Furar Danko 15
........Anyi shagalin biki kam na nunama tsara, dan har a gidan tv na Æ™asa da jiha an nuna. KuÉ—i sunyi kuka abin sai wanda ya gani. Mudai namu ido ni da Yousuf dan ko shagali É—aya bamu halarta ba Isma'il ya hanamu wai baÆ™in ciki muke masa. Amarya ta tare ita da abubuwan ban mamakinta. Dan kuwa dai Mawaddat ta shigo gidan ne a tsaitsaye da tarin gadararta irin na É—iyan wasu masu arziÆ™in. Dan sai da takai hatta kwanakin girkina wani lokacin Mawaddat cemin take wai ta saya tazo ta diremin kuÉ—i a gaban Isma'il baya cewa komai kuma. Akwai lokacin da sai da nai wata guda babu miji, dan kuÉ—i maÆ™udai tazo ta diremin wai ta sayi kwanakin girkina na wata É—aya dan tana buÆ™atar hutawa da mijinta yanda ya kamata. Nayi kuka nayi kuka har na rasa hawayen zubarwa a wannan lokaci, sai Yousuf ne ke lallashina shima idan ya koma gefe yasha kukansa dan yanzu tsakaninsa da É—an uwansa da ga faÉ—a sai Æ™yara. Wannan damuwar tasa yana kammala sakandare da Mawaddat tace ta samar masa gurbin karatu a Æ™asar Æ™etare bai wani ja zancen ba ya amince ya tafi dan gara ya bar musu gidan. Tafiyar Yousuf ta sake sakani a cikin Æ™uncin rayuwa dan abubuwa sun sake rikicewa sosai tsakanina da Isma'il. Takai yanzu sai dai su shirya su tafi yawon shakatawarsu Æ™asashe daban-daban su huta sannan su dawo. ÆŠan fita aikin da nakeyi ne yake É—an ragemun nauyin zuciya, amma sai rana tsaka Isma'il ya hanani fita aiki wai ya dakatar dani. Ban taÉ“a shiga damuwa ba irin wannan lokacin, dan takai ko kuka ma na daina iya yi sai na zuci kawai. Dole kuma nabar aikin na cigaba da fuskantar matsalolin gidan masu Æ™ona zuciya. Ashe wasa farin girki, dan kuwa ba'ai komai ba sai da ciki ya bayyana a jikin Mawaddat, naga abu iri-iri wasu ma bazasu faÉ—u ba. A haka na cigaba da haÆ™uri sai dai na rungumi É—iyana nai kuka na share hawaye har ALLAH ya kai wannan ciki watan haihuwa lafiya suka fara shirin tafiya Æ™asar waje wai haihuwa. Sai dai kuma suna nasu ne ALLAH yana nashi, dan suna saura kwana biyu su wuce Mawaddat ta tashi da naÆ™uda, ga shi lokacin Isma'il ya fita gidan. Naso shareta dan ihun kuka sosai ta dingayi har part É—ina ina jinta, sai dai kuma na kasa saboda hakkin maÆ™waftaka da daraja irin ta É—an adam. Karan farko dana shiga sashenta, haÉ—uwa kam ya haÉ—u iya haÉ—uwa, dan ma ban iya masa kallon tsaf ba saboda halin da take ciki. Ni É—in dai maÆ™iyyarta ni na taimaketa, ganin yanda take murÆ™ususun kuka da ihun naÆ™uda gashi inata kiran Isma'il yaÆ™i ya É—agamin ya sani samo ruwa nai mata addu'a a ciki, ina Æ™oÆ™arin bata dai-dai nan ya shigo gidan, da wata irin sassarfa yay kammu, babu wani tunani ko bin ba'asi yasa hannu ya kaÉ“e ruwan, sai dai harta rigada tasha. Sosai ya balbaleni da masifa yana tabbatar min da duk abinda ya samu matarsa bazai barni ba. Kuka na fashe da shi ina masa bayani amma bai sauraren ba ya É—auketa sukai asibiti tana kukan faÉ—in na yafe mata dan ALLAH. Tausayi ta bani, dan haka na bisu har harabar gidan ina faÉ—in, “Na yafe miki Mawaddat, ALLAH ya saukeki lafiya, nima ki yafemin”. Da Æ™yar ta iya furta “baki mun komaiba sai alheri” dai-dai yana sakata a motar. Dazai barni dana bisu, amma rashin ganin fuska da ga garesa ya sani haÆ™ura na bisu da addu'a zuciyata duk babu daÉ—i, ga jikina yay matuÆ™ar sanyi da ganin yanayin nata.
Kafin su isa asibiti ta haihu a mota dan haihuwar tarigada tazo, gaba ɗaya ya rikice yama rasa miya kamata yayi, ga holdup da suka samu a hanya da ƙyar suka fita, kafin su isa asibiti Mawaddat ta zubda jini sosai har jikinta ya saki. Ko taɓata likitocin basu kai dayi ba UBANGIJI ya amshi abarsa, sai jaririya da aka samu gyarawa. Bayyana muku irin tashin hankalin da Isma'il ya shiga da wanda na fuskanta a garesa ma ɓata lokaci ne. Dan duk da bayanin da likitoci sukai masa akan dalilin rasa ranta cayay sam bai yardaba nice na kasheta, dan ya samu ina bata abu. Wasa-wasa rigima tai girman da har sai da hukuma suka shiga ciki, ALLAH ya soni mahaifinta mutum ne da yasan abinda ya kamata, shine ya balbale Isma'il ɗin da masifa tare da bani kariya har ALLAH yasa zancen ya mutu. Sai dai fa Isma'il ya koma mana kamar wani zautacce, jaririya kuwa tana manne da shi ya hana kowa ɗaukarta har iyayen Mawaddat. Duk kuma yanda sukai masa kurari da jan ido bai basu ɗin ba dole suka barshi da kayarsa. Randa akai addu'ar bakwai mahaifin Mawaddat Alhaji Sufi Garko ya raɗama yarinya sunan mahaifiyarta Mawaddat. A taƙaice dai Isma'il shine ya koma rainon Mawaddat da hanunsa, yayinda soyayyar mahaifiyarta kacokan ta koma kanta, tare da tausayinta. Komai shine kema yarinyar, a saboda ita ya ajiye aikinsa ya koma rainonta. Ko motsi idan tana barci babu wanda ya isa yayi. Idan kuma akayi kosu ƴan biyu ne ya kamasu yay musu dukan mutuwa. Nasha shan mari a wajensa saboda Mawaddat. A haka yarinyar ta taso a taɓare babu kwaɓa komai sai wanda take so za'ayi. Lokacin data isa shiga makaranta ya sakata a mafi tsada dake cikin garin na Kano, Islamiyya ce dai dole ya barta atasu ƴan biyu saboda tsayawar Yousuf da ya kammala karatunsa ya dawo, sai dai bai yarda ba sai da ya kafama malaman sharaɗi akanta. Sabbin matsaloli sun fara akan zuwan Mawaddat Islamiyya, dan bata karatun sai jibgar ƴaƴan jama'a, idan malami yay mata faɗa koya daketa koda akan karatu ne saita faɗama mahaifinsu, shiko ba kunya zai ɗebo ƴan sanda su kama malamin su rufe, wani lokacin ma har marin malaman yake da kansa. Yousuf ne da ya fahimci al'amarin na neman zama wani abu daban ya fara tsayawa akan tarbiyyar Mawaddat, dan ni ko kallon yarinyar na cikayi yanzu zaice itama ina son kashetane kamar uwarta. Dole duk yanda nake kwaɗayin janta jikina kodan maraicin mahaifiyarta da bata sani ba na haƙura na zuba ido dan a zauna lafiya. Dai-daita rayuwar yarinyar da Yousuf ke son yi ce yasa Isma'il ganin ɗan uwan nasa na takura mata. Dan haka ya tattarata ya ɗauke bayan gama Nursery school ɗinta ya maida ƙasar Garmany da zama. Ya ɗauka mata Nanny acan ƙasar aka sakata makaranta. Shima dai wasu harkokin kasuwanci da mahaifin Mawaddat ya sake ɗirasa akai ne yasa zamansa yafi ƙarfi a Garmany ɗin, ga kuma ƴar sonsa da ya maida can. Tafiyar Mawaddat babu jimawa na sake haihuwar yarona Namiji da yaci sunan Mubeen, bayan shi na sake ƴan biyu duk mata da gabonsu Suhaib sai auta Nazeer. Tunda aka ɗauke Mawaddat daga Nigeria bamu sake ganinta ba sai Yousuf dake zuwa akai-akai ganinta, dan shima Isma'il ya tsindumasa akan harkar kasuwancin kawo motocin da yake kanyi a yanzu, duk da dai kuma yana aikinsa anan ƙasar Nigeria saboda shine hubby nasa. Rayuwa ta shuɗa Isma'il ya sake bunƙasa haka ma Yousuf da yay aurensa, ya auri yarinyar kirki mai tarbiyya da sanin yakamata Saliha ɗiyar maƙwafcin nan namu da ya jagoranci bikina da Isma'il. Dan muna zaune lafiya kuma tana matuƙar girmamani. Mawaddat dai bata dawo ba, ko hutu bata taɓa zuwa ba har sai da ta kammala sakandare ɗinta a can sannan tazo mana. A halayen banzanta babu abinda ya canja sai ma ƙaruwa da yayi, dan yarinyar gaba ɗaya a fanɗare take babu wanda ya isa ya sakata ko ya hanata. Ko kallon banza kamata sai ta maida maka murtani, Yousuf ne kawai ke iya tsawatar mata ta nutsu. Hankalina ya tashi matuƙa, dan koba komai Mawaddat ɗiyar Isma'il ce, ita ɗin jininace ai koba aure tsakanina da shi. Dan haka na duƙufa da addu'a akanta kamar yanda nakema nawa yaran. Tawani ɓangaren kuma ina ɗan janta a jikina cikin hikima sai dai ban bata wata ƙofar da zata kawomin raini ba ko kaɗan. Kusan watanta shidda ta sake barin ƙasar zuwa London karatun ta na University, daga haka bata sake zuwa ba sai da ta kammala ta zama cikakkiyar lawyer. Da ƙyar daya ALLAHU Yousuf ya tilastata dawowa gida Nigeria, amma shi Daddynsu ko'a jikinsa. Dawowar tata kuma baisa abubuwa sun canja a yanda suke ba kanta a can baya tsakanina da Isma'il, dan ƙiri-ƙiri yake nuna bambanci tsakanin yarana da Mawaddat, idan nai magana yace arziƙin uwarta da Kakanta muke ci, dole na tattara na watsar da al'amarinsu, dan dama da ƙyar ya biyama su ƴan biyu kuɗin karatu zuwa Saudiyya, a yanzu haka kuma sun dawo suna aikinsu sai dai ba'a nan cikin Kano ba, shiyyasa sai Lokaci-lokaci suke zuwa mana weekend. Mubeen ne kawai tare damu sai ƴanmatana da da Suhaib da auta.....
Wannan kenan.
∆••••∆ ★∆••••∆
A É“angaren su Uncle Smart da Lulu Æ™amshi sun bar anguwar gaba É—aya amma taÆ™i ta faÉ—a masa inda suka nufa. Shi kuma ya shareta ya cigaba da tafiyarsa a nutse. Yanda yake juya steering motar a nutse ya sata É—an tsira masa ido a kaikaice. Sai dai ga duk wanda zai iya kallonta zai É—auka hankalinta nakan tab É—inta ne. Kamar wadda ta tuna wani abu kuma sai ta yamutse fuska da jan siririn tsaki ta maida hankalinta ga tab É—in. Sunyi nisa sosai da anguwar dai-dai wasu gungun masu sai da kayan fruit ta ce, “Malam dakata min”.
Yanda tai maganar a gadarance ya sashi ɗan cizar lips ɗinsa. Ƙoƙarin wucewa yake ta sake maimaitawa cikin daka tsawa. Ƙin tsayawa yay sai da ya gota sosai ya gangara gefen titin ya kashe motar. Jitai wani irin tuƙuƙin baƙin ciki ya turniƙe mata zuciya har ta kasa yin magana ma. Sai huci take lips ɗinta na motsi amma ta kasa furta komai. Shiko ko'a kwalar rigarsa wayama ya ɗauka yana dannawa batare da ko kallonta sau ɗaya yayi ba.
“Amma kai babban illiterate ne!!”.
Ta faÉ—a cikin matsanancin É“acin rai. Idan motar ta motsa to shima ya motsa ballema ya nuna mata yasan da shi take. Zata sake magana akai knocking glass É—in motar, nan É—in ma bai motsa ba, bai kuma sauke gilashin ba sai itace ta buÉ—e motar ta fita zuciyarta na mata wani irin tuÆ™uÆ™i, ji take bata taÉ“a tsanar wani mutum a duniya ba kamar wannan guy É—in, dolene ma ta É—auki mummunan mataki a kansa ta yanda ko Æ™arar takalminta da warwarayen hanunta yaji sai hanjin cikinsa sun kaÉ—u.........✍️
No comments