Recent Updates

Duk Karfin izzata Book 2 Page 55

 


💋 Duk Karfin Izzata 💋 



💋The talent troupe writer's 💋



Wanna Page ɗin naki ne Dear ta Aunty Amyra KUKAN ZUCI All the best my Dear fatan samun nasara da cimma burin na Alkhari love you lodi lodi 🥰💔🔐


         By 

            Star Lady



Page 55



......ganin ba zai iya gyara Toilet ɗin bane yasa ya ɗauke ta cak ya saɓa ta a kafaɗar sa suka fito waje ya wuce da ita ɗayan bedroom ɗin a nan ya haɗa ruwa mai zafi ya gasa mata jiki ya cire kayan jikin sa da ta ɓata masa shima yayi wanka ya ɗauro towel Sanna ya naɗota a towel suka fito waje saman gado ya kwantar da ita sanna ya koma bedroom nashi ya ɗauko phone nashi ya kira jourfree akan yazo ya gyara masa ɗakin ya ɗauka mata kaya tare da kayan sanyi ya fito ya dawo ɗayan bedroom da take ciki kamar yarda ya barta haka ya dawo ya same ta ɗagota yayi ya sanya mata kaya yana faɗin"Sorry my jidda"shiru tayi bata yi magana ba sai nishi take kamar wadda tayi gudu ta gaji"In kawo miki tea"cikin sauri ta girgiza masa kai alamar a'a"To me zakici in kawo miki?"girgiza kai tayi da kyar ta iya cewa"ba bu" "No my jidda ni ban yarda ba dole ki ci wani abun"kukan shagwaɓa ta sa masa tana faɗin"Ni to ka kawo min nono da fura" "Tirkashi nono da fura kuma jidda? Ina zan samo nono da fura kuma?" "Ni shi nake son sha kuma na kauyen mu na shanun bappa" "My jidda kiyi hakuri ki sha Yoghurt kinji ba bu fura a nan ban taɓa gani ba ko nema zan yi ban san ai na zan nemo ba" "Ni gaskiya yaya Aryan shi nake so idan ba haka ba ba zanci komai ba"dafe kansa yayi aran sa yana tunanin in da zai samo nono kuma har da fura wai kuma na shanun bappa tirkashi,ganin ya shiga damuwa ne yasa ta yunkura ta mike zaune ta kwantar da kan ta a bayan sa cikin shagwaɓa tace"yaya Aryan ka bar shi kawai kaji na koshi"juyowa yayi ya rungumeta yana faɗin"Aa my jidda dole za'a ne mo shi kin ji"ya kai karshen maganar tare da ɗauko wayar sa ya laluɓo number Aunty farida ya fara kira yana murmushi. Bugu ɗaya Aunty farida ta ɗaga tana faɗin"Hello Aryan" "Aunty farida ya kike ya Junior da dadyn da?" "Suna lafiya ya Diyana da sauran yan uwan naka?" "Suna lafiya Albirushirin ki Aunty farida"cikin sauri tace"goro"ko kaɗan bata kawo cewa Diyana na da ciki bane tafi tunanin karin girma ya samu awajen aiki. "Aunty farida my jidda na da ciki sati biyu"mikewa Aunty farida tayi tsaye cikin sauri tace"Alhamdulila Alhamdulila Allah hu Akbar dan Allah Aryan ka dawo min da ita nan sai ta hai hu kaji"Aryan na kokarin yin magana Diyana ta fasa ihu tare da tashi daga jikin sa tana faɗin"ciki kuma nashi ga uku wayyo Allah Ummi na shike nan mutuwa zanyi wayyo na mutu na lalace ni wallahi ba zan Aihu ba dan mutuwa ake idan za'a Aihu ai na gani a film jinin mutun karewa yake wayyo Allah shike nan ni kam zan rabu da su Hiyana shike nan tawa ta kare innalillahi wa inna ilaihir rajiun"mutuwar zaune Aryan yayi yana ganin ikon Allah ya rasa ta ina zai fara bata hakuri ya kasa magana ya kasa cire wayar da yake da Aunty farida daga kunnen sa sai magana Aunty farida take tana faɗin"Aryan ka bata wayar bari nayi magana da ita"amma ina Aryan bai jin me take faɗe ba hankalin sa na kan Diyana dake neman tarwatsa masa zuciya yadda yake son cikin nan tace bata so kai ina ai ba zai yiwu ba. A sukwane ta mike tana kokarin sauka daga gadon da alama ta ruɗe cikin sauri ya ajiye wayar saman gadon ya riko ta yana faɗin"My jidda ki dawo cikin hankalin ki saurare ni"kokarin fisge jikin ta take tana ihu tsakanin ta da Allah tana surutai"Ai tun da mukayi Aure nace maka ni bana son Haihuwa dan na gani a Tv idan kutun zai aihu jinin sa na karewa ya mutu shine zaka sa na haihu dan baka sona ko? Mugu kawai kuma ko na mutu ba zan yafe maka ba"fusa iya fusata Aryan ya fusata a zuciye ya ɗaga hannu zai wanka mata mari a zafafe ta ɗago ido tana kallon sa suna haɗa ido yaji ya kasa marin nata cak ta tsaya da kuka da surutan da take ta zuba masa ido kamar mai jiran saukan mari kasa yayi da hannun sa murya a shake saboda ɓacin rai yace"My jidda I'm so sorry I.... Bai kai karshen maganar ba ta fasa ihu ta cigaba da surutan nata kaman mai aljanu ba karamin mamakin tane ya kama shi ba wayar sa ya ɗauko a ransa yana faɗin"nasan maganin ki" katse kiran Aunty farida yayi ba tare da ya mata magana ba ya laluɓo number Ummin su ya fara kira wayar na ringing har sai da ya kusa katsewa sanna hajjiya Fateema ta ɗaga cikin girmamawa yace"Ina kwana Ummu" daga ɗayan ɓangaren Hajj Fateema ta amsa da"Lafiya lou Alhadulillah ya kuke?" "Lafiya lou Ummi daman ina son kiyiwa jiddan magana ne" shiru Diyana tayi tana sauraron sa tana son jin dawa yake waya "Me deejahn tayi?" Hajj Fateema ta tambaya kasa yayi da kai kamar yana gaban ta cike da girmamawa ya fara magana "Daman mun samu karuwa ne take ta kukan wai bata so nayi nayi taki shiru taki sauraro na" zubur Hajj Fateema ta mike zaune daga kwanciyar da take a saman kujera tana faɗin "eyeee ba shakka ina take bata wayar" juyawa yayi ya mika mata wayar kallon sa tayi tana faɗin "Waye ne?" mamaki Aryan yake Diyana mai kukan da ba hawaye sai tayi kukan ta har tayi shiru bazaka ga hawaye ko ɗigo ba. Shiru yayi bai mata magana ba ya sa mata wayar a kunnen ta cikin tsoro tace"Waye ne?" daga ɗayan ɓangaren Hajj Fateema tace"Uwar ki ce" jin muryan Ummin ta yasa ta waro ido waje sosai tana kallon sa ciro wayar yayi daga kunnenta ya ɗaura mata a hannun ta ya mike ya fice daga ɗakin cikin tsoro ta mai da wayar kunnen ta ta tattara nitsuwar ta tace "Ina kwana Ummi" a kule Hajj Fateema tace"Wai deejah me matsalar ki ne? Eh wato ke baki jin magana ko" murya na rawa tace "kiyi hakuri Ummi wallahi ni bana so cikin ne" "What? Deejah ni kike faɗa wa baki son ciki eyee,ba'a Aihuwa ku na haife ku a'a lallai Khadijah kin girma to wallahi ki kiyaye ki bar mijin ki ya samu kwanciyar hankali ina cewa last Month na gama case naku akan gudun shi da kike shine yanzu kuma zaki fito masa da wata iya shegen ko to wallahi ina sa shi ya ɗauko ki ya kawo min ke dan ina ga kina bukatar na dawo dake cikin hayyacin ki" hawaye ta fara yi dan duk duniya ba abun da take tsoro biyun Ummin su cikin raunaniyar murya tace "Dan Allah Ummi kiyi hakuri zan yi duk abun da kike so amma ina tsoron cikin ne ranar na gani a Tv da matar tazo Aihuwa dr yace jinin ta ya zube duka ya kare ta mutu shine nake tsoro" sai yanzu Hajj Fateema ta fahimci in da matsalar take ba tsanar cikin Diyana ke yi ba tsoron haihuwar take dan haka sai ta sassauta murya cikin muryan rarrashi ta fara magana "Deejah ki na ji na ko! idan kin ga Mutun ya mutu kwanar sane ya kare ni meyasa na haife ku kuma ban mutu ba saboda kwanana bai kare ba dan haka ina son ki sani ba sai Aihuwa ba kina kwance saman gadon ki lafiyar ki kalau ma mutuwa tana iya ɗaukar ki wasu ma abinci suke ci mutuwa ke ɗaukan su kuma shi haihuwa bashi da wata matsala kin ji ko? Ke dai kiyi ta addu'ar Allah ya baki ƴa'ƴa masu Albarka karki ji wani tsoro kinji deejahn bappa" dariya Diyana tayi tana faɗin "to shike nan Ummi zan rinƙa yin addu'a,ina su Ammi?" "Ammi suna palon Abba suna yin breakfast nima tafiya can zanyi yanzu sai munyi waya" bata jira amsar Diyana ba ta katse kiran ajiye wayar Diyana tayi saman gadon ta diro kasa ta fice daga ɗakin ta nufi asalin bedroom nasu.


Nan ta isko Aryan yana zaune bakin gado ya buɗe jakar da bgs ya bashi yana duba takar dun jin shigowar ta yasa ya ɗago kai yana kallon ta karisowa tayi kusa da shi ta zauna tana faɗin "Yaya Aryan me kake yi" kallon ta yake ya kasa magana kamar ba itace yanzu nan tace kar ya sake yi mata magana ba har da ce masa mugu ganin yayi shiru bai tankata ba yasa ta anshe takardun hannun sa ta ajiye a gefe ta faɗo jikin sa tana dariya tana faɗin "Yaya Aryan me ya faru kake ta kallo na kaki yin magana"rungume ta yayi sosai yana ɗan murmushi yana godewa Allah daya basu Hajj Fateema a matsayin suruka kuma uwa "Tabbas da Hajj Fateema na nan da jidda ta tafi haka hankali yanzu gashi cikin yan mintocin da basu fi goma ba ta saita min jidda ta wadda ba dan ita ba da sai mu kwana mu wuni rikicin nan ba zai kare ba daga karshe sai ran kowa daga cikin mu ya ɓaci" yayi nisa cikin tunani yaji hannun ta cikin rigar sa tana shafa lallausan gashin kirjin sa kallon face nata yayi kafin yace "tashi ki zauna muyi magana" ba musu ta mike ta zauna da kyau tana kallon sa ɗauko takar dun data anshe daga hannun sa yayi ya miƙa mata yana faɗin "wannan takarda wani Katafaren gidan gona ne dake us Bgs ya baki kyau ta a matsayin gift na cikin dake jikin ki sai kuma wanna ma kullin motar irin na sister daman tun da naga ya bada Oder motocin guda shida iri ɗaya na kawo a rai na ku ya sayawa ashe ko haka ne ke ɗaya sister ɗaya auta ɗaya matar Yusuf ɗaya matar Fahad ɗaya ina ga ɗayan kuma na matar da Ahmad zai aura ne idan mun haɗu a palo anji sai ki masa godiya amma kin san me? idan Allah ya bamu baby boy sunan bgs zamu sa idan kuma mace ce sunan Ammi" cikin sauri tace "A'a sunan Aunty Amarya dai dan Allah" har cikin ransa yaji daɗin hakan sai kuma mood nashi ya sauya dan ta fama masa wani ciwo shiru yayi bai sake magana ba yana jin zuciyar sa na masa zafi a duk lokacin da ya tuna yadda karshen mahaifiyar sa ta kasance sai yaji ya tsani duniya gaba ɗaya ganin ya sauya ya shiga damuwa yasa ta faɗo jikin sa tana faɗin "Yaya Aryan ya batun nonon da furan kuma?" Kallon face nata yayi yana faɗin "tashi ki shirya muje mu nemo in da yake ai dole little bgs ya sha nono ko kuma" saurin rigashi tayi tace "ko kuma little Aunty Amarya" murmushin dole yayi kafin yace "to koma waye dai jeki shirya kizo mu tafi" mikewa tayi ta nufi dressing room har ta kai bakin kofa zata shi sai ta juyo tana faɗin "Yaya Aryan idan na Haifi maza yan biyu dan Allah kasa sunan yaya Prince da sunan yaya Aiman kaji" wani mugun raɗaɗi yaji zuciyar sa na masa ɗaga mata kai kawai yayi ya kasa magana Diyana ta tayar masa da zafi biyu lokaci guda,mikewa yayi ya kwanta yana tunanin rayuwar da sukayi da Aiman nan take idon sa suka sauya sukayi ja cije laɓɓan sa yayi yana jin mutuwar Aiman ta dawo masa sabuwa. A wanna hali Diyana ta dawo ta same sa ta shirya cikin dogon riga abaya baki ta sanya gyalen rigar a kan ta ba ƙaramin tsorata tayi da ganin yana yin saba hayewa gadon tayi tana faɗin "Yaya Aryan lafiya" mikewa zaune yayi yana kokarin ɓoye damuwar sa yace "Muje ko" bai jira amsar ta ba ya miƙe ya ɗauke ta cak suka nufi wajen. Bai dire ta ko ina ba sai cikin motar sa sanna ya shiga ya tayar da gudu suka fice daga gidan suka tafi neman fura da nono.


Misalin karfe 5 na yamma zaune suke a ɗakin su saman katafaren gadon su.

  Hiyana na sanye cikin guntun wandon jeans blue zuwa goiwa da yar riga mai guntun hannu fari tas tayi kyau sosai kan ta ba ɗan kwali ta zuba lallausan bakin gashin ta nan har baya tana zaune a gefen sa ta ɗaura kyawawan fararen kafofin sa a kan cinyar ta tana jan yatsun kafar nasa tana mammatsa masa su yayin da shi kuma yake sanye cikin wandon sojoji guntu zuwa guiwa da farar singlet ya baza lallausan bakin gashin kansa bai ɗaure ba yayi kyau sosai kamar shi yayi kan sa ya ɗaura system a kan cin yar sa yana aiki. Cike da so da kauna sa cikin shagwaɓa tace "Yaya Prince yatsun kafan kan nan suna min kyau sosai" ba tare da ya ɗago kai daga aikin da yake a system ɗin ba yace "okey ma" waro ido waje tayi ta ɗaure fuska tana faɗin "Ni ce ma?" Cigaba da aikin sa yayi yana faɗin "Oh sorry ma" "Uhm Uhm shine zaka sake cemin ma ɗin kuma" sai lokacin ya ɗago ya kalleta yace "Oh I'm sorry ma man tuwa nayi" gunkule hannu tayi zaka kai masa dukan wasa a kirji yayi saurin mike wa yana faɗin "I said sorry ma" da gudu ta mike ta nufesa ɗaga ta yayi cak suka nufi wajen yana faɗin "Lokacin training yayi ma" kukan shagwaɓan ta sama tana faɗin "Ni ka sauke ni mun ɓata tun da ni ce ma" rungume ta yayi cikin shagwaɓa ya kwai kwayi maganar ta yana faɗin "Ni ka sauke ni mun ɓata tun da ni ce ma" "Allah yaya Prince bana so" sake kwaikwayar maganar nata yayi yace "Allah yaya Prince bana so" ya kai karshen maganar dai dai ya sauke ta awajen motsa jikin nasu bubbuga kafa tayi a kasa tana yarfe hannu tana faɗin "Allah bana so ni ka dai na kwai kwayon magana ta" bubbuga kafa shima yayi ya yarfe hannu ya sake kawai kwayon maganar nata yace "Allah bana so ni ka dai na kwai kwayon magana ta" yana magana fuskan sa a ɗaure sosai ɗaure fuska tayi ba tare da ta sake magana ba ta nufi hanyar komawa cikin ita a dole tayi fushi cikin sauri ya jawota jikin sa ya rungumeta yana faɗin "Oh my Eshat idan kikayi fushi dani ya kike so nayi da rai na to na tuba ba zan kara ba" ɗaga kafar ta tayi dan ya fita tsawo sosai ta sa hannu taja dogon hancin sa tana faɗin "Allah yaya Prince ni ban san waya koya maka neman tsokana ba" "wash Allah" ya furta yana ɗan shafa hancin nashi da ta ja,dariya tayi tana faɗin "Soja na kuka dan naja hancin sa" kama hannun ta yayi dukka biyu ya rike da hannun sa ɗaya yasa ɗayan hannun nasa yaja dogon hancin nata ita ma yana kallon face nata "ihu ta saki tana faɗin "Na tuba ashe da zafi" Cool murmushi ya saki tare da kara jawota jikin sa yana faɗin "Soja kam bashi da jini a jiki ne da ba zai ji zafin abu ba idan an masa" turo baki bayi tana kokarin yin magana yayi saurin matso da bakin sa sai tin kunnen ta yana faɗin "My Eshat give me a hot kiss kafin mu fara training kinji? Ɗago ido tayi tana kallon sa kashe mata ido ɗaya yayi tare da ɗaga mata gera ɗaya turo baki tayi tana faɗin "To ai sai ka ɗaga ni tsawona zai iya kamo bakin naka" tun bata gama rufe baki ba ya ɗaga ta cak ya ɗaurata saman sofa dake wajen tare da ɗan rangwafo da kan sa yana shafa bayan ta da hannun sa ɗaya a hankali ta kawo dan bakin ta dai dai sai tin nashi cikin nitsuwa ta kama lallausan lips nashi na kasa ta fara kissing kamar jira yake ya tura hannun sa cikin rigar da ya fara murzan tula tulan ta hannu ta tura cikin rigar sa ita ma ta farurza masa nasa Nipple ɗin kasan cewar tasan ba abun da yafi so irin a masa wasa da su matse ta yayi sosai a jikin sa yana jin wani shocking daga tsakiyar kansa har izuwa tafin kafar sa kankame juna sukayi dukkan su kamar zasu shige jikin zuna suka fara bawa zuna hakkin sa cikin fitar hayyaci yake kokarin tura hannun sa cikin wandon ta cak ya tsaya kasan cewar ya tuna a waje suke,a hankali ya zame bakin sa daga nata tare da komawa saman sofa ya zauna ya jingina kan sa da jikin sofar ya ɗaga kai sama ya lumshe ido yana mai da numfashi faɗowa jikin sa tayi tana mai da numfashi ita ma ba tare da ya buɗe ido ba ya rungumota suka yi shiru na yan mintoci kafin ya waro rinannun idon sa waje kasa kasa yace "Eshat kin gama dani" turo baki tayi tana faɗin "Me nayi kuma" zubawa face nata rinannun ido sa yayi,ba tare da yayi magana ba yayi shiru,hannu tasa ta rufe masa ido tana faɗin "Kai yaya Prince sai kayi ta kallon mutun kuma baka magana" hannun sa yasa ya zame hannun nata tare da mikewa da ita a jikin sa ba tare da yayi magana ba.

  Sai da ya mike sanna ya sauke ta ya kama hannun ta suka wuce wajen mashin na motsa jiki.


  nuni ya mata da hannu sa yana faɗin "Hauki zauna" ba musu ta hau hannu ya sa ya ɗaura mata kafan ta a saman mashin ɗin yana faɗin "fara turashi baya yana dawo kina mai da shi baya" yun kurawa tayi zata dura mashin ɗin baya amma ta kasa,sanya karfin ta tayi dukka amma ta kasa koda motsa karfen,girgiza kai yayi yana faɗin "Eshat ai wanna rashin karfin naki dole na baki training mai kyau matsa kaɗan" matsa masa tayi ya ɗan zauna a gefen ta yasa kafar sa ɗaya kan mashin ɗin kusa da nata ƙafan yana faɗin "muje fara turawa bari ma tayaki" ka ɗan ya ɗan tura mata idan mashin ɗin ta fara tafiya sai ya sake mata ta karisa da kyar,nan yake zufa ya fara wanke mata fuska kau da kan sa yayi daga kallon ta dan baya so tasa ya kasa bata horon da ya dace. Haka tayi ta fama yana tayata kaɗan kaɗan har ta fara iya turawa da kan ta sanna ya mike ya tsaya a gefe ya zuba mata ido tana turawa a hankali hankali matsowa yayi ya bata hot kiss a goshi yana faɗin "Good matar soja tashi muje next" kamar zatayi kuka tace "Yaya Prince dan Allah ka bari sai gobe Wallahi na gaji" girgiza mata kai yayi kafin yace "A'a Eshat da safe training kala uku zakiyi da yamma ki mai mai ta gobe ki sake ɗaukan wasu ukun yanzu muje kiyi gudu zagaye biyar sai ki hau injin kotsa hannu" kwaɓe fuska tayi kamar zatayi kuka ta mike tana ɗinjisa kafa kallo ɗaya yayiwa kafar nata ya kawar da kai dan bai son abun da zai sa yaji jikin sa ya mutu da bata horo kafan nata sunyi ja sosai kamar ka taɓa jini ya fito. Wajen gudu suka wuce yana tsaye ya harɗe hannu a kirji yana kallon ta yace "Fara ina kallon ki" kamar zatayi kuka ta fara gudu zuba mata ido yayi sosai yana kallon ta yana kara jin kaunar ta na shiga ransa.

zagayen farko tayi shi lafiya lou zagaye na biyu ta kawo da kyar a na uku kamar zata faɗi ta kawo tana numfashi sama sama ta zo dai dai gaban sa tana kokarin faɗuwa yayi saurin tarota ya kama hannun ta suka fara gudun tare,da kyar da kyar take numfashin tana hawaye kawar da kan sa yayi ya cigaba da gudu da ita har sai da ta cika zagaye biyar sanna yace "muje wajen motsa hannu" kuka ta sa masa tana faɗin "Dan Allah yaya Prince ka bari na huta" hannun ta ya kama ba tare da ya sake magana ba ya ɗaurata saman mashin na motsa hannu yasa wasu belt ya ɗaure mata hannu ya ɗaure fuska yana faɗin "Oya fara jan sa kasa kina sama da hannu ki" kuka ta ke sosai ta fara da kyar take iya jan hannun ta kasa tana mai da wa sama abun yana da tauri baya jawuwa ta daɗi kawar da kallon sa yayi yana mai jin zafin kukan da take har cikin ran sa bashi da zaɓi dole ya bata horo ko dan kare kan ta. 30mins ta ɗauka tana motsa hannu kafin ya kwance mata hannun nata ya ɗauke cak kamar yar baby yana faɗin "Sorry my Eshat bani da zaɓi ne shi yasa" yana magana yana tafiya da ita suka bar wajen suka nufi hanyar shiga cikin gida tana kokarin yin magana ya gefata cikin katafaren pool dake dake tsakiyar gidan yana girgiza kai da ɗan karfi yace "ki fito da kan ki!" har ɗe hannu yayi a kirji yana kallon ta yadda take fama a cikin ruwan bata iya ruwa sosai ba sai fama take ta kasa fita ta kasa zuwa bakin ruwan ma zuba mata ido yayi yana zin ransa na masa kuna bai san ganin tana wahala bai ankara ba yaga ta fara shan ruwa dan duk gidan wanna pool ɗin ya fi girma ruwan yafi karfin ta a sukwane ya faɗa cikin ruwan ya ɗagota ya ɗaurata saman kirjin sa kan kame sa tayi tana kukan wahala kasa kasa, mikewa tsaye yayi da ita ruwan dai dai kirjin sa ta tsaya masa waje ya fito da ita yana faɗin "Sorry my Eshat" ganin ta gala bai ta sosai yasa ya wuce da ita cikin gida jikin su na zubar da ruwa dai dai lokacin Aryan ya danno hancin motar sa cikin gidan sun dawo daga yawon neman fura da nono tun safe sai yanzu Allah yayi suka samo irin wanda Diyana ke so ya saya mata kala daban daban sai ta ɗan ɗana tace ba shi ba ya sha wahala sosai har yar rama yayi wuni zumbur yana yawo neman fura ita kuwa Diyana tsa ban kyau da tayi jikin ta har wani kwailin yake tana ta sheki ta kara kyau da haske hankalin ta kwance. Tun bai gama kashe motar ba ta fito hannun ta rike da ledojin kayan ciye ciye da kwalama da suka sawo ta wuce cikin gida abun ta. tun daga cikin mota Aryan ya zubawa bgs dake ɗauke da Hiyana ido yana kallon su har suka shiga cikin gida girgiza kai yayi yana faɗin "Allah ya baki ikon kokarin iya jure wanna wahala sister dan nasan bgs ba zai canza magana ba amma abune mai kyau nima zan so jidda ta samu training amma yanzu dai ban isa ba sai gaba" yana cikin zancen nashi ne ya jiyo wayar sa na kiran Sallah alamar lokacin sallar mangariba tayi cikin sauri ya fito ya bi bayan Diyana da ta wuce part nasu ta baza kayan a palo ta fara ci.



To Masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu Masu min comments much kauna 🥰

No comments