Recent Updates

Furar Danko 6

 


𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣

.......Shiru kawai yay yana kallon takarda da key ɗin motar da sakatariyarsa ta kawo masa na tsawon lokaci, kafin ya furzar da huci mai kauri ya tashi zaune sosai da ga kwanciyar

da yay a kujerar office ɗin nasa. Wayarsa mai ƙyau da ɗaukar ido ya ɗauka. Har yay dailing number da akai saving da _Yaya Isma'il_ sai kuma ya katse yana ɗan girgiza kansa. Dan ya san halinsa, wani lokacin ba gane abubuwa yake ba birkitaccen mutum ne. Wata number ya sake lalubowa yay dialing, ring biyu aka ɗauka. 

        “Uncle You.. Good Afternoon”.

Aka faɗa daga can, muryarsa a sauƙaƙe ya amsa da “Afternoon dear! How are you?”.

    “Am good Uncle”.

“Haka ake so. Lulu ta dawo ne?”.

   “Yes Uncle tun ma ɗazun. Sai dai tanata masifa wai Uncle Smart ya barta a airport. Amma Deen ya ce ta masa ihu ne a gaban mutane kuma bai mata komai ba kadai santa. Yanzu kuma Daddy ya goya da bayanta wai zata walaƙanta shi ta koreshi. Uncle ALLAH ni bana so sumasa haka, shi ɗin mutum ne nutsatstse”.

        Wani ɗan murmushin takaici yayi da gyada kansa kamar yana a gabansa. “Karka damu Son! bazan bari su aikata hakan ba insha ALLAHU. Kuma zai dawo aikinsa”.

    Sosai yaron ya shiga ihun murna daga can. Shi kuma ya katse wayar yana mai jin takaicin hali irin na ɗan uwansa. Yanda yake training rayuwar Mawaddat na ɓata masa rai. A rayuwa ko ɗa namiji ne bazakace komai ya nema sai ya samu ba duk arziƙinka da matsayinka. Balle mace da wataran aure zatayi ta koma ƙarƙashin ikon wani. Wanin da ba lallai shi ya iya ɗaukar waɗan nan ɗabi'un nata marasa ƙyau ba. Da wannan ɓacin ran yabar office ranar. Kai tsaye gidansa ya nufa dake anguwar ta Hotoro GRA shima. Sai dai ba street ɗin su ɗaya da gidan yayan nasa ba. Da gudu ƙyawawan yaransa guda uku masu kama da shi sukazo tarbarsa. Murmushi yayi cike da jin daɗi, gaba ɗaya ya haɗasu ya rungume a jikinsa bayan sun gaidashi. Yana ƙoƙarin miƙewa da ƙaramin Deen da sukaje ɗaukar Lulu airport mai wayon tsiya a hannunsa idonsa ya sauka akan matarsa. Ƙyakykyawar mace ƴar duma-duma. Murmushi ya sakar mata kamar yanda take masa itama, ya miƙa mata hannu alamar tazo itama. A hankali ta ƙaraso ta shige jikinsa, rungumeta yay da sumbatar goshinta kamar yanda ya saba. Ko'a jikin yaran dan sun saba ganin hakan ga iyayensu, basa aikata wani abu dazai lalata musu tarbiyyar yara, amma su tarbi juna yayin da wani yay ɗan nesa da gida kona yini guda ne sun nunama yaransu hakan ba komai bane face ƙauna, kuma ya halatta miji yayma matarsa, idan sunga hakan ko'a wani waje ba haramun bane ba. Shiyyasa suma yaran suke kallon hakan a normal ne.


        Da ƙyar ya samu ya gudarma Deen dake bashi labarin faɗan aunty Lulu a airport. Bayan yay wanka falon ya dawo ya zauna cikinsu yana shan fruit salad. Matarsa Saleeha da kowa ke kira da Aunty a family ɗin ta kallesa cikin damuwa da sauƙaƙa harshe. “Abul Mahsin kamar kana cikin damuwa? Wani abun ya sake faruwa ne a office ɗin?”.

      Ƙaramin tsaki yaja da ɗan girgiza kansa. Kamar bazaice komai ba sai kuma ya numfasa. “Mawaddat! Halin yarinyar nan nacimun rai matuƙa Sweetheart. Kullum maimakon abubuwan su dinga sauƙi tana hankali amma sake jagulewa yake. Abinda yafi ɓatan rai Yaya. Shi sam nunawa yake kamar ma komai yana tafiya daidai ne a rayuwar yarinyar. Safiyya ina tsoron UBANGIJI ya tuhumemu akan amanar da baiwar ALLAHr nan ta tafi tabar mana fa...”

       “Tabbas hakane, to amma ya zakayi tunda Yaya yana sama da kai ne. Ita kuma ɗabi'un sun riga sun shigeta tankwarata abune mafi wahala duk da ma kana iya bakin ƙoƙarinka tun bata kai haka ba. Amma babu abinda ya canja”.

     “A wannan karon ina son ya canja kota ƙarfi Saliha. Dan gaskiya na gaji da gani, bana son yarinyar nan ta kuma fi haka gagara...”

   “Tankwarawar ta ƙarfi kam akwai damuwa, dan shi icce tun yana ɗanye ake tankwarashi. Idan ya bushe akace za'ayi zai iya karyewa. Sai dai ni inada shawara. A yanda Deen ya bani labarin abinda ya faru tsakaninta da drivern nan nasan zasu ce zasu koresa ne, inaga karka bari hakan ta faru, inma da dama ya zama driver nata ita kaɗai, dan shi naga ba mutum ne mai wasa ba, ba kuma zai ɗauki halinta ba”.

        A hankali ya sauke ajiyar zuciya. Sai kuma ya furta, “Nagode miki dan tunaninmu yazo ɗaya. Sai dai magana ta gaskiya bamma san yanda zan tunkari yaron ba. Kedai kin san a yanda na samosa ai, aikin nan kuma yana yinsa ne saboda tsare mutuncinsa bawai irin sauran drivers nada bane da take takawa yanda take so. Sannan Aliyu yanada zuciya fiye da yanda kike tsammani da hasashe bar ganinsa hak shiru-shiru baya son magana”.

     “Duk ɗan halak dole ya kasance mai kishin kansa Abul Mahsin. Sannan wannan itace cikar kamalar duk wani ɗan adam na ƙwarai. Karka ƙasƙantar da kanka ga kowa ga komai saboda talauci, ka kasance mai tsaftatacciyar zuciya a baɗini da zahiri, ka kuma zama jarumi a neman na kanka koda duk jama'a na kallon hakan da faɗuwa. Ni nasan baka kawosa yay wannan aikin da ƙasƙanci ba, sai dan wani dalilinka da kuma kare mutuncinsa daga taɓarɓarewar abubuwan da ba'asan mafari ba a rayuwarsa. Kamar yanda kuka samu mahaifinsa a farko kai da Ahmad yanzu ma ku sake samunsa insha ALLAHU zai dawo ya cigaba har ALLAH shima ya kawo masa iyakar komai na jarabawarsa”.

      “Shike nan in sha ALLAHU zan gwada nagani. Ita kuma zuwa anjima zanje gidan na sameta”.

   “Hakan yayi, amma Please smile”. Ta faɗa tana kwatantawa da hannunta a kan baki. Hararta yay yana sakin murmushin.....


           ∆••••∆ ★ ∆••••∆


   Washe gari ma baiyi yunƙurin zuwa aiki ba, sai ma tunanin neman wata mafitar da ya tashi da shi. Kamar yanda ya saba bayan dawowa sallar asubahi ya shiga sashen mahaifinsu domin gaishesa duk da tare suka fita massalaci suka kuma dawo. Ƙyaƙyƙyawan dattijon mutum mai cike da tarin nutsuwa. Da ga gashin kansa har zuwa na gemu fari ne fat. Duk da tsufansa ya bayyana a kallo guda zaka tabbatar da zamanin ƙuruciya ansha ƙyau. Duk da ya ɗan ɗago ya dubesa a lokacin da yake shigowa bai ajiye littafin dake a hannunsa ba. Sai ma ɗan turɓune fuska da ya sake yi. Tsahon mintuna uku baida alamar kulashi, har sai da wasu samari biyu suka shigo, abin mamaki sai ga murmushi ya mamaye fuskar tashi, ya ajiye littafin cike da kulawa idonsa akan samarin dake gaishesa bayan sun ma Uncle Smart kallo ɗaya a gatsine sun ɗauke kai. Oho baima san sunai ba, dan basu isa masa a ido cikin ido ba.

       “Abba Barka da safiya”.

Suka faɗa kusan a tare. Cike da kulawa yake jinjina musu kansa. Ya amsa da “Har an shirya fita kasuwar? Ƴan albarka”.

     “Eh Abba”.

Suka bashi amsa suna miƙewa. Albarka ya shiga saka musu, suko tunda suka amsa sau ɗaya ma basu sake ba. Har zasu fice ya dakatar da su. Cikin ƴar damuwa yake kallonsu. “Nabeel yau kam da ban takuraku ba da kun bama iyayenku kuɗin cefane. Na tashi banda ko nera a jikina gashi babu hanyar samuwarsu garan a yau”.

      A turɓune wanda aka kira da Nabeel ke dubansa. Bakinsa a sama ya ce, “Abba kafa san abubuwan sai a hankali. Kuɗin cefanen gidan nan inba kaiba kuma wazai iya. Sannan jiya fa sai da kasa na baka dubu biyu”. 

     “Nima ai sai da na bashi dubu ɗaya”.

   Ɗayan ya amshe da sauri shima rai ɓace. Ɗan murmushi Abban yayi, yayinda Uncle Smart kejin wani irin raɗaɗin zantukansu ga mahaifinsu akan abinda bai taka kara ya karya ba. Mahaifinsu jarumin ubane da ya tsaya a kansu da ƙare ƙarfinsa wajen gina rayuwarsu. Amma yau sun zama wani abu kowa najin ƙyashin taimaka masa. Ɗari biyar-biyar suka ajiye masa saɓanin abinda ya tambaya suka fice rai ɓace. Gaba ɗaya sai yaji jikinsa ya ƙara sanyi, cikin ƙarfin hali ya fara gaida Abban dake sake ƙoƙarin ɗaukar littafinsa bayan ya kwashe dubu ɗayan da suka ajiye masa. Maimakon amsa masa gaisuwar a zafafe ya ce, “Shima wannan aikin sun korekan?”.

    Kasa amsawa yayi ya ƙara ƙasa da kansa zuciyarsa na ƙuna. Ba'a kan ƙaddararsa ba, ba kuma akan abinda mahaifinsa ke tuhumarsa ba, sai akan damuwa da halin da mahaifin nasu ke ciki....

      “Wai halan bada Ali nake magana ba?!”.

   Ya faɗa cikin fusata.  

“Kayi haƙuri Abba dama....”

“Dama mi? Mi kake son faɗamin? To wlhy bari kaji a wannan karon bazan ɗauka iskancinka ba. Bari ma na faɗa maka gaskiya in har maganar banzarka ce da ka saba to a wannan karon ka shirya barmun gida, dan bazan iya cigaba da wahala da kai ba bayan wadda nayi kana yaro. Na ciyar da kai abinci, na tufatar da kai sutura, na sakaka a makaranta islamiyya data boko har matakin digiri na biyu sannan na cigaba da wahala da kai. Ga kanenka nan na bayan baya sun tsaya da ƙafafunsu harda masu aure amma kai ban daina cidaka abinci ba, wannan wace irin rayuwa ce. To ba asiri ba a wannan karon ko kukar bulukiya aka sauke a kanka bazan ɗauka ba na gaji da shashancin ka, tashi ka ficemin daga nan na baka zuwa dare wlhy ka tsara mai yuwuwa sakarai kawai cima zaune”.

         Idanunsa da suka kaɗa sukai jazur ya ɗago kaɗan ya subesa. “Kayi haƙuri Abba ALLAH ya huci zuciyarka, dan ALLAH ka gafarce ni”.

    Banza ya masa bai sake tankawa ba. Yasan minene shiru a wajen mahaifin nasu. Dan haka ya miƙe ransa a matuƙar ƙuntace ya fice. Har ya nufi hanyar sashensu na samari ya fasa. Ƙirjinsa zafi yake masa. Ji yake kamar ya saki kuka amma bazai iyaba saboda taurin zuciyar tsiyarsa. Sosai mutane ke kai kawo a cikin layin nasu. A halin da yake ciki baya buƙatar yin magana da kowa, dan haka yay ƙoƙarin juyawa zai koma ciki. Daga motar da tun fitowarsa idonsa ya sauka a kanta amma ya kauda kai aka danno masa horn. Ƙin juyawa yay har sai da aka sake na biyu da ambaton sunansa. Cak ya tsaya amma bai juyo ba har Uncle Yousuf da abokinsa Ahmad suka ƙaraso garesa.

       “Kayi haƙuri”.

    Kalmar data tilastashi juyowa da ga bakin Uncle Yousuf..........✍️


No comments