Recent Updates

Kana naka Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

 

KANA NAKA..!*


*Wattpad:Jamilaumar351*

*Mallakar:Janafty*

*Arewabook:Jamilaumarjanafty*

_Saturday 10june_

*Time:12:00pm.*


*Wannan Labarin tundaga farkonsa Har zuwa K'arshen sa Sadaukarwa ne gareka MUHAMMAD KARIM(MK)*


*Labarin KANA NAKA,Tukwai ci ne tare da kyauta na musamman zuwa ga Antyna ANTY SIS♥️Ba rubutu na kike so ba*

*Ni kike so,yadda kika kaunace ni domin Allah kema Allah ya so ki ya kuma lullube rayuwarki da alheri Ameen*


*KIRKIRARREN LABARI NE DUK ABUNDA AKA GANI YA YI DAIDAI DA NA SUNA,KO HALLAYA,GARI KO DABI'A TO ARASHI NE,JUYA WANNAN LABARIN KO SARRAFA SHI TA HANYAR FILM KO D'ORASHI A YOUTUBE CHANNELS SABA'MA HAKKIN MALLAKATA NE*


_Da sunan Allah mai Rahma mai jinkai_


Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DWmMEYuvM0QH3eJh17wR4X


            *🅿️01*


*Shimfid'a.*

Katsina.

Area:Layout.


Karfe Tara ya shigo gidan nasa kamar yadda ya saba duk da yau yayi dare agidan mama chan kofar soro tunda tachan ya fara sauka bayan isowarsa Dazu da mangariba dagachan inda yake aiki a birnin Abuja.

Da kansa ya Tuko kansa Daga Abuja wannan Satin sakamakon Direbansa mallan iliya,mahaifinsa ba Lafiya ya tafi garinsu ya Dubasa bayan ya mai izini..shiyasa gabadaya agajiye yake gabobinsa gabadaya sun sake suna Bukatar Ruwa mai zafi tare da Tattausan Hannun wajen kwantar dasu su koma Daidai kuma Gajiyarsa ta Hada harda Dadewar da yayi mai baiyi Dogon Tuki ba ko Chan karofi zai Tafi Mallam Iliya ke tukasa Abu ne mai Wahala ka gansa yana Tuki da karan kansa.

Cikin muryansa mai Cike da Zati kamar ko yaushe yayi sallama bayan ya shigo Kyakyawan falon gidan nasa,wanda yara duk sun bata Fentin da Rubutu da Maker da Pencil,sun gama Lalata kyakyawan fentin Dake cikin Falon da ba'a sabuntasu ba Sannan ga kujerun nan duk sun ji jiki,sun fara yagewa Kushin din zaman duk yayi kasa,ya yamushe,shi kanshi Cafet din Tsakar Dakin ya fita Hayyacinsa Duk yayi Wusu wusu sannan yayi Datti Sosai.

Sau tari irin wad'anan abubuwan ke saka yayi zamansa Abuja baya kaunar ya shigo Katsina ya Shigo Gidansa yaci karo da yanayin yadda MATAR gidan ta bar yara suka barnata komai na gidam kamar gidan wata mai Saida Kuli kuli Tsabar yadda gidan ya fita Hayyacinsa.

Cikin yanayin kallonsa ya kare ma Falon kallo karamin Tsaki yaja ganin harda Takardun yaran duk sun yaga sun gama Haukata Falon bai nemi kowa ba sanin ba Sautin dawowarsa zataji ba Wacce ko agabanta kake sai kayi mgana kana Faman maimaici take iya jinka.

Yana Sarsarfa zuwa Bangaransa,wanda ke Rufe sai in ya Dawo ne yake budesa da kansa kamar Daga sama yaji Daga bayansa ance"Sannu da zuwa Yaya ISHAQ.."

Cak ya tsaya kafin ya juyo lokaci D'aya yana kara rike yar Jakar Laptop din dake Hannunsa,Girman Idonsa ya kara na ganinta domin har ya koma wanchan Satin bata agidan kenan bayan Tafiyarsa ne tazo gidan kenan..?

Bai damu ba illah baki Daya mele kafin ya ce"Sannu da gida.."

Ta amsa mai tana kokarin Tattara kayan yaran da suka gama Bidirinsu yanzu afalon kafin Yaya Fa'iza ta ja su ciki Domin su yi Fitsari su kwanta.

Bata Damu da yanayin da ya amsa mata  ba inda Sabo ta saba tun tasowarta bata Taba ganin Fara'ar Ya Ishaq acikin gidan yayarta ba sai dai in chan gidan Mama kofar soro ce ko kuma yana Tare da yan'uwansa su a Gare su mutum ne mai wahalan mu'amala.."

Agabanta ya Bude kofar Shashensa ya shige ya rufo kofa ta bisa da kallo ta jinjina kai Gaskiyan Anty Binta batagwara ce Data Dad'e tana Fadin ban da Kaddaran aure ta ina Yaya FA'IZA ta Dace da Ya Ishaq..?Ya Ishaq Dogo ne Farin Buzu tas dashi Domin Mama kofar soro Buzuwar Yamai ce,Sannan Baba Kabiru marigayi Cikakken batsine daya fito Daga Korofin katsina Sai dai kaf ya'yan mama ita suka Dauko Wajen kyau da Nasaba Domin har yau da shekaru suka ja kyanta bai Zube ba Tanan nan mai kyau da ita.

Kuma yanayin Tsahon sa ya biyo na Dangin su Baba ne dake Karofi suma Dagayen katsinawa ne marasa Lalaci sannnan sai ya Hada da Hancin Mama da Sirantar ka ta yasa Ishaq ya zama mai kyau kuma mai aji sannan mai Tarin Ilimi Addini dana Zamani Wanda Duniya ta san sa kuma take ji dashi,Ayanzu haka Babban ma'aikaci ne A Hukumar Tattara Haraji na kasa reshen Abuja(FIRS)Federal Inland revenue Services,Ya dade yana aiki a wajen shekaru hudu da suka gabata da farko a reshen su na Jahar katsina ya fara aiki da su shekara uku kafin ya samu karin matsayi sai aka yi Transfer dinsa ya koma babban Ofishin su na Abuja,sosai yake jin dadin aiki a abuja musamman ma da samun Adalin Shugaba irin Dr. Lawal bako da yakasance shine Shugaba a ofishin su na Abuja kuma Uba garesa ko nace wanda ke shirin zama Surukinsa nan da Lokaci kad'an.


Yaya FA'IZA kuwa iyakarta primary School,primary  di'n ma ba ta gama ba,a karatun Boko kenan na addini kam Saukakkiyace ta wannan Fanni sannan ta karanci sauran littafan addini iya abunda ya sauwaka ammh Duba da wannan Zamanin da muke cike domin kina da karatun muhammadiya ke bakowan kowa bace in baki Hada Fukafukan Ilimin Boko ba,Bama wannan ba Yaya Fa'iza ba irin Zabin Ya Ishaq ba ce ba cin haka ma Tana dq Laluran rashin ji,Bata iya jin mgana ahankali sai an mata da karfi take ji Dashi aka Haifeta Laluran TaMADINA ce ya shafeta Tunda ita din BEBIYA ce da shi aka Haifeta ba ciwo bane.

Tana wannan Tunanin tana Faman gyara Falon acikin ranta Tana Tunanin Yaya Fa'iza batasan ya Ishaq zai dawo yau ba domim kwata kwata bataji tayi zencen ba sannan basu da abinci agidan Taliyace ta Dafa ma su AMIR da Daddaren nan kuma D'ayace duka suka cinyeta ba Saura.

Kayan yaran ta kwashe ta tattara Takardun da suka yanka suka Zubar ta kai waje ta kofar Kitchen ta fita ta zubar a Abunda suke tara shara kafin ta Dawo Cikin Falon Dakin yaran ta Nufa inda yayar tata take domin ta shaida mata Dawowar Mijinta nata.

Da sallama ta shiga duk tasan ba lalle ta jita ba Amir Dake kwance ne ya amsa mata,Anum kuma har tayi barci mustapah musty Tuni har yayi barci,Ahmad ne a Hannunta tana Faman kiciniyar sanya mai pampers alamun wanka ta sake mai.

Karisowa shigowa Dakin yaran tayi mai Dauke da ciki Daya da karamin Tiolet,Adakin akwai gado guda uku kanana na yara,Daya na babban yaya ne Amir D'aya na Anun ce sai d'ayan na Mustpaha ne Ahmad na shan Nono Fa'iza bata yayesa ba wajenta yake kwana 

Akwai Drowers na yaran guda uku acikin Dakin,inda suke ijiye kayansu na makaranta Dana gida,Har HAFSATU ta kariso ta zauna gefen Gadon Amir Fa'iza bata san ta shigo ba Hankalinta na kan saka ma Ahmad pampers ganin haka yasa Hafsatun watsa ma Amir Harara tana Fadin"Wai sau nawa zan maka Fad'an watsar da kayan ku duk inda kuka samu ne.?

Cikin muryan yarinta yace"Na Dauke nawa nasu Anum ne fa.."

Kayan ta Daga tana Fadin"Ai kai ne babba in suka bata sai ka gyara Amir din Umma.."

Jin Abunda tace ne yasa yayi mirmishi kafin yace"To Anty Hafsatu.."

Yafada Lokaci Daya yana kallon Fa'iza wacce har alokacin bata san Hafsatu na Cikin Dakin ba,Har sai da ta mike ta Zube kayan cikin kwandon da yaran ke tara kayan wanki Amir  D'an kimanin shekaru Shidda da wani abu aduniya yace"Anty Hafsatu..Umma fa bata san kin shigo ba, kiyi mata mgana."

Hafsatu tace"Zan mata ka kwanta kayi barci.."

Kai Tsaye yace"Umma nake jira ta gama shirya Ahmad ta mana Addu'an kwanciya barci.."

Hafsatu ta juyo Daidai Lokacin da Fa'iza ta Dago bayan ta gama saka ma Ahmad saukakkam kaya tunda zasu kwanta ne taci karo da idon kanwar nata akanta Cikin Sanyinta da yanayin mganarta Tace"Hafsatu..yau..she kika shigo..?

Ta Fada tana kokarin Daukan Ahmad.

Hafsatu ta zauna gefen gadon Amir tana Fadin"na da'n jima da shigowa.Amir oya bude Hannu muyi addu'an barci."

Ba musu ya Bude hannu itama ta Bude suna karanta addu'ar Barcin da Annabi ya koyar da karfi ita dashi zaku mamakin yadda yaron yake karantowa Tiryan Tiryan wannan kuma kokarin Fa'iza ne bata bari wannan Ilimin nata ya tashi a banza ba Tana kokarin Rabashi ita da ya'yanta.

Fa'iza kuma Ficewa tayi Daga Dakin ganin suna addu'ar Barci Bedroom din Dake kallon Shashen Ishaq ta Shiga ta Shimfide Ahmad a kan gadonta na Royal bed sai dai ya kwana Biyu duk yaji jiki.

Dakin shima dai kadahan kadahan,Wardrope ne babba adakin ssi kofar Tiolet,daga ganin yanayin Dakin shi kanshi Shirgi yayi masa yawa Sannan uwa uba Cafet din Daya malale bedroom din shima duk ya kode yaji Duniya Duk da karfinsa na Italiyan Cafet..

Ta kwantar da Ahmad din kenan zata Fito Daga Dakin suka kusa cin karo da Hafsatu daya sa ta koma da baya tana Fadin"Ban san zaki shigo ba.."

Hafsatu ta bi ta da kallon Tsausayi kafin tace"Yaya Fa'iza kinsan ya Ishaq zai dawo yau..?

Ta fada da dan karfi Saboda ta jita Da Sauri Fa'izan tace"Eh..Me kika ce..?

Tafada Cikin yanayin sanyinta da mganarta Hafsatu ta kara matsowa kusa da ita da dan karfi tace"Ya Ishaq ya dawo nace.."

Fa'iza ta zaro ido kafin tace"Yaushe..?

Wlh bansani ba..?

Hafsatu tace"Dazu ina falo kafin na shiga Dakin su Amir.."

Fa'iza ta kama Hanyar barin Dakin Tana Fadin"Yana bangaransa ne..?

Da karfi Hafsatu tace"Eh..!

Har ta fice tana binta da kallo ganin yadda take tafe tana kokarin Daidaita Hannun Rigar jikinta na Atamfa Daya dan mata yawa yana dan Fado mata.

Kitchen naa fara isa na Bude Fridge na Dauko mai lemu da ruwa na D'ora saman wani karamin Faranti na kuma Dora Kofuna guda biyu na fito lokaci d'aya na nufi bangaran Megidan.

Kofar shashen nashi yana Bude ne ta Tura ta shiga da sallamanta duk da tasan ba lalle yana Falon ba,Agidan kaf bangaransa ne ke da Falo da Bedroom har guda biyu ne,Kuma bangaransa ne yafi ko'ina kyau domin ayanzu ma kyakyawan Falo ne Dake Dauke da Manyan kujeru na alfarma masu ruwan zuma gabadaya Falon Ruwan zuma ne,harta da Labulayen kalansu ruwan zuma da Hadadden Tattausan Cafet din Dake Falon wani Sihirittacen kamshi na tashi na Irin Turaran da Ya Ishaq ke yawan amfani dashi ne..

Akan Center Table din dake falon na Sauke Farantin Hannuna kafin na karisa D'aya daga cikin Bedroom din Dake bangaran  inda na san Ishaq din yana ciki.

Da sallama na Tura kofar na shiga yana Tsaye gaban madubi ya gama saka kayan barcinsa masu Taushi Farare,riga da wando,waya ce a Hannunsa yana mgana cikin Sanyi da Tattausawa.

Ganin haka yasa Fa'iza ta juya zata fita har ta kai jikin kofa Hannunta kan marikin kofar ba zato taji muryansa Cikin Kaushinsa akoda yaushe ya Kirata.


  "FA'IZA.."


dayake da karfi yayi mganar na jisa Da Sauri nq juyo inaa gyara wuyar riga ta kallon da yake min ne ya sanyaya min Jiki D'aya sa na kariso gabansa Jikina na rawa ko kafin nq samu Zarafin mgana ya D'aga min hannu Cikin Fushi yana Fadin"Je ki ma kawai domin ganin ki karin Takaici ne a wajena.."

Yafada kai tsaye Lokaci D'aya yana kauda kai Dauke da matsanancin Takaicin daya Dade yana cinsa tun shekaru Takwas da suka gabata.

Duk da ba duka tna jisa ba nasan ransa ya baci sai na Durkusa kan gwiwiyoyina Cikin yanayina nace"Ka..kayi hakuri.."

Kamar na watsa ma Fushinsa Fetir haka ya taso min yana Fadin"An ki ayi Hakurin..?

Nace bazan hakuran ba..?

Aikin banza ni zaki raina haka Fa'iza..?In shigo gidan nan tund'azu kiyi banza Dani kamar wani kashi sannan kin ga Dama kin shigo bangarena kuma kin gan ina waya ki Tsaya in gama ki gaisheni ne ki ke ke jin asara ko..?

Har da juyawa ko kunya zaki Fice ga Dan iska ko..?

To tashi ki Ficemin Daga Daki bana son ganinki..Domin ganinki ba komai Cikin sa sai karin Takaici da bakinciki..wlh har gobe bazan Daina cewa Hajiyar Karofi da Baba sun cutar dani ba..Cuta ta har Abada da suka Hada aure na Dake FA'IZA.."

Ya karishe Fad'a yana nuna min babban yatsansa Lokaci Da'ya da wani banzan kallo dayake bina dashi kaina na kasa ko motsin kirkin na kasa yi daga inda nake durkushe Domin  indai ana Sabo da Tozarci da Mganangun Cin mutimci to ni na gama Sabo indai Daga bangaran Yaya Ishaq ne.

Baya ya juya min yana Faman kokuwa da bacin ransa yana jina Cikin yanayin mganata  ina kara Fadin.


"Kaayi hakuri don Allah..Ban ji shigowarka bane ina chan ina ma su Anum shirin barci sai yanzu Hafsatu ke shaidamin dawowarka..!

Sannu da zuwa.."


Kyaci yayi kamar wani maciji shifa ba Domin Ya Binta ta Kira sa akan  yazo yaga kayan lefensa da ya bata kwangilar hadawa ba,da babu abunda zai kawosa katsina cikin wannan Satin ballatana har yazo ya shaki wannan Bakinciki.

Juyowa yayi yana kallona Lokaci d'aya kawai ya tsaya yana kara kare ma Fa'iza kallo akasan ransa yana kara Tambayan kansa da gaske FA'IZA matar sace?

Fuskarta ya kara kalla yana jin Shima Tunda yake bai taba ganin mai baki,bakin Fuska irin Fa'iza ba, zai iya Rantsuwa ga Allah kaf ajikinta banda Hakoranta ba inda yake da Haske bakace ta kwantance irin bakin nan mai Duhu da Dususu,Sannan mummuna ce bata da kyau a ganinsa sannan bata da  Tsaho wanda Hausawa suke cewa mai cike Girman kyan y'a mace Gajera ce,da Fadin Fuskarta kamar Fanteka,Da guntun Hancinta da bakinta mai Fadi shima,Abu daya ne zai ce mai kyau a wajen Fa'iza shine tana da Kirar mata Wannan kam masha Allah Dirarriyace Kirjinta da kugunta suna cike da Fasali ya mace ko ayanzu Data Haifi ya'ya Hudu bata Sauya ba Ta na nan da Jikinta mai Fasali daidai misali bata da kiba sai dai Haihuwa ta d'an Budata.

Sai kuma bangaran Ni'imar jikinta ta wannan bangaran bai da ta cewa ya san Fa'iza fiye da yadda ya san kanshi Fa'iza bata shan kayan mata ko wani abun da zai kara mata Ni'ima duk abunda yaji in yazo tarayya da ita shine Hallitarta wanda Ubangiji ya yi mata,bazai kusheta ta wannan bangaran ba,abu daya ne ke masa cikas baya sonta sannan tun farko komai nata a wajensa bamai kyau ba ne shiyasa ta wannan bangaran ya gaza sakin jikinsa to ya saki jiki a wajen Fa'iza yaji me..?Matar da bata iya komai ba,Shiyasa ba kasafai ya cika Raba'arta ba.

Kayan jikinta ya kara bi da kallo,sai da Ransa ya baci har gobe yana jin Mamakin yadda Fa'iza bata taba saka kayan da yayi mata Daidai ba ko Rigar da hannu yayi yawa ko Sikat kagansa kamar Buhu in yayi mata mgana sai tace itake son haka kada watarana su mata Kad'an,Yau ma din riga da Zani ne ajikinta Rigar Hannun dai bai zama ya na yi ya na Sabule mata Jan Bra dinta Data sanya tana bayyana Saman kafad'anta.

Wani mololoon abu ya tsaya mai yaki wucewa a makogwaronsa Saboda Bakinciki kamar shi  ISHAQ KABIR KAROFI kamar shi Ace wannan abar ce Matarsa Uwar ya'yansa..?

In ya kalli FA'IZA sai yaji Fiye da madaukacin Takaicin daya ke ji in ya tuna itace yau MATAR SA..Fa"iza ba mafarkin sa bace a irin Rayuwar ISHAQ KABIR KARAFI..Sam Fa'iza bata dace ko kadan da Tsarin Rayuwarsa ba kowa yasan Ishaq dan gayu ne mai ilimi ne,kyakyawa ne dan Fafane d'an Alfahari ne Duniya tasan da zamansa mai Burin Auran mace FARA mai kyau mai Tarin kwalayen matakan karatun Zamani SAI DAI KASH"

Hakan bai samu ba..Sakamakon kutse da Fa'iza tayi cikin Rayuwarsa ta Ruguza Mafarkinsa har Abada bazai daina Hango FA'IZA a matsayin Nakasun Mafarkinsa ba.

Sannan karin bakin cikinsa yana da Burin kullum in ya Dawo aiki kyakyawan matarsa ta tarbesa ita da yan Gudi gudin ya'yansu Farare masu kyau kamar ya'yan Turaawa tun yana yaronsa yasha yin wannan mafarkin sai dai ina Hajiyar Karofi da Baba sun Saka almakashi sun Datse wannan Mafarkin nashi,Gabadaya ya'yan da suka Haifa da Fa'iza Shekara Takwas da auransu duka ita suka Biyo acikin su ba wanda ya Dauko ko da Hasken Fatansa ne sai Baki irin na uwarsu,Yana Tsananin kaunar yaransa ammh wani Lokacin yana kunyar nuna su ga Duniya Saboda a yanayin Tsarin Rayuwarsa bai kamata Tsarin Iyalansa su zama haka ba.

Duk da irin barnan kudin dayake yi a kansu Fa'iza bata da wannan Tattalin komai sai ta barshi su lalata shiyasa ya gaji ya barta ta karaci muguntarta sai dai yaci ta ita kadai.

Gefen gadon Dake Dakin nasa ya koma ya zauna yana Kad'a Fararan kafafunsa masu cike da gargasa yana kara kallon Fa'iza Dake duke har Lokacin kanta na kasa kamar tamai Sujjada,Kai ya girgiza yana Tunanin yadda yaso ya Dakile ma Fa'iza Haihuwa sai dai ina kana naka ne Allah na nashi,Kowani Tsarin iyali bai karbeta ba,da an saka mata lokaci kadan' sai ya bata matsala na karshe ma da aka saka mata yar Ashanan da jini ya Tsinke mata Dakyar ta sha Ashe Rabon Ahmad ne,Haihuwa take yi akai akai ita ko gajiya batayi da Hidiman yara da Haihuwa kamar akuya..?

Tsakani ga Allah ya'ya indai ta Bangaran Fa'iza ne shifa ya kai makuran Hakura da hakan.

Shi kadai kawai ya saki Tsaki"Mtsewww.."

Kallonta ya sake yi kai Tsaye kafin yace"Where is my Childreen.?

Yafada da dan karfi ta Dago tana Kallonsa Kafin tace"Eh me kace..?

Wani Tsakin yaja Kafin yace"Na manta ba Turanci..Ina yarana na nace..?

Mutum yayi ta wage baki yana mgana har sai makota sun gama jinsa ke ko Sirri ne bamai yi Dake domin kafin ki gama gane abunda mutum ke nufi Duniya ta gama jin Halin Dayake ciki..Mtswwwsss.."


  Yana gama Fadin haka ya mike ya Tsallaketa ya fice Daga Dakin,Kaina na kasa na saka hannuna na share guntun Hawayena kafin na mike Salau Salau nabi bayansa saman D'aya Daga Cikin kujerun falon na samesa ya kunna kallo remot a Hannunsa yana Sarrafawa.

Jikina na rawa na karisa inda na ijiye Farantin dana shigo dashi na Tsiyaya mai ruwa mai sanyi nataso nazo gabansa na Duka ina Fadin"Kayi hakuri..Ga ruwa kasha.."

Sai da ya ga Dama sannan ya kalleni kafin ya amshi ruwan kadan yasha ya maida mata yana Fadin"Da ruwa kadai kika iya tarban mijin ki da yayi kwana Goma baya nan..?

Ya fada yana mai Tsurata mata ido Fa"iza bata ji farkon mganarsa ba sai karshe yasa tace"Kwana goma..?

Tafada Cikin alamun Tambaya kai kawai ya Dafe kafin yace"Innalillahi..Gaskiya an gama Dani..Ishaq ka gama aiki kawai.."

Yafada kamar yayi kuka kafin ya kalleta yana Fadin"Ahmad yayi barci ne..?

Tana kallonsa ya kara ware murya yana Fadin"Eh nace Ahmad yayi barci ne..?

Da Sauri tace"Dukaa sun yi barci.."

Kai ya girgiza kafin yace"Ruwa k'adai ne kuke dashi agidan..?

Yafada muryansa asama kusan fa Fa'iza ta fara maida shi Sama sama ko ba da ita yake mgana ba ya yi mugun Sabon da sai ya Daga murya.

Cikin Ladabina nace"Taliya Hafsatu ta Dafa ma su Amir ina jin ta kare ma..Sai dai bari da sauri nayi maka ko Faten Dankali ne..

Dayake bansan kana Hanya ba."

Komawa yayi ya jingina jikin kujeran dayake kai yana maida Hankalinsa kan Tashar Mbc action din Daya sanya Reastling din da ake yi ya Fara Daukan Hankalinsa ganin haka yasa na Mike jikina na rawa na kwashi Farantin Dana shigo dashi na Fice ya Bita da kallo kamar ya saka kuka ai bazai ce A'a ba  inda kuma bazai Zagi Fa'iza ba kenan ta iya girki,girkinta ba inda baza'a Kaisa ba,Shi kadai ne abu mai kyau a rayuwar Fa'iza ban dashi shi dai bai gani ba ya Dade yana ganin mutane marasa sa'a a rayuwarsa ammh Rashin Sa'ar Fa'iza na musamman ne ta rasa wasu abubuwa masu Muhimmanci a Rayuwarta Rashin Sa'arta ne ma ya shafesa shima Gabadaya Rayuwarsa na neman komawa irin tata ba Domin Mama na Tsaye kansa ba, da Shima ya koma Dangin KURAME kamar yadda Zama da Kaddara ya Hadasa da Fa'iza.

Minti Talatin da wani abu na Sake Dawowa Dauke da Voul cike da Faten Dankali da Hanta sai maltina mai Sanyi Dana Hado mai dashi bai yi Tsaya mgana ba Domin yunwa yake ji Gidan Mama Tuwo sukayi shi kuma na Cimarsa bane abaya dai yaci banda yanzu Dayake cin guminsa.

Kasa ya Sauko ya tankwashe kafa ya sha Fantansa sosai,ya Dora da ruwa Maltina,Yayi gyatsa Lokaci D'aya da Hamdala Duk Fa'iza na gefensa yana Gamawa Jikina har rawa yake yi wajen kwashe kayan daya yayi amfani da su, na maida Kitchen adaran nan na wankesu domin Fa'iza in akwai abunda ta tsana kwano ya kwanar mata akitchen ba'a wanke ba.

Ita dai barta da barin shirgin yara da Rashin Shiga mai Fasali ammh ita da ya'yanta basu da kazanta ko yaya ne wanka ne Safe da yammah ita da yaran Duk Ranar duniya har sun saba suma.

Sai da nagama na kara leka Dakin na wajen Ahmad in sauri ban tsaya na  Tofe shi da addu'a ba yasa na bata Lokaci Wajen Yimai addu'a Hafsatu bata Dakin kila tana Dakin datake sauka in tazo Gidan.

Dayake nayi wanka Dazu da mangariba ban yi Tunanin Sake wani wankan ba na Sauya kayana zuwa wata Dogouwar Riga ta barci mai Taushi mai gajeren hannu,Duk da ina na da masu wando basa Burgeni nafi son Dogayen masu rufe min Har Cinyoyina Fa'iza ta Tsani ta saka kaya taga sun kamata ko sun nuna Tsiraicinta.

Ina cikin Daure gashin kaina Da na Tsefe shi yau da Safe,Hafsatu ce zata min Kitso yau bata samu Dama ba Karfanfan gashina tun na Virgin Dakyar yake Haduwa cika garesa bai da Tsawo inaa Hakin kamasa na Daure cikin Ribbon baji muryan ISHAQ asama yana Faman kiran sunana kamar yadda ya saba.


"FA'IZA.."


"FA'IZA.."


Da sauri na bar abunda nake yi lokaci daya na Rarumi Hulata ta barci na Saka ina niyar fitowa Daga Dakin ya shigo,ganinsa Tsaye a gaban ba Kikam da irin kallon Dayake min yasa nq rankwafa da Sauri ina Fadin"Gani ina..ina..!

Ban karisa ba ya Daga min Hannu Lokaci Daya yana Fadin"FA"IZA hala baki sam zan kara aure bane..?

Yafada yana Tsareni da manyan Idanuwansa.

Gabanna ya Fadi Ras! Sai na Daburce Da yanayin da yayi mganar,ba da karfi bane sai dai ai mganar auran nasa na Haddace ta akaina shiyasa nq karancin Bakinsa.

Cikin Fusata yace"Wai bada ke nake mgana bane kikamin banza..?

Da Sauri nace"Eh..Eh..Na sani..Mamakofar soro ta fadamin..Sannan sannan.."

Daka min tsawa yayi yana Fadin"Sannan me..?

Kinsan bana son wannan sanyin naki in muna mgana ko..?

Mgana bata kai ta kawo ba kiyi ta uban Rabata kamar wani abun arziki zaki Fada.."

Kokarim Boye Raunina nayi Cikin Dakewa nace"Anty Binta batagwara ta Fadamin wanchan satin da muka Hadu gidan Mama."

Wata Uwar Harara ya jefa min kafin yace"Kin sani ammh ko Fatan Alheri bazaki min ba Fa"iza..?

Kina bakinciki ne saboda zan kara aure..?

Da Sauri nace"Ahah.Naga baka nan ne,Shiyasa.."

Takaici ya kamasa kafin yace"Baki da waya ne..?

Ko lambatace baki da ita..?

Koda yake ke ai ba matar kiran jin Lafiyan miji bace za dai ki kira in wata Bukatarki ta taso miki."

Ya karishe Fada yana kallona Cikin Doguwar Rigar Barcin dana sanya kadan ya Rage bai yi Dariya ba.

Dariyan Takaichi wai zaki kwana da Miji ki saka wannan abu kamar kullib goro.

Karamin Tsaki yaja kafin yace"Na zata kina Bakinciki ne nace kin so kanki Fa'iza Shekara Takwas nayi ina Zaune Dake ban kara aure ba..Tsakaninki ga Allah ban miki alfarma da Mutumci ba Fa"iza..?

Fadamin da bakin ki na yi miki adalci ko ban yi miki ba..?

Ya fada da karfi yadda Zan jisa jikina  na rawa nace"kaayi min..sosai kayi min adalci.."

Naso na Daure ammh ina Raunina ya bada ni sai kuka hawaye sharr Tsayawa yayi yana kallon na kafin ya Tabe baki yace"Naji Dadi da kika Fahimci haka..Kada Goggon karofi  da yan'uwanki su tasaki suna Faman tambayanki kice musu ban yi miki adalci ba kiga yadda zamu kwashe.."

Malama ki kuma cire min wannan bargon Dake jikin ki wlh matukar wajena zaki kwana na Haramta miki kara sakamin wadanan Rigunan ai ba Cinikaya zamu yi ba..Ke kinga ma sha ma Zamanki ana tabaki Ke mai cikin Haihuwa Zan D'aure nan da Wata D'aya ne kamar gobe ne.."

Yafad'a Lokaci D'aya ya juya zai Fice Daga Dakin na Bisa da kallo ina D'igar kwallah duk da ba Duka mganarsa na ji ba ammh nasan yana kushe ni  ne kamar yadda ya saba.

Har ya fita Daga Dakin ni kuma har na juya kawai naji dawowarsa da kara Kiran sunana da yayi da karfi.


"FA'IZA..!


Da Sauri na Juyo  Cikin muryata Data Fara sauyawa saboda kuka nace"Na'am..!

Kallona ya tsaya yanayi lokaci d'aya yana rike da Kofar Cikin Mamaki na yace"Kuka..?

Na Dake ki ne..?

Da Sauri na Share hawayena ina Fadin"A"ah kamar wani abu ne ya Fadamim a ido na..!"

Bai Damu ba Kafad'a ya Zakud'a kafin yace"Mama ta fada miki gidana na Abuja Zeey zata zauna..?

Kai na gyada mai bai bani Damar mgana ba yacigaba da Fadin"Fa'iza kinga barin yaran nan suna bata gidan nan Duka duka yaushe muka tare acikinsa ammh kalli yadda suka maidasa..?

Komai naki ba kula ba Lura..?

Ko da yake ke kanki abar akula Dake ne bama ki kula da wani ba Anyway dai tunda kuka lalata gidan in ma mugunta ce ke zata ci..Sai da Safe.."

Daga haka ya Sakar min kofa ya fice na Bisa da kallo hawayena  na kara cika Idanuwana ina jinsa ya Bude kofa ya shiga D'akin  yaransa ya Dade kafin naji ya Fito ya Tafi bangaransa.

Kamar wacce aka Mangara kawai sai na fashe da kuka wiwi,Sai kuma nahau Rufe Bakina,lokaci D'aya da wayata Dake samam madubin dakin ta D'auki Karan neman agaji.

Da Sauri na mike na nufi wayar kirar Kamfanin Itel karama Tunda Anum tataba Fasa min Sreen din Samsumg din da Ya Ishaq ya siya min bai kara siya min wata babbar wayar ba ya Had'ani da karama acewarsa ba amfanin ma Siyan min Shafa shafan tunda ba iyawa nayi ba, ta bakinsa Fa'iza ba turanci.

Gabana sai da ya amsa ganin wacce ke Kirana Maman Naja ce Yaya ASIYA,Sunan d'iyarta ta fari ce wacce ta rasu Naja'atu ammh dayake sunan ya riga ya bita da Maman naja ake kiranta.


*ASSALAMU ALAIKUM*

*KAYA SUN SAKE SAUKA*.

*INGANTATUN SAIWOWI DA SASSAKE NE DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZA DA SU*.

*ABIN BIRGEWA BA SAU DAYA AKE AMFANI DA SHI BA. SANNAN BASU DA BAURI MASU KIDIMARWA*.

*KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR KO KUWA KE DA KANKI ZAKI YI GYARA?*

*INA SAKE YIN ALBISHIR DIN GARIN DAKA MAI KYAU DAN CHADI, SHA DA MADARA KO NONO DA KUMA TSUMIN GAMGAM*.

*INA DA TABBACIN INGANCINSU*.

*TUNTU'BI WANNAN LAMBAR DOMIN KARIN BAYANI*

*08032773332*.

*SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*

🙏.





*Janafty**KANA NAKA...*


*Wattpad:Jamilaumar351*

*Mallakar:Janafty*

*Arewabook:Jamilaumarjanafty*


*Fatan alheri gareki SURAYYAH DAHIRU GWARAM,Madallah da kawar arziki irin ki da karfafa Gwiwarki,Labarin nan yazo ma masu karatu Ina miki fatan alheri a koda yaushe na gaida Uwar Dakin Sa'ada da Gudiyo,sannan na ce Madallah da Uwar Dakin Yabi*🥰



            *🅿️02*


Da sauri na share Hawayena nayi kokarin daidaita yanayina domin ni Fa'iza ko Uwar data Haife ni bana kaunar taga raunina ballatana yan'uwana  da kullum suke kallona abar Tausayi wacce batayi dacen Gidan aure ba acewar su.

Saboda yanayin Raunin ji na, in aka kirani a waya a speaker nake saka ta wato amsa kuwwa yanzu din ma haka nayi na Daga kiran sannan na saka a speaker daidai Lokacin da naji muryan Ya Asiya na kiran sunana na amsa mata cikin dan D'aga murya.

Dagachan bangaran Ya Asiya tace"Fa'iza Ashe Yaya  Ishaq zai kara aure bamu sani ba..?

Fa'iza tayi wani mirmishin yak'e kafin tace"Eh Yaya Asiya zai kaara aure.."

Ya Asiya tace"Shi ne baki Fadamin ba,  kuma baki fada ma Mariya ba ko..?

Fa'iza tayi shuru batayi mgana ba Ya Asiya Haushi ya kamata ta fara Fada Tana Fadin"Kila ma baki sani ba..?

Domin sai ma an Dauke ka da Daraja da kima ne ake sanar dakai wani abun."

Da Sauri nace"Aaha nasani fa..Wlh na sani Mama ta fadamin sannan Anty Binta batagarawa itama ta fadamin."

Ya Asiya Dagachan bangaran ta jimjina kai kafin tace"Shi Uban gayyar bai Samu Fada miki ba kenan..?

Sai a bakin Uwarsa da yayarsa kike ji kenan..?

Anya Fa'iza wannan Rayuwar zata tafi ahaka kuwa..?

Shekara Takwas ai ba kwanaki Takwas bane."

Fa'iza ta share hawayenta da suka zubo mata kafin tace"Ai shima ya fadamin yau daya dawo.."

Ya Asiya tace"Umhh..!

Saboda takaici ma ta kasa mgana,Fa'iza kuma Daman ba ma'abociya mgana bace Ya Asiya Tagaji da shurun Fa'iza yasa ta katse mganar da cewa"Goggon Karofi ke Fadamin Zai yi aure yanzu muka gama waya da ita..Ita kema Fadamin Hafsatu tazo wajen ki shekaran jiya."

Fa'iza tace"Eh tazo shekaran jiya..tazo..."

Sai ta saki wanchan mganar Saboda bata son tayi Tsawo ita kanta Ya Asiya ai ta sani Fa'iza bata kaunar mganar Data Danganci Ishaq da Danginsa in ma ka matsa sai ta saka maka kuka Ajiyar rai ta sauke kafin tace"Yaushe ne Bikin..?

Fa"iza tace"Bansani ba.."

Ya Asiya tace"Allah ya kyauta zan shigo katsinar nima In nazo Duba Tamadina hala ba ma kiji bata ji Dadi ba..?

Ciwon kafafu take fama dashi."

Fa'iza tace"Naji Da Hafsatu tazo ta Fadamim."

Ya Asiya tace"Yaushe zaki leka ki Dubata ke da ke kusa ma Fa'iza yaushe Rabon ki da Dutsenmah Tun Sanda Ta madina ta kwanta asibiti an kusa shekara fa"

Fa'iza tayi shuru ta kasa mgana Saboda bata da tacewa Ishaq ne baya barinta tana son zuwa inda Mahaifiyarta take sai yace me zataje yi tana gidan wani..?

Ya'yansa bazasu je gidan wani suna Rab'e Rab'e ba.

Ya Asiya tayi  shuru yasa ta kyaleta sai ta shigo da mganar"Ina yaran nan..?

Hala sun yi barci..?

Ta amsa mata Ya Asiya tace"Shikenan Sai mun shigo zamu karisawa Tattauna ki kara Hakuri Fa'iza kowani bawa da irin tasa kaddaran..Mu Tamu kaddaran Rasuwar Baba ne itace silar Shigar mu duk Halin da muka shiga."

Fa'iza tace"Haka ne Daman ai KANA NAKA  ne Allah na nashi ne..Sannan na Allah ne Daidai."

Ya Asiya na jinjina kai tana Fadin"Hakane Fa'iza Allah ya mana mai kyau..Mu kwana Lafiya.

Fa'iza ta rakata da Fadin ta gaida yaranta Daga haka sukayi sallama Sannan na  ijiye wayar nq koma gefen gado na zauna ina mai kura ma Madubi Ido duk da ance ba kyau kallon kai a madubi in Duhu ya shiga ammh ni sai ta samu kaina da kare ma Jikinna kallo.

Tare da Fuskata ina Ayyana adadin Lokuta nawa ya Ishaq ya kalleni ya yab'a min..?

Koda yaushe cikin kusheni yake yi an samu ma bayan sun fara Tara zuru'a ya Daina jifana da kalmar Mummuna ammh kalmar Baka sai dai in yan Cin mutumcinsa basa kusa ni na sani Tazaran Dake tsakanina da Ya Ishaq kamar Tazaran kasa da Sama ne ko abaya ban taba mafarkim auran miji kamarsa ba Domin ba Tsarana ba ne, sannan ba kuma Had'i shi kanshi na san ni ba irin wacce ta Dace dashi bane Mama kofar soro kullum tana Fada min hakama Anty Binta batagarawa,To ammh Ba kai kake Tsarama kanka Rayuwa ba Allah ne Kana naka ne yana nashi kuma Tsarinsa ne akan gaba.

Na tabbata ba Domin kakkausan Bakin Baba kan Ya Ishaq ba, da Tuni bayan kasa ta shafe idonsa ya rabu dani  ya samu salama kamar yadda yake Fadi sai dai ina Ya Ishaq bazai iya Tsallaken mganar Baba ba Shiyasa har yanzu muke tare ina D'aukan dukkan cin kashi da Tozarcinsa

Bani da wani gata nan Duniya sai Ishaq shine uwaa na shine Ubana  da Duniya ta Tamadina ga yanayin yadda Rayuwa tazo mata sauran yan'uwanna ba waje daya muka tashi ba Bayan Rasuwar mahaifinmu  Raba mu akayi ni a karofi na fara Rayuwata Kafin dalili ya yanke zamanna achan Baba Kabiru ya maido ni katsina ya Damkani Hannun Mama.

Hawaye na haka suke faman zuba ban iya saka Hannuna domin na tare su  ba Saboda ko na goge su wasu ne zasu kara fitowa a irin wannam Lokacin nake samun Fitar da abunda ya dade yana Damuna,Ba bakinciki nake yi Saboda Ishaq zai kara aure ba,A'a ai daman na sani yafi shekaru yana ikararin zai auri Zab'insa Daidai da Ra'ayinsa tun kafin ma yakai haka zama a rayuwa ballatana yanzu dayake jin kansa ashi wani ne.

Sai dai abu D'aya na sani zuwan Amarya nan tozarcin danake sha sai ya Ninka wanda nake sha abaya abu daya ne naake gudu wulakanci ina tsoro da firgicin Amaryan tazo tasan duka labarina tazo tana ganina a wulakance ta goraanta min Kamar yadda Shima yasha Fadi Fa'iza ba kyau ba Turanci komai nata Total zer0 ne. ammh a raina bana mai Bakinciki don zai kara aure ai yayi ma kokari da muka kwarari wad'anan shekaru bai kara ba,sai yanzu na kuma ji Dadi da matar zatayi nesa damu ko Bakomai kazantar da baka gani ba Tsabtace akasan chan raina kuma ina da kishi Domin ina son mijina so irin wanda Duk Macetagari zata nuna ma uban ya'yanta,duk da tarin Nakasun da auran mu ya kunsa, duk da ko shi din' bai taba sona ba.

sai dai bazan barsa yayi wani Tasiri a kaina ba tunda inda Son ke da muhalli baza'a martabasa ba, zan iya Rantsuwa ko Kaffara bazan yi baa Ya Ishaq baya sona karfin Biyayyar Baba ce take Rike da igiyar auranmu. 

 Naso na sauya Rigar Jikina kamar yadda yace sai dai kuma Tunda yace na bar shi nasan ko da na bisa Shashensa sai ya koreni shiyasa ban bata ma kaina Lokaci ba na Haura kan gadona naa jawo Ahmad jiki na,na Rumgume sa Abu D'aya ke sanyayamin Rai ya'ya na Domin duk duniya bayan Ishaq bani da kamarsu basa san iya adadin Lokacin Dana Dauka inaa kuka ba ammh nasan Har barci ya kwasheni kukana bai Tsaya ba.

Kiran Sallar Farko na  tashi kamar yadda ya zame min  Jiki Fa'iza bata barcin Rana sannan karfe Hudun Asuba take tashi sai kuma wani Dare.

Fita nayi naje Dakin yaran na Tashi Amir da Mustapha zasu bi Babansu masallaci Bayan sun tashi na fita zuwa Dakin Hafsatu na isketa ta tashi har ta Shiga Tiolet sai na Fice su Amir ta Tsaya akansu sukayi alwala Daidai Sanda Ishaq ya fito Daga bangaransa Sanye da Jallabiya baka da Carbi Kofar Dakin yaran ya Coge duk Fadan sa bai isa yayi ma Fa'iza Fadan rashin Tarbiya da kula da yaransa ba wannan in bai Gode mata ba ai bazai Zageta ba.

Amir ne ya karisa ga Baban yana Fadin"Oyoyo Daada sannu da zuwa.."

Yafada yana rumgumesa rike sa yayi yana Shafa kansa kafin yace"Jiya na dawo lokacin kun yi barci.."

Ina musty..?

Yafada yana kallonsa Fa'iza na kiciniyar saka mai wata riga bayan ta cire mai na barci sai faman mutsike ido yake yi alamun barcin bai sake sa ba.

Dariya yayi yana kallonsa kafin ya Bude Hannunsa yana Fadin"Oya come Here..!"

Da gudu yaron ya nufessa ya Fada jikinsa yana Fadin"Daada.."

Shafa kansa yake yana jin Farimciki acikin ransa Fa'iza ya kalla Dake tashin Anum da dan karfi yace"Kyaleta mana.."

Fa'iza ta Dago tana Fadin"Suna da Hadda yau."

Yana rike hannun su Amir yace"Ai da Sauran lokaci ke komai naki na Hanzari ne karfe Biyar din Asuban ne zasu tafi Haddar..?

Bada karfi yayi mganar ba saboda Haka ban ma jisa ba nadai san yayi mgana kuma nasan bai wuce Fada ne irin nasa Daya saba ba,  shiyasa har yaja su Amir suka fice ban kara mgana ba..

Suna Fitan nayi kokarin tashin Anum Saboda tayi sallah ta wartsake kafin su Dawo Daki na muka koma Tare nima na Dauro alwala mukayi sallah Tare da Anum muna idarwa Ahmad ya tashi na Daukesa naga ya bata pampers dinsa,sai na mike na Goyasa na shiga Kitchen bayan na gargadi Anum kada ta koma barci ta zauna tayi azkar din Safe wanda yaran duk sun Haddace..

Ruwan Zafi na fara sakawa saboda nayi ma Ahmad wanka kafin sauran yaran su Dawo Sai kuma na fara kokarin Fere Doya saboda na soya musu na Tafiya dashi makaranta sai ga Hafsah ta shigo Kitchen din da Hijabinta.

Fa'iza Hankalinta na wajen aiki bata san Hafsatun ta shigo ba sai da ta tabata sannan ta dago tana kallonta kafin tace"Kin fito Hafsah..?

Da yanayin mganarta Hafsah tace"Eh Ina kwana.."

Da dan daga Sauti Saboda Fa"izan ta jita sosai.

Ta amsa mata Cikin Sakewarta Hafsah tace"Bari na amshe ki."

Fa"iza tace"A"a barin min wanan aiki..Ga dai ruwa nan na saka in ya Tafasa ki juyo ki yima Ahmad da Anum wanka kafin su Amir su dawo."

Tafada cikin yanayin Raba mganarta Hafsah ta amsa mata da Toh,ba Dadewa ruwan ya Tafasa ta Dauko wani Karamin baho ta juyo ruwan ta kai Tiolet din Dakin Fa'iza da suna da Shower na wanka ya lalace kuma ya Ishaq yace da gan gane saboda haka bazai gyara ba.

Dawowa tayi ta karbi Ahmad ta je ta fara mai wanka ta shiryasa sannan tayi ma Anum nata wanka alokacin har su Amir sun Dawo masallaci suna Falo Tare da Ya Ishaq Sanda Hafsat ta fito Dauke da Ahmad daya fara Rigima ne Fa'iza ta fito Daga Kitchen din tana gaida Ishaq ya amsa mata bai ko kalleta ba Hankalinsa na wajen Amir Dake bashi Labarin abunda ya Faru a makarantasu jiya shi kuma Musty bai da Hayaniya yana Lafe jikin Uban..

Hafsah ma tabi ayarin yar'uwanta ta gaisheshi ya amsa yana Dubanta ganinta Dauke da Ahmad yasa yace"Ina zaki kaishi..?

Hafsah tace"Kuka yake yi zan kai shi ta bashi Nono ne."

Hannu ya mika mata yana Fadin"A kitchen din zaki kai mata shi..?

Wato salon ta jefa shi Cikin wani abu kin santa bata da kula."

Hafsah dai batace komai ba ta mikamai D'ansa ya Cafe shi yana Daga sa sama cikin Fara"a Hafsah bata damu ba ta karisa kitchen din Domin kama ma yayar nata aikin itama gobe zata koma Daman Hutun Midterm break Aka basu a makaranta yasa Goggo ta barta ta taho itama tana Karofi ne wajen Hajiya Indo da suke kira Goggon Karofi ita take rikonta tun bayan da ta karbota wajen mahaifiyarsu Ta madina.

Suna Kitchen din suna aiki Hafsah taji Sanda Anum ta fito ganin babanta yasa ta nufesa cikin murna tana Fadin"Daada yaushe ka dawo..?

Daman Anum akwai kirniya da Rashin jin mgana Yana ganinta itama ya Tarbeta yana Fadin"Anum dina jiya da Daddare na dawo kun yi barci."

Kai Tsaye tace mai ina Tsarabanta yace sai an juma in ya sake fita Hafsah ce ke Sauraran Hiransa da ya"yansa banda Fa'iza da baji take yi Sosai ba sannan Hankalinta na wajen Soya Doya bata ma san Abunda suke ciki ba.

Kafin bakwai na Safe tayi Fa'iza ta gama komai sai ta bar Hafsah a kitchen din tana karisawa,ni kuma sai naje na Shiryan yaran saboda suna da Hadda Tahfiz ne tun Safe sai shida suke Dawowa Allah ya taimake ni Ahmad na wajen Ya Ishaq ya shiga Dashi Shashensa.

Koda bakwai da Rabi tayi sun karya sun shirya Tsab Cikin kayan makarantarsu Ga Basket din kowanne an shiryamai da soyayyar doya da miyar kwai,Sai lemu da ruwa Fa'iza na kokarin Tura Hafsah ta leka tayi ma wani wani makotanci Haruna mgana mai Tuka adaidaita shi ke kai yaran makaramtar Hadda da Boko a wata Ya Ishaq na Biyansa Saboda abaya motace har da Direba ya Daukan musu tunda Anum ta taba koke motar Mama ta sa ya bama Jamal kaninsa motar tana chan gidanta Kofar soro in ya Dawo Hutu Daga Kano inda yake karatunsa na Engeering yake amfani da ita su kuma Ishaq ya Daukam ma yaran mai adaidaita a cewarsa Tunda bata iya Tattali ba shi ba asararrre bane sannan kuma yace Mota bata Dace da ni  ba,irin mu yawo acikin Adaidatan yafi Dacewa damu,ni Dayake ban Damu ba, ba fita take yi sosai ba Daga Gidan Mama sai gidan Anty Binta shima na da'n Rage zuwa tunda ba maraba suke da zuwana ba Karofi kuma sai dai in an yi Rasuwa muje Gabadaya ammh ni kad'ai Ya Ishaq cewa yake bai yarda da ni ba zanje ne na Had'u da yan'uwana azagesa shiyasa ban ma Damu da Fitan ba nima.

Ina shirin aika Hafsah ne sai ga Ya Ishaq din ya fito yace shi zai kai su,jin Haka yaran suka fara Murna sosai,Tare da Ahmad suka tafi har Lokacin bai koma barci ba shima ai yasam Ishaq saboda gaskiya in yana Gida yana bama yaransa Lokacinsa nice dai bani da wannan matsayin.

Har sun fita naa bisu Haraban gidan ina kwalama Amir kira ya juyo yana Fadin"Umma menene..?

Ina Sosa gashin idona nace"Kada ku manta ku karanta addu'ar fita Daga gida."

Da Karfi Anum ta fara karantawa Amir na Binta shi da mustpaha suna gamawa nabisu da mirmishi ina Daga musu Hannu Ishaq dai Tuni ya Shige mota yana Dauke da Ahmad irin wad'anan Hallayar na Fa'iza ba wani Burgesa suke yi ba,Sai dai kuma a kasan Ranta yasan Tarbiya ce mai kyau shiyasa wani lokacin baya mgana.

Ganin ya shiga motar bai bude get ba yasa na karisa na Budemai motarsa ta Fice Daga gidan sannan na maida na Rufe,abaya munq da megadi wani Dattijo,Tunda lokacin da  Yaya Ishaq yaga ina basa Abinci yace don me..?

Ai yana Biyansa duk wata ba wata mgana kawai sai ji nayi ya sallamesa Daganan kuma bai kara Daukan mana wani megadi ba yace Tunda Zan iya na yi Hidiman get din da kaina

Sai da suka tafi naje nayi wanka na Sauya kaya zuwa wata Doguwar Rigar Shadda Dinkin zamani kan na gama Shiryawa Hafsah ta gyara Falon ta share in da yaran suka bata sannan ta gyaro Dakin yaran suma ganin haka yasa nayi mata sannu da aiki ni sai na shiga  Shashen Ishaq na gyara duk da ba sosai yayi Datti ba na Cika shi da Turaran kamshin Daki sanin sa mai son kamshi ne.

Kafin ya Dawo na jera mai kayan  karinsa,na koma Falo muka karya ni da Hafsah muna yi muna Taba Hira duk da Hiran Daga Hafsah ne ita Fa'iza nata Eh ne ko A'a sai mganar da batayi Tsawo ba.

Har muka gama karyawan bai shigo ba,Hafsah tatafi tayi wanka ni kuma na kwashe komai nakai kitchen na Fara kimtsa wajen,Bayan na gama nayi wanke wanke,ina cikin goge gogen kitchen din naji Sallama atsakar Falon Sai na leko da Towel din gogogogen a Hannuna,Baki na washe ina fadin" BADARIYA.."

Cikin bayyana Murna ta ganin wacce aka Kira da Badariya na Tsaye da katuwar leda a Hannunta yar matashiya doguwa Fara Fuska kamar ta Ishaq sai dai ta fisa Haske saboda ita macece Autansu ce Badariya Kabir Karofi.

Karisowa tayi Cikin Falon Tana Fadin"Anty Fa'iza yunwa nake ji wlh..akwai sauran abun kari kuwa..?

Tafada tana wanchalar da gyalen Hannunta Lokaci Daya da ledan Data shigo da ita.

Bata ma saurari Fa'izan Dake faman mata gaisuwan yasu Mama ba

Ta Shiga kitchen din tana Dube Dube ta samu Doya a kula da Miyar Kwai ta Dauko ta Fito Tana Fadin"Anty Fa'iza adana gaisuwarki sai naci na koshi Tukunna."

Dariya nayi  mata bance komai ba na koma kitchen din na Cigaba da goge gogen da na fara ina mai jin Dadin zuwan Badariya din duk cikin ya"yan Mama Ita kadai ce ke sona sai Jamal shi kuma bai da alkibla yau ya min Mutumci gobe kuma akasasin sa shidai baka gane ina ya Dosa,Ammh yana zuwa gidan nan wajen su Amir sannan yana zuwa cin abinci ba wacce tafi Tsanata Daman Tun zamana wajen Mama irin Anty Binta batagwara ita da Ya Ishaq daman basu so zamana agidansu ba Sun gama Dora min karan Tsana wanda har yafi ma wanda Mama take min tun ina da karanci shekaru kafin ma aure ya shiga tsakani da ya Ishaq

Sai da nagama aikin na Sannan ta sake Fitowa Falon na iske su Tare da Hafsah wacce tayi Rashe Rashe kasan Cafet tana Bude kayan da Badariya ta shigo Dasu ita kuma Badariya na kan kujera ta cin Doyarta suna mgana da Hafsah.

Ina Shigowa Hafsah tace"Anty Fa'iza kinga ankon Bikin ya Ishaq.."

Jin Shuru yasa Badariya tace"Bafa ta jiki ba..Anty Fa'iza ga ankon Ya Ishaq..kin gani..?

Sai alokacin najisu nabi Kayan Dake Hannun Hafsah da kallo sai na kasa mgana Badariya da Hafsah suka kalleni  Cikin wani yanayi kafin Hafsah tace"Kilama bata san da ankon ba.."

Badariya tace"Anya..?Anty Binta ta Dauko fa..Ranar agabana da tazo gidan Mama ta Kira ya Ishaq din tace zata Daukan ma Anty Fa'iza ,Anum kuma zata Hadasu dasu Hibba ne.

Hafsah tace"To ba mamaki."

Badariya tace"Wannan da kike Dagawa naki D'aya nawa daya..Yanzu Daga wajen tela nake bai Dinka Less din ba.."

Hafsah ta zaro ido tana Fadin"Wai nawa..?

Badariya ta mata Dariya ai sai tatashi ta Daga Tsalle tana murna ta Rumgume Fa'iza Dake Tsaye tana kallonsu tana Mirmishi Cikin Fara"a tace"Kinga Anty Fa'iza Badariya ta Dinka mana..!"

Fa"iza ta karbi Atamfan tana gani kafin tace"Sun yi kyau.."

Hafsah ta isa ga Badariya ta Rumgumeta tana Fadin"Nagode sister..Allah ya bar zumumci."

Badariya tace"Ameen ammh bani Zaki ma Godiya ba Ya Ishaq ne shi ya siya mana.."

Hafsah bata wani ji mamaki ba,Saboda in yayi Niyya yana da Alheri sosai tana ta godiya tana Santin kayan.

Badariya tace"Za dai kizo bikin ko..?

Nima yanzu aBakin Ya Ishaq nake jin kinzo Daga kai yara makaranta wajen Mama ya biya."

Hafsah tace"Zan zo tunda weekend ne."

Badariya tace"in Goggon Korofin ta bar ki ba..Domin ita kanta ban Tabbatar da zata zo ba..Naji suna waya da Mama tana Fadan Ya Ishaq bai Fada musu zencen auran nasa ba"

Hafsah dai batace komai ba Badariya ce tacigaba da Fadin"To waya fadamawa..?

Daga shi sai Mama sai Anty Binta suke abinsu Amaryan ma suna waya da Anty Binta tunda ita ta Hada lefen.

Hafsah tace"To yaushe  ne ma Bikin..?

Badariya ta tabe baki Tana kallon Fa"iza dake zaune gefe tana kallonsu kafin tace"Anty Fa"iza ta san Lokacin Bikin..?

Hafsah tace"Anya..? Batamin mgana ba."

Badariya tace"Karshen wata ne sauran Sati uku."

Hafsah tace"Allah ya kaimu nan za"a kawo Amaryan..?

Badariya tace"A"a chan Abuja zata zauna..Ai itama yar Abujan ce,mahaifinta shugaban ya ishaq ne a wajen aiki,Itama ai ma'aikaciya ce tana aiki da wani kamfani ban dai san ko na menene ba nima

Haka naji Anty Binta na fada ma mama cikin Hirarsu."

Hafsah tayi shuru jikinta yayi sanyi Tana kallon yar'uwanta wani Tsausayinta ya kamata sai taji Badariya na Fadin"Ya Ishaq ya samu Cikar Burinsa Mace mai kyau Fara Doguwa mai kwalayen zamani ga Kudi da Nasaba..Allah yasa a wanye Lafiya."

Hafsah ta amsa mata da Ameen kawai Domin bata da tacewa,Fa'iza ce ta dan Daga Sautinta tana Fadin"Badariya ya mama..?

Badariya tace da karfi"Tana lafiya..Tana chan tare da D'anta na barsu na fito amso dinki nan sanan kuma yunwa ce ta koroni."

Mirmishi kawai nayi ban ce komai ba ni kowa yasanni  bani dayawan mgnaa Saboda yanayina

Sai Hirar ta koma Tsakanin Hafsah da Badariya da Daman kawaye ne suna Hirar Hajiya Fatima wacce suke kira da Hajiyar Dala tana chan kano tana auran wani Babba a soja.

Hafsah ke tambayan su Suwaiba sun san Bikin ya Ishaq din..?

Badariya ta tabe baki tace"Ke share su basa min mgana ko achart kuma suna da Layina..Naji dai mama na Fadin Hajiyar dalar bata nan ta Raka megidanta India Cheekup,Kinsan ta bata Damu da zumunci ba.

Hafsah tace"Haka naji Goggo na Korafi kinsan zuwanta na karshe kaca kaca suka Rabu da Goggon.."

Badariya ta tabe baki tace"Shiyasa sau Daya na taba zuwa gidanta.

Hafsah tace"Ni ai ban ma taba zuwa ba.Yaya Asiya da ta zauna awajenta in tanaa baki Labari sai kin sha mamakinta."

Badariya tace"Shiyasa tasu tazo daya da Mama fa."

Dariya kawai Hafsah tayi suna ma Hirar Fa'iza ta koma Dakinta tana gyarawa,Hankalinta na kan aikinta duk yadda Tunani ke mukurkusanna naki bashi muhalli,na gyara Dakin Tas sai dai abu daya ne Fa"iza bata iya gyarashi ba shirgi bata iya yadda Zata kakkanta ko'ina yayi kyau ba,Sai dai ta gyara ko'ina ta kuma ta maida shirgin waje D'aya.

Mata kala kala ne, kuma kowacce da yanayin yadda ta iya gyaran waje,Ita fa'iza haka Allah ya yi ta tana da Tsafta jiki da na zuciya sai dai bata san yadda zata gyara komai a bisa muhallinsa ba.

Tunani nake yi anjuma zan yi wanki kayan yaran hade da Uniform dinsu Tunda Anum ta lalata injimin wankin su na koma yi da kaina domin duk abunda yara suka Lalata Laifin a kai na Ishaq ke dorashi.

Kayan Ahmad masu Datti nake fitowa Dashi Sanda Hafsah ta shigo ta kawo min Ahmad,alokacin nasan ya Ishaq ya shigo gidan ganin na riga ta kai mai abun karinsa yasa na zauna ina Bashi Nono,ko kafin ya gama sha yayi barci naa koma na shimfidar dashi,na kwashe kayan Ahmad da na Anum data cire dasafe zuwa Dakin yaran na wuce Badariya da Hafsah a Falo suna Hira Dayake Tv Din dake falon yara sun Lalata kuma Ishaq bai Damu daya gyara ba.

Sai da na gama Hada kayan waje daya na kullesu cikin wani Dankwali Sannan na fito ta nufi Shashen Ishaq.

Afalo na sameshi zaune kan kujera mai zaman mutum Daya ya lafe ni ban ma san waya yake yi ba Saboda ba Karfin ji gareni baa.

Kayan daya gama kari dasu na kwashe  na kai Kitchen kuma ban baro kitchen din ba sai da na wankesu,koda ma fito ta iske Badariya zata tafi mukayi sallama Hafsah ta fita domin ta taka mata...Shashen megidam na koma naji ko akwai abunda yake so saboda karamin abu laifi ne a wajensa..Ina  Shiga Har Lokacin bai gama wayarsa Daga yanayin yadda yake mgana zaka san yana bama wayar Muhimmanci kayan Haushi Fa'iza bata ma jin me yake Fadi shi da Zeey tana mai shagwaban jiya Daga Tahowarsa har tayi kewarsa.

Ganin yadda Fa'iza tamai zaune agabansa ne yasa yace ma Zeey ta bashi Minti biyar sannan ya datse kiran..

Fa"iza ya kura ma ido yana kallonta hankalinta na ma kan Tv dake aiki afalon cikin Tashar Mbc3 cartoon suke yi Ahmad ya kunna ma D'azu da Safe kafin fitarsu.

Mirmishi takaici yayi kafin ya Kirani a Kaushashe kamar yadda ya Saba.


"FA'IZA..!"


Firgigit nayi na Dago ina kallonsa Lokaci daya ina amsawa da Na"am

Kallonta ya karayi yana Nazarina domin Idanuwanta sun kumbura sai kuma ya waske cikin yanayinsa yace"Kin tasani agaba ina waya wani abu ne..?

Dayake a sama yayi mganar na jisa sai nace da Sauri"Kayi hakuuri..Daman nazo naji ko kana Bukatar wani abu ne..?

Karamin Tsaki yaja kafin yace"In ma ina bukata ai zam miki mgana ko..?

Tashi kije abunki ban cika son kina yawan zama a inda nake ba Fa"iza Allah Nagani."

Tsam na mike zan fice dagaa Shashen nasa, lokaci daya kuma ina daga rigata Daga kasa saboda tsawon yamin yawa kallo ya Bini dashi To ai Daman yasan Tunda wuyan yayi mata Daidai Daga kasan Rigar sai ta bata mtsala.

Har zan fice ya Kira sunana da karfi na juyo ina amsawa da hannu yayi min alaman na Dawo da Hanzari na na Dawo na Duka agabansa sai da ya sha Iskarsa sannan ya Tashi ya shiga cikin Dakinsa minti kad'an ya fito Hannunsa Dauke da wani Hoto ya zauna Lokaci Daya yana mika min Hoton na sa ka Hannu biyu na karb'a Fuskata da mamaki da neman karin bayani.

Ya Dora kafa d'aya kan D'aya kafin ya kalleni yana Fadin"Duba ta da kyau ki gani Fa'iza.."

Sannan ki Fadamin ya kika ganta..?


Fa'iza tabi Hoton Dake hannunta da kallo Wata kyakyawan Hallita nagani kamar ita tayi kanta wajen kyau Doguwa mai Dogon Fuska da Hanci har Baka Farace tss mai ja ja ja,Sannan tana da lobawar Kumatu,Wato Dimple Gashinta Har gadon bayanta yake,ga Diri na Cikar ya mace duk da Abaya ne ajkinta Shape dinta ya bayyana sannan tana da Wushirya hakoranta data Bude sun bayyana Farare masu Tsari ga Kunshinta ja ne ya fito akan Fararan Hannayenta masu kyau da sheki Fa'iza tana ganin Ya Ishaq mai kyau ne sai dai dataga wannan sai taga ai shi bamai kyau bane.

Ganin yadda ta bada Zuciyarta wajen kallon Hoton yasa ya Karbe Hoton batare data shirya ba na Dago ina kallonsa ya Daga Hoton yana Fadin"Ya kika ganta..?

Fa'iza cikin yanayin mganarta tace"Tana da kyau..!"

Ishaq yace"Eh ban ji me kikace ba..?

Fa'iza tace"Tana..tana da kyau sosai.."

Ishaq yayi wani irin Dariya kafin yace"Bayan kyau fa..?

Baki Fahimci ta mallaki komai na Kyau da Zatin ya' mace ba..?

Fa'iza tayi shuru batayi mgana ba Ishaq ya kalli Hoton na wani Lokaci kafin yace"Kinsan wacece wannan..?

Fa'iza ta girgiza kai kafin Ishaq ya Cigaba da Fadin"Matar da zan aura ce..Zabi na ce Fa'iza Zainab lawal Bako kenan..Mace ce mai kyau Kamar yadda kika ganni  Mai tarin ilimin Zamani Tana da Degree Biyu sannan tana Shirin komawa Phd dinta,Iyayanta masu Kudi ne da Nasaba ta mallaki Duka Burina na nan duniya nan da Sati uku zata zama matata zata cika min gurbin mafarkina da kika Tarwartsa Fa'iza.

Shiyasa na yanke shawaran zaki Dakatar da Haihuwa hakanan ki bar mai wuri tazo ta fara Haifamin kyawawan ya'yan da nike Mafarki.Yanzu ne zan san ni Ishaq nayi aure,abaya ina jin kunyar nuna ki a matsayin Matata ammh ayanzu banda Haufin Duniya taga Zeey a matsayin Matata ina Rokon ki Fa'iza nayi miki komai a Rayuwar ki yi Free d'ina ki barni naji D'adin Rayuwata ni da Matar data dace dani."

Ya karishe fada ya na kallon Fa'iza da kanta ke kasa ta kasa gane ina mganganunsa ya Dosa Cikin wani yanayi na Dago ina Fadin"Bangane ba..?

Kai Tsaye yace"Zamu jingine AURAN mu ne Fa'iza..Wlh in nace ashekara Takwas din da mukayi da aure ban cutu da auranki ba nayi karya kiyi ma kanki adalci kiyi min adalci nima"

Gaskiya ya Fada Tabbas gaskiya ya Fada Fa'iza ta fada acikin aranta.

Cikin wani karfin gwiwa na kallesa kafin nace"Jingina kamar ya..?

Kai Tsaye yace"Jingina ina nufin ba Saduwar aure tsskanimu a matsayin miji da mata  ba wata mu'alama ta aure ba Raba kwana Tsakaninki da Zeey..Sai dai zan cigaba da kula Dake saboda Darajan ya'yan dake tsakanin mu Kada ki manta ba Mu'alaman miji da mata Tsakanina Dake..Kawai zan kula Dake ne Saboda ya'yana kawai"

Har ya gama mganansa kallonsa nake yi Hawaye sun gama wanke min Fuskata ga mamakinsa sai kawai yaga nayi Mirmishi,mirmishin da zai iya rantsuwa bai taba ganin Fa'iza tayi irin sa ba.

Cikin wata irin muryan da baisan ina  da ita ba yaji nace


"Na Amince.."


Farinciki ya kamasa ya kalleni yana Fadin"Nagode Fa'iza ko bakomai kin yi sakayyah ga Alherin Baba agareki."

Ko kara Sauraransa ban yi ba na mike Zan fice ya Kira sunana na  waigo Cikin Kaushinsa yace"I ya ni da ke..Ban yarda wani yaji wannan mganar ba kina jina..?

Kai na gyadamai ina sharan Hawaye, muryata na rawa nace"Insha Allahu ba wanda zai ji sai indan kai kaso hakan"

Daga haka na fice da Sauri Saura kadan Rigar jikina ta Hardeni na Fadi bai Damu ba Murna yake zai samu Salama Shekara Takwas yana cikin kurkuku sai yanzu yaji sa kamar yana Shakan iskar yanci.

Har na karisa Dakina kuka nakeyi  bana ko ganin gabana sosai,kan gadona na Fad'a gefen Ahmad ina wani gunjin kuka Dake fitowa Daga kasan Raina  Hasbunallahu  wani'imal wakeel shin ni na Tsara ma kaina  Rayuwata a haka..?

Allah ne yayi ni baka mummuna Allah ne ya so ya ganni afasalin daya ijiyeni meyasa ya Ishaq bazai gane haka ba..?

Yau ni Ya Ishaq ke mganar zai jingine auranmu Saboda wata.? Na tabbata ba Domin mganar Baba ba da tuni aurane da Ishaq ya kare to ai yanzu ma ba Maraba..?

Zai jingine ne kawai saboda mganar Baba ba Domin Ra'ayinsa ba,sai kuma domin kuma ya'yansa Ba laifi na  bane domin na fito a mummuna ba, kuma ba Laifina bane domin na fito daga jikin Bebiya ba, ba Laifina  bane domin na kasance an Haifeni  da Laluran rashin ji sosai da yanayin mgana taba, ba Laifi na bane Allah ne ya Tsara min Rayuwata Daki Daki.

Sannan ba Laifi na  bane domin ban zama mai ilimin zamani ba Domin duk yadda ka kai ga Tsara rayuwarka To KANA NAKA ne Allah na nashi kuma na Allah shine daidai kuma Tsari mai kyau.

Ina cikin wannan halin bansan sanda na fara jin tunanin yadda yanayin rayuwata ya fara dawomin acikin kaina ba,tundaga farko har zuwa yau din da Ishaq yace zai jingine aure na saboda wata.

Nafara da Tunano yadda yanayin Rayuwata ta fara ne cikin Farinciki Tun mahaifinmu ALHAJI SIDI KAROFI na raye.



*ASSALAMU ALAIKUM*

*KAYA SUN SAKE SAUKA*.

*INGANTATUN SAIWOWI DA SASSAKE NE DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZA DA SU*.

*ABIN BIRGEWA BA SAU DAYA AKE AMFANI DA SHI BA. SANNAN BASU DA BAURI MASU KIDIMARWA*.

*KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR KO KUWA KE DA KANKI ZAKI YI GYARA?*

*INA SAKE YIN ALBISHIR DIN GARIN DAKA MAI KYAU DAN CHADI, SHA DA MADARA KO NONO DA KUMA TSUMIN GAMGAM*.

*INA DA TABBACIN INGANCINSU*.

*TUNTU'BI WANNAN LAMBAR DOMIN KARIN BAYANI*

*08032773332*.

*SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*

🙏.






*Janafty**KANA NAKA..!*


*Wattpad:JamilaUmar315*

*Mallakar:Janafty*

*Arewabook:Jamilaumarjanafty*

*Book 1*



*Madallah da ku masoyana naji Dad'i na kuma yaba muku da yadda kuka karb'i Labarin nan fiye da Zato na..Nagode kwarai Allah ya had'amu cikin Ladan gabadaya,Madallah da masoyan gaskiya da Amana,nace Madallah da y'an Amanar Janafty*


*ASSALAMU ALAIKUM*

*KAYA SUN SAKE SAUKA*.

*INGANTATTUN SAIWOWI DA SASSAKE NE DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZA DA SU*.

*ABIN BIRGEWA BA SAU DAYA AKE AMFANI DA SHI BA*.

*KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR KO KUWA KE DA KANKI ZAKI YI GYARA?*

*INA SAKE YIN ALBISHIR DIN GARIN DAKA MAI KYAU DAN CHADI, SHA DA MADARA KO NONO DA KUMA TSUMIN GAMGAM*.

*GADALIN MATA AKWAI*.

*INA DA TABBACIN INGANCINSU*.

*SANNAN WACCE TAKE SON A DAFA MATA KAZAR, ZA'A DAFA*.

*TUARAREN WUTA NA ASALIN CHADI AKWIA SU AVAILABLE, SAI KIN GWADA ZAKI BADA LABARINSU*

*TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU DOMIN KARIN BAYANI*

*08032773332*.

*NATION WIDE DELIVERY*.

*SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*

🙏.


         *🅿️03*


Asalin kakanmu wanda ya haifi iyayan mu maza ni da Yaya ishaq bakatsine ne wanda ya fito daga Tsatson katsinawan Karofi.

Karofi kamar Anguwa ce ko wata alkarya dake cikin Garin karamar hukumar Dutsenmah ta Jahar katsina.

Tunda ga Dutsenmah,Katsina Kankara,malumfashi bakori,mahuta da Sauran kananan hukumomin dake zagaye da Garin katsina ba wanda bai san Waye Alhaji Sulaiman Karofi ba,Saboda tun lokacin yana Raye shekaru sama Hamsin da wani abu da suka gabata an yi Attijirin mai kudi,Domin kaf yankin nan ba inda ake siyan Siminti sai a wajensa manyan manyan Store yake kama haya ana cikamai su da Siminti tun yana matashinsa da wannan sana'ar ya fara kuma alhamdulillah ita ta Daukakesa har kuma Allah ya Dauki Rayuwarsa bai sauya sana'a ba.

A yadda Babanmu ya bamu labari Lokacin yana raye Saboda muma ko da mukazo Lokacin Allah ya karbi Ran Alhaji Sulaiman sai dai mun sha Labarin kirkinsa da Dattakonsa bakin Babanmu.

Ya sanar damu cewa Alhaji Sulaiman Kamfani kamfani na Siminti Mota mota ke shigowa Karofi Domin saukemai Siminti kuma ba'a sati duk sai ya kare bayan manyan yan kasuwa yana saida ma marasa karfi da masu siyan daidai misali sannan karin Daukakarsa baya tsawwalla kudi i ya abunda Allah yasa ya samu sai ya sanya musu albarka.

Mutum ne akace nagari kamili mai sanin Darajan dan adam da Dattako,da kowa yake yabonsa Daga uwa har uba duka haifaffun karofi ne,Kenan ba shi da wani garin da ya wuce mai Karofi alokacin.

Yana da matar auransa Daya Hajiya Suwaiba(Hajiyar karofi) ita ta Haifamai manyan ya'yansa guda Uku Hajiya Fatima ce Babba(Hajiyar Dala) sai Hajiya Aisha(Goggon karofi)

Sai karamin su Alhaji Kabiru(Baban katsina)

Sai Autan su Alhaji Sidi( Babanmu)

Wanda rabonsa ne yasa aure ya kullu Tsakanin Mahaifiyarsa Asiya da Alhaji Sulaiman Karofi.

Alokacin baya in aka auro mace daga wani waje ta shigo inda bata san kowa ba,to akan samu a makotan da aka kawo ki kina samu yar D'aki da zata rika shigowa tana tayaki zama da yan aikece aikece to haka ne ya faru da Hajiya Suwaiba ita din yar cikin garin Dutsemah ce kuma auran Soyayya ne ya kulla Tsakanin su mai karfi kafin ta kai su ga aure.

Yadda na samu Labari Hajiya tun tana matashiyarta macece mai kirki da Sanin ya kamata sai dai akan mijinta bata da kauda kai tana son shi Shiyasa take bala'in kishinsa.

Tun sanda aka kawota garin gidan da Alhaji Sulaiman ya gina gefen katangar gidan su Asiya ne, wanda garun gidan Alhaji Sulaiman shi ne garin gidan su Asiya talaakawa ne Futuk,mahaifinta mallan Haruna ya rasu bayan doguwar jinyar da yayi a baya masarin bishiya ne an ce Tun wani Sare wata bishiya da yayi shikenan bai kara lafiya ba har ya rasu Daga Asiya sai mahaifiyarta Atika suke Fafutukar Rayuwa to lokacin da aka kawo Hajiya Suwaiba Asiya ta kan shiga ta taimaka mata da yan aike ce aike ce tunda daman Asiya bata da kiywuya Lokaci kadan suka saba da Hajiya tun balle data fahimci suna cikin Halin matsi ita ke taimaka musu da abinci suturu har kuma ta saka Alhaji Sulaiman shima ya tallafa musu.

Cikin lokaci kadan Asiya ta zama yar Dakin Hajiya Suwaiba duk wanda yasanta yasanta da Asiya,Suna tare ta yi goyon cikin Fatima ta haifeta kowa yaga Asiya sai yaba da kokarinta da Himmanta Hajiya kuwa har ga Allah ta ke tare da Asiya bata taba jin wani abu aranta game da ita ba..

Ana haka har ta sake haihuwan Aisha,lokacin ne Alhaji Sulaiman yazo mata da mganar da ta kusa girgizata wai zai auri Asiya saboda yayi jihadi sannan ta zama abokiyar zamanta na Har Abada.

Ance a lokacin Hajiya Suwaiba tayi tashin Hankali har sai da ta koma gida Ma'ana tayi yaji kuma hakan baisan an fasa ba sai dai ta Dawo ta iske ya gyara ma Asiya dakin dake kusa da nata har an yi biki Asiya ta tare,Ance sillar wannan gabar daga wannan auran ne Hajiya ta kullaci Asiya da Mahaifiyarta Atika akan sun yi auran cin Amana ita kuwa Asiya bata mgana sai kuka ba Laifinta ba ne,Ita batace tana son Alhaji ba shi yace yana sonta batare da sun sani ba ya je ya gabatar da kansa wajen Dangin babanta su kuma sun ga Alhaji ga kudi ga Dattako nan da nan suka basa da Atika tayi mgana suka Rufeta da fada dole tayi shuru.

Sanadin wannan auran ne komai ya fara ko nace shine sillar komai bazan ce Hajiyar karofi ta fara assasan wutar kiyayyar ba Tunda kafin ta Mutu ta yi Tuba tuba irin na Taubatul nasuha.

Zan iya cewa Tsantsan Rabo ne kawai ya kawo mahaifin mu wannan Duniyan,Asalin sunansa ba Sidi ba ne Sidik ne Asiya ce ke kiransa da Sidi har ya bisa zuwa girmansa.

Kusan Lokaci daya Asiya da Hajiya suka yi goyan yaransu ita tana goyan Babanmu ita kuma Hajiya na goyan Baban katsina.

Hajiya ita ta ke zaunar da ya'yanta tana fada musu auran cin Amana mahaifinsu yayi da Asiya har aka samu Sidi saboda haka shi ba Dan'uwan su ba ne bare ne tunda auran cin Amana ne to ba d'an Sunna ba ne shege ne, mgana fa har ta fita Domin ba inda Hajiya bata yada mgana gidan biki ko suna har yakai ga Asiya ko Atika suka daina fita Saboda kananun mganganu.

Har sai da Alhaji Sulaiman yaji ya tsawarta mata ya kuma ja kunnenta da sai ya iya Rabuwa da ita Saboda haka ance ta sha kuka Ranar Asiya tasha zagi da gorin ita ta zama gatan taa ammh Daga karshe ta saka mata da Auran mijinta.

Adalilin irin wada'nan kalaman na bakin Hajiya suka yi tasiri a zuciyar Babbar yarta Hajiya Fatima(Hajiyar Dala) wanda har mahaifin mu ya koma ga Allah bata kaunace sa ba Duk da kuwa an ce Kafin Asiya ta bar gidan Duniya sai da ta rika rokon Hajiya gafara ammh taki yafe mata sai daga bayan ta jima ita da Atika a kushewarsu sannan Hajiyar Karofi ta gane kuskuranta ta gyara alokacin kuma komai ya kure mata.

Babbar Bakincikim Hajiya ganin da tayi Sidi da Kabiru sun taso kan su daya sannan komai Alhaji Sulaiman zai yi musu tare ne,ita kuma bata so har ko yaushe a shege take kallon Sidi Tunda auran cin Amana ne..azaba da ukuba ba wanda Sidi bai shata a hannun Hajiya ba ko kasheshi Hajiya zatayi Asiya ko Tarin ta bamai ji a Tsakar gida tana da hakuri da  kawaici sannan ga Ladabi da Biyayya ko da ta auri Alhaji bata daina yi ma Hajiya bauta ba sai dai bata gani Laifinta daya meyasa ta auran mata miji..?

Babanmu ya fada mana yana d'an Shekara goma sha uku a duniya Mahaifiyarsa Asiya ta rasu da tsohom ciki ta fito daga makewayi jirin Hawan jini ya fardar da ita kwananta Daya asibiti tace ga garin ku nan da Farko Mutuwar ta daki Hajiya ammh Daga baya sai ta saketa.

An yi tashe tashen hankula Har sai da iyaye suka shiga ciki kan zaman babbanmu a wajen Hajiya kememe ko tace bazata rika dan shege d'an cin Amana ba sai Atika aka kai mashi ta rikesa Gefe D'aya Alhaji Sulaiman na kula dashi sai dai duk yadda Hajiya taso ta raba Kabiru da Sidi ta kasa wannan jinin na yawo ajikinsu..sannan Fatima ce kadai ta ke bayanta Aisha kuma babu ruwanta bata Cika Daukan mganarta ba..

Babanmu ya d'anda'na gudarsa a Hannun Hajiya tun da duka bai Rufe shekara biyu a hannun Atika ba,ta rasu sakamakon amai da guduwa shi kuma Alhaji Sulaiman yace hajiya bata isa ba Sidi zai zauna agidan nan tunda shima gidan ubansa ne kamar sauran ya'yanta wannan dalilin ya kawo babban baraka tsakanin ma'auratan,In yana gidan Sidi zai zauna cikin salama ammh da zarar ya fita sai abunda Allah yayi ukuba ba irin wacce bai gani ba,Hajiya ta taba Cire masa riga ta zane shi da wayar radio mai karfi kawai saboda sun fita shi da Kabir suka dawo jikinsu duk kasa shine ta rufesa da dukan meyasa yake jan Kabiru ai ba Daya suke ba shi da'n Shege ne Kabiru kuma yaron sunna ne da sahihin aure ya samar dashi Ance sanadin dukan har sai da Sidi ya suma saboda azaba wannan dalilin yasa Alhaji Sulaiman ya saki Hajiya saki daya sakin daya girgizata ta Dade bata gidan ta kuma kwashe ya'yanta duka ta tafi dasu shi kuma sai ya kyaleta iyayenta sun shiga ciki ammh ba'a samu daidaito ba Saboda Hajiya ta riga ta kara hawa dokin naki kan bazata rike Sidi ba shi kuma Alhaji Sulaima yace ba inda zai kai shi in bazata rikesa ba to ta barshi kusan shekara daya Alhaji sulaiman shi ya Dinga wahala da Sadi komai shi ke yi mai Hajiya kuma ta Dauka Alhaji Sulaiman zai sauko yazo ya bata Hakuri sai taga ba haka ba ne ga su kabiru suna ta Damunta da Babansu shi kuma tunda haka ta faru bai taba Takawa wajenta ba ai yace ba shi yace tatafi da ya'ya ba ita taga dama Saboda haka ba zai bisu ba in har ya'yansa ne zasu nemesa.

Ganin Ba riba ne yasa da Umarnin Iyayanta Hajiya ta dawo gidan Alhaji Sulaiman ammh an yi musi tsakani da Sidi ba ruwanta da shi,Shi dai yana bata girmanta domin kamar uwa ya Dauketa ita kuwa ta tsani ma ta Bude ido ta gansa don dai bata da yarda zatayi.

Cikin wannan Halin Rayuwa ta rika ganganrawa Alhaji sulaiman bai tara dukiya ya rika siyan kaddarori ba sai dai ya gina ya'yansa ya basu kyakyawan ilimin zamani,Matan daga Sakandiri yake aurar da su,Ammh dukkansu sai da ya kai su Hajji suka sauke Farali Hajiya fatima Soja ta aura dan kano ne chan aka kaita,ammh daga baya an sauya mai wajen aiki ya koma Kudu,Kafin zuwa yanzu sun zauna garuruwa da dama kafin ya yi ta samun karin girma har ya kawo matsayin da ya kai a yanzu.

Sai Hajiya Aisha da ita kuma d'an karofi ta aura kuma kamar aboki yake wajen Alhaji Sulaiman sai dai tun alokacin ba'annin juna ba ne..

Alhaji sulaiman bai bar gidan duniya ba sai da ya gina ya'yansa sannan ya aurar da su bayan mata ma har da mazan har kuma ya bar duniya bai ga Nadamar Hajiya suwaiba(karofi),kan Asiya da zuru'ar ta ba,har alokacin bata ganin duk wani daya shafi zuru'ar Asiya da Atika da Daraja saboda abunda ya faru.

Daga kabiru har Sidi sai da suka fara samun Takardan Education kafin su Dora degree din su,Baba kabiru fanni Biology ya karanta,shi kuma Babanmu sai ya karanta Fanni Kasuwanci Business admistration.

Bayan kamallah karatun su dukkansu sun samu aiki Kabiru ya fara koyarwa a wata makaranta gwamnati dake Karofi shi kuma Sidi sai ya samu aiki a wani ma'aikatan littafai dake katsina chan ya tattara ma ya koma Saboda gidan baya mai dadin zama Hajiya ko zai gaisheta sau dubu bazata amsa ba sai tayi kamar bata gansa ba,Sai dai yana bata girmanta a matsayinta na uwa bai taba riketa aransa ba kuma kullun haka Alhaji Sulaiman ke gaya masa Hajiya uwa ce garesa komai zatayi mai kada ya Daukesa a wani abu ya Dauka ajizanci ne na D'an adam.

Shiyasa bai taba kallonta da wani abu ba,Balle da suka taso kamar uwa daya uba daya shi da Kabiru in ba mutun bai sani ba zai dauka uwar su daya ubansu daya sai an fada maka ne zaka san ba Uwa dayace ta haifesu ba ammh suna Diban kama Dukkan su Dogayen katsinawa ne marasa Lalaci Sannan shi kabiru yafi Sidi haske Saboda Hajiya farace,Sakamakon ita Asiya baka ce shiyasa sai hasken sa ya zama mai Duhuwa..

Yana shigowa karofi duk bayan Sati hudu kuma duk alherin da zai yi ma Dangin Mahaifiyarsa,zai yi ma Hajiya sai dai bata karba yana sauke ledan zata Dauka ta kone daga baya sai ta Daina konawa Tunda Alhaji Sulaiman ya ja mata kunnen tana albuzuranci da Dukiya da kaya watarana zanin Daurawa sai ya gagareta sai ta tsorata ta Daina Konawa sai dai ta Sadakar da su.

Kabiru ya riga Sidi aure saboda shi Daga baya shima katsinan ya koma da koyarwa a wata babbar sakandiri,Achan ya hadu da Saudatu ita din buzuwar yamai ce Kasuwanci ke shigo da su Katsina ta Jibiya anan suka Hadu Allah ya hada kauna Tsakaninsu har ta kai su ga aure Saudatu(Mama kofar soro) farace Doguwa kyakyawa kin kowa kin wanda ya rasa ga gashinta har gadon Baya Hajiya tayi alfahari da wannan auran ganin kamar Kabiru ya kece sa'a cikin maza zai auri buzuwa,Barin ma Hajiya Aisha da itace kamar makwafin Hajiyar tafi kowa Fi'ili da karairata Ita Hajiya Fatima babu ruwanta ita datake ma kusa.

Har chan yamai akaje aka nema ma Kabiru auran Saudatu,suka kuma Tare a gidan su dake karofi inda Alhaji Sulaiman ya gina musu barayi guda biyu,Na kabiru da Sidi shima sai da Hajiya ta rika yada mganar ai shi ba Dan gida ba ne bashi da gadon Alhaji shi dai bai kulata ba sai dai yayi mata addu'an shiriya tunda ganin Shekaru sun fara ja Hajiya bata Sauya ba,bai tunanin zata iya sauyawa sai dai shiriyan Allah kawai.

Tun zaman Saudatu karofi taga gata wajen Hajiya kamar ta lasheta barin ma har zuwa ake yi ganinta Saboda kyanta da gashinta,sai taji dadin haka Domin daman tana bakincikin Sidi na aikin kamfani Kabiru kuma ya zama malamin makaranta in tayi mai korafin haka dariya yakan yi kafin yace"Hajiya kenan ko wani bawa da kika gani yana tafe da kaddaransa arzikinsa da aurensa da Haihuwarsa da Mutuwarsa'"

In yace mata haka sai dai ta kallesa ta Harareshi kafin tayi kyafci Sai tace"Ai daman haka zakace Yaron nan Sidi ya gama dakai kai da Aisha Fati ce kadai tasan ciwo na"

Sun riga sun Saba da Halinta shiyasa suke Lallabata su rabu lafiya,yana katsina sai sati sati yake zuwa ganin gida Tun auran su daman Hajiya ta gama karanta ma Saudatu kaf Waye Sidi da auran cin amanan da Asiya tayi da  mijinta,Sannan ta fadamata Sidi ba dan sunna ba ne An haifesa da cin Amana ne,shi yasa ta tsane shi duk da ta Lura Kabiru na bala'in ji da kaunar Sidi shiyasa ranar da ya fara kawo mata shi kadahan kadahan ta karbesu sai faman tab'e baki take yi Sidi na lura da ita bai yi mamaki ba Daman yasan za'a rina shiyasa baya fatan in yayi aure ya kawo matarsa wannan gidan yasan ta zama Nama.

Sai da Kabiru da Saudatu suka Haifi Diyar su ta farko Fatima suna kiran ta Binta sunan Hajiyar Dala taci.

Ashekaran Sidi yayi aure auran da Hajiya taji dadinsa tunda ba auran kece sa'a ba ne,Sidi yar'uwansa ya aura da kakansa na wurin uwa da kuma kakan TAMADINA na wajen Uwa itama sun hada iyaye daya,su biyu kadai mahaifinsu ya haifa kafin ya rasu Tamadina da Usman kuma ba uwarsu daya ba kowanne da Tsatson sa Ita ta Madina mahaifiyarta haifaffiyar karofi ce ita kuma mahaifiyar Usman yar karaye ne dake kano Lokacin data gama Takaba ta roki alfarman Tafiya da Usman garinsu aka bata Tun yana da Shekaru goma aduniya ya bar Karofi.

Hafsatu(Tamadina) shine ainihin sunanta,kuma ta samo sunan ne tun tana karama tun da bakinta ya bude duk wanda yayi mata mgana sai tace madina zata tafi shikenan Hafsatu ya bace sai dai tamadina,sannan Tamadina Bebiya ce kuma ba Ciwo bane da shi aka Haifeta mganar ta baya fita Sosai sannan bata ji sosai,ahaka taso cikin rashin gata tunda kaf zuru'ar su Asiya ba wani mai arziki sai Buga buga kawai.

Tamadina baka ce kuma gajera shiyasa duk wanda yasan Tamadina ya ganni ni Fa'iza zai san kammaninta da suffanta duka na Dauko sakamakon su ya Asiya sun Dauko Tsawon babbanmu da Hasken Fatarsa ni kuma hatta bakin Tamadina ni na Dauko shi har da gadon Rashin ji, na duk daga wajenta na gaje shi.

Ba auran Tausayi Sidi yayi da tamadina ba shi ya ganta yaji yana sonta kuma manya suka shiga ciki,Musamman Alhaji Sulaiman da ya shige ma Sidi gaba,har akayi auran da farko yaso ya tafi da ita Katsina ne sai Alhaji Sulaiman ya hana yace ya barta agida kamar yadda Dan'uwansa yayi shi kuma bazai iya yi mai gaddama ba sai ya bar Tamadina a gidan karkashin Hajiyar Karofi da Saudatu(Mama kofar soro)

Ba iya ni na wahala da Mama ba Mahaifiyata ma taci wuyarta ita da Hajiya suka maidata kamar jaka gashi Tana da lalura sai su yi ta zaginta bataji,Gashi ba daman tayi mgana sai Hajiya ta hantareta tana fadin"Ta fi chan Dangin maciya Amana..Dangin bakake munana kawai masu bakincikin munafunci"

Kalaman tun tamadina bata gane su har ta fara ganesu ta kuma Haddace su,In Sidi na nan ne take samun salama sannan tana jin dadin zama da Uban mijinta Alhaji Sulaiman.

Da kuma Hajiya Aisha(Goggon karofi),Sai Kabiru wanda shima ba ruwan shi ammh Hajiyar Dala sai abunda ta manta cin mutumci in tazo gidan nan Tamadina sai tayi kuka Taruwa suke yi su yi ta cin mata Mutumci wani Lokacin batama jinsu har Jin dadi take yi da Allah yasa bebiyace ita da ta kunshi bakinciki.

Bayan Haihuwar Saudatu in da ta Haifi ISHAQ Bayan Haihuwar Saudatu,Tamadina ta haifi yarta mace Aka saka mata suna Asiya sunan mahaifiyar Sidi taci,Shekara shida tsakaninsu an yi sunanta ba jimawa Alhaji Sulaiman ya kwanta jinya ciwon sugar da bai tashi ba Gabadaya duk abunda ya tara sai da ya kare wajen neman mgani daga karshe bai tashi ba ya koma ga Allah.

Rasuwar sa itace silar Wargajewar komai an yi ta rigima wajen raban gado,Domin Hajiya ta yi tsaye tace Sidi bai da gadon Alhaji Saboda shi din d'an cin Amana ne ganin rigiman tayi girma sidi ya tattara matarsa suka koma katsina ya kama Hayar Daki biyu da Tsarkar gida sai kitchen,Ya kuma ce ya yafe gadon har Abada aka rasa rai ma aka Hakura ballatana Duniya tun faruwar lamarin yasan Hajiya bazata taba kaunarsa ba kawai sai ya Hakura wanda ya hada ya raba,Tundaga Lokacin sai ya Dade bai je karofi ba Sai dai suna mgana ta waya da Kabiru da Aisha tunda su kam basu yar da Zumunci ba..

Ko shekara basu shafe a katsina ba ya samu aiki a wani kamfanin Sarrafa leda dake malunfashi sun basa matsayi mai girma da gidan zama ya tattara tamadina suka koma malumfashi da zama

Acikin shekarun da suka gabata abubuwa dadama sun faru ciki har da Sauyin rayuwar da kowa ya samu Sannan da Nadamar Hajiya,Rana daya ta rika kuka tana a kira mata Sidi ta nemi afuwarsa dayake ita kadai ce agidan yanzu Kabiru shima ya Tattara sun koma cikin katsina da zama Tunda ya zama principal bayan yaje ya karo karatunsa

Sidi yayi matukar mamakin nadamar Hajiya daman bai taba riketa ba ya riketa yana share mata hawaye tare da Fadin bai taba riketa acikin Ransa ba kowa yaji dadin wannan al'amarin ban da Hajiyar Dala domin har Abada bazata kaunaci Sidi da zuru'arsa ba.

Hakama Saudatu(Mama kofar soro) itama ta tsani Sidi da zuru"arsa ganin tafi  TaMadina komai na bangaran kyau da Nasaba ammh a bangaran jin dadin gidan miji,Sai dai su goga domin bata fita komai na inganta Rayuwa ba, Sidi na yima Iyalansa komai sun gado Halin Dattako wajen mahaifin su Alhaji Sulaiman


*****


Shekaru goma da suka gabata.


A cikin wad'anan shekarun goman,komai ya faru kuma ya kare,mun fara samun ingantattaciyar Rayuwa a malunfashi,Bayan haihuwar Ya Asiya sai Yaya mariya sai ni Fa'iza da aka Haifeni da Laluran Raunin ji sai autarmu dataci sunan Tamadina Hafsatu ita an haifeta ma ne Babanmu na cikin Tsananin jinya shima Ciwon sugar yayi gado wajen mahaifin su Alhaji Sulaiman shima kamar shi din sai da komai ya kare tas wajen neman mgani kafin rasuwarsa sai da aka yanke mai kafa Da Hannu bazan taba mantawa ba ina Aji hudu na matakin primary a asibitin gwammatin garin Malunfashi Babanmu ya rasu a hannun Alhaji Kabiru(Baban katsina) da Tamadina Mutuwar da Sanadinta ta gama gigita Rayuwarmu gabadaya sanadinta muka san halin Rayuwa muka san maraici da rashin gata.

Da gidan da muke ciki kadai muka Tsira shima da aka saida shi duk a bashi ya tafi tunda jinya yayi kusan shekara uku sai da komai ya kare aka koma cin bashi duk da Baban katsina na Tallafa mana shi da Hajiyar Karofi.

Mutuwar Babanmu shine Silar Barowarmu Malumfashi muka koma Karofi daga Lokacin kuma komai na Cigabaman mu ya tsaya,Tamadina tana gama Takaba gidan su ta koma,mu kuma ta barmu gaban Hajiya da Farko da nan aka barmu da mun samu Rayuwa mai inganci saboda Hajiya tana kaunarmu kwatankwacin kaunar da take yi ma Sauran jokokinta.

Ammh sai hakan bai samu ba Baban katsina ya tara su Hajiyar Dala yace zasu rabamu a Tsakaninsu Saboda Rage ma Hajiya Dawainiya,Shi farko Yaya Asiya yace zai dauka Ita kuma Goggon Karofi  tace zata Dauki Yaya mariya ta hadata cikin ya'yanta ta rike Tsakani ga Allah.

Shi kuma Baban Katsina sai yace Hajiyar Dala ta Dauke ni Tunda Hajiya ta maida ma Tamadina Hafsatu tunda tana karama ne Lokacin sosai tace ta riketa tukunna har sai ta yi wayo sosai.

Ai Hajiyar Dala agaban kowa da kowa ta Daka tsalle tace bazata Daukeni ba takai gidanta ban ko ji sosai ta Daukan ma kanta Lalura ita bazata iya ba har Hajiyar karofi sai da tayi mata mgana tace bazata Dauki kowa ba,Sai aka kyaleta Baban katsina da ya fara fada Hajiya ta hanasa tace ita zata rikeni shi ya tafi da Ya Asiyan kawai ita zata rikeni Hajiyar Dala najin haka sai tace sai dai ta Dauki Yaya Asiya tunda ita Lafiyarta kalau Baban katsina yaso ya hana sai Hajiya tace abata,wannan shine Dalilin Rarrabuwarmu Yaya Asiya a kano ta tashi Ta samu tayi karatunta har Sakandiri ita kuma Yaya mariya ta taso Hannun Goggon karofi itama tayo karatunta ita kam har matakin N.C.E,Sai Hafsatu wanda Baban katsina yace in ta kara girma shi zai Dauketa Tunda ni Hajiyar karofi zata rikeni ammh duka Dawaniyata Na hannunsu.

Naji dadin barina a karofi da akayi Saboda Tamadina da Hafsatu sai kuma Yaya Mariya dake kusa Damu ko da yaushe suna gidan Hajiya tare damu Ni dai Dakyar Hajiyar Karofi ta bari na gama nakai aji Biyar na matakin primary domin na rubuta jarabawar fita ba  sai fada take yi Me zan ji a makaranta ko me zan gane Tunda ba ji nake yi sosai ba,Baban Katsina ya so nayi karatu ammh sai yaga bayan Hajiya Nima bana so Saboda ina shan Dariya da Wulakanci a makaranta wajen Sa'annina Saboda yanayin mganata da raunin ji na sannan kuma ni bakace bani da kyau shiyasa sai karatun ya ficemin Daga raina na,na saka araina sai mai gata ko mara Lalura yake zama mai ilimi bani da na ke nakasashiya ba.

Ammh Hajiyar karofi bata bari nayi Sakaci da na addina ba,Ta sakani Islamiya da Hadda da Makarantar allo ta Safe da Dare,Shi kam ban yi sakaci ba Kuma dayake karatun Qur'ani ne da Liffafan addini ina ganewa sannan Hajiya bata hanani ba shima na Bokon bazata iya juran dawowa da nike da kuka bane Saboda har waka ake yi min bebiya mamarta ma Bebiya sai nake jin guilt din abun acikin raina da yasa naji na Tsani bokon gabadaya sai Hajiyar Karofi ta maramin baya domin gatan Duniya ba wanda bata nuna min ba.

Rikon Hafsa ya koma Hannun Goggon Karofi Saboda Tamadina tayi aure a Dutsenmah ta auri wani magini ne matan sa Biyu itace ta uku,Sai Baban katsina yaso ya karbi Hafsah Mama kofar soro ta daka tsalle tace bazata rike zuru'ar Tamadina ba dangin Maciya Amana da Bebaye ba Hajiya tayi kuka kamar ranta zai fita tasan duk abunda ta Shuka ne take gani ta zaunar da Mama da Hajiyar Dala ta gaya musu komai ta kuma yi kokarin cire musu wannan Tunanin ammh batayi nasara ba Dole ta zuba musu ido ganin abun na neman ya lalace Sai Goggon Karofi ta raba Gardama ta Dauketa kawai ni da Farko ban san matsala ko matsin Rayuwa ba, sai da  sanadin ciwon Hajiya ya wujijjiga Rayuwata. sannan na kara Fahimtar bamu da gata sannan maraici ya gama Lullube rayuwarmu tun a baya na Fad'a muku ita kanta Tamadina ba su da wani gata balle mu yi Tunanin samun gatan ta barayinta gatanmu kenan Dangin Babanmu su kuma k'alilan din su ke son mu da Kaunarmu.

Bazan taba mantawa da wata rana na Dawo daga allon Safe ina shiga Dakin Hajiya na ganta kwance ba yadda take ni na Ruga na je na kira Goggon Karofi tazo ta gani,aka kwashi Hajiya sai asibiti ashe Faduwa tayi ta samu shanyewar barin jiki,ta koma sai dai a kwantar a tayas,ganin haka yasa Goggon Karofi suka yi shawara da Baban katsina ta maida Hajiya da ni gidanta tana kula Damu gabadayamu,Ko wata uku Hajiya batayi tana jnya ba,jikinta ya kara Rikicewa ga nauyi yayi ma Goggo yawa Mijinta ma'aikacin gwamnati ne ammh kuma akwai Dawainiya shi kuma Baban katsina Lokacin ya na matsayin Daractan Ilimi ne na Katsina gabadaya ya samu Rufin asiri sosai.

Shiyasa Saboda ya rage mata nauyi yace zai daukeni alokacin cikin Fargaba ta kallesa kafin tace"Abban Ishaq kana ganin ba matsala..?

Ajiyar rai ya sauke tabbas akwai matsala yasan Halin Saudatu ammh kuma ai gidansa ne kuma shi ke auranta Dole Fa'iza ta zauna karkashin kulawarsa shiyasa cikin karfin Hali yace"Kada ki damu ba wata matsala ta had'a kayanta da zarar na tashi da ita zan wuce"

Nayi kuka kamar zan mutu da naji Goggo tace na shirya nabi Baban Katsina gidansa Yaya mariya ne da Goggo suka rika Lallashina ni nasan gidan bamai kaunata,Daga maman har Anty Binta da Ya Ishaq wanda in dai suka yi Hutun Makaranta yakan Biyo Baban katsina ya gaida Hajiya wlh baya kallona bazan taba mantawa da Ranar da ya fara ganina agidan Hajiyar karofi ba kallon Sama da kasa yayi min kafin ya kauda kai ya yamutsa Fuska ya kalli Hajiya yana Fadin"Hajiya wacece wannan mummunar bakar yarinyar..?

Hajiya cikin yar Dariya tace"Baka gane ta ba ko..?

Fa'iza ce yar wajen Marigayi Babanka Sidi"

Ina kallo ya kara kallona ya yamutsa Fuska kamar yaga kashi kafin yace"Hajiya bata da kyau Sannan ban taba ganin baki irin bakinta ba kamar ta shafa shuni"

Yafad'a cikin Sigar Tozarci ita ko Hajiya Dariya tayi kafin tace"Kuma kai nayi ma kamu ba"

Agaba na ya Tofar da yawu kafin yace"Allah ya tsareni Hajiya ai ni Matata bata zo duniya ba tukunnah"

Alokacin Hajiya bata Dauka wani abu ba ammh ni da na taso cikin wannan yanayin nasan tozarci ne nayi kuka Sosai.

Ina kuka ina komai Baban katsina ya sakani a mota yana bani baki sai Katsina Hajiyar karofi kuma bata mgana Sosai jikinta yayi zafi,sai dai bin mutane da ido kawai sai hawaye bata mgana.

Tana kallona zan tafi na rike hannunta ta gyadamin kai ina kuka tana Hawaye itama a mota ma kukan na Dinga sharba sai da Baban katsina ya jawoni jikinsa yana Lallahina Fadi yake yi"Kwantar da Hankalinki Fa'iza zan kula dake kwantacin yadda sidi zai kula da dake in yana raye"

Lokacin ba jinsa nayi ba ammh nasan Lallashina yake yi.

Sai dare muka isa katsina anguwar Kofar soro Makeken gidan da Baban katsina ya gina Tun ranar da na saka kafata acikin gidan nan ban kara farinciki ba har fita ta zuwa gidan Ishaq babu abunda ya Sauya.

Nasan dai Baba na gaba ina Binsa a baya da jakar kayana ina kalle kalle har Babban Falon gidan in da mama ke zaune ita da Yaya Ishaq sai Anty Binta da tayi aure ammh acikin garin katsina Sai Jamal wanda ke bi ma Yaya ishaq sai Karamar su Badariya.

Dukkansu Baban suka zuba ma Ido da farko Mama ta fara mai lale bata ganni  ba sai da ya juya yana kallona kafin yace"Saudatu ga Fa'iza ta Dawo Hannuna da zama har na aurar da ita ki kaita Dakin yaran nan ta yi wanka ta Huta"

Ai ranar naga tashin Hankali agabanmu Mama ta dinga Bala'i tana fadin bazan zauna mata agida ba Dangin munana maciya amana Dangin kurame me zatayi dani ban da akara mata wahala Fada dai sosai tana Fad'a Baban katsina na Fad'a har yakai ga Baba ya kusa saka ma Mama Hannu sai da su Ya Ishaq suka Shiga Tsakani ita kuma tayi shewa tace da ya sa ke ya mareta wlh bazan zauna mata agida ba.

Ranar a falo na kwana rakub'e ina rawan sanyi da tsoro,Duk naji mganganun Mama Saboda da karfi take  mganarta Tunda Baba ya shige Ciki itama ta shige a Fusace ban kara ganin kowa ba Badariya ce tazo wajena Anty Binta tajata suka tafi gidanta saboda Kada ta rabe ni Jamal kuma daman ba wani babba ba ne alokacin tashi yayi ya shige Dakinsa ko ajikinsa Ya Ishaq ne ya taso yazo gabana yana min kallon Tsana da kaskanci kafin yace"Dama kece Kurman nan..?

Ko Bebiya ma zan ce..?

Ban ji sa ba shiyasa na kura masa ido kauda kai yayi ya wuce yana fadin"Abubuwan sun yi miki yawa..ga baki ga Muni ga maraici ga Ki kurma"

Daga haka shima ya Tsallake ashe wasa farin girki wani kukan Rahma ne Duk yadda Baban katsina yaso ya inganta Rayuwata ya kasa Domin Mama tafi karfinsa bashi da yarda zai yi da ita,Tunda nazo gidan ta sallami Duka yan aikinta a shekaruna sha Uku a duniya na bautu da aikin Wahala nau'i Dabam Dabam,in na tashi Tun asuba bana komawa sai wani Daran abinci kuma sai an rage nake samun naci Tun ban iya girki ba har na iya aiki kuwa ba wanda ban iya ba In Baba yayi mgana sai tace zata koreni.

Nayi wahala da Mama da ya'yanta sannan nayi wahala da Anty Binta da Ya'yanta Ya Ishaq ko ta gabansa na Gifta sai ya Hantare ni da Mummuna,baka,Tun bana Fahimtarsa har na fara gane hantara ce da Tsana shi da Anty Binta sun ce basa son kallon Fuskata baki na da muni na yayi yawa.

Baba yaso ya maidani makaranta Mama tace zai yi asaran kudin sa ne Tunda baji nake yi ba Sai yace zai maidani islamiya Dakyar ta amince ina zuwa ta Lasar zuwa shidda na yammah ammh sai nagama duka aikina sannan zan fita,anan na samu na Sauke alqur'ani daman kum na d'an yi nisa a karofi,sannan nayi karatun Sauran Littafan Addini da wannan zan iya cewa na Tsira a zamana a gidan Baban katsina.







*Janafty**KANA NAKA..!*


*Wattpad:JamilaUmar315*

*Mallakar:Janafty*

*Arewabook:Jamilaumarjanafty*

*Book 1*


_*Barka da Zagayowar Ranar Haihuwa HAFSAT MUSTAPHA HAFNAN(SAHIBATU),Madallake da ke,Allah ya karo shekaru masu albarka Happy birthday*_


*Assalamualaikum! Phydoors* *collection (home of all you need)tazo muku da kayan gyaran girki masu inganci da Gina jiki da faranta Ran Mai gida harda Ma yaranmu domin inganta girkin uwargida Kai harma da amarya tazo muku da egusi,* *crayfish ,manja ogbono dadai sauransu Zaku iya tuntubar ta wannan nomber 08062181151 ko Kuma shafinmu na yanar gizo https://instagram.com/phydoors_collection?igshid=MzNlNGNkZWQ4Mg==Muna aikawa ko Wani gari da iKon Allah,ko gwada kayanmu da iKon Allah sai Kun dawo* 🥰🤗




       *🅿️04*


Sai kuma girken girken zamani da na gargajiya da na koya a iya zamana agidan mama shima ba wai ita ta koyamin ba,Ni na koya da kaina Saboda ina da karambani Mama bata taba Damuwa dani ba tsakani na da ita sai Harara da hantara,tana ganina a matsayin wata aba mara gata da galishu wuya ce da wahala yasa tun ban iya komai ba har na koya.

Na yarda ina da nakasun rashin ji ammh bani da nakasun wani abun Hallita ajikina ina da rai na da lafiyata to zan yin komai,Na iya wasu girken girken a tashar arewa24 na shirin su Akushi da Rufi wani Lokacin Tibin ita kad'ai afalo tayi ta babatu in nagama aikina sai na Lallabo nazo na zauna Duk da bana jin yadda suke koyar da girken girken ina bin yanayin yadda suke Hada komai ina ganewa.

Sannan da kuma Anty Mamah babbar Diyar mijin  Anty Binta ce mahaifiyarta ta rasu ne dalilin da yasa ma ya auri Anty Binta kenan.

Tana aure acikin asibitin Kashi wato Othorpedic na katsina mijinta Likita ne tana da Yan biyu wato Twins,Mama na yawan Tura ni gidanta Saboda reno Yaran nata duka mazane Hassan da Husaini masu Rigima ne Anty Mahma ba kamar Anty Binta take ba,bata da mugunta  sai dai akwai saka aiki,Kuma tana da kyauta sannan bata kyamatata ko tayi min fada, in naje gidanta kamar jaka har gwara ma gidan mama ina Hutawa sai dai ita bambamcin su bana girki da kaina ita da kanta take shiga kitchen tayi abunta ammh nakan shiga na taimaka mata da yanke yanke da miko miko to da haka nake zura ido ina Fahimtar wasu abubuwan nasan bani da gatan da zan yi karatu ko ina dashi ina jin tsoro zuwa makaranta saboda kada akusheni ko ayi ma Nakasuna Dariya shiyasa na kan kasa ido da raunannun kunnuwana ina duba wasu abubuwan da jin wasu abubuwan iya abunda zan iya ji na kuma d'auka.

Sannan agidan Anty Binta ma na koya su Snaks saboda Diyar Anty Binta ta farko mai suna Halisa zamu iya zama tsaran juna tunda Anty binta tayi aure tana da kananun shekaru alokacin to ita ke sana'ar yin Snaks in naje gidan nakan kasa idanuwana ina lura da abubuwan da take yi a hakan na nake daukan wasu abubuwan.

Da yake ita Halisa tana da bambamci da su ba kasafai take nuna kyama gareni ba sai dai bata shigemin sau tari nakan taya ta aikin Snaks din ta in an kawo mata dayake sana'arta ne tayi suna tunda tana amfani da Social media alokacin.

Tun ina da shekaru goma sha Hudu a duniya jikina ya gogu da aiki babu aikin da zai gagareni komai yawansa agidan Mama tun karfe Hudu nake tashi Daga barci naje kitchen na kintsa Sannan na Dora abun kari sai naje na tada Badariya bayan na saka mata Heater na wanka Saboda zuwa makaranta Domin dokar da Mama ta kwafanin kafin bakwai na Safe na gama komai kada ta fito bata iske abinci a saman dining ba,ko kuma taji kafafunta na taka Datti acikin Falonta Shiyasa ina yin abun kari wani Lokacin ina Share sharen dakuna hatta Dakin Jamal ni nake gyaramai in suka tafi makaramta Saukin ta ma shi bai cika mgana ba barshi da waya a Hannunsa irin su ba kasafai ake gane inda suka dosa ba.

Ya ishaq kuma baya gida sai an yi Hutu yake zuwa yana ABU Zaria inda yake Masters di'nsa nima abakin Anty Binta naji sunan karatun nasa har na iya rikewa,Hatta da kayan Jamal da na Badariya da na Mama ni nake wankewa ammh Baba bai sani ba Saboda yasan duk wata baya fashin bada kudin mai wanki da guga Tunda Mama ta sameni take soke yan kud'ade'nta,in wankin ya taru tun safe in naje baya na fara sai yammah watarana ma bana ko samin zuwa islamiya,Washegari kuma Baba na fita zan dasa guga har sai bayana ya kage ba ci ba sha sai na gama in kuma nace zan tashi ko sallah in yi sai Mama ta kai min duka tana Fadin"Me kika sani a karatun sallar..?Ni fa jin baban su kawai nake in yana Fadin kina da ilimin addini  ke da kike Bebiya gaki ba kyau ba fasalin y'a mace ai bautar da ta dace da irin ku kenan.."

In ta fadi haka bana damuwa sai naga gaskiya ta fada domin na fahimci in baka da kyau ko Asali da gata ko kana da wani nakasun Hallita baka da wani amfani Domin wad'anda suka fi kusanci dakai sune suka fi kowa kyamatarka to inaga na waje wad'anda basu san ka ba, mu'alama ce zata hadaku..?

Ina tuna Lokacin muna Malumfashi Iyayena sun san ina da Lalura ammh ko sau daya basu taba nuna gazawar su ba sun min dukkan gata a malumfashi makarantan da aka kaini ina gane karatu tunda ana yimin yadda zan gane sannan bamai kyamatata Saboda ina da gata alokacin ammh daga Lokacin da gata na ya kare sai nima nake fama da guilt din shiga cikin Mutane ina ganin ban kai ko wani matsayi ba sannan na aminta da mganar Mama iri iren mata irina Bautace ta Dace damu..

Shiyasa duk wahalan da nike sha bana Damuwa ina ganin ahakan ma ni kila nafi wasu ma ire irena,Baba duk baya sanin wasu abubuwan tun da in ya fita tun Safe sai Dare,in kuma ya Dawo yayi sallah yaci abinci zai kirani falo yayi  ta kokarin na bayyana mai abunda nake bukata ko nake so ammh bana iya mgana Saboda Mama ina bala'in jin tsoronta kamar wata mala'ikar Mutuwa.

Baban katsina irin mazan nan ne marasa Bibiyan al'umuran gidansu shiyasa Mama ta samu dama tana Damawarta,Komai na Cefane Mama yake bamawa,Duk watan Duniya ita kuma sai ta samu nata aciki Mama tasan kan kasuwanci,Tana saida dikkakun kayan mata da maza anan ake dinka mata tana aika ma yan'uwanta dake yamai suna Siyar mata kuma har anan tana samun ciniki sosai tana harka da manyan mata bayan dikakku har Tamfofi da Lesuna tana saidawa da takalma Shiyasa take da tarin kawaye da Mutanen arziki da ke shiga suna Fita agidan,Shiyasa ko Sutura ita Baba ke bama kudin ko na Mutanen karofi ne kuma baya Bibiya,Shiyasa sai wanda taga dama ta bawa,ba kuma wanda ya isa yayi mgana duk sallah har da su Yaya Asiya Baban katsina ke yi ma Dinki adadin yadda yayi ma Badariya dani ammh ni ko Sabo daya Mama bata bani na saka sai tace Mace irina da kwance ta dace ni kuma sai mganarta ta zaunamin kayan alfarma masu kyau sai ajikin kyawawan mata wad'anda basu da wani nakasu Mata kuma irina da kwance muka Dace yawancin kayan yaran kawayen Mama nake sakawa Domin na badariya bazai min ba Na girmeta sosai alokacin,Su Yaya Asiya kuwa Kala dai'dai take jifan su dashi Yaya mariya bata da matsala ita da Hafsatu Goggo macece mai Tsayawa akanta ita da iyalanta Yaya Asiya kuma tace duk mugunta Hajiyar Dala tana barinta da Suturu Saboda ita yar gayu ce sannan mijinta Soja ne ya'yanta fes suke itama haka saboda haka Itama Yaya Asiya badai a ganta da kama mara kyau ba.

Ni dai ko da yaushe cikin Tsumma da Ragga In Baba ya gani yayi mgana Mama ta lawayance zance ni kuma bana iya karyatata agabansa,bazan taba mantawa da wata sallah ba,Sallah da na fara yinta a gidan Baban katsina Lokacin na kwashe wajen wata Tara a katsina,kuma tunda nazo ko Karofi kafata bata kara takawa ba Ga Hajiya na raina in Baba zai tafi gaisheta sai naji kamar na bisa,tunda duk karshen wata yake zuwa wani Lokacin shi da Mama suke zuwa wani lokacin shi kadai da Direba ko shi da Jamal.

Hajiya na rai na ita da su Yaya Asiya musamman Hasfatu kewar Tamadina kuwa har na cire sa araina tunda ba samun ganinta zan yi ba Tun bayan dawowata Ko mutum daya Daga karofi bai leko mu ba na dai ga Hajiyar Dala da suka taba zuwa Bikin Dangin mijinta ta sauka anan kawaye ne ita da Mama sai muguntar su tazo daya sai dai ita tafi mama ji da kai da nuna ita din watace.

Sallar azumi ne Dama da azumi duk na Rame na kara lalacewa,Ni bansan gayu ba, bansan komai mai kyau ba ni na dauka abu mai kyau a wajen mata masu kyau ake samun sa,Wani Riga da Sikat na saka cikin kwancen kayan ya'yan kawayen Da mama ke bani ne wuyan zamemin yake haka ma Sikat din yayi min yawa sai da na saka Tsumma na Taresa ajikina Hijabi ne kadai Sabo Shima Anty Mahma ce ta dinkamin domin jiya gidanta na wuni na tayata soyan Nama da aikin cinci Sai Dare ita da mijinta suka maidoni gida ita ta na da kyauta in nayi mata wahala tana min alheri takalmin kafata na Roba ne shima din Na jamal ne da ya daina amfani da shi na Dauka

 Da farko Mama bata so aje dani Sallar idi ba,Sai Baba yace dani za'a tafi Ya Ishaq ya dawo agida yayi azuminsa Shi na lura kamar baya ma san kallo na shiyasa ban cika giftawa ta gabansa ba.

Lokacin da na fito Kofar gida Baba ya ganni sai da yaji kwallah ta cikamai ido,Ya kalli Badariya ta kure adaka ita da Mama,Jamal da Ya ishaq sun ci Fararan Shaddodi sai Faman sheke suke ni kuma bazar bazar kamar mahaukaciya wata yar aikin ma tafini kyan gani ni kuwa bakina kamar zai Tsage Saboda murna zan fita masallaci naga jama'a Tun kafin Baba yayi mgana Mama ta rigasa da fadin"Ke Fa'iza meyasa kika saka wadanan kayan..? Ina naki irin na Badariya..?

Sai na kasa mgana Saboda ni dai bansan da wani kaya ba,ba'a bani ba ganin Baba ya saussauto yana kallonta yasa ta kara karya murya tana Fadim"Bansan meke damun Yarinyar nan  ba Abban Ishaq ko da yaushe bata da aiki sai saka Tsumman kaya nama ce ta hada su in zaka Karofi ka tafi da su arabama mabukata"

Ban yi mamakin kalaman Mama ba Domin tun zuwana gidan ba Dadewa,Ta daina Fada da Baba akaina sai ta koma aiki da Kissa shima shawaran wata kanwartace daga Yamai hure ita tace mata in tana so taci Ribar Rayuwa to ta daina tada Hankali ta yi amfani da kiss,kuma Tabbas kissanta tana Tasiri wajen Baba don nan take ya kalleni kafin yace"Haba Fa'iza ya zaki saka wadanan kaya..? Baki ga sauran yan'uwanki ba ne.?maza je ki sauya kaya mu tafi kada mu makara'"

Da Sauri Mama tace"Zamu bata Lokaci Alhaji muje in mun dawo sai ta sauya"

Sanin Halinsa na rashin bincike kan al'umura yasa tace haka,Haka muka tafi su kamar zara cikin wata ni kuma kamar yar aikin su Shikenan ko da muka Dawo Baba yayi baki yana falon waje har Dare bai kara bi ta kaina ba,Sai da Washegarin Sallah da kwana Biyu mukaje Karofi ranar dai Mama ta bani Sabon kaya na saka ta kuma ja kunnena in taji wata mgana sai na Raina kaina ni ko araina nace wazan gayamawa.?bata san ina da zurfin ciki ba ba tun yau ba,bakomai ake jinsa bakina ba.

Duk da Sabon kayane ammh da na sanya kamar wata Dussa komai ba Tsari ni kaina nasan ba kyakyawa bace ban mallaki komai na mata masu sa'a da gata ba,Kusan daman Hausawa kan ce in kana da kyau ka kara da wanka to ni bani da kyau din sannan ban iya wankan ba ballatana na kara dashi,Wani Lokacin sai Dare nake samun Damar yin wankan Tunda Dakin da nake ciki akwai karamin Tiolet to iya wankan ne ko shi ba don kyau nake yi ba Komai bazar bazar ne bansan iyakarsa ba.

Da mukaje karofi na hadu da su Ya Asiya har sai da sukace har baki na kara na rame sun yi tambayan Duniyan nan kan wani irin rayuwa nake yi agidan Baban katsina naki ce musu komai sai dai in kallesu ina mirmishi naji dadin ganinsu haka barin ma Hafsatu da ta zama kamar ba ita ba ta kara wayau da girma.

Ina jin su a tsakaninsu suna tattauna yadda Rayuwa ta jefa su a inda suke ni dai bana ce musu komai nadai san na Tambayesu tamadina suka fadamin tana Lafiya Yaya mariya na zuwa Dubata ita da Goggon Karofi sukace In Baba ya barni gobe sai muje na ganta.

Ganin Goggon Korofi yasa Mama batayi mgana ba,Baba kuma ya amince washegari chan muka wuni sai yammah muka dawo ita kanta Tamadina ta na cikin wahala gida cike da yara,wahalar tayi mata yawa sai dai ba yadda zatayi ne kwanan mu biyu muka koma Katsina,Na koma da Tausayin Hajiyar Karofi ganin jikinta duk ya kara rikicewa yanzu ma dayan barin shima ya Daina aiki Goggon Karofi da ya'yanta suna matukar kokari kan Hajiya.

Haka rayuwata ta cigaba da tafiya a gidan Baban katsina duk da irin azaban da nike sha achan ban taba jin na gaza ba sai ma nake ganin Sun yi min komai tunda zan ci na sha na kuma samu wajen barci Baba na jin Takaicin rashin Karatu na ko da yaushe naje gaishe shi da Safe sai ya kalleni yace min"Fa'iza kin k'i makaranta ko..?

Baki san ilimin zamani ginshiki ne ga rayuwar ya'mace ba..?

Ni kuma bana iya mgana sai dai na Dukar da kaina cikin Tausasawarsa yake cigaba da Fadin"Da kin Daure Fa'iza ai kina jin mgana zaki gane komai sannan zan yi ma malaman ku bayani kamar yadda nayi ma malamanki na islamiya bayanin Laluran ki"

Ina Dagowa muka Hada ido da Mama ta Sakar min harara sai jikina ya fara rawa cikin yanayin mgana ta nace"Baba shi na addinin ba Ilimi ba ne..?

Sannan shi ba Ginshiki ba ne ga rayuwar mu ba..?

Baba ya jinjina mganata kafin yace"Ginshiki ne Fa'iza babban ginshiki ba kuwa..Sai dai ka hada duka fufukan guda biyu sai ka samu na zaman duniya da Lahira"

Alokacin sai nace ma Baba"Baba ka barni haka..na islamiyan kadai ya isheni"

Zai matsamin sai Mama ta taresa tana nuna mai Tunda ban so to ya kyaleni,Shi kuma bai da Zafi sai ya Rabu dani ammh ko da yaushe kalamansa akaina na alheri ne har ya bar duniya ko kallona yayi sai yace"Fa'iza Allah yayi miki albarka In sha Allahi bazaki Taggyara ba..Ina ji ajikina kina da wata baiwar da Sanadinta zaki Daukaka watarana"

In naji haka sai nayi Dariya araina Domin bana hango ma kaina hakan

Na amince Baban Katsina ya karbo ni Hannun Goggo karofi ne domin ya inganta Rayuwa ta,sai dai bashi da Mafita ne Mama ta fi karfinsa ammh har yau bazan manta kokarinsa akaina ba.

Shi ya fadama malaman islamiyan da nake zuwa yanayina suke bani kyakyawan horo ko an gama karatu gabadaya sai an kara min bita ni kadai,Bani da wata kawa shiyasa ni kadai nake zama iyakata da kowa Mirmishi ko Sannu nasan ana mgamata ammh da yake bana ma ji Sosai ban cika Damuwa da su ba.

A farkon zuwa na gidan Mama cikin kasuwar katsina take zuwa siyayyarta ammh sai Kawarta Hajiya Barira irin masu son kudin nan ne ita ta bata shawaran ta rika zuwa kano kwantin kwari tana saro kaya alokacin Mama sai tace"Kai Barira ya yi nisa ni kinsan ban san wahala"

Hajiya barira ta rika nuna mata yanayin komai tare da fadin nachan sun fi sauki sannan zata hadata da yan kasuwar chan tunda itama tana siyayya achan har sai da Maama ta amince bazan manta ba na zo kawo ma Hajiya Barira abinci na juya naji tana ce ma Mama"ko wannan bakar yarinyar kika tara sai kuje tare ta rika Daukan miki kaya"

Mama ta kalleta kafin tace"Ko Hajiya barira"?

Tace to zauna Daman meye amfanin irin su in ba aikin wahala ba.

Da wannan shawaran Mama ta zauna tana fadama Baba ya amince tunda shi ba mutum ne mai Takura ga iyalansa ba.kuma da tace dani zata bai yi gaddama ba domin nuna mai tayi ina kokari zata nuna min komai Domin tana Tunanin nan gaba ko ban yi karatu ba zan yi kasuwanci to ai Daman haka take fadamai ko na wahalan da nake yi ne,Girki ma Baba yace nayi kankanta Mama tayi Karaf tace gwara na koya Saboda gaba gidan wani zani Daganan Baba bai kara mgana ba.

 Daman tun anan ni nake kaimata Dinki chan batagwara kusa da gidan Anty binta,in ba'a gama ba sai na zauna an gama Wani Lokaci anan nake wuni buhu ne shake da kaya zam Dauko akai zuwa bakin Titi na samu Daidaita sannan in na Dawo na Hau ware ma masu kayan nasu,wad'anda za'a tafi da su yamai kuma duk ni ke shirya su Mama na gefe tana lissafin komai ban isa nace nagaji ba.

Ranar da muka fara zuwa kano sai da na raina kaina Wuni guda acikin kasuwa kuma bata Dauki dan dako ba ni ke daukan mata kaya akai kamar mahaukaciya ga yunwa ga kishi Takalmi a Hannu hijabi a hannu Wlh ko abinci bata siyamin ba Da muka Dawo sai da nayi rashin Lafiya Saboda na Jigata matuka alokacin Mama fada ta Dinga min akan na fara zama mai son jiki to in zam mike tun wuri gwara na mike Bani da wani amfani in ba Bauta ba.

Ni ba kyau ba,Ba ilimi ba,Ba ji ba,ba komai na inganci rayuwa ba,bai kamata na rika nuna gazawata ba tabbas gaskiya ta fada ba ni da wani gata a Duniya Bautar dai da ta Fada shine ya fi dacewa da mata marasa galihu ire irena

zuwa Lokacin da na shafe shekaru Shidda Cif a wajen Baban katsina bazan iya fadin irin bautar da nayi ba abu daya na sani ni Fa'iza ban sauya ba Sai dai na kara girma ammh ba Domin na sauya Daga yadda nake ba Ina nan a  mai raunannan ji,Mara gata baka Mummuna mara sa'an rayuwa in ji ya Ishaq in ya ganni yakan ce Bai taba ganin mace mara sa'a ba irina komai Total zero ne a bangarena ba wani abun so ko sha'awa tare dani nima nasan haka ko badariya dake tasowa mai kyau ce sannan yar gayu kuma yar gata ni kuwa ban ma san me ake kira da gayun ba,Ni dai kawai nayi wanka na suturta jikina mganar gyaran jiki da Tsaftan jiki ban san shi ba Ba kuma wanda ya ke zaunar dani ya koyamin Ko kitso sai ni nagaji da kaina na tsefe shi kitso kuma sai in Mama taga dama zata bani kudi naje,ayi min.

Zuwa Lokacin rayuwa ta Daga,Sosai ba kamar baya ba,kawayen Mama da suka sani tun abaya in suka gani sai like sai suka rika ce ma Mama Daman wannan mummunar dangin mijin naki na nan baki aurar da ita ba.?

Mama kan basu amsa da cewa wazai kwashi Baki da muni da bebanci sannan uwa uba ba ilimi sai su yi ta Dariya suna cema Mama shikenan ta samu yar aiki to ai daman ba marabata da mai aiki maraban mu daya in da Daukoni akayi da sunan aiki za'a  rika biyana albashi,Shine kawai bambamcina da mai aiki acikin wannan gidan.

Su Yaya Asiya duk sun yi aure ita da Yaya Mariya Ya Asiya acikin garin kano tayi aure wani malamin makaranta ne yana da mata da yara,Mai karamin karfi ita kuma Yaya Mariya A karofi tayi aurenta wani dan kasuwa ta aura mai rufin asiri.

Kusan tare akayi Bikin su sai dai na Ya Asiya aka fara yi ,Duka naje bikin su ammh na Ya Asiya sai da Goggon Karofi ta kira Baba ta mai mgana domin tasan Halin Mama munje kano mun yi kwanaki Tunda Bikin tare da manyan ya'yan Hajiyar Dala babansu ya Hada, da Asiya harta duka kudin siyayyan kayan Daki tare ya bada ammh Mama ta zuga Hajiyar Dala akan su ya'yanta suna da gata Asiya kuma ayi mata na Daidai da ita Daga karshe ma ita taci kudin domin duka Dawaniyar Yaya Asiya Baban katsina yayi mata shi,Duk ciki ita kadai ta auri mai karamin karfi gidan falo daya ne sai Dakuma nata da na uwargidan Ba Shakka Baba yayi mata kokari sosai,Bangaran Yaya mariya Goggo da Mijinta sukayi komai ita gidanta ita kadai wannan bikin ne har Tamadina tazo,na Yaya Asiya ne bata je ba, in naga yadda Rayuwar Mahaifiyarmu ta koma sai na kara tabbatarwa lalle bamu da gata gatanmu ya fadi tun Lokacin Rasuwar Baba.

 Da ace Hajiyar Karofi na Da lafiyanta da kila abubuwa sun sauya ammh kuma tana kwance sai dai a kwantar a tayar bama wanda ya zata kai haka araye,ana zuwa gida ana Dubata har yau tana nan jiya iyau bata ko mgana Sai wanda ya kara kunnensa yake ji me take fadi in naje Hajiya ta rika kallona kenan na rike hannunta ina Fadin"Allah zai baki lafiya Hajiya"

Sai dai kaga Hawaye na Bin gefen fuskarta Hajiya na bani Tausayi sosai shekaru kusan bakwai tana jinya tana kwance waje daya,Gidan su na karofi Babban Yaron Goggo Yaya Isa ya gyara da yayi aure yake zaune da matarsa kada abar gidan ba kowa ya mutu Baba ya matsa sai ya zauna da Farko Goggon Karofi bata so hakan ba gudun Rigiman zumunci.

  Ya Ishaq ya dawo gida ya gama karatu har ya samu aiki a Hukumar Tattara Haraji na kasa reshen jahar katsina,Shekaru uku da suka gabata,Sai dai baya zaman gidan in ya fita tun safe sai dare in kuma ya Dawo yana Dakinsa na fada muku tun a baya shi baima son ganina shiyasa bamu cika Haduwa ba, bana zama inda nasan zai ganni Saboda yafi kowa iya kallon wulakanci da kaskanci.

Akwai watarana tana cikin cikin Ranakun da bazan manta da su ba acikin kaddarorina ba,Muna gabda Riskan kaddaran auren mu ni da Ya Ishaq al'amarin ya faru watarana ya kira Mama a waya yace yana son abincin Mutum hudu abokansa zasu zo su yi Dinner anan biki sukayi na wani abokin aikinsu.

Nan da nan Mama ta tasoni na shiga Kirchen daman na fada muku a bangaran girki ni Fa'iza bani da makusa,Harta Mama yanzu in ba girki na ba bata iya cin abinci,Shi ko Baba kullum Mama yake godemawa yana ganin ita ta tallafamin na iya girken girken zamani zuwa kuma Lokacin na rage wasu walwahalun,Saboda Mama ta daina aike na ta samu yaron aike bangaran kasuwancinta kuma komai ta waya ne sai dai a saka mata a mota a aiko mata dashi,sannan ta dauki masu wanki da guga da kuma mai wanke wanke na koma gyaran gida da girki.

Jin baki ya ishaq zai zo da su na Zage nayi musu girki mai rai da lafiya fatan pototo,da Hanta sai white rice da Miyar kifi,Sai nayi musu lemun Abarba Sai na hada musu da na Gwangwani kafin ya kariso Mama ta sani na je na shirya komai afalon Baba,na koma kitchen na Dora abincin dare na gida har bakin suka zo ni bansani ba Na gama girkin Dare doya da Miya Mama tace ayi naje nayi sallar mangariba ina zaune saman sallaya Jamal ya shigo Dakin da nake mai karamar katifa sai tarkace yace min Ya Ishaq na kirana afalon Baba sai da gabana ya fadi ban cire Hijabin jikina ba yamin yawa yana neman gadani na nufi Falon Baba

 Ina shiga da sallama gabadaya zaratan mazan dake falon suka Dago suna kallona ni ban iya kallon su ba,Saboda yadda jikina ke kyarma,ina ji Ya Ishaq ya dakamin Tsawa yana Fadin in kariso,Ni dai nasan nazo gabansa na durkusa kaina na kasa ina ji yace musu"To ga wacce tayi girkin nan da kuka matsu ku ganta"

Ya fada cikin sigar Dariya da karfi yayi mganar yasa naji abunda yace gabadaya shuru sukayi kafin naji sun kaure da Dariya gabadayansu sai naji na muzanta matuka muzantan da ban taba yi ba suna ta mganganu wasu ina ji wasu kuma bana ji nadai ji sanda Ya Ishaq yace"Kai ka yi mata da Hausa No Turanci..Sannan Ears."

Gabadaya suka gwalalo ido kafin ya kalleni yace"Yes..sai kunyi mgana da karfi zata jiku Bebiya ce"

Na kusa dani ne ya matso saitin kunnena yana Fadin"What is your Name.?

Aoh Sorry ya sunanki..?

Na dago idanuwana sun cika da kwallah nace"Fa'iza"

Cikin yanayin mganata gabadaya sai suka sheke Da Dariya har suna Tafawa da junansu Sai naji na kara raina kaina Nasan ni ba bebiyace ba ce ina dai da Raunin ji ammh ba Kurma bace ni Mutane ne suka kara Raunana jina da kushe da Tsangwaman su akaina,Ninasan inaji sai dai sai an yi mgana da karfi Sannan mganata tana  da Tsami Tsami Kuma ina Rabe ta kamar ina in ina kuma saboda Raunin ji na ina karantar bakin mutum in yana mgana Ko Tamadina ba Kurma bace tana mgana sai dai mganata tafi nata fita sannan na fita karfin ji.

Ammh yadda suke kankanba Bebanci na abun bai kai haka ba.

Ban taba jin guilt irin wanda naji ba  Ranar hawaye suna bin fuskata na mike zan fita Ya Ishaq ya dakamin tsawa yana fadan sun sallameni ne..?sai na Dawo kawai na Durkusa ina jin Ya Ishaq na fadin bai taba ganin baki da muni ba sai a wajena su ma abokan irin sa ne suna ta Dariya na kamar sun ga abun dariya ajikina ko acikin Abunda suke ma Dariya aciki akwai wanda na bama kaina ba Allah ya bani ba? abun da nake sakawa araina kenan ina jin wani irin abu a kasan raina.

Sun dade suna kallona suna Dariya kafin Ya Ishaq yace na kauce daga gabansa na mike idona ya rufe bana ko gani,bansani ba na ture Teburin dake gaban su jug din lemu ya fado ya zube Lemun ya fallatsa a jikin abokan nasa dashi kanshi har ga Allah ban lura ba,ba karfi ji ne dani ba shiyasa ban ji karar faduwar wani abu ba,ba ma haka ba yanayin da nake ciki gabadaya ji na sa ganina ne suka Dauke a lokaci d'aya.

 Na dai san kafata ta bigi wani abu ammh yanayin da nake ciki bai sa na Tsaya Dubawa ba.

Sai ji kawai nayi an dawo dani baya an yarfar dani akasa ya Ishaq ya Daga Hannu ya wankeni da mari acikin kalmominsa na tsinci kalmar"Banza Jaka,Mummuna useless har na isa na wulakanta abokansa ko akwai sa,a na acikin su ne..?

Ina dafe da kuncina na bisu da Kallo ya fadi gaskiya ba sa'a na acikin su kamar yadda yake kyakyawan gaye haka suke suma,jikina na rawa na fara bashi Hakuri sai yace sai na juya na basu hakuri haka na Durkushe ina basu Hakuri sai da sukace sun hakura ya bi ni da Hambari ina Rarrafe na bar Falon ranar kwana nayi ina kuka har na fara neman nayi Sabo sai na zauna nace meyasa Allah bai yo ni mai kyau kamar kowa ba..?

Ko dai da gasken ne bani da Sa'a..?

Washegari Da Mama taji Labari Allah ya kara tayi har da fadin da ya fada mata Tun jiya sai ta karamin da Duka.

Ina Falon ina goge goge ne alokacin naji sanda Jamal yace"Kai ma Bro meyasa ka kirata cikin abokan ka.?

Sai da yayi tsaki mai karfi kafin yace"Su suka matsa sai sun ga wacce tayi abincin"

Daganan ban ji meya ke fad'i daga karshe ba,Saboda ya Rage murya Ranar ina aiki ina kuka abaya bana Damuwa in an kusheni ammh yanzu sai naji kamar da gaske ne ni Fa'iza bani da Sa'a

  Ashe abunda Ya Ishaq bai sani ba Matarsa ya Tozarta,Agaban abokansa Domin ko sati ba'ayi ba Baba ya tafi Karofi Sakamakon kiran da Goggo tayi mai kan cewa jikin Hajiyar ya tashi Abun mamaki tana ta kiran sunan sa shi da Mama da ya Ishaq suka tafi suna chan ne nima ina gida Hankalina nakan Hajiya ban san me ya faru ba, ni dai nasan sun Dawo gidan cikin Hargitsi da Rashin kwanciyar Hankali mama sai kuka take yi tana Fadin bamai hada mata zuru'a da Dangin munana da kurame.

Washegari fada ita da Baba har Falo alokacin naji Baba yace"ko bayan Ransa sai auran Fa'iza da Ishaq ya kulli sai dai ta mutu"

Dayake da karfi yayi mganar naji sa ni kaina sai da na gigice ana haka sai ga Ya jamal yazo yana fadin Ya Ishaq ya kwashe kayansa ya bar gida Mama ta fadi kasa Hannunta akai tana kururuwam ta shiga uku ta Lalace

Haka Baba ya tsallake ya barta ban bari kowa ya ganni ba na koma Daki ina rawan jiki mai nake ji,Wai ni Ya Ishaq zai aura.?

Tirkashi ni kaina na hango tashin Hankali acikin lamarin ranar har Anty Binta tazo ita da Anty Mahma da kawayen Mama na kusa,sai mganganu suke ni,ni ina Daki baji nake yi sosai ba, ranar ko girkin ban iya yi ba kuma ba wanda ya nemeni.

Nima Badariya ta shigo take fadamin Wai Hajiyar Karofi tace a hada aurena da Ya Ishaq,ance Dakyar ma aka gane me take nufi Saboda Harshenta ya karye.

Ba Ya Ishaq kadai Hajiyar Karofi ta cuta ba  wlh har dani ina ni ina Ya Ishaq ai tazaran ma mai yawa ne.ranar kafin Baba ya Dawo Mama da su Anty Binta suka kirani Falo suka min Fata fata zagi da gori ba wanda ba su yi min ba har da gorin mu dangin maciya Amana ne to wanda ma naji kenan wanda kuma ban ji bansa me suka fada ba,Dayake da karfi suke mganar Anty Binta ko har tana Hadamin da dunguri Mama taci kuka har ta godema Allah idanuwanta sun kala sun yi jajir Ita damuwarta Ishaq ba bawanda yasan inda ya tafi ya kuma kashe duka wayoyinsa Mama taja kunnina da cewa in Baba ya Kirani ya tambaaye ni in na amsa mganar auran nan sai na gwammace rashin amsawata Domin bata fatan Had'a zuru'a dani Har gaban Abada.


*ASSALAMU ALAIKUM*

*KAYA SUN SAKE SAUKA*.

*INGANTATTUN SAIWOWI DA SASSAKE NE DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZA DA SU*.

*ABIN BIRGEWA BA SAU DAYA AKE AMFANI DA SHI BA*.

*KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR KO KUWA KE DA KANKI ZAKI YI GYARA?*

*INA SAKE YIN ALBISHIR DIN GARIN DAKA MAI KYAU DAN CHADI, SHA DA MADARA KO NONO DA KUMA TSUMIN GAMGAM*.

*GADALIN MATA AKWAI*.

*INA DA TABBACIN INGANCINSU*.

*SANNAN WACCE TAKE SON A DAFA MATA KAZAR, ZA'A DAFA*.

*TUARAREN WUTA NA ASALIN CHADI AKWIA SU AVAILABLE, SAI KIN GWADA ZAKI BADA LABARINSU*

*TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU DOMIN KARIN BAYANI*

*08032773332*.

*NATION WIDE DELIVERY*.

*SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*

🙏.


*Littafin KANA NAKA paid book ne biya kudin karatun ki akan Naira N500 Regular posting sau d'aya a rana.*

*Ko kuma tsarin VIP 1000 Posting sau biyu a rana akan wannan acct din 0552179550 Jamila Umar Gt bank,sai a turo shaidar biya ta wannan lambar 09069067488 Wannan karon babu tsarin kati,kowani tsari zaka yi ka turo ta POS,Mutanen mu na Niger kuma zaku tuntubi Kausar Aglan Nissa ta wannan lambar +22796562223*






*Janafty**KANA NAKA..!*


*Wattpad:JamilaUmar315*

*Mallakar:Janafty*

*Arewabook:Jamilaumarjanafty*

*Book 1*


*ASSALAMU ALAIKUM*

*KAYA SUN SAKE SAUKA*.

*INGANTATTUN SAIWOWI DA SASSAKE NE DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZA DA SU*.

*ABIN BIRGEWA BA SAU DAYA AKE AMFANI DA SHI BA*.

*KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR KO KUWA KE DA KANKI ZAKI YI GYARA?*

*INA SAKE YIN ALBISHIR DIN GARIN DAKA MAI KYAU DAN CHADI, SHA DA MADARA KO NONO DA KUMA TSUMIN GAMGAM*.

*GADALIN MATA AKWAI*.

*INA DA TABBACIN INGANCINSU*.

*SANNAN WACCE TAKE SON A DAFA MATA KAZAR, ZA'A DAFA*.

*TUARAREN WUTA NA ASALIN CHADI AKWIA SU AVAILABLE, SAI KIN GWADA ZAKI BADA LABARINSU*

*TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU DOMIN KARIN BAYANI*

*08032773332*.

*NATION WIDE DELIVERY*.

*SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*

🙏.


*Assalamualaikum! Phydoors* *collection (home of all you need)tazo muku da kayan gyaran girki masu inganci da Gina jiki da faranta Ran Mai gida harda Ma yaranmu domin inganta girkin uwargida Kai harma da amarya tazo muku da egusi,* *crayfish ,manja ogbono dadai sauransu Zaku iya tuntubar ta wannan nomber 08062181151 ko Kuma shafinmu na yanar gizo https://instagram.com/phydoors_collection?igshid=MzNlNGNkZWQ4Mg==Muna aikawa ko Wani gari da iKon Allah,ko gwada kayanmu da iKon Allah sai Kun dawo* 🥰🤗


      *🅿️05*


Lokacin da Baban katsina ya kirani Falonsa adaran da su Mama suka ja kunne ne ammh na kasa iya d'ago ido na kalli Baba ballatana nayi mai gaddama kan lamarin da yazo min dashi cikin wani yanayi na roko da Tausasawa Baba ya sanar dani Umarnin Hajiya na had'a aurena tsakani na da Ya Ishaq shi Uba ne gareni zai iya aurar dani ko da ban sani ba addini ya basa wannan damar ammh bai yi haka ba, sai ya zabi da  ya kirani yana Roko na na amince don ya samu damar da zai cika Muradin Hajiya..

 Ina kallonsa da kumburarrun idanuwana da suka tasa saboda kuka Da damuwa Hawaye suna Biyo Fuska ta wasu na korar wasu Baba nake kallo wani Mutum da nake gani Da kima da Daraja mutumin da nake ganin shi Kad'ai ne ya ragemin gata na aduniya ta ya ya zan iya bude baki nayi mai gaddama.? Amsa masa kuma Daidai yake da Fadawa Ukuba kamar yadda Mama ta shaidamin ita da su Anty Binta..

Na bude baki da niyar nayi mgana kalmar

 " Baba.." 

Kad'ai ya iya fita a bakina sai kawai na saka ma Baba kuka shi kuma bai duba yanayi na ba ya shiga sakamin albarka da Fatan gamawa da Duniya Lafiya sai harshe na yayi nauyin da har Baba ya sallame ni na kasa Furta ko kalma d'aya ammh a kasan raina nasan wannan auran bai kamata ya tabbata ba Domin babu had'i ko gami acikin sa gabad'aya.

Ranar nasha kuka kamar raina zai fita Tun cikin Dare Mama da Baba suke Rigima da karfi suke mganar Shiyasa nake jiyo su sama sama Tunda Baba ya fita sallar asuba bai Dawo ba Mama ta rude ta shiga tashin Hankali Saboda rashin Sanin inda Ya Ishaq ya shiga Tunda yaji mganar auran mu

Ni dai ban san ya akayi ba ina kwance sai ji nayi an rufeni da duka kota ko'ina,ina kuka ina ihu ammh Mama bata Tausayamin ba kuka take yi tana Dukana fadi take yi"Dangin jaraba dangin masifa Saboda ke Abban Ishaq yace zai iya rabuwa dani...?Saboda ke Ishaq ya bar gida ban san ina ya shiga ba..? Kuma ahaka zan amince na hada Zuru'a dake..?wlh sai dai ki mutu ammh ni Saudatu bazan taba Hada zuru'ata da b'ara gurbi irin ki ba Shegiya ya'yan shegu dangin maciya amana Mummuna dake D'ana yafi karfin ki"

 Da karfi take mgana shiyasa na ke jinta ina ta bata Hakuri bata jini ba Badariya na gefe tana kuka tana rokon Mama ta kyaleni ammh bata tanka ta ba Jamal kuwa yana Tsaye shima Fadi yake yi"Mama duka wayoyin ya Ishaq suna kashe ne sannan na kira abokan sa na kusa sun sanar dani bai zo ba kuma bai kira su ba..Gaskiya Baba shima bai yi Tunani ba Ta ina Ya Ishaq ya Dace da Fa'iza..?

Ina ji Mama ta wurgoni Falo tana Fadin"Ai yadda ta saka ya bar gidan nan nayi Rantsuwa bazan yi kaffara ba itama ta gama zama a wannan gidan yau ba sai gobe ba sai ta bar min gidana"

 Da duka da gori da Tsinuwa Mama ta rakani waje ta maida kofa ta Rufe,Dagani sai rigar jikina ta atamfa sai dankwali shima tana Dukana na Rarumeshi na rike a hannuna kafata ba Takalmi Mama ta koreni nan na rakube jikin gidan ina ta kuka na Duba gabas da yammah kudu da arewa bani da wani gata a garin katsina kuma Mama Tunda tayi Rantsuwa to da gaske take Dankwalina na warware na yane kaina Dashi gidan Anty Mamah ya fadomin tana da Sauki Sauki kila ita zata iya taimakamin da kudin motan da zan koma karofi domin chan ne gata na anan duniya..

Da kafata Tun daga Kofar soro har Cikin asibitin kashi,A kafata ina tafe ina kuka kamar zararriya,ban gaji ba Domin halin da nike ciki gajiya bata da Muhalli a wajena Sai dai Anty Mahma ta ganni kwatsam kamar Daga sama tayi matukar kad'uwa da na zube ina bata labarin korar da Mama tayi min Kai ta girgiza kafin tace"Kai Mama meyasa bata bin abu a Hankali ne..?

Bari na kirata.."

Da Sauri na rike mata Hannu naji tana mgana ban ji me tace ba sai dai Yanayin mganarta da wayarta data Dauka sai Tunani na ya bani Mama zata kira ko Anty Binta ni kuma na shiga Tsaka mai wuya acikin wannan Halin Karofi nake son zuwa na Durkushe gaban Hajiya na Roketa ta janye wannan mganar in tana so na cigaba da Rayuwata yadda Allah ya Tsaramin in  bata so ta kara jefa Rayuwata cikin wani Sabon kangi.

Dakyar Anty Mamah ta amince da Rokona ta bani kudin mota ta Daukeni a motar ta da kanta ta kaini Tasha ta sakani a motar Karofi ina ta kuka ta Tausayamin ta Dafa kaina Dake cikin Sabon Hijabin data bani da Takalmi tace"Ki daina kuka Fa'iza ba matsala in sha Allahu Mama zata Sauko"

Har na kai karofi kuka nake yi sai da Muryata ta dishe kukan rashin gata da kuma Tunanin yadda yanayin Rayuwata ya fara na fara jin kamshin gaskiya kila bani da sa'a ne komai nawa ba mai kyau ba ne irin na kowa rayuwata ba Daidai take da Sauran mata ba.

Sai dai Goggon Karofi ta ganni yarkace yarkace kafin na fadamata abunda ya faru sai ta nemi dukana sannan na Zayyane mata komai bazan manta ba sai da ta share kwallah ta kamani ta Rumgume tana Fadin"Abunda Saudatu ta aikata miki kenan..? Daina kuka Fa'iza watarana sai Saudatu tayi kuka idanuwanta akan abunda ta aika miki akwai Allah"

Araina ban taba Hango hakan ba ni kuwa wani matsayi zan taka da Mama zatayi kuka Saboda ni..?

A daran ta Kira Baban katsina ta fadamai Halin da ake ciki yace da Safe zai shigo garin ni kuwa Lallashina Goggo ta dinga yi Hatta Hafsatu dake da karancin shekaru ta shiga Damuwa ganina cikin wannan Halin Hajiyar karofi kuwa tana kwance sai bina da kallo take na kasa na mata wata mgana domin sai naji bakina yayi nauyi ganin yanayin datake ciki Goggo tace tun ranar da Baba ya bar nan jikin Hajiya ya kara rikicewa.

Washegari Baba yazo sun kai ta ba dadi da goggo ta nuna mai ya janye mganar auran nan ita zata rikeni Allah ya bani wani mai sona in yi aurena ammh ba Ishaq d'an Saudatu ba shi kuma Baba yace indai yana Raye sannan shi ne Uba ga Ishaq kamar ya aureni ya gama ina Durkushe gabansu suka rika wannan Hayaniyar ad'akin da Hajiya take jinya itama tana kwance bata iya mgana ba sai gyad'a kai hawaye na bin gefe da gefen Fuskarta.

Baban katsina ya tafi ko sallama bai yi ma goggo ba Allahu akbar adaran Hajiya ta amsa kiran Mahallacinta,Tun daga Lokacin da naji goggon na Salatun mutuwar HaJiya da kaina ya amsa Dum! Har gobe in na Tuna da mutuwar Hajiya sai yanayin ya Dawomin da gaske ne ni Fa'iza bani da Sa'a?

Meyasa duk wad'anda suka Tsayamin suke tafiya su barni Farko Babanmu Sannan ga Hajiya itama har aka kai Hajiya kushewarta bana cikin Hayyacina gida ya cika Har Hajiyar Dala da duka zuru'arta suna nan Hadda Mama da su Anty Binta su Ya Asiya sun Dauka mutuwar Hajiya ce ta tab'ani basu san abunda ke Faruwa ba har kuma lokacin ba'a san ina ya Ishaq ya shiga ba.

Ranar da bazan manta ba,Itace Ranar da aure ya kulli tsakani da Wanda bai Taba sona ba har ko yau da muka Tara zuru'a dashi aurena da Ya Ishaq wanda yau har gobe Mama bata daina aibatani da zuru'aar maciya Amana Dangin Tsiya ba,Ranar addu'ar bakwai din Hajiyar Karofi Baba ya tara Mutane ya Biya Sadaki aka Daura aure na ba wanda ya sani sai da aka Daura Gidan mutuwa sai ya koma Gidan Fad'a da Hayaniya domin Mama kaina tayi tana fadin sai taga bayana Goggon Karofi ta shiga Tsakani Ranar ba iya ni kad'ai ba hadda Mahaifin mu dake kasa yasha zagi Taamadina na gidan sulalewa tayi ta koma gidansu tana kuka,kukan maraici da Tausayin ya'yanta.

Sai alokacin kowa yasan Halin da ake ciki Goggon Karofi ce kad'ai da ya'yanta ke tare dani ban da Hajiyar Dala data mara ma Mama baya,Aranar Mama ta koma katsina ta sha alwashin sai taga yadda auran nan zai Tabbata shi kuma Baba yace sai dai in ba shi ya Haifi Ishaq ba.

Ya Asiya da Yaya Mariya sun koma Gidajen su da Tunanina aransu da Tausayina su kan su sun hango Yadda rayuwa da kaddara suka kara gangarawa dani.

 Kwana Ashirin da Rasuwar Hajiyar Karofi Sai ga Baba ya zo shi da Ya ishaaq,wanda ya gama gudun nasa ya Dawo jiya da Daddare ya samu labarin An daura masa aure dani Ya Ishaq ya kasa katabus domin Baba ya Daga mai murya yace in har yaki karb'ata a matsayin mata to sai dai ya chanza wani uban ba shi ba.

Wannan mganar shine Sarka na Farko da ya fara kulle aurena da ya ishaq,Baba ya bama Goggo kudi ta yi min siyayya sannan ya kama mana Haya a katsina cikin gari in da zamu zauna ni da Ya Ishaq,har suka tafi ban gansa ba shima bai nemi ba,Tun kuma Daga Lokacin Baba ya fara shirin Tarewata Mama kuwa tayi Kukan har tagaji ta Saduda ganin Da gasken Baban bazai fasa ba.

Kafin Ranar arba'in din Hajiya karofi hatta jere na Goggon Karofi da ya'yanta da Yan'uwana sun gama min komai Domin Baba yace ranar addu'ar arba'in Zan tare agidana Yaya Mariya ita takaini gidanta ta tsifemin kai ta wanke ta kaini akayi min kitso da Kunshi Ina ta ce mata ta barshi kunshi da gyaran jiki sai Mata masu kyau ba irina ba ban taba manta kalamanta alokacin Kaina ta Dafa kafin tace"Kema kina da kyan ki Fa'iza sai dai in ba'a gansa yanzu ba ne..Ammh na tabbatar miki nan gaba zasu ga abunda nake gayamiki"

Alokacin mirmishi nayi mata Domin nasan ta fada ne ni kaina nasan bani da kyau sannan ina da nakasu ta bangaran Ji na da mganata

Aranar da Hajiya ta cika kwana arba'in a kushewarta ranar na Tare agidan Ya ishaq aurena ba irin na mata masu kyau da gata ba ne,Daga ni sai kayana da Goggo ta d'inkamin Sabbi ita da Baba domin da Goggo Taso su yi min Rakiya sai ya Ishaq yace baya Bukata dagani sai shi a mota sai Baba da Direbansa.

Daga Mama har ya'yanta ba wanda ya Leko karofi,Baba da kansa ya shiga Dani karamin flat din da ya kama mana mai Falo da Dakuna Biyu sai kitchen da Tsakar gida,Shi ya damka Amanata Hannun ya Ishaq da karin wasu manya manya sarkunan da Tun abaya na fada muku su suke rike da wannan auran namu yau har da nike baku wannan Labarin,Domin cikin kaukkausan murya yace mai"Ishaq ga Fa'iza nan na baka auranta ba Domin ta rasa me son ta ba sai domin cika Muradin mahaifiyata..Wlh tallahi ko da Rana daya in ka zalunce ta ban yafe maka ba Ishaq..Kuma ko da rana d'aya kabi Hudubar mahaifiyarka ka Tozarta Fa'iza shima nace ban yafe ba..Daga karshe matarka ce ta sunna ka Kula da ita kuma in ka Danne mata Hakki Allah na kallon ka sannan nima bazan yafe maka ba Sannan kasani Ranar gobe kiyama bazaka Rabauta ba Ishaq in dai ka saba ma Umarnina.."

Kafin ya tafi sai da ya kara Jadaddamai in ya danne min hakkina na aure ko guda d'aya ya sani bazai kara samun albarkarsa ba,ya tafi bayan yayi min nasiha hakuri sannan ya sanar dani na zauna nayi ma aure Biyayya bazan taba Tabewa ba Duniya da Lahira Tabbas wannan Biyayyar da Baba ya Rokeni har bayan mutuwarsa ban sauka daga kanta ba,nima ita ke rike dani acikin rayuwar aure na da Ya Ishaq.

Warware tarin kalubalen da na Fuskata a zama na da Ya Ishaq abu ne mai yawa da bazasu fadi a cikin k'urarren Lokaci ba sai dai abu d'aya na Sani mun yi zama ne na Biyayyar Iyaye shi Mganar Baba ke rike sa da Bakinsa a kansa nima kuma Karfin Biyayyan da ya Rokeni akanta na ke zaune.

Tunda na auri Ishaq daidai da rana D'aya bai taba kallona ya yab'amin ba,Bai taba jin dadin zama dani ba bai taba godemin ba,Bai tab'a godema Baba Bisa aurena da ya basa ba,Bai tab'a sona ba bai tab'a kallona da Idon Rahma da Salama ba  bai tab'a jin zai iya bani matsayin matarsa mai kima ba nayi Rayuwa dashi cikin k'askanci da Tozarci ko da yaushe cikin aibatani yake yi da Kusheni,Ni fa'iza na Fuskancin Guilt din kushen miji har tsawon shekaru Takwas da auran mu,Ya kulleni agida cikin tozarci bai barni nayi zumunci da yan'uwnaa da Dangi ba,Alwashin da Mama ta Dauka ta cikashi bata bari na kara jin Dad'in Rayuwa Sai da tabbattar da duk abunda tace ma Ishaq akaina shi yake amfani dashi bai horar dani da yunwa ba Yana sauke min kayan abinci duk wata sutura kuma yana yi min ta Hannun Mama sai ta ga Dama sannan na saka abu mai kyau cewarta kullum abu mai kyau bai dace da mace irina ba,ina jin Tsoron Ishaq kamar yadda nake jin Tsorom Mama Tunda muka yi aure bai taba yarda ya nuna ma wani ni matasar bace ko abokansa ba su san yayi aure ba, acewarsa matar Ishaq sai an zo a ganta Mai kyau ce mai ilimi ce sannan yar gata gaba da baya ni kawai wata Tsani ce wacce nayi kutse tare da Ruguzamai dukkan Farincikinsa.

Da gaske yake yi ya fad'i gaskiya ni kaina in na kallesa na kalli kaina sai naji Tabbas na yi mai kutse acikin mafarkin sa Ya Ishaq dogon Namiji ne kyakyawan gaske fari mai Hanci d'an Fafa mai ilimi dan alfahari da son komai mai kyau da Tsari ni kuma Bakace Gajera mummuna,wacce bata da gata,ba ilimi kamar ta bakinsa yace Total Zero Fa'iza komai nata ba sa'a acikinsa.

  Ya Ishaq kunyar nuna ni yake yi a matsayin matarsa domin bai taba gayyato wani inda nake ba yace shi kan shi kunyar kallo na yake yi a matsayin matarsa ma ballatana wani,Ko Ya'yan da na Haifa tare da shi Kaddara ne da Rabon su daman Domin Tunda Baba ya kawoni wannan gidan nake rayuwa ni kad'ai Sai dai ina aikace aikace na bana ganin kowa Dagani sai ni kamar mayya Ba ni da waya bana jin kowa sannan bana ganin kowa sannan ya min gargadin ko kofar gida na fita sai na raina kaina shi kuma sai chan dare yake dawowa da Farko gidan Mama yake biyawa yaci abinci Baba d'aya lura da Haka ya mai fad'a sai ya daina Daman na Fada muku yana morata ta bangaran abinci zai ci kafin ya fita in ya Dawo yaci acewar Mama Ai abinci daman bani na siya ba dafawa ne kawai nawa Saboda haka na Dafa daman Mata ire irena da Bauta muka dace,Sai suzo gidan ita da Anty Binta su yi ta zagina da Gore gore Ishaq na zaune kanzil bazai ce ba Wani Lokacin Anty Mamah ce kan musu mgana sai su Sasaauta.

Bazan manta da muna da wata biyar da aure Anty Hure kanwar mama tazo katsina suka zo ita da Mama Ya Ishaq na gida ranar baije aiki ba,Naje kitchen na kawo musu ruwa ina rawan jiki na fice ashe Mama ta kira Sunana ban ji ba, tamin uzuri bani da karfin ji ammh sai Mama tace naji kawai yanzu na raina ta ne agabansu Ya Ishaq ya mareni ya sani na Duka na bama Mama Hakuri taki hakura Anty Hure ta yi ta Dukana tana rankwashina Ya Ishaq na zaune ko ajikinsa haka suka tafi suka bar ni ina kuka kukan da ya riga ya zame min jiki.

Ko wata rana na Shafin Rayuwata ba ranar da bazan yi kuka ba babu wannan ranar,Sai da na fara tara ya'ya sai suka zamemin sanyin idanuwana ko Ya Ishaq ya kunsamin Takaicinsa in na Kallesu sai naji raina yayi sanyi Tabbas ko wacce uwa ya'yanta sune Duniyarta.

Muna da wata shidda da aure,Baban katsina ya kawo mana ziyara yayi mana Fad'a da kakkausan murya musamman ma Ya ishaq ni kuma yace na rame na lalace yayi tambayan Duniyan nan ko Ishaq na min wani abu ne nace mai a'a bakomai haka ya tafi  bayan ya kara fadama Ya Ishaq cewa in bai Sauke hakkina dake kansa ba ya sani Allah na kallonsa.

A wannan Daran Ya Ishaq yazo min ya karbi Mutumcina da kimata ta y'a mace cikin kaskantattacen yanayi,Cikin Tozarci da bana jin wata mace ta taba Fuskarta ban sani ba ammh a kasa raina naji cewa mata marasa kyau ire irena bai kamata su fuskanci wannan tozarcin ba.

Tunda ya gama dani ya tsallake ya barni cikin mayuwayacin Hali,Halin da ni na tallafi kaina bazan iya fadin irin wahalan da nasha ba,ba wanda ya kula dani sai ni kadai,Nafi Sati bana ji na Daidai da taamakon Allah na Samu na Dawo cikin Hayyacina Tun kuma daga wannan Had'uwar tamu bai kara kallo na ba ko da yaushe ni ke mai Hidima ina rawan jiki a kansa shi kuma kalamansa Daya ne Hajiyar karofi da Baba sun cucesa har fadi yake yi tasan zata mutu ammh kafin hakan sai da ta jefa rayuwarsa a wani Hali sannan ta bar Duniya har yau bai taba gode musu ba ban kuma jin akwai ranar da zai gode musu.

Ashe wannan haduwar tamu itace sillar Zuwan Amir(Kabir) duniya ne Wata uku tsakani nayi ta ciwo a tsaye,Zazzabin Dare da amai kasala da yawan barci,Ya Ishaq baisan Rashin Lafiyata,baisan komai akaina ba ban da na girka mai abinci yaci yana ci yana bi na da mganganun kushe da Tozarci.

Fahimtar ma ban da lafiya girkin da na kasa yi ne yasa ya lekani ya ganni kwance Ba domin yaji Tausayina ba sai Domin Harshen Baba akansa yasa ya Daukeni ya kaini asibiti,Gwajin farko aka tabbatar da ina da shigar ciki dan watanni biyu da wani abu Bansan wani yanayi Ya Ishaq ya shiga ba, ammh nasan muna Hanyar komawa gida ya kalleni kafin yace"Ke haka kike daga tabaki sai ciki Fa'iza..?

Yaushe na tsara ma kaina aure ballatana har na haihu?

Ya manta Haihuwa na Allah ne,Bani na bama kaina ba Allah ya bani ammh da Gudummuwarsa,Cikin Amir ciki ne da nayi sa mai Laulayi na sha bakar Wahala acikin gida ni kadai,ina haka watarana Goggon Karofi ta zo ganina ita da Yaya mariya su suka iskeni ba yadda nake suka kwasheni sai asibiti dalilin kwanciyata a asibiti Cikina ya fallasa ga su Mama kowa yaji ina da ciki sai kowa mamaki ya kamasa.

Mama kuwa mamaki yasa ta kasa mgana,Anty Binta sai kallon Ya Ishaq take yi basu taba zaton zai iya kallona na da sunan auratayya ba.

Baba kuma sai murna yake yi shi ya Kira Ya Ishaq da kansa ya fadamai da yazo asibiti ga Halin da nake ciki Sanda yazo,Baba sai da ya Rumgumesa yana murna lokaci d'aya yana sakamai albarka.

Mama ta fad'a agaban kowa da kowa Bata kaunar hada zuru'a dani,Goggon Karofi tace Tunda Allah ya had'a ita bata isa ta raba  ba,har sai da suka yi ta Hayaniya,naji jiki sai da nayi sati a asibiti likita nata fadan bana cin abinci sannan jinina yayi kasa Goggo kamar ta wuce dani karofi Baba ya Hana Akace gidan Mama tace ai har Abada na gama zaman gidanta Dole gidana aka maidani Goggon Ta zauna Dani tayi sati,Yaya Mariya ita kadai ta koma Karofi,A bakinta Ya Asiya taji tazo har Katsina ta Dubani bana ganin Tamadina bata taba zuwa gidana ba na Tambayi Goggo tace min tana gidanta ni nasan rayuwata cike take da abun Tausayi.

Har Amir yazo duniya ni Fa'iza babu abunda ya sauya gareni daga zuciyar,Ishaq a kaina na wahala wajen Haihuwa kamar bazan rayu ba sannan Amir yazo duniya wanda yaci sunan Baban katsina Kabir,lokacin da na Haihu Anty Binta na asibiti ana kawo musu abunda na haifa ta duba kunnensa ta Kira mama tace"Mama sai hakuri Dangin tsiya yaron ya Debo"

Nayi kuka sosai da wannan kalmar sai dai a kallah na samu wanda zai san zafina wani abu daya fito daga Tsatso na wanda kila shi zai kaunace batare da ya Duba yanayin Halitta na ba ko nakasun jina ba,An kai ruwa Rana kafin Ya Ishaq da su Mama su amince Goggo ta tafi dani karofi nayi jego shima sai da Baba ya saka baki,sannan ya amince a cewarsa wai Goggo sai tayi ta nuna yana zalunta ta na sannan baya so naje na had'u da su Yaya mariya wai ana zaginsa mganganu dai haka yayi ta yi kan yan'uwana da iyayena bani da tacewa.

Sai da na koma karofi sannan Tamadina tazo ta ganni ta rike Amir gam a Hannunta kafin ta mikamin shi ta dafa kaina kawai tayi miirmishi na kalleta sai naji kuka duk ta lalace ta rame ta kara tsufa kamar ba ita ba,Bazan taba mantawa da Goggon Karofi ba domin ita ta kula dani ba,da kila sai da na Rub'e ni kadai ban san komai ba.

Ina yin arba'in ba Dadewa Goggo Karofi ta maidani gidana Ni da Amir mun yi bulbul duka duka sau biyu Ya ishaq yaje ya ganmu kamar Amir din ba D'ansa ba ne,Goggon Karofi da yan'uwana sun yi kokarin wajen gyarani ni kam ban ce musu komai ba, to ina zan fada musu sau daya tak Ya Ishaq ya taba hada jiki dani Rabon Amir ne..? 

To kamar na Amir itama haka Rabon Saudatu(Anum) ya had'amu shima duka Duka Haduwar bai wuce sau uku ba ma na samu ciki Amir nada wata Goma sha hudu wannan karon Ishaq yafadamin sai dai a zubar da cikin ni kuma nace ban amince ba Karo na Farko da na taba kai karas gaban Baba Dalilim da yasa Baba Ya mari Ya Ishaq ya kuma nunasa da yatsa yace"Kada na kara jin wannan mganar a bakin ka..kasan baka son cikin ka yi sa..?

Ka kiyayi ranar da Fa'iza da ya'yanta zasu zame maka inuwa wacce zaka iya rab'ar ta ina jiye maka watan watarana kada kayi nadamar abunda ka aikata"

Wannan marin ya jamin abubuwa Dadama tsakani da Ya Ishaq,kamar ni na bama kaina cikin Dalilin Baba yasa Saudatu tazo duniya(Anum),Da kulawarsa na haifeta Lafiya ita ma kamar Amir ne Baka ce irina,Basu da yadda zasu yi su sauya wannan kaddaran tunda haka Allah ya Tsara Mama ta tsane ni ammh ta kasa Tsanar jokokinta Amir ma ita ta karbesa ta yayesa sai wahalan tamin Sauki,Goggon Karofi Sati daya tamin ta koma ni na mike na Rika kula da kaina har nayi arba'in din Anum.

Ya Ishaq baya barina fita ko'ina Sai gidan Mama ko gidan Anty Binta Su kuma har naje na Dawo bana samun kallon arziki,Karofi kuwa Tun da nayi jego ban kara komawa ba Har Haihuwa Ya mariya tayi ya Ishaq yace gulma zai kaini bazani ba.

Gidan Yaya Asiya kuwa tun bayan auranta kafata bai kara taka kano ba,Ya Ishaq ya rabani da kowa ciki har da mahaifiyata domin har Haihuwa tayi yaron bai zo da rai ba bai barni naje ba wai zan kwaso ma Anum Sanyi Baya sona ammh kuma yana kaunar ya'yan sosai yake kula dasu kamar yadda yake kula da kansa.

Anum na da wata Hudu watarana Baba ya fara rashin Lafiya anje asibiti an yi gwaje gwaje sai aka gano Hantarsa ce ta tabu ba'a sani ba,Ya kwanta asibiti yafi sau hudu duk Hankalin su Mama ya tashi ni kaina Hankalina baya kwance domin Baba shi kad'ai ne ya ragemin Saura gata na,Kwanciyarsa asibiti na Karshe an sallamosa Da ya ishaq zai fita yace na shirya naje na Dubasa Amir daman yana chan tun yaye bai Dawo ba.

Naje na dubasa yana kwance ne yana ganina sai da ya mike,Ya miko min Hannu na Kwanto Anum daga baya na mika masa ita yana ta mata wasa Baba yayi ta min Nasihan hakuri da kuma Umrtana da na zauna nayi Biyayyan aure zan rabauta Ranar gobe kiyama..

Ashe wasiyya yake barin mu yace na kula da ya'yana na basu tarbiya kada na Biye ma Ishaq,nayi hakuri dashi Sannan na kara hakuri da su Mama watarana dani da ya"yana duk sai mun zame musu Inuwar Rab'a,na dawo gida da Tunanin mganganun Baba ashe bazai kwana ba adaran Allah ya Dauki ransa.

Alokacin mutuwar Baba na kara yarda Tabbas ban da sa'a domin duka wada'nda nake gani agata na sun kare bani da kowa anan duniya da zan kallah nace Gata na ne duka sun tafi Na tabbata ko Mama bata kaini kukan mutuwan Baba,na fade lokaci d'aya nayi zuru zuru tabbas Mutuwar Baba ya sanyaya ma Ishaq zuciya sannan ya sa ya rage wasu abubuwan.

Rasuwar Baba ba'a rufe shekara ba Ya ishaq ya samu karin girma zuwa Abuja,chan ya koma aiki sai bayan Sati biyu yake zuwa katsina sai nauyin su Mama da su Jamal duk ya koma wuyansa abubuwa duk suka Tabarbare daman karfin zumumcin Baba ne to yana Rasuwa sai ahankali Hajiyar Dala ta matse kanta gefe itama Goggon Karofi sai ta kama kanta itama Daman basa shiri da Da Mama sai ta Dade bata zo katsina ba ba ita kadai ba Saboda Sanin Halin Ya Ishaq yasa ba mai son Rabata abu kadan yace munafunci ake yi shiyasa Dole dai su Mama ne bani da kowa a garin katsina sai su da ya'yana.

Samun karin girman Ya Ishaq yasa sai ya samu rufn asiri fiye da baya ya gyara ma Mama gida ya koma Fasalin na zamani shi kuma ya siya Fili ya fara gini a Anguwan layout,Jamal kuma ya shiga jami'a sai Badariya da ta zama yammata yanzu sai ni da ya'yansa wanda Darajan su yasa yake Ragamin shima ba wai don ya daina Tozartani ba ne A'a har yau har gobe ni Fa"iza ba kowa bace a wajen Ishaq kabir Karofi

 Cikin mustapha ko ni bansan ina da shi ba sai da yakai wata Biyar Mama data ganni da ciki ta Dinga bala'in na zama kamar beran masar bani da aiki sai Haihuwa ta manta ba ni kad'ai nake samar da cikin ba har da Gudumuwar D'anta ammh bata ganin Laifinsa sai nawa,Na haifi Mustapah ba Dadewa muka tare a sabon gidan da Yaya Ishaq ya gina katon gida mai shashe biyu,Shashen farko mai 3Bedroom da Falo sai kichen,Nawa daya sai na yara sai guda d'aya na baki,Ya ishaq shi ya Zuba Sabbin kaya agidan komai bamu Dawo da Tsoho ba, Mama ta kwashe su ta kyautar ni ko da har nayi Tunanin na aika ma Tamadina da su Dakinta Sai leda ba kujeru ganin Mama tace akwai wacce zata bamawa ban yi mgana ba, Sanin Halinta.

Haihuwar Mustapah yazo da Budi sosai Ya Ishaq har motar hawa ya mllaka ya siya mama nata,Budi ta ko'ona sai hamdala da Godiya yana Dinkamin suturu daidai gwargwardo sai dai na yaransa Dabam suke,Ni wani Lokacin ko yayi niyar yimin Rantsatsun kaya sai kalaman Mama su Dishe niyyarsa tunda tasha fadin siyamin kaya na alfarma barnan kudi ne, Tunda ba kyau zasu yi min ba sannan bansan yadda ma ake gayun ba kuma gaskiya suka fada ba karya sukayi ba ban san komai na gayu ba.

Ni dai iyakata nayi wanka na shafa mai na saka kaya,Abaya telan su mama ke min dinki Mama ta koma ba wata mace saboda sai nace yana kamani ni kuma bana so kaya su kamani na fison a shatamin na rika yawo aciki,ya Mariya ko Ya Asiya ko da wani Lokaci suna kokarin gyarani ni ko bana jin su gani nake yi gyara da gayu na wajen mata masu kyau da gata ban da ni da bani da ko  d'aya daga ciki Dalilin dayasa Ya Ishaq yake Biye ma Mama kenan in ta fadi mgana hakan take indai a kaina ne ballatana ba ran Baba ita ke tafiyar da komai.

Mama ta bada shawaran nayi Tsarin iyali sai dai bai karbeni ba wannan yar ashanan aka sakamin ya sakarmin jini Dole aka ciremin ana ko Ciremin ko wata Biyar ban yi ba na Samu Cikin Ahmad,na haife su kusa da kusa domin a shekara ta takwas da auran mu da Ya Ishaq duka na Haifesu haihuwan gwarne na rika yi don ma Allah yasa ina da jarumta daukan duka kwarmiyan yaran

Cikin ikon Allah cikin ya'yana ba wanda ya Dauko Lalurata sai na godema Allah Ammh wani ikon Allah susan Lalurata barin ma Anum da Amir susan bana ji sosai in zasu yi min mgana sai sun daga muryansu.

Allah ya bani yara masu kirniya,musty Da Amun basa jin mgana komai suka gani sai sun taba abunga ga wanda bai da karfin ji ina chan ina aiki su kuma suna Falo suna barna bana sani kuma Duk abunda suka Lalata sai Ya Ishaq ya dora komai akaina,Shiyasa ya dinga masifan na bari duk sun bata gidan sun bata kayan kallo sun bata in ji min wanki kuma Mama sai tace bazai kara siya ba, a kyaleni na wahala ai da gangan na bari suka bata komai.

Ni kuma bana cewa komai,Saboda bani da wani zabi,Har zuwa yanzu da girma ya kamani da ya'yana ban daina samun tozarcin Wajen Mama da Anty binta ba tun ba'a sani ba har kowa ya sani,Goggo karofi dai hakuri take bani,in ta kirani a waya sai dai fa ta wayan ammh Sai na shekara kafata bata taka Karofi ba Tunda nayi aure Sau Daya naje naga Tamadina Shima Haihuwan Mustapah ne da naje karofi da Ya Ishaq yaji Labari masifa ya farayi wai baya son ya'yansa suna zuwa gidan wasu suna Rabe rabe.

Haka nan nake daga ni sai ya'yana sai Danginsa alhalin yasan bana jin Dadin su ammh ni nawa yan'uwan sai dai zumunci ta waya ya rabani da kowa nawa.Hafsatu ce kawai tana ta da Kulafucin yan'uwana bai da yarda zai yi da ita in sun samu Hutu tana zuwa ta zauna dani hakan sai yasa na Shaku da ita fiye da su Yaya Asiya.

 Nasan Tabbas Ya Ishaq zai kara aure watarana ban daukesa alokacin da najisa ba Nima abakin Anty Binta na farajin mganar auran sannan Mama ta Fadamin nasan bani da wata Daraja a wajen ya Ishaq ammh na Dauka zan ci albarkacin ya'ya ashe bani da wannan alfarman na Kunshi Bakinciki Tundaga ranar farko da na wayi gari agidan Ya Ishaq a matsayin matarsa,Na kunshi takaici a matsayina na Uwar ya'yansa na fuskanci Tozarci a matsayina na kanwarsa tun a baya to wani tozarci ne ni Fa'iza da ya rage ban gani ba..?

Nayi Rayuwar aure shekaru Takwas da wani abu ammh Daidai da Rana d'aya ban Taba Danda'na yadda Dadin aure yake ba na dai yi shekaru Takwas ina Sanin yaya matsayin Tozarci da Gori yake sannan na kara zama Guilt akan kushen Hallita da kuma aibata Nakasa ta nayi rayuwa cikin Guilt din jin ban da sa'a na rayu cikin Guilt din Sannin ni bani da gata na zauna cikin Tunanin Mata ire ire na basu dace da suyi Farinciki ba.

Basu chanchanci miji mai kirki ba, basu chanchanci samun soyayyar ko wani Namiji ba,Sannan basu chanchanci Rayuwar Farimciki ba.

Mata ire irena Rayuwar kaskanci da Torzarci da Bauta  ya dace damu,Ba kokarin mu goga kafad'a da kafad'a da mata masu kyau da gata ba shi yasa na Rayu cikin Tunanin kayan alfarma da shigar alfaarma da Kwalliya  basu dace da ni ba, sun fi dacewa da mata masu kyau da Nagarta kamar yadda Ya Ishaq da mama ko Anty Binta ke yawan fadi akaina.

Tabbas na aminta da duka zencen su da Tunaninsu"




*Littafin KANA NAKA book 1 free ne book 2,3 paid book ne biya kudin karatun ki akan Naira N500 Regular posting sau d'aya a rana.*

*Ko kuma tsarin VIP 1000 Posting sau biyu a rana akan wannan acct din 0552179550 Jamila Umar Gt bank,sai a turo shaidar biya ta wannan lambar 09069067488 Wannan karon babu tsarin kati,kowani tsari zaka yi ka turo ta POS,Mutanen mu na Niger kuma zaku tuntubi Kausar Aglan Nissa ta wannan lambar +22796562223*





*Janafty**KANA NAKA..!*


*Wattpad:JamilaUmar315*

*Mallakar:Janafty*

*Arewabook:Jamilaumarjanafty*

*Book 1*


*ASSALAMU ALAIKUM*

*KAYA SUN SAKE SAUKA*.

*INGANTATTUN SAIWOWI DA SASSAKE NE DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZA DA SU*.

*ABIN BIRGEWA BA SAU DAYA AKE AMFANI DA SHI BA*.

*KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR KO KUWA KE DA KANKI ZAKI YI GYARA?*

*INA SAKE YIN ALBISHIR DIN GARIN DAKA MAI KYAU DAN CHADI, SHA DA MADARA KO NONO DA KUMA TSUMIN GAMGAM*.

*GADALIN MATA AKWAI*.

*INA DA TABBACIN INGANCINSU*.

*SANNAN WACCE TAKE SON A DAFA MATA KAZAR, ZA'A DAFA*.

*TUARAREN WUTA NA ASALIN CHADI AKWIA SU AVAILABLE, SAI KIN GWADA ZAKI BADA LABARINSU*

*TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU DOMIN KARIN BAYANI*

*08032773332*.

*NATION WIDE DELIVERY*.

*SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*

🙏.


         *🅿️06*


Filon da nake kwance akai sai da ya jike saboda hawayena,na kara birginawa ta b'arayin hannun haguna domin hannuna na dama yayi min Tsami sai naji kamar na Danne Gefen Kafafun Ahmad dake kwace gefena da Sauri na mike ina kara gyara mai kwanciyarsa barci yake yi hankalinsa kwance domin akwai haske acikin dakin ban riga na kashe ba ina kallonsa ne ammh a kasan zuciyata fad'i nake shi kam ya huta bai san duk wasu walhalhalun duniya da tashin Hankalin dake cikinta ba.

Hawayena har suna d'iga saman cikinsa nayi saurin matsawa ina sharesu da duka hannayena kafafuwna na zuro kasa kafin na dukar da kai na haka kurun nake jin kamar na yi ta rusa kuka da dukkan karfi na,na Dad'e ina so nayi kuka da karfi ammh bansan Kafad'an da kirjin da zan kwanta na rera kuka a lallasheni ba kawai sai na durkushe saman Dadad'den Cafet din dake cikin bedroom dina na fashe da wani marayan kuka hannayena duka biyu na tallafe fuskata da su wani irin kuka ne dake fitar da karar sauti cikin Yanayin da ni ke ciki.

Meyasa zan damu don Ya Ishaq yace zai jingine aure na dashi..?

Na dauki tsawon Lokaci daman ina jiran ranar da zai auro zab'insa na yi tunanin zan fuskanci tozarci ninki ba ninkin wanda nake karba a wajensa da wajen su Mama ammh bantab'a Tunanin zan fuskancin irin wannan cin Fuskar ba duk da nasan kalaman Baba sune suka yi ma wannan auran nawa tsakani da Ishaq sarka ba domin haka ba Tuni ban kawo lokacin nan acikin gidan sa ba.

Menene laifina domin na kasance a yadda Allah yake fatan ya ganni..?

Nayi kuka,kukan da ban taba irin sa ba Tun bayan da abubuwan suka fara zame min jiki sai dai wannan kukan nawa ya sha bambam da na kowani Lokaci na yau ina kukan yadda Rayuwata zata kare ne ni da ya'yana.

Kwarin gwiwa naji yana shigana irin wanda ban taba ji ba alokacin da wata zuciya ta tunasar dani ni uwace ina da ya'ya bai kamata na zama mai Rauni ba in na Raunana ya'yana suma zasu Raunana in na karfafa nima watarana ya'yana zasu zama karfafa.

Nasan Rad'ad'in maraici daga na uba har na uwa Tamadina tana raye ammh ban san Dad'inta ba,bayan Laluranta kaddara tazo ta raba tsakanimu da ita gwara ko wa dani Domin ni kam Ya ishaq ya rabani da kowa nawa ciki da har da uwar data Haifeni.

  In ni nayi maraici ya'yana bazan bari su yi wannan maraicin ba, zan zame musu komai a wannan rayuwar zan zauna na basu tarbiya sannan na zama Tsani wajen inganta rayuwarsu domin sune Duniyata a yanzu bani da kowa daga Allah sai su sai yan'uwana.

Kamar kiftawan ido naji kukana ya Dauke na kurama Bangon Dakina ido ina Lissafin yadda zan fara gudanar da Sabuwar rayuwar da kaddara ta kara Budemin.

Abaya komai lalacewar aure na da Ya Ishaq bai furta zai jingine ni ba ammh ayau ya furta kuma alama ce ta angaji dakai ana neman maraba dakai,ni ba jahila bace ta bangaran addini nasan menene ma'anar Jingina amusulunci,Nasan zai kula da ya'yansa Saboda Dolensa ammh a yanzu ni ban zama Dolensa ba ya zama Dole na sama ma kaina mafita mafitar rike kaina tsayawa ga kafafuwa na ba saboda kaina ba sai Saboda in inganta rayuwar ya'yana anan gaba.

 Ji nayi wani irin karsashin gwarin gwiwa  na kara shiga har cikin Tsokar jikina,Hawayena na share kafin na yunkura na mike,Fuskata nake ta faman gogewa araina ina nanata sunan Allah,Afili na furta"Tunda ka bukaci hakan ya ishaq zan yi maka hakan kamar yadda ka fad'a domin rama alheri da Baba yayi min..Sannan kamar yadda nayi maka alkawari babu wanda zai ji wannan mganar indai daga bakina ne sai dai daga bakin ka da ikon Allah zan zama Jajirtattaciya uwa ba domin na karfafa kaina ba sai domin na inganta Rayuwar ya'yana anan gaba"

Daga haka na fara laluban wayata dake saman madubin Dakin,Na dannata naga 1pm na dare ta wuce biyu saura,sauke wayar nayi nan saman madubin dakin nawa na Tura kofar Tiolet na shiga na dauro alwala nafito nazo na shimfida Darduma na Fara Nafilar da tazame min jiki duk daare na saka yakinin araina Bayan kowani Tsanani Allah na samar ma da bayin sa masu hakuri Sauka'kawa

Abaya in nayi sallolina na cikin Dare ina addu'ar Allah ya shiryamin yarana,ya saka musu tausayin junansu aransu,ya inganta goben su ya saka musu albarka acikin karatun su,Sannan na kan roki Allah ya sausauta zuciyar Ya Ishaq a kaina Ya sa ka Mama tasoni ta kaunaceni,ammh daga daran yau sai na sauya alakar addu'ata na roki Allah ya bani karfin gwiwa ya ciremin rauni da karaya yasa na tsaya nayi tsawon rai da zan zama Bango abun jigina wajen ya'yana na roki Allah da kyawawan sunayensa Chasa'in da tara akan ya tayani Tarbiyan y'ayana ya kular min da su ya zama gatansu ya tausaya musu ya shiryamin su duniya da Lahira yasa su zama abun alfaharin al'umma da musulaimai gabadaya.

Ban kwamta ba sai wajajen karfe uku na Dare,shima Ahmad ne ya farka da kuka na isa garesa na Daukesa na Fara Lallashinsa ganin yaki daina kuka sai na bashi Nono yana kamawa sai shuru ashe yunwa ce yana koshi sai barci,Garin nima na shimfid'ar da shi sai barci ya kwasheni sai jin Mganar Hafsatu nayi a kaina tana ta kiran sunana Lokaci d'aya tana Buga kafafuwana..

Firgigit din da nayi na farka sai da Ahmad dake rumgume dani ya farka shima a tsorace sai ya fashe da kuka mikewa nayi ina mika Sosai Hafsatu kuma na Tsaye a kaina ita ta D'auki Ahmad tana fadin"Kai sarkin kuka ai garin ka ya waye"

Sama sama na jita mikewa nayi a kasalance,na sauko daga kan gadon cikin yanayin mganata nace"Lokacin sallah ya yi ne..?

Tana zama gefen gadon da Ahmad a Hannunta tace"Eh har su Ya Ishaq sun tafi masallaci da su Amir yau kin makara"

Da karfi tayi mganar shiyasa na jita idanuwana na mutsike bina da kallo tayi lokaci d'aya tana nazarina kofar Tiolet na Tura na shige na rufo alwala nayi a gurguje na fito na iske tana cire ma Ahmad Pampers naji tana fadin bai ma yi komai aciki ba.

Ina kokarin Tada sallah domin har na sanya Hijabi na juya ina kallonta Lokaci daya ina fadin"Ha..Hafsatu..Kin yi sallar ne..?

Kai tsaye tace"ina Hutu dame zan taimaka miki kafin ki idar da sallar..?

Shuru nayi ina nazarin abunda zasu tafi da shi makaranta babu cefane komai ya kare hatta lemun yaran da Biskit sai kawai cikin yanayina nace mata"Babu indomie ta kare dafa musu farar shinkafa ki yi musu amfani da miyar nan"

Da toh ta amsa min ta fice Dauke da Ahmad ni kuma na tada sallah sai da nayi raka'atul fijir sannan nayi sallar asuba ina cikin azkar sai ga Anum ta shigo da karamin hijabinta alamun itama tayi sallan ne bayana ta D'ane tana fadin"Umma ina kwana"

Yaran sun san raunin jina in zasu yi min mgana sai sun daga murya musamman Anun da Amir.

Mirmishi na saki na saka hannu na Jawota gabana, na zaunar da ita ina Fadin"Ina kwana Anum d'ita"

Lokaci d'aya ina jan kumatun ta Anum irin yaran nan ne masu yawon tsiya in suna mgana sai ka zata ana gaya musu ne.

Kuri tayi min da ido ni kuma hankalina na kan littafin azkar din dake Hannuna ina karantawa sai ji nayi kamar daga sama tace"Umma kuka kika yi ko..?

Waya dake ki..?

Ban ji mamakinta ba sanin Halinta da Sauri nace"A'a wani kwaro ne ya fadamin a ido Anum."

Da Sauri ta bata rai kafin tace"ko Daada ne ya yi miki Fad'a?

Shuru nayi ina bin ta da kallo yarinya ce yar shekara biyar da wannan mganar ina laluban amsan da zan bata sai ga su Amir sun shigo yana rike da Hannun Musty dukkan su jikina suka fada Amir dai gefe yayi agabana kusa da Anum yazauna Musty daman akwai son jiki shi ya lafeni sai na rike sa ina jin wani Farinciki in na Tuna nima uwace ina da iyalaina da zasu iya zama abun alfaharina watarana.

Amir ne ya daga murya yana fadin"Ina kwana Umma"

Na amsa masa ina shafa kansa Musty ma da gwarancinsa ya gaisheni na amsa ina Dariya zama na gyara ina Fadin"Kun yi azkar din Safe..?

Amir yace"Umma Daada bai barmu mun yi a masallaci ba ana ta kiran sa a waya sai muka dawo gida"

Amir da kasafai ya cika mgana ba, sai in yaga dama,ban ce komai ba sai na kauce mganar nace su karanta azkar din su na Safe kafin Lokacin wanka yayi.

Nan suka zauna gabana suna karantawa in da suka yi kuskure sai na gyyara musu har Musty da bai gama iya mgana ba yana ta garancinsa.

Muna cikin Hakane Hafsatu ta shigo tace ruwan wankan su yayi zafi sai nace ta bari zan yi musu wankan ita taji da abun karyawan su.

Ko kafin bakwai na Safe gabadayan su sun shirya cikin Uniform din Tahfeeez din su,Babansu ban gan shi ba Domin tun jiyan nan bamu sake had'uwa ba.

Farar taliyar Hafsatu ta dafa musu sukaci da Sauran miyan jajjagen da nakedashi,Sauran kuma nace ta saka musu a basket din su babu lemo ko Biskit sai kawai nace ta dura musu aruwa a gororin su.

Suna zaune afalon suna cin abincin ni kuma ina gyara ma Anum littafanta da ta wargazasu,Ahmad na bayan Hafsatu yayi barci tun da yaji Ruwan zafi ni ban yi wanka ba Hijabin da nayi sallah ne dogo ajikina.

Hafsah na Durkushe gaban Musty ta na bashi abinci abaki Anum sai ta rika Sako hannu tana d'ibar masa abincin sa da karamin Fork din su farare na cin abinci shi kuma sai ya fashe da kuka daman duk ya fisu Rigima.

Hafsah ta gaji da mgana ta kai ma Anum Rankwashi akai tana Fadin"Babbar banza wacce bata san kaninta ba"

Ni ban jin me suke fadi ina dai kallon su Lokaci bayan Lokaci ina Mirmishi sai kukan Anum naji kamar wacce ake yankata na saki littafin Hannuna na mike a firgice da yanayin mganata na fara tambayan Hafsah me ya faru Hararan Anum tayi kafin ta fara min bayani ta karishe da fadin"Anty Fa'iza rankwashinta fa kawai nayi shine ta wani yanka mana ihu kamar ana yankata in baki ma mutane shuru ba sai na bige ki yanzu nan"


"Karki kara dukar min yarinya kada ki Sake Hafsah.."


Kamar daga sama domin mu dai bamu san fitowarsa daga shashensa ba dagani har Hafsa mun ji mganarsa Saboda a kausashe yayi maganarsa,Da sauri dukkanmu muka juya muna kallonsa yana sanye da Jallabiya mai ruwan madara Kansa ba Hula fuskar nan nasa kamar ko yaushe a had'e,Anum na ganinsa ta tashi da gudu ta nufesa lokaci d'aya ta fad'a jikinsa cikin sangarta da shagwaban da ya bani mamaki tace"Daada kaga Anty Hafsah ta Dake ni ko..?

Riketa yayi Lokaci d'aya yasa ka hannu ya Dagota ya riketa a hannunsa ya Tako falon duka yaran suka mike suka bar abincin gabansu suka nufesa suna fadin"Daada.."

Zama yayi kan daya daga cikin kujurun falon yana Daga musty shima ya Daurashi kan cinyarsa Amir ne kawai ke tsaye a gabansa.

Kansu ya Shafa gabadayan su yana Fadin"Eyee..Ya'yan Daada yan makaranta..Mutsy me kaci haka bakin ka duk maiko.?

Da yanayin mganarsa yace"Chaliya"

Dariya yayi yana kwaikwayonsa Hafsah ce ta rankwafa ta gaisheshi ya amsa yana wani had'e rai nima na gaisheshi ya amsa a Dakile.

Kallonta yayi kafin yace"Hafsah ba na so ana dukan min ya'yana..Bana so..Har nawa Anum take da zaki dake ta.?

Hafsah mamaki ya kamata cikin mamakin tace"Rankwashin ta kad'an nayi akai kuma musty take sawa kuka"

Kai tsaye yace"Nace dai bana so kiyaye Ok"

Kai ta dagamai cikin wani yanayi kafin ta Dago ta kalleni sai naji wani iri araina ashe Ni ma kenan bazan iya Hukunta Anum ba tunda Hafsah ai kanwatace,Ahmad ya tambaya tace gashi a bayanta yayi barci daganan ta shige Daki jikinta duk ba Dad'i sai naji ban ji dadi ba sama sama nake ji yana Hira da ya'yansa ni kuma ina Had'a musu jakunkunansu waje daya na shiga kitchen na fito musu da Baskets din su guda uku nazo na ijiye ina Fadin"Anun Amir Musty kowa yazo ya Dauki jakarsa da abincinsa"

Amir da yazo ya Dauki nasa na taimaka masa ya rataya jakarsa,Anum kuma sai ta fara rigiman ba Biskit ba lemu.

Ya ishaq ya Dago yana kallona ni kuma kawai sai na Dauke kai na cikin Yanayin mganata na yi mata tsawa ina Fadin"Anum zan saba miki fa yaushe kika koyi rigiman ban..za.?

Kuka take neman ta sakamin sai na ware mata idanuwana na Daga Hannu kamar zan daketa sai ta yi shuru tana kallon Uban nata nima nasan ni yake kallo sai naki yarda na kallesa kada tsoron sa yayi tasiri a kaina.

Cikin Fadansa yace"Ammh kina ji na fada ma kanwarki bana son ana dukamin ya'ya shine zaki kwantata agabana ko Fa'iza...?

Kaina na kasa kawai sai nace"Ka..kayi hakuri"

Sai na koma na zauna,Kallona yayi kafin yace"Meyasa ba Biskit ba lemu a basket din nasu..?

Kai tsaye nace"Babu sun kare gabadaya"

Cikin Fad'a ya fara fadin"Gaskiya kina da matsala..Ke shikenan kamar ba mace ba..?komai na Dubaran mata baki iya ba..?to sun kare da kika yi shuru da bakin ki baki fadamin ba ke zaki siyo ki kawo..?

Ya karishe fad'a cikin hayaniyar mganar dayace saboda yanayina ya koya kaina na kasa na kasa mgana suma yaran sai suka yi shuru duk sun yi tsuru tsuru.

Fad'a ya cigaba da yayi yana fadar duk mganar da tazo bakinsa ya karishe da Fadin"Ya'yanki ma baki san yadda zaki kula da su ba Fa'iza to meye amfaninki..?

Komai naki zero ne baki da wani amfani wlh aikin banza kawai"

Dagowa nayi ina kallonsa Hawaye sun cikamin ido bana so su zubo saboda yaran duk sun kuramana ido Kama hannun Anum da Musty yayi yana Fadin"Muje zan siya muku a hanya ku jira anan bari na dauko key din mota dina"

Kai suka gyada mai ya juya ya koma Shashensa yana ta tsaki yana shigewa hawayena suka kawo sai na kauda kaina ina kokarin sharewa sai jin Hannun nayi a kan fuskata ina dagowa naga Amir cikin Wani yanayi da Sauri na kakaro mirmishi ina Fadin"Amir..kwaro ne ya fada min a ido"

Bai ce komai ba yasa Hannu ya Sharemin hawayena Lokaci daya yana fadin"Kiyi hakuri Umma"

Kawai sai naji wani Dum acikin kaina jikina yayi sanyi nabi Yaron da kallon Duka duka shekarun Amir bakwai ne ammh yasan ya ganni ina kuka ya sharemin hawaye ya bani Hakuri kawai sai naji wani abu ya tasomin daga kasan raina bansan Lokacin da na kamasa na Rumgumesa ba da dubara ina Dauke Hawayen idanuwana.

Mganar Ya ishaq kawai naji a tsakar kaina yana fadin"In bazaki barsa yaje makarantar ba ne sai ki gayamin na tafi na kai masu zuwa"

Da Sauri na sake sa ina shafa kansa a sannu nace"Kada ku manta ku yi addu'a"

Suka gyadamin kai,Gabadayan su suka dagamin hannu kafin ya tasasu su fice,bayan fitan su na Dade zaune ina Tunanin rayuwa kafin na mike Dakin Hafsah na shiga na isketa ta shimfidar da Ahmad nata barci ita kuma tana Hada kayanta a karamar Jakar gabanta na tsaya ina Fadin"Yau zaki tafi.?

Mganata yasa tasan na shigo ta Dago tana fadin"Eh Yau goggo tace na dawo gobe muna da makaranta"

Gefenta na zauna na Dafa kafadarta ina fadin"Kiyi hakuri kin ji Hafsatu.."

Mirmishin da yafi kuka ciwo tamin kafin ta kalleni Lokaci d'aya tace"Ni mai sauki ne Anty Fa'iza kece za'a bama Hakuri..Allah ya kara miki Hakuri"

Ban ce komai ba sai mirmishi da nayi shuru mukayi na wani Lokaci kafin tace"Zan biya ta Dutsenmah na Duba Tamadina na riga na fadama Goggo zan biya tachan"

Kai na gyada mata kafin nace"Kice ina gaisheta nima in sha..Allahu zan..zan zo na Dubata"

Da kai ta amsa min kafin tace"Allah yasa"

Bamu cigaba da Hira ba na mike na koma kitchen na dora ma Ya Ishaq ruwan tea bayan ya tafasa na juye mai a falas ba komai na cefane har kwai ya kare wani sauran dankali ne bashi da yawa na fere na soyamai sai namai miyar albasa,na tattara komai na kai Shashensa na shiryamai afalonsa na fice Ganin Hafsa ta karbi gyaran gidan ni kuma sai na kwashi wankin yaran da suka taru naje bayan  inda tankin ruwa da famfo yake yi na Fara wanki Uniform na fara wanke musu da Hafsah ta gama sai tazo ta sameni tana tayani sama sama muna Hira,Saboda yanayina Allah yasa bani kuma da yawan mgana sosai


Muna cikin wankin Ya Ishaq ya Leko dauke da Ahmad a Hannunsa yana fadin"Sai ku bar Cikin gida ba kowa sannan ku bar yaro shi kadai adaki..?

Wannan wani irin rashin Hankali ne..?

Da Sauri na tsame Hannuna a ruwan Sabulu na karisa wajensa na karbi Ahmad ya juya batare da yayi min mgana ba sai nabi bayansa muna zuwa Falo ya tssya ya juyo yana kallona Lokaci daya yana fadin"Ga cefane nan..Ki lallaba kinsan ina da Hidima yanzu haka wajen Milyan daya zan yi ma Anty Binta ciko na Hidiman bikin nan sannan ba Lalle na kara miki wani cefane ba sai karshen wata"

Da kai na amsa mai kafin a Sannu nace"Angode Allah ya saka da alheri"

Ko amsa ni bai yi ba yayi gaba daidai Lokacin da wayarsa tayi kara kafin ya shiga ya Daga wayar kasa kasa yayi mganarsa ban ji ba.

Zama nayi na bama Ahmad Nono na maidasa baya na kwantar Domin bazai yarda na ijiyesa ba.

Na dauki Ledojin na shiga da su Kitchen Katan din Bobo ne sai na maltina sai Biskit kwali biyu sai Na ruwa faro sai kwai da doya sai Dankalin Turawa sai kayan miya,na Zazzage komai na jera a muhallinsa

Sannan na koma muka cigaba da wanki ni da Hafsah duka sai da muka wanke har da nawa muna bayan Ya Ishaq ya fice daga gidan bamu sani ba fitowa kawai nayi naga bayanan sannan ba Motarsa nasan bazai wuce gidan Mama ba..ga Hafsah zata tafi bani ko da naira Biyar balle na bata na Mota.

Ina so na bata wani abu ta kaima Tamadina bani da komai sai na Dibar mata Sabulin wanka da na wanki muna da Sauran su bai kare ba, nace ta kai mata,mganar kudin mota kuma tace min kada na Damu goggo ta bata 3k da zata taho zasu isheta ta koma Gida ina ji ina gani Hafsah ta tafi ni na rakata har kofar gida muna Daga ma juna Hannu.

Na dawo cikin gida Nepa sun kawo wuta na zauna na fara gugan kayan Su Amir saboda sai yammah zasu dawo,haka ma Ya ishaq sai da yammah sai nayi Tunanin sai da yamah nayi girkin ni kuma Daman cikina ya cushe hafsah kad'ai taci taliyan nan na Safe ni kuma sai na barta sai an juma.

Ban tashi Daga wajen nan ba sai da na goge rabi da kwatan kayan nan tas sai wad'anda basu bushe ba kawai Sallah kawai ke tadani sai bayan Sallar la'asar na tashi daga wajen shima Saboda girki ne.

Sai alokacin nayi wanka na saka wata bubar doguwar rigar wata atamfa da Yaya Asiya ta dinka mana mu hudu har da ita.

Na shiga kitchen na fara Tunanin me zan sarrafa sai kawai nace bari nayi jallop din shinkafa tunda ina da Sauran kayan lambu sai na Hada da su,Naso na hada ko lemu ne to bani da kankana ba aya ba abarba ba Sinadrin hadawa kayan zobo kuma Daman Badariya ke siyon irin wad'anan abubuwan duk Ya Ishaq baya siyan su sai abunda ya zama Dole.

Sai da na gama komai naje nayi sallar mangariba Allah ya taimake ni Ahmad yau barci ya yini yi bai yi rigima ba Tunda naji su Anum shuru nayi Tunanin Babansu ya Dauko su suna gidan Mama.

Shiyasa na idar da sallah sai na fara jera ma kowanne kayan sa a dirowansa ina Dakin wayata na kara ammh ban ji ba sai chan sama sama naji karan a cikin kaina.

Na daukota na Duba Goggon Karofi ce Ina hada Hausa Ina karantawa wanda bai da wahala sosai in dai kamar na sune ko mgana wacce ba'a rubuta tayi tsawo ba.

Ina Daukan kiran na sakata a speaker Hafsah ce muka gaisa tace ta Sauka lafiya taje wajen Tamadina taji sauki tana ta godiya Daganan ta bama Goggo muka gaisa ta yi tamin nasiha daman ita nata kenan Fadi take yi "Fa'iza ki yi hakuri kin ji ko..?Allah bai manta dake ba..In sha Allahu zaki ci Ribar wannan biyayyar taki"

Shuru nayi ban ce komai ba ta yi ta bani Misalai da matan da suka yi Biyayya agidan aure sannan suka Rabuta ranar Lahira hawaye suka kawo Cikin idanuwana ina tuna Baba a mganarta shima duka kalamansa ne..daga karshe tace min"Naji Isahaq zai kara aure ko..?to sai kin kara Hakuri Fa'iza daman abunda Saudatu take nema ne ya samu ki koma gefe ki rumgumi ya'yanki Allah yayi albarka Allah ya baki Dangana"

Ina share hawayena nace"Ameen Goggo ammh dai zaki zo ko..?

Goggo tace"To sai nagani in zan samu zuwa ammh yara zasu zo su zauna Dake"

Daga haka mukayi sallama na koma na cigaba da aikina naki bari Tunanin auran nan ya shiga zuciyata.

Tun ina saka ran dawowar su da wuri har na sare gani  har Tara tayi nayi sallar isha'i nayi ma Ahmad wanka har yayi barci nima wanka na Sake yi na saka Riga da wando masu taushi na barci Diyar Goggon karofi Anty Nasara ta kawo min su Tsaraban Umra.

Ina zaune afalo ni kad'ai kamar mayya naji Hayaniyar yaran da shigowar su dukkansu jikina suka fado suna murna nima na rike su ina Mirmishi Tun kafin nayi mgan Amun tace"Umma Gidan Mama fa Daada ya kaimu"

To daman yana da inda yafi gidan Maman ne..?

Suka fara gwadamin Tsaraban Kayan lashe lashen da ya siya musu sai ga shi ya shigo yana shigowa da sallama bai ko bari na amsa ba ya fara fada yana fadin"Don iskanci kina ji ina ta Hon bazaki iya fitowa ki budemin get ba..?

Ni wlh har ga Allah ban ji ba cikin sanyina nace"Ban ban ji ba wlh..kayi hakuri"

Tsaki kawai yaja ya wuce Shashensa yana fadin"duk kin ji..ai ba hayaniya a inda kike balle ki fake da Lalurarki"

Ina jinsa ban ce komai  ba sai ma kirkiri mirmishi Saboda yaran kada su Fahimci wani abu,ni ke kokarin kauce ma wasu abubuwan ammh yadda Ya ishaq baya jin kunyar tozartani gaban ya'yana in da ina Biyesa da tuni yaran tun tashi da shi a ransu,sai dai in dai suna wajen da ya fara fadansa zan yi saurin ba shi hakuri na nuna komai ba komai ba ne.

 Kayan makarantan su nace suje su cire kafin su ci abinci sukace min sun sha tea agidan Mama.

Suna shigewa d'aki ni kuma nabi Ya Ishaq Shashensa kada yace ya dawo nayi banza dashi daman na hada mai abincin sa tuni na kai mai shashensa.

Koda na shiga yana Cire kayan jikinsa sallamanta ma aciki ya amsa min na Rankwafa ina mai Sannu da zuwa ya amsa sau d'aya ya dauke kai ya Tura kofar Tiolet ya shige ni kuma sai na karisa cikin bedroom din na Tattara kayan daya cire na ninke mai na bude Wardrope dinsa na sakamai na gyara mai Dakin Dazu daman saboda bai bar key din bane shiyasa.

Ina Dakin ya fito yana Digan ruwa da Sauri na Dauko mai Towel na basa ya amsa yana Goge jikinsa Lokaci d'aya yana kallon kayan jikina ni kuma ban ma Lura ba wardrope dinsa na Bude ina Fadin"Jallbiya zan dauko maka..?

Kai tsaye yace"Bar shi kawai"

Ban damu ba na rufe na koma gefe na Tsaya kaina na kasa kamar Daga sama naji yace"Ina kika samu wad'anan kayan barcin kuma..?

Shuru nayi kafin nace"Anty..Na..Nasara ta kawo min Tsaraban Um umra."

Tabe baki yayi kafin yace"Shi yasa da zata baki sai da ta zabo kalan da zai yi daidai da yanayin ki.. Green wannan kayan ba su yi ba ammh ke kin ga abun sawa da sunan ki yi ma mijinki kwalliya dashi.."

Sai naji na muzanta duk da ya saba kusheni ammh na yau sai yafi Dafani barin ma da ya kara fadin"Kwata kwata na rasa wani abu ne zaki saka ya Dace dake Fa'iza..Alhamdulillah da Allah ya bani Zeey yarinyar mayar dressing ne komai tasa ajikinta sai kin ga kamar don ita aka Hallici kayan zata zo kuga juna don Allah in kun had'u ki fara D'aukan gyara daga kanta"

Kaina sai da ya yi Dum jikina sai yayi min ba Dadi ammh ban nuna ba kayan jikina na kallah har ga Allah  ni ban ga Aibun su ba kore ai kalan yan aljannah ne sai dai daman shi tozarcin sa ba inda baya tashi.

Da naga zai saka kaya sai na fice abuna na zauna afalo ina jiransa haka ya fito yazo ya zauna ya fara cin abinci sai da ya gama sannan na kwashe komai na kai kitchen na koma nayi mai sai da Safe naga yana waya da Hannu kawai yayi alamun naje ni kuma na fice na koma Dakin yarana na iske Amir na koyama Anun aikin da aka bata a makaranta Musty har yayi barci na gyaramai kwanciya na mai addu'a na koma cikin su Anum na zauna ina ganin abunda suke yi ina mirmishi sai da suka gama na saka Amir yaje yayi fitsari shi da Anum suka kwanta muka karanta addu'an barci atare suka Shafa na gyara musu kwanciya  na rage musu fanka na kashe musu wutar Dakin na fita zuwa D'akina na gyarama Ahmad kwanciya nima na kwanta agefensa ina addu'an barci.

Karfe uku na dare yau na tashi nayi Nafilfiluna sannan na fita naje na tashi su Amir,sai ga Baban su ya fito suka tafi masallaci ni kuma muka yi tamu ni da Anum agida.

Kamar yadda n Saba kafin bakwai din Safe sun shirya cikin kayan makarantar su Ahmad na bayana sai rigima yake yi,Ba ya ishaq zai kai su ba Haruna mai adaidaita ne wanda ya saba kai su  baban nasu yau zai koma Abuja.

Shashen shi suka je suka mai sallama sannan suka fito ni na saka Hijabi na rakasu har waje muka gaisa da Haruna sannan suka shiga suka wuce ina Dawowa a gurguje na had'a ma Ya Ishaq abun karinsa buredi da kwai na Soyamai sai ruwan tea na kai mai Shashensa ya fito cikin shirin Tafiya sanye da Suit bakake ya tsuke kamar ba shi ba har da wani damfararen bakin glass na ba mutumci.

Yana zaune yana karyawa ina Gabansa Ahmad na Hannuna ina Lallashinsa sai da ya gama sannan ya mike yana fadin"Fa'iza zan tafi kuma kila sai satin biki zan shigo.karbi ki ga."

Kudi ya miko min yan Dubu na saka Hannun na karba ina godiya Karamar Jakarsa ya Dauka na mike ina Sabe da Ahmad zan karb'a da Sauri yace"Kada ki damu da wannan..Ki kularmin da yarana in akwai wani abu ki kirani a waya..koda yake nasan zaki kira indai kina da bukatar wani abun"

Nidai ina biye dashi har Haraban gidan Ahmad ya karba yayi masa sumba kafin ya miko min shi Sai da ya shiga mota sannan ya Leko yana fadin"Anty Binta zata aiko miki da kayan fitan biki da wasu kaya da ta matsa sai na siya miki in ma da wani abu zaki ji wajen su Mama na tafi..Ban da yawo..Fa'iza gidan Mama da Gidan Anty binta kad'ai kike da izinin zuwa ki Kiyaye"

Daga haka ya rufe motarsa lokaci daya yana fadin"Ki budemin get"

Haka na tafi zugwi zugwai ga goyo a bayana,na saka karfina na bude mai get ya fice na bisa da Allah ya kiyaye hanya na maida get din na Rufe ina Haki sai da na koma falo sannan na Kirga kudi Naira dubu biyar itama nasan Saboda matsalan yara ne daman duk sati in yazo haka ya ke bar min.

Kuma kafin ya Dawo ta kare ko Kudin motar da nake zuwa gidan Mama ko Anty Binta sannan ga Dawaniyar yara yau Anun tace bata da pensil gobe Amir yace zai siya Drowing duk anan kudin ke tafiya.

Tunda ya tafi sai na maida Hankalina wajen kula da ya'yana Kwana Hudu Tsakani da Tafiyar Ya Ishaq Anty Binta ta kirani a waya mu hadu agidan Mama ranar jumma'a da Safe bayan su Anum sun tafi makaranta na shirya na tafi bayan nace ma Haruna gidan Mama zai kawo su Anum in ya Dauko su daga makaranta.

Naje na iske gida cike da kawayen Mama ana ganin kayan lefen da za"a tafi dasu Abuja agobe.

Akwatuna goma shake da kayan alfarma ni ko Aleda Anty Binta ta bani nawa Less d'aya atamfa biyu sai takalmi sai Hijabi na karba da Hannun Biyu ammh sai Mama ta harareni tana fadin"Naga kin karba a wulakance kin raina ne..?

Kaina na kasa na kasa mgana Hajiya Barira aminiyar Mama tace"To ina Laifi wannan kayan Hajiya Saudatu..?ai wlh naga kokarin Ishaq ma matar farko ai ba kowa ke wani wahalar da kai akan su ba"

Mama ta tabe baki kafin tace"Matar ma irin wannan abar ba.."

Suka kwashe da Dariya suna nuna ni, Anty Binta ta kyabe fuska tana Fadin"In ma ta raina ita ta sani..Kila wad'anan take kalla ai inda suka dace za'a kai su Yarinya ba inda basu dace ba"

Ni dai kazil ban ce ba Saboda suna so naji cin mutumcin su da karfi suke mganar su,Haka suka sallameni na kwashi kayana zuwa Dakin Badariya bata nan tana makaranta.

Ba domin nace Haruna ya wuto da su Anun nan ba da gida zan koma saboda su yasa na jira sai da suka Dawo nazo musu da kaya suka sauya ni nayi girki daman indai nazo to kamar jaka haka take komawa agidan Mama.

Sai La'asar na koma gida ni da ya'yana da kayan da Anty Binta ta bani duka an dinka su daman,Washegari kuma Badariya tazo take gayamin an tafi kai lefe har da Hajiyar Dala da Anty Binta da Hajiya Barira kawayen Mama.

Sai fada take wai ba su sanar da Goggon karofi ba araina nace ita din banza ai in dai su Hajiyar Dala na waje kowa ma bai da kima a wajen Mama.



*Littafin KANA NAKA Book 2,3paid book ne biya kudin karatun ki akan Naira N500 Regular posting sau d'aya a rana.*

*Ko kuma tsarin VIP 1000 Posting sau biyu a rana akan wannan acct din 0552179550 Jamila Umar Gt bank,sai a turo shaidar biya ta wannan lambar 09069067488 Wannan karon babu tsarin kati,kowani tsari zaka yi ka turo ta POS,Mutanen mu na Niger kuma zaku tuntubi Kausar Aglan Nissa ta wannan lambar +22796562223*




*Janafty**KANA NAKA..!*


*Wattpad:JamilaUmar315*

*Mallakar:Janafty*

*Arewabook:Jamilaumarjanafty*

*Book 1*


*ASSALAMU ALAIKUM*

*KAYA SUN SAKE SAUKA*.

*INGANTATTUN SAIWOWI DA SASSAKE NE DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZA DA SU*.

*ABIN BIRGEWA BA SAU DAYA AKE AMFANI DA SHI BA*.

*KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR KO KUWA KE DA KANKI ZAKI YI GYARA?*

*INA SAKE YIN ALBISHIR DIN GARIN DAKA MAI KYAU DAN CHADI, SHA DA MADARA KO NONO DA KUMA TSUMIN GAMGAM*.

*GADALIN MATA AKWAI*.

*INA DA TABBACIN INGANCINSU*.

*SANNAN WACCE TAKE SON A DAFA MATA KAZAR, ZA'A DAFA*.

*TUARAREN WUTA NA ASALIN CHADI AKWIA SU AVAILABLE, SAI KIN GWADA ZAKI BADA LABARINSU*

*TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU DOMIN KARIN BAYANI*

*08032773332*.

*NATION WIDE DELIVERY*.

*SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*

🙏.



            *🅿️07*


Bayan ta gama fad'an rashin gayama Goggon karofi sai ta koma fad'an kayan da aka bani bayan tace na dauko mata ta gani Badariya karama ce acikin ya'yan mama ammh da ace itace Babba da abubuwa da dama sun gyaru tana da kyakyawan zuciya da Hali mai kyau.

Ina kallonta ta d'aga kayan a rene tana tabe baki kafin tace"Yanzu Anty Fa'iza abunda suka baki kenan acikin Uban kayan akwati goma da suka tafi kaiwa Abuja..?

Duk da ba duka naji mganar ta ba,ammh na dauki wasu,Sannan ina Bin bakin wanda na saba mgana dashi na kan Fahimci abunda yace ko da ban ji ba.

Ban ce mata komai ba sai ma wani mirmishin takaici da nayi,na sani ko Lokacin aurena ya ishaq bai min lefe ba ballatana yanzu ba da bani zai aura ba,Daman a wanchan Lokacin Baba ne ya matsa masa akan sai yayin lefe ba Sadaka ya aura masa ni ba, awanchan Lokacin Mama ta shiga mganar tayi ruwa tayi tsaki akan ita da kanta zata had'amin lefe nagani na Fad'a da ya kara tambayata sai tace tuni ta bama ya ishaq ya kaimun kaya ahalin kaya ko kala goma basu kai ba sannan saukakku dai ba masu tsada ba daman tun a baya na fada muku Baba shi ba magidanci ba ne mai bin diddigin abunda ke faruwa a cikin gidansa ba  shiyasa wani Lokacin Mama kan yi nasara a kansa da kuma kila an yi masa surkullen mutanen yamai.

Ni ban damu ba saboda ba kayan ba ne a gabana, ko su bani ko kar su bani bazai kankare yadda bani da Daraja a idanuwan ya ishaq da su kansu ba.

Har ta gama fadan ta ban bude baki nayi mata mgana ba to me zan ce..?duk abunda zan ce alokacin bashi da amfani Saboda ajiyan agaban Mutane Anty Binta ta kara maimaita Dakyar ta lallaahi Ya ishaq ya amince ya siyamin ma kala ukun da aka bani Domin da farko cewa yayi bazai siya ba Saboda ko ya siya zai yi asara ne ban san Darajan su ba sai da tayi ta basa baki sannan ya amince to saboda mene zan damu..? Awannan gabar da auran mu ya zama jingina ba lalle ne Hakkokina su rataya a wuyansa ba ni ba Dolen sa ba ne yanzu Saboda haka raina ya daina Damuwa kan duk Tozarcin da zai aikata agareni.

Kuma na kudiri araina bazan saka kayan sa ba,Akallah dai zan fara Dogara ga kaina ko Saboda ya'yana na fara Tunanin zamana ahaka bazai yuyumin ba in ya'yansa Dolensa ne,ni na tashi adolensa bazan bar gidansa yanzu ba Saboda lokaci bai yi ba ya'ya na suna Bukata ta, sosai in na tafi na bar su basu da wanda zai kula da su da Tarbiyan su ina tsoron su tashi Cikin maraicin uwa kamar yadda muma muka tashi cikin wannan maraicin muna da uwa a raye ammh kamar bataa raye ne a wajenmu.

Tattara komai nayi na tusa cikin Wardrope d'ina ban kuma yarda nayi mganar da kowa ba Daman Ya Asiya ce kadai take kirana kan Sha'anin Bikin Yaya mariya ko sau d'aya bata kirani ba ita ta na da Zafi ne Ko zuwa tayi had'uwa goma sai sun yi Cacan baki da Anty binta gata irin tanada Sauri Saurin mgana ne kafin Anty Binta ta fadi daya ta maida mata Biyar Shiyasa bata cika zuwa katsina ba sai da Dalili mai girma waya kuma bamu cika mgana ba Saboda abu kad'an zataji ranta ke baci kuma bata da Hakuri ko kada'n.

Biki nata karatowa barayin su Mama suna ta shirin su gayya Mama tayi bani da Gayya ba Domin tace sai yanzu ta san Ishaq zai yi aure ni ina gida bansan halin da suke ciki ba,bani cikin kwanciyar Hankali Saboda ina ta mafarkin Tamadina sai na tsorta kada tazo ta mutu itama bamu gana ba sai na fara Tunanin ya kamata naje na gaisheta na Dubata Saboda mahaifiyata ce in na rasata a wannan gabar sai nafi kowa kuka Saboda dani kad'ai ne bata gana ba.

Na fara Tunanin Tafiya sai dai matsaalan kudi ne Dubu daya da Dari Biyar suka Ragemin a hannuna cikin Dubu biyar din da Ya Ishaq ya barmun da zai tafi sannan Tunda ya tafi ko sau daya bai kirani yaji Halin da muke ciki ni da yara ba nima kuma ban kirasa ba Sai dai na riga na kuduru niyyar zuwa gaida Tamadina Cikin Satin nan da zai shiga kafin Lokacin Bikin yazo.

Na shirya tafiya ta Ranar asabar in su Amir sun tafi Hadda,Shiyasa Ranar jumma'a da Daddare na yi ma Ya Ishaq flashing Saboda wayata ba kati na ma manta Rabon da na saka mata kati ba na kira daman sai dai mai son mgana dani ya kirani bansan adadin Flashing din da nayi masa bai kira ba sai chan naga kiransa na dauka jikina na rawa na saka ta a amsa kuwwa na kara kunne tun kafin nayi mgana ya Dakamin Tsawar da sai da tasa na razana Cikin Fadansa yace"Haba don Allah wai meye haka Fa'iza..? Sai flashing kike yi min tunda kika ga ban kira ba ai kinsan ina wani abu mai muhimmanci ne ko ina tare da wani mutum mai muhimmanci ke duk abunda kika fara Hankali bai isa ya baki ki bar shi haka ba..?

Sai naji kwallh ta ciko cikin kwarmin Idanuwa na cikin rawan zuciya da na Murya nace"Kayi..ka..yi hakuri..Ban..Sani ba ne.."

Karamin tsaki yaja kafin yace"Zan kiraki in na koma gida ina tare da Zeey ne.."

Daga haka ya katse wayarsa ina jin muryanta kafin ya katse tana fadin"Honey kai da waye kake ta Ihu haka..?kamar a kusa da wayar tayi mganar shiyasa na ji ta.

Ban ji me yace mata ba ya katse kiran sai na Sulale gefen gadona na fashe da kuka Allah yasa yaran duk sun kwanta har ta Ahmad yayi barci kuka nayi wanda naji ya isheni nasan bani da wata Daraja a idanuwan Ishaq ammh ban dauka har agaban wacce zai aura ma bani Daraja ba ,Sai na fara tunanin wani irin karb'a amaryan sa zatayi min in muka fara Had'uwa sannan me ya fada mata akaina..?

Wata zuciya ta amsamin ya fad'amata ke bakomai bace face bebiya mummuna baka mara gata sannan mara ilimin zamani wacce bata da komai atare da ita tuna haka yasa kuka na ya karu bansan tsawon Lokacin da na Dauka ina kukana ba sai da nagaji sannan na tashi na Shiga Tiolet na wanke fuska ta na fito na k'i yi barci ina jiran kiransa na riga na sakama raina Gobe zan je na Duba Tamadina kuma ba yadda zan iya tafiya batare da izininsa ba..

Bai kira ba sai wajen sha d'aya da Rabi na Dare sannan ya kirani ina D'auka fada ya hauni da shi wai ni bai san me nake yi ba sannan bani da Hankali komai ba cikin lissafi nake yi ba ni dai Hakuri nayi ta basa sai da ya sha iska ya gama wulakacin nasa sannan yace"Ina yara na..? Ina fatan suna nan cikin koshin lafiya ko..?

Nayi saurin amsa mai da suna lafiya jin nayi shuru yasa yace"Fa'iza fadi abunda yasa kika addabeni da Flashing ina da shiga office da Safe zan kwanta akan Lokaci"

Cikin yanayin mganata nace"Da dama..Ina so ne gobe naje Dutsenmah na Duba Tamadina"

Cewa yayi bai ji ba na sake bud'e muryanta na kara gayamai sai kawai yace"wacece haka..?

Ban yi mamaki sanin Waye Ya ishaq kai tsaye nace"Babarmu.."

Karamin Tsaki yaja kafin yace"Daman nasan bana ganin kiranki sai wata Bukatarki ta taso miki Fa'iza baki da wani Amfani sai kina da bukatar wani abu..me akayi da kike son ki tafi..?

Kai tsaye nace"Tayi rashin lafiya ne ni kad'ai ne ban je na Dubata ba"

Kyafci yayi kafin yace"Kada nace bazaki je ba kice na hanaki ganin mahaifiyarki Allah ya kiyaye hanya..Sai dai kada ki kuskura ki tafin min da yara na gidan da ba wanda yasan su, salon suje suna Rab'e rab'e ke kanki ai araben zaki je Ahmad na amince kawai ki tafi dashi Shima Saboda yana shan Nono ne"

Ban damu ba nace"Eh daman suna Hadda haruna in ya Dauko su in ban dawo ba gidan mama zan ce ya kai su"

Da Sauri ya tasomin yana fadin"Au Dare ma zaki kai?ko nufin ki Daman chan zaki kwana..?

Cikin daburcewa nace"A"a..Dama..Dama ina so na Biya Karofi na gaida Goggo ne"

Kai tsaye cikin D'agawar Harshe yace"Ban amince ba..Ban kuma baki izinina ba..Dutsemah kadai zaki je shima Dubiya ce in kika Kai dare Fa'iza wlh sai ranki ya baci..Wato ki je a had'u ayi ta gulmana ana zagina nan Goggon karofi ta kirani tana min Fad'a duk akan ki wai in nayi aure  kada na wulakantaki to in tana ganin ban taimake ki ba meyasa sanda Baba ya nuna zai Aura min ke bata famsheni ta aura miki Isa ba..?karewar tana kaunarki da Tausayin ba..bana son Rainin wayau kada ki sake naji kin taka Karofi in kuma naji wlh tallahi kin ji Rantsuwan musulmi Fa'iza zaki ga Other side of me da baki Taba gani ba.."

Hawaye wani na koran wani suke zuban min cikin wani yanayi nace"Ko gidan Ya..ya mariya..?

Dogon Tsaki yaja kafin yace"Ita kuma wannan na yi miki iyaka da ki kara Takawa gidanta tunda bata da mutumci bata da,kunya har ni nan zata rika gani na, tana min kallon banza kamar taga kashi..?,Sannan naji Labarin ta raina Mama ta kuma raina Anty Binta har sa'insa tana yi da ita in dai ni ke auran ki kin bar kara taka gidan da ake cin zarafin Uwa ta da yayata sannan itama ki gayamata kada ta kuskura na kara ganin kafarta agida na in kuma ta bari muka Hadu sai na Koreta wlh"

Daga haka kit ya kashe wayar sai nayi sororo da waya a Hannuna Hawayena suna D'iga a saman wayar gefen gado na koma na zauna kukana ya kasa Fitowa sai dai Hawayen kawai ina Tuna mganganunsa in ya zagi Yaya mariya bazan damu ba Tunda har Goggo bata tsira ba awajensa ni Ya ishaq daman ya saba kirana da duk sunan da yaga Dama,na yarda yace ban da amfani sannan bana Kiransa sai in ina da Bukata Saboda tun farkon fara aikinsa a abuja ina kiransa Ranar ya Dauka ya yi min  fata fata yana min ihu akan  me zan rika Damunsa na D'auka Abuja irin katsina ne..?

Abuja yana harka da Mutane Dabam Dabam bazai zo cikin jama'a yana wage baki da murya Saboda mgana dani ba kada na kara kiransa kada na kunyatasa watarana cikin jama'a Tunda ga ranar ban kara gigin kara kiransa ba kada na kunyatasa kamar yadda yace d'in sannan Halin ko in kula da ya nuna kan Tamadina bai Dameni ba Domin bashi ba ne na farko ba kuma Kila bazai zama na karshe ba.

Tunda ya ke aure na bai Taba taka gidan da Tamadina ke aure da,Niyyar gaida mahaifiyata ba akwai wani zuwan da mukayi karofi bayan Haihuwar Anum ne da Mama da shi a motar abokinsa Dakyar ya aminnce ya biya dani zan kai mata Anum saboda sanda aka haifeta bata zo ba Shima din Sai da na roki Mama ta saka baki ya Biya  dani ammh K'iri k'iri yaki bari na shiga da Amir sannan Daga shi har Mama suka ki' shiga Gidan suka tsaya a mota ni kuma ya bani Minti goma.

Ina shiga ko zama ban yi da kyau ba ya fara Hon ta na rike da Anum a hannunta ni na fad'amata tare da su Mama muke bata damu ba tayi Lullubi ta fito har kofar gida suka gaisa Ya ishaq kuma ki'ri kiri yak'i fitowa Daga mota Mama ce ma ta fito suka gaisa duk yadda Tamadina taso ta Dauki Amir ya ishaq ya ki fitowa da shi yana rike dashi,Sannan ya hanani komawa cikin gidan ko cikakken gaisuwa  bamu yi da ita ba yace na shigo mota mu tafi da nace bamu gaisa ba sai yace sai dai ko na san yadda zan yi na Dawo gida wlh in ya tafi bazai dawo ya Daukeni ba.

Ina ji ina gani na shiga mota  bayan Tamadina ta bani Anum,Tana d'agamin hannun idanuwanta sun cika da kwallah,ni kaina kwallar ta kawo cikin Idanuwana da Dubara na share mun D'auki Hanya Ya Ishaq ya juyo yana fadin"Tab Mama ashe kice Allah ya Dubi Fa'iza da idon Rahma ana jin mganarta har ana gane me take fad'i naji Babarsu ba'a ko jin abunda take fadi sai uban Ihu kawai ake ji tana yi"

Da Dauri na Dago ina kallonsa shi kuma ko ajikinsa maimakon Mama ta kwab'amai a'a sai cewa ma tayi"Eh mana ai uwar su ce ainihin Bebiyan Sai dai kaji tashin Ihu nan kuma wai mgana take yi"

Ya Ishaq yayi dariya yana kallona kafin yace"Allah ya taimake ki Fa'iza da yanzu kema ihun kawai zamu rika ji"

Daga shi har Mama Dariya suka saka har muka iso gida ina kuka Tozarcin ya tashi daga kaina da yan'uwa ya koma Har kan mahaifiyata shiyasa abunda yayi yau ba zame min Sabo ba sai dai shi Tozarci baka Sabo da shi ko yau aka yi maka shi sai kaji ba Dad'i.

Ban karaya ba sannan na yi kudurin sai naje shiyasa da wuri na tashi na shirya yara suka tafi Hadda sannan na yi wanka na shirya Ahmad Na fara Tunanin me zan kai mata bani da komai ban ijiye ba sannan ban bama wani ajiya ba ina bakincikin wannan Rayuwar da nike ciki ko da bani da shi akwai Hakkin uwata a kaina sannan wazai amince bani da shi Tunda kowa yasan Ya Ishaq nada Rufin asiri sanna  ba kowa yasan yanayin Rariyar ba ballatana yasan yanayin zubar ruwanta ba Nasan Su Yaya mariya suna iya bakin kokarin su ammh suma ai ya'yanta ne kamar yadda nake yarta akwai Hakkin kyautata mata a wuyana.

Da na rasa abunda zan kai mata sai na D'ibar mata garin rogo wanda Ya Ishaq kan siya saboda yara in yaga Dama sannan shima yana son gari da siga,sabulin wankan mu ya kusa karewa sai na Dibar mata na wanki da na Klin,sai na Daukan mata Maltina guda hudu na kulle aleda ina da Burin ko kaya na bata ammh bani Dashi sannan bazan iya bama mahaifiyata tsohon kayana ba kamar na ci mata mutumci ne.

Sai nayi Hakuri na Dauki iya abunda nake da shi koda goma tayi na isa Dutsemah sai dai Tamadina ta ganni kamar Daga sama Allah Sarki Uwa bakinta yaki Rufuwa ta rasa ina zata sakani Saboda Murna taji Sauki Sai dai kafafun sun kumbura abokan zamanta sun ce Daga dare zuwa Safe ta tashi da Kafafu a kumbure ana ta dai shafa mganin sanyi.

Tunda muka zo ta kama Ahmad ta goya ram a bayanta sai kallonta nake yi farinciki ya cikani ta tambayi su Amir nace suna makaranta tace meyasa ban kawo su ta ga yadda suka kara girma ba..? Idona ya ciko da kwallah ya'ya na ne suma ammh bani da iko da su ballatana mahaifiyata tayi iko dasu suma dai  ce mata kawai nayi zan kawo su watarana.

Abokiyar zamanta Maman isuhu suke kiranta tayi danwake ta kawomin naci abuna muna ta Hira Da Tamadina duk da mganar nata sai a hankali ammh mu ya'yanta da ta zame mana Dole muna ganewa ni dai ban gayamata wani abu da zai tada mata Hankali ba ko mganar auran Ya ishaq ban mata karfe biyu nayi na tashi na fara shirin tafiya bayan nayi sallah na bata abunda nazo da shi ta Dafa kaina tana ta sakamin albarka.

Ta bani Ahmad na goya a baya na,na saka Hijabina nayi ma mutan gidan Sallama ta rakani har zaure tana D'ingisawa ina ta koma sai tace sai ta Rakani mun yi sallama kamar kar mu rabu har zan tafi ta riko Hannuna na Juyo ina kallonta ta kuramin ido sai naji jikina yayi sanyi cikin mamaki nace"Manene ke faruwa Tamadina..?

Kawai sai ta Dafa kaina ta jijjiga nata kafin tace"Kiii....yi....hakuri..Fa'iza..!

Sai naji raunina ya bayyana da Sauri na kauda kaina ina Boye hawaye na kafin na gyada kai ina fadin"In sha Allahu..Allah ya baki lafiya"

Daga haka muka yi sallama har na kule tana Dagamin Hannu.

Tunda bai amince na biya karofi ba Daganan ma hau motar katsina,na koma gida hud'u saura sallah kawai nayi na fara kokarin dora girki Saboda yan makaranta ammh gabadaya sai ina jin jikina duk yayi wani irin sanyi komai nawa yayi sanyi kamar an zare ma jikina lakka.

Ko su Amir da suka Dawo makaranta sai da suka ga yanayi na Amir mai wayon ciki ne ya dinga ce min"Baki da lafiya ne Umma..?

Sai nace mai a'a saboda kada na tayar musu da hankali sai na warware na shiga cikin su mukaci abinci bayan sun gama mukayi sallar isha'i tare bayan mun idar nayi musu karatun Qur'ani na kara ma kowannen su inda ya ke sannan nace su yi na makarantan bokon su da aka basu amatsayin aikin gida.


****


Tunda Ya ishaq ya tafi bai Dawo ba sai ana Saura kwana uku D'aurin auran sa,sannan ya Dawo shima din gidan Mama ya sauka sai Dare na gansa,gari kuma na wayewa ya kara fita Jamal ya Dawo tare naga suna ta zirga zirgan karbo dinkuna Gidan Mama kuma ya fara cika da baki Badariya ta fadamin Hajiyar Dala ta iso tun jiya sannan da yan'uwan Mama na yamai ni dai ta barayina bana wani shiri Saboda ban ga abunda zan shiryamawa ba.

Ana jibi Daurin aure da yammah sai ga Anty Mamah da Halisa sun zo gida na karb'e su hannun Biyu Saboda suna da kirki Har Halisa ba ta Dauko Halin Anty Binta ba.

Na kawo musu ruwa kenan na zauna muna gaisawa,ba islamiya Saboda alhamis ne Su Amir suna gidan Mama dazu da Jamal ya kawo wasu kayan Shahen Ya Ishaq ya tafi da su Ahmad ne kad'ai tare dani.

Bayan mun gaisa Anty Mamah ta kalleni sama da kasa har sai na Tsargu ina sanye da Riga da zani na atamfa da dankwali kaina na maida kasa ga Ahmad bayana na goya shi.

Anty mahma ta bude murya tana Fadin''Fa'iza ina kunshi ina gyaran kai..? Haka za'a dauko miki amaryan a ganki yarkace yarkace.?

Ban ce komai ba saboda basan me zan ce musu ba  halisa tace"Ko Saboda ba anan Amaryan zata zauna ba ne shiyasa kika zauna ba wani gyara..?

Anty Mamah tace"Wannan ba Hujja ba ne..ya kamata ko kunshi tayi saboda gyaran kanta da kanta Halisa"

Ni dai kaina na kasa ban ce komai ba kamar daga sama sai da ya Ishaq ya shigo Gidan yana waya kamar Sauri ma yake yi Anty Mahma ta tsaida shi ya katse wayar yana Fadin"Mahma jira na fa ake yi a waje"

Da Sauri ta mike tana fadin"Ya ishaq me zan gani haka Uwargida ba kun shi ba gyaran kai anya zakayi adalci kuwa..?

Kallona yayi sama da kasa ina ganinsa ta kasan idona sannan ya kwashe da Dariya kafin yace"Tab a bakin Fatar Fa'iza daman in akayi mata kunshi zai fito?

Ba ni kad'ai ba hatta su sai da mganar ta musu wani yam!

Ina gani suna kallon juna ita da Halisa suka kuma kalleni sai na nuna kamar ban ji me yace ba,menene sabo acikin mganarsa a wajena a wajen su ne sabo.

Anty Halisa ne tace"Kai Uncle akwai ma wadanda suka fi Fa'iza bakin fata kuma suna kunshi ko ita da kake ganin bakinta ka saki kudi a sama  mata mayuka masu kyau da Tsada kaga yadda Fatarta zata goge tayi Fresh kamar ba ita ba,ko Anty Mahma"?

Kai ta gyad'a kafin tace"Sosai ma yadda mayukan gyaran jiki da na fita suka cika Duniya ai da yawan mata ma ba Farin fatar su bane karawa suke da kwaskwarima"

Baki ya tabe kafin yace"Haka kurum na ba'ta kudina kan wannan abar."

Ya fada ya nuna ni da baki kafin yace"ko an yi mata ba kyau zai yi ba asaran kudi na kawai zan yi sannan ku daina cewa wai farin wasu har da kwaskwarima na Zeey din'a  Inganttace ne babu algus,daga mahaifiyarta har mahaifinta Haifaffun Fulanin Adamawa ne"

Halisa tace"Uncle baka taba nuna mana Hoton ta ba"

Ina kallom su ya duba a waya ya nuna mata ta kallah ta kara kalla kafin tace"She is so Beautifull"

Baki ya washe yana jin Dadi Anty Mahma ya mikamawa ta karb'a tana Fadin"Hoto ba zahiri ba ne sai mun ganta ido da ido.."

Dariyan jin Dadi yayi kafin yace"Zaku ganta sati uku zamu yi zamu zo gaisheku in sha Allahu"

Sukace Allah yasa Daganan ya shiga Shashensa ya Dauko abu a leda ya Sake fita suma basu Dade ba sukamin Sallama suka tafi Anty mahma dai kallona kawai tayi tace min kiyi hakuri Fa'iza nayi mata mirmishi kawai ban ce komai ba.

Washegari sai ga Yaya Asiya ta Diro ita da Hafsah da Anty Nasara Goggo karofi ta rantse tace bazata zo ba Tunda dai Mama bata gayamata ba ayi sha'ani Lafiya.

Goggon karofi ta basu kayan miya da yawa sun zo min da shi,Sannan Yaya Asiya ta zo min da kayan kamshin girki da su kori saboda sana'ar da take yi a chan kano kenan Anty Nasara tazo min da less sabo dinkin Buba mai Tsada ta dinkamin kamar in yi kuka Allah Sarki dan'uwa mai rana.

Hafsah kuma ta tsifemin kai ina ta cewa bazan yi ba Anty Nasara tace"Zauna fa'iza ta tsefe miki ki wanke sai ayi miki kitso ki gyara jikin ki ba domin auran da mijinki zai yi ba Sai Domin kema kiji Dadin jikin ki"

Mganar ta yasa na zauna ta tsefemin kai Ahmad na Hannun Yaya Asiya su Amira kuma Daga makaranta basu Dawo gida ba da Jamal ya Dauko su da Motar Babansu gidan Mama ya sauke su tunda naji su shuru.

Ina ta tambayan su Ya mariya sukace zata taho dinki ne ba'a karisa ba ta tsaya karbowa

Da daddare kuma sai gata lokacin har Hafsah tamin kitso tana min yanka Salatif din da zata zana min dayake tana koya,Ko da Yaya mariya ta iso sun wanke kayan miya har sun bada nika sun tafasa sun tambayeni Cafanen girki nace bai bani komai ba kuma bai ce komai ba.

Yaya Asiya tace"Fa'iza kuma baki mai mgana ba..?

Anty Nasara tace"Ban da abun ki Asiya sai tayi mai mgana ai yasan ya kamata..?

Yaya mariya na gefe ta tabe baki bata dai yi mgana ba hira suka cigaba da yi bayan sun bar mganar acikin Hiran ne Yaya mariya tace ita ta fadama Tamadina Ya ishaq zai kara aure tace mata naje ammh ban fada mata ba Cikin Sanyina nace"Kawai sai na fada mata mijina zai kara aure..?

Duka sai suka kalleni Cikin Tausayawa ammh basu ce komai ba

 Sai Dare Ya ishaq ya shigo gida Daman ina ta fargaba,ban san wani Rashin mutumci zai yi ba in yaga Yaya mariya agidan ba,Aiko da ita ya fara cin karo ta fito daga dakina,kallon kallon suka yi ma juna ni kuma ina falo zaune kafafuwana cikin leda Tunda an saka Lalllin,Hafsah ke gefena ta na sakamin na Hannu,jikina ya fara rawa bana so ya wulantamin yar'uwa,Hafsah ce ta gaishe shi ya amsa kamar bai santa ba Yaya mariya kuwa kamar bata gan shi ba haka tazo ta wucesa Ina ganinsa ya Dago yamin wani kallo ni kuma sai na sadda kaina kasa jikina na rawa fitowar su Yaya Asiya yasa bai yi mgana ba suka gaisa har zai shige shashen shi Anty Nasara tace"Ishaq wai me zamu dafa ne na taron Fa'iza gobe..??mun zo mun ga ba komai na cefane ko a wani waje za'a Dafa abincin namu ci ne kawai..?

Ta karishe fad'a cikin Zolaya kansa yasosa kafin yace"Na sha'afa ne ammh bari zan kira Mama ko Anty Binta"

Daga haka ya shige Ciki ya bar mu nan suka bisa da kallon mamaki,Ni dai gabana sai fad'i yake kada ya yi Tijaransa a gabansu,Kunshin da na saka ya Ceceni Domin sai chan Dare na cire sa kuma ya riga ya kwanta sai ban nemesa ba na yi sallar isha'i nayi shirin kwanciya ni da Yaya Asiya muka kwana Daki d'aya Yaya mariya da Anty Nasara da Hafsatu suka kwana Daki d'aya.

Kwana tayi bani baki da Shawarwari ina jinta kuma ina Dauka kalmar dai guda Dayace nayi hakuri to in ban yi hakuri ba ya zan yi..?

Da Safiyar ranar asabar karfe tara na Safe tawagan ango da waliyansa suka mika ko sallama Ya Ishaq bai min bai,bai kuma barmin komai ba,ina wanka naji su Anty Nasara na mganar sun fita shi da Jamal,a tunanin su zai dawo sai zuwan Badariya ta tabbatar da sun mika Hanya kuma ba dawowa zai yi ba Tunda chan amaryan zata zauna.

Ban yi amfani da kayan da Anty Binta ta bani ba Domin Yaya Asiya ma ta dinkama na atamfa mu hudu har da Hafsah dinkin ne Yaya mariya ta tsaya  ta karbo mana.

Ganin har sha Daya tayi kawai sai nace su Dafa sauran shinkafar data ragemana Daman bata wuce tiya hudu ba Tunda Ya ishaq din bai ce komai ba kayan miya kuma sai suyi miya dashi Yaya mariya sai fada take tana fadin"Haba aiko Dai darajan kashin miya ma samu"

To kafin ma a tashi a d'aura sai ga Anty Binta tazo da mganar chan gidan Mama zamu koma ayi bikin gabadaya.

Yaya mariya ta Daka tsalle tace wlh ba wanda ya isa shikenan saboda sun maidani banza a banza taron ma ni da Dangina sai an yi min iko da shi.

Anty binta ko taki tafiya tace kafarta kafarmu ai nan din da gidan Maman duk D'aya ne

Su Yaya Asiya suka shiga tsakaninsu ammh sun fara cacan baki,nayi kuka kukan bakinciki da wannan tozarcin da aka shiryamin Yaya mariya tayi rantsuwan bazata je gidan Mama ba,ko sallama haka ta Dauki kayanta ta wuce karofi ni da Yaya Asiya sai Anty Nasara da Hafsatu dake goye da Ahmad muka tarkata zuwa gidan mama a ka kulle gidan key din ma na Hannun Anty Binta.

Dakin Badariya muka sauka Saboda nan muke da Daraja,kallon mutumci cikin Dangin Mama ko kawayenta ba wanda yayi mana gida cike da mutane sai harkan arziki akeyi su Amir sun shige cikin yara sa'o'in su suna ta wasa Anum ta saka anko Mutsy kuma kayan yan kanti Amir dai ban gansa ba Anum tace dashi Uncle Jamal suka tafi.

Abinci ma sai chan da Rana aka kawo mana shima sai da Anty Mahma ta shigo ne taganmu baki bude tace an kawo mana abinci mukace a'a ita ta fita ta samo mana waina da Jallop din shimkafa sai alala.

Duk yadda naso na Daure ma wannan wulakancin na kasa har ta su Yaya Asiya abun ya tabasu suna tare dani sun kasa fita Hafsatu ce Badariya ta jata.

Kawayen Mama sai dai su lekomu suna Dariya a wulakance,sanda yan Daurin aure suka kira sukace an Daura aure haka Anty Binta ta rika rangad'a gud'a ita da kawayenta itama Mama ance har da rawa sai da ta taka Anty Nasara ta kalleni ina ta sharan kwallah ta dafani kafin tace"Ki yi hakiru Fa'iza ki bar kuka..Watarana sai Labari"

Yaya Asiya abun ya ciwota sai ta kasa ma mgana har da kidan kwarya sai da yan yamai sukayi sannan da Daddare suka kure kid'a da wakar Bikin Ishaq da zainab suna rawa ni dai ina kan sallaya tun bayan da nayi sallar isha"i ban Daga ba ina kai ma Allah kukana.

Washegari ma Anty Mahma ne ta kawo mana kosai da koko muna gama karyawa su Yaya asiya suka yi Haraman Tafiya na kallesu a marairaice kafin nace"Tafiya kuma zaku yi..?

Yaya asiya tace"Kiyi hakuri Fa'iza ya zama Dole ga Hafsah nan ta zauna sai gobe sai ta dawo mukan yau zamu tafi in sha Allahu"

Ban hanasu ba domin suna da gaskiya gwara kayi nesa da in da ba'asan Darajan ka ba.

Da zasu tafi har Dakin Mama sukaje sukayi mata fatan alheri Hajiyar Dala bata ta nan da ita aka tafi Abuja ita zata tarbi Amarya ance suna hanya yau zasu dawo.

Mama sai mgana take har tana fadin"Nasara goggon taku dai taki zuwa to ku shaida mata an daura auran ba'a fasa ba"

Su dai basu mayar mata da mgana ba suka musu sallama suka kama Hanya ransu ba Dadi.

Naso aranar na koma gida Anty Binta tace ban isa ba,Sai an watse taro Sai Yammah mutanen abuja suka Dawo Hajiyar Dala murya har waje ta na bada Labarin gidan arzikin da Ya Ishaq ya nemi aure tazo da Turamen tamfa na iyaye guda goma da kayan gara mota guda har da shaddodi da kuloli kayan uwar miji da Uban miji Robobi cike da kayan fulawa har da nakiya da alkaki.

Nima Anty Binta ta kawomin alkaki da Cin cin,Sai kula mai biyu guda daya na karb'a na saka albarka a bakin Badariya nake jin har da Turmin Atamfa akace abani Mama ta Dauke tace ba za'a abani ba araina nace ko an bani bazan Daura ba ai ban dace da kayan alfarma irin shi ba da su yafi Dacewa.

Agidan muka kara kwanaa sai Ranar Lahadi da yammah muka koma gida bayan ni da Hafsah mun zage mun gyara gidan Mama tas sannan Anty Binta ta bani key din gidan na Tattara duka ya'yana  muka koma gidana Hafsha kuma nace ta bari sai washegari sai ta tafi."




*Littafin KANA NAKA book 2,3 paid book ne biya kudin karatun ki akan Naira N500 Regular posting sau d'aya a rana.*

*Ko kuma tsarin VIP 1000 Posting sau biyu a rana akan wannan acct din 0552179550 Jamila Umar Gt bank,sai a turo shaidar biya ta wannan lambar 09069067488 Wannan karon babu tsarin kati,kowani tsari zaka yi ka turo ta POS,Mutanen mu na Niger kuma zaku tuntubi Kausar Aglan Nissa ta wannan lambar +22796562223*






*Janafty**KANA NAKA..!*


*Wattpad:JamilaUmar315*

*Mallakar:Janafty*

*Arewa book:Jamilaumarjanafty*


*Nagode sosai da addu'o'in ku ga kawu Madalla da ku naji dad'i Allah ya amsa, shi kuma kawu Allah ya jaddada rahma a kabarinsa Ameen summa Ameen.*


MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT Y'A SKWATO__SAKINA HASSAN 08066726866


INA MATA Y'AN KWALISA MASU SON GYARAN JIKI MACCE DA TASAN KANTA KULLUM CIKIN GYARA TAKE


INA MATA MASU FAMA DA RAMA KU KINSA KAYA BASU KAMA JIKIN KI 😫


INA MATAR DA ADDA JIKI BAKI DA HIP BAKIDA BAYA IN KINYI DRESS BAYANKI A SHAFE


INA WADDA KE FAMA DA ZUBEWA NONO KU KE BAKI JIN DADIN GANIN SU KAMAR SILIFAS 


KINYI TA GYARAN BRST HAR KIN GAJI HJY TA GYARAN BRST WAHALA GARESHI DUK WADDA TACE MIKI GA MAGANIN BRST DA SHA ZAIYI TO KARYA TAFADA MIKI GYARAN BRST YANA SON JUREWA DA DAGEWA IN KIN FARA BA'A TSAYAWA INSHA ALLAH SAI KIGA SUN ZAMA NORMAL


MUNA DA INGANTATA ZUMA BRST DA MUNKA SARRAFA DA KAYAN ORGANIC HERBAL SU MACA DASU AGUAJE WADDA INDAI KIN RIKE TA INSHA ALLAH ZAKI GA SUN CIKO SUNYI KOSHI RUBA 2 KU 3 SUN ISA YAZAMA MIKI YADDA KK SO 4K


MUNA DA GARIN HIP DA BRST YAKE GYARA DA GYARAN JIKI DA KARIN NIIMA YAKE YI 4K


MUNA DA INGANTATA ZUMA TA HIP ITA MA MUN SARRAFA TA DA KNGAN TATUN KAYAN ORGANIC HERBAL DA KE FIDDA MIKI HIP 6K


MUNA DA ZUMA KIBA WADDA ZAKIYI FRESH DA BULBUL ITAMA RUBA 2 KU 3 ZATA YIMIKI YADDA KK SO 2K


MUNA DA GARIN GYARAN BRST DA KARIN NIIMA SHIMA GUDA 2 KU 3 ZAKI SHA 2K


GASKIYA DA AMANA ITACE NASARAR.MU


MUNA AIKA KAYA KU INA CIKIN YARDA DA AMINCI


MMN MUJAHID __SAKINA HASSAN MUNA SOKOTO DA KEBBI 08066726866


        *🅿️08*


Da muka koma gida na zame jikina na shige daki nayi kuka na rarrashi kaina daga baya ranar ban yi moruwa ba ina kwance acikin d'aki ina Tunanin makomar rayuwata,Yaran suna tare da Hafsatu har ta ko da Ahmad Amir ne ya dame ta da Ina Umma sai tace na kwanta bana jin dad'i ne tunda taga yanayi na.

Ita ta yi musu girki cikin sauran k'wayanim taliyan da suka rage mana ta dafa sai ta dib'i Tumatir din nan Tafashasshe tayi miya da shi suka ci ta zubomin nace ta dauke sa bazan iya saka wani abu aciki na ba.

Tare da yaran suka yi ta burumtun su afalo ina jin su kafin ta yi musu shirin barci ta rakasu d'aki suka kwanta Ahmad kuma tayi mai wanka sannan ta kawo min shi ya fara rigima na bashi Nono sai yayi barci ni kuma na Rarrafa na tashi na yi alwala nayi Sallar mangariba da isha'in da kasalan Rayuwa ya danne ni na kasa tashi.

Washegari tun safe Hafsah ta shirya bayan su Amir sun tafi makaranta Haruna mai adaidaita na roka ya kaita inda ta hau motar Karofi,ta barni Dagani sai halina acikin gidan da bansan makomata ba.

Tun kuma bayan tafiyarta ban karaji Daga kowa ba hatta Yaya Asiya bata kirani ba Daman goggo nasam tayi Fushi ga abunda kuma daman ya sake Faruwa nasan tun kafin su Anty Nasara su koma Yaya mariya taje mata da Labarin komai.

Harta bangaran su Maman ba wanda ya kara nema na ballatana ace bari a kaga Halin da nake ciki ni da ya'ya to wanda ma Hakkinsa ke kan mu ai bai Damu damu ba ballatana wani ya nuna Damuwarsa a kanmu.

Tunda bayan auran Ya ishaq da Abar kaunarsa ban kara jinsa ba bai kirani ba kuma bai min sakon kudi ba an wayi gari bani da ko sisi a hannuna.

Na shiga damuwa ga shi kayan abinci duk sun kare daga shinkafa sai sauran Taliya ta ragemin Indomie ta kare saboda ina dafa musu sau biyu a sati suna tafiya da shi a makaranta sau ukun kuma na dafa musu taliya Ranakun Hadda kuma sai na Dafa musu shinkafa,Doya da Dankali Sun kare kwai daman kires daya yake siya nama daman ba Cefanen sa ba ne sai in yana gari ne yakan siya in baya gari kuma sai abunda ya zama Dole a garesa.

Lemun yara na makaranta ya kare harda kayan Tea komai ya kare, sauran maltinan da ya siya tun wanchan dawowar na rika basu suna tafiya itama tazo ta kare na koma Hada musu biskit guda biyu suna tafiya da shi Saboda makaranta sai uku ake tashi ana kuma tashi akwai islamiya ana shiga,asabar da Lahadi kuma Tahfez duk makaranta D'ayace sai biyar suke shigowa gida akwai yunwa da gajiya ga yara kanana tunda su basu wayon su fahimci babu ba ballatana su yi hakuri.

Sati biyu da auran Ya Ishaq Dubarata gabad'aya ya kare na zauna nayi lissafin zama a haka bazai haifarmin da D'a mai ido ba dole na mike na nemi sana'a ba domin ni kaina ba sai Domin Ya'yana su Dogara dani.

Na fara Tunanin sana'ar da zan yi sai komai ya kwancemin me na iya..?

Babu abunda na iya sai girke girke shi kuma in ba aikatau zani nayi ko agidajen mutane ko gidajen masu abinci na kan hanya bansan ina zani ba Kuma in wannan ne Ya Ishaq bazai taba barina ba ko ma ya barni Mama sai ta Dakile duk wani abu indai na Cigaba ne Daga bangarena.

Nagama Tunanin ko na samu sana'ar da zan yi ai bani da jari shima din wata mganace mai zaman kanta sai na Saki wannan Tunanin na fara Tunanin yadda zamu kwashe da Anum gobe litini in zasu tafi makaranta bana jin Amir shi ya fi Anum natsuwa ita kam sai a hankali ita da Mutsy tunda yara ne kanana a kan Amir din.

Tun da na tashi a sukuku na dinga yin musu komai inda Allah ya taimakeni tun wannan kayan miyan da su Yaya Asiya suka zo min dashi nayi miya dashi sauran kuma na sakashi cikin karamin Fridge d'ina shi nake diba kad'an kada'n ina amfani dashi Taliya ta kare itama sai na Dafa musu farar shinkafa da miya na zuba musu kowannen a basket din su bani da biskit ba lemu ballatana na Had'a musu da shi kamar yadda suka saba.

Ni da kaina na zauna ina goye da Ahmad da yaki kwanciya sai rigima yake yi,kamar ya tashi da zawon hakori ne jikinsa duk ya saki,Haka na rika bama Anum da Musty abinci nan a baki Amir kuma yana ci da kansa bayan sun gama rigima bai tashi ba sai da Anum ta duba basket din ta ba Biskit ba lemu sai ta fasa kuka ina zaune ina kallonta baki na sake kawai ina kallonta a kasan raina naji bacin rai kawai yana taso min daman ina jin Haushi yadda Anum ta koyi shagwabar banza abu kadan za'ayi mata sai kawai ta fashe da kuka wani Lokacin har da birgima.

Mikewa nayi dakyar bata sani ba sai dai kawai taji saukan mari sai tayi tsit na kalleta raina a bace cikin fada nace"Ki ka ka..ra..min kukan banza anan sai nayi miki dukan tsiya zan baki Babu ne Saudatu..?.

Na kirata da ainihin sunanta sai ta kasa mgana ta koma ta zauna ana son kara fashewa da kuka tana jin tsoro Amir da Musty sai suka tsorata suka koma suka lafe a zaune idanuwansu ya ciko da kwallah ganin yanayin su sai Tausayin su da tausayin kaina ya kamani na koma na zauna na jawo Anum jikina na Rumgume ina share mata Hawaye.

Ta lafe ajikina tana sauke numfashi sai na Fahimci yara irin su Anum basa bukatar tsawa ko fad'a ko Duka a jasu ajiki sannan a lallashe su cikin yanayin mganata na fara lallashin ta ina fadin"Anum biskit din ku ya kare da lemu kuma bani da kudi ki yi hakuri ku tafi in na samu zan siya muku."

Ta dago idanuwanta da alamun kuka tace"Umma Daada fa ya na ina..?

Sai na kasa bata amsa Amir ne yace"Daada na Abuja"

Mamakin sa ya kamani a ina yaji Babansu na Abuja wata zuciyar ta fadamin zai iya sani ai baban nasu na zauna yayi hira da su kamar manyan yara.

Ni dai na samu na Lallashe su suka tafi hakanan na dawo na zauna tayi Tagumi ina tunanin in yau sun hakura gobe fa..?

Ko Badariya da kan lekomu lokaci bayan Lokaci itama shuru naji ta ni ba kudi a waya ba ballatana na kirata,Ina gane lambar kowa saboda da ajami na Rubuta na iya rubutu da Ajamin labarci tunda Hausan ban iya ta sosai ba, ba komai nake ganewa ba.

Haka washegari ma Dakyar Anum da Musty suka yarda suka tafi a makaranta ba biskit ba Lemu,na rasa yadda zan yi da su,kuma ko giyan wake na sha bazan taba kiran ya Ishaq nasan sauran abunda zai biyo baya shi da ya ijiyemu bai Tuna damu ba sai nice zan neme sa,ai ko bai neme ni ba sai ya Tuna da ya'yansa ya Tuna da Hakkin kula da komai nasu yana wuyansa ne ammh bai iya tunawa da wannan ba Tunda ya samu Cikar Burinsa bai damu da komai da kowa ba ni tunda ya jingine ni sai ya tuna da ya'yansa tunda su bai jingine su ba.

Hakanan na cigaba da lallab'a rayuwata yadda Allah ya tsaramin Tun su Anum na rigima har suka zo suka Hakura,Sai kuma suka fara Damuwa da ina Daada bai taba Sati Hudu bai zo gida ba sai wannan karon in suka tambayeni ina Daada kasa mgana nake yi in suka Dameni sai nace ya kusa dawowa aiki ne yayi masa yawa Ranar da Dadaddare bayan mun gama sallar isha'i suna zaune suna aikin makaranta da aka basu Amir na taya mutsy nayi na shi Dayake shi yana primary 1 ne Anum Nursey 2 take Musty kuma Nursey 1 ni ban yi boko ba,ban san komai a bangaran su ba sai dai ina gane wasu abubuwa  na y'an Nursey,iyakata da su bangaran islamiya da Hadda da karatun Qur'ani da azkar wannan bangaran ban yi waasa da shi ba,shi na iya shi kuma zan koyama ya'yana.

Anum ce ta kara tambayata Daada sai nace mata ya kusa Dawowa Amir ya Dago kansa yana fadin"Umma Daada wata Umman ya samo mana achan Abuja..?

Mamakin sa ya karamani na kallesa na kasa mgana Amir tun  yana Shekara Biyu da wattani ya fara  mgana yaro me mai wayau sosai cikin Mganata nace'wa..ya fada maka..?

Kai tsaye yace min"Uncle Jamal..Ba mun je har chan ba..Umma naga Daada yaci gayu sosai"

Daganan ban kara mgana ba ina jin Anum na girgizani tana fadin"Umma da gaske ne..?

Musty na tayata da gwarancinsa,Dakyar na iya bude baki na amsa musu da hakane sai kawai suka fara Murna Anum kenan Amir kuma bai tashi ba Musty kuma ganin ta mike tana Tsalle shima ya mike yana Tayata Ahmad na jikina ya lafe ba barci yake yi jikinsa ne ba Dad'i zawon hakori sannan ba kudi ballatana na kaishi asibiti.

Amir ne ya kalkeni kafin yace"Umma to ta na ina ita Sabuwar Umman tamu..?

Kai tsaye nace"Tana tare da Daadan ku achan Amir"

Cikin mganarsa ta kuruciya yace"Umma to me yasa Muma Daada bai tafi damu dake gabad'aya  mu zauna achan ba?

Mirmishi nayi wanda yafi kuka ciwo kafin nace"Watarana zamu je Amir in sha Allahu"

Zai kara mgana nace su cigaba da aikin da aka basu a makaranta Anum kuma sai ta koma wasa da musty ni kuma sai na zurfafa cikin Tunanin haka rayuwa zata cigaba da tafiya har yara sun fara gane wani abum..?.akwai nan gaba akwai matsala in dai abubuwa suka cigaba da Tafiya a yadda suka faro.

  Ranar da Ya Ishaq ya cika kwana Talatin a abuja,ranar jumma'a da yammh sai ga Anty Binta batagwara tazo nayi mamakin zuwanta ammh ban nuna ba naje na Debo mata ruwa mai sanyi da nakan diba na saka a fridge saboda ruwan ledan ya kare na famfo muke sha.

A wani karamin jug na dibo mata na Hado mata da karamin kofi na koma ma zauna a kasa ina gaisheta Amir da Anum suna Haraba suna wasa Musty kuma ya kwanta Ahmad ne ke goye a bayana.

Ina gaisheta a wulakance ta amsa tana kallona da ni da Falon sama da kasa tana wani yamutsan fuska kamar taga kashi ruwan da na kawo mata ta kallah kafin tace"Wannan ruwan fa..?ba ku da na Gora ne..?

Cikin Ladabi nace"Ya kare wannan na famfo ne nake sakawa a Firij Saboda yayi sanyi"

Baki ta tabe kafin tace"Shi ne kuma D'an pure water bazaki iya siya ba komai kina jiran sai bawan ki yazo ya siya miki,ko ke irin Dubarun nan na mata da suke yi na taimakon mazajen su baki iya ba sai dai komai ki kwanta Shi d'an wahalan  yayi miki ko..?

Na kasa Dagowa ma in kalleta da karfi take mganar shiyasa na ji ta sosai duk da ba duka ba.

ina jin ta har ta gama cin mutumcinta ban iya Dagowa ba,Sai chan ta mike tana zagayen falon tana leka Dakunan ta Dawo tana fadin"Gaskiyan Ishaq ne da yace gwara nazo na duba kada ya kawo Amaryansa yaji kunya..Ji yadda kika lalata ko'ina na gidan nan Fa'iza..?

Tsiyan a kawo wacce bata dace da irin gidan nan ba kenan ba sanin Darajan sa kika yi ballatana ki Lura da shi"

Taja karamin tsaki kafin ta koma ta zauna kafa kan d'aya ta Dauko Jakarta ta Ciro wayarta ta yi Danne danne ta kara kunne ina ji tana mgana ban ji me take fadi ba Daga karshe dai naji tace"kada ka damu ai zan ja mata kunne in ta yi ba Daidai ka dauki mataki a kanta"

Daga haka ta Datse kiran ta kuramin ido kafin ta daga murya tana fadin"Ke wai baki da aiki sai goye ne..?

Kaina na kasa nace"Ba ba shi da lafiya ne..".

Baki ta tabe kafin tace"Uhm..Kina ji..?

Tafada har da rike kunnewanta na Dago kaina ina kallonta na gyada mata Tsawa ta dakamin tsawa tana fadin"Matso kusa dani domin bazan iya Ihu ba ina mgana"

Dole na ja jikina kusa da ita kunnena ta kama guda d'aya ta rike tana fadin"Abunda nake so na gaya miki shi ne..Gobe Ishaq zai zo shi da Zainab   kuma nan zai sauketa da farko yace gidan Mama saboda yasan Halin ki kada ki basa kunya ni nace nan zai sauketa tunda tasan yana da gida har da Mata da ya'ya Saboda haka gargad'i na Farko shine zaki gyara gidan ko'ina yayi fes sannan ki shiga shashensa ki gyara ko"ina nan Zainab zata sauka har ta gama kwanakinta ta koma"

Ta fada cikin daga murya Lokaci d'aya tana kara jan kunnina zafi nake ji ammh na Daure na kasa nuna mata Raunina cikin kara rike kunnina tace"gargadi na gaba shine ki kama kanki kin dai san ba D'aya kuke ba..Zainab yar boko ce sannan yar gatace gaba da baya ki kula sosai ki Tsaya iya matsayinki ki karbeta hannun Biyu ki mata Hidima duk abunda tace tana so ki yi mata kada kice zaki yi gaddama zaman ki lafiya shine Zainab ta koma Abuja ba bu abunda ya faru Ishaq yace na Fad'a miki kada ki kunyata sa agabanta yasan Halin ki baki da Tunani wani Lokacin kina jina ko..?

Idanuwa sun kawo ruwa ammh sai na maida su cikin Rawan murya nace"Eh..e..Naji"

Sannan ta saki kunnena tana fadin"Sannan ki yi wanka ki d'an gyara jikin ki in tazo ta ganki wannan yarkace yarkacen shi zai kunyata sannan yaran nan suma ki yi musu wanka ki sanya musu kaya masu kyau kina jina ko..?

Nan ma kai na gyada mata key din Shashen nasa ta ciro a jaka ta bani na saka Hannun Biyu na karba sannan ta kara da cewa"Zaki yi musu girken girken Tarba sosai yace tana son Sakwara da miyar agusi,Sannan ki yi mata kunun aya da Ferfesun kayan ciki,ki soya mata Naman kaza ki yi pepe dashi"

Kaina na kasa ban dago ba nace"kayan abincin mu duka ya kare shinkafa kadai garemu"

Bata Damu ba ta mike tana fadin"Daman ai kamar ya san zaki kawo korafin babu komai anjuma Jamal zai kawo miki Cefane..Wlh Tallahi Fa'iza in kika kuskuere mganata ki ka bamu kunya gaban Zainab sai kin Raina kanki ki kuma sani ki kara Sani matsayin ku ba D'aya ba Zainab yar gatace gaba da baya sannan yar boko ce mai kyau yar babban gida"

Har Haraban gidan na rakata tana kara ja min kunni da kara Jaddamin matsayina sai naji ban damu ba Domin ko bata fada ba ban isa na Hada kaina da wacce suke kira da Zainab ba,na ganta a hoto na kuma san ruwa ai ba'asan kwando ba ne.

Nayi kokarin yakice duk wani abu dake cikin raina Hankalina ya tafi kan Ahmad da Zazzabin jikinsa yayi zafi panadol na ruwa nake basa shima Sauran na Musty ne da yayi zazzabi kwanaki Ya Ishaq ya siyomin Hankalina duk ya tashi,ga shi yana ta zawo bani da pampers sai napkin nake yi mai kafin Safe ya bata kaya da yawa ina tashi da wankin na tashi,Sai da na gama tsabtace sa sannan na yi musu shirin Tafiya Hadda.

Saboda bani da masaniyar sanda Bakin da zasu iso,Bayan tafiyar su sai ga Jamal ya kawo min cefane nake tambayansa ashe bai koma ba..?

Sai yace min bai koma ba sai sati na sama shima ko zama bai yi ba yayi min sallama ya tafi.

Sai da na fara zagewa na gyara Shashensa,tas na turara turaren wuta mai kamshi sannan na gyara Falon da Sauran Dakunan daidai yadda zan iya sannan na Fad'a Kichen Hankalina ya kwanta Ganin jikin Ahmad yayi sauki har ya samu barci.

Cefane ne da yawa saboda bakuwa zata zo shiyasa aka siyo aka kawo har da Lemuka da ruwa kwai,Dankali Doya,Kayan lambu taliya macaroni da Buhun Shinkafa sai Couscouss,na Sauke komai a muhallinsa har da aya nagani Saboda ai Anty Binta tace Zainab nasan kunun aya.

Banji kyashi ko mugunta ba na zage na fara aiki kan jiki kan karfi miyar Sakwaran na fara yi sannan nayi ferfesun kayan cikin araina ina jin Dadin Dalilinta yara ma zasu samu chanjin abinci.

Na zuba a kololi na rufe naje nayi sallar azahar na zauna na Huta saboda ina Tunanin sai yammh zasu shigo,ashe ma sun zo garin gidan Mama suka fara sauka Badariya ta shiga makaranta sai ta Biyo ta iskeni ina makarda ayan a blander dina wacce Dakyar ma take yi tana yi ta na mutuwa ta tsufa duk taji jiki.

Tana ta fadamin uban kayan da Zainab din ta kawo ma su Mama har da ita an zo mata da abaya ni dai sai dai yake na kasa cewa komai.

Bata jima ba ban yi sakwara ba Ferfesun ta Diba taci sannan tayi sallah Tatafi jin sun iso yasa na mike na Cigaba da aikina kafin La'asar na gama komai hatta dakan sakwaran,nasha wahala sosai ga Ahmad a baya na ya tashi ya saka Rigima Dole na goyasa haka na yi ina yi ina Hutawa ina Haki,Kazan a karshe na Soyata kamar guda biyu ce ta Turawa sannan nayi pepe chicken na shirya komai na ijiye anan kichen din sannan naje nayi wanka na Sauya kaya na saka Atamfa ta riga da Sikat,ko Hoda ban shafa ba domin bani da ita,ban kuma ji ina son na Burge kowa ba sanin ko nayi bazan burge kowa ba.

Karfe hudu daman nace Haruna yaje ya Dauko min su Amir,Shima din yana da Hakuri da Darajan makota wajen wata biyu Ya ishaq bai basa kudin sa,ina Tunanin ranar da yagaji ya daina kai su sai dai na kai su a kafa kuma akwai tazara mai yawa Tsakanin gidanmu da makarantar tasu.

Suna Dawo na taya su suka cire kayan makaranta ko alama ban gaya musu Babansu zai dawo ba Na riga daman na Dibar musu sakwaran ni dai ko ban ci ba,su dai su samu su ci,daki na jasu sukaci achan kada su ci afalo su lalata Su shigo fada'n komai ya Dawo kaina na shiga uku.

Bayan sun gama Daman sun yi sallar su a makaranta,Sai na saka musu Sabbin kayan su Anum nata Murna Amir ne yace"Umma anguwa zamu?

Sai nayi masa shuru ban ce komai ba sai na Tuna naji wani malami yana mgana kan tarbiya yara yace kada yaro ya jefa miki tambaya ki yi shuru to a ransa zai saka wani abu.

Sai nayi saurin cewa"Sabuwar Umman ku ne zata zo Amir"

Dukkansu suka bini da kallo ban damu ba na cigaba da fadin"Tare da Daadan ku zasu zo in kuka ganta ku je ku gaisheta itama Umman ku ce"

Anum da Amir suka Dagamin kai Musty na chan na wasa da kwalliyar jikin Yan kantin da na sakamai riga da wando.

Hatta Ahmad da bai jin Dadi na sakamai yan kati riga da wando,nayi mai Napkin duk da zawon yayi sauki ba kamar jiya ba na goyasa Tunda baya jin dadin jikinsa har alokacin.

Su dai yaran suna ta Tsalle tsalen wasan su ni kuma ina zaune nayi jugum ina Tunanin wani irin Tarba amaryan Ishaaq zatayi min..?

Sannan wani zama zamu yi da ita acikin gidan nan..?

Nayi zurfi cikin Tunanina naji Amir a saman kaina yana fadin"Umma wayarki umma."

Nayi firgigit na kallesa wayatace a Hannunsa ana ta kira ya mika na karba sai da gabana ya fadi da naga Sunan Ya Ishaq na kirana cikin Rawan jiki na Daga kiran tun kafin nayi sallama naji muryansa cikin Kaushi yana fadin"Ina kika kuma jefar da wayar ina ta kiran ki baki D'auka ba..?

Cikin yanayina nace"Ban ji ba ne.."

Karamin tsaki yaja kafin yace"Ina fatan kin gyara ko'ina..?

Yanzu zamu baro gidan Mama"

Kamar yana ganina na gyada kai sannan nace Allah ya kawo ku lafiya 

Bai ko amsamin ba ya katse kiran ya barni da waya a hannu ina Tunanin mafita da farko wlh jikina bai saki ba sai da ya kirani yace gasunan zuwa naji gabbaina sun saki jikina ya fara rawa ina nan zaune ina fama da Faduwar gaba naji kamar ana taba Kofar falo ko Hon dinsa banji ba ballatana Shigowar Mota,to ina ma nake da karfin jin ballatana,yadda hankalina ya bar jikina raunannun kunnuwan nawa ba su saka naji ko motsin shigowarsu ba.

Sai da naji Sallamarsa da mganarsa Su Amir na dago na kalla basu bi ta kaina ba suka fice da gudu suna kiran sunansa Daada kamar yadda suke kiransa.

Ni kuma ina zaune na kasa tashi Jikina gab gab yake yi kamar mazari gabana ya fara Dif Dif kamar an sakamin Wutar lantarki ji na nayi na kasa motsi sai yanzu nake jin yanayi na ba Dad'i ina Tunanin da wani irin kallo Amaryan tasa zata karbeni,?Kamar acikin kaina naji yana Kiran sunana a kausashe kamar yadda ya Saba.

Sai na zabura na mike da Hanzari Daidai Anum na shigowa Dakin ta fara jan Hannuna tana fadin"Umma Daada na kiran ki"

Kamar rakuma da akala haka Anum ta rika jan Hannuna har Tsakiyar Falo inda Ishaq da amaryan suka samu mazauni saman kujera mai zaman mutun biyu Amir na jikin Babansa Musty na Dauke ajikin wata Farar mace Doguwa Lalle tsarki ya tabbata ga Allah shugaban Hallitun Duniya.

Lalle gaskiyan su Anty Binta ne kada na Had'a kaina da zainab,tazaran kamar sama da kasa ne a wajen nisa ashe a Hoto ma an rage mata kyau da Haske kamar balarabiya tana sanye da Wani leshi daga ganinsa mai Tsada ne doguwar riga taci Daurinta gashinta ya zubo har gadon baya Fuskata Dauke da kwalliya mai kyatarwa kafafunta da Hannayenta Sun ci kunshi Lalle baki da Fari kamar don ita ma akayi zanen Saboda yadda kunshin ya haskata kafarta da Takalmi daga ita har Ya Ishaq basu cire takalmansu ba har zuwa Tsakiyar Falon.

Kanta na kasa tana ma Musty wasa yana mata gauranci bata san da ni a Falon ba ni kuma kawai ita nake kallon Sakin Hannuna Anum tayi ta nufi Babanta tana fadin"Daada Umma"

Shima sai Lokacin ya Dago yana kallona ina ganin sanda Fara'arsa ta Dauke kamar yaga mutuwarsa hararata yake yi kasa kasa ni kuma Chanzawarsa nake gani yayi kiba kamar bashi ba Daga gani ya samu kwanciyar Hankali sosai.

Na kasa gaba ballatana baya sannan bakina yayi nauyi shine da yaga haka ya D'aga baki yana fadin"Haka ake tarban baki a karofi ko Fa'iza..?

Sai alokacin ta Dago kanta muka Hada ido hudu da ita ni dai a bangarena sai naji na muzanta ni bansan yanayinta a bagaranta ba sai dai ban gane yanayin da take ciki a Fuskarta ba.

Tayi saurin Shanye mamakin ganina ta kallesa tana fadin"Maman su Amir right..?

Tafada tana bin sa da wani irin kallon da Sai da na kauda kaina kai ya gyad'a mata yana fadin"Yes Fa'iza"

Dukkansu a tare suka sakarmin ido sai naji kafufuwana na rawa lojaci d'aya  sun kasa D'aukana sai na bi ra'ayin su na Durkusa kaina na kasa cikin yanayina nake fadin"Sannun..Sannun ku da zuwa an zo lafiya..?

Bakina har rawa yakeyi Ta kalleni ta kara kallona sannan ta kallesa ya gyada mata kai Cikin Zakin muryanta da ta karye da Turanci tace"Hy Am Zainab Nice to mee u Fa'iza"

Tafad'a cikin wani irin Turancin da na kasa ma jinta ballatana na gane ina jin yana mata mgana kasa kasa ban ji me yace ba nadaj ji tace"Oh sorry Honey..Kiyi hakuri Fa'iza ban san bakyajin Turanci ba kina lafiya..?

Yasu Amir ina Ahmad ko shi ne a bayanki..?.honey goye kada kafafunsa sun lamkwashe ita kuma ta samu problem da kirjinta fa"

Duka alokaci daya ta fad'a,kunnina na kasa yasa naji wasu daga cikin mganar nata sannan na Dago kaina ina kallonsu jin nayi shuru yasa yace mata"Tun kafin mu taho na fada miki yanayin Fa'iza bebiya bataji sosai sai kin yi mgana da karfi sannan zataji jiki Honey"

Kwabe Fuska tayi kafin tace"Really..?

Kai ya gyad'a mata kafin yace"Yes bata ji ki ba sai kin d'aga murya"

Ta kalleni cikin Tausayawa kamar taga mai bara tace"Ayya am sorry"

Ni dai kaina na kasa ban ce komai ba kawai sai naji tace"Whta is bebiya Honey..? I did get u..?

Da Harshen Turanci naji yana mata bayani bana jin me yakefadi sai dai ina gani tana kallona tana d'an kwabe Fuska gani nayi bazan iya jure ganinsu ba yasa na mike da Hanzari zan koma Daki Ishaq ya Dakatar dani da Fadin"Kin ga Kwantomin Ahmad"

Ba musu na karisa na kwantomai na mikamai har ya fara barci su Anum kuma sun samu Chaculate basu ma bi ta kan mu ba.

Kallona yayi lokacin da yake karban Ahmad yace"Ki bude shashena ki kwashe kayan zeey da nawa zuwa chan"

Cikin rawan jiki na koma Daki na Dauko key din ina ganinta tana bina da kallo,ni dai na bude Dakin nazo na Rika daukan jakunkunan da suka zo dashi sai ta karshen ne zan Dauka tace"No.."

Sai ta juya tana fadin"Honey tok to her kasan ban iya mgana da Karfi ba..Tsaraban Kids d'ina ne"

Shi ya fadamin tace tsaraban yara ne sai na kalleta cikin yanayina ina fadin"Sun gode Allah ya saka da alheri"

Ta amsa da fadin"My pleasure"

Mganar abinci nayi yace sai sun yi wanka sun yi sallah tukunnah Jikin Ahmad dayaji zafi yasa yace min ba shi da lafiya ne na dagamai kai sai ya kalleni yana fadin"Meyasa baki fadamin ba.?ai da ko Jamal yazo kun je asibiti an dubasa".

Nidai ban ce komai ba itama kuma wayarta ta Dauko a wata karamar jaka mai kyau tana Dannawa kafin ta mike tana Fadin"Honey am Tired ina son nayi taking Shower'

Mikewa yayi yabi bayanta yana fadin"Me too duk a gajiye nake"

Ina kallon su suka shige suna rangaji Jikinsu na Dukan juna karamar jakar Hannun Zainab Ishaq ya amsa ya rike mata ita kuma sai lamkwashewa take yi tana Turancin da bana ganewa.

Su Amir kuma sun samu Chaculate basu lura ba na Dauki jakar da tace Tsaraban yara ne zuwa cikin Dakina na Bude naga kaya masu tsada Kala biyu biyu na Anum har da riga da wando da takalma ni ma har ni naga Doguwar riga da pakistan riga da wando sai naji kayan basu burgeni ba na Tattara na ijiyesu na fita nace su Amir su yi alwala an kira sallar mangariba.

Tare da yarana muka yi sallar mangariba muna zaune muna azkar Ishaq ya leko ya sauya kaya zuwa Jallabiya yace na kawo abinci,da Hijabin da nayi sallah na shiga Kitchen na Fara Daukan abincin nasu zuwa Shashen megidan basa Falon suna ciki na gama jera musu komai na Fice na koma D'aki duk da cikina na jin yunwa ammh na kasa cin komai a fatar bakina nake jin abinci bazai iya shiga ba sai kawai na sha Ruwa na koma ma kishingid'a ina kallon su Amir nata wasa Ahmad yayi barci,ina zaune a wajen har akayi sallar Isha'i sai na mike nace su bar wasa su sake yo alwala suzo muyi sallah

Bayan mun idar Anum nata rigiman zataje wajen Daada dakyar na lallasheta da yayi barci,kafin su kwanta sai da suka kara cin abinci sannan nayi musu shirin barci sai da sukayi addu'a na tayasu suka Tofa sannan na baro Dakin nasu na koma nawa Ko barayin Shashen Ya Ishaq ban kallah ba Tunda suka shiga Ciki ban kara jin motsin su ba.

Ni kuma na kasa barci da ya fara Fizgata sai na farka gajiya nayi da juyi na shiga tiolet nayo alwala nazo ina ta nafila sai wajen uku na Dare na kwanta shiyasa na makara sallar asuba rana ta farko da Ya Ishaq bai fito ya tara su Amir sun tafi masallaci ba Amir sai fadi yake yau Daada bai je masallaci ba ne Umma..?

Sai nace musu yaje yaga suna barci ya kyalesu har nayi musu shirin hadda nayi abun karyawa Haruna ya Dauke su ya kaisu basu fito ba yaran dakyar na janye su suka tafi batare da sun ce zasu je gaida Daadan nasu ba.

Suna tafiya nayi ma Ahmad wanka na shiryasa nima nayi wanka sai nasha Tea kad'an naji cikina ya Toshe Breakfast din Amarya da ango a kicthen na bar musu komai na shige D'akina araina nace me yasa zan damu..?Ai ya jingine auran mu alfarma yake min da nake zaune ma agidansa yana ci da ni.'


*Littafin KANA NAKA book 2,paid book ne biya kudin karatun ki akan Naira N500 Regular posting sau d'aya a rana.*

*Ko kuma tsarin VIP 1000 Posting sau biyu a rana akan wannan acct din 0552179550 Jamila Umar Gt bank,sai a turo shaidar biya ta wannan lambar 09069067488 Wannan karon babu tsarin kati,kowani tsari zaka yi ka turo ta POS,Mutanen mu na Niger kuma zaku tuntubi Kausar Aglan Nissa ta wannan lambar +22796562223*


*Janafty**KANA NAKA..!*


*Wattpad:JamilaUmar315*

*Mallakar:Janafty*

*Arewa book:Jamilaumarjanafty*


MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT Y'A SKWATO__SAKINA HASSAN 08066726866


INA MATA Y'AN KWALISA MASU SON GYARAN JIKI MACCE DA TASAN KANTA KULLUM CIKIN GYARA TAKE


INA MATA MASU FAMA DA RAMA KU KINSA KAYA BASU KAMA JIKIN KI 😫


INA MATAR DA ADDA JIKI BAKI DA HIP BAKIDA BAYA IN KINYI DRESS BAYANKI A SHAFE


INA WADDA KE FAMA DA ZUBEWA NONO KU KE BAKI JIN DADIN GANIN SU KAMAR SILIFAS 


KINYI TA GYARAN BRST HAR KIN GAJI HJY TA GYARAN BRST WAHALA GARESHI DUK WADDA TACE MIKI GA MAGANIN BRST DA SHA ZAIYI TO KARYA TAFADA MIKI GYARAN BRST YANA SON JUREWA DA DAGEWA IN KIN FARA BA'A TSAYAWA INSHA ALLAH SAI KIGA SUN ZAMA NORMAL


MUNA DA INGANTATA ZUMA BRST DA MUNKA SARRAFA DA KAYAN ORGANIC HERBAL SU MACA DASU AGUAJE WADDA INDAI KIN RIKE TA INSHA ALLAH ZAKI GA SUN CIKO SUNYI KOSHI RUBA 2 KU 3 SUN ISA YAZAMA MIKI YADDA KK SO 4K


MUNA DA GARIN HIP DA BRST YAKE GYARA DA GYARAN JIKI DA KARIN NIIMA YAKE YI 4K


MUNA DA INGANTATA ZUMA TA HIP ITA MA MUN SARRAFA TA DA KNGAN TATUN KAYAN ORGANIC HERBAL DA KE FIDDA MIKI HIP 6K


MUNA DA ZUMA KIBA WADDA ZAKIYI FRESH DA BULBUL ITAMA RUBA 2 KU 3 ZATA YIMIKI YADDA KK SO 2K


MUNA DA GARIN GYARAN BRST DA KARIN NIIMA SHIMA GUDA 2 KU 3 ZAKI SHA 2K


GASKIYA DA AMANA ITACE NASARAR.MU


MUNA AIKA KAYA KU INA CIKIN YARDA DA AMINCI


MMN MUJAHID __SAKINA HASSAN MUNA SOKOTO DA KEBBI 08066726866


       *🅿️09*


Saboda barcin da ban samu jiya sosai da Daddare ba, ina zuwa shimfid'ar da Ahmad da ya yi barci nima sai na bingire barcin ya fara figata sama sama naji kamar ana kiran sunana a saman kaina Dishi dishi na bude ido na kafin naji ana tab'a kafata guda daya da sauri na mike zaune har wuyan rigana yana dan ja ya yage kada'n,Ido hudu muka yi da Yaya Ishaq da ke tsaye a kaina yana sanye da Riga da wando sauka'kku na zaman gida.

Mitsike ido nayi kafin na fara kokarin saukowa daga kan gadon Lokaci d'aya ina Fadin"Ina..ina kwanaa.."

Amsawa yayi da lafiya lau kafin yace"Ina abun karyawan mu fa..?

Ina kokarin gyara daurin D'ankwalina nace"Yana kitchen"

Juyawa yayi zai fita lokaci Daya yana Fadin"To fa'iza sai na fad'a miki abunda ya kamata ki yi..?

Da kika gama sai ki shigo mana da shi ciki ko..?

Daga haka ya fice nima sai na maramai baya shi ya koma Shashen sa ni kuma na fada kitchen na samu Babban Faranti na hada komai na nufi bangaransa yau ma ba kowa afalon sai dai duk sun yi kaca kaca da kwanukan da suka yi amfani da shi jiya Bayan nasauke na Hannuna ni na Duka ina tattara na jiya na kwashe na kai kitchen na Dawo Daukan jug da kananun kofina shi kuma Ya Ishaq ya fito daga cikin bedroom din sa yana ganina yace"Yauwa Fa'iza wai me kika yi mana na karyawa ne yau..?

Kaina na kasa na lissafa mai Baki ya tabe kafin yace"Zeey kuma tace Fatan dankali take so da Safen nan"

Kallonsa nayi kai tsaye Lokaci d'aya ina Fadin"Akwai dankali sai ayi mata"

Da Sauri yace"Yauwa Hanzarta Fa'iza in dai yau bataci abunda take so ba Rigima zata dinga yi min"

Ko kala ban kara cewa ba na fice Ina zuwa Kitchen sai da na yi wanke wanke sannan na fere dankalin na Dora mata ko araina ban ji Haushin su ba,Sai nake ganin ma ai taimako na yayi yana min alfarma ya bani wajen kwana sannan yana ci da ni duk da ya Jingine aure tsakanina da shi..

Kafin na gama ya leko kitchen din nan yafi sau uku ban gama ba yana ta fadin baya son Rigiman zeey,ina gamawa na juye mata a kula na kwasa na kai mata ina shigowa ya karb'a na Hannuna Lokaci daya yana fadin"Fa'iza tayani dauko sauran yau mulki take ji bazata iya fitowa ba tace kinsan mun sha gajiyan Hanya..Dayake tafi sabawa da Tafiyar Jirgi ita"

Ni dai ban tankasa ba,Dayake ma ba Duka mganarsa naji ba yana gaba ni kuma ina bayansa da Farantin kayan karyawansu har zuwa cikin bedroom dinsa nan saman cafet din na Sauke komai ita Amaryan tana nad'e cikin Blanket dakin na bi da kallo komai ga shi nan a kasa hatta kayan da suka cire Kayan zeey din ta bakinsa duk gasu nan a zube a kasa kila wajen daukan wani abu ne ta zazzago kayan kasa ni dai kaina na kasa bazan iya juran ganin Ishaq ya sunkunya yana mata mgana a kunne ba.

Mikewa nayi zan fice da Sauri cikin dan Daga Sauti yace"Ki tsaya ku gaisa da Honey mana Fa'iza"

Dawowa nayi na durkusa nan gabda kofa sannan na Dago ina kallonta itama Lokacin ta D'ago ammh Rabin jikinta yana jikin Ya Ishaq ne da Sauri na maida kaina kasa ina Fadin"Ina kwana..?ya bakunta.?

Cikin yanayin mganata Hannu ta Dagamin kafin ta juya tana ce mai"Honey ni dai zan rika daga mata hannu..kasan ban iya mgana cikin Ihu ba.."

Mirmirshi yayi batare da yayi mgana ba sai ma karan Hancinta da yaja yana fadin"Kin gan ki ko..?ga Abunda kikace kina jin ci nan Fa"iza tayi miki ki taso mu karya kinsan nayi ma Daddy alkwarin zan kula dake sosai"

Kasa kasa suke mganar ina jin tashin Dariyan su,ta kasan ido nake kallon su shi ya tallafota ta mike tsaye jikinta Daga ita sai wata rigar barci Fara iyakarta gwiwanta sannan shara shara ce ana ganin jikinta.. 

Ni dai kafafuwan su na gani a gabana da yasa nayi Saurin mikewa ina fadin"Sai..i..anjuma.."

Ina jinta tana fadin"Honey ita tayi Dinner din jiya ka tabbata ba oder d'insa kayi ba"

Ina ji yana gayamata da gaske ni nayi da karfi tace"Hy..Sai kuma ta koma tace"Sorry Fa'iza ko..?

Ta fada tana kallonsa sai ya Daga mata kai kara kirana tayi da karfi sai na Dakata da Fitan na juyo ina amsa mata tana jikinsa har Lokacin ni kuma sai nayi kasa da kaina cikin mganarta da sanyin Muryanta tace"Kina jina..?..

Sai na Daga mata kai Da Sauri tace"U are good in cooking..I Mean..Honey plz Help me ka fadamata da Hausa zai bani Wahala"

Ina jin Sautin Dariyansa Lokaci d'aya yana Fadin"Fa'iza Abunda Honey ke nufi shi ne Kin ,iya girki sosai"

Baki ta washe tana gyada min kai sai nayi mata martanin Mirmishinta ban ce komai ba ta kalleni ta kara kallona ina gabansu ne shiyasa naji abunda take fadi"Honey ammh ba ka ce min matarka cousin sister d'inka ce Dad din ka ya aura maka ita ba..?

Da kai yayi mata mgana cikin kara bayyana mamakinta tace"So meyasa bakwa kama da juna..? Infact She is  Blank and.."

Sai ta kasa karisawa ta tsaya tana kallona ni kuma sai na kauce ma ganinsu idanuwana suna kallon Kwalliyar Cafet din dake D'akin.

Kai Tsaye Ishaq yace"Kuma gata Mummuna ko..?

Haka kike son fad'a ko..?

Sai ta Rufe baki alamun taji mganar ta mata girma gira ya D'aga mata kafin yace"Yes ki fada kanki Tsaye ai ba karya kika yi ba Fa'iza bata da kyau..Yes Cousin Sister dina ce Ammh da daad din mu da nata baban D same Father suka hada uwa kowa da tasa..Shiyasa zaki ga muna da bambamci sosai da su"

Ina jinta tana fadin"Ok"

Daganan ni ko kara tsayawa jin su ban yi ba, na fice daidai yana ce mata"Shiyasa kika ga su Amir basa kama da ni..Ita suka debo gabadaya"

Ammh nasan soon kin kusa Haifamin masu kama da ni Honey"

Tashin Dariyan su naji ban ko Tsaya ba Sai da na koma Daki sai kuma naji san mganarta bata batamin rai ba,Komai yaje ya Dawo wanda baisan Darajata ba ne ya tayata suka tozartani Saboda na kauce ma Tunanin kayan su Amir da ya fara Taruwa na kwashe na kai baya na fara wanki ina yi ina tilawar Karatun Qur'ani acikin raina bana so kuma Tunani ko damuwa su shiga raina.

Na gama wankin kenan ina Shanya sai ga shi ya leko cikin Shirin Fita sai Tashin kamshi yake yi da key din mota a Hannunsa.

Gayamin yayi zasu fita sai yammah zasu dawo nayi musu fatan Dawowa Lafiya har ya juya sai kuma ya Dawo yana Fadin"in kin gama wankin nan Fa'iza ki shiga Shashena ki gyara saboda kinsan zeey bata saba kowani aiki ba chan ma yan aiki gareta  suke mata komai Dakin duk ya Hargitse ki dan kintsa mana shi kafin mu Dawo"

Batare da wata Damuwa ba na amsa mai ya juya yana fadin na kula da Ahmad ya lekasa yaga har Lokacin bai tashi ba.suna fita ba Dadewa na gama wankin na koma cikin gida Bangaransa na shiga kamar yadda yace na gyara Hatta da Rigar barci da pant da Bra din ta bata Dauke ba nan ta Watsar da su ni na Tattara komai na gyara na kwashe kwanukam da suka yi amfani dashi na kai kitchen nazo na share Dakin na yi goge goge na Fesa Turaren kamshi na Rufe masa Shashensa na koma Dakina nayi alwalan sallar azahar bayan na Idar Ahmad ya tashi da Rigima ni kuma ban wani ci abinci ba sai na Hada Tea na bashi Nono na ba ruwa sosai aciki.

Naji dadin jin jikinsa da Dama yau ya fara Dawowa da kuzarinsa.

Yunwa ce ta kusa min illah yasa na tashi na Dafa Farar shinkafa naci da manja da yajin da Yaya Asiya tazo min dashi muka kwanta barci sai La'asar na tashi bayan nayi sallah na Goya Ahmad na Fada kitchen.

Jallop din Cousscouss nayi da Kifi Saboda acikin Cefanen da Jamal ya kawo har da kifi,Sai na Dibi Naman jiya da ya rage nayi musu Ferfesu da shi.

Kafin mangariba na gama komai Lokacin Haruna ya Dauko su Amir Daga makaranta sai da suka cire kaya muka yi sallah sannan na zubo musu abinci suka ci Anum sai tambayan ina Daada yake shi da Sabuwar Umman su nace sun fita ammh yanzu zasu dawo wasa waasa sai wajen tara da wani abu suka Dawo Lokacin ma ina koya ma Amir Haruffa ne Anum kuma suna ta wasa da Musty suka shigo suna ganinsu suka tashi suka nufesu gabadayan su suna musu oyoyo ita ta Daga Musty shi kuma ya Daga Anum sai ya Rungume Amir..

Daga inda nake ban tashi ba nayi musu barka da dawowa shi ya amsa ita kuma Hannu ta Dagamin saboda bazata iya Daga murya ba ammh Tana da Fara"a sosai nima sai na Daga mata Hannu.

Su da yaran shashen shi suka shiga sai na mike na Shiga kitchen na kwaso musu abincin su na bisu da shi sun baje afalo yaran suna ta wadaka da Ice_cream da su Sweet har da gashishiyar kaza,Zeey din tana zaune gefen Ya Ishaq har kafadunsu na dukan juna tana mgana a waya sai dai ba Hausa take yi ba,sannan ba Turanci ba kamar dai Fullanci.

Na sauke farantin Hannuna na mike kenan ya kirani na Dawo na durkusa a gabansu ya tambayeni abunda na Dafa na gayamai ya juya yana kallonta da ido suka ma juna mgana naga ta tashi tana wani Rangaji Har Lokacin tana mgana cikin Shagwaba ta shige ciki shi kuma kamar wani Sauna ya Bita da kallo ni kaina na kalleta ballatana shi.

Ahmad ya tambaya nace yana barci Sai cewa yayi"Meke damun yaron nan ne..?barcin sa ya fara yawa fa!

Ni dai ban ce komai ba na tashi na fice bayan nace ma Amir suzo su kwanta da Wuri Saboda makaranta gobe.

Falo na koma na Tattara musu littafan da jakunkunan su na kai musu Dakin su na gyara musu in da kowanne zai kwanta na fito musu da kayan barcin su,nayi ta jiran su har goma ta wuce suna tare da su sai kawai na wuce Dakina naje na Duba Ahmad sai sharan barcinsa yake haka kawai na kasa barci batare da ya'yana sun kwanta ba,Ban samu natsuwa ba sai da naji Hayaniyar su afalo na fito falon Amir nayi ma fad'an meyasa basu zo sun kwanta da Wuri ba su san gobe suna da makaranta"?

Anum ya kallah yana fadin"Umma Anum ce taki tasowa."

ina kai kallona wajenta ta wani kwabe Fuska tana Fadin"Umma ni wajen Anty da Daada zan kwana"

Sai yarinyar ta bani Dariya in ban yi wasa ba Anum ta Dauko iyayi wajen Ubanta to in ba Salo ba da shi ta Saba kwana ko yaushe ta san Anty ma..?

Dariya nayi, da yasa yaran suka Tsaya suna kallona hannunta na kama da na Musty Amir na bayan mu zuwa Dakinsu Lokaci daya ina Fadin"Baki san ba kyau yaro ya kwana inda Babba yake kwana ba. ?

Na fada ina zama gefen karamin gadon Anum cikin kallona tace"Umma to ba Ahmad na kwana a wajen ki ba..?

Kai na girgiza ina Dariya Anum akwai kalkalin baki cikin Mgana ta nace"Shi bai girma ba ai bai kai ku girma ba..Da shima ya kai kamar Mutsy ko Anum dina zan daina kwana da shi zai Dawo Cikin yan'uwansa"

Zata kara mgana na Dakatar da ita da Fadin"Shii..Sai gobe sai mu karisa Anum yanzu Dare yayi gobe akwai makaranta ku sauya kaya Mai jin Fitsari ya shiga yayi kafin ku kwanta"

Suka amsa min da Toh ni na saka ma Anum da Musty kayan barcin su araina ina Tunanin in na yaye Ahmad ya kara girma zai dawo kwana wajen su Amir ita kuma Anum Lokacin ta kara girma ita macece sai na cireta cikin yan Maza na koma muna kwana tare.

Sai da na tabbatar da sun kwanta Mun yi addu'an barci na taya muka Shafa jikinsu sannan na baro Dakin na koma nawa nima nayi shirin kwanciya yau da wuri barci ya kwasheni,Kila Saboda na gaji ne sosai sannan abun mamaki har barcin rana nayi ammh kuma na samu ishashen barci da Daddare.

Da Safe ma kamar jiya ne har su Amir suka tafi makaranta basu fito ba Haruna mai adaidaita sai da yayi min mganar kudinsa yace ayi ma megidan Tuni Tunda yaga yana gari nace zan gayamai in sha Allahu yayi hakuri.

Kamar jiya yau ma har kuryar Daki na kai musu abun karyawan su ita Zainab din tana Tiolet kamar yadda yace ban jira ta ba nayi fitowa ina gasgata mganarsa da yace bata aikin komai bata ma iya ba ganin yadda komai kuma ta kara Birkitasa kamar jiya ban gyara ba yau din basu fita da wuri ba sai yammah,Suna cikin Shashen sa sun kule,Ga shi nayi ta Dakon sa nayi masa mganar Haruna basu fito ba sanda kuma suka fito suna tare da ita Hannunuwan su sarke da juna shiyasa ban yi mai mganar ba yace min gobe zasu koma Saboda aikin su zai kaita gidan Anty Binta da gidan Anty Mahma sai kuma su zaga gari nayi musu adawo lafiya.

Yace kada nayi abinci da su zasu ci a waje na amsa mai da toh sannan ya kara Umartana da in shiga bangaransa na gyara musu kamar jiya nan ma na amsa mai da toh.

aiko basu dawo ba sai goma da Rabi na Dare ina Falo ina fama da guga Anum da Musty sun gaji da jiran Dada da Anty  sun yi barci Amir ne ke taimakamin in na goge daman kayan su ne, sai ya rika Dauka D'aya bayan d'aya yana kaima kowa cikin Dirowan kayansa.

Albarkacin Zainab har aka kawo ma su Amir Chips da su pizza,Sai kuma suka Tarar da su Anum din sun yi barci Ya Ishaq shi kadai ya shiga bangaransa ita ta tsaya tana waya naji dai Tana ta ambaton wani suna Daddy tana mgana cikin shagwaba irin na ya'yan gata..sai da ta gama sannan ta Dagamin Hannu sai nima na Daga mata Amir ta yafito da hannu yazo wajenta tana mai mgana ni ban ji me take fadamai ba.

Ta mike tana kallo na inaga abun gugan da taga ina yi ya bata mamaki kusa dani ta kariso da takalminta mai Tsini ta Duka a gabana tana fadin"Sannu fa"

Na amsa mata da mirmishi kallona tayi kafin tace"Hannun ki da bayan ki basa ciwo ne..?ba mai wanki da guga ne..?

Sai ta karkato kanta tana Fadin"Kina jina..?.

Sai ta ma bani Dariya cikin yanayina nace"Ina jin ki mana..ai ina jin mgana in kika yi a kusa dani"

Kai ta jinjina kafin ta kara kallona ta ce"Sannu fa"

Na kara amsa mata sai tace"kina kokari fa..na ji dadin girkin ki..In da a Abuja kike da kin samu kudi..Gidajen mu duk kukus suke d'auka sannan irin ku kuna samun aiki a manyan Restaurant wajen saida abinci kin gane..?

Tafad'a tana kallona Saboda Hausan nata sai a hankali bai zauna ba sai na daga mata kai alamun ina jinta sai kawai taci gaba da fadin"Meyasa baki yi karatu ba Fa'iza..?na tambayi Honey yace kece baki so why.?

Sai kawai na kalleta abunda na Lura da Zeey din macece faram faram bata da girman kai ko D'agawa sannan ita Kai Tsaye ce duk abunda ya shige mata Duhu sai ta yi mganarsa shiyasa ban damu da mganarta ba sai na yi mirmishi kafin nace mata"Ba ni ba ce ba na so..Karatun ne bai dace da Kaskantattun mata irina ba..Wad'anda basu da gata sannan masu nakasun ji irin ta Lalurata.."

Kallona ta tsaya tanayi ina ganin bakinta na motsi ta kasa mgana ita kuma tana so tayi mgana ammh hausan bata san yadda zata min na gane ba,Muna cikin hakane sai ga Ya Ishaq ya leko ya kirata sai ta tashi ta tafi ammh sai da ta waigo ta kalleni nima na kalleta ina tunanin mamakin mganata take yo menene ban sanin mata ba.

Daganan bamu kara haduwa ba sai da Safe da zasu tafi,misalin karfe goma na Safe yara tuni sun tsufa a makaranta,ganin har suna shirin tafiya yasa na yi mai mganar Haruna ina ga saboda a gabanta ne yasa bai yi Fada ba,ya cire dubu goma sha Hudun sa ya bani Saboda duk wata Dubu takwas ne,Sannan ni kuma ya bani Dubu uku na rike a hannuna wai bashi da kudi nidai na amsa ina godiya,Zainab ta bani Hannu mun yi musahaba tana ce min"Sai na ganki kun zo min hutu Abuja ke da yarana"

Mirmishi kawai nayi mata ta Dauki Ahmad har Haraban gidan na Rakasu ko Saboda ganinta ne yasa ya bude get din da kansa Dubu biyar ta bama Ahmad sabbi tace ya raba shi da su Anum,Har motar su ta bar Haraban gidan tana Dagamin hannu nima ina Daga mata bayan sun fice sai na maida get din na kulle na koma cikin Gida ina Sauke Numfashi.

Ban zata haka amaryan tasa zata karbeni ba sai ga shi na sameta a yanayin da ban zata ba.

Da yammah da Haruna ya Dauko su Amir daga makaranta na basa kudinsa yana ta godiya Anum har zata min kukan banza don nace Daada da Anty sun koma Abuja sai da nayi mata jan ido sannan ta shiga Taitayinta.

Tunda suka tafi bai kirani ba,nima ban kira ba nadai san shuru lafiya ne in da ba Lafiya da naji Labari sai nima na kama kaina na cigaba da kula da kaina da ya'yana tafiyar su da Sati Daya Sai ga Goggon karofi tazo min kamar Daga sama nayi murnan ganinta har bansan yadda zan kwatanta ba.

Tazo min da su kuka,Kubewa garin kunu garin Danwake,kayan miya da kuli kuli,Sai ta zo ma da su Amir gyada da mai gishiri da mai bawo,Sai alewan yara,Suna makaranta ko da ta iso da rana ne Lokacin nama zata ko Daga gidan Mama take sai tace min Daga Dutsemah take ta biya ta gaida ta Madina ta dade bataje ba naji Dadin jin Tamadina tana lafiya.

Bakina yaki Rufuwa da Goggo tace min kwana zatayi sai gobe zata koma ni kawai tazo dubawa.

Su Amir nata tsalle da suka Dawo suka ganta,suna son zuwa karofi ammh Ya Ishaq baya bari daga makaranta sai gida sai ko gidan Mama in ma sun je to yini ba kwana ba.

Bamu samu kebewa ba sai Dare bayan yaran sun kwanta Goggo ta na gayamin taji duk abubuwan da suka faru basu yi mata Dadi ba Sai dai tayi ma Yaya mariya fada meyasa ta biye ma Binta ai ko banza ni yar'uwanta ce bai kamata ta taho ta kyaleni ba,Goggo tace kinsan mariya da bakar Zuciya,Sannan ta riga ta rantse ne yasa bata ce ta Dawo ba,ni nake fadama Goggo zuwan ya Ishaq da amaryansa na gayamata mun zauna Lafiya da ita har suka koma Goggo ta cigaba da min nasiha duk akan nayi hakuri ne watarana sai Labari.

Sai Wajen d'aya saura na Dare muka kwanta da Safe kuma da Goggo Tayi shirin tafiya nace ta leka gidan Mama su gaisa tace min bazataje ba Dakyar na Lallasheta tace zata biya tayi mata Murna dagachan zata wuce a bakinta nake jin Hajiyar Dala ta kirata a waya tana mata fadan bata kyauta ba da bata zo ba Goggo tace nayi mata Tas daga Lokacin bata kara kiranta ba.

Sha d'aya na Safe na raka Goggo Har bakin Hanya mun rabu tana ta kara jadaddamin nayi hakuri da rayuwa watarana komai zai wuce sannan na Dage da gayama Allah shine Sarkin Duka Duniya gabadaya.

Mun rabu kamar na bita haka nakeji ammh ba Dama,har da kwallata sai da nayi,Bansan ya Goggo suka kare da Mama ba sai da washegari Badariya tazo take bani Labari Mama har da kuka ta kira Anty Binta da Ya Ishaq akan Goggo Tazo tayi mata cin mutumci Saboda ni..

Gabana ya fadi na zare ido ina kallon Badariya kafin nace"Sabo da ni kuma..?

Badariya tace"Tabbas..Kinsan Halin Mama har Hajiyar Dala sai da ta kira ta fada mata..Ni dai nasan kila Goggo Fada tayi mata shikenan sai cibi ya zama kari Anty Binta nata fada haka ma shi kan shi Ya Ishaq din a waya sai Fada yake barin ma jin Mama nata kuka"

Sai jikina ya fara rawa nasan komai kaina zai dawo aiko hakan ce ta faru Badariya ta tafi ba Dadewa daman Daga makaranta ta biyo sai ga Anty Binta da Mama har cikin gida wanda bazan iya tuna zuwan mama gidan nan na karshe ba.

Zagi da gori da cin mutumci ba wanda basu yin ba ina da goyon Ahmad a baya na Mama ta saka Hannu ta tsinkeni da mari,na Dafe kuncina Hawaye suka Gocemin,Ahmad na barci ne ammh sai da ya tashi Hayaniyar Mama yasa ya tsorata ya fashe da kuka shi yana na Sarari ni ina na zucci.

Mama ta kama kunnuwana ta murde tana fadin"Ni zaki hada ma gulma da munafunci har Goggon karofi ta taka har gidana taci min mutumci don Ubanki..?ai nayi miki komai Tunda na rike ki kuma sannan daga karshe Mijina ya aura miki D'ana kika shiga Cikin zuru'ata duk da bana so..Shegiya mai bakar aniya,Wlh fa'iza na tsaneki na tsani na bude ido na ganki a matsayin surukata"

Anty Binta ta karbe da Fadin"kuma ban da Ishaq din uban waye zai aureta ya zauna da ita ahaka..?

Mama tace'Ki barta zan yi mganinta Tunda bata san mutumci ba"

Haka suka gama zage zagen su,suna yi suna Dungurina suna murdemun kunni sannan suka saka kafa sukayi tafiyar su haka na zauna na Rumgume D'ana ina kuka shima yana kuka har sai yaushe ne zan daina Fuskartar wannan Tozarcin..?

Ba mai Lallashina na gama kukana na Share hawayena,Ashe ban tsira ba Sati biyu da Tafiyar su Ishaq,sai gashi ya Diro ranar asabar da yammah,Abunda yayi min yasa na Fahimci daman saboda yaci min Mutumci ya Dawo.

Har Bangaransa ya kirani na Duka gabansa shima ya ci min mutumci,har yana fadin ba Domin mugun kalaman bakin Baba akansa ba wlh da sai ya Sakeni sai naje Goggon ta auramin Isa ko Yusuf cikin manyan ya"yanta sannan ya kara jamin kunne akan yaya mariya da gaske yake yi kada ta kara zuwarmai gida in kuma wlh tallahi ya kara ganinta sai ya wulakantata.

Na Dago kaina cikin Hawaye muryata ta shake cikin wani yanayi nace"Kayi hakuri..Ba..zan iya fada mata ta daina zuwa ba ne"

Sai kawai na Fashe da kuka Tsawa ya Dakamin yana fadin"To ni zan gayamata in muka hadu Tunda gidan nan nawa ne ina da iko da shi kada na kara ganinta acikin su..In kina Tunanin yar'uwan ki ce in kun had'u wani waje sai ku gaisa ammh ba"a gidana ba kin ji maa na gayamiki"

Sai na kasa mgana kaina na kasa na Share majina kafin nace"Kayi hakuri don Allah.."

Mikewa yayi a fusace yana fadin"Ke dai kika sani kin dai ji abunda na gaya miki..daman abunda ya kawoni kenan Har ga Allah bana son zama agidan nan chan yafiye min kwanciyar Hankali ki kula Fa'iza kada a kara kirana afadamin an hada baki dake an tozarta uwata in hakan ta kara Faruwa zan manta kalaman Baba da komai kema na wulakanta Rayuwarki wlh"

Daman Tozarta ne yazo yi kuma yayi washegari tun Safe ya Dauki hanya,ko sallama bai min ba sai zuciyata ta kara Kek'ashewa na kara Fahimtar cewa ni din ba kowa bace a zuciya Ishaq da duka ahalinsa akwai yuyuwar na nemi abunda zan tsaya da kakafuna ko Saboda gaba da kuma ya'yana domin na Lura hankalinsa yayi gaba daidai da su Yaran ya daina Damuwa da su Sosai.

Tun tafiyar nan da yayi sai da yafi wata bai zo ya ganmu ba,Kudin Hannuna duka ya kare bamai lekomu dagamu sai Allah,kayan abincin mu sai ya kare mun fara shiga yanayi sannan ake aiko mana da Cefane wani Lokacin Direban gidan Anty Binta ko Badariya,a wannan gabar sai da yayi wata biyu da kwanaki sannan yazo ya ganmu shima din sallama suka zo yi Zasu tafi Umra shi da Zeey da iyayanta gabadaya har da ita Zeey din suka zo sallama kwana D'aya suka yi suka koma gidan Mama kuma suka Sauka sai da Safe suka zo min sallama,nayi masa korafin Haruna ya fara mganar rashin biyansa akan Lokaci sai ya fara masifan bazai iya ba gaskiya shi bashi da kudi kuma haka ya tafi bai bani ko sisi ba,Daganan na kuduri niyar bazan kara mai mganar ba Zan neman ma kaina mafita,Bani da wata mafita alokacin sai na maida lamurana wajen Ubangiji na rokensa yaga Halin da nike ciki da ni da ya'yana ya Gaggauta sama min mafitan da zan kula da kaina da ya'yana.




*Janafty**KANA NAKA..!*


*Wattpad:JamilaUmar315*

*Mallakar:Janafty*

*Arewabook:Jamilaumarjanafty*


MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT Y'A SKWATO__SAKINA HASSAN 08066726866


INA MATA Y'AN KWALISA MASU SON GYARAN JIKI MACCE DA TASAN KANTA KULLUM CIKIN GYARA TAKE


INA MATA MASU FAMA DA RAMA KU KINSA KAYA BASU KAMA JIKIN KI 😫


INA MATAR DA ADDA JIKI BAKI DA HIP BAKIDA BAYA IN KINYI DRESS BAYANKI A SHAFE


INA WADDA KE FAMA DA ZUBEWA NONO KU KE BAKI JIN DADIN GANIN SU KAMAR SILIFAS 


KINYI TA GYARAN BRST HAR KIN GAJI HJY TA GYARAN BRST WAHALA GARESHI DUK WADDA TACE MIKI GA MAGANIN BRST DA SHA ZAIYI TO KARYA TAFADA MIKI GYARAN BRST YANA SON JUREWA DA DAGEWA IN KIN FARA BA'A TSAYAWA INSHA ALLAH SAI KIGA SUN ZAMA NORMAL


MUNA DA INGANTATA ZUMA BRST DA MUNKA SARRAFA DA KAYAN ORGANIC HERBAL SU MACA DASU AGUAJE WADDA INDAI KIN RIKE TA INSHA ALLAH ZAKI GA SUN CIKO SUNYI KOSHI RUBA 2 KU 3 SUN ISA YAZAMA MIKI YADDA KK SO 4K


MUNA DA GARIN HIP DA BRST YAKE GYARA DA GYARAN JIKI DA KARIN NIIMA YAKE YI 4K


MUNA DA INGANTATA ZUMA TA HIP ITA MA MUN SARRAFA TA DA KNGAN TATUN KAYAN ORGANIC HERBAL DA KE FIDDA MIKI HIP 6K


MUNA DA ZUMA KIBA WADDA ZAKIYI FRESH DA BULBUL ITAMA RUBA 2 KU 3 ZATA YIMIKI YADDA KK SO 2K


MUNA DA GARIN GYARAN BRST DA KARIN NIIMA SHIMA GUDA 2 KU 3 ZAKI SHA 2K


GASKIYA DA AMANA ITACE NASARAR.MU


MUNA AIKA KAYA KU INA CIKIN YARDA DA AMINCI


MMN MUJAHID __SAKINA HASSAN MUNA SOKOTO DA KEBBI 08066726866


     *🅿️10*


*Wacece ZAINAB...?*


Cikakken sunanta shine Zainab Lawal bako asalin duka iyayanta uwa da uba Fulani ne gaba da baya,Mahaifiyarta Hajiya Halima bata yi karatun boko ba Saboda yar asalin rugar  Njob'oli ne fulani Jahar yola,Shi ma Dr.Lawal din, Mahaifinsa ya'yan maza suke da Mahaifiyar Hajiya Halima auran zumunci ne iyayansu suka kulla a tsskanin ya'yan nasu.

Shi Dr.Lawal a cikin garin Yola ya girma kuma nan aka haifesa saboda Mahaifinsa ya baro cikin Ruga saboda neman ilimi kuma ya samu Dalilin da yasa bai koma cikin ruga ba kenan sai dai Lokaci bayan Lokaci yana zuwa Dubasu,Sannan shima matarsa Daga Rugar aka aura masa shiyasa shima Alhaji Lawal aka ki bari ya bar gida.

Alhaji Lawal bako yayi karatun Boko har matakin Phd dinsa ya fara aiki da Hukumar Tattara haraji ta kasa reshen Jahar Yola,kuma achan ya fara zama bayan an aura masa Halima,Da farko yaso ya Bijirema auran ne,ganin kamarsa mai ilimi dan gayu a had'asa da yar Rugar da batasan komai ba Sai dai ya sauya shawara lokacin dayaje yaga Halima sai yaji zai iya auranta Saboda Tana da kyau Farace doguwar Bafullatana,ga gashi har gadon baya Hancinta har baka kyau kamar ita tayi kanta sai yaji alfahari ya karun masa Saboda Shi yana son abu mai kyau wanda zai zame masa abun Alfahari watarana.

Bayan auran su a yola suka fara zama,Ya na son Halima sosai,Saboda kyanta da sanyin Halinta,sannan Bafullata ne irin sa,Abu daya ne yayi mata cikas rashin ilimin Boko na addinin ma ba sosai take da shi ba Saboda ko acikin Rugar ba kmar yanzu da gwamnati ke basu tallafe tallafe domin inganta ilimi a rugga ba,

Yaso ya barta tayi karatu ammh Saboda Tsananin kishinsa yasa bai barta ba,kuma taso tayi karatun tunda ta dawo cikin gari da zama,ammh ya hanata saboda Yana da Tsananin kishi,bazai jure ganin ta a makaranta tana gwagwamarya cikin maza ba,Sai ya hanata ya nuna mata ilimi mace shine zaman gidan mijinta ta kula da ya'yanta dalilin haka yasa sai ta hakura iyayan su kuma Ilimin bai Dame su ba damuwa suka yi da karatun ba.

Dr.Lawal bako dan boko ne sosai Domin Rayuwar boko yake yi a gidansa shi ya tsara hakan tun farkon zaman auransa da Halima,Ya'yan su biyu ya tsara zasu haifa Saboda a cewarsa bazai zo ya haihu da yawa ba ya kasa Rike ya'yansa ba,Sai dai Kana naka Allah ya riga ya gama nasa Sai da Halima tayi haihuwa Uku suna yin wabi sannan ta Haifi zainab ta Tsaya Tsakaninta da kanwarta Zeenat suna kiranta Zuzu Shekara Biyar ne daga kanta kuma sai ta Haifi namiji sai dai ko arba'in din sa batayi ba ya koma ga Allah Daganan suka tsaida Haihuwa a cewar Alhaji Lawal bako Kada ta kara Haihuwa kyanta da Nagartatan su Lalace ita kuma bata da yadda zatayi bata iya masa gaddama rayuwarta da ita kanta sai abunda ya tsara mata.

Duka ya'yan nasa yadda yaso haka ya tarbiyarta dasu,Halima bata isa ta nuna wani iko kan ya'yanta ba tun suna kanana sai abunda Baban yace shi zasu aiwatar sannan baya shawara da ita gani yake bata san ne take yi ba Tunda bata da Ilimin Zaman duniya.

Zainab da kanwarta Zuzu sun taso cikin Sangarta da Sakewa da kuma Tsananin gata,ba kwaba ba kyara ba Gyara haka suka taso a gaban iyayansu koda sun yi wani abun mara kyau in uwar zata kwaba musu sai Uban ya hana sai ya rika nuna su kadai ne ya"yan su in basu ji dasu ba da waye zasu ji..?Dole ne su ji da su tunda basu da kamar su,In tace hakan bai kamata ba sai yace duk wanda kika ga bai sakar ma ya'yan sa Gata ba bai da shi ne sannan bai san Darajan ya'yan ba ne.

Daga karshe sai ta koma bangaran yaran sai ta Fahimci suma sun fi jin mganar Uban su fiye da ita tun suna yara sun Fahimci mahaifiyarsu kamar Hoto take sai Uban yayi shawara da su,ammh ita bai neme ta ba ko wani abu yace in suka ce Daddy mommy fa..?Sai yace su kyaleta kawai mommy bata san komai a wannan zamanin ba to har suka girma da wannan Tunanin aransu Daddyn su shine nasu uwar su kuma ta nan a matsayin Mahaifiyar su ammh bata da wani Say a gidan da Rayuwar su gabadaya.

Sun taso da Yare guda biyu a bakin su Turanci da Fullanci saboda Daga Uban har uwar basu yarda Yaren su ba In dai suna gida daga Fillaci sai Turanci suke yi Hausa kuma sai dai a waje ko a makaranta,Sannan in sukaje ziyara chan Rugga basa wani yare sai Fillanci sai yaren ya zauna Sosai a bakinsu..

Zainab da Zuzu kyakyawan yan mata ne na gani na fada kamar su, sukayi kan su Saboda kyau da zati to bangaran Uwa da uba duk kyawawa shiyasa suke jajir kamar a taba jini ya fito sannan sun tashi cikin gata da jin Dadi,Zainab ta gama junior secondary dinta suka koma Abuja da zama anan ta ida karatunta ta fada Universty of Abuja ta karanta Chemisty,Gatan duniya ba wanda basu samu ba komai suke nema kafin su yi mgana sun same shi Tun suna kanana komai yan aiki ke yi musu shiyasa su Rayuwar Hutu suka sani da jin Dadin.

Dr.Lawal bako Rauninsa Daya ne ya'yansa yana tsananin kaunar su,Zai iya batawa da duk wanda ya nemi ya tabasu sannan zai iya karta ma kowa rashin mutumci a kan wadanan ya"yan nasa,Yana nuna musu kauna a fili har tana wuce misali Hajiya Halima da suke kira Mommy ko tayi mai mgana sai yace me ta sani kan wannan zamanin tayi mai shuru kawai shiyasa ita nata ido ne sai dai tana addu'an Allah yasa kada su zame mai Raunin da zai zame masa Lalura watarana.

Ishaq kabir karofi ba Zainab ya fara sani ba,Dr.Lawal bako ya fara sani Lokacin da aka mai karin girma da sauyin wajen aiki ya koma Abuja shine ke rike da babban Ofishin su na Abuja,Haka kurum Ishaq yaji Dr.Lawal na Burgesa saboda he is Educated and Innocent,sannan jajirtattace ne kan aikinsa,Shi kuma Ishaq yana da Ladabi da Biyayya ga manyan sa shiyasa suka Saba da Dr.Lawal,Kuma karin ma abun yana ganinsa Farin namiji gaye kyakyawa mai ilimi da sanin ya kamata Dr.Lawal na son harka da mutane masu kyau da wad'anda suka san abunda suke yi,Dalilin Sabawar su yasa Ishaq bai iya kiran sunansa Sai dai yace Daddy kafin shekaru su ja su san komai na juna har gida Daddy kan gayyace sa gidaansa yaje yaci abinci anan yaga Zainab ya nuna yana sonta lokacin tana shekarar karshe a jami'a tana masters d'inta lokacin daya ganta yaji aransa mafarkin daya Dade yana yi ne Allah zai tabbatar masa bai nemi zainab  kai  Tsaye ba sai da ya fara Tuntubar Daddy shi kuma yace ya bashi lokaci ya kara Bincika Ishaq din kuma ya Samu komai yadda ya sanar da shi Cikin Lokaci ya amince batare da Shawara da Hajiya Halima ba Ya'yansa kawai yayi shawara da su,Daman kuma achan Rugga an saka ido kan rashin auran su zainab din,Shi daman baya so ya aurar da su in da zasu sha wahala ne ya fi son ya aurar da su inda yake da Mgana a wajen zai iya kula da ya'yansa ya kuma Tofa komai a lokacin da yaso a kan Rayuwar ya'yansa.

Zainab bata isa tace taki Ishaq ba ganin Farko da tayi mai taji ya shiga ranta suka fara soyayya sai dai da Farko taso ta Damu da taji yana da mata sai ya nuna mata kada ta Damu Fa'iza ba komai bace a rayuwarsa face Uwar ya'yansa ita ce First love dinsa da ta fadama Dr.Lawal Dariya yayi yaji Dadin da yarsa zata kasance Zara Cikin wata Hajiya Halima nata sai dai ido kawai har gwara ma Zuzu bata kai zainab rawan kai da Daukan duka Hallayar mahaifinsa nasu ba ita ta kan tsawarta mata taji,Ita ma tana nan tana karatu a Nile University of Abuja,zainab kuma tana gama karatu tayi Services a wani kamfani karafuna bayan ta gama kuma suka Riketa aiki a wajen,Batare da Ishaq din ya sani ba kuma Lokacin har an yi mgana ta iyaye lokaci kawai za'a sanya har zuwa Lokacin da akayi auran Ishaq bai fahimci bai da wani iko akan Zainab ba sai abunda Mahaifinta yace da shi ta ke amfani.

Shi ya gina auransa kan Soyayya da kyau nasaba kudi da nagartan ilimin zamani,ita kuma ta auresa ne Saboda kyansa da kudinsa sannan saboda Mahaifinta,shi kuma Dr.Lawal bako ya amince da auran ne saboda yana Tunanin Daga Ishaq har Zainab suna karkarshinsa ne zai iya yanke kowani irin Hukunci kan yarsa batare da ya D'aga ido yayi mgana ba.


Muje zuwa..!


****


*Katsina..*

Bayan wata daya.


Mutanen Umra sun dawo an kawo Tsarabobi kala kala nima Badariya ta kawo ma su Amir nasu,abakin ta nake jin Tsaraban ma aiko da shi sukayi ta Abuja suka sauka,Ya Ishaq din kuma bai zo ba,an kawo ma yaran Jallabiya Amir da Musty,Anum kuma Riga da wando,Ahmad kuma kaya riga da wando masu kyau da yarari,Sai Dabino da ruwan zamzam na amsa nayi godiya Daman ni ban saka aka ba ballata don ba'a bani ba na Damu Badariya ta fadamin har Hajiyar Dala an aika mata Da Tsaraba to daman ai ya kamata a aika mata ta chanchanta.


Damuwa ta daya ne yanzu yadda komai ya ke kara lalacewa,Ni ba na jin kaina sai ya'yana sune a gaba,Ko Haruna ni da kaina na shirya na shiga har gidansa Daman makota muke bamu da nisa,Na taba shiga sau biyu tun Fara kai su Amir makaranta,Sunan matarsa Sa'adatu,dayake bana harka da kowa sau daya ta taba shigomin gidan daganan bata kara ba Ishaq bayan Yan'uwana da Dangina har da Mutane ma ya rabani da su Ahalin kuma an ce Mutane Rahma ne.

Naje na same sa na bashi Hakuri akan rashin Biyan sa kudin sa wajen wata uku sai ya nuna min bakomai an zama D'aya tunda Hakkin makota ya hadamu matarsa Sa'adatu ta karbe ni Hannun Bibbiyu,Na isketa tana ta Saida Saide kayan miya da su maggi da gishiri kayan dai kulle kulle na gida na mata sai kuma zuwa ake yi ana siya sai abunda ya bani sha'awa naji Dama ni ce ban iya shuru ba har sai da nayi mata mgana nace dama nice ita ina son nima na Fara sana'ar cikin gida na mata, bata ji ba sai da na kara maimaita mata sannan taji ni Dariya tayi kafin tace"Haba Hajiya kamar ki ina ke ina wata sana'a..?kuna da Rufin asirin ku..Sana"a ai sai irin mu matan talakawa mu samu na Rufa ma kanmu asiri damu da mazajen mu"

Naji mamakin mganarta ni kuma sai nace mata"ai sana'a bata ga Talaka  bata ga mai kudi..Muna yin sana'a ne Domin dogaro da kanmu da kuma ya'yanmu sannan ita mace da neman na kanta a kasanta saboda kada gazawa ya zame mata nakasu watarana"

Sai ta jinjina kai kafin tace"Kuma hakane Hajiya"

Ina kallonta kai tsaye nace"Ba sunana Hajiya ba..Sunana Fa'iza ko ki kirani maman Amir"

Daganan tayi dariya muka cigaba da Hira sama sama,Ban jima ba na koma gida tundaga Lokacin araina na saka ma raina bazan zauna na mutu ni kad'ai acikin wannan gidan da bama ceto sai Allah ba nima zan rika fita na shiga jama'a domin su din Rahma ne.

Muna cikin Haka aka kore su Amir daga makaranta suna dawowa suka fadamin suna zuwa aka koresu kudin makaranta acikin makarantar suka zauna har sai da aka tashi Haruna yaje ya Daukosu hankalina ya tashi na rasa yadda zan yi na so na kira Ya Ishaq na fadamai sai kuma bani da kati ko na flashing kuma bani da ko asi a hannuna sai na koma na Rumgume hannunawana kawai na rasa mafita,kawai sai nace su dakata da zuwa makarantar sai an biya a baya duk Lalacewa yana biyan musu kudin makaranta akan Lokaci basai ta kai ga an koresu ba,ganin sun kwarari sati a agida ba bokon ba islamiyan sai dai nayi musu na Islamiyan agida,Sai suka fara Damuwa suna ta tambaya na Umma meyasa muka Daina zuwa makaranta..?Anum da Musty kenan Amir shi yafi su wayau da sanin me ake ciki,gabadaya na rasa mafita Kwana takwas da Faruwar haka Ranar da yammah sai ga Jamal yazo shima k'wallo suka zo yi anguwan ya shigo gidan ya iske su a bakin Anum yaji basa zuwa makaranta da ya ce meyasa yau basu je ba..?Shine daya tambayeni nace an koresu ne basu biyu kudin makaranta ba yana ta mamaki ya tambayeni ko na fadama Ya Ishaq sai nace mai A'a.

A gabana ya Daga waya ya Kirasa yana fadamai abunda ke faruwa duk da bana jin me yake fada nasan Fada yake yi kuma duk a kaina,Sai da suka gama mgana yace min Ya Ishaq yayi fada kan meyasa ban kirasa na fadamai ba..?

Har Jamal din na fadin"Anty Fa'iza kema da kin kirasa kin fadamai Halin da ake ciki.."

Kallonsa kawai nayi ban yi mgana me zan ce..?ko na fadamai ba ganewa zai yi ba shurun yafi alheri.

Labari har kunnen Mama da Anty Binta na kuma san nasha Zagi da cin mutumci washegari Jamal din yazo ya Dauke su ya kaisu makarantar ya biya komai,Sannan da yammah ya kawo min 20k a bama Haruna kafin ya Dawo na karba nayi godiya da Safe kuma da kaina na shiga na kai mai yana ta godiya nima inayi sai naga ai ni ce da Godiya domin ni yake yi ma alfarma.

Haka rayuwar ta cigaba da gangarawa masu jin dadi suna ji masu jin akasin haka ma sun cigaba da ji,Har azumi ya karato Ya Ishaq bai waiwayo mu ba abun na bani mamaki ace in shi ya manta damu su Mama ai basu manta yana da mata da ya'ya ba ammh sai naga suma basu damu ba kamar hakan ma yafi ye musu,Kayan abinci ko wani sako sai dai ta Hannun Mama ko Anty Binta batagwara,Ni bani da wata Daraja ko kima sai ta zaman ya'yansa kamar yadda yace din.

Tuni yara har sun saba tafiya makaranta ba biskit ba Lemo saboda babu Daga shinkafa sai taliya ake kawo min sai man girki da kayan maggi,duk abunda bazai zama Dole ba ba'a kawo mana shi,Nama ko mun manta rabon mu da shi,ni bana ma jin kaina yaran nake ji sun gaji da Rigima sun Hakura tunda babu sannan Tun suna Zencen Daada har suka hakura suka Dangana ni ce karfin gwiwan su shiyasa bana yarda na Sare ko Raunina ya bayyana agabansu

Ahaka muka fara azumin watan Ramadana,Har kuma muka fara shi muka sauke Ya ishaq bai zo ba,kuma bai taba nema na ba,Ni ma sai na kama kaina sai dai da watan nan mai albarka ban yi barci ba nayi addu'an Allah ya sama min mafita domin ya'yana domin goben su,Kayan sallar yara Sai ana gobe sallah Jamal ya kawo musu Amir da Musty shadda guda biyu sai yan kanti kowanne D'aya d'aya Ahmad ma shadda guda daya sai sauran yan kanti Anum kuma Atamfa da leshi dinkakku sai Doguwar riga guda daya,sai takalma su sai nawa kala daya jal na wata Bakar atamfa,ko araina ban ji zan sakaba sai dai in na zauna ba kaya ammh in dai suturan Ya ishaq ne na hakura da su har abada Tsoffin dai zan cigaba da sawa Tunda  bani da zabi ammh bayan ya jingine aure na dashi na cire ma raina kara Daura wani abu daya fito daga Hannunsa..

Ganin yadda ya kwarari wata Hudu bai zo ya ganmu ba nasan da gaske yake yi ya zabi Zainab a kaina sai ban ji komai ba sai dai naji Bakinciki har da ya'yan sa suma ya jingine su..?

Ban damu ba ni kawai Fafutaka nake yi har akayi azumi akaga gama bamu ci ko tsokar nama ba ballatana su Dankali da kwai sai tsurar abinci kawai nice nake Sarrafa nau'in abincin Tunda Allah yasa na iya sai Wahalan bata mana yawa sosai ba.

Naman Sa da naman kaza Jamal ya kawo min ranar idi da Safe na gyara na soya su Anum nata murna zasu ci Nama sai da nayi musu kwallah ina Tunanin tun yanzu kenan to nan gaba bansan wani Hali ni da ya'yana zamu shiga in dai na zauna ahaka ba,

Allah Sarki Goggo washegarin Sallah sai ga Hafsatu ta aiko da sakon Nama da Cincin da Cake,Naman soyayye da Danye,Sannan da sakon Hijabi Sabo da Anty mariya ta dinkamin da takalmi na karba na rumgume kayan ina kwallah Allah Sarki yan'uwana basu manta dani ba duk da ni ma ban manta da su ba yanayi ne yasa nayi nesa da su ba acikin son raina ba

Ta fadamin daga gidan Tamadina take jiya taje chan ta kwana ta kai mata kaya daga kano Anty Asiya ta aiko dashi sai naman sallah Daga Goggo sai na wajen Ya mariya naji dadin jin Tamadina tana lafiya,Naji takaici bani da abunda zan daga na bama mahaifiyata nima nema nake yi.

Zuwan Hafsah ne ya Debemin kewa Dani da yara Ranar sallah ta uku gidan Mama muka yini sai Dare Ya Ishaq ya sauka shi da Zainab,Anty Binta da Mama suka rasa ina zasu saka su saboda murna mun gaisa da ita sai mamakin ganin chanzawarta nake yi ta zama wata katuwa ta kara gogewa shima gogan ya Sauya kamar ba shi ba har da Tumbi ya sauke.

Darajan zainab yasa da ni da yara da Hafsah ya kwaso mu muka koma gida,Wannan karon ma Shashen sa ta sauka kuma ni na rika wahala da ita da shi,Dalilinta yasa yayo mana Cafane mai rai da lafiya Saboda sai abun take so ake ci acikin gidan,Da kuma zabinta ake amfani..

Hafsah ita kanta da take yarinya sai da ta ga abun bai dace ba ranar da zasu fita yace na shiga na gyara Bangaransa nasa,Suna fita ta kalleni kafin tace"Yanzu Anty Fa'iza bayan Girkin da kike musu har da gyaran inda suka kwana kamar wata yar aiki..?

Ban ce mata komai ba sai ma Dariya kawai da nayi to ai batayi karya ba kamar yar aiki nake agidan nan,Sati Daya suka yi mana suka koma inda suka fito,Hafsah dai ana jibi Tafiyarsu ta koma Karofi Saboda an koma makaranta..

Bayan tafiyar su muka koma Gidan Jiya kamar yadda muka Saba dai,Allah ya taimake ni Matar Ya Isa wajen Goggo ta haihu,yan biyu Dalilin dayasa Mama tace na shirya aje suna Dani,Murna kamar an biyamun aikin Hajji,Dukkamu muka tafi har da Anty Mahma da Halisa da yara,Nima tare da su Amir muka tafi chan na hadu da Ya Mariya,Yaya asiya dai bata samu zuwa ba,naji dadin zuwana karofi Allah yasa kuma Lokacin Tamadina tazo gida na kai mata su Amir ta gansu sai mamakin girman su take yi shi da Anum,Koda wani Lokaci in naga Tamadina sai na tuna da Dan'uwan  ta da akace sun hada Uba,Wanda tunda mahaifiyarsa da Danginsa suka tafi dashi ba"a kara jin Labarinsu ba sai ina Tunanin ko yana Raye..?ina fatan yana Raye domin shi kadai ne shakikin Mahaifiyarmu.

Hajiyar Dala tazo anan take kara Fadin Bikin Diyarta Suwaiba nan da wata Daya,ban saka raina ba Saboda nasan ba barina ma za'ayi naje ba.

Kwananmu biyu muka Dawo gida Mama kuma Yamai tatafi kanwarta Hure mijinta ya rasu ta tafi gaisuwa ta jima tafi Sati biyu Sai Badariya ta Dawo gidana tana kwana in gari ya waye tayi wanka ta shiga makaranta in kuma tana gida mu shiga kitchen tare tana ganin girki Saboda bata iya Sosai ba Tunda bata zaman gidan.

Ita kanta sai da tayi mgana ganin Daga Shinkafa sai Taliya kawai muke da shi tace ban gayama Ya ishaq cefane ya kare ba ne. ?Sai nace ban fada masa ba ashe da ta koma gida Mama ta dawo sai ta fada mata shikenan Cibi ya zama kari wai ina yawo ina fadin Ishaq ya barni da yunwa Mama musamman tazo gidan Har Store ta shiga taga shinkafa ta fara Masifa tana zagina wai wannan abincin dake gidan gidan uban wa zan kai da zan ce ba kayan abinci..?

Har tana fadin nama samu ne mata dadama suna neman irin Damata basu samu ba,Har jamin kunnen tayi kan wai ina albuzuranci da kayan abinci,bai isa ace sun kare ba ko dai ina Saidawa ko kuma ina kyauta dashi Ina mata rantsuwa da abunda zai kasheni ban taba Saida abinci ko nayi kyauta da shi ba,Tace bata yarda dani ba ni bakar Munafukace ni.

Haka tatafi ta barni ina kuka kamar raina zai fita abun ya koma har da kazafin Satan abinci wlh ban taba ba,Ba Halina ba ne sai dai nasan ko zan shekara ina Rantsuwa Mama bazata yarda dani ba.

Sai nayi kuka na ni kad'ai na Share hawayena na riga na yardan ma kaina Allah kadai ke da mafita sannan garesa nake neman mafitana,Acikin wannan tsukin Bikin Diyar Hajiyar Dala ya taso har ga Allah ban sa araina zan je ba sai ga Mama ta aiko Badariya akan na shirya dani za'a tafi kano yara kuna gidan Anty Binta zasu zauna tare da Halisa suna Exams bazata samu zuwa ba.

Ashe ashe da walakin goro a miya,Hajiyar Dala tace azo dani Saboda aikin abinci Shiyasa Mama ta ce na shirya ana gobe biki muka tafi dani da Mama da Anty Binta da Badariya,Su Amir kuma na bar su wajen Halinsa.

Chan muka iske Goggo da Anty Nasara Da Hafsatu Yaya mariya sai adaran da muka isa ta iso,Yaya Asiya kuma ace ciki gareta har ya fito sai korafin na Rame na lalace suke yi  sannan na kara baki na zama kamar tsohuwa ni dai bana cewa komai Saboda bani da tacewa,Tunda muka isa Hajiyar Dala ta Turani Dakin girki,Da Goggo tayi mgana sai Mama tace Saboda na iya ne,kuma don na rika nuna ma ma'aikatan girkin yadda komai zai tafi ni ban damu ba Saboda ai wahala aikina ne.

Ranar Daurin aure da Safe Bak'in Abuja suka Diro Ishaq da Zainab da kanwarta Zuzu wacce bata jin Hausa,ire iren kawayen Suwaibar Hajiyar Dala Hafsah dai da Badariya suna tare,Bamu hadu ba Saboda ina kitchen muna ta aikan abincin yan Daurin aure da ma'ikata,sai Dare na samu kaina ina Dakin da muka sauka nayi wanka kenan,na tada Sallar mangariba su Ya mariya suna Dakin ita da Anty Mahma da ta iso da Safe sai Hafsah,Sai ga Ya Ishaq ya shigo Dauke da Ahmad inaga Hannun Badariya ya karbesa.

Fuskarsa a gintse ganin Ya mariya Ita bata ma san yanayi ba Anty Mahma ce ke mai mgana ya fita ganin ina Sallah ba jimawa ya sake dawowa lokacin na Idar ina zaune ina azkar Tun zuwan su bai neme ni ba sai yanzu na zata ma Ahmad ke rigima ashe wai Girki zan yi amaryansa tace Faten dankalina kadai zata iya ci.,batare da nuna Damuwa ba na amsa masa ya fice Ya mariya ta hade rai ganin ina Ninke Hijabin da nayi salla a harzuke tace"Au ke ce ma baiwar Amaryan tasa kenan..?

Nayi shuru na kasa mgana Anty Mahma tace"Tunda umarnin mijinta ne ki barta taje tayi..Tashi kije Fa'iza"

Da Sauri na kama Hanya zan fice sai Naji Hafsah na fadin"Tab to ai ko achan gidan in yazo da ita..Itace komai nasu abincin su har da gyaran makwancin su"

Ya mariya ta gwalalo ido ni kuma sai na kasa fita na juya ina Harran Hafsah Saboda na jita ina kusa da ita Sanda ta fadi mganar..Anty mahma tace"Kin so ne Fa'iza gaskiya wannan karon ban goyi bayan ki ba..Har da gyaran inda kishiya ta kwanta da Mijina kayyasa.."

Ko da yake naga bakaramin so Ishaq ke mata ba..Ciki gareta naji Anty Binta na fadin shike wahalar da ita mama ai naji da wannan jikan nata Tun kafin ya Fito duniya.."

Ciki..!na nanata acikin raina kafin na girgiza kaina kawai na Fice Daga Dakin ina ji Ya mariya ta fara bala"i ban tsaya jinta ba Domin bazasu taba Sauya ma Tuwo suna ba har Abada yana nan a tuwonsa..

Adaran nan na tike nayi Faten Dankalin Turawa da Hanta,na kuma kai mata da kaina har Bedroom din Hajiyar Dala da ire iren mu bamu da Ikon shigansa.

Ita da kanwarta ne Zuzu,Na ganta duk tayi wani irin fari kamar zabiya tana kwance,Na gaisheta ta amsa tana Dagamin hannu ina ji suna mgana da kanwarta da wani yare shi dai ba Turanci ba kila bayanina take mata naga ta juyo tana min wani kallo ni dai na Fice ban kara kallon inda suke ba.

To bikin ma bai musu dadi ba washegari ya kwasheta suka koma Mama ke yawon fadin Laulayi ne ya sakata gaba mai wahalarwa yace ma ta bar zuwa bikin tace sai tazo Hajiyar Dala kanta ya kara fashewa ballatana da ta kawo kudi masu nauyi ta bata gummuwar Bikin ni duk sai Daga baya nake jin ma sun tafi ban ci Daraja ko arzikin ko sallama ya yi dani ba.

yaya Asiya bata mgana,yaya mariya ne bata iya shuru,Goggo kuma ke Tausanta to ba'a ma yi rabuwar arziki da Goggo karofi da Hajiyar Dala ba Ranar Litini suka koma karofi rayuka ba Dadi,Ba'a san me yahad'asu ba sun dai yi Hayaniya,Mu kuma sai ranar Talata muka koma katsina tsinke na abun Biki ba wanda ya bani ni kuma ban saka rai ba ammh su Mama sun yi guzarin Kayan fulawa da kalanda da jakunkunan rabo kaya dai niki niko ni ko Cincin kad'ai Ya Asiya ta bani na Riko ma su Amir.'


*ASSALAMU ALAIKUM*

*KAYA SUN SAKE SAUKA*.

*INGANTATTUN SAIWOWI DA SASSAKE NE DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZA DA SU*.

*ABIN BIRGEWA BA SAU DAYA AKE AMFANI DA SHI BA*.

*KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR KO KUWA KE DA KANKI ZAKI YI GYARA?*

*INA SAKE YIN ALBISHIR DIN GARIN DAKA MAI KYAU DAN CHADI, SHA DA MADARA KO NONO DA KUMA TSUMIN GAMGAM*.

*GADALIN MATA AKWAI*.

*INA DA TABBACIN INGANCINSU*.

*SANNAN WACCE TAKE SON A DAFA MATA KAZAR, ZA'A DAFA*.

*TUARAREN WUTA NA ASALIN CHADI AKWIA SU AVAILABLE, SAI KIN GWADA ZAKI BADA LABARINSU*

*TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU DOMIN KARIN BAYANI*

*08032773332*.

*NATION WIDE DELIVERY*.

*SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*

🙏.



*Janafty**KANA NAKA..!*


*Wattpad:JamilaUmar315*

*Mallakar:Janafty*

*Arewabook:Jamilaumarjanafty*


MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT 08066726866


Ni MMN MUJAHID Ina da kayn gyara kala kala na kasa da sama Ina Saida supplement da kayan mata kala kala cikin sauki Mai kama da kyauta


Hjy ta ki ajiye kunya kifitu kiyi bayani matsala ki abaki ABINDA yaddace Dake


Ina matan da ke FAMA da bushewa gaba


Ina maccen da take a bushe kamas ba niima miji sai yasa yawun sa ku BASILIN 😳


Ina matar da kishiya ta tayi mata zarra ga miji ke rasa Ina matsala take


Ina wadda mijinta kamar kurma baya nuna ya gamsu Dake Dan ku ayi ku abari duk dai suke dashi


Shin ke ku y'ar kuwa ga mijin ki baya Yi da sanbatu in kinji ana Fadi sai kece karya ce 


Nazo muku da hadin Zuma wadda duk zata magance way'anga matsalolin cikin ikon Allah wanna Zuma ta samu yabo ga duban mutane Sha yanzu magani yanzu ce Banda haufi akanta wanna Zuma tana ta yadda sha'awa Kai tsaye ruba babba 2500 karama 700👌👌 


MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT MUNA SAKWATO DA KEBBI INA AIKAWA KU INA 08066726866


IN BAKI SHIRYA BA KIBARI HAR KI TASHI SAYE 😀

  

       *🅿️11*


Ta gidan Anty Binta batagwarawa muka fara sauka saboda yara nan muka yi sallar mangariba da isha'i sannan nayi shirin tafiya ganin Mama bata da niyyar tafiya, ni kuma Saboda Dare sannan ga yara,Ganina cikin shirin tafiyasa yasa Mama tace na tsaya su Amir su ci abinci,kamar abun arziki na zauna suka ci abinci nima Halisa ta zubomin naci kad'an na kora da ruwa shuru shuru Mama taga na zauna ban tafi ba tagaji dai tamin mgana sai na fad'amata bani da kudi a hannuna ballatana mu yi na adaidaita zuwa gida.

Shikenan Mama ta fara fad'a ta inda take shiga bata nan take fita ba, ta kalleni tana fad'in"Ke kan Fa'iza ban ga amfanin ki ba..Tun da Ishaq ya aure ki bai Huta da wahalhalun ki ba..da an tabaki sai kice baki da ko asi ke ko irin Dubaran matan wannan zamanin baki iya ba? sai dai komai ki kwanta miji yayi miki tunda ya zama bawan ki"

Anty Binta na gefe ta karb'e da Fadi'n"Kuma Mama komai ne sai ka zauna miji ya baka..?,tsakani ga Allah yana ma kokari wlh,ammh duk da haka ba'a gani barin ma Yan'uwanta da Goggon Karofi,su yi ta korafi kuma in za'a duba tafi duka yan'uwanta jin Dadi ita Asiya ai malamin makaranta take aure ga abokiyar zama ita kuma Mariya d'an kasuwa ne mai karamin karfi ba wacce takai jin dad'in da Fa'iza take yi acikin su ammh kullum gani suke tana cikin Wahala'"

Mama ta ja tsaki kafin tace"To ai duk laifinta ne ita ke fad'a musu haka..Shiyasa nace miki Har ga Allah ban so hada zuru'a da Dangin Asiya da Sidi ba, domin nasan ba Dangin Alheri ba ne na tsiya ne kawai"

Ni dai ina zaune kaina a kasa na kanzil ban ce ba sai da suka gama cin zarafina sannan Mama ta zage jaka ta Dauko Dari biyar ta wurgomin tace sai na tashi na bar gabanta bata son ta kara ganina.

Jiki ba Karfi na mike nayi musu sallama yaran suna D'akin Halisa na Bisu na taho da su ko Tausayi na Mama bata ji ba ga goyon Ahmad ga Amir ga Anum ga Musty kuma na Tabbata Direban gidan zai kai Mama gida ni kuma Saboda k'iyayya bazata iya had'a Hanya dani ba.

Haka na fita ina Tare tare da su Allah ya taimake mu kafin mu isa Titi muka samu abun hawa zuwa gida.

Tunda daman dukkan mu a koshe muke sai shirin kwanciya kawai nayi musu,Tundaga Lokacin kuma Rayuwar mu ta cigaba da gudana yadda take tun farko ba chanji.

Ya Ishaq ko Labarin sa bana ji Wayar ma tawa ta Lalace inaga yara ne suka Y'ar  min ita a kasa ta bare biyu da na Had'a kuma nayi nayi ta kawo bata kawo ba sai na Hakura na tattara ta na ijiye ba mai nema na ni kuma ina gida Dagani sai ya'yana tun had'uwar mu da shi a kano sai da ya shafe wata biyu sannan yazo ya ganmu shima kwana d'aya yayi ya koma ko da daman ya Dawo komai na Cefanan mu ya kare daran ranar ma da yunwa yaran suka kwanta da Rana na samu nayi musu danwake da sauran garin Danwaken daya rage Shima jikinsa yayi sanyi daya ga ko kwaran abinci bamu dashi ya kira Mama yana mata mgana ga dukkan alamu komai na mu yanzu ya koma wuyar Mama ne.

Ya bani dubu biyar a hannu sannan ya Biya Haruna kudin watansa biyu ya tafi bayan ya fad'amin zai Dad'e bai zo ba zainab bata da lafiya Laulayi na Matsa mata shi ne ke kula da ita ban damu ba nayi mata fatan Allah yasa a rabu lafiya domin ni yanzu duniya baya gabana ballatana na Damu da abunda ke faruwa acikinsa ni dai kawai ya'yana sune nake ji sannan kuma zaman su nake yi,kuma Allah ne gata na garesa nake kai duka kukanaa..

Tun bayan da ya tafi ko gidan Mama da nake zuwa na Dauke kafata saboda sai in ina da kud'in zan je,kuma koma naje ba tarban arziki nake samu ba Shiyasa na kame kaina agefe Badariya ne ke d'an lekomu Lokaci bayan Lokaci sai Jamal in yazo gida Huta yakan zo Tunda suna yawan zuwa anguwan mu buga Kwallo.

Mama da Anty Binta kuwa Daman indai ka gansu to tabbas ba alheri ba ne ya kawo su.

Bangaran Karofi ma shuru ba wani Labari Hafsatun ma da kan lekoni kwana biyu ban jita ba tun rabuwar mu da ita a kano bana jin kowa nima bamai jina,Dani da yarana muka kulla kawance da juna in sun Dawo makaranta suna tare dani sai in barci yazo sun ma daina Damuwa da Zencem Daada Anum ce daman mai Rigima sai Mutsy to yanzu sun gaji sun Daina yawan damuna da Tambayansa sai nima hakan ya fiyemin saboda wani lokacin na kan rasa amsar da zan basu.

Ahmad na da shekara Biyu,na fara Tunanin ciresa a nono na yayesa ammh bani da komai da zan rika basa Tuni daman acikin Cefanan mu aka daina kawo mana kayan Tea,kuma ba ni da wani garin kuni ballatana na rika Damawa sai na kasa ciresa a nono Saboda kada ya wahala ni kaina bani da Lafiya duk na kara ramewa sannan ina Faman da yawan ciwon kai da jiri tsaye kawai nake ina tafe da Lalura ban sani ba.

Satin da muka shiga a Daddafe nayi sa saboda ciwon kan ya matsa min ga jiri  da zazzabi,sai dai ban kwanta ba Saboda yara,in suka fita makaranta sai na Dad'e ina kwance ina fama da kaina tun ina Daurewa har sai da ciwon ya kwantar dani Daran jumma'a,Cikin Dare na tashi na shiga Bayi na Dauro alwala kawai jiri ya kwasheni na koma na kwanta Tun daga Lokacin jikina ya rikice,sama sama nake jin komai kaina kamar zai Tsage gida biyu ga zazzabi na jin jikina,ina so na tashi ammh na kasa tashi ina jin su Amir suka shigo suna kirana "Umma.."Umma.."

Ammh na kasa amsawa Ahmad ma ya gama Budurina ajikina yana ta Dukana yana kiran sunana da gwarancinsa ammh na kasa tashi,ganin Halin da nake ciki yaran suna Tare dani barin ma Amir dake da wayau ya fahimci bani da lafiya su Anum nata damuna da surutu yace su daina Umma bata da lafiya Anum yar rigima sai ta saka kuka ganin haka Musty ya kama Amir ya Lallashe su.

Ina jin Amir na taba kafata yana fadin"Umma..Umma ana buga get"

Dakyar na iya bude baki nace"je ka bu d'e Amirr.."

Tare suka fita da Anum da Musty yana kai wa daman wajen sakatar tsakiya ne ya bud'e ashe Haruna ne yana ganin su basu shirya ba yace"Au yau ba zuwa makaranta ne Kabiru..?

Amir ya karkace kai kafin ma ya samu mgana da Sauri Anum tace"To ba Umman mu bata da lafiya ba ne"

Haruna yace"Subhanallah..Allah ya bata lafiya"

Aransa daman yayi tunanin haka Tunda bakwai da rabi bai taba fashi basu shirya ba,har zai wuce Anum ta saka kuka tana kiran Umman su,Haruna ya kalli Amir yana fadin"Jikin nata yayi zafi ne..?

Amir ya gyada mai kai yana fadin"eh bata iya tashi ma"

Cikin alhini yace"Bari nayi ma mai dak'i na mgana sai ta shigo ta duba ta..Allah ya bata lafiya"

Cikin Hanzari ko ya shiga gidansa ya samu matarsa Sa'adatu na sharan Tsakar gida tana ganin mijinta cikin mamaki tace"Ah baka tafi ba ne Megida..?

Cikin wani yanayi yace"Wlh ke dai bari naji shuru ne yaran basu fito ba na buga gidan sai ga su sun bude gwanin ban tausayi suna ta kukan wai Umman su ba lafiya"

Sa'adatu tayi salati kafin tace"Wayyo..Allah ya bata lafiya"

Ya amsa da Ameen kafin yace"Sako mayafin ki ki shiga gidan ki ga Halin data ke ciki"

Bata yi musu ba ta ijiye tsintsiyan Hannunta ta shiga D'aki ta sako Hijabi tace bari taje ta gani,a kofar gidan ma taga su Amir taja su zuwa cikin gidan Halin data ganni a ciki yasa Hankalinta ya tashi da Sauri ta fita ta koma gida ta fadama mijinta ga Halin da ake ciki.

Cikin wani yanayi yace"Jikin nata yayi zafi kenan..?.

Sa'adatu tace"Gaskiya ya kamata a tafi asibiti"

Ya jinjina kai yana fadin yana da lambar Ishaq bari ya kirasa sai dai yayi ta kira har sau uku bai daga ba sai kawai yace Sa'adatu ta shiga makotansu gidan wata Habiba ta mata mgana sai a kai yaran gidanta su kuma su tafi dani asibiti tunda ba'a samu Ishaq a waya ba.

Haka ko akayi ta shiga tayi mata mgana Habiba duk da bana Huld'a da ita bata ki ba tace zasu zauna a wajenta har mu dawo tare da Fatan sauki a gareni.

Sa'adatu ta sakamin Hijabi dakyar ta iya fito dani na shiga adaidaita sai general Hospital muna zuwa ganin Halin da nake ciki yasa suka karb'eni suka shiga dani bayan Dube Dube da gwaje gwaje suka bani gado bayan sun Dauramin Drip ana bukatar kudi mganguna,sannan Likitan ya fad'ama wad'anda suka kawo jini na ne ya yi sama sannan ga Zazzabi a jikina sosai.

Na galabaita da sai sun rikeni anan na kwana Biyu,Allah sarki ni ban san inda kaina yake ba ammh ina kwance ne Hankalina na wajen ya'yana sai da yammah na farka da su na Bude bakina Sa'adatu ce a wajena tun Safe girki kawai ta koma gida tayi,ita ke fadamin su Amir na gidan makociyarta Habiba cikin koshin Lafiya ta tambayeni ko ina da Lambar wanda za'a kira a sanar da su nace babu Saboda Lambar goggo kad'ai na Haddace kuma bana so a kirata a tada mata hankali.

Sai Dare Haruna ya biyo bayan ya Taso daga aikinsa ya Dubani ina ta musu godiya,ya kalleni kafin yace"Na yi ta kiran megidan ki bai Daga ba..Ko kina da lambar yan"uwan ki na nan sai ki bada na kira su na shaida musu"?

Kafin ma nayi mgana Sa'adatu ta bashi da amsa da nace babu.

Sai ya kara fadin"To ko gidan kakanin yaran nan zan je na shaida musu..?.

Sai na kasaa mai gaddama na D'aga mai kai kawai nan na kwana Sa'adatu ta kwana dani nayi nayi ta tafi gida tace bakomai su Amir kuma ta kira Habiban ta mata bayani tace bakomai zasu kwana a wajenta.

Washegari da Safe ta koma gida ta yi wanka ta yi abinci da Haruna yazo da Safe yace daganan gidan Mama zai je ya fadamata saboda yasan gida yana kai su Amir watarana in ya Dauko su daga makaranta.

Abun mamaki har Dare ba wanda yazo kuma daya dawo yace yaje ya sanu Maman da kanta ya fadamata,ammh kuma ba wanda ya lekoni sai Habibar ne tazo da yammah ita da su Amir suna ganina suka Nufeni suna kiran sunana na Rumgumesu ina jin Tausayin kaina,basu jima ba ta tafi da su ina ta mata godiya ganin su Amir sun yi tsaf dasu,tace bakomai ai d'a na kowa ne sai Dare sa'adatu ta dawo min da abinci da kayan da zan sauya na rasa da kalmar da zan gode musu su yi min gatan da su mama suka kasa yimin.

Sai da na kwana uku a asibiti sannan Sai ga Mama da anty binta sunzo dubani Lokacin ma naji sauki sosai basu iske sa'adatu ba ta koma gida ina gadon asibiti ma ban tsira wajen Mama ba, sai fad'a take min wai da gangan na kirkiri ciwo saboda ishaq ya dawo gabana ya Lalace to ban isa ba kaina na kasa ina kokarin maida hawayen dake cikin idona Anty Binta ne ta kalleni tana fadin"To meke damun ki..?

Wata mata dake jinyar na kusa da gadona Saboda general ward ne na mata tace"Haba baiwar Allah kya yi mata hankali baki ga bata da lafiya ba ne..?kun sameta ma yau da Sauki Sauki da kun ganta sanda aka kawota sai kun Tausaya mata Hawan jini yanzu ya zama ruwan Dare baga yara ba, ba ga manya ba"

Anty Binta da Mama suka kalli juna kafin Mama tace"Hawan jini..?

Anty Binta tace"Ba dole ta samu hawan jini ba ta sakama ranta bala'i ..Ishaq dai kike ma wannan kwanciyar shima mara lafiyan garesa achan tunda muna nan basai yazo ba"

Mama ta karb'e da cewa"Ai na gayamasa yayi zamansa kawai ya kula da Zainab"

Ina jinsu kaina na kasa ban ce musu komai ba suka gama cimin mutumci suka tafi ko tsinke basu zo min dashi ba,ba tambaya waya kawoni asibiti ina yarana..?ba abunda ya Dame su bayan tafiyar su haka na koma na kwanta ina ta kuka Matar dake kusa tace"Ki daina kuka kada ki kara ma kanki Lalura..Wad'anan dai ko suwaye basu da kirki kina gadon asibitin ma baki tsira ba..?

Ni dai na kasa mgana Likita yazo yayi zagaye da yazo wajena na tashi zaune idanuwana sun kumbura ya duba Fayel d'ina yana kallona kafin yace"Fa'iza Ishaq kin san abunda ke Damun ki..?

Na girgiza kai na alamun a'a cikin Sanin aikinsa yaja farar kujeran dake gefen gadon da nike kwance ya zauna yana fadin"Hawan jini..Jinin ki ne ya d'aga Sosai sannan kina da maleria"

Na dago ina kallonsa duk da naJi matar d'azu ta fad'a sai da nayi mamaki cikin yanayina nace"Hawan jini Likita..?

Sai ya d'agamin kai ya cigaba da fadin"Ki daina yawan Tunani in kina so ki Tsira da lafiyarki..Damuwa ita ta Haifar miki da matsalan da kike ciki..Sannan daga yau ki rika kwana cikin gidan Sauro saboda rigakafin Cizon Sauri Maleria na tada Hawan jini..Shima Hawan jinin yana Tada maleria in suka Had'e ma Mutun kuma bama son haka kiyi kokarin cin abinci sosai ki kuma kiyaye dokokin mu"

Na jinjina kaina kafin nace"Nagode likita..ina so ka sallame ni na koma gida"

Ya kalleni kai Tsaye kafin yace"Mijin ki ne zai dawo..?Domin wanda ya kawoki ya ce shi makocin ku ne mijinki kuma yana wajen aikinsa"

Cikin yanayin mganata nace"Ya'ya na..Likita na bar yarana ba su da kowa sai ni don Allah ka Sallameni"

Mirmishi yayi kafin ya mike yana Fadin"kada ki damu zuwa gobe da Safe zaki koma gida"

Na gyada mai kai daga haka ya wuce gado na gaba ni kuma na koma na kwanta ina Tunanin yadda rayuwata ta kare ace ina kwance bani da lafiya ammh ba wanda ya damu dani nasan da Goggo taji bazata zauna ba ni kuma bana son Damuwarta,Yau in da ace mutuwa nayi babu wanda zai san na mutu shi kawai ke sakani kuka.

Da yammah Sa'adatu tazo na tambayeta su Amir tace yau sun je makaranta,har acikin raina naji Dadi idona ya cika da Hawaye na kalleta ina Fadin"Nagode sosai..Allah ya saka da Alheri"

Ta amsa min da Amin a raina na Guduri niyyar in naji sauki na koma gida zan gyara mu'amalata da duka mokota na Domin na Lura sune Dangina dake kusa dani,Washegari da Safe aka bani sallama sai dai bamu tafi ba ba'a biya kudin gado da Sauran kashe kashe ba,Sai da Haruna ya koma gidan Mama ya fad'amata tace zata zo sai da muka kusa yini a asibiti sannan Anty Binta tazo tana ta wani yamutsan fuska ita ta biya duka kud'in da ake bukata sannan ta siya mgangunar da aka rubuta bata tsaya ba ta kara gaba Sa'adatu ta kamani ta Daukan mana Sauran kaya  muka yi sallama da yan daki muka fice.

Har cikin Dakina Sa'adatu ta kaini ta zaunar dani ina ta mata godiya matar nan bata tafi ba,Sai da ta share Dakunan ta gyara ta Dora girki Saboda yara ita ta Dinga fad'ama makotanmu bani da Lafiya duk da bana shiga ammh suna ta Shigowa Dubani har da Habiba ina ta mata godiya tace bakomai wlh..

Har yammah tana tare dani sai da su Amir suka dawo makaranta sannan ta koma gida bayan har wanka sai da ta tsaya nayi na sauya kaya naci abinci dakyar na sakata ta D'iba abincin da ta Dafa tatafi da shi su Amir sun yi murna da ganina motsi kad'an sai Amir yace"Sannu Umma Allah ya baki lafiya'

Sai na amsa mai da Ameen Amir su Anum kuma ba wayau suna ta wasan su sai dai sun yi murnan ganina Ahmad kuma saboda kwana Biyu bai sha Nono ba,sai ya manta da shi,Sai dai Habiba tace ya sha Rigima kunu take Damawa tana bashi,ya lafe a jikina yayi shuru Tausayin sa ya kamani na Rumgumesa ina jin kamar na fashe da kuka kwana biyu ne bana nan ammh ya'yana ma sai makota ne suka kula da su inaga in ba na tare da su gabad'aya Allah kad'ai yasan wani Hali zasu shiga shiyasa zan Daure zan kuma Jajirce saboda goben su

Washegari da muka Dawo gida ma Tun Safe sa'adatu ta shigo ita ta shirya yaran tayi musu kari dayake ita bata taba Haihuwa ba,bayan sun tafi makaranta tazo ta gyaran gidan,ta koma gida chan anjuma kuma tadawo tayi ma yara girki nasan ko bata fada ba aranta tana so ta tambayeni bani da Dangi ne..?

Ai rashin gatan yayi yawa sai dai bata ce min ba nima ban ce mata ba.

Kwana na Hudu da dawowa asibiti na ji sauki Nace sa'adatu ta daina zuwa tana min wahala na samu lafiya,Ranar har gidan Habiba sai da na shiga na kara yimata godiya sai dai duk wanda yaganni yasan na rame duk na kara Lalacewa.

Sati daya da faruwar abun Badariya tazo Dubani tana bani Hakurin bata sani ba sai abakin Halisa taji har asibiti na kwanta,ta yinin mu sai yammah da Halisa tazo dubani suka tafi tare,Ita ce ma suna mgana da Hafsah ta wayar Goggo ta fad'amata nayi ciwo har asibiti na kwanta ashe su Hafsah suna kano Yaya Asiya ce ta Haihu,suna kano shekaranjiya akayi suna Hafsa ke fad'ama Goggo tana ta Fadan ba wanda ya fadamata ballatana sauran yan'uwana kuma suna ta kiran wayata a kashe basu san ta Lalace ba..

Ranar laraba da Safe sai ga su A gidana Daga kanon suke Yaya Isan goggo yaje ya Dauko su a motarsa,Goggo ce sai Anty Nasara da Yaya mariya sai Hafsatu sai matar Isa Amina,sun zo sun ganni suna ta tafad'a gani na duk na fad'a na rame Goggo ta kalleni tana fadin"In wayarki ta lalace baki aron wata wayar makota ki kiramu Fa'iza"?

Kaina na kasa nace"Goggo ban da lambar kowa a kaina kuma layin yana gida"

Anty Nasara tace"to wa ya zauna dake..?

Kaina na kasa tace"Matar makocin mu haruna mai kai su Amir makaranta"

Su Goggo suka saka salati suka Dire,Yaya mariya tace"Daman wa kuke tunanin zai zauna da ita..?

Mama ko Binta..?azzalumai bakomai a zuciyar su sai mugunta ayi dai mu gani"

Goggo ta juya tana kallonta Lokaci daya tana fadin"Mariya..mariya ana rabaki da kiwon awaki kina fadin kyalla ta Haihu daga Saudatun har Binta ai ba sa'anki ko.?

Yaya mariya ta tura baki kafin tace"Ai gaskiya na fada goggo wlh wani Hisabin sai a lahira kalli yadda Fa"iza ta koma kamar wata yar aiki kalli gidanta kalli kujerun ta duk sun Fita Hayyacin su kuma wai wannan mai kudi take aure Allah dai ya waddan kudin miji in dai na irin mijin Fa'iza ne bashi da amfani ko ni da mijina karamin ma'aikaci ne wlh d'akina yafi na Fa'iza kyau sau dubu Saba'in wlh"

Anty Nasara na gefe ta kad'a baki tace"Ai ba gidan ne ya fita Hayyacinsa ba..ita kanta Fa'izan ku dubeta ku gani yadda duk ta fita kammaninta"

Fadin haka yasa duk suka sakamin ido suna karemin kallo Goggo tace"Duk kubar mganar nan mganar kayan daki zamu sauya mata in sha Allahu ai mune yan'uwanta Dolenta na kanmu Ishaq ba wajibinsa ba ne yayi ma Fa'iza komai ba"

Yaya mariya ta kad'a baki tace"ammh ai yana da shi..kuma bai gagaresa ba in da mutumci a wahalan da Fa"iza tayi da shi da danginsa ta chanchanci komai a wajensa"

Goggo tayi saurin tare mganar da kallona tana fadin"Fa'iza wannan ramar tayi yawa me ke damun ki ne..?

Sai nayi shuru na kasa mgana nasan in nace Hawan jini gareni na bude Sabon Shafi sai nayi kamar ban ji ba Sai da goggo ta kara mgana Sannan na ce mata Zazzabin cizon Sauro ne.

Goggo nata fad'an ko bana kunna mganin Sauro ne ni dai nayi shuru ban ce komai ba.

Hafsatu tayi girki Yaya mariya kuma ta ragemin wankin su Amir,daman sun taru Aminan isa kuma ta gyara Falon da Dakunan.

Bayan sun ci abinci sun yi sallar azahar na saka Hafsatu ta shiga da su gidan Sa'adatu suka yi mata godiya daganan nace suce ta kai su gidan Habiba itama suka mata godiya sukace bakomai ai yiwa kai ne.

Muna tare da su har La'asar akace Dan'uwa mai dadi naji Dadi sosai Yaya mariya ta nuna min Yaya asiya da D'anta a waya hoton da suka Dauka Ranar suna tasha kyau abunta sunan yaron Muhammad Auwal.

Sai bayan La'asar suka yi shirin Tafiya,Yaya Isa daman ya shiga cikin gari ne sai ga shi ya Dawo Hafsatu ta sakamai abinci da yake tana fashin Sallah tana falo Aminan Isa da Anty Nasara na Dakina suna sallah ni kuma ina Dakin su Amir ina sallah da ni da Yaya mariya Ahmad na goye a bayan Goggo Tun da ya fara rigima ta karbesa ta goyasa.

Ni dai na idar da sallah ina zaune ina azkar Sai naji mgana sama sama afalo Yaya mariya ta tashi ta fita,ba jimawa sai ga Hafsatu ta leko tace Goggo na kira na,Ina fitowa nagan su Tsaye sun yi cirko cirko gabana ya fad'i na zata ma wani abu ne,Goggo ta kalleni da Kwalin mganina a hannunta kafin tace"Ashe Fa'iza hawan jini gareki kikace mana wai zazzabin cizon sauro ne..?

Sai na kasa mgana na Dukar da kaina Yaya mariya ta yi kyafci kafin tace"ai bazata fad'a miki ba Goggo..Na rasa me Ishaq ya bama Fa'iza ya shanyeta bata kaunar Laifinsa daga shi har Danginsa"

Goggo ta kalleni ta kara kallo na kafin ta saka salati tana fadin"Na shige su ni Indo..Yanzu da ba domin Nasara taga mganin nan kuma tasan ko na menene ba da haka zata bar mu a matsayin Maleria ke damunta haba wannan ramar na Fa'iza ya yi wa ashe ashe Hawan jini gareta da kananun shekarunta"

Yaya Isa na gefe yayi karamin Tsaki kafin yace"Ba Dole ta kamu da Hawan jini ba Goggo..An aura mata wanda baisan Darajanta ba..Ina jin Labarin zaman Hakurin da yarinyar nan ke yi ku kuma su goggo kun kasa D'aukan mataki akan haka ai aure ba Bauta ba ne ibadan ubangiji ne ba na abokin Hallita ba..Ya maida matarsa kamar wata yar aiki ko baiwa yana chan Abuja ya tare sai yaga Dama yake zuwa Fisabillahi wannan adalci ne..?

Goggo tayi saurin tare shi da Fadin"Mijinta ne ya fi mu iko da ita..Sannan zaman aure ai zaman hakuri ne,Kuma ibada take yi Isa kada kace bamu Dauki mataki ba in ba so kake mu kashe mata aure ba"

Yaya mariya tayi karaf tace"Wlh Goggo da auran Fa'iza dai gwara zawarci"

Goggo ta aika mata da Dakuwa tana Fadin"Ya'yan nata fa ke zaki rike mata su in ta fice ta barsu da kananun shekaru..?

Yaya mariya ta tura baki kafin tace"Su zauna gidan Uban su mana Goggo"

Goggo tayi dariyan takaici kafin tace"Kayya mariya ai rikon ya'yan wani ba kowa zai iya ba sai wanda Allah ya bama wannan..Sannan kuma ya'ya sai uwar su mariya..Yanzu dai Allah ya kyauta..Tunda abun ya zama haka Mariya in ba Damuwa ki kara kwana ko zuwa gobe jibi in megidan naki zai bari lokacin ta kara watsakewa kinga Hafsatu suna da makaranta"

Yaya mariya tace"Bakomai da na kirasa bazai ce komai ba su Abba kuma suna gidan kakkaninsu daman."

Goggo ta kalleni tana fadin"Ga mariya nan zata zauna ta kara taimaka miki zuwa jibi ni kuma zan tafi da Ahmad tunda kin yayesa in kika ji Sauki kika warke sai na Dawo miki dashi"

Ban iya ma Goggo musu ba na tafi na Had'o kayan Ahmad na bata,Nasan tayi hakane saboda ta ragemin wahala sannan duk da ina jin Tsoron me zai biyo baya,ammh bazan iya ce ma Goggo A'a ba saboda ita kamar makwafin Tamadina ne a wajena duk da tana raye.

Ya Isa nata fad'a Goggo bata Biye masa ba Ta lallasheni tare da kara Jadaddamin nayi hakuri watarana sai Labari Goggo ta bani dubi biyar Ya Isa dubu uku kafin su tafi,Suka barni da Yaya mariya ta tasani tana ta min Fad'a wai na zauna na zama sakarya miji da Danginsa suna yadda suka ga Dama dani ni dai ban ce mata komai ba sanin Halinta.

Da yammah ko da su Amir suka Dawo basu ga Ahmad ba,na fad'a musu Goggo tazo ta tafi da shi suka fara Tsallen suma Yaya mariya ta tafi da su ta kyabe baki kafin tace"Wannan uban naku mai bakin hali ai bazai bari ku rabemu ba duk dai abun su bai isa ya sauya ma Tuwo suna ba"

Ban tab'a kawo ma raina Ya ishaq zai iya Dawowa ba sai ga shi washegari da yammah ya Diro dirowan bazata yayi mana Muna falo ni da yaya mariya,ita wayarta take latswa ni kuma ina kwance kan kujera mai zaman mutun uku duk da naji Sauki ammh jikina ba karfi su Amir na makaranta basu dawo ba.

Ko sallama ma bai yi ba sai da ya shigo Falon kuma da Yaya mariya ya fara cin karo suka yi ma juna kallo daya suka Dauke kai ni kuma jikina na rawa na tashi zaune ina gyara Wuyan rigana cikin rawan jiki da na zuciya nace"San..nnu..da zuwa.."

Wani irin kallon da ya bini da shi yasa Hantar Cikina ta kad'a na fara maimaita innalillahi acikin raina ko amsani bai yi ba kamar Hadari haka ya shige shashensa ya Banko kofa.

Na dago na kalli Yaya mariya sai tayi kamar bata ganni ba ta mike ta shige Dakina tayi kamar tana waya ni kuma jikina na rawa na shiga Kitchen bamu da ruwan gora na Daukomai purewater na saka a Filet da kofi gabana na fadi na nufi bangaransa Gabadaya ilahirin jikina ba inda baya raawa ina fatan kada Abunda nake tsoron Faruwarsa ya faru da na shiga Uku.


*ASSALAMU ALAIKUM*

*KAYA SUN SAKE SAUKA*.

*INGANTATTUN SAIWOWI DA SASSAKE NE DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZA DA SU*.

*ABIN BIRGEWA BA SAU DAYA AKE AMFANI DA SHI BA*.

*KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR KO KUWA KE DA KANKI ZAKI YI GYARA?*

*INA SAKE YIN ALBISHIR DIN GARIN DAKA MAI KYAU DAN CHADI, SHA DA MADARA KO NONO DA KUMA TSUMIN GAMGAM*.

*GADALIN MATA AKWAI*.

*INA DA TABBACIN INGANCINSU*.

*SANNAN WACCE TAKE SON A DAFA MATA KAZAR, ZA'A DAFA*.

*TUARAREN WUTA NA ASALIN CHADI AKWIA SU AVAILABLE, SAI KIN GWADA ZAKI BADA LABARINSU*

*TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU DOMIN KARIN BAYANI*

*08032773332*.

*NATION WIDE DELIVERY*.

*SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*

🙏.



*Janafty**KANA NAKA..!*


*Wattpad:JamilaUmar315*

*Mallakar:Janafty*

*Arewabook:Jamilaumarjanafty*


MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT 08066726866


Ni MMN MUJAHID Ina da kayn gyara kala kala na kasa da sama Ina Saida supplement da kayan mata kala kala cikin sauki Mai kama da kyauta


Hjy ta ki ajiye kunya kifitu kiyi bayani matsala ki abaki ABINDA yaddace Dake


Ina matan da ke FAMA da bushewa gaba


Ina maccen da take a bushe kamas ba niima miji sai yasa yawun sa ku BASILIN 😳


Ina matar da kishiya ta tayi mata zarra ga miji ke rasa Ina matsala take


Ina wadda mijinta kamar kurma baya nuna ya gamsu Dake Dan ku ayi ku abari duk dai suke dashi


Shin ke ku y'ar kuwa ga mijin ki baya Yi da sanbatu in kinji ana Fadi sai kece karya ce 


Nazo muku da hadin Zuma wadda duk zata magance way'anga matsalolin cikin ikon Allah wanna Zuma ta samu yabo ga duban mutane Sha yanzu magani yanzu ce Banda haufi akanta wanna Zuma tana ta yadda sha'awa Kai tsaye ruba babba 2500 karama 700👌👌 


MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT MUNA SAKWATO DA KEBBI INA AIKAWA KU INA 08066726866


IN BAKI SHIRYA BA KIBARI HAR KI TASHI SAYE 😀


      *🅿️12*


Ina shiga Bangaransa na iske sa tsaye a tsakiyar falon yana ta safa da marwa saboda bala'i hatta jakar da ya dawo da ita bai iya sauketa ba kamar yana jira na ina shigowa da sallamata yayi saurin zaburowa Sauran, sallaman tawa ma iya makoshina ta makale jikina ya Dauki karkarwa kamar wacce taga mutuwarta.

Hannunsa manuniya yasa ya na nuna ni cikin Matukar fushi yace"Me na gaya miki..?

Nace me na gaya miki Fa'iza akan wannan mara mutumcin yayar nan taki..?

Yafad'a Lokaci d'aya yana dagamin murya sai na tsaya na kasa gaba ballatana baya jikina na wani gif gif kamar wacce wani abu ke ja kafafuwana suka fara barazanar kayar dani sai nabi Raunin su suka rinjaye ni na koma na Durkushe saman kafafuwa na lokaci daya ina sauke sauke farantin Hannuna ina so nayi mgana na kasa tsoro nake ji kada Yaya mariya ta jimu tunda Jikin Shashen sa na jikin Dakina ne bazan so a ce yau mijina ya Tozartamin yar'uwa ba.

Ina wannan tunanin sai ji nayi ya sakar min gigitaciyar Tsawa Lokaci d'aya yana kara fadin"Nace me na fada miki Fa'iza..?

Hawaye suka gocemin na Tsoron abunda zai biyo baya,na yi baya da jikina ina karkarwa na had'a Hannayena cikin yanayin mgana ta da rawan baki nace"Don..Allah..Kayi hakuri ka yi shuru..Na kasa fad'a mata ne bazan iya ba..wlh bazan iya ba.."

Sai hawaye sharr suka gocemin wasu na korar wasu,Tsayawa ya yi yana min wani irin kallo na raini da kaskanci kafin yace"Au bazaki iya fada mata ba ko..?To ni bari naje na fada mata tunda gida na ne ba gidan wani ba"

Ya karishe fada a fusace yana sauke jakar da ya shigo da ita nan tsakar Dakin nasan zai aikata tunda ya furta Da sauri na mike na isa garesa na Durkusa ina kuka ina fadin"Don Allah..don Allah..!

Mgana ta ta kasa fitowa saboda kukan da yaci karfina Ganin yayi banza dani ya nufi hanyar ficewa yasa na kwashi gudu na isa ga kafarsa na kama na rike gam ina kuka kamar raina zai fita ina fadin"Kada ka tozartamin yar'uwa..Ka bari zata tafi..Zata tafi.."

Sai ya tsaya yana kallona kafin yace"Yaushe zata tafin..?

Cikin kuka nace"Gobe..Gobe zata tafi na rantse da Allah.."

Ko sake kallo na bai yi ba ya Fizge kafarsa sai da nayi baya na fad'i ya Fice da Sauri,ina ganin haka na mike sai da kaina ya sara jiri ya kwasheni ammh ban damu ba na marasa baya ba inda jikina baya rawa har da zuciyata ma gudu take yi da sauri a lokacin.

Sai dai me zuciyata ta tsaya waje d'aya lokacin da na fito na iske Yaya mariya Tsaye a tsakiyar falon daga dukkan alamu ta gama jin duka mganganun mu Saboda Ya Ishaq da karfi ya Dinga Tijaransa,Kasa karisawa nayi kawai sai na Tsaya ina raba ido jikina da zuciyata gabadaya yayi wani Dum kamar ya daina aiki na wani Lokaci.

Ya ishaq kuma yana ganin Yaya mariya bai yi wata wata ba ya gyara Tsayuwa yana fadin"Nasan yar'uwan ki bata gaya miki sako na ba ko..?

Yaya mariya ta kallesa cikin idon da bacin rai yasa s Launin su ya sauya kafin tace"Bata gayamin ba..Ammh Tunda kaga ai waka a bakin mai ita tafi dad'i"

Tafad'a Tana kokarin yaki da zafin zuciyar dake taso mata,Taji duka mganganun Ishaq ta dade tana jin Labarin Rashin mutumcinsa, bata taba katari da shi ba sai yau lalle ko zai sha mamakinta domin in ya yi mata kan kara wlh sai tayi masa na itace.

Cikin gadara yace"Na fad'a mata tun kwanaki da kada na kara ganin ki acikin gidana..Bazai yuyu ki rika shigomin gida bakya daraja ni ba..Kamar ni zaki rika gani kina D'auke kai kamar kin ga kashi..?ai ba gaba da ni kike ba ko Yayarku Asiya ba Sana'ata bace ballatana ke karamar alhaki kin raina uwata da yayata suna fada kina fada sannan ki rika shigomin gida kina raina min wayau bazai sabu ba..Kada na kara ganin kafarki acikin gidana Daga yau sai yau..In yar'uwanki zata yi zumunci dake in kun had'u awani waje ban hanaku zumunci ba ammh ba acikin gidana ba"

Ya karishe fad'a cikin nuna cin mutumci har yana nuna ta da Hannu,Yaya mariya tayi dariyan takaici kafin tace"Shikenan sakon naka..?

Ya daga mata kai Lokaci d'aya yana fadin"eh shikenan"

Yaya mariya ta gyara tsayuwa kafin tace"To ai ba saboda kai ko dangin ka nake zuwa wajen Fa'iza ba..Ku ai baku isa ba wlh Fa'iza yar'uwata ce baka isa ka raba jinin dake Tsakanina da ita ba gida kuma bazan fita ba sai dai kayi abunda zakayi"

Tafad'a cikin Jaddada mganarta cikin mamakinta yace"Haka kika fad'a..?

Ta daga kai kafin tace"Kwarai haka nace in kuma kana da yadda zakayi dani Bismillah.."

Kawai sai ta koma ta zauna kafa d'aya kan d'aya tana latsa wayarta cikin Fushi ya juyo yana kallona cikin Tsawa yace"Wlh ki Fad'ama yar'uwanki ta fice ta barmin gida tun kafin raina ya baci na hadata da jami'an tsaro.."

Na zaro ido cikin rawan murya ina fadin"Yan sanda.."!

Ko kulani bai yi ba ya shige bangaransa da Sauri ni kuma sai kawai na fashe da kuka da Sauri na karisa gaban Yaya mariya zan yi mgana kenan ta Dakatar dani da Sauri kafin tace"Kada ki ce Tak in na isa dake fa'iza in sha Allahu yau zan kawo karshen duk zalunci da yake miki acikin gidan nan"

Cikin kuka nace"Yaya mariya yan Sanda fa yace zai kira miki"

Tayi wani mirmishi kafin tace"in shi takamar shi iskanci na shanyesa na Dokesa ya Dade bai kira yan Sanda ba in yaso ya Dauko gabad'aya police din kasar nan gabadaya yau ko ni ko shi acikin gidan nan"

Tafad'a tana mai kara tabbatar min da mganarta nasan Halinta tana da kafiya da Taurin kai ban kara mgana ba ammh na tsorata sanin Halin Ya Ishaq na kasa zaune na kasa tsaye,Kawai sai gashi ya fito yana waya kalmar da naji ita ta Razani Cikin Fushi yake fadin"Yallabai gida na zasu zo akwai wata matsala ne..Ok sai sun kariso.."

Nasan zai aikata ba ni da Daraja a idanuwansa,ballatana Dangina su yi Daraja a wajensa zai iya aikata duk abunda yaga dama bai damu ba,kuma nasan bazai taba Saurarata ba sai kawai na zube gaban Yaya mariya na Hada Hannayena duka Biyu cikin kuka na fara fadin"Don Allah..Don Allah..Yaya mariya ki tafi bana so ya Tozartaki bana so aci mutuncin ki"

Yaya mariya ta dakamin Tsawa cikin fada tana fadin"Bazan fita ba ina nan inajiran duk abunda zai yi"

Shi kuma yace"Zaki gani sai kin raina kanki yau d'in nan"

Bana so wani abu ya faru shiyasa nake rokonta tatafi cikin wata murya tace min"Ni kike roko na bar miki gidan ki fa'iza saboda wannan azzalumin mijin naki..?

Lokacin da ta fadi haka baya falon ya koma bangaransa ganin bazata Fahimci ba yasa na tashi zan koma Shashen nasa sai gashi mun ci karo da juna,cikin sauri na rikesa ina Fadin"Don Allah kayi hakuri..Kada ka kira mata yan sanda"

Ba laifinta ba ne Goggo ne da suka zo Dubani jiya tace ta zauna na kara jin Sauki shine..Shine ma.."

Sai na kasa karisawa Cikin Tsawa yace"Shine me..?

Cikin In ina nace"Ta tafi da Ahmad tunda..Tunda na ya ye..s.."

Tas..! Kake jin karan marin da ya yarfamin sai d na yi gefe dafe da kuncina cikin Bacin rai ya nuna ni da Hannu yana fadin"Wacece ke da zaki yanke hukunci kan ya'yana ba tare da kin Sanar dani ba..?uban wa yace ki kai min yaro na wani waje? Ban miki kashedi kan hakan ba..?.

Nace ban miki kashedi kan haka ba Fa'iza..?shine kika aikata gaban kanki saboda kin raina ni ko..?

Yana mgana yana nunani da yatsa cikin bacin rai sai kawai na koma na durkushe ina kuka yaya mariya ta mike cikin Takaici da bakin ciki kafin tace"Ba dai Ubanmu kake zagi ba ko..?

Sannan daman ai dabba shi ke dukan matarsa wannan abun da kayi ya tabbatar min da cewa kai Dabba ne acikin mutane"

Ya Ishaq ransa ya baci ya taso mata itama ta taso da Sauri na shiga Tsakaninsu na rike Yaya mariya ina wani irin kuka kamar zan shide cikin Shakewar murya nace"Ki tafi..Ki tafi don Allah yaya mariya ki tafi.."

Yaya mariya ta kalleni kafin tace"Zan tafi..ammh ba ni kadai ba tare da ke Fa'iza yau zaki bar ma wannan azzalumin gidansa in kina da amfani in kuma baki da shi zai sani"

Sai na Rud'e na kasa mgana ta ja Hannuna keey kamar rakumi da alaqa zuwa Dakina ta fara Hadamin kayana tana yi tana fadin"Kin gama zaman aure in da ba'a san Darajan ki ba..da ikon Allah hakkin ki bazai barsa ba sai Allah ya saka miki"

Ni dai na kasa mgana sai uban kuka nake yi,Ta gama had'a min kaya cikin karamar akwatin Amir itama ta Hada nata kayan ta zura hijabi,Nima tace na Dauko Hijabi na saka ganin na kasa tashi yasa ta dauko min ta sakamin tajani,har zuwa Falo yana Tsaye hannayensa goye a bayansa yana Safa da marwa acikin Falon.

Yana ganin mu ya saki mirmishi kafin yace"Better..Ni bazan hanaki tafiya da yar'uwanki ba ni dai ban ce ta tafi ba in kuma tabiki wannan ra'ayinta ne sai dai ta sani in dai ta saka ta bar gidan nan to ta Rubuta ta barsa har abada"

Yaya mariya tace"To sai me..?ai daman ta bar sa har abada kenan wannan bakin gidan da bakomai cikinsa sai zalunci da mugunta da ikon Allah sai Hakkin Fa'iza ya Bibiyeka"

Ya ishaq yace"Sai dai hakkin kashe aure ya Bibiye ki dai..Sakarya wacce bata san inda ke mata ciwo ba..Na dai gama mganata ni dai in dai ta Fita to a bakin auranta sannan har Abada bazata Dawo ba"

Yaya mariya ta fincikeni tana fadin"Zaka gani yau kam zaman Fa'iza da kadaddaran auran ku ya kare"

Bai damu ba ya koma ya zauna ya Dora kafa d'aya kan d'aya ko ajikinsa,Yaya mariya ta rika jana har kofar Falo cikin Dashewar murya nace"Ban saka takalmi ba yaya mariya"

Cikin Fada tace"in mun je tasha na siya miki"

Na kara turjewa ina fadin"Yara na..Yaya mariya su Amir fa..?in na tafi wazai kula da su..?

Ta juyo tana min wani kallo kafin tace"Ko mutuwa zasu yi sai dai su mutu nan d'in ne gidan Ubansu ke kuma ai ba gidan naki uban ba ne wuce muje.."

Ta kara jana naki yarda na Bita na Turje ta juyo ta kara kallona afusace kafim tace"Fa'iza kada ki bari na saka miki Hannu"

Na kasa mgana sai kuka ya'yana nake Tunani in na tafi basu da wani Sauran gata bani da mafita sai zabin Dawowa na cigaba da zama acikin yanayin da nake saboda ya'yana.

Yaya mariya mamaki ya kara kamata lokacin da na kwace hannuna daga gareta na juya baya ina kuka nace"Ki yi hakuri..Kiyi hakuri..Ki tafi don Allah..BAzan iya tafiya na bar ya'ya na ba"

Kiyi hakuri"

Sai kawai na kwashi gudu zuwa Cikin D'akina ina kuka kamar raina zai fita kaina har wani bugawa yake yi Dif dif,Yaya mariya ta kasa motsi saboda abunda nayi Ya Ishaq kuma na zaune yana Dariya kasa kasa kafin ya mike yana kallon Yaya mariya cikin gadara yace"Fita ki bar min gida bakar munafuka..Kin dai ji kunya wlh kin kuma yi asara..Yar'uwan naki da kike Hakilo a kanta ta nuna miki baki da wata Daraja sama dani..Sai ki fice min Daga gida kada na kara ganin siraran kafafunki acikin gidana.."

Yafad'a yana nuna mata hannun alamun ta fice ta bar mai gida Takaici da bakinciki yasa Yaya mariya Zubar kwallah ta kalle shi ta kara kallonsa kafin tace"Naji kayi nasara a kaina zan tafi..kamar yadda ka bukata bazan kara zuwa gidan ka ba..Sannan mganar Fa'iza karyan ka ta sha karya ai jini yafi ruwa kauri sannan wata kusan tafi wata..Zan cigaba da zumumci da yar'uwata domin ba kai ka Had'amu ba..Mgana ta karshe shine akwai Allah kuma yana nan a madakata Duk abunda kake aikata ma Fa'iza na sharri da zalunci kai da Mahaifiyarka da yayarka,Da ikon Allah sai kunga sakkaya tun a duniya sai Allah ya jarabceka da iftila'in da sai ka rasa ina zaka saka kanka in sha Allahu sai Allah ya saukar da aya akan maza ire iren ka da basu darajan matan su sannan basa adalci  ya yin zamantakewar su,Kuma kada ka manta akwai Hakkin zumunci shima sai Allah ya tambaye ka, sannan hakkin Fa'iza bazai  barka kayi rayuwar da kake Buri ba Ishaq Kabir karofi."

Tana gama fad'in haka ta Sauke karamin akwatin na data Dauka,ta juya ta fice tana zubar da hawayen bakinciki da takaici duk da kalamanta sun Dakesa ammh bai damu ba ya Bita har get yana gayamata bakaken mganganu sannan ya Dawo Cikin gida ya Iskoni har dak'i yana gayamin duk mganar da ta fito bakinsa har yana fadim Tunda ya aureni bai Huta ba yake cikin Matsala ni ba matar kirki bace ni matar Tsiya ce.

Nayi kuka,kukan da ban taba yi ba,kukan yadda ya tozarta yar'uwata ni ban damu da kaina ba Daman ni bani da wata Daraja ammh Yaya mariya fa..?yar'uwata ce bata chanchanci cin zarafi da tozarci ba.

In da nagode ma Allah Yaran basu dawo daga makaranta ba,da suna gidan nan ban san wani amsa zan basu ba ina kwance ina kuka suka Shigo,Ganin su yasa nayi saurin share hawayena kaina ciwo yake yi duk yadda yaran suka so su fahimci wani abu ban basu dama ba da Amir ya dameni da Umma baki da lafiya ne..?naga fuskarki ta kumbura ne"

Sai nace masa wani abu ne ya fadamin a ido,Nasan inda Ya Ishaq ya mareni ne ya tasa sannan ga kuma kukan da na sha.

Tuni Ya Ishaq ya fice daga gidan na rarrafa na shiga kitchen na Dafa ma su Amir Jallop din taliya,kunyar kaina nake ji da abunda ya faru ace mijina shi ya tozarta yar'uwata da muka fito ciki d'aya uwa daya uba daya,Abun sai ya tsayamin a cikin raina ya kasa wucewa su kansu yaran su san yanayina ya sauya,suna mgana sai dai na bisu da ido kawai da wuri nayi musu shirin kwanciya Saboda ban jin Dadin jikina,Kamar kazar da kwai ya fashe ma aciki haka jikina ya koma,Kayana da Yaya mariya ta hada ni na kwaso su na maida su muhallinsu araina ina Tunanin Lokaci bai yi ba.lokacin da zan bar Rayuwar Ishaq bai yi ba akwai sauran Lokaci.


Ina D'akina zaune ina kuka ni kadai ina sharan hawaye na Ya Ishaq ya shigo Fuskarsa ba Fara'a,Ina ganinsa na Dago kawai ina kallonsa ina jiran naji dame kazo Saboda nasan wani Sabon Tozarci ne ilai cewa yayi gobe geben nan nasan yadda zan yi na karbo masa D'ansa kafin raina ya baci.

Jikina na rawa cikin rawan murya nace"Goggo ce ta karb'esa fa..?Sai naje nace ta dawo dashi..?

Cikin Tsawa yace"Ina ruwana da wata Goggo..Mama ce..?nace Mama ce..?

In ba munafunci kika so ba, meyasa baki aika ma Mama shi ta yayesa ba..?

To wa ma yace ki yayesa batare da kin Fad'amin ba..?

Kaina na kasa nace"Saboda bani da lafiya ne ina asibiti da kuma na Dawo sai yak'i karb'an Nono sai na yayesa kuma Goggo Saboda Tausayina yasa ta tafi dashi fa"

Karamim Tsaki yaja yana fadin"Kedai kika sani na riga na gaama mgana wlh in gobe da yammah tayi Ahmad bai Dawo gida ba sai na Wulakantaki Fa'iza"

Haka ya fice ya barni ina kuka,ina jin wani daci na tasomin a kasan raina ciwo nayi ba sannu ba Tausasawa ba Lallabawa sai tozarci da cin mutumci ya Allah ga baiwar ka Fa'iza ka bata mafita  D'aya daga cikin mafitan da ka ke bama Bayinka salihai.

Adaran nan barci sai dai barawo ya iya Sace ni da Safe kuma da zazzabi da ciwon kai na tashi su Amir na da Hadda Dakyar na iya musu shiri da abun karyawan su,To basu samu ma tafiya makarantar ba Haruna adaidatan sa ya samu matsala Babansu kuma ko motsinsa ban ji ba,Ballatana na saka ran zai kai su,Sai kawai nace su tube kaya su bari sai gobe sai fadi suke Daada bazai kai mu ba nayi musu shuru kawai ina ji Anum ta je tana ta Buga kofar Shashensa tana kiran sunansa Ammh har tagaji bai fito ba.

Sai daga baya da Amir yaja su suka fara wasa ita da Musty sai ta manta ammh da farko har ta fara kukan ta na rigima..

Ni ko kwata kwata hankalina baya jikina Tunani nake yadda Ahmad zai Dawo kafin yammah tayi nasan duk abunda yace zai aikata ammh na gwammace ni na tozarta da na iya cema Goggo ta Dawomin da Ahmad bazan iya ba Har abada bazan iya ba.

Ranar ko girkin rana ban yi ba gari na jika musu suka sha,Nima ba na wani jin Dadi sai da na sha Panadol cikin mganguna na hawan jini kuma yana da karfi sai Dare nake shan sa.

Bani da masaniyar Ya Ishaq na gidan ko baya gidan,Bayan la'asar ina Dakina na idar da sallah su Amir suna Haraban gida suna wasa dakyar na saka su suka dawo cikin gida suka yi sallah wasa na ransu suka koma suka cigaba da yi.

Tashin mgana na rika ji afalo lokaci d'aya da kiran sunana zubur na mike jin kiran sunana kuma Muryan Mama nake ji tana tsagamin kira da karfi kamar zata tsaga gidan.

Na fito da Sauri muka kusa cin karo da Anty Binta ina shirin gaisheta ta bangaje ni ta shige Mama na Tsaye tana Karkad'a jiki kamar wata mazari Cikin Daga murya tace"Shiga ki fito mata da kayanta jiya bata bi Yar'uwanta ba yau kuma zata bita Daga baya fito mata da kayanta yau in dai ba gidan Sidi da tamadina bane sai Fa"iza ta barmin gidan D'ana"

Hankalina ya tashi jikina ya fara rawa na karisa gaban Mama na zube ina gaisheta bata amsa ni ba ta fito da wayarta ta kira,naji dai tana fadin gasu sun kariso daganan ta kashe wayarta ta koma ta zauna tana kad'a kafa Anty Binta kuma ta rika kwasomin kayana ta na min watsi da su a tsakiyar falo na zama mutum mutum na kasa mgana har Ya Ishaq ya fito Daga bangaransa yana sanye da Jallabiya ko barayina bai kallah ba ya isa ga Mama suka gaisa.

Cikin ko in kula ya zauna gefenta yana fadin"Mama meke faruwa ne..?

Yafad'a yana bin kayan da Anty take watso kayana da kallo Cikin Daga murya Mama tace"Zaman fa'iza a gidan ya kare Daga yau..!

Cikin mamaki yace"Saboda me ne Mama..?

Mama ta mike tana nuna ni da yatsa tana fad'in"Har saboda wannan gayyar Tsiyar gayyar matsiyantan ne za'a zo har gida aci maka mutunci muma aci mana wace ce ita..?taimakon ta fa kayi ita har ta isa..?

Wlh sai ta bar min gidan D'a na damam Darajan mahaifin ku take ci dama ta kai iwar haka ammh Tunda daga ita har yan'uwanta matsiyata ne yau sai na muna musu nafi karfin su..Sakinta zakayi ta kara gaba nagaji da Fitina nagaji Tunda ka auri wannan yarinyar tsiya da Jafa'i basu bar Bibiyan rayuwarmu ba,meye amfanin Mata irin Fa'iza..?

Dangin Talauci Dangin kurame dangin tsiya da tsiyataku..?

Nace meye amfanin mace irin ta..?.

Ai tunda basu san an yi musu alfarma yau zasu sani"

Ta karishe fada tana kumfar baki Shuru yayi bai yi mgana ba, ni kuma kaina na kasa ina kuka,Mama ta cigaba da zagina ni da iyayena da yan'uwana tana aibatana Iyayena barin ma mahaifina da yake kwance a cikin kabarinsa naga bazan iya Jurewa ba na Dago kaina cikin kuka nace"Mama ni ki zageni ni ce nayi miki Laifi ammh me mahaifina yayi miki da kike aibatasa yana kwance acikin kabari..?

Sai mama ta saka salati ta Dire tana Fadin"Ishaq kana jinta ko..?

Sai nace ka sakete zaka saki wannan tsinanniyar bakar yarinyar nan kenan..?

Ya Ishaq ya kalleni alokacin nima ina kallonsa ne, ba kuma Saboda ya barni ba ne ina kallonsa ne domin nasan zai iya yanke duk hukunci da Mama tace ai bata san abunda ya faru ba jiya shi yaje ya fad'amata..

Cikin Karsashin muryan sa yace"Mama ni ba domin Sarkan da Mganar Baba ta sakani aciki ba da Tuni na Rabu da Fa'iza domin na Dad'e da sanin ita ba matar kwarai bace Matar Tsiya ce..Sai dai kalaman Baba su suke zaune da ita acikin gidan nan sannan su suka cece igiyan aure na dake tsakani da ita"

Mama tace"Kalamansa baza su yi wani Tasiri ba ai baya raye yanzu"

Kai ya girgiza mata kafin yace"A"a Mama ki yi mata kowani Hukunci ban da na saki..Ina tsoron kada bakin Baba ya kamani in na Saki Fa'iza"

Hawaye suka gocemin zuciyata naji tana wani irin Zafi shi ya D'aga murya yana fadin"Anty Binta bar watso kayan nan haka kiyi hakuri.."

Anty Binta ta fito tana faman Hararata a kaina ta Tsaya ta saka Hannu ta Dago habana ta kwasheni da mari mai kyau Mama tayi kyafci tana fadin"Kara mata tunda bata da mutumci"

Ta d'aga hannu da niyyar kara marina suka ji kukan su Anum acikin Falo sai ta Dakata,ta d'ago tana kallon su suna bakin kofa atsaye Amir na kuka ammh na hawaye,yana rumgume da Anum da Musty dake kuka share share ganinsu cikin wannan Halin sai naji Rauni ya kamani kawai sai na Bude murya na fashe da kuka

Mama da Anty Binta suka saki baki suna kallona Ya Ishaq kuma sai ya mike ya nufe su yana fadin"My Anum"

Ya saka hannu ya riko Anum dake jikin Amir ta ture hannunsa ta nufeni da gudu cikin kuka tana fadin"Umma..Umma"

Sauran ma sai suka mara mata baya na mike zaune na Bude hannayena na Tari ya'yana da silar su ne nake zaune cikin wannan kaskastaciyar rayuwar.

Rumgumesu nayi kam ina kuka da dukkan zuciyata Anum kuma Musty ma haka Amir ne ke faman gogemin Hawaye na shima kukan yake yi sai na Dago kaina nima na saka Hannuuwana ina share musu hawaye Bud'e bakin Amir sai cewa yayi"Umma ki daina kuka in na girma zan rama miki Dukan ki"

Sai wani kukan ya kwacemin na Rumgume sa ina fadin"Ka da ka zama mai Riko Amir..Ka zama mai yafiya saboda Allah ma gafurun Rahimun ne..Ba wanda ya Dakeni kuka kawai nake yi"

Zai yi mgana na girgizamai kawai ina Hawaye Ya ishaq sai jikinsa yayi sanyi Mama kuwa komawa tayi ta zauna tana Fadin"Yau naga makirci"

Anty Binta sai ta kasa mgana na mike na isa ga kayana na ina Tattarawa Amir da Anum suka tayani muka kwashe na Dauki Musty na Sabashi a baya na rike ma su Amir Hannu ban kara kallon barayin su Mama ba na koma D'akina ammh kuka na bai Tsaya ba.

Anum sai fadi take yi "Umma Daada ne ya Dake ki..?

Da Sauri nace"Ba wanda ya Dakeni Anum..ban da lafiya ne"

Amir da yayi shuru yace"Umma Anty Binta naga ta na dukan ki"

Da Sauri nace"A'a bata Dakeni ba..Hakuri take bani sanda kuka shigo"

Daga gani basu yarda ba Domin suna kallona suna kuma kallon junan su,Amir shi ya tayani na maida kayana cikin Wadrope Ranar tare na kwana da ya'yana acikin D'aki Daga ni har su bamu kara lekawa falo ba bansan Lokacin da su Mama suka tafi ba sannan abinci ma ban yi ba,nace zasu sha gari sukace basajin yunwa nima cikina duk ya toshe bana jin cin komai bakina kamar madaciya.

Washegari kuma Ban sani ba Ya Ishaq ya koma Abuja sai da naga an yini an kwana ban gansa ba nasan ya tafi kenan hadda kuma kwana Biyu su Amir basu samu zuwa ba sai Ranar Lititi suka tafi makaranta Lokacin an gyara adaidaitan Haruna.

Duk da bani da Tabbacin Yaya mariya ta fadama goggo abunda ya faru ammh duk sanda na Tuna abun sai naji ba Dadi,Satin Ahmad hudu A karofi Hafsatu ta Dawo min dashi nasha jinin jikina kila Yaya mariya ta sanar da su komai nayi nayi ta tsaya ta kwana tace Goggo tace kada ta zauna an had'ama Ahmad sha tara na arziki su goldemorn da su Madaran yara,kayan Tea har da Ferfesun kaza sai garin kuni da garin danwake Hafsatu sallah kawai tayi ta juya,ko awa daya batayi ba Daganan sai jikina ya karayin sanyi Ahmad yayi kiba sosai Tafiyarsa har ta fara nuna yana Gudunsa ko'ina sai naji Dadin haka acikin raina duk da bana jin kewarsa Domin na maido Anum wajena take kwana ammh shakuwar dake tsakanin Uwa da abunda ta Haifa Allah kad'ai yasanta.

Ko wata Biyu ba'a rufe da Faruwar lamarin da ya faru ba Zainab ta Haihu Namiji nima ba wanda ya Fad'amin Halisan Anty Mamah suka zo anguwanmu ita da Badariya Daga makaranta suka biyo,Shine naji suna Hirar kuma Badariyan ta tambayeni ko naji nace ban sani ba.

Nan take shaidamin shekaranjiya akayi Haihuwan Zainab ta samu Namiji C.S akayi mata Su mama kamar yanzu aka fara samin jika ta nan tana shirin gagarumin Taro sannan Anty Binta kuma tana ta shirya Mutanen da za'a tafi da su Abuja suna.

Ni dai ban ce komai ba,ammh a raina na ma Zainab fatan samun Lafiya da kuma raya abunda ta Haifa bana mata bakinciki Domin ni ban Dauketa a kishiya ba sai miji na sonka ne zai kara aure ka damu kanka, in ka san baka da wani Daraja babu abunda zai Dameka.


*ASSALAMU ALAIKUM*

*KAYA SUN SAKE SAUKA*.

*INGANTATTUN SAIWOWI DA SASSAKE NE DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZA DA SU*.

*ABIN BIRGEWA BA SAU DAYA AKE AMFANI DA SHI BA*.

*KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR KO KUWA KE DA KANKI ZAKI YI GYARA?*

*INA SAKE YIN ALBISHIR DIN GARIN DAKA MAI KYAU DAN CHADI, SHA DA MADARA KO NONO DA KUMA TSUMIN GAMGAM*.

*GADALIN MATA AKWAI*.

*INA DA TABBACIN INGANCINSU*.

*SANNAN WACCE TAKE SON A DAFA MATA KAZAR, ZA'A DAFA*.

*TUARAREN WUTA NA ASALIN CHADI AKWIA SU AVAILABLE, SAI KIN GWADA ZAKI BADA LABARINSU*

*TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU DOMIN KARIN BAYANI*

*08032773332*.

*NATION WIDE DELIVERY*.

*SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*

🙏.



*Janafty**KANA NAKA..!*


*Wattpad:JamilaUmar315*

*Mallakar:Janafty*

*Arewabook:Jamilaumarjanafty*


MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT 08066726866


Ni MMN MUJAHID Ina da kayn gyara kala kala na kasa da sama Ina Saida supplement da kayan mata kala kala cikin sauki Mai kama da kyauta


Hjy ta ki ajiye kunya kifitu kiyi bayani matsala ki abaki ABINDA yaddace Dake


Ina matan da ke FAMA da bushewa gaba


Ina maccen da take a bushe kamas ba niima miji sai yasa yawun sa ku BASILIN 😳


Ina matar da kishiya ta tayi mata zarra ga miji ke rasa Ina matsala take


Ina wadda mijinta kamar kurma baya nuna ya gamsu Dake Dan ku ayi ku abari duk dai suke dashi


Shin ke ku y'ar kuwa ga mijin ki baya Yi da sanbatu in kinji ana Fadi sai kece karya ce 


Nazo muku da hadin Zuma wadda duk zata magance way'anga matsalolin cikin ikon Allah wanna Zuma ta samu yabo ga duban mutane Sha yanzu magani yanzu ce Banda haufi akanta wanna Zuma tana ta yadda sha'awa Kai tsaye ruba babba 2500 karama 700👌👌 


MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT MUNA SAKWATO DA KEBBI INA AIKAWA KU INA 08066726866


IN BAKI SHIRYA BA KIBARI HAR KI TASHI SAYE 😀


       

           *🅿️13*


Babu wanda ya damu dani ballatana su fad'amin haihuwar zainab d'in, ba domin naji a bakin badariya ba kila har sai in mun hadu na ganta da yaro a hannunta,Ya ishaq tunda ya koma ban kara jinsa ba,Su mama kuma da ni da babu a wajen su duk d'aya ne, 

 Baza su damu da naji komai,ta bangaran su ba Shi kan shi Uban gayyar ai bai Damu ba,Domin na tabbatar ma kaina da ni da banza duk d'aya muke a wajensa in ya saka kafa ya koma Abuja ina da yakinin baya tunawa dani ballatana ya neme ni ko a waya na Zargin hakan ne,saboda bai taba tambaya ta daidai da rana d'aya da cewa Fa'iza ina wayar ki ba..?

Ko na ji ina kiran wayarki a kashe me ya faru..?Bai taba min makamanciyar wannan tambayar ba sai na sakama raina bai taba kirana yaji bai sameni ba,Ballatana yasan wayata ta lalace.

Na riga na saka ma raina mata ire ire na ba su da wani muhimmanci,na amince ba ni da kyau sannan ba ni da wani gata ballatana nasaba,Ammh ni musulma ce sannan Allah ne ya Halliceni,a yadda yaso ya ganni,ban taba jin kunyar yadda Allah ya Hallice ba Saboda nasan bai fi son masu gatan a kaina ba nasan duka Bayi muke a wajensa kuma mun zo duniya ne domin bautar ubangiji.

Na kuna riga na sakama raina ba sai na samu soyayyar miji ba,sannan ba kima sai na zama wata aba mai Daraja ba ni dai ya kasan ce watarana  zan zama bango ga ya'yana shikenan Burina ya cika bani da wata Damuwa Ban matsa ma kaina sai su Mama sun so ni Dole ba domin akwai mutanen da ko Naman jikinka ka ke yankawa ka na basu suna Dafawa baza su taba sonka ba sai na sakama raina haka,Sannan nasan ba ni da abunda zasu kaunace ballatana na saka watarana komai zai zama Tarihi.

Ban san ma ba'ayi suna ba ashe an kara Sati d'aya kafin taron suna ana gobe sunan Badariya ta zo take fadamin Sakom Mama akan na shirya su Amir da kayansu na kwana Biyu zata tafi da su,Baban su yace a taho da su ban yi musu ba na tashi na Shirya musu kayan su masu kyau Amir da Musty da Anum Ahmad kuma ya cika Rigima daman su ukun Mama tace za'a tafi dasu sai da ta jira suka Dawo daga makaranta jin zasu Abuja wajen Daada Anum da Musty suka fara Tsalle Amir ne ya kalleni yana kwabe Fuska Lokaci daya yana fadin"Umma ni bana son zuwa a bar ni a gida"

Sai na kallesa Badariya Hankalinta yayi gaba kan wayarta sai bata ji sa ba na jawosa jikina ina Fadin"Haba Baban katsina wajen Daadan ku zaku je da Anty ku fa..?ba kwa so kaga Sabon kanin ku da Anty ta Haifa muku..?

Sai ya gyad'a min kai alamun yana so kumatunsa na shafa ina Fadin"To kada ka kara cewa bakason zuwa..Kai ma zaka je ka ga Sabon kanin ku ko Amir di na..?

Sai yayi dariyan su na yara kafin yace"Umma ke bazaki je ba..?

Kai na girgiza kafin nace"Zan zo ammh Daga baya kaji ko..?

Sai ya jinjina min kai,mganar da nayi mai yasa ya shiga cikin kannensa suna Murna sai da suka yi sallar mangariba suka ci Faten Ramar da nayi ina da Tsakin tun wanda Goggo ta kawomin ne yayi saura Gidan Sa'adatu na shiga na samu Rama dayake suna da Fili tayi shukeshuke har da su Zogale yanzu na fahimci mutane sune Rahma ina shiga makota na bayan kwana Biyu mu gaisa nima Sa'adatu da Habiba sukan lekoni Lokaci bayan Lokaci sai hakan yake min Dad'i ko da ba na ganin wani nawa a kusa dani Su din da nake gani sai suka Debemin kaso mai yawa na kewar da nayi shekaru yana Damuna.

Sai da su Amir suka tafi naji gidan yayi min shuru Kuka sosai Ahmad ya yi da yaga yan'uwan zasu tafi sai da na Shige da shi daki sannan suka samu Tafiya,Dakyar na samu yayi barci ballatana daman Ahmad akwai rigima irin goyon da nayi Anum ne itama akwai Rigima kuma har yanzu bata Daina ba tana tabawa wani Lokacin don ma ina had'a mata da Nasiha sai take rage rigiman wani Lokacin.

Sunan zai kama ranar jumma'a da Safe misalin karfe goma na Safe na gama wankin kayan yara kenan ina Daki ina shirya Ahmad da nayi mai wanka,kwata kwata ban ji sallama ba Saboda lalurata sai da naji Mganar ta kamar daga kofar Dakin da nake ciki,Ina juyowa muka hada ido Hudu da Yaya asiya Sabe da Jaririnta da karamar jakar matafiya a Hannunta.

Na saki baki fararan hakora na suka bayyana cikin yanayina da murnar da ta cikani nace"Yaya Asiya.."

Dariya tayi Lokaci daya tana karisa shigowa Dakin tana fadin"Na'am Yar Fa'i"Daman ta kan kirani da hakan in tana so ta zolaye ni..

Sai nayi Dariya,na bar Ahmad kan gado bayan na gama sakamai kaya na karbi jakar hannunta na sauke a gefe sannan na karbi Muhammad Auwal dake hannunta ita kuma ta Dauki Ahmad ta daga shi sama tana fadin"Kai Ahmadu naga ka kara girma ne daga ganinka Yaya Ishaq ka Dauko Tsawon kafa zaka yi"

Dukkanmu gefen gadon muka zauna na kamkame Muhammad Auwal da ya zama Lukuti da shi Dagani yana samun kulawa da kuma Nono mai kyau.

Cikin nuna farincikina na shiga gaisheta ta amsa itama cikin Fara'a kafin tace"Nace ni dai bari nazo na gani ko Fa'ina na lafiya ko bata san na Haihu ba ne? shuru baki ba wayarki sannan ina ta kiran ki a kashe kwata kwata bana samun ki kin gani Karofi zani nace bari na fara sauka naga Lafiyarki"

Tana fad'a tana karemin kallo Lokaci daya da nazarina sai na sunkuyar da kaina ina wasa da showel din dake jikin Muhammad Auwal,Naji kunya sosai shi yasa na kasa mgana na kuma san ko zan mutu Ya Ishaq bazai barni naje kano ba ko da ma nasan Haihuwarta ballatana ban sani ba sai zuwan da su Goggo suka yi,bayan sun baro kano alokacin.

Ganin na ki mgana yasa ta kyaleni ta Fahimci abun sai bata matsa min ba,Cikin Nazarin Dakin tace"Naji gidan shuru su Amir suna makaranta kenan..?

Kai tsaye nace mata"Suna chan wajen Babansu jiya mama ta aiko Badariya ta tafi da su baban su yace a taho da su"

Yaya Asiya tace"An yi haka jiya naje gida na iske su Hajiya nata shiri ni ban ma sani ba sai ajiyan ake cemin Amaryan Yaya Ishaq ne ta haihu aiki akayi mata gobe taron suna..har ma ake fadin Ishaq din ya yi ma mahaifin ita zainab din kara sunan babanta ya saka Lawal ammh zasu rika kiransa Farhan"

Kai tsaye nace"Allah ya raya sa"

Ta amsa da Ameen tana fadin"Ke ba'a je da ke ba kenan..?

Sai da na dago na kalleta sannan nace"eh bai ce a zo da ni ba"

Ta gyada kai tana fadin"Bakomai bayan an kwana biyu sai kije ki yi mata barka in kuma tazo shikenan"

Ban amsa mata ba na daga Auwal a Hannuna ina Fadin"Kai Yaya Asiya naga ya girma ne kun yi wata uku ne..?

Dariya tayi kafin tace"Watan sa biyu ne fa da kwanaki yana da girman jiki ne irin Goyon Husain ne zan yi"

Na mike ina Sab'asa a baya na kafin nace"Eh ai suna ma kama da Husain din"

Tace"haka kowa ke cewa"

Tsab na goyesa a bayana na Saka zani ya lafe Ahmad kuma daman da yaji Ruwan zafi sai barci kan gado Yaya Asiya ta kwantar da shi muka fito Falo muna Hira ni dai ina ta Fargaba kada ta sako mganar abunda ya faru Tsakanin Ya Ishaq da Yaya mariya sai naji batamin ba.

Ita tayi mana girki Shinkafa da wake da mai da yaji,Ita tazo min da yaji da kori a robobin su tunda Sana'arta kenan na Dauka ina shinshina kamshin Korin cikin jin dad'i nace"Yaya Asiya korin nan nada kamshi nima ina so na iya had'awa ko shi na fara saidawa in za'a siya"

Yaya Asiya tace"Indai za'a siya koyan sa ba shi da walaha Fa'iza..Sai na koya miki ke da ma na sanki da Sauri Dauke abu cikin Lokaci zaki gane komai sai ki rika zuwa kasuwa kina Siyo kayan  had'in kina hadawa da kanki kuma wlh akwai samu in dai kika Samu masu siya sosai"

Tun da naji ta ambaci kasuwa jikina yayi sanyi sanin ko sama da kasa zata Hade Ya ishaq bazai bar ni na rika fita kasuwa ba sai na share zencen ban kara mata mganar ba.

Sai bayan mun yi sallar azahar mun zauna muna cin abinci ta dago tana kallona kafin tace"in na kwana anan Gobe da Safe zan yi sammako na biya ta Dutsemah na gaida Tamadina na kwanan mata Daya daganan na karisa Karofi na sauke gajiya achan sati yace nayi kafin na koma"

Kai na jinjina kafin nace"Tamadina ta na lafiya..?

Kai tsaye tace min"Lafiya ke shuru Fa'iza muna saka ran haka kwanki da ina jego mun yi waya da Megidanta da Abokiyar zamanta sun tabbatar min tana lafiya,ban ce a bata ba ne kinsan ko tayi mgana awaya bazan gane komai shiyasa na bari sai nazo naje na ganta"

Na kasa mgana kunya nake ji ni da nake kusa ammh mahaifiyata na Raye sai ta shekara bata ganni ba Idanuwana suka ciko da kwallah Yaya Asiya ta gani ta kalleni sannan ta Girgizamin kai kafin tace"Kada ki dami Fa'iza nasan yanayin da kike ciki..Ki zauna ki yi ma aure Biyayya In sha Allahu zaki Rabauta ranar gobe kiyama a wajen Ubangiji..Sai dai duk Lokacin da kika samu dama ki rika zuwa kina Dubata bayan mu bata da kowa Fa'iza ita kadaice ta rage mana sauran gatan mu anan duniyan"

Jinjina mai kai nayi ban ce komai ba ina Tunanin to yaushe nake samun Daman. ?Ko karofi sai na jima ban je ba,in kuma naje sai mutuwa ko Biki suna ma ba na kowa ba sai wanda Mama ta amince min naje nake zuwa.

Zuwan Yaya Asiya ya D'ebemin kewa sosai,Sannan na Fahimci ko Rashin Lafiya na bata sani ba sannan ban ji  tamin mganar ba sai nima nayi mata shuru ban gayamata ba.

Da yammah na rakata makota na ta gaida su Sa'adatu da Habiba ina jin Dad'i Lokacin da na nuna ta nace yayata ce itace Babba ad'akin mu Sa'adatu ta kalleta tace"Ba kwa kama Maman Amir"

Dariya nayi ban yi mgana ba Yaya Asiya ce tace"Ai mu mun fi kama da Babanmu..Ita yanzu da ace kin taba ganin Mahaifiyarmu sai ki iya cewa yaya da kanwa ce saboda Tsabar kamar da suke da juna"

Haka ma Habiba tace itama kamar yadda ta fad'ama Sa'adatu haka ta fadamata,Da muka Dawo gida Yaya Asiya tace"Ko kefa Fa'i ki rika shiga Mutane don.Allah..Yafi ki yi ta zama agida ke kad'ai kamar mayya..Mutane Rahma ne sannan Makoci yafi dan'uwaka tunda sai wani abu ya sameka kafin wani naka yazo ya kawo maka Dauki makocinka yazo ya taimake ka"

Cike da gansuwa da mganarta nace"Hakane"

Domin ya faru akaran kaina kuma nagani,Tare muka kwana agado daya yaran mu na tsakiyar mu mun dad'e bamu yi barci ba Duk Mganar Yaya Asiya na Hakuri ne da kuma hakuri da yadda zamantakewar aure tazo min kafin mu kwanta sai da tace min"Fa'iza gaskiya ya kamata ki fara wata sana'ar ai zama haka bazai haifar miki da komai ba sai takaici Daman mun yi mgana da Mariya zamu tarfa miki jari tunda kina sha'awar Korin ko shi zaki jaraba ki gani ko za'a dace..?

Nayi shuru ban ce mata komai ba sai ta kyaleni sai da Safe bayan mun karya tayi shirin tafiya ta karamin mganar cikin yanayin mganata nace"Yaya Asiya bazai bar ni na rika zuwa kasuwa ba"

Tayi shuru kafin chan tace"Kuma da wannan don wannan..To shikenan  dai zamu tattauna muga wata sana'ar zaki fara wacce bazata kawo miki matsala da mijin ki ba"

Da haka muka rabu da ita har waje na rakata,ina ta mata godiya tazo min da caryfish da yawa,tace na rika miya da shi sannan da Bushasshan kifin da tazo da shi zata kaima Tamadina da su Goggo ta D'ibarmin na karba ina jin hawaye suna kawomin cikin Idanuwana kalli yadda yan'uwana suka zame min garkuwa ammh ahaka su Mama ke min kallo kaskastttaciya mara gata.

Na bata sakon gaisuwa wajen Tamadina tace min insha Allahu zata sanar da ita Sannan nace agaida su Goggo da kowa da kowa ammh na kasa cewa ta gaida min Yaya mariya ina Tsanaanin jin kunyarta sannan ina Tunanin ta Rufamin asiri bata bayyana ma kowa abunda ya faru ba.

Sai naji ta burgeni ta zama yar'uwa mai Rufa ma yar'uwata asiri.


****


Sai Ranar Litini da yammah Jamal ya Dawo min da su Amir,sun zo da kaya niki niki da jakunkuna mai Dauke da Hoton Zainab da Ya ishaq da kyakyawan D'an su kamar balarabe sannan kaladan ma ta Hoton yaron Dauke da sunan Lawal Ishaq kabir karofi(FARHAN)

yaci kayan alfarma kamar asace sa a gudu in ka gansa kamar d'an larabawa,Dole yayi kyau daga uwarsa har ubansa masu kyau ne masha Allah.

Sun taho da kayan fulawa da yawa da Soyayyan Naman kaza,Samosa,Meatpie,Sprilroll,Cake,Da sauran sai lemukan gwangwani jaka shake da kaya Sannan sun taho da Sabbin kaya yan kanti a bakin Amir naji yace Antyn su ta basu sabbin kaya.

Su Anum yan Abuja sai tsallen murna take tana ta bani Labarin abunda ya gudana achan Jamal na zaune kan kujera mai zaman mutum d'aya yana Latsa wayarsa shi haka yake bai cika Hayaniya ba cikin Daga murya ya Dago yana fadin"Anun shut up.."

Da Sauri tayi tsit har tana saka Hannunta a baki ta kama tasan Halinsa baya musu da wasa Musty ya kwace motar wasan da ke Hannun Anum,Domin har da tarkacen kayan wasa suka shigo da su.

Ta mika hannu itama ta kwace sai ya kwabe fuska zai saki kuka da Sauri ta dora Hannu saman bakinta tana fadin"Shiii up.."

Dagani Har Jamal sai da muka yi Dariya Amir kuma mai hankali kayan su da suka watsar a Tsakar Dakin yake tattara zuwa Dakinsu ina kaunar yaron har acikin raina Saboda akwai Boyayyen Dabi'un da ya Dauko nawa.

Jamal na je na kawo ma ruwa ya Dago yana fadin"matar yaya anya ruwan nan zai shiga kuwa..?

Ba waku ne..?

Nayi dariya daman nasan Halinsa kafin nace"Tuwon Masara nake yi miyar Kubewa D'anya zaka ci..?

Da Sauri ya mike yana fadin"Tuwo fa..Am ok."

Na wuce sai da Safe..My childreen Good Night'

Anum da Musty suka bisa da Bye bye uncle ni kuma ina yar Dariya nace ya gaida su mama yace zasu ji,nayi mamakin yadda nake yawan ganinsa a gida lokaci bayan Lokaci,sai washegari da ya shigo anguwan ya kara shigowa na tambayesa ashe yana garin.?sai yace min ya koma makaranta wlh yajin aiki aka shiga shiyasa ya Dawo shekaran jiya.


Nasha Labarai wajen yara musamman ma Anum Amir bai da surutu Musty kuma mganar ba wani kwari tayi ba rabi gwaranci ne,Anum sai fadamin take Umma jaririn Anty mai kyau ne muma yaushe zaki haifo mana Jariri mai kyau..?

Sai na kalleta nayi dariya naja kumatunta kafin nace"In sha Allahu zan haifo muku jariri mai kyau Anum"

Ta Dameni sai faman tambayana takr yaushe da nagaji nace mata watarana sai ta fara murna na kalleta ina jinjina yarinta yara dai basu da matsalan komai a duniya.

Nasan ko kayan da Anum suka Dawo dashi Darajan su Anum naci ba Domin haka ba nasan ko abunda ba'a so ba wanda zai kawomin

Naci kayan fulawan da suka zo da shi kazan dai su na saka ma fridge da safe ina saka musu cikin kwandon abimcinsu in zasu tafi makaranta da Lemuka daman kwanakin baya ruwa nake saka musu pure water da ya kare sai dai na d'ura musu na Famfo a Gorinan na su tunda bana da shi ban kuma da hanyar samu.

Ashe gayya ne guda akayi aka tafi Abuja Badariya taje ita da Halisa Anty Mahma da Anty Binta sai Hajiyar Dala da manyan ya'yanta guda Biyu,duk sai da Badariyan tazo ta ke fadamin.

Ranar da tazo gidana ta kwana Tunda basa zuwa makaranta suna yajin aiki kwananta ta uku mama ta matsa mata sai da ta koma gida ita kuma tana som zama saboda tana koyon girke girke a wajena Ammh Mama bata kaunar wani nata ya rabeni ballatana in tasan nata d'in yana so na ko Fad'an da take yi da Goggo saboda ni ne da ace Goggo bata kaunar mu kamar Yadda Hajiyar Dala ba ruwan ta damu da zaman Lafiya za su yi ammh Saboda ni ta yanke alaqa da Goggo sai wanda ya zama Dolen Dolen an had'a Dangi bata da yadda zatayi.

Ana haka ba Dad'ewa Yara suka yi Hutun makaranta suna gida sai na koma koyar da su na addnini a gida na Bokon kuma ban yi musu wasa ba nakan matsa musu su Dauko Littafansu Amir dake gaba dasu ya Rika Duba musu,nasan zafin rashin Ilimin boko tunda har da shi yasa na zama Bora agidan mijina tunda ko nasan zafin kaskasci bazan so wani daga cikin ya'yana ya Dan'dana abunda nayi shekaru ina Fuskarta ba.

Hutun yaran a gida ya taimakamin sosai na rage damuwa sannan walwalata ta Dawo har na fara maida jikina,sun gama cinye Hutun su suka koma makaranta a satin aka fara musu mganar kudin makaranta da Sabbin Littafai Anun kuma jakar makarantar ta mutu tana bukatar Chanji,sannan sabon Registration ne zata shiga primary 1 da suka fad'amin nace su bari in Uncle Jamal yazo su fad'amai Saboda ni bani da mafita.

Shi kuma kamar yasan ana jiransa sai ya Dauke kafa agidan ni dai fatana da addu'a ta kada su koresu daga makarantar karatun su ya tsaya,Ranar jumma'a sukace duk wanda bai biya ba kada ya zo ina jin haka sai na sakama kaina gwarin gwiwa na Fahimci an kawo gabar da ni ce uwar ya'yana kuma nice Ubansu Ranar Monday nace su shirya tare zamu je makarantar suna ta Murna,na yi wanka na saka kaya na mai kyau da Hijabi na shirya Ahmad na kulle gida nabi Haruna muka je makarantar ban taba zuwa ba Ya Ishaq ke zuwa ko Jamal in wani abu ya taso.

Yaran suka rakani har Office din mai makarantar Mace ce ina ta Fargaban ance da Turanci ake mgana ni kuma ban iya ba,Muna shiga Matar ta Dago fara kyakyawan gaske,na samu karfin gwiwa jin ta min mgana da Hausa ganina da su Amir yasa tace"Umman su ce ko..?

Na gyada mata kai ina mirmishi sai tace na zauna su kuma ta kada su aji suka tafi suna lekena.

Bayan mun gaisa cikin yanayin mganata nayi mata bayanin komai nace su yi hakuri babansu baya nan ne ammh in ya Dawo zai biya.

Sai tace bakomai tasan ba su da matsala da yaranmu nan tace zasu yi ma Anum Rigistration su bata Uniform din Primary section sai su had'a cikin Bill din kudin makaranta nace ba Damuwa muka rabu cikin mutumci a raina nace ashe ba ko'ina ne ake mgana da Turanci ba in ko Hakane nima zan iya shiga ko'ina da yarena na Hausa kuma nayi mgana a Fahimceni.

Haruna ya tafi bakin sana'arsa abun hawa na hau zuwa gida,Daman shi kudin da goggo ta bani da na wajen Yaya Isa na had'a na bashi na wata daya yanzu yana bin na wajen wata uku zuwa Hudu shuru Ya Ishaq bai basa kuma ko zuwansa na karshe bai tsaya ba ya tafi ma ban sani ba ballatana ma ya bani yace na basa ni fa na fara Tunanin tashi Tsaye kawai na nema ma kaina mafita na gama Fahimtar Sabon Iyalin da Ya Ishaq ya Had'a ya zabe su sama da ni da ya'yana ko da yake ai ni ya Dade da Zabar Zainab a kaina ya'yansa ne na Fara Gane ya fara mantawa da matsayin su a wajensu.

Sai a satin da naje makarantar ta su Jamal yazo gidan Anum sarkin karad'i ita ta fadamai an ce su biya kudin makaranta,To kwana biyu tsakani suka zo Da shedar an biya komai Anun an bata sabbin kayan makaranta da Text books,ranar kuma da Daddare shi Jamal din ya kawo musu littafan Rubutu da Sabbin Safuna da takalma ganin ba Jaka sai nake gayamai ta Anum ta lalace yace duka kudin da Ya Ishaq ya Turomai sun kare ammh zai yi ma mama mgana kamar nace ya bar shi ba sai yayi mata ba sai na kasa mai mgana.

Ni nasan za'a rina aiko da yaje yayi mata mgana fad'a ta kama yi tana fadin ina fakewa da ya'ya ina mai da D'anta bawa,ba domin Mama tasan ba'a sauya ma Tuwo suna ba da Tuni ta Hana Yaya Ishaq Dawainiyar ya'yansa to tasan dai ya'ya nasa ne sannan yana son su bazai iya kyalesu ba duk da Yaya Ishaq bashi da Kirki a wajena bazan yi mai karyan baya kula da Laluran ya'yansa ba wani Lokacin har da Muguntan Mama aciki gani take ina Fakewa da Guzuma ina Harbin karkasa.

Jakar da kuma taki bada kud'i a siyan ma Anum kenan Jamal yazo yana fadin da ya ke shi Santsi daya ne baya munafunci kaf abunda Mama ta fad'a ya fadamin sannan ya kara da cewa bai da kudi da ya siya ma Anum din Sabuwar jaka nace kada ya Damu ai na Gode da kokarinsa.

Dakyar na Lallashi Anum ta rika tafiya da Tsohuwar jakarta ni kaina naga duk ta mutu ta yayyage ammh ya na iya..?Tunda ba ni da wata mafitan sai dai ina jiran mafitan da na Roki Allah ya samar min kuma ina ji ajikina ya amsa duka addu'o'i na.


   Yau ta kama alhamis ne tun bayan tafiyar yara makaranta da suka maido wuta na fara guga sallar azahar kadai ya tadani sai rigiman Ahmad na shiga Kitchen na Damamai kuni na basa yasha sai ya fara harkan gabansa yana ta wasa da yar motan wasan yara na Mutsy da suka taho da shi Daga Abuja.

Hankalina ya tafi kan gugan da nake yi ban ji sallama ba,Kuma ko ma anyi in ba an matso kusa dani ba ne bana jin sallamr sai da naji an tabani na Juyo da Sauri har na Tsorata sai naga Tamadina da abokiyar zamanta Maman Isuhu suke kiranta.

Ai basan Lokacin da na watsar da gugan gabana ba na Daka Tsalle na Rumgume Tamadina ina murnar ganinta Cikin yanayin mganarta na Rikeni tana fadin"Faaa...Izzzaa..'

Sakin ta nayi na koma ina Dariya ina musu barka da zuwa,Ahmad ne motarsa ta makale jikin kujera sai ya fara kuka,Tamadina tayi Saurin zuwa ta Dauke sa,Ni kuma na kashe Soket din gugan da nake yi jikina na rawa Farinciki kamar ya sumar dani na nufi kitchen na Dauko musu ruwa na kawo musu ina gaishe su.

Sun sha ruwan Tamadina kuma wanda ta rage ta bama Ahmad kamar ya ganeta ya ko lafe a jikinta shi da ya ke da kiwuya.

Kafin ma na tambayesu daga Ina Mamar Isuhu ta ke shaidamin Matar yaron Uwargidan su ce ta haihu aiki akayi mata tana Asibitin katsina shine suka zo Dubata Tamadina tace su Biyo su yi sallah kafin su tafi.

Aiko naji Dadi,Dakina na kai su suka shiga bayi domin alwala ni kuma na fada Kitchen na fara kokarin sama musu abinci Jallop din Shinkafa na Dafa musu da bushasshan kifin da Yaya Asiya ta kawomin ina ta lallabawa Sauran sa kenan nayi takaicin rashin kudi ko Lemu ban da shi ballatana na siya musu kuma bani da kayan had'a Lemu ko daya ballatana na Had'a musu.

Har Daki na kai musu na iske sun Idar da Salla,Ahmad na kan jikim Tamadina yana ta wasan sa ta kalleni cikin mganarta tace"Suuuu...Saurrraaan...yarrran fa..?

Nace"Suna makaranta Tamadina sai yammah zasu dawo"

Ta gyada min kai Allah Sarki Uwa,uwa ce ko da akan bola take kwana,ita fa uwa ta gwammace tayi ma Abun da ta haifa ko da bazai rama mata wannan alherin ba.

Gyad'a Soyayyiya da Masara gashashiya ta kawo ma su Amir da gurjiya dafaffiya Maman Isuhu na Dariya tace abakin asibiti ta siya Masaran nan da gurjiya.

Ta turamin gabana tace na bama Yara sai hawaye suka kawomin cikin Idona na fara godiya Ahmad dai sai bare mai gurjiya take yi tana bashi yana Mamula da Hakoran sa guda Hudu Biyu a gaba biyu a kasa da suka fitomai.

Falo na koma har sai da suka gama cin abimcin,Sannan na koma naga suna shirin tafiya sai naji kamar kar su tafi ammh ba Dama Hijabi na Dauka muka fito ina Tunanin me nake da shi da zan basu..?

Na duba gabas da yammah ba ni da komai ballatana na basu haka muka tafi waje da su,ni nace su zo na kai su makota na da muke mutumci su gaisa.

Sa'adatu kadai muka samu Habiba bata nan taje gidan su daman yar katsina ce acikin gari.

Sa'adatu tana ganin Tamadina tace min"ga maman ku ko..?

Na gyada mata kai ta gaishe su cikin Ladabi daga jin yanayin mganar Tamadina basai ta nemi karin bayani ba tasan inda na gado Lalurata kenan.

Ita ta fitar dani kunya ta basu siga da yawa cikin wacce take saidawa bani da bakin da zan gode ma Sa'adatun tamin komai shiyasa mata mu daina kuskure domin mazajen mu sun hanamu huld'a da makotanmu sai mu Biye musu mu sani Annabi ma yayi Mgamar Hakkin makota sannan mutane Rahma ne duk yadda mutum yake shiga Jama'a yana da Bambamci da wanda ba ya shiga mutane sosai.

Har bakin Titi na rakasu suka samu Motar Dutsemah,Kunya naji da zasu tafi ban basu ko kudi ba Ahmad har da rigiman Tafiyar Tamadina nace Yaro yasan kakarsa.

Sai da suka wuce sannan na koma gida Ranar cikin Annushuwa na yini kamar an mun bushara da gidan Aljanmah sai dai ina ta kallon Tamadina ta kara ramewa nima tana ta kallona duk sanda na kalleta sai mun Had'a ido,Ina Kaunar Uwata a yadda take domin bani da makwafinta in kuma na rasata har Abada nayi maraici gaba da baya.

Haka kurum in na Tuna da kallon sai naji jikina yayi sanyi a raina nace kodai kallon karshe take yi mim..?

Tuna haka yasa sai da gabana ya amsa da Sauri nace a fili"A'a ba haka ba ne Insha Allahu ba yanzu zaki barmu ba Tamadina."

Da su Amir suka Dawo na basu tsaraban Tamadina suna ta murna sukace min waya siya musu ina Mirmishi nace"Kakar ku"

Sai Anum tace"Mama..?

Sai na kallesu nace'A'a mahaifiyata..Sunan ta Tamadina"

Anum tace"Umma bamu santa ba meyasa ba ma zuwa wajenta..?

Sai na kasa mgana nayi gefe da kaina araina ina auna yadda Ya Ishaq ya Rusamin rayuwata gabad'aya ace ya'yana ma basu san wacce ta Haifeni ba ?

sai kirjina ya karayin nauyi da Dubara na share hawayena na Lallab'e su da cewa zan kaisu su ganta Amir dai zai iya ganeta shima ba lalle ba.

A fili na furta"Na ga ta kaina ni Fa'iza wannan wata irin rayuwa nake yi haka..?




*FA'IZA NA GODIYA TACE KU YI HAKURI KOWANI TSANANI SAUKI NA WAJEN ALLAH TACE MADALLA DA KU MADALLAH DA MASOYAN JANAFTY*







*Janafty**KANA NAKA..!*


*Wattpad:JamilaUmar315*

*Mallakar:Janafty*

*Arewabook:Jamilaumarjanafty*


MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT 08066726866


Ni MMN MUJAHID Ina da kayn gyara kala kala na kasa da sama Ina Saida supplement da kayan mata kala kala cikin sauki Mai kama da kyauta


Hjy ta ki ajiye kunya kifitu kiyi bayani matsala ki abaki ABINDA yaddace Dake


Ina matan da ke FAMA da bushewa gaba


Ina maccen da take a bushe kamas ba niima miji sai yasa yawun sa ku BASILIN 😳


Ina matar da kishiya ta tayi mata zarra ga miji ke rasa Ina matsala take


Ina wadda mijinta kamar kurma baya nuna ya gamsu Dake Dan ku ayi ku abari duk dai suke dashi


Shin ke ku y'ar kuwa ga mijin ki baya Yi da sanbatu in kinji ana Fadi sai kece karya ce 


Nazo muku da hadin Zuma wadda duk zata magance way'anga matsalolin cikin ikon Allah wanna Zuma ta samu yabo ga duban mutane Sha yanzu magani yanzu ce Banda haufi akanta wanna Zuma tana ta yadda sha'awa Kai tsaye ruba babba 2500 karama 700👌👌 


MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT MUNA SAKWATO DA KEBBI INA AIKAWA KU INA 08066726866


IN BAKI SHIRYA BA KIBARI HAR KI TASHI SAYE 😀


          *🅿️14*


Tsakanin zuwan Tamadina da saukan su Ya ishaq da amaryan sa Zainab garin katsina kwana biyu ne,Ni bani da labarin suna tafe,Sai da yammah da suka iso gidan nagan su,Ashe wai Mama aka kawo ma Farhan ta gani shine suka zo gayya guda bayan kanwarta zuzu har da wata yarinya mai yi mata reno,sai Iyayanta Guda biyu,ban taba ganin inda iyaye ke rako ya'yansu ganin Dangin miji ba sai akan Amaryan Yaya ishaq na fara gani sai abun bai wani bani mamaki ba ya'yan yan boko ne da suka mallaki dukkan wani kawan duniya.

Shashen sa suka yada Zango dukkansu ni dai iyakata nayi D'awaniya da su kamar yadda na saba na abinci da shimfidar fuska wacce Hausawa sukace ta fi na tabarma.

Har shashen nasa na shiga suna ciki ita da kanwarta mai renon ne ke falo tana Fama da Farhan Yaya Ishaq kuma suna shigowa ya fice bansan ina zashi ba daga gani dai fitace mai muhimmanci.

Hannun mai renon sa na karb'esa ina kallon yaron yayi wani girma kamar dan wata biyar,Tsarki ya tabbata ga Allah nace acikin raina,Saboda ashe a Hoto ban ga komai na kyau da zatin yaron ba sai da na gansa a hannuna Jajir da shi kamar ka taba jininsa ya fito yafi kama da Yaya Ishaq sai dai Hancinsa irin na mamansa ne har da Idanuwan ma kuka yake ta yi yarinyar ta kasa lallashinsa na kalleta Lokaci daya ina fadin"me yasa ya ke kuka..?

Kamar zatayi kuka tace"Ni ma ban sani ba kuma ba yunwa yake ji ba yanzu na basa madaran sa"

Rikesa nayi a jikina ina kara Tattaba jikinsa naji zafi kad'an alamun yana Tare da zazzabi sai na kalleta lokaci daya ina fadin"Kamar da zazzabi a jikinsa bari nayi mai wanka sai a bashi mgani"

Kamar zatayi mgana sai kuma ta fasa ni kuma na fice da shi zuciya ta daya,Daman su Amir na makaranta basu dawo ba,kitchen na shiga na saka Ruwan zafi bayan na goyasa luf kuwa yayi shuru ruwan na zafi na juye a baho na shiga Dakina nayi mai wanka tas da ruwa masu dimi ina cikin yi mai wankan na fahimci Cibiyarsa ne ta dan kumbura ina da wani mgani da Goggo ta bani Tun Ahmad na karami da cibiyarsa ta fara kumbura ina fara shafamai ta koma ta daina ciwo kuma ta Daina kumburin,sai na Dauko daman ban cika banzarta da irin wadanan kayan ba tunda ina da yara na mulke mai Cibiyar da shi cikin kayan Ahmad da suka yi mai kad'an na saka mai riga da wando,na goyasa ram a bayana ba jimawa sai barci ya kwashe sa da shi a bayana na cigaba da Hidima ta Ahmad daman yayi barci ne yana tashi ya kafa rigiman sai na Sauke Farhan dake bayana na goyasa.

Ina Dariya shima na Sunkucesa na Saba a kafad'ana ina fadin"Haba babban mutum ka girma ka bar ma kaninka bambon mana"

Kuka ya fara min na fita da shi Falo na Zubomai abinci na zauna ina basa Shidda Saura sai ga yaran sun Dawo daga makaranta suna ganin goyo a baya suka fara tambayana Umma wa kika goya kamar ma Anum taji Labari.

Ina mirmishi nace"Sabon jaririn Anty ne"

Anum ta daka tsalle tana lekonsa ta bayana kafin tace"Umma waya zo da shi..?

Sai nace"Tare da Daadan ku suka zo da Antyn ku"

Anum ta fara tsalle tana oyoyo oyoyo Daada Musty na tayata Amir dai Dakin su ya shige ya Sauya kaya gudu ta kwaasa zuwa shashen baban nasu nace mata ya fita ta bari ta sauya kaya taci abinci in suka yi sallah sai ta shiga ta gaida Antyn nasu bata da yadda zatayi hakanan ta Hakura ni suka bari da kwashe takalma da jakunkunar su da suka watsar a tsakar Falon.

Anum dakina ta Shige Saboda na maidata da ita da kayanta tare dani,ina shigowa na iske ta watso kayanta kan gado da karfi nace"Anum ba na hanaki watso kaya ba..?

Cikin rigima tace"To umma ban ga wanda zan saka ba ne"

Riga da sikat na Dauko mata na bata ina Fadin"Duk na goge fa kayan nan ammh ji yadda kika wargazasu Anum"

Ganin ban ji dadi ba yasa tace"Kiyi hakuri Umma"

Kanta na shafa ina fadin"Bakomai yar Umma muje aci abinnci"

Musty kuma Amir ya cire mai kayan makarantar ya sakamai, na gida suka fito falo na zubo musu abinci Farar shinkafa da miya,Sa'adatu ta aiko min da Kayan Miya itama daga gidansu aka aiko mata dashi kamar babanta aikin gwari yake yi.

Dukkansu waje daya na Hada musu kamar yadda na saba sun fara ci,Anum da Musty suka fara rigima kamar kullum nace su bari suka ki sai na kalle su ina fadin"Anum zan mai da ke cin abinci ke kad'ai tunda bakya jin mgana"

Jin haka yasa Da sauri Amir yace"Umma ki yi hakuri Musty ke Tsokananrta ki barta mu rika ci tare"

Sai na gyada kai ina fadin"Musty kana son Bulala ne..?

Na fada ina nuna masa hannun alamun duka kafada ya makale dariya nayi kafin nace"To ka daina tsonakar Yaya Anum in baka son duka"

Da sauri ya gyada min kai Lokaci daya yana fadin"To umma"

Cikin Salom mganarsa ,cin abinci suka cigaba da yi a natse ni kuma Farhan dake baya na ne ya motsa sai na mike ina Jijjigasa Daidai da Bude kofar falo da Shigowar Yaya Ishaq bayansa Jamal ne da manyan Ledoji,Nasan har ga Allah bai kalleni ba,ballatana ma yasan wanda na Goya Sannu da zuwan ma da nayi mai ban ji ya amsa ba Jamal ne yake kokarin Sauke Lodijin hannunsa a falon da Sauri ya Juyo yana fadin"Jamal bani Lodojin Hannunka"

Yafada daidai da yaran zasu tashi suna kiran Daada da karfi nace su koma su gama cin abincin su duk da ban kallesa ba nasan sai alokacin ya bini da kallo ni kuma sai na Dauke kaina ba domin ina jin Haushin sa ba sai domin nasan ba ni da wata Daraja a wajensa shiyasa nima na koyi kama kaina.

Jin abunda nace ne yasa ya kalli yaran yana fadin"Ku gama cin abincin ok.?

Atare suka gyada mai kai Jamal ya mika masa ledojin hannunsa ya shige Bangaransa sai da ya shige na Dawo da kallona wajen Jamal wanda ya zauna saman kujera su Amir na gaishesa ya amsa yana fadin"My Childreen how far"

Amir ne ya amsa mai da We are fine Uncle"Dariya yayi yana fadin"Daddy na ya fi kowa gane karatu a makaranta ko Amir..?

Anum ta tura baki tana fadin"Nifa Uncle"

Kallonta yayi kafin yace"Mommy nama tana ganewa itama"

Jin haka yasa ta washe baki Musty kuma ya tayata,Sai alokacin ya Dago muka gaisa,cikin yanayin mganata nace"Ya su Mama..?Daga ina haka da yammah nan..?

Yana sauke ajiyar zuciya na gajiya yace"Wlh Dad din Anty Zainab muka kai Masauki  sannan muka je Restaurant  muka yi oder abinci muka Biya gidan Mama muka kai mata kinsan Mom din Anty Zainab din wajen Mama ta sauka"

Na jinjina kai ban yi mgana ba ya cigaba da fadin"Shine duk najini a gajiye me kuka dafa ne..?

Kai tsaye nace"Farar shinkafa da miya ne a zubo maka ne..?

Kai ya girgizamin kafin yace"Bari mu yi sallah naji an fara kira ma"

Ina shirin mgana Yaya Ishaq ya fito Daga bangaransa, da Sauri bayan sa Zainab ne da kanwarta,Wacce ke jan Hannun yarinyar da suka zo da ita baiwar Allah tana ta kuka.

Ganin su hankali tashe yasa Jamal ya mike cikin wani yanayi yana fadin"Me ke faruwa ne..?

Zainab ne cikin rawar murya tace"Farhan..Ba mu ga farhan ba"

Sai abun ya bani mamaki suna nufin basu ga Farhan goye a bayana ba..?

Kafin na iya mgana Zuzu ta mari yarinyar nan Lokaci d'aya tana Hankadeta cikin fada tace"Ina Farhan.?wa kika bama shi..?

Yarinyar sai ta kasa mgana sai kuka Ya Ishaq ya fara fadin"To ku ina kuka shige ku bar ta dashi..?

Zainab ta fara fadin"Muna ciki ni da zuzu muna mgana mu ka bar Farhan hannun Shema'u"

Ganin abun nasu ya koma kan yarinyar har Ya Ishaq ya fara fada ita kuma sai ta kasa mgana ta Dago tana kallona kafin nayi mgana da Sauri Anum tace"Jaririn Anty..?ga shi nan Umma ta goyasa"

Sai kallo ya koma kaina ni kuma sai na juya bayana suka ga Farhan goye a bayana,yana barcinsa cikin kwanciyar Hankali ina jin su suka Sauke ajiyar rai a tare Zainab tace"Thank god.."

Cikin yanayin mganata nace"Na shiga ne na iske yana ta kuka na karbesa ashe cibiyarsa ke ciwo shiyasa yake Rigima"

Kamar kiftawan ido nagansu a gabana,suna rige rigen kwancen goyen bayana ba Ya Ishaq ba,sannan ba Zainab ba kanwarta ba,zuzu ce ta kalleni tana fadin"So kike ya karye kafarsa..?ba'a fara goyasa ba"

Ni dai ban damu ba da Sauri na Sauko shi Tare suka karbesa ita da Zainab din Mamaki ya rufeni Lokacin da Ya Ishaq ya faramin fad'a meyasa ban yi mgana ba ina ji ana neman Farhan.

Na kallesa cikin yanayina Kafin nace"kayi hakuri na zata ka gansa a bayana"

Cikin Fusata yace"In da na gansa zaki ji muna neman sa..?

Kuma kada ki kara goyasa tunda bai saba ba,Ba irin yaran ki ba ne da kika Saba goyasu ba"

Kamar wata wawiya haka na bisa da kallon Zainab ta kara fadin"Honey kafarsa bata samu matsala ba ko..?

Tafada tana nuna masa suka Taru suna kallon kafarsa yaron suna Tattabasa kamar na shafamai mugun abu,Cibiyar Ta bude tana kallo Zuzu ta leka tana fadin"What is this..?

Wannan kayan fa..?

Tafad'a a wulakance,karbansa tayi Tun anan ta cire mai kayan da na sakamai,Ita da kanwarta suka koma ciki Shi kuma ya bisu,kamar wani bita zai zai,ni dai da kallo na bisu Jamal ne, ya koma zauna yana fadin Allah ya kyauta.

Yaran kuma duk sun yi wani iri,ganin abunda ya faru ni Dariya ma suka bani wai kafarsa zata samu matsala Saboda goye,Allah sarki rayuwa da goye na illa da tuni mu kan mu mun samu illah Tunda a baya kafin zamani ya zo da sauye sauye goyen aka sani ba wani gayu da feleke feleke irin na yan zamani masu nasaba da boko ya gama ratsasu ammh irin mu yan gargajiya ai goyen muka sani.

Daganan dakina na koma Dauke da Ahmad araina nace in na goya nawa ai ba mai cewa zan karya masa kafa,Amir da Musty tare da Babansu da Uncle suka tafi masallaci ni kuma muka yi namu ni da Anum.

Daganan ta tafi bangaran Baban nasu,Ta damu sai taje sai nace ta tafi,Su Amir kuma sai da suka yi Isha'i suka dawo suma ban kara ganin su ba Bangaran suka shige Jamal kadai ne afalo na zubo mai abinci yaci muna dan Taba Hira sama sama bai jima ba yayi min sallama ya tafi.

Daki na koma nayi wanka nayi ma Ahmad,na shiryasa nan da nan sai barci yau bai yi rigima ba sosai su Anum sai goma saura suka Dawo Daki  suna bani labarin sun ci nama da Ice Cream,Amir dai bana jin bakinsa sai bakin Anum da baya gajiya da mgana.

Washegari ba makarantar Boko sai Tahfeez tun safe nayi musu shiri suka wuce,Shinkafar jiya data rage na Dumama ma yara sukaci suka tafi,Sai Sauran Taliyan data rage na Dafa musu da miyar suka tafi da shi ni kaina Sauran Shinkafar naci bamu da dankali ba kwai ba komai na Kayan breakfast ballatana nayi  musu sai na kama kaina,ina gama abunda zan yi na koma daki bayan na tattara kayan yara da suka zubar afalo.

Dakin su na shiga nayi musu kaye kayen kayan da suka watsar sannan na koma nayi wanka na yi ma Ahmad daman na Dama mai kunninsa na dura masa yasha sai ya cigaba da Wasan sa,Ganin ban da wani abu da zan yi sai na dauko Qur'ani na fara karantawa ina cikin karatun ne naji Muryan Yaya Ishaq na kiran sunana sai da na kai karshen Ayan sannan na Tsaya Daga bakin kofa ya tsaya Ahmad na ganinsa ya fara tafiya wajensa yana Washe mai baki ya Dauke sa ya daga sama yana fadin"Ahmad ka zama kato yanzu"

Shi ko sai bangala Dariya yake yi.

Hijabin jikina na gyara sannan na kallesa ina fadin"Ina kwana.."

Ya amsa ba tare da ya kalleni ba ya cigaba da fadin"Ba abun karyawa ne..?

Kai tsaye nace"Babu komai na cefane shinkafar jiya ce da nadafa ta rage muka dumama muka ci ni da yara"

Shuru yayi bai kara mgana ba daganan ya fice Dauke da Ahmad ashe kasuwa ya tafi yayo mana Cefane duk da bamai yawa ba ne zai iya isa har bayan sun tafi muma yayi mana Saura.

Na rana kadai yace nayi Inaga a waje ya siya musu wanda zasu karya da shi,couscouss nayi musu da rana mai Hanta da kayan lambu,basu fito ba nima ban bisu ba sai bayan La'asar na shiga muka gaisa sama sama Farhan na Hannun kanwar ta kamkamesa sai ban zura kaina wajen karbansa ba,na fito na koma Daki Ahmad kamar ya sani yaki ko sauka yaje wajen zainab din data ke kiransa ya lafe ajikina.

Tunda suka zo suna bangaransa komai sai dai na shigar musu da shi ban damu ba domin nasan lada zan samu ciyar da su din da nake yi sannan Gidana suka zo akwai hakkin abinci su a wuyana.

Kwanansu uku da zuwa Ya Ishaq yace na shirya zamu je gidan Mama na gaida iyayan zainab,Da daddare mukaje dukkanmu har da yara da ita Zainab din sai da naga mahaifiyarta da mahaifinta naga inda suka Dauko Kyan Fuska Mahaifiyarsu Hajiya Halima mun gaisa cikin Sakin Fuska Mahaifin su Dr.Lawal ya amsa min a Wani karkace ya kalli yarsa yana fadin"My dota wannan ce abokiyar zaman taki..?

Ta dagamai kai tana fadin"Yes Daddy"

Ya kalleni ina Duke gabansa Ahmad na Hannuna kafin yace"Sannu"

Nayi shuru domin ban jisa ba Itace tace"Daddy ta na da problem din Hearing sai ka daga murya"

Ido ya ware kafin yace"is that serous.."?

Kai ta gyada mai sai naga ya daga glass din sa sama yana kare min kallo araina sai naji girmamsa ya zube ai shi Babba ne kuma namiji irin kallon kurillah dayake bina da shi bai Dace ba.

Su Amir kuwa da suka gaishesa ya amsa yana fadin"Bakaken ya'yan Ishaq kuna lafiya..?

Naji abunda yace sai naji ban ji dadi ba saboda su yara ne abu kad'an za'a fada su dauka wani abu ne Jikansa ya amsa yana ta mai wasa Anum nata son ya bata ta Dauka yace"No..No..baza ki iya ba kada ki kada shi..Kinga farin yaron da babu a gidan ko..?

Duka har su Mama suna falon Ammh ba wanda ya damu da mganarsa sai ma Dariya da Mama tayi tana fadin"Wlh kuwa Alhaji uwar ai sai dai in ta Haihu su dauko bakin Fatarta"

Hajiya Halima ce duk bataji dadin Mganganun ba sai ta juya tana yi ma Zainab mgana,ni dai ina zaune kamar wata yar aikin cikin su na kosa mu koma gida,aiko sai wajen goma muka koma gida,Da safe ina yi ma su Amir shirin makaranta Amir ya kalleni yana fadin"Umma menene baki..?

Gabana ya fadi na kallesa na kasa mgana ya kara cewa"Umma baki ba abu ba ne mai kyau..?

Da Sauri nace"Da baki da fari duk abu ne mai kyau Amir kaji ko..?

Ban kara basa damar mganar ba saboda bansan me zan ce mai a gaba ba,Bana so ya'yana su fuskanci abunda na Fuskanta tsawon shekaru

Ashe basu tsira ba Dole dai sai an goranta ma ya'yana kwanansu shida Zainab din tagayamin washegari zasu koma saboda ayyukansu sun zo sun gaishemu tunda naki zuwa nace mata zan zo in sha Allahu.

Zainab ba ruwanta macece Faram Faram ko ta na da wani abu aranta bata taba nuna min ba Kanwarta ne mai D'agawa da isa harta su Amir basa Rabanta,Har Anum da take da Son Jama'a basa zuwa kusa da ita ta cika Fad'a da isa da fadin rai.

Ni ban isa na hana su Amir shiga bangaran Mahaifin su ba,Suna son Daukan Kaninsu ni kums ban isa na Hanasu ba ai dan'uwansu ne ni bansan abunda ya faru ba da yammah bayan sun dawo daga makaranta Kayan su kadai suka cire ko abinci basu tsaya ba suka tafi chan wajen Farhan har da Amir da bai cika shiga ba in dai ba Tare da Babansu ba.

Ina kitchen ina Zuba musu abimci Amir ya shigo har da hawaye a gefen Idanuwansa na kallesa ina Fadin"Babana wa ya tabamin kai..?

Bai min mgana ba ya fita nima na Dauki abinci zuwa Falo na ijiye Saman Cafet din dake Falon na isa ga Amir daya zauna yayi Tagumi.

Na cire hannun Tagumi ina Fadin"Uhm..gayamin wa ya tabamin kai..?ko Anum ce ta tsokane ka..?

Cikin ido ya kalleni yace"Umma kin ce baki abu ne mai kyau..Ammh yar'uwan Anty tace min ni baki ne kada na Shafa ma Farhan baki na"

A rarrabe ya fadi mganar kuka yaci karfinsa Amir na da zuciya shiyasa bai cika Hayaniya ba.

Jawosa jikina nayi na Rumgume ina Fadin"Ya isa..Shiii..Ya isa"

Na dagosa na Share mai Hawaye ina Fadin"Kada ka damu da mganarta Da fari da baki duka Hallitan Ubangiji ne sannan Duka d'aya suke a wajensa.."

Zai kara mgana na girgiza kai ina Fadin"Ya isa zauna ka ci abinci"

Bai yi musu ba ya zauna sai dai sai ajiyar zuciya yake saukewa Raina sai naji ya baci taya zasu rika Gurbatamin Tunanin yarana Amir dan Shekaru tara da wani abu suna neman sakamai Tunanin banza.

Ina cikin Tunanin naji yace"Umma su Anum suna wajen Anty"

Kai na gyada mai ina fadin"Bari naje na taho da su"

Kai Tsaye bangaran nashi na shiga Zainab din bata falo sai kanwar nata,Sai yarinyar dake kula da farhan Tana rike da shi ita kuma Zuzu tana danna wayarta Anum da Musty suna ta wasan su ya'yan Anty ne su.

Ina shigowa kai tsaye ita na Nufa ina Fadin"Me kika fad'ama Amir..?

Da yanayin mganata ta Dago tana kallon kafin tace"Ni..?

Lokaci daya tana nuna kanta tana wani tabe baki ban damu ba nace"Baki Tunanin shi yaro ne..?in bazaki bari ya Daukesa ba,sai ki hanasa  ba wai ki gayamsa mganar da Hankalinsa bazai iya Dauka ba.."

Ta kuramin ido tana kallona ban damu ba na cigaba da fadin"Kada ki kara gayama yara na abunda zai Dame su bana so..Ke bakuwace ki gama bakuntarki ki tafi bana so ki shiga Tsarin Tarbiyan yara na"

Har na juya na juyo ina kallonta Lokaci da'ya ina Fadin"Sannan in baki sani ba ki sani da Bakin da Farin duka Hallitun Ubangiji ne sannan d'aya suke a wajensa Launin fata bazai taba zama wariya ga musulmin kwarai ba"

Daga haka na juya na kama Hannun Anum Da Musty muka fice ina kallo Har Zainab din ta fito daga cikin Dakin ta tsaya tana kallona ni kuma ko kallonta ma ban yi ba.

Haka kurum naji ni zan iya Daukan kowani cin zarafi ammh bazan aminta arika cin zarafin yarana ba a bata musu Tunanin su ba Shiyasa naja mata kunne tun da wuri.

Ni ban san ashe wannan mganar tajawo min bala'i ba sai da Daddare sai ga Mama da mahaifan Zainab din Har da Anty Binta sun zo gidan,Ya Ishaq da bai yini a gida ba shima ya Dawo Kirana kawai  yazo yayi da kansa Fuskar nan tasa a hade kamar Hadari Allah ya taimake ni yaran sun kwanta da wuri da a gabansu za"a cimin zarafi.

Ima fitowa tun da naga mama da Anty Binta na sadakar wannan taron nawa ne sai kanwar Zainab da ke jikin Mahaifinsu tana ta sharban kuka Fuskar kowa ba fara'a na samu gefe na zauna ina gaida su Mama ko amsani batayi ba ta fara dakamin Tsawa tana fadin"Rike gaisuwarki mara Mutumci me wannan yarinyar tayi miki kika zageta kika ci mata Mutumci..?

Sai da ta fad'a na Dago ina kallon Zuzu din har tana wani matse kwalla da majina sai alokacin na Fahimci komai ban ji nayi nadama ba cikin yanayin mganata nace"ni ban zageta ko naci mata mutumci ba..nayi mata fad'a ne"

Anty Binta tayi zaraf tana fadin"Fada..?Sannu uwarta yarki ce da zaki tasata kina mata fada ishasshiya.?

Hajiya Halima ce tace"a bi a sannu Hajiya"

Mama tace"Hajiya ai bata da mutumci ne..Daman bata so auran Ishaq da Zainab ba,kuma  tun tuni take neman daman cin mana mutumci bata samu ba sai yau"

Ni dai sai na kasa mgana Yaya Ishaq ya kalleni ya watsamin Harara yana Fadin"Daga kawai ta hana Amir Daukan Farhan Saboda bazai iya Daukansa ba sai ki bita har Daki ki zageta ki zagi iyayanta sannan har kina ikirarin cewa gidanki ne uban wa ya ce miki nan gidan ki ne..?

Ko da sunan ki na siya gidan ban sani ba..?

Kaina na kasa na kasa mgana ina jin wannan cin mutimcin Mama tayi kafyci tana fadin"Ahto tambaye ta dai"

Sai kawai na samu bakina da Fadin"Ku yi hakuri ba.."

Muryan Dr.Lawal ta katseni a Fusace yana fadin"Sorry for ur self..Akan ya'yana zan iya shari'a da koma waye..Daga tazo gidanki sai ki ci mata Mutumci..?ke ba domin Ishaq ba kin isa ki ga Zuzu a inda kike..?ai kalan zaren ba kalan yadin ba ne..Ba domin ina jin kunyar shi da iyayansa ba da sai kin gayama aya zakinta akan kukan da kika sa yata tayi kin san wacece ita..?ko ni bana sakata kuka Koda yaushe ina Tattalin Dariyan ya'yana ne ba Zuzu ba ko Zeey da kuka Hada miji kika kara yarda kallon Banza ma ya had'aku sai nayi maganinki sai na saka an batar dake da Dangin ki gabad'aya"

Yafad'a cikin Kaushin murya Hajiya Halima kunya ya kamata ta kasa mgana ta Dafe kai Zainab ce tace"Is ok Daddy. "

A fusace yace"No zeey kinsan ba na Had'a ku da komai a nan duniyan ko..?

Ko mommy ku ta sa ku kuka ina jin Dalili ballatana wata shara chan"

Hawaye suka wankemin Fuska ni ce shara..?ina jin Zainab din na fadin"I know Daddy..Forgive her bata sani ba ne zuzu plz ki bar kuka kada kanki ya fara ciwo..Gobe zamu koma Abuja is ok  kin ji..?

Kai ta d'aga mata ta koma ta lafe jikin Baban nasu yana share mata hawaye yana fadin"Am sorry Angel..am sorry"

Mama tayi kayci kafin tace"Ai daka Dauki matakin da kayi niyya Alhaji da sai tafi gane matsayinta"

Hajiya Halima tace"Hajiya komai ya wuce insha Allahu"

Ni ko ina zaune jikina ya gama mutuwa hawaye suna zubomin na saka gefen Hijabina na share Yaya Ishaq yace"Ki dago ki bata Hakuri tunda ita kika yi ma laifi"

Na kasa Dagowa sai ya dakamin Tsawa haka na Dago fuskata Shabe Shabe da Hawaye cikin yanayin mganata nace"Ki..yi..hakuri.."

Juyawa yayi yana fadin"Ta baki hakuri am sorry Zuzu.."

Kai ta gyada ta na kara kwanciya jikin Baban nata,Mama ta kalleni tana fadin"Sai ki tafi ki bamu waje mara mutumci"

Na tashi da Sauri na shige Daki na,na fada kan gado ina sakin kuka na bansan Lokacin da suka tafi ba sannan ni kaina bansan adadin Lokacin da na Dauka ina kuka ba kaina ya fara ciwo,ko sallar daren da na Saba a daddafe nayi saboda Jiri naji yana Dibana da Safe dakyar na iya tashi na shirya yara suka tafi makaranta kuma ahakan nayi musu abun karyawa na bar musu a kitchen na koma Dakina nasha panadol na kwanta ina jin kamar zazzabi zai kamani.

Ban san tafiyar su ba Domin Wanda ya ijiyeni bai min sallama ba Ballatana Dangin da sukace zasu batar dani,ni da Dangina Saboda an saka yar gata kuka,fitowa kawai nayi naga gidan wayam,sannan na Fahimci Daga ni sai halina acikin gida Zuwa yammah jikina ya Rikice jiri da Ciwon kai nasan jinina ne ya hau Allah gafurin Rahimun a ranar sai ga Hafsaatu ta zo Allah ya aiko ta Domin ta taimakeni ta iskeni kwance ba Lafiya ita ta taimakamin tayi ma yara Girki ta kula da su.

Ina da Sauran mganina na Hawan jini shi na sha bayan naci abinci,Gari na wayewa kamar waraka daga Allah sai naji Sauki,Naji dadin zuwan Hafsatu Goggo ta aiko ta ta dubami tazomin da su Kuka,kubewa,tsaki,garin kunu da wake,har da kudi in ji Goggo na karba araina ina roko ma Goggo Gida a gidan Aljannah Saboda yadda ta rike zumunci bata yada shi ba.

Kwana Biyu Hafsatu tamin ta koma saboda makaranta sannan tana kunshi yanzu sosai take samun masu zuwa nayi mata murna saboda sana'a itace mace a wannan zamanin da muke ciki.


*Littafin KANA NAKA book2and3,paid book ne biya kudin karatun ki akan Naira N500 Regular posting sau d'aya a rana.*

*Ko kuma tsarin VIP 1000 Posting sau biyu a rana akan wannan acct din 0552179550 Jamila Umar Gt bank,sai a turo shaidar biya ta wannan lambar 09069067488 Wannan karon babu tsarin kati,kowani tsari zaka yi ka turo ta POS,Mutanen mu na Niger kuma zaku tuntubi Kausar Aglan Nissa ta wannan lambar +22796562223*




*Janafty**KANA NAKA..!*


*Wattpad:JamilaUmar315*

*Mallakar:Janafty*

*Arewabook:Jamilaumarjanafty*


MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT 08066726866


Ni MMN MUJAHID Ina da kayn gyara kala kala na kasa da sama Ina Saida supplement da kayan mata kala kala cikin sauki Mai kama da kyauta


Hjy ta ki ajiye kunya kifitu kiyi bayani matsala ki abaki ABINDA yaddace Dake


Ina matan da ke FAMA da bushewa gaba


Ina maccen da take a bushe kamas ba niima miji sai yasa yawun sa ku BASILIN 😳


Ina matar da kishiya ta tayi mata zarra ga miji ke rasa Ina matsala take


Ina wadda mijinta kamar kurma baya nuna ya gamsu Dake Dan ku ayi ku abari duk dai suke dashi


Shin ke ku y'ar kuwa ga mijin ki baya Yi da sanbatu in kinji ana Fadi sai kece karya ce 


Nazo muku da hadin Zuma wadda duk zata magance way'anga matsalolin cikin ikon Allah wanna Zuma ta samu yabo ga duban mutane Sha yanzu magani yanzu ce Banda haufi akanta wanna Zuma tana ta yadda sha'awa Kai tsaye ruba babba 2500 karama 700👌👌 


MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT MUNA SAKWATO DA KEBBI INA AIKAWA KU INA 08066726866


IN BAKI SHIRYA BA KIBARI HAR KI TASHI SAYE 😀


       *🅿️15*


Haka nan na cigaba da gungura rayuwata cikin dad'i da akasasin na cire damuwar komai a raina na riga nasan Yaya Ishaq ya zabi zainab daman a kaina sannan yanzu da abubuwa su kara kamari sai na Fahimci bayan ni ma ya zabi Sabon Iyalansa da Zainab ta fara tara mai fiye da ya'yansa sai na saka araina ni kadai suke da bayan ni ba su da kowa

Nasan zafin maraici nasan zafin rayuwa a gidan da ba gidan ku ba,bana fatan daya daga cikin ya'yana su fuskanci abunda na Fuskanta shiyasa duk kai da kawo na da Hakurina saboda su ne.

Ko da yaushe in na yi sallah ina D'aga hannuna sama nayi ma Allah kirari da sunanayensa matsarkaka sannan na yi masa magiya da naci domin ya sama min mafita kan rayuwar da nake ciki nasan bani na Tsara ma kaina ba Allah ya tsaramin kuma yaso ya ganni a haka to bazan yi masa butulci ba, sai dai zan rokesa ya sama min mafita. cikin irin kyakyawan mafitar da yake sama ma Salihai daga cikin bayinsa.

Sannan a koda yaushe addu'ata akan ya'yana shine Allah ya shiryamin su Allah ya jibanci lamarin su Allah ya sa su kaunaci junansu kada Allah ya Dora musu hassada da son kai Allah yasa su daukaka su haskaka acikin al'umma.

  Na cire Ishaq da abunda ya shafeshi acikin raina,Domin ina da tabbacin an kawo gabar daga ni har shi mun Fahimci wani irin zama muke gudanarwa ko da yake ni ai na Dad'e da sanin irin yanayin zamantakewa ta dashi shine a wajensa yake kallon duk abubuwan da yake yi min ahakan ma kamar yana min alfarma ne.

Tunda suka koma ban kara jinsa ba,Nima ban damu ba tunda ko ina da wayar baya nema na sai na maida kaina wajen kula da ya'yana,Ba na ganin kowa sai jamal shima sai in ya shigo anguwar tamu ne,Badariya kuma Mama ke hanata zuwa tunda basu koma makaranta ba sai na Dad'e ban ganta ba.

Ko cefanen mu ya kare sai dai nayi ta Dubaru na, saboda yara in ni nayi hakurin yunwa su baza su iya ba,akwai Ranar da sai mu yini bamu ci ba Daga karshe Garin kunun Ahmad nake dama musu su sha su kwanta,saboda bani da inda zan fita in nema koma naje tona ma kaina asiri zan yi sannan daga karshe ace karya nake yi,ana ganina a katon gida sannan an san mijina babban ma'aikaci ne ba kowa ba ne zai san yanayin da yawan mata suke Fuskanta acikin katon gida ba,da yawan mu ai kurace lullube da fatar akuya.

Ko sa'adatu da muke zumunci da ita sosai ban taba bud'e baki na fad'a mata matsalata ba sai dai yau da gobe bata bar komai ta fara Fahimtar gidan ne kawai da mijin ammh babu wani Sauran jin dadin da nake ciki da ni da ya'ya na har ta kai yara su ka daina zuwa da Abinci makaranta Saboda komai ya kare sai dai ruwa,Tsakin da Goggo ta aiko min dashi da garin Danwake duk ya kare a kitchen di'na ko kwaran Shinkafa bani da shi ban kuma san inda zan je na mema ba.

Mun yi sati cikin wannan yanayin Duka Dubaruna sun kare nima na kasa,Ranar wata laraba ko makaranta basu je ba,Basu ci abinci jiya da Daddare ba haka da Safe Anum da Musty suna kwance suna fama da ciwon ciki kuma nasan na yunwa ne Ahmad kuwa ya lafe ajikina sauran garin kunu ne na dama mai kadan ya sha shima ba domin ya ishesa ba,Amir kuma saboda ya na babba yasa bai nuna gazawarsa ba,Ammh shi kan shi yana jin yunwa ni kaina Dauriyan kawai nake yi ammh na fara Sarewa.

Muna zube afalo kamar kayan wanki kukan zucci nake yi na kasa na Sarari na Daga hannuwana sama nace"Ya Allah ga baiwar ka nan Fa'iza ka fini sanin Halin da nake ciki..Allah kayi gaggawan kawo min mafita d'aya daga cikin mafitar ka ya Allah"

Ban gama sauke Hannuwa na ba naji Sallama ina d'ago kaina naga Sa'adatu ashe Haruna ne yace ta shigo ta duba yau su Amir basu je makaranta ba Allah Sarki bawan Allah wajen wata biyar Yaya Ishaq bai biyasa kudinsa ba ammh bai taba gazawa daga kai su makaranta ba har mgana nayi mai ko zai bari ne yace min bakomai yiwa kai ne.

Ko ban fad'a mata ba ganin mu cikin wannan yanayin ya bata tsoro ta kalleni cikin Tausayawa tana fadin"Maman Amir Allah yasa dai lafiya na gan ku duk a kwance sannan Mallam yace yau su Amir basu je makaranta ba shiyasa yace na shigo na duba ko kuna lafiya?

Ina kokarin mikewa Ahmad ya lafeni na jingina da kujera ina fadin"Lafiya lau Sa'adatu yau din dai basu samu zuwa ba ne"

Shuru tayi kafin ta kalli su Anum lokaci d'aya tana fadin"Anum ko ba lafiya ne yau ban ji Surutun ki ba..?

Kawai sai yarinyar nan ta saka kuka cikin kukan take fadin"Yunwa muke ji tun jiya bamu ci abinci ba"

Musty ma sai ya fara kuka wai shima Yunwa Ahmad na jin su shima ya saka Rigima na saki baki kawai ina kallonsu na kasa mgana ta Dago tana kallo na kafin tace"Haba Maman Amir sai ki bar yara da yunwa in suka samu wata matsalar Dalilin haka fa..?

Sai na kasa mgana Hawaye suka cika kwarmin idona cikin wani yanayi nace"To ya zan yi Sa'adatu..?

Bani da wata mafita sai wacce ubangiji ya kawo min kawai"

Cikin mamaki tace"In shi babansu baya gari ba ga gidan iyayansa ba,bai kamata suna garin nan kuna zama cikin wannan halin ba ai yunwa bala'i ce musamman ma ga yaran nan"

Mirmishin takaici nayi mata ban kara mgana ba da Sauri ta mike ta fita ba jimawa sai ga shi ta Dawo da kuni da yawa abotiki da Soyayyan Dankalin Hausa ta Diremin tana fadin"In ke kin Daure ai su baza su iya daurewa ba saboda yara ne..Zaman taren kenan da ko Amir kika aikomin da nasan abunda zan yi"

Ni dai ban ce komai ba sai godiya nake yi mata nan da nan na tashi na shiga Kitchen na Dauko Kofuna na zo na Zuzzuba musu na saka ma kowa Dankalin,ita tafiya tayi ta barmu bayan ta kawo mana,Sai gashi mun ta  da shi duka Lalle gaskiyan almajiri da yace yunwa bata da Hankali na yarda sai da muka koshi na samu karfin jiki,Amir shi ya taimaka min ya gyara Dakin su ya kwashe kayan da suka zubar a kasa ni kuma na gyara Sauran d'akunan nayi ma Anum da Musty da Ahmad wanka Amir ma na cudamai baya sai bayan sun shirya naje nayi wanke wanke tun jiya ban samu yi ba nima kaina ba ni da karfin jiki.

Zuwa chan sai ga Sa'adatu da Shinkafa yar Hausa takai tiya Hud'u da Garin tuwo da Tsaki,Da kayan miya har da su maggi da mangyada,Na rasa da bakin da zan yi mata godiya na share kwallar data zubomin Lokaci daya ina fadin" Nagode..Nagode yadda kika ji kaina da ni da ya'yana ke ma Allah ya jikan ki"

Ta amsa min da Ameen Ameen ta jima muna hira sama sama da ita kafin ta tafi wannan kayan abinci su suka taimakemu suka fitar damu daga cikim Halin da muka so fadawa na rashin abinci Maman da ya bar ma sallahun komai namu bata Damu ba ko zamu mutu mun dad'e bamu mutu ba.

Abun da ke bani mamaki in ni bata kaunata ya'yan da har da D'anta aka bada gudummuwar fitowarsu duniya bazata tuna da su ba..?ammh bata Damu ina da yakinin ko rasa su sukayi sai nafi kowa asara ita d'anta yana da matar so sannan da yaron so bazata damu domin yunwa ta illatamu ba.

Ni kuma tundaga Lokacin nayi alkwarin ko zamu mutu bazan kara tambayanta wani abu daya Danganceni ni da ya'yana ba in suka Sauke Nauyin dake kansu ruwan su in basu sauke ba bazan matsa musu ba, duk wanda yayi nagari don kansa sannan Hakki ne ranar gobe kiyama sai Allah ya tambayesu domin ai ya'ya abun kiyo ne ga wanda aka bamawa,kuma za'a tambayi kowa yadda ya kiwata nashi.

Haka na dinga ririta kayan abincin nan Saboda in suka kare mu ne a ruwa bamu  kuma da wata mafita sai dai su kofofin ubangiji ba su da iyaka in ya kulle maka wata kofar kafin wani Lokaci sai ya sake bude maka wata Sabuwar kofar.

Dama bana ganin kowa kuma hakan bai dameni ba jamal ma ya jima bai leko ba ashe sun janye yajin aiki an koma makarantu,Nima ban sani ba ni ba Tibi ba Radio ba, ina nan dai Dim d'in sai abunda akazo aka fad'amin yaran ma tun suna damuwa da kallon har ya fita ransu na rika na cusa musu karatu acikin ransu shiyasa lokacin wasan su kad'an ne lokutan karatun su yafi yawa.

Badariya ce da tazo ita da abokiyar karatunta Raliya sun taba zuwa sau biyu da ita,ita take fadamin sun koma makaranta cikin Satin nan sannan  Jamal kuma Yamai sukaje shi da Mama sai shekaranjiya suka dawo jiya kuma ya koma makaranta,Sun iske na yi Tuwom masara miyar kubewa Bushasshiya Da yaji caryfish,sai tayi Dad'i sosai Badariya tace na zubo musu na kawo musu suka zauna akasan Cafet ita da kawarta ta suna ci suna Fira ni kuma ina gefen su Ahmad na jikina ya lafe.

Kawar Badariyan ne ta Dago tana kallo na kafin tace"Gaskiya Anty Fa'iza kin iya girki sosai kiji kamar ka tsinke Hannu"

Mirmishi nayi kawai ban yi mgana ba Badariya tace"ai in dai bangaran girki ne in kika zo wajen Anty Fa'iza ki yi Salute kawai Raly."

Raliya tace"Naga alama irin su ne watarana sai ki gansu da Babban Wajen cin abinci"

Badariya tace"Allah ya amsa bakin ki ai zata iya ta iya girke girken kala kala na zamani da na gargajiya"

Raliya tace"Nasani ai wanchan zuwan Danwake mukaci da salad haka na koma gida ina ma su Hajiyarmu Zencen suka yi tamin Dariya suna fadin Duk Santi ne"

Badariya ta kwashe da dariya kafin tace"basu karya ba santin ne"

Atare suka yi dariya kafin su cigaba da cin abincin su sai chan Raliyan tace"Badar wai ina matar bro din ki da Lokacin ina Kaduna kikace an yi bikin?ko ba anan gidan take zaune ba..?

Badariya tace"Tana Abuja tare da Yaya Ishaq ai yar chan ce ya aura har ta Haihu ma namiji Lawal suna kiransa Farhan"

Kai ta jinjina kafin tace Allah ya raya sai da suka gama cin abincin Badariya ta kwaahe komai ta kai kichen,tazo ta sharemin Falon ina ta barshi bata ji ni ba,Wayoyin su suka dauka suna ta Latsawa suna Hira jefi jefi ni kuma ganin Ahmad yayi barci na mike da niyyar naje na shimfidar da shi sai naji Raliya na fadin"Ke Badar na  manta ban fada miki ba, kinsan Hajiyar mu tana shiga kungiyoyin tallafa ma mata da marayu ko..?

Badariya ta daga mata kai batare da tayi mgana ba ita kuma sai ta cigaba da fadin"To akwai wata kungiyar Womens Charity Faundation kungiyace ta manyan mata da suke tallafama mata da marayu domin su Dogara da kansu suna koyar da Training din sana'o'i da Dadama sannan in sun gama,suna ware kamar Mutane ashirin Hazikan ciki su tallafa musu da jari kyauta"

Kasa kunnina nayi tun da naji mganar tallafama mata sai na koma na zauna inaji Badariya na fadin"Ni kuma meyasa duk kike fadamin wannan..?

Raliya tace"Banza baki cin Ribam zencen..duk shekara suna zaban State din mu na arewa su zo su koyar da sana'o'in da kuma bada tallafin wannan shekarar katsinan mu ne har anbuga Form din Hajiyarmu guda Goma aka kawo mata shine nace bari nayi miki mgana ko zaki yi sai mu cike mu yi tare Allah Foudation di'n suna koyar da abubuwa masu kyau matuka komai da kika sani ko banza muma zamu karu"

Badariya tace"Da karatun zamu ji ko da Koyan sana'a?

Raliya tayi dariya kafin tace"Haka Hajiya tace da nace ta bani Form guda Biyu ni dake sai tace mu ji da karatun ma tukunnah yadda muke da son jikin nan ba abunda zamu iya koya"

Badariya tace"Allah ya saka ma Hajiya da Alheri"

Suka yi dariya a tare ban shirya ba kawai naji bakina ya furta"Zan yi..Badariya zan yi dom Allah"

Gabadaya suka Dago suna kallona Badariya ta kalli Raliya itama ta kalleta suka kuma dawo da kallon su kaina cikin Sauri nace"In ba damuwa ni ina so zan yi"

Raliya tace"Da gaske Anty Fa'iza..?

Ciki  jin dadi kamar an ce ma an Daukeni nace"In sha Allahu.

Badariya tace"To ke kin ji Raly maza ki samo ma Matar bro di'na Form dim ta cike kuma ki fad'ama Hajiya"

Raliya tace"In sha Allahu kuwa ai tashi zaki yi muje gidan tare ki mata bayani mu karb'o tare kada tace shiririta na ne"

Da Sauri ko Badariya ta mike tana Fadin"Yauwa muje..Anty Fa"iza bari muje gidan su Raly din na yi mgana da Hajiya insha Allahu zaki samu"

Kai na gyada musu ina ma Raliya godiya tace"Bakomai Anty Fa"iza ni dai don Allah ki dauki bangaran girke girke yadda zaki kara zama top a harkan sai mu bud'e gidan abinci watarana"

Sai ta bani dariya ammh a raina na amsa da Ameen haka suka fita suia barni kamar an sakani a aljannah haka kurum nake jin farinciki acikin raina na fara Hango mafitar da na Dade ina rokon Allah akanta,sai dai jikina yayi sanyi ganin har kwana biyu Badariya bata dawo ba ballatana naji yadda suka yi,Sai da Satin ya shige wani ya shigo sannan tazo da Form din tana fadin ba kowa a gida ne shiyasa najita shuru cikin mamaki nace"Ina mama taje..?

Badariya tace"Abuja suka je ita da Anty Binta"

Na kalleta cikin wani yanayi kafin nace"Me ya faru..?

Badariya ta tabe baki kafin tace"Farhan ne ba lafiya mura yake ta fama dashi har ta na hanashi Numfashi sai da aka kwantar dashi a asibiti Ya Ishaq duk ya Rud'e ya Rudar da su Mama sai da sukaje suka gansa Hankalinsu ya kwanta"

Cikin jimami nace"Wayyo ya jikin nasa..?

Cikin basar da zencen tace"Yaji sauki sun koma gida ammh naji su mama na fadin baban zainab din yace zasu fita da shi kasar waje a kara Duba Lafiyarsa Nimonia ce ke damunsa"

Na nuna jimami na sosai ina ta addu'an Allah ya basa lafiya Badariya ta fito da Jakarta ta Dauko Farar Takarda Doguwa tana fadin"Kin ji Anty Fa'iza matso mu cike wannan Form"

Cikin Farinciki nace"ashe kin karbo min?

Badariya tace"Eh ai tun ranar mukaje nayi ma Hajiya bayani bata da matsala tana jin ma matar Yayana ce tace bakomai basai mun biya kudin Form d'in  ba tace ki cike a maida mata in sha Allahu zata sanar in Lokacin Traning din yayi ammh akwai pasport guda uku kina da shi..?

Na kalleta saboda ban gane me take nufi ba da Sauri tace"Hoto karami nake mgana wanda za'a lika acikin Form din sauran kuma za'a kai musu"

Ta fada tana nuna min inda za'a saka Hoton sai na gane nace mata bani da shi sai tace"Bakomai in mun gama zan Dauke ki Hoto a wayata in na fita sai na Biya shagon Hoto a Wanke min a maida shi karami yau nake so naje na kai ma Hajiyar, Mama ma karya nayi mata da zan yi subbmitting wani aiki a makaranta"

Kusa da ita na matsa ta sauka kasa saboda yadda zataji dadin Rubutu ta dago tana fadin"da Farko a jikin Form d'in sunanki ake tambaya"

Kai tsaye nace"Fa'iza Sidi karofi"

Ina kallo ta Rubuta sannan tace shekaru na gayamata sai kuma ina da aure..?ta saka eh ya'yana na wa..?

Ta saka,sannan yaushe Mahaifina ya rasu na ce ta saka shekaru goma sha da Rasuwarsa ta saka,sai ina da Mahaifiya..? 

Nace ta saka eh,Sai ina da Sana'a ?in akwai wata sana'a nake yi acikin gida? nace ta saka Babu,Sannan matakin karatuna nace itama ta sani ko Takardan gama primary ai ban da ita Saboda ban gama ba sai Badariya ta saka matakin karatu na addini Saukakkiya a Qur'ani da Sauran Littafai.

Na kalleta cikin wani yanayi kafin nace"Kada su k'i daukata Badariya kila sun fi son masu takardan ko Sakandiri ne ko Hafsatu zan bar mawa..?

Badariya tace"Zasu Dauke ki in sha Allahu ai ba da Takarda zasu amfani ba, da Kwarewa ce ke kuma ai bana jin ki ta wannan bangaran"

Ni dai duk sai naji jikina yayi sanyi ta cigaba da karantomin ko'ina tana Fassaramim yadda zan gane tace ance in da wata matsala ta fanni hallita ko wani ciwo..?

Nace ta saka ina da matsalan ji,ta saka Hearing problem,Sai adireshin gida nace ta saka na gidan yayanta 

Daga karshe sai jerin abubuwan da zasu koyar akwai girken girken zamani da na gargajiya nace ta cike min shi saboda na kara kwarewa, sai Gyaran jiki dilka da Halawa nace shima ta Cikemin,sai kuma koyan yadda ake had'a lemuka kala kala nace shima ta cikemin akwai koyar da Kunshi Fulawa,koyar da manshafawa da su sabulan wanka da na kamahi sai koyar da su yaji kori da kayan kamshin Girki sai koyar da Turaran kamshi na Itace da kwallacha 

suma nace ta cikemin duk zan koya Badariya na Dariya tace"Anty Fa"iza duk ke kad'ai an ya zaki iya..?.

Ina da yakini acikin raina nace"In sha Allahu ai basu da wahalan dauk'a zan iya da amincewar Allah"

Ta amsa min da in Allah ya yarda sannan daga karshe akace in mutum nason a bashi tallafi yace eh ta sakamin eh sannan da kuma abunda zakayi da tallafin in an baka

Na kalli Badariya ina fadin"Kice ina son a bani tallafi nan saboda na kama sana'a daga cikin sana'o'in da suka koyar damu..Sannan saboda na rike kaina na kuma tallafama rayuwar ya'yana saboda inganta goben su watarana"

Haka kuma ta rubuta sai lambar waya nace ta saka min nata tunda ni bani da waya sai ko ta saka lambar wayarta.

Daga karshen karshen sai saka hannuna ta bani na jagwalgwala hakanan,Kafin ta tafi sai da ta D'auki Hotona  a wayarta bayan na saka Hijabi tace zataje a fito mata dashi a gyara muka yi sallama zuciyata ta cika da murna ammh ban daina saka Allah cikin lamarina ba adaran nayi salla sannan nayi addu'an  Allah yasa mafitan nan ta zame min mafitan alheri a rayuwata gabad'aya.

Ni dai ina ta addu'a ko da naji shuru ban damu ba daman nace in mafitan ta alheri ne Allah ya tabbatar min in kuma ba alheri aciki Allah ya kawo min wata mafitar ta alheri Ameen.

Kafin kayan abincin da Sa'adatu ta kawo mana ya kare ta kawo min Dankali hausa da yawa tace itama daga gida aka aiko mata dashi,Babansu ne ya noma na karb'a na saka albarka shi nakan soya ma yara da Safe su tafi makaranta,Wata rana ma har da rana ina soya mana muci mu sha ruwa,kuma dayake na koyama yarana cin komai duk abunda suka samu zasu ci basa zabar abinci shiyasa sai rayuwar tazo min da Sauki.

An yi wata da cike Form din da mukayi ni da Badariya tazo sau d'aya mukayi mgana tace Raliya tace an Tura Tarkadun namu chan kaduna inda Babbar Jibiyar kungiyar take da su zabi wad'anda zasu dauka za'a turo ma kowa ta sakon waya da lambar da ya saka Badariya ta tabbatar min da Hajiyar su Raliya tace ba matsala sai na saka raina asalama araina nace bakin Da Allah ya tsaga bazai taba hanasa abinci ba.

Ana haka kwatsam sai ga Ya Ishaq ya Dawo ranar wata asabar da azahar Lokacin bana gida na shiga wajen sa'adatu  muna hira to yara in sun tafi makaranta sai ni kadai kamar mayya na da zauna tunani ya kasheni sai nake shiga muna hira tana Debemin kewa rashin dangina akusa dani.

Get din a bude na barsa saboda ban yi nisa ba yagaji da Hon ya fita ya Bude ma kansa ya shigar da Motarsa sai da ya shiga gidan ya tabbatar da ba na gidan mamaki ya kamasa ya D'aga waya ya Kira Mama ko nazo Mama tace tafi wata biyu ban zo inda take ba.

Ransa ya baci nan da nan ya fara Tunanin haka nake fita ina barin masa gida a bude ina tafiyata gantalin da baisan yaushe na iya ba,Ni kuma ban san ya dawo ba sai biyu da rabi na Dawo gida domin yi ma yara girki,sannan nazo da Guzurin Dambun Dankalin da Sa'adatu ta zubamin mafarin zamana ma yau saboda na koya ne ina so nima watarana nayi lokacin da na shigo Haraban gidan naga Motarsa ban ji tsoro ko fargaba ba Allah na Tuba in da sabo ai yaci na saba da Tozarcin sa a gareni.

Kaina Tsaye na shiga cikin gida kamar daman yana jira na ne sai yau ya gwada kiran wayata a kashe duk tsawon Lokacin da ta lalace bai sani ba.

Yana ta Safa da marwa a falon ya kasa zama na shigo bayana goye da Ahmad Hannuna Dauke da kwanon Silba da Sa'adatu ta zubomin dambun aciki.

1do hudu muka had'a dashi Sanda na shigo yana bi na da wani kallo na raini kamar yadda ya saba ni kuwa sai na Dauke kaina ina fadin"Sannu da zuwa.."

Nafada ina nufar Hanyar Kitchen nasan yayi mamakin yadda nayi mai shiyasa ko taku uku ban yi ba yasha gabana cikin bacin rai yana fadin"Ni kika gani kika dauke kai kamar kin ga Dan'iska Fa"iza?

A gajiye na kallesa cikin yanayina nace"Nayi maka sannu da zuwa..ina so na shiga kitchen na sauke abun hanuna ne"

Kallo hannuna nawa ya shiga yi Lokaci daya yana fadin"Miye wannan kuma..?

Sai na Bude masa ina fadin"Dambun Dankalin Hausa ne na shiga ta koyamin ne saboda ina so nima nayi ma yara"

Yamutsa fuska yake yi kamar yaga kashi kafin yace"Wannan bakin abun ne zaki yi ma yarana su ci..?Shiyasa kika bar min gida a bude kika fita yawonki me na sha fada miki..?

Ban ce ban amince ki rika fita ko na  nan da chan ba indai ba gidan Mama ba..?shine kike so ki nuna min kin isa har kina shigowa kina ganina kika Dauke kai kamar kin ga sa'an ki ko..?

Na kallesa da Idanuwana da suka yi ciki ciki ban iya rashin kunya ba Saboda ba Halina ba ne ammh dai naji Tsoro nan nasa da nake ji a baya ya gushe araina na kasa ce mai komai kawai sai na rabasa na wuce kitchen na sauke kayan hannuna a zafafe ya biyo ni yana fadin"Fa'iza ina miki mgana kina wucewa yaushe kika raina ni haka ban sani ba..?

Ko tankasa ban yi na sauke kwanon Hannuna ya shigo Kitchen din yana Fadin"Daga gidan uban wa kike..?rokon abinci kika fara na salon zubar min.."

  Bai karisa mganarsa ba yayi shuru ganin Dankalin hausa zube a kitchen din sannan na bude karamar kular dake saman wajen wanda na soya ma su da Safe ne na rage ma Ahmad in ya tashi daga barci yaci,na dauko na barsa akitchen din yana Dube dube cike da mamaki..

Afalo na zauna akasa na kwanto Ahmad daga bayana da naji motsin tashin sa kamar walkiya sai ga shi a gabana yana fadin"Fa'iza wannan dankalin fa..?sannan naga store ba komai wannan watan mama bata aiko da kayan abincin ku ba ne..?

Ahmad na kallonsa ammh sai ya lafe ajikina ba irin zumudin daya saba yi mai a baya ni kuma ban kallesa ba nace"Wannan dankalin shi kad'ai garemu shima daga gidan haruna aka bani kyautarsa kayan abinci kuma ba'a kawo ba"

Daga haka na tsuke bakina daga alamu jikinsa yayi sanyi sai ya fara Fadan meyasa ban kirasa na gayamai ba cikin gajiya da korafinsa nace"A ina zan ganka ballatana na fad'a maka..?

Kai tsaye yace"Ina wayarki fa ?ko bata da amfani ne da bazaki kirani ba..?

Ina bama Ahmad Dankali nace"Bani da waya ta lalace tuntuni"

Sai kuma ya kasa mgana,Daganan ya shige bangaransa bansan ko ya kiran Maman ne me tace mai oho yadai fita sai chan kuma ga shi da Cefanen kayan abinci masu yawa wani Lokacin Ya Ishaq bai da matsala ta bangaran hakkin iyalansa da ya'yansa sai dai Mama itace tafi matssala ta wannan bangaran

Daga karshe yace na kwashe Dankalin nan na fitar mai dashi nace tab wlh bazan kwashe ba,Kafin yazo ai shine ya Rufamana asiri sai ya kasa mgana nasan yana ta mamakin yadda wannan karon nake iya maida masa mganarsa kai tsaye ni ko gani nayi tunda alfarma yake min nima sai na fara mai alfarma saboda ya'yan da suka hadamu tsakanina da shi ba Domin zumunci da baisan Darajansa ba.

Yaran ma da suka dawo ko da suka gansa ba su yi wani D'oki  kamar baya ba, shine daya lura da haka ya rika jansu ajiki washegari kuma yace bazasu je hadda ba ya daukesu suka tafi yawo ya siyo musu kayan kwalama da duk abunda suke so,Daganan ya sauke su gidan Mama sai Dare suka dawo ashe sallama yazo yi ma su mama zasu tafi india inda Mahaifin zainab ya dauki nauyin su Saboda aduba lafiyar Farhan sai a daran da suka dawo ya fadamin ban san Dalili ba sai naji ban damu ba nayi masa fatan isa lafiya da kuma samun abunda akaje nema.

Washegari Litini ya koma ban ma sani ba ashe ya biya Haruna kudadensa har da na wata biyu anan gaba yana ta basa Hakuri,Harunan ya ke shaidamin washegarin talata da na rako su Amir kofar gida araina sai naji sanyi,in zan fadi gaskiya Yaya Ishaq baya so na ammh kuma yana son ya'yansa kuma bai hadasu da komai ba, sai dai sabon iyalansa sun Dauke masa hankali har akan yara sannan da karin muguntar Mama acikin lamarin tunda ita ake barin ma komai.

Ina nan bansan abunda ke faruwa ba Ba mai nema na kuma nima bani da Hanyar neman kowa ashe Tamadina bata da lafiya ta fito daga bandaki ta zame ta fad'i shikenan jikinta yayi nauyi tun tana gida har an kaita asibitin general na bakin asibiti,Har Yaya Asiya dake kano ta sani tazo ammh ni da nake kusa ban sani ba Goggo ganin ba'a samu inda zan ji ba sai ta Kira Mama a waya tace ta fadamin Lokacin Hafsatu suna Jarabawa,bata samun zama shiyasa ma Goggon tace bari ta kira Maman,Tunda Har Yaya  mariya sai da tace tazo ta fad'amin tace ma Goggo sai dai tayi Hakuri bazata iya zuwa ba jin haka yasa Goggo bata matsa mata ba.

Ita kuma Mama da aka fad'amata washegari yamai ta tafi, diyar Kanwarta ta haihu,kuma abun bai Dameta ba shiyasa sai ta sha'afa.

Sai da jikin Tamadina ya kara rikicewa Goggo ta tada Ya Isa tace yazo ya fad'amin nazo in muna da Rabon ganawa da tamadina tana asibiti bata da lafiya.


*Littafin KANA NAKA book2,3.paid book ne biya kudin karatun ki akan Naira N500 Regular posting sau d'aya a rana.*

*Ko kuma tsarin VIP 1000 Posting sau biyu a rana akan wannan acct din 0552179550 Jamila Umar Gt bank,sai a turo shaidar biya ta wannan lambar 09069067488 Wannan karon babu tsarin kati,kowani tsari zaka yi ka turo ta POS,Mutanen mu na Niger kuma zaku tuntubi Kausar Aglan Nissa ta wannan lambar +22796562223*





*Janafty**KANA NAKA..!*


*Wattpad:JamilaUmar315*

*Mallakar:Janafty*

*Arewabook:Jamilaumarjanafty*


*TASTED & TRUSTED*

*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATUN SAIWOWIN MUTANAN CHADI DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZAR AMARE DA WADDA TAKE SON GYARA KANTA*.

*AN GWADA ANGA INGANCINSA SHIYASA NA KE TALLATA MUKU DA K'ARFIN GUIWATA*.

*ABIN BIRGEWA DA WANNAN SAIWAR ZAKI YI AMFANI DA ITA SAMA DA SAU DAYA.*

*AKWAI FULL PACKAGE, AKWAI RABI, TA YADDA KOWA ZAI IYA SIYA*.

*SANNAN BABU BAURI NA TASHIN HANKALI.*

*DA KANKI ZAKI DAFA ABAR KI, KOMAI ANA SAKA WA A CIKI*.

*SHIN KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR, KO KUWA KE CE KIKE SON GYARA KANKI?*

*TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU*

*08032773332*

*DOMIN KARIN BAYANI, SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*..


          *🅿️16*


Na gigice tare da Dimaucewa lokacin da Yaya Isa yake shaidamin Tamadina bata da lafiya ta kwana uku a asibiti bayan tayi sati a gida ba yadda take.

Sai naji na rasa hankalina na wani lokaci, na koma nayi yaraf saman d'aya daga cikin tsofaffin kujerun falona kamar wata kayan wanki.

Hawaye nan da nan suka fara sintiri a saman fuskana kamar an bud'e famfo sai yau na kara tabbatar da cewa Mama bata kauna ta kuma har abada baza ta taba so na ba,Uwa ai ta wuce wasa ace a fad'amata rashin lafiya ammh ta gagara aiko ko Badariya ta shaidamin sai da aka gaji da jirana akaji shuru Goggo ta tado mutum tun daga karofi akazo aka fad'amin, kawai tuna hakan da nayi sai naji raunina ya karu na Fashe da kuka Yaya Isa ya zauna gefena yana fadin"Ki daina kuka Fa'iza jikin da sauki sosai.."

Na dago idanuwana sharkaf da kuka ina fadin"Wa ke zama da ita..?

Kai tsaye yace"Mariya ce..Asiya tazo ta kwana biyu ta koma to bata ma nan aka kai ta asibitin ammh naji Goggo tana fad'amin itama gobe tana Hanya"

Jin haka sai na kara saka kuka ina fadin"Allah ya tada kafad'un ki Tamadina Allah ya baki lafiya"

Ya amsa min da Ameen yana fadin"Ki tashi ki shirya sai na sauke ki a asibitin"

Da sauri na mike jikina yana faman bari har na shiga d'aki na Sunkunci Ahmad dake barci na goya na zura Hijabi sai kamar an tuna min na tuna da su Amir sai jikina yayi sanyi na fito ina Raba ido na neman mafita yanzu in na tafi ina su Amir zasu zauna..?

Ko gidan su Sa'adatu zan ce su zauna kafin na dawo..?Sai dai akwai D'awainiya acikin lamarin yara ba d'aya ba,ba kuma biyu ba har guda Hudu ganin yadda jikina ya kara Sanyi ne yasa yace min"Muje ko..?

Ya fada Lokaci daya yana mikewa sai yaga kuma ban biyosa ba sai ya juyo yana kallona kafin yayi mgana na taresa da fadin"Ya Isa yara na..Su Amir bansan inda zasu zauna ba, in suka dawo daga makaranta ba"

Kai tsaye yace"Su zauna gidan kakaninsu mana"

Sai kawai na koma na zauna ina sharan kwallah Lokaci d'aya ina fadin"Ya isa kaje kawai sai gobe da Sassafe zan taho in sha Allahu"

Shima kansa nasan mamaki yaji da mganata saboda yadda ya ke kallona sai na sake sadda kaina ina jan majina.

Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace"Shikenan ki tabbata goben kin taho kin ji ko..?

Yafad'a cikin alamun Tausayawa acikin lamarinsa na gyad'a mai kai sai ya kara kallona yana fadin"Kina da kudin mota ne..?

Sai na kasa mgana shi kuma ganin haka sai ya cire dubu uku yan Dubu Sabbi ya bani yace nayi na mota na karb'a ina godiya na mike shi kuma ya wuce da sauri nace"Wani ma asibiti kace..?

Bai juyo ba yace"Asibitin general da ke bakin asibiti Dutsenmah"

Na gyada kaina ina fadin"Ka gaisheta ka fad'ama Goggo gobe da Safe ina tafe..Allah ya tashi kafad'an Tamadina"

Ya amsa da Ameen ya fice bayan ya kare ma falon kallo lokaci da'ya yana girgiza kansa.

Komawa nayi na zauna in da na tashi na Rushe da kukan,kukan bakinciki da takaiici ace Tamadina ta kwanta jinya tafi sati ban sani ba to ni a wani bingire zan saka rayuwata ne..?

Ahmad da yaji ina kuka shima ya fara Rigimansa na kwantosa na Rumgumesa na cigaba da kuka sai kawai ya rika bi na da kallo.

Haka na yini cikin wani yanayi motsi kad'an sai na daga hannuna sama ina fadin"Ya Allah ga baiwarka chan tamadina kafini sanin Halin da take ciki..Allah ka bata lafiya ka tashi kafadarta"

Ko abinci da na kan  yi ma yara da wuri ranar sai da suna gabda dawowa na dora musu farar taliya nace sa ci da mai da yaji,Domin bani da natsuwar yin wani abincin da zai bani wahala su kansu da suka Dawo sun ganni duk a sanyaye sannan fuskata da Idanuwana sun kumbura hatta Ahmad rigimamme yau bai yi min rigima ba kamar yasan bana cikin yanayi mai dadi.

Sun dawo suna murnan an basu resit a makaranta na shedar sun biya kudin makaranta har na Team biyu,Alfarma akayi musu saboda naje wajen sau biyu ina basu hakuri sai wannan lekowar tasa ne yaran suka mai mgana inaga yaje ya biya musu, ko kuma ya tura musu.

Ni dai da yake ba wannan ne a gabana ba ko duba Takardan ban yi ba,nace su adana cikin Littafansu.

Amir ne mai wayau cikin su shi ne ya tambayeni Umma baki da lafiya ne..?

Na kallesa cikin wani yanayi sai na kasa basa amsa,sai da daddare bayan mun idar da sallar Isha'i dukkanmu muna zaune sai na kallesu ina fad'in"Kowanne ku ya d'aga hannu ya ce Allah ka bama tamadina lafiya.."

Sai suka tsaya suna kallona Anum ce tace"Umma wace ce?

Da sauri nace"Ina wannan da ta taba kawo muku gyad'a da su masara har nace muku mamana ne kakarku.?

Suka gyad'amin gabad'ayan da sauri nace"To mahaifiyata ce, bata da lafiya ku yi mata addu'a in dai kuka yi sallah"

Fuskarsu ta nuna jimami Amir yace"Allah ya bata lafiya Umma"

Na amsa mai da Ameen atare muka daga hannu muka yi addu'a da Fatan Allah ya bama Tamadina lafiya.

Saboda tafiyata Dutsenma agobe da wuri nace su kwanta ko karatun Dare basu yi ba na kwana ina Tunanin inda zan kai su Amir su zauna kafin na Dawo na duba na hango ba su da inda yafi gidan Mama dole dai ko naki ko naso chan din zan ce Haruna ya kai su in suka dawo ban dawo ba.

Da asuba da na tashi ban koma ba ina gama shirya su na tafiya makaranta na Dafa musu abunda zasu tafi dashi makaranta,Tunda bani da komai sai nayi Tunanin na Dafa wani abu na tafin ma tamadina dashi,Shiyasa da kaina na saka Hijabi na raka su Amir kofar gida muka gaisa da Haruna na fad'amai zai kai su gidan Mama in suka Dawo da yammah ban dawo gida ba,Mahaifiyatace ba lafiya zan je na Dubata ya yi min Fatan Allah ya bata lafiya.

Na duka ina kallon yaran kafin nace"Zaku zauna gidan mama kafin na Dawo kun ji ko..?

Amir ne ya gyadamin kai Anum ce ta kwabe fuska tana fadin"Umma ki tafi dani"Na shafa kumatunta ina fadin"Zaku je Anum insha Allahu ku dai ku yi ta mata addu'an Allah ya bata lafiya"

Da haka na lallabasu suka tafi da Anum ta fara rigiman kayan sawan su ni kuma naga suna da kaya agidan mama bazasu rasa na sawa ba,Suna wucewa na shiga gidan Sa'adatu muka gaisa na gayamata abunda ke faruwa cikin tausayawa tace"Allah sarki wannan da kika kawo min ita muka gaisa ko..?

Na gyada mai kai cikin wani yanayi cikin jimami ta yi min fatan Allah ya Tada Kafad'a,na amsa mata Daman Nama nake so na siya sai tace min sai karfe tara mai naman bakin titi yake fitowa, sai na zauna muka cigaba da Hira sama sama Ahmad na bayana yana barci,Taran nayi muka yi sallama Daga gidanta na gangara bakin titi daga cikin Dubu ukun da Yaya Isa ya bani na siya Naman dubu Daya na koma gida na Dora jallop din Shinkafa,da nama daman ina da Cabeji sai nayi amfani da shi kad'an sai da nagama komai,na samu wata Tsohuwar cooler dina na zuba abincin aciki,sannan na je nayi wanka nayi ma Ahmad muka shirya tare,Atamfa ta na saka wacce Yaya Asiya ta dinkamana mu hudu,na Zura Dogon Tsohon Hijabina da yasha ruwa,kan duk ya kod'e da Takalmina duk yaji duniya ya d'aga tun wani Takalmi da Anty Nasara ta taba bani ne, yafi shekara hudu ina moransa don ma ban cika yawan fita ba,ai da yanzu bani da nasawa.

Rufe get din nayi da key din gidam,Na rike Dubu biyun da suka yi saura da abincin da na Dafa na shiga nayi ma Sa'adatu sallama sha daya da wani na isa gidan Mama,adaidaita na hau na sallame shi na shiga gidan ba kowa ina ta sallama Ashe Mama na falo tana faman kirga kudi sai dai ta ganni na shigo kamar daga sama hankalinta yayi sama bata ji sallamata ba.

Tana ganina kamar taga mutuwarta ta wani zabura sannan ta saka kudin hannunta kasan cafet din datake zaune,Tana wani zare ido tun kafin na kariso ta tareni da fadin"Lafiya ke kuma daga ina yarkace yarkace kamar yar gudun hijira..?

Gabanta na Duka ina gaisheta ta amsa a gaggauce tana kara fadin"Lafiya..?

Kaina na kasa nace"Dama..dama zan je Dutsemah duba jikin Tamadina ne"

Sai Mama ta gyara zama tana fadin"To ashe jikin har yanzu..?ni Goggon taku ta kira ni tace a fad'a miki na sha'afa tafiya ta kamani zuwa Yamai"

Ina jinta ban ce komai ba sai ta cigaba da fadin"Allah ya bata lafiya"

Na amsa da Ameen shuru dai taga ban tashi ba sai ta fara fad'a tana fadin"Wai ni kam sintirman me kika zo kika min a gabana..?

Da Sauri nace"Dama ina so su Amir zasu zo nan su zauna ne in na Dawo da wuri to..inkuma naga jikin nata yayi tsanani zan kwana shine..Shine nace bari nazo na fad'a miki tunda Babansu baya nan"

Har na gama Mgana Mama na bina da wani kallon banza sai da na Dire sannan ta karbe da fad'in"Daman ai tunda na ganki nasan banza bata kawo ki..so kike bayan na gama wahala dake na kuma dawo na ya'yanki..?to baki isa ba malama kije ki Dubata la'asar nayi ki kamo Hanya,Gida ba kowa Badariya ta shiga makaranta Jamal baya garin nima yanzu da kika ganni Hajiya Barira nake jira zamu fita ban san da wa kike so su zauna ba..Kuma Allah na gani bazan soke fitata saboda ke ba"Ta karishe fada tana tabe baki daman ai nasan za'a rina sai kawai na mike ina yi mata sallama ta bi kulan Hannuna da kallo kafin tace"Ke ke..Wannan abun fa ina zaki kai shi..?

Sai nayi mata kamar ban ji ba kuma na jita naki juyowa ina ji tana fadin"Aikin kenan shiyasa kayan abinci ba sa wata suke karewa ga inda ake kwashewa ana kaiwa ashe "

Daganan na jita sauran mganganun nata ban ji ba Domin na fice daga Falon Idanuwana na kawo ruwa naji Nadaaman zuwa ma.

Sai dai na fita Hakkinsu daga ita har Yaya Ishaq din.

Ni da naso naje tun da Wuri sai gashi sai azahar na isa Karofi chan na fara zuwa saboda ban san d'akin da suke ba,Ina ko zuwa na iske Yaya Isa zai kai su Goggo da matarsa da Anty Nasara Goggo na ganina tace"Ga ma Fa'izan nan ta iso..Sai mu rankaya muma asibitin zamu"

Sama sama muka gaisa na shiga Mota sai asibitin General na Bakin asibiti Tamadina na Female ward ne babban Dakin Yaya mariya muka iske a wajenta da Maman isuhu sai matan ya'yan su.

Muka  gaggaisa da tambayan mai jiki sukace da sauki na Ubangiji.

Na kara rud'ewa da naga Tamadina kwance bata motsi numfashinta na sama sama alamun dai tana jin jiki na karisa gaban gadon na tsaya ina kallonta sai kuka na dafa Hannunta da ba karin ruwa ina fadin"Allah ya baki lafiya ta madina"

Goggo ce ta fara bani Hakuri sai na bar gaban gado nayi baya sai yau muka had'u da Yaya mariya tun bayan Tozarcin da Yaya ishaq yayi mata, kaina na kasa cikin jin nauyinta na gaisheta da Tambayan ya mai jiki tace da Sauki sai na sauke kulan Hannuna a gabanta ina fadin"Ga abinci"

Bata kalleni ba tace"Allah ya ba da Lada"

Bamu dade da zuwa ba Nurses suka zo suka fitar damu waje,muka fito baranda d'akin inda mutane ke zama masu jinya da masu Dubiya muma Tabarma Yaya mariya ta shimfida mana muka zauna Yaya Isa ya wuce wajen aikinsa.

Haka na zauna jugun jugum,sai da Yaya mariya tamin mganar salla,Sannan na tuna ban yi salla ba, na mike tace zata rakani masallaci Ahmad ya tashi Lokacin sai Maman Isuhu ta karbesa tace muje mu yi sallan mu dawo su za su yi nasu anan Tunda ga ruwa.

Yaya mariya ta dauko kwanukan da sukayi amfani da shi zataje chan ta wanke sai nayi saurin karb'a muka tafi ,Sallar muka fara yi sannan na yi wanke wanken,muka Dawo muka iske Maman Isuhu na bama Ahmad abinci Goggo ta kalleni tana Fad'in"Yaron nan naki rigimamme ne kuna tafiya ya fara mana rigima"

Ina dariya nace"Goggo har yaye fa kin masa..?

Goggo tace"Nasha rigima dai,don ma yana ganin idon Hafsatu ne. ita ai ya saba ganinta a gidan su"

Sai alokacin na tuna da Hafsah da na tambayeta sai Yaya mariya tace min sai ta taso makaranta zata zo.

Muna zaune ana ta hira sama sama duk rabin hiran na ciwon tamadina ne Maman isuhu tana fadin yadda ciwon ya fara daga zamewarta shikenan abu kamar wasa bata ko iya tashi komai sai an yi mata, suna mganar ni kuma ina faman share kwallah

Goggo tace"Abun ba dadi..Allah dai ya bata lafiya.."aka amsa da Ameen Goggo ke tambayana ashe Mama bata sanar dani ba..?nace bata gayamin ba Goggo ta jinjina kai kafin tace"Allah ya shirya Saudatu"

Yaya mariya na gefe tace"Itama karamar waya ya kamata a nema mata Goggo ace sai arika yin abubuwa mutum bai sani ba, yana chan shi kadai kamar wani mara gata da galihu"

Goggo tace"Haka Isa yace.bari dai komai ya daidaita bazai gagara ba" 

Ana cikin tattaunawar ne sai ga Yaya Asiya ta diro ita da mijinta Dauke da kayan Dubiya katan din maltina da Ruwan gora,Ya duba jikin Tamadina bai jima ba ya bama Goggo dubu goma sannan yayi mana sallama ya tafi yana min tsiya da na gaishesa ya rike baki yana fadin"Wa nake gani kamar Fa'iza Asiya?

Tana dariya tace"Itace mana"

Sai kawai yace"Ke kan Fa'iza bakya zuwa ziyaran kano yaushe rabo na da ganinki..?

Goggo tace"Ai in dai Fa'iza ne haka take gidan kowa bata zuwa"

Bai tsawaita zencen ba ya karbi Ahmad yayi masa wasa yana tambayana Sauran yan'uwansa nace suna makaranta Dubu d'aya ya sama Ahmad a hannu kafin ya tafi Ya Asiya ta tafi rakasa.

Ni dai sai duba yanayin Rana nake yi Saboda la'asar nake son na tafi sai na kalli Yaya Asiya da ta dawo daga Rakiyar ina fadin"Don Allah karfe nawa..?

Yaya Asiya ta duba agogon wayarta kafin tace"Uku da rabi"

Sai na jinjina kai ba wanda dai yace wani abu sai da aka kira sallah mukaje mukayi sallah su Goggo kuma anan sukayi nasu sanda muka dawo an fara barin yan dubiya suna shiga D'akin.dukkanmu muka shige muna kara Duba jikin Tamadina ta nan a yadda take sai dai Numfashi,Bata ma sanin wanda ke kanta Yaya Asiya ta kalli Goggo tana fadin"Anya goggo bazamu sauya ma Tamadina asibiti ba..?

Ko dazu da naje raka babansu Usaini sai da yayi min zencen"

Goggo tace"To nima Isa ya cemin haka ammh ku bari an juma in megidan nasu ya zo sai muji ra'ayin shi"

Mganar Goggo yasa ba wanda ya kara mgana ni sai na zauna wajen kanta na sunkuya na rika karanta mata Fatiha da Suratul yasin sai Arrahaman goman Farko da ayatul kursiyu ina Tofamata a kanta zuwa kirjinta na dauki Wani Lokaci sannan na mike na rike Hannunta ina fadin"Allah ya baki lafiya Tamadina.."

Gabad'aya suka amsa min da Ameen sannan na sauke hannunta na gyara mata kanta saman filo na koma baya ina sharan kwallah Maman Isuhu na fadin"Sai hakuri..Allah zai bata lafiya"

Yaya Asiya da Yaya mariya suka hada baki wajen fadin"In sha Allahu"

Ahmad dake hannun Goggo na karba na goya Yaya mariya na ganin haka ta kalleni cikin wani yanayi kafin tace"Ba dai tafiya zaki yi ba Fa'iza..?

Sai na kasa bata amsa kaina na kasa nace"Tafiya zan yi sai gobe zan dawo tare da yaran gabadaya in sha Allahu"

Yaya mariya tace"Haka zaki tafi ki bar Mahaifiyarki cikin wannan Halin..?

In kafin Goben baki Dawo kin Tarar da ita da rai ba fa..?

Sai naji hankalina ya tashi Yaya Asiya ta daka ma Yaya mariya tsawa tana fadin"Haba Mariya wannan mganar bai kamata acikin wannan yanayin ba"

Goggo tace"To ban da abun mariya in ta zauna ai ba sauki zata saka mata ba..Ki barta tafi Dakinta ta kula da ya'yanta tunda gobe tace zata dawo..'

Yaya mariya sai ta juyar dakai ta fice Daga Dakin Tana fadin"Ai shikenan ta tafi..In ta rasu zata fi kowa kuka na sani Saboda itace kad'ai ta zabi miji da Danginsa fiye damu Ahalinta"

Sai kawai na Fashe da kuka Yaya Asiya ta kamani tana fadin"Daina kuka Fa'i haba Fa'i kamar baki san Halin mariya ba share hawayen ki,Ki tafi goben in Allah ya kaimu sai ki Dawo"

Na kalleta hawaye jage jage ina fadin"Ammh Tamadina bazata mutu ba ko..?zan zo na ganta ko..?

Har suna had'a baki da Goggo da Maman Isuhu wajen fadin Insha Allah sai na share hawayena nayi musu sallama goggo tace ina da kudin mota nace mata eh,har zan tafi Goggo tace na dawo na Dauki kulata tunda an juye abincin na koma na Dauka sannan na fice ina kara waiwayan ta madina.

A baranda naga Yaya mariya nayi mata sallama tayi banza dani bata amsa ba sai kawai na girgiza kai na wuce a bakin asibitin na Hadu da Hafsatu da kawayenta,muka gaisa tace har zan tafi nace mata eh sai gobe zan dawo mukayi sallama suka shige ni kuma na hau adaidaita zuwa inda zan hau motar katsina shida saura na yammah na isa gida ina sauka daga adaidaita Haruna na karisowa da su Amir sai da na sallami mai adaidaitan sannan na isa wajen su yaran suka sauko suka zo suka Rumgumeni nima na rikesu muka karisa wajen Haruna bayan mun gaisa yace min daga gidan Mama suke gidan ba kowa shine ya Dawo da su in ban dawo ba su zauna wajen Sa'adatu zai koma tunda bai tashi aiki ba..nayi mai godiya na tara ya'yana na bude gida muka shiga,Allah yasa  akwai sauran shinkafar da na Dafama Tamadina shi na basu suka fara ci kafin nayi musu girki..

Anum tace min"Umma kakanki ta warke..?

Sai ta bani Dariya na rikota jikina ina fadin"Ba kakata bace kakarku ce Anum ni mahaifiyata ce Mamana kum, kamar yadda kuke da Umma nima ina da Mama"

Sai tayi dariyan su na yara batayi mgana sai nice nace"Ta ji sauki gobe zan kai ku gaisheta kuna son zuwa.?

Suka amsa mim atare,nan dai nace musu gobe da su zan tafi Anum sarkin yawo tana ta murna ita da Musty Amir kuma daman bai da Hayaniya.

Taliya na yi mana mai miyar Jajjage mukaci da daddare kafin mu kwanta kamar yadda na sakama raina ban yi musu shirin makaranta ba Saboda na saka araina tare dasu zan tafi in ta kama na kwana ne bani da matsala.

Kafin takwas na safe duk mun shirya na Dibar musu kaya kala daya dukkansu Ahmad kuma Biyu a wata jaka da Babansu ya siya ma Amir mai girma kuma tana da Hannu aciki na Dura kayan,Buga get din haruna shi ya fitar dani na gayamasa bazasu samu zuwa makaranta ba Dutsemah zamu je tare yayi fatan samun sauki ga Tamadina ya wuce wajen sana'arsa.

Karfe tare muka fito na rufe gidan muka shiga nayi ma Sa'adatu sallama ta karbi address din asibitin tace zata yi ma Habiba mgana zasu zo in sha Allahu nace Allah ya yarda.

Ina da kudi dubu da wani abu a Hannuna zasu ishemu na Dawowa kuma bazasu gagaremu ba,Ni na zauna na dauki Anum da Musty a jikina Amir kuma nace ya zauna a inji saboda Saukin kud'in mota,goma da wani abu tama na a bakin asibiti ina Rike da Hannun Anum musty kuma Amir ne ya rikesa tunda d'ayan Hannuna na Riko Jaka muna tafe ruk'i ruk'i har Dakin da aka kwantar da Tamadina sai dai gabana yayi tsalle waje d'aya sanda naga ba itace bace akan gado sai ma wata mata da nagani.

Na rud'e dakyar na iya gaida gadon na kusa da Inda Tamadina ta kwanta. sannan na tambayesu mai gadon nan,Mara lafiyan na kwance bata mgana, masu jinyata ne guda biyu suka kalli juna in ban manta ba, jiya ma na gansu tare muka yi sallar La'asar da D'aya daga cikin su kamar daga sama mai kibar ciki tace"Ya ku ke da ita..?

Duk da sun ga kamannina da Tamadina cikin rawan baki nace"Ni yarta ce jiya ma ai nazo"

Kamar saukan aradu haka naji mganar"Ayya ai ta rasu yau da asuba kila ma an"

Bata karisa ba ta kusa da ita ta Rufe mata baki sai na kwalalo ido ina fadin"Eheee.."

Kamar ban ji ba sai naji lalurata tayi girma kunnuwana sun toshe bana jin komai Sama sama naji ana fadin"To ko ban gayamata ba,zata sani gwara taji tun yanzu"

Sai wata murya tana fadi'n"Ba haka ake fadin mutuwa ba sai ki barta in ta karisa gidan sai taji"

Ni dai bazan iya cewa ga yadda na iya fitowa daga asibitin nan ba, na dai tsinci kaina a bakin asibiti ina Shatatan Hawaye na manta da su Amir dake tare dani,Sai da naji muryan Amir yana fadin"Umma umma.."

Sannan na dawo hayyacina na juya ina kallon sun yi tsuru tsuru sai na Share hawayena na sunkunci musty na Saba ina rike da jakar kayanmu muryata shake nace"Amir rike ma Anum Hannu"

Gaba nayi ban tsaya bi ta kansu ba yau,ina dai jefa kafane kalaman Yaya mariya na dawomin da cewa in tamadina ta mutu sai nafi kowa kuka,Saboda Halin da nake ciki Tun daga Bakin asibiti har anguwan su Tamadina anguwan mallan yusuf Dutsemah a kasa muka je shi Anum ta gaji da kiran Umma ban ko amsa ta ba, nagaji bata kanta nake yi ba shi kanshi Amir din ya jigata ni kuma nafi su wahala ga Goyo da Musty ga Jaka ko da muka iso futu fitu kamar wad'anda suka fito daga Cirani kofar gidan cike da maza masu karban gaisuwa ni bana wani gani sosai ban iya gane  kowa ba ina gaba su Amir na bin bayana har Cikin gidan da Mata suke cike Damkam ni dai so nake na isa Dakin Tamadina na tabbatar da ta rasu ne ko wasa ne..?

Ban san me matan da na wuce a tsakar gidan suke fad'i ba sai da na Dangana da Dakin Tamadina naga Mutane zazzaune suna ta kuka Goggo na fara Hangowa tana ganina ta Dago tana fadin"Ga fa'izan ta iso ma ba ma sai Isan yaje Dauko ta ba"

Jakar Hannuna na Sauke tare da Musty na karisa gaban Goggo na Duka ina fadin"Goggo kada kice min da gaske ne abunda aka fadamin a asibiti wai Tamadina ta rasu..?

Ina mgana sai hawaye sharr Goggo ta rike kafadata tana fadin"Sai hakuri Fa'iza duk wani mai rai mamaci..Tamadina ta amsa kiran Mahallincinta yau da asuba basu jima da dawowa daga makabartan ba"

Ni dai naji ni na sulale jikin Goggo na fashe da wani kuka,Kukan da yasa Dakin ya rikice Ahmad dake baya na ya fara kuka jin na Dannesa haka ma Musty da Anum Amir ne kawai bai saka kuka ba Goggo ta jani ta sunce goyon ta Dauki Ahmad,Ya Asiya kuma ta mike tana sharan kwallah tana Fadin"Hafsatu riko Amir ga shi chan"

Dukkansu kukan suke yi ammh na zucci ta mike ta rikosa suka zo suka zauna sai ya kalleta yana fadin"Anty Hafsatu Maman Umman ce ta mutu.?

Sai ta gyada mai kai Lokaci d'aya ta Rumgumesa tana kuka.

Bansan adadin Lokacin da na Dauka ina kuka ba, nan da nan wani malolin abu yazo ya taremin makoshi ya kasa wucewa hakuri kawai su Goggo ke bamu Daga baya sai kuka na ya Dauke sai dai Tafarfasan zucci kawai.

Har washegari ban iya saka komai abakina ba Hafsatu ce ke ta Dawaniya da su Anum,Ahmad kuma yana Hannun Goggo har ta da su Yaya mariya sai da na dawo ina basu tausayi suka koma suna Lallashina naci wani abu Dakyar adaran na sha Farau Farau sai dai ko minti goma bai yi ba acikina na amayar da shi na koma ina Numfarfarshi

Bakina baya da wani Dand'ano ballatana na iya cin wani abu,sai Ranar Biyu da rasuwa na samu nasha Fura ya zauna acikina Mutane Dabam dabam sun zo gaisuwa Dangin mazajen su Yaya mariya da mazajen kansu,suna nan da su ake zaman gaisuwa hatta da yan makarantar su Hafsatu sun mata kara na zuwa da kuma kololin abincin su,Hatta da sauran dangin mu ta bangaran uwa suna nan tare damu,ammh ni ba Mijina ba Ahalinsa sai ranar uku sai ga Mama da Anty Binta sun zo da rana suna ta wani jin kai,ko awa d'aya basu yi ba sukace zasu tafi,Muna zaune adakin Tamadina dukkanmu,ni ina gefe kaina a jikin bango ina bin kowa da kallo Carbi ne a hannuna inaja Hijabin Yaya Asiya ne ajikina da shi nake kwana nake tashi wanka kuma tun da nazo ko sau daya ban yi ba.

Mama ta isa kusa dani tana fadin"Ai ya kamata ki koma gida hakanan saboda karatun yara sannan ki bar gida ba kowa kada a haura ayi sata."

Bata bani mamaki da kalamaanta ba, sai na kalleta da Jajayen idanuwana kafin nace"Aka rasa rai ma aka Hakura ballatana abun duniya..?

Na tsareta da idanuwana cikin wani yanayin da na tabbata bata ganina aciki ba.sai ta mike tana fadin"Rai ai da'ya ne, shi kuma asara ai suna da yawa"

Ban ce mata komai ba Anty Binta kuma ko ya Hakuri bata iya ce min ba nima ko ban gaisheta ba,sai dai naji tana Tambayan ina yaran..?

Naji Yaya Asiya na gaya musu Hafsatu ta shiga makota dasu tayi musu wanka,Da zasu tafi Mama bataji kunya ba tace Ishaq na yi mana gaisuwa Dayake basa kasar shi da Zainab.

sun je india a Duba Farhan Saboda Haushi Goggo ce kad'ai tayi fatan su dawo lafiya ni kuwa Idanuwana na Rufe naji wani Tiriri na fitowa daga   

k'asan raina,kaina ciwo yake yi har na bala'i ga jiri,nasan bani da lafiya. ammh halin da nake ciki ban ki nima ace na Mutum ba,da dai irin rayuwar da nike ciki wacce bata da wani amfani.



*Littafin KANA NAKA book2,3.paid book ne biya kudin karatun ki akan Naira N500 Regular posting sau d'aya a rana.*

*Ko kuma tsarin VIP 1000 Posting sau biyu a rana akan wannan acct din 0552179550 Jamila Umar Gt bank,sai a turo shaidar biya ta wannan lambar 09069067488 Wannan karon babu tsarin kati,kowani tsari zaka yi ka turo ta POS,Mutanen mu na Niger kuma zaku tuntubi Kausar Aglan Nissa ta wannan lambar +22796562223*





*Janafty*KANA NAKA..!*


*Wattpad:JamilaUmar315*

*Mallakar:Janafty*

*Arewabook:Jamilaumarjanafty*


*Ina gaida Matar Abba,Maryam jumare.*

*Madalla da ke Hauwa'u(Real smasher)Fa'iza ta ce na gaishe ki*

*Fa'iza na gaida mai sunan k'anwarta Hafsah Hafnan,(Sahibatu) tace sannu da Himma.*

*Fa'iza ta ce na isar da sakon gaisuwarta ga uwar Dakin Gudayo da Yabi,tace madallah da kawar kirki irin ki Surayya Dahiru gwaram.*


*Ishaq na gaida Ahalin Masoyansa gabad'aya,yace na Fada muku. ya ji duk zagin sa da kuke yi groups groups,Har da masu sauya masa suna wai Isiya,Yace kwa yi ku gama shi da Fa'iza mutu ka raba takalmin kaza.*


*JANAFTY NA GAIDA MASOYANTA

 MASU AIKO MIN DA SAKO GA FA'IZA DUK NA ISAR DA SAKON KU,TAJI KUMA TACE TA D'AUKA IN SHA ALLAHU ZATA MIKE TA TAIMAKI KANTA*


        *🅿️17*


Ranar da akayi addu'ar bakwai da Daddare,aka taramu saboda washegari zamu watse. kowacce zata koma gidan mijinta,Cikin taron har da Megidan Tamadina da abokan zamanta. sai manyan ya'yan gidan maza,sai mu sai Goggo da Baba Ati kamar kaka take wajen Tamadina ita kad'ai ta rage acikin dangin mahaifinsu da na mahaifiya tunda daman auran zumunci ne tsakanin iyayan nasu..

Bayan bude taro da addu'a da yi ma Mamaciyar addu'a sai d'an nasiha garemu na hakuri da rayuwa,duk yadda tazo ma bawa sai kuma aka gangarowa mgana kan abunda ta bari na magada.mu kenan to da yake bata bar wani abu ba,sai yan kayanta da gado da Sauran tarkace nan take kuma mukace mun yafe a raba ma bakuta,suka shiga saka mana albarka Megidan su ya ce Tamadina tun iya zaman da yayi da ita, bata taba sab'a mai da gangan ba,saboda haka ya yafe mata duniya da Lahira,haka Sauran abokan zamanta suke ta fad'in alherinta suna fadi'n bata yi musu komai ba mace mai kirki da son zaman  lafiya,Daga karshe Yaya mariya ta muskuta tana kallo Goggo Lokaci d'aya tana fadin"Goggo ya mganar bashi.shin ko sun san ana binta a bashi Saboda a biya a sauke mata nauyi..?

Maman isuhu ta kad'a baki tun kafin Goggo tace wani abu tace'"Allah ya jikan Tamadina ba mace bace mai cin bashi ba,ga yara nan duk sai su tsallakemu su kawo mata ajiyan kudadensu,wlh yadda suka bata haka suke karb'an su ko chanzasu batayi.bata taba cin bashi ba,macece mai godiyar Allah da Wadatar zucci"

Gabad'ayan mu dad'in wannan yabon mukaji,har sai da hakan ya nuna a saman fuskar mu,an tashi taron cike godiya da fatan Allah ya jikan Tamadina bayan Goggo ta sanar da Mutan gidan gobe zamu koma gidajenmu suka nuna alhininsu.

Bayan mutan gidan sun fice suka bar mu, mu kadai Ni ina gefe nayi tagumi bana mgana Amir ne kadai bai yi barci ba yana jikin Hafsatu,Yaya mariya ce da Yaya Asiya ke ta zencen su da Goggo da Baba Ati acikin Hiran ne Yaya Asiya tace"Baba Ati wai har yanzu ba'a samu labarin inda Dan'uwan Tamadina yake ba..?

Baba Ati ta sauke Numfashi kafin tace"Ke dai bari Asiya wlh ba'a samu ba.Kwanaki har chan karayen naje da muka kai yar gidan mallam Akilu aure chan. aka tabbatar min sun tashi sun koma cikin garin kano hannun wani Dan'uwan ita Zuwairan"

Yaya mariya tace"kuma babu lambar waya Baba Ati..?

Ta jinjina kai kafin tace"Gaskiya babu..Ai tun lokacin zamanta a korafi batayi dogon Huld'a da kowa ba Zaman nasu ma da mahaifiyar Tamadina kakar ku kenan ba dadi gaskiya har da shi Mallam din saboda bata so auran ba,mahaifinta ya had'a abun akwai wanda take so shiyasa sanda aka kawota batayi huld'a da kowa ba,ko Haihuwar Usman din Rabo ne kawai da ya rantse yasa aka samar dashi.

Sai kuma mallam din yazo ya rasu.to bayan ta fita Takaba,Danginta suka zo tafiya da ita.sai ta nuna zata tafi dashi to rayuwar nan ba wanda ya damu da rikon D'an da ba nasa ba, saboda ganin Nauyi ne in ma ta barsa anan d'in shiyasa ba Gaddama akace zata iya tafiya da shi Har ga Allah na zata zata rika kawosa ko don yar'uwansa da suka Had'a uba sai kuma gashi Tunda ta saka kafa ta bar Karofi yau shekaru sama da Arba'in da Doriya bata Dawo ba.sannan shima Usman din bai nemi Dangim mahaifinsa ba har yau din nan kuwa"

Ba kuma wanda yasan inda suke ahalin yanzu"

Gabad'ayan mu muka sauke Numfashi Yaya Asiya tace"To Allah yasa yana raye"

Yaya mariya tace"In sha Allahu ma yana Raye kuma in dai da rai da rabo watarana zamu had'u da shi"

Muka amsa gabadayan mu da Allah yasa Goggo ta gyara zama tana fadin"Duk inda yake in dai jinin ku ne zai nemeku jini ai ba karya ba ne".

Muka jinjina mata kai alamun gamsuwa ni ko araina sai na samu kaina da addu'an Allah yasa yana raye domin shi kad'ai ne shakikin Tamadina anan duniya mu kuma kawun mu Namiji kwara d'aya tak da yau zamu bugi kirji muce muna da shi acikin raina ina addu'an in dai yana raye Allah ya bayyana sa da gaggawa.

Washegari da shirin tafiya muka tashi. kowa kagani da Kuzarinsa ban da ni,kwata kwata kamar an zaremin lakkan jikina,Goggo sai fad'a take min wai na kwazzabi kaina bana cin abinci Yaya mariya na wajen tace"Kuma zama da yunwa bazai taba Sauya komai ba..Tamadina ta rasu sai dai mu yi fatan Allah yasa tana kyakyawan karshe"

Sai hawaye ya kecemin suka shiga tsere bisa kumatuna, bayan mutuwar da ta dake ni,yayi sanadiyar tasomin da ciwona da daman kamar jira yake na shiga hali makamancin sa,Mun had'a duka kayanmu na yara Hafsatu ta wanke musu ta had'a musu ta musu wanka,ta shiryasu haka ma su Yaya mariya sai kuma sabon kuka ya tashi muka zauna mu hud'u muka ci kukan mu muka koshi,muka share Hawayen mu. Goggo tagaji da bamu baki ta Hakura ta koma gefe ta zuba mana ido bayan ta kira Yaya Isa tace yazo ya Dauketa ita da Hafsatu da mariya da Baba Ati, Yaya Asiya kano zata wuce nima kuma gidana zan koma.

Da azahar sai ga Hajiyar Dala,mun dauka ma bazata zo ba ne ahalin taji Rasuwar. tunda Goggo da kanta ta kira wayar ta,ta fad'a mata,Tazo tayi mana gaisuwa ta bama Yaya Asiya dubu goma Sadaka batayi awa d'aya ba,Ta ce zata tafi, nan take zencen zata karisa katsina Tare da Direba take jin Haka yasa Goggo ta kalleni tana fadin"Fa'iza tunda kun gama shiri,sai ki bi goggon taki tunda katsinar zata shiga"

Da Sauri tace"Aa ba gidan Saudatu zani fa gidan Wani abokin Major ne. mahaifiyarsa ta rasu zan biya nayi musu gaisuwa suma na wuce"

Ina jin haka nima murya a sanyaye nace"Ki bari kawai Goggo zan tafi da kaina"

Sai goggo ta jinjina kai kafin tace"Shikenan"

Daga haka tayi mana Sallama tatafi Goggo ce ta rakata har Dakunan matan gidan tayi musu gaisuwa, kafin Tafiyarta sai da ta dawo sannan Yaya Asiya ta bata kudin da Hajiyar Dala ta bata Goggo ta karb'a tana fadin"Kudin ku ne ai Asiya ba ni aka bawa ba"

Yaya Asiya tace"Goggo mu bama bukata ayi sadaka Allah ya kai Haske kabarin mahaifiyarmu"

Goggo ta amsa da Ameen itama fita tayi da kudin Dakin Maman isuhu ta shiga ta bata kudin Dakyar ta karba, Goggo tace kun yi wahala damu wajen kwana takwas ku karba ku kara Allah ya Rufa asiri .sannan ta karb'a tana sharan kwallah da kara fadin Allah ya jikan Tamadina.

Yaya Isa ya kira yace gashi nan zuwa,Shinkafa suka dafa mutam gidan suka zubo mana yaran aka zuba mawa suna ci ni dai bakina yayi nauyin  bana jin Dad'in komai kaina wani Dum dum kawai yake yi duniyar ma ba daidai nake jinta ba.

Kwatsam sai gasu Sa'adatu da Habiba sun zo min gaisuwa nayi mamakin zuwan su sai da aka gama gaisawa sannan na kalle su ina fadin"A ina kukaji rasuwar sannan waya kwatanta muku gidan nan..?

Sa'adatu tace"Ai tun da naga an kwana biyu baki dawo ba nace ba Lafiya Megidan ma nata jimamin abun.  yace haka kurum bazaki je ki zauna ba ko don makaranta yara da muka ga an yi kwana biyu sai yace bari yaje gidan kakaninsu su Amir yaji ko Lafiya. to chan yaji abunda ya faru wajen kanwar Baban su Amir ce domin ina ganinta tana zuwa itace ta fad'amai mahaifiyarki ta rasu sai ya Nemi ta kwantatamai gidan nan sai ta mai kwantance mun d'an sha wuya kafin mu gane,sai dai kinsan gidan mutuwa baya boyuwa balle da naga ba'a gane ba sai na rika kwantance da cewa Bebiya bata mgana sai ko gashi an kawo mu"

Na jinjina kaina,kwallah na Taruwa acikin idona makota na ne da ban had'a komai da su ba,Ammh sun nemi inda nake sun zo min gaisuwa Su mama kuwa tun ranar uku basu dawo ba,bana saka ma Yaya Ishaq a lissafi bai Dauke ni da Daraja ba,ballataana ya Dauki dangina da iyayena abun Daraja Har afili na nuna musu jin Dadi'na na nuna su ga sauran yan'uwana da Goggo suka dinga saka albarka har da gurasa Habiba tazo da shi ita kuma Sa'adatu sai ta Dafo Dambun Shinkafa da yaji Zogale Goggo ta karba ta kai ma Mutun gidan suna fad'in Allah ya bada Lada

A nan suka yi sallar La'asar sannan suka yi shirin tafiya sai nace su jirani mu wuce tare Lokacin Yaya Isa ya iso ya tafi masallaci ne,na mike na shiga uwar Dakin Tamadina na Dauko jakar kayan mu da Hijabina.da Yaya Asiya ta wankemim Goggo ta matsamin nayi wanka da Safe na fito falo na ce Hafsatu tazo ta sakamin Ahmad a bayana na goyasa ta sakamin shi har na saka zani na goyasa irin na D'ago kaina sai Duhu ya mamaye ganina na fara Laluban bangon gabana na rasa sai nayi luu ta baya zan fad'i sai  naji an tareni ana salati kuma hannuwana ne da yawa suka rikeni,Sama sama nake jinsu jiri ya rikeni da kaina da ya dauki wani irin azaban ciwo,Kamani sukayi na zauna Yaya mariya ta kwanto goyon Bayana Goggo fad'i take"Daman ni nasan yarinyar nan bata da lafiya, shigen zurfin cikinta yasa taki mgana"

Asiya kira min Isa yayi maza yazo in asibiti zai kaita ya kaita kada ta yi ma kanta Lahani bamu sani ba"

Ina nan zaune Dafe da kaina ina jin Sannu sannu na tashi Daga bangarori Dadama, chan jimawa na zame na kwanta naji shigowar Yaya Isa da Bayanin da Goggo take yi masa,sai yace a kamo ni muje asibiti a dubani.

Yaya mariya ta kamani muka fita mutan gidan na tambayan lafiya tace jiri ne ya kwasheni Maman isuhu tace"Daman daga ganinta bata cika lafiya ba itama"

Ni dai ina jinsu har muka fice muka shiga mota wani asibitin kud'i acikin gari ya kaimu shi ya shiga ya fita muka ga likita akan Lokaci gwajin Farko sai ga jini na ya yi sama Dari Biyu da Doriya sai ucler likitan nata fada ina so na kashe kaina da na fadi zan iya kamuwa da Ciwon barin jiki, ko jini ya haye yayi sama na mutu mgunguna ya bani bayan yayi min alluran jijiya ta ucler sannan yace na rika cin abinci sosai saboda kiyaye lafiyata.

Muna hanyar Dawowa Yaya Isa sai fad'a yake yi,Yaya mariya bata mgana sai dai kawai ta sauke numfashi tace"Uhm" abun yafi karfin ta wannan karon ko da muka koma makotana sun tafi sun so su jira dawowarmu Goggo tace su tafi Saboda Dare sannan sun bar iyalansu agida to sanadin haka komawa Katsina bata yuyu ba da Goggo ta kawo mganar Yaya isa ya maidani sai yace"Haba Goggo kalli Halin da take ciki fa..?,jininta yafi dari biyu a yadda take nan ko kanta bazata iya mora ba ballatana ga yara tare da ita,kawai mu wuce da ita gida in taji sauki sai ta koma"

Sai Goggo ta kasa musamai saboda taga Halin da nake ciki,Ni a motar Yaya isa muka tafi ni da Goggo da Baba Ati da yara su Yaya mariya da yaya Asiya da itama tafiya kano tasha ruwa suka hau ta haya mun yi sallama da mutanen gida muka rabu suna Hawaye muma muna yi.

Sai dare muka isa karofi ni dai abinci suka matsamin naci, nasha mgani na kwanta barci. Salolli na ma sai da asuba na rama su na ji saukin Jirin sai dai ciwon kan ne,Washegari Yaya Asiya ta koma kano Yaya mariya daman muna isowa ta wuce gidanta

Wasa wasa jikina ya ki dad'i har sai da na kara Sati a karofi Goggo na kula da ni,tare da su Amir kamar kada na koma inda na fito sai dai ba Dama ranar da nake da kwana bakwai a karofi Goggo ta saka Yaya isa ya maidani da Yammah bayan taga naji sauki,Tare da sha tara na arziki komai ta had'amin su garin kunu,garin Danwake,Wake,Tsaki,rama bushasshiya da Zogale sai Taliya yar Hausa da yara suke so sai ta saka aka Murzamin ta samin a kwali saboda kada ta karye hatta kayan maggi sai ta siyamin,da kayan miya mai yawa sannan ta saka Yaya isa ya kaini har gida ni da yara ina ta masa godiya shima da ya saukeni ya bani dubi biyar yace na rike sannan ya Jadaddamin naa kula da lafiyata na amsa mai da in sha Allahu.

Gyaran gidan na fara ko'ina duk yayi kura,Amir na tayani da kwashe kaya su Anum kuma sai dai su kara batawa,Adaran Taliya yar murji na Dafa mana na manja mai ruwa ruwa muka ci tare a faranti daya muma Santi muna gamawa bayan mun yi sallah na saka suka kwaso littafan makarantansu nace su duba tunda gobe zasu koma makaranta.

Wasahegari Laraba da wuri na shiryasu na kuma fita da su da kaina,Haruna da Sa'adatu da na leka gidan suka karamin gaisuwa da tambayan ya karfin jikina..?nace naji sauki sai hamdalar ubangiji.

Makota na dake kusa dani wad'anda ban taba ma shiga gidajen su ba sun shigo sun min gaisuwa daga suce Sa'adatu ta fad'a musu ko Habiba naji Dadi Sosai domin ba karamin masoyin ka ba ne zakayi rashin uwa yazo yace maka Allah ya kara hakuri kuma bazaka manta da wannan mutumin ba, wanda kuma bai ce maka Allah ya kara Hakuri ba,shima girman abunda ya aikata yana nan acikin ranka bazaka taba mantawa dashi ba.

Na dawo da kwana Biyu Anty Mamah tazo min gaisuwa tace ta zo sau biyu bana nan,nace mata eh nayi rashin lafiya ne tayi min gaisuwa ta kuma bani Hakurin sun yi tafiya ne chan dangin megidanta Kumo dake jahar Gombe ta jima muna ta Hira sai la'asar tatafi bayan nayi mana Danwake da manja da yaji taci ta koshi,sannan mukayi sallama washegari kuma daga makaranta Sai ga Badariya tazo min gaisuwa itama da ban hakura Mama bata nan bikin D'iyar Hajiya Barira k'awarta tatafi wajen satin ta daya Abuja aka kai Amarya, dagachan ta biya gidan su Zainab ta kwana biyu.

Sai kawai na samu kaina da cema Badariya"Sun dawo ne..?ya mai jiki..?

Badariya tace"Basu dawo ba suna chan jikin Farhan da sauki sun dai Tsaya Hutawar su kawai"

A fili nace"Allah ya dawo da su lafiya"

Daganan ban kara tofawa ba,Bata jima ba ta tafi tace saboda Mama yanzu in taga ta Dad'e sai ta fara fada, nace gaskiya kam ya kamata ta tafin kada dare yayi mata.

Mutuwar Tamadina ta Dakeni matuka,sai dai na zauna nayi Tagumi ina sharan kwallah in Amir yaga nayi Tagumi sai ya cire tagumin yana fadin"Umma ki daina tagumi ummanki zata dawo"

Sai ya bani dariya na jawosa jikina ina fadin"Aa bazata dawo ba Amir..Ai kasan mutuwa ko.?kuma a makaranta an fad'a muku duk wanda ya mutu ai baya Dawowa a rami za'a ha'ka a binnesa shikenan bazamu kara ganinsa ba"

Cikin yanayin mganar sa yace"Ita Umman ki a rami aka sakata..?

Sai na gyad'a mai kai Lokaci d'aya ina fadin"Eh mana..kowa zai mutu muma watarana zamu mutu a hak'a rami a binne mu baza'a sake ganinmu.Mu yi ma wadan'da suka rigamu mutuwa addu'a muma in mun mutu sai mu samu masu yi mana addu'a"

Ya gyad'a min kai kafin yace"To Umma zan rika yi ma umman ki addu'a"

Daman kuma ina yawan fad'a musu in sukayi sallan su rika cewa Allah ya gafartama iyayanmu da magabatanmu da yan'uwanmu,kuma suna yi,Har su Anum haka na koya musu nima in dai na yi sallah sai na Roki Allah ya jikan dukkan yan'uwa musulmai da suka rigamu gidan gaskiya mu kuma Allah yasa in tamu tazo mu samu cikawa dakyau da imani.

An yi addu'ar Arba'in Tamadina,Ni ban je ba Hakama Yaya Asiya su Goggo ne da Yaya mariya suka koma sai dai daga gida nayi mata addu'a da Sadakan Allah yakai haske kabarinta na Rokar mata salama da amimci a wajen Ubangiji a kabarinta,Ni tunda Tamadina ta rasu komai ya fita kaina naji bakowani wani abu ne zai rika batamin rai ba,Na riga nasan na rasa dukkan wani bangare na jin Dadi, Dariyata kadai ya'yana ke gan. sune kad'ai yasa har yau nake tsaye kan kafafuwana,Saboda hakane yasa na Dage da shan mgunguna saboda in nazo na kasa ko nayi Rauni ya'yana baza su iya d'aukan maraici tun suna da kananun shekaru ba. shiyasa karfina da Kuzarina duk Ta dalilinsu ne shiyasa ita uwa ya'yanta kan zama gwarin gwiwanta sau da dama.

Kwata kwata nama manta da mganar Form din da na cike na koyan sana'o'i da bada tallafi,na mikama Allah duka al'amarina,sai kwatsam Badariya tazomin da labarin an Turo mata sako Daga Kungiyar Women charity Foundation kan zasu tantancemu ranar asabar karfe goma na Safe a wata makarantar yan mata Dake cikin gari sai na rud'e na fara rawan jiki ina fadin"Bada..riya..To ni ya zan yi..?bansan ko'ina ba fa..?

Sai tayi Dariya tace"Sha kurum ki zan yi ma Mama karyan makaranta sai nazo na rakaki"

Sai da ta fad'i haka sai hankalina ya kwanta, tun daga ranar ko dayaushe addu'ata d'ayane in da alheri acikin wannan mafitan. Allah ya tabbatar min in ba alheri Allah ya musanya min da mafi alheri.

Sai naji zuciyata ta natsu da al'amarin,Ranar jumma'a Dakyar na iya barci Saboda Zullumin abunda zai faru gobe,Da sassaafe na shirya yara suka wuce Tahfeez nima ban zauna ba na shirya tara da wani abu Badariya tazo na goya Ahmad na saka Dogon hijiba na mai ruwan kasa duk yasha ruwa na rufe gida muka tafi,Ita ta biya kudin adaidaita gaskiya akwai tafiya ba kad'an ba tsakanin gidana da Makarantar mun isa goma saura Haraban makarantar cike da manyan motoci daga gani abun na manyan mata ne.

A wani babban hall na makaranta ake taruwa kai tsaye muka nufi chan mun shiga mun tarar da mata da yawa duk sunzo,muka samu waje muka zauna ina ta raba ido sai da goman tayi sannan Manya mata masu nasaba da ilimi da zati suka rika shigowa suka tsaya a gabanmu, ina ji Badariya namin Rad'a mai bakin mayafi mai jikan nan Hajiyar su Raliya ce na jinjina kaina daga gani kudi da isa sun zauna ajikinsu

A she mu Talatin suka Dauka,Bayan sun kira sunayen kowa da kowa muka mike gabad'ayamu akwai yan rakiya ire iren Badariya,Wata Hajiya ce mai glass take kiran sunaayenmu,na kasa Raunanun kunnuwa a ina jin sunana na mike bayan Badariya ta rike hannuna muka mike tare sannan ta koma ta zauna, ashe Wani kati zasu raba na na shedar Training d'in da zamu yi sannan da wasu bayanan da suka danganci abunda za'a koyar damu.

D'aya bayan d'aya aka rika kiranmu ana bamu wani karamin kati mai dan Fad'i.sannan akwai hoton kowacce ajikin katin har akazo kaina,na mike na kwanto ma Badariya Ahmad dake bayana na fita ina raba ido har gaban Babban ajin na mika hannu na karb'a ta kara kallona sama da kasa har na juya sai ta kirani da fadin sunana"Fa'iza Sidi karofi'

Sai na juyo da Sauri saboda ina gabda ita naji ta fad'i sunana yasa Hajiyar su Raliya ta D'ago tana kallona sai na rankwafa na gaisheta da girmamawa sai ta amsa itama cikin sakewa Lokaci daya tana fadin"Kece matar Brother din Badar..?

Sai na gyad'a mata kai cikin yanayi mganata nace"Eh hajiya tare..tare ma muke da ita"

Sai na juya ina nuna mata Badariya ashe har tataso dauke da Ahmad tazo wajen mu,Ta duka ta gaida Hajiyar Raliya ta amsa tana tambayanta Mama tace tana lafiya sai ta kara kallona tana fadin"Ashe tare kuka zo..?

Badariya tace"Na rakota ne Hajiya"

Kai ta jinjina tana kara kallona nasan har da mamakin ganin yanayina sai matar nan mai glass ta duko tana mata mgana naga tana nuna mata Takardan hannunta sai ta amsa tana Dubawa kafin tace"Fa'iza abu hud'u zaki koya..?kuma a ka'ida biyu ne kina ganin zaki iya..?

Da Sauri nace"Eh zan iya Hajiya.."

Sai dayan Matar tace"Hajiya kinsan dokace Biyu ne ai hudu yayi mata yawa da wanne zataji..?

Sai naga ta duka daidai kunnenta tana yi mata mgana sannan ta jinjina kai,Itama kuma Hajiyar Raliya sai tace muje mu zauna.

Komawa mukayi muka zauna ina ta Raba ido,naga mata kala kala ire irena masu fama da rayuwa da zamantakewar aure,ni dai akasan raina ina jin yakinin zan koyi duka abunda za'a koyamin Saboda shi kad'ai nake ganin gatana a wannan duniyan.

Bayan an gama bawa kowacce Katin ta, sannan suka fara mana bayanin yadda abubuwa zasu kasance zamu fara koyan abubuwan da zasu koyamana nan da sati d'aya zasu raba abun gida Biyu Mrning da Aftternoom,Da Safe za'a koyar da abubuwa Biyar da yammah ma biyar daman goma ne,Da Safe za'a koyar da girke girke da Had'a lemuka,Da yammah akwai koyan yadda ake hada halawa da dilka,Da yadda ake yinta,Da had'a Turaren wuta na Icce da Humra da su Kwallaca,sai na fara nazarin ya abubuwa na zasu kasance..?kenan sai dai na rika zuwa safe da yammah kenan..?

Sannan sun yi mana bayanin awa Bibbiyu ne da Safe tara zuwa sha Daya da Yammah D'aya na rana zuwa uku na yammah,sannan sun bamu shawaran mu natsu zamu iya duka abunda za'a koyar damu tunda na wata uku ne tsawon sati goma sha Biyu ina jin duk abunda suke fad'i Saboda da karfi suke mgana kamar su san da masu Laluran rashin karfi ji irina.

Sun tabbatar mana da cewa acikin mu za'a dibi mutane goma masu hazaka da aka ga sun chanchanta ranar da zamu gama za'a basu Jarin su a Hannunsu,sannan sun horemu da mu maida hankali komai daki Daki zasu koyamana duk abunda bamu gane ba mu yi tambaya. kada mu zama masu duhun kai,Sannan daga karshe sun ce zamu rika zuwa da Littafi da biro mu rika rubuta sunayen abubuwan da za'a koyamana saboda in mun koma gida mu yi bita,Sannan zamu rika rubuta sunanmu kullum inda muka zo da Turanci wato Attendence.

Sannan ko da wani lokaci zamu rik'a zuwa da wannan katin shine shaidar an tantance mu sai mun nunasa za'a barmu mu shiga, zuciyata na cika da Farinciki har na fara tunanin ma na iya duka abunda nasaka raina zan koya,ajikin katina  an saka Abunda nake son koya kamar yadda Badariya ta Rubuta, shi zai nuna inda ya kamata na tsaya sai Sha biyu  na rana aka tashi sun tabbatar mana da cewa kwararun ma'aikata ne zasu jagoranci wannan tafiya tamu mun yi godiya sosai sukace mu yi ma shugabar wannan kungiyar addu'a da fatan nasara Rayuwa, ni ko araina nace duk Sallah sai na sakata nace Allah ya yi mata gatan Duniya da lahira kamar yadda itama tayi mana gata a duniya.

Daga nan muka rabu da Badariya ta taremin adaidaita na Dawo gida zuciya ta cike da Farinciki,Sai dai na Fara Tunanin inda Zan rika kai Ahmad Saboda sun ce ban da yara saboda ba wajen da yara zasu zo ba ne,akwai abubuwan da bai kamata yara su shakesa ba yayin had'asa.

Sa'adatu ta fadomin rai nako shiga na gayamata ta tayani murna ta kuma tabbatar min na rika barin mata Ahmad zata kular min da shi sai naji Sauki na Dauki damaran maida Hankalina kan damar da Allah ya aramin,Naji dadi tun Sha daya zan dawo gida nayi ma yara girki ko na kimtsa gida da la'asar kuma in na Dawo sai naji da girkin su kafin su dawo makaranta.

Har wankin yaran sai da na kwashe na wanke na goge tare da nawa tunda zan fara fita ba lalle na rika samun Lokaci ba,Ranar Alhamis saura kwana biyu a fara koyar damu Yaya Ishaq ya dawo da Safe na sallami yara sun tafi makaranta kenan ina zaune afalo ina bama Ahmad kuninsa ya shigo ban ko ji sallamansa ba ina chan ina Lissafin duniya.

Sai da ya kariso cikin falon ya kara yin sallama sannan na jisa,na d'ago na kallesa,kamar ba shi ba ya kara Kiba har da karin Saje da gemu ga Tumbi alamun yana samun hutu da jin Dadi.

Kamar bakina na ciwo nayi mai sannu da zuwa bayan na kauda kaina.

Ahmad kuma sai ya fara dagamai hannu yana gaurancinsa.

Bakinsa na gogemai da Kyallen dake gefena shi kuma sai ya Duka ya Dagasa sama bayan ya sauke jakar Hannunsa, mikewa nayi ina kakkabe jikina zan wuce dakina araina ina fadin ka dawo adaidai kuwa.

Sai dai ban karisa ba ya D'aga murya kirani na juyo cikin mganarsa yace"Kin yi min sannu da zuwa baki dauki kayana kin kai min ciki ba.kuma zaki wuce ni kamar kin ga wani banza Fa'iza..?

Sai ban damu da kalamansa ba na koma na Dauki Jakar ya mike ina gaba yana baya ya bude shashen nasa. muka shiga a tsakiyar falon na Dire masa jakarsa na juya naji ajikina ya Juyo yana kallona ammh ban tsaya ba,Sai dai kuma har na fice bai yi mgana ba,dakina na koma na shiga kakkabewa ina gyarawa da na gama na koma Dakin yaran ina tattara kayansu da suka zubar ni kad'ai a araina ina auna abunda zan fad'a ma Yaya Ishaq akan fitar da zan rikayi araina naji wannan karon bazan iya Laushin da na saba yi mai ba.

Ina da Dakin yara naji yana ta kiran sunana da karfi na fito na iskesa zaune afalo Ahmad na jikinsa yayi barci a bakin kofa na tsaya ina jiran cewarsa sai ya kalleni cikin mamaki yana fadin"Kika tsaya min a nan kuma..?

Sai na kariso tsakiyar falon na Tsaya sai da yaga dama sannan yace"Ba wani abu ne agidan..?

Sai kai tsaye nace"Kamar na me..?

Da mamaki ya D'ago yana kallona cikin Hargaginsa yace"Ban sani ba..Wannan wani irin tambaya ne? tunda kikaji nace wani abu ina mgana kan abin ci ne"

Ni kaina bansan meyasa yanzu shakkanan da tsoron Yaya Ishaq suka Fita daga raina ba ,cikin Yanayina nace"Oh gaskiya bakomai sai ruwa Danwake nayi ma yara suka tafi makaranta dashi"

Wani kallon mamaki yake bi na da shi, mamakina ya hanasa mgana ni ko na shiga kitchen na Zubo masa Ruwan Famfom da ya bar mu muna sha,Na kawo mai a karamin jug da kofin Roba duk yaji jiki shi gareni saboda aciki zan basa araina kuma nace bazan Dafa maka komai ba domin bansan da zuwan ka ba.

Gabansa na duka na Sauke ruwan na kuma tsiyayamai na mikamasa sai yaki karba ya bini da kallo kafin yace"wannan ruwan fa..?

Ba na gora ba pure water ne..?

Kai tsaye nace"Babu muma wannan muke sha tun ba yau ba"

Sai jikinsa yayi sanyi cikin wani yanayi yace"Acikin Cefane babu ruwa ne yanzu..?

Nace "Babu.." daganan na sauke Kofin hannuna ganin yaki karb'a ina shirin tashi naji yace"Ashe Kuma Babarku ta rasu..?muna chan Mama ke fadamim..?

Kallon da nayi masa zan iya rantsuwa da Allah ban taba masa makwancinsa ba,da muka kusa shekara goma da Aure,Idanuwana na tsaida a kansa bako kyaftawa cikin wani irin amo nace"au ashe ne ma..?baka tabbatar ba kenan..?

Sai yayi saurin cewa"Kinga ba na son korafi Allah ya jikanta da rahma"

Da karfi na amsa da ameen Ameen Saboda addu'a yayi a gaban idonsa na Dauke Ahmad na shige da shi na Shimfidar na koma na zauna a gefensa ina auna waye yaya ishaq a wajena a tsawon wad'anan shekarun da muka dauka tare..?abu daya ya taba bani da zan kallah naji dad'i shine ya maidani Uwa ya bani ya'ya bayan wannan sai Tarin Tozarci cin mutumci kaskanci da Sauke Daraja da na Fuskanta a zama na dashi.

Ishaq shine sanadiyar da aure ya gama fita daga raina kwata kwata.




*Littafin KANA NAKA book2,3.paid book ne biya kudin karatun ki akan Naira N500 Regular posting sau d'aya a rana.*

*Ko kuma tsarin VIP 1000 Posting sau biyu a rana akan wannan acct din 0552179550 Jamila Umar Gt bank,sai a turo shaidar biya ta wannan lambar 09069067488 Wannan karon babu tsarin kati,kowani tsari zaka yi ka turo ta POS,Mutanen mu na Niger kuma zaku tuntubi Kausar Aglan Nissa ta wannan lambar +22796562223*




*Janafty***KANA NAKA..!*


*Wattpad:JamilaUmar315*

*Mallakar:Janafty*

*Arewabook:Jamilaumarjanafty*


*Gaisuwar Fatan alheri ga iyayen Janafty*


*Anty Habiba Abubakar Imam ikra*

*Anty Summayyah Abdulkadir(Takori)*

*Hajiya Hadiza Mahe muhammad(Mama)*

*Hajiya Halima Dalha Shehu(Umma)*

*Hajiya Hauwa Maman unwas(Mommah)*

*Na gaishe ku,Madallah da iyaye kamar ku,Allah yasa a gama da duniya lafiya Ameen*

    *🅿️18*


Na dauki tsawon lokaci aciki kafin na fito,domin nima sama sama barcin ne ya fara fizgata.ko da na fito falo baya nan, da na leka haraban gidan ba motarsa. sai hakan ya bani tabbacin fitarsa kenan ya tafi gidan Mama. domin ba inda yake zuwa da wuce wajenta,ko Anty Binta sun fi mgana ta waya ko su hadu gidan Maman.

Ban damu ba na cigaba da Harkokina, na riga na saka ma kaina yak'inin Tunda har ya zab'i iyalan zainab sama da nawa iyalan nima zan zab'i ra'ayina da ya'yana sama da shi mu ma Ture mganar aure a tsakanin mu sai dai a duba zumuncin da Allah ya riga ya had'a ,kuma shi sada zumunci Umarnin Ubangijine kuma shi Umarnin Ubangiji sab'a masa babban Laifi ne.

 Haka kurum naji ina sha'awar shan Faten Rama ina da sauran tsaki tun wanda na dawo dashi daga Karofi shi na Tankad'e na wanke na d'ora sannan na Jika bushasshiyar Rama nayi amfani Dashi bani da nama ko kifi sai nayi amfani da wake na watsa musu aciki,sai Faten yayi dad'i yana tashin kamshin kayan miya da Daddawa da su Citta,na juye a kula ni saboda bazan iya jiran yaran ba, sai da na Dib'i nawa muka sha ni da Ahmad sannan na sake yi mai wanka nima nayi muka sauya kaya shidda Saura yaran suka Dawo daga makaranta suka cire Kayan makaranta, suka sauya na gida sannan na zubo musu faten a faranti suka na suna santi,bayan sun gama Anum ta fara min labarin makaranta Musty kuma sai wasan zagayen falon yake yi Amir kuma kan kujera ya hau yana Duba Littafansa.

Anum wasa da kaina take yi,kalaba ne daman har ya kusa warware kansa ma, domin ni nayi ma kaina.Ahmad kuma na daka Tsalle saman jikina Amir yace"Umma ki dubamin aikin nan ban gane ba..?

Ya fad'a yana mikomin littafin rubutun sa  na karb'a nayi gefe da kaina Ahmad nata mika hannu da Sauri Amir yace"Umma karki basa zai ya ga min"

Cikin yanayi na nace"Bazan basa ba.Arabiya ne zan koya maka kabari ayi sallah mu natsa tukunna"

Ya amsa min da Toh ya karb'i Littafinsa Kiran sallar mangariba ya tadamu mukaje mukayi alwala mukayi jam'i gabad'ayanmu afalo bayan mun idar na d'aga hannuwana Ina addu'a Sai suma suka d'aga sai da na shafa sannan suka shafa na kalle su ina Fadin"me kuka rokar mana acikin addu'an..?

Amir ne yace"Umma a makaranta an ce mu rika ma iyayan mu addu'a"

Kai na jinjina masa ina fadin"Yauwa to ina so in dai kuka yi sallah ku rika rokar ma Umma Sa'a da nasara a abunda zata yi kun ji ko..?

Da Sauri Anum tace"Umma me zaki yi..?

Kanta na shafa ina fadin"Ba'a fada ma yara sai abun ya tabbata ke dai ki rika yi ma Umma addu'a ai zaki yi ko..?

Da Sauri ta d'agamin kai sai na Shafa kumatun ta ina saka musu albarkar acikin raina Musty da Anum har sun fara wasa na dakatar da su nace su karanta azkar din su,shiyasa suka natsu,Kiran sallar isha'i ya tadamu muka yi sallar tare sannan muka zauna mukayi addu'o'i Anum da karfi ta rika fadin"Allah ka bama Umma sa'a Allah ya bata gida da mota"

Sai ta bani Dariya Amir ya kwab'e ta da Fadi'n"Aljannah ake cewa"

Da sauri tace"Eh Allah ka ba ma Umma Aljannah "

Ba zato kawai Musty yace"Allah ka sa Umma ya hau jigi"

Gabad'ayanmu muka kwashe mai da Dariya idona ya ciko da kwallah na kama Musty na rumgume ina fadin"Ameen Ameen Allah yasa amsa bakin ku ya'yan albarka kuma Allah ya baku duk abunda kuke so duniya da lahira"

Anum ce ke gyara ma Musty sunan Jirgin da bai iya fada ba sai nanata mai take yi yana fadin Jigi sai suka sanyani Nishadi ina ta Dariya Tuni na manta da duk wani bakincikin dake Damuna. zuciyata ta dawo fara tas kamar farar takardan da ba'a taba yi  mata wani Dameji ba.

Falo na tattara su muka koma na hana wasan nace mza a dauko Littafan makaranta a duba sukaje suka Dauko na shiga Tsakiyar su,su kuma sun Zagaye Ahmad ne ya fara kiriniya zai yaga musu littafai sai na Daukesa na goya a baya na ammh duk da haka sai uban zillo yake yi shi sai ya sauka naki ko sauke sa.

Na Amir guda biyu ne Arabiya da na English na Arabiyan na koya masa,Sai na Anum littafin koyon bakake ne da aka saka su,siya itama na nuna mata yadda zata yi na Musty kuma na turanci ne sai Littafin da na saka ya Rubuta Huruful Hija'iya na Damki hannunsa ina koya mai rubutawa da Fadin su a baki, muna rubutawa muna fad'in su d'aya bayan da'ya sauran na turancin da ban iya ba nace Amir ya taimaka musu tunda shi yana primary 3 ne zai je hud'u Anum na 2, Musty kuma 1,Ahmad ne ya rage shima in da ina da kud'i saka shi zan yi, bakinsa ya bude achan kamar yadda Babansu yayi ma Anum da Musty.

Sai da suka gama duka aikin makarantan nasaka suka kwashe Littafan suka maida jaka suka maida su dakin su,sannan na zubo mana Faten nan a katon faranti muka Had'u muna ta sha Ahmad na kan jikina ina basa a baki Musty ma yasa ka rigima sai na rika basa Anum na ganin haka ta kwabe fuska zatayi kuka tace"Ni fa Umma"

 Sai itama na riga bata a baki Amir ne kad'ai ke shan abunsa da kansa muna cikin haka sai ga Yaya ishaq ya shigo da Leda sai dai yaran suka juya suka gansa kwatsam ni nama manta ko alama ban ce musu Daada ya dawo ba.

Haka suka tsallakeni suka nufesa Har da Ahmad,Amir ne kawai ya tsaya a tsaye sauran kuma jikinsa suka fad'a ya tarbesu yana fadin"Oyoyo ya'yan Daada"Anum sarkin Karad'i ta ce"Daada yaushe ka dawo..?mun daina ganinka ko da yaushe muna tambayan Umma sai tace baka nan".

Ina jinsu sai ya kasa bata amsa sai da ya kai ga zaune sannan ya Dauketa ita da Musty da Ahmad ya Dora zaman jikinsa Amir ya zauna agefensa yana fadin"Umman ku bata gaya muku nayi tafiya ba ne..?Kanin ku bai da lafiya jaririn Antynku muka kai Asibiti"

Da Sauri Anum tace"Jaririn Anty mai kyau"?

Sai ya gyad'a mata  kai,sai suka nuna tausayawar su Ledar hannunsa ya warware ya fito musu da Minti da Biskit wajen rabasu musu ne yaga Hannun Anum duk maiko ya shinshina sai yaji warin Daddawa da Sauri ya Dago kansa yana kallona ni kuma shan Fate na, na cigaba da yi kallo basu isheni ba.

Sai ya kalli Anum yana fadin"Me ye a Hannun ki Mamana..?

Da Sauri ta ce"Daada Fatee ne Umma tayi mana dad'i"

Sai ya k'ara kallona ya kuma kalli Farantin gabana cikin yamutsa Fuaka yace"Fa'iza meye wannan..?

Naji sa ammh sai nayi kamar ban jiba. sai da ya kara Daga murya yana fadin"Nace meye wannan kika bama ya'yana Fa'iza..?

Na dago kaina ido cikin ido nace"Fate ne" 

Saboda naga abun na sa kuma ya fara zama renin wayau faten ne bai sani ba..?

Ya maimaita sunan fate a ransa da Fili kafin yace"Me kenan..?ina mikewa nace"Abinci ne shima.."

Su Anum na kallah ina fadin"Kun koshi ne..?dukkan su suka d'agamin kai sai na nufi kitchen da shi nasan ya bini da kallo ammh ban ko waigo ba sai da na shiga na sauke abun hannuna na wanke hannuna na fito ina Fadin"kuje ku wanke hannuwan ku"

Kamar suna jirana suka sauka da gudu zuwa Daki har da Ahmad shi kuma sai ya kalleni yana fadin"Ina miki mgana kina basar dani Fa'iza?

A kaikace nace"na baka amsarka nace maka abinci ne"

Sai ya kasa mgana sai chan yace"Baku da abinci ne a gidan sai kin basu wannan abun sun ci hannunsu sai wari yake yi"

Sai ma ya bani Dariya na murmusa na gyara zama na akasan cafet din Falon ban yi mgana ba da kansa ya mike ya shiga kitchen din yaga bakomai Sai Dubaruna irin na mace mai ya'ya Shinkafa kad'ai ta rage mana itama ko Tiya bata kai ba,ba domin Goggo ta taimakeni ba da Tuni asirina ya Dad'e da Tonuwa a idon duniya domin tun da na dawo daga Rasuwar Tamadina k'waran abincin ban gani ba.tun Cefanen da yayi mana kafin ya tafi shima bamai yawa ba ne,ina jin ba shi da kudi a tare da shi ne lokacin.

Ina ganinsa ya fito cikin wani yanayi ya kuma daga waya ya kira Mama naji yana mgana ammh Dayake ban maida Hankalina akansa ba ban ji me yake fad'i ba.tunanina na chan inda mafita ta take, da Tunanin yadda komai zai faru jibi,Har na kosa ma jibin yayi mu fara kamar na matso da jibin gobe haka nakeji zumud'i kawai nake ji akasan raina kamar nama iya komai  haka nake ji.

Sunana naji yana kira da karfi sannan na Dago ina kallonsa cikin Mganarsa yace"Wani banzar Dabi'a kika samu ina mgana kina ji na,kina yi min banza..?

Kai tsaye nace"Kayi hakuri abun ka ga mara karjin ji sai hakuri"

Sai ya kasa mgana,Bata rai yayi yana Hararata kafin yace"Na rasa wata irin mace ce ke Fa'iza..?

Yanzu kayan abincin ku ya kare bazaki iya kiran Mama ki fad'a mata ba..?jamal baya gida yana makaranta ita nake turo ma kudin cefanan ku duk wata da kudin bukatun yara, ammh yanzu da nayi mata mgana tace bata zauna ba sannan bata san cefanen ya kare ba"

Kallonsa kawai nayi na kasa mgana shi kuma sai ya cigaba da fad'a yana fadin"Badar na zuwa gidan nan fa ko ita bazaki aika wajen maman ba..?Ko ke bazaki shirya ki je ki gayamata ba..?

Sai kawai nace"Kayi hakuri.."

Saboda na datse mganar ganin yaran sun fito kowanne da Biskit da minti a Hannunsu,Shima jin abunda nace ne yasa sai ya kasa cigaba da tijararsa,Daganan sai hankalinsa ya koma kan yaran yana ta tambayan su abunda suke so suna  fad'amai da labarin makaranta ni ko araina ina kara jinjina kaifin ikon Mama akan komai shi kayan abincin sai naje na Fad'amata ya kare kenan zata fidda kudin da ya turo mata ta siyan mana kenan..?kamar tana yi mana alfarma a raina daman na Guduri niyar ko zamu mutu da yunwa na gwammace duk mu mace da naje wajen Mama nace mata bamu da abinci.

Tara nayi na tattara yaran suka je suka yi shirin barci suka kwanta Anum ma da Ahmad na kwantar da su akan gadona,Na fito falo zan d'an gyarasa tunda yaran duk sun zubar da Ledojin Biskit din a tsakar falon na iske sa Lafe kan kujera yana waya a hankali yake yi shiyasa ban jisa ba sai na shiga abunda ya fito dani bayan na gama zan koma Daki sai ya kwalamin kira na Dakata na juyo ina kallonsa a kishingid'e yake sai ya Dago yana fadin"Naga zaki shige ciki ni me zan ci..?

Sai nayi shuru ban ce komai ba ya kara maimaita mganarsa ya karishe da fadin"ina jin yunwa kuma ban tsaya gidan mama naci abinci ba'

Cikin yanayin mgana tace"Sai Faten in zaka sha..?

Yadda yayi da fuska ne sai da naji kamar nayi dariya sai dai na kanne cikin kaushinsa yace"ki sama min wani abu"

Ko bakomai yaci darajan Zumunci da ya'yan da suka had'amu sai na juya zuwa Kitchen ina fadin"Sai dai shinkafa ita kad'ai garemu"

Ina jinsa ya mike yana fadin"Dafamin ki yi min source din miya tunda naga akwai kayan miya dare yayi ba na son na sake fita ne"

A daran nan ma dafamai Shinkafa araina ina kallon gas d'ina ina godema Wutar nepa ba domin anguwar da muke ana barin wuta ba, da tuni na raina kaina Gas ne mai shidda,wanda ke amfani da

Gas da Electric,basan shekara nawa na kwashe ina amfani da shi da wuta ba, tun Auran Ya Ishaq da Tarewansa a Abuja komai ya sauya,a baya yana mana Refliing ko ya aiko Jamal ya yi mana, ammh daga baya komai ya sauya sai da nayi da mai wuta,shi kuma baya da saurin girki,tunda bani da wata mafita hakanan nake hakuri da shi,Daman gas din Yaya Ishaq ya siya san da zamu dawo gidan.

Har goma da wani abu sannan na gama na had'a komai na kai masa shashensa a falo na sauke mai komai yana ciki ko bari ya fito ban yi ba na koma Dakina nayi shirin kwanciya,na kwanta sai barci ban farka ba sai asuba,bayan na idar da sallah nayi ma yara shirin tafiya makaranta saboda yau Jumm'a ne basa dad'ewa sai basu je da Kwandon abinci ba sai ruwa da na Dura musu suna shirin fita su yi ma Haruna mgana sai ga shi ya fito yace zai kaisu suna ta tsallen murna.

Shi ya kwashe shi suka fita ya kai su sai wajen goma ya shigo gidan,da amajirai guda biyu suna ta shigowa da kaya,kayan abinci ne ya siyo masu yawa har da Biskit din yara da Lemun su da ruwa har da kayan Tea wanda har yaran sun manta da shi sun saba da kunu har da su kwai kayan miya da kayan lambu,Dankalin Turawa da yawa haka ya siyo ina zaune ina karishe ma yaran guga afalo sannu da zuwa kawai nayi mai na juya na cigaba da aikin gabana har ya sallami yaran ya shige shashensa ya sake fitowa kayan na nan zube afalo ban kauda su ba cikin fad'a da bacin rai yace"Wai fa'iza wani salon iskanci kuma kika samo..?

Na dago ina kallonsa ya cigaba da Fadin"nine kike nufin zan kwashe wad'anan kayan ko me kike nufi..?

Ban ce komai ba na kashe soket din Abun gugan, na wuce na fara Daukan kayan ina shiga dasu ni ko na daina rawan jikin kan abunda bazai D'ore ba 

Sai da na kwashe duka na shirya komai a muhallinsa ina shirin na koma na cigaba da aikin gabana yace"ki sama min abunda zan ci"

Kamar nace zainab bata aiko maka dashi ba ne..?

Sai na fasa rashin kunya ba Halina ba ne sai na Tashi na shiga kitchen dafamai mai Dankalin Turawa nayi,sai nayi mai miyar kabeji da taji albasa sai na Dafa mai ruwan tea na Dafa mai kwai guda biyu kuma duka na Tattaramai ko abakina domin na koshi Faten jiya na dumama nasha abuna yaran, kuma Farar shinkafa na Dafamusu da Mai da yaji sukaci kafin su tafi makaranta.

Yana zaune afalon na kawo mai ya kalli Filet da jug din da na sanya mai Ruwan zafin kai tsaye yace"Gabad'aya komai naki ya tsufa Fa'iza..Ji kwanukan cin abinci sun fita Hayyacin su mtswww.."

Ya saki tsaki daga karshe ina jinsa ban ce masa komai ba na koma na cigaba da aikin gabana,sai da na gama na kashe komai na kwashe zan koma Daki naji ya daga murya yana fadin"Ki shirya in yara suka dawo makaranta zamu je gidan Mama a gabanta sai ki fad'amata in ni nayi miki iyaka da zuwa gaisheta"

Sai abun ya bani mamaki.matar nan Kwata kwata bata kaunar ganin kwanciyar Hankalina, burinta ta samo hanyar da za'a tozartani, to da ikon Allah kanta zai koma ni dai ina Daraja ta ko ban auri Yaya Ishaq ba. kamar uwa take gareni, tunda ta rikeni bata barni na yi rayuwa a titi ba sannan duk tsananin wuya da Dadi ta killaceni acikin gida rayuwata bata shiga tsaka mai wuya kamar na sauran matan da rashin gata da mafita yasa suka fada harkan banza ba,ballatana ina auran Abunda ta Haifa har abada bazan ki Darajata ba.

D'aya saura na rana yaran suka Dawo shi yaje ya Dauko su da kansa masallaci jumma'a ya tafi da mazan har da Ahmad ni da Anum mukayi tamu a gida,Shinkafa da miya Da salat nayi mana ni da Anum muka fara cin namu kafin su dawo suna Dawowa na zubo mai yaci tare da yaran,Suna ta Murnan tunda na saka musu sabbin kaya nace gidan mama zamu je.

Wajen uku saura na rana muka isa gidan Mama,Mun iske gidan cike Anty Binta,da su Halisa da Anty mahma da ya'yanta kamar ana biki yaran muna zuwa suka had'u da abokan wasa suka tafi suna ta wasan su.

Afalon kowacce tayi shigar alfarma har ta da Mama ko da taga jiya taga yau da na gaishesu dakyar suka amsa min gwara ma Anty mahma Halisa daman ita ta gaisheni har tana min gaisuwa,Ni da Badariya ne muke mgana kasa kasa kan gobe Badariya tace"Kin fad'a ma Yaya ishaq dai ko..?

Na girgizamata kai kafin nace"Ban fada masa ba ammh zan shaida masa yau in mun koma gida"

Badariya ta zaro ido kafin tace"in ya hana ki fa ?nasan Halin Yaya Ishaq barin ma in ya fad'ama Mama wlh bazaata bari ba"

Kai tsaye nace"Wannan karon bazai iya hana ni din ba"

Cikin mamaki take kallona bata samu zarafin mgana mukaji muryan Mama asama tana Sababi sai da na Saurara naji dani take tana cema Yaya Ishaq gatanan ka tambayeta yaushe rabon da kafarta tako gidan nan da sunan gaisheni.?

Anty Binta ta karbe da cewa"Ballatana ni banza abanza mama"

Shi kuma sai ya d'ago daga Danna wayarsa yana kallona Lokaci daya yana fadin"Shiyasa na kawo ta gata gani ta fad'a in ni nayi mata iyaka da gidan nan? Gata nan ni da kaina na yarje mata zuwa Gidajen ku duk sati ta gaisheku ita zaku Tuhuma me ke hanata zuwa"

Mama ta tabe baki tana fadin"Rashin mutumci ne ba wani abu ba.ko yaran nan bata kawo su, nace to in kai ne ma kake so ka raba su da nan gidan basu da inda yafi gidan nan a wajen su ta bangaran ta da take takama wa take dashi ?uwar tasu da ta rage itama Allah ya karbi a binsa sai naga karyan tsiya "

Idunuwana suka ciko da kwallah na kasa mgana zagi da cin mutumci ba wanda Mama batamin ba Anty Binta na tayata sai da Anty Mahma tace"Haba Mama ki barta hakanan mana ba ta baki hakuri ba"

Sai Mama tayi shuru tana Numfarfashi ni dai kaina na kasa ina bata Hakuri Saboda Yaya Ishaq yace na duka na basu hakuri in ba haka ba sai ya sabamin ban ki ba na Duka gwiwa Bibbiyu na basu hakuri dakyar suka Hakura.

Daganan suka yi kamar bana falon suka cigaba da Hiran su sai Badariya tajani Dakinta tana bani Hakuri na kalleta cikin wani yanayi kafin nace"Bakomai duk wanda yayi ma Aure bauta bazai taba tabewa ba..Sannan sakamakon sa na wajen Ubangiji"

Daga haka muka saki mganar mu kama wacce nake ganin zata Fisheni Badariya sai jinjina yadda zan rika zuwa sau biyu arana take yi.nace mata kada ta Damu zan iya ai nace Allah adakin ta nayi la'asar sannan Mama ta aiko wai nazo nayi musu abincin dare haka na kwabe Hijabi na shiga kitchen da Badariya ta shgo zata tayani Mama na ganin haka sai ta kirkiri aikenta sai bayan mangariba ta dawo Lokacin na gama Tuwon shinkafar har na kulle a leda Miya ce bata karisa ba.

Har ta Anty Binta sai da taci tayi guzuri Anty mahma dai da wuri ta koma gidanta mu kuma sai wajen goman Dare tuwon nan ko bakina ban ci ba,su Amir dai sun ci da Babansu duk na Takura na kosa na koma gida.

Kusan Lokaci d'aya muka fito da Anty Binta itama zasu wuce afalon Mama ta kalleni tana fadin"Wai ni kam fa'iza ina kayan ki da Ishaq yake miki ne..?bana ganin ki da su sai tsumma kike sawa"

Gabada'ya suka kalleni harda shi da Mama,Bai dai yi mgana ba sai Mama ce ta tabe baki kafin tace"Daman da Tsumman ta dace.aiko don yan'uwanta su zagesa zata rika mugun shigga alhalin daidai misali yana fita Hakkinta"

Har muka isa gida mganar Mama tamin Tsaye arai bayan wannan kayan Da Anty binta ta bani ko Hijabi Ya Ishaq bai kara dinkamin ba.ammh Mama ta iya bud'e baki ta fadi yana Fita Hakkina, Lalle gaakiyan masu iya mgana da sukace wata shari'ar sai Lahira.

Sai da duk nayi ma yaran shirin barcin daman ko da muka dawo su Anum duk sun fara barci,sannan na Dauki wannan Katin I.d card kenan na nufi bangaran Yaya Ishaq acikin raina ina jin cewa wannan karon bazan iya bin Umarninsa ko ya amince ko bai amince ba wannan karon ba gudu ba kuma ja da baya insha Allahu.

Na shiga na iske baya falo yana cikin Bedroom dinsa ba domin ni nake bukata ba,ba yadda zai sa na bisa ciki Tuni na kiyayewa kusantar inda yaya Ishaq yake saboda Dalilai masu karfi.

Bedroom din na shiga da sallama baya Dakin sai nayi mamakin to yana ina..?

Har na juya zan fita naji karan Bude kofa kii..Sai na juyo muka hada ido shima kallon da yayi min nasan na mamakin ganina ne.

Yana sanye da kayan barci riga da wando, masu taushi Farare na barci,Ya kariso tsakiyar dakin yana fadin"Lafiya..?

Har yana wani gimtse ransa kila yayi tunanin wani abu nazo nema sai yaga na mikamai abun hannuna ya karb'a yana zama gefen gado lokaci daya yana fadin"Wannan kuma na menene.?

Sai dai yayi mamakin ganin Hotona da sunana da dukkan bayanan abubuwana ajikin katin sai ya kara Dagowa yana kallona cikin mamaki ya kara fadin"Fa'iza duk wannan abun na menene..?

Sai na duka a gabansa na gyara zama na Dakyau kafin nace"Kune yan boko ka karanta Dakyau zaka fahimta"

Ya sake karantawa ya Dago cikin mamaki yana fadin"Naga Katin shaida ne na Training din da za'ayi na koyon sana'o'i daga karkashin kungiyar Women charity Foundation."

Shine nace ban gane ba naga hoton ki da sunanki shaidar katin naki ne"

Mirmishi nayi Cikin karfin gwiwa na fara mai bayani da yadda kawar  Badariya da ita kanta suka samo min form din na cike,da kiran mu da akayi wanchan satin mukaje da bayanin komai na karishe mganata da fadin"Gobe zamu fara koyan abubuwa kuma na tsawon sati goma sha Biyu ne,Sannan sau biyu za'a je a rana ni kuma abubuwan da nake so na koya da Safe ake koyar da biyu da yammah biyu kenan kaga a rana sau biyu zan rika zuwa kenan safe da rana"

Har na gama bayanina yana kallona cikin mamakina daya nuna har a saman fuskarsa,Cikin kaushinsa yace"Duk a yaushe kika fara yanke ma kanki hukunci yin wani abu batare da sanina ba Fa'iza?

Nima kai tsaye nace masa"A ranar da ka zabi wata matar sama dani.Nima aranar na zab'i yanke ma kaina da Rayuwata komai batare da na saka ka aciki ba"

 Maganata ta girgiza sa ya tsaya kawai yana kallona,ban damu ba sai ma naji kamar gwarin gwiwan. da na shigo da ita ta ninka wacce na samu yanzu tsoro ko fargaba sun fice daga raina kwata kwata.

Hanuna na saka na karbi katina daidai Lokacin da yace"Ni ki ke gayama wannan mganar Fa"iza..?Rashin kunya zaki yi min.?

Kai na girgiza kafin nace"Ko d'aya kada ma ka dauka ahakan Yaya Ishaq ai ko ba aure tsakaninmu kai yaya na ne,kuma babu rashin kunya har Abada tsakani na  dakai.kawai akwai lokacin da in mgana tazo a muhallinta gwara a fad'eta kawai da a barta tayi ta zama a inda ba Muhallinta ba"

Sai ya kasa mgana sai kallona yake yi cikin mamaki nasan aransa mamakin ya akayi na samun bakin yi masa mgana yake yi ni ko araina nace daga yau bakunan fa'iza sun bud'e kenan Har Abada.

Cikin Ajiyar numfashi yace"Naji yanzu meyasa kika fad'amin..?

Na gyara zama na nace"Saboda ya dace ka sani ko ba komai ina gadin gidan ka. 

da kuma kula da ya'yanka in fita ta kamani naa jera sati ba ma wata ba, yana da kyau ka sani d'in shiyasa nake shaida maka"

Kai tsayae yace"In kuma nace baza ki fita ko'ina ba na isa ko ban isa ba..?

Ya fada yana kallona cikin ido nima sai na Dago ina kallonsa bansan Lokacin da bakina ya furta"a wannar gabar Isar ka bata isa ba Yaya Ishaq.."

Sai ya zabura yana kallona cikin bacin rai ya nuna da hannu yana fadi"Ni kike cema isa ta bata isa ba Fa'iza"?

Sai ya mike yana Huci Lokaci d'aya yana fadin"Lalle kin fara rai na ni kin manta waye ni a wajen ki kenam? Gantalin da kika farayi na shiga makota yasa kika koyi rashin kunya da rashin Tarbiya ko..?

Sai nima na mike kai tsaye nace"Na fada maka kada kawo mganar rashin kunya a wannan muhallin saboda kai kanka kasan ba Halina ba ne yanzu ta kamane kasan wasu abubuwa.."

Cikin Hargagi ya katse ni bayan ya tasomin yana fad'in"To nace bazaki yi ba in kuma zaki nuna ban isan ba ne bismillah Fa'iza wlh sai na nuna miki Oder side of me da baki taba gani ba"

Ban bari ya sauke mganarsa ba nace"A matsayin ka na waye kake fad'in bazan yi ba..?

Yadda nayi mganar ta basa mamaki sai ya tsaya yana kallona Lokaci d'aya yana nuna kansa cikin mamaki yace"Ni ki ke fad'ama wannan mganar..?

Kai tsaye nace"Eh tambayar ka nayi a matsayinka na waye..?

Mirmishin gefen baki yayi kafin yace"Ina da matsayin yaya gareki sannan kada ki manta ni mijinki ne"

Nima mirmishin takaicin nayi kafin nace"Mijin jingina..?ko yayan da baisan Hakkin kanwarsa a kansa ba..?

Nace mijin Jingina Yaya Ishaq ka ke kira Miji..?

Mgana takara  girgizasa ban bari ya fita daga Girgizan ba na Dora da Fadin"a shari'an ce kai ba mijina ba ne yanzu.Saboda ka zabi wata matar sama dani,ka jingine aure na shekaru biyu kenan,ni matsayina kawai ina kula da ya'yan ka ne sannan in amtsayin Yaya kake mgana baka da wannan Hurumin saboda sai yaya ya zama nagarttace nagartansa zai yi yab'o har ta yab'anyan, da k'anwa bazata iya zarta da wani abu batare da yardan sa ba,Duka baka cike kowani Gurbi ba shiyasa nace isar taka bata isa wannan karon a wajena ba"

Baya ya juyamin ya kasa juyowa ya kalleni, ban damu ba sai nayi kokarin Dauke Hawayen da suka kawo idanuwana na cigaba da fadin"Tun Lokacin da ka zabi iyalan Zainab sama da ni da ya'yana.isar ka ta zama bata isa akaina ba, sannan tun alokacin na Zab'i ya'yana sama da kai,kuma tun  lokacin da ka zabi Dangin zainab Sama da Dangina nima na zabi Dangina sama da naka dangin, ban ce Dole sai ka amince ba ina fad'a maka ne Dole zan fita na nema ma kaina mafita Kuma Dolenka, ka kare mganar hakan daga bakin kowa in kana gudun fallasar Jinginannen auran mu zuwa kunnuwan da bazaka so hakan ba"

Shuru yayi ya kasa juyowa ni kuma da nagama mgana sai kawai na kama Hanyar fita cikin Shakewar murya yace"ya'yana fa wazai kula da su.?

Na juyo muna kallon juna ido cikin ido kafin nace"Nima ai ya'yana ne..Ni nake kula da su Lokacin da ka zab'i zainab da ahalinta sama da su.ai a yanzu ba'a wulakance ka gansu ba, nayi alkawarin zan kula da su domin nan duniya nice gatan su nima sune karfin gwiwata da dalilan da yasa nake zaune cikin kaskantataciyar rayuwa"

Ina gama fadin haka na bude kofa na fice har nakai dakina hawaye ne ke kwaranyomin sai na zauna agefen gado na rumgume abun hannuna a saman kirjina,na fashe da kuka,a hankali a hankali kuma ina samun salama da Sauki acikin zuciya ta.

Sama na kallah nace a fili"Allah kana ji kuma ka na gani.

Ya Allah ka sama min Mafita, mafita mai amfani a rayuwata da ya'yana. ka hananin jin kunyar duniya ka bani dukkan karfi da juriyan daukan duka Jarabawowinka."



*TASTED & TRUSTED*

*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATUN SAIWOWIN MUTANAN CHADI DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZAR AMARE DA WADDA TAKE SON GYARA KANTA*.

*AN GWADA ANGA INGANCINSA SHIYASA NA KE TALLATA MUKU DA K'ARFIN GUIWATA*.

*ABIN BIRGEWA DA WANNAN SAIWAR ZAKI YI AMFANI DA ITA SAMA DA SAU DAYA.*

*AKWAI FULL PACKAGE, AKWAI RABI, TA YADDA KOWA ZAI IYA SIYA*.

*SANNAN BABU BAURI NA TASHIN HANKALI.*

*DA KANKI ZAKI DAFA ABAR KI, KOMAI ANA SAKA WA A CIKI*.

*SHIN KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR, KO KUWA KE CE KIKE SON GYARA KANKI?*

*TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU*

*08032773332*

*DOMIN KARIN BAYANI, SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*..




*Janafty*



[7/5, 6:22 PM] +234 810 299 5100: *KNKB2001*


*Ki biya ki karanta cikin salama,Kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta min littafi,Sannan kada ki yad'amin shi,Pay N500 regular ko kuma VIP N1000, Via Jamila Umar Gt bank 05521790550,ban da tsarin kati wannan karo a turo ta POS, Shaidar biya ta wannan lambar 09069067488*


Duka na tattara yaran muka bi Jamal zuwa gidan Mama hankali tashe,Har da Hafsah muka iske gidan cike da mutane,Kawayen mama da su Anty Binta,Anty mahma da sauran makotan abokan arzuka.

Yadda naga Mama na kuka sai da ta karyamin zuciya ni kaina na shiga tashin hankali mai tsanani. na kasa dora wannan sabuwar kaddarar data bullo mana lokaci d'aya a kan mizani. abu d'aya na sani ina da yakana da yakinin na yarda da Allah sannan na aminta garesa kowani tsanani yake,kuma dukkan sauki daga garesa ne.

Sai ban bi ayarin yan kuka ba. Na koma gefe ina hailala da yi ma Allah kirari da istigifari,domin nema ma Yaya ishaq mafita da salama acikin sabon halin da ya wayi gari acikinsa.

Ganin ba wanda ya tuna da kiran mutanen karofi sai na Dauki wayata na fita daga falon Mama nayi nisa da Hayaniyar mutane,na kira Goggo na shaida mata abunda ke faruwa Allah Sarki dan'uwa rabin jiki sai Goggo ta Rud'e hankalinta ya tashi ta dinga Daukan Salati tana Direwa,mun rabu tace gatanan zuwa bari ta shaida ma su Yaya Isa halin da ake ciki.

Ni da kaina na kira Yaya Asiya na gayamata Halin da ake ciki. itama tana ta salati tana Direwa,kowa in yaji abunda ya faru sai ya tambayi garin yaya..?mu kuma bamu da masaniyar yadda abun ya faru,abu d'aya muka sani ana Tuhumarsa da Batar wasu makudaden kudad'en gwamnati, lamarin akwai d'aga Hankali aciki.

Zuwa yammah gidan Mama ya cika da jama'a yan jaje da masu zuwa kallon abunda ke faruwa suna komawa gefe suna dariya. Da yammah hatta Dangin Mama na yamai sun iso mazan su da matansu har da Hure,itama sai uban kuka take yi ba kiran sunan Allah ballatana Salati.

Goggo ta iso tare da Yaya Isa da Yaya Salisu,basu jima da zuwa ba sai ga Hajiyar Dala ita da megidanta ashe yana gari duka an taru a falon Mama ana faman maida zencen,ni dai ina gefe sanye da Hijabi bazan ce ban yi kuka ba sai dai ban yi kuka na fitar Hayyaci da su mama suka dinga yi ba. ni nafi muka duka lamurana ga ubangijina, yara ma haka suke kuka tun ballatana ganin manya nayi Amir kad'ai ne bai yi kuka ba,sai Hawaye domin shi yazo wajena yana fadin"Umma da gaske yan sanda sun kama Daada.?shikenan bazai Dawo ba..?

Sai na jawosa jikina na share masa hawaye Lokaci d'aya ina fadin"Basu kamasa ba sun dai rikesa suna masa tambayoyi,ka yi ma Daada addu'a da ikon Allah zai jibanci lamarinsa, Sannan ya warware al'umaransa ya Dawo gida lafiya"

Sai ya dagamin kai Daganan bai kara kuka ba. na riga na cusamai yakinin Da sanin Allah komai ya faru sannan garesa ne dukkan wata mafita take.

Mijin Hajiyar Dala babba ne a matakin gidan Soja yasan manyan mutane sosai sai bige bigen waya yake domin nemam makaman zencen,Ammh shuru kake ji har Dare sallah kawai ya fitar da mazan matan mu kuma muka gabatar da tamu acikin gida,

A d'akin Badariya nake yada Saukata in nazo tana kwance sai kuka take yi, su Anty Mahma na bata baki da na idar da sallah ina azkar Lokaci d'aya bakina na motsi ban jirka daga inda nake ba sai da na Daga Hannunwana na rokar ma Yaya Ishaq sauki da salama acikin kaddaransa,na Roki Allah ya kubutar da shi cikin Aminci.

Tare muka shafa addu'an da su Anty mahma ta kalleni tana fadin"Sannu Fa'iza kin fi mu karfin gwiwa,muma bari mu tashi mu yi sallar mu roki Allah sauki kan al'amarin yafi wannan koken koken da muke ta yi"

Nayi yake ban ce komai ba,kamar bazan yi mgana ba ammh kukan Badariya ya Dameni sai na karisa kusa da ita na zauna na Dagota zaune ina Share mata Hawaye ta kalleni nima na kalleni, kafin ta kara saka kuka tana fadin"Anty Fa'iza Yaya ishaq bamu san wani Hali yake ciki ba..Mama nata kuka"

Sai ta fada jikina ni kuma sai na riketa ina Lallashinta har sai da ta samu natsuwa sannan na kalleta ina Fadin"Kuka ba mafita ba ce Badariya.in mun yarda Allah ke da Kaddara sannan shike da sa'a da Aminci to mu mika masa duka Kukan mu, sai ya Dudemu ya share mana Hawaye.Tashi ki yi sallah ki rokar ma yayanki sassauci da warwarewar al'amarinsa,sai kiga da ikonsa komai ya Daidaita"

Da ga alamu mganganuna sun shigeta nan take ko ta mike ta shige Tiolet Halisa na gefe tayi tagumi sai itama ta mike tana fadin"Madallah da wannan Tunatarwa taki Anty Fa'iza.Da su mama ma za'a samu mai Tunasar da su da sun bar wannan kukan sun koma ga Allah"

Anty Mahma tace"Mai dakatar da kukan Mama abu d'aya ne sai in Ishaq din tagani a gabanta kila sai kukanta ya tsaya"

Ni dai ina jin su ban ce komai ba,Dakin na bar musu na fita falo neman su Ahmad,Saboda Halin da gidan ya yini ko abinci ba wanda ya nema ni kuma naga in mu manya ne yaran fa..?sai na shiga kitchen na Dafa musu jallop din taliya na zubo musu ina bin yaran daya bayan D'aya ina ba su suci abinci,ashe Anty Binta na takaice dani,D'an wajen Anty mahma ke kusa da ita na nufesa da karamin Filet din na zubamai ina fadin''Anwar taho kaci abinci..".

Ba zato kawai naji an yi sama da Filet din ya koma ya kife a kasa sai hankalin kowa ya koma kanmu Anty Binta na gani tsaye a kaina Tana faman Huci Idanuwanta sun kala sun yi jajir ta nuna ni da yatsa tana fadin"Acikin wannan halin da muke ciki ke har ta abinci kike..?ina lura dake tun dazu abunda ya faru bai Dameki ba, kamar ma murna kike da Faruwar haka me ake da auran mace irin ki Fa'iza macen kaddara macen da bata san mijinta ba"

Sai na kame a tsaye na kasa mgana sai dai na Sadda kaina kasa Mama ta Dakata da kukanta tana kallona, sai kuma aka rasa me mganar mazan duk suna waje ana ta buge bugen waya domin samun mafita.

Anwar ne yabi taliyar kasa yana ci,Alamun yana jin yunwa wata kawar Mama tace"yara fa najin yunwa, tayi Dubara da ta dafa musu in mu mun hakura saboda tashin hankali,su yara ne basu san komai ba"

Goggo tace"To shi yaro ma me ya sani.?shi dai yaci ya koshi"

Ganin ba'a bata gaskiya ba sai ta fara Borin kunya tana fadin"ku fa ganta wlh ko Damuwa ma batayi ba.kamar cewa ma take gwara da akayi hakan"

Goggo ce ta shigar min cikin bacin rai tace"Assha.Haba Binta ta ya ya mijin ta uban ya'yanta na cikin wannan Halin kice bata damu ba..?ai ba kowacce damuwace ke nuna kanta ba, in mu muna nuna Damuwar da kuka ita sai ta fimu hankali ta nuna Damuwarta wajen Ubangijin komai da komai, kinga kenan tafi mu Dubara mai kyau"

Sai aka fara fadin haka ne kuwa a wajen,ba'a bata gaskiya ba. ganin bata samu nasaran tozartani ba sai ta kalleni a wulakance ta juya ta tafi ni kuma sai na Dauki Anwar na tafi da shi domin na zuba mai wani abincin na basa yaci kada a Dauki alhakin karamin yaro da yunwa.

Har dare ba wata mgana mai Dadi,Domin har alokacin mahaifin zainab yace basu bari an ga Yaya Ishaq ba, duk mazan nan suka kwana da Safe kuma suka hadu suka Dauki Hanyar Abuja har da mijin Hajiyar Dala da shi a Hotel ya kwana da Safe da shi da Tawagansa suka Dauki Hanyar Abuja.

Nan kuma Yaya isa da su Jamal da Kawun Mama dake yamai da suka iso jiya,suka tafi tun a hanya ake ta kiransu sukace basu isa ba,bayan kuma sun isa sai suka daina Daukan wayoyin mutane hankula suka kara tashi Sai Dare sannan Hajiyar Dala tayi waya da megidanta yace shi ya wuce kano ma ammh yana ta kokarinsa abu ne da ya had'a da Gwammati, sunce zasu Tuhumesa ne kuma har Lokacin basu bari an gansa ba.

Wannan labarin ya kara Tada Hankula cikin kwana Biyu ba'ayi barci cikin salama ba,Yaya Asiya tazo jaje ita da ya'yan Goggo na Karofi har da Yaya mariya nima makotana duk sun zo,yimin jaje abun duniya baya boyuwa Tuni mgana ta bazu a gari,Mutane na maau saran Zobo da kunin aya a wajena suna ta kirana bani da sukuni ga masu son Turaren kamshi har da masu biki na abinci, bani da sukuni hakuri nayi ta bama Mutane ina gaya musu halin da nake ciki na Mijina na Hannun masu Binciken Gwamnati a abuja.

Goggo tunda tazo bata koma ba tana tare da Mama tana bata baki Hajiyar Dala data kwana biyu sai ta koma cikin kwana Biyar mama ta fita Hayyacinta su Anty Binta sun gaji da kukan sun hakura, Tuni wadanda sukaje Abuja sun dawo labarin bai Sauya ba, sai dai sun tabbatar da cewa Mahaifin zainab na iya bakin kokarinsa haka ma Mijin Hajiyar Dala ana ta shiga da fita.

Ganin sai zama haka kawai muke yi,Sai nayi tunanin gwara na tattara yara mu koma gida mu cigaba da gayama Allah,tunda ko mun zauna anan gidan abunda Allah ya tsara shi zai faru kuma bamu isa mu sauya masa kaddara ba, sai dai in muna addu'a sai kaddarar tazo masa saukakkiya.

Kwanan mu shida da Safe na samu Mama a dakinta ita da yan'uwanta na yamai bayan na duka na gaisheta ta amsa muryanta a shake kaina na kasa nace mata zan kwashe yara zamu koma gida, sai kawai tayi shuru batayi mgana ba,Hure na gefe sai ta tabe baki kafin tace"Ai ba sai kin gayamata ba ki yi gaban kanki kawai.Ai Anty ita ke da rashi saboda ita ke da D'a"

Baki da asara ko da an rasa Ishaq"

Sai mganganu ya fara tashi a tsakaninsu Mama ce ta katse da fadin"ku kyaleta ta tafi.."

Muryanta a shake ni kuma ganin haka sai na sanyaya murya ina fadin"Mama naga zaman bai da amfani ne ga d'awainiya gwara mu koma gida sannan ga makarantarsu duk ya tsaya zamu cigaba da gayama Allah a duk inda muke da ikonsa komai zai warware"

Wani kallo Mama tayi min kafin tayi tari ana mata sannu sai ta kara kallo kafin tace"Na dad'e da sanin baki da asara a komai Fa'iza, ki yi tafiyarki Domin zamanki bai da amfani ammh ki bar masa ya'yansa anan su d'in Dolensa ne saboda Mahaifin su ne, in suka rasa sa bazasu taba samun madadinsa ba"

Daga haka sai ta koma ta juyar da kanta tana share hawaye, jin abunda ta fada yasa na tashi na fita ni ba haka ne nufi ba ganin ta min gurguwan fahimta sai na fasa gudurina.

Goggo na sama na gayama yadda muka yi da Mama sai ta Dafa kafadata kafin tace"Da kin nemi shawara ta da baki yi mata mgana ba,me neman kuka ne fa aka jefe shi da kashin awaki.Ki rabu da ita ki zauna din har muga abunda Allah zai yi"

Tun da Goggo ta fad'amin haka sai na bar mganar Tafiyar ashe na gudu ban tsira ba mgana ta ding yawo tsakanin Dangin Mama da kawayenta Anty Binta Kirkiri a gabana tace Daman ban damu ba so nake nakoma gida na cigaba da sana'ata tunda shine a gabana,naji haushin wannan mganarta kuma ban kyaleta ba sai da na kalleta ido cikin ido sannan nace"Ko ban damu saboda yana mijina kuma uban ya'yana ba.Zan nuna alhini na saboda yana matsayin Yayana wanda iyayenmu suke abu d'aya ballatana shi din Uban ya'ya na ne"

Daga haka na huce na barta,sai ta fashe da kukan nayi mata rashin kunya mgana taki ci taki cinyewa Goggo ta kashe mganar da Fadin"Haba Binta mu bar wannan ceceku cen tunda ba shi ba ne a gabanmu.Mu ji da abunda ke gabanmu don Allah"

Ammh Anty Binta batayi shuru ba sai da tace"Ai gani tayi tana kama kud'i sai ta dauka daidai muke da ita.Abunda bata sani ba komai lalacewar Daji bai kai in giwa ta mutu kiyasha ya jata ba, ko tana mace tana da Madaukakiyar Darajarta"

Dakyar mgana ta mutu sai da Wata kanwar uwa take ga Mama ta tsawarta ma Anty Binta sannan mganar ta Dakata ammh tana ta kananun mganganu a kaina niko bansan tanayi ba ina Dakin Badariya.

Washegari ya kama Sati daya kenan da labarin da iso mu,an yi an yi an shiga an fita duka labarin bai sauya ba,Hankula ko sun fara kwanciya sai su kara tashi jin ba wani labari mai Dadi.

Sai a ranar muka yi waya da Zainab da yake muna da lambar juna sai dai mukam jima bamu yi mgana ba. sai in wani abu ya taso ko rashin lafiya,Ita ta kirani ni na shafa da ita ballatana ma na kirata, mun gaisa cikin Alhini muka yi ma juna jaje,Sai dai ban wani ji ta cikin wani yanayi ba,Ita take fad'amin mganar Yaya Ishaq sai manyan Gwamnati sun shiga tunda Fitar da kudi ne na ma'aikata kuma ta Office dinsa da saka Hannun sa komai ya fita ba yadda za'ayi ya fita,Tace Babanta ya samu ganinsa sau daya ammh har yanzu ba wani mganar su bada Belinsa,Mun dade muna mgana da ita nace mata ina gidan Mama tayi ta mamakin tace ita da yara sun koma gida sai dai bata bar zuwa wajen aiki ba,Saboda sun ki bata Hutu a raina nace Mama taji kuwa..?sai ga shi tana fadamin Ko da yaushe suna Mgana da su Mama,kuma susan tana zuwa wajen aikinta nan take na Fahimci abun,inda ake raina an fi kai Hari chan bangaran.

Ranar da yammah sai ga Hajiyar su Raliya tazo,ni ina chan Dakin Badariya ban sani ba,Mama na ganinta da su Anty Binta suna ta Rawan jiki mama ta santa tunda kawancen Raliya da Badariya ba yau ba ne,Sai dai ita Hajiyar su Raliya ce bata zurfafa zumunci da Mama ba, sai kuma gashi ni jinina ya had'u da nata da zuru'arta.

Bayan gaisuwa da jajanta abunda ya faru sai Hajiyar su Raliya ta nemi ganina Mama ta tabe baki kafin tace"Kila ma bata gidan domin tun jiya take son ta koma gida dayake bata damu ba"

Hajiya batace komai ba,Da Badariya tazo gaisheta sai tace ta kira mata ni,Ina Dakinta tazo ta kirani ina jin tace Hajiyar su Raliya na mike na fita da Hijabi suna falo na duka na gaisheta cikin Fara'a ta amsa ni tana fadin"Haka ake yi Fa'iza abu ya faru haka bazaki kirani ki fadamin ba..?

Sai dai naji a bakin Raly.?

Kaina na kasa ban ce komai ba sai ta Cigaba da fadin"ba'a haka Fa'iza irin wannan sai ki kirani ki fadamin ko ba a Uwar kika Daukeni ba..?Goggon karofi ta karbe d'iyarta kenan.?

Goggo na gefe tayi dariya kafin tace"Ba ruwana Hajiya ke da Diyar ki"

Kaina na kasa na shiga bata Hakuri sai tace bakomai su Mama haushi duk ya cikasu kallona tayi tana fadin"Ya abun ya faru ne ina so na sani saboda naji in zan iya taimaka wa"

Kafin nayi mgana Anty Binta ta karb'e da bayanin yadda ake ciki Hajiyar su Raliya,ta gyada kai kafin tace"Akwai Kanina yana aiki da Hukumar EFCC din achan Abuja, bari na nemesa naji ko zai iya taimaka mana"

Nan da nan bakin Mama ya washe a gaban mu ta kirasa suka gaisa ta rattamai bayanin komai sai ya nemi sunansa da inda yake aiki Anty Binta ta fadamata sai ta turamai yace ta bashi nan da zuwa Dare zai bincika mata halin da ake ciki.

Bata wani jima ba, tayi ma su Mama sallama,akan yadda akace in sha Allahu gobe zata dawo ita da sauran yaranta Mama godiya kamar zata kwanta mata Hajiya ta kalleta kafin tace"Bakomai kada ki damu babba ne a wajen zai binciko komai..Zan iya yin komai saboda Fa'iza kamar diya take a wajena Ahalina Ahalinta ne,zan iya bakin kokarina bazai gagara ba insha Allahu"

Basa kaunar su ji an ambaceni kuma basa kaunar alfarma ta barayina har waje na rakata ni da Badariya,Direba ya zo da ita ta shiga mota tana ce min sai zuwa gobe,Ta tambayeni su Amir nace suna cikin gida,na dawo cikin gida naji ana ta maimaita zencen nidai a raina ina fatan Allah ya kawo mafita.

Washegari da wajen yammah sai ga Hajiya ta dawo ita da Raliya da yayyin Raliyan suna zuwa ni suka nema daman suna zuwa gidana,Ita kuma Hajiya ta nemi su mama ta gayamusu halin da ake ciki,Hukumar ta na bincike ne,sannan akwai yuyuwar komai da ya fita da saka hannun Yaya Ishaq saboda haka in sun gama Bincikensu zasu yi mgana, sannan sun hana Belinsa saboda cases din na da girma Hankula sun kara tashi tace dai a Dage da addu'a komai zai daidaita.

 Wasa wasa har an shud'e Sati Biyu shuru dai mgana d'aya sai sun gama Bincike,Gajiya nayi da zama na Tattara na koma gida na da yara Goggo ma ta koma Karofi mama an barta da Anty Hure ne mutum yamai suma sun koma kowa ya Saduda yasan Allah ke yi,Mama ta saka ana ta Sadaka da Saukan Qur'ani ni kuma agida banzauna ba ni da yara muna ta kai ma Allah kukan mu,Ban kara bi ta kan Zobo da kunin aya ba,Saboda Halin da nake ciki ko makaranta yaran basu koma ba Hafsa ce ta koma makarantar ta tana zuwa.

Wajen wata da'ya da Tsare Yaya Ishaq aka bama yan'uwansa Daman ganinsa Su Yaya Isa dai suka koma Abuja mgana ta tabbata ba yadda Yaya Ishaq zai fidda kansa saka hannunsa da yardansa aka fidda kudad'en,zai biya taran kudaden gabad'aya da tsabar kudi ko Kaddara.

Lokacin da labarin yazo mana Sai murnan kowa ta koma ciki kudi ba kadan ba wajen Million 70,ina Yaya ishaq yaga wannan kudin ko Kaddara..?su Yaya isa sun dawo suna mganar ya lissafa abunda ya mallaka, gida biyu nan katsina d'aya sai na Abuja sai mota sai gidan mahafinsa,Sai tsabar kudi miliyan d'aya da rabi asusun bankinsa sai fili a nan katsina,Hukumar tace zata zo ta Duba duka kaddarorin zata kwace zai zama karkashinta.

Sai naji na rude ina ta maimaita innalillahi acikin raina Hankali tashe na kalli Yaya isa ina fadin"Aikin sa fa Yaya isa..?

Ya kalleni cikin Tausayawa kafin yace"Ba mganar aiki Fa'iza ya samu ma ya fito lafiya"

Su mama sai kuka Daman a gidan ne ake maida zencen,Agidan muka kwana Dagani har yara saboda ana saka ran dawowar Yaya ishaq acikin Satin.

Haka ko akayi hukumar tazo ta Duba Gidajen da Yace kada a saka gidan Mama,Mama ta saka kuka miye amfanin gidan in bashi a Had'a dashi,Sannan akwai tsabar kudi a wajenta na sana'arta miliyan uku Anty Binta ma ta saka miliyan Biyu,suka tura ta asusun bankin Ishaq,Saboda kudin su rage nauyi.

muna ji muna gani Hukumar ta kwace gidan da muke ciki da gidan Mama da filin da ya siya acikin gari chan ma Abuja ta karbi wanda zainab ke ciki da motar hawansa, sannan sun bamu Notice Wata daya mu tashi Saboda wajen ya zama mallakin Gwamnati

Lalle mun ga tashin Hankali mai suna tashin hankali,Wannan labarin sai dai mun Dauki Dangana tunda zasu sake sa,Bai amsa laifinsa ba ya riga ya rantse bai da hannu akan lamarin, zasu sake sa ammh ba su kyalesa ba in bukatar wani Binciken ya shigo zasu kara nemansa,Shima da taimakon manya acikin lamarin mijin Hajiyar dala da Kanin Hajiya dake hukumar tare da Mutanen Mahaifin Zainab Dr.Lawal bako.

Mama ta tsine ma duk wanda ya saka Danta cikin bala'i tayi mugayen addu'o'i akan sa,Ta ce tunda ya jefa Rayuwar d'anta cikin bala'i shima bazai ga rayuwa mai kyau ba.

Watan Yaya Ishaq biyu a Hannun Hukuma suka sakesa,Daga Abuja tare da Dr.Lawal da Zainab da yara, sai su Yaya Isa da su Jamal suka iso da shi katsina ko da suka iso karfe goman Dare ne an so ya kwana sai gobe yace Zai je yaga Mama yasan tana cikin Damuwa.

duk da Dare ne, gida cike yake da masu dakon dawowarsa.

Mama na jin Dirin motarsu ta Fice da gudu ita ta bude masa Mota ya fito Allahu akbar Duk wannan fafan da kyau da nasabar ta Yaya ishaq ta tafi cikin wata Biyu.

ya rame ya fita Hayyacinsa sai sumar kai da kasumba ta rufe masa fuska, yayi duku duku kamar ba d'an kwalisa Ishaq Kabir Karofi ba.







*03/07/2023*

*Janafty*

[7/5, 6:22 PM] +234 810 299 5100: *KANA NAKA..!*


*Wattpad:JamilaUmar315*

*Mallakar:Janafty*

*Arewabook:Jamilaumarjanafty*


*Ina gaida Matar Abba,Maryam jumare.*

*Madalla da ke Hauwa'u(Real smasher)Fa'iza ta ce na gaishe ki*

*Fa'iza na gaida mai sunan k'anwarta Hafsah Hafnan,(Sahibatu) tace sannu da Himma.*

*Fa'iza ta ce na isar da sakon gaisuwarta ga uwar Dakin Gudayo da Yabi,tace madallah da kawar kirki irin ki Surayya Dahiru gwaram.*


*Ishaq na gaida Ahalin Masoyansa gabad'aya,yace na Fada muku. ya ji duk zagin sa da kuke yi groups groups,Har da masu sauya masa suna wai Isiya,Yace kwa yi ku gama shi da Fa'iza mutu ka raba takalmin kaza.*


*JANAFTY NA GAIDA MASOYANTA

 MASU AIKO MIN DA SAKO GA FA'IZA DUK NA ISAR DA SAKON KU,TAJI KUMA TACE TA D'AUKA IN SHA ALLAHU ZATA MIKE TA TAIMAKI KANTA*


        *🅿️17*


Ranar da akayi addu'ar bakwai da Daddare,aka taramu saboda washegari zamu watse. kowacce zata koma gidan mijinta,Cikin taron har da Megidan Tamadina da abokan zamanta. sai manyan ya'yan gidan maza,sai mu sai Goggo da Baba Ati kamar kaka take wajen Tamadina ita kad'ai ta rage acikin dangin mahaifinsu da na mahaifiya tunda daman auran zumunci ne tsakanin iyayan nasu..

Bayan bude taro da addu'a da yi ma Mamaciyar addu'a sai d'an nasiha garemu na hakuri da rayuwa,duk yadda tazo ma bawa sai kuma aka gangarowa mgana kan abunda ta bari na magada.mu kenan to da yake bata bar wani abu ba,sai yan kayanta da gado da Sauran tarkace nan take kuma mukace mun yafe a raba ma bakuta,suka shiga saka mana albarka Megidan su ya ce Tamadina tun iya zaman da yayi da ita, bata taba sab'a mai da gangan ba,saboda haka ya yafe mata duniya da Lahira,haka Sauran abokan zamanta suke ta fad'in alherinta suna fadi'n bata yi musu komai ba mace mai kirki da son zaman  lafiya,Daga karshe Yaya mariya ta muskuta tana kallo Goggo Lokaci d'aya tana fadin"Goggo ya mganar bashi.shin ko sun san ana binta a bashi Saboda a biya a sauke mata nauyi..?

Maman isuhu ta kad'a baki tun kafin Goggo tace wani abu tace'"Allah ya jikan Tamadina ba mace bace mai cin bashi ba,ga yara nan duk sai su tsallakemu su kawo mata ajiyan kudadensu,wlh yadda suka bata haka suke karb'an su ko chanzasu batayi.bata taba cin bashi ba,macece mai godiyar Allah da Wadatar zucci"

Gabad'ayan mu dad'in wannan yabon mukaji,har sai da hakan ya nuna a saman fuskar mu,an tashi taron cike godiya da fatan Allah ya jikan Tamadina bayan Goggo ta sanar da Mutan gidan gobe zamu koma gidajenmu suka nuna alhininsu.

Bayan mutan gidan sun fice suka bar mu, mu kadai Ni ina gefe nayi tagumi bana mgana Amir ne kadai bai yi barci ba yana jikin Hafsatu,Yaya mariya ce da Yaya Asiya ke ta zencen su da Goggo da Baba Ati acikin Hiran ne Yaya Asiya tace"Baba Ati wai har yanzu ba'a samu labarin inda Dan'uwan Tamadina yake ba..?

Baba Ati ta sauke Numfashi kafin tace"Ke dai bari Asiya wlh ba'a samu ba.Kwanaki har chan karayen naje da muka kai yar gidan mallam Akilu aure chan. aka tabbatar min sun tashi sun koma cikin garin kano hannun wani Dan'uwan ita Zuwairan"

Yaya mariya tace"kuma babu lambar waya Baba Ati..?

Ta jinjina kai kafin tace"Gaskiya babu..Ai tun lokacin zamanta a korafi batayi dogon Huld'a da kowa ba Zaman nasu ma da mahaifiyar Tamadina kakar ku kenan ba dadi gaskiya har da shi Mallam din saboda bata so auran ba,mahaifinta ya had'a abun akwai wanda take so shiyasa sanda aka kawota batayi huld'a da kowa ba,ko Haihuwar Usman din Rabo ne kawai da ya rantse yasa aka samar dashi.

Sai kuma mallam din yazo ya rasu.to bayan ta fita Takaba,Danginta suka zo tafiya da ita.sai ta nuna zata tafi dashi to rayuwar nan ba wanda ya damu da rikon D'an da ba nasa ba, saboda ganin Nauyi ne in ma ta barsa anan d'in shiyasa ba Gaddama akace zata iya tafiya da shi Har ga Allah na zata zata rika kawosa ko don yar'uwansa da suka Had'a uba sai kuma gashi Tunda ta saka kafa ta bar Karofi yau shekaru sama da Arba'in da Doriya bata Dawo ba.sannan shima Usman din bai nemi Dangim mahaifinsa ba har yau din nan kuwa"

Ba kuma wanda yasan inda suke ahalin yanzu"

Gabad'ayan mu muka sauke Numfashi Yaya Asiya tace"To Allah yasa yana raye"

Yaya mariya tace"In sha Allahu ma yana Raye kuma in dai da rai da rabo watarana zamu had'u da shi"

Muka amsa gabadayan mu da Allah yasa Goggo ta gyara zama tana fadin"Duk inda yake in dai jinin ku ne zai nemeku jini ai ba karya ba ne".

Muka jinjina mata kai alamun gamsuwa ni ko araina sai na samu kaina da addu'an Allah yasa yana raye domin shi kad'ai ne shakikin Tamadina anan duniya mu kuma kawun mu Namiji kwara d'aya tak da yau zamu bugi kirji muce muna da shi acikin raina ina addu'an in dai yana raye Allah ya bayyana sa da gaggawa.

Washegari da shirin tafiya muka tashi. kowa kagani da Kuzarinsa ban da ni,kwata kwata kamar an zaremin lakkan jikina,Goggo sai fad'a take min wai na kwazzabi kaina bana cin abinci Yaya mariya na wajen tace"Kuma zama da yunwa bazai taba Sauya komai ba..Tamadina ta rasu sai dai mu yi fatan Allah yasa tana kyakyawan karshe"

Sai hawaye ya kecemin suka shiga tsere bisa kumatuna, bayan mutuwar da ta dake ni,yayi sanadiyar tasomin da ciwona da daman kamar jira yake na shiga hali makamancin sa,Mun had'a duka kayanmu na yara Hafsatu ta wanke musu ta had'a musu ta musu wanka,ta shiryasu haka ma su Yaya mariya sai kuma sabon kuka ya tashi muka zauna mu hud'u muka ci kukan mu muka koshi,muka share Hawayen mu. Goggo tagaji da bamu baki ta Hakura ta koma gefe ta zuba mana ido bayan ta kira Yaya Isa tace yazo ya Dauketa ita da Hafsatu da mariya da Baba Ati, Yaya Asiya kano zata wuce nima kuma gidana zan koma.

Da azahar sai ga Hajiyar Dala,mun dauka ma bazata zo ba ne ahalin taji Rasuwar. tunda Goggo da kanta ta kira wayar ta,ta fad'a mata,Tazo tayi mana gaisuwa ta bama Yaya Asiya dubu goma Sadaka batayi awa d'aya ba,Ta ce zata tafi, nan take zencen zata karisa katsina Tare da Direba take jin Haka yasa Goggo ta kalleni tana fadin"Fa'iza tunda kun gama shiri,sai ki bi goggon taki tunda katsinar zata shiga"

Da Sauri tace"Aa ba gidan Saudatu zani fa gidan Wani abokin Major ne. mahaifiyarsa ta rasu zan biya nayi musu gaisuwa suma na wuce"

Ina jin haka nima murya a sanyaye nace"Ki bari kawai Goggo zan tafi da kaina"

Sai goggo ta jinjina kai kafin tace"Shikenan"

Daga haka tayi mana Sallama tatafi Goggo ce ta rakata har Dakunan matan gidan tayi musu gaisuwa, kafin Tafiyarta sai da ta dawo sannan Yaya Asiya ta bata kudin da Hajiyar Dala ta bata Goggo ta karb'a tana fadin"Kudin ku ne ai Asiya ba ni aka bawa ba"

Yaya Asiya tace"Goggo mu bama bukata ayi sadaka Allah ya kai Haske kabarin mahaifiyarmu"

Goggo ta amsa da Ameen itama fita tayi da kudin Dakin Maman isuhu ta shiga ta bata kudin Dakyar ta karba, Goggo tace kun yi wahala damu wajen kwana takwas ku karba ku kara Allah ya Rufa asiri .sannan ta karb'a tana sharan kwallah da kara fadin Allah ya jikan Tamadina.

Yaya Isa ya kira yace gashi nan zuwa,Shinkafa suka dafa mutam gidan suka zubo mana yaran aka zuba mawa suna ci ni dai bakina yayi nauyin  bana jin Dad'in komai kaina wani Dum dum kawai yake yi duniyar ma ba daidai nake jinta ba.

Kwatsam sai gasu Sa'adatu da Habiba sun zo min gaisuwa nayi mamakin zuwan su sai da aka gama gaisawa sannan na kalle su ina fadin"A ina kukaji rasuwar sannan waya kwatanta muku gidan nan..?

Sa'adatu tace"Ai tun da naga an kwana biyu baki dawo ba nace ba Lafiya Megidan ma nata jimamin abun.  yace haka kurum bazaki je ki zauna ba ko don makaranta yara da muka ga an yi kwana biyu sai yace bari yaje gidan kakaninsu su Amir yaji ko Lafiya. to chan yaji abunda ya faru wajen kanwar Baban su Amir ce domin ina ganinta tana zuwa itace ta fad'amai mahaifiyarki ta rasu sai ya Nemi ta kwantatamai gidan nan sai ta mai kwantance mun d'an sha wuya kafin mu gane,sai dai kinsan gidan mutuwa baya boyuwa balle da naga ba'a gane ba sai na rika kwantance da cewa Bebiya bata mgana sai ko gashi an kawo mu"

Na jinjina kaina,kwallah na Taruwa acikin idona makota na ne da ban had'a komai da su ba,Ammh sun nemi inda nake sun zo min gaisuwa Su mama kuwa tun ranar uku basu dawo ba,bana saka ma Yaya Ishaq a lissafi bai Dauke ni da Daraja ba,ballataana ya Dauki dangina da iyayena abun Daraja Har afili na nuna musu jin Dadi'na na nuna su ga sauran yan'uwana da Goggo suka dinga saka albarka har da gurasa Habiba tazo da shi ita kuma Sa'adatu sai ta Dafo Dambun Shinkafa da yaji Zogale Goggo ta karba ta kai ma Mutun gidan suna fad'in Allah ya bada Lada

A nan suka yi sallar La'asar sannan suka yi shirin tafiya sai nace su jirani mu wuce tare Lokacin Yaya Isa ya iso ya tafi masallaci ne,na mike na shiga uwar Dakin Tamadina na Dauko jakar kayan mu da Hijabina.da Yaya Asiya ta wankemim Goggo ta matsamin nayi wanka da Safe na fito falo na ce Hafsatu tazo ta sakamin Ahmad a bayana na goyasa ta sakamin shi har na saka zani na goyasa irin na D'ago kaina sai Duhu ya mamaye ganina na fara Laluban bangon gabana na rasa sai nayi luu ta baya zan fad'i sai  naji an tareni ana salati kuma hannuwana ne da yawa suka rikeni,Sama sama nake jinsu jiri ya rikeni da kaina da ya dauki wani irin azaban ciwo,Kamani sukayi na zauna Yaya mariya ta kwanto goyon Bayana Goggo fad'i take"Daman ni nasan yarinyar nan bata da lafiya, shigen zurfin cikinta yasa taki mgana"

Asiya kira min Isa yayi maza yazo in asibiti zai kaita ya kaita kada ta yi ma kanta Lahani bamu sani ba"

Ina nan zaune Dafe da kaina ina jin Sannu sannu na tashi Daga bangarori Dadama, chan jimawa na zame na kwanta naji shigowar Yaya Isa da Bayanin da Goggo take yi masa,sai yace a kamo ni muje asibiti a dubani.

Yaya mariya ta kamani muka fita mutan gidan na tambayan lafiya tace jiri ne ya kwasheni Maman isuhu tace"Daman daga ganinta bata cika lafiya ba itama"

Ni dai ina jinsu har muka fice muka shiga mota wani asibitin kud'i acikin gari ya kaimu shi ya shiga ya fita muka ga likita akan Lokaci gwajin Farko sai ga jini na ya yi sama Dari Biyu da Doriya sai ucler likitan nata fada ina so na kashe kaina da na fadi zan iya kamuwa da Ciwon barin jiki, ko jini ya haye yayi sama na mutu mgunguna ya bani bayan yayi min alluran jijiya ta ucler sannan yace na rika cin abinci sosai saboda kiyaye lafiyata.

Muna hanyar Dawowa Yaya Isa sai fad'a yake yi,Yaya mariya bata mgana sai dai kawai ta sauke numfashi tace"Uhm" abun yafi karfin ta wannan karon ko da muka koma makotana sun tafi sun so su jira dawowarmu Goggo tace su tafi Saboda Dare sannan sun bar iyalansu agida to sanadin haka komawa Katsina bata yuyu ba da Goggo ta kawo mganar Yaya isa ya maidani sai yace"Haba Goggo kalli Halin da take ciki fa..?,jininta yafi dari biyu a yadda take nan ko kanta bazata iya mora ba ballatana ga yara tare da ita,kawai mu wuce da ita gida in taji sauki sai ta koma"

Sai Goggo ta kasa musamai saboda taga Halin da nake ciki,Ni a motar Yaya isa muka tafi ni da Goggo da Baba Ati da yara su Yaya mariya da yaya Asiya da itama tafiya kano tasha ruwa suka hau ta haya mun yi sallama da mutanen gida muka rabu suna Hawaye muma muna yi.

Sai dare muka isa karofi ni dai abinci suka matsamin naci, nasha mgani na kwanta barci. Salolli na ma sai da asuba na rama su na ji saukin Jirin sai dai ciwon kan ne,Washegari Yaya Asiya ta koma kano Yaya mariya daman muna isowa ta wuce gidanta

Wasa wasa jikina ya ki dad'i har sai da na kara Sati a karofi Goggo na kula da ni,tare da su Amir kamar kada na koma inda na fito sai dai ba Dama ranar da nake da kwana bakwai a karofi Goggo ta saka Yaya isa ya maidani da Yammah bayan taga naji sauki,Tare da sha tara na arziki komai ta had'amin su garin kunu,garin Danwake,Wake,Tsaki,rama bushasshiya da Zogale sai Taliya yar Hausa da yara suke so sai ta saka aka Murzamin ta samin a kwali saboda kada ta karye hatta kayan maggi sai ta siyamin,da kayan miya mai yawa sannan ta saka Yaya isa ya kaini har gida ni da yara ina ta masa godiya shima da ya saukeni ya bani dubi biyar yace na rike sannan ya Jadaddamin naa kula da lafiyata na amsa mai da in sha Allahu.

Gyaran gidan na fara ko'ina duk yayi kura,Amir na tayani da kwashe kaya su Anum kuma sai dai su kara batawa,Adaran Taliya yar murji na Dafa mana na manja mai ruwa ruwa muka ci tare a faranti daya muma Santi muna gamawa bayan mun yi sallah na saka suka kwaso littafan makarantansu nace su duba tunda gobe zasu koma makaranta.

Wasahegari Laraba da wuri na shiryasu na kuma fita da su da kaina,Haruna da Sa'adatu da na leka gidan suka karamin gaisuwa da tambayan ya karfin jikina..?nace naji sauki sai hamdalar ubangiji.

Makota na dake kusa dani wad'anda ban taba ma shiga gidajen su ba sun shigo sun min gaisuwa daga suce Sa'adatu ta fad'a musu ko Habiba naji Dadi Sosai domin ba karamin masoyin ka ba ne zakayi rashin uwa yazo yace maka Allah ya kara hakuri kuma bazaka manta da wannan mutumin ba, wanda kuma bai ce maka Allah ya kara Hakuri ba,shima girman abunda ya aikata yana nan acikin ranka bazaka taba mantawa dashi ba.

Na dawo da kwana Biyu Anty Mamah tazo min gaisuwa tace ta zo sau biyu bana nan,nace mata eh nayi rashin lafiya ne tayi min gaisuwa ta kuma bani Hakurin sun yi tafiya ne chan dangin megidanta Kumo dake jahar Gombe ta jima muna ta Hira sai la'asar tatafi bayan nayi mana Danwake da manja da yaji taci ta koshi,sannan mukayi sallama washegari kuma daga makaranta Sai ga Badariya tazo min gaisuwa itama da ban hakura Mama bata nan bikin D'iyar Hajiya Barira k'awarta tatafi wajen satin ta daya Abuja aka kai Amarya, dagachan ta biya gidan su Zainab ta kwana biyu.

Sai kawai na samu kaina da cema Badariya"Sun dawo ne..?ya mai jiki..?

Badariya tace"Basu dawo ba suna chan jikin Farhan da sauki sun dai Tsaya Hutawar su kawai"

A fili nace"Allah ya dawo da su lafiya"

Daganan ban kara tofawa ba,Bata jima ba ta tafi tace saboda Mama yanzu in taga ta Dad'e sai ta fara fada, nace gaskiya kam ya kamata ta tafin kada dare yayi mata.

Mutuwar Tamadina ta Dakeni matuka,sai dai na zauna nayi Tagumi ina sharan kwallah in Amir yaga nayi Tagumi sai ya cire tagumin yana fadin"Umma ki daina tagumi ummanki zata dawo"

Sai ya bani dariya na jawosa jikina ina fadin"Aa bazata dawo ba Amir..Ai kasan mutuwa ko.?kuma a makaranta an fad'a muku duk wanda ya mutu ai baya Dawowa a rami za'a ha'ka a binnesa shikenan bazamu kara ganinsa ba"

Cikin yanayin mganar sa yace"Ita Umman ki a rami aka sakata..?

Sai na gyad'a mai kai Lokaci d'aya ina fadin"Eh mana..kowa zai mutu muma watarana zamu mutu a hak'a rami a binne mu baza'a sake ganinmu.Mu yi ma wadan'da suka rigamu mutuwa addu'a muma in mun mutu sai mu samu masu yi mana addu'a"

Ya gyad'a min kai kafin yace"To Umma zan rika yi ma umman ki addu'a"

Daman kuma ina yawan fad'a musu in sukayi sallan su rika cewa Allah ya gafartama iyayanmu da magabatanmu da yan'uwanmu,kuma suna yi,Har su Anum haka na koya musu nima in dai na yi sallah sai na Roki Allah ya jikan dukkan yan'uwa musulmai da suka rigamu gidan gaskiya mu kuma Allah yasa in tamu tazo mu samu cikawa dakyau da imani.

An yi addu'ar Arba'in Tamadina,Ni ban je ba Hakama Yaya Asiya su Goggo ne da Yaya mariya suka koma sai dai daga gida nayi mata addu'a da Sadakan Allah yakai haske kabarinta na Rokar mata salama da amimci a wajen Ubangiji a kabarinta,Ni tunda Tamadina ta rasu komai ya fita kaina naji bakowani wani abu ne zai rika batamin rai ba,Na riga nasan na rasa dukkan wani bangare na jin Dadi, Dariyata kadai ya'yana ke gan. sune kad'ai yasa har yau nake tsaye kan kafafuwana,Saboda hakane yasa na Dage da shan mgunguna saboda in nazo na kasa ko nayi Rauni ya'yana baza su iya d'aukan maraici tun suna da kananun shekaru ba. shiyasa karfina da Kuzarina duk Ta dalilinsu ne shiyasa ita uwa ya'yanta kan zama gwarin gwiwanta sau da dama.

Kwata kwata nama manta da mganar Form din da na cike na koyan sana'o'i da bada tallafi,na mikama Allah duka al'amarina,sai kwatsam Badariya tazomin da labarin an Turo mata sako Daga Kungiyar Women charity Foundation kan zasu tantancemu ranar asabar karfe goma na Safe a wata makarantar yan mata Dake cikin gari sai na rud'e na fara rawan jiki ina fadin"Bada..riya..To ni ya zan yi..?bansan ko'ina ba fa..?

Sai tayi Dariya tace"Sha kurum ki zan yi ma Mama karyan makaranta sai nazo na rakaki"

Sai da ta fad'i haka sai hankalina ya kwanta, tun daga ranar ko dayaushe addu'ata d'ayane in da alheri acikin wannan mafitan. Allah ya tabbatar min in ba alheri Allah ya musanya min da mafi alheri.

Sai naji zuciyata ta natsu da al'amarin,Ranar jumma'a Dakyar na iya barci Saboda Zullumin abunda zai faru gobe,Da sassaafe na shirya yara suka wuce Tahfeez nima ban zauna ba na shirya tara da wani abu Badariya tazo na goya Ahmad na saka Dogon hijiba na mai ruwan kasa duk yasha ruwa na rufe gida muka tafi,Ita ta biya kudin adaidaita gaskiya akwai tafiya ba kad'an ba tsakanin gidana da Makarantar mun isa goma saura Haraban makarantar cike da manyan motoci daga gani abun na manyan mata ne.

A wani babban hall na makaranta ake taruwa kai tsaye muka nufi chan mun shiga mun tarar da mata da yawa duk sunzo,muka samu waje muka zauna ina ta raba ido sai da goman tayi sannan Manya mata masu nasaba da ilimi da zati suka rika shigowa suka tsaya a gabanmu, ina ji Badariya namin Rad'a mai bakin mayafi mai jikan nan Hajiyar su Raliya ce na jinjina kaina daga gani kudi da isa sun zauna ajikinsu

A she mu Talatin suka Dauka,Bayan sun kira sunayen kowa da kowa muka mike gabad'ayamu akwai yan rakiya ire iren Badariya,Wata Hajiya ce mai glass take kiran sunaayenmu,na kasa Raunanun kunnuwa a ina jin sunana na mike bayan Badariya ta rike hannuna muka mike tare sannan ta koma ta zauna, ashe Wani kati zasu raba na na shedar Training d'in da zamu yi sannan da wasu bayanan da suka danganci abunda za'a koyar damu.

D'aya bayan d'aya aka rika kiranmu ana bamu wani karamin kati mai dan Fad'i.sannan akwai hoton kowacce ajikin katin har akazo kaina,na mike na kwanto ma Badariya Ahmad dake bayana na fita ina raba ido har gaban Babban ajin na mika hannu na karb'a ta kara kallona sama da kasa har na juya sai ta kirani da fadin sunana"Fa'iza Sidi karofi'

Sai na juyo da Sauri saboda ina gabda ita naji ta fad'i sunana yasa Hajiyar su Raliya ta D'ago tana kallona sai na rankwafa na gaisheta da girmamawa sai ta amsa itama cikin sakewa Lokaci daya tana fadin"Kece matar Brother din Badar..?

Sai na gyad'a mata kai cikin yanayi mganata nace"Eh hajiya tare..tare ma muke da ita"

Sai na juya ina nuna mata Badariya ashe har tataso dauke da Ahmad tazo wajen mu,Ta duka ta gaida Hajiyar Raliya ta amsa tana tambayanta Mama tace tana lafiya sai ta kara kallona tana fadin"Ashe tare kuka zo..?

Badariya tace"Na rakota ne Hajiya"

Kai ta jinjina tana kara kallona nasan har da mamakin ganin yanayina sai matar nan mai glass ta duko tana mata mgana naga tana nuna mata Takardan hannunta sai ta amsa tana Dubawa kafin tace"Fa'iza abu hud'u zaki koya..?kuma a ka'ida biyu ne kina ganin zaki iya..?

Da Sauri nace"Eh zan iya Hajiya.."

Sai dayan Matar tace"Hajiya kinsan dokace Biyu ne ai hudu yayi mata yawa da wanne zataji..?

Sai naga ta duka daidai kunnenta tana yi mata mgana sannan ta jinjina kai,Itama kuma Hajiyar Raliya sai tace muje mu zauna.

Komawa mukayi muka zauna ina ta Raba ido,naga mata kala kala ire irena masu fama da rayuwa da zamantakewar aure,ni dai akasan raina ina jin yakinin zan koyi duka abunda za'a koyamin Saboda shi kad'ai nake ganin gatana a wannan duniyan.

Bayan an gama bawa kowacce Katin ta, sannan suka fara mana bayanin yadda abubuwa zasu kasance zamu fara koyan abubuwan da zasu koyamana nan da sati d'aya zasu raba abun gida Biyu Mrning da Aftternoom,Da Safe za'a koyar da abubuwa Biyar da yammah ma biyar daman goma ne,Da Safe za'a koyar da girke girke da Had'a lemuka,Da yammah akwai koyan yadda ake hada halawa da dilka,Da yadda ake yinta,Da had'a Turaren wuta na Icce da Humra da su Kwallaca,sai na fara nazarin ya abubuwa na zasu kasance..?kenan sai dai na rika zuwa safe da yammah kenan..?

Sannan sun yi mana bayanin awa Bibbiyu ne da Safe tara zuwa sha Daya da Yammah D'aya na rana zuwa uku na yammah,sannan sun bamu shawaran mu natsu zamu iya duka abunda za'a koyar damu tunda na wata uku ne tsawon sati goma sha Biyu ina jin duk abunda suke fad'i Saboda da karfi suke mgana kamar su san da masu Laluran rashin karfi ji irina.

Sun tabbatar mana da cewa acikin mu za'a dibi mutane goma masu hazaka da aka ga sun chanchanta ranar da zamu gama za'a basu Jarin su a Hannunsu,sannan sun horemu da mu maida hankali komai daki Daki zasu koyamana duk abunda bamu gane ba mu yi tambaya. kada mu zama masu duhun kai,Sannan daga karshe sun ce zamu rika zuwa da Littafi da biro mu rika rubuta sunayen abubuwan da za'a koyamana saboda in mun koma gida mu yi bita,Sannan zamu rika rubuta sunanmu kullum inda muka zo da Turanci wato Attendence.

Sannan ko da wani lokaci zamu rik'a zuwa da wannan katin shine shaidar an tantance mu sai mun nunasa za'a barmu mu shiga, zuciyata na cika da Farinciki har na fara tunanin ma na iya duka abunda nasaka raina zan koya,ajikin katina  an saka Abunda nake son koya kamar yadda Badariya ta Rubuta, shi zai nuna inda ya kamata na tsaya sai Sha biyu  na rana aka tashi sun tabbatar mana da cewa kwararun ma'aikata ne zasu jagoranci wannan tafiya tamu mun yi godiya sosai sukace mu yi ma shugabar wannan kungiyar addu'a da fatan nasara Rayuwa, ni ko araina nace duk Sallah sai na sakata nace Allah ya yi mata gatan Duniya da lahira kamar yadda itama tayi mana gata a duniya.

Daga nan muka rabu da Badariya ta taremin adaidaita na Dawo gida zuciya ta cike da Farinciki,Sai dai na Fara Tunanin inda Zan rika kai Ahmad Saboda sun ce ban da yara saboda ba wajen da yara zasu zo ba ne,akwai abubuwan da bai kamata yara su shakesa ba yayin had'asa.

Sa'adatu ta fadomin rai nako shiga na gayamata ta tayani murna ta kuma tabbatar min na rika barin mata Ahmad zata kular min da shi sai naji Sauki na Dauki damaran maida Hankalina kan damar da Allah ya aramin,Naji dadi tun Sha daya zan dawo gida nayi ma yara girki ko na kimtsa gida da la'asar kuma in na Dawo sai naji da girkin su kafin su dawo makaranta.

Har wankin yaran sai da na kwashe na wanke na goge tare da nawa tunda zan fara fita ba lalle na rika samun Lokaci ba,Ranar Alhamis saura kwana biyu a fara koyar damu Yaya Ishaq ya dawo da Safe na sallami yara sun tafi makaranta kenan ina zaune afalo ina bama Ahmad kuninsa ya shigo ban ko ji sallamansa ba ina chan ina Lissafin duniya.

Sai da ya kariso cikin falon ya kara yin sallama sannan na jisa,na d'ago na kallesa,kamar ba shi ba ya kara Kiba har da karin Saje da gemu ga Tumbi alamun yana samun hutu da jin Dadi.

Kamar bakina na ciwo nayi mai sannu da zuwa bayan na kauda kaina.

Ahmad kuma sai ya fara dagamai hannu yana gaurancinsa.

Bakinsa na gogemai da Kyallen dake gefena shi kuma sai ya Duka ya Dagasa sama bayan ya sauke jakar Hannunsa, mikewa nayi ina kakkabe jikina zan wuce dakina araina ina fadin ka dawo adaidai kuwa.

Sai dai ban karisa ba ya D'aga murya kirani na juyo cikin mganarsa yace"Kin yi min sannu da zuwa baki dauki kayana kin kai min ciki ba.kuma zaki wuce ni kamar kin ga wani banza Fa'iza..?

Sai ban damu da kalamansa ba na koma na Dauki Jakar ya mike ina gaba yana baya ya bude shashen nasa. muka shiga a tsakiyar falon na Dire masa jakarsa na juya naji ajikina ya Juyo yana kallona ammh ban tsaya ba,Sai dai kuma har na fice bai yi mgana ba,dakina na koma na shiga kakkabewa ina gyarawa da na gama na koma Dakin yaran ina tattara kayansu da suka zubar ni kad'ai a araina ina auna abunda zan fad'a ma Yaya Ishaq akan fitar da zan rikayi araina naji wannan karon bazan iya Laushin da na saba yi mai ba.

Ina da Dakin yara naji yana ta kiran sunana da karfi na fito na iskesa zaune afalo Ahmad na jikinsa yayi barci a bakin kofa na tsaya ina jiran cewarsa sai ya kalleni cikin mamaki yana fadin"Kika tsaya min a nan kuma..?

Sai na kariso tsakiyar falon na Tsaya sai da yaga dama sannan yace"Ba wani abu ne agidan..?

Sai kai tsaye nace"Kamar na me..?

Da mamaki ya D'ago yana kallona cikin Hargaginsa yace"Ban sani ba..Wannan wani irin tambaya ne? tunda kikaji nace wani abu ina mgana kan abin ci ne"

Ni kaina bansan meyasa yanzu shakkanan da tsoron Yaya Ishaq suka Fita daga raina ba ,cikin Yanayina nace"Oh gaskiya bakomai sai ruwa Danwake nayi ma yara suka tafi makaranta dashi"

Wani kallon mamaki yake bi na da shi, mamakina ya hanasa mgana ni ko na shiga kitchen na Zubo masa Ruwan Famfom da ya bar mu muna sha,Na kawo mai a karamin jug da kofin Roba duk yaji jiki shi gareni saboda aciki zan basa araina kuma nace bazan Dafa maka komai ba domin bansan da zuwan ka ba.

Gabansa na duka na Sauke ruwan na kuma tsiyayamai na mikamasa sai yaki karba ya bini da kallo kafin yace"wannan ruwan fa..?

Ba na gora ba pure water ne..?

Kai tsaye nace"Babu muma wannan muke sha tun ba yau ba"

Sai jikinsa yayi sanyi cikin wani yanayi yace"Acikin Cefane babu ruwa ne yanzu..?

Nace "Babu.." daganan na sauke Kofin hannuna ganin yaki karb'a ina shirin tashi naji yace"Ashe Kuma Babarku ta rasu..?muna chan Mama ke fadamim..?

Kallon da nayi masa zan iya rantsuwa da Allah ban taba masa makwancinsa ba,da muka kusa shekara goma da Aure,Idanuwana na tsaida a kansa bako kyaftawa cikin wani irin amo nace"au ashe ne ma..?baka tabbatar ba kenan..?

Sai yayi saurin cewa"Kinga ba na son korafi Allah ya jikanta da rahma"

Da karfi na amsa da ameen Ameen Saboda addu'a yayi a gaban idonsa na Dauke Ahmad na shige da shi na Shimfidar na koma na zauna a gefensa ina auna waye yaya ishaq a wajena a tsawon wad'anan shekarun da muka dauka tare..?abu daya ya taba bani da zan kallah naji dad'i shine ya maidani Uwa ya bani ya'ya bayan wannan sai Tarin Tozarci cin mutumci kaskanci da Sauke Daraja da na Fuskanta a zama na dashi.

Ishaq shine sanadiyar da aure ya gama fita daga raina kwata kwata.




*Littafin KANA NAKA book2,3.paid book ne biya kudin karatun ki akan Naira N500 Regular posting sau d'aya a rana.*

*Ko kuma tsarin VIP 1000 Posting sau biyu a rana akan wannan acct din 0552179550 Jamila Umar Gt bank,sai a turo shaidar biya ta wannan lambar 09069067488 Wannan karon babu tsarin kati,kowani tsari zaka yi ka turo ta POS,Mutanen mu na Niger kuma zaku tuntubi Kausar Aglan Nissa ta wannan lambar +22796562223*




*Janafty*




*KANA NAKA..!*


*Wattpad:JamilaUmar315*

*Mallakar:Janafty*

*Arewabook:Jamilaumarjanafty*


*Gaisuwar Fatan alheri ga iyayen Janafty*


*Anty Habiba Abubakar Imam ikra*

*Anty Summayyah Abdulkadir(Takori)*

*Hajiya Hadiza Mahe muhammad(Mama)*

*Hajiya Halima Dalha Shehu(Umma)*

*Hajiya Hauwa Maman unwas(Mommah)*

*Na gaishe ku,Madallah da iyaye kamar ku,Allah yasa a gama da duniya lafiya Ameen*




         *🅿️18*


Na dauki tsawon lokaci aciki kafin na fito,domin nima sama sama barcin ne ya fara fizgata.ko da na fito falo baya nan, da na leka haraban gidan ba motarsa. sai hakan ya bani tabbacin fitarsa kenan ya tafi gidan Mama. domin ba inda yake zuwa da wuce wajenta,ko Anty Binta sun fi mgana ta waya ko su hadu gidan Maman.

Ban damu ba na cigaba da Harkokina, na riga na saka ma kaina yak'inin Tunda har ya zab'i iyalan zainab sama da nawa iyalan nima zan zab'i ra'ayina da ya'yana sama da shi mu ma Ture mganar aure a tsakanin mu sai dai a duba zumuncin da Allah ya riga ya had'a ,kuma shi sada zumunci Umarnin Ubangijine kuma shi Umarnin Ubangiji sab'a masa babban Laifi ne.

 Haka kurum naji ina sha'awar shan Faten Rama ina da sauran tsaki tun wanda na dawo dashi daga Karofi shi na Tankad'e na wanke na d'ora sannan na Jika bushasshiyar Rama nayi amfani Dashi bani da nama ko kifi sai nayi amfani da wake na watsa musu aciki,sai Faten yayi dad'i yana tashin kamshin kayan miya da Daddawa da su Citta,na juye a kula ni saboda bazan iya jiran yaran ba, sai da na Dib'i nawa muka sha ni da Ahmad sannan na sake yi mai wanka nima nayi muka sauya kaya shidda Saura yaran suka Dawo daga makaranta suka cire Kayan makaranta, suka sauya na gida sannan na zubo musu faten a faranti suka na suna santi,bayan sun gama Anum ta fara min labarin makaranta Musty kuma sai wasan zagayen falon yake yi Amir kuma kan kujera ya hau yana Duba Littafansa.

Anum wasa da kaina take yi,kalaba ne daman har ya kusa warware kansa ma, domin ni nayi ma kaina.Ahmad kuma na daka Tsalle saman jikina Amir yace"Umma ki dubamin aikin nan ban gane ba..?

Ya fad'a yana mikomin littafin rubutun sa  na karb'a nayi gefe da kaina Ahmad nata mika hannu da Sauri Amir yace"Umma karki basa zai ya ga min"

Cikin yanayi na nace"Bazan basa ba.Arabiya ne zan koya maka kabari ayi sallah mu natsa tukunna"

Ya amsa min da Toh ya karb'i Littafinsa Kiran sallar mangariba ya tadamu mukaje mukayi alwala mukayi jam'i gabad'ayanmu afalo bayan mun idar na d'aga hannuwana Ina addu'a Sai suma suka d'aga sai da na shafa sannan suka shafa na kalle su ina Fadin"me kuka rokar mana acikin addu'an..?

Amir ne yace"Umma a makaranta an ce mu rika ma iyayan mu addu'a"

Kai na jinjina masa ina fadin"Yauwa to ina so in dai kuka yi sallah ku rika rokar ma Umma Sa'a da nasara a abunda zata yi kun ji ko..?

Da Sauri Anum tace"Umma me zaki yi..?

Kanta na shafa ina fadin"Ba'a fada ma yara sai abun ya tabbata ke dai ki rika yi ma Umma addu'a ai zaki yi ko..?

Da Sauri ta d'agamin kai sai na Shafa kumatun ta ina saka musu albarkar acikin raina Musty da Anum har sun fara wasa na dakatar da su nace su karanta azkar din su,shiyasa suka natsu,Kiran sallar isha'i ya tadamu muka yi sallar tare sannan muka zauna mukayi addu'o'i Anum da karfi ta rika fadin"Allah ka bama Umma sa'a Allah ya bata gida da mota"

Sai ta bani Dariya Amir ya kwab'e ta da Fadi'n"Aljannah ake cewa"

Da sauri tace"Eh Allah ka ba ma Umma Aljannah "

Ba zato kawai Musty yace"Allah ka sa Umma ya hau jigi"

Gabad'ayanmu muka kwashe mai da Dariya idona ya ciko da kwallah na kama Musty na rumgume ina fadin"Ameen Ameen Allah yasa amsa bakin ku ya'yan albarka kuma Allah ya baku duk abunda kuke so duniya da lahira"

Anum ce ke gyara ma Musty sunan Jirgin da bai iya fada ba sai nanata mai take yi yana fadin Jigi sai suka sanyani Nishadi ina ta Dariya Tuni na manta da duk wani bakincikin dake Damuna. zuciyata ta dawo fara tas kamar farar takardan da ba'a taba yi  mata wani Dameji ba.

Falo na tattara su muka koma na hana wasan nace mza a dauko Littafan makaranta a duba sukaje suka Dauko na shiga Tsakiyar su,su kuma sun Zagaye Ahmad ne ya fara kiriniya zai yaga musu littafai sai na Daukesa na goya a baya na ammh duk da haka sai uban zillo yake yi shi sai ya sauka naki ko sauke sa.

Na Amir guda biyu ne Arabiya da na English na Arabiyan na koya masa,Sai na Anum littafin koyon bakake ne da aka saka su,siya itama na nuna mata yadda zata yi na Musty kuma na turanci ne sai Littafin da na saka ya Rubuta Huruful Hija'iya na Damki hannunsa ina koya mai rubutawa da Fadin su a baki, muna rubutawa muna fad'in su d'aya bayan da'ya sauran na turancin da ban iya ba nace Amir ya taimaka musu tunda shi yana primary 3 ne zai je hud'u Anum na 2, Musty kuma 1,Ahmad ne ya rage shima in da ina da kud'i saka shi zan yi, bakinsa ya bude achan kamar yadda Babansu yayi ma Anum da Musty.

Sai da suka gama duka aikin makarantan nasaka suka kwashe Littafan suka maida jaka suka maida su dakin su,sannan na zubo mana Faten nan a katon faranti muka Had'u muna ta sha Ahmad na kan jikina ina basa a baki Musty ma yasa ka rigima sai na rika basa Anum na ganin haka ta kwabe fuska zatayi kuka tace"Ni fa Umma"

 Sai itama na riga bata a baki Amir ne kad'ai ke shan abunsa da kansa muna cikin haka sai ga Yaya ishaq ya shigo da Leda sai dai yaran suka juya suka gansa kwatsam ni nama manta ko alama ban ce musu Daada ya dawo ba.

Haka suka tsallakeni suka nufesa Har da Ahmad,Amir ne kawai ya tsaya a tsaye sauran kuma jikinsa suka fad'a ya tarbesu yana fadin"Oyoyo ya'yan Daada"Anum sarkin Karad'i ta ce"Daada yaushe ka dawo..?mun daina ganinka ko da yaushe muna tambayan Umma sai tace baka nan".

Ina jinsu sai ya kasa bata amsa sai da ya kai ga zaune sannan ya Dauketa ita da Musty da Ahmad ya Dora zaman jikinsa Amir ya zauna agefensa yana fadin"Umman ku bata gaya muku nayi tafiya ba ne..?Kanin ku bai da lafiya jaririn Antynku muka kai Asibiti"

Da Sauri Anum tace"Jaririn Anty mai kyau"?

Sai ya gyad'a mata  kai,sai suka nuna tausayawar su Ledar hannunsa ya warware ya fito musu da Minti da Biskit wajen rabasu musu ne yaga Hannun Anum duk maiko ya shinshina sai yaji warin Daddawa da Sauri ya Dago kansa yana kallona ni kuma shan Fate na, na cigaba da yi kallo basu isheni ba.

Sai ya kalli Anum yana fadin"Me ye a Hannun ki Mamana..?

Da Sauri ta ce"Daada Fatee ne Umma tayi mana dad'i"

Sai ya k'ara kallona ya kuma kalli Farantin gabana cikin yamutsa Fuaka yace"Fa'iza meye wannan..?

Naji sa ammh sai nayi kamar ban jiba. sai da ya kara Daga murya yana fadin"Nace meye wannan kika bama ya'yana Fa'iza..?

Na dago kaina ido cikin ido nace"Fate ne" 

Saboda naga abun na sa kuma ya fara zama renin wayau faten ne bai sani ba..?

Ya maimaita sunan fate a ransa da Fili kafin yace"Me kenan..?ina mikewa nace"Abinci ne shima.."

Su Anum na kallah ina fadin"Kun koshi ne..?dukkan su suka d'agamin kai sai na nufi kitchen da shi nasan ya bini da kallo ammh ban ko waigo ba sai da na shiga na sauke abun hannuna na wanke hannuna na fito ina Fadin"kuje ku wanke hannuwan ku"

Kamar suna jirana suka sauka da gudu zuwa Daki har da Ahmad shi kuma sai ya kalleni yana fadin"Ina miki mgana kina basar dani Fa'iza?

A kaikace nace"na baka amsarka nace maka abinci ne"

Sai ya kasa mgana sai chan yace"Baku da abinci ne a gidan sai kin basu wannan abun sun ci hannunsu sai wari yake yi"

Sai ma ya bani Dariya na murmusa na gyara zama na akasan cafet din Falon ban yi mgana ba da kansa ya mike ya shiga kitchen din yaga bakomai Sai Dubaruna irin na mace mai ya'ya Shinkafa kad'ai ta rage mana itama ko Tiya bata kai ba,ba domin Goggo ta taimakeni ba da Tuni asirina ya Dad'e da Tonuwa a idon duniya domin tun da na dawo daga Rasuwar Tamadina k'waran abincin ban gani ba.tun Cefanen da yayi mana kafin ya tafi shima bamai yawa ba ne,ina jin ba shi da kudi a tare da shi ne lokacin.

Ina ganinsa ya fito cikin wani yanayi ya kuma daga waya ya kira Mama naji yana mgana ammh Dayake ban maida Hankalina akansa ba ban ji me yake fad'i ba.tunanina na chan inda mafita ta take, da Tunanin yadda komai zai faru jibi,Har na kosa ma jibin yayi mu fara kamar na matso da jibin gobe haka nakeji zumud'i kawai nake ji akasan raina kamar nama iya komai  haka nake ji.

Sunana naji yana kira da karfi sannan na Dago ina kallonsa cikin Mganarsa yace"Wani banzar Dabi'a kika samu ina mgana kina ji na,kina yi min banza..?

Kai tsaye nace"Kayi hakuri abun ka ga mara karjin ji sai hakuri"

Sai ya kasa mgana,Bata rai yayi yana Hararata kafin yace"Na rasa wata irin mace ce ke Fa'iza..?

Yanzu kayan abincin ku ya kare bazaki iya kiran Mama ki fad'a mata ba..?jamal baya gida yana makaranta ita nake turo ma kudin cefanan ku duk wata da kudin bukatun yara, ammh yanzu da nayi mata mgana tace bata zauna ba sannan bata san cefanen ya kare ba"

Kallonsa kawai nayi na kasa mgana shi kuma sai ya cigaba da fad'a yana fadin"Badar na zuwa gidan nan fa ko ita bazaki aika wajen maman ba..?Ko ke bazaki shirya ki je ki gayamata ba..?

Sai kawai nace"Kayi hakuri.."

Saboda na datse mganar ganin yaran sun fito kowanne da Biskit da minti a Hannunsu,Shima jin abunda nace ne yasa sai ya kasa cigaba da tijararsa,Daganan sai hankalinsa ya koma kan yaran yana ta tambayan su abunda suke so suna  fad'amai da labarin makaranta ni ko araina ina kara jinjina kaifin ikon Mama akan komai shi kayan abincin sai naje na Fad'amata ya kare kenan zata fidda kudin da ya turo mata ta siyan mana kenan..?kamar tana yi mana alfarma a raina daman na Guduri niyar ko zamu mutu da yunwa na gwammace duk mu mace da naje wajen Mama nace mata bamu da abinci.

Tara nayi na tattara yaran suka je suka yi shirin barci suka kwanta Anum ma da Ahmad na kwantar da su akan gadona,Na fito falo zan d'an gyarasa tunda yaran duk sun zubar da Ledojin Biskit din a tsakar falon na iske sa Lafe kan kujera yana waya a hankali yake yi shiyasa ban jisa ba sai na shiga abunda ya fito dani bayan na gama zan koma Daki sai ya kwalamin kira na Dakata na juyo ina kallonsa a kishingid'e yake sai ya Dago yana fadin"Naga zaki shige ciki ni me zan ci..?

Sai nayi shuru ban ce komai ba ya kara maimaita mganarsa ya karishe da fadin"ina jin yunwa kuma ban tsaya gidan mama naci abinci ba'

Cikin yanayin mgana tace"Sai Faten in zaka sha..?

Yadda yayi da fuska ne sai da naji kamar nayi dariya sai dai na kanne cikin kaushinsa yace"ki sama min wani abu"

Ko bakomai yaci darajan Zumunci da ya'yan da suka had'amu sai na juya zuwa Kitchen ina fadin"Sai dai shinkafa ita kad'ai garemu"

Ina jinsa ya mike yana fadin"Dafamin ki yi min source din miya tunda naga akwai kayan miya dare yayi ba na son na sake fita ne"

A daran nan ma dafamai Shinkafa araina ina kallon gas d'ina ina godema Wutar nepa ba domin anguwar da muke ana barin wuta ba, da tuni na raina kaina Gas ne mai shidda,wanda ke amfani da

Gas da Electric,basan shekara nawa na kwashe ina amfani da shi da wuta ba, tun Auran Ya Ishaq da Tarewansa a Abuja komai ya sauya,a baya yana mana Refliing ko ya aiko Jamal ya yi mana, ammh daga baya komai ya sauya sai da nayi da mai wuta,shi kuma baya da saurin girki,tunda bani da wata mafita hakanan nake hakuri da shi,Daman gas din Yaya Ishaq ya siya san da zamu dawo gidan.

Har goma da wani abu sannan na gama na had'a komai na kai masa shashensa a falo na sauke mai komai yana ciki ko bari ya fito ban yi ba na koma Dakina nayi shirin kwanciya,na kwanta sai barci ban farka ba sai asuba,bayan na idar da sallah nayi ma yara shirin tafiya makaranta saboda yau Jumm'a ne basa dad'ewa sai basu je da Kwandon abinci ba sai ruwa da na Dura musu suna shirin fita su yi ma Haruna mgana sai ga shi ya fito yace zai kaisu suna ta tsallen murna.

Shi ya kwashe shi suka fita ya kai su sai wajen goma ya shigo gidan,da amajirai guda biyu suna ta shigowa da kaya,kayan abinci ne ya siyo masu yawa har da Biskit din yara da Lemun su da ruwa har da kayan Tea wanda har yaran sun manta da shi sun saba da kunu har da su kwai kayan miya da kayan lambu,Dankalin Turawa da yawa haka ya siyo ina zaune ina karishe ma yaran guga afalo sannu da zuwa kawai nayi mai na juya na cigaba da aikin gabana har ya sallami yaran ya shige shashensa ya sake fitowa kayan na nan zube afalo ban kauda su ba cikin fad'a da bacin rai yace"Wai fa'iza wani salon iskanci kuma kika samo..?

Na dago ina kallonsa ya cigaba da Fadin"nine kike nufin zan kwashe wad'anan kayan ko me kike nufi..?

Ban ce komai ba na kashe soket din Abun gugan, na wuce na fara Daukan kayan ina shiga dasu ni ko na daina rawan jikin kan abunda bazai D'ore ba 

Sai da na kwashe duka na shirya komai a muhallinsa ina shirin na koma na cigaba da aikin gabana yace"ki sama min abunda zan ci"

Kamar nace zainab bata aiko maka dashi ba ne..?

Sai na fasa rashin kunya ba Halina ba ne sai na Tashi na shiga kitchen dafamai mai Dankalin Turawa nayi,sai nayi mai miyar kabeji da taji albasa sai na Dafa mai ruwan tea na Dafa mai kwai guda biyu kuma duka na Tattaramai ko abakina domin na koshi Faten jiya na dumama nasha abuna yaran, kuma Farar shinkafa na Dafamusu da Mai da yaji sukaci kafin su tafi makaranta.

Yana zaune afalon na kawo mai ya kalli Filet da jug din da na sanya mai Ruwan zafin kai tsaye yace"Gabad'aya komai naki ya tsufa Fa'iza..Ji kwanukan cin abinci sun fita Hayyacin su mtswww.."

Ya saki tsaki daga karshe ina jinsa ban ce masa komai ba na koma na cigaba da aikin gabana,sai da na gama na kashe komai na kwashe zan koma Daki naji ya daga murya yana fadin"Ki shirya in yara suka dawo makaranta zamu je gidan Mama a gabanta sai ki fad'amata in ni nayi miki iyaka da zuwa gaisheta"

Sai abun ya bani mamaki.matar nan Kwata kwata bata kaunar ganin kwanciyar Hankalina, burinta ta samo hanyar da za'a tozartani, to da ikon Allah kanta zai koma ni dai ina Daraja ta ko ban auri Yaya Ishaq ba. kamar uwa take gareni, tunda ta rikeni bata barni na yi rayuwa a titi ba sannan duk tsananin wuya da Dadi ta killaceni acikin gida rayuwata bata shiga tsaka mai wuya kamar na sauran matan da rashin gata da mafita yasa suka fada harkan banza ba,ballatana ina auran Abunda ta Haifa har abada bazan ki Darajata ba.

D'aya saura na rana yaran suka Dawo shi yaje ya Dauko su da kansa masallaci jumma'a ya tafi da mazan har da Ahmad ni da Anum mukayi tamu a gida,Shinkafa da miya Da salat nayi mana ni da Anum muka fara cin namu kafin su dawo suna Dawowa na zubo mai yaci tare da yaran,Suna ta Murnan tunda na saka musu sabbin kaya nace gidan mama zamu je.

Wajen uku saura na rana muka isa gidan Mama,Mun iske gidan cike Anty Binta,da su Halisa da Anty mahma da ya'yanta kamar ana biki yaran muna zuwa suka had'u da abokan wasa suka tafi suna ta wasan su.

Afalon kowacce tayi shigar alfarma har ta da Mama ko da taga jiya taga yau da na gaishesu dakyar suka amsa min gwara ma Anty mahma Halisa daman ita ta gaisheni har tana min gaisuwa,Ni da Badariya ne muke mgana kasa kasa kan gobe Badariya tace"Kin fad'a ma Yaya ishaq dai ko..?

Na girgizamata kai kafin nace"Ban fada masa ba ammh zan shaida masa yau in mun koma gida"

Badariya ta zaro ido kafin tace"in ya hana ki fa ?nasan Halin Yaya Ishaq barin ma in ya fad'ama Mama wlh bazaata bari ba"

Kai tsaye nace"Wannan karon bazai iya hana ni din ba"

Cikin mamaki take kallona bata samu zarafin mgana mukaji muryan Mama asama tana Sababi sai da na Saurara naji dani take tana cema Yaya Ishaq gatanan ka tambayeta yaushe rabon da kafarta tako gidan nan da sunan gaisheni.?

Anty Binta ta karbe da cewa"Ballatana ni banza abanza mama"

Shi kuma sai ya d'ago daga Danna wayarsa yana kallona Lokaci daya yana fadin"Shiyasa na kawo ta gata gani ta fad'a in ni nayi mata iyaka da gidan nan? Gata nan ni da kaina na yarje mata zuwa Gidajen ku duk sati ta gaisheku ita zaku Tuhuma me ke hanata zuwa"

Mama ta tabe baki tana fadin"Rashin mutumci ne ba wani abu ba.ko yaran nan bata kawo su, nace to in kai ne ma kake so ka raba su da nan gidan basu da inda yafi gidan nan a wajen su ta bangaran ta da take takama wa take dashi ?uwar tasu da ta rage itama Allah ya karbi a binsa sai naga karyan tsiya "

Idunuwana suka ciko da kwallah na kasa mgana zagi da cin mutumci ba wanda Mama batamin ba Anty Binta na tayata sai da Anty Mahma tace"Haba Mama ki barta hakanan mana ba ta baki hakuri ba"

Sai Mama tayi shuru tana Numfarfashi ni dai kaina na kasa ina bata Hakuri Saboda Yaya Ishaq yace na duka na basu hakuri in ba haka ba sai ya sabamin ban ki ba na Duka gwiwa Bibbiyu na basu hakuri dakyar suka Hakura.

Daganan suka yi kamar bana falon suka cigaba da Hiran su sai Badariya tajani Dakinta tana bani Hakuri na kalleta cikin wani yanayi kafin nace"Bakomai duk wanda yayi ma Aure bauta bazai taba tabewa ba..Sannan sakamakon sa na wajen Ubangiji"

Daga haka muka saki mganar mu kama wacce nake ganin zata Fisheni Badariya sai jinjina yadda zan rika zuwa sau biyu arana take yi.nace mata kada ta Damu zan iya ai nace Allah adakin ta nayi la'asar sannan Mama ta aiko wai nazo nayi musu abincin dare haka na kwabe Hijabi na shiga kitchen da Badariya ta shgo zata tayani Mama na ganin haka sai ta kirkiri aikenta sai bayan mangariba ta dawo Lokacin na gama Tuwon shinkafar har na kulle a leda Miya ce bata karisa ba.

Har ta Anty Binta sai da taci tayi guzuri Anty mahma dai da wuri ta koma gidanta mu kuma sai wajen goman Dare tuwon nan ko bakina ban ci ba,su Amir dai sun ci da Babansu duk na Takura na kosa na koma gida.

Kusan Lokaci d'aya muka fito da Anty Binta itama zasu wuce afalon Mama ta kalleni tana fadin"Wai ni kam fa'iza ina kayan ki da Ishaq yake miki ne..?bana ganin ki da su sai tsumma kike sawa"

Gabada'ya suka kalleni harda shi da Mama,Bai dai yi mgana ba sai Mama ce ta tabe baki kafin tace"Daman da Tsumman ta dace.aiko don yan'uwanta su zagesa zata rika mugun shigga alhalin daidai misali yana fita Hakkinta"

Har muka isa gida mganar Mama tamin Tsaye arai bayan wannan kayan Da Anty binta ta bani ko Hijabi Ya Ishaq bai kara dinkamin ba.ammh Mama ta iya bud'e baki ta fadi yana Fita Hakkina, Lalle gaakiyan masu iya mgana da sukace wata shari'ar sai Lahira.

Sai da duk nayi ma yaran shirin barcin daman ko da muka dawo su Anum duk sun fara barci,sannan na Dauki wannan Katin I.d card kenan na nufi bangaran Yaya Ishaq acikin raina ina jin cewa wannan karon bazan iya bin Umarninsa ko ya amince ko bai amince ba wannan karon ba gudu ba kuma ja da baya insha Allahu.

Na shiga na iske baya falo yana cikin Bedroom dinsa ba domin ni nake bukata ba,ba yadda zai sa na bisa ciki Tuni na kiyayewa kusantar inda yaya Ishaq yake saboda Dalilai masu karfi.

Bedroom din na shiga da sallama baya Dakin sai nayi mamakin to yana ina..?

Har na juya zan fita naji karan Bude kofa kii..Sai na juyo muka hada ido shima kallon da yayi min nasan na mamakin ganina ne.

Yana sanye da kayan barci riga da wando, masu taushi Farare na barci,Ya kariso tsakiyar dakin yana fadin"Lafiya..?

Har yana wani gimtse ransa kila yayi tunanin wani abu nazo nema sai yaga na mikamai abun hannuna ya karb'a yana zama gefen gado lokaci daya yana fadin"Wannan kuma na menene.?

Sai dai yayi mamakin ganin Hotona da sunana da dukkan bayanan abubuwana ajikin katin sai ya kara Dagowa yana kallona cikin mamaki ya kara fadin"Fa'iza duk wannan abun na menene..?

Sai na duka a gabansa na gyara zama na Dakyau kafin nace"Kune yan boko ka karanta Dakyau zaka fahimta"

Ya sake karantawa ya Dago cikin mamaki yana fadin"Naga Katin shaida ne na Training din da za'ayi na koyon sana'o'i daga karkashin kungiyar Women charity Foundation."

Shine nace ban gane ba naga hoton ki da sunanki shaidar katin naki ne"

Mirmishi nayi Cikin karfin gwiwa na fara mai bayani da yadda kawar  Badariya da ita kanta suka samo min form din na cike,da kiran mu da akayi wanchan satin mukaje da bayanin komai na karishe mganata da fadin"Gobe zamu fara koyan abubuwa kuma na tsawon sati goma sha Biyu ne,Sannan sau biyu za'a je a rana ni kuma abubuwan da nake so na koya da Safe ake koyar da biyu da yammah biyu kenan kaga a rana sau biyu zan rika zuwa kenan safe da rana"

Har na gama bayanina yana kallona cikin mamakina daya nuna har a saman fuskarsa,Cikin kaushinsa yace"Duk a yaushe kika fara yanke ma kanki hukunci yin wani abu batare da sanina ba Fa'iza?

Nima kai tsaye nace masa"A ranar da ka zabi wata matar sama dani.Nima aranar na zab'i yanke ma kaina da Rayuwata komai batare da na saka ka aciki ba"

 Maganata ta girgiza sa ya tsaya kawai yana kallona,ban damu ba sai ma naji kamar gwarin gwiwan. da na shigo da ita ta ninka wacce na samu yanzu tsoro ko fargaba sun fice daga raina kwata kwata.

Hanuna na saka na karbi katina daidai Lokacin da yace"Ni ki ke gayama wannan mganar Fa"iza..?Rashin kunya zaki yi min.?

Kai na girgiza kafin nace"Ko d'aya kada ma ka dauka ahakan Yaya Ishaq ai ko ba aure tsakaninmu kai yaya na ne,kuma babu rashin kunya har Abada tsakani na  dakai.kawai akwai lokacin da in mgana tazo a muhallinta gwara a fad'eta kawai da a barta tayi ta zama a inda ba Muhallinta ba"

Sai ya kasa mgana sai kallona yake yi cikin mamaki nasan aransa mamakin ya akayi na samun bakin yi masa mgana yake yi ni ko araina nace daga yau bakunan fa'iza sun bud'e kenan Har Abada.

Cikin Ajiyar numfashi yace"Naji yanzu meyasa kika fad'amin..?

Na gyara zama na nace"Saboda ya dace ka sani ko ba komai ina gadin gidan ka. 

da kuma kula da ya'yanka in fita ta kamani naa jera sati ba ma wata ba, yana da kyau ka sani d'in shiyasa nake shaida maka"

Kai tsayae yace"In kuma nace baza ki fita ko'ina ba na isa ko ban isa ba..?

Ya fada yana kallona cikin ido nima sai na Dago ina kallonsa bansan Lokacin da bakina ya furta"a wannar gabar Isar ka bata isa ba Yaya Ishaq.."

Sai ya zabura yana kallona cikin bacin rai ya nuna da hannu yana fadi"Ni kike cema isa ta bata isa ba Fa'iza"?

Sai ya mike yana Huci Lokaci d'aya yana fadin"Lalle kin fara rai na ni kin manta waye ni a wajen ki kenam? Gantalin da kika farayi na shiga makota yasa kika koyi rashin kunya da rashin Tarbiya ko..?

Sai nima na mike kai tsaye nace"Na fada maka kada kawo mganar rashin kunya a wannan muhallin saboda kai kanka kasan ba Halina ba ne yanzu ta kamane kasan wasu abubuwa.."

Cikin Hargagi ya katse ni bayan ya tasomin yana fad'in"To nace bazaki yi ba in kuma zaki nuna ban isan ba ne bismillah Fa'iza wlh sai na nuna miki Oder side of me da baki taba gani ba"

Ban bari ya sauke mganarsa ba nace"A matsayin ka na waye kake fad'in bazan yi ba..?

Yadda nayi mganar ta basa mamaki sai ya tsaya yana kallona Lokaci d'aya yana nuna kansa cikin mamaki yace"Ni ki ke fad'ama wannan mganar..?

Kai tsaye nace"Eh tambayar ka nayi a matsayinka na waye..?

Mirmishin gefen baki yayi kafin yace"Ina da matsayin yaya gareki sannan kada ki manta ni mijinki ne"

Nima mirmishin takaicin nayi kafin nace"Mijin jingina..?ko yayan da baisan Hakkin kanwarsa a kansa ba..?

Nace mijin Jingina Yaya Ishaq ka ke kira Miji..?

Mgana takara  girgizasa ban bari ya fita daga Girgizan ba na Dora da Fadin"a shari'an ce kai ba mijina ba ne yanzu.Saboda ka zabi wata matar sama dani,ka jingine aure na shekaru biyu kenan,ni matsayina kawai ina kula da ya'yan ka ne sannan in amtsayin Yaya kake mgana baka da wannan Hurumin saboda sai yaya ya zama nagarttace nagartansa zai yi yab'o har ta yab'anyan, da k'anwa bazata iya zarta da wani abu batare da yardan sa ba,Duka baka cike kowani Gurbi ba shiyasa nace isar taka bata isa wannan karon a wajena ba"

Baya ya juyamin ya kasa juyowa ya kalleni, ban damu ba sai nayi kokarin Dauke Hawayen da suka kawo idanuwana na cigaba da fadin"Tun Lokacin da ka zabi iyalan Zainab sama da ni da ya'yana.isar ka ta zama bata isa akaina ba, sannan tun alokacin na Zab'i ya'yana sama da kai,kuma tun  lokacin da ka zabi Dangin zainab Sama da Dangina nima na zabi Dangina sama da naka dangin, ban ce Dole sai ka amince ba ina fad'a maka ne Dole zan fita na nema ma kaina mafita Kuma Dolenka, ka kare mganar hakan daga bakin kowa in kana gudun fallasar Jinginannen auran mu zuwa kunnuwan da bazaka so hakan ba"

Shuru yayi ya kasa juyowa ni kuma da nagama mgana sai kawai na kama Hanyar fita cikin Shakewar murya yace"ya'yana fa wazai kula da su.?

Na juyo muna kallon juna ido cikin ido kafin nace"Nima ai ya'yana ne..Ni nake kula da su Lokacin da ka zab'i zainab da ahalinta sama da su.ai a yanzu ba'a wulakance ka gansu ba, nayi alkawarin zan kula da su domin nan duniya nice gatan su nima sune karfin gwiwata da dalilan da yasa nake zaune cikin kaskantataciyar rayuwa"

Ina gama fadin haka na bude kofa na fice har nakai dakina hawaye ne ke kwaranyomin sai na zauna agefen gado na rumgume abun hannuna a saman kirjina,na fashe da kuka,a hankali a hankali kuma ina samun salama da Sauki acikin zuciya ta.

Sama na kallah nace a fili"Allah kana ji kuma ka na gani.

Ya Allah ka sama min Mafita, mafita mai amfani a rayuwata da ya'yana. ka hananin jin kunyar duniya ka bani dukkan karfi da juriyan daukan duka Jarabawowinka."



*TASTED & TRUSTED*

*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATUN SAIWOWIN MUTANAN CHADI DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZAR AMARE DA WADDA TAKE SON GYARA KANTA*.

*AN GWADA ANGA INGANCINSA SHIYASA NA KE TALLATA MUKU DA K'ARFIN GUIWATA*.

*ABIN BIRGEWA DA WANNAN SAIWAR ZAKI YI AMFANI DA ITA SAMA DA SAU DAYA.*

*AKWAI FULL PACKAGE, AKWAI RABI, TA YADDA KOWA ZAI IYA SIYA*.

*SANNAN BABU BAURI NA TASHIN HANKALI.*

*DA KANKI ZAKI DAFA ABAR KI, KOMAI ANA SAKA WA A CIKI*.

*SHIN KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR, KO KUWA KE CE KIKE SON GYARA KANKI?*

*TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU*

*DOMIN KARIN BAYANI, SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*..




*Janafty*


*KANA NAKA..!*


*Wattpad:JamilaUmar315*

*Mallakar:Janafty*

*Arewabook:Jamilaumarjanafty*


*Fatan alheri,ga mutane masu kirki da karamci.*


*Aisha muhammad alto(Sisinah)Sannu barka da arziki kin yi kokari da kika Haifa min D'a,Allah ya raya mana Baby boy.*

*Fatan alheri zuwa ga Khadija Salisu yusuf(Ummina)*

*Halima yusuf gwarzo(Besty) ina miki fatan alheri*

*Nana Halima(Masoyiya)ina gaishe ki Fa'iza tace na fada miki,tana kaunarki kamar yadda kike kaunarta.*

*Ina gaida Uwar biyu Mrbb,Allah ya raba lafiya*

*Sannu gwana uwar Dakin gwanaye,Feedhom nace Allah ya sa afi haka.*

*An gaida Uwar Muwaddata da Anum Ramlat Abdurrahaman Manga,Maidambu,ina godiya Allah ya saka da alheri*

*Ina miki Fatan alheri Uwar Farha Fatima miss flower(Rabin raina).*

*Sannu Amina minajo na,Fa'iza na gaida Masoyiyar asali.*

*Sannu Anty maryam,Fa'iza tace nayi miki godiya,da shawarwarki ta fara sanin cewa itama Yar Adam ce.*


 

*Madallah da mutane masu karamcin irin ku,Nagode sosai Allah ya bar zumunci,ya kuma had'amu a aljannah* 




           *🅿️19*


Saboda Zumud'i ko fargaba zan ce, sai wajen uku saura na dare na iya samun, barci kuma cikin ikon Allah Kasala da nauyin jiki sun kasa barina na tashi na dauro alwala.

nayi salollin Nafila sai dai ina daga kwancen ban daina Hailala da ambaton Allah akan dukkan lamurana ba.

Washegari kamar yadda na saba tashi da wuri haka na tashi, na shirya yara na sama musu abun kari. sukaci sakamakon sun saba tafiya ba abinci,yau din ma haka suka tafi sai dai kamar yadda na sabar musu sai sunci sun koshi suke tafiya yadda kafin yunwa ta jigatasu, lokacin sun dawo gida sai na ba ma kowannen su Goran ruwan faro guda d'aya sun tafi da shi koda bukatar shan ruwan ya taso musu.

Suna tafiya nima ban zauna ba, na fara shiri falo kawai na gyara Dakin yara kuma nace sai na dawo nayi wankana na shirya kaina shima Ahmad na shiryasa bayan na Dama mai kokon sa. na duramai a wani karamin jug,Sauri sauri nake yin komai kada farkon fari kuma nayi latti na samu Tsoffin littafan su Amir da suka gama amfani da shi na Dauka da pencil saboda rubutu duk da ban iya Turanci ba, kuma ban iya Hausa ba, ai na iya rubutu da ajami kuma ina iya karantawa shiyasa ban damu ba.

 na tabbatar ma kaina duk abunda na Rubuta zan iya ganesa.

Na hada da katin  shaidana na goya Ahmad a baya na daukan mai wasu kayan. ko da ya bata na jikinsa na fito Falo Tara saura,naci karo da Yaya Ishaq a falon yana waya kallo d'aya nayi mai ban kara ba,shi kuma ganin kamar tafiya zan yi yasa ya katse wayar Hannunsa,ta gabansa na gifta cikin yanayin mganata nace"Ina kwana.."

Ina fad'in haka na kama hanya zan fice sai ya mike jiya ya kwana yana mamakina sai da yaga abunda nayi yau sannan ya amince da gaske nake yi,sai ya saka baki ya kirani da karfi na Dakata na juyo ina kallonsa kai tsaye yace"Ina kike shirin zuwa..?

Ni kuma sai naga kamar yana batamin Lokaci sai na juya ina fadin"In da na fad'a maka jiya..Ina Sauri ne kada na makara"

Na fada ina jimke dubu d'ayan da na Dauko cikin kayana sun sha ajiya tun Kudin da Yaya Isa ya bani ne Lokacin da ya maidoni gida, Dubu buya kad'ai na Taba ukun suna na nan ina Boye da su, sai da hakan ta faru na Daga hannu nagodema Allah domin zasu yi min amfani.

Kawai sai naga ya sha gabana a matukar fusace cikin d'aga murya yace"Ni kike nuna ma ban isa dake ba Fa'iza..?

Baya naja ina fadin"Ban ce baka isa ba.Sai dai na nuna maka isar taka ce wannan karon, bazata isa a wajena ba ka bani hanya na wuce ina bata Lokacina"

Sai ya tare hanyar ni kuma sai na kasa wucewa cikin Daka tsawa yace"Ki koma nace ba inda zaki je"

Sai nayi wani kayattacen mirmishi takaici na Fahimci in na zauna haka Ishaq zai cigaba da Nakasa rayuwata kamar yadda ya saba to wannan karon ya makaro domin d'an zaki ya riga ya girma.

Sai kawai na kallesa ido cikin ido kafin nace"Sai dai kayi hakuri wannan karon bazan ji mganarka ba.Na fada maka tun Ranar da ka zabi Zainab da Ahalinta sama da ni..Nima Daga wannan ranar na zab'i Rayuwata da ya'yana sama da kai"

Mganganuna sun dake sa sai ya kasa motsi har na raba ta gefensa na wuce abuna,Kafin na fita sai da nayi addu'an fita gida,sannan na karisa gidan Sa'adatu muka gaisa na kwanto mata Ahmad Allah yasa yayi barci ta karbe sa tare da kuninsa tamin Fatan Alheri daganan na fita na samu Adaidaita sai cikin gari.

Makarantar ta yan mata ne zallah suna barayin su sannan mu kuma inda zamu zauna wani babban aji ne, ko da nazo mata sun fara taruwa sai dai ma'aikatan basu riga sun kariso ba,na gaisa da matan dake kusa dani muka zauna jiran su tara da wani abu suka iso,,Rukuni rukuni suka jeramu a layi mun nuna katin shaidarmu sannan suka sanyamu a rukunin da zamu fara koyan abunda ya kawomu.

 Ni rukunin girke girken aka sanya ni shi zasu fara koyar damu sai sun gama sai ayi barayin Had'a lemuka da rana ne Rukunin Koyar da Turaren wuta da Had'a Dilka..

Sai na Fahimci da Safe duk abun ci ne zasu koyar damu shiyasa sai suka raba abun,Ni dai ban tsaya kalle kalle ba na saka ido sosai,ina Fahimtar komai masu koya mana Rukunin Farko,Su biyu ne dukkan su mata ne, Daga ganinsu sun san kan aikin su Sanye da Fararen riga da Hula na masu kirkin da muke gani a Kwatin Talabijin.

 Ranar farko wainar kwai suka koya mana da miyar gyada mai allayahu,sosai na karu na kuma rubuta sunayen abubuwan da suke fad'amana bamu gane ba,Suna yi suna yi mana bayani yadda zamu fahimta sannan in baka gane ba sai kayi Tambaya komai da komai na girken girken su, sun zo da shi suka kafa karamin Dakin girki a babban D'akin da muke ciki, nayi tambaya in da naga ban gane ba.kuma sun kara yi min bayani suna da Sauki kai matuka da iya mu'amala.

 Daman kuma Koyar damu ne aikin su, har kuma mh iya sun kuma tabbatar mana da cewa zamu iya girke girke masu kyau da inganci.bayan an gama dukkanmu muka D'andana mu biyar ne a rukunin Girke girken,muna ta santi saboda yayi dadi sannan da alkawarin in muka koma gida zamu gwada mu gani.

Sai rukuni na biyu Had'a lemuka,Zobo suka fara koya mana Had'ashi,Duk da na iya zobo sai naga nawa shirme ne ashe ga inda ake zobo nan,Ranar anan Rukunin ya kare shima sun bamu mun sha dad'i,Daga karshe sukace in da bamu gane ba mu yi mgana ni dai akwai karambani daman duk abunda ban ji ba sai da na tambaya suka kara gayamin,Ranar farko kawai da fara zuwana naji araina zan iya komai insha Allahu na dawo gida da Farinciki na iske Ishaq baya gidan ban Damu ba daman na fita da key da na ga ya Kulle gidan sai na bude bayan na Biya na Dauko Ahmad.

Ko girki ban yi ba Dakunan kawai na gyara na share, Lokaci yayi na makara ma a rukunin Rana sai d'aya da Rabi na isa har an fara an raba mutane kowa da Rukuninsa sai da na nuna Katina sannan aka kaini Rukuni na,Abu na farko da suka fara koya mana yadda zamu had'a Turaran kamshi na Icce ne ranar shi mukayi har aka tashi,shima in da bamu gane ba suna bamu ikon Tambaya in da kuma zaka manta sai ka Rubuta na dawo gida karfe hudu da Rabi na yammah na biya gidan Sa'adatu na kara dauko Ahmad sallah kawai nayi na shiga kitchen Saboda yan makaranta suna hanyar Dawowa.

Duk da na gaji ammh ban damu in dai aikin wahala ne na saba shi kuma ya zame min jiki,sai da nayi wanka sannan naji dadin jikina Yara suka dawo makaranta da yammah suna ta Tambayan Daadan su nace ya fita bansani ba,ko saboda abun da ya faru ne sai da yaran suka gaji da jiran sa, suka kwanta sannan ya Dawo ina Falo ina Tattara kayan da suka zubar daya shigo nayi mai sannu da zuwa bai amsani ba sannan bai kalleni ba. ya shige bangaransa a raina nace ko nace a banza.

Washegari ma ya rigani fita,Nima ko Lokaci nayi na yi tafiyata kamar jiya,Sai dai na Fahimce zan rika shan wahala in dai ina jeka ka dawo sai na yanke shawaran in mukayi sati uku, zan fara zama achan sai mun gama Rukunin rana sannan zan dawo gida gabadaya kud'ina kada su kare wajen adaidaita na rasa mafita.

Yaya Ishaq kuma tun daga wannan sa'insan tsakanin mu mgana bata kara Hadamu ba, ni dai ina fita Hakkinsa in mun had'u ina gaishesa shine baya amsani duka duka kwana Hud'u yayi ya koma ko sallama bai yi min ba. ganewar ma da nayi bai kwana agidan ba nasan duk tsanaani in dai yana gari to zai kwana agidansa.nima ko na tattarasa na watsar domin da gaske nake yi na zabi Rayuwata da Rayuwar ya'yana sama da tashi Rayuwar.

Na cigaba da zuwa wajen koyon sana'o'i na hankalina kwance kusan indai akace wannan abun shi kad'ai ne Hope din ka da Fatan ka to gabad'aya Tunanin ka da Rayuwarka zaka Dorasa akansa ne,ya kuke gani in hakan ta faru da mace irina da daman jiran mafita take yi..?to kamar misalin nice Domin na maida gabad'aya Hankalina da natsuwata kan abunda nake koya,Shiyasa duk nafi kowa ganewa a Duka Rukunina tun bamu Rufe wata ba Ma'aikatan suke yaba hazakata da Kokarina,Gashi abubuwa Hudu nake koya ammh kwakwalwata tana Daukan abubuwa dadama. sannan ina gane duk abunda aka koya mana.

 Muna rufe wata d'aya da Farawa na koma ina zuwa sau d'aya in na tafi sai Hudu nake dawawo saboda in aka tashi Rukunin Safe sai na zauna sai Rukunin yammah Tunda ma'aikatan suna nan suma ka'ida sai Hudu na yammah suma suke tashi, duk abunda muke yi suna daukan komai sannan suna Rubutawa saboda suna turama kungiyar Bayanan komai.

Yau da gobe zara bata bar komai ba kudin hannuna suka kare sai na koma takawa da kafata yara na fita makaranta nake fita da nisa sosai kafin na kai na jigata ammh hakan nake Daurewa na sama kaina yakinin ba wanda ya isa ko ya samu yana kwance, sai da ya fita ya wahala,Muna Hutu Ranar jumma'a duk sati sau Shidda kenan to ranar ne nake samun na gyara gida, har yi ma yara wanki da Sauran aikace aikace ni kaina nasan na Rame saboda wahala.

 Badariya sai da muka raba rabin watanninmu sannan tazo gida ranar wata jumma'a muka hadu a bakinta nake jin Anty Binta tazo sau biyu bana gida ta je ta fad'ama Mama sai Fada take,Tana fadamin Maman ta kira Yaya Ishaq din tamai mgana ba'a san me ya fada mata ba,basu kara mganar ba,Badariya tace ita dai tayi gum da bakinta bata tofa ba, tana ji Mama na fad'an na fara gantalin bin gidajen makota.nayi dariya nace gwara da kika yi shuru baki ce musu komai ba.

Araina naji mamaki ban Dauka Yaya Ishaq zai yi Laushi ba ni dai abunda na sani bazan zauna Damar da na Dade ina jiranta ta Kubcemin ba,Bandamu domin ba ta su nake ba ta kaina nake da ni da ya'yana. Badariya taji dadin yadda na fadamata muna koyan abubuwa da Dadama,sannan wahalata ta ragu saboda Sa'adatu ta Daukemin Laluran Ahmad sai abun yazomin da Sauki,Ban gayama kowa ba So nake ko yan Karofi na basu mamaki Fata na da Dakiyata azabeni cikin mutanen goman da za'a basu tallafi saboda zai yi min matukar amfani.

Yadda Yaya Ishaq ya tattarani da ni da ya'yana gefe d'aya.haka nima na tatrarasa na watsar Sai dai ya'yansa ban isa na cire musu tunaninsu akan sa ba,ko bakomai mahaifin su ne,ya zama Dolen su ni kuma ko da yake mijina ai ba Dole na ba ne,Na riga na jigata da tafiyar kasan da nake yi ammh ban ji ko sau d'aya na gaza ba nayi fashi sau Biyu shima Ahmad ne yayi ta zazzabi ba Halin na fita na bar shi kuma zuwa da yara an hana, shiyasa na zauna na Kula da shi har yaji sauki muna gabda cinye wattani ukun mu,Badariya ta dawo wajena da kwana ashe Mama da Anty Binta Abuja sukaje sulhu Zainab ta samu ciki sai suka yi sa'insa da Ishaq akan Farhan bai yi kwari ba, zata zubar da cikin shi kuma ya hana ita kuma sai ta Ture mganarsa ta yi mgana da mahaifinta yace ta zubar, tako je aka markadesa shine rigima ta kai su ga Har Ishaq din ya mari zainab din ai ko Badariya tace Mahaifinta ya Kira Mama yana fadin Ishaq ya gama marin auransa kuma sai yayi mganinsa sai ya yi kararsa a kotu,Ai ba jaka ya aura masa ba.shine Mama ta rud'e ta yi ma Anty Binta mgana ta rakata suka tafi Abuja su sulhunta mganar.

 A raina sai nace tun yanzu..? Auran barikin fa kenan,ai na Dauka ko me zainab tayi Yaya Ishaq zai yi hakuri da ita,tunda ita yar so ne kuma ita ya zaba ban dai nuna komai ba nayi fatan Allah ya Daidaita su Saboda ni bazan yi Dariya don haka ta faru ba Namiji ai duk inda yake yana amsa sunan sa na Namiji ne.

Wajen kwananta hud'u a gida na sannan su Mama suka dawo, sai ta koma gida Saboda harkan gabana nake yi yasa ban damu da na Bibiya ya suka kare ba,Nidai bana fatan tun yanzu auran su ya samu matsala ina Fatan su tara kyakyawan zuru'an da Yaya Ishaq yake mafarki da fata ko zai daina kallona a matsayin wacce ta zama Sillar shiga tsakaninsa da mafarkinsa da Burinsa.

Mun cigaba da zuwa muna koyan abubuwan da ake koya mana har ga shi yau da gobe bata bar komai ba zamu kammalah,Watanni uku kamar kwana uku ne a wajen Ubangijinmu,Ranar jumma'a muna Hutu asabar zamu gama gabad'aya ranar Lahadi kuma za'a sallame mu da Takardan shaidar abunda muka koya, a kuma wajen za'a bama wad'anda suka chanchanta tallafi.

Ranar jumma'an ina gida tunda bama zuwa ranar Sai ga Badariya da Raliya sun zo min da labari mai dadi bayan mun gaisa na kawo musu ruwa su Amir suna haraban gida suna waasa.

Raliya ta kalleni tana fadin"Anty Fa'iza ina tayaki Murna kin yi abu mai kyau, Hajiyar mu tana ta fad'amin a duk report din da ake kawo musu a duka Rukunin da kike Dauka kin zama zakara sosai ma'aikatan suke yabawa da kokarin ki"

Sai naji dadi na godema Allah acikin Raina Badariya na gefenta tace"Ai Anty Fa'iza ba daga nan ba Raly ni daman nasan zata iya"

Raliya tace"Haka na fad'a ma Hajiya..Nidai mun zo cin sauyin Sabon girki ne Anty Fa'iza me zamu samu..?

Na mike ina Dariya nace"Daman jiya alalan mai kifi da kwai aka koya mana yau daman ina da niyar gwadawa"

Ihu suka saka gabadayan su Badariya tace"a hada mana har da lemu mai Dadi don Allah"

Sai nace to a raina ammh ina Tunanin ina zan samu kudin kifi da kwai, tunda ina da wake kamar Badariya ta sani taja Raliya suka fita ba jimawa sai ga shi sun dawo da cefane har da kankana da kankara sukace Lemun kankana suke so nan da nan ko na shiga Kirchen na fara aiki suka shigo suna Tayani da hira da d'an taimakon da bazai gagara ba.

Nikan Waken Amir na aika ya kai mana makota muke da gidan nikan, kusa da gidan Habiba ne daman in dai aike ne ko nika kusa haka to Amir nakan aika Tunda ba nisa sosai,cikin awa uku muka gama alalan kwai da kifi na kuma had'a musu lemun kankana nan sukayi sallar mangariba suka zauna suka ci suna santi Raliya tace"Anty Fa'iza in da saura a samin a leda sai na kai ma Hajiyarmu alalan nan taci taji itama"

mirmishi kawai nayi daman na Mudu daya da rabi nayi na Dibar mata da yawa tace kowa sai yaci a gidansu ta karishe da Fadin"Zan miki tallah Anty Fa'iza dole mu bude Fa'iza Kitchen"

Badariya tace"Sosai ai Oder zamu fara yi wannan girki ai ko Hotel ko Restaurant albarka"

Haka suka yi ta zuzuta girkin da zasu tafi mukayi sallama suka tabbatar min da jibi zasu zo tunda taron a babban Hall din makarantar su ta Umaru musa yar'aduwa za'ayi.

Washegari da mukaje gwaji dukkanmu mukayi,Ma'aikatan duka gefe suka koma suka bar mana abunda zasu yi ranar, Kunun gyad'a muka yi bangaran abun sha kuma ni na zama zakaran rukunin mu sai bangaran girki kuma yam ball muka yi ma'ana Fanken doya,shima ni na zama zakara na Rana ma rukunin hada Kolaccha  ma ni na Jagoranci Rukunin mu,haka bangaran had'a Dilka da Halawa anan wajen muka mulkama kafafun mu da Hannuwan mu,wasu har da Fuska ni dai ban saka ba,Sannan mun had'a Turaren Humra na ruwa mai kamshi shima muka goga a jikin mu saboda muji yanayin kamshin,Ranar sai Yammah na dawo gida su Amir gidan Sa'adatu suka zauna sai da  na dawo.

Ranar Lahadi kuma na fada ma su Amir su yi min addu'a yau zan gama abun da nace musu ina yi suka yi ta cewa Umma Allah ya baki sa'a na amsa da Ameen.

Saboda taron gamawa ne Tare da Ahmad naje bansan makarantar ba, mai adaidaitan ya kaini hall din ba Boyayye ba ne ina zuwa na tambayi inda ake taro wasu yanmata suka nuna min, da wuri naje wasu duk basu zo ba ammh naga wasu daga cikin mu.

Karfe sha d'aya aka fara taron manyan mata masu alaqa da kungiyar duk sun zo ciki har da Hajiyar su Raliya na ganta ba su gayyato yan jarida ba Saboda basa son duniya ta sani su don Allah suka yi,Sai mu kawai da muka samu Horan sai kuma yan'uwan wasu daga ciki da ma'aikatan da aka Dauka suka koyar damu sai yan kallo.

Su Badariya sun zo su da gayyar kawayen su sai dai hannu suka Dagamin, tunda su suna baya mu kuma gaba akace mu jeri mu Talatin din da muka samu Horan.

Bayan jawaban godiya da kuma Fatan alheri ga wannan kungiyar aka gayyaci wata Hajiya Zubadai  itace kamar ma'ajin kungiyar reshen Jahar katsina ta fito tayi jawabi akan manufar kungiyar da kuma manufar taron da suka shirya garemu na mata talatin da suka koyar da su sana"o'i goma.

daganan aka bata sunayen mu ta rika kiran mu d'aya bayan d'aya muna karban Takardan shedar abunda muka koya ni ce ta goma acikin wad'anda ta kira Fa'iza sidi karofi. Dayake tana amfani da amsa kuwwa abun mgana, najita na fita Ahmad na goye a bayana ta bani Takardata sai da nayi Hawaye,Ina gani wata ta kusa da ita nayi mata rad'a a kunne ta kalle tace"Fa'iza sidi karofi ko..?

Na jinjina mata kai sai ta bani Hannu muka gaisa cikin kayattacen mirmishinta tace"Weldone Fa"iza"

Duk da ban ji me tace ba nasan yabo ne sai na jinjina mata kai sannan na koma na zauna,ina Duba Takardan Hannuna da Turanci ne sunana kad'ai na iya ganewa aciki,ammh nasan ko a hakan na tsaya na cinma wata gagarumar nasara a rayuwata ba Nakasashe sai Mai nakasar zuciya, sannan akace babu maraya sai Raggo. in ka tashi ka nema bayan ka bama Allah zabi to shi kuma Allah zai saka maka da kyakyawan sakamako.

An cigaba da kiran mu har zuwa ta karshe sannan wata Hajiya laila daga kaduna itace mai rike da mikamin P.R.O na kungiyar ta fito zata bada shedar girmamawa ga wad'anda suka zama zakaru a rukuninsu,Allahu Akbar ban taba zata ba, Ba zato ba Tsammani naji sunana Fa'iza sidi karofi na fita aka bani wani d'an kwalba mai ban sha'awa da sunana ajiki sannan matar ta tsaidani tayi jawabi da turanci sannan tayi da Hausa tana mgana akan cewa ina da Hearing problem, sannan ban yi boko ba.ammh na iya zama ta farko a fanni masu kokari a dukkan abunda na Koya, sannan ta sake bani wani abu nazare a wuya na ta makalamin na Girmamawar na koyi abu hudu masu wahala a acikin wattani Uku,Sai tafi raf raf ta bani Hannu muka gaisa har tana yi ma Ahmad dake bayana wasa ko da na koma na zauna sai na daga hannuwana sama ina fadin"Allah na gode maka..Alhamdullahi ya Allah dukkan wata ni'ima daga gareka ne"

Matan dake kusa dani suna ta min murna ina amsawa bakina har kunni na juya ina hangen su Badariya ta D'agomin hannu na Daga mata kyautan da takardan da aka bani, ita kuma sai ta Dagamin babban yatsanta alamun jinjina.

Bayan ni an kira mata uku suma an basu lambar girmamawa ta zama zakaru a rukuninsu,Daganan an wakilta uku daga cikin mu suka fita suyi jawabin godiya ni dai nace bazan iya ba Saboda ban taba fita gaban jama'a nayi mgana ba ko karban kyatuttukan ma Dakyar na iya fita kamar zan fadi haka na rika ji.

Ma'aikatan da suka koyar damu suna sun yi jawabin godiya ga wannan kungiyar sannan sun gode mana Bisa yadda muka basu had'in kai har muka koyi abunda ake so mu koya har kwalliya ta biya kudin sabulu.

Daganan sai suka koma gefe suna mganganu bayan minti goma aka sanar da kungiya ta ware zakaru guda goma da kungiya zata bama tallafi,Sauran kuma da ba'a basu ba,ba domin ba su kai ba ne a'a haka tsarin kungiya take suma nan gaba zasu iya samu.

Gabana sai ya fara fadi na riga nayi yakinin ko ba'a bani ba bazan bari abunda na koya ya tafi a banza ba sai ga shi nice ta Biyu Fa'iza sidi karofi Hawaye sharr suka zubomin na kasa sharesu bakina har kunne na fita. Kudin a Farar takarda ne an nade sannan ga sunan kungiyar ajiki Hajiyar su Raliya ta bani na Duka har kasa zan karba sai kawai na Daidaici gabas duk da goyon Ahmad dake bayana ban damu ba nayi Sudujul Shukur sai Hall din ya Dau Tafi da kabbara ina dagowa ina hawaye Shabe shabe na saka hannuwa bibbiyu na karb'a sai ta bani abun mgana tace nayi godiya,muryata ta shake ga kuka sannan ga yanayina cikin mganata nace"Alhandulillah ya Allah Godiyar ta sace.Domin abu mai kyau ko akasasin sa daga gare sa ne,Ina godiya ga wannan kungiyar na gode..Madallah da mutanen kirki, madallah da mutanen kwarai masu karamci.

Nagode Allah ya jibanci lamuran ku, kamar yadda kuka jibanci namu Allah ya suturtaku kamar yadda kuka suturtamu Allah ya albarkaci dukiyar ku da ya'yan ku da iyalan ku gabadaya, Allah yasa wannan aikin taimakon naku ya zama mizanin ku a gidan Aljannah..Nagode Nagode, na yaba ubangiji ya gani sannan yafini yabawa"

Ina ma wannan kungiya fatan alheri Nagode"

Duk da mganar bata fita sosai ammh sun fahimta sai tafi su kuma suna ta amsawa da Ameen,ina tahowa muka had'e da Badariya muka Rungume juna Fadi take"Congratulation Anty Fa'iza"

Ahmad da yaji matsa sai kuka na Sauke shi ta Dauke sa ta dagasa Sama tana fadin"Kai yau ranar farin cikin Umman ka ne ba kuka"

An ta kiran sauran ana basu suna addu'a mata da yawa muna cikin wata Rayuwa masu kuka in an basu suna da yawa,asauran da ba'a basu ba suma ance kungiya zata san abunda zatayi musu daga karshe sun horemu da mu tashi Tsaye mu mori abunda muka koya, acikin Gidajen mu da kadan kad'an watarana sai mu zarce Tunanin mai Tunanin sun Hore mu kada mu zama ballagazun mata mu zama mata wad'anda zasu iya shiga ko'ina saboda kansu da ya'yansu. maraici ba komai ba ne in dai mace ta mike ta nema to zata samu da yardan Allah,Sannan sun horemu da mu gyara kanmu mu zama masu tsafta da kwalliya da ado saboda kada mu zama Borori a gidan mazajen mu, ni dai ban bi ta kan wannan mganar ba saboda da mata masu kyau da nasaba ake yi ba irin mu da muka ke da nakasu a komaii ba, abu daya na sani wannan wajen da nazo ya kara Budemin ido akan rayuwa na Fahimci harkan nema ba bambamci mai kyau ko mara kyau in ka iya kawai ka Huta.

sai biyu na rana aka tashi Taron Haka Badariya da Raliya suka rikamin Gayya gayyan kawayen su muna gaisawa,Badariya ko bata gajiya da Fadin matar yaya na ne fa Sai naji wani abu ya soki raina ko yayan nata bai taba nunani haka acikin mutane kamar ta ba, shiyasa nake kaunar Badariya kwatankwancin yadda take kaunata.

Nayi sallama da matan da muka saba dasu yayin koyan abubuwan da muka koya,Ban samu ganin Hajiyar su Raliya ba suna cikin mutane sai nace Badariya ta bari ta rakani har gida nayi mata godiya.

Ranar saboda farinciki ina komawa gida na tasa kudin nan a gabana ko Bude su ban yi ba ina ta ma Allah kirari da Hamdala,Yara suna Dawowa makaranta na rika daga su sama ina Juyi afalo fad'i nake yi"Umma tayi nasara ya'yan Umma..nayi nasara"

Sai suma suka rika murna suna tsalle Har da Amir ma kamasu na Rumgume hawaye suka gocemin komai na zama a duniya ya'ya ne karfina da ba domin su da ban san kuma ya zan yi ba.

Na shiga gidan sa'adatu washegari nayi mata godiya kwana uku tsskani Badariya tazo mukaje gidan su Raliya chan kusa da anguwan su Anty mahma ce nayi mata godiya tana yaba'min har tace Raliya ta kawo mata alala yayi dadi suna bada girke girken Suna ko Birthday, ko biki in sha Allahu Zata saka arika nema na nace nagode sannan tace nayi shawara da mijina ko yan'uwa na samu wani abun sana'a na siya da kudin hannuna wanda zai taimake ni kada na kashe su a banza nace mata in sha Allahu,muka yi mata sallama ta bani sabulai da Turare kamshi da kudi tace na siya ma Ahmad sweet muka fito ina ta yaba kirkin matar a hanya nace Badariya in ta na da kudi a waya ta kira mun Goggo tace tana da shi,ta ko daga waya ta kirata bayan ta Dauka ta ma zata Hafsat take nema sai tace mata tana bayi

Bayan sun gaisa,Sai Badariya tace Fa'iza ke son mgana da ita.

Yadda Goggo ta jini cikin farinciki yasa ina cewa ina son ganinta tace"Zan zo in sha Allahu gobe daman kamar kin san cikin satin nan nace zan leko na dubaki,najiki cikin farinciki fa:i daga gani wani babban albishir ne ko Ishaq ne ya biya miki Umra".?

Bansan Lokacin da na kyalkyace da Dariya ba,Itama nasan zolayata take yi.muka rabu akan sai tazo, daganan Badariya ta nufi gida nima na Dawo gida.

Kwana Biyu tsakani sai ga Goggo Ya Isa ya kawota da Safe bayan mun gaisa na basu ruwa na Dauko kudin da Kyautar da aka bani da Takardan shedan abunda muka koya, na sauke gabanta lokaci d'aya na kora mata jawabin komai bakina har kunne Goggo ta Dauki kudin ta farke ta Fiddo su sabbin yan Dubu Dubu ta nuna ma Isa tana fadin"Isa kaga Bud'i daga Allah ko..?.

Yaya isa ya karba ya gani duka kayan ya jinjina kai kafin yace"Lalle Fa'iza na tayaki murna dakyau"

Goggo tace"Duka kyauta Fa"iza..?

Na gyada kai ina Mirmishi Goggo tace"Masha Allah..Allah ya saka musu da alheri Allah ya biya su kudin nan sunzo a daidai daman mun yi mgana da Sauran yan'uwanki nace su had'a miki kudi wanda zaki rike ki fara wata sana'ar zama haka bazai yuyu ba,sai kuma muka ga abun alheri ai shikenan ma fad'uwa tazo daidai da zama kenan"

Goggo tace na ijiye kud'in zata koma in na chan sun hadu zata sake dawowa,na tambayi Goggo dame zan fara na sana'a?

Da sauri Yaya Isa yace"Ki fara da sai da zobo da Kunun aya, da ruwa tunda kin koya kuma kin iya sauran sana'o'in ko daga baya sai ki fara bazai gagara ba"

Nima na yarda da shawaran sa haka ma Goggo sun tafi da niyar goggo zata kawo min kudin in su hada na bangaran su.

sai na had'a dashi Tare da Yaya Isa zasu kara dawowa.sai ayi shawaran Fridge din da za'a siya mai kyau, wanda zan fara sana'ar dashi.



*TASTED & TRUSTED*

*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATUN SAIWOWIN MUTANAN CHADI DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZAR AMARE DA WADDA TAKE SON GYARA KANTA*.

*AN GWADA ANGA INGANCINSA SHIYASA NA KE TALLATA MUKU DA K'ARFIN GUIWATA*.

*ABIN BIRGEWA DA WANNAN SAIWAR ZAKI YI AMFANI DA ITA SAMA DA SAU DAYA.*

*AKWAI FULL PACKAGE, AKWAI RABI, TA YADDA KOWA ZAI IYA SIYA*.

*SANNAN BABU BAURI NA TASHIN HANKALI.*

*DA KANKI ZAKI DAFA ABAR KI, KOMAI ANA SAKA WA A CIKI*.

*SHIN KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR, KO KUWA KE CE KIKE SON GYARA KANKI?*

*TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU*

*08032773332*

*DOMIN KARIN BAYANI, SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*..












*Janafty*



*KANA NAKA..!*


*Wattpad:JamilaUmar315*

*Mallakar:Janafty*

*Arewabook:Jamilaumarjanafty*


*Madallah da gidajen Sada zumuntar dake cike da mutane masu karamci,Naji dad'i sosai ina ganin sharhin ku Janafty tace Son so.*


*JANAF NOVELLA.*

*SURRAYYA DEE FANS.*

*KANA NAKA COMMENTS SECTION.*

*SABO DA KAZA COMMENTS SECTION.*

*TAKORITES.*

*JANAFTY'S.*

*JANAFTY GIVEAWAY ROOM.*

*ZAUREN KHADIJA CANDY.*

*KITTY NOVELS.*

*BENEFICIAL WRITERS.*

*FEEDHOM NOVELLA.*

*MY WATTPADIAN PIPU,FA'IZA TACE SANNUKU DA KOKARI.*


*Kuna da yawa baki ma bazai kirga adadin ku ba,ammh Fa'iza taji kuma ta gani,tace na fada muku ana kyawun tare.*

*Tagode kwarai Allah ya bar zumunci da kauna*



          *🅿️20*


Ranar da Goggo suka zo suna tafiya,da yammah sai ga Yaya Ishaq ya dawo,wanda rabon sa da garin tun zuwan da yayi muka yi sa'in sa kan Fita, gashi har mun gama.kimanin wata uku kenan baya nan, ammh a haka har yana da kwanjin son ya zaunar dani a gida, sannan yana da bakin fad'in mgana kan ya'yan sa. ya'yan da in ya saka kafa ya tafi mantawa yake yi da su, ba domin Allah da Dubaran mu na mata ba,da Tuni wata mganan ake yi ba wannan ba.

A she tare da zainab suka zo ban sani ba,Sai bayan ya fita ya dawo da Daddare yaran suka nufesa suna murnan ganinsa ni bai min mgana ba ko a d'azun da ya shigo na gaishe shi bai amsani ba sai dai ya kalleni ya kauda kansa, sai dawowar da ya sake yi ne bayan ya raba ma yara tsaraban Sweet din da yazo musu da shi, ya fito yana fad'amin na shirya yanzu ni da yara zamu gidan Mama na gaida Zainab tayi rashin lafiya an yi mata aiki an cire mata tsakuwar ciki, da kamar zan ce bazani ba. sai kuma na fasa ban yi mgana ba yaran suna ta murna ni kuma sai na Had'e rai na ko Kyallin Fara'a ta bai gani ba.

bayan sallar isha'i yazo ya kwashemu sai gidan Mama.

Naga abun mamaki Mama haka take rawan jiki akan Zainab da Farhan kamar zata kwanta mata,afalon Mama muka sameta an kara mata filo ta ma fa warke,ammh Mama ji da ita take yi shiyasa taki bari ta sauka a gidan saboda acewarta na fara halin gantali bazan kula da ita ba sosai gata ba ta da lafiya mun zo ba Dadewa sai ga Anty Binta ta iso itama dai kamar Maman kamar zasu maida Zainab ciki

ni dai Farhan na dauka ina mamakin girmansa har ya fara Tafiya fari da shi Dumur mur kamar yaron Turawa ko da yake meye maraban sa da Turawan..?sai bangalamin Dariya yake su Anum suna mai wasa yaana kara sakin Dariyan su na yara.

Mun gaisa da Zainab nayi mata sannu ta amsa min ina d'an nesa da ita ne bayan mun gaisa sai na sauya wajen zama ina rike da Farhan a hannuna Anum tazo ta rikemun hannu tana fadin"Umma Anty tace kizo"

Sai na Dago ina kallon Zainab sai ta yafito ni da Hannu da zan tashi sai Farhan ya sauka kasa yabi Anum da ta mai chakulkuli ta gudu ,gefenta na samu na zauna ashe Mama da Anty Binta suna kallon mu bansani ba.

Gaisuwa take so tayi min bayan ta muskuta daga zaunen da take ta kalleni tana fadin"Kwanaki Honey yake fadamin maman ki ta rasu ko..?

Sai na jinjina mata kai cikin Tausayawa tace"Ayya sory for d lost..Allah yajikanta da gafara"

Da karfin gwiwa na amsa mata da Ameen,ita ta cigaba da ja na da Hira ni sai dai nayi yaken Dariya sai korafin take yi ban taba zuwa Abuja ba, ammh ita tazo ta sauka wajena yafi a kirga ina Dariya nace"Megidan ne bai taba min tayin zuwa ba"

Cikin mamaki tace"Kai.!Ni kuma Honey ce min yayi kece baki son zuwa fa"

ban yi mamakin mganarta ba,sai nayi Saurin cewa"Na bari sai kin haifa ma su Anum kani tukunna, Farhan ya girma yana bukatar kani ko k'anwa"

Sai ta zabura Lokaci d'aya tana Fadin"Aa bazan iya ba maman Amir ai ko ke naga kokarin ki da'yan ma is ok"

Ni dai ina ta Dariyan mganarta a raina nasan zasu kwashi yan kallo da Yaya ishaq shi da mafarkin sa kenan auran mace mai kyau da samun ya'yan Turawa,ga shi ya samu sai kuma ya fara ganin mike ai bazata sabu ba,Anty Binta da Mama kamar su mutu da bakinciki ba so su Zainab din ta sakarmin ba sun so yadda suke min wulakanci itama ta wulakantani sai Allah ya fisu.

Ammh duk da haka basu kyaleni ba, su dai in basu tozartani ba basa jin Dad'i a gaban Ishaq din da Jamal da yace cikin satin nan ya dawo Badariya ce kad'ai  bata nan tana gidan Anty mahma,Allah yasa yaran suna chan suna wasa hankalin su baya kanmu Mama ta kalleni cikin yanayin kaskancinta gareni tace"Ke kuma wani gantalin kike zuwa kwanaki Binta tayi ta zuwa bakya nan..?

Sai na maida kaina kasa na kasa mgana Domin nayi alkwarin bazan ce mata komai ba..

Anty Binta ne tace"Ai bazata fada miki ba ta fara zama gagararriya.Shi kan Shi Ishaq din ta fara fin karfinsa,da na kirasa na fad'amai ga halin da ake ciki bude bakinsa sai cewa yayi na kyaleta tayi duk abunda taga dama"

Mama tace"Uhm nima ai haka ya fadamin sai na kawo ido na saka musu daga shi har ita.Ni damuwata d'aya in ta fice ta bar masa gida ba kowa a shiga a sace wani abu ai shi ke da asara ba ita ba"

Kaina na kasa ban dago ba araina nace ina abun sata a wannan gidan..?shi kan shi yasan bai ije komai ba kamar yadda ban yi mgana ba shima kala bai ce ba sai faman dannan waya yake yi ita kuma Zainab waya aka kirata daga gidan bata tashi daga Falon ba ammh ta sauya yare zuwa Fillanci..

Nan Mama tayi nata cin mutumcin Anty Binta na tayata daga karshe Mama tace"Ai tunda Uwar su ta rasu naga tana wani tashen iskanci, mutuwa ai d'ayace kuma duk abun ki dai baki isa ki dawo da ita ba.Ni Allah na tuba mq cewa nayi gwara da ta rasu ta Huta rayuwa ko'ina ba inda tayi kyau"

Subhanallah na fada a fili na Dago ina kallon Mama bata damu ba tacigaba da Fadin"Shiyasa yana kirana yace suna tafe nace ya sauke Zainab anan yadda bata jin dad'in nan ga shi Fa'iza kuma ta saka Mugunta a ranta ai sai ta bar Yar mutane ta shiga wani Hali mu shiga uku"

Anty Binta tace"gwara da kika yi haka Mama"ni dai ban ko kara Dago kaina ba,zaman duk ya isheni ga shi Badariya bata nan zainab kuma tana gama waya ta tashi ta shiga ciki zata kwanta Yaya ishaq ya bita har sai da na gaji da jiransa sannan ya fito yaran har sun fara barci,Mama Tuni ta Dauke Farhan ta shiga da shi Ciki Musty da Ahmad ne suka yi barci nan saman Cafet ammh Mama bata damu da su ba,Anty Binta ta rigamu tafiya mu bayan mun fito Mama ta kira Yaya Ishaq ya koma ciki fiye da minti goma sannan ya fito muka tafi har muka isa gida ci kanki bai ce min ba nima haka, Domin naga yana wani shan kamshi ne da cin mgani a raina nace Indai ta fa'iza ne kayi a banza domin ban ma san ka nayi ba.

A satin yara suka yi Hutu daman sun gama jarabawa,karshen Team,Na lura wannan karon zasu dade tunda bayan zainab ta kwashe Kwana hudu gidan Mama sai ya maidota gida nan shashen shi inda ta fara sauka,su Anum nata murnan Farhan ya Dawo gidansu da kuma suka Dawo sai naga baya cewa nayi abinci da su, sai dai ya Rika fita yana siyo musu nima sai na kama kaina.Daman ba abincin gareni ba Shinkafa kad'ai ta ragemana itama Saboda wanchan cefanen ya siyo ta da yawa ne,Yadda bai nema ba nima ban Tusa kaina ba,Sai dai ina na shiga kullum da Safe mu gaisa da Zainab wani Lokacin ita takan fito falo mu gaisa har mu taba hira tana da Sakin jiki komai ta gani sai tace Maman Amir kaza maman Amir kaza.

Shi megidan nakan gaishe sa, sai dai ba kullum yake amsawa ba sai yaga Dama ni ko ban damu ba saboda ban ga abun da nayi mai masa da zai nemi kara Rataye ni a sama ba,Farhan kuma ya zama d'an wajena nike dawaniya da shi har kwana yana yi a wajena,nasan Ko Yaya ishaq din yayi mgana ita Zainab  zatace ya kyalesa a wajena Saboda ta taba cemin wai bana gajiya da goya yara da Dawaniyar su..?

Ni kuma sai nayi Dariya nace mata ina son yara, kuma Dawaniyar su bai taba bani wahala ba. cikin mamakina tace zata kawo min Farhan nan da zarar ta yayesa bata son wahala ga aiki bata zama Allah yasa ma tana da mai renon sa ,ko ta kaisa gidansu a bakinta nake jin dukkansu sun samu Hutu ne shiyasa zasu fi sati kafin su koma.

Ranar da suke da kwana takwas da zuwa sai ga Goggo da Yaya isa,ya sake kawota na rika ina zan saka da Goggo da tazomin da su garin kunu garin Tsaki da garin masara,yaji kayan kamshi wake mangyad'a da su manja,sai garin Danwake da Taliya yar Muji ina ta Murna sai dai ashe zan ninka Murnata Dubu Dari.Goggo ta kawo min tace Dubu Hamsin ya'yan Dakinta suka hada'min Dubu Hamsin yan'uwana Yaya Asiya da Yaya Mariya har da Hafsatu ta saka Dubu Biyar kunsan na fada muku tana kunshi kuma Sosai take da mutane.

Kuka ya gocemin na karb'i kudin ina Fadin"Duk ni kad'ai Goggo.?

Goggo tace"Duk Fa'iza ita kad'ai yar gatan  Mutanen karofi sun ce ki kara jari.Allah ya sanya ma wannan sana'ar da zaki fara albarka"

Na amsa da Ameen ina zuba musu Godiya ni muna Dakina ne ni da Goggo shi kuma Yaya isa yana falo shi da su Amir.

Sai da muka fito domin muji shawaran Yaya Isa kan abunda za'a siya,Goggo ta lura da Farhan ta tambayeni waye nagayamata sai ta rike baki tana fadin"Ikon Allah girman dan mutum ba wuya.."

Ta daukesa Dayake ba shi da kiwuya sai Dariya yake mata Goggo na shirin mgana sai ga Yaya Ishaq ya shigo falon da farko yayi mamakin ganin su Goggo, Daga baya sai ya basar ya kariso suka gaisa da Isa. ya kuma gaida Goggo sannan ya shige shashensa Goggo ta kalleni tana Fadin"Har amaryan nasa na gidan kenan..?

Nace"Eh tana ciki ko zamu je ku gaisa ne.goggo itama aiki akayi mata aka cire tsakuwar ciki fa"

Goggo bata damu da cewa bai taba kai mata Zainab ba,tace min sai mu shiga ta Dubata kafin mu wuce yanzu dai mu fara abunda ya kawomu.

Su Anum na fattaka zuwa Waje Farhan ya sauka a hannun Goggo ya Bisu duka kudin na zube ma Yaya Isa bayan nayi mai godiya sannan nace"Yaya isa ni dai a siyamin babban Fridge saboda zan fara gwada zobon da kunin ayan nagani"

Yaya isa yace"Hakan shine Daidai ne Nayi mgana da wani abokina suna kawo su masu kyau daga Parthercourt, kayan suna jirgin ruwa sun kusa isowa yanzu abunda za'ayi zan tura masa kudin fridge din da katon sitafileza,Tunda kuna samun wuta basai kin had'a da injin ba. Sauran kudin kuma sai ki rike a Hannunki saboda siyan abubuwan hadin da zaki fara sana'ar da shi ko ya kuka gani..?

Goggo ta jinjina kai kafin yace"Hakan ma yayi.Allah yasa zata fara cikin nasara"

Muka amsa mata da Ameen nan take ya kira abokin nasa sukayi mgana yace a turamai dubu Dari da Hamsin dubu hansim sai na rike a Hannuna,Muna cikin mganar sai ga Yaya Ishaq ya fito ya sake fita ko sannu bai ce mana ba, muma ba wanda ya kara bi ta kansa, kamar yadda bai taba tambayata ba nima ban taba Tunanin na fadamai komai a kan abunda na je na koya ba

Da gaske nake yi na zab'i Rayuwata da rayuwar ya'yana sama da nashi muradin.

Bayan Yaya isa ya cire kudin sai ya bani Dubu Hamsin a hannuna,sannan suka yi shirin tafiya har Goggo ta manta na tuna mata na rakata har Shashen Yaya ishaq,Zainab din na ciki ni na leka nayi mata mgana ta fito tana mika nace mata Goggon mu ce tazo Daga chan karofi, bayan sun gaisa Goggo ta mata sannu da jiki ta amsa tana kallonta Lokaci d'aya tana kallona kafin tace"Ammh suna kama da Momyn kano sosai Maman Amir"

Sai nayi Dariya kafin nace"Eh kanwartace fa Goggon"

Sai ta rike baki tana fadin Honey bai taba min mganarta ba.Dagani har Goggo yake mukayi mun kasa bata amsa,Tana tambayana yadda muke nace mata da goggo da Momnyn kano da Mahaifin su Yaya ishaq da mahaifin mu Uban su d'aya,Ta jinjina kai cikin karin mamaki daga gani bata san wani abun ba sai abunda aka nemi ta sani kawai ta sani

bamu jima ba Goggo ta mata sallama muka fito ta Daura After dress saman kayanta ta fito anan ne ma Yaya isa ya taba ganinta suka gaisa nace mata Babban yaron Goggo ne ta jinjina kai tana fadin"Suna yana yi da Honey"

Sai da ta fad'a na kara kallon Yaya isa naga suna da'n dibar kama kamar yadda ta fada d'in.

Mun rabu da su Goggo kan sai an kawo Fridge din Yaya isa zai kawo min Goggo tace na aika makotan mu na kusa nace zan fara saida Zobo da kunun aya da ruwa, saboda na samu masu siya aiko ban zauna ba su Goggo na tafiya na zari Hijabi nace ma zainab zan fita yaran kuma sukace sai sun bini Amir ne kad'ai ya zauna a gida haka na tasa har da Farhan gidan Sa'adatu na fara shiga na isketa tana yin shasshaka,kusan yara da Rigima su Anum suka saka Rigiman sai sun ci ina zare musu ido tayi dariya kafin tace"Kaji maman Amir kina zare ma yara ido ku zauna a gama sai kuci"

Dariya kawai nayi ta mana shimfidar Tabarma a tsakar gida Farhan ta Dauka tana fadin"Basu koma ba kenan..?.Sai na Daga mata kai, Saboda ranar ta shigo taga zainab din sun gaisa sai a ranar tasan ma ina da Abokiyar zama,domin ko a hira ban Fad'a mata ba.

Tana aikinta muna Taba hira cikin Hiran nan ne nake gayamata sana'ar da zan fara tayi murna cikin Murnan ne take fadin"Aiko zan aika miki kusa damu ana siya fa a baya, chan gidan akwai matar da ta zauna tayi sana'ar kuma wlh tana samun ciniki da kuma suka bar anguwan sai ba wanda ya kama gashi muna samun Wuta sosai za'a siya in sha Allahu"

A fili na furta Allah yasa daga shiga na gayamata sai ga shi na shantake ba yara ba nima sai da ta zubo mana Shasshakan muka ci da manja da yaji. sannan na Tarkata su muka koma gida Yaya Ishaq da Zainab na Falo suna cin gashashiyar kaza, yaran suka nufesu ni kuma nayi dakina Zainab ce kad'ai tamin mgana Gogan kuwa ko kai bai ma Dago ba.ni ko a jikina nasan yana mamakina ya Dauka irin da ne da zan rika binsa jikina na bari yana min wulakanci,Sai dai yanzu shi kanshi yasan takun ya sauya.

Sati biyu suka yi a katsina suka koma Abuja,har na fara sabo da Zainab sannan ga Farhan, da zasu tafi Yara har da kuka shima yaro ai yafi son inda yara yan'uwansa suke. shima Rigiman ya saka Uban ya lallashesa Dakyar,Anum kuka Musty kuka suma sai sunje sai Zainab tace na had'a musu kayan su ta tafi da su kamar zan ce a'a sai kuma naga bani da wannan Hurumin balle da naga Uban gayyar bai ce komai ba., sai na shiga Daki na Hada musu kayansu a jaka,ba masu yawa ba saboda bana so su rasa din Tahfiz din su,Allah ya taimakeni Ahmad na barci da shima za'a sha Rigima da shi.

Ji na yayi ina fad'a ma Zainab kada su Anum su jima saboda hadda Karaf ko sai a kunnensa cikin Kaushinsa ya kalleni kafin yace"Kada ki kara nuna min iko akan ya'yana Fa'iza, ki kiyaye ni Wlh"

Har yana nuna min hannu a raina nace shi kuma wannan me akayi masa..?sai nayi kamar ban jisa ba. Saboda Zainab da ya'yana yasa nayi musu Rakiya daganan gidan Mama suka biya suka musu sallama sai gida ya zama Dagani sai Amir sai Ahmad.

Sun tafi ko sati ba su yi ba Yaya Isa ya kawomin Dankareren Fridge dina da Starplayzer,murna ta kamani sai da nayi kwallah na Shafa na taba nayi addu'an da Fatan nasara da Yaya isa zai tafi nace yace ma Goggo Hafsatu tazo ina nemanta haka ko akayi washegari sai gata ita nasaka ta zauna ta Rubutamin duka abunda zan bukata, ina so mu shiga kasuwa na siyo kayayyakin mahad'in sana'ar  mai yawa yadda zai jima bai kare ba.

Kamar Badariya tasan ina nemanta sai gata tana ganin Fridge din tace"Allahu akbar Anty Fa'iza wannan abun arzikin haka.?

Ni dai sai Dariya nake yi,Farinciki ya kasa boyuwa a saman fuska ta,  albarka tayi ta sakawa itama, sai bayan ta zauna nayi mata bayanin kudin da aka had'anin Daga Korafi taji dadi tace"Allah yasa a mizani"Zuwanta yasa sai ita da Hafsatu suka dinga tsara yadda komai zai fara sun yi mganar goruna, nace ina da wasu da na tara Badariya tace duk da haka za'a karo Saboda abun fa so suke ya habaka kuma ya shahara.

Hafsatu tace"Kuma nan gaba kad'an har da Sticker zata buga a saka sunanta ajiki"

Badariya tace"in sha Allahu muna fatan ya zagaya nageria gabad'aya wannan kunin ayan da zobon namu ai ba irin nasu ba ne"

Dariya nake ta yi musu naga sun fi ni zagewa,Ranar bamu je kasuwan ba sai Washegari Badariya ta dawo muka tafi mu uku dayake nasan abubuwan hadawar shiyasa sai siyayyan bata Dauki Lokaci ba kudi basu fi dubu Goma ba suka Rage bayan mun Dawo gida mun siyo sabbin Goruna,na wajena wanda na Tara Hafsatu ta wankemin su tas a daran na Dafa ganyen zobon da Safe kuma na Had'a shi ni da Hafsat muka dura su a gorinaa muka saka su acikin Fridge dayake ba waje a kitchen falo na ijiyesa, kunin aya kuma nace sai naga yadda wannan ya fara karbuwa Ruwa daman Tun jiya Hafsatu ta saka aka siya aka Dura aciki.

Bayan yayi sanyi na Dauka na aika ma Sa'adatu da Habiba guda uku uku, Dayake Hamsin hamsin nayi saboda Farkon Farawa ne,Shi lamarin Ubangiji daman haka yake ballatana ga wanda yasan Allah ke yi sannan ya maida lamarinsa a wajen sa, cikin Sati uku da fara sana'ata sanu a anguwanrmu,balle su Sa'adatu sun ta min tallah,Da D'aya d'aya Biyu  biyu aka fara zuwa siya sai gashi an gane ni, da ina yin na mudu da rabi na zobo sai na Dawo na Tiya har da rabi,Ni kad'ai nake abuna Hafsatu ta koma gida Karofi Satin su Anum hud'u babansu ya Dawo da su kwana D'aya yayi ya koma kuma yaga komai tunda yana gidan masu siye siye suke shiga suna fita yadda bai min mgana ba nima ban damu da yasan komai ba,To ina ruwan kaska da kifi..?

ni alokacin ma Sabgan gabana ta isheni.

Ko wata biyu ban rufe da farayin zobo ba na fara had:awa da kunin aya, Ruwa kuwa Mota ke saukemin Haruna yayi min Hanyar motar ruwa take kawomin har Kofar gida tana Saukemin.Saboda Hidiman yara sun koma makaranta yasa sa'adatu takan shigo ta tayani Wani Lokacin kuma Badariya na lekoni,Itama ta bangaranta ba abunda zan ce mata sai godiya tunda taje da shi makaranta kawayenta suka sha suka fara santi, Tundaga b'atagwara suke zuwa siyan zobo na da kunin Aya na, Har kuma Lokacin Mama ko Anty Binta basu san  halin da ake ciki ba.

Ban rufe wata shidda da fara wannan sana'ar ba,na sanu sosai a rana na kanyin zobo fin ma Tiya hud'u kuma ya kare,Sannan na chaba Lokacin azumi nayi ciniki,sai na Dafa zobo sau biyu arana kunin aya kuwa na Tiya Biyar shidda duk yana karewa Musamman daga gidansu Raliya Direban  su ke zuwa ya siya fin na Dubu uku in ji Hajiya balle da yake sanyi ga Dad'i ga gard'i sannan cikin Tsafta ba kazanta.

Na aika da shi har Karofi Goggo da su Yaya mariya sun sha sun kuma saka albarka,Yaya Asiya ce kadai bata sha ba tayi nisa,na yarda da mutane da suke fadin in kana da abun yi na sana'a damuwa ma bata da wani muhalli a wajenka,to hakan ne ya faru dani ne, ni mantawa ma nake yi da ina da wata matsala tunda nasan dadin Goma Biyar shikenan Rayuwata ta sauya Daga duhu zuwa haske cikin Lokaci kalilan Allah ya Daukakani,Sannan nayi amfani da Damar haka na tallata ma mutane na ina had'a Turaren wuta humra da na Kamshin Daki, da kwallacha sannan ina yin Dikar Amare da Halawa.

Duk da Ribar zobo da kunin aya na siya kayan amfanin wannan bangaran,Aiki na farko da na fara na Hajiyar su Raliya ce diyar kanwarta zatayi aure ta bani kwangilan had'a Turaren wuta na Rushi da na Humra,Sannan ni nayi ma Amarya Gyaran jiki,kuma ta bani kwangilar abinci,Kafin na rufe shekara na yi suna ta wannan bangaran Domin ina yin Girki a gida in dai bai wuce Takeway ashirin ba ko Hamsin,in ya wuce haka sai dai naje gidan masu sha'anin sai dai bana kwana wasu ni nake siyan komai na girki sai dai su bani kudin a Dungule in kuma yana da yawa sai dai na amshi kudin sallama.

Taimakona D'aya da Hafsatu ta gama jarabawarta ta Dawo wajena ta na taimakamin,Su Mama sun ji na fara sana'ar kunin aya da zobo, to azaton su Sana'ar bata D'ore ba shiyasa basu damu ba.shi kuma Yaya Ishaq yana ganin komai ammh kamar an Daure masa baki bai taba min mgana ba, nimana zama Busy women ban da Lokacinsa balle na tsaya masa bayani.

Sai dai na gayamai sana'ata ta jama'a ne,sannan ina zuwa kasuwa kuma in fita ta kamani ta bangaran kwangilan girki zan fita,sai yace min ai na zab'i Rayuwata sama da aure nayi duk abunda naga Dama babu ruwansa dani,tunda yace haka na fita Sabgan sa,to ni zai gayama aure..?

Auran da a D'ofane ya ke..?

Daganan ban kara bi ta kansa ba harkan Gabana nake yi,Ya'yana kuwa ba na yarda na shiga Lokacin su ko ya yane ina basu Lokaci na domin sune dukkan karfin gwiwata.


*******


*BAYAN SHEKARU BIYU..*


Katsina.

*Layout*

8:12pm.


Zaune nake saman sabon gadona da ban jima da sauyasa ba,ina ta had'a kayana da kwanakin nan nq maida Hankalina wajen hadasu waje daya. Duk wani abu daya Danganceni in dai nawa ne,wanda kuma bai da alaqa da ni,na bar shi,ina cikin zakulo kayan Wardrope dina na chan kasa kasa da na jima ban saka su ba, naci karo da ledan kayan da Anty Binta ta taba bani na Fadar kishiya auran Zainab.

Wanda Yaya ishaq ya yi min kusan shekaru Biyar da wani abu ko Kallon su ban karayi ba,Bayan su ma akwai wasu na sallah da Mama ta tab'a aikomin sau d'aya,suma din banta Amfani dasu ba,na rika ware su agefe nawa wanda na d'inka da gumina da wanda yan'uwana suka Dinkamin ina ware su a gefe daya.

Kamar wani abu ya shiga kaina sai na Dakata na koma nayi Tagumi da Hannuuwana Bibbiyu.shin hukuncin da nake shirin Dauka bazai shafi rayuwata da na ya'ya na nan gaba ba..?

Sai wata zuciyar tace"Ko ban zabi hakan ba.Hakan ya dace domin babu amfani cigaba da zaman".

Da haka na kara samun yakinin cigaba da aikin gabana,Ban ji shigowarta ba sai ji nayi an fad'omin a saman kaina har sai da na Tsorata Ina Dagowa naga Anum sai na bata rai ina Fadin"Bansan sangarta ke har gobe baki girma Anum..?

Baki ta tura kafin tace"Umma yaya yace ki zo lokacin karatu ya kusa"

Agogon dake dakina na Daga na kallah, karfe takwas da rabi ya wuce da sauri na Dafe kaina kafin nace"Ban san lokaci ya tafi ba,muje kada Mallam Amir yamin Bulala"

Dariya Anun ta farayi lokaci d'aya tana fadin"Umma sai Yaya ya dake ki..?

Ina Dariya nace"Sosai malami na ne fa, in na makara zai min Bulala"

Itako abun ya bata dariya ina rike da Hannunta har tsakiyar falona,Wanda ya sauya yanayi a baya kujerun duk sun mutu da Cafet d'in ammh yanzu na Sauya sabbin kujeru da Italian Cafet sannan na sauya ma falon da Dakunan Sabon Fenti na siya ma yaran Sabon Tibi,Ko a yanzu ma Mbc3 ke aiki shi kad'ai ,Ahmad ne ke saka rigiman sai an kunna masa.

Kanwata Hafsatu na kalla dake kan kujera ta kishigid'a da katon katakon ta na yanka salatif, Anum nace ta yanka ta yi mawa da Daddare nagaji da ganinta da Farar kafa,Musty na zaune a kasa inda Karamin allo yake kafe a Tsakiyar falon,Amir na kallah dake tsaye yana faman rubutu da Alli.

Hafsatu ta Dago tana fadin"Umma ta makara yau"

Ina yar Dariya cikin yanayina nace"laifin ki ne.da baki ankar dani akan Lokaci ba"

Zama nayi a kasa kusa da Musty,ina leka abunda yake rubutawa a littafinsa cikin dariya yace"Umma zane nake yi"

Fuska na gyara kafin nace"Sarkin zane fa to me ake zanawa yaron Umma?

Da Sauri Anum ta leka sai ya Boye yana bata rai,ta na kokarin kwacewa ganin sun fara kokawa sai na Raba fadan ina fadin"Anun koma ki zauna yaron Umma nuna min abunda ka ke zanawa.?

Sai da ya boye kada Anum ta gani Gida yake zanawa mai kyau daman Tunda Musty ya fara wayau bai da aiki sai zane zane ni kuma in dai nayi sallah sai na rokar masa Allah yasa zane zanen ya zama Hanyar cin abincinsa..

Karb'a nayi na Dubawa lokaci d'aya ina fadin"Kai kai..Wannan gida ya had'u chanchad'i"

Cikin nishadi yace"Umma irin wannan gidan zan gina miki,in na girma nayi kudi"

Na kalli gidan sannan na kara kallon Musty wanda yake cikin shekaru na takwas har da wani abu,Kansa na Shafa ina fadin"Allah ya ida nufi yaron Umma,ka cigaba da dagewa da karatu watarana buri zai cika in sha Allahu"

Anum na tura baki tace"Umma ni fa nace zan gina miki gida"

Ina jin haka sai nayi dariya nace"To shikenan ke sai ki siyamin mota"

Da sauri tace"Aa Umma sai dai Jirgi"

Ina jinjina kai nace"Lalle waya ga Umma ajirgi babban mgana"

Dariya na saka suma suna tayani Amir daya gama Rubutunsa ya tsaya kikan bayan ya goya hannuwansa a kirji kamar wani babba,da muryansa da ta fara tashi daga na yara zuwa na manya ya fara fadin"Umma kin makara kuma kin zo kin ta sa ya'yanki kuna ta surutu"

Da Sauri na kama bakina ina fadin"To Mallam ayi mana afuwa kai kowa ya kama bakinsa"

Da Sauri suka ko kama Hafsatu na gefe tayi Dariya tana fadin"Umma da ya'yanta"

Juyowa nayi ina nuna mata Amir ji nayi yace"Umma.."

Da Sauri nace"Anty Hafsat ce ba ruwana"

Kai ya girgiza kafin ya juya yana kallon Ahmad sannan ya kara juyowa yana fadin"Umma kalli d'anki bai da aiki sai kallo"

Ahmad muka kallah da ya bada hankalinsa kan abunda yan aljanu suke yi a tibi ko jin mu ma ba yayi Dariya ta na Danne ina fadin"Ayi masa afuwa Mallan yaya"

Sai ya juya da yar sandansa yana fadin "Zamu maimaita karatun mu na jiya Umma ki karanta min"

Sai na gyara zama kalmomin Turanci ne da ma'anar su.

Na fara karantawa daga Number 1,kamar haka.

Mother _Uwa

kenan da Hausa.

Na biyu kuma Son_Yaro da Hausa.

Na uku kuma Brother_Yaya.

Husband_Miji.

Wife_Mata.

Sister_yar'uwa.

Uncle_Kawu.

Grandmother_kaka.

Mother inlow_Uwar miji.

Sister in low_Kanwar miji

Friend_aboki.


Tsab na karanta duka kuma na fassara Amir ya kalleni kafin yace"Please clapp for  Umma"

Sai tafi Raf raf har da Hafsatu cikin masu tafawa cikin jin Dadi nace"Mallam na dauke wad'anan sai na gaba kuma"

Sai ya jinjina kai ya goge wannan ya sake Rubutu wasu.

Sannan ya shiga karantawa yana Fassarawa.


Beautifull_mai kyau

Handsome_kyakyawa.

Marrige_aure.

Divorse_Saki.

T.Shrt_Riga.

Trolley_akwati.

Money_kudi.


Bayan ya gama karantawa sannan yace mu amsa bayan shi,da ni da su Anum muka bud'e murya muna amsawa bayan mun gama yab''i daya bayan daya yana mana bayani kowacce kalma da ma'anarta da Hausa kuma sosai na natsu ina ganewa lokaci da'ya ina kallon Amir daya girma shekarunsa yanzu sha Biyu a duniya ya gama primary zai shiga Jss1 ne,Anum kuma tana shekaru na goma ne Musty takwas Ahmad kuma shidda,Sosai na ke karuwa da ilmin ya'yana Tuni nasan kalmomin turanci irin su come,Sit Down,standdup,zagi ma nasani da Turanci,Nima fa yanzu ba wani karamin kalman da za'a fadeta da Turanci wacce bana ji.

sannan ina kan koyan sanin kalmomin Turanci masu saukin Fad'a da masu ma wahalan,Amir ke koya mana ni da yara Kokari garesa sosai kokarinsa har ya girmi shekarunsa. ina jin su ya tada Aum tana karantawa ni kuma nayi Tagumi ina kallon ya'yana sannan ina auna Shekarun da suka gabata.yadda na sha gwagwamarya da kuma yadda Daukakan Allah ta sameni Lokaci daya.

Ina nan a fa'iza ta yar gargajiyata saboda ko zan sauya a komai Tunanin ado ko kwalliya basu dace ga mata munana irina masu nakasun hallita har yanzu bai bace daga tunanina ba,Sai dai ni Fa'iza na samu cigaba ta Fanni Rayuwata gabad'aya yanzu haka bazan ce kaf katsina ba ammh rabinta da kewayanta sun san wacece *SAFMA* Ko Fa'iza sidi karofi mai Turaran kamshi da dilkan amare Safma sunayen ya'ya na ne da ni kaina nake amfani da shi, a Kunin aya na da zobo sai kuma Ina saka Sticker ajikin Turaren wuta ko kwallachaa,Sannan ina amfani da shi wajen girken girken da nake yi na Birthday ko na suna ko wani biki wanda in nayi shi a gida,acikin Shekaru biyun da suka gabata ban san irin godiyar da zan yi ma Allah bisa tarin Ni'imarsa ba, da a baya Naira Biyar ma  sha'awa take bani ammh ban da yanzu da na rike manya manyan kudade basan adadin su ba,  

Yanzu haka na bude acct inda nake tara kudad:e na,Sannan na mallaki wayar hannu Badariya da Hafsa sun yi matukar kokarin wajen koyamin yadda zan yi amfani da ita, sun kuma Bude min shafuka a instergram da Sauran su da sunan SAFMA,domin inganta sana'a ta suma ba'a bar su a baya ba wajen tayani tallata sana'ta.

Ni kaina bazan iya kirga mutanen da nake hulda dasu ba yanzu,Sannan bansan adadin costumer na ba, abu da'ya na sani in yau nayi ma wata aiki gobe sai ta kawomin uku daga bayanta saboda na Tsaida gaskiya sannan na rike Allah.

Nasan bani da kyau sannan bani da gata,ammh kuma ina da baiwa duk wanda na hadu da shi mu'amalan aiki ta had'amu shikenan mun zama D'aya Baban katsina ya Dad'e yana cemin ina da baiwa ban sani ba sai yanzu in na Duba kaina ayanzu da ban jiran ayin komai da ni da ya'yana, sai na Tuna Tamadina naso tana raye na jiyar da ita dadin Duniya?sai dai ban manta da ita ba ina yawan mata Sadaka da fatan Allah ya jikanta da Rahma.

Matar da ta fara zame min uwa ita da ya'yanta a garin katsina itace Hajiyar su Raliya da ya'yanta ita ta zamemin makwafin Mama a garin nan ta Daukeni kamar yarta duk wani Cigaba ta bangaranta na fara samu ya'yanta da yan'uwanta a Dangi suka D'aukeni nima sai na Daukesu a Dangina ballatana da ta Fahimci halin zamantakewar da nike ciki sai ta zama tsanin dukkan wani Cigabana.

A yanzu haka kaf danginta da zuru'arta ni nake had'a ma ya'yansu turare da gyaran jiki in za su yi aure,Sannan ni nake yi musu kwangilar girken girken sha'aninsu suna zuwa wajena kai Tsaye nima ina zuwa wajen su kaina Tsaye sun daukeni dagani har ya'yana ahalinsu susan yan'uwana da Goggo suna zumumci da su Hajiyar su Raliya mace ce mai mutumci da Sanin Darajan Dan adam, kuma ko da nake da abun hannuna a yanzu ni da ya'yana alherinta bai taba yankewa a gareni ba.

Haka ma Badariya itama bazan manta da ita ba, Ita ta fitar da Zobo na da kunin aya na a jami'ar su ta Umaru musa yar'aduwa aka sanni na zama Dila ana sara, ni yanzu kusan in ba na gida gida da suka saba siya makota ba, na daina saida zobo da kunun aya rabe rabe sai dai a sara kamar D'ari ko sama da haka.

ballatana yanzu da Hafsa itama take aji daya a jami'ar itama tana zuwa dashi kuma ya kare,Har ta Yaya mariya duk sati tana zuwa ta karb'a Saboda ta fara yi da kanta sukace sun fi son dan'danon nawa sai kawai ta koma tana sara a wajena.

Ta ko'ina budi ya budemin na Roki Allah mafita kuma ya bani sannan na rokesa albarka acikin lamarin shima ya sakamin,Yanzu har ma'aikata na Dauka su uku suna taimakamin wajen hada zobon da kunin aya sai Sa'adatu da ita nake biyanta duk wata Saboda tana taimakamin kuma bazan manta da alherinta ba.

Sannan kuma Dawowar Hafsatu wajena sai itama na jawo mata Mutane Saboda Ina gyaran amare ita kuma tana kunshi sai gidanmu ya zama wajen shige da Ficen mata manyan masu abun hannuwan su,

Ni da ya'yana mun daina jiran wani ya yi mana ko ya bamu,na daina jiran kowa,ko Kudin makarantar su na biya musu ya kai su biyu,mganan kayan abinci da Cefane mantawa nake ma ina da Miji,na riga na saka ma raina ni kad'ai ce sannan ni ce uwa da uban ya'yana.Iyakata duk abunda naga zai yanke min na shiga kasuwa na siyo.

Ishaq ya dad'e da sanin Fa'iza yanzu bata jiran wani ko wata ballatana ta wulakanta.

Snnan ni na saka Ahmad a makaranta, naga ya wuce misali a gida ban jira kowa ba na kaisa da kaina,nayi masa registration,sannan Sauran bukatun yarana ma ba na jiran sa,ko Maman da ya saba wakiltawa ta kawo musu in taga dama.

Ya'ya na suma suna kece raini cikin Sutura mai kyau,da Tsada ashe rashin samun jin dad'i ne yasa fatar su ta Dishe da suka samu sauyin rayuwa da mayuka da sabulai masu kyau da Tsada sai ga shi sun yi tas da su, hatta  ni bakin nan nawa ya rage nayi shar dani na kara kiba kamar ba ni ba.

Don ma ban maida hankali wajen gyara ba,da kila da yanzu fa'iza ta sauya sauyawa ta sosai.

Yaya Asiya da tazo kwanakin baya ta taga yadda rayuwata ta dawomim fad'i ta ke yi "Allah mai girma.Shi yasa akace kowa yayi hakuri zai dafa dutse har ya sha romonsa,ga shi Fa'i ta dafa tana shan Romon sa"

Sai dai nayi dariya domin suma daidai misali ina taimakon su tunda ina da shi,Bangaran Yaya ishaq kuma zan iya shaidar sa ta banganran, bai taba nuna bakinciki ko hassada kan samuna ba,Kamar yadda bai tabamin mganar ta yaya komai ya fara Fa'iza..?nima ban taba gayamai ba kuma bai Damu da ya sanin ba.

Nima ba ni da wannan lokacin,sai dai shi kanshi yasan Fa'izar da ya sani a baya yanzu ba ita bace wannan Fa'izar ta samu ingantattacen Rayuwa,da sauyin da na tabbata ko a mafarki bai taba tunanin ni Fa'iza zan samu ba,sai dai shi Allah ba ruwan shi da wannan in ya tashi,Daukakarsa ba nasaba ko chanchanta yake dubawa ba,Bayi duka D'aya muke a wajensa.

Da gaske dukkanmu mun zab'i Rayuwar da muka ga zata Dace damu shi ya zabi zainab da iyalanta, nima na zabi ya'yana da sana'ata sai yayi wata uku bai zo katsina ba,ko yazo kwana d'aya biyu ya koma,ni ko baya gabana da zuwansa da rashinsa duk d'ayane a wajena,yadda baya shiga Sabgata haka nima ba na shiga tasa kowa tasa tafissheshi.

Suma yaran suna girma suna kara Fahimtar Babansu yafi son zama wajen Antyn su fiye da zama a inda Umman su take sun rage zumud'in zuwansa.

Zainab ta kara haihuwa an samu Fadil ita ta matsamin ta kuma matsa ma Mijinta naje har Abuja karo na Farko sunan fadil kuma nayi mata abun arziki kamar yadda take yi ma ya'yana Anty Binta kamar ta kasheni haka takeji sai dai ba dama Saboda Dan zaki ya riga ya girma, duk da basu daina cin zarafina  ita da Mama ba,ammh sun rage suna shakkar min wani abun ganin yarana sun girma sannan nima na wuce Tunaninsu yanzu Fa'izar yanzu ba Fa'izar da suka saba tozartawa a baya ba ne.

A sunan Fadil di'n zainab da mahaifiyarta sun sakarmim komai ni nayi gabacin girke girken da akayi kuma ba'a ji kunya ba, abokan aikin Zainab suka zo suna ta santi,Dani da yara dukkanmu mukaje mun fi Sati a Abuja,kuma Uban gayyar na Abujan lokacin, ammh yadda ban gabansa nima haka na nuna masa tuni na daina masa ma karan,Sai mu had'u in ban ga dama ba, sannu bana ce masa,shi kuma mamaki da girman kai yasa ya ke nuna kamar bai ganni ba.

kwana Goma muka kwashe  a garin Abuja Sannan muka Dawo katsina, har kums gobe Zainab bata tab'a min wani abu na Tozarci ba,sai kanwarta ita kuma ance bata kasar ta tafi kasar waje karatu.

Mama ta samu labarin Daukakata Daga sama ne, bata yarda ba sai da tazo ta ganin ma idonta komai ta koma gida tana fada,ta kira Yaya ishaq ta tirkesa kan ya barni ina tara mata agida sannan ina yawon zuwa gidaje da sunan yin girki, tunda aikin abinci sana'a ce da zai bar ni ina gantali da sunan girki.

Badariya ke fad'amin a gaban Anty Binta yace bazai iya hanani abunda nake so ba,kamar yadda shima ban taba hanasa abunda yake so ba. daganan sai ya kashe bakin su,Nasan sun yi min abubuwa da Dadama ammh ban rike su a raina ba, Mama har gaban abada matsayin uwa take gareni ina yi mata alheri sai dai bata tab'a karba ba har Atamfofi na taba siyan musu dukkan su Har Hajiyar Dala Mama ta Dawo min dashi tace a Fad'amin ban yi arzikin da zan siya mata zani ta Daura ba.tun kafin Ubana Sidi yasan kudi ta sani bazan Rud'eta da abun duniya ba.

Bana damuwa da mganganunta,Anty Binta dai ta amshe tana fadin nima haka na rika tatsan kaninta abun nasu ma kamar sun haukace Koda yaushe Goggo ke nuna min Ribar Hakuri tabbas kuma nima naga Ribar wannan hakurin da nayi shiyasa nake nuna musu komai ba komai ba ne.

To ni ina naga lokacin biye musu ma..?

Ina da abun yi lokaci na sana'ata ne da ya'ya na,ko D'an nasu da suke takama da shi Fa'iza ta daina ara masa lokacinta yanzu ballatana su.


****


Kiran sunana da Amir yake yi ne ya Dawo dani Daga tunanin da na shiga Firgitgit na sauke Tagumina ina fadin"Uhm me kuke fad'i..?

Amir yace"Umma wannan dogon Tunanin fa..?

Gyara zama nayi ina fadin"Ina tunanin watarana zakayi aure ka kawomin suruka nima"

Sai ya bata rai su Anum suka saka Dariya ya daka musu tsawa Hafsah tace"A"a kyalesu su dara Mallam"

Sai ya yi fushi ya wurgar da Sandar Hannunsa ya wuce fuu ya shige Dakinsu,Na bisa da Dariya Saboda shi yasha fadi'n bazai yi aure ba sai yayi kudi ya kaini Saudiya.

Su Anum na bari suna rubutu kan karamin allon na koma kusa da Hafsah ina fadin"Hafsah inaga fa hostel zaki koma ki fara bincikawa tun yanzu"

Sai ta dakata da abunda take yi ta kalleni tana fadin"Meyasa..?

Mikewa nayi ina fadin"Ba yanzu zaki san dalili ba.Ki dafa ma yaran nan indomie ki  hada da kwai,kuci ni cikina ya cika"

Da Toh ta amsamin tabi ni da kallo tana mamakin meyasa nake wasu abubuwan kwana Biyu haka fa Sa'adatu tace na gayamata zan bar mata sana'ar zobo da Kunin aya nan da Lokaci kad'an,kuma naki cewa komai, bayan haka Ni kaina nasan Hafsat ta fara zargin wani abu ni kuma bazan bari ta fahimci komai ba ko Goggo bata san abunda na Kudura a cikin Raina ba, har gobe ina jin bakinciki da Yayata mariya bata kara takowa inda nake ba sai dai mu had'u a karofi ko in naje gidanta tunda yanzu na samu sake Fita free,to ina ma jiran sa kenan..?

Shi da sai ya yi wata uku bai zo ba,nima ko nake gaban kaina.

ammh indai gidana ne Ya mariya ta daina zuwa tun sanda mai shi ya yi mata iyaka da shi.

Cikin Sati d'aya na gama Had'a kayana waje daya,Ranar ma cewa nayi basai anyi zobon yammah ba, na safe daga daya kare a barsa haka,Da Daddaran nace ma Hafsat gobe zan tafi karofi tare da ita su Anum kuma Gidan Mama zan kai su,mamaki ya sa ta kasa mgana nima ban kara ce mata komai ba Domin ta shiga D'akina taga kayana a had'e waje daya kamar wacce zata tashi,ko zata yi Hijira.

Ni ko da na koma D'aki sai na shiga Tunane tunane na tuna sanda na saka Ahmad a makaranta har barazana Ishaq ya yi min in ina nuna mai iko kan ya'yansa sai ya rabani da su ya kai ma Mama su,niko a lokacin sai nace mai kada yayi gaggawa ya bari Lokacin da zasu koma karkashin kulawan maman ai ya kusa,

sannan na fad'amai suma ya'ya na ne, sannan komai nayi musu ban fadi ba ni uwace garesu kuma in yana ganin don yace na kula dasu ai baya biyana, balle yace aikin kudi nake yi masa.daga Lokacin bai kara tada mganar ba.

Na kwana sallah da neman zabin Allah duk da zuciyata naso ta karye Saboda in na kallesu bansan yaya zasu ji in yau suka wayi gari bana tare dasu ba sai dai ko bana so lokaci yayi da zan hakura da rayuwa tare da Ishaq kabir karofi.

Allah mai aiko da kaddara a lokacin da yaso washegari da safe su Anum na shirin tafiya makaranta ni kuma ina dakina ina faman jan casbaha ina hawaye,Kirjina yana ta zafi Saboda yanayin da nake ciki naji Hayaniya afalo da Mganganu sama sama,da Sauri na fito da Hijabina sai naga Jamal hankalinsa tashe yara duk sun yi cirko cirko a falo.

Hankali tashe na karisa ina fadin"Lafiya Jamal me ya faru ne..?

Cikin wani irin yanayi yace"Wlh Yaya Ishaq ne EFCC suka kama shi Daga  Wajen aikin su na Abuja. tun jiya yana Hannunsu,Zainab ta kira Mama ta na kuka take fad'amata"

Sai naji na Rude yara ma suka fara tambayan me ya samu daada.

Cikin Tashin Hankali nace"Me yayi..?su waye EFCC..?

Cikin tashin hankali yace"Wata hukuma ce ta federal goverment da ke kula da sace sacen kudad'en gwammatin kasa,To abun dai kamar shiryawa akayi ance wasu miliyoyin kudi ne suka yi batan Dabo a ma'aikan su Yaya ishaq da aka tsannanta Bincike sai aka gano da saka Hannanunsa kudaden suka fita, shine hukumar tazo ta kamasa ance ko ganinsa basu bari an yi ba har yanzu.."

Sai na sulale na zauna kan kujera ina salati Amir ne yabi bayana da Salatin su Anum kuma kuka suka saka suna Kiran sunan Daada cikin kad'uwa nace"Hafsah cire mu su kayan makaranta mu..mu tafi gidan Mama"

Jamal Ahmad ya Dauka yana Lallashi ni kuma sai na koma D'akina na kalli kayana da suke had'e waje d'aya sannan na Maida su gefe a Fili na Furta"Ashe har yanzu Lokaci bai yi ba..?

Shin sai wani Lokaci ne ya Dace na Fara wata Sabuwar rayuwar..?


*Karshen littafi na D'aya*


*Nan na kawo karshen Littafi na D'aya na KANA NAKA,akwai sauran gwagwamarya,ga dai Ishaq a hannun EFCC,ko ya zata kaya..?*

*Ya matsayin aikin sa?Ina kudurin Fa'iza..?Zata tafi ne ko zata sauya ra'ayi..?ya makomar auran Zainab da Ishaq..?tunda da yuyuwar Abuja zata gagareshi shiga wannan karon?ya Mama zata yi..?Ishaq shine duka karfinta,Wani irin Daukaka ce take Bibiyan Fa'iza..?*

*Duka tarin amsoshin ku suna cikin Littafi na biyu da na uku,akan farashi mai sauki regular N500,sai kuma tsarin VIP1000,wannan karon bana son tsarin kati,a turo ta POS, akan wannan acct no din 0552179550 Jamila Umar gt bank,Zamu tafi Hutun sallah,sai bayan sallah in muna Raye zamu dora daga littafi na biyu,ammh in dan kun cika adadin ku na Mutane 250 da suka siya,ni nasan ina da masoya Fa'iza ma nada masoya ku yi Dafifi wajen rakata har border domin jin Abunda zai cigaba da gudana a rayuwarta da Ishaq,Janafty tace ta gode Allah ya hadamu a aljannah Ammen*








*Janafty*





*KNKB2001*


*Ki biya ki karanta cikin salama,Kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta min littafi,Sannan kada ki yad'amin shi,Pay N500 regular ko kuma VIP N1000, Via Jamila Umar Gt bank 05521790550,ban da tsarin kati wannan karo a turo ta POS, Shaidar biya ta wannan lambar 09069067488*


Duka na tattara yaran muka bi Jamal zuwa gidan Mama hankali tashe,Har da Hafsah muka iske gidan cike da mutane,Kawayen mama da su Anty Binta,Anty mahma da sauran makotan abokan arzuka.

Yadda naga Mama na kuka sai da ta karyamin zuciya ni kaina na shiga tashin hankali mai tsanani. na kasa dora wannan sabuwar kaddarar data bullo mana lokaci d'aya a kan mizani. abu d'aya na sani ina da yakana da yakinin na yarda da Allah sannan na aminta garesa kowani tsanani yake,kuma dukkan sauki daga garesa ne.

Sai ban bi ayarin yan kuka ba. Na koma gefe ina hailala da yi ma Allah kirari da istigifari,domin nema ma Yaya ishaq mafita da salama acikin sabon halin da ya wayi gari acikinsa.

Ganin ba wanda ya tuna da kiran mutanen karofi sai na Dauki wayata na fita daga falon Mama nayi nisa da Hayaniyar mutane,na kira Goggo na shaida mata abunda ke faruwa Allah Sarki dan'uwa rabin jiki sai Goggo ta Rud'e hankalinta ya tashi ta dinga Daukan Salati tana Direwa,mun rabu tace gatanan zuwa bari ta shaida ma su Yaya Isa halin da ake ciki.

Ni da kaina na kira Yaya Asiya na gayamata Halin da ake ciki. itama tana ta salati tana Direwa,kowa in yaji abunda ya faru sai ya tambayi garin yaya..?mu kuma bamu da masaniyar yadda abun ya faru,abu d'aya muka sani ana Tuhumarsa da Batar wasu makudaden kudad'en gwamnati, lamarin akwai d'aga Hankali aciki.

Zuwa yammah gidan Mama ya cika da jama'a yan jaje da masu zuwa kallon abunda ke faruwa suna komawa gefe suna dariya. Da yammah hatta Dangin Mama na yamai sun iso mazan su da matansu har da Hure,itama sai uban kuka take yi ba kiran sunan Allah ballatana Salati.

Goggo ta iso tare da Yaya Isa da Yaya Salisu,basu jima da zuwa ba sai ga Hajiyar Dala ita da megidanta ashe yana gari duka an taru a falon Mama ana faman maida zencen,ni dai ina gefe sanye da Hijabi bazan ce ban yi kuka ba sai dai ban yi kuka na fitar Hayyaci da su mama suka dinga yi ba. ni nafi muka duka lamurana ga ubangijina, yara ma haka suke kuka tun ballatana ganin manya nayi Amir kad'ai ne bai yi kuka ba,sai Hawaye domin shi yazo wajena yana fadin"Umma da gaske yan sanda sun kama Daada.?shikenan bazai Dawo ba..?

Sai na jawosa jikina na share masa hawaye Lokaci d'aya ina fadin"Basu kamasa ba sun dai rikesa suna masa tambayoyi,ka yi ma Daada addu'a da ikon Allah zai jibanci lamarinsa, Sannan ya warware al'umaransa ya Dawo gida lafiya"

Sai ya dagamin kai Daganan bai kara kuka ba. na riga na cusamai yakinin Da sanin Allah komai ya faru sannan garesa ne dukkan wata mafita take.

Mijin Hajiyar Dala babba ne a matakin gidan Soja yasan manyan mutane sosai sai bige bigen waya yake domin nemam makaman zencen,Ammh shuru kake ji har Dare sallah kawai ya fitar da mazan matan mu kuma muka gabatar da tamu acikin gida,

A d'akin Badariya nake yada Saukata in nazo tana kwance sai kuka take yi, su Anty Mahma na bata baki da na idar da sallah ina azkar Lokaci d'aya bakina na motsi ban jirka daga inda nake ba sai da na Daga Hannunwana na rokar ma Yaya Ishaq sauki da salama acikin kaddaransa,na Roki Allah ya kubutar da shi cikin Aminci.

Tare muka shafa addu'an da su Anty mahma ta kalleni tana fadin"Sannu Fa'iza kin fi mu karfin gwiwa,muma bari mu tashi mu yi sallar mu roki Allah sauki kan al'amarin yafi wannan koken koken da muke ta yi"

Nayi yake ban ce komai ba,kamar bazan yi mgana ba ammh kukan Badariya ya Dameni sai na karisa kusa da ita na zauna na Dagota zaune ina Share mata Hawaye ta kalleni nima na kalleni, kafin ta kara saka kuka tana fadin"Anty Fa'iza Yaya ishaq bamu san wani Hali yake ciki ba..Mama nata kuka"

Sai ta fada jikina ni kuma sai na riketa ina Lallashinta har sai da ta samu natsuwa sannan na kalleta ina Fadin"Kuka ba mafita ba ce Badariya.in mun yarda Allah ke da Kaddara sannan shike da sa'a da Aminci to mu mika masa duka Kukan mu, sai ya Dudemu ya share mana Hawaye.Tashi ki yi sallah ki rokar ma yayanki sassauci da warwarewar al'amarinsa,sai kiga da ikonsa komai ya Daidaita"

Da ga alamu mganganuna sun shigeta nan take ko ta mike ta shige Tiolet Halisa na gefe tayi tagumi sai itama ta mike tana fadin"Madallah da wannan Tunatarwa taki Anty Fa'iza.Da su mama ma za'a samu mai Tunasar da su da sun bar wannan kukan sun koma ga Allah"

Anty Mahma tace"Mai dakatar da kukan Mama abu d'aya ne sai in Ishaq din tagani a gabanta kila sai kukanta ya tsaya"

Ni dai ina jin su ban ce komai ba,Dakin na bar musu na fita falo neman su Ahmad,Saboda Halin da gidan ya yini ko abinci ba wanda ya nema ni kuma naga in mu manya ne yaran fa..?sai na shiga kitchen na Dafa musu jallop din taliya na zubo musu ina bin yaran daya bayan D'aya ina ba su suci abinci,ashe Anty Binta na takaice dani,D'an wajen Anty mahma ke kusa da ita na nufesa da karamin Filet din na zubamai ina fadin''Anwar taho kaci abinci..".

Ba zato kawai naji an yi sama da Filet din ya koma ya kife a kasa sai hankalin kowa ya koma kanmu Anty Binta na gani tsaye a kaina Tana faman Huci Idanuwanta sun kala sun yi jajir ta nuna ni da yatsa tana fadin"Acikin wannan halin da muke ciki ke har ta abinci kike..?ina lura dake tun dazu abunda ya faru bai Dameki ba, kamar ma murna kike da Faruwar haka me ake da auran mace irin ki Fa'iza macen kaddara macen da bata san mijinta ba"

Sai na kame a tsaye na kasa mgana sai dai na Sadda kaina kasa Mama ta Dakata da kukanta tana kallona, sai kuma aka rasa me mganar mazan duk suna waje ana ta buge bugen waya domin samun mafita.

Anwar ne yabi taliyar kasa yana ci,Alamun yana jin yunwa wata kawar Mama tace"yara fa najin yunwa, tayi Dubara da ta dafa musu in mu mun hakura saboda tashin hankali,su yara ne basu san komai ba"

Goggo tace"To shi yaro ma me ya sani.?shi dai yaci ya koshi"

Ganin ba'a bata gaskiya ba sai ta fara Borin kunya tana fadin"ku fa ganta wlh ko Damuwa ma batayi ba.kamar cewa ma take gwara da akayi hakan"

Goggo ce ta shigar min cikin bacin rai tace"Assha.Haba Binta ta ya ya mijin ta uban ya'yanta na cikin wannan Halin kice bata damu ba..?ai ba kowacce damuwace ke nuna kanta ba, in mu muna nuna Damuwar da kuka ita sai ta fimu hankali ta nuna Damuwarta wajen Ubangijin komai da komai, kinga kenan tafi mu Dubara mai kyau"

Sai aka fara fadin haka ne kuwa a wajen,ba'a bata gaskiya ba. ganin bata samu nasaran tozartani ba sai ta kalleni a wulakance ta juya ta tafi ni kuma sai na Dauki Anwar na tafi da shi domin na zuba mai wani abincin na basa yaci kada a Dauki alhakin karamin yaro da yunwa.

Har dare ba wata mgana mai Dadi,Domin har alokacin mahaifin zainab yace basu bari an ga Yaya Ishaq ba, duk mazan nan suka kwana da Safe kuma suka hadu suka Dauki Hanyar Abuja har da mijin Hajiyar Dala da shi a Hotel ya kwana da Safe da shi da Tawagansa suka Dauki Hanyar Abuja.

Nan kuma Yaya isa da su Jamal da Kawun Mama dake yamai da suka iso jiya,suka tafi tun a hanya ake ta kiransu sukace basu isa ba,bayan kuma sun isa sai suka daina Daukan wayoyin mutane hankula suka kara tashi Sai Dare sannan Hajiyar Dala tayi waya da megidanta yace shi ya wuce kano ma ammh yana ta kokarinsa abu ne da ya had'a da Gwammati, sunce zasu Tuhumesa ne kuma har Lokacin basu bari an gansa ba.

Wannan labarin ya kara Tada Hankula cikin kwana Biyu ba'ayi barci cikin salama ba,Yaya Asiya tazo jaje ita da ya'yan Goggo na Karofi har da Yaya mariya nima makotana duk sun zo,yimin jaje abun duniya baya boyuwa Tuni mgana ta bazu a gari,Mutane na maau saran Zobo da kunin aya a wajena suna ta kirana bani da sukuni ga masu son Turaren kamshi har da masu biki na abinci, bani da sukuni hakuri nayi ta bama Mutane ina gaya musu halin da nake ciki na Mijina na Hannun masu Binciken Gwamnati a abuja.

Goggo tunda tazo bata koma ba tana tare da Mama tana bata baki Hajiyar Dala data kwana biyu sai ta koma cikin kwana Biyar mama ta fita Hayyacinta su Anty Binta sun gaji da kukan sun hakura, Tuni wadanda sukaje Abuja sun dawo labarin bai Sauya ba, sai dai sun tabbatar da cewa Mahaifin zainab na iya bakin kokarinsa haka ma Mijin Hajiyar Dala ana ta shiga da fita.

Ganin sai zama haka kawai muke yi,Sai nayi tunanin gwara na tattara yara mu koma gida mu cigaba da gayama Allah,tunda ko mun zauna anan gidan abunda Allah ya tsara shi zai faru kuma bamu isa mu sauya masa kaddara ba, sai dai in muna addu'a sai kaddarar tazo masa saukakkiya.

Kwanan mu shida da Safe na samu Mama a dakinta ita da yan'uwanta na yamai bayan na duka na gaisheta ta amsa muryanta a shake kaina na kasa nace mata zan kwashe yara zamu koma gida, sai kawai tayi shuru batayi mgana ba,Hure na gefe sai ta tabe baki kafin tace"Ai ba sai kin gayamata ba ki yi gaban kanki kawai.Ai Anty ita ke da rashi saboda ita ke da D'a"

Baki da asara ko da an rasa Ishaq"

Sai mganganu ya fara tashi a tsakaninsu Mama ce ta katse da fadin"ku kyaleta ta tafi.."

Muryanta a shake ni kuma ganin haka sai na sanyaya murya ina fadin"Mama naga zaman bai da amfani ne ga d'awainiya gwara mu koma gida sannan ga makarantarsu duk ya tsaya zamu cigaba da gayama Allah a duk inda muke da ikonsa komai zai warware"

Wani kallo Mama tayi min kafin tayi tari ana mata sannu sai ta kara kallo kafin tace"Na dad'e da sanin baki da asara a komai Fa'iza, ki yi tafiyarki Domin zamanki bai da amfani ammh ki bar masa ya'yansa anan su d'in Dolensa ne saboda Mahaifin su ne, in suka rasa sa bazasu taba samun madadinsa ba"

Daga haka sai ta koma ta juyar da kanta tana share hawaye, jin abunda ta fada yasa na tashi na fita ni ba haka ne nufi ba ganin ta min gurguwan fahimta sai na fasa gudurina.

Goggo na sama na gayama yadda muka yi da Mama sai ta Dafa kafadata kafin tace"Da kin nemi shawara ta da baki yi mata mgana ba,me neman kuka ne fa aka jefe shi da kashin awaki.Ki rabu da ita ki zauna din har muga abunda Allah zai yi"

Tun da Goggo ta fad'amin haka sai na bar mganar Tafiyar ashe na gudu ban tsira ba mgana ta ding yawo tsakanin Dangin Mama da kawayenta Anty Binta Kirkiri a gabana tace Daman ban damu ba so nake nakoma gida na cigaba da sana'ata tunda shine a gabana,naji haushin wannan mganarta kuma ban kyaleta ba sai da na kalleta ido cikin ido sannan nace"Ko ban damu saboda yana mijina kuma uban ya'yana ba.Zan nuna alhini na saboda yana matsayin Yayana wanda iyayenmu suke abu d'aya ballatana shi din Uban ya'ya na ne"

Daga haka na huce na barta,sai ta fashe da kukan nayi mata rashin kunya mgana taki ci taki cinyewa Goggo ta kashe mganar da Fadin"Haba Binta mu bar wannan ceceku cen tunda ba shi ba ne a gabanmu.Mu ji da abunda ke gabanmu don Allah"

Ammh Anty Binta batayi shuru ba sai da tace"Ai gani tayi tana kama kud'i sai ta dauka daidai muke da ita.Abunda bata sani ba komai lalacewar Daji bai kai in giwa ta mutu kiyasha ya jata ba, ko tana mace tana da Madaukakiyar Darajarta"

Dakyar mgana ta mutu sai da Wata kanwar uwa take ga Mama ta tsawarta ma Anty Binta sannan mganar ta Dakata ammh tana ta kananun mganganu a kaina niko bansan tanayi ba ina Dakin Badariya.

Washegari ya kama Sati daya kenan da labarin da iso mu,an yi an yi an shiga an fita duka labarin bai sauya ba,Hankula ko sun fara kwanciya sai su kara tashi jin ba wani labari mai Dadi.

Sai a ranar muka yi waya da Zainab da yake muna da lambar juna sai dai mukam jima bamu yi mgana ba. sai in wani abu ya taso ko rashin lafiya,Ita ta kirani ni na shafa da ita ballatana ma na kirata, mun gaisa cikin Alhini muka yi ma juna jaje,Sai dai ban wani ji ta cikin wani yanayi ba,Ita take fad'amin mganar Yaya Ishaq sai manyan Gwamnati sun shiga tunda Fitar da kudi ne na ma'aikata kuma ta Office dinsa da saka Hannun sa komai ya fita ba yadda za'ayi ya fita,Tace Babanta ya samu ganinsa sau daya ammh har yanzu ba wani mganar su bada Belinsa,Mun dade muna mgana da ita nace mata ina gidan Mama tayi ta mamakin tace ita da yara sun koma gida sai dai bata bar zuwa wajen aiki ba,Saboda sun ki bata Hutu a raina nace Mama taji kuwa..?sai ga shi tana fadamin Ko da yaushe suna Mgana da su Mama,kuma susan tana zuwa wajen aikinta nan take na Fahimci abun,inda ake raina an fi kai Hari chan bangaran.

Ranar da yammah sai ga Hajiyar su Raliya tazo,ni ina chan Dakin Badariya ban sani ba,Mama na ganinta da su Anty Binta suna ta Rawan jiki mama ta santa tunda kawancen Raliya da Badariya ba yau ba ne,Sai dai ita Hajiyar su Raliya ce bata zurfafa zumunci da Mama ba, sai kuma gashi ni jinina ya had'u da nata da zuru'arta.

Bayan gaisuwa da jajanta abunda ya faru sai Hajiyar su Raliya ta nemi ganina Mama ta tabe baki kafin tace"Kila ma bata gidan domin tun jiya take son ta koma gida dayake bata damu ba"

Hajiya batace komai ba,Da Badariya tazo gaisheta sai tace ta kira mata ni,Ina Dakinta tazo ta kirani ina jin tace Hajiyar su Raliya na mike na fita da Hijabi suna falo na duka na gaisheta cikin Fara'a ta amsa ni tana fadin"Haka ake yi Fa'iza abu ya faru haka bazaki kirani ki fadamin ba..?

Sai dai naji a bakin Raly.?

Kaina na kasa ban ce komai ba sai ta Cigaba da fadin"ba'a haka Fa'iza irin wannan sai ki kirani ki fadamin ko ba a Uwar kika Daukeni ba..?Goggon karofi ta karbe d'iyarta kenan.?

Goggo na gefe tayi dariya kafin tace"Ba ruwana Hajiya ke da Diyar ki"

Kaina na kasa na shiga bata Hakuri sai tace bakomai su Mama haushi duk ya cikasu kallona tayi tana fadin"Ya abun ya faru ne ina so na sani saboda naji in zan iya taimaka wa"

Kafin nayi mgana Anty Binta ta karb'e da bayanin yadda ake ciki Hajiyar su Raliya,ta gyada kai kafin tace"Akwai Kanina yana aiki da Hukumar EFCC din achan Abuja, bari na nemesa naji ko zai iya taimaka mana"

Nan da nan bakin Mama ya washe a gaban mu ta kirasa suka gaisa ta rattamai bayanin komai sai ya nemi sunansa da inda yake aiki Anty Binta ta fadamata sai ta turamai yace ta bashi nan da zuwa Dare zai bincika mata halin da ake ciki.

Bata wani jima ba, tayi ma su Mama sallama,akan yadda akace in sha Allahu gobe zata dawo ita da sauran yaranta Mama godiya kamar zata kwanta mata Hajiya ta kalleta kafin tace"Bakomai kada ki damu babba ne a wajen zai binciko komai..Zan iya yin komai saboda Fa'iza kamar diya take a wajena Ahalina Ahalinta ne,zan iya bakin kokarina bazai gagara ba insha Allahu"

Basa kaunar su ji an ambaceni kuma basa kaunar alfarma ta barayina har waje na rakata ni da Badariya,Direba ya zo da ita ta shiga mota tana ce min sai zuwa gobe,Ta tambayeni su Amir nace suna cikin gida,na dawo cikin gida naji ana ta maimaita zencen nidai a raina ina fatan Allah ya kawo mafita.

Washegari da wajen yammah sai ga Hajiya ta dawo ita da Raliya da yayyin Raliyan suna zuwa ni suka nema daman suna zuwa gidana,Ita kuma Hajiya ta nemi su mama ta gayamusu halin da ake ciki,Hukumar ta na bincike ne,sannan akwai yuyuwar komai da ya fita da saka hannun Yaya Ishaq saboda haka in sun gama Bincikensu zasu yi mgana, sannan sun hana Belinsa saboda cases din na da girma Hankula sun kara tashi tace dai a Dage da addu'a komai zai daidaita.

 Wasa wasa har an shud'e Sati Biyu shuru dai mgana d'aya sai sun gama Bincike,Gajiya nayi da zama na Tattara na koma gida na da yara Goggo ma ta koma Karofi mama an barta da Anty Hure ne mutum yamai suma sun koma kowa ya Saduda yasan Allah ke yi,Mama ta saka ana ta Sadaka da Saukan Qur'ani ni kuma agida banzauna ba ni da yara muna ta kai ma Allah kukan mu,Ban kara bi ta kan Zobo da kunin aya ba,Saboda Halin da nake ciki ko makaranta yaran basu koma ba Hafsa ce ta koma makarantar ta tana zuwa.

Wajen wata da'ya da Tsare Yaya Ishaq aka bama yan'uwansa Daman ganinsa Su Yaya Isa dai suka koma Abuja mgana ta tabbata ba yadda Yaya Ishaq zai fidda kansa saka hannunsa da yardansa aka fidda kudad'en,zai biya taran kudaden gabad'aya da tsabar kudi ko Kaddara.

Lokacin da labarin yazo mana Sai murnan kowa ta koma ciki kudi ba kadan ba wajen Million 70,ina Yaya ishaq yaga wannan kudin ko Kaddara..?su Yaya isa sun dawo suna mganar ya lissafa abunda ya mallaka, gida biyu nan katsina d'aya sai na Abuja sai mota sai gidan mahafinsa,Sai tsabar kudi miliyan d'aya da rabi asusun bankinsa sai fili a nan katsina,Hukumar tace zata zo ta Duba duka kaddarorin zata kwace zai zama karkashinta.

Sai naji na rude ina ta maimaita innalillahi acikin raina Hankali tashe na kalli Yaya isa ina fadin"Aikin sa fa Yaya isa..?

Ya kalleni cikin Tausayawa kafin yace"Ba mganar aiki Fa'iza ya samu ma ya fito lafiya"

Su mama sai kuka Daman a gidan ne ake maida zencen,Agidan muka kwana Dagani har yara saboda ana saka ran dawowar Yaya ishaq acikin Satin.

Haka ko akayi hukumar tazo ta Duba Gidajen da Yace kada a saka gidan Mama,Mama ta saka kuka miye amfanin gidan in bashi a Had'a dashi,Sannan akwai tsabar kudi a wajenta na sana'arta miliyan uku Anty Binta ma ta saka miliyan Biyu,suka tura ta asusun bankin Ishaq,Saboda kudin su rage nauyi.

muna ji muna gani Hukumar ta kwace gidan da muke ciki da gidan Mama da filin da ya siya acikin gari chan ma Abuja ta karbi wanda zainab ke ciki da motar hawansa, sannan sun bamu Notice Wata daya mu tashi Saboda wajen ya zama mallakin Gwamnati

Lalle mun ga tashin Hankali mai suna tashin hankali,Wannan labarin sai dai mun Dauki Dangana tunda zasu sake sa,Bai amsa laifinsa ba ya riga ya rantse bai da hannu akan lamarin, zasu sake sa ammh ba su kyalesa ba in bukatar wani Binciken ya shigo zasu kara nemansa,Shima da taimakon manya acikin lamarin mijin Hajiyar dala da Kanin Hajiya dake hukumar tare da Mutanen Mahaifin Zainab Dr.Lawal bako.

Mama ta tsine ma duk wanda ya saka Danta cikin bala'i tayi mugayen addu'o'i akan sa,Ta ce tunda ya jefa Rayuwar d'anta cikin bala'i shima bazai ga rayuwa mai kyau ba.

Watan Yaya Ishaq biyu a Hannun Hukuma suka sakesa,Daga Abuja tare da Dr.Lawal da Zainab da yara, sai su Yaya Isa da su Jamal suka iso da shi katsina ko da suka iso karfe goman Dare ne an so ya kwana sai gobe yace Zai je yaga Mama yasan tana cikin Damuwa.

duk da Dare ne, gida cike yake da masu dakon dawowarsa.

Mama na jin Dirin motarsu ta Fice da gudu ita ta bude masa Mota ya fito Allahu akbar Duk wannan fafan da kyau da nasabar ta Yaya ishaq ta tafi cikin wata Biyu.

ya rame ya fita Hayyacinsa sai sumar kai da kasumba ta rufe masa fuska, yayi duku duku kamar ba d'an kwalisa Ishaq Kabir Karofi ba.







*03/07/2023*

*Janafty*


*KNKB2002*


*Ki biya ki karanta cikin salama,Kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta min littafi,Sannan kada ki yad'amin shi,Pay N500 regular ko kuma VIP N1000, Via Jamila Umar Gt bank 05521790550,ban da tsarin kati wannan karon.  a turo ta POS, Shaidar biya ta wannan lambar 09069067488*



Mama ta rikesa cikin Fitan Hayyaci,da Dimaucewa ta furta"Ishaq.."

Ashe zan sake ganin ka..?

Sai ta rushe da kukan da ta Dade tana yin sa ammh na yau na Dabam ne, cike yake da tsantsan farinciki sannan hade da fargaba da fidda tsammani.

Rumgumeta ya yi shima cikin wata murya mai cike da laushi da sanyi yace"Mama.."

Sai ya kasa mgana gabad'ayan mu muna kansu,mu kanmu Tausayin ya kamani dole ka tausaya ma uwa indai ta bangaran abunda ta haifa ne. Dakyar Mama ta bari aka shigo da Yaya ishaq gida,ko kan kujeran da ya zauna tana kusa dashi kuka take yi tana Sharb'ewa fadi take yi"Duk wanda ya yi sanadiyar shigar ka wannan Halin Ishaq Allah ya Dai'Daita sa,ya hana sa zaman lafiya a cikin wannan duniyan"

Sai ta kara fashewa da kuka tana cigaba da fad'in"Tsakanin mu da shi Sai Allah ya isa bazamu taba yafe masa ba"

Shi ko yana ta faman lallashinta Fadi yake yi"Ba ga shi na dawo ba Mama? don Allah ki daina wannan kukan hakanan"

Su Goggo kuwa sai sannu Ishaq kawai suke ce masa yana amsawa Hajiyar Dala tace"Sannu Ishaq ka auna arziki Allah ya kyauta gaba"

Cikin yanayin Sanyi jiki yake amsawa Badariya da Anty Binta suka rumgumesa suna koke koke yana mirmishin karfin Hali yace"Kuka dai..?ba ku gani ina lafiya, Daddy ka fad'a musu ba wanda ya Dake ni fa"

Dr.Lawal bako na zaune a gefe ya murmusa kafin yace"Tun muna Abuja nake fadama Jamal haka,ammh bai bar kuka ba kamar wani mace"

Sai aka juya ana kallonsa yana ta sharban Hawaye Ishaq yamika masa hannu yazo kusa da shi Cikin karfin Hali yace"Kun gani ina lafiya basu dake ni ba in baku bar kuka ba,Mama ba zata bari ba"

Ni ko ina gefe daya ban tusa kaina ba Farhan ne a sabe a Hannuna yana ganina ya kirani"Umma.."

Ni kuma na Chabesa da yake har Hutu an taba kawosa wajena kuma indai suna garin to yana wajena sosai yaron ya saba dani.

Sai dai nayi hamdala da godiya acikin raina da ya kubutar da shi Lafiya,duk da an rasa aiki da dukiya sai dai an gode Allah Yaran dake d'akin Badariya basu san abunda ke faruwa ba,suna tare da Halisa,Su na kyalla ido su ka gansa sai suka nufesa suna kiran sunansa "Daada.."

Da sauri duka ya Tare su Anum ce akan gaba sai musty da Ahmad Amir dai a gefensa ya zauna yana fadin"Alhamdulillah Daada ya dawo"

Mirmishi ya saki ya shafa kansa yana fadin"na dawo Baba na"

Anum ta fashe da kuka su Ahmad na tayata Ishaq ya fara lallashinta sai ta tsagaita tana fadin"Daada.."

Sai shesshekan kuka ya tareta sai ya rumgumeta yana fadin"Ina fatan baku yi kuka da baku ga Daada ba ko..?

Anum tace"Bamu yi ba da mun fara Umma zata hanamu sai tace mu yi maka addu'an Allah ya kubutar dakai,mu addu'a muka yi ta maka"

Amir ya karbe da fadin"Umma nata karatun Qur'ani ta d'aga hannu ta na ta maka addu'a Daada nima nayi maka sosai"

Gabada'yan falon sai yayi tsit ana Sauraran yaran Yaya ishaq jikinsa ya karayin sanyi kaunar ya'yansa ya kara kamasa ya kamasu duka ya Rumgume yana Dagowa muna Had'a ido ina shirin na gaisheshi tare da barka da arziki karo na farko a Rayuwata tun da na san Yaya Ishaq da ya taba ambaton sunana cikin Tausasawa.


"Fa'iza.."


Idanuwana a bude na dago ina kallonsa shima ni yake kallo, ba ma shi kadai ba.kaf mutanen dake falon sai kallon su ya dawo kaina,mamaki da al'ajabi basu bar ni na iya amsa mai ba, sai ya kara shayar dani wani gumbar mamaki cikin karin Laushin da yayi ya sake fadin"Nagode..Nagode sosai da baki bari ya'yana sun yi kukan rashi na ba.ko achan in na Tunasu nakan shiga damuwa ammh da zarar na tuna kina nan sai naji sanyi a raina ina da yakinin zaki Kula da su fiye da yadda zan kula da su'"

Ya karishe fada yana kallona da zurmamun idanuwansa da suka zurma Saboda wahala abun mamaki baya karewa har da mirmishi yayi min na Daskare a tsaye na kasa mgana Sabon Ishaq nake gani a gabana ko kuwa dai tsohon ne wanda na sani..?

Ni kaina baki na yayi nauyi,Nauyin da dakyar na iya fuzgo mganar dake bakina sannu da arziki nayi masa, sannan na hada da Allah ya kyauta cikin yanayina nace"Allah ya baka ikon cin wannan jarabawar Allah kuma yasa a mizani"

Cikin Muryansa mai cike da sanyi da Haiba ya amsa min da fadin"Ameen Fa'iza Ameen Ameen"

Tare da su Goggo suma da suka amsa ni Ni dai tsabar mamakin da nake ci bai sakeni ba naji ana cewa ya kamata a barsa yayi wanka yaci abinci ya huta zuwa gobe da Safe.

Mama da kanta ta rakasa har dakin Jamal ita da su Anty Binta,Mazan kuma fita suka yi Hotel zasu kama su kwana,Sai alokacin muka gaisa da zainab muna ma juna barka da arzikin Farhan na wajena ya makaleni tana Dariya ta bar min shi ta shige Dakin Mama inda ta saba sauka.

Ni kuma daman ba ni da wannan gatan Dakin Badariya ne wajen saukata nan muka shige ni da yaran,basan ya suka kare ba ni dai daganan bayan na gama shirya yara sun kwanta nima na kwanta,Kafin nayi barci na dade ina tunanin Yaya Ishaq da Sabon Tausasawarsa gareni, wata zuciyar ta ankarar da ni da cewa kada na sakankan ce kada na manta Hukuma ce ta tsare shi na tsawon Lokaci yana cikin firgicin da bazai yin wani abu ba kada hakan ya rud'eki daganan na watsar da wannan Tunanin na kwanta barci,ammh sai da na tashi wajen uku na Dare na Dauro alwala nazo na yi nafilfilun godiya ga Allah.

Washegari da na tashi,na riga na saba da aikin da jikina bazai iya zama haka ba,Hafsat bata nan tana Hostel wajen wata kawarta ta kwana tun jiya,Mun dai yi waya da asuba na fada mata Yaya Ishaq ya dawo sai tace ma ta gani a waya Badar ta saka,Sai da nayi sharan duka Dakunan na gyara nayi abun karyawa sannan na kama yaran nan duka nayi musu wanka, Goggo nata min sannu da kokari Su Anum nata Tambayan Daada Hajiyar Dala tace yana Hutawa ba'a so a damesa.

Sai bayan na natsa na kira Yaya Asiya na gayamata sai da tayi hamdala,ta nuna alamun murnanta ammh Yaya Mariya ko ajikinta cewa kawai tayi Allah ya kyauta da nace ko zata zo ne..?sai tace min zaria zata tafi suna, kanwar mijinta ta haihu ban ja mganar ba, sanin bazata zo din ba Yaya mariya akwai kafiya da riko Daman sau d'aya tazo shima ba wai jaje tazo ba,Goggo ce ta dinga mata fada yasa tazo kuma har tatafi Allah ya kyauta bata iya ce ma Mama ba, Da Yaya Asiya ta mata fad'a bude bakinta sai cewa tayi"wani Jaje kuma Yaya Asiya..?Alhakin Fa'iza ne fa ke bibiyan Ishaq da danginsa"

Bige mata baki Yaya Asiya tayi ta na mata fada sai bata kara mgana ba, kuma tunda tatafi bata Dawo ba.

Chan da rana sai ga su Anty Nasara da mutanen karofi gida ya cika da yan Taya murna kamar Biki kawayen Mama har da yan'uwanta na yamai da suka yi sammakon tasowa da makota ammh Yaya Ishq din na barci har alokacin bai tashi ba, ana ta dai yi ma Mama barka da arziki bakinta Har kunne Hajiyar Dala tun safe ta bi mijinta suka koma Bayan Mama tayi ta Godiya,Kuma duk wanda yazo sai ta nuna Zainab tace ayi mata Godiya mahaifinta ne ya tsaya ma Yaya ishaq har aka sako shi,sannan sai ta zauna ta bada labarin sharri a ka kulla ma Danta,kawayenta na tayata mugayen addu'o'i ga wanda yayi sanadiyar haka.

Ni dai ina gefe ban tusa kaina ba,Da kaina na kira Hajiyar su Raliya na fadamata tace sun yi mgana da kaninta ya fadamata an sakesa tace min zata shigo in ta samu sarari yanzu harkokin sun yi mata yawa ne,muka rabu bayan nayi mata fatan alheri da nasara,Yaya Ishaq bai tashi ba sai yammah ya rama Sallolin dake kansa yaci abinci Lokacim Tuni Goggo da iyalanta sun wuce Karofi sai ga Mama nayi mata godiya Goggo tace bakomai an yi ma zumunci ne.

Ya iske Dangin mama da makota da kawayen mama da su Anty Binta,ana ta yi mai barka da arziki,yana amsawa kayan Jamal ya saka riga da wando sai naga yana yawo acikinta ahalin yafi jamal cikan namiji a baya sai dai zama waje d'aya da Tunane tunane yasa duk ya zabge.

Ni aikina shine Saukewa da Dorawa da an yi baki Mama tace a kawo abinci da ance ya kare sai tace ina nake da bazan sake dora wani abu ba? ko meye amfani na.?daman nasan ba ni da amfani shiyasa ban damu ba Zainab kuwa yar gatace tun safe tana ciki tana hutawa tace min Kanta ke ciwo saboda tafiyar Mota Fadil ma ni ta bama shi nayi mai wanka na goyasa duk wanda ya ganni da goyo sai yayi mamakin sanin Tunda Ahmad ya girma ya wuce Goyo,Sai na juya aga Fadil ne,ni renon yara bai dameni ba kafin ma nasan zafin Haihuwa na iya kula da yara ballatana yanzu da na haifa nasan zafin su,Ni nake Dawainiya da yaran manyan da zasu iya cin abinci da kansu suci wadanda baza su iya ba na zaunar da su na basu,Zuwa Dare gidan ya watse sai na jiki jiki bayan sallar isha'i mahaifin Zainab ya iso daga chan inda ya kama yana Hutawa shima a falo aka taru har da ni ina chan gefe  fadil na Hannun kakansa yaran kuma suna jikin Baban su.

Mgana yake akan gobe zai koma Abuja Mama da su Anty Binta suna ta mai godiya ya kada kai yana fadin"Bakomai Ishaq kamar Zeey na Dauke sa shima D'ana ne,Ina so na shaida masa kuma ku zama shaida,Na basu gidana na Abuja su zauna da Zeey Saboda bazata iya zaman wani waje ba in ba Abuja ba,nan ta saba sannan yaran nan sun fara rayuwarsu achan bazau yuyu a sauya musu muhalli ba sannan ta na aiki,Sannan kada ya damu nauyin komai ni zan Dauka kafin ya samu wani aiki zamu iya bakin kokarin mu bazai gagara ba In sha Allahu"

Mama ta hau godiya har da Hawaye shi ko Yaya Ishaq mama ya kallah kafin ya kalli mahaifin zainab yace"Daddy ban ki mganarka ba,ba kuma don na raina kyautatawarka a kaina ba, sai don yanzu ba da ba ne.In a baya aiki ya kaini Abuja yanzu fa..?Ina ganin zamana a Abuja yanzu bamai yuyu ba ne"

Kai tsaye batare da Damuwa ba yace"Why da bazai yuyu ba Ishaq..?ai auran soyayya kuka yi da Zeey, kai ka ganta kace kana sonta itama ta amince dakai na aura mata kai,kuma kai ka zabeta na tabbata zaka bita a duk inda take ballatana ma wannan ba abun damuwa ba ne kada kaji komai aikan ka ya kusa dawowa ko ba wannan ba wani zai samu kaji ko..?

Zai sake mgana Mama ta Dake masa Hannu da kafarta ina lura da su ya Dago yana kallonta yana so yayi mgana ta hanasa har ga Allah sai da naku sa yin Dariya.

Mama ta juya tana fadin'"Kai Alhaji mungode sosai Allah ya bar zumunci shirmen sa kawai yake yi me zai hana ya bita chan in ya zauna anan me zai yi..?mungode sosai Zainab ki tayamu godiya fa"

Tana mirmishi tace"Bakomai Mama"

Niko ina gefe araina nace wai me mata da iyalai ne ake cewa in ya zauna anan me zai yi..?ayi dai mu gani in tusa zata Hura wuta.

Bai wani jima ba yayi ma su mama sallama da cewa gobe zai je kano ya bi jirgi zuwa Abuja.Yaya ishaq da zainab din suka fita rakasa jikokinsa na Hannunsa,ya dade yana Tattaunawa da yarsa kafin ta Dawo cikin gida har ga Allah naso mu koma gida sai naga ko shi kan shi Gogan bai yi mgana ba, kada nazo nayi mgana cibi ya zama kari sai nayi shuru da bakina ammh har ga Allah ina cikin Takura.

Sai da muka shafe kwana Hudu a gidan mama yayi mganar komawar mu Gida Mama tace mutane na zuwa Jaje da murna ya zauna,Zainab kuma aranar Direba yazo ya Dauketa ita da ya'yanta ta koma Abuja saboda aiki a gabana a gaban su Mama tace ma Yaya Ishaq yaushe zai zo..?ina kallonsa ya gimtse fuska kafin yace bai sani ba sai ta wuce tana fadin zasu yo mgana ta waya Mama har bakin mota ta rakata kamar zata goyata saboda kauna.

Mu kuwa sai da mukayi kwana Biyar naga zaman dai yaki ya kare na Tattara yara na nace zan koma gida,Sai yace mu tafi shi sai anjuma da Daddare jamal zai rakosa zasu karisawa Tattauna mganar da suka fara da Mama,naji dadi da bai hanani ba sannan itama Maman yan mutumcin na kusa batace komai ba ko da yake mai zugatan bata kusa Anty Binta kenan.

Ina komawa gida duk yayi kura na zage na gyara ko'ina Amir na tayani shida Anum saboda na koya ma yara na aiyukan da basu da wahala saboda gaba,bayan mun gama muka yi sallar la'asar sannan na Dora girki Sa'adatu da Habiba sun shigomin daman sun je har chan gidan Maman sun min barka da arziki da su mukayi ta Hira sai yammah suka tafi,girki daman farar shinkafa ne Amir ke dubamin ya iya hae dafa indomie da, taliya kadan bamai yawa ba,Da miya nayi mana ina da komai na kayan cefane na saboda tunda na fara samun gumina na daina jiran ayi min komai,tsaye nake  a kaina kuma na tsaya akan ya'yana, ko yanzu din ma nace su kimtsa gobe sai makaranta fashin ya isa haka duk da sun koma karatun zango na farko akwai Laluran biyan kudin makaranta ga kuma abubuwa duk sun Chude ni dai na gama lissafina ko zan yini ina aikin sana'ata ne bazan gaji ba,Saboda ina so yarana su samu Ilimi bana fatan su rasa damar su kamar yadda na sara.

Ina da Aiki da yawa na Hada Turaran wuta da Humra,sannan akwai masu Dilka wasu har kudin su sun turomin rashin natsuwa ne yasa ban ce musu komai ba sannan ga yan sarin Zobo da kunin Aya suna jirana,So nake sai hankula sun kwanta na Dawo da sana'ata kafin komai ya daidaita naga kuma inda Rayuwata zata kara Cillamu tunda sun bamu Notice nan da wasu kwanaki zamu tashi ashe da gaske zan tashi daga wannan Muhallin sai dai ba irin wanda na Kudiri niyya ba.

Yaya Ishaq bai dawo ba sai washegari da Daddare muna zaune da yaran suna duba aikin da aka basu a makaranta,Ni kuma ina ta lissafin kudaden mutanen dake kaina acikin wani Littafi inda ban gane ba na Kira Amir ya dubamun suka shigo shi da Jamal,ya rakosa yaran suka mike suna Ihun ga Daada nima mikewa nayi ina musu maraba dukkansu nan falon suka yada Zango na shiga kitchen na kawo musu ruwa muka gaisa da Jamal shima na gaishesa ya amsa hankalinsa na wajen yaran.

Jamal nayi ma mganar abinci yace sun ci abinci a gidan Mama sai dai ko In Yaya ishaq zai ci shi kuma sai yace sai dai zuwa anjuma, jamal bai Dade ba yayi mana sallama shi kuma ya nufi bangaransa yaran suka bisa yanzu har Ahmad ya Daina barci da wuri.

Ni yaran suka bari da tattara musu littafan da suka watsar na kai musu Dakin su na adana musu nima na shige dakina, ina cigaba da lissafin abubuwa bani da wasu kayan Hadin sai na siyo sannan Kudina na Hannun Hafsah nake bama ajiya basa Hannuna.

Ina so na kirata sai na Duburce na rasa ta inda zan latsa na nemo lambarta,Daman sun koyamin ba duka na iya komai a wayar ba,Sai na mike na leka shashen shi na gansu a falo suna da Budirin su na kira Amir sai dai ban ga baban nasu ba,Anum tace ya shiga wanka Amir na ba ma wayar shi ya nemo min Lambar Hafsah ya kiramin nayi mgana da ita tace min tunda na dawo gida gobe zata dawo nace yauwa gwara ta dawo din.

Ina cikin Gyaran gado na Anum ta shigo da gudu tana fadin"Umma Daada yace ki hado masa Tea"

Sai na amsa mata da Toh sai da na gama gyara gado sannan na fita na Dora ruwan zafi na saka mai citta da kanunfari,da Top tea suka Dahu tare na tace sannan na juye mai cikin karamin Fulas din da na siya,Tunda na siya sabbin kayan aikin Kitchen,su dai da suke nawa Tsoffin na Sadakar ne ammh na falo kam suna cikin wani Daki dake haraba kwashewa kawai nayi na sauya sabbi,nasan Halin sa tsab in yaji tijaransa zai ce ina kayansa Tunda shi ya saka komai na gidan kafin mu dawo.

Da kaina na shiga na kai mai yaran dai ke ta duduma afalon shi bai fito ba na sauke mai saman Karamin Center table din dake falon na kalle su ina fadin"Dare yayi aje a kwanta gobe akwai makaranta"

Anum sai ta dira baki tana fadin"Umma mu wajen Daada zamu kwana."sai na rike baki kafin nace"Da wajen Daadan kika saba kwana..?zaki wuce ko sai na mangareki"

Nayi kamar zan kai mata Hannu sai ta goce ba zato kawai naji tace"To Umma Anty in tazo tana kwana anan ke ko baki taba kwana a dakin Daada ba.."

Ta fada daidai Lokacin da ya fito daga cikin Daki yana sanye da jallabiya yaji kuma abunda tace ni ma mamakinta ya sandar dani na shiga tafa hannu Cikin mamaki ya kalleni nima na kallesa sai kawai na kauda kai na sukunci Ahmad da ya barci ina Fadin"Sai da safe..Amir riko Musty kuje ku kwanta"

Daga haka na fice sum sum suka bi bayana Mazan na fara kula har suka kwanta sannan na dawo Daki mamakin Anum ya gama kamani na tashe ta tayi fitsari sannan ta koma ta kwanta araina nace yara ma kada a raina su,su na ankare da motsin kowa Allah mai iko har nayi barci da Tunanin Anum a raina.

Haka muka cigaba da gungura rayuwar mu,Yaya Ishaq sai zaman gida ba inda yake zuwa sai ya bani tausayi magidanci ne fa da ya saba fita aiki da Zirga zirga yanzu ya Dawo sai dai ya kwanta in ya gaji ya zauna,Mutane na zuwa masa jaje cikin mutanen Mama,ko jamal yazo su wuni yana tayasa Hira,Hafsat ta dawo ita na Tura ta shiga kasuwa ta siyo min kayan da bani da shi na kunin Aya da zobo sai na Hada Turaruka ina da nayin Dilka na Halawa ne ta siyomin.

Yaya Ishaq na da sati biyu da Dawowa na Fara sana'ata,yana shashensa bai fito ba sai dai komai ina yi masa,fita ko sai dai yaje gidan mama da daddare ya Dawo,tun Safe da na tashi ban koma ba ranar sau biyu nayi zobo Safe da Yammah Saboda yan sari ko da ya fito da yammah ya ganni ina ta Jera Robobin a katon Frezer na bai min mgana ba,nima ban yi masa ba yadai ce zai shiga gidan mama nace a dawo lafiya.

Ina matukar Tausayamai Saboda akwai Tausayi ga wanda ya samu karayan arziki da kuma rasa aiki,Tunanin inda zamu koma nake yi, saboda ina lissafin saura Kwana goma Wa'adin da suka bamu ya cika yadda bai min mgana ba nima na zura masa ido ranar da yadawo yake fadamin abokan aikinsa daga Abuja zasu zo su yi mai Jaje akawai abincin da zan iya Dafa musu? nace muna da Cefane sai ya kalleni cikin mamaki kafin yace"Wa yayi muku cefanan..?

Kai tsaye nace"ni mana"

Cikin karin mamaki yace"ina kika samu kudi..?

Ina Yar dariya nace"Baka ga ina sana'a ba ne..?

Sai kuma yayi shuru bai kara mgana ba,washegari suka zo sun kai su goma

Hafsah bata shiga makaranta ba ranar ita ta tayani muka yi musu abinci mai rai da lafiya na hada musu da Kunin Aya da zobo na da ke saidawa.

Suka ci suna ta santi,Daganan gidan Mama ya kaisu sai dare ya Dawo,kwana uku tsakani yace min Mama ta kirasa kan mganar gida zai je yaji,da zai tafi na basa dubu daya nace yayi na adaidata sai yaki karba wai yana dashi ni nasan bashi da shi,bazai karba ba ne sai na kyalesa na cigaba da Harkan gabana.

Daya dawo daddare karo na farko Tun aure na da shi ya taba zama ya yi shawara dani,sai ranar wai mama nata saida kayan gidanta na wuta da kayan katako tana so ta had'a kudin gida ne muma tace abunda zamu Dauka mu fara hade su waje daya Sauran sai a saida su.

Ni ko sai naga kamar tsarin bai yi ba na kallesa nace"Ni ko da zaka bada shawaran da kudin da za'a siya gidan da zamu zauna me zai hana mu kama Haya na shekara daya..?kada ka manta akwai Hidima fa gata abinci gata yau da kullum ga na Makaranta da Dawaniyar yara ga Jamal yanzu yake aji Hudu Badariya wannan Shekaran zata gama ga Laluran Mama duka suna kanka ne shine naga sauran kudin in aka kama Haya sai a toshe wasu ramukan da su ko ya kagani..?

Sai yayi shuru yana kallona kafin yace"Kuma fa Hakane Fa'iza ni sam ban yi wannan tunanin ba"

Har acikin raina ni na fadi ra'ayina ne ban dauka zai ji mgana ba ta sai ga shi har su Maman da ya kawo mganar sai suka aminta,Mun fara shiryen shiryen tashi,na hada kayan da zamu Dauka wadanda kuma za'a saida aka fitar har da Tsoffin wad'anda na fitar duk aka saida su gabad'aya.

 kayan bangaransa yace a saida su duka,Katifa kadai yace za'a bar masa ta ishesa ni dai na ware gadona da na yara sai kujeruna sai kayan sana'ata da kayan amfanina na Kitchen, sauran kuma aka kira Dilallai suka yi musu kudi hakama gidan Mama kusan rabin kayan duk sai da su akayi abun akwai tausayi sosai

Yan'uwa ma sun mana kokari Goggo ashe bata zauna ba ta saka ya'yanta suka hada kudi Dubu dari ta kawo tace a kara ita Hajiyar Dalan ma ba wanda ya kara jinta Ina gani Yaya Ishaq nata sunne kai kunya duk ta kamasa.

Da kudin da Anty Binta ta hada da wanda mijinta ya taimaka harta Dangin mama suma sun taimaka aka Hada Miliyan Daya da rabi da su,aka samu gida acikin gari sai kuma Allah ya saukaka mana abun kusa da makarantan yara ne, ko ba abun hawa zasu taka da Kafarsu,Gida ne flat na daidai misali,Shashen Farko falo da Bedroom guda uku sai Kichen sannan kowani Daki akwai tiolet sai dayan Shashen Bedroom biyu da falo ba kitchen sai tsakar gida sai daga wajen Koridon kofar waje akwai wani Daki sai akace Jamal zai zauna anan.

Tun kwana Biyu kafin Wa'adin ya cika kayan mu suka fara yin gaba mu zamu zauna a mai Dakuna uku, mama kuma da Badariya zasu zauna a dayan Shashen,Allah sarki Rayuwa Daman KANA NAKA ne shima Allah ya riga ya gamasa nasa,ranar da zamu tashi yara nata murna zamu tashi,har gwara Amir shi ya fi so wayau.

Ni kaina sai da nayi hawaye inda ka saba da kewar yanayin rayuwa su Sa'adatu duk da su muka kwashe sauran kayana sannan nace don Allah ta gwada sana'ar zobo saboda mutanen dake barayin kada ciniki ya Gudu bayan na tashi,tace in sha Allahu zata jaraba.

Su Mama su ma a ranar sukayi parking din komai,Goggo bata zo ba ammh Anty Nasara tazo ita da Yaya Asiya muna tare da su da Hafsat da makota na bangaran su mama kuma yan'uwanta da su Anty Binta.

Yaya Ishaq da jamal su suka samo motocin da suka kwashe kayan suma sai da suka Chaji kudad'e masu yawa.











*Janafty*



[7/5, 6:22 PM] +234 810 299 5100: *KNKB2003*


*Ki biya ki karanta cikin salama,Kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta min littafi,Sannan kada ki yad'amin shi,Pay N500 regular ko kuma VIP N1000, Via Jamila Umar Gt bank 05521790550,ban da tsarin kati wannan karon a turo ta POS, Shaidar biya ta wannan lambar 09069067488*


Kafin mu karisa chan gidan sai ga Matar Yaya isa tare da kanwarta,Yaya mariyasa nasan bazata zo ba.duk da ta bada uzurin bata jin dadin jikinta,ammh ni nasan dalilin ta.

tare da su da makotana su Sa'adatu muka tare a daidaita zuwa anguwar Ajiwa,koda mukaje mun iske su Mama achan,Gidan mai kyau ne saboda sabon gida ne sannan wanda ya zauna agidan bai dade ba ya tashi. kuma basu lalata gidan ba,ammh dai yaya Ishaq ya sake fenti ya gyara bayika sannan an gyara glop din wuta in da suka samu matsala shi kan shi da'n wannan gyaran sai da ya ci kudad:e sosai.

Mun iske su Anty Mahma har sun gyara barayin da mama zata zauna,bata dawo da wasu kaya ba Falon kujeru biyu aka saka sai cafet. sai Dakin Badariya katifa da Wardrope sai kayanta, Dakin mama ne aka jera mata gadonta da wadrope dinta,Da muka zo sai da muka shiga Shashen Mama muka ga waje muka saka albarka yara daman tuni Jamal ya taho da su nan muka iske su sun warware suna ta murna abun ka ga yaro Amir ne kadai muka zo tare da shi.

Da taimakon Anty Mahma da su Yaya Asiya suka share bangaren da zan zauna suka gyaramin, sun maidamin kujeruna a falo da Cafet sai tibi. wanda naso a had'a a saida Yaya ishaq yace a barta tunda an saida na bangaransa,Duka kayan kitchen dina sun koma Saboda yana da girma har babban Freezerna,na kasuwanci ya samu waje da Buhu buhun robobina da sauran aya da ta ragemin sai Ganyen zobo da sauran kayan abincin da muka dawo da su, suka jeramin a Store din kitchen sannan suka gyara Dakin Yaya ishaq kusa da Dakin yaran ne da aka jerama gadajen su da wadrope din su,Shima katifa ce kadai sai akwatin kayansa sai Cafet karami na tsakar daki ni kuma suka maidamin gado na da sauran kayyakina kafin yammah waje ya fito ya yi kyau suka wanke tsakar gidan tas ya bushe gwanin ban sha'awa abun da yafi burgeni ta bangaran shashena akwai Daga gefe wani karamin Rumfa kamar na shan iska inda a raina nace zan rika hada hadar da sana'ata a wajen.

Hafsatu ta yi abinci na saka aka dibar ma su mama,aka akai musu da shi,Saboda Dare dukkan nan suka kwana Anty Mahma ce ta koma gidanta har Anty Binta nan ta kwana Yaya ishaq kuma suka kwana Dakin korido shi da Jamal, sai da safe bayan an karya suka fara shirin tafiya.

Yaya Asiya da Anty Nasara suna min fada da nasihan kan sai na ninka Hakura na wajen iya zama da mama, in a baya zama bai had'amu ba yanzu kuma ya had'amu sai na zama mai Taka tsantsan da kiyayewa.

Ban ce musu komai ba. ammh ina ji a raina zan iya zama da mama a kowani Hali ai ni ba bakuwar cin mutumcinta ba ne  na riga na saba da Hallayarta na zauna da ita tsawon shekaru fin biyar naci wahalarta bayan kuma na auri Dan'ta ban tsira ba, to ban ga abunda zai bani tsoro akan hallayar Mama ba.

Kafin azahar suka koma karofi narakasu har bangaran Mama suka mata sallama bamu fahimci yanayinta ba,sama sama ta amsa tare da yi musu godiya,sai da suka tafi naji wajen yayi min bambarakwai irin baka Saba ba Hafsah dai tana ta kara gyara dakunan,su Anum kuma suna ta Murna Musty har ce min yayi"Umma ina son sabon gidanmu'

Nayi mai mirmishi kawai ban ce komai ba araina ina jinjina yarinta Amir ne kadai yasan halin da ake ciki Anum kuma uwar Shiriritace Dadi suke ji ganin har da Mama ta Dawo gidanmu da zama basu Dakinta basu Shashen da muke basu tsakar gida suna murna,Abu daya yasa gidan ya sakeni Burgeni akwai ruwa sosai domin akwai Famfo a tsakar gida, sannan suna da wuta kamar anguwan da muka taso,sai dai ita wannan anguwan tafi cika da mutane daidai misali ba kamar na masu  hali da dukiya ba.

kwanan mu biyu a gidan sauran kud'aden da suka rage Hannun Yaya Ishaq ya yi mana siyayyan kayan abinci da su, da suka dawo siyo cefanen kayan abincin.Dakin Mama suka sauke komai ina cikin Dakin yaran ina gyara musu kayan da yake duk an hada kayan ne waje da'ya basu raba musu ba, ni kuma da na samu natsuwa sai na zauna ina ware ma kowa nashi ina saka musu a inda ya dace.

Sai ga Anum tazo kirana in ji Daada na kalleta cikin mamaki sanin baya nan tun safe ya fita cikin yanayin mgana nace"Ina Daadan yake..?

Kokarin hawa kan kayan da nake kan gyarawa tayi na hanata ina Hararanta sai ta juya tana Tura baki kafin tace"Yana Dakin Mama"

Jin haka yasa na tsaida abun da nake yi na fita falo na Dauki Hijabina Hafsah na zaune a kasan cafet tana Duba Littafinta Amir na gefenta kamar yana gane me take rubutawa na Fice ina fadin"ina dakin Mama"

Suka bini da toh da sallama na shiga,Na iske Mama zaune kan kujera jamal na gefenta yana danna waya Yaya Ishaq na nesa da ita ga kayan abincin nan a falon ta Badariya bata nan taje gidan Anty Binta da Safanan.

Har kasa na duka na gaida Mama da gida ta amsa a Dake kafin ta kalleni tana fadin"Kayan abinci ne ya rikita da Sauran kudin da suka rage a hannunsa ya siyo.Shine yayi mganan za'a sauke a bangaran ki zaki rika Dafawa kina bamu nace ya kiraki gaki ga shi ga ni,ki fad'a da bakin ki in zaki iya dafa mana abinci kina bamu bana son abunda raina zai rika baci Daga baya"

Kalamanta sai suka bani mamaki na Dago ina kallonta shima na juya muka Hada ido sai ya Dauke kansa nima sai na maida kaina kasa cikin Ladabi nace"Ai mama ko ba na auran Yaya Ishaq kina da hakkin da zan dafa abinci na baki indai muna zaune waje d'aya bakomai bazai gagara ba, da yardan Allah"

Kai ta daga sama kafin ta karkace kai tace"Shikenan a kwasa a kai dakin ki"

Har na mike zan fice tace"Sai a bi a hankali kin dai gani ba irin baya ba ne lokacin da akwai, yanzu babu.  sai kiyaye da barna Ahto"

Ban ce komai ba na fice a raina ina mamakin Mama yadda bata kaunar taga na zauna lafiya cikin Aminci sai ta Kirkire wata mgana da zata zama cin Fuska a gareni.

Jamal ya shigo da kayan ina Dakina Hafsah ta leko tamin mgana nace ta gwadamai inda zai saka su,Ita ta nuna mai Store ya shiga ya jera komai ba wani abun sakawa a fridge sai kayan miya,sai kayan lambu da suka siyo ba su da yawa,Tun daga ranar ni nake abinci Safe da rana da yammah har Dakina nake  kai ma su Mama cikin wata Cooler mai girma yadda zai ishe su ita da jamal da Badariya,Ni kuma na ji da Yara sannan da Babansu kamar yadda wahalan komai nasa ya dawo wuyana yanzu tunda yana gida bai fara fita ko'ina neman aiki ba, kamar yadda yace zai fara fita ya gani ko za'a dace.

Da kaina na shiga makotan mu gidajen da ke kusa damu muka gaisa na gabatar da kaina a matsayin makotan da muka dawo anguwan cikin Satin da ya gabata, na daina barin kaina Cikin Duhu tunda na san shiga mutane nada Dadi ban kara yarda na zauna agida ba.

Duk kuma inda na shiga sai yi musu tallar ina Saida zobo da kunin aya, sannan ina hada Turarukan wuta na Daki da Humra da kwallacha sannan ina Dilkar Amare na gyaran jiki,Sai girke girken suna biki ko walima na kuma ce su min tallah wasu har suna tambayata ko akwai zobon nace ban fara ba tukunnah,sai mun natsa agidan, sannan sun tabbatar min da zasu siya Insha Allahu sai naji dadi kwarin gwiwa ya shigeni Duk daman masu sari ta wajena basu hakura ba sun ce duk inda nake zasu biyo ni su siya Saboda inganci zobo na da kunin Aya na.

Su Anum sun koma makaranta ba nisa da safe ko Yaya ishaq ya rakasu su tsallaka titi ko Jamal,watarana har Amir ko Hafsah,Amir ne kadai ke gida shi da zai fara Junior section ga ba kudi ammh ina iya bakin kokarina ina so ya fara zuwa da wuri kafin wannan zangon karatu na farkon ya kare.

Muna da Sati Biyu da dawowa Sabon Muhallin mu na cigaba da sana'ata Ranar tare da su Hafsah da Badariya suka taimakamin muka hada zobon da kunin Aya,ta waya na kira masu sara,bayan yayi sanyi chan da yammah suka zo suka Dauka Mama sau daya ta leko komai batace ba ta tabe baki ta koma ciki Sannu Sannu sai ga shi an fara ganeni ana zuwa Siya,ballatana anguwan akwai Dandali na matasa sosai tunda suka gane shikenan da yammah haka nake Ciniki sosai,Daga Mama har Uban gayyar basu taba ce min ba nima ban ce musu ba ina kokarin kiyaye abunda zai saka a tozartani.

Jamal zai koma makaranta,ga kudin mota ga pocket money da kudin kayan abinci ga kudin makaranta Haka ma Badariya,Anty Binta tazo ranar sun dade a daki suna tattaunawa dukkansu sai dai har kwana Biyu ba wani mafita,Na lura shi kan shi Hankalinsa duk ya tashi a ranar suma su Anum aka basu takardan tunasarwan Biyan kudin makaranta Saboda damuwa abinci daren sa ma yadda na kai masa haka na koma na dauke sa bai ci ba,Da safe ma ruwan buni kadai ya sha ya fita ashe gidan Anty Binta yaje itama duk bata da wani kudi duk da su ta kwashe aka rufa asiri,Ammh tace ta ma mijinta mgana zai biya ma Badariya nata kudin makaranta sai dai a nemo na jamal ita zatayi kokarin nema mai na abinci kafin Lokacin tafiyarsa.

Haka naji yana Mama bayani da Daddare da ya dawo ni kuma na shiga

kai mata abinci.Mama tayi tagumi duk ta shiga damuwa kawayen nata da take takama da su,Duk sun janye daga gareta daman sai kana da shi ake yi da kai,Sannan itama babu jarin yin kasuwancin komai ya tsaya ita kanta duk ta rame ta Fige alamun ba natsuwa ba kwanciyar Hankali.

Sai da yadawo bangarena na zubo mai abinci naga ya kasa ci yayi Tagumi sai naji ya bani Tausayi Namiji har namiji ammh lokaci kadan ya nemi ya susuce,batare da Tunanin komai ba ko shawara da wani ba,ina da kudi a banki na sun kai dubu dari da Hamsin daman shawaran Yaya Isa nabi da ya ce na tara wani abu ko Fili na siya kaddara ne saboda watarana,Washegari da Safe na bama Hafsah Atm dina zata tafi makaranta nace ta ciro kudin dake ciki Duka ita kanta tayi mamaki sai dai bata tanka ba.

A hanyar dawowarta ta tsaya ta ciro kudin Dubu Dari da ashirin ta bani na adana su sai da Daddare da ya dawo Futu futu daman ya Dauki Takardunsa ya fita,Ko da ya dawo ya gaji salla ma acikin gida yayi ta ya kasa fita tun safe bai ci komai ba,Ruwan Citta da kunfari na Dafamai yasha cikinsa ya warware sannan ya Dora da abinci.

Inda na fahimci damuwa ta masa yawa su Anum tana kiriniya bai bi ta kansu ba sai na saka Hafsah ta tarka su zuwa Dakin su nace su Dauko Littafan su,kafin su kwanta

Sai da suka bar Falon sannan na shiga Daki na fito mai da kudin hannuna na basa da farko kin karb'a ya yi sai da nace ya karba sannan ya karba cikin mamaki yana fadin"Wannan kudin fa Fa'iza.?

Ina zama nesa da shi nace"ka biya ma Jamal kudin makaranta shi da  Yaran nan, zaman haka bazai yuyu ba tunda an fara sai a karisa"

Sakin baki yayi yana kallona Lokaci daya yana kuma kallon kud'in bakinsa na rawa yace"Duka wannan kudin Fa'iza na waye..?

Kai tsaye nace"Nawa ne dubu dari da ashirin ne Allah yasa zasu isa"

Kai tsaye ya maidomin da kudin a gabana yana fadin"Bazan karb'a ba"

Nima sai na turamai ina fadin"Kayi hakuri ka karba dukkanmu bamu da zabi ne"

Sai yayi shuru ya kasa mgana,cikin wannan shurun ne wayarsa dake gefensa ta dau kara ina gani ya Duba yaja tsaki ya kashe haskenta ya mike daga zaune ya koma kan kujera yana fadin"Fa'iza duk ina kika samu  kudad'e haka?

Cikin mamakin Tambayarsa nace"Ina sana'a ai ka sani"

Yana kallona yace"wata sana'a kike yi haka da ta ke kawo miki kudad'e haka..?

Ina yar dariya nace"Kunin Aya da zobon da kake sha kullum,to shine abunda nake saidawa"

Ido ya zaro kamar bai sani ba ahalin nasan ya basar ne ban bari ya kara mgana ba,na tashi da kudin na karisa gabansa na sauke mai saman cinyarsa ina fadin"Don Allah ka karb'a"

Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya Dauki kudin yana fadin"Zan karba ammh ba kyauta ba,bashi.In na samu aiki na warware zan biya ki kudin ki"

Sai nace mai shikenan na amince nan ya zauna yana lissafin kudaden ya Dago yana cemin"Zai iya isa na biya ma su Anum kudin makaranta ammh Amir fa?

Nazari nayi kafin nace'Shi ka kyalesa gaba sai a saka shi in an samu"sai ya jinjina kai yana fadin"Nagode Fa'iza"

In yayi min godiya har mamakin sa nake yi tun ina mamaki har na daina adaran yaje ya fada'ma Mama kuma har aka bama jamal kudin ya koma makaranta ko mganar batamin ba nima don Allah nayi ban damu ba,daman  bana jiranta.

Bansan cewa zaman Hafsah a gidan nan na damun Mama ba, sai da ta kirani a gaban Yaya Ishaq tace yanzu ba da ba ne nasan ba shi da shi ammh na kara kawo mai Dawainiya ina ganin suma suna fama da kansu,Ni dai har tagama mganar ta ban ce komai ba ina mamakin me zaman Hafsah ya tare ma Mama..?ban da abinci bata cin komai agidan nan,kudin mota da duka Dawainiyarta da Sana'ata nake yi mata Yaya ishaq ne ya tare mganar yasa Mama ta kyaleni sai abun ya dameni a cikin raina kamar Goggo ta sani tace Ko Hafsah zata nemi Dakin makaranta ne ta koma, ni ko naga ina garin kamar bai dace ba da ma ace bana nan ne,shine ammh Tunda ina nan ta zauna a wajena ai nima ina moranta ta bangaran sana'ata.

Sai kuma korafi na biyu ne,mama ta fito da Tsirfan Masu zuwa a bani kunin Aya da zobo sun fara damunta ballatana da taga ina samun ciniki da yake akwai makarantar secondaryn Gwamnati ta mata dake kusa damu, tunda suka gane ni, shikenan arana sai na Dafa zobo fin sau biyu kunin Aya da yawa nake yi,Masu sari in basu zo da wuri ba sai dai su samu kad'an sai ta fara fadan ana damunta da Hayaniya sai na Fahimci bakincinta da na d'anta  take so na zauna ya kasheni ni ko nace araina, bazan miki Rashin kunya ba ammh kuma baki isa ki hanani sana'ata ba.

Amir ne ke taimakamin tunda yana gida sai Hafsah in tana gida Badariya ma ba'a barta a baya ba, Kuma Maman tana sha kuma in tayi baki ina basu,ammh bata gani ba tamin mgana ban ce mata komai ba shima ta same shi ta mai mgana inaga shi ya kashe mgana bata kara tara ta da mganar ba.

Ni dai na toshe kunnuwana na cigaba da sana'ata ganin wannan abun da tayi bai sa na dakata ba ko kuma shi Wanda take gani bai taka min Burki ba, sai ta fara fadin ina barinta da yunwa ina chan ina sana'ata sai rana ta take nake dafa abinci har da kwanciya ciwo sai da aka kai ta Chemist,ulcer ta kamata saboda zama da yunwa Anty Binta ta zo ta kirani dakin Mama ta na ta masifa Yaya Ishaq na jinta bai ce komai ba nima har ga Allah ban yi niyar mgana ba Saboda ni dai nasan ina dafa abinci akan Lokaci tunda na safe kafin tafiyar yara makaranta ne na rana kuma shi nake fara dorawa in na Dafa Zobon Farko na Dare kuma duk latti na bayan isha'i na gama abinci na kai mata ammh ban tsira ba.

Sai da naji Anty Binta tace zan daina sana'ar da nake yi tunda Saboda ita zan kashe musu uwa da yunwa sai alokacin na dago na kalleta ban ji tsoro ba nace"Gaskiya Anty Binta ki yi hakuri ammh bazan daina sana'a ta ba.Domin banga ta inda hakan ya zama Takura ba"

Sai ta saki baki tana kallona kafin ta kallesa tana fadin"Kana jinta dai ko..?

Rashin kunya zata min a gabanka baka ce komai ba..?

Sai ya muskuta kafin yace"Anty Binta mu bi komai a sannu in zaki ce mata ta gyara sai ki yi mata fada ammh babu Adalci mu hanata sana'arta"

Mama na kwance ta daga kai tana fadin'"Ki yi shuru Binta ta siye shi da kud'i tunda yaga ta fara nuna tausayawa garesa shikenan bai iya tsawarta mata"

Cikin mamaki ya kalli Mama kafin yace"Mama wannan wata irin mgana ce..?

Mama ta zabura ta mike kamar daman chan lafiyarta kalau tana fadin"ai gaskiya na fad'a kada dai ta manta kafin tayi maka uban ka ya fara yi mata gata, sannan ya rufa mata asiri, kaima kazo ka rufa mata,ka zama gatan ta, in adalci kuma zatayi ai jarin  ba Ita ta ginama kanta ba kai ka gina ma ta shi"

Da sauri yace"Aa wlh bani da hannun akan sana'arta ban san komai akai ba"

Anty Binta ta koma ta zauna tana fadin"Shiyasa naso na dauke Mama ka hana ashe zaka bari matarka ta gana mata azaba ne ban sani ba..?

Yaya Ishaq yace"Anty Binta ki bar wannan mganar matukar ina raye Hakkin kula da mama da su Jamal yana wuya na ne sai dai in ciwo ko mutuwa sun kwantar dani"

Ina zaune ina jinsu so nayi na tashi na fita ammh kada suce na raina su,yasa na zauna kaina na kasa ina tsintar wasu mganganun su.

Mama da ranta ya gama baci tayi Kyafci kafin tace"Ta gama da shi ne Binta shiyasa kiri kiri yaje ya Duba Zainab yaki zuwa itama ai tana da Hakki akansa wajen wata daya da rabi bai je ya ganta ba,wannan ai sai mahaifinta ya yi fushi da shi Tsakani ga Allah wannan bawan Allah babu abunda bai yi mana ba ammh nasara uban me ishaq ke yi acikin gidan nan da bai tafi ba"

Mamaki ya kasheni wato Zainab ce matar so ni sanda yake tafiya sai yaga Dama yazo ai bata taba cewa ina da Hakki akansa ba takaici yasa nayi mirmishi mganar ma ta gundureni sai ya kashe zaman nawa da cewa"Je ki abun ki Fa'iza"

Mikewa nayi na fice a raina ina fadin daman ya koma chan wajen zainab din domin da zamansa da akasinsa duk daya ne a wajen fa'iza ba abunda suke Tunani ba ne.

Bansan ya suka kare ba ammh sun kai ruwa rana domin ina jin tashin muryoyin su shi da Anty Binta ina Dakina bansan tafiyar ta ba,mama bata so ta gansa yana zaune agida gani take yi kamar wani abu yake min ko zamansa wani Dadi yake yi min,Abunda bata sani ba ni mantawa nake yi ma yana gidan tun safe in yara suka tafi makaranta zan kama sana'ata Amir na tayani in Hafsah bata gidan ita a tunaninta na tsare shi a Dakina ne yana bani wani abu tunda ta Furtamin da na shiga gaisheta washegari ta kalleni sama da kasa kafin tace"Ki sakar min d'a Fa"iza na rasa me kike son ya baki bayan wanda ya baki a baya ke ko gajiya da nanikan namiji bakya yi ciki ko goyo ne baki gaji da yin sa ba ko me..?

Mganarta sai ta bani Dariya sai da na Murmusa kai tsaye nace mata"Ko d'aya Mama haihuwa ai Fa'iza ta gama shi in dai a nan gidan ne na bar ma Zainab ita ya dace ta cigaba da tara miki Jokoki"

Tasan mgana na gayamata ammh sai bata kara mgana ba,ai kunyan marasa kunya a sara sannan tsohon da bai ji kunyar hawa jaki ba shima jakin bazai nauyin yarfa sa da kasa ba.

Hajiyar su Raliya bata san mun sauya gida ba,taje camoron kanwarta zata aurar da Diya su Raliya kuma sun je lagos hutu gidan Yayan mahaifin su,suna dawowa suka hadu a makaranta Badariya ta fadamata ranar tare suka suka zo,a shashena suka zauna tare da Hafsah,suka ci abinci suna Hira Raliya tace Hajiya bata sani ba ammh zata dawo kwanan nan zata gayamata.

Mama taji Haushin shigar su Dakina da Raliya ta shiga mata sallama har da ni sai harara ta takeyi har tana fadin''Haka ake yi sai ki shigar da yarinyar daki ai ba wajen ki tazo ba sai ki bar ta da Badariya kawar tata"

Daganan na Fahimci Kishi Tsagwararon shu Mama ke yi da ni a baya don bamu zauna waje d'aya ba ne yanzu kuma Abun nata na fitowa ,Cigaba na ne bata so tafi kaunar ganin na wulakanta ko na Tozarta to ai ba ita ke da Rayuwata ba,in ita tana nata ne shi Allah kankat ne ya riga ya gama nasa tsarin mutum bai isa ya hana faruwar kaddara da ya Riga ya zana ba.

Ba'a rufe sati ba sai ga Hajiya Tazo Raliya ta rakota tayi ta min fadan meyasan ban kirata ba ni dai hakuri na bata,Tana ta kallon gidan cikin wani yanayi,da zata tafi ta bani Dubu Hamsi sannan taji dadin yadda sana'ata bai tsaya ba tace na cigaba da yi in sha Allahu watarana sai na bama kaina mamaki sai da zata tafi ta shiga Dakin Mama suka gaisa,Ta bata dubu goma mama nata godiya.

Har waje na rakata tace min Direba zai kawo min sako ba yawa,Sannan tace akwai Bikin diyar kawarta da zasu yi a kaduna tana tunanin kwangilan Hada turaruka ni zatace a bamawa sannan tana tunanin Amaryan zata zo gidan sai nayi mata gyaran jiki ina ta Murna daman ta wannan bangaran ita kan kawo min Costumer,sau daya na hada Turaren Rushi da na Humra da muka dawo gidan nan shima na riga na karbi kudin aikin su ne tuni yana hannuna.

Da Daddare naje kai ma Mama abinci sai da tambayeni a wulakance wai a ina nasan Hajiyar Raliya..?

Kai tsaye nace mata"Su ne shugabannin kungiyar da suka bamu tallafi bayan sun koya mana sana'o'in hannu domin Dogara da kanmu"

Sai ta tabe baki kafin tace"Ina ce sanadin Badariya kika santa?

Sai na daga mata kai sai kawai tayi tsaki kafin tace"Aikin mur in ji tusa."

Ban tanka ta na fice washegari sai ga Direba da kayan abinci shake da Mota Ishaq na gida Lokacin nayi mai bayani sai kawai ya kalleni yana fadin"ina fatan ba rokon ta kika yi ba ko..?

Sai abun ya bani haushi na wuce sa na shige daki ina fadin"To ba dole fa a fada masa ya juya da kayan kawai"

Daganan ko kara bi ta kansu ban yi ba, sai naga ana shigowa da kayan a raina nace abun ma iskanci ne sai da na natsa na kirata nayi mata godiya tace bakomai indai ina bukatar wani abu na kirata kamar uwa take gareni nace mata in sha Allahu.

Muna da wattani biyu da kwanaki a sabon gidan da muke ciki,Yaya Ishaq ya tafi Abuja ranar wata asabar shima din Mahaifin zainab ya kira sa akan yazo yana nemansa ba shi ko da kudin Mota Mama ta kira Anty Binta ta bashi ya kama hanya sai da ya bar gidan nan Hankalin Mama ya kwanta.

Kamar yau ya tafi washegari Goggo tazo ganin wajen da muka koma Yaya Isa ya kawota,shima Hafsah ya kira tayi mai kwatance Dakin Mama ta fara shiga suka gaisa anan Mama wai ke Tambayan Goggo ina Hajiyar Dala..?

Goggo tace"Baki sani ba ta tafi raka mijinta kasar awaje a duba lafiyrsa"

Sai Mama ta kasa mgana tunda da Yaya ishaq ya fito daga hannun jam'an tsaro Mama bata kara jinta ba tun tana kiranta ta na bata uzuri har dai ta daina samunta goggo mamaki ya cika ta  daman ana jin kan Saudatu da Fatima ne..?

Da mamakin ta baro dakinta zuwa shashena ta iskemu muna ta Dura zobo a gorina,Goggo na zolayata fad'i take yi"A'a kaga Hajiya fa'i mai zobo da kunin Aya"

Amir da Hafsah suka kwashe da Dariya Yaya isa na gefe yana taya su, shi sauran na jiya da yammah mai sanyi nace Hafsat ta kawo masa yana sha yana fadin"Goggo gaskiya Fa'iza ta iya hada zobo sosai yake da dad'i"

Goggo ta kalleni kafin tace"Ke fa'i taso ki saka ma yayan ki waigi ya fara santi"

Gabadayanmu muka fashe da Dariyan mganarta, shima Dariyan yake yi yana gyad'a kai kamar wani kadangare.





*INGANTACCEN ZANCE*.


*Akwai da INGANTATUN SAIWOWI na gyaran mejego ko amare*.

*Haka uwargida ma ba'a barta a baya ba da irin nata tagomashin*

*Kaya ne masu kyua ba garabiti ba, takanas ake kawo su daga chadi.*

*Idan kina da kannen da za'a aurar, ki zo ki yi musu tanadi na mussaman*.

*SAIWOWIN itatuwane da basu da illah*

*Da sau'ki zaki same su, amma aikinsu yawa ne dasu.* 

*Kawai ki tuntu'bi 

Surayya HALIN YAU a wannan lambar dan samun gamshasshen bayani*

*08032773332.*

      ✍️.




*Janafty*




[7/5, 6:22 PM] +234 810 299 5100: *KNKB2004*


*Ki biya ki karanta cikin salama,Kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta min littafi,Sannan kada ki yad'amin shi,Pay N500 regular ko kuma VIP N1000, Via Jamila Umar Gt bank 05521790550,ban da tsarin kati wannan karon a turo ta POS, Shaidar biya ta wannan lambar 09069067488*


Itama cire hijabi tayi ta shige cikin mu. tana tayamu zuba zobon a sabbin Gorunan da na siya,muna yi muna hira cikin Annushuwa lokaci d'aya muna darawa in abun dariyan yazo,Yaya Ishaq ne bayan ya gama shan na shi zobon zai shiga cikin gari ya mike yana fadin"Fa'iza zan dawo daukan Goggo dole na tafin ma da Madam zobon nan domin itama tana min labarin sa"

Hafsah na gefe tace"Yaya isa har da kunin Aya.."

Da sauri yace"Eh har da kunin Aya a had'amin dashi"

Gabad'ayanmu muka kara kwashewa da Dariya yana sosa kunnensa da key din motar dake hannunsa yace"Goggo kin jamin yara na min dariya ko.?

Goggo tace"Kayi abun dariyan ne.Ke Hafsah bisa ya kwaso min tsaraban Fa'iza kafin ya tafi"

Har zai fice daidai lokacin yaji Goggo na tambaya ta Yaya Ishaq sai nace mata ya tafi Abuja sai ya koma ya zauna cikin mamaki yana fadin"Daman bai daina zuwan Abujan nan ba..?

Goggo tace"Kaji wata mgana shi da yake da mata da ya'ya kake fadin bai daina zuwa ba"

Yaya isa yace"Haba Goggo.In a baya ya je yana aiki ne yanzu kuwa ba ya aiki ga wahalan rayuwa in a baya yana da motar kansa, yanzu ko babu ko na motar da zai rika zirga zirga ai wani abu ne mai zaman kansa shima ya kamata ya zauna yayi ma kansa Tunani haba.."

Ni da goggo kamar had'in baki ba wacce ta tankansa ya cigaba da fadin"In har tana son shi ta baro chan ta dawo nan, ai gidan nan shima ban ga laifinsa ba inda rayuwa ta juya dakai sai ka juya kai ma ka fuskanceta"

Goggo tace"Ya za'ayi ta dawo bayan achan take aikinta a kace"

Yaya isa yayi tsaki yana fadin"Mganar banza ne Goggo in dai tana son shi kuma ya isa da ita duk inda yake zata bisa.ammh gaskiya wannan tsarin bai yi ba, duk wanda yaji haka sai ya raina ma wayaun Ishaq. baisan zama ba aikin yi ba ne, yana ganin kamar abun wasa ne sai rayuwa ta fara kwallo da shi zai Fahimci Shayi ruwa ne"

Dariya ta kusa subucemin da mganarsa ta karshe ya mike yana fadin"Ita Fa'izan ba mutum ba ce, ba ga ta nan ta biyo sa inda yake a kuma yadda yake ta zauna da shi ba, sai ita yar gwal wahala ce bata ishesa ba Allah ya ba da sa'a"

Daga haka ya mike bayan yace Hafsah tazo ta shigo da kayan ni kuma sai nace Amir ya bita ya tayata bayan fitan su ni da Goggo bamu tada zencen ba sai muka shiga wata Hiran na Dabam Goggo ta kalli falon ta kara kallo kafin tace"Nan din ma ba laifi sai ku lallaba kafin muga Abunda zai yi"

Na gyad'a ma Goggo kai ina fadin"Ai anguwan nan tayi Goggo sosai nake samun Ciniki"

Goggo na dariya tace"Dakyau Allah yasa albarka Allah ya tunkud'o ciniki Fa'i ta biyamin hajji da kudin zobo da kunin Aya"

Ina dariya na rika fadin Ameen Ameen Goggo har da Umra ma goggo na Dariyan jin dadi tace'"Allah ya ida nufi Fa'iza"

Hafsah ne suka dawo da kaya Nasan Goggo da Dawainiya bata zuwa Hannu Rabbana tace su garin kuni ne mu lallaba ina ta godiya har da Taliyar yar muji garin Danwake garin Tuwo da tsakin masara kubewa danya,kuka daaddawa,da bushashiyar Zogala da rama sai gyada mai bawo da Mai gishiri da ta kawo ma yara Tsaraba Dadi ya cikani sai cewa nake yi"Allah ya saka da alheri Goggo na zama yar gatan ki"

Goggo tace"Daman ke yar gata na ne tuni zaman ki ne kawai bai yuyu a Hannuna ba"

Nasan haka domin duk wata kauna Goggo ta nuna mana barin ma ni,Su Hafsah tuni sun ja gyad'a gefe suna ci ita da Amir na balla musu Harara ina warce ledan Lokaci d'aya ina fadin"Wannan na sauran yara na ne yan makaranta"

Amir yace"Umma wannan yayi musu yawa fa..?

Na bude ledan ina gani sai naga da yawa sai na debo a hannu na zube a gabansu na boye sauran ina fadin"yara kun ci rabon ku"

Goggo na mana Dariya naji Dadin wannan zuwan na goggo muka yini muna Hira,Hafsah tayi abincin rana bayan ta gama nace ta dibar mama da Badariya da taje kai mata sai tace sai yanzu aka ga daman bata abincin..?

Ita dai Hafsah bata tanka ta ba sai da ta Dawo daki take gayamin Ban ce komai ba Goggo tace"Sai kin kara Hakuri daman fa'iza yanzu Saudatu zatayi ta tsiro da abubuwa saboda ta kuntata miki, to kada ki biye mata Har a gobe uwa take gareki"

Kai na jinjina ina fadin"Goggo ni ban da Lokacin wannan kina ganin bama zaune nake ba"

Goggo tace"Ba shakka Sana'a ai mganin Damuwa ne da sha'anin Duniya,"

Sai da muka yi sallar la'asar sannan Goggo ta yi shirin tafiya daman da La'asar Ya Isa yace zai dawo shima daga ma'aikatar su ta nepa dake Dutsemah ne aka turo su meeting babban Headquater su na katsina da ya gayama Goggo tace zata Biyosa.

Aiko sai ga shi hudu da wani abu sai faman hon yake yi ma Goggo tunda yaki shigowa na zuba ma Goggo kunin Aya da zobo mai yawa shima Yaya isa na bashi na shi Goggo sai fada take yi tana fadin"bai yi yawa ba Fa'iza? kada mu karya fa jarin"

Ina Dariya nace"Cikin Riba ne fa Goggo"

Sai ta karba tana fadin"To Allah ya yi albarka Allah ya sanya miki nasibi da karama acikin Kasuwancin ki da sana'arki"

Na dinga amsa mata da Ameen na rakata Dakin Mama tayi mata sallama ni da Hafsah da Amir har kofar gida muka rakasu Yaya isa ya zaro dubu biyu ya bani naki karba sai ya harareni yana fadin"Kyauta na baki ni ba kudin zobo ba ne"

Jin haka yasa nayi dariya na karb'a ina masa Godiya Hafsah na ganin haka tace"Yaya isa kada ka manta yar makaranta marainiyar Allah"

Dagowa yayi yana fadin"Data zaki saka ko..?

Da Sauri tace"Eh Yaya ai muna Browsing sosai"

Sai ya yi dariya ya zaro dubu ya bata yace a saka data ayi ta browsing ta karba tana godiya sai kuma ya bama Amir dari biyar yana fadin"Kai baka fara zuwa makarantar ba ne..?

Da Sauri nace"Bai fara ba sai zangon karatu na biyu Yaya isa"

Sai ya jinjina kai har Goggo ta shiga mota sai ta leko ta window tana fadin"Kinga na manta Maman isuhu tazo da kanta ta kawo min goro da mintin biki Isuhunta zai yi aure tace kada a yada zumunci don Allah"

Fatan alheri nayi kafin nace"Da wahala zuwa na Goggo kinga ga Mama ina fita sai kiji ance ban kyauta ba"

Goggo tace"Hakane ki yi zaman ki ni da mariya sai mu leka"

Da haka muka yi sallama suka tafi muna Daga musu hannu sannan muka koma cikin gida,Danwake nayi mana da Daddare Hafsah kuma sai ta hada kunin Aya zobo ma bamu yi na yammah ba nagaji nace ta bari da Safe yan sari ma basu samu ba duk a gida ya kare.

Aiko Mama tayi ta fad'a wai danwake ne abinci da daddare kamar a gidan yari..?yarda aka kai mata haka Hafsah ta Dauko kulan da safe da zatayi wanke wanke, Badariya bata dawo ba kila gidan Anty Binta ta kwana,haka na cigaba da Hakuri da Mama ammh Allah ke da kullum da Sabon korafin da take tashi da shi sai dai bana biye mata,Yaya Ishaq tunda ya tafi bai kirani ba nima ban damu ba sai dai nasan suna waya da Mama.

Sana'ata na maida hankali bani da wani Hutu sai dare ya tsala wani Lokacin Saboda kada ayyuka su Chudemin karfe uku na Dare nake tashi na Dafa Zobo a tsakar gida tunda na koma amfani da gas na kasa 4kg,Sai na siya babban murhun gawayi ina amfani da shi wajen Dafa zobo,har girki ina yi akai saboda gas din ya rika yi mana auki sosai.

In na tashi ukun nan kafin asuba na Dafa zobon,sai naji da saka ruwan wanka. wani Lokacin Hafsah ke abun karin Safe in zata fita da wuri in kuma tana gida sai nayi in ta tashi sai ta Hada zobon ta kuma share gidan da Dakunan in kuma bata gidan duk ni nake had'awa nayi kunin Aya saboda yana Saurin Lalacewa nafi hadasa da yammah saboda an fi samun Wutar Dare kafin safe yayi sanyi.

Hakan ma bai burge Mama ba, duk yadda nake taka tsantsan sai da ta fito tace min wai warin ganyen zobo na tayar mata da zuciya ni ko sai nace sai dai ko ki yi ta sheka amai bazan daina wannan sana'ar ba,kuma duk kushen mai kushe da Hassada ta Allah ba tashi ba.

Duk yadda nayi sai tace kaza kaza ita dai kada ta ganni cikin ni'imar Allah sai dai na zauna ta rika tusamin Haushi da tozarcinta nan kuwa bata isa ba,yanzu ba irin da ba ne an samu Sauye sauye da dama. daman haka Rayuwa ta gada Kifi na ruwan sanyi sai ya iya juyawa ya gansa ana zafi kamar yadda ya faru da ita.

Na toshe jina da ganina na cigaba da sana'ata ina rufa ma kaina da ya'yana asiri,har da ita kanta Mama muna da kayan abinci ammh bamu da Cefane da Riban sana'ata nake mana komai Dawainiyar yara na makaranta na yau da kullum Badariya ma ina bata na mota har da wata matsalan in ta taso in dai tamin mgana ina da shi zan Dauka na bata.

In da na biye mata na koma na zauna yadda ta matsa Yaya Ishaq ya tafi Abuja da ta gane bata da wayau.Anty Binta take takama da ita itama bata da komai yanzu sai karya da Girman kai da tijara fal cikinta domin ban ga abun arzikin da take kawoma Maman ba,Da farko da Mama tace Ucler ya kamata kayan Tea ta siyan mata da suka kare bata kara siyan ba na Tabbata bayan Yaya ishaq ba mai iyawa da Dawainiyar Mama.

Sai da ya shafe fin sati biyu a cikin na uku ya dawo na zata zan gansa da abun arziki ne niki niki yadda Mama ke fadin sun musu komai babu abunda yazo da shi daga shi sai kayansa kamar ma a kidime yake ba wani kwanciyar hankali sai ramar da ya karayi, ashe wai takardunsa yasa yaje mai da shi ko za'a dace yasaka shi yayi zama ba wani labari mai Dadi gajiya yayi da zaman ya dawo ina Tsakar gida ina shara naji Mama nata mai fad'an meyasa bai jira ba ya Dawo dayake Mama ta iya mgana a sama sama.

Yayi mgana sai dai nashi ne yayi kasa ban ji abunda yace ba, ni dai ba gulma ba na cigaba da aikina,Yadda bai ce min kanzil ba nima ban ce mai ba sai na tambayesa ya ya baro su Farhan..?

Sai yace min Farhan ya fara zuwa makaranta Fadil kuma gidan su zainab ke kaisa in zata fita aiki Daganan bai kara mgana ba, nima na kama bakina fadan da ba ruwan ka ai Dadin kallo ne da shi.

Sai ranar da yayi kwana Biyu da Dawowa yana zaune afalo ni kuma ina safa da marwa aiki ya had'e min Hafsah da wuri ta shiga makaranta ga aikin zobo ga girki,Amir ne ya taimaka yayi min sharan Dakuna da Tsakar gida,gajiya yayi da ina wucesa ko barayinsa bana kallah yasa ya kirani nazo gefensa na tsaya yana kwance ne ya mike yana fadin"Nagode bisa Dawainiyar da kika yi da yara da su Mama bayan ba na nan"

Sai kawai na wuce ina fadin"Ba damuwa daman kasan kula da yara aikina ne Mama kuma itama kamar uwa take gareni, kada ka godemin domin na yi mata Hidima"

Daga haka na wuce kitchen na Dauki Abunda zandauka nayi waje achan nake girki gas ya kare Hafsah nace taje ayi Refiling bata samu zama ba ne.

Har na fice yana bina da kallo nasan a ransa yana mamakin yadda na sauya ne bakina ya bude fiye da yadda yayi tsammani,Haka muka cigaba da Rayuuwa yau dadi gobe Tsumma,ahakan ma ni nake tallafe da kananun Lalurorin gidan nan ammh Mama bata gani take yi komai nake yi alfarman da suka yi min ne nake rama musu. 

Ni ko Don Allah nayi abunda take yi bai Taba Damunaa ba,Ba inda Yaya Ishaq yake zuwa yana gida sai dai in masallaci in ya gaji da barci ya fito falo ya kunna kallo in yagaji ya kwanta,ko ya shiga Shashen Mama,duk yadda baya so damuwa ta samu zama a jikinsa sai da ta samu duk yayi baki ya rame hatta na katin waya gagaransa yake yi,kuma yana da girman kai da Fafa bazai yi tambayata ba ni ko bani da masaniya kananun matsalolin da na gani ne nake mgancen su.

Ana cikin Haka jamal ya yo masa waya Kudin hannunsa ya kare sannan kayan abincin sa ma sun kare Bai fadamin ba sai ya shiga bangaran Mama ya fadamata kai tsaye mama tace"Sai kayi ma matarka mgana nasan bazata rasa ba,gidan nan yini ake shiga da fita saboda sana'arta"

Kai tsaye yace"Mama ni bazan iya taba tambaya Fa'iza kud'i ba"

Mama tayi karamin Tsaki kafin tace"Kiramin ita ni zan gayamata"

Amir ya kwalama ya kira da ya shigo sai yace ya kirani ni kuma ina Falo na Dukufa da littafin, ina ta lissafin kudi so nake wannan karon daga rabin Solon Ganyen zobo na siya Solon buhun ina tattara Riban hannuna sannan Aya ma tiya goma nake so na siya,da yawa da Dabino na ijiye kwakwa kuma tana lalacewa kadan zan siya sanda Amir yazo ya kirani shine a raina so nake nayi kokarin na biyasa masa kudin makaranta ya fara zuwa zamansa ya fara Damuna,so nake na fara ji da Hidimarsa kafin su kuma a fara mganar na su Anum

Ijiye komai nayi na saka Hijabi na tafi Dakin Mama da na shiga a kasa na duka ina gaisheta da lafiya ta amsa kafin ta daga murya tana fadin"Jamal ne yayo waya bai da kudi a hannunsa nasan kina da kudi ki bada ko dubu ashirin ne sai a sakamai ya lallaba"

Sai mamakin Mama ya kamani kamar ita ta tarfamin jarin cikin sanyina nace"Sai dai Dubu goma baza'a samu ashirin ba"

Mama ta saki baki kafin tace"Wlh karya kike yi ba za dai ki bada ba ne, meye amfanin samun naki in dai bazaki taimaki mijinki naki ba"

Ina jinta ban yi mgana ba shi ya katse mganar da cewa na tashi na tafi haka na koma Dakina ina jinjina karfin Halin mama shikenan lissafina ya Sauya daman yan riban da su nake Hidiman yau da kullun kudi fa ana zaran su basa zama,Sai na cire dubu goma na ware kayan da nace zan siyo na ijiye bazai samu ba saboda kudin sun yi gibi,ko da ya dawo dakin bai tada mganar ba sai ni da kaina na dauko kudin na basa ya karba Jikinsa a sanyaye lokaci daya yana fadin"Ki rika Rubutawa Fa'iza zan biya ki kudin ki da zarar na samu aiki in sha Allahu"

Ko kulasa ban yi ba sai dai na dago na kallesa kamar bazan yi mgana ba sai kuma nace"Kai dai baka na lissafe da abunda ka karba ba?ai shikenan."

Daganan sai bai kara mgana ba ya saka takalmi ya fita yaje ya tura ma Jamal kudin,ya dawo Yaya Ishaq na bani mamaki ko irin ya dan fita waje ya zauna bai iya ba yana gida koda yaushe dole damuwa tayi masa yawa,kamar zan yi masa mgana sai wata zuciya ta kwabeni na kama kaina.

Zainab na kiransa ko da yaushe ni ban san Halin da suke ciki ba sai wataranar asabar da Safe na shiga kai masa abun karyawansa naji yana waya ya daga murya sai fada yake yi Cikin kaukkausan murya yake fadin"Zeey na fada miki bazai yuyu nazo abuja na tare ba,bani da aikin yi ba wajen zuwa ke ba zaman gida ba ki fice tun safe ki barni da mai aiki, Fadil ma ki bar mun shi ya Debemin kewa gida kike tafiya da shi gwara na Dawo gida na zauna nan din ma ina da uwa da wata matar da kuma yara"

Ni dai daga haka na sauke abun hannuna na fice yayi nisa a mganarsa bai ma san na shigo ba.

Da na fita acikin raina sai abun ya fadomin sai naga Zainab na da gaskiya abunda ya zabar mata tun farko ne meyasa yanzu zai sauya..?ai yasan da akwai rashi da samu akwai rayuwa akwai mutuwa kuma ya zabi hakan duk wanda ya siyi rariya yasan zata zubda ruwa yadda ba wanda ya sani cikin mganar nima nayi kamar ban ji komai ba, na cigaba da Sabgan gabana.

Ina ta buga bugan  yadda zan had'a kudin makarantar Amir saboda su Anum sun kusa hutu sannan ga kudin makarantar Tahfez din su yanzu sun ciresa a kudun makaranta Daban za'a biya hakuri na bada wanchan Team din ba'a biya ba yanzu kuma baamai karban uzurin mu,Shiyasa nake aiki ba rana ba Dare rana na Dafa zobo sai Uku,saboda zafi da nake tunkara da Wahala yasa kaina ya fara ciwo da ganin Jiri ina jin haka nasan jinina ne ta haye sama bana samun Hutu ga amfani da Hutu nasan in ya kwantar dani abubuwa ba zasu tsaya sai naje kemist aka auna ni aka ga jinina ya Hau sai aka bani mganguna,Dalilin haka yasa kwana Biyu nayi baya da Wutar Sai dai Hafsah ta Dafamin kafin tatafi makaranta sai ta barmun na hada,kunin Aya bai da matsala da kaina nake yin ta tadawo da wuri sai ta sake Dafa na yammah ni kadai araina ina fadama kaina Fa'iza bi sannu Sannu zafin nema baya kawo samu.

Allah maji rokon bayinsa domin ban daina rokon mafita daga garesa ba,kawai sai ga kiran Hajiya tana fadamin bikin da ta fadamin na kaduna saura sati biyu,In na samu Lokaci nazo gida na sameta ina jin haka ko ban yi wasa ba,Allah yasa Ranar Hafsah na gida sai na bar mata komai Yaya Ishaq na dakin Mama da na shiga ciki na shiga na gayamai zan fita Hajiyar su Raliya ta kirani kan wani aikin Turaren wuta bai ce komai ba yace a dawo lafiya Mama kuwa sai da ta tofa kallona tayi tana fadin"Da zaki kwashi kafafu ki fita abinci wa kika bari ya dafa ya bamu..?

Kai tsaye nace"Hafsah zata dafa ai ba jimawa zan yi ba zan dawo"

Baki ta tabe kafin tace"Wanki na ya taru wannan satin naga baki zo kin kwashe kin wanke ba ko kin gaji ne..?

Yadda tayi mganar kamar wata baiwar ta ko yar aikinta Tunda muka Dawo gidan nan ni nake kwashe kayan Mama in sun yi Datti na wanke mata. 

  kuma na zauna na goge mata,ba kayan Mama ba Har na Yaya Ishaq ni nake wanke masa wani lokacin saboda bai saba ba,Sai dai in aiki yayi min yawa sai nace yakai wanki da guga zan ba da kudin.

wannan satin da ban ji dadi ba ne ko na yaran Hafsah ta rage musu nasu ammh ji yadda take min mgana kamar tana biyana.

Kaina na kasa nace"Banjin dadi ne wannan satin ban yi wanki ba, ammh za'a wanke in sha Allahu"

Yaya Ishaq mamaki ya kamasa cikin mamakin yace"Mama bata jin dadi yanzu ko Badar baza ki saka ta wanke miki kayan ki ba..?baki ga ayyuka sun mata yawa ba ne..?

Sai Mama ta fara bala'i tana fadim"Kaga Badar din ne a gidan..?da makaranta zataji ko da aikin gida ba zaune take ballatana kace"

Kai tsaye yace"Ai ba kullum ake makaranta ba Mama ita Hafsah ai karatun take yi kuma bai hanata ta taya yayarta aiki ba."

Mama ta cika tayi fam ta faara fadin"Na lura ai yanzu yarinyar nan tafini Daraja a idon ka saboda tana Dauke maka wasu laluron,har Abada bazan so Dangin jaraba da cin Amana ba'"

Naga cin mutumci zai yi yawa sai na tashi na fice sai yi take yi ban bi ta kanta ba, na dauki pos dina da na siya da kudi aciki nayi tafiya ta, adaidaita na hau har anguwan su Hajiya kusa da jami'ar alkalam.

Nasameta a gida da tana shirin fita ne ma sai gani,sai ta fasa bayan mun gaisa tamin bayanin komai zan had'a Turaren rushi da na Humra sai kwallacha sai zan yi ma Amaryan gyaran jiki,duka zasu bani dubu dari biyu,Naji kudi sai na rude cikin Firgici nace"Hajiya duka nawa..?

Hajiya na dariya tace"Eh kudin aikin ki da ladan ki ba'

Sai na hau mata Godiya sai ta bata rai tana fadin bata so na koma na zauna araina ina Hamdala,Nan take ta bani dubu dari a hannuna sauran tace zata Turamin ta banki ta karishe da fadin"Sati mai shiga amaryan zata zo nan zaki zo ki yi mata ko sai dai ta biyo ki gida..?

Cikin Ladabina nace"Hajiya sai dai gida kinga ga yara sannan ga Mama bazai yuyu na rika Dadewa a waje ba"

Hajiya tace"Eh hakane shiyasa da suka yi mganar girki nace su dauki wata kawai zuwan ki kaduna da wahala"

Na jinjina mata kai sai tace ba Damuwa fita zatayi duk abunda ake ciki sai mun yi waya,tare muka fita da ita bayan ta bani kyautar atamfa da Mayafi,sai turare da lotion mai kyau,tare muka taho Direban ta ya Daukoni sai da suka saukeni a gida sannan ya wuce da ita in da zataje.

Bakina kamar gonar auduga haka na shiga gidan cikin murna naja Hafsah Daki na zayyana mata komai na nuna mata kudin cikin Farinciki tace"yaya Fa'iza Hajiya tana da kirki tana son ki da arziki"

Ina jinjina kudin hannuna nace"Bari Hafsatu Allah dai ya biya ta kawai"

Aranar bamu je kasuwa ba sai washegari mukaje da Hafsah ta tayani na sissiyo abunda zan bukata ina Dawowa na Dukufa na fara aikin Hada Turaruka,araina ina jin duka matsalolina zan kauda su in na samu wannan riban aikin,Aikin zobo sai ya koma sau daya a rana kunin Aya ma sai da yammah Lokaci na bada kacokan kan hada Turarukan nan ban rufe kwana hudu ba, na gama su duka,Kwallachan ne ma ta bani wahala ita sai da nayi kwanaki ban gama ba,inagamawa na kira Hajiya sai tace na ijiye komai a Hannuna in su Laila sun gama gyaran jiki in zasu tafi sai su tafi dashi.

Haka ko akayi satin bikin Amaryan Laila mai kyau da ita yar gayu ga ilimi ga nasaba ga kudi,ma'aikaciyar banki ne a kaduna suke Raliya ta dinga rakota kullumn da yammah muke farawa sai shida,A tsakar gida nake bazamana Tabarmana a rumfar nan Ishaq na Daki baya fitowa ga Hafsah wani Lokacin harda Badariya sai abun ya kara armashi,Laila ba ruwanta ga sakin fuska Anty Fa'iza kasa da sama take kirana kamar yadda Raliya ke Kirana,Sannan jininta ya shaku ita da Anun ta dinga rokona in bar ta su Tafi Bikin ta kaduna da ita Amana Hajiya zasu dawo da ita ban yi mgana ba sanin Halin Babansu da Mama ba lalle su bari ba.

Sati daya nayi ina mata sai ga shi ta fito shar da ita abunka ga farar fata,ga jiki lawai lawai sai tashin kamshi take yi,Da naga ta matsa da mganar Tafiya da Anum sai nayi ma Yaya Ishaq mgana da kaina nayi mamaki da ya barta ammh yace kada ta Dad'e a dawo masa da yarsa. ranar Litini Laila taji Dadi tana ta Godiya Direba yazo ya kwashe su ranar karshe da kayan su aranar kuma Hajiya ta Turomin sauran kudina, na daka tsalle ina murna nayi sujuda na gode ma Allah.

Batare da sanin Yaya Ishaq ba,naje na yi ma Amir komai har Uniform an basa na Biya musu kudin Tahfeez sannan na shiga kasuwa na siyo mai takalmin makaranta da jaka da littafai,yanzu nima sana'a ta Budemin ido nasan sirrin shiga kasuwa lungu da sako.



*INGANTACCEN ZANCE*.


*Akwai da INGANTATUN SAIWOWI na gyaran mejego ko amare*.

*Haka uwargida ma ba'a barta a baya ba da irin nata tagomashin*

*Kaya ne masu kyua ba garabiti ba, takanas ake kawo su daga chadi.*

*Idan kina da kannen da za'a aurar, ki zo ki yi musu tanadi na mussaman*.

*SAIWOWIN itatuwane da basu da illah*

*Da sau'ki zaki same su, amma aikinsu yawa ne dasu.* 

*Kawai ki tuntu'bi Surayya HALIN YAU a wannan lambar dan samun gamshasshen bayani*

*08032773332.*

      ✍️.




*Janafty*

[7/5, 6:22 PM] +234 810 299 5100: *KNKB2005*


*Ki biya ki karanta cikin salama,Kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta min littafi,Sannan kada ki yad'amin shi,Pay N500 regular ko kuma VIP N1000, Via Jamila Umar Gt bank 05521790550,ban da tsarin kati wannan karo a turo ta POS, Shaidar biya ta wannan lambar 09069067488*


Ranar monday da safe bayan yaran sun shirya Hafsah tayi musu abun karyawa,Musty sai tura baki yake yi shi bazai je makaranta ba yau. 

Na kallesa ina kokarin saka masa safa yana Turje kafa cikin haushi na mangarar da kansa ina fadin"Zaka tsaya ko sai na dake ka..?

Sai ya fara kokarin sakin mun kuka na ko zare mai ido ina fadin"Na dake ka ne da zaka min kuka..?

Amir na gefe da ya shirya Tsaf yau zai fara zuwa makaranta yace"Umma cewa yayi bazai je ba, saboda Anum bata nan yau"

Na kallesa da mamaki sai abun nasa ma ya bani dariya na jawosa jikina na Rumgume ina fadin"Haba babban mutum na Umma.Anum din ai yau zata dawo yi hakuri ka saki ranka kaji"

Cikin muryan kuka yace"Da gaske yau zata dawo..?

Da sauri na amsa mai da Insha Allahu sai ya saki ihu Ahmad na tayasa Amir na gefe an saka hannuwa aljihun wandonsa kamar wani babba na kallesa ina Dariya Hafsah ta fito daga Daki tana fadin"A'a yan jss ba zama ne yau..?a tsaye zamu tsaya..?

Fuska yayi bai yi mgana ya Dauki Sabuwar Jakarsa ya rataya yana fadin"Umma yaran nan su zo mu tafi"

Na bisu da Allah ya kiyaye hanya bayan na rike ma Ahmad jaka zan rakasu kofar gida Hafsah ta daga murya tana fadin"Amir shine ba mgana..?zaka zo ka same ni ne.."

Muna gabda fita daga falon naji muryan Yaya Ishaq a sama yana fadin"Yaushe Amir ya fara zuwa makaranta ban sani ba..?

Su sun riga sun fice sai na mikama Hafsah jakar Ahmad tabi bayan su ni kuma sai na Dawo tsakiyar falon, yana daga kofar Dakinsa alamun yanzu ya fito sanda zamu fita daga falon zuwa waje.

Cikin sanyi na, na gaishesa ya amsa a gajarce yana sake fadin'Ko ba shi ba ne nagani da kayan makaranta ya fita da su Ahmad ba.?

Kai tsaye nace"Shine ni naje nayi biya komai ranar jumma'a yau suka ce ya fara zuwa tunda karatu yayi nisa"

Sai kawai ya tsaya yana kallo na Fa'iza ta sauya sauyin dake basa mamaki bai isa in zata yi abu ta nemi shawaransa ba, ance mai hali baya fasa halinsa kawai sai ya fara fada yana fadin"Meyasa kika raina ni ne Fa'iza kin ware ni kan sha'anin ya'ya na ban isa ki fadamin Amir zai fara zuwa makaranta ba sai dai ki rika yin komai kanki tsaye..?sai yanzu na yarda da mganar Mama, kina ganin yanzu kina samun kudi kina Dauke laluran kanki da na gida shine kike ganin zaki iya yanke hukuncyi kan ya'yana to baki isa ba,ba na so.."

Ya karishe fad'a har yana nuna min yatsa kawai sai na saki baki ina kallonsa na kwaso gauron numfashi zan tare sa da mganar ya wuceni Fuu kamar kabubuwa ya fice sai Dakin Mama na bisa da kallo hannuna sabe da Haba na a fili na furta"Yau naji karfin hali ko na gani zencen ni Fa'iza"

To in ba karfin hali ba sai yanzu kasan da ya'yan ka ne?a baya da kake banzar ta dasu ka zabi wasu akan su ba'ayi maka mgana ba sai yanzu ne kake da bakin mgana..?

Kawai sai nayi tsaki na cigaba da Harkan gabana abun karyawansa ma sai Hafsah ya ma mgana ta basa, ni Daki na shige na kwanta a raina nace bazan sake yarda ka rika sakani Damuwa ba.

Daman da kullatan fad'an safe ya shiga kuma Dakin Mama ta kara ma Wutar fetir, da yammah sai ga Direban Hajiya ya kawo Anum da sha tara na arziki kaya akwati guda nata ga kayan wasa har da karamar Ipad na game din yara,da Sabuwar jakar makaranta da littafai da kayan biki cike da Jakar bikin ga Hoton Amarya da ango nan sannan ga kudi dubu goma Sabbin yan Hamsim Hamsin a Cikin wata farar takarda,Harda takalma masu kyau sai sweet da chaculate na su musty,Anum da shigem kaud'i sai murna take yi bakinta ya tsinke da Labari har Yaya Ishaq dake ciki sai da ya fito,Yana kallon kayan Anum na ganinsa ta nufesa ta rikesa bakinta yaki yin shuru an bata kaza sun je kaza sun je kaza.

Fuskarsa ba fara'a ko kad'an,kamar ta Fahimta ne yasa ta bar ta batunsa ta kwashe kayan taje ta nuna ma Mama Hafsah taso ta hanata nace ta kyaleta ta shiga ba dad'ewa sai gata tazo kiransa in ji Mama, ya tashi ya tafi ba jimawa sai ga shi ya shigo ina faman tattara sauran kayan da Anum ta watsar ya daga murya yana fadin"Daga yau ya'ta bazata kara zuwa wani gida kwadayi ba"

Sai na Dago ina kallonsa ni yanzu ya Daina bani mamaki a baya sai nake ganin Rayuwa tasa yayi sanyi ammh daga Safiyar yau na Fahimci lambo yayi.

Kamar zan yi mai mgana sai na fasa na zata shikenan kawai sai naji yana fadin"In ke zaki je kije, ammh kada ki kara tura ya'ata wani gida da sunan kwaad'ayi."

Sai na sake dagowa ina kallonsa ban yi nauyin baki ba nace"to ai in dai kace naje kamar kace itama taje ne.Saboda ni ya'yana na zaba akan ka.Kai kuma ka manta ka zabi Zainab da iyalanta a kaina da ya'yanka..?

Tsuramin ido yayi nasan yana mamakin kalamai na ne ni kuma ganin yaji mganata yasa na juya nayi shigewata Daki na barsa nan bansa ya yakare ba, Anum ta dawo da kayan ba jimawa su Amir suka dawo da ga makaranta sai Ihu ya tashi Anum ta Dawo labarai ta rika basu na abunda ya faru a chan har da abunda taci ta kwaso musu kayan suka yi min Baja baja da falo sai da na fito nayi musu fad'a Amir ya hau taya Anum tattara kayan yana fadin"Kiyi hakuri Umma zamu kwashe"

Sai na Sassauta ina fadin"Lokacin sallah yayi ayi alwala ku tafi masallaci Anum tazo muyi namu a gida"

Da haka suka kwashe kayan suka maida Dakinsu mazan suka fita alwala Babansu na dakin Mama ya tarasu suka tafi masallaci mu kuma mukayi namu agida ba abinci sai Hafsah tayi Taliya jallop,ta sa ka kazan da Anum tazo da shi na biki aciki,ita muka ci da Daddare kafin mu kwanta na raba ma yaran kayan Fulawan da Anum tazo da shi na Bikin harda lemuka na kuma aika ma Mama nata,ta kuma karb'e ko kunya, sai da safe na Kira Hajiya nayi mata godiya.

Daga wannan lokacin sai ya Dawo sak Yaya Ishaq din da na sani mara ragowa sannan mai tsanani sai na Fahinmci,wani abu har da zafin Talauci ya sake firgitasa sai dai bai min tijaran da ya saba da agaban mama ko mutane, saboda yaga bakina ya bude yanzu zan maidasa mganar da bazai so ta fita wani yajita ba.

Duk nayi biris da shi domin har ga Allah ba ina zaune saboda ina son sa ba ne,babu wani birbishin so a cikin zuciyata in a baya na so shi Saboda yana Uban ya'yana yanzu ko wannan Darajan bana dubawa,abu d'aya na sani ina zaune ne saboda ya'yana ba saboda shi ko jiginannen auransa ba. Shiyasa nake kama kaina ina chan ina Hidimar sana'ata da ga shi Har maman bana ta kansu,Anty Binta ma ta rage zuwa akai akai su Anty Mahma ma sai dai su leko mu ni kuma ban fasa abunda na yi niyya ba,Kananun lalurori har manyan ma ina Daukan su da sana'ar da nake yi,wannan zafin ran da na Talauci ban yarda na zauna ya saukemin ba,Ya saba in ya gama min Tijara na rika basa Hakuri ammh yanzu da ya fara in bana jin mgana zan bama banza ajiyarsa ko na bar masa wajen.

A cikin wannan takun sakan da muke yi ne, kayan abinci suka kare dole ni na fidda kudi na siya Mama da gadara duk abunda take bukata zatace na bata kaza kamar ita nake yi ma wahalan,sai dai ban taba biye mata ba, ina ganin ta a matsayin uwa shiyasa ban taba Daga kai akanta ba. shi kuma komai nayi sai yace na rubuta in ya samu aiki zai Biyani ni ko nace shi ya Lissafa da kansa mana 

Muna cikin haka zazzabi ya Sarke sa kamar wasa ya kwantar da shi Ranar kwance ya yini Dakin mama,Yadda bai fad'amin ba shi da lafiya ba, nima ina da Miskilanci ko lekawa Dakin Maman ban yi ba ballatana nayi mai sannu Abakin su Amir naji Daada bai da lafiya, Mama ce ta leko da kanta Dakina da bata taba shigowa ba, sai dai ta tsaya daga bakin kofa tana ce min na bada kudi Amir ya raka Ishaq kemis  bai jin dadi,kamar nace bani da shi sai kuma ban ce ba na ba ma Amir dubu biyu suka tafi a ka mishi allurai da mganguna ashe maleria ce ta kamasa,ni iya dakina da dakin yara nake siyan ma mganin Sauro na kunna sai Dakin Mama ban yi tunanin yana jin cizon sauro ba ma.

Abu kamar wasa daga zazzabi sai zawo cikin dare haka ya kwana zagayawa,da safe har da Amai duk  karfinsa ya kare,washegari daga zuwa bayi sai dai na je na daukosa duk ya bata jikinsa da amai da zawo duk yadda nake kauce ma wata mu'amalan ganin sirin juna tsakanina da shi sai da na yaye wannan Hijabin ranar,Tun kafin auran sa da Zainab ko Hannuna sai da kuskure yake gegata ballatana ganin juna a yanayin da bai dace ba,Sai ranar ni nayi masa wanka Maman dai bata yi masa rana ba,Ina yi ina kauce kauce shi kuma jiki yayi lakwas duk yayi laushi sai abun yayi min wani barambaram kwai namiji da suna Hajara.

Bayan na yi masa wankan na koma na wanke bayin da kuma kayan shi da ya bata, sannan na fita baya damu kad'an inda Chemist yake na kira mai zaman wajen yazo ya gansa ya dora masa karin ruwa da allurai abu kamar wasa nan take sai da ya chajeni dubu Hudu,kada mutum ya raina ciwo komai kankantarsa,Yara sai dai suka Dawo makaranta suka iske sa rashe rashe ana masa karin ruwa,sai duk jikinsu yayi sanyi sai da nayi ta lallashin su sannan suka saki jiki yasha wahala rana zuwa dare duk ya fada abinci ma,ya kasa ci sai da Anty Binta tazo mai da Ferfesun kayan ciki ya samu ya ci kad'an yace bakinsa D'aci ga zazzabi ga amai da gudaawa.

Anty Binta bata neman zaman lafiya sai da tayi korafin wai meyasa ba'a kaisa asibiti ba? Mama tace mugunta ta ta ce ta tashi kuma ina da kudin naki kaisa asibitin,ni bana biye musu sai na nuna ma ban jisu ba Mama fa sai ciwon d'anta ta taba shiga bangarena ita kuma Anty Binta in asibitin banza ne meyasa bata Dauke sa ta kai sa ba..?

Wlh na yarda da maganan Hausawa da sukace in kana da abun yi,ba komai ke damunka ba. a baya ne in Mama ko Anty Binta sun min wani abu yake damuna nayi ta kuka yanzu na manta rabo na da kuka akan su,To ayyukan gabana ma sun isheni inaga naga Lokacin sauraransu ko suna yi baya Damuna, kamar irin na riga na zama Jan wuya a lamarin ballatana yanzu da nake yawan samun masu son Turaruka ta bangaran Hajiya sai ayyukana suka yi min yawa.

Ashe sun raina kulawar da nake basa balle da suka ga kurajen baki sun fito mai yaba yaba na alamun wucewa Mura, sai Mama ta saka Anty Binta ta kira Zainab na ta fad'amata wai tunda bazan iya kula dashi ba,yana da wata matar zata zo ta kula da shi,Sanda akayi ma bana gidan naje kasuwa da na Dawo Hafsah take fadamin sai nayi mirmishi ban ce komai ba.

Ashe ko sun kirata sun zuzuta abun Hankali tashe ta d'au alfarma a wajen aiki ta taso,ita da Fadil Farhan saboda makaranta ina tsaka da Hidiman Zobo na ta shigo,Direba na binta da kayanta A karamar a kwatinta kwata kwata ban yi mamakin ganinta ba, na tsallake komai na tarbeta sai dai Mama bata bari ba,ta janyeta zuwa Dakinta chan ta sauka a fili nace a gayyas.

Na koma dakina na cigaba da aikin da nake yi,Chan ba jimawa sai gasu sun shigo ita da Mama,Zainab na rike da Fadil sai alokacin muka gaisa kallo na take yi tana kare ma falon kallo Mama tayi mata Jagora har dakin Yaya Ishaq ni dai ban bisu ba saboda ba wanda ya gayyaceni sun dan jima aciki sannan suka fito sai ta kalleni tana fadin"Maman Amir zobo kike saidawa yanzu?

Ina yar dariya nace mata'"Eh wlh muna tabawa ya hanya..?ina Kika baro mana Farhan..?

Kai tsaye tace"Yana wajen mommy saboda makaranta"

Mama sai jiranta take yi daga waje ganin muna ta mgana yasa ta Dago labule tana fadin"Zainab muje ki yi wanka ki yi sallah sai ki ci abinci"

Sai ta amsa mata kafin ta fitan sai da tace min"Ashe Honey haka yayi ta rashin lafiya..?

Sai na gyada mata kai ina fadin"Ai yama ji sauki yanzu'

Cikin jimami tace"Ayya Allah ya basa lafiya"

Na amsa mata da Ameem sannan ta fice zuwa Dakin Mama ni ko sai da na gama zuba zobo na sannan na shirya ma zainab abinci daman da rana Shinkafa da miya nayi mana da Salat har dare saboda na gaJi bazan iya wani girki ba,har dakin Mama na bita da shi har da zobon na zuba mata

Bata a falo kila tana ciki Mama sai Hararata take yi ban bi ta kanta ba na sauke abincin hannuna na fice abuna.

Sai da na had'a kayan wanke wanke bayan yara sun dawo makaranta ni nace su shiga Dakin Mama su gaida Antynsu suka shiga gabadayansu suka gaisheta daganan bayan sun ci abinci suka shige Dakin babansu Fadil na Hannunsa suna ta wasa Amir ne kadai ke falo yana duba Littafansa na makaranta.

Da kaina na shiga zan dauko kololina da wanda na kai ma Mama nata,na iske zainab na zaune tayi wanka ta sauya kaya waya a hannunta tana ta Dannawa sannu da gida tamin na duka ina kwashe kwanukan da suka yi amfani da shi Mama na gefe nasan hira suke yi da na shigo ne Maman ta Dauke mganar ammh saboda salon cin Mutumci sai ta gyara zama tana fadin"Zainab nace ba.."

Sai ta Dago tana fadin"Na'am Mama"

Mama tace"Daman so nake naji ko zaki d'an kwana biyu kafin ki koma..?

Zainab ta yamutsa fuska kafin tace"Anya? hutun kwana biyu suka bani a wajen aiki"

Mama ta kalleni ta gefen ido tana fadin"Gaskiya gwara ki tsaya ki kula da shi.ita wannan baya gabanta ta sana'arta take yi tunda ta fara wannan sana'ar nata bata kallon kowa da Daraja kema matarsa ce shiyasa nace Binta ta kiraki kizo ke kila kya kula da shi yadda ya kamata"

Sai tayi Dariya batace komai ba ni kuma ina cigaba da Tattara kwanukana ina jinta daman tayi mganar ne saboda naji.

Ganin Zainab batayi mgana ba yasa Mama ta cigaba da fadin"Ni dama in kin tashi tafiya zaki tafi dashi chan Abujan,zan fi samun kwanciyar Hankali zamansa anan bai da wani amfani"

Na mike kenan Zainab tace"Mama naga Maman Amir fa na kula da shi"sai Mama ta wani yarfa Hannu tana fadin"Wlh bata kula da shi, wannan da kika gani ai muguwa ce ta sosai"

Tafad'a Lokaci daya tana nuna ni da baki kamar zan fita na barsu sai na fad'a kamar an min wahayin mganar na Tsaya ina kallon Mama kafin nace"Aiko baki ce ta tsaya ta kula da shi ba tunda tazo, na sakar mata komai Tunda itama matarsa ce, kamar yadda yake da Hakki a kaina itama yana da Hakkin akanta"

Daga haka na juya nayi ficewata Mama ta rakani da fadin"babu abunda ta iya yanzu sai rashin kunya har shi ta raina"

ni dai bansan ya suka kare ba ina wanke wanke abun na dawomin ni kaina ina mamakin yadda bakina ya bude wani Lokacin na yarda ba shawara ko nuniya ke saka mace tayi baki a gidan mijinta ba Wuya ce mutanen duniya ke chanzata,batare da tama sani ba kamar yadda yake faruwa dani domin ban taba kawowa ma kaina zan iya maida ma Yaya Ishaq mgana ba ko shi ko Anty Binta ba sai ga shi shakkar da nake ji da yanzu wlh bana gani,wani abun ma ina raga musu ne saboda wasu Dalilai.

Tunda Mama ta raina kokarina ni ko a raina nace sai na bata mamaki na tsame hannuna a kula da shi ai daman ba hakki na ba ne, ita da bai jingine auranta ba,yafi zama Dolenta ta kula da shi nifa daman taimako ne da Darajan ya'ya sai ta wani Fanni in na Duba zumumci.

Sai ana mangariba na gama wanke wanken nan sai lokacin Hafsah da Badariya suka dawo,Amir da su musty sun bi babansu zuwa masallaci daya fara rarrafa d'azu,sannu da gida suka yi min kowacce ta shige inda tafi wayau.

Ina komawa Daki daman na Dafa ruwan zafi nayi wanka,Hafsah kuma nace in tayi sallah taci abinci taje makotan mu ta Dauko min ninkan Ayan da dazu yaron gidan ya shigo Siyan zobo na bashi sai ta amsamun na shige Dakina nayi wanka nayi sallah na zauna ina azkar,ina ga sai da sukayi sallar isha'i suka dawo shi Uban Gayyar Dakin Mama ya shige yaran kuma suka dawo Daki Hafsah da ta dawo dauko nikan na saka ta raba sauran abinci nace ta diba ta kai Dakin Mama da yawa Saboda Zainab sauran su ci su da yara.

Akace Namiji ya iya munafunci nidai tunda na shiga ban fito ba Hafsah na bari da hada kunin Aya,Ashe da ya gama zamansa Dakin Mama tare da Zainab suka dawo Dakinsa sai suka bar Fadil wajen Mama bakinta washe,Adakin nasa ta kwana ni ban sani ba ko da na tashi da asuba ban lekasa ba ina ma yara shirin tafiya makaranta,muna falo da ni da yaran suna cin abinci sai gata ta fito tana mika sanye da rigar barci Riga da wando masu taushi gashinta kanta ya bazu wata hula ce ta saka ana ganin kanta,sau daya na kalleta ban kara ba ita ta fara gaisheni na amsa ta cikin Sakin Fuska har ga Allah ban ji Haushi ba, to me zai dameni ai ba yau aka fara ba an dade ana haka.

Abun karin ma na aika Dakin Mama basu ci ba Zainab ta basu kudi suka siyi kayan tea Badariya tazo kitchen dina ta soya musu kwai, ni ina Dakina Hafsah ke fadamin nace saji da shi dai.

Sai da chan rana na shiga na Duba sa yana kwance sun yi kaca kaca da Dakin,daga nesa na tsaya na gaishe shi da jiki ya amsa sai naga yana karemin kallo sai na Tsargu da Sauri na kalli kaina Riga da sikat ne a jikina Atamfar ni na siyeta da kudina na Dinkata sai dai dinkin yayi min Cif a jikina ganin yadda ya kuramin ido ne yasa kawai na juya zan fice da Sauri ya yunkura ya mike yana kiran sunana na Juyo ammh ban karisa gabansa sai yace"Fa'iza kariso mana bana jin dadin yadda kike maida Dakina kamar bakon ki"

Sai kalamansa suka bani mamaki kai tsaye nace"ai bakon ne a wajena.."

Bai damu ba sai ya dan kalli D'akin yana fadin''Haba Fa'ita kwana biyu ba'a zo an gyaramin Dakin ba.  sannan kuma ga kayana duk sun yi Datti wlh ko na sawa bani da shi"

Na kura masa ido ina Dariyan sunan da ya kirani wai Fa'i ta abunda ban taba ji ba ko acikin mafarki har da wani lankwasa wuya yake yi na yaudara sai kawai nayi Dariya kafin nace"Ai wannan ba Hurumina ba ne Hurumin Matarka ce ka kirata ta gyara dakin sannan ta kwashe kayan naka ta wanke"

Kai tsaye yace"Saboda me sai zeey.?ai ke kika saba yi Fa'iza kada ki bata ladan ki don Allah"

Karfin Halinsa ke bani mamaki cikin gajiya da mganar na juya ina fadin"Ba bata lada ba ne, Itama Hakkin ka na kanta ta kula dakai tunda tazo ta amsheni daman ni taimako nayi ba Hurumina ba ne"

Har zan fice ya kwalamin kira "Fa'iza..'

Sai na juyo ina fadin"Wlh bazan yi ba ka kire Zeey din taka mana, inace ita ma Matarka ce"

Sai kawai ya koma ya zauna yana fadin"Fa'iza yaushe na fara mgana kina min gaddama sannan yaushe na fara mgana kina sa'in sa da ni..?

Kai na tsaye nace"Tun ranar da ka furtamin da kanka ka zabi wata matarka fiye da ni nima tun ranar na zabi rayuwata da ya'yana sama da kai.Komai kaga ina yi maka don Allah da taimakon zumunci ne"

Daga haka na fice na barsa da sanyin jiki Hidmar hada zobo na fara satin nan Hafsah karatun Safe suke yi,Allah yasa tamin shara da Safe wanke wanke kadai nayi sai na share tsakar gidan na wanke ina wajen Zainab ta shige bata fito ba, ni ko dakin ban koma ba Fadil ne ya dinga kuka a Hannun Mama ta kasa lallashinsa sai na shiga na karbesa sai na Fahimci yunwa yake ji ina da Sauran garin kuni nan da nan na dora ruwan zafi daya tafasa na Damamai na Duramai tas ya shanye sai barci,naja zani na goyesa ram a bayana na cigaba da ayyukan gabana Mama daman tagaji da renon ta shige Daki tayi kwanciyarta Tunda baiwarta ta Dauke komai.

Da rana Danwake nayi da salat,aiki duk ya Chudemin Zainab kam da uban gayyar sun shige daki ba mai jin motsin su, Fadil na Dakina yayi barci da ya tashi nayi mai wanka nima nayi ban san fitan ta ba ta koma Dakin Mama tayi wanka ba,sai da ya tashi ya fara rigima na lekata sai na ganta na mika mata shi ina fadin"Ya tashi yana rigima"

Ta karbe tana fadin"Daman tunda naji sa shuru nace yana Hannun ki"

Mirmishi nayi mata na fice,ina komawa Daki na ci karo da shi ya fito Daga kitchen da ya gani sai yayi Turus ni kuma sai nayi kamar bangansa ba zan wuce dakina yace"Dama..dama kuna da ruwan zafi ne..?garin ai ko sanyi zazzabi bai sakeni ba kada na Dawo da shi da wanka da ruwan sanyi"

Da nayi niyyar na yi wucewa ta ne sai wata zuciyar tace ashe ya Dameki..?sai na juya ina"Ka kira Zainab ta saka maka mana"

Sai ya bude ido yana kallona,na ganin na juya yasa yasha gabana yana fadin"Don Allah Fa'iza don Allah nace.Zeey bata shiga kitchen achan komai ma'aaikata ke yi mata"

Rashin kunya ba Halina ba ne yasa na juya na koma kitchen na kunna gas na Doramai ruwan zafin na fice na barsa nan falon inaga da yayi zafi ne ya kashe gas din ya juye,yau alhamis ne da la'asar yara suka dawo makaranta Amir ya taimakeni ya tayani Dura zobon a gorina Anum na shirya mana nayi na Safe har ya kare wannan na yammah ne,Addu'a nake yi Allah ya dawo da Hafsah ta dora girki sai biyar da wani abu ta shigo tana shigowa Amir yace'"Umma ga Antyn Hafsan ta dawo"

Daga ganinta ta gaji ta sauke jaka tana fadin"Da Antyn Hafsah tayi me..?

Ina Dariya nace'Yaji ina ta cigiyarki ne aiki yayi min yawa ban dora girki ba"

Sai ta ce"Bari naci abinci na dawo hayyacina"Da sauri nace"Yauwa yar albarka mu in mun gama sai mu had'a kwanuka mu yi wanke wanke"

Da Sauri Anum tace"Umma ni zan yi"

Ina dariya nace"Ko baki ce ba tare zamu yi kafin nan gaba ki iya na sakar miki,ammh kafin sai kin share inda muka bata"

Musty yace"Ummi ni zan share"

Nace"To ya'yan Umma yan albarka"

Ahmad na gefe yace"Umma zan wanke miki robobi"

Amir yace"Kadai samu na wasa"

Gabadayanmu muka saka Dariya gabadaya bani da damuwa indai ina ganin Dariyan ya'yana su nafi damuwa da su bangaran su Mama tunda zainab tazo ta bud'e musu bakin aljihu suna cin dadin su yau nama gobe kaza ni dai ya'yana suna daki basu gani ba,ballatana su saka rai ammh fa Fadil na wajena ni nake mai komai har wanka uwar tana nanike wajen miji ana shan soyayyah.

Washegari da Safe bayan yara sun tafi makaranta na fada ma Hafsah yau zobo Sau daya zamu yi,sai kunin Aya shiyasa da Safen bayan yara sun tafi makaranata na samu kujera na kwanta sai barci Hafsah ke dafa zobon awaje basu da shiga makaranta yau,ai naji dadin zaman Hafsah a wajena tana bala'in taimakamin kan sha'anin gida da sana'ata wani lokacin ba domin ita ba,bansan ya zan rika yi da wasu ayyukan ba.

Na fara barci sama sama na rika jin Hayaniya na gyara kwanciyata saboda ban ji hayaniyar ko ta macece ba,Sai da Mama ta shigo har Falona ina kwance kawai naji ta Dakamin duka na Bude idanuwana da suka yi ja Saboda barci sai naga Mama a saman kaina 

Tsakani ga Allah ina gajiya saboda aikin Hannu nake yi komai sai na sarrafashi da kaina.

Ina kokarin tashi zaune kawai ta hau ni da fad'a nama kasa gane in ta dosa sai da nace"Lafiya Mama..?

Cikin wani kallo tace min"Bansani ba.Kya ce lafiya mana kina kwance kina barci,shi kuma ga shi chan bai da lafiya shi kika bari da wankin kayansa"

Sai taga na mike kawai zan shige cikin D'akina kai tsaye ta saka hannu ta fizgoni na dawo gabanta tana zare min ido tace"Don ubanki ina mgana kina wucewa,ni sa'arki ce.?




*INGANTACCEN ZANCE*.


*Akwai da INGANTATUN SAIWOWI na gyaran mejego ko amare*.

*Haka uwargida ma ba'a barta a baya ba da irin nata tagomashin*

*Kaya ne masu kyua ba garabiti ba, takanas ake kawo su daga chadi.*

*Idan kina da kannen da za'a aurar, ki zo ki yi musu tanadi na mussaman*.

*SAIWOWIN itatuwane da basu da illah*

*Da sau'ki zaki same su, amma aikinsu yawa ne dasu.* 

*Kawai ki tuntu'bi Surayya HALIN YAU a wannan lambar dan samun gamshasshen bayani*

*08032773332.*

      ✍️.





*Janafty*




[7/12, 10:17 PM] +234 906 320 7298: *KNKB2006*


*Ki biya ki karanta cikin salama,Kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta min littafi,Sannan kada ki yad'amin shi,Pay N500 regular ko kuma VIP N1000, Via Jamila Umar Gt bank 0552179550,ban da tsarin kati wannan karon, a turo ta POS, Shaidar biya ta wannan lambar 09069067488*


Ba nufina in yi Mama rashin kunya ba ne, saboda a uwa na Dauketa sai na Sadda kaina kasa ina fadin"Naga fad'an bai shafeni ba ne Mama"

Sai ta saki baki tana kallona lokaci daya tana fadin"Wato bai shafe ki ba? ko ni ki keso na kwashe kayan nasa na wanke mai ishashiya Dangin Jaraba?

Sai na dago kai kamar zan yi mgana sai na fasa na kama Hanya na fita Tsaakar gida yana Zaune kan kujerata ta tsuggunon Tsakar gida, ga kaya a gabansa ya saka Hafsah ta taran masa ruwan famfo Har ga Allah Dariya sai da ta kusa kamani yadda yayi kamar mai ko wankin,Karisa fitowa nayi ina fadin"wanki da kanka ina Zainab din..?

Ko kallo na bai yi ba nima sai na juya ina kallon Mama da ta zata da na fito zan karbesa ne, sai taga akasin haka kafin tayi mgana na tare ta da fadin"Mama kada kiga laifina ba ga Zainab ba, ai itama matarsa ce. kince tana da Hakki a kansa kamar yadda nake dashi daman kuma kin kirata tazo ta kula dashi tunda kin ce ni ba takansa nake bi ba,Ki kirata tana ciki ta fito ta karb'i kayansa ta wanke shima ai yana daga cikin Hakkokin da kika mgana"

Ina gama fad'in haka na kama Hanyar Dakina Mama ta rakani da kallo cikin mamaki tace"Fa'iza yanzu ni kike fadama wannan mganar..?

Kafin nayi mgana ya katseta da fadin"Don Allah kyaleta Mama tun jiya na roketa ta rantse bazatayi ba"

Sai mama ta shiga tafa Hannu tana salallami ni ko nayi shigewata Dakina na kwanta a gado na,ban san ya suka kare ba sai wajen sha d'aya na Safe na tashi na iske Hafsah ta gama Had'a zobon tana jiran ya huce ni ita ke bani Labarin yadda suka kare Zainab din ta fito tana wani yamutsa fuska tace a kwashe kayan aka kai wanki da guga zata bada kudin wai har tana fadin"Honey sai da nace kayi zaman ka achan ka ki inda kana chan wani kuma wanki ne sai kayi da kanka..?

Dariya ma abun ya bani Hafsah tace"Yaya fa'iza wlh kin burgeni gwara da kika fara nuna ma Mama abunda take yi bata kyautawa"

Mirmishi kawai nayi ban ce komai ba,ni ba mgana na maida mata ba Abunda ta bukata nayi mata daman na rantse bazan kara yi masa komai ba indai matarsa na nan,ba ni sun raina nawa ba? to yar masu da shi tazo tayi musu su gani.

Ashe mgana bata mutu ba mama ta rika yawo dani wai Ishaq bai da lafiya bani da Tausayi da Imani na barsa zai wanke kayansa da kansa, da Mama tamin mgana nayi mata rashin kunya da Yammah sai ga Anty Binta tare da Anty Mahma har Dakina Anty Binta ta biyoni tana gayamin duk mganar da tazo bakinta cin mutumci sai wanda ta manta,Kamar na sani nace Hafsah ta tafi da Anum da Amir gidan nik'an Aya Ahmad da Musty ne kuma suna Dakin Mama wajen Fadil.

Ko daga kaina ban yi na kalleta ba,sai da naga ta Dage wai in nace zan cigaba da yi ma Mama rashin kunya zamana ne zai kare a inda aka rufamin asiri sai alokacin na Dago ina kallonta kafin nace"To ko a yanzu din ma me ya rage..? Adai yi sha'ani an cuci na kauye"

Bata Fahimci mganata ba ta cigaba da fadin mganarta ta dauka irin da ne har tana kokarin kamamin kunni nako mike nayi baya ina kallonta cikin Hargowa tace"Zaki dake ni ne Tattaciya..?bar ganin kin fara wannan sana'ar ta biyar goma dama bamu san asalin balbela ba ne sai ta gaya ma da ga kasar masar ta fito.."

Na lura suna adawa da samun Cigaba na, a raina ko nace sai dai ku mutu sana'a yanzu na fara shi wlh.

Ganin ta fara isata da mgana ga Musty ya shigo ya tsaya yana kallon mu yasa nace"kiyi hakuri Anty Binta ni fa ba rashin kunya nayi ma mama ba. Cewa tayi ta kira zainab ne saboda tazo ta kula da shi,Tunda ni ba na kula dashi. nayi laifi domin na sakar mata komai tunda gata tazo.? ai acikin kula dashi har da yi masa wankin kayansa.."

Kawai sai ta kalleni bataji kunya ba tace"Lalle kin cika mara kunya Zainab din sa'arki ce ko Matsayin ku da'ya da zaki rika had'a kanki da ita..?

Sai na dago ina mirmishi kafin nace'Tabbas ba matsayin mu d'aya ba, nasan wannan tun kafin ya aurota ya raba mana matsayi kuma kuka rabamananwannan matsayin. sannan ni nasan ba sa'ata bace saboda ni marainiya ce ban aje ba sannan ban ba wani ajiya ba, sannan ni ba yar gata bace kuma ba yar boko irinta ba, ni yar gargajiya ce da wahala da komai na ke rayuwata kin ga ni kaina nasan tazaran dake tsakani da ita kamar tazaran sama da kasa ne ku yi hakuri na manta ne ammh daga yau zan kiyaye zan kuma tsaya a iya matsayina"

Sai ta kad'a kai tana fadin"Da kin ma kanki kiyamullaili"

Ta juya ta fita Musty ya rugo da gudu ya rikeni yana fadin"Umma zagin ki take yi..?.

Da sauri nace"A"a hira muke yi Musty"

Yaro da Fahimtar abu sai yace"Umma naga fa fada take miki"

Nasan sa da surutu su Amir na Dawowa zai gaya musu sai nace"Waya fad'a maka..?

Hira muke yi baka gani ba.?

Sai yayi shuru ya kasa mgana ni kuma sai na daga sa sama ina juyi da shi sai ya fara bangalan dariya.

Har Anty Mahma sai da suka kitso mata zencen ta shigo Dakina tana fadin"Gaskiya Fa'iza baki kyauta ba,ban san ki da haka ba,Bai kamata bai da lafiya ki barsa da wanki ba. kuma ina ruwanki da Zainab ita da ba mazauniya ba, dubiya tazo yi zata koma inda ta fito ke dai kiyi aikin ladanki kada ki manta duk abunda kika yi na lada agidan mijinki za'a ninka miki ne kin karanta na kuma san kin san haka"

Gani nayi in na tsaya mata bayani ma bata Lokaci sai kawai nace"In sha Allahu baza'a kara ba"

Sai taji dadi ta dafani tana fadin"Yauwa ko ke fa Fa'iza in anjuma ki shiga ki bama Mama Hakuri shima ki basa Hakuri"

Sai na gyad'a mata kai araina ina jinjina al'amarin wannan rayuwar.

Sai ta gyara zama tana fadin"Hajiya Fa'iza mai zobo da kunin aya naga fa alaman kin fara samun kasa da wannan sana'ar kin zama big madam"

Sai ta bani dariya na dara ina fadin"Kai Anty mahma da zoyala"

Agabanta Hafsah ta had'a kunin Ayan da zasu tafi na bata harda zobo ta karba tana fadin"Kada mu zama karya Jali fa..?.

Sai nace"Kada ki damu bazaku karya ba"

Sai tamin godiya ta fice zuwa Dakin Mama ina jin tafiyar su ita da Anty Binta Gogan daman dakin Mama ya yini shiyasa Tun safe bamu hadu da Zainab ba sai da Daddare muna falo ina ma yara karatun Hadisi suka shigo ita da shi,Yaran sun riga sun sani in suna karatu ba na barinsu su tashi sai ba su tashi ba Ahmad ne ya mike da gudu ya nufesa sai ya Dagasa sama yana fadin"Kai ma fa ka fara zama Lukuti irin musty"

Saukesa yayi ko sauraran gaurancin da Ahmad ke masa bai yi ba Zainab kuwa kala batace min ba,gani nayi kamar ranta yana bace ne sai nima na kame kaina haka suka shige ko sannu Daga shi har ita ba wanda yace min. nima ban damu ba na cigaba da yi ma yara karatu bayan mun gama nayi musu Tarihi sannan nace su je su kwanta.

Ni da Anum da Hafsah muke kwana adakina Hatta Ahmad na maida shi tare da su Amir da Safiyar asabar suna da Tahfezz karfe Takwas na tafi kaisu da kaina Saboda Amir ya shiga ajin yan Hadda akwai littafan da zai siya sannan ina son naji karin bayani,na jima a makarantan suna ta gayamin kokarin yarana musamman Anum da Amir malamin Qur'anin su Anum yake min godiya lokaci d'aya yana Fadin"Saudatu ta fadamin Ummansu ke musu karatu agida sosai na yaba miki kin yi kokari kuma hakan da kike yi ya kara taimakon yara wajen hazaka da maida Hankali da ace iyaye mata da maza zasu san amfanin koyar da yaro kad'an daga abunda ka sani agida da yara da yawa sun zarce Tunanin iyayansu"

Na jinjina kai ina yarda da mganarsa Saboda ban zauna ba ko na bangaran Bokon da ban iya ba ina sawa su koyama junansu na addinin kuma da na kwarewa ban ta gajiyawa ba domin shi kadai gareni da zan basu su godemin watarana.

Sai wajen Tara na Dawo gidan na iske Rigima acikin gidan Tsakanin Zainab da Yaya Ishaq,Allah ya taimaka Hafsah bata nan na aiketa kasuwa ammh Badariya na gidan,Suna Dakinsa ne ammh fad'an nasu yayi kamarin da gabadayansu suke daga muryoyin su,da na dawo na kasa karisawa Dakina kamar zan shiga na gani wata zuciyar ta kwabeni tana fadin"Ke fa'iza ina ruwanki.?

Aiko sai na kama kaina na kama Sabgan gabana dakin yaran na fara gyarawa na fito falo kenan Sai ga shi ya fito har yana Tureni bai sani ba nayi Saurin yin gefe kamar kububuwa haka ya shige Dakin Mama itama sai gashi ta fito tabi bayansa tana fadin"Wlh baka isa ba Ishaq"

Itama tabi bayansa Fuu kamar zata tashi sama,sai gani rike da baki ina binsu da kallo ina nanata sunan Ishaq din da naji ta ambata, tunda nake ban taba jin ta kira sunansa gatsal ba sai dai Honey, ashe su Honey an jiki yau din nan.

Domin duk rashin karfin jina haka na rika jiyo tashin muryoyin su Mama nayi suna yi kamar ta kasa tsawarta musu ne sai ga Badariya ta shigo da Fadil tana Lallashinsa yana ta kuka na ijiye tsintsiyan Hannuna na karbesa ina fadin"Me ya same shi?

Badariya sai ta koma ta zauna tana fadin"Rudewa yayi da hayaniyar iyayan.Ni kaina barci nake yi sai da na tashi a firgice"

Kamar zan tambayeta sai kuma na fasa,Daman nasan zata koramin yadda akayi Kitchen na shiga na Dauko Purewater nazo na zauna ina basa yana karba da sauri alamun kishi yake ji cikin alamun Tausayi nace"Allah sarki bawan Allah kishi yake ji"

Badariya tace"Komai ma zai ji tun safe an fara fada,Daman ni nasan sai haka ya faru yadda Yaya Ishaq ya gina auransa ba kan turba mai kyau ba ne Anty Fa'iza"

Sai na kalleta ina fadin"Hala me ya ke faruwa..?.

Sai ta gyara zama tana fadin"Nima ban san kan mganan ba ina dai jin Kan tafiyar Anty zeey ne.Babanta ya Turo mata Mota tuni Direban ma ya iso zata koma Abuja to ina ga shine Yaya yace wlh bazata tafi ba sai dai in ta tafin ta fara shirin dawowa nan gabadaya ku zauna tare. shi bazai rika binta ba tunda baya aiki achan yanzu ita kuma ta Daka Tsalle tace bai isa ba sai ta tafi kuma bai isa ta ijiye aikinta ta Sauya rayuwarta Saboda shi ba,in bazai Bita ba sai dai ya bar shi"

Sai na jinjina kai jikina duk yayi sanyi Badariya tace"Ta wani fanni fa tana da gaskiya abunda ya zaba mata ne Tun farko rana tsaka ba shi da Hujjan da zai ce a'a duk wanda ya siya rariya yasan zata zubda ruwa"

Kafin nayi mgana Zainab ta shigo Dakin tana kiran Badariya ta kawo mata Fadil na mike na mika mata shi ta fita dashi nima sai na bita Daidai Zainab din ta fito da karamar akwatinta ta kalli Badariya tana fadin"muje mota da shi"

Taci gayunta ta yafa mayafinta abun nasa ya shafeni ko sallama batamin ba ta juya ta fara tafiya kenan Ya fito Daga Daki cikin Daga murya yace"Wlh Zainab in kika saka kafa kika fita daga gidan nan batare da izinina ba kin tafi kenan"

Dam!naji mganar nasa na d'ago ina kallonsa ita ma sai ta tsaya cak kafin ta juyo tana kallonsa Mama ta fito daga Daki hannunta a saman kai tana fadin"Na shiga uku ni Saudatu me zan ji haka..?Don Uban ka ka janye kalaman ka ko ranka ya baci"

Idanuwansa sun sauya launi yace"Bazan janye ba Mama haka nace.Wlh bazan zama jani talau ba..Ni ke auranta ko ita ke aurena..?

Mama ki duba fa wannan mgana taya za'a kafa min sharadin zuwa Abuja ina naga ko kudin mota.?zirga zirgan kansa ina naga kudin yinsa..?in a baya ina da aikin yi na dauki wannan Dawainiyar yanzu ta sani bani da shi To meyasa bazata zo ta zauna da ni a inda nake da shi ba in dai har da gaske tana so na?

Yafad'a cikin bayyana bacin ransa,Mama kuwa ta kasa mgana Ni kaina ban ce komai ba ni da Badariya muna tsaye cirko cirko,kamar wasu zakaru,ita ko Zainab sai batayi mgana ba ta jawo akwatinta ta shige Falona ta fito da waya tayi kira sai ta sauya Harshe turanci da Fillanci.

Shi kuma Mama ta shigar da shi Daki bansan me take fadamai ba,chan kuma sai ga Anty Binta suka sake kulewa Daki itako Zainab tana falo na kafa d'aya kan daya tana girgizawa karamar akwatinta na gefe sai hura Hanci take yi bini bini ana kiranta a waya tana mgana yadda batamin mgana ba nima sai na kama kaina na fito ina harkan gabana.

Zuwa azahar ina waje ina Dafa zobo na sai ga Mahaifin Zainab ya fad'o gidan kamar daga sama ashe jirgi ya shigo ya iso kano,Direban da yazo daukan Zainab yaje ya Daukosa Kai tsaye ya shigo cikin Hanzari ina gaishesa ko amsani bai yi ba cikin Kaushi da Dagawar murya yace"Ina Ishaq din..?

Muryansa ya fito da Zainab Daga dakina tana ganinsa ta nufesa da Sauri ta fada jikinsa ta fashe da kuka tana Fadin"Daddy wai ni Ishaq zai ce in na fita a bakin aure na..?ni Daddy Ishaq fa..?

Sai ta kara saka kuka,Cikin Kakkausan murya yace"Shi..Am here bai isa ya fad'a miki wannan mganar ba,Who is he.?

Mganarsa da kukan Zainab ya fito da Ishaq da Mama da Anty Binta suna ganinsa suka fara kame kame Mama ke fadin"Alhaji sai da ta taso ka?

Kallonta kawai yake yi bai yi mgana ba Ishaq ne ya nufesa yana fadin"Daddy k.."

Hannu ya d'agamin cikin tsawa kafin yace"Kayi min shuru Butulu kawai."

Sai ya tsaya ya kasa gaba ballatana baya Su Mama sai ido yayi kasa,Hannun Zainab ya kama kafin yace"Ina son mgana da kai domin ba zama nazo yi ba"

Da Sauri Mama tace"Mu shiga daga ciki Mana Alhaji"

Wani kallo ya watsa mata Lokaci d'aya yana fadin"Ba ni da wannan lokacin.Nazo ne Ishaq ya maimaita abunda zeey tace ya gayamata.."

Yafada yana bin su da wani kallo ni dai ina gefe ina kallon ikon Allah.

Ishaq ya sausauta murya yana fadin"Daddy da ka shigo ciki don Allah"

Cikin Tsawa yace"Ina da Lokacin shiga ciki ne ballatana naji shirmenka?nace ka maimaita abunda ka fad'amata so nake naji da kunnena"

Ishaq sai ya gyara Tsayuwa yana fadin"Daddy gaskiya na fada mata nace baan iya juran binta Abuja ba sai dai ta dawo nan mu zauna tare"

A wulakance yake kallonsa kafin ya nuna gidan cikin Yatsina yace" A wannan kejin gidan zata zo ku gamutsu da iyayanka da matarka..?

Yafad'a yana masa wani kallo lokaci daya yana kare ma gidan kallo a wulakance,Gabadaya su Mama sun daskare sun kasa mgana Yaya ishaq kuma sai ya sunkuyar dakai ya kasa mgana cikin kakkausan murya ya cigaba da fadin"Na ce a wannan a kurkin gidan kake tunanin y'ata ta bar komai nata ta dawo ta zauna dakai saboda kai ne autan maza ko?

Yaya Ishaq ya dago yana fadin"ammah Daddy.."

"Dakata min shashasha butulu a irin wannan gidan ka ganta ka aureta..?

Nace a irin wannan gidan ka ganta ka aureta da zakace hakkun Dole sai tazo ta zauna da kai a haka..?

Ya fada bayan ya katsesa,cikin Fusata da Bacin rai.

Ya nuna Zainab cikin Daga murya yana fadin"Lokacin da ka y'ta kace kana sonta acikin rayuwar hutu da jin Dadi ka ganta.cikin iliminta da tarin gata ka ganta kaji sha'awanta ka nemi auranta na aura maka ba domin ka chanchanta ba, sai domin nayi maka alfarma ina kallon ka kamar D'ana ashe baka da mutumci ban sani ba..?yar tawa kake so ka saka ka maidamin ita bazawara..?

Yaya Ishaq yace"ni ban ce zan saketa ba"Ya taresa da fadin"Ba ka ce ba kalaman ka me suke nuni..?kace in ta fita kada ta dawo..?so kake ta ijiye rayuwarta da Aikinta da komai nata tazo ta tare a wajen ka, to ka ba ta mene..?Kada kaa manta ko da ka ganta chan ta fara gudanar da rayuwarta bazata iya zama a ko'ina sai a inda ta saba.Bazan lamunci wannan rainin da iskancin ba,in ba ma kana Butulu ba an dauke maka nauyin ya'yanka na Dauke ma nauyin gida da zirga zirgan ai duk hakkin ka ne sannan na Dauke maka nauyi ita kanta Zainab din hakan ma baka gode ba kawai naka ka shiga mota ka rika zuwa kana dubasu ne zai zame maka matsala..?batulci zakamin ko kuwa zafin Talaucin ne yasa ka fara Nuna min akan ya'ta..?

Ya fad'a yana kallonsa cikin fusata,Sai wajen ya Dau shuru Mama bakinta yayi nauyi sai Anty Binta ta rika ma alama da tayi mgana itace tayi karfin Halin cewa"Alhaji ayi hakuri duk mganar bata kai haka ba a zauna a warwareta"

Ko kallo bata ishesa ba yace"Zan iya warware mganar ko wata iri ne ba sai na zauna ba,Kan ya'yana zan iya shari'a da ko waye na lura D'anku baisan  mutumci da Hallaci ba,duka abunda nayi mai bai gani ba in na barsa da Dawainiyar Zainab din zai iya Dauka ne..?to bai isa ba ku fadamasa bai isa ba.ba haka na aura masa yata ba kuma bai isa ya dawo min da ita haka ba, zan tafi da ya'ta kuma ya zama Wajibi ya janye kalamansa a kanta,Domin shima yasan hakan bazai taba yuyu ba ni ba sakaran Uba ba ne kan ya'yana sai nayi shari'a dakai wlh."

Abun mamaki Yaya Ishaq sai gashi ya kasa mgana Har da mama,Anty Binta ne ke bada Hakuri yace sai Ishaq ya janye kalamansa,Mama ta kallesa tana fadin"Kana ji ana mgana kana banza da mutane shashasha kawai"

Ransa bace yace"Na janye kalamai na"

Da sauri Mama tace"Ya janye Alhaji don Allah kayi hakuri Zainab kema ki yi hakuri don Allah"

Bai ko saurare su ba ya kalli yarsa yana fadin"Ina fadil.?

Sai ta juya tana neman Badariya ita ko daman tana dakin Mama tana ji ta fito da Sauri yako karbesa ko kunya yaja hannunsa yarsa ya dago yana kallon su Mama da suka yi Tsumu tsumu,Lokaci daya yana fadin"Zan tafi da y'ata zata kuma zauna ta jiraka.Hajiya ki gayamsaa duk bayan Sati biyu zai rika zuwa yana ganin matarsa da yarsa in kuma yaki jin mganata wlh tallahi zan saka Hukuma aciki saboda tun farko yasan Da Tsarin ya amince da haka sai yanzu zai sauya mganaa..?ina ruwan aikin Zainab da rashin aikinsa..?da zai wuce a kanta..?to zan kai kararsa bai isa ya tozartamin ya' ya zauna lafiya ba.in kuma bai ji mgana ba zan nuna masa waye lawal bako dan mutanen Adamawa"

Daga haka yaja hannun yarsa ita kuma ta dauki Jakarta suka fice Daga gidan,Sai aka rasa tsakanin Mama da Anty Binta ko Yaya Ishaq wanda zai motsa ni ko Allah ya kyauta nace araina na cigaba da duba dahuwar zobo na,Mama da ranta ya gama baci da Ishaq ta kallesa tana fadin"Ka kyauta ga abunda taurin kanka ya jawo ma ka nan, kaje in ya cire hannunsa a kanka sai ka duka ka Dauka."

Anty Binta tayi tsaki kafin tace"To me ma ya kawo mganar ta ijiye aikinta ta dawo nan ta zauna..?in ta Dawo kana da wajen da zaka ijiyeta ne..?

Sakarci kawai achan ya baku gida ya Dauki dawainiyar su Farhan da komai nasu ammh baka gode ba sai ka Tsiro da wata mgana Saboda kada a zauna lafiya.?

Idanuwansa jajir ya dago yana fadin"Don Allah ya isa.Ya isa nace.."

Mama ta saki baki tana kallonsa Anty Binta tace"To dake ni don na fada maka gaskiya Ishaq dake ni nace"

Gefe ya koma yana numfarfashi Kafin yace"Bazan dake ki ba ammh bazan fasa fad'a muku wannan ba gaskiya muka taka ba.Ta yaya wannan abun zai yuyu Mama duk bayan fa Sati Biyu ina naga kudin motar..?

Bude bakin Mama sai cewa tayi"Ba ga matarka nan na sana'a ba. tana da kudi sai ta rika baka Lokacin da kake da shi taci gajiyanka yanzu sai ta rama ma kura aniyarta"

Ina duke ne sai da na dago ina kallon mama tako zabgmin harara tana fadin"Munafuka ta saka shegen kurman kunnuwanta tana ji tana Dariya"

Sai na maida kaina kasa na cigaba da aikin Gabana shiko a fusace yace"Sai kawai saboda ina jani talau saboda zuwa na ganta sai na rika karban kudin mota wajen fa'iza wannan wani irin mutuwar zuciya ce?Haba Mama ki ma bar wannan mganar bazai yuyu ba wlh na jawo ma kaina bansan haka abun yake ba"

Yafada cikin kosawa Mama tace"Da auran Zainab din ka jawo ma kanka..?kada ka manta sun maka komai..?

A fusace ya katse Mama da fadin"Basu min komai ba Mama don Allah ki Daina fad'in haka me suka min.?da girma na ya ganni aikina Bashi ya nemamin ba,Auran yarsa da nayi nawa ya yafe min komai sai nayi Mama Dawainiyarta da yake mgana yaushe ya farayi..?ko da take aiki duk watan duniya 100+ nake tura mata nata da na Hidiman yara in adalci zan yi kudin zasu isheni..?nawa nake turo miki ke da Fa'iza da Dawaniyar yara sai kuma don yanzu Kaddara ta hau ni sai afini nuna iko Kan matata da ya'yana wannan wani irin kaddararran aure ne..?

Ya karishe fad'a kirjinsa na Dagawa alamun bacin rai ganin ya birkice yasa Mama ta fara lallabasa tana fadin"Taho mu shiga ciki"

Kin shiga yayi ya cigaba da fadin"Meyasa kuna ganin gaskiya bazaku bi bayanta ba.?In adalci zai yi bazai min uzuri ba..?ko bai san bani da aiki ba ne yanzu zaune nake nima lalurorina Dauke min su ake yi bai taba Duba Lokacin da nake wata biyu har uku a Abuja ya taba  ko sau d'aya ya yi min fad'a cewa na rika zuwa gida akai akai ina da wata matar da ya'ya..?bai taba ba yana jin dadin haka sai yanzu don kaddara ta fad'amin na rasa aikina sai yace Dole duk bayan sati biyu sai naje na Duba yarsa..?bazan iya ba Mama wlh bazan iya ba gwara na zauna anan ko banza ina ganin gilmawar ya'yana da mahaifiyata tare da Matata,achan kuwa ban ma ganta ba yaran kuma basa yini a gidan ni kad'ai kamar maye ina musu gadin gida.wlh ban taba jin abunda nake ma Fa'iza Laifi ba ne sai yau kuma na Tabbata Hakkinta ne ya fara Bibiyata, na Danne mata tarin hakkokinta daya rataya a wuyana, ko da sau daya ban taba duba hakan ba nasani akwai hakkinta dake Bibiyata na sani har da Hakkin Fa'iza Mama"

Ya karishe fad'a kamar zai yi kuka ban taba ganinsa cikin rauni haka ba inaji ajikina kallona yake yi ni kuma sai naki Dagowa sai ma na mike na Sauke tukunyar zobon na shige Daki Hawaye suna cika kwarmin idona.

Rana ta farko da Yaya Ishaq ya taba Furta ya zalunceni ashe yana sane da abunda yake aikatawa..?

Maganganun sa ya sanyaya ma su Mama jiki shi dai ina ji ya shuru takalmansa ya fice daga gidan, su mama kuma suka shige Daki jiki ba kwari.

Ranar gidan haka ya yini ba walwala nice ma na dinga zirga zirgan girki da Hada zobo har na gama abincin na zuba ma su mama na sakamai na kai Dakinsa bai shigo ba,yara suka Dawo makaranta kusan Lokaci da'ya suka shigo da Hafsah daman aiki aka basu taje kaiwa sai kuma na fara Damuwa da rashinsa suna ta tambayan ina Daada sun leka baya dakin mama haka ma baya Dakinsa sai nace musu ya fita.

Wasa wasa Yaya Ishaq bai shigo gidan nan ba sai Dare,kafafunsa Futufutu daga gani tafiyar kasa ya sha abunda yasa ya warware da ya dawo Jamal ya iske ya dawo shiyasa ya saki ransa.

Ruwan wanka ma Amir ya aiko yace wai Daada yace don Allah Umma ki saka mai ruwan wanka.

Sai ya bani Tausayi na tashi na saka mai na kai mai har Tiolet din dakinsa na aika Amir ya kirasa,sai da na baro  ya shiga wankan nazo na gyara Dakin da Matarsa ta gama bata sa ammh bata gyara ba,araina in naji kamar tausayinsa zai yi min tasiri a raina,sai nayi Saurin na kauce ma haka sai wata zuciyar tace saboda su Amir bazan bar Babansu a wulakance ba.

Koda ya fito dakin Tsab ya ganshi  ga abincinsa a gefe,sai ya zauna gefen katifarsa yana fadin"Anya ban yi wauta ba..?

Ko dai dai bakin Baba ne ya fara kamani..?.

Ya tuna Baba yasha fad'amai ya rike Fa'iza Amana in ya wulakantata bai yafe masa ba,sannan yana tausayamasa ranar dazai san amfaninta lokacin kuma tayi masa nisa..'

Tuna haka yasa yaji hankalinsa ya tashi bayan fitansa bai san ina ya nufa ba shi dai yasan yayi ta gagari a gari inda yaga masallaci ya tsaya yayi salla yasha a ruwa karon farko da ya tsaya ya fara Tunanin kuskuran da ya tafka a rayuwarsa tun farkon auransa da Fa'iza har zuwa yau..?sai a yau yake jin tabbas zai iya yuyuwa girman hakkin Fa'iza ko Bakin Baba ne sune suka yi Zaren Dabaibayi suka fara taba Rayuwarsa. lalle ko in hakane ya zama Dole ya fara gyara mu'alamansa da Fa'iza ya roketa ta yafe masa kila Furucin Baba zai sake sa.

Yana cin abinci hawaye sun cika kwarmin idanuwansa Ya tuna burinsa na auran Zainab da ra'ayinsa sai gashi Burinsa bai masa komai ba, yau ta kawo Fa'izan da ya raina ya hantara ya wukalanta itace komai nasa ta dauki laluransa har da ta kannensa da ta mama daman Laluran ya'yansa tun yana da aikinsa ya bar ma Fa'iza ragamar komai kaicon sa"

Cokalin hannunsa ya sauke abincin kamar yana cin mgani kansa ya Dafe dake juyamin cikin Fitan Hayyaci yace"Innalillahi yanzu ya zan yi..?ta wata Hanya zan gyara kuskurena..?duk da tarin laifukana a wajen Fa'iza zata iya duba na ta yafe min..?

Tuna haka yasa yaji hawaye masu duni sun zubo masa yayi wauta rud'in duniya da Irin Tarbiyan Mama sun kai shi sun rabo duniya da mutanen cikinta sun saka ya hau keken bera ta kaisa tsakiyar kasuwar nadama ta gungurar da shi me Fa'iza tayi masa da ta chanchanci Tozarcin da ya shafe shekaru yana yi mata..?

Da wani ido zai kalleta sannan da wani yare ko harshe zai fara bata Hakuri ta sauraresa..?Anya Lokaci bai kure masa ba kuwa..?




*12/07/2023*

*8:00pm*

*Janafty*

[7/12, 10:17 PM] +234 906 320 7298: *KNKB2007*


*Ki biya ki karanta cikin salama,Kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta min littafi,Sannan kada ki yad'amin shi,Pay N500 regular ko kuma VIP N1000, Via Jamila Umar Gt bank 0552179550,ban da tsarin kati wannan karon, a turo ta POS, Shaidar biya ta wannan lambar 09069067488*


Gabad'aya sai yaji abincin da yake ci ya koma masa mad'aci sai ya ture komai kawai ya koma ya kwanta rigingine,idanuwansa na kallon rufin dakin Lokaci d'aya rabin jikinsa da kafafunsa suna kasa ne daga kasan katifar.

tunani ya farayi tunda ga zaman Fa'iza a gidansu har zuwa Had'a auran su da Baba ya yi shi da Hajiyar Karofi abubuwan da suka faru,Zaman auren su da Fa'iza yadda ya tafiyar da ita da kyara hattara tozarci da cin mutumci,sai ya koma yana tambayan kansa me ye illah Fa'iza da ya tsaneta..?ko miye laifinta da yaki karb'anta a matsayin matarsa meyasa bai darajata ya karb'eta ya daidaita sahun ta da matan maza nagari masu takwallali da sanin ya kamata ba.?Sai yaga bata da wani laifi Fa'iza mai Hakuri ce Fa'iza mai biyayya ce Fa'iza mace tagari ce, burin kowani Namijin kwarai zamowarta baka ko mara kyan fuska wani abu ne na bangaran Halitta in da ya jata ajiki ya sota ya tattaleta ya tattali lafiyanta da jikinta sai Fa'iza ta Daukemin Tunanin kowata mace duniya. sai bai yi ba yayi fatali da Umarnin Allah ya toshe kunnensa da furucin Baba a kansa ya zauna da Fa'iza cikin Takura iko,Umarni da Bauta cikin Tozarci da cin mutumci har da wulakanci ya tuna yadda yake barinta da wahala kan cikinsa da kuma ya'yan da shine Silan fitowarsu duniya.

Ya tuna yadda ya kwallafa rai wajen ganin ya samu cikar Burinsa na auran mace mai kyau da gata da ilimi da nasaba, bai taba rokan zabin Allah ba shi dai kawai ya auri mace mai wadanan abubuwan sai Kuma ya basa,Domin ya jarraba imaninsa ya kuma sa ta haifa masa ya'ya daidai da Zabinsa sai kuma ya nuna masa ikonsa tunda ya auri zainab ba ga wani abu na armashi a auran shi da ita ba,sai dai eh! ya cika burinsa na auran mace mai kyau da nasaba ammh ba mutumci aciki ba ganin Darajan juna kamar yadda yake ganin yayi ma Fa'iza alfarma haka Zainab da Ahalinta suke ganin sun masa alfarma ya tuna yadda yake yi ma Fa'iza iko akan komai hatta akan ya'yan data Haifa ya tuna ya rabata da Danginta da yan'uwanta duk bata taba dagaa kai ba ,ya mu'amalanci yan'uwanta ta mummunan siga ba ta taba d'aga kanta ba,sai ya tuna Zainab gabadaya rayuwar auran su Mahaifinta ke jan ragamar shi sai abunda yace da shi Zainab take amfani in kuma yace a'a shi din banza bazata taba yin wani abu batare da cewar mahaifinta ba ko sanin ba,kan ya'yansa ma iko yake nuna mai babu shakuwa ta uba da ya'yansa tsakaninsa da su Fadil suna gidan iyayanta sai an ga dama ake kawosu ya gansu ko da yana garin in yayi mgana sai Zainab tace Daddy yace wajen sa zasu zauna gidan ba kowa Zuzu bata nan,A komai shi ke da ta cewa shi ya zama Hoto,yana Tuna sanda yake da kudi Fa'iza bata dora komai daga samunsa ba,ammh yau gashi ya rasa komai na shi biyar ma sha'awa take basa ta zauna da shi ahaka tana kuma Dauke da Laluransa ita wacce yake ganin ta fita ta kuma yi daidai da shi ta gujesa saboda bai dashi,bazata iya baro aikinta tazo ta zauna da shi ba sai dai shi ya bita,ta nuna mai daman ba sonsa take yi ba. Ta aure sa ne saboda kyansa da wani kyalkyalin duniya kamar yadda shima ya gina nasa auran ashe ba'ayi ma Allah Wayau..?

Ishaq yana da taurin zuciyar da ko abu ya damesa ba dai kaga kukan sa ba.ko mutuwa akayi sai dai yayi kukansa a boye ammh sai ga shi kwance Hawaye suna sauka ta gefen kunnuwansa duka biyu,suna jika zanin gadon dake jikin katifarsa zuciyarsa ta yi wani irin nauyi kamar ana yi mai wahayi haka abubuwan daya aikata suka rika dawomai Daki daki acikin kasan ransa fad'i yake yi"Allah na tuba. Allah na tuba ka yafemin"

Kansa yake girgizawa yana ji a ransa in ma Fa'iza bata yafe masa ba, bazai ga laifinta ba ammh baya raba d'ayan Biyu duk bala'in dake bibiyansa akwai Hakkinta,ya tuna sanda ya wulakan ta Mariya da kalaman data furta masa alokacin, ya tuna ta fadamai ko ba Hakkin Fa'iza ba,sai hakkin Zumunci ya tambayesa watarana. Ga shi tun ba'aje ko'ina ba ya fara gani rana tsaka aka samu saka Hannun Fidda makudan kudad'e bai san hawa ba bai san sauka ba,ya shiga matsala karshe bayan ya rasa aikinsa sai da ya rasa duk abunda ya mallaka Allah ya barsa da ransa ne saboda ya gane kuskusransa in da yaso gidan yari za'a kaisa ya kare rayuwarsa a banza.

 Sai hankalinsa ya dawo jikinsa ya tuna ko abokansa yanzu da suka san ba shi da aiki sun gujesa tunda bai da shi bazai iya ma kansa komai ba ballatana su.hatta abokan aikinsa nachan Abuja bamai kiransa sun ma fara mantawa da shi, daman haka Duniya ta gada in yau mune to gobe fa wasun mu ne.

Bai taba daukan furucin Baba a matsayin wani bakar sarka mai wuyar warwaruwa a garesa ba,ya dauka tunda bai saki Fa'iza ba ya fita daga Furucin sa abunda bai sani ba Shi Furucin iyaye kan ya'yan su yana tasiri har mutuwar su Baba ya bashi Amanar Fa'iza sannan ya kakkausa mgana kan in ya wulakantata bai yafe masa ba shi ko adadin sau nawa ya wulakanta Fa'iza bazai iya sani ba..?

Zumbur ya mike kamar an tsikare shi da ya Tuna da shirmen da ya tafka na Jingine auran sa da Fa'iza tun kafin ya auri Zainab bazai manta ba tun a wannan Lokaci wani abu na auratayya bai kara shiga tsakanin su ba,Shekaru Biyar kenan Innalillahi ina zai kai girman hakkin Fa'iza daya Dauka..?bai taba Tunanin ita ma Mutum bace mai lafiya..?bai taba Tunanin zata shiga masifa da bala'i saboda jinginarsa ba..? Ya tuna Zainab macece mai yawan bukata har tama fisa shi wani lokacin,yana da Hakuri wani Lokaci ammh ita bata da Hakuri ta wannan Fanni shiyasa bazata yarda ya yi wata D'aya bai je ya ganta ba. Mahaifinta yasan zata cutu shiyasa ya Tsaya mata Ita Fa'iza wa take da shi da zata kai masa kukan ta ya tsaya mata..?

 Sai kamar ana gayamasa da kansa yace"Allah.."

Shi ya tsaya mata"

Hannayensa duka biyu ya saka ya Tallafe fuskarsa yana jin kamar ya fashe da kuka,Sai dai duk abunda ya faru da gudummuwar Mama yasan ita din uwa ce garesa da bai da kamarta ammh ta bada gudummuwa wajen kara karkatar da Rayuwarsa zuwa hawa kan keken bera in da tana ankar da shi ko in yayi ba daidai ba ta yi masa Fad'a da bai kai haka Lalacewa ba.Sai ya tuna Baba lokacin yana gabda rasuwa yake mai fad'an ya zama adali sannan magidanci mai kyautata ma iyalansa,Kada ya biye ma Mahaifiyarsa wajen kuntata ma Fa'iza kada ya manta marainiya ce bata da kowa kada ya wulakantata domin mace ce tagari ce in ya rasata ba lalle ya samu mace kamarta ba.

Kamar karamin yaro haka ya dinga rera kuka yana fadin"Ka yafe min Baba..Ka yafe min Baba na Tafka kuskure ka yafe min"

Shi kad'ai haka ya dinga sambatu  Daran nan barcin sa rabi da Rabi ne da asuba Dakyar ya iya tashi fuska da Idanuwansa sun kumbura saboda Damuwa da suka dawo masallaci sai da Jamal ya tambayesa ko zazzabin ne.? yace ya warware saboda Mama ta sanar da shi lokacin da yayi rashin lafiya.

Daki ya sake komawa ya kwanta yana Sake saken yadda zai fara gyara mu'amalan sa da Fa'iza sai dai ba shi da wannan kwarin gwiwa yana tunanin bama ita ba ko waye yaji abunda ya faru zai yi tunanin Saboda yanzu ba shi da shi ne yaga amfani Fa'iza ammh har ga Allah daga daran jiya zuwa wayewar gari zuciyarsa ta cika da Fa'iza sunanta alherinta,Sanyin ta,Ladabinta da Hakurinta kaunar ta Kunyar ta,had'e da nauyinta sun hade masa waje d'aya sun ki barinsa yayi wani sukuni tunda ya dawo masallaci bai bari sun hadu ba ya shigo Daki,Wajen Mama kadai ya leka suka gaisa.

Gani yayi har bakwai ta gota kuma yaji hayaniyar yara afalo suna ta shirin Tafiya Makaranta,Sai ya mike Dakyar yana rawan jiki ya kwashi kular abincin jiya da ta kawo mai da Kofin ruwa,ya fito falo ya iskeni ina Ta fama da Musty wajen saka masa Rigar makaranta Hafsah  Lahadi ne tana gida ita ke Kitchen ta na yi musu abun kari Amir ya shirya tuni shi yake taimaka wajen shirya Ahmad Anum kuma ta shiga Daki neman Hijabinta bata gani ba ,Dagani har yaran Hankalin mu yayi gaba bamu san fitowarsa ba sai da Anum ta fito daga Dakin su tana ganinsa ta bude murya tana fadin"Daada ina kwana"

Muryanta yasa duk muka Dago muna kallonsa Amir ma ya saki Ahmad yana gaida shi ya amsa yana ta sakin fuska kamar an saka shi Dole sau daya na kallesa na kauda kai na,Musty na saki ina fadin"kullum kai ne rigimamme ko Ahmad ya daina rigima ammh kai babban kwabo baka daina ba"

Ina shirin nace Amir ya karbi kayan hannunsa sai naga yaje ya karba ya wuce kitchen shi kuma ya kariso falon yana fadin"Musty na ne Umma ke ce ma Babban kwabo..?

Ya fada yana daukan sa,Ahmad na ganin haka shima ya fara zillo sai ya koma ya zauna yana fadin"To karfin Daada kuma ya kare"

Duka suka hayesa ya dauke su yana Nishi suna Dariya ni kuma sai na Duka ina kwashe kayan da suka cire ina shirin gaishe shi Saboda na Dauka zan gansa cikin wani yanayi sai naga ya ware kamar jiya baya cikin Damuwa ba zato kawai naji muryansa yana fadin"Ina kwana Fa'iza.."

Dankari makari mamaki ya cikani sai naji kamar ban ji daidai ba,na juyo ina kallonsa kai tsaye ya sake fadin"mun tashi lafiya ya kwanan yara..?

Yadda ya kafeni da ido ne yasa bakina na rawa nace"la.lafiya ina kwana"

Da Sauri na wuce dakin yaran har ina cin Tuntube wajen waigensu to Allah na Tuba abun ne naji sa wani bambaramkwai namiji da suna Hajara ban gama mamaki ba sai da naga Hafsah ta zubo musu taliyar data dafa musu ya zauna kasa a cikin su yana bama Ahmad da Musty a baki in Anum ta bude sai ya saka mata Amir kuma sai yace"Daada kai ma bude baki na baka"

Sai ko ya bude baki ya basa,mamaki ya sandar dani wani abu ne da ban taba gani ba ko a baya,zai dai dauke su yayi musu wasa ammh wahalar su kan bai sani ai abun mamaki na gaba sai da suka gama,Shi ya tarkata su yace zai kai su har makaranta,Saboda Halin Rayuwa yaran ma sun koyi hakuri ba kullum suke tafiya da abinci ba watarana ruwa ne sai ranar da na samu ciniki sosai har da Lemu ina siyan musu, yau ma nayi niyya ganin shi zai kai su sai na bashi naira Dubu nace ya siya ma kowannen su Lemu da biskit.

Bai yi min gaddama ba ya karba yana fadin"Ni kar na siya ma kaina Umma?

Sabon salon nasa ne ya girmeni sai na wuce kitchen ina fadin"Kaima ka siya"

To fadan da yafi karfinka ai sai ka maida shi wasa,ina cin abinci ya shigo nayi mai sannu da zuwa na bude baki na ce abincin nasa na Dakinsa sai kawai naga ya tankwashe kafa a gabana ya zauna ya tsoma min hannu acikin Farantin da muke ciki ni da Hafsah ta tashi taje ta Dauko mana Ruwa ne.

Baki na saki hade da Hanci ina kallonsa shiko ko ajikinsa Hankalinsa kwance ya fara ci a baya nasan Halin Fafansa,Ko abinci ban taba gani yaci da Hannu ba, sai da cokali ammh yau da Hannu yake ci har yana sude hannu,ganin haka yasa na tsame hannuna zan yi mgana yayi saurin tare ni da fadin"ki ci mana Fa'iza. ko baki son ci da ni ne.?

Kai na girgiza ina fadin"Aa tare da Hafsah muke ci"

Kafin yayi mgana ta fito Dauke da Ruwa itama ina gani ta saki baki taga bakon abu,yana ganinta ya Dago yana fadin"kin ji Hafsah jeki zubo naki kici ki barni na samu Ladan cin abinci da Matata yau"

Kalmar Matata din ne na rika nanatawa kaina ya yi wani dum sai ya kasa Dauka duk da yaso na sake naci abinci da shi,sai na kasa saboda abu ne da ban saba gani ba.

Kai ranar naga abu ni Fa'iza Shigowar Jamal ya ceceni suka zauna afalo suna Hira ammh Fita goma shiga goma in na dago idonsa na kaina mamakinssa ya cikani kamar wamda yayi gamo..?

Ashe wasa farin girki tundaga ranar Yaya Ishaq ya sauya daga Ishaq din da na sani ya koma wani mai sanyi mai kula mai tallali,yanzu ya daina zama in dai yana gidan komai zan yi sai ya taimakamin yara ko da nayi musu wanka shi zai shirya su ya basu abinci ya kuma kai su makaranta,Ko gyaran Daki nake yi sai yazo ya amsa ko ya fara tayani tun yana bani mamaki har yazo ya daina bani.

Sai wani kafa kafa yake yi dani wanda sam wannan Sabon dabi'an nashi bai burgeni ba domin nafi sabawa da wanchan Ishaq din,Ranar kwana Biyu Tsakani na fito da wankin yara kawai shima ya fito yace zai tayani jikina ya fara rawa kada Mama ta fito ta gan shi na shiga uku.na fara Hada sa da Allah ya bari yace bazai bari ba, sai kawai na sakin masa wankin na koma gefe ina kallon sa.

Ganin haka yasa sai jikinsa yayi sanyi ya ciro hannuwansa a ruwa yazo kusa dani yana fadin"To na bari shikenan..?

Ajitar rai na sauke ina fadin"Kana so ka jamin fad'an Mama ne in ta fito ta ganka kana wanki..?

Na fada cikin fargaba har ga Allah yanzu ina gudun abunda zai sa a tozartani.

Sai kawai ya koma ta bayana bakinsa gabda kunnena yana fadin"Ina ruwan Mama don ishaq ya taya Fa'iza wankin kayan ya'yan su"

Jikina ya fara rawa nayi gefe ina Haki,sai ya bini da Dariya kafin ya shige Daki ya juyo yana fadin"Yau ba zobo ne da kunin aya kuma..?

Ina zama kan kujeran tsugunno nace"akwai sai na gama zan Dafa kunin Aya kuma sai Hafsah ta Dawo"

Ni dai har na gama wankin nan Ina auna wasu abubuwan a fili na furta"kamar wanda akayi ma wahayi'"

Jamal Sati daya yayi mana ya koma makaranta, ni na basa kudin mota,da na kashewa Anty Binta ta hadamai yan kayan abinci,Ya tattara ya koma makaranta yanzu kam ina samun ciniki sosai,Har ta Badariya ni nake bata na mota da na laluran makaranta,Da dawaniyarmu na yau da kullum ba domin sana'ar na ba da Tuni asirin mu ya tonu.

Yanzu in ina aikin Zobo haka Yaya Ishaq zai fito yace sai ya tayani ko nace ya bari bazai bari ba.sai na basa wani aikin zai kyaleni,sannan yanzu ya samu wata banzar Dabi'a ya rika shigemin yana so mu rika hada jiki da juna to banzan dabi'a mana yaushe jikina ya zama abun sha'awa a wajen sa da zai zo ya na rab'ata,da na ga haka sai na rika kauce masa ammh sai naga kamar bai Damu ba sai ya nuna kamar bai gane ba,yanzu ko Hafsah bata nan yana tayani zuba zobon a gorina ko ya wanke min Aya Mama dai bata taba gani ba sai ranar aiko tayi ta fad'a daga karshe ta fashe da kuka tana fadin"Shikenan Fa'iza kin asircemin D'a ya zama bawanki.Allah ya isa tsakanina da Dangin Sidi da tamadina sai mun yi shari'a da su ranar gobe kiyama"

Raina ya baci saboda ta kira iyayena a Kabarin su sai na kallesa Idanuwana sun ciko da kwallah ina fadin"Kagani ko sai da nace ka bari.nasan Halin Mama ga shi yanzu ka janyo ma iyayena Zagi suna kwance a kabarin su"

Ba zato kawai naji ya mike ya rikoni ban tsinci kaina a ko'ina ba,sai akam kirjinsa ya Rumgume ni dukkan mu sai da mukaji wani abu kamar wuta ya jamu Mama daman tana gama fadin mganarta ta shige daki tana cin mutumcina,Tuni naji na gigice na fita Hayyacina,da gaggawa na turesa na fizge jikina ina numfarfashi sai naji abun yazo min kamar daga sama wai Yaya Ishaq ni ya Rumgume..?

Hawaye suka zubo bisa kumatuna sai ya miko hamnu zai share min,na matsa baya ina fadin"Me ye haka..?

Bai damu ba,sai yayi mirmishi yana fadin"Hawayen da na yi sanadiyar fitar su zan goge miki"

Wlh sai mganarsa ta bani dariya,har sai da na dara ganin ina dariya sai shima,ya biyemin yana Dariya ni ko baisan shi nake yi ma Dariya ba Sabon acting din nasa ne naga bai Dace da shi ba.

Acikin Satin sai ga Hajiyar Dala tun da muka yi Hijara bata taba zuwa ba har muna neman wattani shida Mama ta jata Daki ana ta Labarai,duk yadda suke da Mama bata kwana ba,Sai yatsina take yi,Ta shiga har Dakina ta gani duka sai wani yamutsan fuska take yi,ishaq na gida ta kallesa tana fadin"Shikenan Ishaq ka dawo zaman gidan aiki dai shuru..?

Yana zaune kan kujera yace"Wlh Goggo a cigaba da tayamu da addu'a"

Mama na daga gefe ita ta rakota ta tabe baki tana fadin"Ba shiyasa nake masa fad'a bai ji ba,Mahaifin zainab wlh tsab zai sake nema masa aiki ammh ya Tsaya yana shiririta ko da yake an mallakesa ya zama mai Duran zobo da kunin Aya"

Hajiyar Dala tace"ke ko ta ga yana gida sai zaman kashe wando mana. Ya koma chan Abuja ya zauna nan din ai kina nan sai kiga in ana ganin idonsa an fi saurin sama masa aiki"

Mama tace"Gayamai kila yaji ki"

Hajiyar Dala ta wuce tana fadin"Ishaq kayi ma kanka fada dai"

Daga haka ta fice Mama tabi bayanta shine naga ya Damu ammh ni ko agefen gyalena guga daman suka tarar ina yi sai na zama kurma na nuna musu kamar ban ji su ba,shine bayan fitar su ya zabga tagumi.

Na zata wani abun arzikin Hajiyar Dalan ta kawo maman,ashe kwalin Taliya da macaroni ne sai kudi da ta bata naji tana fada ma D'anta,Tundaga Lokacin sai na daina Bashi Fuska,da ya fito zai karbeni aiki zan yi tuku tuku da rai sai jikinsa yayi sanyi shi da yaransa dai sai son barka ya maida kansa kamar wani kaninsu, ya Lura sun fi shakuwa dani fiye da shi,sai yake neman shima su fara wannan Shakuwar da shi ni baisan adadin Shekarun da na kwashe ina bama ya'yana Lokaci ba ne.

Alhamdulillah da duka ni'imarsa gareni Domin kasuwar Turarukaa sun bud'emin Sanadin Turaren da Hajiya ta saka na hada ma Diyar kawarta Laila ta Kaduna,sai mutane suka rika gani suna suna yaba kamshi ina ta samun ciniki ba abunda zan ce ma Hajiya sai godiya ta aikomin da kayan sawa ni da yara na dauka Gogan zai yi fada sai naga har da shi ake duba kayan ana murna,na kirata nayi mata Godiyan kayan da kuma Godiyan Yayan mijin Laila da sanadin laila taga Turaruka na,suka burgeta ta aiko na had'a mata na Dubu hamsin kwallacha da Humra,kuma na samu alheri sosai da ita naji dadi ko da yaushe in nayi sallah sai nayi ma Allah Godiya sannan na gode ma Hajiya tare da wadanda suka yi sanadiyar tsayuwana da kafafuwana.

Ishaq ya kafe bazai rika bin Zainab Abuja ba,mama ta kasa tankwasa shi ga shi mahaifin zainab ya kara kiran mama yayi mata gargadi mgana har Yamai sai ga kanin Mama da kanwarta Hure sun zo shi ya yi ta ma Ishaq Fad'a akan meyasa zai bijire ma mganar Mahaifiyarsa Dalilin daya sa ya yarda zai je kenan ammh sai yace bashi da na mota kamar Dole aka Turo mota tundaga Abuja tazo ta Daukesa.

Ina Daki ina gyara kayan Dirowa ya shigo da Jaka a hannunsa daman tunda naga zuwan su kawun yamai nasan za'a rina.

Kusa dani ya zauna ni kuma sai na zame na sauka kasa bai damu ba yace"Zan tafi Abuja fa'iza"

Kai Tsaye yaji nace"Allah ya kiyaye hanya a gaida zainab da yaran"

Sai yayi shuru ya kasa mgana ni kuma bana son muna kebewa a daki mu kadai sai na dakatar da abunda nake yi na mike zan fita karaf ya riko Hannuna.

Sai naji wani iri na ratsani na juyo da Sauri ina kokarin kwace hannuna sai ga shi ya mike gabda ni yana fadin"Ki kula da gida da yara"

Ina kwace Hannuna da ga rikonsa nace"In dai wannan nan ba sai ka bar min Sallahu ba kaima kasan aikina ne"

Ina shirin fita ya kira sunana ina Juyowa,har ga Allah bansan ya taso ba sai ji nayi ya sakar min sumba a kumatuna na gefen dama Lokaci d'aya yana fadin"Fa'izan Ishaq ki kulan min da kanki"

Har ya fice ina binsa da kallo Gabadaya sai da gabban jikina suka yi sanyi zuciya bata da kashi,sai ga shi na yini ina tuna yanayin da na shiga da ya sumbaceni sai da wata Zuciya ta ankar da ni da fadin"A kul din ki Fa'iza ki tsaya iya matsayin ki"

Sai nayi kokari na yakice wannan Tunanin Lokacin Hafsah taje korafi ta kwana Biyu sai ni kadai sai yara suma sun ji ba Dadi da baya nan Anty Hure kuma ta nan tare damu Badariya yanzu tafi zama gidan Anty Binta.

Azumi ke gabato mu ina ta kokarin na siya kayan zobo da kunin aya masu yawa tunda nasan in Allah ya Budamin zan samu ciniki sosai a raina na guduri niyar ba Jamal ba Har Yaya Ishaq sai nayi ma kayan sallah ko guda D'ai d'ai ne ya'ya na ko sai na gwangwaje su da ikon Allah.

Yaya Ishaq sai da yafi sati uku sannan ya Dawo,Namiji kenanbyana baya son zuwa sai gashi ya shantake har da kiba yayi,Sai da ya dawo yana min dadin bakin cewa mganar neman aikinsa ce ta taso shi shiyasa ya tsaya,ni ko bi ta kansa ban yi ba,tunda ba sabon abu ba ne, Ba laifi wannan karon yazo da kudi har ya siya mana kayan abinci,ya rage rabin kudin makarantan yara daman na biya musu rabi sai ya cikasa.

Watan azumin Ramadana yazo,ba laifi albarcin watan alfarma mun samu tallafi Goggo ta aiko mana da Buhun shinkafa da taliya da su garin Danwake garin kuni,taliya yar murji,Ni kuma da abun da nake da shi na shiga kasuwa nayi mana kananun Cefane Mijin Anty Binta ma ya bamu gero da shinkafa da siga,Bamu da matsalan abinci a lokacin sai godiyar Allah, Anty Asiya ta aiko min da yaji da kori da Shadda na Ahmad kala biyu,Ganin mun samu rufin asiri bangaran abinci sai na maida hankali ga sana'ata da azumi na chab'a ciniki sosai Hafsah ke taimakamin tare da yara saboda basa makaranta da azumi.

Da kudin ciniki da na tara na azumi. na siyan mana kayan sallah da ni da yara nayi ma Hafsah kala da'ya da ita da Badariya na yi ma Jamal shadda shi da yara sai kuma Yaya Ishaq na siya masa nasa shi kad:ai daga gidan Hajiya aka aiko mana da Naman sa mai yawa ana gobe salla da Sakon kudi dubu Hamsin muyi Hidiman Salla kamar nayi kuka ni da ya'yana mun zama abun son mutane ban tsinke ba sai da Raliya ta kawo kaya masu kyau na mata na Anum in ji Laila Daga kaduna.

Sai ga Mama bakinta Gum ba karofi Tunda taga an rufa asiri har da ita ake cin arzikin,Anty Hure ma tana nan a wajen mu tayi azumi har ta zobo da kunin aya suna sha har suyi kyauta dashi, daga karshe ce min tayi zan koya mata,tana so ta siya komai anan in taje chan ta gwada nace mata toh.

Ana gobe sallah na ba ma Mama kayan sallarta da Jamal har Anty Hure nayi ma Turmi,Mama ta karba a reni ko saka albarka bata yi ba,Jamal har daki ya biyoni yana godiya Yaya ishaq bayan ya gama ganin nasu Mama da yara bayan ya shiga daki na Dauko nasa na bashi duka an dinka,Hafsah ta ba wani dan ajin su yana dinkin maza ya dinka musu,suna mutumci da mai dinkin ne.

Sai kawai Ya rumgumeni yana fadin"Nagode Fa'iza Nagode kwarai. Madallah da Fa"iza..Fa'iza matar Ishaq"

Da wayau na zame jikina daman ina so nayi mai mgana kan Zainab Saboda ina jinsu tana ta kiransa baya son daukan wayarta, kan mganar zuwansa da azumi bai je ba Mama kuma tamai mgana bazai saurareta ba.

 Sai nayi amfani da wannan damar na sako mai mganar shuru yayi yana kallona kafin yace"kina so naje da sallah ne ke kuma fa da ya'yana..?

Sai na jinjina kai ina fadin"itama ai matarkace tana da hakki akan ka, sannan itama tana da ya'ya suma kuma suna da hakki a kan ka"

Kawai sai ya kuramin ido yana kallona kafin ya kama hannayena duka biyu ya rike lokaci daya yana fadin"Wata irin zuciya Allah ya yi ma Fa'iza..?

Sai nayi mirmishi kai tsaye nace"Zuciyar hakuri da Takwali ne"

Sai ya girgiza kai yana fadin"Da kuma zuciyar  Diomod wanda samun mai macen aure irinta acikin maza dubu sai mai sa'a Fa'iza"

Sunkuyar da kaina nayi ina jin jikina na yam yam! saboda yadda yake murza yan yatsuna,sai kawai naji Tattausan muryansa gabda kunnina yana fadin"Zuciyar Fa'iza me hakuri ce zuciyar Fa'iza mai biyayya ce da yafiya Allah yasa zata iya yafe ma Ishaq gigimemen laifin sa a gareta?

Dagowa nayi ina kallonsa muka yi ma juna kir,kallo ne yake min cikin wani yanayi dake kassara zuciyar ko wata lafiyayyar diya macen da aka zaunar da ita, ana yi mata irin wannan kallon da Ishaq Kabir karofi ke bi na dashi"








*Janafty*



*KNKB2008*


*Ki biya ki karanta cikin salama,Kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta min littafi,Sannan kada ki yad'amin shi,Pay N500 regular ko kuma VIP N1000, Via Jamila Umar Gt bank 0552179550,ban da tsarin kati wannan karon, a turo ta POS, Shaidar biya ta wannan lambar 09069067488*


Ba iya kallon dake narkar da zuciya ba,Sai da ya had'a da langon Matso da jikinsa yana gogan jikina lokaci d'aya da Numfashinsa yana sauka a dokin wuyana,sai suka taimaka wajen fitar dani daga Hayyacina har ina shirin manta matsayina?ballatana da naji yadda hannayensa ke kara kaina acikin Hannayena.

Ban dawo Hayyacina ba sai naji mganarsa a dokin wuyana gabda da bakina yana fadin"Fa'iza zaki iya yafe ma Ishaq.?zaki iya basa rayuwarki a karo na biyu..?

Kamar an dawo dani cikin Hayyacina haka na zabura na mike jikina na rawa,yana shirin riko ni na fizge hannuna na fice daga Dakin da Sauri zuwa Dakina,bai biyo ni ba ina tunanin Saboda ganin yara ne,ni ko gado na na fada ina kokarin daidaita kaina Sai kuma daga baya naga wautata na manta matsayina ne da zai rudeni na saki jiki..?

Meyasa sai yanzu yake tunanin yayi min laifi yake neman gafarata..?

Ko ya manta nice dai Fa'izan da ya sani yar gargajiya kurma mara ilimi da gata baka mummuna ko ya manta wad'anan nakasun a tare da ni ne..?

Sai naji bana son na fita mu kara haduwa,Na shige daki duk hayaniyar yara da buruntun su naki fitowa ina jin su afalo yana ta sha'aninsa da yara da Hafsah sai washegari Ranar idi muka had'u shima gaishe shi kawai nayi sai ya amsa yana wani kafe ni da ido nayi saurin kauce ma kallonsa.

Da shi da yaran suka shirya gabadaya har da Jamal,sai a ranar naga ya Dawo da gayunsa sai dai ba kamar da ba,da zasu tafi masallaci muna tsakar gida muna tuwon Shinkafa miyar agushi ni da Hafsah ban sani ba naji ya karkato wajen kunnena yana fadin"Ishaq na jiran wankan sallar Fa'iza domin ya tanadar mata babban Tukwaici"

Sai na tsorata garin juyowa saura kad'an na fada tukunyar miya ya saka Hannu ya tareni yana fadin"Ki kula da kada ki yi min asara"

Sai na sunkuyar da kai ganin Hafsah na Dariya sai ya bi bayan su jamal yama Fadin"Hafsty ki kular min da matata kada ta fada cikin miya ta ragemin kara'in da na shirya mana da sallar nan"

Har ya fice ina kara jinjina mamakinsa,Hafsah ma ta kalleni tana fadin"Naji dadi Yaya fa'iza yaya Ishaq ya sauya kamar ba shi ba"

Saboda bana cikin yanayin mgana yasa ko tankata ban yi ba.

Ba su jima da fita ba muka gama komai ni na wanke tsarkar gida Hafsah tayi wanke wanke,Ni nace taje tayi wanka na fara gyaran Dakin data gama ta shirya sai tazo ta karbeni itama Goggo ta aiko mata da kayan salla na kala Biyu.

Ba domin ya roka ba sai domin daman nayi ra'ayin cin kwalliyata da gumina sai na saka wata karamar super waz din da na siya ta Dubu Goma sha biyu,mai kalan ja da fari dinkin riga da zani ne ammh rigar fited ce ta kama jikina Dam na saka Sabbin Dan kunne da sakarna da abun Hamnu,Ban yi kitso ba sai dai na wanke kaina na tufke Hafsah ce zata min kitso kuma bata samu damar min ba, saboda layin yan lalli taje karofi tayi gabda sallah ta dawo wajena Anum kad'ai tayi ma kitso,ni kuma aiki yayi min yawa ballatana daman ni ba yar kwalliya bace.

Ko kafin su dawo na aika ma da Mama nata tuwon da naman salla sannan zobo na musamman nayi saboda gida da sallah,Na kuma shiga da kaina har daki na gaishe su nayi musu barka da sallah Anty Hure ta amsani da fara'a Maama ko sama sama tana kallona tana tabe baki ban damu ba,na fita ko ba soso da sabulu sannan na sauke nauyi.

 Suna dawowa suma abincin na kasa musu suka ci,shi ko sabon mijin nawa sai kallona yake yi,to sabon mijina mana Tunda komai ya sauya,ashe ban sani ba Hoto ya dinga Daukana sai da naji Anum na fadin"Laa Umma zo ki ganki a wayar Daada"

Sai na juya ina kallonsa sai ya basar yana dagamin gira jijjiga kaina nayi a raina ina tambayan kaina wannan chanjin duk na menene..?

Duk yadda yaso ya samu kebewa dani naki basa daman hakan,washegarin sallah da kwana Biyu na samu ya tafi Abuja kudin mota ma ni na bashi ya tafi bayan ya jaddamin in ya dawo yana so zamu yi mgana nace Allah ya Dawo da shi lafiya.

Ya bamu izinin tafiya yawon sallah Shiyasa ban zauna a gidan ba, muka sha yawo ni da yara da Hafsah har gidan Anty mahma mun je da gidan Hajiya,na leka har anguwan da muka taso mun yi zumumci da makotan arziki su Sa'adatu yini zir mukayi sannan muka dawo ita kuma Mama tana gida ita da ya'yanta su Anty Binta washegari da wuri muka gama girki shinkafa da miya nayi da Salat na saka a babban cooler sai karofi da na shiga gayama Mama chan zamu kwana sai gobe zamu dawo sai ta kalleni tana fadin"To in kin tafi da yunwa kike so ki bar ni kenan..?

Zan yi mgana kenan Anty Hure,ta karbeni da fadin"Kyaleta taje baka ga ni ba, zan yi mana girkin"

Ba dai a son ran Mama muka tafi karofi ba,Chan ko naga yan'uwana har Yaya Asiya nan tayi sallah ita da iyalanta ga Yaya mariya da sai dai mu hadu a karofi har yau ina jin takaicin wannan abun in na tuna.

Kowa ya ganni sai yace na sauya kamar bani ba ni kaina nasan na samu kwanciyar hankali ba kamar baya ba sannan sana'ata ta taimakamin wajen inganta rayuwata mun sha ziyara a karofi ni da yara da su Yaya Asiya mune har gidan kakanin mu Baba ati na gidan muka gaisheta tare da yi mata barka da sallah ko alokacin sai da muka mata mganar dan'uwan Tamadina ko an ji Labarinsa tace har yanzu shuru.

Duk aranar mukaje har Cikin garin Dutsemah muka gaishe da abokan zaman Tamadina kuma sun ji dadi sosai suna saka albarka ballatana da Yaya Asiya taje musu da Nama da cincin din da tayi suna saka rika albarka su da megidan da ya'yan su.

Daga kwana daya sai ga shi sai da nayi Biyu Shima sai da Goggo ta yi fad'a sannan muka koma,aiko Mama ta cika Fam kamar zata fashe,Sai kananun mganganu take yi wai an barta ita kadai a gida,mamakinta ya kamani wani irin ita kad'ai..?ina jamal ina Badar..?ga Anty Hure ga Anty Binta da iyalanta nasan nan suka yi bidirin su,ammh saboda korafinta a kaina baya karewa sai da ta tofa ni dai ban ma yi lokacin ta ba shi kuma wanda ta saba zaunar da shi tayi din har ya yi lokacin nata baya nan dole ta kama bakinta tayi gum.

Muna dawowa na cigaba da sana'ata saboda yan makaranta da masu sari,Ranar da Yaya ishaq ya cika sati da Tafiya da Daddare sai ga zainab ta kirani a waya daman da Maman Fadil na saka akayi mata Saving wayar na Hannun Anum ta kafa mata kahon zuka duk ta saka Hafsah ta cika min waya da game game gwara ma Amir shi karatun Qur'ani yaje aka turo masa saboda Haddansa ammh Anum Sai shiririta ko na hanata Dauka sai tayi dubara ta dauka,Ga shi kamar aljanna ko ni ta fini sanin kan wayar in an gama game ayi ta daukan Hotunan banza duk ta cikamin waya.

To ranar ma wayar na hannun su ni kuma ina kitchen ina gyara aya na kunin Ayan gobe saboda Ayan Hafsah bata duba ba,duk akwai datti ajiki sai ya samu gyara.

Anum ce ta rugo ta zo ta kawo min wayar tana fadin"Umma..umma ana kiran ki"

Karba nayi ina kurama sunan ido,yanzu na kan iya karanta suna naga maman fadil sai na rasa ma wajen Dauka,Anum ya kallah ina fadin"Anum matsa min wajen daukan"

Sai ta karba tana dariya Lokaci d'aya tace"Umma ni fa nasan bazaki iya dauka ba tunda naga kina Zare ido"

Kanta na mangara ina fadin"Gidan ku Anum"

Dariya take yi lokaci daya ta Daga kiran bayan tace"Umma a saka a amsa kuwwa ne?

Hararan ta nayi ina fadin"in baki saka ba tare da kunnuwan ki zan ji wayar"

Dariya ta kyalkyacemin da shi Anum Ai shakiyace ta maidani kamar kakarta. kab'ar wayar  nayi ita kuma sai ta fice tana dariya ashe ta jima da Dauka ni kuma ina amsa jin ba'ayi mgana ba yasa na yi sallama lokaci d'aya ina fadin"Maman Fadil kina jina.?

Kawai sai naji muryansa cikin sanyi da zati yana fadin"Ba maman Fadil ba ce,Baban Fadil da Anum ne"

Sai nayi kasake ina jinsa da waya a Hannuna nama kasa mgana jin nayi shuru yasa yace"Kin yi shuru Fa'iza..?

Dakyar na tattaro yawun bakina sannan na iya samun mganata ta fita gaishesa nayi ya amsa yana fadin"Ya gida ya yara na..?ina fatan komai lafiya..?

A gajarce nace komai lafiya,kawai sai yayi kasa da murya yana fadin"Nayi kewarku Fa'iza na kosa na dawo wlh"

Kam na kame da waya a hannuna ina kifkifta ido kamar nan ne nake da Raunin ganin ba kunnuwana ba.

Har yana kara lankwashe murya wajen fadin"Ko baki yi kewaata ba ne Faa'izaaa!"?

Yadda yaja sunan nawa ne sai da Tsikar jikina ta tashi yar abunda na Dade ban ma san yanayin shi ba,Ganin yana neman kwace min yar natsuwata yasa na basar da tambayansa ina fadin"Ya su Zainab da yara..?

Kasa kasa yace"Suna lafiya..Gata ma ta shigo ku gaisa"

Na dauka fad'e kawai yake yi sai da naji mganarta tana fadin"Honey waye hala..?

Kai tsaye naji yace mata"Karbi mana..Fa'iza ce'

Sai ta karba da murnanta muka gaisa ta tambayi su Anum nace suna gaisheta cikin yanayin mganarta tace"Na zata tare da su Honey zai taho sallah sai na ganshi shi kad'ai Maman Amir"ina yar dariya nace"Shine bai bukaci yazo da su ba ne,ammh ki bari da Babban sallah. Nima ai ina binki bashi zuwan su Farhan ko..?

Da sauri tace"Zasu zo ina so sai na yaye Fadil ne na tattaro miki su gabadaya Fadil ai d'an gidan Umma ne,ko wannan zuwan yana ganin Honey ya fara gauranci yana kiran sunanyensu Anum Umma ko Rad'am a bakinsa"

Dariya nayi ina fadin"Ina ruwan Farhan"

Cikin mganarta ta cigaba da fadin"Daddy ne ya hana da wannan hutun ma kin gansa,ammh zan kara tuntubansa in ya bari zaki gansu"

Kai tsaye nace"Allah yasa ya bari din"

Bamu jima muna mgana ba muka yi sallama ina ji tana cewa"Honey ga shi"sai nayi saurin latsan dan jan abun nan alamun kashewa bazan iya da sababbin kalaman da Yaya Ishaq ya koya a kaina ba,Bani da wajen sauke su ballatana su samu muhalli sai ga shi ya kara kira sai na kwalama Amir ya kira yana zuwa na mika masa wayar ina fadin"Baban  ku ne,jeka ku taru da yan'uwanka zai yi mgana da ku" 

 Da Murna ya karb'a suka fita falo ina jinsu suka Dauki wayar suna ta Bidirinsu gajiya yayi ya kashe wayar ko kudin ne kila suka kare, tunda ya Fahimci ni din ne bana bukata jin mganarsa sai ya shafa ma kansa lafiya.

Bai dawo ba sai da ya kwashe kwana Goma tsakanin miji da mata daman sai Allah,har ga Allah bana son auran Zainab ya kare saboda haka,ance ba'a son kishiya ammh ni Fa'iza ina kaunar Zainab da zuciya d'aya ta karbeni ta mutumtani fiye da yadda wanda ya ijiyeni ya mutuntani,bawai don tana ma ya'yana Hidima ba a'a ance Halin mutum ka fad'esa bata da wulakanci bata da girman kai,tunda nake da ita bazan ce ta taba min wani abu da ya sosa min raina ba. tana kaunata tana kaunar ya'yana nima shiyasa nake kaunarta da ya'yanta bana fatan kuma auransa ya samu matsalan ina addu'an ya kauda dukkan Fitina ya Dauwamar da su har abadan saboda sun fi dacewa da juna.

 Zainab ta aiko ma da yara Tsaraban kayan sallar da tayi musu yan kanti harta Amir yan kanti ta siya masa ni kuma sai ta aiko min da Takalmi da Jaka da mayafi,Mama kuma Atamfa da leshi har da kud'i Badariya ma da nata Jamal ma boyel da takalmi shima uban gayya sabbin kaya ya Dawo da su fin kala Biya Mama an samu Duniya sai washe baki take tana jin dadi fadi take yi"Kaga to in da abun arziki yake zaune da digadigansa Ishaq ammh ka zauna kana wani shirme,in da ka zauna wazai biyo ka da wannan kayan arzikin..?

Shuru yayi bai mata mgana ba,yasan shi da Zainab akwai kauna da Fahimtar juna matsalan ilmin addininta Ragagge ne batasan miji yafi ubanta iko da ita ba, gani take yi da ita da miji duka suna karkashin ikon Mahaifinta ne shi kuma Daman haka yake so,kada ikon ya'yansa ya tashi Daga Hannunsa har Abada yana son komai ya'yansa zasu yi cewarsa ne da ikonsa,Ko wannan zuwan ya sake zuwa ya basa hakuri sai da ya gama gayamaasa mgana har yana fadin bai kai ba,bai kuma isa ba, kaunar da yake masa ne yasa ya aura masa Zainab ammh shi ai ba sa'an auranta ba ne Daganan yasan Allah ne ya kai shi inda za'a koya masa Rayuwar duniya indai bai santa ba.

Mama nata mgana ko jinta bai yi ya fada kogin Tunani sai da Jamal ya tabashi sannan ya dawo Hayyacinsa Mama tace"Ka daina wannan zurfin Tunanin fa"

Anty Hure da bata koma ba har Lokacin tace"Kuma hawan jini yafi kama yara yanzu ba".

Shi dai shuru yayi bai yi mgana ba Sai da Mama ta tambayesa ya mganar aikinsa sannan yayi ajiyar zuciya yace"Mganar aiki ana ta nema Mama ni ma ban zauna ba in da naji ana neman masu karatu irin nawa ina Tura Cv dina ko za'a dace.."

Mama tace"Yanzu shikenan ka rasa wanchan aikin naka.?.

Kai tsaye yace"Sai dai fatan samun wani Mama ammh wanchan sai babban Rabo kad'ai ne zai iya dawo min da aikina, shima bayan Hukuma ta wankeni daga wannan zargin"

Mama ta jinjina kai kafin tace"bakomai muna gayama Allah ko waye ya yi maka sanadin barin ka aikin ka da ikon Allah shima bazai taba samun kwanciyar hankali ba"

Aransa ko sai yace"Ba wani bane Hakkin Fa'iza ne. Allah ne yaso ni ma da Rahma ba sai na mutu ranar lahira na tashi da bari d'aya na jikina na Rinjaya na ba.Subhanallah Allah ya Tsaremu"

Sai jikinsa ya dau d'imi ya tuna wa'azin da yaji lokacin dayaje Abuja na wani malami ya na fadin azabobin da Allah ya Tanadar ma mai kuntata ma matarsa da wanda ya kara aure bai kwantanta adalci a tsakanin matansa ba ,sai yaga kamar malamin yasan shi,kamar da shi yake yi wa'azin jin wannan wa'azin ya sa tsoron Allah ya kara kamasa.

wannan azumin ya Dawo da kudirin niyar bama Fa'iza hakuri su Fuskanci Sabuwar rayuwa ammh ya kasa kwarjini Fa'iza take yi mai,sannan bata sakar mai fuska, kuma bata yadda su kebe inda ba Mutane kamar bata son ma taji dame yazo ya Lura da ita tana da'ri da'ri da shi.

Ni ko ta bangare na bansan yana yi ba, duk da ai ya fad'amin in ya dawo zamu yi mgana ammh sai na rika kauce ma haduwa dagani sai shi ko bana wani abu,in Hafsah na makaranta da yara bana yarda nayi zaman daki ina Tsakar gida ina tsiro aikace aikace sanda Sakon Zainab ya iso da kaina na kirata nayi mata godiyan Dawainiyar tayi yawa sai ta yi dariya kafin tace min"'Haka Honey yace. Ammh sai da yayi korafin ban siya ma Uwargida nata Leshin ba"

To na dai ce a bini bashi zan biya in sha Allahu"har muka gama waya ina mamakinsa wai uwargida..?lalle abunda ya baka dariya wata rana shi zai saka kuka gashi ina gani akan Ishaq kabir karofi.

Duk neman Hanyar da zai samu kaina yayi bai samu ba,na kauce ma wannan haduwar tamu,kwatsam sai ya Tsiri shigewa dakina ya kwanta saman gadona Hake hake Allah na tuba ko a zamanin baya, baya shigowa Dakina iyakarsa in kira ne ko mgana daga bakin kofa ballatana yanzu da komai ya sauya.

 Ni ban ma san yana shiga ya kwanta ba,Saboda in yara sun tafi makaranta ni kuma ina waje ina aiki Dakina sai dai in nazo daukan wani abu nakan shigosa,ranar ma Zobo aka zo siya na Dubu d'aya naje neman ledojin da nakan tara acikin dirowa ta, har ga Allah ban gansa ba ina ta duba ledan sai ji nayi kafa daga bayana tana zungurin Bayana na tsorata na juyo a firigice sai kawai naga Namiji kwance a kan gadona ban ko ga fuskarsa ba saboda ya rufe kansa a tsakanin Filo gefe nayi gabana na fadi jikina ba inda baya rawa ammh bakina bai yi ihu ba sai naji nace"Subhanallah waye anan..?

Ashe yana ji sai ya Dago kansa yana Dariya ido na zaro ina kallonsa kafin nace"kai ne..?

Mikewa zaune yayi yana fadin"To da waye zai shigo miki daki ya kwanta in ba mijin ki ba..?

Sai na jinjina kai mamaki ya cikani,Ban ce masa koomai ba na koma na cigaba da neman ledata,Saboda yanzu kuma sha'aninsa nasa yafi karfin Tunanina kawai ban ankaraba sai ji nayi ya chachumeni ta baya ya rumgumeni ya hadani da kirjinsa,tudun kuguna na dukam bayansa Hannayensa Cak ya dadumo kirjina kamar ya samu wani abun har da sauke ajiyar zuciya nan da nan jinin jikina ya daina aiki ya Tsaya cak! sai na rasa ina zani tun ballatana da Bakinsa ke saitin wuyana ya na fesar min da Numfashi ko a lokacin da rabon ya'ya ke giftawa tsakanina dashi bai san wadan'an abubuwan ba. shi dai bar sa ya biya bukatarsa in ya Damesa. Ba domin ya damu da ni ya nawa Bukatan ba.?shiyasa tun a wanchan Lokacin bazan iya dora komai akan bukatawata ba, na dai san ni bakuwa ce a harkan bansan komai ba.

 Yanzu da yake yi min wad'anan salon sai nake neman rasa hankalina, a yanzu ma Hannayensa suka fara kasa zuwa wajen cikina yaraf na saki hannayena jikina na rawa ban dawo Hayyacina ba sai da ya daga riga ta,ya dafa haannunsa saman marana Fatar Hannunsa ta had'u da nawa lokaci daya muka gwama Numfashi Hmmmm!!!!!"

Bai kyaleni ba,sai ma bakinsa da ya kai saman kunnena ya lasa sai da naji ji kamar na shid'e na sake dawowa,Lokaci d'aya da ya yi amfani da wata irin karuwar murya yana fadin"Fa'ii...ki zo ki tayani barciii..'"

Lokaci da'ya yana matseni a jikinsa inaji ta baya abu na dukan bayana na rikice iya rikcewa kamar wata gaula,Yana shirin ya kai hannunsa akasan zanina na shammacesa nayi kasa bai zata ba sai ya koma kan gado ya zauna Dabas ni kuma kamar wata yarinya sai na saka gudu na fice Daga Dakin, Allah yasa masu siyan zobon suna tsakar gida da sun sha kallon yadda na fito a razane,Kitchen na shiga ina Sauke numfashi har Lokacin Salon sa da Sautin muryansa basu bar jikina ba sai da na Huta sannan na samu ledan Aya na juye cikin wani Bokiti na zuba musu zobon na fita na mika musu shima ganin na gudu sai bai biyoni ba,Ranar wasan buya na rika yi masa bana son ma mu had'u,Da daddare dukkanmu muna falo shi yake koyama Amir lissafi ni kuma ina Rubuta ma Ahmad Huruful Hija'iya a wani Takarda inda zai ta maimaitawa Saboda ya iya rubutawa da karantawa,Dagowa goma sai naga idonsa kaina Lokaci da'ya yana dagamin gira da na Fahimci haka sai na daina yarda ina dagowa na yi kamar bashi ma afalon da zamu kwanta yayi ta tsiro da sani aiki ni kuma sai na saka ya'yansa daga karshe sai ya kalleni yana fadin"Fa'iza ina jin zafi ina so nayi wanka"

Ban kallesa ba nace"Amir tashi kaje famfo ka tarar ma baban ka ruwa in ya cika Hafsah sai ta Dauko"

Sai ya bata rai har Amir ya mike sai yace"Kai koma ka zauna. ke na saka in kuma baki yi shikenan"

Ina kallon rubutun gabana nace"To Abban Anum baka ga aiki nake yi ma yara ba..?

Amir ko sai ya mike yana fadin"Daada bari na cika maka"

A chunkushe ya mike yana fadin"yi zaman ka zan yi da kaina"

Dariya ta kusa kamani sai na Danne da kansa ya fita ya Debi ruwan yazo ya kai tiolet din Dakinsa, chan kuma ina Murnan na rabu da k'aya sai ga shi ya leko yana fadin"Baki shimfid'a zanin gadon da kika wanke ba ne Fa'iza..?daman yasan nayi wanki jiya kuma har da kayansa na wanke da zannuwan gado saboda bana so na shiga Dakin ya Ritsani ne yasa naki shiga na maida zanin gadon, sai kawai na kalli Amir ina fadin"Yana nan saman Dirowa dauko ka kaje ka shimfid'a masa"

Ai ban gama Rufe baki yace"Bar shi bana so'

Daga haka ya koma Daki sai da nayi Dariyan data kawomin Amir ya kuramin ido ina Dagowa muka had'a ido sai na Dauke kai ammh yaron nan sai cewa yayi"Umma Daada ne ya saka ki aiki fa..?

Sai na ware mai ido ina fadin"Eh Daadan fa sai akayi ya ya..?

Sai ya kasa mgana araina nace ji yaro da iyayin tsiya to dai har muka shiga barcin ban kara ganinsa ba ni kadai in tuna yadda ya yi jiya sai naji Dariya tazo min,Washegari da safe da ya fito na gaishe sa a dake ya amsa kayan karyawansa kuwa yana fita rakasu makaranta na shiga na ijiye mai na fito. sai da ya dawo ya iskeni ina karyawa a falo yana ganina sai ko ya zo ya zauna karshe dai tare muka ci ni dai ban sake ba sai da muka gama ne ya kalleni yana fadin"Yanzu abunda kika yi jiya kin kyauta kenan..?

Ido na waro kafin nace"Me nayi..?

Sai ya yi wani kamar maraya kafin yace"Au baki ma sani ba ko..?jiya nace ki gyaramin shinfid'a kika saka Amir ko..?

Sai na dukar da kaina ina fadin"Ai lokacin ina ma yara a karatu ne"

Ban dire ba ya tareni da fadin"Ko kina menene in na kira ki na sakaki aiki zaki ijiye kizo ballatana gyaran Shimfidar miji. Kin ga jiya kin kwana mala'iku na fushi da ke"

Mamaki ya bani na kallesa sai yace"Eh mana ai kin fini sanin haka tunda Lokacin kina gaban Mama a kwai ki da son zuwa islamiyan nan ta la'asar"

Araina sai nace ashe ya sani ganin ya nace da mganar ne yasa nace"To kayi hakuri"

Nan da nan yaji dad'i ya washe baki yana fadin"Yauwa ko kefa yar albarkata. Ina fatan in nakara kiran gyaran Shimfid'a baza'ayi min gaddama ba ko?.sai na gyada mai kai saboda ya kyaleni aiko bai barni ba. sai ya rika jana da Hira yana shigemin ni ko ina baya baya labarai har da wad'anda basu Shafeni ba abun mamaki har yana tambayata yaushe zamu je karofi mu gaida su Goggo..?

Sai kawai nace ranar da ya shirya sai yace sai weekend saboda yara.

Ban ko tsaya mamakin sa ba domin yanzu ya daina bani mamaki in dan yayi wata mganar ko ya yi wani abun.

Jamal ya yi shirin komawa makaranta acikin kayan abincin mu na dibar mai Taliya da shinkafa da man girki sai na bashi Dubu goma, biyar yayi pocket money, biyar yayi na mota nace in na samu zan bama yayansa ya Tura masa ya karba yana ta godiya har yana fadin"Allah ya kawo babban Shago Matar bro.'

Ina yar dariya na amsa mai da Ameen haka ya tattara ya tafi to yayan bai da ko sisi yana nema nema. itama kanta Maman bata da shi kawayenta duk sun gajeta ba wacce tafi bani mamaki sai Hajiya Barira bata zo ba tun bayan da Yaya Ishaq ya fito Sannan Mama ta shirya taje gidanta bata sameta ba,Kuma bata biyo sahu ba kuma bata Hakura da binsu ba shine da yagaji ya yi mata mgana fadi yake yi"Mama yanzu rayuwar nan ba irin da ba ne. In kana da shi ayi dakai daga Lokacin daka rasa bamai son rabarka ka zame masa wahala Mama.ni kaina alokacin da nake dashi abokai har da na banza kuma ai mun taimaka musu ammh yanzu ko kare bana gani ballatana kira an san bani da shi kowa Tsoron haduwa dani yake yi kada na gayamasa matsalata"

Ko nace ya taimakeni"

Mama ta gyada kai tana fadin"Uhm nagani,ammh na Dauka ko kowa zai gujeni ban Dauka harda Hajiya barira ba, ta bani mamaki kamar mafa blooking dina tayi fa"Dariya yayi yana fadin"Shi yafi komai sauki Mama bazata yarda ku hadu ba, tasan baki da shi yanzu zaki yi Tunanin samun wani abu daga barayinta, a baya kina da shi kuna nima ina dashi kinga dole ta rab'eki ki kama kanki da kowa kawai ki Rumgumi kaddaranki Mama kina gani ko a yan'uwa sai wanda yaga Allah ne yake tunawa dakai in ka shiga Halin babu, sai kuma wanda ma kake tsammanin zai tsaya maka ranar da baka da shi, sai kiga shine ke baya baya dakai. wanda ka gujema Lokacin da kake da shi shine in ka shiga Halin Rayuwa zai taimake ka"

Mama na hawaye tace"Hakane wlh nagani Ishaq"

Tana tuna Hajiyar Dala ko wayarta bata son dauka yanzu. Ammh Goggo ko bata zo ba zata aiko da Sakonta tabbas Lokacin da suke da shi basu mu'amalance ta da kyakyawan mu'amala ba,ammh ita bata rike su ba ta Duba zumunci ta kuma bi Umarnin Ubangijinta..

Nan ya fice yana fadin"to haka halin mutanen duniya yake Mama Lokacin da kake da shi ayi da kai, in kuma baka dashi ayi da wanin ka"




*Janafty*




*KNKB2009*


*Ki biya ki karanta cikin salama,Kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta min littafi,Sannan kada ki yad'amin shi,Pay N500 regular ko kuma VIP N1000, Via Jamila Umar Gt bank 0552179550,ban da tsarin kati wannan karon, a turo ta POS, Shaidar biya ta wannan lambar 09069067488*



Haka muka cigaba da lallab'a Rayuwarmu yau fari gobe Tsumma. abunda aka samu aci agode ma Allah ba domin ina samun,masu son Turaruka ba,da tuni jarin Zobo da kunin aya sun Dargane da Hidiman gida na yau da kullum,To riban da nake samu na turarukan,sun fi 

na su auki. da shi nake had'awa muna rufa ma juna asiri sannan Allah ya sanya ma kasuwancina Nasibi komai na yi sa sai ya kare kuma ana nema,Shi kan shi Yace min ya gaji da zaman gida ba abunda yake yi ranar har ce min ya yi ko zan fara doramai zobon da kunin Aya ne yana zuwa tasha ya zauna min..?

Sai da naji kwallar Tausayinsa na kallesa yana bakin kofa zaune duk ya rame ya lallace ba wannan farin ba kyau ba fafa ba,kwanbo rayuwa kenaan.

A lokacin ban ce mai komai ba sai da ya karamin mgana sannan nace mai"Ko fita da shi baka ga inayi ba, a gida ake siye shi. Kai ma da wata mgana ka ke"

Cikin bayyana yanayin dayake ciki yace"Bazaki gane ba ne Fa'iza wlh na gaji ne ko Dako zan je na fara ne..?

Na kallesa ina maimaita"Dako..?

Sai ya gyad'amin kai yana fadin"Shima sana'a ne kuma akallah zan rika samun wani abun da zan rika taimaka miki da shi"

Da sauri nace"Aa ka bari dai mu yi Tunanin wata sana'ar tukunnah"

Da haka ya bar mganar tunda muka yi wannan mganar sai ta Dameni sai naga yana da gaskiya shi magidanci ne,zama agida kad'ai ya isa yasa bawa Damuwa na yi ta tunanin sana'ar da zai fara ban samu mafita ba, yanzu fa ko wata sana'a ta kudi ce sai kana da shi,ni kuma d'an jarin nawa kad'an ne Riba kuma agida muke cinye su don ma yan'uwa suna ta tallafawa.

Babban sallah tazo tana matsowa bani da matsala tuni na wanke ma yara kayan su na goge ga kuma na wajen Zainab, daman basu saka ba,ni daman bani da matsala in dai ya'yana zasu saka su fita cikin tsara Allah ya gama min komai Mama bata nan ta tafi Yamai da Hure zata koma sai ta bita,tafi wata achan ina jin Yaya Ishaq na fadi'n kila chan zatayi sallah Sai kuma naji gidan ba Dadi ba Mama ko yaya mutum yake  Rahma ne haka ma yaran su yi ta fadin"Daada yaushe Mama zata dawo..?sai yace"Zata dawo in sha Allahu"

Ga Hafsah ma sun yi Hutu ta koma korafi tayi ma su Goggo Hutu, Badar kuma tana gidan Anty Binta suna ma Jarabawar Fita ne bayan sallah zasu gama makarantar gabada'ya ita da Raliya tun nesa da kofa tazo ta sameni tace min"Anty Fa'iza zamu gama makaranta akwai kudin riga da zamu yi na graduation din mu, wajen dubu ashirin ake so kowannen mu ya bada kinsan ba ni da shi Mama bata da shi ko da ta na nan Yaya ne kuma kina gani kece komai nasa yanzu,Anty Binta kuma bata ta kaina da na fara mata mganar kudi zata fara masifan itama bata da shi ke kad'ai gareni Anty Fa'iza don Allah ko rabi kika ragemin bakomai nagode".Sai ta bani Tausayi wane ni na manta da Badariya da Sanadinta na samu Rufin asiri, batare da sanin kowa ba na bata Dubu goma nace zan cika mata in na samu shima Dubun goma Sa'adatu ce chan inda muka taso ta samo min wata mata mai son Turare Humra,to da yake ina da Sauran kayan amfani sai nayi mata amfani da shi na samu ba laifi,Sai na koma ina Fafutukar yadda zan sama mata cikon sauran ga shi kuma salla ya matso,Allah ya taimakeni na samu aikin zobo da kunin aya na masu son da yawa da sallah dakyar na had'a mata dubu biyar na kara mata godiya har da kuka ta Rumgumeni tana fadin"Nagode miki Anty Fa'iza yadda kike jin kanmu Allah ya baki wanda zai ji kank'i watarana Allah ya Dauwamar da farinciki da arziki da wadata acikin rayuwarki gabad'aya"

Na amsa mata cikin fara'a ina Fadin"ke meye na kuka share hawayen ki ko sai na kira miki Ya'yan ki ne..?jin haka yasa ta goge Hawayenta,ni na hanata nace ko yayanta kada ta fad'amawa ana saura kwana Hudu sallah tazo da murna tana Fad'amin Hajiyar su Raliya ta biya mata kudin sannan ta bata dubu goma tayi dinkuna sai tace zata maidamin da kudina na riga nayi niyya sai na karbi biyar din da na bata Daga baya na barta mata goman nace tana da bukatu tayi amfani da shi,Badariya ta yi murna tayi murna kamar bakinta zai yage addu'a kam na shata ni ko tana da Muhimmancin da bazan manta da alherinta gareni ba.

 Atamfa taje ta siyo da less sai mayafi da takalmi da jaka,Sai kayan shafa ina D'aga kayan ina fadin"Ehee! kaga yan mata."

Tana Dariya tace"To Anty Fa'iza mace sai da kwalliya mazan nan, kuma suma kyale kyalen suka fi so"

Na aminta da mganarta yasa nace"Hakane Allah ya kawo miji nagari"ta amsa tana rufe fuska ni kuma ina binta da Dariya sai da Yaya Ishaq yaga kayan ne ya tsareta sai ta fad'amai gaskiya kallo na yayi yana fadin"Lalle kina da d'aure ma karya gindi ke baki bukatar kayan kwalliyan sai ita..?

Ina dariya nace"Me Fa'iza zata yi da kayan kwalliya ai wannan sai irin su Badar mata masu kyau da nasaba"

Ita Badariya bata gane mganata ba sai ta karb'e da fadin"Kai Anty Fa'iza wlh kwalliya bata zaba bace.Mu mata kowa yasan yan ado ne da kwalliya"

Shi kuma da yasan kan mganata sai yayi gum ya koma yana kallona ni ko na basar da shi,Daga ni har shi bamu san Zainab da yara zasu zo mana sallah ba,Mun samu tallafi shinkafa da naman sallah Daga gidan Hajiya Daga Korofi kuma Goggo ta aiko mana da kaji da kayan miya mangyada su maggi da sauran Cefane,an yi idi lafiya an sauko ranar nayi mana  shinkafa da miya sai nayi mana cowslow,Sai zobo da kunin Aya Saboda Sallah Jamal ma ya dawo da da bai da kudin mota, yayan yace ya zauna chan yayi sallah nace hakan bai kamata ba na hada dubu hud'u aka turamai nace ya taho gida yayi sallah cikin yan'uwansa.

Ranar idi da yammah sai ga Direba ya kawo zainab da yara,Gida sai ya Rud'e da Murna su Anum nata tsalle da Murna ganin kannensu Farhan na ganina ya Nufeni bakinsa har kunne yana fadin"Umma.."

Na daukesa na daga sama yaro kamar balarabe wajen kyau yana bangalamin Dariya nace"Farhan d'an Umma"

Tazo da naman sa an soya tare da naman kaza anyi pepe dinsa ga su cake samosa da su sprill role, ta zo da kantan kantan na lemuka da biskit, ta ce min Saboda sallah ko kuma in mun yi baki,Nace mata"Angode. Sai dai gaskiya sai kunin aya da zobo ya kare tukunnah"

Tana dariya tace"Ga abun arziki wazai bi ta na kwalayen bature masu shegen zaki"

Ishaq basa gidan shi da jamal sai dai suka dawo suka ganta kuma daga alamu uban gayyar yaji dadin ganin matarsa, Dakin mijinta na Sauketa,Yaran kuma suna tare dani Direban daya kawo ta bai koma ba. tace zai tsaya sati d'aya zasu yi zai maida su sai aka sauke sa Dakin Jamal.

 Sosai wannan sallar tayi mana Dadi,babu abunda yafi kwanciyar Hankali Dadi ni nake hidiman abinci na gida da na yara, Zainab sai da tana tayani da Hiran duniya,Farko da na sauke Zainab a dakinsa samu na yayi yana min mgana wai meyasa sai Dakinsa na sauketa,dakina fa..?

Na kallesa ina fadin"Saboda mene?sai mu gamutsu da ni da ita da Anum kamar ba bu wani da'kin..?

Kuma nan din ta saba sauka in tazo a Dakin naka shi yasa na sauketa anan"

Sai kawai ya juya yana fadin"Ki bude dakin Mama ki sauketa anan mana"

Mamaki ya bani Namiji sai a barsa da gulma ya gama wannan borin kunyan, sai ga shi suna kulewa a daki bamai jin su ammh yazo zai min dad'in bakin su na maza.

A gida muka cinye sallar mu sai ranar washegarin sallah da kwana uku Zainab ta matsa sai na shirya mun fita. da zamu tafi,na saka atamfata da Hajiyar su Raliya ta dinka min,Zainab tace ban isa ba ta dinka mana Less mai kyau iri d'aya,har dinki daga Abuja aka dinko ta matsamin sai na saka Saboda kada tace ko ban karb'i kyautar nata ba ne,yasa na saka Doguwar riga A shape dinkin ya fita haka ya fitar min da Shape dina in kika ganni a lokacin bazaki taba yarda na haifi Yaro dan shekara sha biyu kamar Amir ba.

Ina nan da kuruciyata sai dai kowa yasan Fa'iza yar gargajiya ce,ammh zainab bata barni haka ba,Hijabi na saka tace ban isa ba Dole na Dauko mayafin data aikomin da shi da Takalmi da jakata na saka,sai gani na fito ras dani na yarda da Hausawa da sukace kowa ya gyara ya sani ni kaina sai nake ganin kamar bani ba.

Zainab ta kalleni sama da kasa kafin tace"Komai yaji ban da abu d'aya"

Ina dariya nace"Ban yi kyau ba ko..?

Sai tace"Aa fa.Lalli ne yayi miki cikas"

Sai kawai na wuceta ina fadin"Lalle ai naku ne na fararan mata yan gayu"

Domin tayi nata Hannu da kafa, abun ka ga farar fatar kamar don ita aka fito da zanen jan kunshi tana bi na a baya muka fito daga daki Lokaci daya tana fadin"Wlh ko ke kika yi ba karamin kyau zai yi miki ba Maman Amir"

Ina jinta ban ce mata komai ba, ina jan abu zai fito a wannan bakar fatar tawa ina fitowa yaran na Falo suka dago suna kallon mu sai kawai Anum da Amir suka hada baki wajen fadin"Laa! Umma kin yi kyau wlh.."

Musty da Ahmad ma suka karb'a Farhan na jin haka shima yace"Umma jin yi kyau"

Fadil na gauranci yace"Chauu.."

Gabadaya muka saka Dariya,Ni na sabe Fadil na rike yaran duk sun ci yan kanti mazan kaf iri d'aya Zainab tayi musu Anum kuma an cakare da Doguwar riga da takalmin yan gayu Badariya ta kaita akayi mata jan kunshi da kitso da yake bata dauko suma na ba,tana da gashi an yi kitson gaba yaji bit sai yanga take da farko ma kin saka Hijabi tayi sai da nayi mata jan ido,Zainab ta hana sai ta Dauko mata wani karamin mayafi ta nad'a mata, muka fita daman ta fad'ama megidan zamu fita gari gidan Anty Binta mu gaisheta yace to.

Ban kulle dakin ba tunda suna waje da Jamal jakata na Hannun Amir na Zainab na hannun Anum ta kama ta rike in ka ganmu bazaka taba cewa muna cikin wani hali ba,ko mijin mu bai da aiki ba kila in an fad'a maka ma bazaka yarda ba.

Suna tsaye suna mgana da Jamal yaran suka fara fitowa ganin su shar da su yasa yafara washe baki Jamal ne yace su  jere a dauki Hoton Tarihi ko da muka fito har Baban duk suna ta Hotuna Zainab ce a gaba sai ni a baya ina rike da Fadil zainab nata min Tsiyan na nad'a mayafi a kaina,nace mata ban iya saka shi a saman kafad'a ba ne.

 Tunda muka fito idonsa ke kaina kallo kamar zai fad'i,har yana wani bude ido sai ji nayi kawai ya kira sunana"FAA'IZAAA...!

na dago ina kallonsa Fadil dake ta mika masa hannu alamun ya Daukesa bai ma gansa ba ya saki baki da hanci yana kallona Ya nuna ni yana fadin"Fa'iza ke ce.?

Sai dariya ta kamani nace"Ba Fa'iza ba ce Wannan Uwar Fadil ce"

Sai nan ya gano abun da yayi sai ya fara sosa keya Jamal yayi dariya yana fadin"Matar bro ba bro ba,koni ban gane ki ba da farko".

Hararansa nayi ina fadin"Uhm ka manta ne"

Karaf ko Anum tace"Daada yaga Umma tayi kyau ya saki baki yana kallonta"Zainab ta kwashe da Dariya tana fadin"Yes my Daugther"

Sai kunya ta kamani na sadda kaina ya matso ya karbi fadil daga hannuna ammh sai da ya gogi jikina Lokaci daya yana fadin"kin yi kyau,Sannan kamshin yayi dad'i"

Sauran Humran da nake hadawa ce in ta ragu sai na ijiye ban ma cika shafawa ba yau ma Zainab ce ta matsamin sai da na shafa,da sauri nayi baya ina yake sai ya basar ganin Zainab kusa dani sai ya kalleta yana fadin"Matan Abuja sun yi kyau"

Hararan soyayya tayi masa tana fadin"Ai yanzu ta zama matar katsinawa"

Dariya mukayi gabad'aya Fadil ne ya fara kuka yana mika hannu muna juyawa muka ga yara har sun rigamu shigewa mota nayi dariya ina fadin"Dole fadil yayi kuka yaga za'ayi masa kan ta waye"

Mikamin shi yayi yana fadin"Sai kun dawo, kada kuyi dare jamal fita zai yi ni kad'ai ne agidan"

Zainab ta wuce tana fadin"Honey sai fa mun zaga gari ka ma yi hakuri kawai"

Ni dai ban ce komai ba muka shige mota wata bakar Jeep ce kaf ta Daukemu su Anum an kame agaba kamar motar gidan su dariya ma tabani,Gidan Anty Binta muka fara zuwa mun iske har su Anty Mahma,suna gida sun yi mamakin ganin mu dukkanmu a tare sannan cikin shiga mai kyau Anty Binta haka take ta kallona kamar idonta zai fad'o ina gaisheta ta amsa min cikin wani yanayi.Anty mahma ko ihu ta Buga tana fadin"ku zo ku sha kallo wajen Hajiyar Zobo da kunin Aya"

Badariya na gidan tace"Kin manta harda Turaran humra da kwallacha"

Dariya suka bani Zainab tace"Maman Amir yadda kika san bata haifi Amir ba"

Anty mahma tace"Fa'iza nada jiki mai kyau gaskiya"

Mun dade agidan kafin mu yi sallama Anty Binta dai sai kallo na take har muka tafi, sun yi mgana da zainab tace yaushe tazo tace shekaran jiya Daga gidanta Badariya ta biyomu muka taho tare da ita,jin nace har gidan hajiya zani mata yawan sallah.

 Ba gidan Hajiya mukaje ba da muka fita ba,sai da muka fara zuwa anguwan da muka tashi. Allah sarki gidanmu an buge sa ya zama sai Filin gwamnati Sa'adatu da Habiba sun yi murnan ganin mu sosai,na kullo musu nama da lemu da Zainab ta zo mana da shi, duk wanda yayi maka mutumci kada ka manta da shi, gidan Hajiya sai yammah muka je bata gidan sai su Raliya da yayyinta da suka zo sallah, ammh sun kirata a waya nan muka yi sallar mangariba muka ci abinci sai gata ta Dawo tana shigowa su Anum suka nufeta suna oyoyo Hajiya ta tarbesu tana fadin"Oyoyo Ya'yan Hajiya"

Zama tayi muka gaisa Zainab ta gaisheta ta amsa sai na gabatar mata da ita sai ta kalleta tana fadin"Maraba da Fa'iza da Zainab naji dadin wannan ziyaran Allah ya hada kawunan ku"

muka amsa da Ameen ta karbi Fadil tana fadin"Wannan ne kama da yan sudan di'n fa..?

Ina dariya nace"Kanin Farhan ne"

Tana dagasa sama tace"Naga kaman su da Amadin ki".

Hajiya ba ruwanta tana da sakewa muna ta Hira da ita tun zainab bata saki jiki ba har ta saki yaran kuma tuni su Raliya sun jasa su cikin gida,duk yadda muka so mu tafi kafin isha'i sai da ta hanamu shi ko Babansu sai kira yake yi Zainab nace mai muna Hanya sai da muka yi sallar isha'i muka yi shirin tafiya ta bamu kyautan atamfofi super guda biyu,yaran kuma kudi sabbin yan Hamsin kowannen Bandir d'aya Badariya kuma tace ta dawo ta karb'i nata Sakon har haraban gidan ta rakomu ita da ya'yanta da sai tambayan Hajiya suke itace Fa'iza me Turare da dilka..?.Sai Hajiya tace itane sai kiga wad'anda basu sanni ba suna gaisheni cikin girmamawaa.

Sai da muka kamo hanyar gida sannan Zainab tace min"Yar'uwan ku ce Hajiyar nan..?

Na girgiza kaina ina fadin"Aa sune shugabannin wata kungiyar taimakon mata da marayu,wad'anda suka koya mana wannan sana'ar da nake yi. sanadin haduwar mu kenan sannan Raliya diyarta kawar Badar ce"

Sai ta rausayar da kai tana fadin"Tana da kirki sosai"

Na jinjina kai ina ba'a mgana,hirar ta muka rika yi har muka isa gida,Badar na fad'in irin kudin su ya'yan Hajiya manya maza duk ma'aikan gwamnati ne,matan ma suna auran manyan manya a garin katsina,itama aiki take sannan suna da manyan kungiyoyin mata na taimakon mutane"

Ko da muka koma Gogan ya cika saura Kiris ya fashe sai hararan mu yake yi,Zainab tace"Honey mun dawo"

 Yana kwance kan kujera yace"Na ganku,sannan ku da zuwa sai a tube a sama min abunda zan ci"

Ina kwantar da Fadil da yayi barci akan kujera nace"Yunwa kake ji.?ina abincin da na bar maka a kula..?.

Yana daga kwancen yace"Ban yi ra'ayin ci ba,sabo nake so"

Ni da zainab muka kalli juna sai ta zauna wajen kafafunsa tana fadin"Maman Amir barayin ki ne wannan, ni bari naji da lallashi"

Ban damu ba,na shige dakina na sauke mayafina da kayan hannuna na shige kitchen.  yaran kuma suna ta murna da Budirin kudin da aka basu suna nuna mai ya karb'a yana fadin"Tunda kun zama masu kudi kowa sai ya bani goron sallah"

Suka fara Dariya yana taya su bansan ya suka kare da Amaryansa ba, ni dai Shinkafa na sake dafamai sai nayi mai miyar albasa da naman kaza na kawo mai da maltina na iske suna hira da matarsa sai na shige daki nayi wanka na Sauya kaya na gaji ga barci yaran ma da kansu nace suyi shirin kwanciya,Fadil kawai na karb'a mukaje muka kwanta Farhan tare da su Amir zai kwana Anum kuma sai ta gama iyayinta zata shigo ta kwanta.

Mun so washegari mu je karofi ya hana,Sai da aka kara kwana sannan muka tafi gabadaya har da shi da Badariya da Jamal,sai dai su Goggo suka ganmu kamar daga sama mamaki da murna ya hana Goggo sakat sai fad'i take"maraba da bakin alheri. ni kadai da zaratan masu gida haka,Allah yasa kun zo da cefanen ku"

Amir ya zaro mata kudi yana fadin"Nawa kike bukata Tsohuwa..?.

Ta ko warce kudin tana fadin"Duka nake so"

Sai ya fara fadin'Ke ko goggo baki san wasa ba"

Gabadayanmu sai da muka yi Dariya Yaya Ishaq dai duk yaji kunya,Kansa na kasa yana gaida Goggo ita ko a Fuska bata nuna masa wani abu ba,Su Anty nasara duk suna gida aka gaisa sai fa alokacin wasu suka san Zainab da su Farhan,mune har gidan su Yaya Isa achan muka sallar la'asar daganan muka isa gidan Yaya mariya tayi mamakin ganin mu sai kallo na take yi cikin gatse tace min"To su Fa'iza dai akwai ki da  son a sani yawo da kishiya"

Allah yasa zainab ta shiga ciki tayi waya,da Yaya mariya tamin baramb'arama a gabanta,ban bata amsa ba ta kara kallona tana fadin"Naga kin yi wani d'anye ne ko dai ciki kika kunso ne..?

Dariya na kwashe dashi ina fadin"Ciki? ai mun bar ma masu mazaje a hannu"

Dariya ta yi lokaci d'aya ta daki kafad'ata tana fadin"Oh Allah! ji yadda Fa'iza ta koma  shekaru biyar bqya, wazai ce Fa'izan nan ce mai shuru shuru da an yi mgana ta hau kuka tana kuyi hakuri"

Tafad'a tana kwaikwayon mganata ni dai ina ta Dariya Hafsah na gidan daga barci ma ta taso na kalleta ina fadin"Sannu yar hutu gidan Goggon kenan..?tana sosa ido tace"Yau fa nazo chan hayaniyar yara"

Yaya mariya tace"To ai ga hayaniyar nan Fa'iza ta tattaro miki har da gayyar sod'i ba katin gayyata"

Sigina na rika yi ma Yaya mariya ammh ta nuna kamar bata gane ba,Allah ya taimakeni da Zainab din ta fito sai ta gyara bakinta sai dai Taki sakin jiki da ita sai ma had'e rai da tayi shiyasa bamu dade ba muka tafi sai ko ta rakomu har gidan Goggo nan suka had'e Da Yaya Ishaq akayi kallon kallo ta Dauke kai abun mamaki ammh shi sai yace"Mariya ba gaisuwa..?to ni bari na gaisheki tunda ta wani fanni ni kaninki ne an yi salla lafiya ne  ?

Ba ita ba har su Goggo sai da suka yi mamaki sai dai ba wanda ya nuna hakan,Yaya mariya ko da lafiya ta amsa mai kafin ta Dauke kai, daman taji labarin sa a wajen Hafsah kafin ta tafi sai da tajani gefe tana fadin"Ke naga wannan wawan mijin naki na wani rawan kafa akanki saboda yaga yanzu ba shi da komai, kina sana'a kina yi mai wahala to in kika sakar masa ke kika sani,kada dai ki manta da abubuwan da suka faru a baya wlh kada naji kin sakarmai ki bari sai ya samu aiki yi in har chanjin na gaske ne sai ki gani"

Ban ja da nisa ba nace mata toh kawai nasan halinta yanzu ina ta wata mgana sai ajimu daga waje,

Kafin mangariba muka tafi,da Tsaraban su gyada da aya,Sannan na taho da ayan na da ganyen zobon da Goggo tace na bada kudi ayo min Sautin su a kauye anfi samun sauki,To shine na ba ma Hafsah da zata zo ta zo mata da kudin, shine na dauko kayana ita dai Hafsah tace sai ta kara kwana biyu zata dawo.

Tunda muka dawo bamu sake fita ba muna gida muna warware gajiya,Zainab sati daya tayi ta koma Abuja ni kaina sai da naji kewa ballatana yara da suka saba da kannensu,shi ko Yaya ishaq ranar da ta tafi har ce min yayi yaji dadin tafiyarta kila na sauraresa yanzu kai namiji sai a barsa, nan yake shigewa daki da ita fa yana amfana ammh baazai yarda ba sai ya yi dadin baki.

 An gama Hutun salla yara sun koma makaranta Mama dai taji dadin yamai bata dawo ba,Hafsat ta dawo saboda makaranta,Badariya kuma na gidan Anty Binta tsakani da sallah ba Dadewa suka yi graduation na gama makaranta,Raliya har walima Hajiya ta shirya mata agida,an yi waliman ko sati ba'ayi ba Hajiya ta aiko min da Kayan saka ranan Raliya,nayi murna sosai Badariya itama tazo tana fadamin har da na Halisa itama an saka,yar wajen Anty Binta zatayi aure a kano dan'uwan mijin  Hajiyar Dala ne,ita kuma Raliya chan wajen bikin Laila suka hadu da shi,Yaron yayar wanda Laila ta aura ne.

Bansan me ya faru ba sai gani kawai nayi Badariya ta had'o kayanta tazo ta Bude dakin Mama ta share ta dawo,kamar bazan mata mgana ba sai naga tana cikin damuwa ranar bayan fitan yara makaranta na bita har Dakin sai na isketa tana kuka.

Na tsorata na zauna gefenta ina tambayanta me akayi mata take kuka..?

Sai ta mike zaune tana cemim"Don Allah Anty Fa'iza aure na waye..?

Kai tsaye nace"Aure na Allah ne Badar me ya faru ne..?

Sai ta sakamin kuka tana fadin"ba na fada miki an saka ranar auran Halisa ba?

Na daga mata kai sai ta cigaba da fadin"Shine shine fa tunda ta samu ssurayin nan take min gani gani har Anty Binta tana gani Halisa na min wulakanci don ina zaune a gidan su,Gori kala kala take min wai bani da Tsayayyen saurayi sai shirme shine fa a Shekaranjiya Salisun da zata aura yazo daman ya sanni don yace ta kirani mu gaisa muna gaisawa muna hira sai zuwa tayi ta cemin wai don Allah na fita tana so ta gana da saurayinta nayi kane kane kamar ina so nayi mata sinacin"

Ta karishe fada cikin kuka cikin wani yanayi nace"Miye sinacin?

Kai tsaye tace"Wai zan kwace mata shi Haba Anty Fa'iza ko Hali na ne ai bazan yi ma Halisa ba,mamanta uwa daya uba d'aya muke da ita ballatana ba Halina ba ne"

Sai na rike hannunta ina fadin"To miye na kuka tunda kinsan ba haka ba ne..?

Sai ta kalleni tana fadin"Na shiga damuwa ne anty Fa'iza na kai minzali nima kawayena duk da muke tare sun yi aure,ga Raliya itama an saka mata rana,ni kuma gaskiya Halisa ta fada bani da wani Tsayayyan Saurayi, sai ka samu kana murna sai ka nemi mutun ka rasa ga halin da yaya yake ciki akallah dai nima na kauce sai wata Lalurar ta Dauke muku Anty Fa'iza"

Sai kawai ta kara saka kuka ni ko na Dage ina ta lallashinta sai da tayi shuru sannan na kalleta ina fadin"Saurareni Badar.shi aure da kike gani na Allah ne,Sannan mutum bai isa yayi ma kansa aure ba. shi kamar zanen kaddara ne irin na mutuwa da haihuwa ne lokacin da Allah yace kun ya fakum ba wanda ya isa ya hana Faruwarsa,kada kice zaki saka damuwa don wance tayi aure wance batayi ba ki dai ki bar ma Allah zabi ki kama kanki ki Tsarkake mu'amalan ki da Allah da Mutane kina Zaune Allah zai kawo miki miji nagari kiyi auranki. kada Surutun mutane ya Dameki ita kuma Halisa ki kyaleta in dai namiji ne ai d'an Babansa ne kina zaman zaman ki sai nuna mata kalan da zata gane tayi kuskure ki kwantar da Hankali Allah na sane da bayinsa masu takawa da Hakuri"

Sai da na Tabbatar da mganata ta shigeta kuma ta aminta da mganganu sannan na fito daga Dakin ni kad'ai a Tsakar gida ina aiki Tausayin Badariya ya cikani kowaani bawa da nashi kabulen Rayuwar in kana gida baka yi aure ba, ace kaki aure shi kuma mijin ba Tukunya ba ne balle ka tantance na gari,sai ga shiga gidan wani auran kaji gwara zaman ka agidan ku ma,ammh duk lalacewar aure yana da Daraja saboda Ibada ce ta Ubangiji.

Nayi alkawarin a duka Khamsin Salawatul di'na zan saka Badariya aciki,domin Allah ya sama mata mafita alokacin ma sai da na daga Hannayena sama nace"Ya Allah ga Baiwar ka nan Badariya ka fi ni sanin Damuwarta a cikin zuciyarta Allah ka kawo mata mafita daga cikin kyawawan mafitan da kake bawa bayin ka Salihai,Allah ka turo mata miji nagari wanda zai share mata hawayenta"

 Sannan na shafa a raina ina jin Wani iri,rayuwa kenan kowa da irin tasa kaddaran.






*Janafty*




[7/17, 7:32 PM] +234 703 465 7829: *KNKB2010*


*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000*

*09069067488*



Har ga Allah na taya Badariya damuwar halin data ke ciki,Saboda ina aiki in abun ya fad'o min a rai sai na tsaya nayi mata addu'a acikin raina ballatana da naga tafi kwana biyu kafin ta warware sai nayi amfani da wannan damar na kara jawota a jiki ina kara nuna mata in dai tayi yakini da Allah ke yi to ta saki ranta mun rokesa kuma shi Allahu Rahimun ne,yana share ma bayinsa hawayensa da haka na samu ta saki jikinta. sai ya kasance in yara sun tafi makaranta Hafsah ta fita zata fito  taimaka min da aikin gida,wani Lokacin har da na sana'ata muna yi muna hira hakan sai ya rika debe mata damuwa.

 Ba'a fi sati da dawowarta ba ranar sai Yayan nata ya kirata,ina falon lokacin na shigo da bahon da na jera gorunan zobo zan shiga kitchen na jera a frezer ta ma shigo ta tayani ne ya kirata,Kasa kunne ba Halina ba ne ballatana da nake da raunin ji da nasan ko na kasa kunnen ba lalle bukata ta biya ba,sai ban damu da naji abunda yake tambayanta ba, na shige na cigaba da aikin gabana sai ita ne ta shigo bayan ya sallameta tana cemin"Anty Fa'iza kiji Anty Binta"

Sai na dago ina fadin"Me ya faru da Anty Bintan..?

Cikin yatsina Badariya tace"Wai yaya Ishaq ta kira tana fad'an wai daga mun yi hatsaniya da Halisa ko sani batayi ba na hado kayana na dawo gida"Mirmishi nayi kafin nace"To shi yayan me yace?baki ta tabe bakin tace"Me kuwa.?fad'a ya yi min wai na rika hakuri da rayuwa"

Sai na cigaba da aikina ina fadin"Ya fada miki gaskiya. Ke uwa kike ga Halisa bamai sauya wannan sunan a wajenta har abada"

Daga haka bata kara mgana ba illah hmm!da tace min ta zo ta kama min muna jera gorunan tare ganin haka nima sai na saki mganar muka kama wata,Yadda shi ma bai min mganar ba haka nima nayi kamar ban sani ba ni nasan ina da miskilanci kuma abun nawa ya had'u ne sanadin mijin da nake aure da irin yadda ya tafiyar dani wajen zamantakewarmu,shiyasa na zama ba komai nake mgana a kai ba.ballanta na nuna na sanin din na koya ma kaina ga duk abunda ba'a ce Fa'iza zo kiji ba, ko zo ki gani ba. na fahimci bawa zai fi zama lafiya in ya bar abunda ba ruwansa hadisi ne guda kan haka.

Fargaba na d'aya shekara ta na neman kare mana acikin wannan gidan akwai Karin Dawainiya na kudin Haya,kudin makarantan yara,ga jamal da sai wannan shekaran zai gama ga abinci da Hidimdimun yau da kullum,har takai ga mun fara awon abinci saboda komai namu ya kare sai abunda ba'a rasa ba,da na rasa mafita sai na auno masara aka nika nayi Tsaki da gari yau tuwo gobe fate jibi dambu sannan na kira Goggo nace ta saka ayi min garin Danwake da Taliyan murji ,Hafsah zata zo satin karshe ta taho min da shi ban fito na gayamata muna cikin wani Hali sai dai hikimarsu ta manya yasa sai ta Fahimceni,sai tace ba sai na aiko Hafsah ba,Yaya Isa zai shigo katsina Ranar jumma'a zai taho min da shi

Da haka muka rabu saboda na lura komai in baka Tsara ba sai ka kwana aciki,a kwana a tashi na fara yi ma dan jarin nawa Rugu rugu ga masu siyan zobo da kunin aya sosai ammh kuma ba da yawa nake yin sa sosai yanzu ba,Nafi son ma a bani aikin Had'in Turaruka nafi samu sai dai shi zobo da kunin Aya sana'a ce ta cikin gida da zata tallafi Hidiman da bata gaza dubu goma zuwa kasa ba,duk yadda Yaya Ishaq nake ganin yana cikin Damuwa iya wanda na gani ne acikin Ransa bansan zafin da yake ji ba koda yaushe cikin fad'i yake yi"Kiyi hakuri Fa'iza na barki da wahala.Kiyi hakuri"

Ammh duk da haka ban barsa ya zauna bai je ya duba Zainab da yara ba,tun bayan tafiyarta yafi wata bai je ba ni na matsa mai sai kawai yace min"Kina ta matsamin naje naje..To ina naga ma na motan zuwa ko a kasa kike son na tafin..?

Sai na kallesa kafin nace" A bun bai kai haka ba,Ko ita ka fad'ama baka da na mota ai zata turo maka ka tafi din"

Wani kallo yayi min kafin yace"Sai na gayamata bata fiki sanin bani da shi ba ne..?

Ina jin ya harzuka sai na kama bakina ni kadai nayi kulla kulla na, na had'a cinikina na kwana Biyu, dubi biyar nabasa nace yayi na zuwa na dawowa bazai gagara ba,Ranar naga fad'a kamar zai dageni ya watsar da kudin yace na kwashe su bazai je ba, naki jin mganarsa na barsa masa su a tsakar daki na fice.  ina jinsa yana fadin"Fa'iza ki dawo ki kwashe kudin ki nace,Haba matar nan so kike hakkin ki ya kamani.?gabad'aya kin Lullube rayuwata da alherin ki,so kike na mutu Allah ya sakani a wuta ko Fa'iza ai shikenan kin kyauta"

Ina jinsa sai da nayi dariya wai ina so ya mutu ne ya shiga wuta Allah na Tuba daga taimako ni bana so auran su ya samu matsala ne sannan na dandana rashin miji a kusa bana fatan itama ta dan'dana duk da rayuwata ba irin nata rayuwar ba ne, ita tana da gata gaba da baya ba irina bace da gatan kalilan ne.

 Bansan ya akayi ba bayan kwana Biyu ya shirya yace zai tafin duk da bani da Tabbas nasan Mama ce zata matsa mai tana chan ne ammh na tabbata hankalinta na nan gani take yi yanzu tunda bata nan to sai a hankali,da ya tafi kwana goma yayi ya dawo. Sai dai yazo da kudad'e sun kai dubu hamsin yace Mahaifin zainab ya basa sannan ana ta dai kokarin neman aiki a ma'aikatu Dabam Dabam a bangaran da ya karanta wato na'ura mai kwakwalwa, ni ko a raina da fili sallata da zama na ina rokar masa Allah ya kawo masa aikin da zai amfanesa da kasa bakid'aya.

 Da kudin da ya samo ya siya mana kayan abinci,duk da Goggo ta aiko mana har da shinkafa da Yaya Isa ya kawomin sakon nan kuma na bashi kudin yaki karba yace tace kada ya karbo na kirata ina ta godiya sai tace"Babu godiya tsakanin mu Fa'iza da ina da shi abunda yafi haka ma zan miki shi"na aminta da mganarta yanzu Goggo ba irin da ba ne mijinta Tuni yayi Ritire yana gida sai kudin Fashion yaran ne ke kula da komai harta kudin makaranta Hafsa sune ba abunda zamu ce da goggo sai godiya,Sauran kudin kuma ya ijiye amfaninsu zai iya zuwa kwanan nan sai yabi shawarana ya bar min kudin a hannuna na adana.

Tunda ya dawo na lura ya dawo da Dama daman da yake yi dani,Sai na fara shan jinin jikina,wani abun ma Saboda Badariya na gidan ne yasa yake ragamin,daya fara shigemin nake zaraf na shige dakin Mama ko na fito Tsakar gida na kirkiri aiki,haka kurum bana so mu kadaice saboda gudun kada ya ruguzamin shirina.

Da daddare kuma baya samun dama Saboda yara ina yi musu karatun Qur'ani saboda Anum ma ta shiga ajin Hadda Baban ma yana yi musu na boko duk dare in mun gama su yi shirin kwanciya,ko yana son mgana dani sai nayi saurin jan Anum mu shige Daki mu kwanta ba Halin kuma wani abu saboda idon yara,da kuma idon Hafsah tunda tare muke kwana da ita.

Yau muna zaune bayan mun gama cin abinci da ni da yaran duka muna kasa ne ina musu karatun Qur'ani Anum tana izifi goma ne Amir kuma ya wuce ashirin,su Ahmad kuma suna kasa kasa izifi biyu,shi yana kishigid'e saman kujera yana kallon mu har muka gama,Sai Amir ya mike yana fadin"Daada yau ba zaka koya mana karatun ba ne,?

Yana daga kwance murya a shake yace"Ban ji dadi Amir sai gobe..yau ka famshe ni ka koya ma kannen ka"

Sai Amir ya amsa mai yace su Anum su dauko littafan makarantan su,sai suka dauko ya fara duba musu,ina gefe har na fara gyangyad'i saboda gajiya Hafsah daman in yana falon bata cika zaman falon ba,sama sama naji Anum na kiran sunana"Umma..Umma!

Sai na yi Firgigit na farka ina hamma cikin,lokaci daya nayi mika ina fadin"Nagaji ne menene kuke kirana..?.Amir yace"Umma kema ki zo mu yi karatun tare"

Wata Hamma ta kara kwace min cikin kasala nace"Amir nagaji wlh ka bari gobe"Amir ya ware ido yana fadin"Umma yanzu kin daina karatu fa?kila ma kin manta na baya"

Nace"in ji wa..?ban manta ba kawai Hidima ce ta sha kaina ammh zan dawo makarantar nan ayi hakuri dai yau mallam Amir"

Su Anum suka yi dariya ina tayasu yana daga kwance yace"Amir kai ne malamin Umman taku..?

Kafin yayi mgana fadi ba'a tambayeka ba ta mike ta isa garesa ta fara basa labarin Anum akwai shigen Surutu kamar wata aku,tana bashi Labari yana kallona yana mirmishi Lokaci daya yace"Kice Umma ta fara jin Turanci"

Anum ta kyalkyace da dariya tana fadin"Sosai Daada"

Gani ya yi ina mika bayana duk ya sake kawai sai ya mike yana ce ma Anum"Je ki ku cigaba karatun ku"

Sai ta koma wajen zamanta shi kuma sai ya taso da ina shirin mikewa ne sai naji mganarsa a kasa kasa daidai kunnena yana fadin"Naga duk kin gaji muje dakina na tayaki da Tausa, duk zasu sake kiji dadin jikin ki"

Ai ina jin haka na koma na zauna ina Kifta mai ido sai ya kuramin ido sai na zame masa kurma nace"E he..me kace..?mirmishi yayi kafin yace"Kinji ai me nace zaki iya tashi ne ko sai na Dagaki..?ya fada Lokaci d'aya yana dagamin gira sai na juya ina kallon yaran bakina sake shima sai ya kallesu hankalinsu baya kanmu alamun in tashi yayi min sai naki tashi sai kawai naga ya mike yana gyarawa ai ban san lokacin da na mike a guje na shige daki ba,tsayawa kawai yayi yana kallona yaran suka Dakata da karatun suna kallon sa Anum tayi farat tace"Daada me ya faru da Umma take gudu..?

Yana shafa kansa ya juyo yana fadin"ta gaji ne kafafunta sun sake, sai tayi gudu saboda su sauka''

Tana daga ido Lokaci daya tace"Exercise kenan Daada"

Yana zama kan kujera yace" yauwa my Anum"

Amir dai bai ce komai ba ammh sai Hararan Anum yake yi ta cika Kaudi da fadi ba'a tambayeta ba sai da ya mata mgana sannan ta daina damun Dadan nasu da mgana wanda ya shiga Zurfin Tunanin in fa ya tsaya biye ma Fa'iza to bazai samu daman gyara kurakuransa na baya ba, har sai nagaba sun zo sun iskeshi a ransa ya shiryamata wani wayau da bata isa wannan karon ta tsallake ba.

Da safe bani da masaniyar abun da ya kulla yara sun tafi makaranta Hafsah ma kusan tare suka fita Badariya na Daki bata fito ba, ni kuma na gama kaye kayen daki kafin na fita Tsakar gida sai na koma Daki ina lissafin kudin da suka Rage a hannuna na bama Hafsa kudi kafin ta fita zata shiga kasuwa ta siyo min aya da zobo na wajena bai wuce yau ba zai kare, sai kayan maggin gida da man girki da nace ta Siyo min ko ba da yawa ba. siyan kullum duk baka gane masa kayi ta ganin kudi na narkewa ka rasa ina suke zuwa.

Na dukufa ina kirga kudin Hannuna har ga Allah ban ji motsinsa ba sai kawai naji mganarsa yana fadin"Hajiya Fa'iza mai zobo da kunin Aya ana ta lissafi ne..?

Sai a lokacin na dago na gansa ya Coge a kofar shigowa dakin yana kallona yana min mirmishi,Sai nima na maida masa martanin mirmishin nasa ina fadin"Ka manta baka cike mai Turaren wuta da kwallacha ba"

Sai kawai ya karisa shigowa Dakin yana Fadin"sana'a goma da ashirin wai Fa'iza yaushe kika zama yar kasuwa haka..?

Dariya nayi ban yi mgana ba na zata zai zauna ne sai naga ya coge yana miko min hannu Lokaci daya yana fadin"A bani in taya kirgawa mana."

Kai na girgiza ina fadin"ina kudin suke balle ka tayani kirgawa? riban wannan satin ne duka duka dubu hudu ne da yan chanji"

Sai ya gyada kai yana fadin"Ina laifi ai motsi yafi labewa Allah dai ya kara Rufamana asiri"

Na amsa da Ameen ina kallonsa sai ya yarfa Hannu yana fadin"Na gaji da zama ne waje da'ya shine zan dan fita na mike kafa"

Sai na jinjina masa kai ina fadin"Ya kamata to a dawo lafiya"

Har ya kama hanya zai fice ni kuma na mike sai kawai ya juyo yana fadin"Fa'iza na manta"

Sai na juyo ina kallonsa Lokaci daya ina sauraransa kai tsaye yace"Taimakawa zaki yi ki shiga ki gyaramin Shimfid'ata da daki na duk yayi kura kafin na dawo"

Yadda yayi mganar ba wasa ne yasa kaina Tsaye nace"Shikenan za'a gyara in sha Allahu"

Sai kawai ya fice yana fadin"Allah yayi miki albarka FA'I TA.."

A fili na amsa da Ameen  har ga Allah a raina ban kawo wani abu ba Sai da na gyara Dakina da dakin yara,na falo daman na kimtsa shi,sai na shiga Dakin nasa na fara gyara masa,Tiolet na fara shiga na wanke na fito ina gyaran Daki na kakkabe Shimfid'a na gyara har ina sauya masa zanin gado naga nasa yayi datti sai na kudiri a raina zan hada da wankin yara na wanke masa da sauran kayansa da suka yi datti.

Ina cikin gyaran gado,ya shigo ban ji ko shigowarsa ba har ya samu nasaran rufe kofar damam abunka ga wanda ke da raunin ji,sannan gabad'aya hankalina yana ga abunda nake yi na duka ina saka zanin gadon jikin katifar na gama na mike kenan sai ji nayi an rumgumeni ta baya kam! Lokaci d'aya ana saki karfaffan ajiyar zuciya ni kuma har ga Allah na tsorata ban Zaci ganinsa ba gabana ya yanke ya fadi ras sai da kaina ya sara min jiri na neman kada ni, jinin jikina cak ya tsaya ya daina gudu ga shi ta baya ya rikeni sai na fara kokarin kwatan kaina ina fadin"Wa...ye..?

Cikin rawan murya hannayensa duka Biyu yasa ya zagaye cikina da karfin da na kasa motsi kawai sai na Dage iya karfina zan yi ihu zaraf ya juyo dani ina fuskartarsa Saboda yadda yaji ina zufa ne,ga haki Lokaci da'ya Fuskata ya tallabo da Hannayensa duka Biyu Lokaci d'aya yana fadin"Fa'iza..Fa'iza ni ne fa"

Sai da naji muryansa naji Numfashina na daidaita,Abun ka ga mai hawan jini abu kadan ke haye mana sai na sauke ajiyar zuciya ina kallonsa cikin mamaki shima kallona yake yi na bude baki nayi masa mgana cikin mamakin ganinsa kawai Dif!

Kamar an kawo wutar lantarki an Dauke haka naji Jikina ya amsa ya koma kuma ya saki Lokaci da'ya, sakamakon bakin Yaya ishaq da na tsinta dumu dumu acikin nawa bakin yanayin da ban san yadda zan kwantata muku ba.ni dai da Hankalina Yaya Ishaq bai taba sumbatata baki da baki ba,ban ki in muna cikin auratayya yana bukatar natsuwa yana yi shima ba cikin soyayya ba ko natsuwa ba. cikin Tilastawa da neman biyan bukatar sa.

Shiyasa sai na rude na gigice na fita daga Hayyacina ban kara Dimaucewa ba sai da naji Hannayensa na kara kaina ajikina da zafi zafi duk inda Hannunsa yakai a jikina sai ya taba,tsayuwa ce ta nemi gagaranmu sai kawai ya bini muka zube bisa Katifar da na gama gyara masa ya kasance ina kasansa shi kuma yana sama na,bazan iya fassara yanayin ba abu d'aya na sani yayi nasara motsa sha'awata da nayi shekaru da Binneta yayi nasaran yayyafa mata ruwa data Farfad'o batare da sanina ba,Doguwar rigar yadi ne ya jikina daga sama ya zage zif din yayi kasa da ita,ba san da wani lokaci hakan ya faru ba na dai san naji hannayensa suna kai da kawo saman kirjina sannan hancinsa na shinshino duka fatar jikina tare da Game numfashinsa da karamin Nishin dake fita da kofofin Hancina.

Na fita daga duniyar da muke ciko ko nace ya taimaka wajen fitar dani daga Hayycina har yayi nasaran raba ni da Rigar jikina hannayensa dumu dumu acikin maraata,Fatar jikinsa tana gogar fatar jikina numfashi na ya sarke sai wani Uhmm...!

Kawai nake saki,wani irin tafiya ya dinga yi dani tafiyar da tunda nake bantaba sanin ana iya kai macen wannan bangaran ba,Ban kawo ma kaina abunda yake shirin faruwa dani ba sai da naji bakon al'amarin da bayan shudewar mintina Arba'in yana kokarin kwace natsuwata kamar almara naji wani bakon al'amari na kokarin Ratsani Ratsawar da na manta ya yanayinta,kansa na tsakanin wuyana cikin Shakar Nunfashi naji yana karanto addu'ar da sai in zaka kadaice da matarka kake karantata kamar irin an buga kaina Gaf!yayi gaba sai yayi baya sai naji ni Tsamo Tsamo na dawo duniyar da ya tafi ni ina Dago idanuwana da suka yi min nauyi na kallesa a saman kaina daga ni har shi mun rasa suturun jikinmu,shi kokarinsa ya kai ga inda yayi alkawarin jinginewa na har abada ai kamar an sako min wani karfi bansan Lokacin da nayi wani yunkuri d'aya ba sai ga shi na barar da shi a gefena har keyarsa na bugun bangon Dakin na tabbata ba karfina ba ne Ya riga yayi laushin da bazai iya moran ma kansa wani abu ba.

Kafin ya dawo hayyacinsa nayi gefe ina Raruman kayan na,daga inda na turesa ya Dafe keyarsa dishi dishi yake ganina Tsabar Halin da yake ciki cikin muryan da ta shige ba'a ko jinta ya kira sunana"Faaaa...izaaaa"

Naji dai jan sunan nawa ammh ban tsaya bin ta kansa ba,na rarumi zanin Gadon da na cire zan wanke na nade jikina da shi ba inda jikina baya rawa,kuka kawai naji ya Sarkeni kawai sai na fashe da kuka har da Shessheka.

Da rarrafe da jan jiki ya kariso gabana sai ji nayi ya rikoni nayi saurin kwace kaina cikin ihu nace"kada ka sake ka tab'ani..'

Kada ka sake..".

Na fad'a cikin ihu lokaci d'aya da kuka sai ya kasa kara tabanin ya koma gefe yana kallona,da kafarsa ya ja gajerun wandonsa ya saka kaina na maida kasa ina kuka,kamar ana dawomin da komai haka abubuwan da suka wuce suka rika dawomin na Dade bana fama da Kuncin zuciya tunda Allah ya samamin mafita ammh yau sai naji kamar komai anan yake faruwa kirjina yayi nauyi bakinciki ya cikani da na kasa sarrafa kaina agabana ya Durkusa kamar jaririn dake neman nono wajen uwarsa,yana shirin kara tabani nayi gefe da sauri ina kara rike zanin gadon dake hannuna gudun kada ya rabu da jikina,Sai ya Daga hannu cikin kasala da sanyin jiki,idanuwansa sun sauya Launi Jijiyoyin kansa sun mike gabad'aya cikin alamun Sararawa yace"Na bari naji bazan taba ki ba,ammh kiyi ma girman Allah ki bar kukan nan ki tsaya muyi mgana Fa'iza"

Sai a lokacin na dawo hayyacina na Fahinmci gadar zare ya hadamin Allah na sona da Rahma da na Rufta acikin shirinsa da na shiga uku. 

 Bani kuma da sauran mgana burina da na dad'e dashi acikin raina zai mutu batare da na cika sa ba.

Rokona ya cigaba da yi ganin naki daina kuka ganin yana magiya kamar zai yi kuka yasa na saurara da kuka na, sai dai ban daina jan Numfashi ina Jan majina ba,zaman dirshan yayi a gabana cikin wata irin muryan da bazaka taba cewa Ishaq kabir karofi gaye dan kwalisa ne ya mallaketa ba murya ce da zata iya kasaara jikin ko wacce d'iya mace mai lafiya in dai ta jisa da muryan ya fara mgana cikin karyayan sautin da ni kadai zan jisa yace"Haba Fa'iza haba fa'iza meyasa..?kin san halin da kika sani Tsawon wannan lokacin..?ki dubeni kiga yadda na koma a gabanki don Allah ki kara bani dama na gyara kuskurena na yarda na amince ni mai laifi ne ammh kada ki horani ta wannan bangaran na amince ki min duk abunda kika ga dama,ammh ba ta wannan bangaran ba ki bari na samu natsuwa daga gareki koma menene sai ya biyo baya.."

Sai da ya Dire mganarsa na Dago jajayen idanuwana na wurgasa masa wani harara da mamakin jin kalamansa na karshe,cikin karya wuya yace"Don Allah Fa'iza.."

Har da kokarin sake rikoni na ko kara matsawa baya shima yana kara matsaoni da karfi nace"Ka na matsowa wlh zan yi maka ihun kwarto wlh"

Cak ko ya tsaya yana kallona cikin mamaki yace"Kwarto fa,kwarto fa Fa'iza..?

Kai tsaye ina kuka nace"Eh Kwarto nace. kuma ka kara matsowa kusa da ni kasha mamakina"

Sai ya koma gefe na ya zauna yayi Tagumi kamar wani maraya Lokaci daya yana fadin"Ina cikin wani Hali don Allah Fa'iza ki bar ni na samu natsuwa daga wajen ki don Darajan don Allah Fa'iza ki ji tausayina"

Banza nayi da shi ina ta sharan hawaye ya kara kwaso magiya har ya gama ban ce masa komai ba, sai ya matso kusa dani na zaro mai ido sai ya koma da baya hannunsa a sama yana fadin"Wlh bazan taba ki ba..ammh in kika min haka kin min adalci kenan Fa'iza.?zina kike so naje nayi ko kuma kina so na fad'a wata Halakan ne..?

Idanuwana suna fitar da kwalla na Dago ina kallonsa cikin Muryata nace"Adalci ka ke mganar ban yi maka ba..?kai kasan menene adalci kuwa..?kuma  da kake mganar ka da ka fad'a zina ko halaka, au sai yanzu kasan Ana iya fad'awa wannan halakar.?ammh baka taba Tunanin matar daka jingine Shekaru Biyar baka taba waiwayanta da sunan bata hakkinta na aure ba.Ita baka taba Tunanin wata Halaka zata fad'a ba..?ko ita ba Mutum bace..?ko ita bazata iya fadawa zinar ba ne..?

Na fada cikin wani yanayi Lokaci kamar alokacin yake fadamin ya zabi Zainab sama dani sannan ya jingine aurena fiye da shekaru biyar ammh Saboda Namiji bai da kunya har zai iya nema na da wani abu..?

Wani irin kallo nake bin sa da shi kallon tarin takaicinsa da bakincikin da yayi shekaru yana kunsamin Hawaye suna kwarnya a saman fuskata.

 Kansa ya dafe cikin wani yanayi lokaci d'aya yana fadin"Na sani..nasan ni me laifi ne Fa'iza kiyi hakuri ki yafemin nasan nayi miki tarin laifukan da bazasu yafu lokaci d'aya ba, ammh ki duba ki gani wlh nayi nadama nayi nadama ki bani dama na gyara kuskurena"

Cikin kuka nace"Ina nadaman da kayi..?yaushe ka fahimci Fa'iza mutum ce kuma macece kamar zainab..?

Sai ya kasa mgana ya fara mgana cikin kame kame yana fadin"Tun tuni Fa'iza,Wlh tuni na gane kuskurena.

nayi nadama kema kin sani"

Kai tsaye nace"Babu abunda na sani.Abu d'aya na sani cewa baka sona baka taba kaunata ba.ka zauna dani ne saboda Baba..ka ce bani da amfani kace ni ba matar kwarai bace, ni ba matar rufin asiri  ba ce kace ni  Fa'iza ban dace dakai ba,Alfarma kake yi min,ka manta ka sha fad'amin baka Daukeni a bakin komai ba..?ka manta da kanka ka kirani ka nemi alfarman na barka ka yi rayuwar aure da Zainab ni kuma ka jingine aurena ba.?ko ba kai ba ne ka zabi wata macen sama dani ba?meyasa sai yanzu kake tsammanin komai zai zo maka da sauki..?.

Na karishe fad'a ina tsiyayan hawaye,wani Turiri da hayaki na fitowa daga kasan raina,Hannuwana ya riko jikinsa na rawa yace"Na sani ki bar tuna baya wlh a wanchan Lokacin bansa me ya shiga kaina ba ne,Ammh wlh na dawo hayyacina na gane kuskurena na fahimci sakacina da laifina na fahimci sakacin da nayi Wlh na tuba na tuba..nabi Allah na biki Fa'iza na dade da sanin kin fiyemin kowacce mace amfani a Rayuwata kuma na dade da sanin nayi kuskuran furta kalaman jingianan auran mu fa'iza,ki bani Dama mu sake gyara rayuwar auran mu a karo na biyu don Allah Fa'iza.."

Yafad'a lokaci d'aya yana jimke hannuwana cikin nasa sai kawai nayi Dariya lokaci d'aya da kuka kamar Mahaukaciya kafin nace"Fa'iza ce fa,kurma diyar Bebiya,Baka mummuna,Mara ilimin boko,mara gata mara kyau da nasaba,macen da bata chanchanci namiji kamar Ishaq kabir karofi ya so ta ba.Ni ce fa Fa'iza yar gargajiya nan,ina nan ban sauya ba.Ni ce dai wacce ka ke ciyar dani Saboda ina zaman kula da ya'yan ka, Fa'izan ne da ka ke tafiya wajen wata macen kafi wata biyu baka kirata a waya kaji yaya lafiyanta ba, Fa'izan da da bata san komai ba, sai ibadar aure da kula da ya'yanta da aka bar mata amanar su Fa'izan da ka rabata da kowa nata ciki har da mahaifiyarta marainiya da bata dukan wani gata, bata da uba bata da wani babban yayan da zai Tsaya ma rayuwarta ita ce dai wannan Fa'izan da Mama da Anty Binta suka maida abar wulakantawan su da cin mutumcin su, wannan fa Fa'izan da baka san ganinta Fa'izan nan ce da kake jin kunyar nuna ta amatsayin matarka, ita ce wacce kake jin kunyar duniya taga ya'yan da kuka Haifa tare ita wannan Fa'izan bata d"

Ban karisa ba ya rufemin baki da Hannunsa ina kuka,hawaye jage jage,da majina shima idanuwansa Jajir kamar zai yi kuka yace"Fa'iza ki bar tuna baya..Na rantse da zatin Allah na gane kuskure na,Wlh kin fiyemin kowacce mace a wajena yanzu.Ki yi min aikin gafara ki yafemin laifuka na nayi miki alkawarin zamowa mijin da baki taba jin Labarin kamarsa ba'

Don Allah Fa'iza ki yi hakuri"

Kauda kai nayi kada kalamansa su sakani rauni cikin shakewar murya nace"Saboda yanzu ka rasa komai yasa nake da amfani a wajen ka..?

Da Sauri yace"Wlh Talllahi ba haka ba ne. Allah ne ya dubeni da idon Rahma..Ya ganar da ni da wuri ba sai na mutu kasa ta kasa karb'ana Saboda bazan zamo adali gareki ba,Wlh Fa'iza in baki yafe min ba to Baba ma dake chan kabarinsa bazai taba yafemin ba"

Kiran sunan Baba da yayi sai rauni ya kamani cikin kuka nace"Allah sarki bawan Allah mai son zumunci da son ya'yan yan'uwa. Allah ya jikan baba da Rahma"

Da rawan jiki ya amsa da ameen Lokaci d'aya yana fadin"Ki yafe min Fa'iza ko don darajan Baba.Ki yafemin ki kuma bama Rayuwar auran mu Dama ta biyu don Allah.."

Sai kawai na kallesa ina fadin"Ta ya ya zaka Zauna da wacce baka taba so ba..?

Da Sauri ya Rumgumeni yana fadin"Wlh INA SON KI FA'IZA..wlh ina sonki"







*Janafty*

[7/17, 7:32 PM] +234 703 465 7829: *KNKB2011*


*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*

*09069067488*


Kalaman Ina sonki Fa'iza. Sun shiga jikina sun kusa kassarani sai nayi masa kuri da ido kawai,bawai don na yarda da mganarsa ba,Ba kuma don na taba rikesa a raina ba,so nake ya kyaleni yasa na yi saurin cewa"To ka sakeni mana"kara kamkameni yayi yana fad'in"Sai kin ce kin yafe min. kuma kin amince ki bama rayuwar auran mu Dama ta biyu"

Cikin Sarkewan numfashi nace"Na yafe maka ban taba rike ka a raina ba Yaya Ishaq,a komai in kayi min bana ganin laifinka. alfarman da kayi min da kake zaune dani baka taba korana ba,shima wani abu ne,na yafe maka duniya da Lahira"

Sai kawai ya kara kamkameni yana Dariya cikin farinciki yake fad'in"Thank you so much Fa'iza.Na gode nagode.."

Lokaci d'aya yana sumbatar bakina nayi saurin kwace jikina ina fadin"Na yafe maka ammh kuma ina da Sharad'i na"

Sai jikinsa yayi sanyi ya koma yayi min kuri,yana kallona bakin sa na rawa yace"Me ne sharad'in Fa'iza.?

Yana bani mamaki sunan Fa'iza a bakinsa kamar shi ya rad'amin.

Ina kallon cikin idanuwansa nace"Na yafe maka duka abubuwan da kayi min. Sai dai indan har kana so na kara bama auranmu wata Dama, sai dai kayi min alkwarin bani Lokaci har zuwa sanda naga dama sai nayi maka mgana"

kamar ya had'iye wani abu sai da naji karan miyan da ya wuce ta makogwaronsa mukut.

Ban damu ba, na cigaba da fadin"in kuma  ka matsa min to zan fasa yafe maka.sannan kuma bazan iya cika muradinka na bama auran mu wata Damar ba"

Da Sauri yace"Aa to to na amince.ammh Fa'iza har zuwa wani lokaci?kada ki dauki Lokaci kinga fa Halin da nake ciki..?

Kai Tsaye nace"Ba ruwnka da Lokacin da zan d'auka  alkawari shine kada ka takuramin in kuma ka takuramin zan fasa gudirina"

Da Sauri yace"To bazan takura miki ba"

Yafad'a harda daga hannu,Hawayena na Share ina kara rike zanin gadon hannuna kada ya subucemin,a marairaice ya kalleni kafin yace"Fa'iza ki yi ma girman Allah ki barni na rumgumeki ko na samu saukin abunda nake ji"

Ido na sakarmai cikin mamakin kalamansa kafin na daure fuska nace"Sai yau ne ka fara shiga wani Halin Saboda ni ko yanzu ka fara di'n..? Ban basa damar mgana ba nacigaba da fadin"kuma kada ka fara karya alkawarin ka,nima zan karya nawa"

Da Sauri ya matsa baya yana fadin"Na bari.Wlh na bari bazan kara tab'aki ba,sai kin ce na tabakin"

Sai ya kusa bani Dariya sai da na murmusa,kokarin mikewa nake yi ya mike zai riko zanin gadon na balla masa Harara da Sauri ya juya yana Raruman kayana ya mikomin yana fadin"Dama..dama kayan ki zan d'auko miki"

Ban yi musu ba nasaka hannu na karba,da sauri ya bani Hanya yana fadin"Ranki ya dad'e ki huce lafiya".

Ban tankasa ba na fara tafiya ina Tattare zanin gado yabi ni da kallo har na fice ya koma ya zauna saman katifar yaraf kamar an sauke kayan wanki kansa ya dafe yana fadin"Allah na tuba..Allah ka yafemin..Ya Allah ka lallashi zuciyar Fa'iza ta sake bama auran mu wata damar"

Ban kara ganinsa ba,tunda na koma dakina naci kukana sai da na koshi sannan naje nayi wankar Tsarki na Tsabtace jikina, ranar ko Kunin aya ban yi ba zobo kawai na Dafa,Shima Daki ya yini sallah kawai ke fitar dashi ,sai da Hafsah ta dawo ta kai nikan kunin ayan,abinci kad'ai nayi mana sai gyaran gida,ko da Daddare kwanciyata nayi a daki ban fito karatun dare ba, Anum tazo na korata bace bani da lafiya ba jimawa sai ga shi ya shigo har gadon ya zauna yana Taba goshina da Sauri na jaye kaina ina bata rai da wata murya yace"To taba goshi ma sai ya zama laifi..?

Saurin matsawa nayi ina fadin"Ai a shari'a ma yanzu kai ba mijina ba ne,in nace bazan zauna dakai ba,ba wanda zai matsamin na zauna dakai"

Ina gani jikinsa yayi sanyi cikin wani yanayi yace"Fa'iza wata shari'ar ce ta ce haka..?

Kai tsaye nace"Baka sani ba..?ai musulunci yace Haramun ne ka yi wata Hudu baka kusanci matarka ba. Sannan jinginan aure a musulunci kamar sakin aure ne"

Kafin na karisa yayi saurin tareni da fad'in"Ba saki ba ne Fa'iza wlh ban sake ki ba. kuma har abada kinsan auran mu ba saki in sha Allahu"

Ina jinsa ban tankasa ba na koma na kwanta shi kuma sai ya mike yana fadin"Da alamu dai lafiyan ki lau yau laifina ya shafi ya'yan Umma kenan..?.

Baya na juyamai ban kara masa mgana ba ina jinsa har yana gyaramin bargo ya fice yana fadin"a huta lafiya Fa'in Ishaq"

Tun daga ranar bai kara matsamin ba da ya fara na d'ago na ballamai harara sai ya koma gefe yace"Yi hakuri".

Ko Allah ya baki hakuri,Daganan sai na samu lafiyansa,ko bakomai na daina fargaban zai ritsani ko zai mamayeni irin na ranar,ammh duk da haka ina taka tsantsan da shi Saboda naga da gasken yake yayi nadama,kuma na karb'i nadamarsa ammh ba domin zan iya karban bukatansa na sake basa wata damar ba.

Mama ta dawo bayan tayi kwarari wajen wata biyar a yamai, yan'uwan ma sun so tayi zamanta achan ne Mama taki sana'o'i suka dinga yi a chan ita da Anty Hure kuma sun had'a mata yan kudade kafin ta dawo da su aka samu aka biya kudin makarantan yara,aka siyan kayan abinci tunda yan kudad'en hannuna mun cinyesu wajen siyan abinci sannan ya turama Jamal shima wani abun,Ga Badariya itama suna shirin zuwa bautar kasa ne ita laluranta kad'an ne babban abu shine kud'in haya da kud'in makarantar Jamal tunda shi ajin karshe zai shiga ya maimaita aji hud'u,yana karatun Software enginearing ne.

Kudin Hayan nan da shi nake kwana araina,kud'i ba yan kad'an ba wajen dubu Dari hudu ne wannan gidan,Shi kan shi ya damu tunda mai gidan ya fara mganar kudinsa tun watan daya gabata sai ya bashi hakuri yace ya karamai Lokacin,mai gidan daman ba shi da kansa ba ne,Komai na Hannun babban d'ansa ne,kuma ba wani kirki da ya cika ba,Don ma yana ganin mutumcin Yaya Ishaq da Tuni ya fara yi mana sallama.

Zagayowar wannan shekaran sai dai Godiyar Allah jamal ma gida ya Dawo,Anty Binta kuma da an yi mgana sai tace tana da biki a gabanta,bata da kudi shi bai ma nemanta,Mama ce ta kan kirata a waya tana fad'a mata sai ta fara korafin itama akwai hidima agabanta,Abuja ma yanzu sai yafi wata bai je ba,Ita Zainab din ne ma,takan turo masa kudin ya tafi yayi sati ko kwana goma ya dawo nima ta kan kirani lokaci bayan Lokaci mu gaisa auran nasu har mamaki yake bani kamar Dole,to ita tana son mijinta kuma mahaifinta yasan haka, shiyasa bazai yarda auran ya lalace ba shima Ai yana son matarsa da baya sonta da Tuni ysan mafitarsa.

Tun mai gidan nan na d'aga mana kafa,har yazo ya daina Sauraran ban hakurin Ishaq ranar da Safe yayi mana Dirar makiya Allah yasa yara suna makaranta da abun bai yi dad'i ba,Da kakkausan murya ya ce mana ya bamu nan da sati daya in bamu biya ko rabi ba sai dai mu bar gidan. Hankalin mu ya tashi bamu ijiye ba,ba kuma mu ba wani ajiya ba.

Yaya ishaq ko barcin kirki ba yayi duk ya bushe a tsaye gashi yana ganin Jamal a gida shima ba kudin abinci da pocket money ballatana ya koma makaranta har shi da kansa yayi ma Anty Binta mgana tace bata da kudi ta shiga adashe ne,ni kuma jarin hannuna duk yayi kasa sai na Bukatun cikin gida.

Mama ma duk hankalinta ya tashi,Mama a baya datake yar gayu yanzu wahala duk yasa ta tsufa kamar ba ita ba,Sai dai ya shiga D'aki yana Tufka yana warwara ba mafita Hafsah mganar kudin makarantar Jamal ta sani shi kadai takai labarin Karofi wajen Goggo,sai ga shi ta kira Jamal yaje wajenta ita da ya'yanta sun had'amai dubu sittin tace ya biya kudin makaranta,bayan ta hadamai kayan abinci,haka yazo mana da kayan arziki Mama sai kunya ya kamata har da kuka sai gashi ta Biyoni har daki tana cemin"Fa'iza ke kika yi ma Goggon taku mganar jamal hala..?

Ina zaune nace"Aa Mama inajin Hafsah ne da taje wannan satin"

Sai mama ta kasa mgana ta fita ta koma Dakinta abun mamaki sai ga Mama da shiryawa ta tafi karofi yima Goggo Godiya sai da ta kwana Biyu ta Dawo tana fad'in irin alherin Goggo da ya'yanta a raina nace da ba Hajiyar Dala ce kad'ai yar'uwar mijin ki ba,ashe kin san da Goggon,Hajiyar Dala da take ganin tana tare da ita ko jinta ma ba'a yi.

Yanzu naga Mama ta daina Takura min,ba kamar baya ba. Kuma bata shiga harkata,  naga ma alamun Ta koma wata shuru shuru a d'aki kamar bata nan,Aranar da satin d'ayan da mai gidan ya bamu,zai cika kasa barci muka yi,a daran ranar har ce ma Yaya Ishaq nayi"Me zai hana ka yi ma zainab mgana ko akwai taimakon da zatayi maka ta bangaran su..?

Kai Tsaye yace"Aa bazan roki kowa ba Fa'iza ai susan ina bukata kuma basu Dauko sun bani ba. In sun bani zan karba in basu bani ba, bazan taba rokan su ba"

Sai ya bani Tsausayi daganan ban kara masa mgana ba, sanin da nayi tunda yace bazai yi mgana to bazai yin ba,Da Sassafe bayan ya raka su Amir makaranta gidan Anty Binta ya tafi,yana chan bai dawo ba sai ga yaron megidan da wasu matasa majiya karfi har gidan suka shigo Hafsa na makaranta Badariya ke gida tunda sunanta bai fito a bath A ba.

Tijara ya fara yima sannan yace watsi zai saka ayi mana da kaya,Mama ta fito nima na fito ni ke basa Hakuri Mama ko cikin gadara tace"Ka dad'e baka sa an yi mana watsi da kaya ba, ban da yanayin rayuwa kai har ka isa ka wulakantamu. shekaran da ta wuce kai baka isa kazo kana mana barzanar banza ba,rayuwa ce ta maida mu haka"

Ta fad'a cikin baci rai,ido cikin ido ya kalleta kafin yace"Tsohuwa ina daraja Furfuranki ammh ke baki gani ba ko..?

Kai Tsaye Mama tace"in kana Daraja Tsufana ai da baka tsaya ina fad'a kana fad'a ba"

Kai tsaye yace"Gidan nan ai ba na tsoho ba ne ko?to in dai bana Tsoho ba ne sai kin fita daga gidan nan,yau na zata abun naku na mutumci ne. kuma Darajan d'anki kikaci wlh da yau sai kin raina kanki ina ruwana da rayuwarki a baya  wama ya sani ko a lokacin baya d'in da kike da arzikin ba alheri kika shuka ba tsiya ce shiyasa kika ga karshen ki?

Ai sai Mama ta saka kuka tana fadi'n yayi mata rashin kunya na riketa ina fadin"Haba Mama ba girman ki ba ne ki Tsaya kina tanka tanka da shi"

Sai mama ta kasa mgana nan na saka Badariya ta shiga da ita ciki D'aki sai kuka take yi.

Wani Lokacin masu gidajen haya kalilan ke da burb'ishin mutumci saboda nasan bamu da gaskiya Kuma a maganar Gaskiya Mama ta zak'e da yawa ne shiyasa.

Hakuri na rika basa ina fadin"Kayi hakuri don Allah ,ya fita ne ya dawo yanzu zai shigo"

Kai tsaye ya kalleni ba wani babba ba ne, bazai wuce sa'an Yaya Ishaq d'in ba kawai dai irin ya'yan masu kudi'n nan ne, kallo na yayi yana fadin"wanchan tsohuwar ai ta bata komai Hajiya.Kai ashiru ku shiga ku fara fito musu da kayan su waje"

Sai na durkushe a gabansa na had'a hannayena ina fadin"Kayi wa girman Allah kayi hakuri.In kayi mana watsi da kaya ka tona mana asiri ina zamu..?ka da ka manta mu musulmai ne kuma duk inda musulmi yake dan'uwan musulmi ne,In ka rufamana asiri ka suturtamu sai kai ma Allah ya Suturtata taka ranar gobe kiyama. kayi hakuri don Allah zamu biya ku kudi'n ku da zarar mun samu"

Na fad'a cikin magiya sai kawai ya Tsaya yana kallona cikin Tausayi kafin ya ce na mike sai na mike ammh ban sauke hannayena ba cikin Tattausan murya yace"bakomai naji rokon ki na yi muku lamani ku zauna ammh kuyi adalci ku biya da zarar kun samu"

Da sauri nace"Wlh zamu biya.In sha Allahu"

Daga haka ya gyad'a kai ya yi ma samarin mgana suka fita tare  ajiyar zuciya na sauke, na koma kan kofa na zauna ina kuka ahaka Yaya Ishaq ya shigo futu futu kafafunsa, dani ya fara cin karo ina kuka cikin tashin Hankali yace"Kuka Fa'iza me ke faruwa..?

Ya fad'a yana zama kusa da ni da Sauri na Share hawayena ina kallonsa Daga sama har kasa ganin yadda yayi Futu futu kamar wanda yayi tafiyar kasa cikin mamaki nace"A kasa ka tako..?

Bai bani amsa ba ya kara fadin"Me ya faru ne..?

Sai nayi masa shuru yana shirin kara mgana ba sai ga Badariya ta fito ita ya tambaya ta maida masa yadda akayi har yadda na duka ina rokon su sannan ya amince ya d'aga mana kafa cikin d'aga murya ya kalleni yana fad'amin"kika duka mai Fa'iza..?kika dukamai fa..?

Saboda wani dalili..?

Yafad'a cikin bacin rai sai kawai na mike ina fadin"Ba dukawa bace roko ne da neman alfarma, in ban duka ba da yanzu kazo ka ganmu a kofar gida an fara yi mana watsi da kaya"

Daga haka na shige daki sai kawai ya bini da kallo ga takaicin yaje bai samu Anty Binta ba, sun fita da mijinta a kasa ya tako tunda batagwarawa har Ajiwa,sai kuma yazo ya iske wannan tashin Hankali D'akin mama ya shiga ya isketa tana kuka dakyar ya Lallasheta tayi shuru tana fadi'n wai mai gidan ya zageta yasan halin Mama shiyasa ya kalleta yana fad'in"Mama bafa kowa ya ke da ragowa ga manya irin ku ba. Sannan kema Mama me ya kaiki sa'in sa da shi.?mu ne fa bamu da gaskiya hakkinsu ne a kanmu bamu biya ba kuma sun yi mana Hallaci bai kamata ki nemi zaginsa ba"

Ganin ya rufeta da fad'a yasa ta sauya mganar da cewa"Ka samu Bintan? ya kuka yi..?

Kai tsaye yace"Bata nan sun fita da megidanta a kasa na dawo duk nagaji"

Mama ta yi tagumi kafin tace"Allah ya warware mana ko zakayi ma Zainab mganar ne..?

Da Sauri yace"Aa Mama Allah zai kawo wata hanyar"

Sai bata kara mganar ba,sanin halinsa Tunda yace a'a to bazai kara bi ta kanta ba,Batare da sanin kowa ba, ta Kira Zainab ta fada mata komai ita Zainab d'in ne ta kirani tana fadin"Haba Maman Amir sai ki boyemin wannan abu haka..?

Sai nayi mamakin a ina taji nadai san bashi ya fad'a mata ba,sai da naji tana fadin Mama ta kirata ta fad'amata sannan nayi mata bayani sai tace bari ta kirasa to bansan ya suka kaya tsakanin su ba, ta dai turo masa kudin kuma ya biya mana kudin Hayan ranar da ya Tura ma mutumin kudin har sai da yace mai"Gaskiya kayi sa'an mata mai hankali da iya mgana."

Da ko ya dawo gida tasani yayi agaba da masifa da fad'a wai na fito ina ma wani gardi magiya kallonsa kawai nayi kafin nace"Yaushe ka fara kishin Fa'iza..?

Kai tsaye yace"Ke Fa'iza ki fita daga idona. ko a baya bana barin ki sakakaka.nasan abunda nake yi kada ki kara batamin  rai da mganganun ki na banza"

Daga haka ya barmin wajen yana ta masifa a raina nace topah Sabon Salo Tusa a lasifika.

Hankalin mu ya kwanta tunda Allah ya Rufa mana asirin duka,Badariya Sunanta ya fito a Bach B, an tura ta Camp yola Raliya kuma Abuja suka barta,Hajiyar su Raliya ta bata kudin mota da kudin kashewa na har ta dawo,Hajiya ta Dauke mana wannan nauyin ta tafi da tarin nasihan yayanta da mama akan ta kula da kanta,Sati uku tayi ta dawo gida,Sai kuma cuku cukun yadda zata dawo kusa gida tayi bautar kasarta.

Haka muka cigaba da Rayuwa yau fari gobe Tsumma Goggo na lekomu ita da su Anty Nasara nima nakan lekasu,Makota na su Sa'adatu basu manta dani ba,Nima ban manta da su ba, ina leka su wani Lokacin sana'ata ne baya barina fita har kuma yau Yaya mariya bata kara takowa gidana ba.sai dai mu yi mgana da ita ta waya.

Hajiyar Dala ko ba wanda ya kara jinta ko garin ta shigo bata zuwa Anty Binta kuma ta maida hankalinta wajen Shirin Bikin Halisa daya rage Saura wattani bata cika zuwa ba ma.

Ina zuwa gidan Hajiya gaisheta Lokaci bayan Lokaci anan ne har tace Yaya Ishaq ya kawo takardunsa daga barayinta tagani ko za'a dace da murnanta nazo nayi mai magana sai kawai ya kalleni kafin yace"Ina fatan ba zuwa kika yi kikace kina so ta nema min aiki ba..?.

Wani Haushi ya bani, ba ka da ko sisi sai shegen girman kai hararansa nayi ina fadi'n"Sanarwa na bada a masallaci baka ji ba..?

Sai ya maida abun wasa ya taso zai rikeni na matsa baya kafin nayi mgana yayi saurin tareni da fadin"Kai na bisa wuya afuwan na manta ne"

Sai kuma ya bani Tausayi yadda yayi mganar,ni da kaina naje na kai ma Hajiya Takardunsa,a amsa da yakinin acigaba da addu'a za'a dace.

Ana cikin haka Badariya ta samu aka ijiyeta kano inda zatayi bautar kasarsta sai Mama tace ta zauna gidan Hajiyar Dala Badariya tace bata son zama,Maman ta had'a ta da Yayan nata yayi mata fad'a Nima nayi mata nasiha sosai ina fadin"Kiyi hakuri kije ki zauna ke mace ce yafi ki zauna a inda baki sani ba,duk tsiya ke yarta ce bazata ce zata kore ki ba"

Da haka Badariya ta amince ta tattara kayanta ta tafi kano Bayan,Maman ta samu tayi mgana da Hajiyar Dala Anty Binta dai sama sama take da Badariyan acewarta ta mata rashin kirki,tunda abun da ya faru tsakaninta da Halisa da har yanzu ita da Badariyan basu koma Daidai ba, ba sa gaba suna mgana da juna,ammh sama sama.

Raliya kuma kaduna aka ijiyeta,Sai ta zauna gida kawar Hajiya gidan su Laila kenan.

Tafiyar Badariya ba jimawa sai ga waya daga Abuja akan wani kamfanin Sarrafa fattu da Mahaifin zainab ya taba kai takardunsa sun nemesa,Dole ni nayi murd'a murd'a na basa kudin mota ya tafi,bayan tafiyar sa mun yi mgana da shi sau d'aya ya samu sun yi interviuw sai jiran kiran su bai dawo ba ne saboda baya so bayan ya koma su sake kiransa,To yana zaman jiran kiran nasu ne,Zainab ta fara rashin Lafiya har da kwanciya a asibiti,Ashe ciki gareta da sauran rabo a Tsakaninsu.

Daya kirani ya fad'amin ne bayan suna asibitin da ita nace in ta farka ya bata waya na gaisheta sai dare ya samu ya Had'amu na gaisheta bai fadaminciki gareta ba, ita ce tace min"Maman Amir bakin ki dai ya amsu,zai zo miki da Farhan ki yaye min shi tunda Honey yaki bari na huta hakanan"

Daganan sai na d'ago mganarta nayi murna sosai da Fatan alheri da ta basa wayan nayi masa murnan karuwa sai kawai sai yayi yar  murya yana fad'in"Saura ke. kema na kusa har ba miki alluran.."

Da Sauri na katse wayar ina mamakin a gaban matarsa yake fadin hakan?a fili na murmusa,sannan acikin raina nace haihuwa ai na bar ma, matan so ba irin mu da rabo kan rantse ba.

Kamar cikin na bata wahala ne an dawo da ita gida kwana biyu jikin ya rikice sai da aka kara maidata ita asibitin shiyasa bai dawo ba,Kuma har yanzu basu kirasa ba kuma yace an kira Mutane biyun da suka je interview tare,ni dai na lallashe da cewa Allah ne mai yi kuma shi ke ba da aiki in alheri ne Allah ya basa in kuma ba alheri ba ne, Allah ya musanya masa da wanda yafi alheri.

Ya shafe kusan wata a Abuja ba yara ba ni kaina ina kewarsa kaji Fa'iza da Samun waje wai ina kewar mijin aro.?da Sauri na cire tunaninsa a raina na cigaba da Sabgan gabana ni nake rike da karfin gidan duk da muna da sauran kayan abinci, sannan daga Gidan Hajiya ma ta aiko mana da shi,Sannan na samu aikin yin Humra da kwallacha da kudin nake ta riritawa muna cefane da Hidiman yara..


******


Wata ranar asabar data kama kwanan Yaya Ishaq Talatin da hud'u da tafiya Abuja mun yi waya da shi a daran jiya har da yara suka gaishe da Antyn nasu tana gida an bata Bedrest,Da gaske yake da yace yayi kuskure kuma yayi nadama zai gyara kuskuransa,yana kokarin kirana in dai baya garin sannan zai ji ya gidan yake tafiya mganarsa kenan"Nagode Fa'iza Allah yayi miki albarka"

Safiyar ranar sai da na zane Musty sannan yaje Tahfezz da shirin sa bazai je ba,ya zauna yana min rigima na shiga jikinsa da Bulala,Daman tun jiya nake jin jikina ba dadi,da Safe kuma sai fama da sanyin jiki Hafsah ta shiga makaranta zasu su yi wani aiki ita da Sauran yan ajinsu tunda ta fita ina kwance afalo ban yi komai ba sai dai in masu siyan kunin aya da zobo sun yi sallama na mike na basu, Tunda jiya nayi da yammah shiyasa yau da Safe nace bazan yi ba sai da yammah.

Wayata na cikin Dakina na baro ta ana ta kirana ban ji ba,barci ne ya kwasheni nan saman kujera acikin barci sai na ganni a gari Dabam ba karofi ba kuma ba katsina ba,bakon wajen da mutanen da ban sani ba,Kamar kuma acikin barci naji ana kiran sunana a firgice na mike ina Salati sai naga Mama a saman kaina, na mike zaune ina raruman da'nkwalina da ya fad'i saboda barci lokaci d'aya  ina fadin"Mama.."

Kallona tayi cikin nazarina kafin tace"lafiyarki kuwa.?Isa tun dazu yazo yana  ta sallama baki ji ba..?

Sai gabana ya fad'i na zare ido ina fad'in"Wani Isan.?Yaya isa."

Kafin na karisa ya d'ago labule ya shigo a gaggauce yana fad'in"Fa'iza maza dauko hijabin ki Karofi zamu tafi yanzu"

Gabana ya fad'i ras! Cikin Dafe kirji nace"karofi..?me ya faru ne..?

Na fad'a ina wuce Mama zuwa gaban Yaya Isa itama Mama sai tabi bayana tana fadin"Isa lafiya kuwa.?

Cikin natsuwa yace"Lafiya lau kada ku damu.Goggo tace na dauko su ita da Hafsah akawai wanda zai gan su ne"

Dagani har Mama sai muka bisa da kallo zan yi mgana da sauri ya tare ni da cewa"Ki sako hijabi muje sauri ake yi Fa'iza"

Jikina na rawa na ruga daki na Dauko Hijabi na fito ina fad'in"Mama su Amir"

Da mamakina sai kawai tace"kuje ko taliya zan dafa musu,tunda akwai komai kafin ki dawo"

Sai kawai nabi bayan Yaya isa da gudu daya riga ya fice gabana na fad'i jikina na rawa a raina nace kodai Goggo ce..?da sauri nace"Aa ba haka ba ne"

A mota na same shi na bud'e gidan gaba na zauna cikin Sauri yace"na kira hafsa tana makaranta zamu biyu mu dauketa"

Sai kawai na Sadakar Mun rasa goggo,kawai sai ji yayi na fashe da kuka cikin kukan nake fadin"Allah Sarki Goggo"

Tsawa ya dakamin yana fadin"Wayace miki wani abu ya samu Goggon.?

Cikin hawaye nace"To me zai saka kazo da gaggawa ka daukemu zuwa karofi..?

Hankalinsa na wajen tuki yace"To ba mutuwa ba ne abun farinciki ne, Dan'uwan mahaifiyarku ce ya bayyana, shi da mahaifiyarsa yau a karofi"

Na ji dai kalmar dan'uwan mahaifiyarku a kunnena sai na Dafe kirji ina fadin"Ta madina..?

Kai ya gyad'amin yana fadin"Shifa..Sauri suke yi shiyasa Goggo ta tasoni daga gun aiki tace na dauko ki keda Hafsah"

Daganan ban kara bi ta kansa ba farinciki da wani irin zumud'i ya sarkeni hannuwana na da'ga sama ina fadin"Alhamdulillah..Allah abun godiya"

Har muka isa makarantan su Hafsah bakina yaki rufuwa a waya ya kirata ta fito a gaggauce itama kamar ni duk ta Rud'e sai da yayi mata bayanin da yayi min sannan itama ta rud'e da Murna tana fad'in"Yaya Isa ya ka gansa? yana kama da Tamadina..?

Mirmishi yayi yana fadin"Tsammanin abunda baku yi tsammanin ba. muje dai zaku gansa labari bazai gamsheku ba."





*Janafty* 


[7/17, 7:32 PM] +234 703 465 7829: *KNKB2012*


*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*

*09069067488*


Har muka isa karofi ban sani ba, na lula cikin wani irin farinciki da zakwad'i abun da ka dade kana hasashensa bai faru da wuri ba sai yanzu.

 Wani irin farinciki ne ace yau ga wani naka daka jima kana jin labarinsa baka taba ganinsa ba, kafin isar mu gidan Goggo a cikin zuciyata na wasaafa yadda zan ga Dan'uwan Tamadina bansan iyaka ba nadai san bakina yaki zama waje d'aya na kasa natsuwa har Hafsah tafini mallakan kanta.

Tunda Muka iso kofar gidan Goggo sai kuma jikina yayi sanyi maimakon na zama ta farkon shiga gidan sai na kasance ni ce ta karshe na koma na rab'e bayan Hafsah kamar wacce tayi karya, gabad'aya sai naji gabbaina sun saki na fara tunanin wani irin tarba ko maraba zai yi damu alhalin bai taba ganin mu ba? sannan meyasa ya kai wad'anan shekarun batare da ya waiwayemu ba?har sai da Allah ya Dauki ran Tamadina basu gana ba?

Ya ya zamu gansa..?mu ma ya ya zai gan mu..?yadda ya zata ko ba yadda yayi tsammani ba?

Duk wad'anan tunanin suka taimaka wajen da dakushe murnanta a fili har Yaya Isa yayi sallama kofar falon Goggo Ya shige Hafsah tabi bayansa nice karshen shiga falon, sannan sallamata ma a saman bakina ta makale idanuwana suka fara wurgawa cikin falon ina neman bakon fuska naga Goggo da megidanta,Sai Baba Ati da wasu Tsofaffi maza daga gidan su Tamadina ne,Sai wata Dattijuwa mai natsuwa da Haiba zaune kan kujera cikin shigar alfarma kallo d'aya zaka yi mata kasan ta samu dukkan gatan duniyan da suka Boye shekarunta.

Gefenta a kasa wajen kafafunta wani kamilin megidanci ne baki sai dai bakinsa ya hade da hutu da jin dad'i da Fatarsa ta sauya,yana Sanye da Shadda Mai ruwan kasa har da babban Riga tana maiko kansa da Hula zanna na mutanen maiduguri,yana duke ne ammh ina iya ganin yadda yake saka karamin farin kyale yana Tsane ruwan Hawayensa,Yaya mariya na gabansa itama a duke kamar kukan take yi, Dattijuwan nan ta rike mata hannu alamun lallashi.

Daga sama naji murya Goggo tana fadin"Alhamdulillah ga Fa'iza nan da Hafsatu nan sun iso.."

Kamar an zabure sa haka ya mike cikin Haibarsa da muryansa da ta dakeni yace"Ku matso nan ya'ya na ku matso naji dumin ku..Ku zo ga Abban ku"

 Yake fad'a cikin nuna tsananin murnansa sai alokacin na kara kallonsa ba shakka jini ba karya ba ne ina ganin kama ta jini Tsakaninsa da Tamadina Hafsat ne ta nufesa zata duka ta gaishesa sai kawai ya Rumgumeta,hawayensa na zuba ni kuma ya miko min hannu sai na sulale kasa a gabansa idanuwana sun ciko da kwalla,Dattijuwan nan ta kallemu ta kara kallon mu musamman ma ni sai kawai ta fashe da kuka tana fadin"Allahu akbar daga ganin wannan na shaida jinin Lauratu ne"

Sai kawai ta rikice tana rusa kuka Goggo ta matso tana fadin"Haba Hajiya zuwaira ashe kukan naki bazai isa hakan nan ba..?.

Cikin kukan take fadin"Dole nayi kuka, Dole na koka na yi sanadiyar da na yanke ganawa Tsakanin yan'uwan juna.?kaico na.."

Tafad'a cikin wani yanayi da sauri ya tareta da fadin"Inno ni ne kika yi ma wannan laifin kuma nace na yafe miki ba shikenan ba..? Ni dai naji ciwon rashin ganawa da yar'uwata guda d'aya da nake da shi,Ammh nayi murna daya kasance ta barmun zuru'an da bazan jima ina kuka ba, in na kallesa zan tuna yar'uwata ta bar min su ne domin kada in na zo nayi kukan rashinta"

Gabad'aya kalamansa sai suka sakani rauni bansan Lokacin da na fashe da kuka ba ganin haka yasa sai Hafsah ta d'auka Yaya mariya ma daman mun sameta tana kukan ta ne.Wacce aka kira da Inno ta sauko kasa tana neman Durkusa mana cikin kuka tace"Ku yi hakuri ku yafe min ya'yan nan na zalunce ku na yanke ganawa tsakanin mahaifyarku da dan'uwanta"

Da Sauri ya saki Hafsa bayan ya zaunar da ita ya karisa gareta ya rikota ya maida ta saman kujera yana fadin"Inno ki daina wannan kukan don girman Allah"

Sai ta ji mganarsa ta koma tayi shuru tana sharan kwallah kasa ya zauna a gabanta yana kallonmu d'aya bayan d'aya kamar yadda muke kallonsa. Lokaci da'ya yana Dauke Hawayensa da Farin hanky din dake hannunsa.

Cikin Kayattaciyar Muryansa ya dago yana kallon su Goggo kafin yace"Cikin su wacece tafi kama da yar'uwata..?

Har Baba ati da goggo suna had'a bakin wajen fad'in"Gata nan a gabanka Fa'iza kamar Tamadina ta tsaga kara yadda ka ganta haka mahaifiyarta take. sai dai ita bambamcin Tamadina bebiya ce ita kuma Fa'iza jinta ne yake da rauni"

Kawai sai ya kuramin ido Lokaci d'aya yana fadin"Naji dadi da akwai fuskar da zan rika ganin yar'uwata a ciki, baku da Hoton yar'uwata ku nuna min ya'yana..?.

Ni dai na kasa mgana Hafsah ce tayi karfin Halin cewa"Yaya Asiya na da shi a wajenta"da alamun karin bayani ya ke kallon mu Yaya mariya ta jinjina kai tana fadin"Itace babbarmu wacce su Goggo suka ce tana kano tana aure"

Sai ya jinjina kai yana fad'in"Rashin sani ne ai kano gida ce a wajena chan na girma nayi karatuna kuma chan nayi aure,kafin chanjin aiki ya Dawo dani nan kaduna,yanzu komai ya kare tunda Allah yasa nazo kuma na ganku nayi alkwarin bazan kara sakacin da zaku rasani ba"

Sai ya fara sharan kwallah ya cigaba da fadin"Yau yau din nan Inno ta fad'amin ina da yar'uwa bayan ta sanar dani inda dangin Babana suke,a gaggauce na taho ko iyalaina ban zo da su ba suna kano ana auran kanin Mai dakina,yaran duka suna chan,ni kaina Tafiya gareni zuwa porthercourt gobe akwai Taron da muke dashi daga wajen aikin mu aka turamu,ammh nace bazan zauna ba sai nazo na ga ahalina ina zuwa kuma sai na samu labarin dangi duk sun kare itama yar'uwan nawa Allah ya yanke ganawa tsakanin mu da ita"

Inno na sharan kwallah tace"Allah ya jikan Hafsatu ina kallon fuskarta ranar da zan bar garin Lokacin bata wuce shekara Biyar ba"

Aka amsa da Ameen Ameen mu dai sai kuka muke yi muna sharban hawaye Shi ma kukan yake tayamu ammh nasa bamai sauti ba ne,yana dai yi yana tsane hawayensa,da farin Hanky din dake Hannunsa..

Baba ati ta gyara zama tana fadin"Zuwaira wani dalili ne yasa tunda kika tafi baki kara waiwayomu ba sai yau.?Sannan wannan yaron baki taba sanar da shi komai game da mahaifinsa da Danginsa ba..?

Inno ta fara kuka kasa kasa tana fadin"Ba laifin Usman duka acikin abun da ya faru kada ku manta na bar garin nan yana da kananun shekarun da bazai iya tuna komai ba!

Duka abunda ya faru laifina ne shiyasa nace ku yafemin"

Hannayenta ya rike cikin Lallashi yana fadin"Inno ashe kukan nan ban ce ya isa haka ba..?

Da jajayen idanuwanta tace" USMAN rashin kuka na ba zai sa laifina yaki bayyana ba,da gaske na zalunceka na tafi dakai na raba ka da Dangin mahaifinka gashi karshen karshen sai da na kawo ka gare su"

Sai ya kasa mgana Saboda bata kiran sunansa sai dai tace mai BABAN Nana kamar yadda matarsa ke kiransa.

Gyara zama tayi tana kara gyara zaman mayafin dake kanta tace"Bani da wani kwakwaran Dalilin aikata abunda na aikata Sai dai nace rashin son da ban yi ma mahaifin Usman ba aka aura min shi,alokacin ina da wanda nake so ammh Mahaifina yayi min Dole,ya aura min shi aka kawo ni wannan garin kada ku manta tun Lokacin da aka kawo ni,ban yi zaman Dad'i da kowa hatta da kakarku da ta haifi mahaifiyarku Lauratu,Sannan ban saki jiki da kowa ba,bani da aiki sai kuka sai zama cikin Damuwa Ko Usman Rabo ne ya rantse tsakanina da mahaifinsa  aka same shi,ko da zama ya kare tsakanimu da shi bayan rasuwarsu zuciyata bata Rusuna ba. gani nake yi in na barsa a wajen ku bazaku barsa ya zauna dani ba, shiyasa tunda kuka amince na tafi da shi a raina nakudiri niyyar zan Nisanta shi da abunda ya shafi wannan nahiyar,Tsakaninsa da mahaifiyarku bai fi shekaru uku ba yana gabanta domin neman irin haihuwan yakai mallam ga aurena sai bayan na haifi Usman sannan Lauratu ta Haifi Hafsatu tabbas nasan an haifeta da laluran rashin ji da mgana,Sai dai bamu zauna da lauratu ba,Duk da mun yi zaman kishi na mutanen na wanchan lokacin,Ni ba kishi nayi da ita ba, ni tsanar duk abunda ya shafi mallan nayi shiyasa itama ban yi mu'amala mai kyau da ita ba,Ita kuma tayi kishi dani a matsayin wacce ta auran mata miji duka duka zamana ko shekara goma ban yi ba na bar karofi na koma karaye gidan mahaifina ba jimawa shima ya rasu.sai yayana ya Daukeni zuwa cikin Hukumar Dala ta kano inda yake zaune da iyalansa yana kasuwanci.

Shi ya rikeni ya rike Usman har ya zama abunda ya zama,A baya shi ba mai arziki ba ne,d'an kasuwa ne mai karamin karfi ammh daga baya ya samu arziki har mun koma cikin garin kano a anguwar mandawari da zama,A hannunsa Usman yayi karatu,tun bayan dawowarmu kano Usman na yawan son ya tuna yar'uwansa da Dangin mahaifinsa,Sai dai ina kokarin shafe Tunanin acikin ransa a hankali a hankali sai abun ya shafe a ransa,Da kuma girma ya kamasai sai dangina suka zame masa komai yaya na shi ya bashi auran Diyarsa Azizatu ya aura a shekarun baya har sun tara zuru'a a tsakanin su,Daga baya Usman ya so ya san wani abu kan Dangin mahaifinsa ni nayi masa iyaka da hakan nayi masa Kaushin muryan cewa in ya kara tambayata garin mahaifinsa ko abunda ya Dangance shi sai na Dagamai Nono, daga Lokacin Bai karamin mganar ba.sai naji dadin haka ammh a raina ina jin ba dadi kamar wani abu mai nauyi ya zauna a kirjina,har ga Allah kiyayyar mallam ce da na sakama raina ta Haifarmin da haka na dad'e ina mafarkai marasa kyau har barci bana samu a Lokacin Dalilin haka yasa na zauna sai nayi Tunanin wannan shine babban laifin dana aikata wanda Allah bazai yafe min ba,nayi mafarki da mallam yana fad'amin na ki had'a kan ya'yansa Allah bazai barni ba.yau da Safe na kira Usman na fad'amai komai a kansa sannan na shaida masa yana da yar'uwa a garin Korafi inda na Haifesa"

Ta karishe fad'a cikin kuka Lokaci daya tana fadin"Ku yafe min ya'yan nan wlh sharrin dokin zuciya"

Ba wanda ya iya mgana sai ajiyar zuciya na mutanen dake falon Mu ko sai kuka muke kamar yanzu akace Tamadina ta rasu,Baba ati ta gyara zama tana fadin"Ashhha.Shiyasa dokin zuciya ba dadi..Yanzu ina amfanin wannan..?lauratu dai da mallam Hashimu sun bar duniya itama Tamadina Allah ya karbi abunsa ba domin wad'anan yaran data bari ba da yau kin jefa d'anki cikin Damuwa saboda bazai ga wani abu daya Danganci yar'uwansa ba"

Goggo tace"Koma dai menene yanzu ya wuce daman chan Allah bai kaddara saduwa tsakaninshi da Tamadina ba,Mu yi hamdala tunda muna da sauran rayuwa.Ga ya'yanta nan data bari shiyasa nace a dauko su su ganka kaima ka gansu Asiya ce kadai bata nan saboda tana nesa"

Yana duke a gabanmu kansa na kasa yana sharan kwallah cikin Raunin murya ya dago yana fadin"Naji dad'i da na iske zuru'ar yar'uwata.ku kalleni nan daga yau ku masu gata ne.Bazaku kara kukan maraici ba"

Yaya mariya ta dago tana sharan kwallah Lokaci d'aya tana fadin"Kawu.."

Da Sauri yace"Ba sunana kawu ba. ABBA zaku rik'a kirana kamar yadda y'yana ke kirana.nayi shekaru da nauyin kirji ina tunanin akwai wani abun da ban isa garesa ba acikin wadanan shekarun ba,na samu wadatar Rayuwa da cigaba nayi karatun addini nayi na boko har matakin Masters,na fara aiki da Hukumar wutar lantarki na jahar kano. kafinMakotan su Baffa sanadiyar gidan kakanin megidana shi chairman ne na babban Headquater refinering and petrochemical,Limited Edo state,Sanadinsa na samu aiki a Nageria National petroleum corporation NNPC,na kaduna wato Kaduna Refinaring and petrochemical company,Nayi auri da Diyar Baffa Azizat,mun haifi yara Hudu babban su shine Abdul'Ahad ma'aikaci ne hukumar sadarwa ta layin Mtn,zai yi aure wattani kad'an masu zuwa sai Nana Fadila tana Lagos tana aure sai Nana Fatima tana Dutse tana aure,Sai Nana khadija dake gabanmu yanzu tana aji daya ajami'ar kaduna ina zaune a anguwan NDC kaduna ina da gida da motar hawa sannan Ina da Rufin asirin da na Dauko mahaifiyata Gata nan Inno muna zaune tare da ita da. Bikin ma da ba ta tafi tare da su Maman Nanah ba,Tana faman da matsalan ido,jiya ne ranar zuwanta ganin likita yasa nace ta tsaya in na kaita ajiyan yau sai na wuce kano da ita sai kuma muka wayi gari cikin wannan al'amarin nan take na kira Direba nace mu Dauki Hanyar katsina bazan iya sukuni ba sai nazo naga Ahalina"

Ya karishe fad'a yana kallon mu gabadaya su Goggo suka amsa da Masha Allah.

Cikin yanayinsa yace"Ya'yana ku fadamin a inda kuke aure da adadin yaran ku..?ina mazajen ku..?ko dai yake nima ban zo da iyalaina ba. ammh da zarar na dawo daga Tafiyar da zan yi zamu zo gabad'ayan su ku gansu suma su gan ku"

Cikin yake Yaya mariya ta fara fad'in sunanta da adadin ya'yanta sannan ta fad'i yaya Asiya sai ni muryata a shake nace"Fa'iza ya'yana hud'u Kabir Amir,Saudatu Anum,Musty da Ahmad Ina aure a katsina"

Hafsah kuma karamar mu ce tana wajena shekaran nan ta fara karatu a jami'ar katsina"

Cikin gamsuwa ya gyad'a kai yana kallonta kafin yace"Aa Transfer zan yi mata zata koma kasu su yi karatu tare daa yar'uwanta Nana khadija,bazan bari ku yi nesa dani ba bangaran karatu fa baku gayamin inda kuka tsaya a karatun ku ba..?

Sai na kasa mgana Yaya mariya tace tayi Nce cikin gamsuwa yace"Meyasa baki cigaba ba Mariya..?

Sai ta sunkuyar da kanta sai yayi mirmishi kafin yace"Zaki cigaba insha Allahu ilimi shine mace zan dauki Nauyin karatun ki da komai,su Nana Fatima kowacce sai da ta gama Degree tayi aure Nana Fadila Nurse ce tana aiki da aibitin Gwamnati na garin Lagos"

Ni dai na riga na zama mutum mutum ina jin sunayen wasu ahalin namu da bamu taba sani ba,ni ya kallah kafin yace"Ke fa Fa"iza..?a ina kika tsaya a karatun ki..?.

Sai na kasa bashi amsa kaina na maida kasa kafin nace"Ban yi karatu ba ni"

Cikin mamaki yace"Bangane ba..?

Da Sauri Goggo tace"Fa'iza batayi karatun boko ba sai dai na addini,kasan Lokacin rasuwar mahaifin su mun raba su ne a Tsakanimu ta zauna hannun Kabiru ne kafin rasuwarsa D'ansa ma take aure yanzu Haka mai suna Ishaq"

Kai Tsaye yace"Aa wannan ba Hujja ba ne. Da za'a barta batayi karatu ba,Ai ilimi ginshiki ne ga y'a mace Dole Fa'iza zata koma makaranta domin ta sake inganta rayuwarta"

Cikin rauni nace"ko primary fa ban yi ba,sannan ina da raunin ji"

Cikin yar dariya ya Dafa kaina Lokaci d'aya yana fadin"Kada ki damu girma baya hana neman ilimi lesson Teacher za'a sama miki ya koyar dake kafin ki fara shiga makaranta,Mganar raunin ji kada ki damu makafi ma sun yi karatu kuma sun zama wani abu indai ni ina Raye y'ayan yar'uwata bazasu taggayara ba,na ji takaici da ban sameta a raye taji gajiyan dukiyata ba,ammh bakomai tunda ga ku, kamar wani nauyi ne a wuyana kamar yadda Nauyin su Nana khadija ya rataya a wuyana"

kai tsaye yake mganarsa Kuma babu tsoro ko shakka,Nan ya rika mana Tambayoyi kan Rayuwarmu muna bashi amsa ya tambayemu muna sana'a ko kasuwanci ne muka gayamasa ni na fad'amasa ina zobo da kunin aya ina Turarekan kamshi.

Mirmishi yayi cikin jin dadi yace"Good ina son naga mace da ta iya sana'o'iin hannu.Dakyau Fa'iza zamu inganta wannan kasuwan cin naki'

Ban san Lokacin da nayi mirmishi ba,Sai Hira ta tsinke a tsakaninmu shi kuma sai kiransa ake yi a waya ya koma gefe ya sauya harshe zuwa Turanci yana ta mgana mu ko Inno tajamu jikinta tana fadin"Ya'yan nan ban ji kun ce kun yafe min ba..?

Dukkanmu muka ce mun yafe mata tana dariyan jin dadi tace"Nagode. Daga yau kun tashi daga marasa kaka kun koma yan gatan Inno.Daga yau ni kakarku ce Baban Nanah Kuma Uba yake gareku Aziza kuma uwa take gareku su Nana fadila kuma yan'uwan ku ne"

Wani farinciki ya Lullub'eni daman zan ga wannan ranar..?

Ashe mu ma muna da gata bamu sani ba..?Nan Yaya mariya ta kira Yaya Asiya ta fad'amata haka ta dinga Tsallen Murna aka bata Inno suka gaisa Lokacin Abban ya gama wayar aka bashi suka yi mgana mutum ne mai barkwanci da son yan'uwa Yaya Asiya ta kirasa da kawu yace"Sunana Abba.Ya'yana haka suke kira kuma ya'yana ne haka zaku rika kirana.

An ce kina kano ai yan'uwanki da maman ku duk suna kano sun je sha'ani nima daganan ni da Inno kanon zamu je zan sauketa ni kuma zan hau jirgi zuwa Porthercourt,muna da Taro ammh da zarar na dawo zan kawo su dukkansu su gan ku,kuma kuga sauran yan'uwan ku"

Cikin murna Yaya Asiya tace"Na kosa Abba don Allah ku zo da wuri"

Cikin Dariya yace"Kada ki damu ba domin kuna gidan mazajen ku ba, da duka Gidana zan maida ku.ko o a yanzu kowacce da mijinta zata zo da ya'yanta ina son ganin iyalan ku gabad'aya"

 D haka suka yi sallama da Yaya Asiya duka duka ko awa uku bamu yi ba tare ba, ammh mun saba da juna ji muke yi kamar in ya tafi bazai dawo ba,kamar bazamu kara ganinsa ba,Sai dai ana ta kiransa jirgin karfe hudu da rabi zai hau a kano shiyasa suka yi shirin Tafiya idanuwan mu ya ciko da kwallah ya rike Hannayen mu yana fadin"Kada ku damu da zarar na Dawo daga tafiyar da nayi zamu zo sai kun gaji da ganinmu kuma zan tafi daku gidana kuje ku yi min sati d'aya na san komai akan ya'yana suma susan komai a kaina"

Bai zo da komai ba Saboda tafiyar Gaggawa ce kud'i ya zube mana da bamu san nawa bane Direba ya kawo su da wata bakar Jeep dankareriya,Su Baba ati ma ya cika su da kudi da Sallaman yana dawowa daga tafiya da shi da iyalansa zai dawo,Inno ma tana ta sallama da alkwarin wannan karon zumunci an fara kenan har Abada,kafin ya tafi ya karb'i lambobin mu har da na Yaya Isa,mune rakiya har bakin mota da zai shiga mota ya dafa kan Hafsah yana fadin"Auta sai na dawo ko.?domin kece auta Nana Khadija zata girme miki,Zamu dawo in sha Allahu bayan Abba har Babban Yaya ma kuna da shi"

Da haka muka yi sallama suna d'aga mana hannu muna daga musu hannu,Cikin gida muka koma ana ta maida zence Goggo ta kallemu tana fadin"Kunga abun Allah ko..?

Allah ya nufa ganawar sai a wannan lokacin ne"

Yaya mariya tace"Naji dadi Goggo naji Dadi yau naga wani ahali daga Ahalin Tamadina murna kamar zata kasheni"

Ta fad'a cikin farinciki Hafsah kuma ta Daka Tsalle tana fadin"Abba yace ni ce auta kuma muna da Big bros muna irin na ya'yan yan gayu"

Ni dai sai faman washe baki nake yi farinciki ya gama cikani Yaya Asiya ta kasa zama sai kira take muna bata labarin abunda ya faru,Murna kamar me tace itama cikin  Satin nan tana Tafe su Baba Ati sun koma gida da Tarin alherin Abba garesa muma kudi ne sun fi dubu dari ya zube mana,Goggo ko kwandala bata Dauka ba sai muka raba a tsakanimu,nan mukayi azahar da la'asar saannan muka tafi ni da Hafsah muna masu Farinciki ko da muka koma gida yara sun dawo makaranta Mama abun mamaki ita ta dafa musu Taliya Jallop muna shigowa Musty da Ahmad suka zo suka makaleni suna kiran Umma Umma daman nayo musu Tsaraban su Chaculate,Dakin Mama na fara shiga na gayamata na dawo ganin yanayi na fara'a yasa ta kalleni kafin tace"Ina fatan su Goggon lafiya..?

Cikin Tsananin Farinciki nace"Lafiya lau Mama. Daman Abba ne yayan Tamadina ya zo yau shine goggo ta saka aka daukomu"

Mama sai ta kasa gane kan mganar Cikin Mamaki tace"Bangane ba Wani Yayan tamadinan..?

Cikin zakwad'i na fara bata labari Cikin karin mamaki Mama tace"Ikon Allah ashe tana da dan'uwa kuma shima yana da iyalansa..?.

Kai tsaye nace"Sosai ma don ma tafiya ta kamasa yanzu, iyalan nasa kuma suna kano biki ammh yace da zarar ya Dawo zasu zo gabad'ayan su ganmu mu gansu muma..,"

Sai Mama ta kasa mgana mamaki duk ya cikata Dakina na shiga Anum ta tare ni tana fadin"Umma nayi miki wanke wanke."

Amir kuma ya amsa min da cewa"Umma nayi miki shara"

Ina dariya nace"Allah yayi muku albarka ya'yan Umma"

Ahmad ke dane kafata yana neman kadani na murde kunnensa ina fadin"Umman zaka kada ko..?

Sai ya fara Dariya Musty na tayashi,Kan kujera ta na fada ina Sauke Hijabin Jikina Hafsah ta shige Daki Amir har ya shiga kitchen ya zubomin abincin Ya kawo min kenan yana fadin"Umma ga abinci na kawo miki ruwa..?

Kafin nayi mgana Anum ta Ruga taje ta Daukomin ruwan na karba ina fadin"Amun di'na ta zama yan mata fa"

Sai ta rufe fuska wai kunya ina ruwan Anum,Mama ce ta kwalama Amir ya kira ya fita sai ga shi ya Dawo da kudi wai cinikin zobon da akayi bayan ba na nan mamakin Mama ya kamani itace har da siyar min da zobo..?ban dai ce komai ba sai da na Huta naci abinci na leka nayi mata Godiya bata amsani ba,Ranar cikin Farinciki muka karishe yini,Yaran har sun Fahimci ina cikin farinciki sai da Amir yace"Umma kina ta dariya ko kin samu kudi ne..?

Dariya na saka ina mamakin wayon Amir yasan dariyata yasan Bacin raina,Kansa na shafa ina fadin"Sosai Amir, ammh ba kudi na samu ba abunda yafi kudi Daraja da Tsada na samu"Amir na mirmishi yace"Umma menene shi..?

Cikin bayyana Murnata nace"Zan gayamaka kaji"

Daganan sai ya bar mganar,Bamu yi mgana da Yaya Ishaq ba,sai washegari ban gayamasa ba ammh yanayin murna na sai da ta bayyana a waya sai da yayi min mgana yace"Fa'iza hala yau an kwashi cinikin zobo da kunin Aya ne kwasha kwasha naji jiki cikin Fara'a.?

Dariya ya bani har sun Fahimci in na samu kud'i ina murna sosai ban gayamasa ba na bari sai ya Dawo kwana Biyu Tsakani sai ga shi ya Dawo,ban kai ga ma gayamasa ba Har Mama ta rigani sai da daddare yake min mganar na kallesa ina da'gama masa kai alamun hakane cikin kallona yace"Na tayaku murna.."

Cikin farinciki nace"Mungode..Yace ai in suka zo har kai yana son gani"

Cikin mamaki yace"Ni kuma..?

Lafiya kuwa..?

Sai na girgiza kai ina fadin"Ban sani ba ya dai ce dukkan mu yake son ganin mazajen mu"

Daganan sai bai kara mgana ba,nima ban kara cemai komai ba kudin hannuna Jarin zobo na da kunin Aya na kara,Sannan nayi Humra makotan mu wata Amarya ta bani na yi mata,har da kwallacha.

Kwana Takwas da zuwan Abba Ya kira Hafsah yace gobe shi da duka iyalansa,Daman su Nana Fadila Daga biki basu koma ba ya Tsaida su yace sai sun zo anyi zumunci Yaya Asiya daman ta kwana Biyu a karofi,Murnan kamar zan zuba ruwa a kasa nasha,Har chan karofi ya kira Goggo ta saka aka gyara bangaran Hajiya na gidan Yaya isa inda za'a sauke su,sai kuma mganar abinci Matan Yaya isa da Yaya Salisu zasu ji da komai,Ga Yaya mariya da itama mun yi waya tace zata shirya musu abinci mai da rai da lafiya ni kuma nace zan yi zobo da kunin aya na Taho dashi a goben dani da yara da Yaya Ishaq da sai da Daddare na fadamai.

Yayi shuru kamar bazai yi mgana ba sai chan yace"Allah ya kaimu goben"

Mun yi zencen da Badariya da yake ta dawo shekaranjiya tace itama zata je kawai da Safe sai Yaya Ishaq ke fadamin Mama ma tace zataje ban yi mamaki ba araina nasan zataje ganin komai ne,kenan duka gidan zamu tafi,Itama Yaya Asiya mijinta aranar zai kamo Hanya da sauran yaran ni ma dani da iyalaina,Har girki sai da nayi jallop din shinkafa mai rai da lafiya da taji kayan lambu da nama nayi zobo da kunin Aya mai yawa,Na daukan mana kaya tunda dawowa badai ranar ba Kulle gidan mukayi,Tashar Mota Ishaq ya samo mana har kofar gida,Karfe d'aya da wani abu muka tashi Hafsah suna ta mgana da Yaya mariya har da Abban sun yi mgana yace Tafiyar ta su ta Motace,suna hanya sun Tsaya su yi sallah ne ammh sun kusa karisowa

Mun isa karofi Biyu da wani abu na rana, gida cike su Anum nata murna sun zo Karofi,har alokacin basu iso ba ammh sun ce sun shigo katsina suna gabda karisowa.

Yaya Asiya ta fimu murna saboda ita basu taba Haduwa ba ammh mu kanmu murnan ya cikamu,Yaya Isa da su Yaya ishaq da mazajen su Yaya mariya suna kofar gida,mu kuma muna cikin gida muna Dakon zuwan su.





*Janafty"*

[7/17, 7:33 PM] +234 703 465 7829: *KNKB2013*


*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*

*09069067488*


Wajen misalin karfe uku na rana mukaji diran motoci da Hayaniya daga kofar gida,mu muna cikin gida sai muka kasa zama muka mimmike kan kafafun mu,muna masu kurama kofar falon Goggo ido domin ganin masu shigowa.

Yara ne almajirai daga waje suka fara shigowa da jakunkuna da akwatina, sai kuma bayan su wasu fararan yara kyawawa mace da namiji suka shigo mace iyakar ta sa'ar Anum namijin kuma kamar Musty ne,Da gudun su suka shigo daidai Lokacin suma su Anum sun kwasa aguje zasu fita waje sai suka had'e da yarinyar nan,Tsayawa suka yi suna kallon juna kamar susan juna sai kuma dukkansu suka washe baki suna Dariya Anum tace"Laa..Ke.."

Itama yar yarinya sai tayi dariya sai da Kumatunta suka loba kafin tace"Kema kinsan Gidan nan ne..?

Sai gabad'aya mamakin su ya kamamu kafin mu samu mu fita daga mamakin Ina Anum ta san wannan yarinyar mai kyau da ita,sai ga wasu mata Farare yan gayu sun biyo bayansu,da yi sallama sun shigo d'ayar Babar itace ke dauke da karamin yaro a Hannunta sai d'ayan da bata kai ta Tsawo ba tana rike da jakunkunansu na Hannu da wayoyinsu dukkansu Bakin less ne mai adon pink ajiki da mayafansu, a kallo farko in kayi musu zakasan yan gayu ne sannan masu ilimi ne da Nasaba mu dai muna ta bin su da maraba ji kawai ka ke yi ana"Maraban ku."

Sannunku da zuwa"

Goggo kuma ita ke faman fadin"Maraba da baki maraba da bakin mu"

Suna amsawa cikin sakewa lokaci daya suna kallon mutanen dake falon bayan su kuma wata matashiyar yarinya ce tsawon Hafsah inaga itace Nana Khadija itama kayanta iri Daya da na yan'uwanta,tana tafe da wata karamar jaka ta mata a bayanta,Daga ita sai ga wata Farar Mata ta bayyana Tare da Inno dukkansu cikin Fara'a mu dai bakin mu bai daina kiran musu sannun su da zuwa ba.

Gabadaya waje suka samu suka zazzauna,Yaya Asiya tayi ma Inno barka da zuwa data zauna a kasan Cafet ta mike kafa Saboda gajiyan zaman mota.ta kalleta lokaci d'aya tana fadin"Mariya ce ko.?

Kan Yaya Asiya na kasa tace"Aa Asiya ce"

Sai Inno ta rike baki tana fadin"Asiya..Sannu Asiya kece bamu had'u wanchan zuwan ba,ba shakka Allah ya jikan Hafsatu da rahma"

A ka amsa da Ameen Nana khadija tace"Don Allah ina so zan shiga toilet"ina kusa sai na kalli Hafsah ina fadin"Hafsah rakata"

Sai Hafsah ta mike tace tazo ta rakata ta mike suka shige bedroom kowa ya bisu da kallo gwanin sha'awa.

Yar farar matar nan tace"Inno lalle Jini d'aya ba wasa ba, kinga Nana khadija kamar ta da wannan yar sa'arta ta ta, hala tana cikin ya'yan da marigayiyar ta bari ne..?

Inno tace"Itace Auta Hafsatu kenan. Ga Asiya nan itace Babban su sai Mariya sai Fa'iza gasu nan kun gansu ku bari Shi Baban Nana ya shigo shi da Abdul'ahad zaku ji sauran bayanin"

Daganan Goggo tace ko zasu yi sallah sukace sun tsaya a bisa hanya sun yi sallah,Sai dai aka fara kokarin gabatar musu da abinci Farar matar nan da daga ganinta itace mamansu tace"mu fa ba baki ba ne mun tsaya a inda muka yi sallah mun ci abinci zamu ci anjuma mu da mun zo kenan sai mun gama Zaga dangi gabad'aya ai abinci sai kun gaji da Dorawa kuna saukewa ko Inno..?

Tafad'a cikin barkwanci Inno tace"Kwarai kuwa"

Goggo tayi Dariya kafin tace"Ina shi Alhajin bai shigo ba..?

Inno tace"Ya tsaya da mazan dake waje"

Bata ma gama rufe baki ba sai ga su sun shigo,Yaya Isa ne yayi musu jagoranci,Abun mamaki da zugan yaran nan su Amir kamar sun san shi Bayan shi kuma wani zankaded'en Saurayi ne kamar shi, sai dai shi Saurayin fari ne sannan ya fishi jikin Murjewa,suna shigowa yaran na biye da su zuga guda Maman Nana tayi dariya tana fadin"Baban Nana baban yara kenan"

Baya ya juya yana fadin"Ina ya'yan nawa..?ku shigo mana ku ai ba surukanta zamu yi ba,Duk ya'yana ne ku ku shigo nan ai duk mun zama Daya"

Sai ga su Yaya ishaq sun shigo da mijin Yaya mariya da na Yaya Asiya sai Yaya Salisu waje aka basu suka zazzauna aka shiga gaisawa da tambayan Hanya,sannan muka tashi dukkammu muka durkushe a gabansa muna gaisheshi ya amsa bakinsa har kunne ya saka hannuwansa Biyu ya Dagomu yana fadin"Ku tashi ku zauna ya'yan Abba"

Gabadayamu muka zauna a gabansa yabi mu da kallo kafin ya yi mgana Yaya Asiya ganin yana kallonta yasa tayi Saurin cewa"Asiya ce Abba'

Gabadaya sai da akayi dariya shima Dariyan yayi yana fadin"Zan kama sunan sai kika rigani Ase ase ya gida da yaran..?kanta na kasa ta amsa mai sai ya fara waige yana fadin"To ni jikokin nawa yawa ne dasu kai yara maza kowa yaazo wajen mamansa mu gani"Kamar suna jira kowannen yazo ya rabe jikin uwarsa Anum har da kwantomin saman wuya rad'a take so tamin a kunne ban jita ba.

Abba ya kallemu ya kara kallonmu sai ya juya yana kallon Inno Lokaci d'aya yana fadin"Alhandulillah yar'uwata ta bar min zuru'a inno"

Inno ta gyad'a kai tana fadin"Ba shakka nima ai duk ta kara min yawan magidanta da kishiyoyi"

Abba na Dariya yace"Inno Maman Nana sai dai tayi hakuri Kishiyoyo gareta Rututu ba adadi"

Maman Nana ta washe bakinta fararan Hakoranta suka bayyana Lokaci daya tana fadin"Bakomai ban damu ba dad'in abun ma duk na Roba ce nice dai uwar Nana ta karfen"

Gabadaya dariya akayi daga ganinta itama akwai barkwanci su Mama na gefe suna Dariya Saurayin ya dago ya kallah yana fadin"Babban yaya ta kanka zan fara fa"

Mirmishi yayi mai kayatarwa kafin yace"Girman ka ne Abba"

Badariya ta kara kallonsa ita tun shigowarsa taga kamar ta san shi, sai dai ta kasa tuna a ina shi kuma bai ma Lura da ita ba D'aya bayan d'aya ya fara Gabatar da mu kafin ya karishe da fadin"Duka wad'anan kannenka ne nauyi ya kara hawa kanka Babban yaya.kamar yadda kake tafiyar su da Nana Fadila haka zaka tafiyar da su ya'yan yar'uwata da na baku Labarin bamu had'u ba har Allah ya Dauki ranta wad'anan sune iyalan data bari"

Cikin gamsuwa yace"In sha Allahu zaka sameni mai kulawa da kannena kamar ko yaushe"

Jinjina kai yayi kafin ya Kallemu yana fadin"Fa'iza Asiya,Mariya da Auta ga yayan ku nan sunan sa Abdul'Ahad zai yi muku Jagoranci kamar yadda zan jagorance ku, ku gaisa da shi"

Daya bayan d'aya muka rika gaishe shi yana amsaawa cikin Sakewa kafin Abba ya yafito Nana Fadila ta matso kusa da shi Tana fadin"Na'am Abba."

Cikin Dattakonsa ya nuna mu yana fadin"Ga yan'uwanki nan.Kinga Asiya itace kamar age mate din ki to ki riketa Amana ku zama kamar yadda kike da Nana Fatima"

Cikin gamsuwa tace"In sha Allahu Abba"Nan itama muka gaisa ya yafito Nana fatima ya gabatar mana da ita yana fadin"Ga age mate din ki nan Fa'iza ki kula da ita kamar yadda zaki kula da Nana khadija tana da raunin ji Hallita ne haka aka haifeta ki kula da ita"Da sauri ta rike Hannuna tana fadin"Ni daman Abba ina ganinta naji ina sonta"gabadaya sai akayi Dariya Abba ya Kira Nana khadija da Hafsah ta Dawo rakata Tiolet ya had'a su da Hafsah sai Yaya mariya taga an wareta Cikin damuwa tace"Abba ni wa zaka damka ma Amanata?

Yana dariya yace"Amanarki tana hannu nagari D'iyata. Maman Nana ga wata amanar na kara miki Dukkansu ya'yanki ne kamar su Nana fadila ki zama uwa tagari garesu kamar yadda na sanki kada ki kara bari suyi kukan maraicin rasa uwa"

Da Sauri ta Gyada kai Lokaci d'aya tana jawo Yaya mariya ta Rumgume tana fadin"In sha Allahu Baban Nana,Mari babban kifi rabu da wad'anan yaran ke da uwa kika samu sukutum ga Abdul'Ahad da zan saka yafi shagwabaki"

Yana dannan wayar sa yace"Itace fv sister di'na ma daga yau Ammi"

Nana Khadija ta shagwabe fuska tana fadin"Kai yaya ni din fa..?.

Yana tabe baki yace"Kin zama tsohon yayi"Sai dariya gabadayanmu Farinciki ya samu muhalli a zukatanmu Abba ya gabatar da su Baba ati ne a matsayin Goggon su kad'ai data rage mu su sannan ya gabatar da Maman Nana a matsayin matarsa uwar su Fadila sai su Goggo a matsayin Dangin mahaifin mu.

Badariya ya gani ya nunata yana fadin"Wannan fa ban ganeta ba..?

Da Sauri nace"Kanwar mijina ne Badariya Abba"

Cikin gamsuwa yace"Itama ya'ta ce sannu Badariya"kanta na kasa ta amsa tana gaishesa sai lokacin Abdul'ahad ya lura da ita ammh shi karon farko ya gane ta,har Hoton wayarsa ya Dauko yana gani to ai dolensa ya ganeta duk kan Hoton Raly dake wayarsa rabin sa tare da wannan kawar nan tata take yi, in bai manta ba sunan  kamar Badar sunan ta, in suna tare wani Lokacin har gaisawa suna yi ta kalleshi shima ya kalleta ammh ganin kamar bata ganesa ba sai shima ya basar.

Yaran duka Abba yasa muka yi masa bayaninsu,muma muka tara su wajen shi muna fada musu Abba ne su gaisheshi Amir ya karisa ya gaishe shi ya Dagosa yana fadin"An ya Fa'iza bazaki bani abokin nan nawa ba yaron ya burgeni akwai natsuwa sosai'

Ina dariya ban yi mgana ba Da Sauri yace"Kada ki damu in dai bangaran megidan  ne ke da shi Duka ya'ya ne ina da iko a kanku da ya'yan ku gabadaya"Nana Fatima na gefe tace"Allah ya bar mana Abba"

Nana Fadila da Inno na tayata Dariya shi bai ma jinsu ba Hankalinsa na wajen Anum kuke tana faman tambayansa"Kai ne Abban Umman mu.?ya gyad'a mata kawai sai ta kalleni tana fadin"Umma ba kin ce Baban ki ya rasu ba har muna addu"a ba?

kafin na samu amsar bata ya amsata da cewa"Wani Sabon Abba ta samu ke kuma kin samu sabon megida ko bakya so na..?.sai su Anum aka noke kai ana dariya kafin tace"Ina sonka mana ammh sai na girma zamu yi aurre"Gabadayanmu muka saka Dariya Ammi tace"Kaji min yarinya Daga haduwa sai fashin miji"Abba ya Dora t saman cinya yana fadin"Maman Nana dai ana ta kishi"Sai dariyan barkwancin su muke yi, Sai yarinyar da suka fara shigowa naji Nana Fadila na kiranta Falaq,ita tayi ma mamanta Rad'a a,kunne sai ta Dago tana kallon Anum kafin ta kalli Ammi tana fadin"Ammi Kin ji Falaq tace Anum tazo bikin uncle Junaid ta ganta a gidan Anty Laila"

Sai kallo ya koma kan Anum tana jin haka jikinta na rawa tace"Nima na ganta"Sai mamaki ya kamani Ammi tace"Haba ni fa ina ta yi ma yarinyar nan kallon Sani sai da Falaq ta fad'a na tuna kunga yara da rashin mantuwa ko..?

Nana Fadila tace"Ko ita ce Anum d'in da kika Dameni da zencenta da kika koma gida.?sai yarinyar ta Daga kai sai mamaki gabadaya ya kamamu Abba yayi mirmishi kafin yace"To yara dai sun san juna sai aji ta ina aka haihu a ragaya"

Ammi ta kalleni tana fadin"Fa'iza ko har dake aka zo bikin Lailan ne bamu hadu ba.?Laila ta kaduna..?

Sai alokacin na tuna bayan Amir yayi zaraf yace"Umma Anty Laila da take zuwa ita da Anty Raliya"

Da Sauri nace"Laila..Oh na tuna ta Aa Anum kad'ai taje bikin ita ta roki babanta ya barta suka tafi da ita"Sai da ake mgana Badariya ta tuna inda tasan Abdul'ahad da Sauri ta kallesa tana fadin"Abdul'Ahad right.?

Sai ya jinjina mata kai yana fadin"Yes Badar ko..?

Sai ta fara Dariya kallo ya koma kansu ta kalleni tana fadin"Anty Fa'iza kinsan waye..?wanda zai auri Raly ne fa."sai na bude baki ina fadin"Raliyar ki.?sai ta gyada min kai sai na kasa mgana Ammi tace"ikon Allah kusan Raliyar da Abdul'ahad zai aura kenan..?kusan Hajiya Aisha Saulawa kenan?

Kai tsaye nace"Nasan ta sosai akwai zumunci a tsakanina da ita da ahalinta. Raliya kuma yar gidana ce Aminiyar badariya ce, kanwar mijina"

Sai mamaki ya kama kowa,Ammi ta bude baki kafin tace"Ke Fa'iza ba dai ke bace mai Turaran kamshi na Katsina ba..?

Sai ta bani dariya na gyad'a mata kai lokaci daya sai na Tuna da Sauri nace"Ba dai ke ce yayar mijin Laila da na hada turare humra da Kwallacha wajen ki ba..?

Sai ta fara Dariya tana fadin"Baban Nana diyar taka fa sananniya ce.

Ba shakka ina turaren da nace maka naga Amaryan junaid dasu masu kamshi na tambayi inda akayi mata tace Daga katsina kawar mamanta Hajiya Aisha ta bada akayi mata?ka manta har kana min tsiya shegen son kanshi bazan iya siya a kaduna ba sai na lula har katsina..?

Sai ya daga mata kai yana fadin"Duk na tuna"Da sauri tace"To ai di'yar kace mai hadawan Allah mai iko sannu Fa'iza"

Sai kallo ya koma kaina Nana Fatima tace"Ammi wai turaran da na sace din nan da nazo duba Inno..?

Dakuwa tayi mata tana fadin"Asirin ki ya Tonu kaga barauniyar gidan ka Baban Naana ina fad'an an dauke min Turare kace baka da barawo a gidanka to wannan fa..?

Gabadaya dariya muke cikin Had:e rai yace"Yayi mata kamshi ne ta ara ko Nana Fatima..?

Da sauri ta daga kai Lokaci daya tana fadin"Fa'izata zata sake had'amin nawa Ammi na dibar miki"

Dakuwa ta sake yi mata tana Dariya AbdulAhad na dariya nace"Nana Fatima kamar itace mujaheed d'an sandan farin kayan wajen Lauya mgana"

Abba yace"To Za'ayi mata taron dangin abun kuma ma nasu ne.daman haka abun yake ba gashi da aka had'u ba yara suka fara shaida da juna ba"

Nan fa falo ya kaure da Hira suma basu da bakunta sun saki jiki suna ta Hira damu,Ammi ko ta shige cikin mu ba ruwanta Inno dai Goggo tajata Daki don ta Huta Mama ba baka sai ido ta zama kamar mujiya afalon da na gabatar da ita a matsayin uwar miji na, cikin girmamawa Abba ya gaisheta sau taga ba ma raina gorin asalin datake yi min sai da ta raina kanta da taga Abba da Ahalinsa.

Abdul'Ahad kuma na gefe ya Kira Raliya sun yi mgana da yace ga wata su gaisa sai ya bata Badariya tayi matukar mamakin inda suka Hadu sai Badariya ta bata labari tuni ta bazama Dakin Hajiya tana gayamata yadda komai ya wakana Daman tun a satin Abdul ya gayamata zasu zo katsina wajen dangin mahaifinsa tana ta mamakin daman su ba yan kano ba ne..?sai yace eh asalin Babansa haifaffan garin karofin katsina ne.

Abba da shi da yara aka barsu suna ta Budiri da kuma mazan su Yaya Ishaq kowannen ya gabatar da kansa garesa,Duk rashin sakin jikin Yaya Ishaq ya saki jiki da Abba Saboda yana da Dadin zama sallar la'asar ya fitar da mazan zuwa masallaci mu kuma muka yi namu acikin gidan yaran kuma tuni sun hade kansu suna wasa.

 Bayan an dawo sallah ne aka zauna zaman cin abinci,su Abba a kofar gida suka baza musu tabarma suka zauna mu kuma muna cikin gida,Girkina aka ci daga karshe zobo da kunin Aya har ana Fada da Nana Fatima da Nana Khadija Goggo na Dariya tace"sai kun gaji da sha duk sana'ar yar'uwan ku ce gatan  nan Fa'iza"

Ammi ta saka salati tana fadin"Allah mai Hikima sannu Fa'iza kai masha Allah"tana sha itama tana santi hakama abinci da akace ni nayi ta kalleni Lokaci d'aya ta kalli goggo tana fadin"Goggo Fa'iza yar baiwa ce gaba da baya fa ba'a sani ba"

Nana Fadila ne ta kara mata jaka a baya da sunan waigi ta ko mako mata Dakuwa suka koma gefe suna Dariya,ashe suma mazan sun yi santi sai da Daddare bayan an sake Taruwa a tsakar gida ciki zafi ga ba wuta ana Hira Abba yace"wacce cikin ya'yana tayi shinkafar nan mai dan karen dadi?

Da sauri Nana Fatima tace"Abba Fa'iza ta ce"Nana fadila tace"Ji bakinta Fa'izan mu dai malama ai bataki ke kad'ai ba ce"

Sai suka fara gaddama muko murna da Farinciki yaki barin mu,Abba ya  raba rigiman da fadin"Naji fa'izan kowa da kowa ne shikenan"

Daganan sai ya kashe mganar ya kalleni yace"Fa'iza komai da ruwan ki kenan..?masha Allah Allah yasa albarka"

Aka amsa da Ameen sai ya kalli Ishaq dake dauke da Ahmad Lokaci da'ya yana fadin"Ishaq ka yi dace gaskiya zaka karamin Sadaki saboda wannan girkin da zobon data kware akwai cikon Sadaki"

muka saka dariya gabadaya Ammi tace"Baban Nana zaka zama surukin zamani ne..?

Da Sauri yace"Daman nace miki ni surukin da ne..?

Yadda yayi mganar ne ma Dole sai da mukayi Dariya Allah Sarki Rayuwa daman haka Allah ya kan shirya lamuran bawa, sai kusan sha Biyu su Abba suka tafi masauki bangaran da aka  gyara musu ,Mijin Yaya mariya gida ya koma ya kwana kuma shi ya sauki su Yaya ishaq a gidan iyayansa Dakin kaninsa shi da mijin Yaya Asiya muko duka nan gidan goggo muka kwana har da Mama da Badariya mu da yan'uwan mu raba Dare mukayi muna Hira kamar mun shekara tare Nana Fatima na zama Fa"izanta abu kad'an sai kiji tace"Fa'ina kaza kaza"

Ita ya'yanta Biyu,Jidda da jalil kanana ne,Saboda sai da tagama Service dinta tayi aure Nana Fadila ke da uku FalaqFahad,Da Fairuz,Yadda kuka san mun dade da sanin juna saboda yadda muka shaku daga Dare zuwa Safe suma suna da Tarbiya daidai gwargwado Ammi ta basu tarbiya itama irin Abba ne akwai barkwanci.

Da Safe ni suka yi ma chaa na shiga kitchen nayi musu abun karyawa da su Yaya isa suka jifgo cefane,ko wajen karyawan har sai da akayi santi Tunda nan mazan suka zo gidan Goggo aka had'u aka karya gabadaya.

Yaya Abdul'Ahad na shan ferfesun kayan ciki da nayi musu ya kalleni yana fadin"Ina fatan kina koya ma Raly irin wannan girke girken ko?

Sai Falon ya kaure da Dariya Ammi tace"Baban Nana saka ma d'anka waigi shima Cikin Dariya yace"Ammi ba fa santi nake yi ba"

Abba na gefensa yace"My son yi santin ka dadi'n abun ba kai kad'ai ba ne har da Baban Nana shima yayi santin"Kai Abba akwai ban dariya Ammi tace"Baban Nana kasan wa na ke tunawa in na samu abinci mai dadi haka..?

Yana shan tea ya zuka ya dawo da mug din yana fadin"Engr.mana"

Cikin gyad'a kai tace"Wlh shi ke fad'omin rai kasan shi da son abincin Hausawa na gargajiya da na zamani."

Abba yace"Ki bari musamman ace ya samu zobon nan na Fa'iza da shi da Maltina ko coke har abada,kinsan ya tsani lemukan ba gwamgwani ko da yaushe korafinsa Baban Nana duk kayan basir ne zakin su ya yi yawa"

Ammi tace"Allah sarki Engr kamar ba Jinin yarbawa"

Abba yace"To ai kinsan ya sirka ta bangaran Hajiya Shukra shiyasa zaki ga rabin sa bahaushe rabinsa bayarbe ba, ba domin ma ya tashi cikinsu ba sai in akace miki ya had'a iri da yarbawa sai ki karyata"Ammi tace"Nima ka manta ganin farko da nayi masa sai da na karyata"

Abdul'Ahad na gefe yace"Abba kana ji da Engr nan Sosai"

Abba yace"Mutum ne har da rabin mutum..Ya yi min abunda bazan taba mantawa ba yayansu.Engr ya goya mutane Dabam dabam irina da yazama madubin su kirkinsa nake fada'maka sai ka zauna da shi zaka san hakan"

Abdul'Ahad ya jinjina kai bai ce komai ba,Abba da Ammi suka cigaba da mganganunsa kan Engrn da su,suka  san shi.

 Haka dai muka gama karyawa cikin Nishad'antarwa da Annshuwa,ranar a gida muka yini ana ta hira sai yammah muka fita Lokacin Yaya Ishaq ya koma gida shi da Mama da yara wanda Dakyar na samu Anum tabisa da ta saka rigiman bazata ba nace bata isa ba makaranta,Badariya na tare dani sai gobe zamu koma katsina Tunda suma Jibi zasu tafi saboda ayyukan su Abba su, suNana Fadila kuma zasu koma gidan mazajen su.

Da yammah Karofi muka zaga har gidan su Tamadina da yazama duk ya rushe Abba yace zai saka a bige shi a gyara zai zama nan zasu rika sauka in suka zo,Baba Ati kuma da ita zasu tafi zata zauna tare da Inno a gidan Yaya mariya muka kai wajen goman Dare,Muna ta Hira,

washegari kafin mu wuce Katsina sai da muka biya Dutsemah gidan da Tamadina tayi aure har da Abba akaje sun gaisa da mutan gidan da shi kanshi megidan suna ta fadin irin Hallayar ta madina Abba ya cika su da kudi muka bar su,suna kwallah muma muna yi Daganan muka rabu da Abba,ya koma karofi,mu kuma

Direban Abba ya kaimu har katsina da Abdul'ahad shi ya rigamu yin gaba wajen Raliya yaje ,Gidana muka sauka Nasan ko ban fad'a ba sun ga yanayin gidan susan muna da karamin karfi,Nan muka ci abinci mukayi sallah mun iske Anty Binta a gidan sai kallon su Nana Fadila take da ya'yansu taga ba ma raina a wajen su,sai la'asar na rakasu gidan Hajiyar Raliya har da Ammi,inno na gidan goggo tace bata iyawa kafa ciwo Hajiya taji Dadi ta karbemu hannu goma kamar yadda ta saba.

Ammi ta kalleta tana fadin"Hajiya ashe ya'ta ce ma ke turarukan kamshi bansani ba..?

Hajiya na dariya tace"To ba gashi yanzu kin sani ba!

Ammi tace"Wlh ai naji dadi kamshi har karkashinn Gadon Baban Nana insha Allahu"

Gabadayamu sai da muka Dara Raliya nata kunyana nace"Ni daman ai Antyn Raliya ce, ba kunya Tsakanimu Hajiya nata mamakin lamarin na zauna nayi mata bayani atakaice tace ikon Allah kenan itama Raliyan a bikin Laila suka had'u da Abdul'ahad duk da daman an san suna sanadin Iyayan Laila.sai dare muka baro gidan Hajiya da Sha tara na arzikin da ta hada mana, adaran suka koma karofi Washegari kuma suka koma gida Saboda a ranar Nana Fadila da Nana Fatima zasu koma gidajensu.

Kafin rabuwar mu Abba ya Tattauna damu kan abunda muke bukata sai muka kasa mgna sai yace bakomai Ko mazajen namu da bai samu zama Sosai da su ba, saboda ba Lokaci ammh zai gayyace su har gida su Tattauna mun raba ma junanmu Lambar wayanmu,Kwana uku muka yi tare kamar mun shekara tare Basu kyamace ni ba, duk rashin son mutane na, na shaku da su Nana fatima mutane ne masu karamci ilimi waye kudi da nasaba da sanin ya kamata.yaya Asiya ita yar gida ne Ammi yar kano ce Haifaffiyaa Dala ta kano,kuma daman ga bikin Raliya dake gabatowa mun zama iyalai D'aya kaduna zata yi diban manyan baki.

Badariya da Raliya sun fi kowa murnan wannan al"amarin,Ko Yaya ishaq sai da ya yabi kirkin Ahalin Abba gabadayansu.

Kuma kowa ya gansu yasan suna da kudi kuma sun taki gwamnati,Abba kamar yadda ya fada tare da Baba Ati suka koma Inno nata jin Dadi ta samu abokiyar zama tuni har Abba ya damka ma su Yaya Isa kwangilan gini an fara baje gidan ana sake sabon Faundation.

Sai da nafi sati ban koma da sana'a akan zobo da kunin aya na ba,Saboda rashin zamana waje d'aya,Muna yi da waya su sosai barin ma Nana Fatima har megidanta data koma sai da ta bani muka gaisa,Kowa ya ganni yasan na samu natsuwar zuciya da kwanciyar Hankali muma mun zama yan gata abu kad'an Abba yace me muke so..?Hafsah ta zama auta kowa ita yake riritawa yanzu haka ta kosa su samu Hutu ta gudu kaduna gidan Abba tayi Hutun ta achan.

Sati daya tsakani da zuwan su Abba ranar da Daddare muna zaune Yaya Ishaq yakalleni yana fadin"Abban ku aikin me yake yi?

Tunani nayi kafin nace"Na manta kamar ko a NN Me naji su Yaya Asiya na mgana?

Sai Yace"NNPC dai ko..?

Sai nace"To kila nan din ne".kai ya jinjina kafin yace"Akwai kudi gaskiya babban ma'aikatan matatar mai ne fa"

Ni dai ban ce mai komai ba, ammh kowa yaga Abba ai yasan ba karamin mutum ba ne.

Acikin watan Abba ya kira kowannen mu a waya kowa ta fadi abunda take so ni dai jari nace ya karamin yana Dariya yace"To Fa'iza aammh ai ni burin gina miki katon gidan abinci nake da shi, tare da shagon gyaran jiki da kayan kamshi"Sai na Bushe da Dariya ina fadin"Allah ya amsa Abba"

Dubu dari biyu ya turamin yace na rike a hannuna kafin yaga abunda Allah zai yi Dukkammu haka yabimu ya bamu kuma yace zai kira duka mazajemmu ammh sai yaje warri ya Dawo  warkshop din da zasu je suyi na wattani biyu in ya Dawo zai nemesu,Sannan ya aiko mana da kayan sawa dukkanmu mu da yaranmu da mazajen mu,abun sai wanda ya gani da wad'anan kudin na cigaba da Rufamana asiri,sannan gefe daya muna waya da su Nana Fatima muna tsara shiryen shiryen Bikin Raliya da aka matso da shi kusa,Da sai bayan wata hudu za'ayi yanzu kuma an maido da shi bayan wata biyu Saboda Yaya Abdul'ahad zai tafi kasar waje karo karatu kuma da matarsa zai tafi.

Mama dai kam kamar bata gidan ko motsinta ba'aji ta daina shiga duka Hurumina,sai dai bansan tsakaninta da Da'nta ba,Anty Binta kuma tana ta Hidiman auran Halisa ba'a cika ganinta ba,Mganar aiki kuma shuru kake ji sannan har Abujan Mahaifin zainab ya kirasa ya koma ammh ba wani Labari.

 Sai daga baya na Fahimci Saboda kawai ya rika zuwa yana zama da zainab ne,ammh tuni sun san akin bazai samu ba,tuni har ma'aikatan da aka dauka sun fara aikin su.







*Janafty*

[7/17, 7:33 PM] +234 703 465 7829: *KNKB2014*


*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*

*09069067488*


Zukata tuni sun kwanta,gabbai sun samu natsuwa hankula sunyi ruku'u sun rusuna.

  Ta kowani bangare na juya na irin shafukan kaddara da kan bud'e ma bawa to ta kowani tsanani daman Allah yayi alkwarin sauki,hakan ce ta kasance dani duk lokacin da naga rayuwa ta chude'min ko tamin zafi da ikon Allah sai wata kaddara ta bude ma rayuwata sabon shafi da zai zama bango ko majingina gareni

Bayyanar Abba garemu daga Allah ne, sannan zamowarsa makwafin Uba garemu shine jin dadin mu,Sannan har makwafin uwa ya Dauke mana Ahalinsa kuma sun Dauke mana makwafin yan'uwa da Dangi,sai alokacin muka san muma ya'ya ne,Abba ko tari bai yarda mu yi ba tare da yasan Dalilin yin sa ba,Yace duk abunda muke bukata kiransa kawai zamu yi a waya mu gayamasa,to mu saka aran mu komai muke so mun samu,Yaya Asiya tuni har ta je gidan su Ammi a kano tasha karamci ta tabbatar mana da cewa Duka Ahalin Abba masu karamci ne,Tace sai nuna ta ake yi ana fadin"Diyar yar'uwan Baban Nana ne na kaduna"Ko'ina aka kaita sai an karramata duk da Ammi bata garin tana kaduna,Direba aka saka yakai ta har gida,Sannan sun karbi lambar wayarta da alkawarin zasu rika zuwa suma. Ammi suna da yawa a gidan su matan Mahaifinta hudu ne kuma duka sun haiyayyafa,Sannan tana da kanne maza sosai wasu duk suna garuruwan da suke aiki da matansu kamar mijin Laila Uncle Junaid Staff ne a kasu Kaduna State University. yana chan sai dai lokaci bayan Lokaci suna zuwa ganin gida shi da ita.

Azumi ne ke kara gabato mu ma wannan karon,Zainab saboda ban samu zama ba bamu kara mgana a waya ba tunda na gaisheta kwanaki da jiki,shi kuma Gogan bai min zencenta ba.  Ni ma kuma ban cika Tusa kaina inda ba'a sakani ba, tunda muka yi alkawarin da shi ya daina matsamin ammh fa bai daina Takurani da kallo ba,ko kuma ya rika shigemin jikinsa na gogan jikina bana son haka nayi mai mgana sai kawai ya kalleni yace"Ba kyau Fa'iza wlh ba kyau. Ki bari kada Allah yayi fushi da Da ke"

da naji haka sai ban kara mai mgana ba,sanin gaskiya ya fada,Tunda bai sakeni ba har yanzu yana da Hakki a kaina kuma shi Allah ba ruwansa da wannan,mganar jinginan auran mu kuma wannan wani zama ne mai zaman kansa.

Sai na rabu da shi tunda na samu ya daina sakani gyaran Shimfid'a yana Rutsani sai na gode ma Allah,Abba Dubu Dari uku ya kara turo ma kowannemu mu yi siyayyan azumi har da su Goggo suma bai kyalesu ba,bakina yaki rufuwa Kana naka daman Allah ya gama nashi kuma nashi Tsarin shine daidai na zata Yaya Ishaq zai yi fad'a sai naga bai ce komai ba ya dai ce"Abban nan naku naji da ku Fa'iza"Sai na samu kaina da yin kayattacen mirmishi,Hajiya ma ta aiko mana da kayan abinci,Domin ita a di'ya ta daukeni ba kowa ba,Alherin Hajiya gareni mai girma ne da bazan taba iya mantawa da ita ba.

A satin za'a fara azumi yara sun yi Hutun makaranta suna gida da Safe muna waje ni da Anum da Amir muna wanke wanke Ahmad da Musty na fad'a kan shara nagaji da yi musu mgana ne na kyalesu sun ki bari ina jira na tashi ne yaro yaji a jikinsa,Hafsah na makaranta jarabawa suke yi ta kosa su gama ta gudu kaduna,Badariya na kano ammh suna chan suna ta shirin Biki ita da Raliya ta waya.

Daga Daki ya fito kamar an jehosa Fadi yake yi"Bazai yuyu ba. Wlh bazai yuyu ba in kika bari aka cire cikin nan na rantse da Allah Zainab aure na dake ya karem Bazan iya ba Nagaji haba.."

Yake fad'a cikin Tsawa da Daga muryan da sai da Mama ta fito daga Daki zani a hannu cikin wani yanayi ni kaina sai da na saki aikin da nake yi na mike gabana na faduwa.

Mgana yake a waya kamar kuma da Zainab yake mgana sai kara shan wallahi yake in aka cire cikin nan sai ya rabu da ita cikin bacin rai yace"Me kuka maidani daga ke har mahaifin naki.?sakarai shashasha ko sai yadda akayi da shi ko.?to wannan karon ba Kotu ba Allah yasa majalisar Dinkin Duniya zai kaini wlh sai kin yi zawarci ni bazan iya wannan auran naku ba da kuka fifita yahudanci Fiye da Islama acikin lamuran ku"

Kokarin yi mai bayani take ya Daka Tsaki ya katse wayar yana Huci,Mama ta kallesa tana fadin"Meke faruwa ne Ishaq.?

Sai ya kalleta Har idanuwansa sun cika da kwallah cikin wani yanayi yace"Mama ki duba fa ki gani,wai cikin yarinyar nan babanta yake so a zubar..'"

Sai ya kasa karisawa saboda yadda ransa ke Tukuki,Mama tace a zabure"Cire ciki kuma Saboda mene. ?Kamar zai yi kuka yace"Saboda Hujjar su na banza wai yana wahalar da ita, hala ciwo take ko kuma wani abun ne ya sameta ana raba mai ciki da laulayi ne mganar banza kawai,Mama ne Zainab da Mahaifinta suka maidani jani talau..?wannan wani irin kaddararren aure ne..?

Mama zatayi mgana kenan wayarsa ta fara kuka yana dubawa yace"Babanta ne"Yau ko arzikin Daddyn bai samu ba,kamar bazai Dauka ba Mama tace ya Dauka mu dai mun ga yana mgana Yaya Ishaq na cika ya bude baki yace"Daddy.."

Kamar katsesa ya yi yana mgana kamar kiftawan ido sai ji mukayi K'aras,ashe wayarsa ce ya buga da bango sai da ta dargargaje,A firgice muka yi baya har da yara da suka yi Tsuru tsuru basu saba ganin haka ba. Mama ta firgita ta rikesa da karfi tana fadin"Kai Ishaq ka natsu mana"

Haki yake yi kamar wanda yayi gudun mutuwa cikin hakin yake fadin"Shi ke auranta ko ni Mama.? A shari'an ce na fi shi iko da ita meyasa komai shi zai zartar da shi.?Rabon da wasu suke nema da kudin su,mu mun samu shine zai yi sanadiyar zubarwa saboda bai da Hankali yana Uba ammh uban banza wanda baisan ya kamata ba..?

Mama ta kara rikesa tana fadin"Kwantar da hankalinka ka natsu."

Cikin Hargagi yace"Wani  iri na natsu mama..?Har ce min yake sai an zubar nayi abunda zan yi, wai akan ya'yansa zai yi iya yin komai wlh Mama indai aka zubda min jinina ba shege ba,d'an sunna wlh sai Zainab sai tayi zawarci aurena da ita ya kare har Abada,in ya'yana ne zan karbo kayana Fa'iza ta had'a da su Amir ta rike min su"

Mama ta yi saurin tareshi tana fadin"Abi komai a sannu Ishaq"

Ni dai nayi tsuru ina kallon ikon Allah Amir yaje ya tattaro wayar baban nashi ya had'ata ya miko min yana Fadin"Umma ga wayar Daada"

Sai na saka Hannu na karba ban kallesa ba nace ya had'a kan kannensa su shiga Daki,Anum sai da yayi mata jan ido ta tafi ta tsaya tana Kura ido da Daukan komai sai anjuma kaji tana maimaitawa.

 Sai da suka shige ne na kallesa Mama ta Dake sai faman bashi Hakuri take yi,tana ya kwantar da Hankalinsa shi kuma yana kara rantsuwar Wlh matukar Zainab ta yarda Mahaifinta yasa aka cire cikin nan auran su ya kare.

Kai Tsaye nace"Saboda me zaka ce zaka Saketa..?

Sai duka suka dago suna kallona, ni ko na gyara tsayuwa a raina nace yau ce ranar maida martani Mama ce tace"Haba Fa'iza ai suma abun nasu ba su saka Tunani aciki ba"

Kai Tsaye nace"Zainab ce fa Mama. Zainab matar so yar Dangi,yar gata masu kudi da nasaba"

Sai ta kasa mgana ta Tsaya tana kallo na,Shi ma haka sai ko na kara fadin"Eh ai Zainab ce mai kyau ce ba Mummuna ba, sannan yar asali mai ilimin zamani yar gata yar masu kudi yar dangi mai cikakken gata,matar nuna wa duniya,wacce zata haifa maka ya'ya farare masu kyau ba irin ya'yan Fa'iza ba,matar da kuka zabeta sama da kowa matar da kuka fifita ta fiye da kowa matar da kuke so da kauna. Meyasa saboda wannan matsalan kace zaka saketa ke kuma Mama baki Tsawarta masa ba..?

Na karishe fad'a ina tsareta da ido kunya ya kamata sai ta kasa mgana shiko Tsawa ya dakamin bai so na kara mgana na warware komai ban kulasa ba na cigaba da fadin"Ita fa ka zaba sama da ni. Ka fifita ta sama da ni,Ka fifita zuru'arta sama da tawa zuru'ar, sannan ka fifita  ya'yanta sama da nawa ya'yan,to ta ina kake Tunanin zaka hanata abunda take so.?ai tun farko a haka ka ganta, kuma ka ji ka gani kana sonta.."

Cikin hargagi yace"Ya isheki Fa'iza..Ya isheki haka nace"

Ya karishe fad'a kamar zai Dakeni sai nayi baya na tsorata kada yakaimun duka,Cikin wata murya yace"Ki bari Fa'iza ba kyau irin haka. don Allah ki bari kada ki kara Tunzarani"

Sai da na tabbatar da nayi baya sannan nace"To ka daina mganar Sakin nan  bai dace ba gaskiya, ai ku ba yara ba ne, kun fara tara kyakyawan zuru'a a tsakanin ku"

Sai kawai ya Dafe kansa ya koma kasa ya zauna Dirshan yana kara Dafe kansa,Mama na gefe jikinta yayi sanyi da kunya yasa ta kasa mgana,ni ko sai naji zuciyata wasai ko banza na gasa musu mgana sannan na maida musu martani.

Yana girgiza kansa yake fadin"Nayi Nadama Fa'iza nayi nadama ba tun yau ba.wannan auran bai amfaneni da komai ba sai bacin rai da Nasani,ban bi Turban Annabi ba wajen auran nan sai Allah ya barni da zabina,ya bani mace tagari ban gode masaa ba,na rika Hange hange ina ganin na wuce da ajin Fa'iza,Sai ga shi na bi auran kyau da nasaba da ilimi daga karshe hakan bai amfaneni da komai ba.."

Da Sauri nace"Ya amfaneka mana Zainab na sonka sannan kuma ta fara tara maka irin zuru'ar daka ke so"

Idanuwansa Jajir ya d'ago yana kallona kafin yace"Bata so na, in da tana so na,da bata fifita ta mganar mahaifinta akan nawa ba. Tana ganin tana da kyau alfarma tamin data aureni,Tana ganin tana da ilimin da Taimakona tayi ta aure ni,tana ganin tana da Gatan da ban isa da ita ba. kaico na da nabi Rudin duniya da Rudin Shed'an,ga shi yanzu ina Nadama Shiyasa duk wanda bai bi Turban Annabi ba, tun a duniya zai Tabe Annabi ya fad'ama mu auri mai addini domin itace mafi kyawun cikin su"

Dagani Har Mama ba wacce tayi mgana ita kunya da Sanyi ni kuma na shiga wani yanayi mara Dadi a lokacin.

Shuru yayi yana sauke Numfashi kafin yace"Mahaifinta bai Daukeni a bakin komai ba,gani yake taimakona yayi alfarma ya yi min don ya bani auran yarsa shiyasa yake takani yadda yaga dama har cikin gidan nan ya tako ya ci zarafina na, kasa komai ammh wannan karon wlh bai isa ba. sai na nuna masa na fisa cikakken iko da yar tashi ta zubar da cikin ta gani Sai dai kuma a bi wani Sarkin"

Da haka ya shuru takalmansa yayi waje Mama na kiransa bai ko Juyo ba,Ni dai nace Allah ya kyauta na koma ina cigaba da wanke wanke na, Mama na Tsaye ta kasa gaba ballatana baya har ga Allah ba wai dadi naji ba ammh raina bai baci ba,Gwara su fara gani Tun yanzu ban ga laifin su ba,Irin Rariyan da ya siya ne kuma don tayi zubar ruwa shatata bai kamata yayi korafi ba.

 Ina gama aikina na shige Daki abuna,Na fara wata Hidiman yaran kuma karatu na iske su suna yi,Duk da nasan suna jin tashin mganar Baban nasu daga falon,tsakar gida na fito zan Dafa zobo na,Sai naga Mama an kwashi kafafun da sanyin jiki ta koma Daki Ranar sai dare ya shigo gidan ajaran majaran a falo ya fadi kan kujera yana sauke Nunfashi ina mai sannu da zuwa ya amsani a Dake kafin yace na sama mai ruwan wanka.

Sai da ya rarrafa ya shiga Dakinsa na bisa na kai masa wayarsa da ya fasa da tawa ina fad'in"Ga shi matarka nata kira, tana son mgana dakai"

Domin tun bayan La'asar Zainab ke kirana tana tambayansa nace mata ya fita ta Dameni ta kira yafi sau goma Daga gani bata cikin natsuwarta ne.

Yana cire rigan jikinsa ya d'ago yana kallona ina shirin ficewa yace"Dawo ki Dauki wayarki"

A kausashe nako ki dawowa na fice ina jinsa yana fadin"Lalle itama ko zan fasata wlh" a fili na furta"Kana fasamin waya zaka biyani kayana"

Daganan na fita zuwa kitchen sai da ruwan yayi zafi sannan na juye mai na ba ma Amir ya kai mai ban koma Dakin ba, abinci ma Anum ta shigar mai da shi yaran suna falo suna karatu ni kuma ina Daki,Hafsah na gefe na muna mgana sai ga shi ya shigo daga gani yanzu ya fito wanka ga kansa nan na digar da ruwa yana shigowa yace"Hafsah jeki falo wajen yara zan yi mgana da yayarki"

Ba musu ta fice ya kariso gabana yana fadin"Ki ka bama Amir ruwan zafi in ya kona sa fa..?

Sai na kallesa kafin nace"Ba yau ya saba dauka ba, zai iya ne"

Sai ya kuramin ido kafin yace"Ba kyau Fa'iza na horu fa don Allah ki yi hakuri".ganin ya fara sauya mganar yasa na mike na fice,na bar masa Dakin jiki a sanyaye ya koma Dakinsa ya shirya abincin ma afalo ya fito ya ci,Ina gefe sai kallona yake yi ni ko nayi kamar ban gansa ba.

Wayata sai washgari ya aiko Anum da ita, ban ko Duba  ko sun yi mgana ba. ammh naga an kirani Hafsah ta Dubamin tace Abba ne da Nana Fatima daman sune rana bata fitowa ta fadi basu kirani sun ji lafiyata ni da yara na ba,Har ga Allah ina kaunar Nana Fatima kamar yadda take kaunata,Sai da na natsa sannan na kirata muka gaisa sai tace measurement din yara da nawa take so na Rubuto mata sai nace ta bari sai Hafsah ta dawo zata turo mata,mun cigaba da mgana duk akan Bikin Yaya Abdul'Ahad ne da Raliya bayan sallah Tana fadamin Nana Fadila ta fitar mana da anko imu imu gabadayanmu,Na lura suna ji da Bikin nan ko don shine na farkon da zasu fara na Namiji, barin ma Ammi kamar Abdul'Ahad ba yaron ta na fari ba,ba ruwanta da kawaici da ita ake shiryawa komai.  Abba kuma daman ba mazauni ne ba ne tafiya na yawan kamasa Ammi ce akan komai.

Da Hafsah ta dawo na saka ta tura mata har da na takalmaa,Ban san cewa Yaya Ishaq bai yi mgana da Zainab ba, sai da ta kara kirana bayan na Dauka mun gaisa sai ta sakamin kuka na rud'e na zata ma ko wani abun ne ya faru cikin Kid'ima nace"Lafiya Maman Fadil..?.

Cikin kuka tace"Maman Amir ki saka baki Honey ya daina fushi dani wlh ba laifina ba ne. Daddy ne ya matsa kuma ni nace mai bana so tunda Honey baya so kuma ba'a cire cikin ba. wlh nayi ta kiran sa wayarsa a kashe bana samun sa"

Sai shesshekan kukan ta, na fara lallashinta kafin nace"Daman jiya baku yi mgana ba ne da na kai masa wayar ..?

Da Sauri tace"kashewa ya dinga yi Maman Amir yaki ya saurareni ma, Daddy fa har fushi yake yi dani saboda naki amincewa da mganarsa Maman Amir don Allah ki basa hakuri wlh ban cire cikin ba, yana nan kada yace zai sakeni wlh ina son mijina"

Sai ta bani Tausayi cikin sanyi na nace"Kiyi hakuri ki daina kuka in ya Shigo zan mai mgana"

Da haka muka rabu sai mganarta ta Tsayamin arai, tana son mijinta har ga Allah nice shaida,ammh Mahaifinta ne ya riga ya saba da juya al'amarin ya'yansa,Ni kuma na kudiri niyar daidaita Tsakaninsu saboda itace Dahir dinsa,Da ya shigo Dakin Mama ya tsaya,sai da ya jima sannan ya shigo Dakina yara suka mike suna mai Sannu da zuwa Dakinsa ya shige Saboda ina da mgana dashi da kaina na tafi kai masa abinci,yana zaune ya yi Tagumi ammh yana ganina sai ya cire Tagumi,sannu da zuwa nayi masa na sauke mai abincin a gabansa ya jawo yana fadin"Me muka samu ne..?

Ina zama nesa da shi nace"dambun Shinkafa ne da zogale"

Cikin yanayin sa yace"Salon ya shake mu Fa'iza"ina Dariya nace"Tuwo naso nayi ban samu gyad'a ba,sai yara sukace Umma ki yi mana Dambu"

Bai ce komai ba sai da ya tashi ya wanko hannunsa ya fara ci sannan yace"Ko bakomai zamu dora da zobo mai sanyi"

Yafad'a yana kashe min ido sai nayi dariya yana ci muna hira,Sai da ya gama ya kuma dora zobo mai sanyi kamar yadda yace sannan na sako mai mganar Zainab kici kici yayi da Fuska kafin yace"Ina ruwanki da wannan mganar Fa'iza..?

Na rausayar dakai nace"Da ruwana mana ai yar'uwata ce musulma kuma shi ai sulhu alheri ne"

Sai kawai ya mike yana fadin"To ki cire bakin ki a ciki ba ruwanki ahto.."

Sai naga daga taimako kawai sai na tattara kwanukan daya bata na fice ina fadin"Allah ya kyauta"

 Da gatse ya amsamin da Ameen sai abun ya bani Dariya a raina nace mata da miji sai Allah sai su shirya ma ban sani ba.

Kuma saboda Zainab din yaki kai wayarsa ya gyara. ya gwammace ya zauna ba waya nidai tunda yace ba ruwana na cire bakina data kara kirana,sai nace mata nayi mgana yace zai kirata in ya gyara wayarsa Da dai taga ba Nemanta zai yi ba an fara azumi Takwas sai gata ta iso,ita kadai ko Farhan bata zo da shi ba, ta yayesa yana gidan su Tace ko Daddy bai son ta taho ba Shari'a har Falon Mama ammh Gogan ka yace shi fa ya gaji kowa yayi ta kansa baiwar Allah sai kuka take yi a raina nace ita kuma nata Jarabawar kenan na soyayya Allah yasa mu dace.

 Yadda yake yi mata ban dauka zai iya kallonta ba, ammh dayake Namiji sunnsa Namiji sai ga shi sun shirya an shiga kurya an yi lamo,Daganan na san sha'anin mata da miji sai Allah Shi da har masifa ya rikamin wai na ce ta tafi nace dayake ni na kawo ta ba,Bata koma ba sai da suka Daidaita da juna kwananta Biyar ta koma Abuja,motar Haya ta shiga abunda bata tayi ba ammh ga shi Namiji ya sakata acikin wani Hali.

Ni daman tunda yace na cire bakina na kama kaina, ko da tazo ta zaunar dani tana gayamin har abunda ma bansani ba iyakata da ita hakuri kawai Domin kamar yadda yace ba ruwana to ba ruwana din.

Mun yi azumi sha biyar Hafsah suka samu Huta,Washegari Yaya Abdul'Ahad yazo wajen Raliya shi ya wuce da ita Tare da Anum da Laila ta matsa sai an zo mata da ita haka kurum Allah ya hada kaunarta da Anum da taji ma dagantarkar dake Tsakani sai tace daman ba haka kawai take kaunar Anum ba ashe jini d'aya muke da mijinta.

Musty har da kuka akan sai ya bi Anum Dakyar Babansa ya Lallashesa akan zamu je da sallah sannan ya Hakura,Azumi nada ashirin da Biyar sakon Abba na kayan sallarmu ya iso karofi aka kai,Yaya Isa ya kawo min nawa har gida duka da ni da yara.

Har da Babansu,kala biyar biyar,harda na Anum data ke chan Da na Hafsah kenan wasu za'a sake dinka musu Yaya mariya haka aka kai mata nata ita da Yaya Asiya,Bakina yaki Rufuwa na kira Abba ina masa godiya sai yace"Ba godiya tsakanimu Fa'iza duk abunda nayi muku ba komai ba ne, ku ya'ya na ne kamar yadda zan yi ma Nana Fadila haka zan yi muku"

Sai na kasa mgana,Saboda farinciki ya gamamin komai ganin ba na Mama aciki sai na saka kudi na siya mata kala uku har da Hijabi da takalmi ta karba Karo na farko da Mama ta taba godemin bayan nayi mata wani abun alheri..

 Shi kuma Yaya ishaq da nace ya kira Abba yayi masa godiya sai yace"Ba kin kira shi ba?sai na Dagamai kai cikin basarwa yace"Ya wadatar kin hada da godiyata da naki godiyar"daganan ban kara mai mganar ba,na lura ba duka halinsa ba ne ya sauya wani Lokacin rashin Mutumcinsa na nan bai tafi ba,Wannan karon dai mun yi sallah cikin Farinciki da wadata Jamal ya Dawo gida sallah shima nayi masa kayan sallah har da Hula da takalmi,Badariya a kano tayi sallah Tace Hajiyar Dala ta mata kala Daya nima na tura mata kudi tayi guda Biyu ta kara da shi Saboda yanzu ina samun kudi sosai tunda bana taba kudin sana'ata tunda Abba ya karamin jari abubuwa suka daina Cushemin ga shi muna da kayan abinci sosai,wannan sallar ko Anty Binta bata kawo mana komai ba ganin bana neman komai,Naman salla kuma Abba sa ya saka aka siya aka yanka a karofi aka raba mana Nama,Ni kuma na siya mana kaji,sai bayan na siya ma Hajiya ta aiko mana da shi,Sai dai ma muka rika kyautarwa,Ranar sallah na uku naje Karofi ni da yara muka kwana Daya muka Dawo sai kuma washegari naje Gidan su sa'adatu nima tazomin ranar Sallah na biyu,Daganan na sauka gidan Hajiya ana ta fentin gida saboda Biki bayan salla da Sati Biyu ne.

Hajiya tace wajenta zan zauna kaduna sai za'a tafi da Raliya sai na bisu mu tafi ina Dariya ina fadin"Hajiya su da suke jiran mu tun ana sauran Sati daya..?

Hajiya tace"Aa su mariya su je ammh ke kina gidan nan ai Raliya kanwarki ce, ke zaki mata gyaran jiki da Hadin Turaruka'"Na dauka Hajiya wasa take yi sai da Ammi ta kirani tana fadin"Fa'i shikenan sai Hajiya ta mana Haka.? Ina uwar d'iya ammh ana min fin karfi akan ya'yana".

Nidai dariya na dinga yi ban yi mgana ba ina jin Abba na gefe na fadin"D'anki zata gyara ma Amarya fa Maman Nana"

Sai tace"Kuma fa hakane to na d'aga kafa. ammh da sharad'in a Turaran Amarya za'a dibarmin nayi ma Baban Nana kwalliya da shi"

Abba yace"Shikenan kuwa na uwar miji da matar d'a ba"

Ni dai sai dariya nake yi in ka Biye ma Abba da Ammi sai cikin ka ya Kulle Tuni muka shiga shirin Biki,Biki ne na manyan mutane,Balle Abba wannan ne na farkon da zai aurar da Namiji,an aiko da katinan Daurin aure kayattu Abba yace duka jama'ar Karofi yan'uwa na kusa kusa yana gayyatarsu,Har Hajiyar Dala Yaya Asiya ta gayyata ita da suke ta shirin su ita da yan gidan su Ammi ga Nana Fatima a kusa da ita, tunda har gidan juna sun je ina Dutse ina kano.

Hajiyar Dala taga bikin na irin nasu ne tace zataje har kaduna,sai mamaki take yi yadda Lokaci da'ya Gata ya Lullube rayuwarmu yanzu babu abunda ya'yan gata zasu nuna mana muna.

Nima a barayina na gayyaci su Anty Binta da su Anty mahma,da mama ni daman ina gidan Hajiya kamar yadda ta fad'a,Hajiya tamin dinkunan ankon Biki,Kala hudu har da na Lonching din da zata hada na mata zallah,achan kaduna ma su Nana Fatima sun ce duka kayana sun zama Ready na fitar Biki achan zasu yi Dinner din su gabad'aya.

 A na saura sati daya biki Badariya ta Dawo suka fara shirye shiryen saboda gyaran jiki sai suka tare a gidana nan suke kwana,gefe daya kuma ina hadin Turaruka ga zuwa gidan Hajiya ba na ko zaman gida,Abba ya kirani yace na turo yara suzo tunda ni sai ranar Daurin aure,sannan a kaduna za'a Daura auran Raliya gidan kanin babanta Hajiya tace ayi chan yafi sauki kawai,su Goggo duk zasu tafi kaduna ana gobe biki sai na had'a su da yaran suka fara yi min gaba da su Mama su goggo tabi Anty Binta kuma ita da Anty mahma da Halisa direban Anty Binta zai kai su, su Yaya mariya da su Yaya Asiya tuni suna kaduna ana sha'ani da su sai kirana suke yi naji kamar nima nayi tsuntsuwa na ganni achan.

Tun ana gobe biki na tare gidan Hajiya,gidan ba kowa sai Yaya Ishaq da jamal,zasu Daurin aure gobe domin Abba yace yana son ganinsa,mota guda Hajiyar su Raliya ta basu zasu bi tawagan mazan da zasu tafi daga nan katsina. mu ko muna chan muna ji da Lonching,na hadu da manyan mata sosai kawayen Hajiya,Amarya bazatayi walima ba sai ranar Lahadi da yammah bayan an kaita gidanta,Hajiya da ya'yanta ni suka saka kan abinci akwai ma'aikata ammh ni nake nuna musu yadda za'ayi.

Ranar asabar daya daga cikin asabar din karshen mako aka Daura auran Raliya Kasim Saulawa da angonta Abdul'Ahad Usman karaye a garin kaduna a masallaci sultan bello,Ana gama Daurin aure ango da Tawagansa suka nufo katsina inda akayi pinic party dasu da kawayen Amarya adaran Ranar,Washegari sai shirin kai Amarya tun Safe aka shirya Daman tuni an je an yi mata Jere a gidanta acikin garin kaduna zai zauna anguwan Sarki chan yake da gidansa mai kyau.

Amarya su suka fara yin gaba ita da kawayenta da angwaye,mu kuma sai da muka Tsaya muka shirya wasu kaya muka tafi da su,Sai yammah muka isa kaduna,gidan Raliya muka fara sauka chan na iske su yaya mariya da su Nana Fatima sun zo tarban Amarya muka Rumgume juna muna murnan ganin juna, sanye nake da Less din da Hajiya ta dinkamin na yinin ta nayi kyau duk da ban yi kwalliya ba,Da anan za'ayi walima sai aka sauya akace Ndc za'a koma gidan Abba achan za'ayi,gabadaya muka tattara muka koma chan,Hafsah sai wajen walima na ganta ita da Nana khadija sun ji kaya iri daya kamar yan biyu su Anum kuma an saje cikin su Falaq sai dai naji ana fadin Umma haka su Ahmd sun ci gayu suma suna ta wasan su cikin yara sa'aninsu.

 Su Yaya ishaq da mazajen su Yaya Asiya Abba ya hanasu tafiya suna nan tare da shi,Sai bayan isha'i aka tashi Daga walima,aka kuma fara shirin Tafiya Dinner ni dai ina ganin in da ake bikin yan gayu,sai ga shi duniya juyi juyi na gaba ya koma baya.

 Sai ga shi su Anty Binta da Mama ne a rab'e mu kuma mune amara kirjin biki.





*Janafty*





[7/19, 2:47 PM] Hauwa Galadima: *KNKB2015*


*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*

*09069067488*


Kuma daidai gwargwado ba'a wulakantasu ba,an kula da su sosai duk abunda suke so shi suke yi,ba mai hanasu.

 Balle kuma ga Badariya da sune manyan kawaye,Raliya ta mata komai na kayan fitan biki,kawancen su ba irin na sauran kawaye ba ne hatta duka ankunan biki duk Hajiya ta siya ma Badariya,Sai dai kunya ce da nauyi yasa suka koma gefe suna kallon abunda ke gudana.

 Sanda muka zo naga Abba muka gaisa shima wajen Ammi yazo suna mgana,Baya gidan suna Hotel inda bakin sa suka sauka har da su Yaya Ishaq suna chan suma,Abba sai da yayi min tsiyan ido na kenan..?

Ina dariya nace"Abba kanwata na tsaya nayi ma rakiya"

Ammi tace"kuma matar yayanki ba"

Mukayi dariya gabadaya Ammi bata manta ba sai da tamin mganar Turaranta nace nazo mata da shi sannan tace na fita ko ba soso da Sabulu, abunda na lura da shi Ammi macece wayayyiya mai son kamshi da gayu,domin yar gayu ce ta Bugawa a jarida in ba an fad'a maka ba,baka isa kace itace mahaifiyar Yaya Abdul'Ahad ba,Tana ta shiga tana fita ko a jikinta damu da yaranta duka D'aya ta Daukemu.

 Da ita da kawayenta da yan'uwanta suma suna ta shirin zuwa Dinner din Shashen Ammi aka sauke Amarya da Tawaganta,mu kuma shashen Abba gida ne ba ni da gida ba wajen Haduwa da kayan more rayuwa,babban gida mai shashina ba adadi harta Yaya Abdul'Ahad yana da shashensa a gidan. 

 Da zai iya zama da matarsa basu takura juna da su Ammi ba,nan su Nana khadija suka zauna da Kawayensu,dasu Hafsah da aka zama yan matan kd,su Goggo kuma suna Shashen Inno ita da su Baba Ati suna nasu sha'anin.

Muna shashen Abba sai shirin Tafiya ake yi Kaya iri d'aya Suka dink'amana Dukkanmu har da Nana khadija da Hafsah,wani uban su material mai ja da baki,yayi kyau matuka dukkammu dinkin Dogayen riguna suka yi mana,Irin na zamani Fitted,sai head ja,da zamu nada da takalmi ja da Karamar pos har da mai yi mana kwalliya na musamman. yaran kuma daga mata har mazan su shadda Fara aka dinka musu sai akayi amfani da zare ja wajen aiki da kwalliya,Ina kallonsu suna ta shiryawa tuni har an fara yi ma su Nana khadija kwalliya,Da farko kayan naga kamar baza su yi min ba, sai da Nana Fatima ta saka nata ta matsamin nima na sake yin wanka na shirya sai ga shi kayan yayi min cif a jikina kamar an gwadani,na juya na kara juyawa na kalli Nana Fatima ina fadin"Wannan ba irin namu ba ne Nana, sun matseni fa dinkin yanmata ne"

Harara na tayi tana fadin"Ni juya na zage miki zif din riga. Ba wanda yace ga dinkin yanmata da matan aure kaji matar nan"Ina dariya na juya ta zage min,na ja head din ina shirin Daurawa ta Fizge tana fadin"Meye haka.?kai tsaye nace"Daurawa zan yi mana"Da karfi tace"Daurawan ta. Mai kwalliya zata daura miki bayan ta gama miki kwalliya"

Sai na Bude ido Lokaci d'aya ina fadin"Ni za'ayi ma wannan fenten fenten haba Nana mana wannan sai su Hafsah"

Dariya tayi Lokaci d'aya tana fadin"Har su fa'i yau sai sun yi kwalliya"na zata wasa take sai gashi tamin Taron dangi Nana Fadila tace"Muma nan kwalliyar zamu yi fa'i banga abun damuwa ba'

Na marairaice ina fadin"Anty Fadila ban fa taba yi ba, na dauka kwalliya na masu kyau ne da yan gayu"

Sai suka kalleni suna Dariya Nana Fatuma tace"Kaji wani Tunani kuma. kwalliya da gayu na macen data san kanta ne Fa'i,kuma yau ko zaki suma ne sai kin yi kwalliya"

Taruwa suka yi suna ta gayamin amfanin kwalliya ni jinsu kawai nake yi, ko kunshi da gyaran kai da nayi Hajiya ta matsamin da na rakata gyaran kai tace sai an yi min, sannan da mai kunshi tazo tace na zauna ayi min gaskiyan mganan hausawa da suke cewa duk wanda ya gyara zai ga dakyau ni kaina nasan nayi kyau a baya ina Tunanin bakin Fatata  bazai saka lalli ya zauna ba sai gashi ya fito ras da shi,Tabbas na yarda ko kana da kyau ka kara da wanka ni kaina da yanzu na samu sauyin rayuwa Fata ta fara gogewa.

 Ban gama mamaki ba sai da naga har su Yaya Asiya sun sha kwalliya an buga musu Dauri ita da Yaya mariya na kallesu na kwashe da Dariya ina Fadin"Yaya Asiya wai kema ahaka zaki Dinner din.?

Fari tamin ido tana fadin"Kwarai ma kuwa Fa'i bari ma na kira baban Usaini yace min Abba yace suma sai sunje fa"

Ta wuce tana wani juya jiki gabadayammu muka saka Dariya mamakin yadda ta sauya kawai nake yi Yaya mariya ko sai faman duba madubi take yi na kalleta nace"Yaya mariya mata a gidan Manaja"

Ta juyo tana fadin"fad'i ki kara kuma dagani ba kari"

 Kawai sai Nana Fatima ta saki guda suka tafa da Yaya mariya chaa sukamin Dole bayan an gama ma Nana Fadila na zauna nima akayi min kwalliyar zamanin da a baya na Dauka sai a Fuskar mata masu kyau ake yinta,kuma yayi kyau ba irin mu munana kuma bakake ba.

Fuskata naji duk ta Daure,har abun ido aka karamin ina bana so ba na so Nana Fatima tace sai an sakamin,Ina tura baki tayi dariya tana fadin"Sai fa kin zama yar gayu kema Fa'i ga mijin ki na ganshi dan gayu da shi ammh ke baki son gayu"

Yaya Mariya ta tabe baki tana fadin"in dai Fa'iza ne abun haushi yanzu kika fara gani, gabadaya ta maida kanta baya shiyasa har miji ya raina ta ya yi mata kishiya'

Sai Nana Fatima ta Tsaya tana kallona cikin mamaki tace"Fa'i daman kina da abokiyar zama ne shine ban sani ba..?

Sai na kauda zencen da cewa"Kun san fa kari ba kyau a addini"

Yaya mariya tace"Allahu akbar Sayyada"

Da na Dake bana so ne sai Nana Fadila tace kada a sakamin a barmin ido na haka,Sai da aka gama na duba madubi sai naga kamar ba ni ba gabadaya Fasalina ya Sauya na sake kallon kaina na koma na kalle su kafin nace"Wai fuskata ce haka..?

Sai suka kwashemin da Dariya,Nima kaina sai da nayi dariya,ko wajen saka Takalmi an sha Fama dani yayi min Tsini Nana Fadila tace"Ke da ma baki da tsawo fa'i ai na irin ku ne"

Kamar zan yi kuka nace"Ban saba sawa ba. Kuma ban iya tafiya da su ba"Nana Fatima tace"Zaki koya yanzu malama"Haka ta sakamin shi mai igiya,ina tafiya ina neman fad'i Suna min Dariya. 

 Ammi ta shigo tana fad'an ga motoci chan a waje ana ta Daukan mutane goma ta kusa dare yayi sai taga ina tafiya ina Tangad'i salati ta saka Tana fadin"Me zan gani haka Fa'i..?

Ina matse ido nace"Ammi bazan iya tafiya da shi ba don Allah kicesu kyaleni"Ammi tace"To bari kada ki yi kuka ki bata kwalliyan ki.."

Tafiya kuma da takalmi ya zame miki Dole ana mganar gayu fa'i ko ni kalleni Da wanda ma ya fishi"

Tafada tana d'agamin kafarta mamaki ya kamani nata baki ne mai igiya kalan leshin jikinta a bunka ga farar Mace Less din data saka baki ne sai ya haskakata na zata Ammi zata Sassautamin  ne,itama fad'a ta kama min tana fadin"Saki jikin ki ki yi tafiya ba zaki fadi ba. In baki koya ba sai yaushe Fa'i? yanzu in Tafiya ta kamamu na shiga Villah haka zaki je kina yi mana?

Suka ko kwashe da Dariya Nana Fatima tace"Sai mu tafi mu barta"Ammi tace"Aa fa da ita zamu rika shiga ko'ina bame barinta a baya"

Dole zata koya yadda baki da Tsawon nan ai irin takalman ki kenan yarinya"Ina ji ina gani suka hanani cirewa Yaya mariya tace"'Fa'iza fa sai a hankali komai na gayu bata iya ba"

Ammi tace" 

Zamu ko b'ata da ita.Ko ni da nake sauke ku ina gayu na ina Dalili. Shiyasa ban jita tana tashin kamshi ba,kamata yayi yadda kike sana'ar kayan kamshi da jikin ki da Dakin ki sai sun kama kamshin ki, ammh ba ko d'aya"Sai kunya ta kamani na Sadda kaina kasa ammh ita ko ajikinta ta cigaba da min fad'a tana fadin"Mace sai da gyara Fa'iza muma fa duk burga ce,Adon ne ke cetan mu"Tafad'a tana fari gabadaya muka saka Dariya Nana Fatima tace"Ammi to har kishiya fa'i fa gareta..?

Ammi ta saka salati kafin ta mangare ni tana fadin"Ba fad'an yanzu ba ne zama zamu yi,mu yi mata  na musamman wuce muje"

Saboda kada Ammi tayi mgana yasa ban ce komai ba, da naga zamu fita dagamu sai wani karamin mayafi,ance Tuni Yaya Asiya da Nana Fadila sun tasa yara sun yi gaba,Mun fito Falo sai ga ango yasha kamshi sai Nana fatima ta fara kirari yayi Tsaki yana fadin"Ku daman baku tafi ba..?

Tana dariya tace"Tawagan ango zamu bi"Kai tsaye yace"To ku cigaba da jira. Ammi wai ina Abba sai kiran wayarsa nake tana kashe"

Ammi tace"ban san to ina ya tsaya ba. Dazu dai ya kirani yace ga Engr ya sauka daga a kaduna daga Lagos yazo masa murna, bai samu zuwa Daurin aure ba"

Abdul'Ahad yace"Engr din yazo ne Ammi?

Tace"Baka ji me nace ba ne, yazo ammh inaga ya wuce domin Baban Nana yace min Karfe goman daran nan jirgin su zai tashi daga abuja zuwa London zai raka kakarsa ganin Likita"

Kasan tana fama da matsalan koda"Abdul'Ahad sai ya fice yana fadin"Ammi in kin same sa kice ya tabani"

 Mu dai waje muka fita motoci sai kad'an tunda duk sun wuce sai Amaryan da tawaganta su kuma angwaye zasu bi,Allah sai ya jeho mana Mijin Anty Laila uncle Junaid yaje ya kaisu Laila ya dawo Nana Fatima ta Dafe mana shi ya kaimu ni da ita da Yaya mariya Ammi agida muka barta tace za'a kawota.

Wani Hadadd'en wajen Event ne mai girma da fad'i goma ta wuce ammh kamar rana chan muka iske su Anty Binta da Mama sun je suma,su Goggo dai na gida sun ce a raba su da zuwa wani shegantaka da Daddare.

Amir na ganina ya taso yazo kusa dani ya kama Hannuna yana fadin"Umma kin yi kyau"

Nayi dariya ina shafa kamshi nace"Kai ma haka Amir dina."

Su Anum suna tare dasu Hafsah da Nana Khadija kowa ya kama bangaran da zai zauna muna sai muka kama Tebur d'aya dukkanmu mu Bakwai har da su Hafsah su Laila suna nasu bangaran,Gabadaya ji nake yi a takure saboda shigar jikina ga uban Takalmi Kallon da su Mama suke min ne yayi min yawa na tashi naje na gaishe su Allah ya taimakeni ban Turgud'e ba.

Anty Binta haka take kallo na kamar na Sauya mata har sai da tayi mgana da cewa"Lalle Fa'iza kece haka..?

To kada dai ki manta kina da aure ba Budurwa bace ke'"

Ban ce mata komai ba, sai ga Nana Fatima tazo tajani muka yi gaba tun ina Dari Dari har dai na saki jikina ina ganin zuwan su Yaya Ishaq shi da Jamal sai mijin Anty mariya,da wasu da ban sani ba,kuma a Tebur din bayan mu suka zauna ina da Tabbacin basu gane ni ba.

Ammi tazo ita da tawaganta daga ita sai Tawagan amare da angwaye.

Matuka wajen ya hadu bazaka ma gane Dare ba ne,an ci an sha an sha rawa sannan an yi nishadi,Badariya ta bada Tarihin Amarya wani daga cikin abokan ango shima ya ba da Tarihin ango.

 An kira kannen ango mun fita mun yi liki Daman Ammi ta bamu yan Dubu sabbi muka  zubda da su,ana bikin Duniya in da ake yi jama'a haka muke taka kudi,Sannan an bamu fili mun rausaya Nana Fatima in na yi kokarin Sulalewa ta rikoni,ni na samu na yafa mayafin su basu yafa ba a Hannu suka Rike.

Mun koma wajen zaman mu sai igiyan takalmina ya warware na duka in gyara ina Dagowa muka hada ido da Yaya ishaq sai naga ya kauda kai kamar bai gane ni ba,sai na mike na isa gabansa cikin wani irin takun da bansan na iya ba kuma abun mamaki Tsab na saba da tafiya da takalmin kafata ina zuwa gabansa nace"Hy.."

Ina mai kura masa ido na make murya yasa bai yi Saurin Dagoni ba. Jamal baya wajen ya koma chan Teburin gabammu.kauda kai yayi yana wani basarwa zan kara mgana sai ga Amir yazo yana fadin"Umma.."

Yaron nan shi ya Tona min asiri a Firgice ya Dago yana kallona yana kuma kallon Amir kafin yace"Bangane ba..Wata Umman..?

Amir yace"Daada Umma ce fa baka ganeta ba ne..?

Yadda ya saki baki da Hanci yana kallona ne yasa na bushe da Dariya ina Talle ma Amir keya Lokaci daya ina Fadin"ji yaro ya batamin shiri na"

Amir shi kanshi Dariyan yake yi ganin yadda Babansa yayi daga sama har kasa yake kallona,daman shi bai so zuwa ba Abba yace sai sun zo tunda suka zo yake ganin yan mata kenan har su Yaya Asiya bai gane ba, tunda ya Dauka yaran yara mata ne kawai a wajen.

 Kirjinsa sai duka yake yi yana kallona Amir da ya ga haka sai ya Sulale ya barmu kujeran gefensa naja na zauna ina fadin"Samari."

Sai kawai ya miko hannu ya kama Hannayena duka Biyun yana Fadin"Fa'iza wai don Allah da gaske ke ce..?

Sai na kara saka Dariya kawai ban tsammani ba sai naji saukan sumba a saman bakina cikin wani yanayi yace"Kin yi kyau Fa'iza ashe ke mai kyau ce ban taba sani ba.."?

Ina shirin bashi amsa naji Tafi a bayana ina juyawa Naga Nana Fatima da Sauri na kwace hannuna ina Hararanta karisowa tayi gabanmu tana Dariya Lokaci d'aya tana fadin"Allah ya kamaki wato kina nan kin zo gwada ma miji kwalliya ammh nan ina fama dake kin ki Tsayawa ayi miki,Ranka ya dade a biya ladan kwalliya domin sai dakyar ta amince akayi mata"

Ba musu ya saka hannu a aljihu ya zaro kudi ya damka mata,suma Abba ne ya basu yace na liki ne,Tako amshe Abunta tana fadin"To yanzu sai ka mora kallon ka..Fa'i."

Ina juyowa ta kashe min ido tayi gaba na bita da dariya,kai tsaye nace"Ina ka samu kudin tukwaici..?

Cikin wata murya yace"Abba ya bamu wai na liki ni ai ga babban liki na nan"yafad'a har yana wani lashe baki yar Dariya nayi cikin yangar da wlh bansan na iya ba,kai wani lokacin bakin mutane na taimakawa wajen Dakushe tasirin da muke da shi a Rayuwa, yanzu da na samu masu yabani da Daidaitani da Sauran mata har na fara tunanin to dame suka fini..?

 Kiri kiri Yaya Ishaq yaki barina na matsa ko'ina har yana fadan na saka karamin mayafi,rai bace ya kalleni yana fadin"Wato kyale kin da nake yi yasa kika maidani sauna ammh bari mu koma gida zaki shiga hannu"

Ina jin haka na shiga Taitayina,Sai da za'ayi Hotuna Anty Fadila Dakyar tazo ta jani shima sai da tasha korafinsa sai bina yake da kallo barin ma takalmin kafana a ransa bai san sanda ya furta"Jar uba.."

Fa'iza fa ta tashi kan sa ,ya so yayi wauta da farko ballatana da kayan suka kamani,gabadaya Shafe dina ya bayyana kamar ban haifi yaran nan ba Tuni kishi ya kamashi muna Hotunan kamar ya fizgoni ya rumgume haka yake ji bamu muka bar wajen ba sai Dayan Dare Shima ba'a tashi ba nan muka bar Amarya da sauran mutane Yaya Ishaq bai sauke ajiyar rai ba sai da muka tafi ba shi kadai ba duk wanda ya ganni sai yace Fa'iza kin yi kyau barin ma Badariya juyi goma sai tace"Kai matar yayana tafi kowa a wannan bikin"

Bamu san yaushe suka dawo ba sai da Safe su Hafsah sukace sai uku na Dare araina nace lalle kaduna bariki.

 A ranar  muka raka Raliya dakinta Dangin Hajiya da kawayenta suka wuce bayan sun damka amanarta ga Ammi da su Inno,Mama da Anty Binta a ranar suka tafi bayan Ammi ta hada musu sha tara na arziki tare da Jamal suka Tafi Abba dai ya Tsaida Ishaq yace yana so zai yi mgana da shi. Domin yadda ya samu labarin a bakin Goggo Mijina baya aiki yanzu nice duka hidomomin gida shine yake so ya gansa su Tattauna.

Kuma in dai ba wannan Lokacin ba bai kuma da Sauran hutu in aka gama Bikin.

Hajiyar Dala bata zo ba rasuwa akayi mata, Yayan megidanta ya rasu dole ta Tsaya ammh taso ta zo ta bama idanuwanta abinci,sai dai tagani a waya tunda Badariya nata zuba Hotuna yaran ta na Nuna mata,Hajiyar Dala tayi mutuwar zaune da taga Hotona da Badariya ta saka a kasan Hoton ta saka"Matar yaya na tafi ta kowa. Anty Fa'iza"

An ce har Jamal ya Dauka shima ya saka a Status d'insa, gogan bai da waya bai san wainar da suke toyawa ba,Hajiyar Dala aranta sai da tace kamar an yi min wankin in ji nice na koma wata classis haka a baya tasan ni yarkace yarkace kamar yar Gudun hijira,ammh yanzu kuma taga na zama wata mai aji da Daraja.

 Inaga ta wayar Jamal Zainab tagani ta tambaye shi yace ina kaduna muna Biki sai ta kirani tamin Allah ya sanya alheri kai tsaye kuma tace min"Ashe kuna da yan"uwa a kaduna.?ni ko sai nace mata eh na kara da fadin"Kanin Mahaifiyarmu ne mai rasuwa"Sai ta jinjina kai tace"Allah sarki"

ba mu jima muna wayar ba,bayan tambayan yara da gida muka yi sallama.

 Zuwa talata kaf gida ya watse hatta Goggo ta koma karofi sai mu har Yaya mariya tanan sai gobe zata tafi Yaya Asiya kuma aranar suka tafi da yammah tabi yan gidan su Ammi daman tare suka iso,Amarya na gidanta suna hutawa ita da ango Badariya na gidan tare dani zamu koma da yara.

Wasa wasa ina neman yin Sati a kaduna Gida duk ya watse,Nana Fatima ta koma Dutse,hakama Anty Fadila ta koma lagos,Abba ne ya Tsaidamu ni da Yaya Ishaq shiyasa bamu koma ba shima kanshi ya koma Office sannan ga wannan Hayaniyar Biki shiyasa bamu samu zama ba. ammh nasan Ba domin Yaya Ishaq na ganin girman Abba ba,bazai zauna ba,sai korafi yake min shi ya gaji da zaman wuri d'aya da cewa yayi zai tafi ya barni sai na Taho daga baya nace ya dai Tsaya yaji me Abban zai ce masa.

 Sai Ranar Alhamis da Daddare suka samu zama da Abba. Tunda bikin ya watse ni nake yin girki,Umarnin Abba ne har kayan hadin zobo da kunin Aya an siyo da sauran lemuka ina ta Shagwabasu da cimata.

To ranar ma daddaran Lemun abarba nayi musu,sannan na soya musu kaji nayi pepe din su sai tashin kamshi yake yi,daman Tuwon shinkafa nayi miyar agusi da naman rago an kai musu sai Ammi tace na bi su da wannan su dora daga baya.

Sanye nake da Hijabi mai ruwan kasa har kasa Nana Khadija ta Dauko min Voul din kazan muka shiga Falon Abba sun ware suna ta Hira da Yaya Ishaaq Abba ne fa da ba ruwansa.

Har kasa na duka ina gaida Abba ya amsa yana fadin"My Dota me muka kara samu ne.?

Ina mirmishi nace"Abba pepe chikchen ne sai lemun abarba"

Abba ya bude kamshi ya Dakesa sai ya lumshe ido yana fadin"Gaskiya Ishaq kayi hakuri ku kara ko Sati d'aya ne nima na Mori yata da girken girken nan nata masu dadin Tsiya"

Yana mirmishi yace"Sai ayi haka Abba?

Abba ya kalleni kafin yace"Fa'i Allah ya kawo kudi Abba ya bude miki katon gidan abinci.."

Ina Dariya na amsa da Ameen khadija na gefe tace"Abba ga Vacany na farko kun fara samu nasan albashin zai yi tsoka"Abba yace"Aa sai mun yarda da kwarewarki bama son masu son jiki"Sai ta fara dira kafan Shagwaba da Sauri yace"Ni fa ba da nake ba"

Yadda yayi ne yasa muka Dara mikewa muka yi muka fice yana sakamana albarka.

Bayan sun taba kazan sun sha Lemun Abba ya koma ya kishingida yana fadin"Fa'iza ta shagwabani da abincinta gaskiya Maman Nana ta kara koya kafin tatafi in baso take na rika barin mata kayanta ba"

Ishaq yace"Baza'ayi haka ba Abba"

Abba yace"To a san yadda za'ayi dani Allah"

 Haka dai suka yi ta barkwanci.

Abba baya so ya fara mai mganar kai Tsaye kada Ishaq din ya Dauka da wata manufa sai ya fara sako mai mganar aikin Gwamnati suna hira cikin Hiran ne Abba ke tambayansa ina yake aiki kansa na kasa yace"A baya dai nayi aiki da Hukumar Tattara Haraji ta kasa ammh yanzu bana aiki da su bisa ga wani abu da ya faru"Sai Abba ya gyara zama kamar bai sani ba yace"Subhanallah me ya faru..?kai Tsaye kuma Ishaq din ya warware masa komai, Abba ya jinjina kai ko ni bai yi mganar dani ba.

Yaya isa daya fadamai sai ya Tattauna da Goggo ta kara yi mai bayani ammh yanzu yaji wasu a bakin Ishaq din.

Kai Tsaye Abba yace"A abuja kace kayi aiki da su ko..?

Kai ya gyada yana fadin"Eh Daga katsina chan suka maidani nafi shekara Bakwai ina aiki dasu a wajen"Sai Abba ya muskuta yana Fadin"Nako san chairman din ku na wajen. Dr.Lawal Bako zan kirasa ko zai iya yin wani abu akai,ai bai kamata a bar shi haka ba, sai a tsananta Bincike har a gano gaskiya"

Da Sauri Yaya Ishaq yace"Kasan shi ne Abba?

Abba yace"Yes Tare muka yi Mastering Degree din mu a Buk kano Shekarun baya"

Sai Yaya Ishaq ya murmusa kafin yace"To ai surukina ne. Ina auran yarsa Zainab"

Abba ya ware ido kafin yace"Au daman kana da wata matar ne bayan Fa'i.?sai ya gyad'a mai kai cikin Mamaki Abba yace"Ikon Allah to tana ina ban taba ganinta ba..?

Kai Tsaye yace"Tana chan Abujan Abba.."

Abba sai ya kasa mgana ya Dauko wayarsa yana fadin"Ammh kuma duk da wannan dangantarka bai saka an tsananta bincike ba? domin daga gani kamar Trap ne aka had'a maka acikin kuma ma'aikatan naku ne"

Yaya Ishaq yace"Gaskiya ba'ayi ba. Lokacin dai an ta fad'i tashi Saboda Shigar EFCC kan mganar"

Abba yace"Suma EFCC din ina da wanda zan kira kan mganar ammh bari na fara kiran Dr.Lawal din ina da lambarsa mukan taba juna Lokaci bayan Lokaci"

Kai tsaye ko ya lalubo lambarsa ya Doka masa kira ya kuma sakata a amsa kuwwa kira uku ana hud'u ya Dauka cikin Dariya Dr.Lawal yace"Kaga Matatar mai da kanta ba Sako ba. Allah ya taimaki Engr"

Abba yayi mirmishi yana Fadin"Dr bako kana lafiya..?ya iyalai..?

Shi Dr.Lawal yaje ya karo karatu ne har yazama Dr,shi kuma Abba bai yi ba,aammh dukkansu Chemical Engerniaring suka karanta a makaranta.

 Bayan sun gaisa Abba yace"Kai ashe mun hada suruki d'aya bamu sani ba..?Dagachan Bangaran Dr.Lawal yace"Suruki wani surukin nawa kenan..?

Abba yace"Suruki nawa gareka..?

Dr.Lawal yace"D'aya mijin Zeey ne, Ishaq dan katsina ne"

Abba ya yi dariya kafin yace"Shi fa. Nima ai yana auran y'ata"

Sai Dr.Lawal ya mike daga kishingid'en dayake yana fadin"Wata y'ar taka Kuma Engr.?

Abba yace"Sunanta Fa'iza abokiyar zaman ita yar taka kenan"

Sai ya mike tsaye a razane yana fadin"Dama yar ka ce ita..?

Abba yace"Diyar kanwata ce mai Rasuwa. Ga ni ga Ishaq din sun zo Daurin auran Abdul'Ahad ne muna Hira sai muka tabo bangaran aiki, To yana gayamin a office din ku na Abuja ya taba aiki nace na sanka shi kuma yace ai surukin sa ne kai"

Dr.lawal ya share zufa yana fadin"Ikon Allah.."

Abba yace"Kaji fa."

Dr.Lawal yace"To ai baka gayyace ni bikin yaron namu ba".?

Abba yace"Kaina yayi zafi ne kuma kasan mun jima bamu yi mgana ko ta waya ba"

Daganan suka cigaba da Hira Abba ya Sako mganar Ishaq da Tunanin a saka Kwamitin Bincike a gano bakin zaren mana Dr.Lawal yace"Ai hukumar EFCC ke cikin mganar Engr shiyasa"

Kai Tsaye Abba yace"Kada ka damu ni dai ka nad'a kwatimin bincike ta bangaran ka, ni kuma zan yi mgana da megidana Engr mahaifinsa Shine Chairman na EFCC a yanzu haka so nasan zai taimaka mana insha Allahu"

Dr.Lawal a ransa yace aiki ga mai kare ka,Sun dad'e suna mgana yace zai nada masu binciken tunda zai shiga mganar nan take ya kira Megidan nasa bai same shi ba sai ya kalli Ishaq yana fadin"Zan kirasa kuma ina gayamai Cikin Satinan za'a dauko Fayel dinka a Sabunta bincike da ikon Allah za'a wanke ka"

Yaya Ishaq nata godiya,ni bansan me suka Tattauna ba. washegari Direban da Abba ya bamu aka maidamu gida a jeep dinsa ni da yara da Badariya da Hafsa da zata koma makaranta booth din mu cike da kayan Biki.

Bai fad'amin yadda suka yi da Abba ba, sai bayan kwana Biyu da muka natsa sannan yake gayamin nayi murna sannan nasan tabbas tunda Abba yace zai shiga mganar an yi an gama.

 Har Mama ya fad'amawa sai addu'an Allah yasa adace take yi,da fatan a gano gaskiya.

 Ko da aikinsa bazai dawo ba,ammh yana da kyau kada sunanka ya zauna a matsayin barawon Gwamnati.





*Janafty*

[7/19, 2:47 PM] Hauwa Galadima: *KNKB2016*


*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*

*09069067488*


Wannan shekaran data zagayo. bamu sha wahalan rayuwa ba,saboda Abba ya tsaya mana,shi ya biya kudin makarantan yara da sauran bukatumu na yau da kullum.  hatta da kayan abinci ya cike mana wannan bangaran,Yace komai muke bukata mu kirasa bamu da damuwa Ishaq kuma daman ya fad'a masa shi a D'a ya dauke sa ba suruki ba, shima uba yake garesa kamar yadda yake uba gareni

 Shikenan shima sai ya saduda yana karban komai da girmamawa,Mama ma haka tana ta min godiya,ni ko nace mata bakomai,Badariya ta koma kano wajen Hidimar kasarta Jamal ma ya koma makaranta sun shiga Semister karshe a makaranta.

Gefe daya ina cigaba da sana'ata ban Dakata ba,Sannan ayyuka sun karu min yanzu saboda akai akai nake hada Turaruka yanzu daga chan kaduna da kano ko'ina akayi mganar Turare sai Ammi tace Fa'in mu tana Had'asu masu kamshin Dadi,in nayi sai dai na bama Hafsah ta kai tasha a saka a mota kuma kudin aikina cas a Hannuna,Allah yasa ma Anum na gida ta gama primary zata shiga JSS Section.

 Muna waya da su Nana Fatima kusan kullum muna sanin Halin da juna ke ciki,Yaya Ishaq yaki ya gyara wayarsa sannan yaki ya siya wata. Matarsa sai kirana take yi ni na zama alkali a Tsakaninsu wani Lokacin sai ta kira baya gida sai ya barni da gayamata ya fita,gajiya nayi ranar muna zaune da Daddare shi ya gama yi ma yara karatu sun kwashi Littafan su zuwa Daki,Hafsah na kitchen tana Dafamin zobo wanda zan yi na safe da shi,ni kuma ina gefe zaune a kasan cafet,shi ko har ya koma ya kwanta a saman kujera.

Dagowa nayi ina kallonsa kafin Nace'"Na manta. matarka ta kira d'azu baka nan"

Yana ji na bai yi mgana ba sai na tura masa wayar gabansa ina fadin"Gaskiya ka siya waya. ko ka gyara taka, nagaji da Damuna da matarka take yi, kana kuma barina da bayani in baka gida"

Sai alokacin ya bud'e ido yana kallona cikin shakewar murya yace"Ba zan siya ba sannan ban yi ra'ayin gyarawan ba"

Ban yi mamaki ba daman nagansa yau sai a hankali yana jin yan tsiyan nasa, sai na rabu da shi aiko ko tashi bamu yi a wajen ba sai ga kiranta na leka naga itace na mike na fice daga Falon zuwa tsakar gida ina faman kaye kaye ban sanin masa ba ko sun yi mgana.  ni dai da nadawo naga wayata nan saman kujera na Dauki kayana na wuce Daki.

Abunda na lura Zainab da mahaifinta sun sauko suna neman sulhu da Ishaq shi kuma yaki basu wannan damar Saboda bayan kwana Biyu ta sake kirana baya nan domin yakan d'an fita ya mike kafa ina ji a gefenta tana mgana tana fadin Daddy wai baya nan ya fita sai naji an yi mata mgana kafin tace min in ya dawo nace ya Kirata Daddy zai yi mgana dashi.

Da ko ya dawo na bi shi har Daki na Fad'amasa sannan na bar masa wayan a wajensa sai gashi ya biyoni nima har Daki ya mikomin wayata yana Fadin"Ki daina kawo min wayar nan Fa'iza wai sau nawa zan fad'a miki ne.?

Sai na bude baki ina kallonsa cikin mamaki nace"To in ta kira sai nace mata me..?kai tsaye yace"ki fad'a mata gaskiya bana son mgana da ita"

Nima kai Tsayen nace"Tace ka kirata Daddy na son mgana dakai"

Yadda ya wurgamin wayar ya fice a Fusace ne yasa sai da nayi Dariya Allah yasa wayar kan gado ta fad'a,Na dauki wayata ina fadin"Bani na kar zomon ba"

Zainab bata barni ba, ta rika addabata da kira kunya sai na rasa me zan ce mata sai taga kamar ni ne bana son had'asu,Gajiya nayi nace gwara na fito nayi masa mgana Tattara yaran nayi zuwa Dakin Mama harda Hafsah saboda chan yafi kusa da tsakar gida yafi iska,Kayan sa da na wanke masa na ninke masa basu kawo wuta ba,ballatana na goge masa,Sai na Tattara na kai masa Dakinsa tun da ya shigo ya shige ciki sannu da zuwa ma dakyar ya amsamin Abincin sa Anum na bama ta kai masa ko da na shiga yana wanka domin naji karan saukan Ruwa a makewayi.

Sai na sauke kayan Hannuna saman katifarsa na zauna gefen katifar ina jiransa bai jima ba ya fito da Dogon wando a jikinsa,Kansa na digan ruwa yana gogewa da karamin Towel,Sai da ya tsaya yana kallona alamun yayi mamakin ganina ni kuma ganinsa ba kaya yasa na mike ina fadin"in ka shirya sai na dawo'

Ban jira cewarsa ba na fice shima bai Dakatar dani ba,Na koma Falo ina yan kaye kaye yara dai ba'a rabasu da Lalata waje ko sau goma zaka gyara shi kuwa,ba jimawa sai ga shi ya fito da jallabiya da farantin abincinsa a nan falon ya zauna ya ci abincin ya sha ruwa,sai ya koma ya kishingid'a yana Hamdala ni kuma falon na Tattara domin ina taka datti Musty ne yayi sharan,ba domin ya share dakyau ba.

Ina ta jira ko zai ce me nake son fadamai sai naji yayi kamar bai ma ganni a falon ba,Sai na samu gefen kafafunsa na zauna ina fadin"Mgana fa nake so mu yi"

Kai Tsaye yace"kunne ke ji ai"

Sai na bude baki zan yi mgana sai na Rufe saboda ina tunanin bazai karb'i mganata ba Sai ya dago yana kallona kafin yace"Uhm ina jin ki"

Sai na dukar da kai ina Fadin"Tsakani ga Allah baka kyautawa abunda kake yi"kai tsaye yace"Da na yi me kuma..?

Ina gyara mganata nace"Kan mganar Zainab mana ka barni ina mata karya. Haba don Allah baka je bafa tun zuwan nan da kayi kafin azumi,Itama ai tana da Hakki a kan ka, kuma Allah zai tambayeka akan hakan ka dauki waya ka kirata ku yi mgana don Allah"

Kamar bazai ce komai ba har sai da nace"Kaji.."

Sai ya gyara zama kafin ya mike ya zauna dakyau yana fad'in"Kina bani mamaki Fa'iza wai wani hakki kike mgana..?ke sau nawa ina zuwa wajenta na tare kuma tasan hakkin ki na shiga ammh bata taba min mganar naki Hakkin da ke kaina ba, sai ke ki bi ki dameni Haba."

Ya karishe fad'a yana Tsareni da idanuwansa da suka fara shigewa Ciki,sai na sunkuyar da kai ina Fadin"ni ba ruwana da wannan. Abunda na sani ne nake gayamaka kai ma nasan ka sani,Tunasar dakai nake yi ciki fa gareta tana Bukatar kulawarka"

Kai Tsaye yace"ke ciki nawa kika Dauka kika haifeshi batare da kulawata ba..?

Sai na kasa mgana kafin nayi mirmishin takaici nace"Ni sunana Fa'iza ni ba yar kowa ba ce. sannan ni ba yar gata bace Fa'iza ba Turanci komai nata zero ne Zainab kuma mai kyau ce yar gata yar Dangi tana da ilimi tana jin Turanci sannan kowa na sonta, kaga kenan Tsakanina da ita akwai Tarin bambamcin da ko a wajen Daidaito na miji bazamu zo Tsara d'aya ba".

Ina kallon cikin Idanuwansa na fadamai haka sai kawai ya rausayar dakai yana fadin"Ashe bazaki bar wannan mganar ba Fa'iza..?baki manta komai ba kenan..?

Ko daman kin fad'ane kawai baki yafe min ba..?

Da Sauri nace"Wlh na yafe maka duniya da Lahira"

Da Sauri ya Tareni da fadin"To me kike son nayi ne ki daina damuna da wad'anan mganganun ne"

Kai tsaye nima nace"ka Saurari zainab sannan kaje ka dubata tana bukatar kulawarka"

Sai ya kankance ido ya mike yana fadin"To bazani ba. Nace bazani ba,Sai ki sani naje dole..Haba mata kin bi kin dameni..?zaman ki nake yi a gidan da zaki rika min kora da Hali.?na riga nayi rantsuwan da bazan kara bin Zainab ba, in tana so na tasan inda nake zata Biyo ni. kuma kin ji ma na rantse bazaki sakani yin kaffara ba. Ba ruwanki in ta kara kiranki kada ki sake d'aga wayarta Umarni ne na baki ba Shawaran ki nake nema ba Fa'iza"

Ya karishe fad'a yana kureni da ido,na bude baki zan yi mgana ya saka min yatsa a saman bakina yana fadin"Shii..Mu rufe babin wata zainab mu yi mganar mu Fa'iza ina mganar mu ta kwana..?baki ga duk na galaibata ba ne saboda rashin ki..?

Kai Tsaye nace"Shiyasa nake so kaje inda zaka samu abunda kake muradi"

Sai kawai ya mike tsaye yana Nuna ni da yatsa cikin bacin rai yace"Rashin kunya zaki yi min Fa'iza don kinga ina Lallaba ki ko..?ko karfi na saka miki Bani da laifi Saboda ke Halaliyata ce. ina binki a Hankali ne Saboda nayi miki laifi ba domin kin fini iko da kanki ba"

Mamaki ya kamani kamar zan yi mgana sai na fasa sai kuma ya Saussauto ya koma ya Duka gabana ya Riko Habana ya dago fuskata yana Fadin"Don Allah Fa'iza ki manta komai mu bama auran mu wata Dama nayi miki alkawarin bazaki kara kuka dani ba don Allah. Wlh na wahala na fara susucewa"

Ya fada lokaci d'aya yana langwabe min kai kamar karamin yaro,sai nayi wuf na kwace fuskata na mike shima sai ya mike zan gudu ya rikoni kafin nayi wani motsi ya kamkameni a jikinsa duk mutsu mutsu na na kasa kwace kaina sai na Saduda kaina ya Dago yana kallon cikin Idanuwana yace"Saboda kin ga ina kyale ki ko..?ni kuma sai na bude baki zan yi mgana, sai kawai naji ya Had'e bakina da nasa waje daya ya fara sumbatata lokaci daya yana kara kaina da Hannayensa a cikin jikina. duk iya kokarina na kwace kaina na kasa tun muna Tsaye har muka zube saman kujera yana Jagwalgwalani fargabana D'aya kada wani cikin yaran nan ya shigo gashi yaki barin bakina ballatana na yi masa magiya sai da ya maidani Tubus ko yatsana ban iya dagawa, Saboda yadda Hannayensa suka Ladaftar dani,Mganar Ahmad muka ji daga kofar daki yana kiran"Umma.."Umma"

Shi ya ceceni zaraf ya tashi daga kaina Daman doguwar rigace ajikina ya Dagemin ita har wuya,saboda bala'i shi ya saukar min da rigan yana kallona takaici da bakinciki suka tasomin,Kallona yayi cikin yar dariya kafin yace"mganin ki kenan. na lura ni nake kyaleki"

Daga haka ya wuce dakinsa yana Dariya sai hawaye suka zubomin nayi Saurin sharewa,saboda shigowan Ahmad yana fadin"Umma barci nake ji"Cikin kasala ina share hawayena nace"je kayi fitsari ka kwanta"

Daga haka na mike na shige Dakina ina share kwallah kamar wacce aka daka kan gado na fada ina cigaba da kukana abu d'aya ya tsayamin a rai in ya cigaba da min haka watarana zai karyamin lagona kuma faruwar haka kamar rugujewar Burina ne.

Kuma ni bazan bari hakan ya faru ba,Wannan kudirin nawa ya Dade a raina cika shi tamkar wajibi ne.

Bansan adadin da na dauka ina kuka ba sai da naji shigowar su Hafsah naje na wanko Fuskata,nazo na kwanta Na rufe ido da suka shigo sai suka yi tsammanin nayi barci nan ko idona Biyu,Har suka yi shirin kwanciya suka kwanta,ni kuma na kasa barci ina Tunanin yaushe ne mafitan da na Dad'e da neman ma kaina zai cika..?

Shin zan iya yin abunda nake hasashe ko ba zan iya ba..?

A haka har barci ya kwasheni,Sai chan wajen ukun dare na tashi nayi alwala na fara Nafila bayan na idar na Daga Hannuna ina addu'ar Allah ya bani juriya da kwarin gwiwa sannan kada yasa ya'yana su zama raunin da zai sa su shiga Tsakanina da Burina.

Washegari Fuskata a Had'e na tashi shi kanshi ya ganni ko gaishe shi ban yi ba shine yace"Ina kwana Anty Fa'iza"

Kallonsa nayi na basar na cigaba da aikin gabana sai ya kwashe da Dariya yana fadin"Wai fushi kika yi..?zaki yi ma mai Dalili yarinya"

Ina jinsa nayi masa banza Da rana Zainab nata kirana sai na rasa ya zan yi da ita.?Sai kawai na dauki wayar na tafi Dakin Mama yana ko kwance kan kujera Mama na zaune a kasa suna Hira yanayin yadda na shigo yasa Mama ta kalleni tana fadin"Fa'iza lafiya..?

Shima sai ya sakamin ido yana nazarina Gabanta na duka na ijiyemata wayar ina fadin"Mama ki masa mgana kila ke yaji mganarki"

Matarsa ke damuna da kira shi kuma in na kai masa sai yak'i mgana da ita. Har ga Allah mama bana so Zainab taga laifina,sai taga kamar ina mata Tsakani da mijinta ne"

Mama sai ta kallesa tana fadin"Shi ina wayarsa ne..?

Kai tsaye nace"Bai gyara ba kuma yaki siyan wata. saboda yasa matarsa ta rika jin Haushi na"

Sai Mama ta Rausayar dakai kafin tace"ka kyauta. Tashi kije Fa'iza zan yi mai mgana"

Na ko mike na ficewata ban ko kallesa ba,inaga Mama tayi mai fad'a yasa ya dauki wayar suka yi mgana,washegari kuma da Safe wajen sha daya sai gata Direba ya kawosu ita da yara,Na karbeta hannu biyu kamar yadda na saba kai Tsaye wannan karon Dakin mijinta ta sauka yana dakin tana zuwa ya shuru Takalminsa ya fice ya'yansa kawai ya Kula ga cikinta har ya fitio ta kara kiba kamar ba ita ba.

Bayan na gama abincin rana munci muka zauna zaman Hira a manganunta na fahimci ita kaddaranta Soyayyan Yaya Ishaq ne shine Rauninta Kuma mahaifinta na kaunarta bazai so abunda zai sosa mata rai ba.

Kai Tsaye ta kalleni tana fadin"Maman Amir Honey yaki ya yafemin laifin da ban ma aikata ba. Daddy mu kad'ai ya Haifa Dagani sai zuzu komai muke so a duniyan nan yana bamu shi baya so yaga muna wahala ganin yadda kwanakin chan nayi ta fama da Laulayi ne yasa yace a cire ciki ammh da nuna bana so ai bai kara mganar ba. meyasa shi Honey bazai sauko ba Har Daddy fa ya so yaje chan su yi mgana yaki ya Saurareni,yanzu haka Daddy na chan ya kafa kwamitin Bincike a ma'aikatarsu kan Case dinsa ammh duk bai gani ba yanzu nazo ko kulani bai yi ba"

Sai Hawaye sharr sai ta bani Tausayi,Ashe an fara binciken ni bama mu yi mganar da Abba ba. Tunda yace min bai samu sun yi mgana da Engr din ba har yanzu saboda baya kasar bai dawo ba,Ina kallonta tana kuka,sai a raina nace ita kuma nata kaddaran kenan..?tana son shi Kuma Dole Mahaifinta ya barta ta biyo abunta take so in har shima yana son abunda yarsa ke so.

Lallashinta na dinga yi ina bata baki ta kara kallona tana fadin"Wlh maman Amir ina cikin wani Hali Cikin nan sani Son kasance da shi yake yi. ammh yaki Saurarena a kwanakin baya kamar zan yi hauka haka nakeji,saboda yanayin jikina yasa sai da na samu sauki na taho"

Na Tausaya mata saboda haka nayi fama da wannan sha'awan Lokacin cikin Ahmad ammh ban samu ba,Domin Yaya ishaq bai saurareni ba akwai ranar da har kuka nayi masa yace shi baya cikin mood din ya gajiye ya Dawo bazai iya min wani amfani ba, ranar kamar zan yi hauka naji kamar na Mutu da addu'a da Taimakon Allah sai da cikin yayi kwari komai ya lafa tsakani ga Allah na Tausaya mata matuka shiyasa na Rike mata Hannu ina fadin"kada ki damu zai sauko in sha Allahu"

Tana sharan kwallah tace"Yaushe zai sauko..?ko fa kallona bai yi ba..?

Don Allah ki yi masa mgana ki tayani basa Hakuri"Sai na kasa mgana kawai ina kallonta ina zan kara mgana nima ta kwabemin Saboda na lura da yadda nake masa mganarta alokacin yake kokarin nuna min nima ai matarsa ce.

Ni dai ina ta bata baki ina fad'amata zai sauko cikin hakane yasa nace"To kiyi masa abunda yake so ki bar aikin nan Maman Fadil sai ya sama miki anan ki dai dawo kusa da shi hakan zai fi"Sai tayi shuru kafin tace"Daddy ne ya hana fa. Ammh wlh naso haka tun da na Fahimci bazan iya zama nesa da shi ba"

Ni ko sai naga na samu damar da zan gayamata gaskiya sai na gyara zama ina fadin"Mahaifa suna da iko a kanmu ne idan muna gabansu. ammh da zarar sun aurar damu mun bar karkashin ikon su mun koma karkashin ikon Mazajen mu,Ki gane wani abu shifa miji ba abun wasa ba ne yana da cikakken iko akan ki Zainab. Yafi mahaifinki iko akan ki, in yace kada kiyi abu kika yi Allah zai yi Fushi dake in ransa ya baci,ko da mahaifinki kika sabamawa dalilin Umarnin mijinki Allah bazai kamaki da laifi ba,a ko'ina Umarninsa na saman na kowa in dai a kanki ne"

Sai tayi shuru tana kallona alamin bata san haka ba ni ko sai na cigaba da Fadin"Annabi muhammad Salallahu alaihi wasallam ya fad'amana in da Allah zai wajabta Sujudda Tsakanin mutane da ya wajabta Sujuda ga mata zuwa ga mijinta.Saboda a nuna Daraja da girman miji ga matarsa"Sai ta waro ido tana fadin"Yanzu duk ina cikin Fushin Allah ne Maman Amir..?

Sai na girgiza mata kai ina fadin"Cikin Rashin sani ne. Shi kuma Allah bai kama mutum da laifin da bai sani ba,Ni dai shawaran da zan baki ki yi kokari ki gyara zamantakewar dake Tsakanin ku,Sannan ki daina Fifita mganar Mahaifinki saman tasa baki kyauta ba ki bashi hakuri ki nuna masa zaki bi Umarninsa sannan zaki Girmama duka muradansa akanki sai a zauna Lafiya"Sai ta damke hannuwana Tana fadin"Nagode sosai Maman Amir.Ban taba ganin kishiya mai kyakyawan zuciya kamarki ba"

Sai kawai nayi mata mirmishi sai gashi na zake ina gayamata yadda zatayi ya sauko,ni nace ta sake wanka ta d'au gayu yau a sha soyayya. Sai Dariyan jin dadi take yi,Mama na Dakinta tana jin mu bata ko leko ba naga yanzu ta daina ma Zainab din Rawan jiki,yara suna dawowa makaranta suka fara Murnan ga Anty ga su Farhan,ko Dakin nasa ma ni na shiga na gyara shi Saboda bata iya ba. Da Daddare tuwon shinkafa nayi mana miyar ganye,da gyad'a sai Dare ya Dawo ina ta mamakin shi ko ina yaje haka?

 Ruwan wanka ma da yace na sakamai yana zafi na juye na bama Zainab nace ta bisa Dakin dashi ta karba ta wuce to bansan ya suka kare ba,Saboda afalo muka hadu muka ci abinci gabad'aya. ina kallo sai kallonsa take yi shi kuma yana basarwa kamar an matsi bakina nace"Wai ina kaje yau tun Safe ne.?

Kamar yana Jirana kawai sai ya harareni kafin yace"masallaci naje na zauna ina kai kararki wajen Allah. Ki nemi yafiya ta.

wlh in ban yafe miki ba, bazaki yi albarka ba Fa'iza"

Sai na saki baki ina kallonsa kuma agaban yara ga Hafsah. zaraf Anum tace"Umma me kika yi ma Daada..?

Kafin nayi mgana yace"Tambayeta dai Anum.."

Zainab na gefe tace"Kema fushi yake yi dake Maman Amir..?

Kawai sai ya kai mata Harara yana Fadin"Ina ruwanki..?

Sai ta kalleni nima na kalleta nayi mata signa da ido sai ta mike nima na mike ina fadin"Amir ka kwashe kwanukan nan ka kai kitchen.

Anum ki share falo Hafsah ki yi ma yaran shirin kwanciya Fadil dina taho muje mu kwanta"Yaro ko ya taso daga wajen Uban ya nufoni na Daukesa na kalli Zainab ina fadin"Ki shiga ki gyara masa shimfid'a. Sai da Safe"

  Sai ta amsamin da Toh,ta wuce nima na wuce da kallon mamaki ya bimu da shi kuma muka ki basa damar mun Fahimcesa yaran kuma suka rika fad'in"Umma sai da Safe,Anty Sai da Safe"

ni dai tunda na shige Daki kamar Allah ya aikomin da barci ina Kwantar da Fadil nima nabi gefensa na kwanta sai barci sai asuba na tashi,Da Safe basu ma fito da wuri ba. Sai chan rana tunda naga ta fito tana Annushuwa na kalleta ina fadin"Ya ya.?

Sai ta bani Hannu muka tafa Lokaci daya tana fadin"Komai ya daidaita.

Ammh fa yace sai na ijiye aikina na Dawo nan sannan zai san ina son sa"

Kai Tsaye nace"Sai ki nema wani anan ba Shikenan ba"

Kai ta gyada min kafin tace"Haka za'ayi. Nasan zamu sha rigima da Daddy ne"

Ina shirin mgana kawai daga bayanmu mukaji muryansa yana Fadin"Fa'iza wlh kiji Tsoron Allah. Ki kuma Tubar masa saboda abunda kike yi sam bai dace ba."

Kafin nayi mgana tayi zaraf tace"Honey laifin me Maman Amir tayi ita kuma..?

Sai ya harareni yana fadin"Tambayeta ita ai tasan komai"

Sai ta juya tana kallona kafin tayi mgana na tare ta da fadin"Kada ki biye masa bansan abunda yake mgana ba"Saboda kada ya kara mgana na yi wuf na fice ina sauke Numfashi,shikenan ma'auratan suka Daidaita kansu,Sati daya tayi mana sannan ta koma ta kuma ta tabbatar min zata yi kokarin ta ijiye aiki sannan ta Lallabi Daddy ko gida ya siya mata a nan ni ko araina nasan Yaya Ishaq bazai yarda ba. kuma Tsakani ga Allah wannan gidan yayi mana kad'an ace mata Biyu da yara ga Mama shima ai sai ya Duba ammh yadda bai sakoni aciki ba nima ban Tusa kaina ba..

 Maganar auran Halisa ya taso Anty Binta ana ta shirye shirye ni dai nace zan gyara amarya ta bangaran jiki da kamshi,kuma Anty binta na fad'amawa sai gashi tana min godiya sannan tamin mganar zatayi Zobo da kunin aya ranar walima tana so nayi mata,girki ma in ba damuwa na shige gaba ban nuna mata komai nace duk zan yi,mun yi waya da Badariya tace bazata dawo ba,ni na bata baki tace zata dawo ana gobe Daurin aure tunda kano za'a kawo amarya sai ta biyo su ta dawo abunta nace shikenan kuwa.

 Da kudina na siyo kayan hadin Turaruka na had'ama Halisa da na Rushi da Humra da kwallacha sun kai na Dubu ashirin,sannan ga na gyaran jiki tun ana saura sati daya biki take zuwa kullum da yammah ina mata Gyaran jikin.

Ranar da muka kwana uku muna yi sai dare na gama mata,ita da wata kawarta suka zo,kuma tare suka tafi a dakin Mama nake yi mata ita tunda ta gidace,Mama sai mamaki take yi tana fadin"Ikon Allah.."

Ranar na gaji,ko zobon yammah ban Dafa ba Hafsah na makaranta,bata dawo da wuri ba,Ban iya ko yin abincin Dare ba saboda bayana ya rike sai nayi wanka na gasa jikina da Ruwan zafi nayi sallar mangariba ina zaune ina lazumi Hafsah ta shigo ina ta mata fadan ina ta Tsaya sai tace min bata samu abun hawa ba ne da wuri, sai na Sassauta nace in ta huta ta Dafamana ko Cousscouss ne.

Tace to bari tayi sallah Yaran kuma suna Falo Yaya Amir na biya musu karatu ina jin tashin muryoyin su daga Falo,Chan sai ga Hafsah da wayarta ta kawo min Abba ke son mgana dani bayan na dauka mun gaisa yacee"Kuna lafiya ina matata da megidan naki..?

Nace"Duk suna lafiya Abba"

Sai yace"To madallah kan mganar Binciken da nace za'ayi kan Case din mijinki ne,Engr ya dawo nayi mgana da shi yace ba matsala sai dai zamu kara jira Tunda mahaifin nasa yana London Mahaifiyarsa ke chan za'ayi mata Dashen koda. hankalinsu duk ba'a kwance yake ba shiyasa har yanzu bai yi masa mgana ba"

Sai nace"Ayya Allah ya bata lafiya Abba"Sai ya amsamin mud'an taba Hira har ya bama Ammi muka gaisa tana min Tsiya"Hajiya Fa'i mai turaran kamshi"

Dariya nayi ina fad'in"Kai Ammi"

sai kawai tace"Abban ki ma yace y'ata ta iya had'a Turaren kamshi"

Kunya suka bani su ko ba ruwan su Abba da Ammi sai su,mun gama wayar kenan naga mutum tsaye a kaina ina dagowa cikin mamaki nace"Sannu da zuwa"

Sai kawai yace"ina son mgana dake. ki sameni a dakina"

Daga haka ya fice mamaki ya kamani na rike haba a fili nace"Topha..!

Ina shirin tashi aka fara kiran sallar Isha'i sai na mike nayi salla na idar kenan na mike ina ninke Darduma Anum ta leko tana fadin"Umma Daada na kira"

Sai na gyada mata kai ban ko cire Hijabin jikina na fita zuwa Dakinsa ina Shiga sai faman safa da marwa yake yi har sai da nace"Lafiya..?

Kai tsaye yace"Ina jin yunwa ina abincina.."

Kai Tsaye nace"Aiki nayi nagaji sai da Hafsah ta shgo nace ta dafa mana ko Taliya"

Sai kawai naga ya karisa ya rufo kofa da Sauri nace"Ya da rufe kofa..?

Yana juyowa yace"Yau zamu yi ta kare Fa'iza hakki na zaki bani nagaji"

Gabana ya fadi na kwalolo ido waje hakkina..? Na maimaita a raina.

na shige su ga shi in nayi wani ihu yara na falo suna jin mu.

bakina yayi nauyi ina ji ya ja har hannuna bakin katifarsa ya cire min Hijabin jikina cikin rawan murya nace"Abincin fa..?

Kai Tsaye yace"Zamu ci in mun gama. Fa'iza bazan iya jira ba"

Bakina naji yayi wani Dif.  Jikina kuma Kamar mara Lakka, kamar rakuma da akala haka yafara bi da ni a gaggauce kamar daman ni yake jira.








*Janafty*





[7/19, 2:47 PM] Hauwa Galadima: *KNKB2017*


*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*

*09069067488*


Saboda yanayin da zuciyata take ciki yasa kwata kwata gangan jikina bai karb'i sakonnin dayake aika min da shi cikin zafin nama ba,Doguwar riga ce a jikina har ya samu nasaran Rabani da ita,ammh na kasa wani motsi na riga na Sadakar bani da wani Tsumi ballatana Dubara a lokacin.

 Bakina ne yayi min wani irin nauyi, ina ji kamar ya kumbura saboda irin yadda Yaya Ishaq ya rika sumbatata a raina sai cewa nake yi daman haka Sumbarta take..?

Sharaf nayi masa ko hannuna ban yarda na motsa ba,kwance nayi masa kamar ruwa ya cinye ni,Ina jinsa yana gwama Numfashi,sama sama sannan Lokaci d'aya yana sauke ajiyar rai chan naji yana kiran sunana fad'i yake yi"Fa'iza ki rikeni. Ki rumgume ni don Allah"Ya fad'a cikin wani irin yanayin da ba kowa zai iya sanin yanayin ba.

 Nayi masa banza kamar ban ji ba, kuka ne ya taho min daga karkashin Zuciyata sai hawaye sharr sannan na saki Shesshekan har yana jina.

Sai naji kamar an zare masa lakkar jiki ya koma ya kwanta a gefe yana maida numfashi. ni kuma ina ta kukana sai ya mike zaune cikin yanayin Sarkewar murya yace"Yanzu Saboda zan karbi Hakkina ne yasa kike wannan kukan Fa'iza.?

Shuru nayi masa ban yi mgana ba sai dai ina cigaba da kukana kamar karamar yarinya sai kawai ya mike Kaina na juya gefe har ya gama Suturtata jikinsa,ina daga kwance kawai naji ya yi wuf ya tadani zaune yana fadin"Tashi ki saka kayan ki"

Sai na bisa da kallo ina Tunanin ko ya fara samun matsala ne ganin yana komai a gaggauce.

 Mikar dani Tsaye ya yi ya na kokarin sakamin rigar na rike hannunsa muryata a shake nace"Bari zan saka da kaina"Kamar wacce zan gudu ina gama sakawa ya jawo hijabi ya zuramin Saboda Sauri kamar zai ciremin kai, nayi baya ina kallonsa da Tarin mamakinsa Maikon hawaye sun cikamin ido ban samu damar mgana ba. kawai ya finciki hannuna ya isa ga kofa ya Bude yana jana muka fito Falo yaran duk suna falon suna ganinmu suka bimu da ido ganin yana kokarin Fita daga Dakin yasa na Turje ina fadin"ina zaka kai ni..?.

Bai ko Saurareni ba ya fincikeni zuwa waje sai kawai naga mun shiga Dakin Mama Lokaci d'aya yana fadin"Mama kin kwanta ne..?

 Mama na zaune saman kujera da waya a hannunta kamar ta ma gama wayar ne muka fad'o dakin yadda ta ganmu ne yasa ta mike a firgice tana Fadin"Kai lafiyan ku kuwa..?

Gabanta ya zaunar dani yana Fadin"Mama gata nan ta fad'a miki meyasa take hanani Hakkina..?

Ki tambayeta meyasa take guduna bata kaunar na rabeta. Mama Fa'iza na gudu na a Shimfid'a"

Shi yake mganar nan ammh ni kunya da bakinciki sun rufemin ji na da ganina na wani Lokaci,Tsabar yadda na kad'u na girgiza da wannan wulakancin na Ishaq .ashe shi yana da bakin mgana ban sani ba..?ni shekarun da ya kwashe a jingine da aurene wajen wa na taba kai karansa.?sai shi ne yake da bakin mgana."

 Kaina na dunkule a kasa ina kuka kamar na mutu haka nake ji Saboda kunya ita kanta da Mama sai da ta kasa zama kunya duk ya Rufeta ta kasa mgana tana mamakin d'an yau.

Kallonta yayi a rikice yana fadin"Baki ce komai ba Mama..?

Sai Mama ta juya baya tana fadin"Fa'iza ki yi hakuri don Allah.Kada ki kara gudun mijinki a shimfid'a. kai kuma ka bita a hankali kada ka matsa mata."

Wannan mganar ku ce Tsakaninku ne, don Allah kada ku kara sakani"

Daga haka ta shige uwar Dakin ta tabar mu nan zaune,shi yana Tsaye ne kamar wani Saraki.

 Kafafuwana sun yi min zafin da na kasa tashi sai da na ganshi Durkushe a gabana yana fadin"Kin ji dai abunda Mama tace ko..?kada ki karamin Gaddama in dai na kira ki a Shimfid'ata"

Sai kawai na Dago Rinannun Idanuwana na sauke a kansa cikin wata irin murya mai cike da Takaici nace"Meyasa ka kawo k'ara na wajen Mama..?

Sai hawaye ganin kukana sai kuma ya Rud'eni ya fara kokarin son rikoni yana fadin"To ke ne Fa'iza duk yadda zan yi dake kin ki ganewa shiyasa na kawo kararki wajen Mama"

Ture hannunsa nayi dake kokarin rikeni na mike Dakyar ina fadin"n ban taba kawo kararka ba.

Ban taba fad'ama kowa halin da nake ciki ba,ko da yan'uwana ne. sai kai ne da bakin ka yafi nawa Tsini..?.

Na karishe fad'a a Fusace cikin kuka Sai shima ya mike yana kallon Dakin da Mama ta shige Lokaci daya yana Fadin"haba mana.."

Kuma wai yana kokarin rikoni Saboda bai da kunya a fusace na make Hannunsa ina fadin"Tunda kaso a fasa komai za'a fasa kowa yaji"

Ganin ina nufar dakin da Mama ta shige yasa ya rikoni da karfi yana Fadin"Don Allah a'a Fa'iza don Allah"

Daman ba fad'a zan yi ba sai na Turesa na kama Hanya na fita Daga Dakin mama,zan shiga Dakina ya Taremin Hanya yana faman marairaicemin sai kawai na juya da gudu nayi hanyar waje saboda naji hayaniyar yara har lokacin suna falo kamar abinci suke ci bana so su Fahimci abunda ke faruwa.

Shima da gudun yabi bayana yana kiran sunana gaba na ya sha yana Haki yace"Ke ke ina zaki..?

Cikin duhun Korodin dakin Jamal na balla masa Harara ina fadin"Tafiya zan yi..Zan tafi ne wlh bazan zauna dakai ba"

Na fad'a masa cikin Tabbacin mganata sai ya Rude ya fara fadin"Ban gane ba.

Wani irin tafiya kije ina kuma..?.

Kai Tsaye nace"In da baza'a takurani ba sannan inda nima zan kai kararka.Nima ai ka jingine shekaru ina maka gadin ya'yan ja wa na taba kai ma kararka..?sai ni Zaka kai ma Mama karar na hanaka kaina ina ce ba kai ka ce na kyaleka ba..?

Ba kai kace na barka kayi Sabuwar Rayuwa da wacce ka zaba ba .?

Meyasa sai yanzu zaka matsamin na gayamaka aurena dakai ba aure ba ne yanzu,Jingina ne.."

Na karishe fad'a cikin Tsawa lokaci daya ina kuka sai ya kasa mgana Saboda yadda na ke ture hannunsa in yakai min zai rikeni Cikin fitan Hayyaci yace"Ke ba ki Afuwa ne Fa'iza..?wlh na yi nadama na tuba na bi Allah na biki kiyi ma girman Allah ki saurareni"

 Da Sauri na daga masa hannu ina Fadin"Bazan saurareka ba. Na fada maka ka daina cewa aure aure, auren mu a jingine yake in ka cigaba da matsamin na rantse da wanda raina ke Hannunsa zan bar gidan nan Daman ya'yan ka ne kuma sun yi girman da zasu kula da kansu. Ahmad ne matarka ta had'a da na Hannunta da wanda zata haifa ta rike maka ammh in dai na tafi to Har abada BAZAN DAWO BA"

Na karishe fad'a ina Tsaida kallona a kansa Cikin Firgici yace"Eh. A'a kije ina.?Fa'iza kina son ki kasheni ne..?

In kika tafi to na zauna da uban wa.?.kai Tsaye nace"Ka zauna da Zainab wacce ka zaba sama da ni"

Kara girgiza kai yayi yana fadin"Aa ba inda zaki.Ba zaki tafi ba Fa'iza in ba so kike na laalace ba"

Cikin kuka nace"To wlh in ka kara matsamin sai na tafi kuma nayi Rantsuwan in na tafi bazan dawo ba. Sannan in ka kara kai karata ba ma wajen Mama ba,wlh ni kuma sai na Fallasa ma duniya komai, tasan Tsakanina Dakai auran jingina ne"

Kamar na watsa mai ruwan zafi haka yaja baya yana fadin"Na shiga uku don Allah kiyi hakuri Fa'iza, eh naji Wlh naji na yarda bazan kara matsa miki ba ammh kimin rai kada ki fad'i wannan mganar wani yaji don Girman Allah.."

 Kukana na Tsagaita kafin nace"To naji bazan tafi ba. kuma kamar yadda nayi maka alkwari tun a baya sai dai kai ka fadi mganar da bakinka ammh ni nayi maka wannan alherin kamar yadda ka Rokeni,kada ka kara cewa zaka Takuramin ba wani hakkin ka dake kaina, domin tun kafin auran ka da Zainab ka rokeni da nayi maka adalci na kyaleka kayi rayuwa da wacce ta dace Dakai a lokacin ban yi maka korafi ba.  sannan ban taba maka gaddama ba har Tsawon yau din nan To nima bana son kayi min Korafi abunda ka zaba ne, nake yi maka kada ka kara damuna ni bani da jikin da zan baka ka mora sannan ban chanchanci wannan binbinin daga gareka ka ba. kyaleni don girman Allah.

"Na karishe fad'a cikin Kuka ina Had'a Hannayena jikinsa a Sanyaye yace"Duk naji na yarda mu koma cikin gida kuma ki daina kuka ga yara chan kada su dauka na Dake ki ne"

Ban yi musu ba na daina kukan na Share hawayena na kama hanya na koma yabi bayana muna Zuwa Tsakar sai ga Hafsah ta fito daga Dakin Mama abinci ta kai mata tana ganin mu tace"Fita daman kuka yi..?

Da Sauri yace"Eh eh.."

Dagaji bai da gaskiya ni dai daga shi har ita rabasu nayi na shige ciki Suna cin abinci yaran Anum har ta mike taga nayi Zaraf na shige Daki har da banko kofa,sai suka yi wani shuru Baban nasu na shigowa suka sakamai Ido duk sai ya Daburce Anum ne tace"Daada me ya samu Umma..?

Da sauri yace"Umma.."

Ya kasa mgana Amir ne ya kwace sa da Fadin"Kila bata da lafiya ne" jin haka yasa yace"Eh eh bata jin Dad'i kuci abincin ku"

Daga haka ya wuce Dakinsa yana Zufa yaran suka bisa da kallo harda Hafsah da ta zargi wani abu na faruwa sai dai bata ce komai ba ta kira Amir ya Dauki abincinsa yakai mai,sai gashi ya Dawo dashi yace bazai ci ba. nima kuma sun kawomin nace su Dauke bazan ci ba,da suka shigo ma sun fara min Hayaniya na koresu nace kaina na ciwo,Su kansu sun san an tabani gabad'aya har wayewan gari suma duk sun yi wani iri ban ma fito ba Hafsah ta musu komai Hatta zobo ita ta Dafa ta barmin na hada ta wuce makaranta shara da wanke wanke kuma Anum tayi shi ban fito ba sai da rana Saboda zuwan dangin Mama daga yamai dole ta sani na Dora girki,Yaya Ishaq na dakinsa in ji Anum ammh ban ko duba barayinsa ba,Da yammah Halisa tazo nayi mata Dilka washegari da Safe muka hadu na gaisheshi ya amsa sannnan na gayamai yau zan je gidan Anty Binta akwai Walima ba gaddama yace a dawo lafiya, ni kadai na tafi yara suna makaranta Anum kuma tun safe tabi Anty Hure suka tafi.

 Sai Dare muka dawo chan Badariya ta iskemu an yi walima ni nayi zobo da kunin Aya sannan tare da ni akayi cake din Rabo,Da Sassafe kuma na koma Saboda girki duk da ta Dauki ma'aikata ammh ni zan rika nuna musu komai yara basu je makaranta ba Hafsah da ta shiirya ita da Badariya ta taho da su,Hajiyar Dala ta zo ita da Suwaiba,Yaya Asiya ce bata samu zuwa ba Yaya mariya ma tazo abun mamaki har da su Anty Nasara,gida cike da baki na nesa da na kusa, aranar za'a Daura aure,sai washegari Lahadi da safe a wuce da Amarya mun yi waya da Nana Fatima da farko ban fad'a mata zan zo kano ba saboda nayi Tunanin in na tafi wazan bar ma gida? ammh Daga baya sai na fasa nace sai naje shi ya zauna ya kula da gidan da ya'yan sa.

ban yi anko ba saboda bata nuna ma kowa ba,ammh nima na yi shigar alfarma cikin kayan da Hajiya ke dinkamin ne super wax na saka,Da Daddare gida na muka dawo da su Anty Nasara yaya mariya dai chan muka barta daman nasan bazata Biyoni ba.

 Amir na aika nace ya gayamasa zan raka Halisa kano,kai Tsaye yace Allah ya kiyaye hanya,Da yake shima da Safen ya shirya ya fita saboda Daurin auran Safe ne Na fad'ama Mama zanje kano sannan zan bar yara Saboda makaranta Ga Hafsah ga babansu tace ai daman ya kamata naje ni ko bata sani ba gidan ne da D'anta suka isheni. zan yi musu yaji na kwana Biyu.

Kaya kala Biyu na dauka da abunda zan Bukata,Anty Nasara ce zataje Goggo gida zata koma Hajiyar Dala Daman yan gida ne suna cikin masu tafiya.

 Karfe goma da rabi aka Daura aure zuwa sha biyun rana an fara tafiya Saboda kada ayi dare ni mota D'aya muka hau da Badariya da Anty Nasara,Yaya mariya bata je ba megidanta bai barta ba.

Anum har da kukanta sai taje sai da nayi mata Jan ido Amir daman bai da damuwa sauran kuma suna wajen Babansu.

Ban taba zaton zan iya tafiya na bar ya'yana ko da na yini d'aya ba sai ranar, na gwada ne daman naga ko zan iya sai dai muna tafiya ne ina jin kamar na bar baya da kura.?wazai kula da su..?Hafsah tana zuwa makaranta shi kuma bai iya komai ba ballatana ya Kula da su, sai dai hankalina ya kwanta da na Tuna na Horar da ya'yana Musamman Amir da Anum zasu kula da Sauran kannensu.

Dama already an yi ma amaryan jerenta gidanta mai kyau ita kad'ai,da muka isa abinci muka ci sai sallah sai kuma dan Saura gyare gyare kawayen Anty Binta sun kama komai yasa mukayi musu sallama sai gidan Yaya Asiya. chan muka kwana muna Hira harda Badariya,washegari Litini muka shiga kasuwa na raka Anty Nasara nima har na siya ma Anum takalmi mai kyau na mata, da muka dawo har da Yaya Asiyan muka leka gidan Amarya chan muka hadu da ya'yan Hajiyar dala sai dare Direban da zai maida su gida ya Saukemu gidan Yaya Asiya ranar Talata Anty Nasara tace mu tafi sai nace ta tafi zan taho bata Damu ba ta wuce karofi a ranar,ni kuma bansan Dalilina nakin komawar ba Yaya Asiya kuma tasha Ishaq ne ya barni Har tana jin dad'i.

Tun da muka zo bai kirani ba sai ranar Laraba da Daddare ina Dakin Yaya Asiya ita kuma tana wajen mijinta naga kiransa sai nayi mamakin sanin bai da waya bayan na Dauka mun gaisa sai yace"yaushe zaki dawo.? Yara sun damu fa"

Sai na basar da tambayar sa,ina ya samu waya na tambaye sa,kai Tsaye yace"Zainab ta aikomin daga chan"

Sai na yi shuru ban yi mgana ba ganin haka yasa sai ya mika ma yara wayar duk dai korafin Umma yaushe zaki dawo ne? nace zan dawo kada su damu ina Tunanin har da shi ya Dinga matsa musu su ji yaushe zan dawo ni ko a raina nace ba yanzu ba,ko zan dawo .har ga Allah ba da niyyar zuwa Dutse nazo ba sai da Yaya Asiya ke min Tadi'n ba nisa fa daga kano to Dutse gidan Nana Fatima kamar almara sai  ko nace zani na kirata na Fad'amata ta daka Tsalle da Ihu tace in na hau mota da nazo tashar Dutse na Kirata zata zo ta Daukeni nan da nan naji Kwadayin zuwa na yi ma Yaya Asiya karya da ta tsareni da tambayan shin an bar ni..?

 Nace mata eh mana ya barni sai ta kyaleni mijinta yarakani na hau Mota ranar jumma'a gabana na fad'i hakan nan na Daure bayan na roki Allah ya yafe min na yi doguwar tafiya mijina bai sani ba, Sai ko gani a Dutse ina kiranta sai gata tazo ta Daukeni har tasha muka Rumgume juna.

Sai gani a kayattacen gidan Nana Fatima mijinta babba ne Aikinsa D'an sanda farin kaya ne,Ita da mijinta kamar zasu goyani yana Dawowa a gaba na suka rumgume juna yana da fara'a kamar ita yana ganina Tun kafin na gaishe shi yace"Sannu da zuwa Fa'in mu maraba da zuwa Dutse"

Ina mirmishi na amsa masa duk yadda zan baku labarin gidan Fatima da Ahalinta sun wuce haka,Ya'yanta Jalil da jidda tun saba dani kamar sun sanni daman gani da son yara, Daki guda Nana Fatima ta ware min kuma har ta Kira chan gida ta fesama su Abba zuwana. Ammi tace kafin na koma Nana Fatima ta rakani har kano na gaida Hajiyar su tace in sha Allahu zata kaini,gani nayi dai ban kyauta ba, ranar da na kwana na yini na kirasa na fad'amasa ina Dutse gidan Nana Fatima. kai tsaye yace"Kika tafi har Dutse baki fad'amin ba Fa'iza..?ai naga dai duk lalacewar aure sunansa aure"

Sai na kasa mgana nasan ban kyauta ba yasa nace"Kayi hakuri.."

Bai ce komai ba illah yaran da ya mika ma wayan muka yi mgana Duk sun damu da in dawo daman mun yi waya da Hafsah ta fad'amin Ahmad nata rigiman bana nan,sai na fara Tunanin komawa gida kwana hudu nayi a Dutse kamar kar in dawo,Nana Fatima macece mai kirki ita da mijinta sun fita dani naga gari sannan zama da fatima yasa na kara sanin ita mace mai Daraja ce sannan yar kwalliya ce.

 A na gobe zamu tafi kano da ita ni dagachan zan wuce katsina take kara min mganar Zainab kai Tsaye nace"Ina da abokiyar zama ammh tana Abuja chan take zaune"

Cikin karin mamaki tace"kuma tana da ya'ya..?

Ina dariya nace"Sosai biyu har da cikin na uku ma"

Sai ta rausayar dakai tana fadin"meyasa ita tana Abuja ke kuma kina katsina..?

Ganin Nana Fatima ce akwai yarda Tsakanina da ita yasa na gayamata kadan daga abunda ya shafeni sai dai ban gayamata irin zaman da nayi da Ishaq da jinginar aurena  dashi ba,sai dai na gayamata Dalilin da ya sa zainab ta zauna abuja ni ina katsina.

Cikin mamaki tace"Tab kuma tana zuwa gidan ki na katsina ki sauketa a Dakin ki..?

Ina Dariya nace"A'a dakin dai megidan"

Sai ta bude baki tana mamaki Dariya ta bani na kwashe da dariyan ina fadin"Rufe bakin Mana"

Sai ta rufe lokaci d'aya tana Fadin'"Lalle kina da karfin zuciya wlh bazaki kwanar min a shashe ba..Tabdijam"

Dariyan yadda take jinjina abun nake yi a raina nace don ma bataji ni ke Dawainiya da su ba da sai ta zageni,a kwana Hud'un da nayi da ita na kara sanin wasu abubuwa na kuma kara yarda kwalliya da ado  na duka mata ne,ba na bambamcin Fata ko kyawun Fuska ba.

 Na kuma kara sanin ko kana da kyau to ka kara da wanka sai kafi haka kyau gata dai mai kyau da ita ammh kwalliya da gyara bata rabo da shi har mgana nayi mata nace"Nana baki gajiya da kwalliya da gayu..?me zaki gyara ke da komai Allah ya baki mai kyau a jikin ki"

Dariya tamin kafin tace"Ko kana da kyau Fa'i ka kara da wankan sannan ki yi shuru kawai ba komai Allah ya bamu ba. muma duk barazana muke da kwalliya da gayun yana karamana kwarjini"

Kuma na yarda da mganarta,Domin naga gayu in da ake kiran gayu a wajenta tana fadin Ammi yar gayu ce sannan bata shiri da wanda bai son gayu,nace tabbas na shaida haka Sai naji nima ina so na fara gayun nan na shiga Sahun manyan mata Cikkaku.

 Washegari Direban mijinta ya kaimu kano har gidan Yaya Asiya tare da ita muka dumguma zuwa gidan su Ammi,sun yi murna sosai sai nuna ni suke yi suna tambayan ita ce Fa'in Azizat mai turaran kamshi sai Nana Fatima ta gyada kai wasu daman mun Hadu Bikin Yaya Abdul'Ahad,Balle kuma daman Yaya Asiya ta zama yar gida,Duk yadda naso na wuce katsina a ranar bai samu ba saboda mun jima muna Hira a gidan su Ammi ita kanta Nana Fatima tayi yammh don dai motar gida ce.

Mun fito gidan su Ammi Nana Fatima ta nuna mana wani katon gidan Bene tana fadin"ina Engr din da zaku ji Abba na yawan mganarsa..?

Sai muka d'aga mata kai Saboda duk wanda yasan Abba yasan Labarin megidansa Engr.

Cikin Nuna mana gidan Nana Fatima tace"Ga gidan kakaninsa ta bangaran Uwa.nan aka haifi mahaifiyarsa dalilin makotansu da gidan su Ammi ma Suka hadu da Abba."

A tare da Yaya Asiya muka jinjina kai ina kallon gidan daga gani masu gidan suna da kudi sosai,irin kamar fasalin gidan da Abba ke ginawa a karofi sai dai wanchan ba gidan ba Bene ba ne.

Muna tsaye jikin motar da zata maida ta gida muke mganar Yaya Asiya ta ce"To ina masu gidan..?

Nana Fatima tace"Hajiya Tafisu ce mahaifiyar Hajiya Shukra ce kadai a gidan sai ya'yan yan"uwa Datake riko megidan ya rasu da jimawa daga ita sai yan aiki a cikin wannan gidan"

Na  jinjina kai ina kara kallon gidan da akace mace d'aya ce aciki Nana Fatima ta cigaba da fadin"Shi Engr babansa bayarbene mutumin Beneu ne, Hajiya Shukra ce bahaushiya suna Abuja da zama. Sai dai dangin su kaf suna Beneu har kakansu tana chan da ciwo ya kamata ne ma ta koma hannun Hajiya Shukra,Engr kuma shi a Edo yake aiki"

Ni dai har gajiya nayi da labarin Engr Nana Fatima ko ta zage har Yaya Asiya na tambayan"Tab.To ya"yansa nawa..?

Nana Fatima tace"Tab. Bai da ya'ya fa, ya taba aure sau da'ya sati biyu matar ta kone da gas shikenen bai kara aure ba. kuma fa Abba ya girmesa, matashi ne sai dai yana da kirki sannan ya taka matsayi mai girma da kananun Shekarunsa"

Gani nayi sun bud'e hirarsa da Sauri na katsesu da fadin"Nana kada ki yi Dare"

 Sai da nayi mgana ta farga Mukayi sallama Ta shige mota suka tafi,Dole na kara kwana gidan Yaya Asiya washegari motar asuba na hau sai katsina,Ance in mace mai ya'ya ta fi sati bata a gida sai abunda ta gani nima haka na tarar,kudin zobo da kunin aya sun ci ubansu,Hafsah sau Daya take yi a rana watarana ma in bata da Lokaci batayi,sannan kudin kuma suna tabaawa in zasu siya wani abu ,sannan yara wlh sun yi kewata ranar da na dawo yini Ahmad yayi Tsalle acikin gida,Shi kan shi Gogan bakinsa har kunne har da fadin"Mutanen kano da Dutse maraba"a Tsime na amsa masa nazo musu da Tsaraban Dutse da Nana Fatima ta bada a kawo masu,nafi kwana Biyu,gidana da kasuwancina bai Dawo daidai ba,Na yarda mace itace gida ranar da bata to sai kame kame har Mama tayi murnan Dawowata..

 A satin kuma naje Karofi,Matar Yaya isa ta haihu naga ginin Abba an kusa gamawa a raina nace komai in da kudi an yi an gama,ammh duka duka yaushe aka fara ginin nan har an kusa gama shi..?ban kwana ba na dawo gida Hafsah chan na barta zatayi weekend,ina kuma Dawowa na iske wani sabon salo ban sani ba ko Mahaifin zainab ko ita wanda ya kirasa kan zainab zata baro aikinta ta biyo shi katsina ammh sai ta fara neman wani anan sannan zata zauna agidanta ne ita kad'ai in ya amince shi ko yace bai amince ba sai dai tazo mu zauna tare a wannan gidan.

Yana gayamin takaici ya kume ni na kallesa nace"To gidan da zata zauna wazai Dauki nauyin sa..?

Kai Tsaye yace"Daddy ne mana"

Nima kai tsayen nace"To meyasa bazaka barta ta zauna inda zata Sake ba.?Mganar gaskiya gidan nan yayi mana kad'an ban ga inda ita da yara zasu zauna ba abun kuma yayi yawa"

Hade rai yayi kafin yace"To wai haukatani zaku yi ne..?

Nace Haukatani zaku yi ne..?

To anan zata zauna nace"

Sai na bude ido kafin nace"Ba damuwa ta zo mu zauna din na d'an Lokaci ne, kowa zai san matasayinsa"

Mgana na gasa masa ammh bai gane ba,Ya gimtse bakinsa nima na kama kaina ina ji har Mama sai da tayi  masa mgana tace gidan yayi mana kad'an ammh bai jita ba.

  Har Anty Binta sai da mama ta kira ta shaida mata, itama fad'a ta hau yi masa na gidan ya yi mana kad'an,shi kuma yace ba ruwanta shi ya yi alkwarin bazai kara yarda a rika juyasa ba.

  Karfin Hali kenan baka da ko asi sai bakin rai da isa,tab zan ko ga yadda wannnan zaman zai kasance. 

 Sai dai na roki Allah kafin hakan ya faru Allah ya bani mafita.






*Janafty*

[7/19, 2:47 PM] Hauwa Galadima: *KNKB2018*


*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*

*09069067488*


Magana fa taki ta kare,Saboda Yaya Ishaq yayi rantsuwan Zainab bazata zauna a ko'ina ba sai gidan nan tare da mu,kuma bazai amince Mahaifinta ya kama mata gida ba.

 Kowa yayi mishi mgana ammh bai ji ba,daman yana da Taurin kai wani Lokaci sannan rashin aikin nan nasa yasa zafin zuciyarsa ta karu,Mama gajiya tayi da mai mgana ta kyalesa har da kaninta Dake yamai ta had'a shi ko zai ji mganarsa ammh yace matsayarsa kenan.

Ni tunda nayi mai mgana yace nan din zata zauna ban kara masa mgana ba,na cigaba da Harkokin gabana. Ammh ganin ya dage da gaske yake yi yasa naji kamar nima in kai k'aransa wajen Abba ko Yaya Abdul'Ahad da kan kirani shima duk bayan kwana Biyu yaji lafiyata,Sai kuma na fasa saboda kai kara ba Halina ba ne sannan bayyana sirrin aurena ba Halina ba ne shima,ammh mganar gaskiya Yaya Ishaq zai tauyemin hakkina,Kuma gani yayi ya saba shiyasa yake so ya gwamatsa mu acikin wannan gidan.

 Ni ban ma jin kaina nafi jin yarana Saboda komai daman nake yi saboda su ne, an saba tauyemin hakki na Hakura saboda su daman.

Sai nafara tunanin in Zainab ta dawo gidan nan a ina zai sauketa..?

Dakinsa dai falle d'aya ne,Sai bayi rayuwar mace bazai yu yu acikin wannan Dakin ba,bansani ba ko Dakin yara zai sauketa ko kuma ni yake so ya fitar dani daga dakin ya sakata ban yi dai mgana ba na zura ido ina ganin ikon Allah.

Ban sani ba ko sun yi ta ja'in ja da Zainab din ne,kan mganar sai kuma Kwana Hud'u da fara mganar sai ga Mahaifinta Dr.Lawal ya diro gidan Dakin Mama ya sauka sannan,sun jima suna mgana da Mama domin da kan shi yace shi Ishaq din ya basu waje zai yi mgana da Mama, daman wajenta yazo sai ya koma Daki yana cika yana batsewa ina tsakar gida ni dai ina Harkokina ban bi ta kansa ba. sai bayan awa D'aya da wani abu Mama ta leko ta kirasa,ya shiga shima ba jimawa sai ga shi ya fito ya kirani Lokacin kuma na gama Dafa zobo ne, sai na bar ma Anum ta kular min da shi kafin na fita na koma Dak'i na sanya Hijabi nayi sallama Dakin Mama na shiga.

Mama da Dr.Lawal ke zaune kan kujera shi kan shi Uban gayyar yana zaune a kasa nima sai nabi ayarinsa na zauna a kasa dagachan bakin kofar cikin Ladabi na kara gaisheshi, sai naga ya amsa cikin kulawa ba kamar sauran Lokutan da in na gaisheshi yake amsani a wulakance ba.

 Mama ce ta kalleni tana fadin"Kan mganar Dawowar Zainab nan ne. Yazo mun yi mgana yace a kira ki  Saboda mganar ta shafeki"

Tana rufe baki yayi gyaram murya ya cigaba da fadin"Ai itama y'ta ce Hajiya. Engr Usman karaye mutumin kwarai ne mun yi zumunci sosai da shi Lokacin muna masters a Buk bayan mun gama shi sai bai cigaba ba,ni kuma sai na tafi nayi Phd dina,nayi mamaki da ya ce min ke y'a kike a wajensa"

Kaina na kasa ban yi mgana ba sai yanzu nasan wato Dalili kenan da ya fara sakemin Tunda yasan Abba, kai wannan rayuwar sai Allah wa ka sani waya sanka ne. ya manta nan ya taba cewa zai batar dani har da Dangina akan yarsa ammh yanzu ko kunya ya zauna yana fadin nima yarsa ce'

Ina jinsa sama sama yana cigaba da bayaninsa Ishaq yake yi ma fad'a akan ya nemesa yazo ammh yaki zuwa.

Mama ce ta karb'esa ta basa Hakuri da Fadin"Ayi hakuri Alhaji ni kaina bansan meke damunsa ba kwanakin nan"

 Mirmishi yayi kafin yace"Rashin aiki ne Hajiya kuma ina nan ina masa kokari. yanzu haka kwamitin Binciken da na kafa ya fara nisa kuma da yakinin insha Allahu za'a samu mafita"

Mama ta amsa da karfin Gwiwan Allah yasa a dace da mafita na Alheri,suka amsa da Ameen nima sai na amsa acikin raina Yaya Ishaq kansa na kasa bai ko Dago ba,Sai da shi da kansa ya kira sunansa sannan ya Dago yana amsawa,Cikin mirmishi Dr.Laawal yace"haka ake yi sai kayi fushi da Baban ka.?ni har Abada a D'a na Dauke ka. Kaunar da nake yi maka yasa na baka auran yata mafi soyuwa gareni. Wlh tallahi ba domin kai ba ne bazan taba yarda Zainab ta baro inda ta saba rayuwa zuwa wani wajen ba,Sai dai tana sonka sannan ta shirya ta zauna dakai,ammh sai nace ga Sharad'ina zan nema mata gida inda zata zauna domin bisa adalci ban ga wajen da zata zauna anan ba,Kuma ga Dawainiyar yara achan duk na Dauke ma kasu gata nayi maka sai kuma naga baka gani ba,kana Tunanin ina maka iko ne da matarka,Sannan nace zan nema mata aiki a nan garin,da aikinta ka sameta baka kuma da ikon da zaka hanata. Ammh sai naji kace baka yarda ba,Sai dai ta zauna anan tare da ku kai kanka kayi ma kanka Adalci,Ta yaya zaku zauna awannan gidan kalli fa gidan ga yara ga ku haba sai kace akuyoyi zaka saka ba Mutane ba..?

 Ya fad'a cikin zolaya da yanayin mganarsa zaka san sulhu yake nema Saboda yarsa shi kuma nashi Jarabawar kenan,ammh duk wad'anan mganganun bai shiga kunnen Yaya Ishaq ba. yana dagowa sai cewa yayi"Gaskiya ni Daddy bazan amince kace zaka kama ma Zainab wajen zama ba, nan din zai ishemu muma aciki muke zaune me ya ci mu..?Fa'iza nan take zaune da su Amir kuma akwai ishasshen wajen da zata zauna bazata Takura ba, idan ma har zan raba musu gida sai dai in ni na kama Hayar da kudina ko na siya gidan. ammh alfarman ne Daddy bana so, ba domin kuma na raina kokarin ka a kaina ba,a'a wlh nagode sosai bisa Dawaniyar ka gareni"

Ya karishe fad'a cikin Ladabi Dukkanmu shuru muka yi ni sai satar kallonsa nake yi ina ganin mamakinsa mutum ka Dage baka da ko asi lalle zan ga yadda za'ayi wannam zaman.

Mama ranta ya baci ta taso mai tana fadin"Kai dai ka cika Taurin kai meyasa baka jin mgana ne..?

Kai tsaye yace"Mama ki bar ni kawai akwai abunda nake dubawa ne. Indai tana so na to zata iya zama dani a duk inda rayuwa ta kaini. kamar yadda Fa'iza ke zaune dani"

Ya fada yana kallona sai na kauda kai nace ji wannan zai jazamin bakinjini Daman sunan Abba ne ya wankeni,To yana ambaton sunana tsakani ga Allah,Shi ko Dr.Laawal jinjina kai yayi kafin yace"To duk naji zencen ka, nuna min in da in Zainab d'in ta Dawo zata  zauna..?

Kai Tsaye yace"ko ta zauna ad'aki na akwai Tiolet aciki. ko kuma dakin yara sai su koma Dakin Mama tunda Badar na kano duk inda ta zaba duk D'aya ne"

Baki na bude galala ina kallonsa yako hade rai yasha mur,Mama tace"Wannan wani irin lissafin banza ne..?Kai ya girgiza ma Mama yana fadin"Ba lissafin banza ba ne Mama. Mganar su Fadil kuma Fa'iza zata rika kula da su"

Jar uba bansan haka mutumin nan ya raina ni ba sai yau, wato mganar yara Boyi boyi yar reno zata kula da su kuma bai ji kunya ba,Saboda daman baisan adalci ba kuma bai san yadda ake yi ba,Kamar zan yi mgana sai kuma na fasa saboda gani nayi ko nayi mgana babu amfani ammh na rantse da Allah in ya fitar min da ya'yana daga bangarena to sai dai mu fita tare da ni da su,domin  bai isa ba.

Dr.Lawal dariya yayi kawai. Tsakani ga Allah uzuri ya yi masa talauci ai bone ne,Yana saka zafin rai da tunani masara kyau Mama zata fara fad'a ya Dakaatar da ita da fadin"kyalesa Hajiya na Fahimce sa. Shikenan zata Dawo ammh sai aikin nata ya samu,Ina kan nema mata ne,kai dai ka gyara mata muhallin da kasan bazata Takura ba tunda a inda ka Daukota ba'a Takure ka ganta ba"

Kai Tsaye yace"Daddy gidan iyayena Dabam gidan aure dabam. Ba lalle sai ta samu abunda ta ke samu a gidan su ba,in ina da shi zan yi mata abunda yafi wanda take samu a gidan su, in kuma bani da shi zan kwantata daidai misali"

Kai ya jinjina yana fadin"Gaskiya ne'"

Ni kaina nayi mamakin yadda yau ya yi laushi,ammh ba'a san yadda ransa ke bace ba ne. Saboda Zeey yake komai ta rokesa tana kuka kada ya yi Fad'a da Ishaq she love her Husband kuma ta shirya zama da shi a ko'ina. da ya nuna bai amimce ba, sai dai a raba auran sai Hajiya Halima tayi masa Bore ta tafi Chan rugar adamawa ta kai karansa wajen iyayensu akan zai kashe ma zainab aure,Kiransa suka yi suka yi masa Fad'a sannan da ikirarim Zainab akan in ya kashe mata aure to zata shiga Duniya sai ya rud'e zai iya juran komai ammh ban da Nesa da ya'yansa sannan zai iya rasa farincikinsa akan na ya'yansa ba haka ya Dauka yaron yake ba ya Dauka yadda ya rika Juyasa a farko yanzu ma haka zai juyasa. Sannan bai taba zaton Reshe zai juye da mujiya ba,ya dauka shi ne zai so zeey kamar ransa ya rika binta a daidai wannan Lokacin basu ne zasu rika lallaba shi bashine zai rika Lallabasu sai ga shi komai yana Faruwa ba yadda ya yi zato ba shiyasa yayi kokarin Daidaita Fushinsa.

Sannan yana mamakin kamar Engr Usman da ya sani mara d'aukan reni da Tsage gaskiya shine Diyarsa ke zaune in da bata Daraja,Tun farkon had'uwarsa da Ishaq  yasan Fa'iza bata da wani Daraja a wajen sa.

balle in akayi duba da abubuwan da suka yi ta faruwa,Sai dai yayi tunanin kila ra'ayinsa ne ammh shi kam bazai iya barin yarsa cikin wannan Wahalan ba Allah na gani.

Bai jima ba,suna gama mganar su ya tafi Daman jirgi ya shigo daga Abuja zuwa kano sai ya Dauko tashar Taxi zuwa katsina kuma yana jiransa zai maidasa,ni dai tun a matsayar farko ya sallameni na fito na cigaba da aikina ammh mamakin bawan Allah nan bai fita kaina ba wai yara su koma Dakin mama..?lalle bai taba ganin Haukana ba ne zai gan shi kwananan kuwa karyan Iskanci ma yake yi wlh raina ranar yini yayi a bace,ko fara'a ban yi ba shima kila hakan ya gani sai bai min mgana ba,Sai washegari yaran sun tafi makaranta Anum na tsakar gida tana shara basu fara daukan yan Jss1 ba ne wannan karon da wuri ba shiyasa. ammh komai nata Abba ya riga ya Turomin kudin Sakata kawai za'ayi.

ina D'akina ina had'a kudaden hannuna Hafsah zan kira akwai wasu kudi a hannunta ta biya kasuwa in ta Dawo ta siyomin siga na ya kare.

Kamar Daga sama naga ya fad'omin cikin daki a kaina ya tsaya a gabana kere kere,Sau d'aya na kallesa ban kara ba na cigaba da had'a kudina sai naji ya zauna gefena yana fadin"Fa'iza baki ganni ba ne..?

Kai tsaye nace"In na ganka me zan yi maka..?kai ka shigo min Daki ko Sallama baka min ba"

Sai ya gyara zama yana fadin"To Salamu Alaikun shikenan"

A tsime na amsa masa daganan na bama banza ajiyarsa na lura yana so yayi mgama ya kasa sai kame kame yake yi har da tashi yana leka band'aki da kara Duba Dakin na d'ago ina kallonsa cikin mamaki kafin nace"Hala kayi ajiya ne kake nema.?.

Sai ya fara sosa kai yana fadin"A'a ina duba dakin ne sai yau na Lura yafi Dakin yaran nan girma ashe.."

Sai na yi kasake har kofafin hancina na budewa na shaki iska a kasan makoci na kafin nace"Uhm"

Kai tsaye kuma yace"Shine sai nayi wani Tunani me zai hana ke ki koma Dakin yaran nan ita kuma Zainab sai ta zauna anan tunda yafi girma kinga ita ba rayuwar mu da'ya da ita baa,akwai Danne hakki in na ce ta zauna Dakin yaran nan yayi mata karami kinga Dakinta na Abuja?

Wlh yayi biyun wannan Fa'iza.."

Daman nasan za'a zo wajen mai Hali bazai fasa halinsa ba. meyasa nake Tunanin Ishaq zai iya daidaitani da Zainab.?har abada ta fini a wajensa matsayina bazai taba zamowa d'aya da nata ba,Nagode ma da ya sa Rud'add'en kalamansa basu Rud'eni na sake bashi kaina ba.da yanzu na fi kowa nadama.

 Maganar bata D'akina ce ma ta tsaya min arai,na bude baki yafi sau biyar ina rufewa sai kawai na maida Hankalina kan kirga kudin hannuna kama kansa ya yi,sai ya durkusa a gabana Lokaci d'aya yana fadin"Kin gane Fa'iza ki Fahimceni wlh ba da wata munafa nayi wannan mganar ba. Nasan ke zan iya sakaki komai kiyi min sannan zaki zauna dani ko a dakin Bukka ne,ita kuma ba kamar ke ba ce shiyasa kikaji nace haka don Allah kada ki Daukeshi a wani abu"

Ya karishe fad'a yana min uban magiya sai kawai na mike idanuwana ne suka ciko da kwallah me na zama ne.?na tabbata har abada in dai a Rayuwar Ishaq kabir korofi ne ni Fa'iza bazan taba samun daraja ba.

Gaban Wadrope d'ina na tsaya kawai na rasa me zan yi ma saboda takaici,Ina jinsa ya mike yana fadin"Kin ji Fa'iza baki ce komai ba..?

Juyowa nayi bayan na Saita kaina Lokaci d'aya nace"Me kake so nace.?ai ba shawarata kake nema ba Hukunci ka yanke sai kuma ka ke bani Umarni,ba komai kada damu ni daman ban taba had'a kaina da matarka ba nasan tafini Daraja. Zan kwashe kayana kada ka damu ka fad'amata zan bar mata Dakina na har Abada"

 Na fada Lokaci daya ina kokarin wucesa na fita Daga dakin kawai sai ya Riko hannuna a fusace na juyo ina kallonsa irin kallon da na sakar mai ne yasa ya sakeni da Sauri a Shake nace"Nace maka zan bar mata dakin nawa har abada daman ai D'ofane nake kada ka damu. Hafsah daman ba zama zatayi ba Abba na nema mata Transfer zata koma kaduna yara kuma ya'yanka ne ko a soro ka zaba musu su zauna bazaka samu matsala da Fa'iza ba"

Ina gama fadin haka na fice daga d'akin domin ji nayi iskar Dakin tamin kad'an,na rasa ina zan shiga sai kawai na shige kitchen na fara safa da marwa Anum ta shigo kawo kwanuka ban ma ji shigowarta ba sai ji nayi tace"Umma lafiya..?Da sauri na goge kwallar da suka kawomin,na juyo ina kirkiro mirmishi kafin nace"Bakomai kin gama wanke wanken.?

Kai ta dagamin kafin tace"Yanzu zan wanke tsakar gidan ko Umma..?

Sai na jinjina mata lokaci daya ina fadin"Gama ki tayani zuba zobon nan in ya wuce kada su kawo wuta bamu saka ba"

Sai ta amsamin da toh Umma,Falo na koma shi kuma daidai ya fito ina ganinsa sai na juya na fita wlh bana son ma ganinsa,a kwanakin baya sai naji kamar Burina zai samu Rauni na fara Tunanin sauke kudurina,ammh yanzu na ji na samu karfin gwiwan da zan iya tunkaran komai menene tabbas ina Bukatar Sabuwar rayuwa ina son na shaki iskar yanci nima.

Gabadaya yini yayi son kara min mgana ni kuma ban yarda mun had'u ba,ga shi dai nace na amince ammh kuma Fuskata ba fara'a Da Daddare na kira Abba muka gaisa sai na masa mganar Hafsah cikin barkwancin sa yace"Ina ta kokarin nema mata Transfer Fa'i..Wlh tallahi ko kuma ba domin aure ba,da gabad'aya zan tattaraku a gidana"Sai nayi dariya ina Tambayansa Ammi yace"Tana chan ta na kwalliya kinsanta gayu gayu dai Mamam Nanah taki ta bar ma yara"Da Sauri nace"Abba ta bar ma yara ka kyallo wata yar caras"

Sai ya fara Dariya yana fadin"Fa'i Laala..aiko baku isa ku hanani kara aure ba.ku gama shafa dai jan bakin da hoda sai nayi ehe"

Ni dai sai Dariya nake yi tuni Abba ya mantar dani Damuwar da nake ciki mun jima muna mgana,Sannan muka yi sallama,Mun gama wayar kenan sai ga Kiran Nana Fatima itakam sai da taji yanayina ba Dadi tace"Fa'in mu ya ya ne.?naji ki wata so silent ne"

Sai nayi saurin ce mata kaina ke ciwo sai tace na sha mgani na kwanta da Safe zamu yi mgana da haka muka yi sallama sai kawai na kira Goggo ita har ta Tsorata cikin Tsoron tace"Fa'iza lafiya kuwa.?goma saura na Dare fa"

Ina dariya nace"Lafiya lau Daman na kiraki mu gaisa ne naga kwana biyu kin manta da D'iyarki"Sai goggo tayi dariya kafin tace"Kina raina Fa'i nasan kina lafiya ke da yaranki,hidima tayi miki yawa Fa'iza kinsan sana'ar hannu tana da wahala nasan sai hankali yanzu"Gyada mata kai nayi kamar tana ganina kafin nace"Na saba goggo ba matsala ga Anum kinsan tana gida sannan in Hafsah na gida tana taimakamin,haka ma yaran ma in sun dawo. Amir kinsan san shi sarkin aiki su shara har girkin su taliya ya iya Goggo"Sai goggo taji dad'i har sai da ta bayyana min cikin Murnan ta tace"Masha Allah Dakyau.Dama iyaye su rika tunani irin naki Fa'iza su rika koyama yaransu, aikace aikacen gida tun suna da kananun shekaru, saboda taimakon iyaye da kuma taimakon kansu a duk inda Rayuwa zaata kai su Allah yayi albarka Allah ya shirya miki yaranki,Allah ya Daukaka su alfarman Annabi muhammadu salallahi alaihi wasallam"

sai na samu kaina da Hawaye sun cikamin kwarmin idanuwana, ina amsawa da Ameen Ameen cikin jin dad'in da ya bayyana har a murya ta. kafin nace"Goggo Baba ati tana kaduna abunta..?

Goggo tace"Tana ko chan Fa'iza ta samu hutu,Inno tace bata son ta dawo ta samu abokiyar zama ai ma ginin Abban naki an kusa gamashi kila in ya kammallu ta dawo"

Kai tsaye nace"Kila ta dawon to.nima Hutu nake son nazo miki Goggo

"Dariya tayi ina jin ta Dauka Zolaya ce sai tace"Ina maraba da Fa'iza Allah ya kawo ki lafiya"na amsa mata da Ameem daganan ta tambayeni megidan da Yanayin zaman mu da Mama nace lafiya lau kamar bata gidan.

Goggo tace'"Nima naga duk tayi sanyi.Rayuwa ta gara Saudatu daman na fad'amiki watarana sai tafi ruwa sanyi a wajenki"na jinjina kai ina Tunanin yadda Mama ta zama kamar kankara yanzu,Duniya ce da mutanen cikinta suka maida ita haka.

Bayan munyi sallama da Goggo na jima ban yi barci ba,Hafsah tana Dakin yara tana karatu sun kusa fara Jarabawa Ni da Anum me muke kwance ita har tayi barci ni kuma ina faman sake sake a daran nan na yanke ma kaina abunda zai fissheni bayan na roki Allah kada ya barni ni kad'ai ya yi min jagoranci.

Da Safe wasai na tashi,Duka aikin gidana ni nayi abuna. Abun kari kawai Hafsah tamin,Sai aya data wanke ta mikamin nika kafin ta fita,ni kuma sai ta barni da Dafa zobo,Ganin yadda nayi ne ko da Safe saboda a gaban yara ne muka gaisa na Sakar mai Fuska suna watsewa na had'e raina gim ko fara'ata bai gani ba.

Mama ta aiko Anum ta kirani ina zuwa na durkusa na kara gaisheta ta amsa cikin kallona Lokaci d'aya tana fadin"Ishaq ya same ni da wata mgana. Wai zaki koma Dakin yara Zainab zata zauna a dakin ki  nace kin amince ne yace eh! shine nace sai na tambayeki"

Kai tsaye nace"Eh Mama yau zan fara ma Tattara kayana. yaran kuma duk inda ya ijiyesu daidai ne a wajena"

Sai ta muskuta tana fad'in"yaran ba matsala ga daki nan su zo mu zauna damam xaman kada'ici ya isheni kece bana so mu kara yi miki wani rashin adalci kamar yadda muka yi miki a baya,Shiyasa nace sai naji ta bakin ki,ki fad'amin in hakan bai miki ba to bai isa ba"

Sai nayi mirmishi takaici kafin nace"Bakomai Mama na amince ni daman ba mazauniya ba ce.Dakin daman ai jingina ne, Zainab ce ke da wajen zama na har abada"

Nasan bata gane kan mganata ba, sai dai nauyin baki yasa ta kasa min mgana har na fice,ina komawa Daki bayan mun gama hada zobo mun zuzzuba agoruna Anum ta jera a Frezee,kunin Aya ne zan had'a shi jira nake nepa su kawo wuta.

Anum na bar ma sharan Falo da gyaran kitchen, ni kuma na shiga Dakina na fara had'a kayana a waje daya duk abunda nasan nawane na Daukosa babban ghana d'aya gareni itama sakon kayan sallar yara aka kawo aciki daga kaduna kuma tamin kad'an sai na kira Hafsah nace in ta shiga kasuwa ta siyomin manya guda biyu

  Kafin dare wardrope dina  kaf ba kayana aciki Hafsah ta siyomin manyan ghana guda biyu sun isheni na dura komai nawa,aciki akwai wasu kayan da ko di'nka su ban yi ba. na Ishaq ne ban kara dinka kayan da ya siyamin ba,tun bayan auransa da zainab hatta kayan da Anty Binta ta bani na Fad'an kishiya suna nan suma na Had'a masa kayansa waje daya.

Gadajen yara daman duk ya b'abb'alle,sai nayi tunanin na basu na Dakina da wardrope din ya ishe su saka kayan su,nasu  kuma a gyara ma Anum tunda ita macece ni ba zama zan yi ba,so kayan basu da amfani a wajena.

Da dadadre suna falo da shi yana musu karatu,na fito ina kallon Amir kafin nace"Amir ku fara had'a kayanku waje daya,ka taya kannen ka su had'a nasu .Anum na fara had'a miki naki kema kije ki karisa in kun gama"

Da mamaki suke kallona ammh sai na juya zuwa kitchen ina ji suna tambayanta Umma ina zamu..?

Sai na bar mishi ya basu amsa sai kuma ya kasa ina kitchen din ya Biyoni yana fadin"Fa'iza bafa yanzu ba ne naga kina ce ma yara su had'a kayansu'

Ina juya tumatur din da Hafsah ta Dora Tafashensa akan wuta nace"Eh gwara su fara had'awan tun yanzu kada sai lokacin yayi kuma basu samu sararin had'awa ba. gwara tun yanzu kowa yasan matsayinsa"

Na fad'a ina kokarin rab'asa na bar kitchen din sai ya bake hanyar yana fadin"Fa'iza.."

Kai Tsaye na kallesa ina fadin"Na'am Ishaq"

Sai mamaki ya hansa mgana,Girata na Daga ina fadin"Bani hanya na wuce"

Ba musu ya matsamin na fice ina jin wani irin Tukuki acikin kaina Amir ne ya taso yana fadin"Umma ina ZAMU KOMA..?Ko zamu yi tafiya ne.?

Ban kallesa ba nace"Ku yi abunda nace Amir kaji"

Sai ya amsamin da Toh ammh sai jikinsu duka yayi sanyi,nan na barsu na shige Dakina ina Sauke numfashi,Adaran na saka Hafsah ta taimaka musu suka had'a kayansu itama ban bata ikon mgana ba sai dai ta tambayi yaran Anum tace"Umma bata ce mana komai ba"

Sai itama bata kara mgana ba, ammh ta kara tsorata da ganin na kara had'a kayana a karo na biyu wannan karon bata san kuma me zai iya Dakatar dani ba.

Lalle kana naka Allah na nashi Washegarin jumma'a da Safe Ishaq ya samu wayar Dr.Lawal inda yake sanar da shi an gano saka hannun nan ba nasa ba ne, kwaikwayo ne na wani abikin aikin su.Mr James mutumin osun State ne Daga office din sa sai na Ishaq,da shi aka had'a baki aka kwaikwayi saka hannu Ishaq Daga office dinsa aka fitar da wad'anan kudaden,yanzu Mr james din ya tafi gida chan Osun,abu d'aya ya rage bangaran Cibiyar Bincike ta EFCC ita zata ba da umarnin a kamo James ya fad'i gaskiya sannan ta wanke shi Daga zargi.

Da murna ya fito yana fad'a mana,ni da Mama da muke tsakar gida ita tana shan iska ni kuma ina Dafa zobo,sai na manta da abunda ke tsakanina da shi na mike ina fadin"Alhandulillah. Ka kira Abba kira Abba ka fadamasa"

 Mama ko sai da tayi sujuda tana godema Allah sai kuka shi ko Jiki na rawa yace"Shima Daddyn haka yace na kira Abba..yayi ta kiransa bai same sa ba'

Kiransa yayi sau biyu bai Dauka ba nima na Ruga daki na Dauko wayata na kirasa bai Dauka ba.

Sai na Kira Ammi bayan mun gaisa na tambayi Abba tace ya tafi Office ina fad'ama Ishaq yace"kila ya shiga meeting ne. mu basa Lokaci"

Anum na gefe tace"Daada me ya faru..?

Cikin farinciki ya dagata sama yana Fadin"An gano gaskiya Anum.angano bani da hannu a satar kudin ma'aikanmu"Sai itama ta washe baki tana fadin"Congratulation Daada"

Sai da yagama juyi da ita sannan ya sauketa yana kallona Lokaci da'ya yana Fadin"Fa'iza kinga abun Allah ko..?

Sai na jinjina kai ina fadin"Allah yasa karshen wahalan kenan"Mama ta amsa da ameen ta mike tana fadin bari ta kira Binta Yaya ishaq ya hanata da fadin"ki bari mu yi mgana da Abba tukunnah"

Da sauri nace"Eh Mama gwara labarin ya kamallah Tukunnah"Sai ta gyada kai yini mukayi Duba waya ko Abba zai kira sai Dare ya kira Yaya Ishaq,kafin shi yayi masa mganar ya fara yi masa. yace sun yi mgana da Dr.Lawal yanzu nan ya kira Engr sun yi mgana shima ya ce Mr ABDULGHAFFAR ABDULBASIT BABATUNDE ya dawo Office satin daya gabata,zuwa gobe ko jibi ya sauraresa"

Nima Abban ya kirani yayi min bayanin komai ya karishe da fadin"Last friday ai muna Abuja da ni da Maman Nana mun je duba Hajiya Kudirat olamide,itace kakar Engr sun dawo gida bayan an yi mata Dashen koda,da mukaje mun samu Engr din a gida sai na kara tunasar da shi mganar aiko yana masa mganar yace a tuna masa in ya shiga office sai fara Duba Case din,balle da Engr ya fad'a masa Ishaq Inlow ne a waje na,ya  tabbatar min da ba matsala mu jira cewarsa kawai"

 Da wannan labarin mai Dad'i muka kwana sai dai na Tsananta addu'a na Allah ya kawo mafita da karshen al'amarin.

 Har yara na saka suka yi ta addu'an Allah ya kawo ma Daada mafita shima nace yayi ta addu'a da ikon Allah sai an wanke sa daga wannan zargin.




G

*Janafty*




[7/19, 2:47 PM] Hauwa Galadima: *KNKB2019*


*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*

*09069067488*


Allah maji rokon bayinsa kwana Biyu Tsakani. ranar Litini da misalin wajen sha biyu na rana ya samu wayar Abba in da yace maza ya taho kano yanzu zai had'u da Abdul'Ahad a Airport din Aminu kano zasu hawo jirgi zuwa nan Abuja.

A na nemansa a Office din Chairman na EFCC,daganan bai yi mai wani karin bayani ba. shiyasa sai ya Rude,ya fito daga daki yana fad'amin cikin wani yanayi kafin ya kara da cewa"Gaba na ta fad'i Fa'iza. Allah yasa ba wata matsalan ce ta sake kunnowa ba"

Cikin son kwantar masa da Hankali nace"Haba ba komai abunda muke fata ne jeka ka fad'a ma Mama,bari na saka maka ruwan wanka ka shirya kada ka b'ata Lokaci"

Bai min gaddama ba ya wuce Dakin Mama ya fad'a mata ni kuma na je na kunna gas na saka mai ruwan wanka Tuna murhun gawayina yana waje girki na d'ora akai,sama sama ruwan yayi zafi na sake mai nice har bayi sai da na kai masa.  

Da kuma ya shiga wankan na Lalubo masa kayan da zai saka,yana wankan sai ga yaya Abdul'Ahad ya kirasa ni na d'auka muka yi mgana yace yana kano yana Jiransa, daman ya kawo Raliya ta gaida su Hajiya ne, sai ga kiran Abba so in ya taso ya kirasa yadda zasu hadu a Filin jirgin kawai.

Ko da ya fito wankan mun gama wayar,Sai rawan jiki yake yi ya kasa natsuwa fad'i yake yi"yanzu a chan kano zamu hadu da Abdul'Ahad din?

Kai Tsaye nace"Eh mana yanzu ma ya kira wayarka na d'auka muka yi mgana,yace in ka taso ka kira sa"

Sai ya amsamin da toh fita nayi na basa waje ya shirya nasan ba shi da kudi cikin kudad'en sana'ata na kirgo Dubu Biyar na bashi Saboda nasan in dai suna tare da Abba bazai rasa kudi ba in yaje koda na dawowa ne, har ya shirya cikin shadda fara riga da wando,Sai Hula daya sanya ina shigowa yace"Ba sai na dauki wasu kaya ba ko.?

Kai Tsaye nace"Me zakayi da kaya kuma? in ma kwana ya kama ka kana da Muhalli da wasu iyalan achan ka manta ne"Sai ya sauke ajiyar rai kafin yace"Wlh duk na Rud'e ne Fa'iza"

Ina mika masa kudin Hannuna Lokaci daya ina fadin"Ka kwantar da Hankalinka babu abunda zai faru ai Yaya Abdul'Ahad yace Abba na chan shima in kaji zuciyarka bata natsu ba kayi ta ma Allah kirari da Hailala, yafi ka zauna kana wannan zullumin"

Cikin gamsuwa ya gyad'a min kai kafin ya karbi kudin da nake mikamasa Lokaci d'aya yana fadin"Wannan fa na menene..?

Nasan ya rude ne, kila ya Dauka haka zai tafi ba kudi sai na juya ina fadin"a kasa zaka je kanon.?

Sai ya Dafe kansa yana fadin"Shaa..Fa'iza wlh na manta"ina jinsa yana bin bayana har Tsakar gida Inda Mama ke jiran fitowarsa.

Sallama yayi mana ya tafi mama na sakamai albarka da fatan Allah yasa mu dace. ni kuma mun rabu kan sai ya kirani naji yadda ake ciki.

Mun yi masa fatan sauka lafiya tare da Fatan Allah ya tsaresa ni da mama Anum bata san tafiyarsa ba taje kai min nikan Aya,sai da ta dawo nace tayi ma Daada addu'a ya tafi Abuja.

Tafiyarsa ba Dad'ewa Yaya Abdul'Ahad ya sake kirana na fad'a masa ya kama Hanya sai yace ya yi ta kiransa bai Same shi ba,yana ga network ne, bari ya Saurareshi.

Mu dai ya tafi ya barmu da zullumi,bayan ya isa kanon mun yi waya yace suna Filin jirgi yanzu zasu tashi zuwa Abuja .

Daganan shuru bamu kara jinsa ba,Dagani har Mama muna ta zullumi ni kuma kunya ta saka na kasa kiran Abba ko Yaya Abdul'Ahad kada suga kamar na damesu shiyasa na daure Ammh ko Mama bayan mintina sai ta leko d'akina tana fadin"Fa'iza shuru Ishaq bai kiraki ba ko..?

Ni kuma sai nace mata"Mama in ya kirani ai zan gaya miki. kuma nasan in sha Allahu zai kiramu"

Daganan sai muka koma muka Nad'e hannaye,muna jiran tsammani sai wajen karfe goma sha d'aya saura,ya kirani lokacin yara har sun kwanta Hafsah ce kadai a falo tana karatu,saboda sun fara jarabawa,ni kuma ina dakina sai dai ko da na Dauka bana jinsa har sau biyu,daga baya sai ya kira Wayar mama da ita suka fara mgana kafin ta leko da kanta ta kawo min waya bayan mun gaisa sai kawai ya bige da cemin"Wato Fa'iza ki ji tsoron Gwamnati da kuma in kana da Kafa a Gwamnati. kinsan  24hrs ya yi yawa Efcc ta saka an kamo Mr James tun jiya kuma yayi mgana. Dalilin dayasa ma aka kirani kenan ma"

Cikin son jin ya aka haihu a ragaya nace"To ya kuka yi da su yanzu..?

Cikin Farinciki yace"Ya amsa laifinsa Alhamdulillah an wankeni daga wannan zargin. ashe da wani suka had'a baki,kinsan kana zaune da mutum bakasan ya tsaneka ba ni wlh lafiya nake zaune da kowa,Yanzu haka dai an yi cike ciken Takardu an tura chan ma'aikatanmu,kuma Efcc ta bani Hakuri tare da alkawarin zata maidamin da kudina da ta karb'a sun rike Mr james a hannunsu suna kara Bincikensa. ammh ni nace na yafe masa Har abada"

Cikin jin dadi nace"masha Allah. Alhandulillah gwara daka yafe masa, ammh shi miye riban abunda ya aikata..?

Kai Tsaye yace"Matsayina ya ke so. Kuma ya samu tunda bayan Dakatar dani shi aka d'aura akan kujerata"

Cikin mamaki nace"Ikon Allah daman ai abun duniya fararre ne kararre ga shi yanzu komai ya kare masa"Cikin jimami yace"Wlh kuwa. Muna chan har karfe Takwas na dare da ni da Abba da Daddy da Abdul'Ahad,da wasu cikin ma"aikatan mu, sai shi chairman na Efcc din da Sauran ma'aikatan su da wanda suka ja Ragamar case dina a hannunsu.Wh Fa'iza Abba yayi min kokari ke kinga yadda Chairman din nan ya dinga bama Abba hakuri.?gaskiya mutumin nan yasan karamci kuma ba fa ba Bahaushe ba ne, Fa'iza Bayarbe ne. abunda na Lura dashi Megidan Abba da yake kira Engr na ji da Abba sosai. tsakani ga Allah cikin gaggawa akayi komai aka gama,kuma Engr ma ba shi a wajen,naji Abba yace yana Edo ki tayani godiya Don Allah"

Ajiyar rai na sauke kafin nace"Alhamdulillah Allah ya kara Tsarewa yanzu kana ina ne.?ko kuna tare da su Abba ne..?

Da sauri yace''Ina wajen zainab nan zan kwana zuwa gobe. Abba daganan jirgi ya hau zuwa warri suna da taro gobe Abdul'Ahad kuma ya hau jirgin kano"

kai na tsaye nace"Ba damuwa ai kana gida kayi zaman ka mu nan ba mu da matsala"Shima kai Tsayen yace min"Aa zan dawo ai ba wajenta nazo ba, itama"

Ban tsaya jan mgana ba tunda ba Hurumina ba ne,in ba wajenta yaje ba, me ya hana yabi yo  Ya Abdul'Ahad su dawo tare ya tsaya nan zai kwana?shine zai zo yana min wata mganar banza jin nayi masa shuru yasa ya kira sunana sai na amsa sai kuma ya kasa mgana sai kawai ya bige da Fadin"Sai dai na dawon"

Yara ya tambaya nace sun kwanta yaso yajani da mgana nace mai barci nake ji duk nagaji cikin Dariya yace"Ai ina samun wani babban aiki duk zaki daina sana'ar nan ta wahala Fa'iza"

Sai ya bani dariya har sai da na Dara kafin nace"To ai ko ni ce da kaina na samu babban aikin ban ji zan dakatar da wannan sana'ann tawa, domin tamin komai a Rayuwa sai dai na nemi Hanyar ingantata kawai'

Da sauri yace"Eh hakane kam.."ina ji sama sama ana mgana ta gefensa ban Tsaya ji ba na kashe wayata na yi kwanciyata sai dai har ga Allah na tayasa murna sai naji kamar komai dake faruwa Mafitan da na Roki Ubangiji ne ya sama min ne.

Zuwa washegari mgana ta watsu a Dangi Mutanen karofi dai Hafsah ta Fada musu su jamal kuma duk mama ta kira su ta fad'a musu abunda ke Faruwa. sannan sai ta kara da fadin wlh duk sanadin Kanin mahaifiyar Fa'iza shi ya tsaya har aka wanke Ishaaq,Har daki mama ta biyoni Tana min godiya ta kuma saka na kira Abba ta kwararamai godiya.

Abba yace"Hajiya kada ki damu.Da Fa'iza da Ishaq duk d'aya suke a wajena duk abunda nayi kamar nayi ma Abdul"Ahad ne"sai kimar sa ta karu a idon Mama,sai da yaya Ishaq ya kwana Biyu sannan ya dawo ranar kuma Anty Binta tazo ita da Anty mahma,sun zo yi ma Mama barka da arziki,Shima din yana samun wayoyin yan'uwa da abokan arzuka harda abokan aikinsa da suka Dad'e ma basu yi mgana, suma labarai yakai headquater din su tunda EFCC ta tura Takardan wanke Ishaq din daga dukkan zargi.

Su Goggo duk sun kirani hatta ko da Yaya mariya,ta kirani su Nana Fatima ma duk sun kirani tace Abba yace su kira su yimin barka da arziki,Har da Ammi kuma naji dadi sosai masoyin ka ne Zaka yi rashi ya janjanta maka sannan in kasamu shima ya tayaka Murna,su Amir nata murna domin ce musu yayi da kansa kud'in Daada ya Dawo ya'yan Umma nan suka Biye masa suna ta tsallen Murna.

Allah shi ke ba  da samu da rashi kuma shi ke da Daukaka da Nasara shu kuma ke da Fad'uwa da Tashi,kwana Biyar Tsakani da EFCC ta wanke Yaya Ishaq ya samu kiran gaggawa daga Headquater dinsu na Abuja aranar ya tafi sai dai mota yabi,bai kirani ba ina ta neman wayarsa a daran a kashe sai da asuba kawai zainab ta kirani ina Dauka tace"Congratulation to us Maman Amir kinga Kuduran Allah ko..?.

Mamaki ya kamani bansan kan mganar ba,ina shirin tambayanta sai kawai ta zarce da fadin"Jiya da Honey yaje ma'aikantan su upper ce suka basa ta maida shi aiki da matsayi mai girma,sun mai da shi office din su na Lagos zai fara aiki nan da wata D'aya"

Karfaffan ajiyar zuciya na sauke a Fili na furta"Alhamdulillah!

Cikin Farinciki tace"Wlh ai tun jiya nayi ta neman wayarki ni da shi bamu samu ba, yanzu haka ya tafi masallaci ne,shi nace bari na kiraki na fara yi miki albishir"

Ciki jin dadi nace"Masha Allah. Allah ya sanya albarka,ya sa alheri a cikin aikinsa damu gabad'aya"

Ta amsa min da ameen ameen bamu jima,muna mgana ba muka yi sallama,Daganan sai na tashi na shiga Dakin Mama na isketa tana azkar bayan mun gaisa na fada'mata abunda Zainab ta fad'amin Mama ta washe baki tana Hamdala ta daga hannu sama tana yi ma Allah godiya.

Daganan dakin yaran na koma na iske sun idar da salla,Amir da Musty suka hada baki wajen fadin"ina kwana Umma"ina mirmishi na amsa ina fadin"Daada ku ya samu aiki a lagos"Sai suka fara murna har da tsalle Ahmad kenan.

Fita nayi na koma falo sai ga Hafsah ta fito na gayamata, Anum na bayanta ta Daka tsalle tana fadin"Eyyee zamu koma Lagos ehyee.."

Sai tsalle take yi ina kallonta ina mirmishi,sai da gari yayi shaa Yaya Ishaq ya kirani cikin Tsananin murna yace"Fa'iza albishirinki"

Ba da niyyar gwasale shi ba nace"Zainab ta riga ka. Har na shaida ma Mama da yara"Sai naji kamar gwaiwarsa tayi sanyi duk da haka bai nuna ba nan take na tayasa murna ya amsa yana fadin"Wlh ban taba saka rai aiki nan zai dawo gareni ba,Ammh sai ga shi sun kirani sun bani takarda har da karin girma da kuma sauyin wajen aiki"sai na tare sa da fadin"Haka Allah ke lamarinsa. Sai ya baka ya kwace in kuma yaga dama sai ya maida maka mafiyinsa"

Cikin gamsuwa ya gyada kai yana fadin"Hakane wlh. Allah ya datar mu"

Na amsa mai da Amen mun yi sallama yace zuwa anjuma zai kamo hanya ina shirin nace sun yi mgana da Abba?sai na sha'afa sai ga shi ma Abban ya kirani da kansa ina Dauka yace"Congratulation Dougther yanzu na samu labari wajen Dr.Lawal"

Cikin mirmishi nace"Daman yanzu nake shirin kiran ka Abba"

Kai tsaye yace"Gashi ni na rigaki,Duk na kira sauran yan'uwaki na shaida musu. Allah ya tayasa riko Zaki koma kusa da yar'uwanki Fadila tana ta jin dad'i da na shaida mata"

Sai mirmishi na ya Dauke da yake da cijewa muka gama wayar nan,yinin ranar sai amsa waya nake yi har mamakin yarda mganan ta Je, kunnen kowa nake yi,Yaya Asiya tace min Goggo ta fad'amata sai ban yi mamaki bam Saboda ni na kira ta da kaina na fad'a mata.

Ranar ya dawo da Daddare,yana shigowa ni ya fara cin karo dani a Tsakar gida ina kaye kayen kaya sai ji nayi ya Daukeni Caraf ya dagani sama yana juyi dani cikin Firgita nace"Innalillahi ka sauke ni don girman Allah"bai saukenin ba sai da yaji muryan Mama sannan ya saukeni Tana fitowa ya sakeni ya nufeta yana Fadin"Mama.."

Cikin jin dadi tace"Na'am Ishaq naji abun arziki Allah ya sanya alheri"

Ya amsa mata cikin fara'a ta dafa kansa tana sakamai albarka,mganarsa yaran sukaji suka firfito suna masa oyoyo d'aya bayan d'aya ya dinga dagasu yana saukewa Anum sarkin mgana tace"Daada yanzu Lagos zamu koma..?cikin shafa kumatunta yace"Sosai chan zamu koma."

Musty yace"Daada dukkan mu?

Ya gyad'a masa kai Lokaci d'aya yana fadin"Dukkan mu mustapha.."

Amir ne ya kalleni yana fadin"har da Umma da Mama..?

Kai tsaye ya bashi amsa da"Eh har da Anynku dasu Farhan"

Sai suka saka Ihu,yana biye musu da Dariya ni dai sau daya muka hada ido na kauda kaina,Daki na koma shi kuma da yaransa suka shiga Dakin Mama sai chan ya fito Hafsah tayi mai Fatan alheri ya amsa bakin nan har har kunne.

Garin ana d'an zafi zafi da ruwan Sanyi yayi wanka na kai masa abinci yana ci yana bani labarin abubuwan da suka faru cikin hirar nasa ne yake ce min"Sai zuwa gobe zamu yi shawara Fa'iza. nan da wata d'aya suka ce zan fara shiga office bana so na kara raba iyalaina Waje d'aya zan had'eku bari kudi su shigo kawai"

Ina kallonsa nace"Yaushe su sukace zasu maida maka kudaden na ka..?

Yana lomar shinkafa yace"Ko wani Lokaci zan iya gani suka ce"

Ni dai ina jinsa yana ta Tsara abubuwansa nayi masa gum sai in ya sako sunana ne zan daga kai nace tom ko Umh,naja bakina na tsuke ni dai gajiya nayi naje na kwanta shi da yaran sa falo suka Dawo suna ta Shagalinsu tun ina jinsu sama sama har barci ya Dsukeni.

Tun daga washegari muka yi samun bakin Taya murna wad'anda basa kusa sun yi mana ta waya Goggo tazo Yaya isa ya kawota tayi mishi Murna,Anty Binta baki har kunne,ita da Mama,Jamal yana makaranta suna Jarabawa Badariya dai sai ta zo gida ta kwana Biyu,ranar da ta dawo zuwa tayi ta Rumgumeni tana fadin"Ina murna matar yaya. Allah ya sanya alheri"

Na amsa mata da mirmishi sai ta fara zolayata da fadin"Har mun fara kewa Anty Fa'iza yanzu chan ikkon zaku koma.?

Kai Tsaye nace"Za dai ku koma Badariya"

Cikin jimami tace"Ni ina kano kin manta,ban gama hidimar kasa ba"

gyada kai nayi ina fadin"Duk da haka dai. in kika gama chan zaki koma indai ba aure kika yi ba"

Daganan muka cigaba da Hira duk akan mganar aikin ne,ni da kaina na Kira Hajiya na sanar da ita,tace zata zo taya murna abun mamaki har da kawayen Mama da suka gujeta a baya har da su a masu taya murna. Hajiyar Dala bata zo ba ta dai kira mama a waya da dashi da Uban gayyar ta masa murna nima su Nana Fadila duk sun kirani ita har ta fara murnan zan dawo kusa da ita. ban ce mata komai ba sai yake a raina ko nace kiyi hakuri Fadila hakan bazai tabbata ba.

Baki muka yi ta samu ta ko'ina abun har mamaki yake bani,shi kan shi yace wasu wlh sun manta ma dashi Lokacin da ya rasa ammh sai ga shi har da su a sahun masu murna,mganar da yace zamu yi duk bamu samu mun yi ba. nasan kan mganar tafiya lagos ne tuni mutane har sun gama daukan zencen Lagos zamu koma gabad'ayanmu har da yara.

Yaya mariya bata zo ba. A waya ta kira ni bayan mun gaisa tace"Ashe kuma abun alherin da ya samu kenan..?

To Allah ya sanya albarka.Goggo ke tad'in Lagos zaku koma daa ke da yaran gabad'aya"sai kawai na ce mata haka yace,yaya mariya bazata sauya ba sai ta karkace baki tana fadin"itama yar abujan fa?ina fatan chan zai barta domin Lagos ke kad'ai zaki zauna kamar yadda ki ka bar mata Abujan ita kad'ai"

Sai nayi dariya kafin nace"Ya ce gabad'ayanmu zamu koma har da Mama"sai ta tabe baki kafin tace"A na nan dai jiya iyau"

Ban biye mata ba shiyasa bamu dad'e muna mgana ba muka yi sallama.

Bamu samu zama ba sai da mutane suka Tsagaita,Ranar ma da daddare,Dariyan Musty muka sha wai har yayi ma yan ajinsu sallama su zasu koma Lagos gabad'aya.ina Dariya nace"kaji yaro da zakewa. "

Yaya Ishaq na gefe yace"Ba wani zakewa ya fad'a musu gaskiya da ya tafi ba sallama fa..?

Amir yace"Umma da Anum na zuwa makaranta da tuni kowa ya sani"

Ita muka kallah yadda tayi yasa muka kwashe da Dariya,kowa yasan zata aika da bakinta kamar na aku,har fa gidan da muke kai nika da taje sai da tace lagos zamu koma zamu tashi Daga gidan nan kamar an tambayeta,Amir ke fadin da yaje kai nika suka tambayesa,kallonta nayi ina fadin"To wa ya aike ki gwana..?

Cikin Shagwaba tace"Umma sallama nayi musu kada suga min daina kai nika"Sai ko muka kara saka Dariya sai ta fara kokarin kuka Ya jawota jikinsa yana fadin"manta da su mamana ki fad'a ma kowa lagos zaku koma sannan ki kara da fad'a musu a jirgi zaku tafi"Da sauri ta waro ido tana fadin"Daada jirgi fa mai tashi sama..?

Ya daga mata kai kawai sai ta fara Tsalle tana murnan zasu hau jirgi Ahmad da Musty na tayata,Amir dai na zaune yana bin su da kallo.

Yaro shi yana son sauyin muhalli,Amir ne yayi hankalin cewa'Daada in muka koma chan wata makarantar zaka sakamu?

Yana dariya yace"Amir d'an makaranta. Kada ka damu makaranta mai kyau zan saka ku in sha Allahu"

Daganan ya cigaba da biye ma yaran suna masa tambayana yana amsawa.

Ni har zan shige daki yace yana son mgana dani,dole na hakura sai da yaran suka yi mana Sai da Safe suka shige Dakin su,sanin in yace muje Dakinsa bazani ba yasa muka zauna afalo ya fara da gayamin EFCC ta dawo mai da kud'insa kimanin Naira miliyan Sitti,Tunda ba lalle kudin mutum su dawo duka ba.

Shine  ya ke ce min yanzu ya yanke shawaran zai fara yin gaba yaga yanayin garin da komai,zuwa ya sama mana inda zamu zauna tunda Abba yace zai had'asa da mijin Nana Fadila.

Ban yi mai musu ba nace shawaran shi tayi sai ya cigaba da fadin"gida nake son siya babba wanda zai wadace mu. In bai samu yanzu ba, sai na kama Haya zuwa gaba in na samu a hankali a hankali sai na siya na kaina"

Kai Tsaye nace"Gwara ka mallaki naka zai fi. Kuma mganar ka siya babba kada ka yi asaran kudin ka,ka siya daidai zaman mata d'aya da Dakunan yara,kana da maza sannan mace Daya gareka Anum,Ga mama ga su Badariya duk da ita tace sai ta gama hidiman kasa tukunnah"

Cikin mamaki yace"Bangane wajen mace da'ya ba.?ina miki bayanin itama Zeey na gayamata ta fara shiri,kila ku zaku fara yin gaba ita sai daga baya zata same mu achan"

Mirmishi nayi kafin nace"Ka gane mganata mana. ni fa bazan bika Lagos ba"

Sai ya yi karamin Tsaki kafin yace"To sai ki zauna a ina.?kai tsaye nace"A nan mana"harara ya sakar min kafin yace"kina Hauka ne.?ina wata Duniya kina nan?wazai barki di'n? kafata kafarki, kafar yarana Fa'iza"

Sai ban ce komai ba na kauda kai bai Damu ba ya cigaba da fadin"Abba yace na siya mota saboda zirgan zirgan  zuwa wajen aiki da sauran dai Bukatu"jin sa kawai nake yi ina tunanin ya dauka wasa nake yi sai na kara gyara zama nace"Da gaske nake yi. ni bazan bika Lagos ba"

Sai kawai ya mike yana fadin"Bina ko kamar kin gama shi Fa'iza meyasa zan barki.?ba mai kara rabamun hankalina yanzu iyalaina duka waje d'aya zan had'asu"

Kai Tsaye nace"Yanzu kuma.? Ni fa kada ka manta na saba zama ni kad'ai a baya ma kana Abuja ina katsina, kuma na zauna lafiya sai don ka koma Lagos..?

Kallon sai ki yi yayi min ya shige Dakinsa ya bugo kofa sai ya bani Dariya ya Dauka wasa ne?lalle ko zai ga wasa alokacin da bai yi tsammani ba.

Ya samu mun fara tattara kayanmu,ni daman ma na had'e nawa na yara ne ba'a gama had'awan ba,yace bazai saki gidan ba sai in ya siya wani inda zamu rika sauka inda munzo,tunda dagamu sai kayan sawa zamu tafi sauran kayan gida Sabbi za'a siya kawai,har sun yi mgana da megidan ma ya bashi kudin Shekara,Hafsah kuma daman bata da matsala Transfer dinta ya samu kaduna zata koma,ranar muna tattara kayan kitchen waje daya Anum tace"Umma shikenan kin daina zobo da kunin aya..?

Kai tsaye nace"In ji wa..?zobo da kunin aya yanzu na fara"

Na tuna ko ranar da Hajiya tazo min murna na fad'a mata lagos aka kaisa tun kafin na yi mata bayani tace duk inda naje kada na saki sana'ata domin sana'ar hannu abu ne mai kyau da amfani kuma na aminta da mganarta na Jaraba kuma naga riba,kuma dayake nima baama Lagos din zani ba ballatana ya dameni, inda zan koma da zama na tabbata zan rika yin ciniki sosai.

Kuma ko da muke tattara kayan ina sana'ata ban fasa ba,Mama ma nata shiri tunda yace in yaje ya dawo har da su Anty binta za'a tafi saboda suga waje,Sati hudu Tsakani ya tattara ya tafi,jirgi ya bi daga kano zuwa Abuja,bayan ya isa headquater din su ya saka hannu sun bashi accepted letter,Daman yana zuwa ya kira mijin Nana Fadila shi Costume ne,gidanta ma ya sauka yaci abinci ya huta sannan suka fita duba gida,sun duba inda yafi kusa da ma'aikatan su anguwan Apapa lagos,ya siya apartmemt,gida ne mai girma ba sosai ba,Falo hud'u mai Dauke da bedroom da Tiolet guda takwas,yana da girma gidan tunda akwai Haraba sosai,sai kudi wajen miliyan Ashirin gidan tunda Sabo ne shima mijin Nana Fadilan wani kaninsa ke harkan gidajen shiyasa suka samu da sauki,Ya siya gidan sannan kuma yayi oder din gadaje da kujeru da sauran kayan bukatu da ya Kirani ya fad'amin sai nace"ka san kana da yara a siya musu kananun Gadaje. Ga uku anan ga biyu Farhan da Fadil,Anum kuma ko ita da Badariya sai ka had'asu,Mama kuma tana Dakinta ita kadai sai jamal kada ka manta da shi"

Cikin gamsuwa yace"ban manta da shi ba wajen zai isa ba takura fa. na Dauko muku hoton gidan in na Dawo zan nuna miki"Da haka muka rabu sai da yayi sati sannan ya Dawo da shirin zai tafi damu gabadaya Zainab kuma sai daga baya zata biyomu ita.

Sallama yace duk mu yi da abokan arzuka da yan'uwa da makota,Ranar a karofi muka yi yini,washegari kuma da muka dawo na zaga cikin gari naje nayi ma Sa'adatu da Habiba sallama saboda  sabo har suna kwallah,makaranta yara daman tun kwanaki naje na sanar da su suka ce zasu yi kewar hazikan Dalibai.

Hajiya ma naje mataa sallama,ta bani kyautan kaya da su Turaruka da mayama mai na gyaran jiki muka rabu cikin mutumci,Abba dai shi ya hana naje yi masa sallama duk da ko ba inda suke tunani zan tafi ba, yace shi zasu je har lagos suga muhallina.

Anty Binta da da Mama sai Anty Hure da tazo zasu tafi daga bangarena yace a samu mutum biyu sai Goggo ta wakilta Anty Nasara da matar Yaya Isa tunda Yaya mariya tace bazata samu zuwa ba,Yaya Asiya kuma yaronta bai da lafiya yana fama da kyanda.

Tafiyar jirgi yace zamu yi,zamu je kano daga katsina kenan,Ya siya mana Ticket gabadayanmu zamu tashi karfe uku na ranar talata,damu da kayan sawan mu,ana gobe Tafiyar na had'a komai nawa na kayan zobo na da kunin aya.

Sannan na cire soket din Freezer di'na,duk kulle kullen da Goggo ta aikomin da shi na had'a cikin kayan yaran nasa zai musu amfani.

Na zata ina da Dauriya sai ga shi na fara raunanaa, in naga yadda yaran ke Tsallen Murna ina Tunanin ya ya zasu ji gobe in har na ce musu ba Tafiyar mu d'aya ba..?






*Janafty*

[7/19, 2:47 PM] Hauwa Galadima: *KNKB2020*


*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*

*09069067488*


Ko yaran ban bari sun fahimci Halin da nake ciki ba,daki na shige ina kokuwa da yanayina. 

 Nace kada su dameni da Hayaniya Hafsah bata nan daman tun jiya ta wuce karofi daganan Abba zai turo mota a Dauketa zuwa kaduna.

Yaran ne kad'ai da babansu ke ta Budurin su da murnan gobe zasu hau jirgi,sannan zasu koma Lagos da zama,kayan su dai masu muhimmanci na hada musu saboda tafiyar jirgi ce yace ko shi daga baya zai saka a taho mana da komai gabadaya,Badariya tana kano sun kusa gama Hidimar kasa bata da Lokaci sai dai zata taho daga baya.

 Kwana nayi ina kuka Sai dai ban kwanta ba ina sallah hawayena sun kasa tsayawa sai kuma naji kamar abunda nake shirin yi bai kyautu ba.?kamar in nayi haka na karya raunin zukata da dama ciki har da ta yarana. da suka fi kowa shakuwa dani ammh sai wata zuciyar ta tunasar da ni Babban Dalilina da yasa naji na kara samun karfin zuciya.

Sai dai a komai in zan yi ba ma yin gaban kaina Allah nake fara sawa cikin Duka al'umarana,Shi na daga hannu na roka da kyawawan sunayensa sannan na yi masa magiya na yi masa naci ina kuka ina fadim"Ya Allah kasan damuwar dake damuna acikin zuciyata, sannan kasan wahalwahalun da nayi ta fama da su yayin biyayyan auran da kai ka Umarcemu da yin sa.

 Sannan kasan komai da ya faru tunda kai mai ji ne kuma mai gani ne na yanke wani Kuduri a raina ya Allah in har ba alheri acikin Tunanina, Allah ka hanani aikata wannan kudurin nawa in kuma Hakan shine alheri a gareni da Duniyata gabad'aya Allah ya bani Hakuri ka sanyamin juriya kada kuma ka barni ni kad'ai kayi Riko da Hannayena sannan ka yimin Jagoranci a duka al'murana,sannan ya'yana Allah ka tallafe su,  kayi musu albarka, ka kara shiryamin su cikin addininka"

 Ina addu'an kukana yaki Tsayawa sai na kife kaina a kan hannayena ina ta rafzan kuka,ni da barci sai wajen hud'u na asuba shiyasa na makara sallar asuba sai da naji sa a kaina yana Tab'a kafafuna na bude idanuwana jajir da suka kumbura saboda kuka,na sauke a kansa cikin mitsike ido na ce"An yi sallah ne..?

Kai Tsaye yace"Har mun dawo masallaci ni da yara kina kwance ashe baki tashi ba..?

Jin haka yasa na yunkura Dakyar na mike ina fadin"Ban yi barci da wuri ba ne"

Kai tsaye na wucewa zuwa Tiolet sai ya bini da kallo yaga idanuwana sun tasa ammh ganina a kan darduma sai yayi tunanin sallar Dare nayi,Ficewa yayi falon wajen yaran har Anum ta kunna gas ta Dora ruwan zafi saboda wanka,Amir kuma ya saka a Heater tunda akwai wuta.

 Sai da idar da sallah na fito falon ina ganin an saka ruwan zafi nasan Anum ce uwar zumud'i ban dora abun kari ba sai da duk sukayi wanka har da Baban nasu,sannan na fere dankalin Turawa na soya musu sai ruwan Tea muna da sauran kayan ciki sai nayi mana Ferfesu da yawa saboda Mama da Anty Hure,su Anty Nasara suna Karofi sai yau zasu taho ammh ina Tunanin zan Dakatar dasu.

Saboda tafiyar dake gaban mu yasa suna gama karyawa suka fara shiri ni dayake ban iya saka komai aciki na ba gabad'aya komai baya min dadi.

Yaya Ishaq yana dakin mama shi da yaran zainab ta kirani bayan na Dauka mu gaisa tace"Maman Amir yau sai kwanan Lagos ko?

Sai nayi yake kafin nace"Uhm ke bakin k'i mu je mu gyara gidanmu tare ba.?tana dariya tace"Wlh ba haka ba ne zan tsaya shirye shirye ne Daddy wannan karon bai bani matsala ba,da Full yes din sa zan koma ai ko Sati biyu baza'ayi ba zan same ku achan in sha Allahu"Jin haka yasa nace"To Allah yasa"

Ta amsa da Ameen mun taba Hira sama sama na tambayeta yara tace suna makaranta,mun yi sallama cikin girmama juna kamar yadda muka saba,har ta kashe sai na sake kiranta tana dauka nace"Maman Fadil ga amanan yaran nan. Don Allah ki kula da su sannan kiyi hakuri da su,Amir da Anum sun girma nasan zasu yi miki kokarin kula da sauran kannensu. In sun yi ba daidai ba ki tsawarta musu ki yi musu fad'a ki Tsaya kan tarbiyan su don Allah, in sun fi karfin ki ki had'a su da Babansu shi sai ya yi musu hukumci"

Bata gane kan mganata ba yasa tace"yaran da duka nakin da nawan kike hadawa ki rike Maman Amir..?kinsan bani da juriyan kwarammiya yara fa..?kina ma wata mgana muna komawa ai su Farhan daman ya'yan ki ne"Sai nayi mirmishi kafin nace"Ki rike mganata zaki tuna da abunda na gayamiki watarana"ban tsaya sauraran mganarta ba na katse wayata ina maida numfashi anya zan iya kuwa.?sai wata zuciyar tace min zaki iya in sha Allahu Fa'iza.

Anty Nasara na kira tana Dauka sai tace min gasu nan gidan Goggo yanzu zasu taho kai tsaye nace"Ku yi zaman ku nima ganinan tafe"

Cikin mamaki Anty nasara tace"Ga ki nan zuwa..?ban gane ba.?kun fasa tafiyar ne..?

Kai Tsaye nace"Aa.."

Anty nasara tace cikin mamaki"Bangane a'a ba ki bude baki ki yi min mgana Fa'iza"Bana son mgana alokacin sai kawai nace"Sai dai nazo"

 Da sauri na katse kiran,ina jin kaina yana saramin ban zauna ba na mike na rika fito da jakunkunan kayana na zuwa falo,Sai ledan kayan da ba cikin kayana zan hada shi ba.

Ina cikin aikin ne sai ga shi ya shigo yana ganin haka sai yace"Yauwa daman mganar da na shigo nayi miki ne,bari naje tasha na yo tashar Ko Sharon ne yadda zasu daukemu da kayanmu duka"

Kai na gyad'a mai kafin nace"ni ma ka yo min tashar Ko karamar Golf ne don Allah"

Cikin mamaki ya juyo yana kallona lokaci d'aya yana fadin"bangane ba..?sharon fa zata ishemu in na yo tashar ta"

Kai tsaye nace"Aa ina so zan aika ma Goggo wannnan Frezer din karofi ne, in na barsa anan ba'a amfani da shi zai lalace. shiyasa nayi mgana da ita zan aika mata da shi"

Kamar zai yi mgana sai ya fasa ganin zai fita yasa nace"Kayi ma su Amir mgana su zo su fitar da kayan su"

Ya amsa min da toh ina ji ya leka Dakin Mama yana musu mgana,sai da suka zo nace su fito da kayan su tsakar gida daman tun jiya nagama duka kaye kaye muka kwashe komai muka adana cikin rawan jiki suka fara fito da kayan suna murna suna jin Dadi kallon su kawai nake yi ina zaune ko wanka ban yi ba Anum ce tace"Umma ke bazaki shirya ba ne..?

Sai na Rausayar da kai ina fadin"Zan yi wanka yanzu Anum"

Nan suka fice suka barni,ina sake sake ganin zaman bazai amfaneni ba yasa na mike na shiga daki,tubewa nayi na shiga wanka,kokarin daidaita kaina nake yi saboda in na rasa kwarin gwiwa bazan iya aiwatar da kudurina ba.

  Na fito wankan kenan ina Shafa mai,naji dawowar Yaya Ishaq da maganan su Mama sai hayaniyar yara kamar suna fita da kayan ne waje da Sauri na Zura Doguwar rigar leshi,daman kwalliya ba aikina ba ne,Dankwali kawai na dora na zura Hijabi,na fito da sauri duk suna Tsakar gida har su Mama yana ganina yace"Ga motar chan a waje."

Nasan wanda nayi masa mgana ne kai Tsaye nace"akwai yara a waje ne..?

Juyawa yayi yana fadin"Bari na duba"

Ba jimawa ya Dawo,da wani Saurayi tare suka kama suka fita da Babban Frezer din da Starplezer,Anty Binta da ta shigo kenan ta ci karo da su suna fita da shi shine ta shigo tana fadin"Ina za'a je da wannan frezer din.?ba dai Lagos ba..?

Dayake na gayama su Mama karofi zan kaisa sai itace ta bama Anty Bintan amsa ni dai muna gaisawa na koma daki na shirya a gurguje saboda kada na bata Lokaci,hijabina na saka Dogo har kasa ni na kulle sauran Dakunan gabad'aya na fito da jakar hannuna na,karama na duba duk sun gama fita da kayan suna  jidan sauran zuwa waje ne, har da Baban nasu ina kulle dakin na juyo ina kallon Amir da zai Dauki karamar ledar da na fito da ita da Sauri nace"Kai bani ledan nan"

Ba musu ya mikamin na karba ina fadin"ina kayana.?kun kai waje ne..?

Cikin natsuwarsa yace"Daada ya saka a mota"ina shirin mgana sai ga shi ya shigo yana fadin"Ku hanzarta fa Goma ta wuce mu isa kano akan Lokaci,ke kuma ga mai motar nan yana mganar lambar wanda zai kira in ya isa karofin..?

Anty Binta har ta fice,Mama ce da Anty Hure ban damu ba nayi karfin halin yi masa mgana ganin zai sake fita cikin Dakiya nace"Ina son mgana dakai"

Ba shi kad'ai ba har Mama sai da tayi mamaki gabad'ayan su suka kuramin ido,Sai nayi saurin Kauda kai ina juyawa na koma na bude dakin na shige daidai Lokacin da yake fadin"Fa'iza zamu makara fa kinsan jirgi ba jiranmu zai yi ba"

Ina kokarim daidaita yanayina nace"In sha Allahu bazaku makara ba"

Biyo bayana yayi muka Tsaya a Tsakiyar falon,na juya bayana ina maida hawayena a bayana ya tsaya yana fadin"Kin kuma juya.?wata mgana ce..?

Sai na juyo cikin karfin hali,idona yake son kallo saboda ya Fahimci yanayina ni kuma sai naki basa Dama,jikina ne ya kara yin sanyi Sabida ba jimawa mun yi mgana da Anty Fadila tace ita da mijinta zasu zo Filin jirgi daukan mu sai min je gidanta mun huta sannan su rakamu Sabon muhallin mu,da ita taje jiya ta kara gyara shi bayan kamfani yazo ya saka kayan Furnitures.

Har muka gama waya ban samu abunda na gayamatabba, ina jin kunyar gayamata cikin masu sauka a Lagos ba Fa'iza a ciki.

Ledan hannuna na mika masa sai ya saki baki yana kallona cikin sanyin jiki yace"Meye wannan kuma..?

Kai Tsaye nace"Duba ka gani mana"

Sai ya amsa ya bude yana gani Lokaci d'aya yana kallona da mamaki da alamun karin bayani da sauri nace"Kayan ka ne. Tun daga lokacin da ka jingine aurena da kai na daina amfani da duk wani abu naka,Abinci dai naci sannan ka bani wajen kwana Darajan ya'yana nagode kwarai Ishaq."

Na fad'a ina kallonsa ido cikin ido yadda ya kafeni da ido ne yasa nasan karin bayani yake so sai na yi ta Mazan cewa"Kayi hakuri Ishaq. Bazan iya binka Lagos ba."

Cikin Daga murya yace"What..?wannan wata irin mgana ce Fa'iza don Allah ki bar wannan wasan bana so.."

Ya fad'a har yana d'agamin hannu,sai nayi mirmishin takaici kafin nace"Ba wasa nake yi ba. Da gaske nake yi, daman na fad'a maka ka bani Lokaci naga ko zan iya bama auran mu wata Dama ko ba haka ba..?

Kamar gaula haka ya gyad'amin kai sai ya bani Damar cigaba da mgana ina fadin"To abunda na Dad'e da yankewa kenan,rasa aikin ka da abunda ya faru yasa na dakatar da kudirina,ammh yanzu tunda ka samu aiki komai ya wuce zama na dakai ya kare daman auran ka jingina ne,  shine nake rokom ka ka karisa ballesa daga wannan jinginan ma'ana ka Furta min SAKI da kan ka"

Na gama fad'a ina maida hawayena lokaci daya ina jin karfin gwiwa na shigata shi ko ledan hannunsa ne ta kubce ta fadi kasa cikin Tsananin Firgita kamar kiftawan ido na ji sa ya Damki kafaduna duka Biyu yana fadin"Fa'iza ki daina irin wasaan. Wani irin saki.?ki yi tunani mana kina tunanin zan iya sakin ki ne.?so kike na rabu dake wai Fa'iza..?

Kai Tsaye na gyad'a masa kai cikin idonsa nace"Kwarai haka nake nufi ka Sauwake mun auran ka domin bazan so ka cigaba da zama da matar da baka so ba. Ka auri zab'inka a wanchan Lokacin kace nayi maka adalci in barka ka yi rayuwa mai Dad'i da matarka. ni ma a wannan karon ina neman wannan adalci nima a wajenka kayi hakuri ka sakeni, daman a jingine nake kamar yadda ka fad'a"

 Ban ko gama mgana ba kawai naga ya sakeni da karfi yana fadin"Ina. Wasa kike Fa'iza har fa mun shirya jirgi na jiranmu fa ?kowa yasan yau zamu tafi sai yanzu ki sauya mgana..?ga yara chan na murna sai na fita nace musu me..?su Mama na Tsakar gida me zan gaya musu..?to wai kina nufin na tafi ni kad'ai dagani sai yara.?wa zai kula damu Fa'iza rayuwar mu ta fara tare dake kuma Dole mu karisa tare Fa'iza har Abada babu saki ko yaji Tsakanin aurena da ke"

Nima cikin Tsawa da Daga murya na taresa da fadin"Ammh akwai jingina acikin auran namu ko..?sannan akwai Tozarci da wulankanci duk aciki ko.?kayi hakuri na riga na yanke hukunci bazan iya cigaba da zama dakai ba.."

Sai ya juyo yana kallona cikin Fitan hayyaci yana fadin"In sake ki na Lalace Fa'iza?kin manta abunda Baba ya fad'amin?yace in na rabu dake na rasa mata tagari sannan bazai taba yafemin ba in na barki,don girman Allah ki bar wannan mganar ki bari in muka isa chan na yarda mu zauna da Mama ki fad'a mata komai tayi mana Sulhu, ammh zuciyata bazata iya Daukan wannan mganar ba. plz ki bari don Allah"

 Ya fad'a har yana hada hannayensa alamun roko gabadaya tsoro da firgici sun bayyana a saman fuskarsa gabadaya,jikinsa kuma sai rawa yake yi,ina kallonsa kamar zan yi rauni sai  kawai na tuna da irin zaman Tozarcin da nayi da shi na Tsawon shekarun auran mu,kuka ya kwace min na juya baya na ina fad'in"Kayi hakuri ba zan iya ba.."

Sai kuka shabe shabe,Ban sani ba ashe duk'amin yayi sai ji nayi yana jan Hijabina Lokaci d'aya yana fadin"Ki yi ma girman Allah Fa'iza ki yi hakiri ki bar mganar nan. Hankalina tashi yake yi in naji kina fadin saki da kuma cewa bazaki bimu ba.?Ta yaya kike so na fara rayuwa a in da baki..?

Bansan Lokacin da na juyo,har ina bangajesa cikin daga muryan da bansan ina da shi ba nace"Zaka iya. Nace Ishaq zaka iya.."

A baya ka zauna da wata macen inda bani kuma baka mutu ba. Na fuskanci Kaskantattaciyar rayuwa a gidan auranka,na fuskanci tozarci a wajen ka da wajen dangin ka a karkashin auran ka,ka rabani da kowa nawa ciki har da mahaifiyata ka rabani da yan'uwana duk wani mai so na baka kaunarsa,baka son ganin Dariyata sai kuka na Ba a macen aure ka Daukeni ba,ka Daukeni a baiwa,mara gata,jahila wacce bata da ilimin zamani,sannan mummuna baka wacce ka ke zaune da ita Saboda alfarma,wacce tayi ma rayuwarka karan Tsaye Fa'izar dai da tayi ma mafarkin ka kutse, Fa'izar da ka zaunar da ita kana rokonta da ta taimaka tayi maka adalci ka zama na mace Daya,Matar da ka fifita a kan Amaryan ka,Fa'izar da baka san ciwon ta ba,baka san cikin ta ba,baka san zafin nagudar haihuwar ya'yanka da ta dinga yi ba, itace dai wacce ahaka ake kiranta kamar akuya ta cika Haihuwa Fa'izar da ka nemi datse mata Haihuwa saboda baka kara kaunar Zuru'a da ita,Ni ce dai Fa'izan da kasa nuna ma duniya ni matsayin matarka kana jin kunya,Nice Fa'izan da ka ke barina wata da wattani Saboda wata mace ni ce Fa'izan da na dauki dukkan Tozarcin yan'uwan ka har da na Dangin matarka saboda Fa'iza bata da gata,Fa'iza ba kyakyawa bace. Sannan bata da ilimin zamani ba wayayyiya bace ba kuma yar gayu ba ce,sannan ita ba fara bace bata kuma iya haihuwan Fararan ya'ya ba,ni ce Fa'izan da kake kirana mara amfani Fa'izan da auran ta bai amfana maka komai ba ni ce dai Fa'iza nan wannan mai raunin jin,wacce ka ce ka tsani mgana da ita saboda tana saka ka ihu ko ka manta ne..?

nice fa nice fa kake kiran bazaka iya Rayuwa a inda bani ba..?karya ka ke yi..Wlh karya ka ke yi.."

Na karishe fad'a cikin Tsawa Lokaci daya da kuka sai kawai na zube saman Cafet din ina wani irin kuka mai cin rai ban sani ba ihu na da mganata yasa su Mama rugowa Dakin,duk a gabansu na rika amayar da abunda ke cikina.

Su kansu jikinsu yayi sanyi sannan sun kasa gane wasu abubuwan 

Shi bai ma gansu ba sai ya rarrafa cikin Fitan hayyaci ya na kokarin rikoni nayi maza nayi baya da jajayen idanuwana ina fad'in"Kar ka kara tabani. Kar ka kara in ba haka ba wlh zan sharara maka mari"

Na fad'a ina nuna sa da yatsa cikin bacin rai da bai taba ganina aciki ba

  Sai ya kasa karisowa gabana,cikin rawan baki da na murya yace"Fa'iza ba kin ce kin yafemin ba..?

Me ya sa..?

Kai Tsaye nace"Eh da gaske na yafe maka,.ammh ba shi zai goge tabon da kayi ma rayuwata ba.

Dalilinka aure ya fita kaina na Tsani duka maza sannan nake Tausaya mata ire ire na da Tunanin wata irin Rayuwa su kuma suke fuskanta a gidan nasu auran..?ka taba Tunanin ko sau d'aya kayi min adalci?

Nace ka taba wannan tunanin.?

Sai kawai na kara fashewa da kuka ina fadin"A  gabana ka kori yar'uwata uwa d'aya uba d'aya,Har kana ikirarin in ka kara ganinta a gidanka zaka had'a ta da Hukuma?ashe ko bata ci darajan aurena da kake yi ba, bazata ci Darajan zumunci ba Ishaq..?

Mahaifiyata ta rasu bata san Dadina ba. Har ta koma ga Allah ban taba zama da ita na yini d'aya ba.

Ranar da zata rasu ma baku barni na kwana da ita ba,ta rasu ban sani ba.

Na rasa uwata ammh ko gaisuwa baka zo min ba, kana wajen wacce ta fini muhimmanci a wajenka.Sai da ka dawo baka iya ce min Fa'iza ya hakuri ba sai Duba na kayi kana ce min ashe wai kuma babarku ta rasu..? Wai ne ma baka Tabbatar ba.?shine kake so na manta..?ko kuwa yadda ka ware ni daga cikin sauran mata a dalilin auranka yasa nayi shekaru ina fama da Gulit din mata masu kyau da gata ne suka chanchanci ado da kwalliya,a gidan ka na fuskanci mata ire irena basu dace da samun soyayyar miji irin Ishaq kabir karofi ba. Shiyasa na yanke shawaran karshen zama na dakai yazo daga yau.Na rantse da Allah bazan bika ko'ina ba. Daganan karofi zan koma daman ranar da Baba yace zai had'a aurena dakai Mama ta koreni sannan tayi alkawarin bazan koma mata gida ba,Karofi na koma wajen Goggo kuma chan aka daukoni nan duniya bani da gatan da ya fi gaban Goggo gabanta zan koma na zauna Domin Fuskarta Sabuwar rayuwata"

 Na karishe Fad'a ina share hawayena lokaci Daya na mike da Sauri ina fadin"Zainab zata iya kula da kai. Yara kuma Amir da Anum sun yi girman da zasu iya kula da kansu. Ahmad da mutsy ba su da matsala zasu kula da su.

Ba lalle ba ne don na faro rayuwata dasu na karishe ta da su ba..Haka Allah ya kaddara Labarin ya kare daga wannan Lokacin"

Na fad'a Lokaci daya ina Daukan karamar jakata,Mama na gefe sai sharan kwallah take Anty Hure ta sha gabana tana fadin"Haba Fa'iza ku ba yara bane. yi hakuri mu tafi in mun je chan sai a zauna a fahimci juna'

Kallonta nayi kafin nayi mirmishin takaici na tuna har da ita a masu biye ma Mama suna cin zarafina,sai kawai na kad'a kai ina fadin"Bakin alkalami ya riga ya bushe Anty Hure.."

Na kad'a kai na zan fita waje,Ishaq ya yi kukan kuran shan gabana yana rike Hijabina na balla masa harara ina fadin"Cikani kafin raina ya baci"

Yaki ko sakina fad'i yake yi"Fa'iza ina zaki.?Fa'iza kada ki yi min haka..?me zan ce ma yaran chan..?

Fa'iza..Fa'iza"

Sharr sai kuka abunda ban taba gani ba,kai na kauda abubuwan suna dawomin kamar yanzu komai ke faruwa,kwace hijabina nayi ina fadin"Na fada maka kuma zan kara fad'a maka na gama zaman aure da kai. Na tsani aure na tsani kowani zamantakewa,Ka sauwak'e min Ko kuma ka k'ara Turgud'e shi daman jinginanne ne"

Na turesa zan wuce sai ya makale kafafuwana yana fad'in"Kada ki yi min haka Fa'iza,Kada ki yi min haka"

Kasa kwace jikina nayi sai kawai na juya ga Mama tana kuka nima ina Hawaye nace"Mama ki fad'a masa ya cikani don Allah"

Sai Mama ta sunkuyar dakai shi ko,sai alokacin yaga su Maman sai ya sakeni ya Rumtuma wajenta ni kuma sai na kwashi Sauri na fita Daga Falon ina Fitowa sai nayi Turus ganin yaran duk Tsaye suna jin abunda ke faruwa ga Anty Binta itama.

Cikin mamaki tace"Fa'iza meke faruwa ne har kofar gida ana jin Hayaniyar ku..?

Ban bata amsa ba Ishaq ya fito rike da Hannun Mama ya kawota gabana yana fadin"Mama ki gaya mata wlh nayi nadama.bKi gayamata abunda Baba ya sha fada'min,Yace in na rabu dake zan lalace Fa'iza ko so kike kada nayi albarka..?

Komai ban ce ba kaina na kallon kasa ina Digar kwallah,Mama ma sai sharan hawaye take yi Anty Binta ta kalli Anty Hure tana fadin"Anty meke faruwa ne..?

Anty Hure cikin Damuwa tace"Fa'iza ce tace bazata bisa lagos ba. Tana neman saki ne da wasu mganganun da ban gane ba.."

Sai ta waro ido kamar yadda yaran suka yi cikin wani yanayi tace"Fa'iza yanzu kuma?kika ma zauna dashi a bai da shi sai kuma yanzu da Dadi yazo sai kice haka.?aa ku bari muje chan sai mu zauna mu tattauna kin ji ko..?tafad'a gabanta na fadi domin bata san ya wannan al'amarim zai kare ba.

 Jallonata nayi ina tuna Yadda tayi Tsawon shekaru tana Tozartani har da ita masu saka bakin na zauna sai kawai na share hawayena ina fadin"lokacin da bai da aiki wannan yanayin da mata ire iren Fa'iza ya Dace shiyasa ban tafi ba tun a wanchan Lokacin,sai yanzu kuma da komai nasa ya dawo sai nayi Tunanin Lokacina ya kare daman kema kin sha Fad'a jin dadi bai dace da mata ire irena ba,wahala ce da bauta ta Dace dani kamar yadda Mama ta sha fada. Shiyasa zan tafi zainab itace ta Chanchanci zama da shi Tunda ita ta tako kashin arziki sannan bata yi kama da matan bauta ko wahala ba.."

Dukkansu Tsaye suka yi an kasa mai mgana ina gani Anty Binta na zaran ido sai kawai nayi Dariyan takaici kafin nace"Na kwashe fin shekara goma ina bautar aure kuna ganin komai ammh baku taba zaunar da shi kin fad'amasa bai kyauta ba..?sai ni yau don a shekaru goma sha Biyar da auran mu na yunkuro sai ku nemi Danne ni.?wannan karon ba wanda ya isa ya hana Fa'iza tafiya.

Zan tafi kuma tafiya ta har abada"

Ina gama fad'in haka na ratsa Mama zan wuce sai ta riko Hijabina tana kallona,yanayinta zai sakani rauni sai na daga kaina sama cikin wata murya tace"kiyi hakuri Fa'iza.

Ba domin na isa ba..Ki yi hakuri ki Duba yara nan kada ki bar su yi maraicin uwa"

Ta fad'a tana nuna su Amir,Anum har ta fara kuka da su Ahmad zuciyata ta karye ammh ban damu ba Hawayena na Shatata saman fuskata nace"Ke kan ki shaida ce Fa'iza bata dace da D'anki ba.,yaran nan kuma rabo ne Allah ya sa na same su,maraici kuma baza su yi maraici ba Mama kina nan ga Zainab,sannan shi ma babansa zai kula da su tunda ya'yansa ne sune Dolensu bazan ce a zama da shi bai Tabamin wani abun alheri ba,yayi min Tunda dalilin sa yasa yau nake amsan sunan uwa,ammh mganar na Duba yaran nan bai taso ba. Nima a lokacin da yake tozartani ko sau d'aya bai tab'a Duba darajan ya'yana ba.."

Na fad'a ina kallon su, bana so na cigaba da mgana a gabansu kada su ji,kamar ma Amun da Amir tunda suna da wayan su.

 Na tuna Lokacin da Anty Binta tazo ita da Mama suna min watsi da kaya akan sai na bar gidan,meyasa yau don nace zan tafi sai su damu..?

Wani tukuki ya taso min dayasa har jiri na fara gani cikin Duhun ido na juyo ina fadi'n"daman kuna so na tafi,Aurena ba alheri ba ne ko ba haka kuka fad'a ba..?meyasa don yau nace zan tafi kuke magiyan kada na tafi..?Wlh kaina tuni ya Dauki Dumi kuka na kara Fashewa dashi na juya ga ya'yana da suke kallona cikin rauni hatta Amir da ba kasafai ake ganin kukan ba yau har da majina,Ahmad kuwa da gudu ya nufeni ya rumgume ni yana fadin"Umma zan biki ni dai"

Musty ma ya kariso yana kuka ya rikemin Hijabi gam yana fadin"Nima Umma ke zan bi na fasa zuwa Lagos din"suna mgana kukana na karuwa Anum ma ta rugo ta makalemin jiki ta fashe da kuka tana fadin"Umma nima ke zan bi"

Ina Kuka suna kuka Amir na Tsaye shi bai zo ba na dago ina kallonsa cikin kuka nace"Amir ku yi hakuri ka zo ka taimaka min ka lallashi kannen ka"

Sai kawai shima ya rugo da gudu ya Rumgumeni yana fadin"Umma zaki tafi ki barmu?don Allah kada ki tafi Umma kada ki tafi ki barmu"

Sai kuka yadda suke kukan ne yasa naji gabbaina sun yi sanyi in na tafi na barsu yaya rayuwarsu zata kasance?sai na juya ina kallon Ishaq da idanuwansa suka kad'a jajir,sai kawai naji Duhu ya rufeni da Hanzari na yakice su a jikina na duka Bisa gwiyoyina dukkansu na rike hannayensu cikin nawa sannan na Dauki na Amir na rike ina fad'in"ba inda zan je ina karofi gidan Goggo zan koma,In ina bukatar ganin ku zan zo ko ku kuzo wajena,sannan zan rika kiran ku a wayar Anynku muna gaisawa kun ji ko?

Ahmad ya makale kafada yana Fadin"ni dai umma zan biki"

Musty ma yace haka Anum Sarkin kuka tace"Umma ki tafi damu chan gidan goggon mana"

Ina girgiza kai hawaye na zubomin nace"Bazai yuyu ba Anum. ku kuna da Baba sannan ga kakar ku nan bazai yuyu ku bini ba,ni kuma bani da uwa ba ni da uba,Goggo itace gata na shiyasa zan koma wajenta ku kuma Babanku na da mata Antynku ga kannen ku su Farhan,ku zauna lafiya da junan ku ku zama masu jin mgana Amir kai ne Babba ka rike kannen ka Amana ka ja su ajikinka a matsayinka na Babban Yaya,ku zama masu jin mgana da Tarbiya Anum ki kula da Ahmad kin ga shine karamin cikin ku kada ku takurama Antynku komai tace ku yi kuyi kun ji ko..?.sai suka kasa dagamin kai ina kokarin Dauriya na saki Hannayensu na rika bin su daya bayan d'aya ina share musu hawaye ina fad'in"kada ku ce zaku rika saka Anynku mgana,Amir karatu ka rika duba na kannenka,Karatun Qur'ani ku rika bita kada ku manta da azkar din safe da maraice,ban da abokan banza sabon waje ne bakusan kowa ba,kada ku manta da Tarbiyan da na baku Anum kece mace ki rika taimaka ma Antynku da ayyukan gida kuna ji ko..?

Sai gabadayansu suka bare min baki Amir jikina ya fad'a yana fadin"Umma mu ba ma a son Antynmu ke muke so.."

Hawaye suka kwaranyomin na kamkamesa ina kuka Anum ta ruga wajen Babansu tana fadin"Daada kaje ka ce Umma kada ta tafi.."

Tana fada tana jan Hannunsa,sai ya biyota har gabana shima dukawar yayi,yana fadin"Don Allah Fa'iza ki duba yara nan"

Ban ko amsa mai ba na hada ya'yana na Rumgume gabad'ayanmu muka saka kuka,Mama na gefe sai ta juya kawai ta fice tana kuka Anty Binta ma duk jikinta yayi sanyi in Fa'iza ta tafi ya kuma abubuwa zasu tafi?Zainab wannan yar son jikin da bata iya komai ba, ta ina zata yi da Dawainiyar yara?akwai matsala babba kuwa.

Suna kuka ina kuka da na ga bazai Fissheni ba na rarrashi kaina na koma ina ba su hakura suka makaleni suna kukan sai sun bini Hon din masu mota ne ya ankarar damu suna jiranmu,Ishaq ya marairaice yana fadin"Na siya mana Ticket Fa'iza asaran kudina kike so nayi..?

Kai tsaye nace"Ai ban ce ka siya har dani ba. Tunda ban ce maka zan bika ba"

Cikin wani yanayi yace"To dukkanmu mun fasa bazamu tafi ba, mu tattara muje karofi a warware komai"

Cikin yak'e nace"Kada ka biyoni Karofi Ishaq ka lallaba ya'yanka ku tafi,kada ka manta aikin. ka fara ba jimawa rashinka a office zai iya zame maka matsala sannan meyasa bayan ka kashe kudin jirgi zaka fasa?

Na fad'a ina kuramai ido gani yayi kamar na fara saukowa yasa da Sauri ya rikeni yana fadin"Fa'iza zuwan bashi da amfani idan baki kin sani ko?

Kai tsaye nace"Bazan bude baki nayi mgana ba.ka lallashi yaran nan ku tafi in kuma kace zaka bini karofi zaka Fallasa kanka da kanka. Daman na Fada maka da bakina bazan fad'i komai ba,sai dai in kai ka fad'a da kanka"

Shuru yayi yana ajiyar zuciya a Firgice kamar wanda yayi karya,Ban damu ba naja hannun su Ahmad da Musty,su Amir suka biyo bayana muna zuwa kofar gida masu motoci na jiran mu sawa nayi aka Fitomin da akwatina da jakunkuna na,nace a sakamin a karamar Golf din nan,Mama na gefe tana sharan kwallah,su Ahmad nata kuka har Lokacin sai na Daure saboda bazan bari su hanani Tafiya ba,key din gidan na isa gaban Ishaq na Damka masa ina Fadin"Key din gidan nan, ne Sauran kayana in ka sauwakemin zan zo na kwashe"

Makullin fad'i ya yi a kasa,ya kasa amsa ni kuma na juya ina goge kwallah na bude bayan mota na shige,Su Amir sun yinkuro zasu shiga na rufe kofar da karfi ina kuka ina ganinsu suna kuka suna dukan jikin mota ammh na kasa motsi,Direba ya shigo yana fadin"Hajiya yaran nan zasu hanamu tafiya fa"

Kai tsaye ina kuka nace"Glass.! d'agamin"

Ba musu ya d'agamin na Leko da kaina da sauri suka nufeni Ahmad sai fadi yake Umma nima zan biki shi da Musty,Amir na share ma Hawaye Na rike hannun Anum ina fadin"ba na ce ku lallashi kannen ku ba..? To in dai kuna kuka bazan dawo na Dauke ku ba"jin haka yasa suka daina kukan Amir yace"Umma to kizo mu tafi tare"kai tsaye nace"Aa ku fara yin gaba, ni zan zo daga baya..Ka kula da kannen ka kaji ko Amir"

Sai ya gyad'amin kai dukkansu na Shafa kansu ina fadin"Allah ya yi muku albarka"Sai kuka yaci karfina cikin kukan nace"Direba muje"

Lokaci daya na maida glass din na zuge,mun fara tafiya na juyo ina daga musu hannu Ahmad ya kwace yabi motarmu yana kiran sunana har yana Fad'i ina gani Baban yaje ya daukesa,Anum kuma Mutsy ta rike tana kuka Anty Binta ta rike Amir kasa Daurewa nayi na juya ina kuka kamar in ce Direba ya Tsaya sai kuma wata zuciyar tace"Fa'iza ki sani ko kin koma baki da wata daraja. Ishaq Zainab kadai yake so ke alfarma yake miki"

Ammh ya'yana fa..?basu saba da kowa ba sai ni wazai kula da su..?zasu fara sabuwar rayuwa a inda bani ya ya zasu tafiyar da rayuwar su.?Zainab bazata kulamin da yarana ba bazata iya ba,yar gatace bata saba da wahala ba ,yaranta ma yan aiki ke daukan mata su,Tarbiyan su da na dauk'i shekaru ina ginawa in ta rushe fa..?

Kuka nake yi da karfina har sai da Direba ya juyo yana fadin"Hajiya ki yi hakuri,In bazaki iya tafiya ba sai mu koma ko kuma ki taho da su naga yaran basu son tafiyarki hala rabuwa kuka yi da Baban nasu,duk da shima naga kamar bai so tafiyar ta ki ba..?

Irin dirobobin nan ne masu fad'i ba''a tambaye su ba.

murya shake nace"Karofi..Karofi zaka kai ni"

Na katse mganarsa lokaci d'aya ina cigaba da kuka zuciyata na Zafi kaina ya fara Dif Dif ga jirin danake ji. alama ce ta jinina ya haye sama.

Har mun yi nisa sai naji bazan iya wannan jarumtar ba ya'ya na,ya'yana kawai nake tunani.

Sai kawai na ce ma Direba"Tsaya mallam.."

Sai ya juyo yanaa fad'in"In tsaya..?

Sai kawai na gyad'a mai kai da sauri ina fad'in"Mu juya mu koma..! mai dani da sauri'

  Ina haki na fad'a,Tunani na da zullumi na,kada kafin mu koma mun iske sun tafi.

  Na fasa bazan iya nesa da yarana ba. tunda na iya kwashe tsawon shekaru goma sha, cikin tozarci na jure me zai hana yanzu bazan jure ba..?kuma yayi nadama zan karbi Tubansa zan bisa naje na zauna tare da yarana.

 Muna tafe ina fadin"Kayi gudu don Allah ka yi sauri."

Yadda nake mganar zaka san bana cikin Hayyacina.






*K'arshen littafi na Biyu,Littafi na uku zai zo in na samu natsuwa insha Allahu,Ammh ba gabadaya zai zo ba,zai zo kamar yadda muka fara daga farko.*

*Nagode..Nagode da Soyayyarku Allah ya bar zumunci Ameen*



*Janafty*

*19/17/2023*




 




No comments