muje chan gidan ko..?
Kaina na kasa na kasa mgana sai ta Dafa kaina tana fadin"ki saki jikin ki kin ji ko..?nan din ma duk gidan ki ne kina jina ko.?
Sai na daga mata kai sakin Hannuna tayi kafin tace"Baku yi mgana Da Babatunde ba ko..?
Meeting garesu nima tun safe da mukayi mgana ban kara jinsa ba"
Sai naji Hankalina ya kwanta jin yana Lafiya sauran yan'uwanta ma suna ta saka albarka kamar zasu lasheni.
Bayan fitan su su Kafaya suka shigo dukkansu kaya iri da'ya suka saka Atamfa riga da sikat har da Murjanin su,Rumgumeni suma suka yi suna murnan ganina Yan biyu ne masu kama daya baka iya bambamce su.
Harda Mirmishin su iri daya ne.
Suna kallo na suna min mirmishi sai na Tsargu naga kamar sun ganni ba yadda suka yi Tsammani ba ammh basu nuna ba.
Kafaya tafi yawan mgana ita tace min"Anty Fa'iza u are welcome..'"
Ita kuma Sharifa ce min tayi"Bro Tosin na son ki sosai ya bamu Amanarki yace mu kula dake sosai kiji abinci kada ki zauna da yunwa"
Dariya kawai nayi nasan zai aika su Ammi na gefen mu suna ta kallon mu gwanin ban sha'awa zama suka yi dani suna min hiran Engr ina dariya ashe har a gida haka yake na Dauka yana rage wasu abubuwan ashe ma ni banga komai ba.
Sai da akayi la'sar suka fita suka barmu muma muka yi sallah Ammi da su Anty Nasara sai fad'i suke nayi dacen suruka da dangin miji Hajiyar Dala dai ba baki sai dai nazarin abubuwa da take gani,sai bayan mun yi sallah ne aka aiko cewa mu shirya zamu tafi chan gidan daman bamu fito da kayan mu ba,sai muka natsa sannan Maa tazo ta tafi dani wajen Paapa dake falonsa.
Dattijon ne mai kamala,yana zaune yana karatun Jarida da siririn gilashinsa mai karamai karfin gani,har kusa da kafafunsa Maa ta kaini ta zaunar tana fad'amai ga ni nan ya sakamin albarka.
Ba ruwan shi kaina ya dafa yana ta sakamin albarka daga karshe yace"Allah ya sa ku zauna lafiya ki yi hakuri kin ji ko..?Oluwatosin Good Boy ne ammh in bai yi miki daidai ba. juzt call me nima papa din ki ne kin ji ko?
Sai na gyada mai kai ina Godiya ya bani kyautar kudi cheque Maa ta amsamin,nayi masa sallama muka fice bayan yace bazai samu zuwa Beneu ba. saboda aiki sai dai akwai brothers dinsa da Danginsa yasan i will Enjoy it.
Bayan ni ma har su Ammi sun je sun gaisa sannan muka tafi gidan Engr Dake Apo,a motar Papa direba ya tukamu ni da Maa da Ammi sauran kuma suka Biyomu daga baya,su da yake basu da wani al'adu kamar namu na Hausawa Nakiya kawai da alkaki Ammi tayi musu aka raba biyu aka bamasu Maa sauran kuma Ammi tace sun munje Benue tunda iya abunda muke da shi zamu yi.
Gidan Engr dake Apo Abuja karamin gidane ammh ya hadu falo biyu Bedroom hudu sai compaund akwai kitchen da bayika sai ta chan baya akwai tsakar gida da Famfo.
Ammh gidan ya had'u yaji kayan alatun rayuwa har da wajen shakawatawa da wajen lilo,Akwai megadin dake tsaren gidan,Kowa sai santin gidan yake masha Allah.
Hajiyar Dala fad'i take yi"Allah mai kyauta da kari yanzu Fa'iza ne a wannan gidan..?
Tana tunanin ko yayanta da suka auri masu da shi ba wacce ta samu gida kamar nawa,daganan ta sare tasan na riga na sha kwana daman ai abunda ya baka dariya watarana shi zai baka Tsoro.
A babban bedroom din gidan Maa ta saukeni tana min addu'a su kafaya ne suka rika zagayawa da mutane suna ganin gidan da suka dawo suka baje suna labarin gidan Yaya Mariya tace"Faa'iza mutumin nan kudi garesa kenan"
Ashe bamu ga kudi ba sai da Maa ta saka aka bude dayan bedroom d'in shake da akwatina bakwai babu abunda babu aciki harda zinare sai makulin mota kamfanin Peageua,ashe itace muka gani a haraban gidan,tab ashe kudin da yabani na kayan cin bikin ya hada lefensa ba tare da ya gayamin ba.
Kayan ciki kuma masu tsada ne da yarari,bakin dangina ya kasa rufuwa dai masha Allah ke tashi,Hajiyar Dala da Anty Nasara ke fadin darajan kayan da Tsadan su, tuni ta saki ta san duk hassadann mai hassada Faa'iza dai ta dace da gidan kima da arziki.
Yaya mariya da Yaya Asiya fadi suke"Fa'iza. yanzu ke ce da wannan kayan alfarman harda mota..?
Allah mai hikima in yaso sai ya fidda matacce acikin rayayye in kuma ya so sai ya fidda rayayye acikin mattacce"
Daman haka Allah yake lamarinsa ga Faa'iza ta hau wani mataki na rayuwa,ahalin kuma bata da ilimin boko kuma bata da kyau sannan ba fara bace sannan ita ba kowan kowa ba. Allah ta rike shi kuma ya bata Engr a matsayin miji domin ribar Hakurinta.
Ni ko ina gefe bana mgana sai mirmishi zuciyata da gangan jikina sun cika da kewar Engr da Tunaninsa na kara gwada kiransa ban samu ba. kamar ya kashe wayarsa ni duk wannan kayan basa gabana na samu kwanciyar Hankali da salama shine abunda nafi kwad'ayi.
Ammi bakinta har kunne itace kiran Abba tana fad'a mishi har Goggo sai da ta kira Badariya ko Fadi take"Masha Allah Anty Fa'iza ta tako wlh.."
Nana Fatima sai faman daukan Video take saboda su Hafsah daman sun ce ta Dauki musu duk abunda ya wakana su Anun ko tuni sun fice suna chan wajen Lilo suna wasa
Sai yammah su Maa suka koma gida da Daddare Direba da su kafaya suka kawomana abinci kala kala da ababen sha,Daman Maa ta fad'ama Ammi karfe takwas zamu tafi tunda tafiyar Mota ce in muka isa za'ayi taron gabatarwa bayan la'asar na chan garin haka suke yi in bako ya shigo cikin su,anayi masa taron Introduction kowa ya san shi,shima yasan kowa.
Sai dare Engr ya kirani ina Dauka sai na sakamai shagwaban da bansan na iya ba ina fad'in"Tosin yau ka sakani cikin Damuwa.."
Duk yau fa ban ji muryan ka ba.?
Shima cikin damuwa yace"Tife na Meeting muka yini yi fa. kema kinsan ban samu dama ba ne da sai na kiraki..To yaya..?kun isa tun dazu ko..?kuna gidan Papa ko gidan ki.?
Kinsan fa Saboda zumudin nafara jin muryan ki ko naji sanyi yasa ko Sweethear ban kira ba"
Ni na zayyane masa abunda ya faru sai naji ya sauke ajiyar zuciya kafin yace"Alhandulillah. Gobe sai da rana zan kariso benue lokacin kun iso kuma ko..?
Sai na dagamai kai kafin nace"Maa ta karbeni sosai ita da su kafaya harda Paapa shima yana yi ma addu'a"
Cikin jin dadi yace"Haka suke ba su da damuwa ballatana su san ina son ki, so suna Daraja duk abunda nake so ne"
Na aminta da mganarsa cikin gamsuwa nace"Naga wasu kayan kuma har da mota fa?ka manta ka bani kudi na siya wasu a kaduna..?
Kai tsaye yace"me kika gani..?
wai wad'anan yan kayan..?me kika sani akan Abdulbasit Faa'iza..?
Ai baki san komai ba sai zama yayi zama sannan kila zaki kara sanina sai kuma in nayi wani abun zaki ce daman Haka kake Tosin"
Sai da dai ya sakani Dariya mun jima muna hira kafin yace naje na kwanta Saboda tafiyan gobe.
Ai ban kwanta ba na Dauro alwala na fara jera salollin godiya ga Allah har sai da na gaji. washegari ma Daga gidan su Engr aka kawo mana abinci Direba ne ya kawo mana wannan karon da wuri muka shirya Maa da su kafayat suka Biyo ma Dauke da katuwar BMW din Papa da Direba aciki aka sakani sai Ammi ta dawo nan su kafayatu kuma suka koma wacce muka zo da ita.
Tun safe daman mukayi waya da Engr yace shi sai 12pm zai baro Edo zamu hadu achan to muna Hanya sai yayi ta kirana kunyar Maa yasa ba na Dauka sai ya koma yana kiranta bini bini sai yace"How is Faa'iza? Is she ok.?
Ita bata damu ba sanin Halinsa da naci kan abunda yake so.
Tafiya tsakanin Abuja zuwa Benue akwai nisa,mun ma yi gudu sai 2pm na rana muka isa asalin Babban gidansu muka sauka wato gidan Sheik Abdulbasit Abdulfattah.
Ya'ya da jikoki cike da gida gabadaya kannen Paapa da yayyensa sun zo da iyalansu,gida ya cika da mutane gasu nan kowannen kalansa Dabam Dabam sai dai sun yi shigan su na yaren su musamman ma mazan.
Dakin Hajiya Kudirat aka saukeni su Ammi kuma sauran dakunan haka ta rikeni tana yaren su ni ba ji nake yi ba. tsohuwa ce fa ta tsufa gaskiya sai dai Hutu da jin dadi.
Daman Hijabi na saka har kasa,sai wata farar amtafa super mai baki da Fari shiyasa ma Hijabin jikina Fari ne,sauran matan kannen Papa da yayyensa ma suka yayyemeni suna ta yare hatta Maa naji itama ta juya yare su kafayatu ko muna zuwa sun shige cikin Dangi.
Ankawo abinci su amala da miyar kuka taji ganda da nama sai jallop d'in shinkafa da kaza abinci dai cima kala kala suma su Ammi suna chan ana karrama su.
Bayan mun yi sallah ne muka natsa ni daman ina tare da Anum da Falaq ne. Maa tayi musu bayanin yanayin taron kayan da zan saka tace matar Uncle din Engr Tobi. Bimpo kenan zata kawo nawa kayan,ni kuma sai daga baya su Ammi suka zo dakin suka sameni Anty Nasara na juya baki tana fadin"Jama'a kun ji yadda yare ke tashi.?
Yaya Mariya tace"Komai sai da sanadi ga shi Sanadin Fa'iza nazo tsakiyar abun naci kuma amala kamar cikina zai fashe"
Dariya aka saka mata Anty Fadila tace"Kai dangin sun burgeni. komai tsab gasu wayayyi kamar ba yarbawa ba."
Hajiyar Dala tace"Uhm ai naga abun mamaki ayi ta cewa yarbawa kazamai masu kashi a leda kaza kaza ni ko da muka zo ban ga haka ba ga su nan Tsab da su kamar ma mu hausawan"
Ammi tace"Ai in kin lura sun surka kowani yare a cikin su, ba kabilanci ko jin kyamar wani yaren".
Haka dai suka yi ta hira suna Tattaunawa ni dai bana saka musu bayan la'asar Maa tace daman za'a fara tarom muna idar da sallah Wata yar matashiya tazo shiryani Wanka ma sake na fesa turaruka sannan aka bani wani less baki da Fari na saka Riga da zani ciki da alaku har Daurin zanin matar ta dauramin ta min Daurin Kallabi irin na su,sai dan kunne da sarka ga murjani da ya saukomin har Cikina hannayena ma ta sakamin su da yawa,Takami baki ta bani mai tsini yana da igiya sai karamar Jaka pos ligth makeup tayi min sai nayi kyau kamar bani ce uwar yara Hud'u ba.
Suma su Anty Nasara sun shirya,abun dariya har da ciki da alakun suma suka yi suna fadin suma fa duk an zama daya,Har su Anum suma an shirya su da kayan yarbawa su kafayane da wannan aikin yara sai suka saje kamar anan muka same su.
Sai biyar akace su Ammi su fito dani Ita da Hajiyar Dala a haraban gidan an shirya kujeru da kuma in da zamu Zauna sai da muka fito naga ashe Engr ya iso ban sani ba,domin bai kirani ba shima irin less din jikina ne da shi yaci hulansu na ashoke har da karyata gefe sai alokacin na hango kamarsa da yarbawan gefensa aka zaunar dani ina zama ya ramkwafo yana Fadin"Eh Tife..Tife.."
Idanuwana na kan mu shiyasa na kasa juyawa sai dai mirmishi masu Hotuna nata aikin su,sai gani na fito ba mayafi Cikin mutane sai faman kunya nake ji na kasa sakewa shima daya Fahinci haka sai yace"Ki yi hakuri yanzu za'a gama
Nima fa ina jin kishin yadda wasu mazan ke kallemin halalina"
Tokarinsa nayi da gwiwan hannu na ya koma gefe yana dariya, an yi jawabi Maa ita ta gabatar dani ga Hajiya Kudirat itace head of the family,sai kuma suma suka min jawabin maraba da Yarbanci da Turanci Engr yace a fasaara da Hausa,dole a ka samu wani ya yi mgana da Hausa kuma nasan saboda ni ya yi sai naji na kara son shi.
haka aka rika min layi ana gabatar min da su Daya bayan d'aya Engr ya koyamin irin gaisuwan su kamar na indiyawa kayi kamar zaka Duka sai a dafa kanka a saka maka albarka sunaye ko wlh na kasa rikewa ga sunan birjit suna da yawa sosai wlh kamar tsaki.
An ci an sha kuma an yi rawa Engr yaso yajani muyi rawa naki sai yaja su Anum da daman suna tare da shi. suna ta rawa an zubda kudi kamar ba'a son ranar su ba Anty Nasara da su Nana Fatima sun shiga sun sha rawan su,ko ajikinsu ina gefe ina Dariya,sai mangriba aka tashi na samu kudi tunda duk wanda za'a gayamin sunan shi in na gaishe shi sai ya bani kudi sakamakon gajiya yasa ina sallar isha'i sai barci ko Engr ban nema ba,su Anum ko na Tare da shi bama Daki daya muka kwana da su ba Wajen Maa suka kwana.
Da safe kuma akayi walima,gabadaya aka taru afalon gidan manya da yara aka yi karatun Qur'ani izifi Ashirin,naga ranar ilimi naga kuma gidan ilimi ni na fara Bude karatun Daga suratul Muhammad muka fara,Engr kuma shi ya Rufe karatun ashe shima haka yake da kira'a an rarraba charbi da Dardumai sai da yammah kuma akayi party shi a Hall akayi na cikin gari shima an ci an sha kuma an chase,sai washegari ni da Engr zamu wuce Edo su kuma su Ammi zasu koma kaduna.
Mu muka fara tafiya gabadaya kaya na daman suna hade ne waje d'aya. Ammi ta yi ta jadaddamin na rike kamshi da Tsabta biyayya da sanin kan miji sannan bata jina ta bangaran girki,Mun rumgumeni ni da Anum har sai da nayi kwallah tace zata bini nace zan je da ita Engr ma yace da ita zamu tafi Ammi ce tace ba inda zataje.
Sai da naga rabuwan da gaske na fara kuka suna ta min nasiha na rumgume yaya mariya da Yaya Asiya suna ta fadin Fatan alheri Fa'iza.
Haka ni da Badariya kamar wasu yara A babbar Prado din Engr fara zamu tafi dagani sai shi sai Direba.
An kai ni wajen Hajiya kudirat ta sakamana albarka sannan ta bani kyautan warwaro da ashoben su da murjanai,sai duka kannen Papa da yayyensa suma na samu kyatuttukan na kudi da kaya tare da addu'a daga garesu.
Gabadaya kuma suka rakomu har bakin mota,Abaya na saka maroon mai zanen baki sai Nana Fatima tamin nadin mayafin baki nayi kyau sosai duk da ina kin sakawa sai gashi na saka takalmin kafata ma baki ne,mai Tudu duka kayan jikina ba na kudi kad'an cikin ma wanda muka siyo ne da Ammi ne.
Ina ji ina gani Ammi ta sakani a mota suna d'agamin hannu Engr ma ya shigo Direba ya rufe shi ya tsayama Lallashin Anum ammh tana ta kukan sai ta bimu a raina nace Anum ta girma bazata daina shagwaba ba.
Mun dauki hanyar Edo cike da kewa na tuna Maa yadda ta rika sakamana albarka da fatan zaman lafiya itama tace duk abunda nake so na kirata ita uwa take gareni.
Hawaye haka suke bulbulomin Duk Dauriyan Engr haka ya rumgumoni yana Lallashina kamar karamar yarinya fad'i yake"Shii..am sorry matata..Ko mu koma ne kawai mayi shagalin mu achan..?
Wata uwar harara na Dago ina hawaye na makamai sai ya yi Dariya yana Fadin"To ba ke bace kina ta kuka ina kike so na saka raina don Allah..?
Hawayen ya fara sharemin yana Fadin"Kin yi bamkwana da kuka har Abada sai dai na farinciki.
Ki bari kawai mu sha kara'in mu ba gani ba..?ko ni ne baki son gani kike kuka saboda mun baro su..?
Sai na kasa mgana na sunne kaina a saman kirjisa ina mirmishi kamar yadda na yace bayason kuka dole na shanye hawayena ina ji ya saka hannayensa duka biyu ya rumgumoni.
Kaina na saman kirjinsa yana lallashina kamar wata karamar yarinya ni ko na lafe ina samun natsuwa Lokaci d'aya da natsuwar zuciya.
Sai kuma na fara tunani had'e da kuma Fargaban wata irin kuma rayuwa zan fara gudanawar tare da Engr..?
Shin wani irin bambamci zan samu a zaman aure na da shi..?
Fatan farinciki nake yi ma kaina ko ya ya ne. Fargabata har da yadda nayi aure abunda ban taba tunanin yinsa nan kusa ba.
*Janafty*
[8/2, 1:50 PM] U.M Collection ZMFR CM: *KNKB3019*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/HXUeSwhG3NGL9o1va9kUkT
IN KUN JI KIRA SAMU NE! JAMA’A NA CE KUNA DA LABARIN HAJIYA FATIMA MAI KAYAN MATA NA ASALIN MUTAN SOKOTO, IN BA KU DA SHI NA CE KU HANZARTA NEMANTA DOMIN FITO DA MARTABARKI TA ‘YA MACE. HAJIYA FATIMA TA YI FICE WAJEN KAWO ZAFAFAN KAYAN MATA MASU TADA TSOHUWAR SOYAYYA, BA IYA NAN BA TANA BA DA HA’DIN DA DUK KIKA YI AMFANI DA SHI, BA KISHIYA BA ‘KARYAR MACE MIJINKI YA JI DADINTA SAMA DA KE, HAJIYA FATIMA NA DA GUMBAR UKU BALA’I, GUMBAR MATSI, GUMBA MAI RAWANI, GUMBAR UBAN BUDURWA, IN DAI MATSI NE DA NIIMA KE KARE ZANCEN, DUK MACCEN DA MIJINTA BAI TA’BA MATA KUKA BA TA ZO TA GWADA KAYAN HAJIYA FATIMA SAI TA RUFE BAKI NAI GUDUN MAKWABTA SU JI YO SU.
MACEN DA KA FAMA DA ZUBEWAR NONO KO KANANAN NONO TA ZO TA GWADA MAGANIN HAJIYA FATIMA A KWANA HUDU KACAL ZAKI FARA GANIN SAUYI.
MACEN DA KA FAMA DA RASHIN KIBA BABU HIPS BA NONO, BA MAZAUNAI TA ZO TA GWADA MAGANINMU DA IZININ ALLAH TA QARE DA WAGGA MATSALA
AKWAI MAGANIN SANYI SADIDAN WANDA DUK KIKA JARABA SHI SAI KE BASUWA TUKWICI SABODA INGANCINSA, DUK WANI DATTIN DA KE MARARKI HAKA ZA KI GA YANA FITA GUDA-GUDA
AKWAI BA’KAR ZUWA WADDA KA BA’KIN AIKI KAN ‘DA NAMIJI DUK KISSHATA KE GAMA DA TIJARAR ‘DA NAMIJI.
AKWAI HATSABIBIYAR MALLAKA, WANGA SET NA NA MANYAN MATA, GUMBA,TSUMI,ZUMA DA GARI NE NA MALLAKA BAN DA MAI KISHIYA.
KU NA IYA TUNTU’BATA TA 08167888934, DON ALLAH IN BA SHIRYA SIYE KIKA YI BA KAR KI MIN MAGANA. MUNA GARIN SOKOTO MUNA AIKE KO INA CIKIN AMINCIN ALLAH
Dayake mai taxi d'in yasan gari kuma Engr ma ba baya ba.
cikin lokaci kankani sai gamu a kofar Apartment din Su Anty Fadila kamar suna jiran mu ko nace suna jin Dirin mota suka fito gabadayan su harda yaran.
Anty Fadila tundaga nesa take faman washemin baki ni ma haka ina ta so na karisa gareta da Sauri ammh Engr yaki sakin hannuna,Sai da na kallesa da wani irin duba da muka kadai muka san ma'anarsa sannan ya saki Hannuna yana min mirmishin nan nasa mai narkan min da zuciya.
Da sauri sauri muka tari juna mu da Anty Fadila muka rumgume juna kamkam muna murnan ganin juna mijinta kuma suka yi hannu da Engr,Mai taxi din na jiran mu tunda Drop ne zai kai mu har gidan Yaya Ishaq ne.
Dagoni Anty Fadila tayi cikin tsananin mamaki tana karemin kallo kafin tace"Fa'inmu ce wannan kuwa..?
Sai ta bani dariya har kara tattaba kumatuna take yi,ina Dariya mijinta na tayamu Engr kuma na faman mirmishi ya kame fuskarsa kadan.
Kallon Engr tayi tana fadin"Engr ranka ya dade a enging aka saka mana Fa'in namu aka sauyata?
Ya yi dariya kamar bai zai yi mgana ba sai daga baya yace"Ni ne enging din kenan Anty Fadila.."
Sai da ya fad'a sannan taji kunya taja hannuna muka wuce Engr da Babansu Falaq suka tafa kamar sun shekara da sanin juna Suka bi bayan mu su da yaran dake ta gaishe da Engr.
Allah sarki dan'uwa mai Dadi abubuwa na musamman Anty Fadila ta shiryamana,A falon gidan muka fara yada zango aka gaggaisa,su falaq sun zo wajena suna gaisheni na jawo su na rumgume ina tambayan su makaranta,Engr da Babansu falaq ko kamar sun shekara da sanin juna sai Hira kawai ta Tsarke a tsakanin su tunda ma in ka kallesu zaka iya auna shekarun,saboda yanayin jikinsu sannan kuma dukkansu suna da Ilimi da wayewa shiyasa saurin sabo bai yi musu wahala ba,ballatana Engr da na sani ko a akan hanya ne sai ya bar wanda ya san shi Tsabar mganarsa da iya mu'amala da Mutane.
Kiran sallar mangariba ne ya tashe su suka fita masallaci su da yaran maza ni kuma Anty Fadila tajani Bedroom dinta domin nayi sallah.
Bayan na dauro alwala ta bani Sabon Dogon Hijabi nayi sallah,ita kuma ta fice inaga dakin yaran taje tayi sallah ina zaune ina azkar sai gata ta dawo.
Gefena ta zauna muka kara gaisawa cikin matukar jin dadi kaga wani naka alokacin da bakayi Tsammani ba.
Kallona kawai take yi tana karawa kafin tace"Ikon Allah Fa'i ko dai su Ahmad sun samu kani ne..?
Mirmishi nayi kafin nace"Ko d'aya Anty Fadila kawai kwanciyar Hankali ne na samu shiyasa"
Anty Fadila sai ta rumgumo gefen kafadata tana Fadin"Am happy for u Fa'in mu. Wlh ganin ki kawai da nayi sai na kara jin Hankalina ya kwanta na Tabbata kin yi dace Engr mutum ne nagari mai nagarta da har ina jin Haushin baki komama Ishaq ba,ganin yadda ya susuce akan ki,ammh daga baya sai na Fahimci wani abu duk sanda Allah ya baka abu ka yi wasa da shi to fa in ya subuce maka ba lalle ya iya dawo maka ba"
Kai tsaye nace"Hakane Anty Fadila".
Kumatuna taja kafin tace"kinga yadda kika koma..?kin kara fari kin kara kiba kin kangi kuwa.?kin zama yar gayu Fa'in mu..?Wlh tallahi in ba wanda yasan ki ba in zamu yi ta kwana muna rantsuwan kina da Saurayin yaro ba mai yarda damu ikon Allah"
Dariya nayi kafin nace"Ni kaina ina mamakin chanzawata"
Anty Dadila ta karbe da fadin"Haka ake so. Allah ya kara zaunar daku lafiya da soyayya duk da naga akwai ta,Sai kuma Allah ya kawo rabo na alheri ina so naga danku ko yar'ku ke da Engr"
Cikin raina na amsa mata ban iya amsa mata a bayyane ba nan muka zauna muna ta hiran mu ta kira Abba ta fad'amai gamu a gidanta har ta bani shi muka gaisa ina jin kunyarsa shi ko ajikinsa faman tambayanta yake yi mun dawo lafiya..?
Yana gida Lokacin har Ammi sai da ya bata muka gaisa tana min tsiya da fadin"Ina fatan kin kara kiba kin zama lukuta yanzu.?
Na kasa amsa ma Ammi sai Anty Fadila ne ta karbi wayan tana zuzuta kyan da nayi Ammi sai hamdala take yi,har Nana Fatima sai da ta kira ai tana jin muna Lagos ta daka Tsalle tana Fadin"To wlh nima zan duba Hanya saura ayi min danwaken zagaye"
Muka yi ta dariya mun manta da mazan har sun dawo suna falo sai da Babansu falaq ya leko yana fadin"Sai a gaya mana yan'uwanta ka,an wani shige daki to muna dai mun zama abokai"
Dariya muka yi gabadaya sannan muka fita saman Dining din su muka had'u gabadaya mukaci abinci Shinkafa Fara da miyar albasa,sai Pepe Chicken,da kebbab sai Lemun arbarba mai apple,ina kusa da Engr bai ji kunyar su Anty Fadila ba. ballatana yara sai ya bani abinci a baki kamar yadda ya saba na rika nokewa sai ya kalli Anty Fadila yana fadin"Kin dai ga kanwarki ko..?
Mun saba tun a gida da kaina nake ciyar da ita kuma yau kawai Saboda ta ganki ta fara sauya hali"
Babansu Falaq ne yace"To ka sani an fa kule acikin daki"
Anty Fadila ta mintsi hannunsa tana Fadin"Kasan dai bazan hana ayi ma Engr love ba ko..?
Kawai nasan kunya take ji kasan kanwar tawa da kunya da kun koma gida zaka ga ta saki"
Kai tsaye Engr na kallona yace"Tabbas nasan ko tana da kunya ammh ma fara kokarin yaki da wannan kunya tsakani ga Allah tana hanani kara'i na yadda nake so"
Kunya kamar na nutse don ma yara suna gefe ne kuma hankalin su baya kanmu Anty Fadila suna ta Dariya ni dai dakyar na iya cin abincin nan shima kadan bada yawa ba,Engr ma ganin ban wani ci ba shima bai ci da yawa ba nasan Halinsa bai iya sakin jiki yaci abinci a waje sai ya Dawo gida mun ci abincin tare.
Bayan mun gama cin abincin mun dawo Falo ne,Anty Fadila ta kalleni tana Fadin"Ammh nan zaku kwanar mana ko..?
Ina rufe bakina Lokaci daya ina Fadin"Kwana kuma..?A'a gobe zamu tafi kano yanzu nan ma daganan yaran nan zamu je mu gani,kafin mu koma masauki."
Engr na jin mu bai sakamana baki ba,Anty Fadila ta rike baki tana Fadin"Shine baku zo da wuri ba Fa'iza.."
Engr ne yace"To kisan amarcin ne har yanzu bai sakemu ba"
Dariya tayi kafin tace"To kun sanar da su kuna tafe..?
Sai Engr ya kalleni Saboda bai sani ba ko na kira su ni kuma sai nace"Ban fad'a ma Zainab din ba, ammh bari na kirata yanzu"
Kiran sallar isha'i yasa suka tashi zuwa masallaci mu kuma muka muka shiga ciki.
Bayan mun idar da sallah ne na Kira zainab tana tsokanata da Amarya amarci yasa bata samuna a waya kai tsaye nacemata"Ba ma kasar ne ni kuma ban ce ya siyamin wani layi ba. wayar tana kashe ne sai da muka dawo na kunnata"
Zainab ta fara fadin"Uhm su Maman Amir to ya amarcin..?
Allah yasa an samo mana d'an Honeey moon"
Ina dariya ban biye mganarta ba nace"Kina gida ke da yaran ne..?
Kai tsaye tace"Ina gida yau ma ko aiki ban fita ba,bana jin dadi.
Yaran kuma suna Falo tare da Honey da Mama"
Cikin zolaya nace"Ko dai ko dai..An sama ma Islam.."
Kafin na rufe baki ta tareni da fadin"Ba Ameen ba. Haba Maman Amir ai haihuwa mun bar ma sabbin Amare irin ku"
Kalamanta suka sakani Dariya ita da tayi uku ni hudu gareni ammh take tunanin haihuwa sai irin mu Allah Sarki nima ina so Allah ya bani ko Domin Engr dake son ya'ya a rayuwarsa.
Kamar daga sama Zainab taji nace muna nan shigowa anjuma.
Cikin mamaki tace"Bangane ba..?
Kina lagos din ne..?
Kai tsaye nace"Tun shekaran jiya ai ta nan muka sauka,gamu gidan Anty Fadila zamu kariso"
Sai ta saka Ihun murna nayi dariya ina fadin"Kada ki fad'ama yaran nan fa so nake kawai su ganni. Kuma.. kuma ni da shi ne,ki fad'ama megidan naki"
Ban jira cewarta ba na katse kiran nasan Halimta ihu zatamin ban damu da address din gidan ba tunda nasan Anty Fadila tasan gidan ko ita zatayi ma Mai Taxi din kwantance wajen.
Karfe tara saura muka yi shirin Tafiya bayan naje na dauko musu ledan Tsaraban su na bama yaran suna ta Godiya Anty Fadila ta bani wata Gumba mai shegen dadi tace haka nan zan rika shanta nasan Darajan gyaran jiki yanzu shiyasa ba na wasa da shi yanzu.
Babansu Falaq ya yi ma Direban Taxi kwantancen gidan nan da nan ya gane wajen mun rabu cikin jin dadi,Engr da Baban Falaq suka karbi lambar juna har muka kule suna d'agamana Hannu.
Ban dauka zan ji fad'uwar gaba ba sai da nasan mun d'au hanyar zuwa gidan Yaya Ishaq sai naji gabana na fadi ina rasa natsuwata Engr ya lura da haka ko daga yadda Hannuna ya jike da Zufa dake cikin nasa.
Matse hannu nawa ya yi sai da na juyo ina kallonsa sannan yaa jinjina min kai alamun kada na damu sai na samu natsuwa naga mai zai Dameni gani kusa da Engr in har indai ina kusa da shi to na kaddara sai dai Kuduran Allah zan iya neman wani abu na rasa sai na dora kaina kafad'ansa ina Sauke ajyar zuciya shi kuma sai ya kara rikeni Cikin Salon kulawa irin ta shi.
Ba jimawa sai gamu a Anguwan Apapa,Dayake kuma Gidajen suna Tare ne waje d'aya bamu sha wahalan ganewa ba,tunda daman Anty Fadila tace 16 ne lambar gidan.
Sai da muka fito daga Taxi din sannan na Kira Zainab ringing daya ta Dauka da Sauri tana fadin"kun kariso ne Maman Amir?
Sai da na amsa mata kai kafin nace"Eh muna waje"
Sai tace bari su fito kafin mu yanke kiran a tare,gefe na koma gabana na Tsananta fad'i sai Engr ya matso gareni ya rike hannuna cikin nasa na Dago ina kallonsa sai ya sakarmin Mirmishi nima na maida masa.
Mun kurama kofar gidan ido a kan idanuwan mu Zainab ta fito,Sanye da Doguwar Riga na wani yadi maroon ta yafa wani siririn bakin mayafi bayanta kuma Yaya Ishaq ne cikin Jallabiya mai ruwan madara.
Zainab na ganin mu ta saki mirmishi nima sai na sakar mata ta fara taku zuwa garemu muma sai muka fara takawa Hannuna gam cikin na Engr. muna tafe jiki na gugan jikin juna.
Idanuwana Zainab suke kallo ammh bansan ta yadda akayi ba idanuwana suka sauka kan Yaya ishaq ba,ido hudu muka hada da shi,Mirmishi nayi masa sai yayi kasa da idonsa ammh bai dauke ba gabadaya,shi kuma ni yake kallo tare da kallon hannuna cikin na Engr dake Sarke da juna.
Gabana ya yi wani ras!har sai da takalmin kafata ya turgud'eni zan fad'i Engr ya yi saurin rikoni yana kallona nima shi na kallah cikin sanyin muryansa yace"Are u ok..?
Da kai na amsa masa sannan ya sakeni ammh bai yarda ya saki hannuna ba.
Sai da muka kariso gabda juna sannan ya sakeni ganin kuma Zainab ta bude hannuwanta bakinta kamar Gonar Auduga tana fadin"Oyoyo Oyoyo ga maman Amir"
Nima sai na bude hannayena muka Tarbi juna cikin fara'a muka rungume juna.
Kafin mu saki juna muna bin juna da kallo cikin fara'ar da taki barin fuskokin mu dani da ita.
Yaya Ishaq ko hannu ya mikama Engr cikin jin nauyi suka yi musabaha tare da gaisawa Engr ko a fuska bai nuna masa da wani abu ba.
shima ya tarbesa cikin Fara'a kamar wani abu bai taba shiga tsakaninsu ba
Zainab ta rike hannuna tana gaishe da Engr ya amsa mata cikin fara'a da Tambayan yara.
Tace duk suna lafiya tana kamkame da Hannuna tace"Bismillah mu shiga ciki"
Sai muka yi gaba,ni da ita su kuma suka bi bayan mu duk sai naji na takura na kalli Ishaq ta gefen idanuwana sai da gabana ya fadi da ganin irin ramar da yayi kamar wanda ya shekara yana jinya.
Shima duk da ban sani ba ya kalleni sannan nasan yana mamakin sauyawata.
Zainab ke min mgana kasa kasa da cewa"Kin ganki kuwa maman Amir..?ko dai an samo mana bby Honeymoon ne?
Dariya nayi ban yi mgana,ita ta shiga gaba tana janye da hannuna har cikin Falon,yaran duk suna falon Har da Mama da Shema'u.
Zainab na kan gaba ta kareni tace"Anum.."
Anum dake zaune kan kujera tana duba littafan makarantar ta yan SS1 ce,First time,musty na zaune a kasan Cafet ya na zanensa na fama Ahmad Kuma na gaban Tv shi da Farhan suna kallon Mbc3,Amir kuma na daga chan gefen Mama wani Novel din Turanci ne a hannunsa yana karantawa Fadil na kan jikinsa ya lafe kamar mara lafiya.
Kiran sunan Anum da Zainab tayi yasa duka yaran suka dago suna kallonta Batayi mgana ba illah kaucewa da tayi na bayyana afalon. ina saka yarana a ganina naji idanuwana sun cika da kwallar Farinciki da wani irin kewa da ban taba ji ba.
Gabadayan su suka mike har da Amir kuwa da naga ya kara zama wani Zabgege ga tsawo ga jiki irin na Ubansa Dukkansu bakin su ya kasa motsi mamakin ganina suke yi,Ahmad ne ya bude murya kafin yace"UMMAA..!
Sai na gyada mai kai sai hawaye sharr na Farinciki suka zobomin na zube gwiwoyiyina a kasa na bude hannayena ina fadin"Umma ce Ahmad di'n Umma"
Ai da gudu ya rugo ya fada jikina sai ya fashe da kuka Musty ma ganin haka ya watsar da Abun da yake yi ya iso gareni yana fadin"Umma..!
Sai kuka shima nima kukan nake yi,Farhan ma ya kariso yana kallona yace'Umma..'
Kamar yana tamtama sai na jawosa jikina na hada da su Ahmad na Rumgume ina fadin"Farhan din Umma ina Fadil..!
Sai kawai naji an chakumeni ta baya ashe Fadil ne bakina yaki Rufuwa ina kuka ina Hawaye ina Dariya Lokaci daya ina fadin"Fadil..Fadil d'in Umma"
Yana Dariya yace"Umma umma..Ina kika tafi bana ganin ki?
Ya fad'a yana shafa Fuskata kamar yana Tantamar ni ce ko ba ni ba ce.
Ni ko kuka ya hanani mgana Duka na hadasu na rumgume ina Hawaye ina Dariyan jin dadi raina nake jin wani salama da kwanciyar Hankali suna shigata
Amir da Anum sun kariso gabana ammh sun kasa bin ayarin yaran,sai da na ji Anum na fadin"Umma mu kin manta damu..?
Tafad'a idanuwanta taf da kwallah sai na mika mata hannuna Daya ta kama ina Hawaye nace"Ina ni ina mantawa da Anum din Umma"
Amir dake gefe yace"Umma ita Kadai..Ita k'adai..kika gani"
Yafada muryansa tana wani irin rawa,da kuma wani kewa a cikinta.
Na dago ido na ina kallonsa sai na mika masa Dayan hannun ina fad'in"Babana bazan manta dakai ba kaima zo. kuzo wajen Umma"
Gabadayansu suka taho atare suka Duka suka bi bayan kannensu a tare Amir da Anum suka fashe da kuka nima kukan nake yi kasa kasa har yana bayyana ammh na farinciki.
Mama dake gefe ta Dauke kwallarta tana mirmishi,Dazu taga Zainab tazo ta kira Ishaq kila zuwan Fa'izan ta shaida masa Allah sarki Uwa. ita uwa tana da girma girman da Ubangijine kadai yasan iyakarsa.
shema'u ta kalli Mama kafin tace"Maman Innar su Anum ce..?
Mama ta gyada kai batayi mgana ba Ranta ya cika da wani nauyi da ta rasa ko na menene tasan dai na kunya da nauyin Fa'iza ne sannan da Tausayin yaran nan.
Ba ita kadai ta share kwallah ba Hatta Ishaq sai da ya juya baya yana goge kwallar da suka cika kwarmin Idanuwansa. Engr na kallonsa sai ya nuna kamar bai gani ba. yana Daga baya ya sagale hannayensa a bayansa yana kallona ni da ya'yana wani irin kauna da soyayya da baisan yana yi min yaji ya kara sarkeshi, ya tabbata ba karamin kaddara bace ta fidda ni daga gidan mijina sannan ya kara Godema kaddara data kaddara auran mu.
Zainab ma sai da ji kwalla sun kawo mata,sai daga baya baya ne aka samu sauki ammh ko da yaushe yaran cikin kiran Umma suke Fa'iza ba a iya Rayuwar ya'yanta take da tasiri ba har a rayuwar su Farhan domin mai kulawa dakai baya bace maka aranka har abada.
Zainab ce ta matso tana Fadin"To ku saki Umman naku ta zauna ta Huta mana"
Jin haka yasa su Amir suka tashi da Musty Ammh Ahmad da Fadil makalemin sukayi kamar zan gudu haka na mike suna rike da hannayensu Ahmad bakinsa ya bude fadi kawai yake yi"Umma nan zaki kwana..?
Fadil kuma"Umma ni zan biki gidan ki"
Ina Dariya nace"Yaran Umma duk sun kara girma"
Na fada ina kara ganin girman Ahmad da Musty Farhan da Fadil har mamakin girman yaran nake yi mutsy fa ya kamo tsawo na Amir ko in muka jera sai ace yayana ne ni daman gani ba Tsawo kuma ba wani jiki ba yar Firit don ma na kara kumari da a baya ne kila sai dai ace nice karamar su sai ko in anga Fuskar ta manya.
Engr ne yayi gyaran murya kafin yace"Umma kad'ai kuka sani ko..?
Sai alokacin su Amir suka gansu kunya ta kama Anum baki bude tace"Laaa Baba.."
Amir ma yace"Baaba.."
Sai su Ahmad suka tsaya suna kallon su,Amir yace"Sannu da zuwa Baba.."
Makale kafad'a ya yi kamar yaro kafin yace"No..Oya nima hug irin wanda kuka bama Umman ku"
Sai suka tafi a tare suka fada jikinsu ya Rungumesu cikin Fara'a.
Ahmad da Musty suka kalleni sai nayi mirmishi na gyada musu kai ganin suma yana mika musu hannu.
Sakin su Amir yayi ya rumgumosu yana Fadin"Yauwa ya'yan Umma da Baaba.."
Harda su Farhan daya bayan Daya ya dinga dagasu yana kuma kiran sunayen su mamaki ya cika su Musty yace"Kai ya sunan ka tunda mu kasan sunan mu.?
Yana dariya yace"Ni sunana Baaba baka ji su Amir sun kirani da Baaba ba..?
Musty ya kallesa ya kara kallonsa kafin yace"Baaba..?
Cikin alamun tambaya ni ya kallah alamun hakane..?
Ina shirin nayi mgana sai kawai muka hada ido da Yaya Ishaq ya kureni da ido sai na kasa mgana na maida kaina kasa.
Ahmad ne ya yi karaf yace"Sunan ka da mamanka ta saka maka"
Engr ya kwashe da dariya,irin Dariyan da yake yi in yana jin Nishadi. kafin yaja kumatun Ahmad yace"Sunana da mamana ta sakamin Abdulbasit ne."
Zai kara mgana Anum tayi saurin cewa"Ahmad shima Baban mu ne kamar Daada.."
Sai ya washe baki yana Fadin"Baaba..Sai su Farhan suka Dauka shi kuma yana ta amswa da Fara'a ina ganin Fara'ar take fuskarsa ta kaunan yara acikin idanuwansa.
Zainab ta ce mu karisa ciki muna Tsaye sanda ya mike Dauke da Farhan da Fadil lokaci daya yana rike da Hannun Ahmad,Su Anum suka bi bayansa kallona yake yi da alamun nagode Fa'iza kin ga ma bani komai. Tunda kika saka na zama Uban ya'yanki nima.
Sai da muka kariso falon naga Mama ita tafara gaisheni sai na sauko daga kan kujera na duka ina gaisheta har Gaban Abada Mama uwa ce agareni bazan taba kin darajata ba ta amsa cikin Fara'a da nauyi.
Engr ma yadda nayi haka yayi sai naga Mama na kauda kai tana sharan kwallah fadi take yi'"Allah ya baku zaman lafiya Allah ya kad'e Fitina"
Ba kunya Engr ya rika amsawa da Ameen Ameen.
Sai alokacin na iya dagowa na gaida Yaya Ishaq ya amsa fusakarsa cikin yanayin da ban gane ba.
Zainab Shema'u ta saka ta kawo mana ruwa da lemu,yaran kuma suna tare da Engr duk tambayan da suka yi masa sai ya basu amsa shi fa yadda yake iya zama da manya haka yake iya zama da yara kafin wani Lokaci su Ahmad sun saki jiki da shi. Ishaq na gefe kamar mutum mutumi sai dai mirmishi kad'ai yake yi.
Allah kadai yasan Halin da zuciyarsa take ciki alokacin,Wlh tallahi bai taba sanin haka yake tsananin son Fa'iza ba sai da ta auri waninsa. A yadda yayi fama da zuciyarsa akan soyayyar Fa'iza ya tabbata ko Zainab da take zabinsa bai sota haka ba.
Ya shiga jarabawar rayuwa da baya Fatan wani ya shiga irinsa Son matar da ba Muharaminsa ba,tunda Zainab ta fad'amasa zuwan Fa'iza da Engr ya rasa natsuwarsa sai yaji abunda ya Binne na soyayyar Fa'iza na neman taso masa, ganinta da yadda ta sauya sai ya kara Saranda ya tabbatar ma kansa Fa'iza ta samu wanda ya fisa komai da komai sannan ganin irin kaunar dake idanuwan Engr ya tabbatar masa da cewa in ba ta Allah ce ta kasance ba Har gaban Abada Fa'iza tayi masa nisa nisan da ko shekara Dari ya yi yana Gudu bazai iya cimmata ba.
Ganin Fa'iza da yayi yau da irin sauyawar da tayi sai Shed'an ke kawata masa ita zaune yake ammh Kamar baya cikin hayyacinsa yak'e kawai yake yi Mama ta fad'a masa ya cigaba kawai da addu'a ammh fa Jarabawa ce da alhakin Fa'iza ke Bibiyansa shi yasa Allah ya Dora masa kaunarta alokacin da ta riga tayi masa Nisa mai tarin yawa.
Yana nuna kamar ba ni yake kallo ba, ammh ni kaina na takura saboda duk sanda na dago ido shi nake ganin idanuwansa a kaina,Na dauka Engr bai gani ba ashe karyan so na ma yake yi. duk motsinsa yana gani sai dai ya barsa kamar bai gani ba.
Anum ce ta dawo kusa dani muna ta Hira kasa kasa Zainab kuma ta shiga Kitchen in ma abinci ne cikin mu ya cika ruwa kadai na sha Engr ne kadai ma yasha maltinan da aka kawo mana Tunda shi daman yana son maltina.
Mama na gefe bata sakamana baki nice ma na sako mata mganar Badariya,yasa ta dan saki jiki muna mgana da ita,har take fadamin kwanaki tazo ma tayi sati,araina nasan wani abu ya faru ammh tunda bata fad'amin ba sai ban nemi na sani ba.sai dai na fadamata zan je in sha Allahu in na koma Abuja.
Muna zaune Zainab ta kawo abinci ina ganin haka nace"Anya abincin nan..?mun koshi gidan Anty Fadila"
Zainab tace"Tab kun ma isa..?
Nan fa kamar Dole ne"
Dariya nayi ban kara mgana ba,Da gaske muke yi mun koshi saboda kada su ji ba dadi sai Engr yace zai ci shi da yaran shi ni kuma sai Mama tace Zainab ta sakamin mu shiga ciki zan fi sakewa.
Haka ko akayi har Dakinta ta kaimin Farar Taliya ce da miya ba wani Taste ma,ba kayan lambu,sai dai naman Rago da akayi miyar da shi,Dagani kila Shema'un ce tayi girkin domin gadai shi nan ne,Tsakura nayi kadan Saboda kada taji ba dadi ban ci ba na sha ruwa saboda bakin lemu ta kawomin ni kuma bai cika damuna ba na fi shan Madaran Hollandian ko Nutri ko Fresshyo.
Nan da nan Hira ta Bude a Tsakanina da Zainab tunda yaran Engr ya janje su ban damu sanin da ni da shi Duk Daya ne,Sai daga baya Anum ta shigo sai Zainab ta fita ta bamu wuri,Amir ma ya biyota sauran yaran ne ke falo wajen su Engr.
Na saki jiki muna Hira da su bansan Lokaci ya tafi ba sai da Zainab ta shigo tana fadin"Maman Amir daman ba nan zaku kwana ba..?
Ina rike baki nace"Kwana kuma..?haba masauki zamu koma"
Zainab tace"Ai yanzu yake fad'a nace sai dai shi ya tafi ya bar mana ke ki kwana zuwa da Safe don Allah"
Kuma yace shikenan in kina so sai ya barki din"
Har ga Allah nima zan so na kwana din tare da ya'yana ammh ban nuna hakan ba sai da na kintsa kaina muka fita falo muka iske har Engr yasa an shigo da Tsaraban yaran sun bude a falon suna ta murna.
Muna fitowa Engr ya mike yana fadin"Dare fa ya yi Faa'izaa.."
Kallonsa nayi kafin ma mayi mgana Zainab ta rigani da cewa"Ba nan zaka bar mana ita ba yallabai..?
Sai Engr ya kalleni cikin yanayin sa kafin yace"In tana so sai na barta.."
Yanayin mganarsa da kallon da ya yi min yasa nasan mganar ba har zuci ba ne duk da ina so ammh bazan yi abunda zai bata ma mijina rai ba.
Da sauri nace"Zainab ki bar mganar kwana gobe fa zamu tafi kano .In sha Allahu in muka dawo zan kara zuwa yara kuma in sun samu Hutu ina Biko su zo min Hutu don Allah"
Zainab ta marairaice kafin tace"Kai mamam Amir naga megidan ya bari"
Sai kawai nayi mata yake,Engr dai bai yi shuru ba yace ma Ishaq yana neman alfarman su Amir suzo mana Hutu murya ba karkashi yace"In sha Allahu"
Har dakin Mama muka shiga yi mata sallama Engr ya bata kudi ban san ko mawa ba ne tana ta godiya,mun fito duka har yaran suka rakomu suna na ne dani suna rigiman sai sun bini Ahmad da su Farhan kenan ni kuma ina Lallashin su da cewa in suka yi Hutu za'a kawo su gidana su yi kwanakin Hutun su.
Alokacin ne Ishaq ya nemi gafaran Engr shi kuma yace bakomai Bai taba rikesa aransa ba.
Har Mama sai da ta rakomu wajen mota sai da na fara shiga sannan Engr. Zainab na d'agamin hannu ita da yaran Ishaq ya leko ta barayina yana Fadin"Ki yi hakuri Faa'iza da abunda ya faru a baya"
Ina mirmishi nace"Bakomai.."
Yayi min mirmishi na maida masa nima,suna d'agamana hannu har Motarmu ta tashi,sai da na share hawaye Engr ya jani jikinsa yana Fadin"Kiyi hakuri kin yi kukan nan fa har kin gaji.."
Sai na kasa tsaida kukana jina acikin jikinsa shi kuma bai gaji ba yana aikin Lallashina yana fadin"Naga kin so ki kwana ki yi hakuri zuciyata bata iya barin ki,ki kwana gida daya da Ishaq ba. Bazan iya ba Faa'izaa ki yi hakuri.."
Ban ji Haushinsa ba na dago kaina ina Fadin"Nima kayi hakuri"
Mirmishin ya yi min kafin yace"Nayi miki afuwa tun kafin ki rokeni"
Ki yi hakuri na roki Ishaq d'in in sun samu Hutu lokacin mun zo Abuja zasu zo mana in sha Allahu"
Da irin kalamansa ya gama lallashina har muka isa masauki ya bama mai Taxi Atm ya cire kudadensa masu yawa.
Ranar min jima bamu barci ba,muna Hiran yaran Engr na yaba ma Zainab da Ishaaq tunda yaran mun gansu Tsab ba cikin wahala ba ni kuma na fad'a masa zainab ko a baya batayi zaman kishi dani ba.
Ta so ni ta kuma kaunace ni nima shiyasa nake kaunarta.
Shima kai tsaye yace tunda tana so na shima yaji yana kaunarta, domin shi duk wani mai sona to yana son shi shima.
Washegari karfe 12biyun rana jirgin mu ya tashi zuwa kano,Da muka sauka Direban gidan Hajiya Tafeesu yazo ya Daukemu chan muka fara sauka yar Tsohuwa mai kirki da karamci gida cike ko da Dangin Maa,da ya'yan yan'uwa su karbeni cikin karramawa da Soyayya kamar su lasheni,nan muka kwana.
A shashe na musamman ni da Engr,Hajiya Tafeesu ta sakamana albarka da Fatan zuru'a Dayyiba kamar bakinta zai cire. sai da Safe bayan mun yi wanka muka shiga gidan su Ammi na gaishesu ,bamu jima ba Daganan muka je gidan Yaya Asiya Engr ya kaini da kansa cikin Daya daga cikin motocin gidan ya kuma barni chan na kwana wajenta itama tana ta zuzuta kyan da nayi.
Mun kwana muna Hirar rayuwa ashe Zuwan da Mama tace Badariya tayi gajiya tayi da wahalan uwar Yusuf da matansa har takai basa bata abinci maman na kulle Store shine tayi yaji taje Lagos sai da Yusuf yaje ya Daukota da kansa,to gwara ma Badariya Labarin Halisa ba Dad'in ji Yaya Asiya ta fad'amin miji duk ya saida kayan dakin Halisa tunda Dila me na yan kwaya yana sha kuma yana Saida ita.
An taba ma kamasa dakyar aka sake shi Fad'a kuma ya kacame tsakanin Anty Binta da ya'yan Hajiyan Dala akan tace ai susan halinsa suka yi shuru ya auri yarta,Fada har da Gore gore,A raina nace Dara taci gida.
Kafin Engr yazo ya Daukeni sai da Yaya Asiya ta rakani gidan Halisa ya ma saida wannan gidan sun koma gidan Haya,wajen su goma agidan daki Ciki daya Halisa har sai nayi mata kwallah Rayuwa kenan,da zamu tafi Dubu biyar na bata ta amsa tana ta min godiya muka fita muna Tausayamata.
Ranar yawo muka sha agari mune har Shoprite ba inda bai kaini ba sai Dare muka dawo,washegari muka tafi Dutse gidan Nana Fatima,mun ko ga Tarba Nana Fatima tayi zencen sauyawata har sai da nagaji har addu'a ta rika yi Allah yasa ciki gareni. ni kuma in mata Dariya Engr ma ya hade da mijinta suna ta shan Hira abun su agidan muka kwana Barayin megidan suka barmana mu da zamu yi kwana daya sai gamu mun yi biyu. Ranar yawo muka fita cin abinci mu da su da yaran sai dare muka Dawo sai washegari muka koma kano a ranar muka bi Jirgin Dare zuwa kaduna.
Gidammu muka sauka bamu kira kowa ba,Saboda muna cikin gajiya sai da muka yini muka kwana sannan mukaje gida.
Sai dai su Abba suka ganmu kamar Daga sama,Ammi sai da ta Rumgumeni ita da su Hafsatu suna ta min Ihun wai na zama kamar black american.
Nan Engr ya barni sai Dare yazo ya Daukeni tunda sun ma fita tare da Abba ne,da zamu tafi Abba nata sakamin albarka ko bai Fada ba nasan yaji Dadin ganina ahaka.
Engr hutunsa ya kare zai koma bakin aikinsa sai yace zamu je Karofi mu gaida su Goggo,daganan Abuja zamu tafi chan zai barni ya koma Edo in ya Sake dawowa sai mu koma tare.
Haka ko akayi sati daya muka yi muna Hutawa a kaduna na sake Dibar wasu kaya tare da Hafsatu da Nana Khadija muka tafi sun gama jarabawa har sun samu hutu.
Arana daya mukaje karofi muka Dawo,Inno daman tana Karofi cham muka sameta,mun je har gidan Yaya Mariya sannan mun shiga Dutsemah gidan da Tamadina tayi aure Engr ya yi musu Kyauta,daganan mun shiga katsina har gidan Hajiya na kai mata Engr ta gansa tana ta Saka albarka,ban manta da makotana ba Sa'adatu da Habiba na kuma saka Engr yayi musu alheri suma suna ta Mgaanan na sauya na zama kamar bani ba.
A katsinan muka kwana Hotel ya kama mana washegari muka Dauki Hanyar Abuja a mota,daga ma'aikatansu na kaduna aka bamu mota da Direba,gidan su Papa muka Fara sauka sai Dare muka karisa gidanmu su Hafsah ganin su kafaya suka ce nan zasu kwana Maa tace a barsu muka rabu suna ta godiya da Tsaraba.
Engr yaji dadin zaman su gidan su Papa yace gwara su bar shi yayi kara'in bankwana aivko ya yi. kwana Biyun nan mun yi soyayya kamar bazamu kara had'uwa ba.
Ranar lahadi ya Hau jirgi zuwa Benin,ya barni cike da kewarsa ba domin Su Hafsah ba da na sha kewa ko da yake ga su Kafayatu.
Sai da gajiya ta sakeni na samu sararin kiran mutane muna gaisawa.
*Janafty**KNKB3020*
*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*
*09069067488*
*Prologue*
*Ina rubuta muku wannan shafin alhinin kewarku da zan yi*. Na gode wa Allah da ya haska mini wannan labarin*.
*Na kuma gode muku. Dan haka wannan shafin kacokan sadaukar wa me ga duk wacce ta saka ku'dinta ta siya. Na gode, Allah ya saka da alheri*.
*Sai mun sake haduwa a sabuwar tafiya nan ba da jimawa ba*.
*Janafty tana muku albishiri din bayan Faiza ta kau ce, Yabi zata bakunce ku nan ba da jimawa ba, cikin littafin BAK'AR TA'ADAH*.
*Son so fisabidillahi*
Tafiyar Engr Edo ta dauke sa kimanin Sati uku da wasu kwanaki ne sannan ya dawo. lokacin su Hafsatu sun gama min Hutun su.
Sati uku suka yi min sannan suka koma saboda an koma makaranta har ga Allah naji dadin Hutun su a wajena tun ballatana ga su Kafayatu da suka saba da su watarana duk gidana ma suke kwana, A taru ayi ta Hira ana dariya Su hafsa na son koyon yarbanci su kuma suna son iya Hausa sosai Diramansu ma abun dariya ne.
Engr kudi ya turomin masu yawa tun yana chan muka je nayi musu shooping kamar yadda yace haka ma Papa ya bada kudad'e yace aje kasuwa su dauki duk abunda suke so.
Maa ma ba'a barta a baya ba. dukkansu kowacce da akwatinta shake da Sabbin kaya da kayan amfani sai wanda ya gani.
Sannan Direba ya kai su har gida sannan ya juyo Abba da Ammi sun kira suna ta fad'an Hidima tayi yawa nace ba ruwana Aikin Engr ne tunda nace haka sai na kashe bakin su.
Sanda ya dawo na fad'amai abunda su Abba suka ce dariya kawai ya yi kafin yace"kyaleni da Rigimammen baban nan naki. ya kirani zai fara mganarsa nace ni sisters d'ina nayi ma alheri ko Haramin ne..?
Ai daganan bai kara mgana ba nasan mganinsa"
Tsungulinsa nayi ina fadin"Uban nawa..?sai da ya yi wata dariya kafin yace"Nima ai Ubana ne. Tunda ya bani ke ammh wani lokacin ki kauda idanuwan ki bayan Uba shi abokin aikina ne"
Dariya kawai nayi ban ce masa komai ba tunda nasan gaskiya ya fada tare na gansu kuma ban isa nasan Tsakanin su ba.
Sati Daya ya yi min ya koma,yaso ma mu koma tare zuwan Hajiya Kudirat Abuja yasa ya barni. bamu tafi tare ba yace sai in dan ya dawo.
Shiyasa gudun zaman shuru na kan je gidan su Papa na yini watarana har kwana ma ina yi Hajiya Kudirat ne ta tsawatarmin akan na rika zama agidan mijina yau da gobe sai naga na Saba,jin haka yasa sai Papa yace su Kafayatu su bini in Oluwatosin ya dawo sai su dawo gida hakan sai ya ragemin zaman kadaici tunda muna tare da su basa dai yini a gida ne suna makaranta sai weekend wani Lokacin ma Ranar Lahadi ne kadai suke gida. ammh tunda muna kwana tare a kallah dai nasan akwai mutane a kusa dani,kuma a baya nasan na yi zaman kadaici ammh lokacin akwai yara suna Debemin kewa yanzu ko bayan kewar mijina har da ta yara ina yi kuma ko da yaushe cikin Tambayar Zainab nake yi yaushe zasu samu hutu Saboda ina so suzo su yi min Hutun su awajena.
A na cikin haka sai ga wayar Badariya daman na jima bana samunta a waya tun sanda muka dawo in na kirata wayarta a kashe nayi ta Damuwa har sai da na fad'ama Engr sai yace mu mata mun cika raggon azanci meyasan bantaba karban lambar mijinta ba..?Da sai na kirasa naji ko lafiya sai da ya fad'a naga gaskiyansa kuma ban taba wannan tunanin ba shiyasa akace mu mata karkatattu ne duk ta inda aka gyaro mu sai mun sake karkacewa.
Lokacin da naga kiranta da Zumudi'na na amsa kiran sai dai yanayin da na jita ya fad'armin da gaba cikin damuwa bata budemin komai ba kawai tambayata tayi ina ina..?Nace mata ina Abuja sai ta nemi da in turo mata address din ta manta Dakyar ta iya kawo kanta.
Ban rike anguwan da kwatancen ba Sharifatu na bama ta rubuta mata duk sai jikina ya yi sanyi da na kara tambayan ta meke faruwa muryanta a matukar Shake tace min"Zamu yi mgana Anty Fa'iza in da na zo"
Sai na kyaleta har tazo din,har ga Allah na zata ba ta saka ranar Tafiyar ba,ban dauka da wuri haka ba sai dai a daran da misalin Tara na Dare sai ga Badariya cikin wani yanayi mara Dadin ji da gani tazo a galabaice saboda Tafiyar mota tana ta faman amai ga jikinta da zazzabi.
Na rude sosai da ganin yanayinta Fadi nake yi"Badariya lafiya..?
Ko wani abu ne ya samu Yusuf din..?
Duk bata bani amsa ba tana cikin wani yanayi,tsabar na rude ma na rasa taimakon da zan bata sai su kafaya ne sukace bari su kira Family Doctor din su yazo ya dubata jin haka yasa na samu Tunanin kaita Dakina na taimaka mata tayi wanka,sai rawan Sanyi take yi hakoranta na Haduwa waje daya ga shi ta rame ammh naga ta kara fari kumatunta sun cika sosai.
Suna ko kiransa ba jimawa sai ga shi yazo ya dubata sai ya Dibi jininta yace da safe zai kawo Result bai bata mgani ba allura kadai ya yi mata Sai Drip da ya saka mata ta samu barci,haka na ta sata ina kallonta Lokaci daya na zabga tagumi.
Engr ranar yasan ba na cikin sukuni Tunda ka'idan kafin na kwanta nakan kirasa,mu yi bamkwana yaga ban kirasa ba kuma ya kirani ban dauka ba Allah nagani ban ma ji kiran ba wayar na inda na idar da sallar Isha'i.
Sai ya kira Sharifa itace ta fad'amai nayi bakuwa tazo ba lafiya.
Sai yace ta kawomin wayar ta wayarta ne muka yi mgana na fadamasa Badariya ce ga kuma Halin da tazomin cikin damuwa.
Sai ya shiga lallashina da irin tausasan kalamansa.
Hankalina tashe nace"Abunda ke damuna ina mijinta yake da ya barta ta yi doguwar tafiya ita Kad'ai?
Engr yace"Allah masani kuma ga shi ba lambar shi mijin ballatana akira aji ko lafiya"
Kai tsaye nace"Sai dai in wayarta.Gata nan a hannuna"
Engr ya yi shuru kafin yace"ko kuma ki bari ta farka sai ki fara jin ta bakinta kada mu yi gaggawa"
Da haka ya samu ya lallasheni da zamu yi sallama yace"Kada ki damu zata farka cikin lafiya. In kika saka damuwa ina kike so ni kuma na saka kaina Babyna..?
Sai ya bani dariya daman Burinsa kenan yaga Dariyata,Kuma daman yasan in yace Bby sai nayi dariya don in yace min haka sai nace"Wata Bby da ya'ya zarata har hudu..?
Bby kamar wata Anum.?
Shiyasa in ya tashi zolayansa haka yake kirana tun ina jin wani iri har nazo na saba.
Shawaransa na bi ban kira kowa ba,To in ma zan kira bani da zabi Tunda wayar tana cikin Password ne Dole sai in ta farka tukunnah.
Ba ta kuma tashi ba sai da asuba,Cikin ikon Allah ta tashi da kwarin jiki Daki daya muka kwana na bar mata Kan gado ni na kwana saman Cafet.
Ba tare da taimakona ba tayi wanka ta Dauro alwala ta fara rama salolinta ni kuma na fita zuwa kitchen tunda na saba bana barcin Safe,Wani lokacin tare da su kafaya muke abun kari wani Lokacin sai dai su fito su ga nayi musu komai.
Yau ma hakan ce ta kasance,Indomie na Dafa sai na dafa musu kwai ni kuma daman na fi son sayayye sai na soya na Dafa Ruwan tea mai kayan kamshi,Na kuma soya Buredi,ina da Sauran Soyayyan Nama sai nayi musu pepe. Ko kafin takwas na safe na gama komai na goge kitchen din daman na fi yin abincin rana da yawa tunda ina aika ma su Maa da shi su yi ta saka albarka shi kan shi Engr bai sani ba sai dai in su Maa din suka fad'amasa domin ya yi min mgana ba Dawaniya ba ce..?
Nace masa ba Dawainiya bace,daga karshe sai yace Allah ya ba da Lada.
Koda na koma Daki Badariya na kwance ammh ba barci take yi ba,gaisawa muka yi na tambayeta jiki cikin sakewar murya tace min taji sauki..
Gefen gadon na zauna ina fadin"Kin kira yusuf kin fadamai halin da kike ciki..?wai ma tsaya da sanin sa kika yo wannan Doguwar tafiyar..?kuma baki fad'amin jiya zaki kamo hanya ba"
Shuru tayi kafin ta yamutsa fuska tace"Bai sani ba"
Kai tsaye na kalleta da tambayan"Bai sani ba..?
Bangane ba..?
Sai ta koma ta lumshe ido kafin tace"Miye baki gane ba..?
Nace miki bai san na taho ba,bama shi ba ba wanda ya sani"
Ban yi mamaki ba ganin yanayin yadda ta zo sai na muskuta kafin nace"To sai ki kira yanzu ki fad'a masa"
Kai tsaye tace"A"a.."
Mamaki ya isheni na mike ina fadin"To ni bani lambarsa na kirasa na fad'amasa kina wajena kada hankalinsa ya tashi in yaji bakya gida"
Da sauri tace"Bazan baki ba Anty Fa'iza"
Ina kallonta nace"Saboda menene..?
Sai ta muskuta ta mike ta gyara zama kafin tace"Saboda bana so yasan inda nake. Na gaji Anty Fa'iza Ina so na rabu da auran Yusuf ko na huta da wannan bala'in da nike ciki"
Ta karishe fada cikin gunjin kuka sai naji Tausayinta ya fad'amin.
Na karisa gareta na zauna gefenta na rumgumota jikina ina Lallashinta Fadi take yi"Nagaji nagaji. Bala'in yau daban na gobe Dabam,ga na Matarsa ga na mahaifiyarsa ta tsaneni bata son ganina bata barina nayi girki ta karbe makullin Store sai taga dama zan ci abinci,matarsa kuma har gidan take zuwa tamin Tijara,ban ce komai ba shi ma kamar ta shanyesa baya iya Daukan mataki in nayi mgana sai yace nayi hakuri yana raga mata ne Saboda Hajiyar su, Wlh nagaji ne Anty Fa'iza gwara ya sakeni na koma gida yafiye min zaman auransa na rashin kwanciyar Hankali"
Tana gama fad'amin haka ta fashe da kuka ma ban tausayi ga wanda ya Saurara ni kaina ta rauna na min zuciya ina tuna a baya nima fa na Fuskanci iri wannan rayuwar da Badariya take fuskata.
Cikin Bubbuga bayanta nace"Subhanallah har yanzu matsalolin nan basu gyaru ba..?
Shi Yusuf din bai dauki wani mataki ba..?
Sannan yanzu me ya faru kika taho.?
Badariya na gunjin kuka tace"Yaushe zai iya daukan wani mataki yana taorin matarsa yana tsoron uwarsa,Kwanaki fa har yaji nayi na tafi lagos na kafe bazan koma ba sai ya sauyamin gida da Hajiyarsa saboda bala'in ya yi yawa da yunwa nake kwana da nayi mgana sai tace Danta ya gaji da ci da juya nazo ba na Haihuwa sai ci nayi kashi abinci fa sai dai na siya,shi bazai iya mgana ba sai dai ya bani kudi a hannuna na rika cin abinci gajiya nayi sai nayi tafiyata Tunda bata amince ya sauyamin gida ba,Dakyar ya lallasheni na dawo da alkwarin zai sauyamin gida na ni kadai ammh kuma mgana ta shiriran ce,Shekaran jiya matarsa tazo gidan tana ta zagina tana ce min Juya in sha Allahu dukiyar da na shigo ci bazan sameta ba har tana zagin Ubana dake Kabari ni kuma raina ya baci na Rama shine ta jani da Dambe har mukayi fad'a,Du keni in Daketa muka yi Lokacin Hajiyar bata nan daganan sai akace taje gidana gaishe da Hajiya bata nan najata da fad'a har nayi Sanadiyar barar mata da ciki daman ina bakin ciki. Yusuf baya nan ammh Hajiya ta kirasa a waya tace ko ya sakeni ko yaga bacin ranta.
Shi ya kirani yana kuka yake fad'amin ni kuma da naji haka nace gwara a rabun kowa ya huta tunda yaki saki na sai na zabi na tafi inda bazai ma sani ba ballatana ya nemi shiyasa na yanke shawaran zuwa wajen ki Anty Fa'iza na tabbata ko kowa bai Fahimceni ba ke zaki Fahinceni"
Kafin ta gama bani labari naji raina yayi wani duhu jikina duk ya yi sanyi Badariya mai kaunata ce ban so kaddaranta tazo a haka ba, ammh kuma bawa bai isa ya tsara ma kansa Rayuwa ba,muna namu ne Allah kuma na nashi nashin ne kuma na gaskiya.
Kuka take yi kamar ranta zai fita ina Lallashinta da ban hakuri kfin nace"To yanzu shi Yusuf din yana ina..?
Badariya tace"baya nan,Rabo na da shi tun jiya a fligth mode na saka wayata,mun rabu dai yace yayansu yace ya dawo sai a zauna kada ya sakeni sai indan ya dawo ni kuma daman na shirya tafiyata Shiyasa ban Tsaya ba"
Tun daga yanayin mganarta nasan da gaske ta gajin,sai ban matsa mata ba na kyaleta sai dai nayi ta bata baki da ban hakuri kafin na barta naje nayi wanka na shirya ko da na fita falo su kafaya sun tashi suka gaisheni na amsa sun shirya zasu shiga makaranta sai nace su dibi abun karyawa su karya kafin su fita ni kuma na Dibar mana ni da Badariya na kaima har Daki.
Abincin ma dakyar ta sauko taci,Tasha dai tea,sai Soyayyan Buredi shi kuma kadan taci sai amai haka ta shiga Tiolet tana kwarara shi ni dai ban ce mata komai ba ne ammh naga Ciki Sabo a tare da Badariya.
Su kafaya kafin su fita har Daki suka shigo suka Duba Badariya sannan suka min sallama suka tafi makaranta Dukkansu sun iya mota,suna da kuma Motocin su yau wannan ta tuka gobe wanchan ta tuka.
Suka barmu da Badariya tana bani labarin zaman hakurin datake yi a gidan Yusuf ba kwanciyar Hankali,ni kuma ina kara Tausanta da kalmar nan ta Hakuri ita na rike kuma naci Riban Hakurina.
Sai yammah Dr din yazo ya kawo sakamakon bayan ya yi mata bayanin tana da shigar ciki na wata Biyu da wasu kwanaki ta kiyaye aikin wahala sannan ta rika cin abinci ta samu Hutu Badariya ta kasa mganar har bayan Tafiyanta ni ce nace mata"To ina zaki kai wannan rabon Badariya..?
Baki san abunda Allah ya kaddara Tsakanin ku ba tace ke da Haihuwa sai dai kiga anayi tun ba'aje ko'ina ba sai Allah ya nuna mata bata isa ba. Kinga sunan juya da suke kiran ki sai ya kare daga yau"
Bata ce min komai ba sai dai tana ta sharan kwallah Saboda matsalan Badariya yasa sai dare muka yi waya da Engr da ya tambayeni ya ake ciki na Fad'amasa yadda ta fadamin da kuma cikin da aka gano a jikinta.
Engr ya fara fad'a yana fadin"Shima dai kamar wani sakarai haba .Ba'a haka sai ya sulhunta lamarin ita matarsa ai karkashinsa take in bata son a zauna lafiya ya yi mganinta mana ita kuma mahaifiyarsa matsayinta Dabam ya kamata in dai yana son matarsa ya san yadda zai iya gyara kowani bangare ammh a bar yarinya na Fuskantar wannan matsalan bai Taso ba Faa'izaa ki riketa a wajen ki Sati mai zuwa zan dawo da kaina zan kira mijinta mu yi mgana, in yana sonta ya gyara gidansa in kuma bazai iya ba to kowa ya kama hanyarsa"
Har mamakin Engr na rika yi haka yake da fad'a sai dai nasan shi baya Daukan re ni jarumi ne kuma jajirtattace ne,Da na fad'ama Badariya abunda yace sai taji dadi jin yace zai Shiga mganar zuwan Badariyq yasa su kafaya suka koma gida nima da Badariya ta kara jin sauki munje da ita ta gaida su Maa muka yini achan sai Dare Direba ya maidamu gida.
Badariya sai fadi take yi"Gaakiyan dangin mijin ki masu karamci ne Anty Faa'iza"
Sai dai nayi mirmishi Saboda abunda na sani ne aka sake fad'amin.
Kafin satin da Engr zai dawo Badariya ta murmure tunda ina takura mata taci abinci duk da tana amai ga laulayi da Zazzabi take kwana,wayarta tana Kashe shiyasa bamu ji labarin irin neman da Yusuf ya yi mata har Lagos ba,Da kuma irin yadda Hankula suka tashi tunda duk an nemi kowa bata wajen su ni kuma kila ana tunanin ina amarci kila Badariya baza ta zo wajena ba.
Sai ana gobe Engr zai dawo zainab ta kirani a bakinta nake jin hankulansu duk a tashe suke Badariya ta bar gidan mijinta ba'a san inda take ba.
Tana bani Labarin yadda Hankalin Mama da su Yaya ishaq ya tashi da shi kan shi Yusuf din sai naji kamar na gayamata gaskiya sai kuma na fasa akallah dai na jira dawowan Engr sai na tada Hankalina na nuna Damuwata da Alhini na.
Bayan mun gama wayar na fad'ama Badariya sai ta tabe baki tace"Mama da yan'uwana kawai na damu ammh ba domin Yusuf ba"
Ban biye mata ba,ganin yadda tayi fushi illah na rika ce mata"Ke dai fad'i gaskiya kin yi kewarsa sosai ma ko baki yi don komai ba kya yi saboda abunda ke cikin ki"
Gajiya tayi ta kyaleni tunda taga na Rike mganar na ki saki,Washegari da Shirye Shiryen Dawowar Engr muka tashi,Badariya ta kama mun muka yi masa abincin kala kala na saukansa jirgin yammah ya biyo sai bayan mangariba ya iso gidan.
Lokacin n cakare cikin Riga da sikat na Atamfa mai ruwan ganye cikin kayan akwatin daya dinkamin ne Tunda anan Abujan Maa ta bada aka dimkamin bayan na fad'a mata Measurement dina.
Kayan sun karbeni Saboda Daidai jikina ne Badariya tamin Saukakkiyar kwalliya hade da Daurin maryam babbangida sai nayi kyau dani kamar a Sureni a gudu..
Ai ko Engr cak ya sureni haka ya Dagani Sama bai ji nauyi na ba,ya rika zagayen falo dani ni kunya duk kunya ya kamani ganin Badariya na wajen ashe tun Rumgumar Farko ta komaa ciki ta bamu waje.
Dakyar na iya lallabasa ya yi wanka ammh sai da ya yi kara'in nasa dai ta bakinsa dai ba yayan ya yi ba kanin ne duk ya batamin kwalliya yasa sai da na gyara Daurin d'ankwalin Tunda har kan sai da ya sha Jagwagwala.
Sai bayan ya yi wanka ya yi sallar mangariba da aka kira Isha'i sai ya jamu jam'i ni da shi bayan mun Idar ne muka fita falo na gabatar mai da abinci sai yace na kira Badariya su gaisa na leka na sameta itama ta Idar da sallar Dariya naga tana yi min sanin Dariyan da ma'ananta yasa ban tanka mata ba ammh ina ce mata Engr na mgana afalo ta mike tana Fadin"An gama yar shillan dake..?
Sai na juya baya ban kara yarda mun hada ido ba na fice ina mirmishi.
In na zauna ina kod'a Engr sai aka ga kamar ina zugasa ne ammh mganar gaskiya Engr shi ya kaini duniyar ma'auratan da bansan ma akwaita ba.
Shi ya jiyar dani irin Dadin da mata suke ji a tare da mazajen su.
Shi ya kara fahimtar dani aure da zamantakewa ashe ni a baya wahala kawai nayi,ban taba Dauka haka Aure ke cike da Ni'ima ba sai da na Samu Engr.
Duk da kowani aure yana da nashi kalubalen,zo mu zauna a kace zo mu sab'a,ammh ni ta bangare na cika da Hamdala na kuma kara da Alhamdulillah.
Tunanin da ya cika raina kenan ina zaune gefensa yana cin abinci sama sama yake mgana saboda bai cika son mgana in yana cin abinci ba.
sallamar Badariya da shigowarta falon yasa ya Dakata ya dago yana amsawa
Nesa dani ta zauna tana gaisheshi ya amsa cikin fara'a kafin yace"Matata zubo muku abincin mana tunda na lura yau wareni akayi tunda naga an zubamin nawa ni kad'ai"
Mirmushi nayi kafin nace"Ni bana jin yunwa ne shiyasa sai dai in Badariya"
Da sauri tace"Anty Fa'iza ki gayamasa mun ci da muka gama girkawa tun a bakin Tukunya"
Hararanta nayi shi kuma sai ya kada kai yana fadin"Fa'izaa na yafe miki ba ma sai kin nemi gafarata ba"
Dagani har Badariya muka yi Dariya matsamim ya yi sai da muka saka abincin muka ci kad'an tunda gaskiyanta ne tun a kitchen muka koshi sai dai an dauki Lokaci cikin ya Zazzage.
Saboda gajiyan dake jikinsa yasa yace sai da safe zasu tattauna da Badariya da wuri muka shige ciki,saboda yana ta fad'amin ya yi kewata in zai koma kafata kafarsa bazai iya ba.
Ai ko naga kewa haka ya rika min rawan jiki da Sambatu ni kaina na karbesa dakyau tunda nima nayi kewarsa sosai Rayuwa juyi juyi sai ga shi ni Fa'iza ke son al'amarin a baya Wlh tallahi al'amarin bai taba dad'ani da kasa ba.
Da Asubaa yana kwance ni na tsokane sa muka buga kafi siga dad'i,Da safe ma kafin mu tashi yace zai kara na bata fuska ina Fadin"Baka gajiya ne..?
Duk sai ka tsotseni ko..?
Yana dariya ya kamoni yana Fadin"Bamu gajiya zaki ce. kema ai ba gajiyan kike yi ba in fa kika ji ni nayi kamar zan sauka sai ki yi saurin rikeni kina Uhm uhm"
Ya karishe fad'a yana kwaikwayon yadda nake yi ga kunya ga Dariya Engr halinsa sai shi bakina ya Mutu murus na kasa mgana ya sumbaceni kafin ya Dagoni yana Fadin"Bafa tsotseki zan yi ba. Yarinya ina da Fertilerzer mai kyau kinga yadda kika koma..?Tife din gaske kenan ke da zaki bani dama nayi ta damawa ina cigaba da kara'i na"
Ai ko na basa dama kamar yadda ya bukata.
sai ya koma bayan mun natsa fad'i yake yi"Kamar ma ban yi ba. Wlh komai ya sauya ya kara sugar"
Kansa na dungure ina Fadin"Kuma sai akace komai kaji sai ka fad'a..?
Bakinsa ya kama yana fadin"To in kama bakina kenan..?
Harda wani ladabin Dole Mirmishi nayi kawai ban yi mgana shi kuma sai ya kamani ya Rumgumeni yana Fadin"Allah ya yi miki albarka. Allah yasa ki haifo kannen su Ahmad dozin Biyu haka"
Mukamikinsa na Tokare ya yi gefe yana wash,Sosa wajen ya fara yana Fadin"Yaushe kika zama Muguwa Faa'izaa..?
Ya ja sunan kamar wani abu,Hararansa nayi sai ya gane laifinsa da Sauri yace"To na rage Dozin Daya"
Tiolet na shige na barsa ina ji yana Fadin"To naji rabin Dozin ga su Amir goma kenan ina laifi Father of 10"
Sai dai na bige da mirmishi ina wanka Soyayya da kaunar Engr sun taru sun cikamin kirji sun hanani sukuni yadda yake kaunar ya'yana wlh ko Ishaq albarka shiyasa nake yi masa kara in muna mganar su sai dai nace ya'yan ka.
Yaran nan suna da lambarsa barin ma Anum uwar karambani sai dai yace min sun kira shi da wayar Mama Amir ma suna mgana da shi,Zumunci dai ne kila bazai Dore ba tsakanin Engr Da Ishaq kowa na ganin zumunci da wani matsala ne shi Engr haka nan baya so ya shigo masa shima Ishaq din har gobe yana kaunar Fa'iza shiyasa baya son Doguwar mu'alama da wanda ya hanasa mallakar Fa'iza a karo na biyu. sai dai yaran bai isa ya raba su da mahaifiyasu ba yasan Fa'iza ta shanye abubuwa dadama Saboda yaran nan suna mata kauna ta sosai kuma shima Engr yasan yana kaunar su Darajan yana Son Fa'iza yana jin kishin yadda yaran ke kiran Engr Baba sai dai ba shi da yadda zai yi yasan ni ko ya fad'a ko kada ya fada Engr mutum ne nagartattacen kuma Kishinsa duk akan Fa'iza ta auri wanda ya fisa ne yana ganin ta cigaba fiye da in da ta dawo ma auransa.
Da safe bayan mun gama karyawa Engr ya zauna da Badariya suka Tattauna ta fad'amai komai kuma ya gamsu a wajenta ya karbi lambar Yusuf ya kirasa suka gaisa ya fad'amasa sunansa Engr Abdulbasit Mijin Fa'iza yar'uwan Matarsa Badariya daman don ya shaida masa ne matarsa na wajen su da sauran bayanai yusuf ya rude Engr yace zai bashi address yazo nan Abuja yana son ganinsa.
Abun mamaki da Sassafe sai ga shi jiyan ma bai samu jirgi ba ne da Shigar dare zai yi irin yadda Hankalinsa ya tashi yana son Badariya kuma bazai iya Rabuwa da ita ba.
Engr bai bari yaga Badariya ba sai da suka tattauna na tsawon awa Biyu sannan ya kira wayata yace na Turo Badariya,mu dai tare muka bar su biyu su fahimci juna bayan Engr yace mata ta saki ranta in sha Allahu wannan matsalan angama da ita.
Bai yi wani bayani ba sai chan ba jimawa Badariya tazo tace min yusuf yace tare zasu koma naji Dadi na yi ta mata Fatan alheri ina kara jadaddamata ta yi hakuri ta kuma kara Hakuri.
Badariya tayi mirmishi kafin tace"Nagode Anty Fa'iza ke da Mijin ki kin yi min dukkan gatan da Dangina zasu yi min Allah ya saka da alheri. Yusuf yace an daidaita bayan tafiyata Yayansu ya shiga mganar Hajiyarsu ta amince ya sauyamin gida sannan an yi min iyaka da matarsa kuma ya fadamin megidan ki ya yi masa Fad'a sosai ya kara nuna masa tunda yana sona to yasan Darajata"
Nasan halin Engr daman bazai yi wasa ba muka rumgume juna,muka fita tare har Falo Yusuf nata godiyan Hidima itama Badariya nayi Direban gidan su Papa ya kira shi yazo ya kaisu Filin jirgi Yusuf bakin nan kamar Gonar auduga tsakanin miji da mata sai Allah har ta fad'a masa tana da ciki.
Nima ranar tukwaici na musamman na bama Engr saboda jin dadin yadda ya maida matsalan Badariya kamar tawa muna kwance kaina na saman kirjinsa bayan ya gama shagalinsa yace"Ki daina min godiya duk mai kaunarki nima ina kaunarsa kin fad'amin yadda Badariya ta kaunace ki saboda Allah nima sai naji ina Kaunarta Saboda wanda ta kaunace ki domin sa"
Kuma fa ba wani labari na bashi ba nadai fad'amasa Badariya mai kaunatace shima yace tunda tana kaunarki nima ina kaunarta,Washegari gidan su Papa muka yini ni da shi muna ta Hidimanta ma Hajiya Kudurta da Burinta ya gama cika Tunda Oluwatosin ya yi aure kuma daga gani yana cikin kwanciyar Hankali ita da Maa suna ta godiyar Abinci har Papa sai da ya yi min mganar ina ta Dawaniya da su bana gajiya..?
Kaina na kasa ina mirmishi nace ba wani Dawaniya aciki suna ta min godiya da zamu tafi Maa ta bani Mayafai da Turarukan wuta sai ban ce mata ina hadawa ba na bari sai naje kaduna na hado mai kyau da kanshi na kawo mata.
Da muka dawo gida nayi ma Engr mganar turaruka sai yace na bari akwai tsarin da yake so ya yi min yadda Sana'ata zata tafi tare da zamani daman na fad'amasa ina so maje kaduna ko nayi sako,asiyo min kayan hadin na hada a gida saboda Maa,kuma tunda naji yace haka sai ban kara mgana ba, nasan tunda yace yana da Tsari to ina tabbatar ma kaina Tsarinsa a kaina mai kyau ne.
Ban sani ba ko Badariya ta kira chan Lagos ta fad'ama su Mama komai,?ni dai sai kiranta nagani tana ta min godiya har Anty Binta ma ta Kirani sai gashi da bakinta take fad'amin Halin da Halisa ke ciki da mashayin mijinta kuma an yi an yi yaki sakinta.
Tana kuka tana fad'amin ko zan fad'ama Engr in zai iya wani abu nace mata zan fada masa in sha Allahu.
Ni kuma ganin taimako ne sai nake gayamasa,nima sai alokacin yake fadamin Yaya Ishaq ya kirasa yana ta Godiyan abunda muka yi ma Badariya kamar mun yi mata wani Hidima,mganar Halisa kuma yace sai ya shiga kano zai ga mijin Halisan da kansa ko jari ne bai da shi a bashi ammh sai in har zai daina shan kwaya da saida su.
Nan take ma yace akwai abokinsa dake aiki da Kotun musulunci a kano Lauya ne zai sa ya gayyacesa ya yi masa nasiha da barazana ko za'a dace.
Ta hannun Anty Binta aka samu lambar wayarsa aka turama Lauyan shi kuma yace in sha Allahu zasu zauna da shi.
Kwana Biyu tsakanin Lokacin muna shirin tafiya Edo washegari tunda yace tare zamu koma ya Kira Engr ya fad'amasa ya nemesa sun zauna ya Fahimci rashin sana'a ne da kuma rashin gata yasa ya fad'a wannan harkan sai kuma Tarayya da abokan banza,ammh ya yi masa alkawarin in yau ya samu wanda zai tsaya masa zai bar wannan sana'ar daman sha ba kullim yake afata ba,zai koma makaranta sannan zai zama nagari
Engr na jin haka yace tafiyarmu sai Jibi washegarin jirgi yabi zuwa kano sai Dare ya dawo yace min kamar ya yi ma mijin Halisa kuka ga namiji har namiji ammh zuciya ta mutu,yace ya bashi Miliyan daya zai fara kasuwanci sannan zai koma makaranta Tunda yana da Diploma kuma ya yi masa alkwarin zai zama nagari in dai zai Tsaya masa shi kuma yace zai Tsaya masa har abada, ya bashi lambarsa yace in yana bukatan wani abu,Har kuma gidan yaje yaga Halisa yana Fad'amin ko abinci basu da shi ga gidan Haya an yi yawa. sai ya ce masa ya samu wani gidan da zasu kama su kad'ai zai biya kudin to sun rabu akan sai an samu zai kirasa.
Idanuwana suka ciko da hawaye Allah Sarki rayuwa na rumgumesa ina masa Godiya sai ya rikeni sosai yana Fadin"ko kashi ne indai dan'uwanki ne abun Darajawa na ne Faa'izaa"
Ban ji wani bakinciki domin ya taimaki Halisa ba yar'uwata ce har Abada ban isa in raba wannan jinin ba,ballatana abuda ya faru a baya ya Dade da wucewa ni din ne kuma na rabu da Ishaq na auri wani wanda yasan Darajata da mutumci,ban taba rikonsa araina ba ina yin komai Saboda Zumunci ne.
Sai ga Anty Binta na kuka tana min godiya ita da Mama tsakani na ko da Halisa kamar uwarta haka ta Dauke ni. kira akai akai Anty Fa'iza kaza Anty Fa'iza tun balle da suka samu gida karami Flat,Engr ya biya musu kudin haya na shekara Biyu,sun koma sannan Rayuwa ta fara zama daidai bata iya yin komai sai da shawarana.
Sai da muka koma Edo sannan na Tura mata 50k nace itama ta fara sana'an cikin gida sai ta nuna min tunda ta iya su Cake,donut bari ta gwada sai nace hakan yayi ta kuma tallata cewa tana aikin su Sai a biyata,bansan irin addu'an da muka sha Daga ita har mijin nata ba,
Ni da Engr ne madubin su yanzu a baya Hajiya Dala suke ganin zata iya musu komai sai ga shi yanzu an ce tsakanin su ba Mutumci Hajiyar Dala da kanta ta Kirani Duniya mai ya yi tunda yanzu ina auren mai kudi nima kuma ina da abun hannuna na wuce reni.
Da bakinta take fad'amin fadan su da Anty Binta daga karshe tace"Chan sanda Halisar ta hadu da shi nama sani ya yi musu barin kudi lokacin ana samun dillar kwayoyi na kai masa,kuma koda suke ganin dan'uwan megida na ne. yace fa Zaman makota ne na iyayensa da kakkanin yaro ammh basu hada komai da shi ba. ammh daga karshe Binta da Saudatu na ganin laifina ai ni kiri kiri na fad'a musu cewa hakkin ki ne ke bibiyan su suke ta ganin haka daga Halisan har Badariyan'"
Mamaki bai barni nayi mgana ba ina Tunanin ita duniya daman haka ta gada tunda har yau Hajiyar Dala ke kirana tana sukan Mama da ya'yanta komai daman ka gina shi da amana,ba ma ita ba kaf ya'yanta suna kirana da masu auren da yanmatan alhalin a baya ba wanda ma yasan da zamana ba..
Autan ta ma Futuha,ta kirani tazo Abuja bikin kawarta ko ina nan nace mata ina Edo ammh sai na had'a ta da su Kafaya ta kwana Biyu a gidan su Paapa kuma suka karammata da zata koma Ta jirgi paapa ya siya mata Tiket bayan abun arzikin data koma da shi sai ga shi ta koma tana labarin iyayen mijin Anty fa'iza suna da kirki kadan kadan sai na zama abun so a family kowa yana nema na, har da wanda ban taba zato ba in na zauna ina Tuna matakin Rayuwata tun daga farko har zuwa yanzu hannuwana kadai nake Dagawa sama na godema Allah Tunda Duka Ni'imarsa da ta mamaye rayuwata sanadinsa ne yau ga shi Fa'izar da ake gudunta sai ga shi na zama abun son kowa da kowa Allah kenan.
Muna Edo kafin mu koma Abuja,Zainab ta kirani tace yara sun samu Hutu ammh bata ji Yaya Ishaq na mganar zuwan su wajena ba,ina jin haka sai naji na kosa suzo sai na gayama Engr shi kuma ya Kira Ishaq ya kara rokonsa sai ya cika masa ido yace zasu zo yana jiran jamal ne tunda bazai sako su su kadai ba.
Jin haka yasa Engr ya karbi Lambar Jamal din suka yi mgana shi kuma ya Siyama duka yaran ticket yace su biyo Jirgi in zasu taho mu hadu a Abuja.
Duk yadda naso na boye murnata na kasa sai da na bayyana Engr nata min Tsiyan nace na bar masa ashe zence ne namu na mata kunya naji ganin har Zalamata ta fito Sarari.
In da ta ni za'a bi har Islam azo min da ita Zainab tace bata yayeta ba in bari sai in ta isa yaye zata kawomin na yayeta da kaina,ammh duka yaran su Shidda zasu mana Hutu suma Zainab tace suna ta murna zasu wajen Umma.
A satin muka dawo Abuja mukaje muka yi shooping saboda Engr yace bayaso su nemi wani abu su rasa,kamar Yadda Babansu yace Jamal ya taho da su ni da Engr mukaje Filin jirgi muka Daukosu haka yara nan suka kamkameni suna Ihun kiran sunana Umma Umma har da Anum babban banza Amir dai yana gefe shi Babba bai cika harkan yara ba.
Sai ga Jamal a gidana bai kuma san haka saukin kan Engr yake ba, sai da suka zauna suna ta hira ni kuma ni da yaran muna cikin gida,Amir daki guda na sauke shida Musty ,Dayan dakin kuma su Ahmad,Anum kuma nace ta zauna adakina.
Duk inda na saka kafa nan suke sakawa komai suka gani sai sun yi mgana Labarai ko haka nake shan su gidan sai ya karade da hayaniyar yara daman nayi abinci kafin su iso ai sai kowa yace ga abunda zai ci wannan yace Shayi wannan indomie ammh ban damu ba haka na shiga kitchen ina yi musu ra'ayinsu zuciyata Fes kamar an yi min albishir da gidan Aljannah.
Jamal jirgin yammah ya sake bi zuwa kano,ya yi ta godiya karramansa da Engr ya yi har yace ma ya kawo C.V Dinsa tunda acikin Hiran su ya fadamasa Software Engering ya karanta,Zuwan yaran yasa walwalata ya karu ranar dai tare da su Engr ya barni na kwana Amir ne kadai ya kwana shi kadai da Musty ammh har Ahmad a dakina suka kwana Engr mutum ne mai kawaici da kauda kai ya kyaleni naci Lokacina ni da ya'yana ba Takura ba shiga Hakki.
Ni da kaina da na gano zakewata sai na rage rawan kafa shima cikin su yake shigewa ayi ta wasa har da Chinness yake biyo musu suna yi shi da su Ahmad Amir kuma in kaga suna mgana kace Amir wani babba ne,Ballatana Anum iyayin karanbana fadi kuma ba'a tambayeta.
Yadda muka saba tun a baya zuwan su ma haka muke yi karatu tare da cin abinci tare,Sannan Anum na zage mata da koya mata girke girke zamani Tunda chan bayi suke ba ita kanta Zainab din tana neman mai koyamata.
Mun fiffita yawo da su na kaisu gidan su Papa suka yi musu ma kwana uku,Maa ke son yara kamar kada su dawo,sannan mun je parks da su Engr ya kaimu suka yi wasa suka sha Hotuna,yaso ya koma ammh yace sai ya maida su har Lagos yadda gobe za'a ji dadin barin su Sati uku daman akace su yi saboda makaranta.
Naso su kara Engr yace a'a gwara su koma akan Lokaci,Farhan da Fadil na kai su gidan kakkanin su ni da Engr muka je sai ga Dr.Laawal kamar ya kwantamin Hajiya Halima daman ban taba samun matsala da ita ba. naga kanwar Zainab zuzu ta dawo daga kasar waje ita kanta da ta ganni tayi mamaki sai ga shi itace da sakin jiki muna mgana har tana karban lambar wayata nan na barsu suka kwana Biyu Zuzu ta kirani tace suna ta kiran yan'uwan su, sun ki zama ita ta dawo da su,To ranar ma bana jin dadi kasala ga zazzabi ga dacin abinci ga shi mun Tsara tare zamu maida su lagos.
Ciwo fa rigis ya kwantar dani Tsaraban yaran ma su Kafaya Engr ya bamawa suka je suka yi musu shopping ni kuma ya kwasheni muka je asibiti gwajin Farko aka gani ina da Shigar ciki wata uku,Murna gurin Engr kamar zai shid'e nasha Rumguma tun a gaban likita tun kuma muna asibitin ya labartama su paapa ina da ciki suma kamar shi haka suke ta murnan.
Dole Saboda Laulayi wajen Maa na koma shi kuma yaje ya kai yaran aranar suna da sati uku da kwana Hudu ne,achan ya kwana da Safe ya Biyo Jirgi zuwa Edo suna da Meeting dalilinsa da yasa ma bai dawo Abuja ba sai dai waya fa akai akai muke yi ko su Abba shi ya fasa mganar cikin a wajensu ni kunya ma nake ji in naga yadda ake rawan jiki a kaina Motsi kadan Maa tace menene..!
Motsi kadan granny tace ina lafiya..?
Haka su kafaya ashe haka ake renon ciki ni na saba nawa cikin har nayi sa na haifesa ba wanda yasan zafina sai ga shi na zo inda kamar a lasheni tun kafin abun cikin ya fito duniya.
Bansan ya akayi ba kowa sai da yaji Labarin cikin na ba Dangina ba ga nasa Danginsa ba.
kunya nake ji wlh gani nayi mu ba yara ba miye na yamad'di.
Zainab ma tace Badariya ta fad'amata ta kirani tana min tsiya ina Dariya.
Ranar da Ishaq yaji ina da ciki sannan ga yara sun dawo da labaran mu ni da Engr sai kishinsa ya kasa boyuwa har ya bayyana ma zainab tunda kamar fada ba gaira ba dalili ya rufeta.
Sai da Mama ta shiga mganar tace ya rika addu'a Allah ya yaye masa jarabawa ce da sakamako
Oho ni bansan yana yi ba ina nan cikin jin dadi da kwanciyar Hankali.
Sai da cikina ya yi wata biyar na bi Engr zuwa Edo muka shimfid'a wata Sabuwar rayuwa komai kuma na shirin haihuwa tun muna Edo muka gama shi chan na fara awo na kafin cikina ya kai wata Takwas na koma Abuja yace anan zan haihu kusa da iyayensa.
Na sauka lafiya haihuwar asibiti ce Ammh ban jima ba na haifi ya' mace mai kama da Engr har gashin idon su tun a ranar ya yi mata Huduba da Hafsat zamu rika kiranta Tamadina sunan mahaifiyata nayi kuka nayi Dariya na karan da Engr ya yi min,Abba ma ya taka rawan gani Tunda sunan yar'uwansa ne,an yi suna na gani na fad'a na masu kuma da shi duka Ahalina sun zo har da Zainab da Mama da yara,Anty Binta da Ahalimta tare da Halisa da komai da ya Daidaita,Badariya ma tazo da jegonta tunda itama ta haifi diyarta mace taci sunan Hajiyar Yusuf itama suna zaune lafiya tunda sun daina shiga harkanta.
Hajiyar Dala ma da ya'yanta sun min kara sun zo,na shiga na fita sannan na samu kyattuka Papa mota ya bani Kirar Honda karama mai kyau na mata Maa kuma ta siyamin Zinare mai Tsada Dangin su ma na Benue kuwa naga karan yarbawa zannuwa ashebe babu abunda basu taramin ba,ba ni kadai ba hatta dangina da abun arziki aka salleme su kowacce da Turmi da kudi a hannunta.
Sai bayan suna ne Goggo karofi tazo ta zauma dani har nayi arba'in Allah Sarki goggo na,Ita ce uwa ta tun Tamadina na raye har kuma gobe ita ce. itama haka Direba ya maidata gida da kayan arziki daga gareni da mijina da Danginsa, na zama Topic of Diccussion a family din mu kowa sai dai kaji yana Fadin Faa'iza haka Faa'iza kaza.
Bayan tafiyar Goggo na cigaba da renon Tamadina a gida bayan Engr ya bani Direba ya kaini garuruwan yan'uwana na yi musu barkan arba'in sannan na sauka a kaduna agidan mu nan na kwana Biyu sai da Engr yazo muka koma Edo tare da shi da D'iyarmu.
*BAYAN SHEKARA BIYAR..*
Bayan shekaru Biyar da suka gabata,Duk inda ake neman cigaban Rayuwa ni kam na gama samu ni Fa'iza sidi karofi ashekarun biyar din baya.
Mun rasa Hajiya Kudirat,Shekaru biyu baya,Inno da Baba Ati suna nan a raye cikin koshin lafiya da kwanciyar Hankali.
A bangaran rashi kenan bangaran Karuwa kuma bayan Tamadina na kara haihuwan ya'ya biyu Namiji da mace,mai sunan Papa muna kiransa Paa da mai sunan Maa Shukra muna kiranta Tauhidat,Bangaran ya'yana kuma Amir ya gama secondary school dinsa Da taimakon Engr ya samu gurbin karatu a Universty of Washington yana karantar Medicine,shekara uku da suka gabata,sai Anum dake karatu a Lagos States University lasu,tana karanta harkan mganguna phamacry.
tana shekara ta Biyu sai Mutsy dake University of Lagos yana shekarar farko ya na kuma karanta harkan zane zane,Ahmed sune bana zasu zana jarabawar Fita Su farhan na matakin SS1,Jamal ya yi aure
zuwa Lokacin na riga na zama Babban Mace na taka duka matakin nasara a rayuwata Dalilin Engr yasa na zama wata macen da ban taba mafarki ba,Jamal ya yi aure anan kano kuma Engr ya yi masa hanya ya samu aiki da NITDA information Tecnology Development agency.
Dake reshen jahar kano yana nan zaune a gidan kansa da Matarsa Abida.
Engr kuma ya zama Chairman a ma'aikansu sannan ya zama d'an kwangila Papa ya gama Lokacinsa a EFFCC yanzu haka ya yi Ritaya yana gida yana Hutawa,Su kafaya sun yi aure kuma dukkansu auren gida suka yi ya'yan kannen papa suka aura Kafaya na Abuja Sharifatu na Oyo inda Mijinta ke aiki Hafsatu ma da Khadija sun yi aure rana daya ita Khadija V.c din Kasu take aure ita kuma Hafsah tana aure a zaria tana auren wani likita dake aiki a ABU chika.
Shekara biyu da suka gabata gida ya Rage daga Ammi sai Abba,sai ta Dauko ya'yan kannenta guda biyu tana rike da su saboda zaman kadaici,yanzu zamana ya fi yawa a Abuja tunda ga yara bazamu ta tsallake tsallake ba Sai dai ina bin mijina Edo ina dawowa kaduna kuma muna zuwa sai muke sauka a gidan mu bamu da matsala.
Engr ya yi min Tsari mai kyau game da kasuwancina ya Budemin katon shago mai kama da plaza inda aka sama wajen sunan SAFMA TURAREN WUTA AND KWALLACHA.
ni kuma nake had'a turuka na da kaina sai dai ina da yara masu taimakamin,Turarukan wuta ne masu kamshi da nagarta kaf fadin Nageria ba wanda baisan Safma turaren wuta ba, ko Hajiya Fa'iza mai Turaren wuta da gyaran jiki ba. Tunda Engr yace duka kasuwanci ne na had'a na rika yi daga gari gari ina aika turarena sannan ina hadama amare kuma ina yin gyaran amare,na koyama mata dadama sana'ata a kyauta kuma suma suna chan suna cin gajiyan sa.
Sannan na had'e da kungiyar Women charity Faudation da suka taba tallafamin nima ma zama acikin su ina kuma bada taimako daidai gwargwado.
Yaya Abdul'ahad da Raliya suna chan Tunda bayan ya gama karatunsa sun rikesa achan itama bayan Walid ta kara Haihuwan mata biyu sai da muka gansu a hoto,sau daya suka zo gida suka yi wata daya suka koma.
A mataki na rayuwan da nake ciki yanzu Allah ya gama cikamin duka Burika na,Ban yi ilimin zamani ba amnh ba inda zan shiga a raina ni sannan ban zama mai ji ba,ina nan da raunin ji na Engr bai taba kyamatata ba.
Ni da kaina nayi tunanin naje Ear center a dubani duk da an haifeni da laluran ne, tunda na tab'a ji an ce masu irin laluran mu ma ana saka musu wata yar Na'ura domin karfin jin su ya karu.
Ammah sai Engr ya hanani yace shi fa ni yake so,saboda haka na zauna ahaka baya son wata Fa'iza bayan bakar daya sani mai raunin ji.
Shiyasa sai na bar mganar na kuma Rumgumi kaddara ta nagodema Allah,Yan'uwana duka na tallfesu,Ina da kudi ina da dukiya,da bansan iyaka ba Kuna Engr bai taba sama ma Nemana ido ba kudin da nake samu ta bangaransa bai taba fasa bani ba,Koda yaushe supporting dina yake yi yana karamin karfin gwiwa na zama giwar mata a dangi kowa ya taso da matsalansa waje na kuma zan mangance masa. ban taba duba baya ba komai ina yi ne sannan ina Duba zumunci
Ban taba shafa man da zai sakani Haske ba,sai dai jin dadi da hutu da shafa mayuka masu tsada yasa fata ta sauya na zama yar lukwai lukwai dani,a yanzu haka ina da Shekara arba'in ammh in ba fad'a nayi ba bazaka taba ganewa ba tunda ina nan yar Caras dani daga ni har Engr kamar alokacin muke cin zamanin mu.
Engr ya tallafa min na kai Goggo da Mallam Hajji sun sauke Farali sannan na gyara gidan da Tamadina tayi aure na kuma bama maman isuhu jari Sa'adatu da Habiba ko ba bu abunda bana yi musu,jari na basu dukkansu suka kama sana'a
Yaya Asiya itama ta fara harkan Saida zannuwa,Yaya Mariya kuma ta koma makaranta ta hada Degrre dinta hafsah ma tana zaria tana aikinta tana cin moriyar karatunta.
Bangaran zainab da Ishaq kuma sai hamdala kowa ya rumgumi kaddaransa tunda yasan har Abada Fa'iza tayi masa nisa,sai dai yayi namijin kokarin rike kan ya'yansa Engr ma yaso ko Ahmad ya bar mana mu rike yace bazai bani ba ai bai gaza ba nima ban damu ba tunda na Haifi wasu ya'yan haka na gayama Engr ya kyale masa ya'yansa tunda muma mun haifi namu.
Ni da Zainab zumuncin mu har a gidan Aljannah,ta daukeni kamar yar'uwanta haka nima muna gayama juna sirruka sannan muna bama juna shawara tana zuwa gidana in ta shigo Abuja nima ina zuwa wajenta in na Shiga Lagos ammh gidan Anty Fadila nakan sauka sai dai naje mu ga juna mu yi zumumci.
Daga yaran har Zainab har su Mama ba wanda ba na yi ma alheri sai dai su ji kunyata ammh ni,ko ajikina saboda zumunci sannan kuma na manta baya ni gaba nake dubawa saboda da ban yi hakuri ba da ban kawo matakin Rayuwa mai ingancin da ni ke ciki ba yanzu.
Yanzu haka da bikin Anum ya taso zata auri yaron gwamnan Jahar katsina abikin wata course mate dinta Aisha Kabir Mahuta ya ganta yace yana so,dayake har katsinan ta biyo Aisha shi kuma wanda Aishan ta aura babansa yayi mataimakin gwamna itama Aishan babanta sanata ne.
Ban taba tunanin ko a mafarki zan zama surukar gwamna ba sai ga shi Allah mai Daukaka ya Daukakani.
Ishaq ya yi mana kara ya nemi Engr da shi akayi mganan aure su kuma suka yanke sadaki da komai.
Wata Biyar suka saka,kuma ba'a kasar nan zasu zauna shi a babbar Birnin U.S amarecia yake aiki da wata ma'aikata mganguna.
Ban saka bakina akan harkan bikin ba na barma Zainab komai itace uwar amarya ko abu ne sai dai nace tayi ma su Anty fadila mgana ko su Yaya Mariya mganar kayan gyara ne kad'ai nace zan yi ma Surayya dee marubuciyar Halin yau mgana na gyaran amare na kuma gayamata tace ba damuwa mun gama mganan zata had'ama Anum mganganun gyara da Saiwar kazan Gudiyo.
Tunda taji ma y'ata ce shikenan tace ai itama uwa ce,kada na damu zata gyara Anum,saboda tun bayan kayan da na siya a wajenta lokacin bikina da Engr muka saba muke zumunci da ita.
Sannan sai Turaruka da nace zan yi mata da Hannuna.
Mganar kayan daki kuma Engr da Ishaq suka ce zasu gyara mata kayattaccen gidanta mai sama da kasa dake katsina jamal kuma zai yi kayan gara a matsayinsa na Uba.
Su yaya Mariya da su Anty Fadila kayan kitchen da su labulayya,Abba kuma yace tunda an waresa shikenan zai d'inkama Amarya kayan fitar Biki.
Bikin ya matso sai shirye shiye ake yi gidan Ishaq na katsina za'ayi taron. tunda sai bayan wata biyu zasu tafi America.
Amir na chan bai samu zuwa ba. ammh Anum tace zasu kai masa Ziyara ita da mijinta bayan bikin
*****
*MURFI..*
Bayan gama shagulgulan bikin Anum da angonta Mas'ud Ibrahim Mahuta. shima mahaifinsa dan garin Mahuta ne kamar mahaifin Aisha.
Ta kuma tare a gidanta Katon gaske sama da kasa har da Swimming pool babu kuma abunda babu na kayan alatu iyayenta sun mata bajinta matuka Abba shi ya ba da auran Anum Saudatu Kanin gwamna mai ci alokacin Dr.Ibrahim Mahuta ya karbi Auran,an yi shagulgula sosai abunka na masu da shi duka dangin mu kwanmu da kwarkwatan mu a katsina muka yada zango har Yaya Abdul'ahada da Raliya sun zo kasar Saboda auran Anum
Ni kaina nafi sati a katsina kafin na koma Abuja,Tauhudat kadai ke tare dani Tamadina da Paa suna Abuja saboda makaranta,da Maa zasu koma suka koma tare da su yaran sun saba da kakaminsu basa ma kewar mu ni da Baban nasu balle shi da baya zama.
Mutane na sun min kara Hajiyar su Raliya bazan manta da ita ba taro na agidanta nayi shi manyan mata duk sun zo Sa'adatu da Habiba ba'a bar su a baya ba suma iyayen amarya ne.
Ishaq ya danne komai an yi biki Lafiya an gama lafiya ban tusa kaina ba na kame kaina a matsayina na uwa na bar ma zainab da su Yaya mariya wannan bangaran. mgana kuna in dai ta gemu da gemu ne su Engr da su Abba ne komai.
Sai ga shi Yarana da Ishaq ke kira bakake yake jin kunyar nuna su sanadinsu ya shiga gidan gwammati sannan yaga mutane da dama yan siyasa, sanadin Anum baisan iya Daraja da kimar da ya samu ba,ba shi da bakin mgana illah ya kara nadama ga abunda ya aikata a baya.
****
Dagani har Engr muna da Gajiya a tare damu,Jiya ma Musty ya koma makaranta tare muka dawo Abuja dashi su Ahmad kuma suna katsina zasu koma tare da Babansu.
Dagani sai Tauhidat agidan Engr na ta barcin gajiya sanda muka yi wanka ni da Taihudat mukaje gaisuwan safe.
Gefensa na zauna ina mai kuramasa ido ina kallonsa cike da mirmishi.
Addu'a da fatan alheri nake ta kwarara masa har sai da idanuwana suka ciko da kwallah.
Tauhidat na kallah dake gaurancinta tana yafito kafar Baban nata kallonta nake yi ita kadai ta Dauko kalan Fatata da kamata,Tamadina da Paa kuma kaf din su ahalin su Engr ta Dibo Tamadina Maa tace kamar kafayatu tana karama.
Kaina na kara kallo ina sanye da wani leshi mai Tsada ne,kimanin kudi dubi Dari da goma,na siye shi Saboda kalan mai ruwan zuma ne Engr na son kalan,a kayi min dinkin Buba yayi cif ajikina,Yau ba zan fita Shago ba, akwai yaran dake kulamin da shi ko bana nan in wani abu ake so zasu kirani a waya.
Na kara kallon kaina naga yadda na koma cikin shekara shidda zuwa bakwai yadda Allah ya haskaka rayuwa ta.
Ni Fa'iza ban taba zaton watarana matakin rayuwa zai kaini ga haka ba ammh nasan naci Ribar Hakuri ne da addu'a.
Mijina kuma bani da bakin mgana sai masa fatan ya gama da duniya lafiya kuma yasa na zama matarsa a gidan aljannah bani da abunda zan iya rama masa alherinsa gareni.
Ashe Tauhidat tayi barci a hannuna ban sani ba sai da naji ta sunkuya sannan na kwantar da ita ta chan gefen na dawo na Zauna kusa da kafafun Engr na fara masa Tausa ina Fadin"Sannu Baban Anum aurar da y'a ba wasa ba.."
Nazata barcinsa ya yi nisa sai gani nayi ya Bude idanuwansa tar a kaina Ido na waro kafin in yi mgana ya yi caraf da hannayena bai yi wata wata ya fad'o dani jikinsa bayan ya jawoni.
Saman kirjinsa na fad'a ya kamani ya Rumgume kamkan na wani Lokaci muna jin bugun zuciyar juna
Kafin ya sausauta rikon da ya yi min yana Fadin"Ban gaji ba domin yanzu zan dora da shagalina ki bari in nagama sai ki min tausan gabadaya"
Na dago kaina zan yi mgana ya hade bakin mu Waje daya ya dade kafin ya Sararamin yana Haki yace"Tsakani ga Allah nayi hakuri yaron nan Mus'ab haka ya kirani yana godiya kuma nasan shima yaji dadin da nake ji ne indai Anum tayi gadon ki. ammh ni sai dai ayi ta min kwalele bata sab'uwa fa ina son kanwar Tauhidat ko kaninta.."
Dariya na saka ina fadin"Surukin zamani..'
Engr ya karishe da fadin"Kuma ya had'u da surukan zamani ba.."
Kai na girgiza nasan waye Engr har aransa shi Surukin zamanin ne ina fatan kada watarana ya bani kunya gaban mijin Anum.
Biye masa nayi muka sha shagalin mu Tauhidat na gefe tana ta sharan barci muka juya muka kalleta ni da shi kafin mu yi mirmishi.
Cikin sigan rad'a yace"Allah yasa na jefa kwallo a raga."
Yafad'a yana shafa cikina sai na Danne hannunsa kan cikina yana Fadin"Ameen Habibina Allah ya barni dakai har a Ajannah"
Saboda burina kawai na kara samun ciki ni da Engr mun yanke shawaran in mace na Haifa.
Goggon Karofi zan yi ma takwara.
In kuma Namiji ne Abba ne.
Ya amsa min yana sumbarta wuyana kafin yace"Allah ya yi miki albarka kin bani komai Faa'izaa. ya'ya mata,Kanwa,yaya,abokiya kece komai nawa kodayaushe fatana mu Dauwamana tare har Mutuwar mu kin zama ni na zama ke,Allah ya bamu Tsawon rai mu aurar da Amir da Musty da Ahmad sannan mu kai Tamadina da Tauhidat gidajen mazajen su"
Ina dariya nace"Ameen Lokacin ka zama Kaka Kenan..?
Wata muguwar Dariya ya yi kafin yace"Granny zamani ba. Ban yarda na Tsufa ba fa,ke kuma ai lokacin kin zama su Goggo Faa'izaa. Haka zaki ji ya'yan su Anum suna Goggo..Googgo..'"
Har yana kwatantawa na mintsine shi da hannu ina fadin"Kai kuma fa ya sunan ka..?
Yana dariya ya karya murya kafin yace"Granny.
Granny mana is in Stayel haka.."
A yadda ya fad'i sunan ne yasa muka fara Dariya dagani har shi.
Dariya mai cike da farinciki da nishadi.
nishad'in da nake fatan ya Dauwama har abada a rayuwarmu.
*ALHAMDULILLAH*!
*ALHAMDULILLAH*!
*ALHAMDULILLAH*!
*Nan na kawo karshen Labarin KANA NAKA. Kuskuren da ke ciki Allah ya yafe min,in da kuma nayi daidai Allah ya ba ni lada*
*Godiya ta Musamman ga Masoyana da suka yi Tururuwa wajen siyan wannan labarin Tabbas kauna ce,nagani kuma na yaba Allah ya saka da alheri VIP001 Tare da FA'IZA'S HOUSE,jinjina ta musamman gareku tare da kyatattun Sharhin ku, Allah ya had'amu a gidan Aljannah Firdausi Ameen*
*Kafin na sake dawowa da wani sabon Labarin in muna raye,zan tallata muku sabon Littafin mu mai suna BAKAR TA'ADA.*
*Na marubuciya Surayya Dahiru gwaram,marubuciyar Halin yau da Sabo da kaza,ba domin tana kawata zan tallata muku labarinta ba,a'a sai domin yabon gwani ya zama dole kada ku bari a baku labari,Na tabbata zaku ji dadin sa kamar Kana naka kila ma fiye da Hakan in sha Allahu*
*Allah ya jikan iyayenmu da magabatanmu,Allah ya jikan Kawu Abdullahi Allah yasa yana Dausayin Aljannah Allah ya jikan Muhammad Tukur mijin kanwata Allah yasa yana Kyakyawan matsayi,Allah ya gafartama Alhaji Abubakar Mijin Ummi Allah yasa chan ta fiye musu nan Gabadaya. Mu kuma Allah yasa mu cika da kyau da imani Ameen ya Rabb*
*INA SON NA MAIDA KANA NAKA ZUWA HARDCOPY.*
*AMMH HAKAN BAZAI SAMU BA SAI DA HAD'IN KAN KU,IN AKWAI MASU BUKATA ZASU IYA MIN MGANA TA WANNAN LAMBAR 09069067488*
*Janafty*
*02/08/2023*
*JAMILAUMAR*
No comments