Recent Updates

Duk Karfin izzata Book 2 Page 49

 


💋 Duk Karfin Izzata 💋 



💋The talent troupe writer's 💋




         By 

            Star Lady




Page 49




KANO


ABBA & AMMI


zaune suke a palon sa su biyu suna hira cikin nitsuwa Abba yace "Aisha ina son ki bani hankalin ki sanna ki bani nitsuwar ki ki sa aranki komai ya faru da bawa mukaddari ne daga Allah sanna ki É—auki hakan a matsayin jarabawa" shiru Ammi tayi ta tattara hankalin ta dukka ta bawa Abba kirjin ta na dukan uku uku dan tun da taji Abba yace hakan tasan ba lafiya ba,cigaba da magana Abba yayi "kuskure dai mun riga munyi duk da cewa haka Allah ya kaddara amma nima ina da nawa laifin ni nake hana ki zuwa kallon yan uwan ki har abubuwa suka rinÆ™a faruwa wallahi rashin zumunci bai yi ba kwata kwata,ko da sau É—aya ne a sati ya kama ka rinÆ™a wai wayan yan uwanka ko ka kirasu awaya dan jin ya suke amma ke na hana ki zuwa wajen yan uwan ki tsawon shakara 7 zuwa 8 ina mai baki hakuri ta wanna É“angaren ki min afuwa" ita dai Ammi shiru tayi ta zuba masa ido zuciyar ta na dukan uku uku burinta kawai taji me Abba ke son sanar da ita "fateema ta sanar min É—azun habiba ita ta kashe mahaifin su hiyana da hannun ta yanzu mun sa jami'an tsaron sun kama ta" zubur Ammi ta mike tana faÉ—in "what!? Habiba ne ta kashe Ahmadu da hannun ta!!?no ba wasu yan sanda da Za'a haÉ—a ta dasu ni da nake da hukuma da doka gaba É—ayan ta a gida dole ta karÉ“i hukunci dai dai da abun da ta aikata a É—aure min ita ba wanda zai mata hukunci sai Safras shine dai dai zai iya hukuntata akan abun da tayi"mamakin yadda Ammi ke magana har da kiran sunan bgs ya hana Abba magana da alama yau Ammi ta fusata sosai ta fita hayyacin ta"A'isha koma ki zauna" ba musu ta koma ta zauna tana faÉ—in"ban yarda kowa ya taÉ“a habiba ba idan ba Safras ba shine zai iya yi mata hukunci dai dai da abun da tayi dan bana son amata kisan farat É—aya" "A'isha habiba tayi laifi dayawan da dole ta ansa hukunci kisa ni da kai na nace a rufe ta sai komai ya dai dai Safras ya dawo hayyacin sa ya mata hukunci habiba ita ta haukata Hajj fateema sanna ta haukata diyana ta azabtar da su hiyana bayan nan ga laifin zina ga shirka babban laifi fiye da komai a duniya haÉ—a Allah da wani wa iya zubillah bayan nan ga kisan kai ai dole habiba ta karÉ“i hukunci kisa taje can lahira ta samu Ubangiji data haÉ—a da wani ya mata nashi hukunci,shirka shirka shirka babban laifi ne number 1 a duniya wadda idan kana aika tashi ka mutu ba makawa jahannama kai tsaye zaka tafi babu wanda Allah ya tsine masa sau biyar a Qur'ani sai boka ai idan mutun yana da hankali ma wallahi ko sau É—aya Allah ya tsine wa mutun bazaka kusancesa ba bare har sau biyar kai jama'a ya kamata murinÆ™a tunawa zafa mu mutu muje mu samu Allah da kuke haÉ—awa da wani awanna lokacin shi kan shi wanda ka haÉ—a da Allah neman ta kansa yake yana neman Rahman Allah kuma ba samu zai yi ba daga shi har masu binsa zasu samu azaba mai tsanani basu samu Rahman Ubangijin ko É—igo,ya Allah ka kiyashe mu haÉ—a Allah da wani Allah ka bamu ikon rike ka kai ka É—ai" "Amin ya Allah" Ammi ta amsa da shi,cigaba da magana Abba yayi "sanna magana ta gaba Aisha yau kwanan 16 ke nan da accident na su Safras ina son ki sani ba accident su kayi ba zan faÉ—a miki hakan ne ba wai dan ki tada hankalin ki ba ko kice zaki shiga tsakanin mata da miji zan faÉ—a miÆ™i ne dan ki kaiwa hiyana agaji dan har yanzu bata ko motsi idan har na isa da ke karki tofa wani magana mara daÉ—i cikin maganar nan dan Safras yayi nadama abun da bai taÉ“a a rayuwar sa saboda son hiyana ya kwanta a hospital nan dukka yaran nan a tunanin su na haifesu ne kawai basu san cewa dasu nake kwana dasu nake tashi a rai na ba duk abun da suke akan ido na suke komai abun da ya faru Safras ya kusanci hiyana cikin fushi bayan haka baya cikin hayyacin sa shine aka samu matsala yanzu tana gidan sa na us karki nuna musu kamar kin san komai ki kyale su a matsayin accident É—in yanzu ki shirya kije ki kula da hiyana tana bukatar kulawar uwa kusa da ita duk da cewa har yanzu bata farka ba amma komai na jikin ta ya dai dai ta bugun numfashi ta ya dai dai ta sai dai ciwo da bazaa rasa ba zata iya farkawa akowani lokacin awanna lokacin tana bukatar kulawar uwa da kuma soyayya kin san irin wanna abun idan ya faru da mutun wuya mutun yake rayuwa idan ya rayu kuma wani sai kiga ya farka da taÉ“in hankali saboda razana da yayi bana fatan hakan ya faru da ita ina fatan ta farka lafiya lau nasan zataji tsoron Safras sosai karki bari wani magana na Safras ya je kunnen ta kisa ta manta da Safras har sai komai ya dai dai ta sai ta samu sauki sosai a hankali zamu komar da ita dai dai kuma mu nuna mata Safras na son ta da gaske"tsabar  tausayin hiyana Ammi bata san lokacin da hawaye ya fara bin kumatun ta ba"haba Aisha menene abun kuka addu'a zaki mata ki shirya da wuri amma ina son ki san wani abu É—aya duk in da Safras yake zai zo wajen ku dan yanzu ma bai yarda hiyana ta mutuba yanzu haka yana gadon asibitin ma yana bincike akan ta tabbas zai zo duk da nasa a canzawa hiyana gida Aryan yayi kuskuren kai ta gidan Safras,yanzu cikin sauki Safras zai gane tana raye shi da yake da Camera a gidan da bana shi ba ina ga gidan sa kuma kin san akoi Cameran kuma yana bincika Cameran tabbas zai ga kwanciyar hiyana a gidan sa tayi jinya dan haka zai nemota ko ina ne shiyasa ban wahalar da kai na wajen kai ta wani kasa ba na barta a us É—in dan nasan ko ina na kai ta zai nemota ni wani lokacin ma kai fin Æ™waÆ™walwan Safras na bani mamaki da tsoro idan ya tsaya yayi tunani akan abu tofa komai wuyar abu sai ya samo solution akai ina fatan kafin ya bar asibiti ya fara neman ta Allah ya bata lafiya sanna idan ya zo gare ku karki shiga tsakanin sa da matar sa koda tana jin tsoron sa ki basu waje shiya san yadda zai shawo kanta dan duk duniyar nan yanzu shi kaÉ—ai zai iya sa hiyana ta sauko ta yarda da shi yasan yadda zai yi ya gyara abun da ya É“ata dan haka ki basu waje ki musu fatan alkhari dan yanzu ban son abun da zai sake É—aga wa Safras hankali saboda yanayin da yake ciki ba zan iya jure ganin sa cikin tashin hankali ba nafi son sa fiye da komai yanzu a rayuwata ki kula da hiyana sosai dan Allah"shiru Ammi tayi tana mamakin wanna lamari "lallai Safras bai kyau taba amma ba yanda zanyi dole nabi umarnin mijina dan naga dai dai a rayuwa" da wanna tunanin ta mike ta fice daga palon,dogon numfashi Abba yaja tare da sauke ajiyar zuciya kafin ya mike ya shiga bedroom nashi


*Uk*


Zaune Aryan yake kusa da bgs yana fuskantar Aunty farida dake zaune saman lallausan kujerar dake cikin ɗakin hospital ɗin ba laifi bgs ya samu sauki sosai sai dai yanzu ya koma gidan jiya da rashin magana dan idan Aryan zai kwana yana masa magana sai ya ɗauki mintoci kafin ya ɗaga musu kai ko ya girgiza kai amma magana da baki kam shiru kake ji abun har ya fara bawa aunty Farida tsoro dan gwara da abaya ma idan kawa bgs magana ko da zai ɗauki mintoci amma zai amsa maka da baki saɓanin yanzu sai dai ya ɗaga kai kwata kwata bai san ana magana kusa da shi,dan isu magana da Aryan har dafe kai yake alamar sun dame sa tun ranar daya farka ya tambayi ina hiyana Aunty farida tace masa ta rasu tun lokacin bai sake magana ba suyi magana har su gaji baya amsawa har sun fara sabawa da yanayin sa.

Shiru suka zauna kowa da abun da yake tunani mikewa bgs yayi ya cire ruwan da aka sa masa tare da zuro kyawawan kafafun sa kasa ya mike tsaye ya rame sosai kamar ba shi ba"bgs ina zakaje? Cewar Aryan shiru yayi ko kallon in da Aryan yake bai yi ba ya wuce ya nufi hanyar fita daga É—akin kallon Aunty farida Aryan yayi yana kokarin yin magana Aunty farida ta rigashi da cewa"lallai Prince shi ciwon ma karo masa sabon wulakanci tayi eyee ko kallo bamu ishe saba kenan?"girgiza kai Aryan yayi kafin yace"aa Aunty farida kin san fa daman can haka yake saboda sister yasa ya sauya ya fara magana to yanzu dai sai kuyi hakuri sai komai ya dai dai ta sister ta dawo kila mu dace ya dawo ya cigaba da magana ko ba yawa ne"hararar sa Aunty farida tayi tana faÉ—in"dama ya za'ayi ka ansa laifin Prince tun da bakin ku É—aya sai ka tashi muje ai wai masu jinya ne,mara lafiya ya tafi ya barmu a shanye kamar wasu babbakankun kaji"mikewa Aryan yayi ba tare da ya sake magana ba mikewa itama tayi suka jera suka bi bayan bgs.

 lokacin da suka fito ba bgs kuma ba Fahad dake zaune a wajen,da sauri suka nufi parking space na hospital É—in suna mamaki wato shi bgs bazai ma jira asallame su ba. 

Ko da suka je ba su bgs kuma ba motar Fahad tsaki Aunty farida taja kafin ta wuce ta nufi nasu motar shi Aryan abun ma dariya yaso bashi. Suna cikin tafiya a kule Aunty farida tace "lallai Fahad wato shima har da bin Prince ɗin duk sun haɗu sun mai damu mahaukata" "haba Aunty farida wlh ba haka bane ina da tabbacin bgs yace zai yi tuki da kansa ne Fahad yace bari ya tukasa gudun kar asamu matsala tun da ba gama samun lafiya yayi ba kin fa san halin bgs dan Allah karki ga laifin Fahad ko nine a matsayin da Fahad yake abun da zanyi kenan" "hmmmm bayan bakin ku ɗaya ke nan ba"shiru Aryan yayi bai sake magana ba dan yasan Aunty farida bazata taɓa yarda ba.


After 1 week


Tsaye yake gaban desktop computer sa yana bincike alokacin Aunty farida ta komai Nigeria ya rage daga Aryan da jiddan sa sai Fahad da amrin sa,har lokacin hiyana bata ko motsa ba yanzu kwanan ta 23 a sume, da sallama Aryan ya shigo ɗakin binciken nasu ganin abun da bgs ke bincika yasa yaja da baya ya koma waje dan yasan in ya kariso bazasu wanye lafiya ba. Yana fita ya ɗauki jiddan sa kamar yar baby suka bar gidan dan bashi da amsan da zai bawa bgs shi da kansa bai san in da Abba ya mai da hiyana ba gashi kuma bgs yaga lokacin da ya shigo da ita gidan sa na us yaga lokacin da aka fita da ita ba makawa shi zai kama ya tambaya ina take. Wanna tunanin yasa ya bar gidan tare da jiddan sa wani tampatsetsen hotel yaje ya kama musu dan su ɓuyan wa bgs.


A ɓangaren bgs kuwa waro ido sosai yayi yana ganin aika aikan da yayiwa hiyana ta cikin system nashi sosai ya kara nadamar abun da yayi mata harcikin ransa yake jin zafin abun tunani ya farayi wanene ke tare da hiyana dan ya datsi layin wayar sa ko Cameran wayar sa dan sanin in da suke yasan dai bazaa barta ita ka ɗai ba dole tana tare da wani cikin family bayan wanna likitan daya gani.


cikin sauri ya fara datsan wayar dukka yan gidan tare da Camerorin su can ya hango Aryan a hotel rungume da jiddan sa tsaki yaja ya wuce su ya cigaba da datse datsen sa ya gwada Ummi ba ita ke wajen hiyana ba ya gwada hajj fateema dan ya É—auki number ta a wayar Ummi da ya datsa ita ba ita bace dan tana gida kwance bata ma san meke faruwa ba anki faÉ—a mata an rufe mata dan kar abun ya mata yawa ya jarraba aunty Farida ba ita bace bai taÉ“a kawowa Ammi ce zata je kula da hiyana ba dan yasan duk wani abu da ya shafe sa Ammi bata shiga that's why bai tuna ita É—in bace sai da ya datsi wayar kowa dake gidan harda mazan su Omar daga karshe sai yace bari ya gwada na Ammin dan ya gani ko dai awan nan karon ta shiga masa gwajin farko wayar Ammi ya nuna masa location us waro ido yayi cikin sauri ya shigar da bayanan wayar Ammi system nashi tare da datsar Camera wayar ta kyakkyawar face É—in kyakkyawar matar sa ya fara cin karo da shi tana kwance bata ko motsi tayi kiba sosai saboda ruwa da jinin da aka ta sa mata zuba mata ido yayi sosai yanajin kaunar ta na ratsa shi kasa kasa "yace forgive me My Eshat forgive me nayi kuskure na miki laifi sosai" kamar a mafarki yaga ta fara motsi ajiye wayan Ammi tayi saman table hakan yasa baya ganin ta sosai cikin sauri ya fara bincikan location É—in dan yaga ko akoi Cameran awajen yayi Sa'a kuwa hotel É—in akoi Camera cikin sauri ya datsi Cameran su hakan ya bashi damar kallon É—akin gaba É—aya a hankali hiyana ta fara motsi idon ta a rufe ta fara sambatu ga Ammi ta matso kusa da ita ga dr a gefe tana zaune "yaya Prince ba zan iya ba akoi zafi mutuwa zanyi yaya Prince zan mutu na tuba ba zan sake ba ina son ka wlh ba zan sake cewa bana son ka ba ba zan sake fita ba kayi hakuri ka barni haka bazan iya jurewa ba zan mutu mutuwa zanyi"karo na farko arayuwar sa hawaye ta fara bin kuncin sa yau ne first time da yayiwa wani É—an adam kuka kawar da kai gefe yayi yana kara danasanin abun da ya aikata,ita kanta Ammi sai da tayi wa hiyana hawaye a karo na biyu. 


rungumota Ammi tayi kasa kasa tace "A'isha kiyi hakuri kinji kiyi kokarin kici jarabar da Allah ya jaraɓceki"jin muryan Ammi tayi kamar voice ɗin bgs dan haka sai ta kara birkichewa ta mike da iya karfin ta tana faɗin "dan girman Allah yaya Prince ka kyale ni haka idan kai baka sona wallahi na san Ammi na Ummi na su aunty Farida suna sona dan Allah ka kyale ni haka" "A'ishah nice fa ba Safras ba" ai Ammi na kara magana ma kara haukata ta take dan yau ganin face ɗin bgs take a fuskar Ammi kai ba Ammi kaɗai ba har dr dake zaune kallon face ɗin bgs take a fuskar su kokarin guduwa take ta fita daga ɗakin cikin sauri dr ta riko ta tana faɗin "i think yarinyar nan ta samu problem a kwakwalwa fa"waro ido waje Ammi tayi tana kokarin magana hiyana ta katse su da cewa "yaya Prince ka sake ni ka sake nace karka kashe ni dan Allah ka kyale ni haka wallahi mutuwa zanyi idan ka sake taɓa ni"hawaye sosai bgs yake yana kallon duk abun da ke faru ba karamin haushin dr ya ji ba da take cewa hiyana ta zare ciro wayar sa yayi ya ɓoye number ya kira Ammi dan yasan idan ya kirata da number sa bazata ɗauka ba yayi Sa'a kuwa ganin private number yasa ta ɗauka da kyar ya iya magana saboda kukan da yake "Ammi dan Allah karki katse ina son ku fita ɗakin ku barta ita ka ɗai dan a razane take tana tsorace sosai fiskana shine abu na karshe data kalla kafin ta shiga doguwar suma that's why take kallon face na a tattare da kowa ku kyale ta na yan mintoci ko 1h zata dawo dai dai idan baku fita kun kyale ta ba zata iya birkicewa gaba ɗaya"yana kai karshen maganar ya katse kiran dan ba zai iya jin zagin ta da Ammi zata masa ba,ajiye wayar ita ma Ammi tayi ta dubi dr tace"sake ta muje"ba musu dr ta kwantar da hiyana a gado suka fita suka ja kofar suka rufe ta ta baya mikewa zaune hiyana tayi a tsakiyar gadon ta haɗe kafafun ta ta kifa kai da guiwa ta fara rera kuka tana sambatu kamar zararriya"ni wai me nayi wa duniyar nan ne da duniyar bata sona daga wanna wahalar sai wanna daga wanna sai wanna innalillahi wa inna ilaihir rajiun ya Allah na tuba na tuba ka yafe min yaya Prince kai ne mutumin dana fiso bayan iyaye na amma yanzu sai da kasa naji ba wanda nafi tsana a duniya biyun ka gwara nayi haɗu da malakul maut dana sake haɗuwa da kai yaya prince arayuwa ta"tana sambatu tana kuka,kamar yadda take sambatu tana kuka haka shima bgs yake yana sambatu yana hawaye"I'm sorry my Eshat tabbas daga yanzu wahala ki ta kare In Sha Allah zan baki kulawa fiye da yadda zan kula da rayuwa ta nayi laifi dayawa amma duk laifina duk tsanata da kikayi hakan ba zai hanani zuwa gare ki ba ki shirya ansan masoyin ki gani nan zuwa"ya kai karshen maganar tare da goge hawaye face na shi ya fito daga ɗakin ya fice waje kai tsaye ya shiga mota ya nufi Airport.


Kwana biyu yayi a us ba tare da ya karisa wajen da su Ammi suke ba yana zulumin isa in da suke dan bai san ya hiyana zata an she sa ba a wanna kwana biyun hiyana ta kara samun sauki ta dawo dai dai ba laifi sai dai itama bata cika magana ba daga um sai umm take cewa ko idan an mata magana ta girgiza kai.


yauce ranar sa ta uku a us ya shirya cikin kayan hausawa dakakkiyar shadda fara tas mai bala'i tsada da hula baka sai takalmi baki ya sanya dangareren agogon diamond mai matukar kyau da tsada a kyakkyawar farin hannun sa yau yayi kyau sosai kamar shi yayi kan sa sai kamshi yake zuwaba sosai kamar ango ya rage tsawon gashin kansa ya bari zuwa wuyar sa sanna ya nufi hotel É—in da su Ammi suke.


Mamaki ne ya kama shi lokaci da ya isa hotel ɗin Aunty farida Aunty mardiya Aunty salma Ummi Ammi Aryan Fahad diyana amrat Khalid Zahra Yusuf lamrat Abba duk sunzo Omar Haidar Hajj fateema ce kawai ba su zo ba dan su basu ma san meke faruwa ba sai Aisha yar Sadiq da Zainab suma suna gida basu zo ba karo ta farko a rayuwar sa yaji kunya ta kama sa ji yayi kamar ya koma ji yayi da yasan zai samu family gaba ɗaya da bai zo ba dukkan su suna dakin da hiyana take, hiyana na zaune saman gado tana sanye cikin doguwar riga abaya baka ba ƙaramin kyau kayan suka mata ba kan ta babu ɗankwali ta zuba bakin lallausan gashi tan nan har gadon baya tayi kumatu abun ta mul mul gwanin ban sha'awa tayi haske sosai kamar ka taɓa jini ya fita diyana da Zahra sun sata a tsakiya aunty Farida na gefen su sauran family wasu suna saman sofa wasu saman gadon Abba na zaune kusa da Ammi saman sofa Ummi na gefen sa.


gently ya sako kafar sa cikin ɗaki ta kasar ido yake satar kallon hiyana yar kiban da tayi ta masa kyau ba kaɗan ba ji yake kamar yaje ya rungumo kayan sa amma ba hali. wucewa yayi yaje ya gaida Abba da Ammi da Ummi da fara'a Abba da Ummi suka amsa har mamaki yake ya fara tunanin "to ko dai basu san me ya aikatawa hiyana bane" Ammi kuwa fuska a ɗaure ta amsa dan har yanzu idan ta tuna yadda tazo ta samu halin da hiyana ke ciki sai taji idon ta ya tara ruwa,da fara'a Aunty Farida tace"ango ina wuni"mamaki ya hana shi amsawa gani yake kamar mafarki yake,cikin girmamawa su Aryan suka ɗaga masa gaisuwa hararar wasa ya wurgawa Aryan a ransa yana faɗin"daman kana gaishe ni ne idan ba awajen aiki da ya zama dole gaisuwar ba",bai gama mamakin gaisuwar su Aryan ba yaji yo zazzakar voice ɗin hiyana tana fadin"ina wuni yaya Prince"waro ido waje yayi a sukwane ya kai kallon sa kan kyakkyawar face nata dan ko a mafarki bai taɓa tunanin hiyana zata masa magana yanzu ba,bai ankara ba yaga gaba ɗaya family sun mike sun fice daga ɗakin sun basu wajen,


suna fita hiyana ta ɗaure fuska sosai kamar ba ita ke hira da murmushi dasu diyana yanzu ba mikewa yayi ya dawo kusa da ita ya zauna cike da so da kauna yace"Eshat ban taɓa tunanin zaki min magana yanzu ba all my thought har yanzu kina fushi da ni"a kule tace"dan ganin idon su Abba yasa na maka magana ba dan wani abu ba"juyowa yayi da kyau suna fuskantar juna calmly ya fara magana"i know Eshat nayi miki kaifi sosai na san mawuyacin abu ne ki manta da abun da na miki amma ina son ki sani ilove u from the bottom of my heart nake faɗa miki maganar nan ki yarda dani"shiru tayi bata sake magana ba ta sunkuyar da kai kasa tana wasa da yatsun hannun ta"my Eshat ya jiki?"nan ma shiru ta masa "my Eshat ɗago kai ki kalle ni kinji?"Kara sunkuyar da kan ta kasa tayi dan aduniya ba abun da yake bata tsoro yanzu kamar fiskar sa"my Eshat ki min magana mana "kasa kasa ba tare da ta ɗago kai ba tace"yaya Aryan ya faɗa min komai jiya ya zo ya nuna min video ka lokacin da ya zo ya same ka ka shake likita sanna Aunty farida ma ta nuna min video kwanciyar da kayi a asibita da ranar da ka farfa to amma ni duk da haka ban yarda ba kuma ba zan zauna da kai ba"waro ido waje yayi da sauri yace"Eshat kenan baki yarda ina son ki ba" "eh ban yarda ba kuma ba zan taɓa yarda da kai ba"tana kai karshen maganar ta mike ta nufi hanyar fita tana ɗingisa kafa da sauri ya rikota tare da jawota ta faɗa saman faffaɗar kirjin sa hannu yasa ya ɗago habar ta yana kallon face nata"my Eshat me zan miki ki yarda ina son ki?"yunkurin tashi take a jikin nasa take tana ture sa tana faɗin"ni ba wani abun da zaka min na yarda babu wani sauran yarda kuma tsakanin mu"zuba mata ido yayi yana kallon yadda take motsa ɗan karamin kyakkyawan bakin ta tana masifa ganin da gaske take son tashi daga jikin sa sai ya sake ta ta mike tana ɗingisa kafa ta fice da daga ɗakin,bin bayan ta yayi da kallo har ta fice kafin ya sauke nauyayyar ajiyar zuciya yace"ba dai kin fara saukowa ba bazan takura miki ba a hankali zan dawo miki da sona da kike ikirari ya koma kiyayya sai kin zamo idan baki ganni ba bazaki iya barci ba bari dai mu koma gida"ya kai karshen maganar tare da mikewa shima ya fito nan ya samu su Abba a palo suna hira wuce su yayi ya nufi waje kasa kasa hiyana ke satar kallon sa har ya fice, murmushi Aryan da Aunty farida keyi dan duk abun da hiyana ke yi suna kallon ana so ana kai wa kasuwa



To Masu karatu sai mun haÉ—u gobe idan mai dukka ya kai mu

No comments