Furar Danko 19
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣9️⃣
........Smart kam tuni ya shanye titin layin zuwa babban titi, da ƙyar ya samu napep. Tafiyar da bata wuce mintuna talatin ba ta kawosa anguwarsu. Kasancewar da sauran hasken gari koda ya shiga sai ya ɗan watsa ruwa tare da zuwa ya gaida Abba da su Ammah, sai dai ya iske Ammah ma ta fita ita da aunty Amarya Barkan ƙanwar Aunty Amaryar da ta haihu a can Gadon ƙaya tun la'asar, sai su Maryam kawai da suka dawo islamiyya. Dan haka bai zauna ba suna gama gaishesa ya fito ya koma ɗakinsa. Ba wasu abokai ne da shi ba shi dama sai Ahmad kuma ba anguwar yake ba. Dan Mutum ne mai ƙarancin kwaramniya. Idan kaga abokinsa da har zasu iya zaman doguwar hira to sai dai abokan karatunsa, amma na cikin anguwa sai gaisuwar mutunci kawai, duk da dai a da anyi abotar yarinta, sai dai kasancewar sa mara sakewa da mutane suke masa kallon mai girman kai duk suka janye jikinsu da shi, shi kuma bai nuna ya damu ba. Abokan karatun kuwa akan jima ma ba'a haɗu ba sai ta waya ko wani taro mai muhimmanci ya haɗa. Shiru ya kwanta kamar mai barci, da gani kasan duniyar tunani ya faɗa, dan babu abinda yake sai furzar da huci akai-akai da ga bakinsa, hakan kamar ɗabi'a ce data zame masa jiki in dai yana cikin damuwa.. Abubuwa ne masu yawa ke ci masa rai, ciki harda batun bauɗaɗɗiyar yarinyar can, shi mutum ne da baya shiga sabgar da ba tashi ba koda kuwa a cikin gidansu ne sai idan yaso, amma sai yake ji zuciyarsa na ingizashi akan taimakon ubangidan nasa da yarinyar, badan komai ba sai dan ƙannensa mata da bazai taɓa fatan su tsinta kansu a irin wannan rayuwar ba. Yasan idan har ya tsamota da ga wannan musifar yayi jihadi, sai dai bai san ta ina zai farama taro wannan al'amari nata ba. Karan farko yaja sirrin tsaki, sai kuma ya tashi zaune yana ɗan furzar da huci tare da kai hannunsa saman goshinsa yana ɗan murzawa. Ganin yaƙi samun nutsuwar hutawar da yake buƙata ya sashi tashi ya fito a ɗakin, nan ƙofar gidansu ya zauna yana ɗan gaisawa da mutane masu wucewa har akai kiran sallar magrib. Bai fito da ga massalacin ba sai da akai isha'i, yana kwaɗayin shiga gidan suyi hira da Ammah dan wannan ɗan lokacin kawai yake da damar haka gareta, amma zuciyarsa nata masa tuni akan Lulu da abinda yaji suna magana ita da ƙawarta zasuyi a daren na yau da sunan wai murnar samun lafiyarta. duk yanda yaso yaƙar zuciyarsa abin ya gagara, saboda yana ji a ransa ba alkairi za'a shuka ba wajen, dan haka ya fito da ga layinsu ya samu Napep zuwa hotoro gra. bai damu da kuɗin da suka tsuga masa ba. Ɗan nesa da gidan ya sauka, amma ya tsayar da mai napep ɗin, ya samu jikin wata bishiyar dabino kusa da katangarsu ya tsaya, ya kai mintuna talatin da wani abu a wajen yaji motsin an buɗe gate ɗin gidan, ido ya zuba na son ganin wanda zai fito. Ilai kuwa Lulu ce, dan a kanta idanunsa suka sauka saboda haske dake tako ina a street ɗin, gashi ta sauke glass ɗin motar sosai har kana iya hango kalar kayan da take sanye da su. Tayi ƙyau matuƙa ga uban ƙamshinta na isowa har inda yake tsaye saboda yanda ta gumbuɗashi kamar ba mace ba. A ɗan kasancewarsu na kwanaki ya fahimci sam bata tausayawa ƙamshi, haka kawai sai yaji tanan ɓangaren ta ɗan samu sassauci a garesa, duk da tana saka nata ƙamshi ne ba bisa ƙa'idar da ya kamata ace mace ta saka ba. Da sauri ya ƙarasa ga mai napep da ke zaman jiransa. “Kabi wannan motar Please, amma karka bari ta fahimci muna biye da ita”. Ya faɗa yana nuna ma mai napep ɗin motar Lulu da ke tafiya a hankali kamar bata son tuƙin yau. Yanda take tafiyar ya bama mai napep ɗin damar binta cikin hikima har zuwa wata sabuwar anguwa, dai-dai wani gida da alamu suka nuna shima ba'a daɗe da kammalashi ba ta tsaya, da ga inda suke yana hangen yanda ta kai waya a kunnenta alamar kira take ko an kirata, tana ajiye wayar ana buɗe gate ɗin gidan. Da sauri ya fita tare da miƙama mai napep kuɗi yana faɗin, “Abokina nagode ko”. Bai jira amsarsa ba ya nufi gidan, kasancewar akwai ƙarancin haske a anguwar dan kamar ma basu da wuta sai ƙarar gen... Ɗin gidan data shiga yake jiyowa ya samu damar bin motar tata ta gefe suka shiga tare batare da mai-gadin ya lura ba. Motoci ne kusan bakwai a gidan duk an parker a babban compound ɗin kamar wasu masu biki, tun kafin ta fito a motar ƙawayen nata suka baibayeta da ihun faɗin, “Sai Lu ɗin mu!!!, sai ƙamshin mu!!!”.
Fuskarta ƙawace da wani shegen murmushi ta fito. Wani shegen gown ne a jikin nata ta lafe mata kamar babyn roba. Da sauri ya kauda idanunsa yana mai jan sirrin tsaki da taune lips ɗinsa da ƙarfi. Bai sake kallon inda suke ba har suka shige ƙofar da yake ƙyautata zaton ta cikin gidan ce. Huci mai zafin gaske ya furzar tare da gyara tsaiwarsa. A ɓangaren su Lulu kam suna can cikin ƙaton falon gidan da ya sha kayan alatu. Abinda zai baka mamaki bawai iyakar su kaɗai bane ƴammatan ashe, akwai dattijan maza a shekaru bawai a cikar kamala ba har su huɗu, tun shigowar su Lulu kusan su duka suka zubo mata idanu fuska a washe, yayinda ita kuma nata murmushin ya ɗauke ta wani yamutse fuska tana kallon Nadiya, sai kuma ta juya ta fito a fusace. Da sauri Nadiya tabi bayanta tana faɗin, “Please Lu ki saurare ni.”
“Anƙi a saurareki ɗin, Nadiya kin san dai na tsani irin wannan ko...?”
“Na sani, amma bamu da wani zaɓi ne wlhy Lu.., dan ALLAH ki fahimce ni, kin san dai bazanyi abinda zai ɓata miki rai da gangan ba....”
“In ba kinyi da gangan ɗin ba miya kawo waɗan nan tsoffin banzar nan? Ni ban hanaki huɗɗa da su ba, amma ki sani duk randa suka zubar da ke bayan gama lalata miki ƙuruciya kiyi kukanki ke kaɗai kar ki tunkareni. Amma ki daina sakamin su a sabgogin rayuwata”.
Ɗan murmushi Nadiya tayi cikin rashin ɗaukar zancen na Lulu da muhimmanci ta ce, “Naji, ni dai yanzu kiyi haƙuri mu koma ciki dan ALLAH. Dan wannan fa zaman naki ne, dan ke akayisa, mun riga mun gama tara mutane, su Shony fa tun daga ktn suka taho a yammacin nan domin wannan shagali kawai. Abinda yasa ki ka ga su Alh. Baita anan ma saboda su Shony ne, dan sun riga sun kirasu cewar zasu shigo Kano, amma wlhy badan ke bane ba”.
A hankali ta furzar da iska, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya. “Shike nan amma ki kiyaye gaba, dan in har kika sake sakamin sabgar waɗan nan mutanen a tawa wlhy sai mun rabu. Suma su Shonyn idan suna buƙatar haɗuwa da su ne suje can su haɗu bai shafeni ba”.
“Naji na yarda baza'a sake ba. Suma kuma zan musu bayani yanda zasu gane Muje to dan ALLAH suna jiranmu”.
“Bani details ɗin mai kayan nan na tura masa kuɗinsa karna shiga wata sabgar. Sannan wannan gidan na waye uwar kwashe-kwashe kika kawo mu kuma?”.
Gidan Nadiya ta kalla tana ƴar dariya tare da faɗin, “Gidan wanda ya sayar mana da kayan ne, wlhy Guy ɗin akwai kirki gashi so handsome kuma, ya bamu shawara ne muzo nan musha shagalinmu dan zaifi mana sirri kasancewar kinga dare ne, ke kuma ba cika son shiga clubs na nan Kano kikai ba kin ce ƴan hayaniya da ƴan iska sun cika yawa”.
Cikin rashin damuwa ta ɗage kafaɗa kawai, batare da ta sake tofa komai ba ta bar wajen. Binta Nadiya tai suka shige tare.... Gaba ɗaya zuciyar Smart ta sake jagulewa da takaici, dan duk abinda Lulu da Nadiya ke tattaunawa yana jinsu batare da su sun lura da shi ba. Shigarsu da kusan mintuna uku sautin kiɗa ya fara tashi kaɗan-kaɗan saboda rufe windows da sukai duk dan kar kiɗan ya fita wa mutanen anguwa. Kansa ya ɗan dafe yana mai ambaton sunan ALLAH, gaba ɗaya ma ya rasa miya kamata yayi, duk da yazo nan ɗinne da burin ganin abokan sheɗanar tata da kuma hanata shan komai. To amma ta ina zai fara ma?. Ya kwashe kusan mintuna ashirin yana ƙullawa da kwance ta yanda zai shiga wajen.... Ƙarar hayaniya da ta fara tasowa kaɗan-kaɗan da ga cikin falon ta maidosa da ga dogon tunanin mafita da ya tafi, ajiyar zuciya yaja kamar wanda aka farkar da ga barci tare da tsurawa ƙofar idanu. Wasa-wasa hayaniyar ta daɗa karfi har yana iya shaida muryar Lulu saboda tsayawar ƙarar sautin kiɗan da ke tashi, da alama sun kashe ne ko wata matsala ta faru. Falon ya nufa da sauri batare da tunanin komai ba ko neman izinin ya tura ƙofar ya shige, yanda ya gansu a yamutse ga Lulu na ɗurama wani hamshaƙin Alhaji zagi har tanayi kamar zata tsole masa ido da ɗan yatsa ya sashi yin turus, mamaki ne ko takaici oho baima sani ba, kayan shaye-shayene da na ciye-ciye ko'ina a barbaje, yayinda alhazan nan guda huɗu da ya shaida fuskar biyu a cikinsu kasancewarsu wasu manyan ƙusoshin attajirai kuma ƴan siyasa masu faɗa aji a garin na kano ɗaya ke tsaye cikin fusata kamar zai daki Lulu, sauran ukun na zaune sun zuba mata ido harda wanda take zagin da shi fuskarsa ma ƙawace take da murmushi kamar bashi akema tujarar ba. Kalaman Lulu ne na ƙarshe-ƙarshe da kukan da ta fashe da shi ya dawo da shi hayyacinsa.........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
No comments