Recent Updates

Furar Danko 14


 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲





  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗




           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻



𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣4️⃣




______________________________

*_Wai wai wai_*

       _wani kaya sai amale,don raqumi bazai iya dauka ba_


*MAAB LUXURY* _GIDAN ADO DA KECE RAINI_


*MAAB LUXURY* _DUNIYAR QAWATATTUN KAYAYYAKI_


*MAAB LUXURY* _TUNQAHON GIDA DA GININ GIDAN GABA DAYA_


_IDAN NACE ZAN LISSAFO BAZAN GAMA BA A NAN KUSA,DON SUN CANCANCI KOWANNE IRIN SUNA_


*DAME DAME SUKE SIYARWA NE?*👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽


_SUN KAWO MUKU DALLADALLAN KAYAYYAKIN GIDAH NA KAWATARWA DANA KITCHEN MASU HASKA DAKUNAN GIRKI… KWASHA KWASHA_


_SU DIN KARSHE NE A DUNIYAR KAYAYYAKIN GIDAH DANA KITCHEN NA KECE RAI NI… INA UWAYEN GIDAH, AMARE? ANTOCI, KAWUNNI, YAYYU MAZA, KANNE DA MA IYAYEN MU MAZA?_


_KU ZO A DAMA DA KU A WANNAN DAMAR ME DAUKE DA DIMBIN KAYAYYAKI MASU KYAU A KUDI DEDE MISALI WANDA KOWANE ZAI IYA MALLAKA IYA KARFIN SA_


_KU ZIYARCI SHAGON DA KE A KANO.. TITIN AHMADU BELLO WAY_


_KO KUYI ORDER DA GA SHAFUKAN SADARWA TA INSTAGRAM: @Maabluxuryhome_

_FACEBOOK:@maabluxuryhome_


  _SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDAH,, INGANCI DA RAHUSA, KYAU A DADE ANA AMFANI DA SU SAI KAYAYYAKIN MAAB LUXURY HOME_


 _A NUMBER ONE  STOP SHOP FOR HEAVENLY ORIGINAL HOME DECORS AND KITCHEN UTENSILS_


_MAAB LUXURY HOME GOT YOUR HOME AND YOUR KITCHENS COVERED… JUST A VISIT/CALL/DM AWAY_


   _08034631010 MAAB LUXURY HOME👈🏽_

______________________




........Wannan haɗin kan nasu da ƙaunar juna ya ɗan dinga ragema Malam Ibrahim raɗaɗin ciwo, dan duk da yana kwance a duk sanda suke tattalin Yousuf a tare kamar wasu mata da miji duk da ƙarancin shekarunsu sai yaji farin ciki har fuskarsa kan nuna hakan. Gashi shima suna kulawa da shi matuƙa sai kace wasu manya. Yana da shekara biyar kwance ya yanke shawarar ɗaura musu aure saboda halin rayuwa, a lokacin shekarar Isma'il goma sha tara a duniya. Itako nada goma sha huɗu. Maƙwafcinsu ne ya jagoranci komai, ranar wata juma'a sun dawo makaranta Isma'il ya gama jarabawar ƙarshe ta kammala sakandire, ita kuma jsce suka iske an ɗaura musu aure. Ita bata wani ɗauki abin da muhimmanci ba, kasancewar da sauran ƙuruciya a tare da ita. Sai ma biyema Yousuf dake da shekara biyar a duniya tai suna murnarsu. Yayinda Isma'il ya shiga yanayin damuwa, dan shi harga ALLAH kallon ƙanwa yake mata uwa ɗaya uba ɗaya bawai matar dazai iya aure ba. Lura da hakan da Malam Ibrahim yayi ne ya sashi zaunar da shi yay masa nasiha mai ratsa jiki data saka jikinsa yin sanyi, tun kuma da ga wannan lokacin ya fara koyama kansa sonta ita Kareema (Mommy) tunda dama akwai ƙauna ta jini da shaƙuwar zaman waje ɗaya a tsakaninmu. Karatu muka cigaba da yi abinmu batare da anyi maganar tarewa ba, haka shima Yousuf an sakashi makaranta, gefe kuma muna cigaba da jiyyar babanmu malam Ibrahim. Isma'il na shekara ta uku a jami'a, ni kuma shekarar ƙarshe a sakandire jikin Baba ya sake rikicewa, ganin haka yasa maƙwafcinmu da muka zama tamkar ƴan uwan jini a yanzu shirya bikinmu ni da Isma'il dan yana fatan gani kafin yabar duniya. Haka ɗin kuwa akayi, aka gyara gidan tare da kawo abubuwan da suka dace da amarya sati ɗaya da kammala jarabawata ta ƙarshe akasha biki. Anan dai gidan muka tare, inda kwanaki goma sha ɗaya da tarewar tamu ALLAH yayma Baba rasuwa shima. Mun shiga ruɗani da tashin hankali matuƙa irin wanda bazai misalu ba. Dan da ƙyar al'amura suka daidaita mana bayan wani lokaci. Mun cigaba da rayuwa cikin shaƙuwa da soyayya mai ban mamaki, ga ɗan ƙaninmu Yousuf da muke tattali matuƙa, inda wanda bai sani ba zai iya ɗaukama ɗan mu ne sai idan ka kalleni ne zaka san ban kai haihuwarsa ba. Alhamdullah Isma'il ya kammala jami'a bayan rasuwar Baba da shekara biyu, ya kuma samu result mai ƙyau. Haka shima Yousuf ya shiga fimare 4. Burina a kullum shine na koma makaranta na cigaba da karatu nima, sai dai Isma'il na lallaɓani akan na bari ya samu aiki abubuwa su sake warware masa. Banyi musu ba nayi haƙurin, cikin ikon ALLAH kuwa sai ga aiki ya samu cikin sauƙi kasancewar a wancan lokacin ma neman masu irin kwalinsa ake ido rufe suna yanga dan aiki saima sun zaɓa. Wannan samuwar aiki shine mafarin komai, dan daga lokacin abubuwa suka fara canja salo a saɓanin yanda nake kallonsu ko na tashi na sansu.

         *_Alhaji Sufi Ado Garko_* shine ya kasance ogan Isma'il a wajen aiki, mutum ne mai tarin dukiya da mutunci. Bashi da mugunta da ƙeta, dan ba aikin gwamnati kawai ya dogara da shi ba ɗan kasuwane babba da akeji da shi sosai a lokacin. Ƙwazo da amanar Isma'il ta fara janyo masa soyayya a wajen Alhaji Sufi ya fara jansa a jikinsa tare da ɗorashi akan wasu harkokinsa na kasuwanci a bayan fagen aikinsu na gwamnati. Alhamdullah wannan al'amari ya fara canja mana rayuwa, dan kuɗi sun fara shigowa Isma'il fiye da farkon samun aikinsa. Inda ya cika alƙawarin maidani makaranta, shima Yousuf ya shiga Sakandire. Shekarata ɗaya da komawa makaranta sai ga ciki. Isma'il da Yousuf da ni ɗin kaina mun shiga matuƙar farin ciki da baida misali. Na haihu lafiya bayan ciki yakai haihuwa, inda ALLAH ya bani ɗa Namiji wanda yaci suna Ibrahim muna kiransa da Abba. Na cigaba da rainon Abba koma nace Yousuf ya cigaba da rainonsa, dan tattalin yaron yake tamkar ƙwai a cokali. Sai dai ALLAH baiyi mai zama bane yanada shekara ɗaya da wata uku ya rasu. Yousuf ya sha kuka sai mune muka koma lallashinsa. Sai dai me ashe a lokacin ma ina maƙale ne da ciki batare da mun sani ba. Sai bayan rasuwar Abba ne ya bayyana. Munyi murnar hakan na cigaba da rainon ciki da karatu, yayinda ALLAH keta ƙara ɗaukaka Isma'il ta silar Alhaji Sufi Garko. Bayan isar cikin jikina haihuwa shima na haifesa, sai dai wannan karon ƴan biyu ne duk maza. Wayyo murna zo kaga farin ciki a wajen Yousuf da Isma'il dama ni kaina. Yara sun sake cin sunan Ibrahim da Salisu iyayenmu. Ana kiransu da Hassan da Hussaini ɗinsu. Bayan haihuwar ƴan biyu da shekara biyu na kammala karatuna, sai dai Isma'il yace bazanyi aiki ba sai da naita roƙonsa ni da Yousuf harda kukanmu sannan ya amince. Shine ya amshi takarduna da kansa domin nemamin aiki kamar yanda ya sanar min mai-gidansa Alhaji Sufi Garko yace ya kawo zai sama min gurbin a kamfaninsa insha ALLAHU. Kasancewar yace ya kai masa takardun gida a cikin weekend ya sakashi shiryawa ranar wata asabar. Wannan shine karo na farko a rayuwarsa da zai je gidan ogan nasa. Tare da Yousuf suka tafi, inda akai musu tarba ta mutuntawa, gidane katafaren gaske da ya basu mamaki, dan a ranar suka sake tabbatar da lallai Alhaji Sufi Garko mai kuɗi ne sosai. Suna zaune a falon Alhaji Sufi da aka saukesu saboda karamci saɓanin falon baƙi ƴarsa ƙyaƙyƙyawar budurwa data dawo daga karatu da ga ƙasar larabawa ta shigo falon amsar saƙo wajen mahaifinta. Tunda ta ɗora ido akan Isma'il ta kasa ɗaukewa, dan Isma'il ƙyaƙyƙyawan mutum ne ɗan gaye sosai, ina faɗa muku zancen gaskiya ne badan yana mijina ba. Ba Isma'il kawai ba hatta Alhaji Sufi ya lura da irin kallon da ƴar tasa kema yaronsa na ƙurilla. Yayinda Yousuf shi kuma abin ya bashi haushi saboda kishina ni ƴar uwarsa. Wasa-wasa Muwaddat ta kasa barin falon tana manne da su har suka bar gidan duk da bayan gaisuwar shi Isma'il bai sake kulata ba ma. Aiki dai an ɗaukeni ta silar Alhaji Sufi, sai dai tunda Yousuf ya bani labarin ƴarsa da abinda ya faru naji komai ya fitamin arai. Ban dai yima Isma'il maganar ba, amma kullum cikin kasa kunne nake naji abinda zai biyo baya. Shiru-shiru banji komai ba har na shiga wata shida da fara aiki ga kuma ciki ya sake samuwa. Abinda ya bani mamaki a wannan karon Isma'il bai wani nuna murnarsa sosai akan cikin ba kamar nasu ƴan biyu da Abba. Sai dai banyi magana ba. Bayan haka al'amuransa da yawa sun ɗan fara canjawa a yanda na sansu. Zai fita aiki da sassafe batare daya karyaba yanzu, bai dawowa kuma sai goma na dare. Wani lokacin ya tsakuri abinci, wataran ma baya ci sai yace min ya ƙoshi a gajiye yake. Tun bana ɗaukar al'amarin wani abu har ya fara damuna naima Yousuf maganar. Shima da yake yaro ne mai hankali da lura ashe ya fahimta yay shirune kawai. Kuɗi na sake shigoma Isma'il abubuwa na ƙara rikicewa a tsakaninmu da ban san kansu ba, dan haka Yousuf dake ƙoƙarin kammala sakandire ya lallasheni akan zai bincika. Yaron nan shine yay ƙoƙarin binciko mana komai, inda ya gano ashe Isma'il soyayya suke da Muwaddat ta bugawa a jarida, saboda shi ma yanzu haka ta koma aiki ma'aikatarsu. Hankalina ya tashi da gani har Yousuf, inda duk yanda naso danne abun a raina na kasa Isma'il na dawowa na taresa da maganar. Da farko naga shock a fuskarsa, amma da yake halin maza sai ya dake ya shiga borin kunya akan wane munafuki ne yay masa sharrin nan. Ƙin faɗa masa nayi, amma duk da haka yace yasan Yousuf ne. A daren ya tado Yousuf da ga ɗakinsa ya zagesa tas. Hakan da yay ya sake ɓata min rai muka kwasa da shi sosai abinda bai taɓa faruwa ba har ya kaisa ga marina, ya kuma tabbatar min nama shirya aure shi da Muwaddat babu fashi sai dai mu mutu ni da Yousuf ɗin. Kamar yanda ya faɗa kuwa ya cika, dan baifi sati biyu dayin rigimar tamu ba aka tsaida bikinsu shi da Muwaddat. Wannan tashin hankalin dana sakama kaina saboda yanda ya sake birkicemana a gidan ni da yaran da Yousuf yasa cikin jikina ya ɓare. Bai nuna ya damu ba ya cigaba da shirye-shirye aurensa. Inda Alhaji Sufi Garko ya ce ƴarsa fa tace bazata zauna a gidan da muke ba. Dan haka ya bashi mukullin ƙaton gida da dalleliyar motar hawa, nima mota da kayan faɗar kishiya kai kace ma nice amaryar kuma wai da ga gidan iyayenta. Shima Yousuf da ƴan biyu da nasu hidimar. Wannan abu ya sake ɗagamun hankali dan a ganina Isma'il dai auren jari ma yake shirin yi. Taruwa mukai muka tada masa hankali ni da Yousuf amma yace ko zamu mutu auren Muwaddat babu fashi wlhy. Hakan kuwa akayi, dan wata ɗaya kacal da komawarmu sabon gidan da ya zama dole garemu akai bikinsa shi da Muwaddat........✍️


      

     *_Karku rikice wannan Mawaddat ɗin mahaifiyar Lulu ƙamshi ce ba Lulun muke nufi ba😂_*

         


_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim Musa

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070



VIP🔥💯

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥




*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

No comments