Furar Danko 17
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣7️⃣
........Sai da ta zagesa ciki-ciki da kalmar illiterate sannan ta shiga motar Nadeeya ta rufe da faɗin, “Sai mun haɗu anjima. Dan yau dole ne a warware gajiya Lulu ƙamshinmu ta samu lafiya. Barama na nemo Ɗan-takife ya haɗa mana kayan aiki yau network na gasken-gaske zamu hau”.
Yatsu biyu ta ɗaga mata tana murmushi, shi kuma yaja motar batare da bari ta faɗi abinda tai niyyar faɗa ba. Dama tun a kallo ɗaya da yayma Nadeeya ya fahimci itama tana shaye-shayen. Dan ita har jikinta ma ya fara nuna kansa saboda har taba tana sha. Masifar da batai masaba a farko ita ta fara zazzaga masa yanzu akan dan mi yasa zaija mota bata bashi iznini ba. Ko sau ɗaya bai nuna yasan ma tanai ba balle ya tanka. Hakan kuma na ƙara fusatata da cimata rai akan al'amarin sa, dan a duniya ta tsani tayi ma mutum abu ya mata shiru, amma shi kulatama bayayi balle ya bata haƙuri kamar yanda sauran masu aiki ƙarƙashinsu ke mata. Suna isa gida tun bai gama tsayawa ba ta fice a motar, cikin gargaɗi ta ce, “Sai nayi maganin wannan zafin kan naka baƙauye kawai”.
Da kallo kawai ya ɗan bita, sai kuma ya janye idanunsa yana ambaton auziyya saboda yanda skert ɗin yay mata ɗam illahirin surarta na juya kansu. Bayan ya kashe motar ya ɗan ja kusan mintuna biyu zaune shiru abubuwa da yawa na masa kai kawo, ajiyar zuciya ya sauke a hankali yana mai cigaba da ambaton ALLAH tare da buɗe idanunsa dake lumshe har kalarsu ta canja. Ledar nan daya cire a fruit ɗinta ya ɗauka ya fito a motar, kai tsaye ya nufi wajen su maigadi. Suna cikin gaisawa Nazeer autan gidan ya fito. Sai da ya gaishesu dan sukam Mommy tsaye take akan tarbiyyarsu, bata yarda sun raina kowane ma'aikaci ba a gidan duk da wani lokacin su Hussaina kan so ɗaukar hallayar Lulu suce zasu taka ma'aikatan a bayan idonta. Duk kuma randa ALLAH yasa kunnenta yaji ko idonta yaji bata musu da wasa, shiyyasa ma suke shakkar aikatawar. Cikin ladabi Suhaib daya maida hankalinsa garesa ya ce, “Uncle Smart Aunty Lu ce tace na ɗauka leda a mota. Ta kuma ce wai karkaje ko ina yau har sai idan itace tace”.
Karan farko da al'amarinta ya so fara bashi dariya. Amma sai bai nuna ba ko'a fuska. Miƙewa kawai yay yaje ya Bama yaron ledar data aiko a ɗauka. Wadda ganin bai biyota da ita bane yasa ta fara masifa, da farko ma catai Suhaib ɗin ya kira mata shi, Mommy ce ta hana tace ya amso kayan kawai. Duk rashin mutuncinta tana jin shakkar Mommyn, dan haka ta cema Suhaib ɗin to ya faɗa masa yau kar yabar gidan nan sai da izinin ta. Kai kawai Mommy ta girgiza, a zuciyarta tana tausayin hallayar Mawaddat ɗin, dan tsaurin idonta da izza na bata tsoro. Koba komai ɗiya mace take, komai daɗewa ƙarƙashin ikon wani zata koma. Wanin ma da bata san shi kuma tashi kalar tsagerancin ba.
Koda Suhaib ya kai mata ledar fruit ɗin sama-sama kawai ta cire ta ajiye musu ta shige da sauran ɗakinta. Babu wanda yayi magana sai binta da sukai da kallo kawai. Duk da tana buƙatar wanka hankalinta ba'a can yake ba. Kayan shaye-shayenta kawai take buƙatar ɗan ɗorawa, dan kwana biyun nan da bata sha ba jinta take kamar mara laka a jiki, kuma kamar ana mata susa a brain. Tsaf ta gama zazzage kayan fruit ɗin a ƙasa batare data damu da yanda aka gyara ɗakin ƙal-ƙal ba. Duk da ba wani a cinkushe suke ba haka ta shiga tonawa da mamakin rashin ganin waccan ledar. Da gaske dai babu alamar ledar, dan haka ta miƙe zumbur, bataima kowa magana a falon ba ta fice. Har yanzu yana zaune a wajen su maigadi da sauran masu aikin gidan. Hira suke suna kwasar dariya shiko yana zaune shiru sai waya da yake dannawa, wani lokacin yakan ɗanyi murmushi da hirar tasu musamman idan sun sakosa a ciki. Cikin jan tsaki a zuciyarta ta ce, (Baƙauyen banza sai jin kan tsiya ko ubanwa zaima) dai-dai wajen motar da suka dawo ɗin ta dogare tana faɗin, “Kai!!”. Dukansu juyawa sukai suna kallonta. Shikam ko motsi ma baiyiba balle ya nuna yasan da zuwanta.
Baƙin ciki, takaici kamar zasu kashe Lulu. Cikin takaici da izza tace, “Wai kai banzan nan bada kai nake ba”. Yanzun ma shiru bai ɗago ba. Sai dai mai-wanki ya zunguresa da faɗin, “Aliyu da kaifa take inaga”.
Nan ma shiru yay yaƙi nuna yaji. Dan haka ta nufo wajen a fusace. “Wai kai mika ɗauki kanka? Waye ubanka a ƙasar nan?!!”.
Idanunsa ya ɗan rufe sai kuma ya buɗesu a hankali. Karan farko ya ɗagosu a buɗe gaba ɗaya ya zuba mata su. Wani irin motsawa zuciyarta tayi, dan wani irin kwarjini da shakkarsa ce ta daki ƙirjinta har zuciyarta na sukur-sukur a cikin jiki. Cikin ƙarfin hali ta watsa masa harara da faɗin, “Dalla malam daina kallona da wannan shegunayen idanun naka uwa na macizai”.
Bai janye idanun ba, haka kuma bai tanka mata ba dai, sai ma sake tsatstsareta yay da idanun duk da masifar da hakan ke haifar masa shi kansa. Neman daburcewa take, dan tama kasa cigaba da masifar da ke ta mata tuƙuƙi a zuciya. Fahimtar hakan da yay ya sashi motsa laɓɓansa karo na farko da nufin yin magana. Cikin deep voice ɗin nan tasa dake fita da dakewar da nutsuwar fitar da lafazi ya furta, “Duk macen data cika mace mai suturtawace akan kanta koda ga muharramanta ne, hakan kansa ko bata kira daraja gareta ba, darajar kanzo ta risina mata a gaban wanda ya fita ma balle wanda ke a ƙarƙashin ikonta. Wannan gata da musulunci yayma mace har a lafazinta ana so ta zama mai ƙyautatawa akan harshe”. Yana gama faɗa ya miƙe tare da miƙa ma mai-wanki dake kusa da shi key ɗin motar. “Mu kwana lafiya” ya faɗa cikin miƙa masu hannu ɗaya bayan ɗaya sannan ya nufi hanyar gate batare da ya sake ko kallon inda take tsaye ba.
Babu abinda ta fahimta a kalamansa, sai dai abin mamaki ta kasa koda motsa yatsanta garesa balle maida masa murtani ko yin masifa kamar yanda ta saba har ya fice gidan abin sai kace wani siddabaru.
“Aunty wani abu za'a ɗakko a motar?”.
Mai-wanki ya dawo da ita hayyacinta. Kamar wadda aka farkar a barci a zabure ta ce, “Ubanka zaka ɗakko min wawa kawai” ta juya zata bar wajen. Sai kuma ta dawo ta shiga nuna maigadi da yatsa. “Idan har kabar wancan ɗan iskan ya shigo gidannan a gobe a bakin aikinka kaima. Shima kuma ba ƙyalesa nayi ba, sai naga waye ubansa a garin nan, mi kuma yake taƙama da shi? Dan wlhy sai na wulaƙanta rayuwarsa ta yanda ko sunana yaji sai ya saki fitsari a wandonsa”.
(Ko kuma ke ki saki ba) mai-wanki ya faɗa ƙasa-ƙasa yana danne dariya. A zahiri kam kawunansu a ƙasa babu wanda ya motsa harta isa motar da suka dawo ta buɗe, ko'ina sai da ta leƙa amma babu alamar abinda take nema. Rai ɓace ta nufi komawa dan a zuciyarta ta fara bata *_Ƙwaro_* bai saka mata abubuwan nan bane. Dai-dai tana shigewa motar Uncle Yousuf nayin horn. Da sauri maigadi ya tashi ya buɗe gate ɗin. Fitowar Uncle Yousuf ɗin a motar shi da Smart ya sakasu sakin ajiyar zuciya a tare, a hankali mai-wanki ya saki dariyar da yake ta riƙewa tun ɗazun ganin Uncle Yousuf ya dawo da Uncle Smart ɗin tun ba'aje ko'ina ba. Hakan yasa mai bayin fulawoyi tayasa shima. Sai da sukai mai isarsu sannan mai-wanki ya ce, “Yau fa gamai maganin fitsararriyar nan. Ga kuma Alhaji ƙarami ya dawo da shi tun minti biyar basu cika ba, maga yaya wasan zai kaya. Dan wlhy ya mugun burgeni guy ɗin nan. Ga shi da alama ta tsorata da shi. Ai ban taɓa tunanin anan kusa za'a samu mai maganin masifaffiyar matar nan ba, sai gashi kuwa a cikin waɗanda tafi rainawa da cima zarafi wato mu ma'aikata, dan kawai muna neman guminmu a ƙarƙashin dukiyar gidansu sai take jin mune ƙasar takawarta a duniya”.
Nisawa maigadi dake kaiwa zaune yayi yana sakin wani ɗan murmushin manya. “Ai ni tun randa yaron nan ya fara zuwa nasan ba kanwar lasa bane ba, dan a cikin idanunsa zaka fahimci shima taƙadarin kansa ne”.
“Shine dai-dai da ita ai. Wulaƙancin yarinyar nan wanene bamu gani ba. Sau biyu fa tana marina”. Mai-wanki ya faɗa cikin ƙunar rai alamar har yanzu yana jin raɗaɗin marin a zuciyarsa, sai dai babu yanda zai yi...
Kafaɗarsa mai bayin fulawoyi ya dafa shima cikin ƙunar rai dan ya taɓa shan marin Lulun, “Ai ga mai rama mana nan yazo da ikon ALLAH. Fatanmu dai ALLAH yasa Alhaji Yousuf ya tsaya kan hanata korarsan da tace”.
“Ai insha ALLAHU bazata taɓa samun wannan damar ba ma. Dan randa ta dawo ashe shi aka aika ɗakkota tai masa halin nata yay tahowarsa ya barta acan, kamar dai yau ɗin nan da ya manna mata hauka, amma Alhaji Yousuf ɗin yaje ya dawo da shi aiki matsayin ma drivern ta, kaga ko da ace dane ai tun ranar zata koresa bayan taci masa zarafi kamar yanda takema na baya ko, kuma ya koru ɗin kenan. Nima a wajen Mubeen naji yana labartama yayansu Husain ta waya jiya”.
“Ai Alhaji ƙarami yana birgeni wlhy”. Cewar maigadi. Haka suka cigaba da gulmar Lulu da a gabanta to tari basu iyawa bare satar kallonta..........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenku😭🙏_*
No comments