Recent Updates

Duk Karfin izzata Book 2 Page 56

 


💋 Duk Karfin Izzata 💋 



💋The talent troupe writer's 💋




         By 

            Star Lady



Page 56




Kukan wahala kasa kasa take masa tana fitar da numfashi mai zafi har cikin ran sa yake jin tausayin ta dannewa kawai yake dressing room ya wuce da ita ya san halin ta da tsoron sanyi dan haka sai ya sanya mata kayan sanyi masu nauyi ya shirya cikin jallabiya ya ɗauko ta kamar yar baby ya dawo da ita cikin bedroom ɗin ya dire ta saman gado tare da jan blanket mai laushi ya rufe ta ya wuce toilet ya ɗauro alwala ya fito ya nufi masallaci,tana ganin ya fice ta lallaɓa ta mike ta nufi toilet ta sanya ruwa mai zafi tayi alwala duk da kayan sanyin dake jikin ta hakan bai sa ta dai na rawan sanyi ba akoi ta da tsoron san yi sosai kuma gashi kasar na du da sanyi.

 alwala tayi ta fito ta shifiɗa dadduma ta sanya katon hijabi har kasa sanna ta tada sallah. Da kyar ta iya yin Sallah a tsaye ba tayi wani dogon karatu ba a sallar haka da ta idar bata yi wani dogon addu'a ba ta mike ta koma saman gado ta kwanta ta rufu da blanket tana jiran lokacin sallar issha ta yi.


Sai da aka yi sallar issha sanna bgs da Aryan suka dawo lokacin ta ɗan samu karfi tayi sallar issha sanna ta shirya masa abinci dare a saman table,ta koma saman gado ta shige cikin lallausan blanket ta kwanta tana kokarin barci ya shigo bakin sa ɗauke da sallama da sanyayyar voice na sa,kusa da ita yazo ya zauna ya sa hannu ya ɗan yaye blanket ɗin yana kallon face nata cike da so da kauna ya ce "My Eshat sarkin ragwanta ba dai cemin za ki yi zazzaɓi ki ke ji ba?" Kara runtse idon ta ta yi tana faɗin "Sannu da dawowa" "Tashi kizo muci abinci" "A'a na ƙo shi" miƙewa ya yi ba tare da ya sake magana ba ya ɗauke ta cak suka wuce wajen table ɗin. Zama ya yi ya ɗaura ta saman cinyar sa ya na faɗin "Me zaki ci?" Lan gwabar da kan ta ta yi ta kwanta ta yi lamo a faffaɗar kirjin sa cikin shagwaɓa ta ce "Yaya Prince duk abun da zaka ci ni ma shi zan ci" kiss ya man na ma ta a goshi ba tare da ya sake magana ba da kan sa ya ciro plate ya zuba musu rice and beans da miyar steew ya ji kaji da kayan ciki sai kam shi yake ta shi kallon ta ya yi yana faɗin "wan nan dai miyar gida Nigeria ne waye ya yi?" "Ni na yi ma ka" ta ba shi amsa cikin wani irin yana yi na shagwaɓa kara rungumeta ya yi sosai ya man na mata kiss a kumatu har cikin ran sa ya ji daɗi sosai dan ya gaji da cin abin cin turawan nan ɗaukan spoon ya yi ya fara bata abincin a baki tana zuba masa shagwaɓa san ran ta ya na biye mata shi kuma. 

Sai da ya tabbatar ya cika mata ciki da abinci tab san nan ya sauke ta daga kan cinyar sa ya kwantar da ita saman sofa ya fara cin na shi abincin. Sosai yau yaci abinci kasan cewar miyar ta masa daɗi ba ka ɗan ba,a cikin ran sa sai al barka yake sa mata kafin ya kammala cin abincin sa barcin gajiya ya ɗauke ta. 

Bayan ya kammala ya wuce toilet yayi wanka ya shirya cikin kayan barci riga zuwa guiwar sa mai ma ɗauri, gabar rigar a buɗe faffaɗar kirjin sa awajen ga yalwataccen gakin kwantaccen gashin kirjin sa na ɗaukan ido gyara gashin kan sa ya yi,ya feshe jikin sa da perfume na sa mai bala'i kam shin daɗi sanna ya nufi in da take kwance saman sofa ya sa hannu ya ɗauke ta cak suka wuce gado ya kashe wutar ɗakin tare da rage gudun A.c kasan cewar san yin da take ji ta takure jikin ta waje guda ya janyo musu lalausan blanket na su ya rufe su shima a gajiye yake ba jimawa barcin gajiya ta ɗauke sa asuba ta gari.


A ɓangaren Aryan kuwa yana shiga part nasu ya isko Diyana ta tasa kayan ciman ta a gaba ta na ci wuce ta yayi ya shiga bedroom ya ɗauro alwala ya fito ya wuce masallaci bai dawowa ba sai da ya yi sallar issha sanna ya dawo lokacin ta yi sallah ta kwanta tana buga game da wayar sa yana shigowa ya wuce toilet dan yin wanka yayi shirin barci sanna ya dawo ya haye gadon yana faɗin "My jidda ba zaki kara cin wani abu bane?" Girgiza masa kai tayi tana faɗin "A'a na ƙo shi sai dai in je in kawo ma ka idan zaka ci" "A'a na ƙo shi ni ma da man dai ke na ke son na tabbatar kin ko shi ne?" "Eh na ko shi" gyara kwanciyar sa yayi tare da jawo ta jikin sa ya ansa wayar ta sa ya shiga contact ya laluɓo number Abba.

  Bugu ɗaya Abba ya ɗaga cikin girmamawa Aryan yace "Barka da dare Abba" daga ɗayan ɓangaren Abba yace "Aryan kuna lafiya?" "Eh Abba muna lafiya ya gida? Ya su Ammi?" "Dukkan su,suna nan lafiya" "My Abba al bishir" da murna Abba yace "goro" "Abba my jidda na da cikin sati biyu" miƙewa Abba ya yi daga kwamciyar da yake saman katafaren gadon sa ya na faɗin "Diyana ta ɗin? Wayyo Allah Alhadulillah Alhadulillah kai yau ina zan sa rai na kai dole gobe na yi azumi dan nuna wa Allah farinciki na da godiya a gare sa ina take bata waya dan Allah wani kyau ta ya kamata na bata wayyo Allah" murmushi Aryan yake yana mamakin irin ruɗewan da Abba yayi wan nan ma ciki aka ce ba a haifi yaron ba ma tukun nan. Mikawa Diyana wayar Aryan ya yi ta ansa cikin zumuɗin jin an ambaci Abba da murna ta kara wayar a kunnen ta tana faɗin "Abba na ina kewar ku sosai" "Kina son ganin mu ne?" Tana kokarin cewa eh Aryan ya yi saurin rufe mata baki tare da anshe wayar ya katse kiran dan ya san halin Abba Diyana na cewa eh tana son ganin su zai sa dole a kai ta Nigeria shi kuma ba zai iya rabuwa da ita ko na kwana ɗaya ba. 

Cikin shagwaɓa yace "Haba my jidda idan ki ka ce wa Abba kina son ganin su ki ka tafi ni kuma da wa zaki bar ni? Kara shigewa jikin sa tayi tana faɗin "A'a ai ba zan tafi na bar ka ba dan kar wata ta ce tana son ka idan na tafi, dan na lura turawan nan basu da hankali shi yasa bana musu dariya dan ma kar su ga hakorina a waje su zo su manne min su samu su rinƙa ganin ka" mamaki ya hana shi magana a ransa yake tambayar kan sa "Ko wa ya koya wa jidda wannan karatun kuma oho yarinya kamar wata aljana kullun cikin tsaro zance ko ina ta jiyo wannan kuma gashi dai ba tayi magana da Aunty farida ba kwana biyun nan bare na ce tsarin Aunty farida ne kai my jidda ke nan my jidda duniya" yayi nisa cikin zancen zucin da ya ke wayar sa ta fara kara yana dubawa ya ga Abba ne cikin sauri ya ɗauka tare da manna wayar a kunne sa yana faɗin "Sorry my Abba network ne ya katse kiran" daga ɗayan ɓangaren Abba yace "Network ko kuma kai ina da tabbacin kai ka katse kiran dan kasan Diyana zata ce zata zo kuma kasan tana faɗa min zan ce ka kawo min ita to dai ka gudu baka tsira ba cikin ta na kai wata biyar ka dawo min da ita nan mu bata kulawa su Khalid sun iso ne ma na manta in tambaya ye ka?" Ɗan sunkuyar da kai ƙasa ya yi a ran sa yana ya bawa kai fin ƙwaƙwalwar Abba yana da saurin gane abu shi bgs ya ɗauko cikin girmamawa yace "ɗazun mukayi magana da Khalid yace min jirgin su ya kusa sauka kasan cewar basu tashi da wuri ba da yamma suka taso na sa sojoji suje Airport su ɗauko su" "ya aka yi ba su ta shi da wuri ba? Me ya tsayar da su,ba su ta shi tun lokacin da muka ta shi ba? "Wallahi Abba ni ma ban sani ba amma idan sun iso zuwa da safe koma mene zamu ji" "to shike nan dan girman Allah Aryan ka kula min da Diyana sosai na san kana kokari amma ka kara sosai kar ka bari cikin nan ya nemi wani abu baka nemo ka ba shi ba ka kula min da ita da cikin ta sosai ka sa mata ido sosai ka san ta da son wasa to ka rinƙa hana ta wa su abubuwan dan gudun matsala ka na ji ko?" Kallon face nata ya yi sai hamma take alamar barci idon ta sun kan kan ce sun yi ja kasa kasa yace "In Sha Allah Abba na zan yi duk abun da kace" "To Allah ya muku albarka yanzu ku yi barci da safe zamu yi waya" "To Abba ka gai da su Ammi sai da safe" "Allah ya tashe mu lafiya" Abba ya ba shi amsa tare da katse kiran ajiye wayar Aryan ya yi  saman bedside drawer ya jawo ta jikin sa ya rungume ta sosai, tare da ja musu lallaudan bargo ya rufe su asuba ta gari.


After 2 month

 

A yanzu cikin Diyana ya rage mata laulayi ta rage amai da ciye ciyen da take ta kara nitsuwa kamar ba ita ba ta kara ƙiba sai ta koma sak Ummin su a kamanni Aryan na bata kulawa sosai ko motsi ta yi sai ya tambaya lafiya ga cikin nata wani mahaukacin girma da yake ko cikin lamrat dake cikin watanni na biyar bai wuce kamar na Diyana dake cikin watanni na uku ba abun har mamaki yake bawa Aryan gashi cikin bai yi wani kwari ba bare ya mata scanning ya gani.


A ɓangaren Zahra auta cikin nata ya fara girma ita ma yanzu cikin nata yana wata na huɗu kenan tayi ki ɓa sosai ita da Diyana sai juyi su ke hips na su kamar zai fashe breast na su ya kara cikowa saɓanin Lamrat da tayi yar rama ta ɗan yi duhu Amrat ma yanzu tana da ciki wata ɗaya duk cikin su Hiyana ce dai shiru ba baya ni



A ɓangaren bgs da Eshat kuma Duk wani training da bgs ke ba ta, ta fanni motsa jiki yanzu ta iya ita da kan ta ma tana yi ba sai ya taya ta ba yanzu har rige rige take da shi idan suna gudu ko press up ta samu karfi dai dai yadda yake so a yau suka shirya za ta fara koyan har bi da bindiga da ko yan faɗan hannu ta yi kyau abun ta sai kara freash take sai dai ta ɗan rage ƙiba saboda motsa jiki da take.


Misalin karfe 4 na yamma suna zaune a wajen motsa jiki shi da ita dukkan su suna sanye cikin guntun wando na sojoji iri ɗaya da t-shirt na sojoji yar karama mara nauyi ba karamin kyau kayan sojojin suka mata ba dukkan su ba su ɗaure gashin kan su ba sun bar shi a watse har baya, ya kara kyau sosai shi ma hankalin sa a kwance yana zaune saman sofa yana kokarin haɗa mata bindigar wasa ta fara da shi,ita kuma tana tsaye tana faman sanya hand gloves da ya bata. wayar sa dake saman table dake kusa da ita ya fara ringing, cikin sauri ta sanya hannu ta ɗauko ta miƙa masa kallon mai kiran yayi kafin ya ansa wayar cikin sauri yayi picking call ɗin tare da manna wayar a kunnen sa yana faɗin "Barka da yamma Ammi" daga ɗayan ɓangaren Ammi tace "ɗazun da muka yi waya na so sanar da kai sai na man ta" "menene Ammi" yayi maganar tare da ciro wayar daga kunnen sa ya sanya ta a hand-free ya a jiye a gefen sa ya ci gaba da haɗa bindigar da ya ke "Daman akan wanna mata da ta kashe mahaifin su Hiyana ne daman nace a barta ka mata hukunci sai Yusuf yace ba zai yiwu a mata hukunci ba har sai ta haife cikin dake jikin ta shi yasa nace a ajiye ta sai ta haihu in sanar da kai ka mata hukuncin da ya dace to ta haihu da hai huwar nata ma sati biyu ke nan ya ka mata kazo ka mata hukuncin da ya dace dan ta cutar da su Hiyana sosai ta haukata musu mahaifiyar su ta kashe musu mahaifi ta kuntatawa rayuwar su sosai ga laifin zina da shirka dukka" yana kokarin yin magana ya jiyo sautin kukan Hiyana daga bayan sa a sukwane ya juyo yana kallon ta ta kifa kai da guiwa tana kuka ajiye bindigar hannun sa yayi ya ɗauki wayar ya cireta a hand-free ya mai da kunnen sa ya fara magana "Ammi zan sa a mata hukuncin da ya dace zamu yi waya an jima da daddare" "to Allah ya kai mu daren amma gaskiya ina son ka hukunta ta da kan ka" "Amin Ammi ke dai zamuyi waya an jima" "to" kawai Ammi tace sannan ya katse kiran tare da a jiye wayar ya nufi wajen da Hiyana ke zaune ya zaune kusa da ita tare da sanya hannu ya ɗago ta cak ya ɗaura ta saman cin yar sa yana faɗin "Me ya faru my Eshat?" Cikin kuka tace "Yaya Prince daman Inna ce ta kashe bappa na innalillahi wa inna ilaihir rajiun wallahi ba zan taɓa yafe mata ba ta cutar da mu a rayuwar mu, yaya Prince dan girman Allah ka mata hukunci mai tsananin gaske gaji?" rungume ta yayi sosai a jikin sa yana ɗan bubbuga bayan ta a lamar rarrashi kasa yayi da murya da sigar rarrashi ya fara magana "Da ban yi niyar hukunta ta da kai na ba amma saboda ke zan yi hakan ki dage ki gama koyan har bi da bindiga next month sai muje Nigeria na mata hukuncin da kai na kin ji? Amma duk da haka zan sa a tsare ta prison a rinƙa bata horo mai tsanani kafin na zo" kara shigewa jikin sa tayi tana kuka ƙasa ƙasa hannu ya sa ya ɗago habar ta yana kallon kyakkyawar face nata "My Eshat ya isa haka kukan nan kin ji ko zan hukunta ta dai dai da abun da ta mana, please kiyi shiru wanna kuka da kike tamkar kina caka min mashi ne a zuciya please ki yi shiru" ya kai karshen maganar tare da sanya kyakkyawar hannun sa yana goge mata hawaye shiru ta yi ta dai na kukan cikin raunaniyar murya tace "Yaya Prince ka san me?" Girgiza mata kai ya yi a lamar a'a ba tare da ya yi magana ba "Yaya Prince ni ma ina son in samu ciki kaga su Diyana fa dukkan su sun samu ciki har ma nasu cikin ya girma" dogon numfashi ya ja tare da sauke nauyayyar ajiyar zuciya Hiyana ta taɓo masa in da ya ke masa ciwo "My Eshat ni kai na bani da wata buri da ya wuce in gan ki da ciki kin haifa mana yara dozen abun na damu na amma koma me na san Allah ne bai kawo ba" shiru ta ɗan yi kafin tace "Ya Allah ya bamu masu Albarka" manna mata kiss yayi a gefe kumatu yana faɗin "Good haka ake san bawa ya ka sance mai tawakkali kar ki rin ƙa addu'ar Allah ya baki Aihuwa ki rinƙa addu'ar Allah ya baki zuri'a ɗayyiban kin ji In Sha Allah muma mun kusa samun na mu ƴa'ƴan" tana kokarin yin magana Aryan da Yusuf suka iso wajen bakin su ɗauke da sallama cikin sauri ta mike daga jikin sa tana ɓoye fuska dan karsu Aryan su ga tayi kuka cikin girmamawa tace "Ina wuni yaya Aryan" da fara'a ya amsa da lafiya lou sister" "Yaya Yusuf ina wuni" da fara'a shi ma ya amsa da "Lafiya lou" juyawa tayi ta na kokarin barin wajen Aryan ya yi saurin cewa "A'a sister zo ki yi zaman ki sallama kawai zamu yi da shi" koma wa ta yi ta zauna ku sa da bgs ta ɗan sunkuyar da kai ƙasa.  Hannu Aryan ya miƙa wa bgs yana faɗin "to zan tafi amma ban sanar da jidda akan zan ta fi ba dan inna faɗa mata ba zamu kwashe lafiya ba, na baku amanar ta ban san me zai kasan ce ba kila na dawo da rai ko akasin haka to idan ban dawo da rai ba idan ta haifi ɗa Namiji kasa masa sunan ka idan kuma mace ce ka tambayi jidda ta sa mata suna" kunyar kiran sunan Aunty Amarya yake saboda bai san ta da abun da ya wuce miƙa masa hannu bgs ya yi suka gaisa yana faɗin "Idan mace ce sunan Aunty Amarya In Sha Allah lafiya lou zaka dawo da kan ka zaka raɗawa ƴa'ƴan ka suna" ya kai karshen maganar tare da mikewa suka rungumi juna ya na yi wa Yusuf a lama da hannu akan ya zo cikin sauri Yusuf ya kari so suka rungumi juna su ukun kukan Hiyana ya dawo da su hayyacin su cikin sauri suka raba jikinsu, su ka juyo suna kallon ta "Eshat lafiya meke faruwa" bgs ya tambaya ya na koma wa kusa da ita ya zauna cikin kuka tace "Yaya Aryan ina zaka je? Me ya sa ka ke magana idan baka da wo ba asawa yaron Diyana sunan yaya Prince?" Kallon bgs Aryan ya yi a ya yin da shi ma bgs ɗin shi yake kallo "sister nasan kina da fahimtar zaki fahimce ni zanje kama wanna mutumin da ya taɓa kama ku ke da Khalid ne mun samu address na su suna da yawa sosai yana da yara a kasa she da ban da ban, mun samu labarin zasu yi taron karshen shekara da suke ko wani karshen shekara a Dubai wanna ita ce ka ɗai daman da muke da shi na kama su gaba ɗayan su dan ko wani shekara a kasa da ban da ban suke taron kin ga idan bamu yi zafin naman kama su wanna shekarar ba ba lallai wata shakara mu san kasan da zasu yi taron ba zan jagoranci tawaga biyu ne muje bgs yana wani aikin shi ya sa ba zai ja goran ce mu ba ki kula min da jidda In Allah ya yarda ba zamu wuce kwana biyu ba" ya kai karshen maganar tare da juyawa cikin sauri ya bar wajen shi kan shi bgs dannewa yake har cikin ran sa yake jin zafin tafiyar Aryan ji yake kamar zasu rabu ke nan.

A yau dai bgs bai samu daman fara koya mata harbi da bindigar ba saboda tafiyar Aryan duk ya kashe masa jiki ya rasa meke masa daɗi da kyar ya iya ɗaukan ta saboda kasala suka wuce cikin gida Yusuf ya wuce ɗakin binchiken su dan ya fara aikin sa ita kan ta Hiyana jikin ta ya mutu mu samma idan ta tuna Diyana ta tuna maganar Aryan in da yake cewa idan ban dawo ba ka sawa ɗana sunan ka da kuma in da yake cewa zamu je kama yan ta'adda sau da dama tana ɓoyewa tayi wa Diyana da Aryan kuka Diyana kuwa tana ɗaki tana sharan barci saboda alluran da Aryan ya mata ba dan haka ba ba za ta taɓa barin sa ya tafi ba shi yasa ya mata alluran barci Yusuf Khalid Fahad duk basa cikin jin daɗi yau dukkan su tunanin Aryan suke gaba ɗaya samarin Abba har da su Abba da Hiyana yau basu yi barci ba Sallah suka kwana yi suna yiwa Aryan addu'a mu samman Ammi da Aunty farida dan Yusuf ya kira kowa a gida ya faɗa musu ba karamin aiki Aryan ya tafi ba yana bukatar addu'a ya zama dole a faɗa wa kowa a gida dan su taya shi da addu'a bgs da kan sa ya kai Hiyana ɗakin su Diyana akan ta taya ta kwana dan yana zargin alluran zai iya sakin ta cikin dare kar ta tashi ta fara kuka dan ya san halin ta Diyana na barci Hiyana na Sallah tana kuka tana ta yi wa Aryan addu'ar samun na sara da dawowa lafiya haka sauran ma kamar yadda suka ga rana haka suka ga dare tun farkon dare har karshen ta suna kan dadduma Abba da Ammi sun shiga damuwa sosai Aunty maryam itama tana Sallah tana kuka ta rokon Allah ya dawo mata da ɗan uwan ta lafiya daga shi sai Omar suka rage mata.


Hasashen bgs ya tabbata domin kuwa karfe ukun dare Diyana ta farka da zazzaɓi mai zafi da kyar ta iya waro idonta ta mike zaune saman gadon tana kallon ɗakin kamar bakuwa can ta hango Hiyana a kan dadduma kara waro ido tayi tana kallon Hiyana tana mamakin me ya kawo Hiyana ɗakin su da daddaren, a hankali ta zuro kafafun ta kasan gadon ta mike ta nufi in da Hiyana take dai dai wajen glass table dake tsakiyar ɗakin jiri mai karfi ya kwashe ta ta faɗi saman table ɗin ta buge cikin ta ji kake tass table ɗin ya tarwatse azababben ihu ta saki tare da dafe cikin ta tana juyi awajen a sukwane Hiyana ta juyo tare da mikewa da gudu ta kariso wajen ta a razane ta koma baya ganin jinin dake bin kafar Diyana kara itama Hiyanar ta saki a guje ta fita ɗakin ta koma bedroom nasu babu ko sallama ta faɗa cikin ɗakin bgs na zaune saman dadduma yana rike da al Qur'ani mai girma jin motsin mutun ya sa ya ɗago kai waro ido waje ya yi yana kallon ta murya na rawa tace "Yaya Prince Diyana ta ji ciwo jini na zuba sosai" tun bata kai karshen maganar ba ya ajiye al Qur'ani dake hannun sa ya mike ya nufi waje yana fita ta bi bayan sa da gudu.

Diyana na in da Hiyana ta bar ta tana kuka ta dafe ciki tana juyi a wajen duk ta ɓata wajen da jini kallo ɗaya bgs ya mata ya dafe kai yana karanto sunan Allah a ran sa cikin sauri ya ɗauke ta cak ya fito da ita ya wuce ɗakin su na duba marasa lafiya sai kuka take ta kan kame sa saboda azaban ciwon da cikin ta ke mata da gudu Hiyana tabi bayan su ita ma sai kuka take.


A ɓangaren Aryan kuwa lokacin yana can Dubai yana shirin yaki yana kokarin jera bullet a kugun sa bayan ya gama ya ɗauki kana nan bindiga huɗu ya sanya biyu a cikin sa ta gefe da gefa, biyun kuma ya sanya a gefen takalmin sa ta ciki haka ɗai yake jin gaban sa na faɗuwa zuciyar sa na tsinke wa sunan Allah yake ta ambata a ransa a zuciyar sa yana tunanin ko dan saboda yaki da zai je ne ya sa zuciyar sa ke tsinke wa kwata kwata bai taɓa kawo wa ransa matsala daga gida ba yayi shirin sa tsab ya fito wajen rundunar jibga jibgan sojojin su da zasu tafi tare da su bugun gaban nasa sai kara tsananta yake dannewa yayi ya umarci horarrun sojojin sa akan su raba kan su gida biyu wayan da za su fara shi ga wajen da kuma wayan da zasu yi shiga ta biyu sanna ya rufe da cewa kowa da ya kunna tracker jikin sa saboda tsaro dan mutumin da zasu je kamawa yana da mutane sosai sanna suna da manya manyan maka mai a hannun su.

 Bayan sun gama shiri Aryan ya jagoranci rundunar farko suka yi gaba, sau ran suka biyo su a baya ɗan ne sa ne sa da su cikin sahara suka kutsa hancin motocin su tun daga baki bakin shiga saharan suka kashe motocin su suka fito suka fara tafiya da kafa Aryan ya ɗana kuna mar bindigar sa yayi gaba suka rufa masa baya tafiya suke suna lallaɓawa kamar wasu ɓarayi awani wajen ma sai su tsugunna sun yi tafiya a tsugunne 


To masu karatu sai mun haɗu Monday idan mai dukka ya kai much kauna 🥰💔🔐

No comments