Recent Updates

Furar Danko 7

 


𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 7️⃣



.........Hannu ya basu batare da ya yarda ya kallesu ba. Uncle Yousuf yay murmushi da amsar hannun sukai musabaha bayan ya gaisa da Ahamd dake ƴar dariya saboda harar da Uncle Smart ɗin ke masa ƙasa-ƙasa. 
        “Idan ban takura da yawa ba ina son muyi magana Please Smart Mawashi”.
     Karan farko ya ɗan ɗago idanunsa da har yanzu suke da damuwa ya dubi Uncle Yousuf mai maganar. Kamar zaiyi magana sai kuma yayi shiru. Uncle Yousuf ya sake murmusawa da faɗin, “Please”.
        Bashi da yanda ya iya dole ya amince masa, sai dai maimakon cikin motarsa da ya buƙata suje anan cikin soron gidansu suka zauna saman bench. Shiru na wasu mintuna kafin Uncle Yousuf ya nisa. “Jiya na dawo na samu takarda da key ɗin mota a hanun sakatariyata Aliyu, sai dai ban gamsu da bayanin dana gani a rubuce ba shiyyasa nace Ahmad ya rakoni nazo da kaina”. Ya ƙare maganar idonsa a kansa alamar son jin amsa. 
       “Na ajiye aikin ne kawai”.
   Ya faɗa cikin dakewarsa.
“Ko miyasa?”.
Ahmad ya tambaya cikin kafesa da idanu.
Kansa ya jinjina yana ɗan furzar da iska, sai kuma ya dubu Uncle Yousuf maimakon Ahmad da yay tambayar. “Saboda bazan iya ba Alhaji. Ni mutum ne da ba komai zuciyata ke iya ɗauka ba duk da na kasance talaka mai nema.”
      “Haka ake so duk mutum na ƙwarai ya kasance Aliyu Hydar. Amma har yanzu baka faɗa mana dalilin ba?”.
    Murmushi ya saki mai ciwo a karo na farko. Ya ɗan dubi Uncle Yousuf ɗin sai kuma ya ɗauke kai. “Miye amfanin maimaita abinda bashi da muhimmanci koya wuce Alhaji. Kawai na ajiye shikenan ya wuce. Nasan insha ALLAHU zaku sami wanda ya fini, ni kuma zan tara gaba maybe abincina ba'a nan yake ba”.
         “Nasan bazaka juraba kamar na baya da suka shuɗe domin Kanada banbanci da su. Sai dai irinka na jima ina fata ni kuma, dan kai kaɗaine zaka iya da ita har ma ka tankwarata. Har yanzu nasan baka san ni wanene ba Aliyu Hydar, sai dai ka sani ban nema kamin wannan aikin ba dan kana buƙatar aikin da kuɗi zai shigo maka. Tun randa na ganka wajen abokina yayan abokinka Ahmad naji a raina ka cancanta zama wani ɓangare da zai jagoranci haska wata fitila ta rayuwarta. Ita ɗin a fanɗare take, tabbas a haka ta tashi shiyyasa tanƙwarata yayma kowa wahala a cikinmu. Ada kallon komai muke a bigire na ƙuruciya da tunanin wata rana zata daina, sai dai ranar har yanzu taƙi tazo, bamu san kuma ranar da zata zo ba, ko kuma tazo ne ta wuce batare da mun farga ba oho?. Nasan kana da ƙanni mata maybe ma harda yayu, kasan irin zafin da nakeji a raina koda a kwatance ka kwatanta da ace sune, miyasa bazaka gane ba ne....?”
      Yanda ya ƙare maganar a raunane cikin sigar tambaya yasa Uncle Smart fesar da iska mai nauyi. A ɗan zafafe batare daya dubesu ba yace, “In dai har ku da kuka haifeta kun gagara tanƙwarata ni kuma taya kuke tunanin iyawa? Mahaifinta fa na raye, hakama mahaifiyarta, sannan gaku ku ƴan uwanta, Alhaji Please kayi haƙuri bazan iya ba fa. Bana son raini, bana iya jurarsa ga kowa. Bana son wulaƙanci ko ƙasƙanci duk da kasancewata talaka mai nema. Ina ganin kimarka dan ALLAH karka bari mu shiga wata hanya daba ita ta dace mukai ba dan alkairi ya haɗamu kuma bazan taɓa na manta da kai ba, dan kamun abinda mutane da yawa basu minba na alkairi ka gaida gida”. 
       Yana gama faɗa ya miƙe. Dakatar da shi Ahmad yayi, kamar bazai tsaya ba sai kuma ya dakata tare da juyowa. Miƙewa shima Uncle Yousuf ɗin yayi yana ɗan murmushi. Hannu ya kai ya dafa kafaɗarsa, “Shike nan na fahimceka kuma nagode sosai. Ina son mutum irinka mai tsayawa akan ra'ayinsa da riƙe mutuncinsa. Zan jima inajin raɗaɗin rabuwa da kai Aliyu. Amma dan ALLAH ina roƙon alfarmar kazo office ko zuwa gobe ne domin amsar hakkinka, kuma bana son kace da ni a'a”.
        Baki ya buɗe zai yi magana Ahmad ya dakatar da shi. “Dan ALLAH karkace a'a Smart, ban sanka da musu ba karka fara akan Yaya Yousuf, sannan kayi nazari akan roƙon da yay maka, nasan kanada damar taimakons.....”.
     Hararar da ya ɗan ballama Ahmad ɗin ce ta sashi yin ƙaramar dariya batare da ya ƙarasa ba. Ɗauke idanunsa yay da faɗin, “Shike nan insha ALLAHU idan na samu lokaci zanje, amma kai ma kasan kawai dai dan ta Yaya boss ne wlhy”.
        “Na sani Mawashi. Yaya boss kuma na godiya da wannan karamci”. Bai ce komai ba, sai murmushi da Uncle Yousuf dake saurarensu yayi. Har cikin rai ɗabi'un yaron birgesa sukeyi matuƙa. Yana son ganin mutum mai nutsuwa musamman matashi kamar haka. Ba irin matasan yanzu da shegen rawar kai yayma mafi yawansu katutu ba...

     Har mota ya musu rakiya. Bayan wucewarsu sai yaji ya kasa komawa cikin gidansu dan baisan da wane irin harshe zaima Ammah bayani akan sake rasa wannan aikin ba shima, duk da dai jikinsa yay ɗan sanyi da kalaman Ahmad na ƙarshe, amma dai bai yanke hukunci ba na sake amsar aikin har yanzu. Sai dai in ya tuno bayanin Abba ya kanji faɗuwar gaba. Tabbas yasan wanene Abbansu, sam baya magana biyu. Mutum ne tsayayye da idan yace e to e ɗinne da har ransa. Idan kuma yace a'a to a'a ɗin ce fa. Da ƙafa yabar cikin anguwar tasu, rashin abunyi da sanin ina zai dosa ya sashi miƙewa a titi yay ta tafiyarsa kawai. Yayi tafiya mai nisa da bai san ina yake jefa ƙafa da ɗaukewa ba ya fahimci kamar binsa akeyi a baya. Tsamm yayi na tsarguwa tare da tsayawa, sai dai abin mamaki babu alamar wani tare da shi a ƙafa, wanda ke a kan mashina ma da napep babu alama, hakama na mota. Dakewa yay ya cigaba da tafiyar, still dai ya sake jin tabbas akwai mai binsan. Yanzu kam bai juyo ba sai ya yanke titin ya shiga cikin wani layi, ya ɗan yi nisa da layin sosai ya samu rumfar wasu masu kayan kafinta ya ɗan dakata cikin dabara kamar mai gyara igiyar takalmi. Ta cikin mirror da aka jingine ya hango wasu samari biyu, sai dai suna ɗan waskewa cikin ɓadda kama. Hakan ya ɗan bashi mamaki, dan shi dai a rayuwa duk da yana da tsatstsauran ra'ayi bashi da abokin faɗa. Cigaba yay da tafiyar dan son gane iya gudun ruwansu badan yasan sirrikan layukan inda yake ba. Sai da sukaje ƙarshen layin sosai ya fahimci akwai matsala, ya ɗan ji wani abu a ransa amma sai ya dake, wata hanyar da yake ƙyautata zaton zata ɓillesa da titi ya bi, sai dai yana shan kwanar tsukin wajen suka sami nasarar rufesa ruf ata gaba da bayansa. Ɗaya bayan ɗaya ya bisu da kallo har ya sauke akan napep ɗin da aka faka a gabansa. Cikin dakewa da ambaton sunan ALLAH ya ce, “Ku kuma fa?”.
     “Zaka sani amma ba'a nan ba”.
Ɗaya ya bashi amsa cikin gatse da nuna masa bindiga dake soke a ƙugunsa. Bindiga bata kasance abar wasa ga kowa ba. Duk ƙarfinka da taurin kai a duk inda mai ita ya kasance shike zama a saman ƙarfin ikon ka. Dan haka ya shiga napep ɗin zuciyarsa na saƙa masa abubuwa masu yawa game da mutanen. Biyun da suka dinga binsa ne kawai suka shiga gefe-da-gefensa, mai napep yaja suka fice daga layin, sai da suka fita gaba ɗaya wanda ke gefen haggunsa ya jefa masa wani ƙyalle a fuska, da sauri na kusa da shi ya kama ya ɗaure masa idanu yayinda wanda ya fara jefa ƙyallen ya ɗora masa bindiga a gefen ciki ta yanda bai isa musawa ba. Duk da ya sake firgita haka ya dake a zahirance, a baɗini kuwa yana mai ambaton sunan ALLAH......

    Tofa, su kuma waɗan nan daga ina?. Wayyo Uncle Smart ɗinmu😫😢

          ∆••••∆ ★ ∆••••∆

   Tun daga main falour na gidan kana iya jiyo tashin sautin kiɗan dake fitowa da ga ɗakinta, duk da kiɗane mai taushi na mawaƙiya Shakira yanda ta ƙure voluen yasa ake iya jiyowa. Tun safe babu wanda zai ce ya ganta yau a gidan har zuwa yanzu da agogo ke nuna ƙarfe takwas da wasu mintuna. Mafi yawan yaran rai a ɓace suke fitowa daga ɗakunan su dan sautin kiɗan data saka ya takurasu da hanasu barcin safen. Hatta da ƙananun Suhaib da Imran da fita makaranta kan hakanasu barcin safen ji suke ta takura musu, musamman Imran dake son ƙarasa Assagment ɗinsa amma ya gagara fahimtar komai. Kaf ɗinsu sun gama hallara a dining, sai dai fuskar kowanne a turɓune da takaici. A haka Daddy da Mommy suka fito suka samesu, a kallo ɗaya zaka fahimci itama Momy ranta a ɓace yake, sai dai shi Daddy kam ko'a jikinsa. Yaran ma na gaidashi bai wani saurarensu ba hankalinsa nakan kiran Tabawa mai aiki. Da ɗan gudu-gudu ta fito a kitchen hannunta riƙe da ƙaramin ludayi da alama girki takeyi.
       “Babyna fa?”.
Ya faɗa kai tsaye yana nuna upstairs. Itama upstairs ɗin ta kalla, cikin sake rissinawa tace, “Barci takeyi Alhaji, tace zuwa ƙarfe tara da rabi na tadata”.
     “Shi kuma wancan kiɗan da ga ina?”.
“Itace ta kunna”.
Nunin ta tafi kawai ya mata batare da ya sake cewa komai ba. Mommy da tai kicin-kicin da fuska ya kalla, sai kuma yabi sauran yaran nasa da kallo. Hafiz dake ƙoƙarin kai shayi bakinsa wanda a haihuwa shike bima Lulu ne ya ce, “Humm Daddy yanzu bazakace komai ba kenan?”.
    “Akan me?”.
“Aunty Lu. Ai ko kafiri ba kowa ke iya saka kiɗa ya kwanta da shi ba. Kuma ina da tabbacin ko sallar asuba batayi b.....”
     “Kai ban san shashanci da ƙazafin banza, wai Hafiz ita ɗin sa'arka ce? Kuma kai ubanwa yace maka batai sallar ba”.  
    “Ai ba sai wani ya faɗa masa ba abinda kowa ya sani ne. Ni ban san wane irin makahon so kakema Mawaddat ba a gidan nan, kuma ka sani wannan ba gata bane kashe mata rayuwa kakeyi matsayinta na mace. Da haka kowace yarinya ake rainonta a gidansu da baka gammu haka ka aura ba matsayin iyayensu Alhaji. Dan ALLAH ya kake so nayi da raina akan Mawaddat ne?”.
       Wani banzan kallo ya galla mata ita da yaran baki ɗaya yana cika da batsewa, sanin yanzu zasuyi sama ya sata miƙewa tabar dining area ɗin zuciyarta na ƙuna da raɗaɗi. Ta rasa mike damun mijin nata akan babbar ƴarsu mace, yana nuna mata ƙazamar rayuwa a matsayin soyayya, iya bakin ƙoƙarinta tana yi akan Mawaddat amma abubuwa sake taɓarɓarewa sukeyi. A hankali hawaye masu raɗaɗi suka silalo mata saman kumatu.........✍️

No comments