Recent Updates

Furar Danko 13


 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲





  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗




           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻



𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣3️⃣



______________________________

*_Wai wai wai_*

       _wani kaya sai amale,don raqumi bazai iya dauka ba_


*MAAB LUXURY* _GIDAN ADO DA KECE RAINI_


*MAAB LUXURY* _DUNIYAR QAWATATTUN KAYAYYAKI_


*MAAB LUXURY* _TUNQAHON GIDA DA GININ GIDAN GABA DAYA_


_IDAN NACE ZAN LISSAFO BAZAN GAMA BA A NAN KUSA,DON SUN CANCANCI KOWANNE IRIN SUNA_


*DAME DAME SUKE SIYARWA NE?*👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽


_SUN KAWO MUKU DALLADALLAN KAYAYYAKIN GIDAH NA KAWATARWA DANA KITCHEN MASU HASKA DAKUNAN GIRKI… KWASHA KWASHA_


_SU DIN KARSHE NE A DUNIYAR KAYAYYAKIN GIDAH DANA KITCHEN NA KECE RAI NI… INA UWAYEN GIDAH, AMARE? ANTOCI, KAWUNNI, YAYYU MAZA, KANNE DA MA IYAYEN MU MAZA?_


_KU ZO A DAMA DA KU A WANNAN DAMAR ME DAUKE DA DIMBIN KAYAYYAKI MASU KYAU A KUDI DEDE MISALI WANDA KOWANE ZAI IYA MALLAKA IYA KARFIN SA_


_KU ZIYARCI SHAGON DA KE A KANO.. TITIN AHMADU BELLO WAY_


_KO KUYI ORDER DA GA SHAFUKAN SADARWA TA INSTAGRAM: @Maabluxuryhome_

_FACEBOOK:@maabluxuryhome_


  _SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDAH,, INGANCI DA RAHUSA, KYAU A DADE ANA AMFANI DA SU SAI KAYAYYAKIN MAAB LUXURY HOME_


 _A NUMBER ONE  STOP SHOP FOR HEAVENLY ORIGINAL HOME DECORS AND KITCHEN UTENSILS_


_MAAB LUXURY HOME GOT YOUR HOME AND YOUR KITCHENS COVERED… JUST A VISIT/CALL/DM AWAY_


   _08034631010 MAAB LUXURY HOME👈🏽_

_______________________




........Washe gari da ranakun da suka biyo baya babu wani ƙwaƙwƙwaran aiki da yayi kasancewar wadda aka ɗaukesa aikin a yanzu da ita bata fita. Sai dai yaje ya zauna wajen masu gadi har lokacin tashi yayi ya koma gida. Ganin hakan yasa yau bai fita da wuri ba yabi su Maryam makaranta kamar yanda yakan yi lakaci zuwa lokaci batare da sun sani ba. Yakan ɗan binciki halin da suke ciki da yanayin karatunsu. Sai goma yabar makarantar. Lokacin da ya iso gidan aikin nasa sha ɗaya saura kaɗan. Tunda ya turo gate ɗin ya shiga akanta ya fara sauke idanunsa. Tsaye take a can jikin wata farar mota da ke ƙaton compound ɗin nasu. Kallo ɗaya da yay mata bai sake marmarin ƙarawa ba saboda shegun kayan da ke jikinta. Skert ne blue da ya kamata ɗam-ɗam ya fidda mata halittar jikinta da ƙyau, sai ƴar riga mai santsi kalar gwaiduwar ƙwai. Babu ko ɗigon kwalliya a fuskarta sai wani ƙaton glasses data toshe idanunta da shi, kanta da hula irin ta zamani da ake yayi. Dan ƙyau kam tayi ƙyau, sai dai ga ɗabi'a da tarbiyyar ɗiyan musulmi bahaushen arewacin Najeriya babu abinda shigar tata ke nufi ga duk wanda zai kalleta sai ƙarancin tarbiyya da wayewar banza. Ga wayayyu kuma irinta hakan normal ne.

     Tsaki ya ɗan ja a ƙasan maƙoshi yana ƙara tsuke fuska. Su maigadi dake zaune kamar a tsorace duk ya bama hannu suka gaisa. Yanda suke kamar a noƙe ya bashi mamaki. Sai dai yana niyyar kaiwa zaune mai wanki ke faɗin, “Ɗan uwa Hajiya Muwaddat fa kai take jira. Tsaiwar da kaga tayi can tun ɗazun take zuba tijara har mu ma nan sai da muka samu rabonmu na zagi, kasan ita sanda aka raba mutunci tana cikin bargo ƙudindine shiyyasa bata samu ba”.

        Shiru kamar bazai amsa ba. Sai kuma zuwa can a dake ya ce, “Tunda kun maida kanku sakarkaru gareta ba”. Da ga haka yaja bakinsa ya tsuke tare da ciro wayarsa da ga aljihu zai fara sana'ar danne-dannen nasa. Wata irin gigitacciyar tsawa Lulu data gama kaiwa wuya da takaicinsa ta daka masa. Sai dai ko gezau wai an tsikari kakkausa. Cikin takun nan nata na izza da yanga ta ƙaraso gate ɗin. Ashariya ta mulmulo tare da faɗin, “Wai kai ɗan uban wanene? Mi kake taƙama da shi ne, tsabar kai cikakken mara mutunci ne kazo a makare ina tsaye tun 8:30 ina jiranka amma kazo ka zauna anan irin ma kai baka gannin nan ba. Na rasa mi Daddy da Uncle Yousuf suka gani gareka suka takura da sai kai ne zaka zama driver na a gidan nan illiterate irinka..”

      A hankali ya rumtse idanunsa sai kuma ya buɗesu a kanta. Wani irin yankawa zuciyarta ta shigayi da sauri-sauri, dan wani irin kwarjini mai cika idanu yay mata. Amma saboda tsabar ƙarfin halinta da taurin zuciya sai ta cigaba da masifar kamar zata cinyesa ɗanye. Harda cewa sai tayi maganin rawar kansa a gidan. Sosai su maigadi ke'a rikice. Shiko yanda ya dake sai ma ka ɗauka ba dashi takeyi ba. Dan tuni ya maida hankalinsa ga wayarsa...

       “Wai ya akayi ne?”.

   Mommy da hayaniyar Lulu ke zuwa mata cikin kunne sama-sama tun ɗazun ta fito dan ganema idonta ta faɗa tana ƙarasowa. Cikin masifar nan tata ta juya tana faɗama Mommyn abinda yay mata. Dai-dai nan shima Daddy ya fito da alama ma wanka ya fito dan bathrobe ce a jikinsa. Mommy ta juya ga Uncle Smart, sai dai kafin tace masa komai ya shiga gaidasu ita da Daddyn da sai yanzu Mommy da Mawaddat suka lura da shi cike da girmamawa kamar bashine ya watsar da al'amarin Lulu ba tun ɗazun. Cikin kulawa suka amsa masa, Daddy ya dubesa cikin alamar sanyin yanayin daya riskesa a kwanaki biyun nan akan halin da Lulu ke ciki tare da faɗin, “Ya akai ka makara haka Aliyu Hydar?”.

        Bai iya ƙarya ba ko kwana-kwana. Sak yake shi akan komai. Dan haka kai tsaye ya ce, “Alhaji na ɗan biya ta school ɗin ƙannena ne dan sanin halin da suke ciki akan karatunsu tunda naga kwana biyu ba wani waje nake zuwa ba”.

      Lulu zatai magana a hargitse Daddy ya katseta cikin lallashi. “To kiyi haƙuri haka tunda dai kinji uzirinsa ai ko Babyna. Kuje ya kaiki haka nan rana na ƙarayi wannan gyaran jikin naki dake ɗaukar lokaci kamar za'a sauyaki”.

     Takaici kamar ya kashe Mommy da ke kallon mijin nata. Sai dai batace komai ba.

        Lulu dake wani cika da batsewa ta ce, “Amma Daddy kana ganin kofa haƙuri bai bani ba. Tsabar wulaƙanci kallo ma ban ishesa ba balle gaisuwa sai da Mommy ta fito ma ya taso da ga inda yake zaune tsabar shi mashahurin mara mutunci ne”.

      “Oh oh”.

Daddy ya faɗa yana dafe kansa. Sai kuma ya dubesa da faɗin, “Kaga dan ALLAH bata haƙurin nan a rabu lafiya kaji Aliyu”.

     A harzuƙe ta ce, “Bana buƙatar haƙurin nasa Dady, sai da aka roƙa min. Ka barsa zanyi maganinsa tare da sauke masa girman kansa, banza mutum ba kowan kowa ba sai ɗaukar kai wata tsiya kana driver. Shiyyasa na tsani irin jahilan nan da ko primary basu yi ba sai ji da kai motsoww!!”.

         Maganganun ta sun masa zafi, amma sai ya miƙe kodan darajar Daddy da Mommy. Key ɗin jikinsa ya ciro yana nufar motar. Tsawa tai masa tare da wurga masa wani key ɗin. “Ba ita nake so ba stupid Men! illiterate kawai”.

    Key ɗin data jefa masan yabi da kallo na kusan minti ɗaya, kafin ya ɗago ya ɗan kalleta sai kuma ya ɗauke kansa yana mai cije lips ɗin sa ya ɗauka batare da yace komai ba nan ma. Daddy ya ɗan girgiza kansa da faɗin “ALLAH ya shiryeki Muwaddatan-warahamah. Koda ya gyara motar zuwa gabanta ƙin shiga tayi. Daddy da ke tsaye zaman jiran ganin sun fita lafiya yay masa nunin ya fito ya buɗe mata. Bai musa ba ya fito fuskarsa na karayin wani kicin-kicin. Batare daya kalleta ba ya buɗe mata ƙofar. Sai da taja tsaki da faɗin, “Motsoww! baƙauye kawai da ko aikinsa bai sani ba” sannan ta shiga. Maidawa yay ya rufe suka fice a gidan. Karan farko Mommy ta saki murmushi, dan tabbas tasan a wannan haɗin akwai ƙura. Lulu masifa da izza. Aliyu jan girma da rashin ɗaukar raini. Taga dai yanda wasan zai cigaba da kasancewa tsakanin ɓera da mage.

     Karaf murmushin Mommyn a idon Daddy da ya juya zai koma ciki. Ya wani ɗaure fuska da faɗin, “Aniyarki ta biki idan ma wani abu kike ƙullawa akan yarinyata”.

       Sarai Mommy ta jisa amma sai bata tanka ba, dan ta fahimci masifa yake nema da ita akan Muwaddat ɗin tunda suka dawo asibiti. Itako taƙi bashi kowacce irin damar cimata mutunci dan a yanzu kam bazata ɗauki abinda ta ɗauka a baya ba kan Mahaifiyar Muwaddat ɗin da ita kanta yarinyar. Suna shiga ciki tai wucewarta ɗakinta bata bisa ba duk da ƙananun maganar daya cigaba da faɗa masu ƙona zuciya. Har da cewa ƙilama itace taima Muwaddat ɗinsa asiri take shaye-shaye saboda tana baƙin ciki da ita a gidan. Tana shiga ɗaki ta fashe da wani irin kuka mai cin zuciya. Sai da tai mai isarta ta share hawayenta, dan duk yaran sun wuce makaranta da ga ita sai masu aiki. Duk yanda take jurewa da dakewa akan al'amurin mijin nata game da ƴarsa a yanzu hakan yana neman fin ƙarfinta. Dan al'amarin akwai ciwo sosai matuƙa gaya. Cikin ƙanƙanin lokaci tai ninƙaya a tunanin shekaru ashirin da shida da suka shuɗe kafin yau....


*_SHEKARA ASHIRIN DA SHIDA DA SUKA SHUƊE_*


     Malam Ibrahim Jiƙamshi shine sunan mahaifin su Isma'il (Daddy), yayinda Malam Salisu Ibrahim Jiƙamshi ya kasance ƙaninsa ɗaya tilo da iyayensu suka haifa (Mahaifinta). Sun rasa iyayensu tun suna ƙananun yara, dan haka suka tashi da tsananin ƙaunar juna da shaƙuwa a hannun kakarsu Iyan Jiƙamshi. Iyan Jiƙamshi kakarsu itace har taga aurensu su duka biyun, dan ALLAH yay mata rasuwa ne bayan haihuwar Isma'il da ita Kareema. Duk da bawani wayone da su sanda ta rasu ba bazasu iya manta wasu ƴan abubuwa da suka shafeta ba. Iyan Jiƙamshi ita tabarma Ibrahim da Salisu wasiyyar haɗasu aure idan sun girma, ba komai yasa haka ba sai ganin yanda Isma'il (Daddy) ke yawan kaffa-kaffa da ita tun tana jinjira kasancewar ta ita ɗaya ƙanwarsa da yake gani. Bayan rasuwar Iyan Jiƙamshi da shekara biyu ALLAH yayma mahaifinta Salisu rasuwa shima. Wannan mutuwa ta matuƙar girgiza Ibrahim matuƙa da har takaisa da baro garin Jiƙamshi gaba ɗaya ya dawo cikin Kano tare da ita Kareema daya amshe wajen mahaifiyarta dan bayan ta kammala takaba anta bashi shawaran aurenta ciki harda mahaifiyar su Isma'il (Daddy) amma yace bazai iya ba. Bazai taɓa iya auren matar ƙaninsa Salisu ba. Wannan daliline yasa iyayenta cewa ta bashi ƴarsu tazo gida ta samu miji. Ba rabuwar daɗi akayi ba, dan mahaifiyarta ta tafine ta barta tana kuka mai tsanani, haka ma Ibrahim da matarsa da Isma'il. Riƙonta ya koma hannun iyayen Isma'il (Daddy), inda suke tattalinta da kulawa matuƙa su da ɗan su Isma'il. Dawowarsu Kano da shekaru uku aka haifi Yousuf, inda ALLAH yayma mahaifiyarsu rasuwa itama a wajen haihuwarsa. Abubuwa sun sake rikicewa, inda mutuwar ta sake taɓa rayuwar Ibrahim matuƙa har sai da ta zama sanadin kamuwarsa da ciwon ajali shima. Yayi jinya sosai ta kusan shekara takwas, yayinda ita da Isma'il suka raini Yousuf tamkar uwa da uba a garesa..........✍️




_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim Musa

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070



VIP🔥💯

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥




*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

No comments