Furar Danko 20
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣0️⃣
........Cikin kuka da dafe kanta tana ɗan layi alamar ta fara shiga maye ta ke faɗin, “Wlhy! Idan baka fita sabgata ba sai na keta maka rigar mutuncin tufafi da mutanen gari ke kallonka da shi, dan dama shi kaɗai ya saura gareka. Nace banayi! Banayi wai na minene wannan takura duk inda na saka ƙafa kana biye dani, shine yau harda bani wine saboda kai tsinanne ne, ka taɓa ganin na sha wine ne duk rashin ji na azzalumi!! Shin wai ku kuna ɗaukar duk macen da ke shan wannan abubuwan dan bama kanta farin ciki ita ɗin ƴar iska ce ko me? Manyan banza manyan kawai, ku gama hura hanci ga al'umma ku dawo bayan fage kuna lalata musu tarbiyyar yaransu. Ka sani har gaban abada bazaka taɓa samun wannan jikin ba, bama kai ba duk wani maye sai gani sai hange dan ni ba mazinaciya bace, bar ganin ina wannan rashin jin nasan ciwon kai na wawa kawai da ƙi ƙ.....” ta kasa ƙara sawa saboda shuuu da tai zata faɗi. Da sauri Nadiya ta tarota. Fisge jikinta tai tare da ɗagowa gaba ɗayanta kan ƙafafunta ta ɗauke fuskar Nadiya da mari haggu da dama.. A fusace Alhajin nan da ke tsaye tun ɗazun cikin ɓacin ran zagin da Lulu kema abokin nasa yayo kanta. Hannu ya ɗaga zai kwasheta da mari shima, sai dai cak ya tsaya jin an riƙe masa hannu ta baya. A karo na farko duk wanda ke'a falon ya farga da shi. Kallon ido cikin ido sukaima juna shi da Alhajin da ke faman huci. Idanu ya lumshe cikin girgiza kansa da faɗin, “Haba kai kuwa ai babba babba ne, ba'asan namiji kuma da faɗa da mace ba. Bakaga abokinka yanda ya nuna mazantaka ba? Tunda kun gama zubar da kimarku garesu banga abin tada jijiyar wuya ba idan irin haka ta taso a tsakaninku ai......”
“Kai kuma a matsayinka na ubanwa anan?”.
Maimakon amsa sai ya ƙara tsaresa da idanunsan nan masu kwarjini da suka gama ƙwarewa a kallo mai girgiza zuciya cikin nuna gargaɗi (Na macizai inji Lulu😂). Sakin hannun Alhajin yayi, kafin cikin yanayin nan nasa a daƙile da kowa ke ɗauka girman kai ya ɗage kafaɗunsa da ɗan taɓe lips ɗinsa. “Sanin ɗan waye ni bazai maka amfani ba, idan dani kake son sani sai na baka amsa da cewar drivern ta ne”.
“What?! Driver fa?!!. Ubanwa to ya baka damar shigo mana nan har da tsoma baki a cikin abinda bai shafeka ba?”.
Shi ba mai yawan magana bane, dan haka maimakon amsa masa a yanzun ma sai kawai ya zuba masa ido. Hon. HD Nakowa sai ya sake fusata. Magana zai sakeyi cikin fusata Alhaji Ɗan-kande Baita ya dakatar da shi.
“Kaga HD please it's ok mana. Kai ɗan saurayi jeka kawai waje ka jirata nan ba huruminka bane ba”.
Wani banzan kallo Smart ya watsa musu su dukan, sai dai baice komai ba ya juya ga Lulu da ke zaune a kujera sharɓe tanata surutai da zagi har yanzu. Hanunta kawai ya fisga ta miƙe, batare da wani binta a hankali ba ya jata tana turjewa sukai waje. Da ƙyar ya iya kaita har motarta, dan haka ta maido da zagin da take ma Hon. Babale Misau kansa. Hakan bai damesa ba, sai ma rufeta da yay a motar ya koma falon ɗaukar handbag ɗin ta dan key ɗin motar na ciki....
“Ban yarda da wannan yaron driver bane ba, dan haka ina son a binciko min ɗan uban wanene shi a faɗin garin nan na kano”. Hon. HD Nakowa ne ke faɗa dai-dai Smart na sake shigowa falon ɗaukar tarkacen Lulu. Nunawa yay kamar baiji mi Hon. Nakowan ya faɗa ba, ya nufi handbag ɗin da ya gani ɗazun a hanunta da takalmanta masu azabar tsini ya kwashe ya sake juyawa ya bar falon ko kallo basu ishesa ba.....
Gotawarsu kaɗan da gidan wata dalleliyar mota ta iso ƙofar ita kuma. Horn yay aka buɗe masa. Yanda sautin kiɗa ke tashi a cikin motar zai baka tabbacin yana cikin nishaɗi matuƙa. Duk da yasan taro ake a gidan nasa hakan bai hanashi jin mamakin ganin wasu manya-manyan motoci guda uku ba, bawai ƴammatan bazasu iya zuwa da motocin bane, a'a kawai dai yasan sun musu girman da bazai yiwu ace sune suke hawansu ba. Cikin kai-kawo zuciya ya fito yana ƙara ƙarema motocin kallo, cikin ɗan basarwa irin na masu akwai ya ɗage kafaɗu da ɗan taɓe baki yay ciki abinsa ransa fal nishaɗi yau zai haɗu da mafarkinsa. Yayi alƙawarin sai ya ɗanɗani yarinyar nan dan ta tsare masa ko'ina na zuciya tun a randa ya ganta. Da wani irin sauri yaja birki ya tsaya yana ƙarema falon nasa da ya hargitse kallo, bawai na tarkacen da suka zube bane kawai dan yasan wannan ne ya kawosu ai. Iya shegen da ake aikatawa a falon duk da shima yasan yana aikatawa ya sashi zama turus, dan shi dai Nadiya batace masa zasu gayyato namiji ko ɗaya ba. Amma sai ga har mutum huɗu manyan mutane sa'ar Daddynsa, kai abinma tashin hankalin shine harda abokan Daddyn nasa ma da suka sanshi ya sansu. Da baya-baya ya koma ganin hankalinsu su bai kai kansa ba saboda shagala a ɓarnar da suke aikatawa da yaran mutane. Duk cikinsu baiga Lulu ba, gashi kuma an tabbatar masa da tazo wajen awa biyu baya da suka shuɗe. Waya ya ciro yay kiran Nadiya, an jima ba'a ɗauka ba dan har tana batun tsinkewa sannan aka ɗauka. Cikin wata irin murya ta ce, “Ranka ya daɗe barka da dare”. Sai da ya ɗan cije leɓen haushi kafin ya amsa mata da “Ta iso ne?”. Cikin muryar nan na wadda ta gama buguwa da shiga yanayin masha'a ta amsa masa da “Tazo amma shegen driver ɗin nan nata ya kwasheta sun tafi”.
“What!!” MM Atik Kumo ya faɗa da ƴar tsawa. Bai jira cewar Nadiya ba ya yanke wayar ransa a ɓace. Mota ya shige ya zauna tare da kwantar da kansa kan steering. A karo na biyu ya rasa damarsa akanta, tunda yake wata mace bata taɓa shiga ransa irin haka kamar yanda Lulu ƙamshi ta shiga ba. Da gaske sonta yake, yana kuma tsananin buƙatar mallakarta. Bai damu ace sai da aure ba, dan shi a halin yanzu babu maganar aure ma a gabansa duk da kullum faɗan momynsa kenan shine yay aure. Sai dai da to kawai yake amsa mata a duk sanda ta titsiyesa. Tun randa suka haɗu da Lulu a airport ya kasa hutawa da tunanin surar yarinyar da tsiwarta, burinsa kawai ya gusar da ƙishinsa gareta dan kowace mace tama daina birgesa a dalilinta yanzu. Sake kaiwa steering duka yay tare da tashi zaune yayma motar key a fusace ya bar gidan......
★★
Driving ɗin yake cikin ɓacin rai da takaici, yayinda ita kuma ta keta faman surutai da zaginsa akan ya maidata sai ta koyama Hon. Babale Misau da Nadiya da suka haɗa baki hankali. Faɗi take ita ba ƴar iska bace, duk wanda yace zai mata iskanci sai ta wulaƙanta shi.....
Wani irin baƙin ciki ne ya sake turniƙe zuciyar Smart dan surutanta sun ishesa, sake tunzura fushinsa suke zuciyarsa na ƙuna. Wani shegen birki ya taka a harzuƙe har sai da tai gaba ta bugu da kujerar gabanta ta sake buguwa da jikin ƙofa sannan ta koma ta zauna daɓar. Dafe kanta tai dan azaba kamar zata fasa kuka, sai kuma ta harzuƙo cikin fushi da masifa ga rashin kasancewa a hayyaci da ya ƙara hauhawar masifar tata ta ce, “Kai wai miyasa baƙauye ne akoda yaushe? Mugu so kake ka kasheni ka gudu da motan ko? Illiterate kawai, ba abinda ya iya sai shashashanci baƙauye”.
Idan motar nan ta motsa Smart to shima ya motsa, yakai matuƙar wuya so yake ya mata masifa dan maƙogwaronsa sai kaikawo ya ke a wuya amma yanata ƙoƙarin hana kansa, sai ma wayarsa da ya ɗauka ya fara danne-danne abinsa. Hakan ya sake fusata Lulu, da ma yaya lafiyar kura balle ta tsinke. Tana ƙalau ma yaya aka ƙare da jaraba balle yanzu da ya haɗa da maye. Sosai ta cigaba da zazzaga masa masifa ko haɗiyar yawu ma batayi, ganin badai zai kulata ba ta kama murfin ƙofar zata buɗe ta fita amma sai taji yayi lucking motar. Wayyo azabatun azaba. Yau dai kam yaga masifar ƙare dangi, dan bakinta baiyi shiru ba har sai da barci ya fara rinjayar mata idanu. Da wahala kaga Lulu tasha abu ya sakata barci, shiyyasa ko cikin abokanta ake ji da ita da kwarzanta ƙarfin kanta, amma yau da yake wani mugun haɗine MM Atik yay mata batare da ko Nadiya ta sani ba yasa abinda yafi ƙarfin kanta kala-kala wani ma bata taɓa shansa ba. Tun randa suka haɗu a airport bai huta ba, biye yake da ita yana ninƙaya cikin al'amurranta har sai da ya gama sanin ita ɗin wacece. Dan haka ya jawo Nadiya a jikinsa ya dinga jiƙata da kuɗaɗe harta amince da shi bawai yazo dan ya cutar da aminiyar tata bane son gaskiya yake mata. Ita da shi suka haɗa plan ɗin wannan phaty na samun lafiyarta, ya kuma saya musu duk kayan shaye-shayen tare da basu gidan hutawarsa da ya gama ginawa kwanan nan, shi yayi hakane dan ya rutsa Lulu a can, yayi imanin in har ya sameta sau ɗaya da kanta zata cigaba da nemansa kamar sauran ƴammatansa tana kawo masa kanta. Sai dai kuma kash, bayan ya gama wahalar haɗa dukkan plan ɗinsa wani shegen driver ɗinta ya zo ya rusa masa komai.........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
No comments