Recent Updates

Furar Danko 16


 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲





  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗




           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻



𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣6️⃣



.........Wanda yay knocking glass ɗin ya gaisheta cikin girmamawa. Hannu kawai ta ɗaga masa. Bai damuba dan yasan halinta. Cikin yarensu na gayu ya ce, “Mi hajjaju ke buƙata?. Kankana, lemon zaƙi, abarba ko tuffa?”.

     “Wanne gareku a ƙasa”.

   “Duk akwai hajjaju, akwai ma sabon ɗiba daga lambu kuma sabon icce ne nata tsumayenki ko zaki shigo amma shiru”.

         Karan farko hankalinsa ya ɗan fara komawa garesu. Kaɗan ya ƙara sauke gilashin motar yana kallonsu ta mirror. Muska taɗan yamutse da faɗin, “Daga wane garden aka kawoshi?, miye kuma tsaftarsa da ɗanɗanonsa?”.

      “Hajjaju akwai sirri a ɗanɗano kam, gashi ya nuna luguf amma dai zan iya haɗa miki da shi kije kiga samfur”.

     “Okay” kawai ta faɗa da miƙa masa kuɗi masu yawa da zasu iya kai naira dubu hamsin. Da sauri ya juya ita kuma ta buɗe motar ta zauna batare data rufeba ƙafafunta a waje. Shiko Smart cikin hikima ya cigaba da bin saurayin da kallo ta mirror da ya saita har yana iya hango wajen masu fruit ɗin. Yanda saurayin ya ɗanyi diri-diri zuwa ƙasan teburinsa kafin ya ɗago ya fara zuba fruit a ledan hanunsa ya sashi sake maida hankali garesa. Bai wani jimaba ya dawo da leda shaƙe da fruit. Ta ɗayan gefen ya zagaya ya ajiye gefenta, ita kuma ta shiga ta maida motar ta rufe. Ƙin taɗa motar yay har kusan minti ɗaya. Badai tace masa komai ba sai ma ƙoƙarin kai waya take a kunnenta. 

        “Kina shago ne?”.

    Yaji ta faɗa batare da tayi sallama ba. Bai kuma san mi'akace mata da ga can ba ta dai katse wayar. Batare data kallesa ba ta faɗa masa inda zasu a taƙaice. Shima komai baice ba ya harba motar saman titi zuciyarsa na faman kai kawo. Lokaci zuwa lokacin yakan kalla ledar fruit ɗin ta cikin mirror. Sun ɗan samu huldup a hanya dan haka suka ɗan ɓata lokaci kafin suzo. Tun daga waje zaka san wajen saloon ɗin babba ne kuma na manyan mata masuji da manda a gidan sanyi. Ƙin fita tai ita a dole sai ya fito ya buɗe mata. Shiko ya shareta kamar bai fahimta ba. Aiki ta cika tai fam, dama ƙulle take da shi ta fara zazzaga masa masifa har mai saloon ɗin data kasance ƙawarta ta iso. Ita ta buɗe mata cike da murna tana faɗin, “Oyoyo my Lulu ƙamshi gawa taƙi rami” tai maganar tana jawo ganunta dole ta fito suka rungume juna. Suna niyyar barin wajen ta balla masa harara da jan tsaki tana faɗin, “Ka kuma jirani harna gama villager kawai Mtsowww”.

       Idanu ƙawar tata ta wani tsira masa dan sai yanzu ta lura da shi. A hankali ta furta “Woow vary handsome fa, my Lulu Ina kika samo sa?”.

      Harara ta balla mata da jan tsaki ta fisgi hanunta suka bar wajen. Itako sai ƙara waigowa take dan ba ƙaramin tafiya da imaninta Uncle Smart ɗin da tun kallo ɗaya da yay mata ta mirror ya ɗauke kai bai sake ba dan itama dai irin Lulu ɗin ce. Sanye take cikin skert da riga na atamfa sun masifar matsata kamar tai nishi su yage. Ga uban attachment kan yasha da zaro-zaro na farce da gashin idanu kamar ɗiyar aljanu. A dire take kuma ƙyaƙyƙyawace amma hakan baisa yaji ta ishesa kallo ba. Yanda take tafiya da waigensa yasa Lulu cikin takaici faɗin, “Wai ke Deeyah wace irin banzar yarinyace ban san kayan zubar da mutunci fa kema kin sani”.

      “Wayyo my Lulu bazaki ganeba wlhy, Guy ɗin nan yay masifa-masifar haɗuwa dan ALLAH ina kika samosa?”.

     “Mtowww! Ban sani ba banza kawai”.

   Ta faɗa dai-dai suna shigewa cikin shagon saloon ɗin. Tuni yaran Nadeeya suka fara zubewa gaisheta dan sun san halin masifarta. Ko kallo basu isheta ba takai zaune a ɗaya daga kujerun saloon ɗin. Babu kowa a wajen sai Nadeeyar dama da yaran, dan duk randa Lulu zatazo gyara dokar da take sakawa kenan kar a amshi kowa bata buƙatar hayaniya da gwamutsen numfashi. Duk da hakan na tauye Nadeeyar haka take haƙuri tabi yanda take so dan a zauna lafiya. Amma kuma tana biyanta kuɗi sosai da yafi na aikin duk da itama Nadeeyar da ga babban gida ta fito, sai dai ko kama ƙafar kuɗin gidan su Lulu basuyi ba, su Lulun ma zasu iya kallonsu a faƙirai.

       Nadeeya fa ta damu da son sanin wanene. Yayinda Lulu ta mata banza. Batai zuciya ba tama cikin yaranta sginal da ido. Fahimtar abinda take nufi da yarinyar tayi ya sata kaɗa mata kai. Cikin fakar idon Lulu ta ɗauka drinks da ruwa ta fita. Har yanzu yana zaune a motar ko buɗewa bai yiba, sai dai ya sauke gilashin tare da kwantar da kujerar yanda zaiji daɗi.

       Ita kanta yarinyar sai da taji wani iri datai tozali da shi. Dan Uncle Smart ƙyaƙyƙyawan mutum ne kuma nutsatstse ɗan gaye ga masifar tsafta, irin mutanen nan ne masu shegen tsaftar shiya da a wajen wasu suke ɗaukar harma tai yawa, duk da baida kuɗi bai kuma tashi cikin dukiya ba ALLAH ya bashi lafiyayyen fata mai ɗaukar idon mai kallonsa ga kamala da cikar haiba. Rashin yawan walwalarsa da shiru-shiru na zame masa adon kwarjini ga duk wanda zai dubesa ko zama da shi. Cikin ɗan daburcewar harshe ta gaishesa. Hannu kawai ya ɗan ɗaga mata dan tunda yay mata kallo ɗaya ya ɗauke kansa. Cikin ɗan in'ina ta ce, “Dama Aunty tace a kawo maka wannan”.

      Kamar zai share sai kuma yay magana cikin deep voice ɗin nan nashi mai rikita marasa jin magana musamman ƙannensa, mai kuma saka ƴammata da yawa mutuwa a kansa, “Waye aunty?”. Cikin motsa lips ɗinsa a hankali. 

      (Masha ALLAH kaji wani dakakkiyar murya mai ratsa zuciya) ta faɗa a zuciya. A zahiri kam tai saurin faɗin, “Madam ɗinmu ƙawar aunty Lulu ƙamshi, Aunty Nadiy.....”

      “Ba buƙata”.

Ya katseta cikin ɗauke kansa da lumshe idanu yamayi sama da gilashin gaba ɗaya. Tsaye tai sororo kamar kayan ado, sai kuma tabar wajen jiki a sanyaye. A cikin shago har an fara kwance ma Lulu kalbar kanta da wanke mata ƙafafu, yayinda suke hira da Nadeeya ƙasa-ƙasa. Sai dai hankalin Nadeeyar gaba ɗaya na kan ƙofa ne. Da mamaki tabi yarinyarta data dawo da abinda ta fita a hannu. Sai dai batace komai ba gudun kar Lulu ta ganota. Kusan mintuna biyar da barin yarinyar wajen ya buɗe idanunsa. Haka kawai zuciyarsa ke masa kaikawo akan ledar fruit ɗin nan. Duk da wani gefe na kwaɓarsa ya kasa hana kansa dubawa. Ɗakkota yay, ɗaya bayan ɗaya ya fara fidda fruit ɗin da aka loda a sama. Kamar yanda zuciyarsa ke raya masa acan ƙasa wasu abubuwa ne daban, fiddosu yay baki ɗayansu ya maida fruit ɗin ciki tare da ajiye ledar a inda ya ɗauka. Wani irin dokawa ƙirjinsa keyi da sauri-sauri ganin mugayen ƙwayoyin dake a ƙasan, kasancewar shi ba ma'abocin shaye-shayen bane babu abinda ya fahimta a tare da su, sai dai yasan dole ƙwayoyin zasu zama na shaye-shayen ne. Sake naɗesu yay da ƙyau ya adana acan ƙasa inda ƙafafunsa suke, da ga haka ya sake buɗe motar ya fiddo ƙafafunsa dan yasha iska.

        Awani kusan huɗu Lulu ta kwashe a wajen gyaran jikin nan. Dan sai wajen 3 ta fito. Kallo ɗaya da yay mata sai da gabansa ya faɗi, yay saurin ɗaukewa yana jan siririn tsaki. Oho ita bama ta lura da shi ba. Dan yana da ga can gefe a bench na wani mai sai da ƙwa-ƙwa da aya da dabino dake ɗan jikin symbol ɗin shigowa harabar plaza ɗin. Tana da ga tsaye tana hararar motar da tunanin ko yana ciki amma shiru, a fusace ta fara knocking glass ɗin nan ma babu alamar za'a buɗe.

        Ashar ta mulmulo cikin ƙufula da faɗin, “Mi wannan illiterate ɗin ke nufi da nine wai? Barin wajen yay ko mi?”.

        “Kai haba shi ya fara wannan ganganci kamar bai san wacece Lulu ƙamshi ba ne”. Nadiya ta faɗa cikin ƙara fasa mata kai.

     “Ai da alama har yanzu ban sanar da shi ɗin ba. Guy ɗin nan fa mara mutuncine da kike ganinsa. Na barshi ne ban koreshi ba tun a ranar farko saboda sai na gama wulaƙanta rayuwarsa sannan da nuna masa banbancin da ƙasa da sama ke da shi”.

          Cikin ƴar dariya Nadiya ta sake faɗin, “Ai wannan karon drivern naki ne sam bai kama da driver ba wlhy. Irin wannan haɗuwa haka, da gani kuma akwai girman kai fa, koda yake ya kai yayi ne dan ya haɗu ba kary.....”

      “Mtsowww kema shashasha ta biyu da har kika zauna masa kallo haka. Ina wani abin haɗuwa mutum na warin talauci da jahilci. Ƙaton banzar bana zaton (A) kota kai girman garinsu ya sani”.

     Cikin dariya Nadeeya ta ce, “Kai Lulu harda sherinki, wannan ɗan ƙwalisar ne za'ace bai san miye A ba?. Da gani yayi karatu wlhy danni kamar ma na taɓa sanin fuskarsa a cikin ƴan ƙwallon Kano pillars sai dai nasan da wuya ace wancan ne”.

           Tsaki Lulu ta sake ja cikin gatse ta ce, “Sai dai ƴan ƙwallon kwashe gotta ɗin anguwarsu. Dalla malama ni kin isheni”.

      Nadeeya zata sake magana ya iso wajen, dan duk da ba jin mi suke faɗa yake ba da ga inda yake haka kawai zuciyarsa ke raya masa maganarsa suke, maganar kuma da bazata wuce zagi ya sha ba a wajen ƴar balaja'un tsagerar yarinyar nan. Wani banzan kallo Lulu ta watsa masa. Sai dai batace komai ba. Shima ɗin bai nuna yasan tana yi ba ya buɗe mata motar batare daya jira shigarta ba shi ya shige nasa mazauni.........✍️




_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim Musa

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070



VIP🔥💯

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥




*_ALLAH ya gafartama iyayenku😭🙏_*

No comments