Recent Updates

Furar Danko 18

 


𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲





  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗




           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻



𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣8️⃣




.........A ɓangaren Lulu kam sosai ta haukacema ƙwaro ta waya da masifa shiko ya dinga rantsuwar ya saka mata. Har abokinsa da yay komai a gabansa ya bama wayar ya zame masa sheda amma taƙi yarda. Sai ma katse kiran tai da tabbatar masa sai ya san ita ya cuta wlhy... Gado ta faɗa zuciyarta na mata wani irin tafasa, babu abinda ke mata kai kawo a rai irin maganganun drivern ta, haka kawai zuciyarta ke ingizata akan son sanin ma'anarsu. Wayarta data yasar gefe ta jawo. Nadeeya ta kira, ana ɗagawa daga can Nadiya ta fara da faɗin, “Bastie dama fa yanzu zan kiraki, dan gama wayata da Gajere kenan yace za'a samu kaya a wajen ogansa kona mil. ake s.....”

       “Kinga ni ba wannan ba...”

    Ta faɗa cikin katse Nadeeyar. 

“Oh to ina saurarenki, na jiki kamarma cikin ɓacin rai, miya faru kuma? Badai driver ɗin ba kuma?”.

      “Komai ma ya faru, har ma abinda banyi zaton faruwarsa ba ya faru. Wani Hausa nake son ki fassara min”.

   “Tofa! Wane Hausa kuma?”.

Batasan ta haddace abinda ya faɗa matan ba sai da ta zayyanosu tsaf a yanda ya faɗesu babu ko gargada. _“Duk macen data cika mace mai suturtawace akan kanta har akan muharramanta, hakan kansa ko bata kira daraja gareta ba, darajar kanzo ta risina mata a gaban wanda ya fita ma balle wanda ke a ƙarƙashin ikonta. Wannan gata da musulunci yayma mace har a lafazinta ana so ta zama mai ƙyautatawa akan harshe”._ 

     “Woow Madam irin wannan kalamai haka kamar wata mai tsara baitikan waƙe, dan ALLAH waya shiryasu haka....”

    “Mtsoww malam dilla fassararsu nake buƙata nace”.

    “Oh sorry, tab wlhy fa kalaman sunyi tsauri, ni kaina ban san yanda zan fassarasu ki gane ba dan hausan ba gama isata yay ba. Amma ina zuwa bari na tambaya”.

         Tana ƙoƙarin ajiye wayar cikin jan tsaki Suhaib na mata knocking. “Uwar miye?”. Ta faɗa cikin masifa. Cikin tunzura baki Suhaib da ke da ga ƙofa dan bai shiga ba ma ya ce, “Uncle Yousuf ne yazo, ya ce kizo” da ga haka yay wucewarsa.

      Tana son Uncle Yousuf matuƙa, tana kuma girmamashi saboda wasu dalilai nata na kanta. Dan haka tace ma Nadiya tana zuwa ta yanke wayar. Da mamaki mai nuna ɓacin rai take duban Smart da ke zaune a ƙayataccen falon nasu kusa da Uncle Yousuf. “Mi wannan abun yazo yimana nan Uncle You?”. Ta faɗa tana nuna Smart da ke zaune babu alamar ɗari-ɗarin nan irin na ma'aikaci da iyayen gidansa a tare da shi. “Ni na kirawoshi” Uncle Yousuf ya bata amsa cikin ɗaure fuska. “Uncle nifa bana buƙatar sake ganinsa” ta faɗa itama a harzuƙe. 

      “Da yay miki mi?”.

   Baki ta tura gaba cikin kumbura fuska ta ce, “Wlhy na tsanesa, har ni wannan mutumin zai zaga. Korar ma da nai masa yanzu ba'ita kenan ba Uncle, ya jira hukuncin da zai biyo bayanta. Har ni zaima banza ina masa magana, sannan ya biyoni da baƙaƙen maganganu a gaban su maigadi, har shi waye? Mi yake jin kansa? Ɗan u......”

     Hannu Uncle Yousuf ya ɗaga mata, “Ya isa haka. Mawaddat wai yaushe zakiyi hankali ne dan ALLAH. Yanzu abinda kike yi ko su Suhaib ƙannenki zasu aikata ne? Ke kullum cikin korar mutane. Yanzu dai ina son ki nutsu ki kwantar min da hankalinki, dan shiyyasa ma na dawo da shi gidan a yanzu dan na haɗu da shi a hanya ne. Ban kawo Aliyu gidan nan dan ki koresa ba, zan ƙara jaddada miki a yanzu shi ɗin zai dinga kaiki duk inda kike so dan saboda ke kaɗai ma na ɗaukesa aiki. Zai zo ƙarfe bakwai da rabi saboda takwas kike fita aiki, zai dawo da ke ƙarfe biyar da rabi kamar yanda kike dawowa shike nan ya tashi sai kuma washe gari period na gama magana.”

       “Amma Uncle....”

Hannu ya ɗaga mata alamar baya buƙatar ta sake cewa komai, rai ɓace tabar wajen kamar zata fashe dan haushi. Da ga haka ya juya ga Smart da ke zaunensa a yanda ta shigo ta samesa batare da yabi takanta ba. “Wannan shine lokacin zuwanka aiki da tashin ka. Amma weekend zaka iya zuwa da ga goma zuwa huɗu sai ka tashi. Zan baka duka tsare-tsaren fitarta a rubuce, sai kuma idan zuwa wani waje ya kamata kasan aikinsu yana sakasu ɗan yinan-yinan koba shiri. Dan ALLAH ka ƙara hakuri, al'amarin Mawaddat sai addu'a, ga yanayin da take ciki na ƙara kangarar da ita. Kai tsakaninku ma akwai cigaba, dan naga alamar tana shakkar ka sosai”.

      Karan farko ya saki ɗan murmushi da shafa kansa. “Alhaji wane tsoro kullum ana zageni da kirana illiterate ko villager. Kawai dai zanyi haƙuri domin mutuncinku da ceto rayuwarta, dan koba komai nima inada ƙanne mata, ina son kuma ALLAH ya karemin su a duk inda suka shiga.”

     “Gaskiya ne wannan Aliyu. Ina godiya matuƙa a gareka da sake baka haƙurin di. Yanda ALLAH ya haɗa wannan zuminci a tsakaninmu ALLAH yasa muci moriyarsa har a gidan aljanna. Amma ina son naji wannan kalamai da aka faɗama yarinyata haka har suka harmutsa min ita, duk da nasan abu kaɗan ma fusata Mawaddat yake”.

    Murmushi Smart ya sake yi a karo na biyu da faɗin, “A Alhaji ai ba'ayi haka ba. Tunda ya wuce a barsa kawai sai na gaba idan ALLAH yasa za'ayi a gabanka, duk da ina tsoron kuma karta kwaɗa min mari dan yau ma dai da ƙyar na sha shiyyasa ma na gudu”.

       Dariya sosai Uncle Yousuf yake kwasa da faɗin, “A lallai ka tsira da ƙyar, dan a ma'aikatan gidan nan ɗai-ɗai ne basu sha marin Lulu ƙamshi ba kam”.

    “To kaji ko Alhaji. Bara nayi nan kafin ta sake fusatowa ma, nasan yanzu bai zama lallai na sha ba”.

Dariya Uncle Yousuf ɗin ya sake kwashewa da shi, shi kuma ya fice yana ɗan murmushinsa mai sanyi, har ga ALLAH yana ganin mutunci da kimar Uncle Yousuf, yaji kuma zai iya haƙuri da yarinyar kodan shi ɗin. Mutum ne da yasan daraja da kimar mutane, duk yanda kake baya wulaƙantaka ko nuna maka ɗagawar shi ɗin wani ne. Ya iske har lokacin su maigadi na gulmar Lulu, ganinsa baisa kuma sun daina ba sai ma kwarzantashi da suka shigayi akan abinda yaymata. Komai baice musu ba sai kansa da ya ɗan girgiza kawai ya ciro wayarsa ya fara sana'ar tasa, ba kuma wani abu yake a ciki ba face game ɗin ball.

      

       Bayan kamar awa ɗaya Uncle Yousuf ya fito zai wuce gida, Lulu ce tai masa rakkiya har wajen motarsa, aiko ta dinga antayama Smart da bai san tanayi ba harara. Dariya Uncle Yousuf ya dingayi ƙasa-ƙasa, dan sarai ya lura da ita, sai dai baice komai ba yayma su maigadi alheri kamar yanda ya saba. Godiya da addu'a suka shiga kwararo masa. Murmushi ya dinga musu kawai, dan harga ALLAH yana jin matuƙar daɗin addu'oi nan nasu. Duban Lulu da keta faman yamutse fuska yay, cikin tsokana ya ce, “To Daughter kin bani aron drivern naki ko na tafi da shi”.

       Fuska ta sake kwaɓewa da faɗin, ni nama bar maka Uncle You, Dan bana buƙatarsa sai shegen girman kan tsiya”. 

     Dariya yayi, yana mai kiran Smart dake zaune kansa ke ƙasa. “Shiga muje” kawai yace masa. Bai musa ba ya raɓa ta gaban Lulu dake faman binsa da kallon banza, ciki-ciki ta furta, “An samu motocin banza sai hawa ake”.

       “Ko ke kika zama mota hawa zanyi”. Ya faɗa shima a ƙasa-ƙasa lokacin da yake shigewa cikin motar. 

   “Kai ɗin banza! Shashasha!”

Ta faɗa a zafafe har tana zaburowa. Wani shegen murmushi ya sakar mata a karon farko yana ɗan ƙara gimtse fuskarsa kamar bashi ya furta ba ya shige motar abinsa. Wayyo ba'a taɓa Lulu ba ma ya aka ƙare balle. Dariya sosai Uncle Yousuf yake yi, dan ya fahimci akwai abinda ya faru duk da Smart ɗin ya fuske abinsa kamar bai aikata komai ba. Har yaja motar suka fice bata bar masifar ba. 

     “Na kula dai kai kake fara kunna min yarinya ka noƙe”. Uncle Yousuf dake dariyarsa har yanzu ya faɗa dai-dai yana harba motar saman lafiyayyen titin anguwar. Kaɗan Smart ya shafo kansa yana ɗan murmushi batare da yace komai ba. Sai da sukai ɗan nisa ya zaro ledar da ya cire a cikin kayan fruit ɗin Lulu. Buɗeta yay, tarin ƙwayoyi kala-kala suka bayyana. Motar neman ƙwacema Uncle Yousuf ɗin tayi, da sauri ya gangara gefen titi cikin rawar harshe ya furta, “Wannan fa Aliyu?”. 

      Cikin damuwa da ɓacin rai shima ya bashi amsa da, “Fitar da mukai ɗazun abinda muka fara tsayawa akai order kenan a wajen wasu masu fruits kafin mu ƙarasa inda tace zataje”.

       Sosai jikin Uncle Yousuf ke rawa, dan har ga ALLAH shikam bawai bai yarda da maganar Doctor Khalifa bane, kawai dai rashin ganin al'amarin a zahirinsa ya sa bai kai masa ƙololuwa a rai ba, shiyyasa ma ya ɗora Smart ɗin dan ya samu tabbaci. Kamar wanda ya shiga ɗimuwa ya sake furta, “Aliyu Hydar! Ka tabbata a jikinta ka samu waɗan nan ƙwayoyin?”.

       Cikin salon dakewar nan tasa da rashin son magana ya ɗan ɗage kafaɗunsa da faɗin, “Yaah! A gabana ma aka saya”.

   “Dolene na saka a kama yaron nan dake sayar mata, bara ma na kira CP....”

Da sauri Smart ya dakatar da shi. “Niko a nawa shawaran Alhaji kamar kama yaron ba shine mafita ba tun a yanzu. Domin inaji a jikina ba dashi kaɗai take huɗɗa ba. Dan ka saka an kamashi kamar ka fargar da itane ta sake sabon salo ita da abokan mu'amalarta. Kaga kenan ba hanyar da zamu rabata da al'amarin muka ɗakko ba kenan, dan yanzu aka fara wasan kamar”.

     Sosai maganarsa ta shigi Uncle Yousuf ɗin, dan haka ya ɗan dakata da ga ƙoƙarin kiran cp da yake shirin farawa, sai dai idanunsa sun kaɗa jazur harda ƴar guntuwar ƙwalla a cikinsu. Shiru babu wanda ya sake magana a motar har kusan mintuna huɗu, kowa da abinda yake tattaunawa da zuciyarsa.. Shine ya kashe shirun nasu da furzar da iska mai zafi. “Alhaji ni zan wuce, dan yamma nayi gashi ina son na isa gida da wuri”.

     Cikin damuwa ya gyaɗa masa kai batare da ya iya furta komai ba har sai da ya fita yana ƙoƙarin rufe ƙofar motar ya kira shi a hankali. Ɗan duƙowa yay yana amsawa, Uncle Yousuf ya miƙa masa kuɗi masu yawa. Kansa ya girgiza da faɗin, “Kayi haƙuri Alhaji, tun farko na faɗa maka kada irin haka ya dinga shiga tsakaninmu. Hakkina kawai nake buƙata a kowane ƙarshen wata kamar yanda mukai alkawari. Na barka lafiya”.

        Ajiyar zuciya mai ƙarfi Uncle Yousuf ya sauke ta re da sakin ɗan murmushi yana mai binsa da kallo. Tabbas a girme yasan zai iya bama Aliyun shekara bakwai. Amma dattako da kamunkan yaron na sakashi jin ya cika masa ido tamkar wani babba garesa. Wata irin kima da kwarjini yake masa a zuciya da cikin udanu. Yana matuƙar son ganin mutumin da yasan ciwon kansa a rayuwa da riƙe mutuncinsa. Ya yarda ya nema halak ɗinsa koda za'a kallesa a mai riƙe da sana'a mai ƙasƙanci, amma bai yarda ya ƙasƙantar da kansa ba wajen a bashi ya amsa balle zuciyarsa ta mutu. Insha ALLAHU zai taimaki rayuwarsa.........✍️




_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim Musa

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070



VIP🔥💯

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥




*_ALLAH ya gafartama iyayenku😭🙏_*

No comments