Recent Updates

Duk Karfin izzata Book 2 Page 54

 


💋 Duk Karfin Izzata 💋 



💋The talent troupe writer's 💋



Wanna Page ɗin naki ne masoyiya ta GIDAN AUNTY yanzu kuma IBTISSAM All the best my masoyiya fatan samun nasara da cimma burin na Alkhari love you lodi lodi 🥰💔🔐


         By 

            Star Lady



Page 54


Uk

....Yau tun safe jirgin su Ammi ya ɗaga daga uk suka koma Nigeria Khalid Yusuf Fahad Zahra Lamrat Amrat su kuma jirgin su ya ɗaga daga uk zuwa us ba yadda Khalid bai yi da Ahmad akan yazo su koma us ba Ahmad yaki ya kafe akan ba zai dawo us ba sai tare da matar sa Hajjo ba haka su Khalid suka kamo hanyar us ba tare da shi ba shi kuwa ko ajikin sa sai murna yake ya bi su Ammi suka koma Nigeria.


US


Yau tun asuba Diyana ta tashi zazzaɓi mai zafin gaske sai kuka take wa yaya Aryan kasa hakuri Aryan yayi ya fara dubata yayi duk wani gwaje gwajen sa bai ga wani abu dake damun taba ga jikin ta yayi zafi sosai. Daga daga karshe dai ya yanke shawarar yi mata alluran zazzaɓi tare da alluran barci ba jima barci yayi awon gaba da ita ajiyar zuciya yaya Aryan ya sauke ya kwanta kusa da ita tare da jawo ta jikin sa yana jin yadda jikin nata yayi zafi kamar wuta haka ya daure ya manna ta da jikin sa ya rungume ta sosai har barci yayi awon gaba da shi.


Misalin karfe 8 na safe ta farka daga nauyayyar barcin da ya ɗauke ta tun bayan Sallah asuba slowly ta waro manya manyan idon ta waje da kyar ta mike zaune tana bin ɗakin da kallo kamar bakuwa.

a hankali ta zuro kyawawan fararen kafafun ta kasan gadon kafin ta mike ta nufi toilet dan yin wanka.


After 45mins ta fito daga toilet ɗaure da lallausan farin Towel na bgs a kirjin ta gaban mirror ta nufa cikin sauri ta shafa body lotion nashi masu kyau da tsada ga kamshi,ta feshe jikin ta da body spray nashi mai bala'i kamshin daɗi sanna ta wuce dressing room nashi.

Jim kaɗan ta fito shirye cikin dogon wando baki mai stone a jikin sa da wasu manya manyan flowers sky blue daga kafar wandon ta sanya riga top sky blue ta ɗaura jaket a saman kayan na wadda yazo mata har guiwa kasan cewar garin nasu akoi sanyi sosai ta gyara gashin kanta ta ɗaure a tsakiyar kanta,ta zubo jelar gashin har gadon baya ta sanya hular sanyi a kanta flat shoe ta sanya a kafar ta baki ba karamin kyau bakin takalmin yayi a kyakkyawar kafar nata ba kasan cewar farin kafa ya haɗu da bakin ta kalma fitowa tayi ta nufi kitchen ɗin palon kasa. 

Nan ta samu Ilham na zaune saman sofa tana shan Yoghurt mamaki Hiyana take shan Yoghurt da sanyin safiyar nan cikin girmamawa tace"Aunty ina kwana?"washe baki Ilham tayi tana faɗin"Kai Amaryan mu yau kece da kanki kike tafiya ina Oga? Bai ɗauke ki ba"wuce Hiyana tayi ta nufi cikin kitchen tana faɗin"yana wajen motsa jiki"Ilham na son suyi Hiyana na fiskewa dan bata son yawan magana. 

Breakfast mai rai da lafiya ta shiryawa bgs ta ɗauka ta wuce part nasu in da ta bar Ilham a nan ta dawo ta wuce ta. Bayan ta ajiye musu breakfast ɗin ta dawo kitchen ɗin ta ɗauki ruwan lemu tare da ruwan roba guda biyu masu sanyi ta ɗaura saman plate ta haɗa da glass cup ta ɗauka ta fito ta fice daga palon gaba ɗaya tayi waje.


Kai tsaye wajen motsa jikin su ta nufa tana taku kamar mahauniya wajene mai girman gaske ga kayan motsa jiki kala kala awajen injuna da mashunar motsa jiki kala kala acike awajen daga gefe kuma wajen gudu ne mai matikar girma akaware dan gudun motsa jiki an kawata wajen da furanni masu kyau da ɗaukan ido ga wasu kyawawan Towel masu laushi da aka gerewa masu motsa jiki idan sun gama su goge jikin su wajen nan ya haɗu iya haɗuwa idan nace zan tsaya zayyana muku kawatuwar wajen nan to sai mu kwana mu wuni bamu kammala ba.

  

  tun daga nesa ya zuba mata ido ya kasa cigaba da ɗaga karfen da yake waya Aryan ya ɗauka ya fara musu video yana murmushi yana matikar son kallon abun da ke sa bgs farinciki.

 tun tana nesa har ta kariso wajen bai kawar da kallon sa daga kan taba saman table dake wajen ta ɗaura plate ɗin ta ɗauki glass cup ɗin ta buɗe roban ruwan ta zuba masa ta ɗauka ta kariso wajen sa har kasa ta duƙa tace"Ina kwana yaya Prince" mai da karfen hannun sa yayi ya ajiye a mazaunin sa ya mike zaune yasa hannu ya ansa cup ɗin ruwan dake hannun ta ya kafa a ɗan bakin sa ya shanye tas ya ajiye cup ɗin a gefen a nitse yace"Tashi ki zo"cikin sauri ta mike ta matso kusa da shi mikewa yayi ya riko hannun ta suka wuce wajen kananan karfe na yan koyo wajen yan level 1 kenan da hannu ya mata nuni da kananan karfe biyu yana faɗin"ɗauko su" kallon sa tayi da mamaki shi kan shi Aryan dake wajen ɗaga nashi karfen yana musu video yasha ruwan mamaki zuba musu ido yayi yana kallon ikon Allah yana jiran yaga me bgs zai yi.

Hannu ta sa tana kokarin ɗaukan karfen amma ta kasa ɗauka"bar biyun ki ɗauki ɗaya"ya faɗa yana kallon ta hannu biyu tasa da kyar ta ɗauki guda ɗaya ta juyo tana kallon sa tana mai da numfashi"Ɗaga sama mu gani"da kyar ta iya ɗagawa da hannu biyu ya wuce kirjin ta sai nishi take,jinjina kai yayi kafin yace"ajiye muje"da sauri ta ajiye tana mai da mumfashi hannun ta ya rike suka fara gudu awajen gudun nasu mai girman gaske,a sukwane Aryan ya mike ya nufesa yana faɗin"Bgs me kake yi haka"shiru bgs yayi bai tanka sa ba ya cigaba da jan hannun ta suna gudu suna kewaye wajen. Tun tana iya jurewa har ta fara hawaye,cigaba da jan ta yayi suna gudu ba tare da ya lura da hawayen dake kan face nata ba.

Sau biyar suna kewaye wajen a na shidan ne ta kasa jurewa ta fara tangal tangal tana kokarin faɗuwa ta na kokarin yanke jiki ta faɗi cikin zafin nama ya ɗagata da hannu ɗaya ya goyata a bayan sa yana faɗin"Raguwa daga yau zaki fara karɓan horo kullun karfe shida na safe zaki rinƙa tashi ki fara motsa jiki sai kuma karfe 6 na yamma shima zaki motsa jiki zuwa mangariba"kasa magana tayi dan sai numfashi sama sama take wajen table da ta ajiye masa ruwan ya dawo da ita ya sauke ta kasa daga bayan sa ya zuba mata ruwa a cup ɗin da ta bashi ruwa ɗazun ya mika mata yana faɗin"Ansa ki sha"girgiza masa kai tayi da kyar ta iya faɗin"Bazan iya sha ba" "A'a ai dole ki sha"haka ba dan taso ba ta ansa ta sha tana sauke ajiyar zuciya, kallon ta yayi from head to toe kafin yace"ku dai mata baku san motsa jikin ku shiyasa da kun fara girma ku fara korafin baya ko kafa na ciwo to daga yau zaki fara ansan horon sojoji dan karki haifa min ƴaƴa ragwaye"tana kokarin yin magana Aryan ya kariso wajen yana faɗin"Sister jeki cikin gida"kasa tayi da kai tana faɗin"Ina kwana yaya Aryan"tayi maganar tana murje idon ta "Lafiya lou"ya bata amsa yana kallon kafar ta da sukayi ja sosai saboda gudun da tayi"Yaya Aryan ina Diyana"kallon bgs yayi ta kasan ido kafin yace"tana barci"wuce wa tayi ta nufi hanyar shiga cikin gida ba tare da ta sake magana ba tana tafiya tana ɗingisa kafa har ta shige cikin gida.

kallon bgs da kyau Aryan yayi kafin ya fara magana"Amma bgs kasan me kake kokarin yi kuwa? Taya zaka fara koyawa matar ka wanna aikin?"hararar bgs ya wurga masa ya ɗan yi shiru na yan mintoci kamar ba zai yi magana ba sai kuma yace"Ni ko nasan me nake yi kamar yadda kaji na faɗa haka ne daga yau kullun safe da yamma Eshat zata motsa jiki ciki kuma har da koyan harbi da bindiga ni bance zatayi aikin sojaba amma duk wani abu da soja zai yi to zan koya mata"kara waro ido waje Aryan yayi yana faɗin"Why bgs why? Zaka mata haka Sister ba zata iya jurewa horon sojoji ba ka dubi yana yin jikin ta mana wallahi bazata iya ba zata wahala" "Aryan!! Eshat zata koyi aikin soja da duk wani abun sojoji keyi,batun yanayin jikin ta kuma hakan yasa ma zan bata training na aikin soja saboda jikin nata idan ka lura yanayin jikin tan nan yana bukatar ta rinƙa motsa jiki sanna da kake cewa ba zata iya ba babu wanda aka haifa da iyawa kowa koya yayi,ba lokacin guda zan sakar mata komai ba a hankali hankali zan koya mata duk abun da ya dace kana ganin tsabar rashin karfi tana tafiya kamar zata faɗi ai dolema na horar da ita ko ta samu karfi"shiru Aryan yayi yana nazarin maganganu bgs"tabbas ta wani ɓangaren bgs yana da gaskiya amma idan akayi laakari da yanayin sister ita kaɗai ma tana tafiya kamar zata faɗi bazata iya ɗaukan horon sojoji ba"Aryan yayi nisa cikin tunani da zancen zuciya bgs ya katse sa da cewa"meke damun Diyana?"yar firgigit yayi kafin yace"Bgs dan Allah kabar sister sai gaba ka fara koya mata"shiru bgs yayi na yan mintoci kafin yace"Na gama magana akan Eshat karka sake dawo min da maganar yanzu dai tambayar ka nayi meke damun Diyana?" "Wallahi ban sani ba nayi duk wani gwaje gwaje da zan mata amma duk a banza ban ga komai ba" "ka mata pregnant test ne?"da sauri Aryan ya girgiza kai yana faɗin"A'a ban yi mata ba"ɗaukan ɗan ƙaramin Towel dake gere awajen bgs yayi yana goge gashin kan sa da zufar dake bin wuyar sa ya nufi cikin gida. Sai da ya kai bakin kofar fita waje ba tare ya tsaya da tafiyar da yake ba yace"Kaje ka mata"cikin sauri Aryan ya dauki ƙaramin towel yabi bayan sa. 

Kusan tare suka shiga palon kowa yayi part nashi.


Aryan na shiga bedroom nasu ya fara aikin yiwa Diyana gwajin ciki ɗiban jinin ta yayi ya fito ya wuce ɗakin kula da kansu duk abun da yake tana barci sakamakon Alluran barcin da ya mata. 


A ɓangaren bgs kuwa lokacin da ya shiga ɗaki zaune bakin gado ya isko Hiyana tana faman matse kafar ta tana kwalla gently ya tako zuwa gaban ta tare da zama gefen ta ya sanya kyakkyawar hannun sa ya kama kyakkyawar kafan nata ya fara matsa mata a hankali hankali yana kallon face nata,cike da so da kaunar ta ya fara magana"I'm sorry my Eshat"faɗowa jikin sa tayi tana kuka kasa kasa shafa kan ta ya fara yi ya cigaba da magana"kimin alkawari zaki koyi duk abun da zan koya miki hakan zai sani farinciki sosai ba aikin soja zakiyi ba kawai zaki ɗan rinƙa motsa jiki ne ko in ce zamu rinƙa motsa jiki tare dan ki samu karfi sosai sai kuma harbi da bindiga da zan koya miki dan kare kan ki ban sani ba ko zan rayu da ku har yarana su girma ko kuma zan mutu to koma dai me ina da bindiga masu register wadda ko bana nan idan an kawo muku hari zaki iya kare ku ta hanyar harbi da bindigar kinji?" Kara shigewa jikin sa tayi tana faɗin"Yaya Prince akoi wahala ba zan iya ba"rungumeta yayi sosai yana faɗin"zaki iya my Eshat a tare zamu rinƙa yi a hankali zan koya miki komai yanzu dai ki amince min zanyi farinciki da hakan"shiru ta ɗan yi kafin tace"tom shike nan zanyi yadda kake so"ɗaukan ta yayi cak ba tare da ya sake magana ba ya wuce da ita saman sofa mai zaman mutun 3 ya ɗaura ta ya juya ya nufi toilet yana faɗin"ki fara breakfast bari nayi wanka"mikewa tayi ta kwanta tana jiran shi shi kuma ya wuce toilet dan yin wanka


A ɓangaren Aryan kuwa


Gwajin farko ya nuna masa Diyana na ɗauke da ciki sati 2 dukawa yayi awajen cike da murna yayiwa Allah sujudur shukur yana ɗagowa cikin sauri ya ciro wayar sa ya kira layin bgs wayar na ta ringing bgs bai ɗaga ba har sai da wayar ta kusa katsewa sanna bgs ya ɗauka tsabar zumuɗi da farinciki ko sallama bai wa bgs ba yace"My blood My jidda tana da ciki oh my god yau ji nake kamar an min albirushir da gidan aljanna"katse kiran bgs yayi ba tare da yayi masa magana ba ya mike ya dubi Hiyana dake zaune tana cin chips yace"ki cigaba da breakfast ɗin ina zuwa"bai jira amsar taɓa ya fice daga ɗakin ya nufi ɗakin binciken sa.

Yana shiga ya buɗe wani ɗan karami ɗaki dake cikin ɗakin binciken ya shiga jim kaɗan ya fito hannun sa rike da wata yar jaka mai shegen kyau ya fito kai tsaye part ɗin su Aryan ya nufa yana farinciki.

  yana kokarin shiga yajiyo muryan Aryan daga bayan sa yana faɗin"My blood yau Allah ya amsa min addu'a ta"hannu bgs ya miƙa masa sukayi musabaha sanna suka rungumi juna dukkan su suna cikin matsanancin farinciki ji suke kamar an musu albashi da gidan aljanna raba jikin su bgs yayi yana faɗin"Congratulations my blood ina ganin nafika murna"murmushi Aryan yayi yana faɗin"Thank you my blood amma dai baka fini murna ba"miƙa masa jakar hannun sa bgs yayi yana faɗin"ka bawa Diyana sabon godiya ta farko kenan ta gama mana komai ina farinciki yau sosai inaga na jima banji daɗi irin na yau ba na ma rasa kyautan me zan maka kai ita dai Diyana ka mika mata wanna godiya saura Khalid da Yusuf" "wani Khalid da Yusuf ɗin? To ai ina ga ma yanzu cikin matar Yusuf ya kai wata 3 zuwa sama haka ita ma Auta cikin ta zai kai 2 Month"waro ido waje bgs yayi yana kokarin yin magana sukajiyo kakarin amai na Diyana wucewa bgs yayi ya koma part nasu yana faɗin"Ana kiran ka aciki"cikin sauri Aryan ya shige cikin bedroom nasu a tsakiyar ɗaki ya sameta ta duƙa tana tikar amai da alama aman yafi karfin tane ta kasa isa toilet cikin sauri ya karisa wajen tare da ajiye jakar da bgs ya bashi a gafe yasa hannu ya ɗagata cak suka nufi toilet gaba ɗaya ta ɓata masa jiki da amai dan har suka isa toilet bata dai na tikar amai ba. A tsakiyar toilet ya sauke ta yana kokarin wucewa ya haɗa mata ruwan wanka ta kankame sa dan jiri take gani kukan ta sa masa tana faɗin"Yaya Aryan zan faɗi"tayi maganar cikin kasalalliyar murya riketa yayi da kyau ya ɗagata ya ɗaurata saman gefen baf ɗin wanka cikin sauri ya fara haɗa mata ruwan. Bayan ya gama haɗa ruwan yana kokarin ɗagata amai ɗin ya sake dawowa da karfi ta fara kwara amai ɗin a cikin baf ɗin wankan gaba ɗaya ta ɓata ruwan wankan tana kokarin faɗuwa saboda aman ta yaci karfin ta yayi saurin rikota yana faɗin"Sorry mai jidda"wahalallan kuka ta sa masa tare da riko shi kam tana mai da numfashi,kallon cikin ruwan wankan yayi kafin ya dawo da kallon sa kanta ya rasa ya zai yi ya zubar da ruwan ya haɗa mata wani dan aman Abincin da taci jiya da daddare tayi shiru sukayi dukkan su biyu shi yana tunanin yadda zan yi da amai nan ita kuma tana fama da murɗan da cikin ta keyi


To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu

No comments