Duk Karfin izzata Book 2 Page 46
💋 Duk Karfin Izzata 💋
💋The talent troupe writer's 💋
By
Star Lady
Page 46
Ba karamin É“acin rai Abba ya shiga ba sai dannan sa Hajj fateema da Aunty farida suke shiko Aryan tun jiya da ya tafi shiru shiru ko kiran su awaya bai yi ba. "Abba dan Allah ka dai na sawa kanka É“acin rai haka bamu son ganin ka cikin damuwa, yanzu dai muyi hakuri mujira mugani zasu dawo ko da haka sun sallame mu"cewar Hajj fateema a kule Abba yace "ni ba É—aukan ta da yayi suka tafi bane ya É“ata rai abun da ya batan rai shine yau rana ta farko na zana layi wani daga cikin Æ´aÆ´ana ya tsallaka kuma a cikin Æ´aÆ´an nawa ma wadda nafi kauna fiye da komai shi ya tsallaka layin da na zana abun yamin ciwo sosai sannan kuma ina son sanin ko suna lafiya dan duniyar yanzun nan kana tare da yan uwan ka lafiya kana É—an bada baya sai kaji wani abu ya faru to gaskiya ina son sanin wani hali suke ciki ai na suke dan wlh tun jiya zuciya ta ke bugawa ina jin ajikina kamar wani abu ya faru dan a banza haka Safras ba zai kashe duk wata layin da za'a same sa ba" shiru hajj Fateema ta É—an yi dan ita kan ta idan ta tuna hiyana sai gaban ta ya faÉ—i ajikin ta tana jin ba lafiya ba dannewa kawai take saboda dalilai biyu na farko hiyana ce yar farin ta na biyu kuma karta tada hankali ta karawa su Abba tashin hankali ban da haka ita kanta cikin damuwa da tashin hankali take kirjin ta sai dukan uku uku yake.
Har karfe 1 na rana Abba na tare da su Aunty farida yau ko fada bai je ba dan É“acin rai a É“angaren Ammi ma hakan take ta shiga damuwa sosai
karfe 1:30 bayan sunyi sallar azahar Abba ya haÉ—a family sa gaba É—aya a palon sa banda Hajj fateema kasan cewar ita bata samu yin Sallah akan lokaci ba tana É—akin Ammi tana sallar azahar.
Kallon Khalid Abba yayi yana kokarin yin magana Hajj fateema ta shigo bakin ta ɗauke da sallama tare da wani kyakkyawar balarabe dogo fari tas mai bakin saje yana rike da hannun kyawawan yara biyu farare tas masu kama da shi ga wasu kyawawan yammata kan su ɗaya su uku suna biye da su abaya kallo ɗaya zaka musu ka gane raina ta zauna musu. Da fara'a Abba ya tarbe su har gaban Abba Abu Abdurahman yaje ya duka ya bawa Abba hanu suka gaisa sauran yan matan da yazo da su kuwa sai kallon banza sukewa su Aunty mardiya suna kwaɓe fuska dan basu san kowa awajen ba.
lokacin da idon babban cikin su ya sauka kan Fahad dake zaune yana latsawa waya ba karamin girgiza tayi ba dan atunanin ta bgs ne ihu ta fasa tana ja da baya tana faÉ—in "Oum Ayaam see this man here" a tare gaba É—aya mutanen palon suka zuya suna kallon in da take nunawa ganin Fahad ne yasa Hajj fateema tayi murmushi taje ta rungumota tana faÉ—in "Fariza calm down this is not Safras" shiru Fariza tayi sai lokacin ta lura ba bgs bane dan bgs yafi Fahad murÉ—aÉ—en jiki da kuma tsawo da cika,amma duk da haka fariza a tsorace take taki sakin jikin ta shi kanshi Abu Abdurahman ya girgiza lokacin da ya gane nan ne gidan su Safras cikin harshen turanci yace "dan girman Allah ku nunamin wacece mahaifiyar jarumin na mijin nan gaskiya Safras duniya ne duk in da ake neman namiji Safras ya kai ina son inga wadda tayi sa'ar haifan wanna É—aya tamkar da dubun" kallon Ammi Aunty farida tayi kafin tace "ga mahaifiyar sa nan" a sukwane Abu Abdurahman ya kai kallon sa kan Ammi "eh tabbas mahaifiyar sa ce ga kamanni nan wow gaskiya madam ke mai Sa'a ce ina tayaki murnan samun wanna babban kyau da Allah ya miki na É—a Safras zakin duniya" Abu Abdurahman ya washe baki sai dariya yake yana yabon bgs bai ma san yau gaba É—aya Abba da Ammi hau shin bgs suke ji ji suke kamar su shakosa dan saushi cikin sauri Abba ya canza topic É—in hirar cewa "Abu Abdurahman muna son ka sanar damu in da ka samu Hajj fateema har ka Aure ta" Abba yayi sauri canza topic É—in hirar ne dan bayason Abu Abdurahman ya cigaba da musu zancen bgs abun na É“ata masa rai.
Gyara zama Abu Abdurahman yayi cikin harshen turanci ya fara magana "a jidda na haɗu da ita a lokacin tana ciwon hauka naje wani meeting ina fitowa bayan sallar mangariba na sameta wasu samari suna tsokanar ta kallo ɗaya na mata Allah ya jarrabe ni da son ta nasha fama kafin na samu ta yarda na ɗauke ta a motata alokacin matata ma haifiyar su Fariza ta rasu ta barni da ƴara huɗu kana yan uwana sunyi sunyi nayi Aure naki dan ina kaunar mahaifiyar su Fariza amma kallo ɗaya nayiwa fateema naji duk duniya ba wanda nake so sama da ita,ban san kowa na taba ban san ita yar ina bace ni dai kawai na ganta a ciwon hauka, ina ɗaukan ta gidana na wuce da ita tsawon shakara biyu ina mata magani malamai da dama na kira sun zo sun dubata duk wani malami dana kira maganar ɗaya suke min shine asiri aka mata da farko naki yarda dan ni ba irin mutanen nan bane masu yarda da tsuɓɓace tsuɓɓace daga karshe dai na hakura na yarda na fara nema mata maganin makarin asiri, abu na farko daya fara ɗaga min hankali shine lokacin data fara samun sauki sai na fahimci tana da ƴaƴa awata kasar dan mafi yawancin lokaci zakaji tana faɗin "wayyo ƴarana Aisha ta" ni kuma ina bala'i son ta bazan iya rabuwa da itaba dan haka sai nayi kokarin mantar da ita rayuwar ta na baya amma ina abun yaki yuwa domin kamar yadda take kara samun sauki haka take kara zancen ƴaƴan ta bazan iya jure rabuwa da ita ba bani da wani zaɓi da ya rage min nasa amata haɗin asirin da zata manta komai da kowa na rayuwan ta na baya haka ko akayi ta samu sauki ta warke sumul amma bata iya tuna komai na rayuwar ta na baya,duk wanna shakara biyu da fateema ta kwashe a gidana yan uwana basu sani ba daga karshe na koyawa fateema sona sosai sanadiyyar kawo fateema gidana da nayi ne yasa na kwashe su Abdurahman na kai su Madina karatu kuma na hana su dawowa hutu dan karsu zo suga fateema su ɓata min shiri shiyasa na kai su gidan babban yayana Madina sai da na tabbatar fateema tana sona na gama shirya komai da kaina nayi mata hayan iyaye na tura yan uwana gidan suka nema min Auren ta ban bata lokaci ba dan kar asiri na ya tonu nayi gaggawar auren ta dan ko sati biyu ban bari an cika da nema min auren ta ba aka ɗaura Auren ranar ji nayi tamkar an sani a aljannan alokacin fateema tana da karancin shekaru dan bazata wuci 23 years ba hakan yasa na sata nakaranta tana da ƙwaƙwalwa sosai nan take komai ya buɗe mata ta fara karatu gadan gadan na ɗauko mata mai mata lesson a gida lokaci da su Fariza suka dawo daga madina fateema ta rungume su sosai kamar ƴaƴan data haifan hakan yasa na gane ita ba yar kasar makka bace dan matan larabawa yan uwana basu yarda su rike ƴaƴan mijin su hakan yasa na ji tsoron karayin aure abaya lokacin da maman su fariza ta rasu dan kar yarana su sha wahala naji daɗi kuma na kara son fateema ninkin yadda nake son ta da saboda rike min su fariza da tayi da zuciya ɗaya ji nake kamar na mai data cikina ko zan huta saboda so da kauna rayuwar mu tayi daɗi sosai,muna cikin farin ciki da anna shuwa,sai da muka shafe shekara 7 da fateema bata samu aihuwa ba sai a shekara na 8 ta samu ciki nayi murna sosai kuma har lokacin ban ji labarin mai neman fateema ba,da lokacin aihu yayi kasar turai na fita da ita taje ta aihu a can nan Allah ya bamu twins Ayaam da Ayana" ya kai karshen maganar yana nuna kyawawan yaran dake jikin Aunty farida "wanna shine takaitacen labarin tsakani na da fateema" salati Abba ya sa kafin yace "kasan tana da Aure amma saboda son zuciya ka ɓoye ka Aure ta kan Aure innalillahi wa inna ilaihir rajiun duniya ina zaki damu ya Allah ka raba mu da sharrin zuciya wanna zuciya wanna zuciya itake gefe dayawan mutane wuta ya ilahi ya lillahi ya Allah ka sassauta mana zuciyar mu zuciya bata da amfani ko kaɗan wanna case na kun sai mun dangana da manyan malamai dan muji ya matsayin Ayaam da Ayana shin halastattun ƴaƴa ne ko dai suna cikin ƴaƴan shubuha ko dai kai tsaye shegune laila ha illallahu Muhammadar Rasulullah sallahu alaihi Wasallama ka chuchi wayan nan yaran subhanallah ni gaba ɗaya kun ɗaure mun kai" tun da Abu Abdurahman ya fara bayani Hajj fateema ke hawaye yanzu daman Abu Abdurahman cutar ta yayi ita ta ɗauke sa a matsayin masoyi shi ya kara sa ta manta da iyayen ta mijin ta da ƴaƴan ta lallai ɗan Adam baa gane shi ta shigar sa a ido idan kaga abu Abdurahman kaga cikakken musulmi duk in da ake neman cikakken musulmi Abu Abdurahman ya bayyana a face nashi ashe zuciyar sa ba ta musulunci bace tabbas bai kamata mutun ya yarda da mutun ta fannin shigar kamala da siffar kamala ba wlh gwara mai shigar banza ansan dai daman shigar banza yake amma mutun yayi shigar musulunci ya cuceka kai amma Abu Abdurahman ya cutar da addini musulunci tir da shi. Da kyar su Aunty farida suka shawo kan ta tayi shiru suka lallaɓata suka wuce part din Ammi da ita
dukar da kai Abu Abdurahman yayi yana faÉ—in "karki gujeni fateema ina kaunar ki idan kika barni mutuwa zanyi wlh innalillahi nayi nadamar yin hakan" kallon su Fahad Abba yayi yace "ku kai shi É—akin baki zuwa gobe zan kira malam sai muji me matsayar Auren su da Æ´aÆ´an su tun da shi baban su hiyana ma Allah ya masa rasu ina ganin abun zai zo da sauki" yana kai karshen maganar ya mike ya fice ya nufi fada.
Karfe 4 na yamma Ammi ce zaune a bakin gadon Abba Abba na tsaye ya jingina da jikin gadon suna tattaunawa "Aisha munyi kuskure munyi kuskure babba" "wani kuskure kuma mukayi ranka ya daɗe?" "Aisha duk abun da su Safras ke aika tawa yanzu mune sula mu muka ja" "mu kuma ranka ya daɗe ban gane mu muka ja ba" dogon numfashi Abba yaja tare da sauke ajiyar zuciya kafin yace "A'isha mu godewa Allah dayasa har yanzu ƴaƴan mu basu fi karfin mu ba suna jin maganar mu wlh na jinjina musu Aisha idan baki manta ba tun yaran nan basu wuce shekara 9 a duniya ba muka ɗauke su muka maisu kasar turai a tunanin mu gata muke musu Aisha ba gata bane da kan mu muka lalata yaran mu wlh Allah ma yana son mu da rahma da yasa har yanzu suke jin maganar mu Allah na son mu da yasa basu sauka daga tarbiya irin na hausa fulani ba alhadulillah ƴaƴana basu taɓa zina ba basu taɓa shan giyaba basu taɓa sata ba munyi Sa'a ta nan ɓangaren amma idan kika duba ɗabiun Safras ya banban ta da ɗabiar hausa fulani ni kuma ban taɓa damuwa da hakan ba ina ganin ya girma zai iya yiwa kan sa faɗa sai yau na gane kuskuren yin hakan Safras idan yayi zuciya ba mai iya tinkarar sa ko mu da muka haifesa Safras bashi da kunya ko kaɗan in fact Safras bashi da cikakkiyar imani duk na san da hakan a tunani na idan na masa Aure zai iya sauyawa sai kuma na ga akasin hakan ni yanzu damuwa ta karyaje yayiwa yar mutane wani mugunta dan zai iya kashe ta ba damuwan sa bane tun da ya iya jefata cikin ruwa kuma ya iya sa bindiga ya harbeta bayan nan ya bata wahala kala kala Aisha ina na damar tura ƴaran nan kasar turawa da wuri dana bari sai sun girma sun mallaki hankalin kansu" ya kai karshen maganar kamar zai yi kuka "kayi hakuri ranka ya daɗe In Sha Allah babu abun da zai faru" jinjina kai yayi kafin yace "Allah yasa" tare da zama kusa da ita sukayi shiru kowa da abun da yake tunani
A É“angaren su bgs kuwa
Ba yadda likitocin nan basu yi ba akan bgs ya sake musu likitan su amma yayi, numfashi likita na gab da ɗauke wa Aryan ya iso cikin zafin nama yasa hannu ya ɓanɓaro hannun bgs daga wuyar likita nan take likita ya faɗi kasa sumamme, a fusace bgs ya juyo ya damki wuyar Aryan,ganin Aryan ne yasa ya zame hannun sa kallon tsab Aryan ya masa cikin sauri yace "bgs lafiya meke faruwa? Meke damun ka? Me ya kawo jini jikin ka? Accident kayi ne? Ina sister? Me yasa kake cikin rafin rai haka? Kamin magana dan girman Allah ina sister?" "Ta mutu ta mutu Aryan ni da kai na na kashe ta ni da kai na na kashe ta Aryan nayi nadamar zuwata duniya nayi k....bai kai karshen maganar ba Aryan ya ɗauke sa da wata wawan gigitatchiyar mari cikin tsawa da zafin ran da bai taɓa shigaba yace "ka kashe ta kake faɗa min!!? Innalillahi wa inna ilaihir rajiun Safras yanzu menene amfanin zuciya dan ina tabbacin cikin zuciya ka kashe ta kana cikin hayyacin ka bazaka kashe taba ka cuce mu bgs ka cuci su Ammi yanzu ina gawar nata yake?" Sulalewa wa bgs yayi ya zube kasa ya kifa kansa a kasa idon sa sunyi ja kamar jini jikin sa har ɓari yake tsabar tashin hankali da ɓacin rai da kyar ya iya faɗin "Aryan ka kashe ni kayiwa Allah ka kasheni na bi matata wlh ba zan iya rayuwa ba tare da Eshat ba son ta ya mamaye dukkan jinin jiki na na cutar da ita ta mutu da bakin ciki na bazan yafe wa kai na ba zuciya ta cuceni zuciya bata da wani amfani a rayuwa sai dai ya kai ka ya baro ka idan ka biyewa zuciya to tabbas zakayi dana sani mara amfani kamar dai ni ɗin nan innalillahi wa inna ilaihir rajiun Aryan ka kashe ni bazan iya kashe kai na ba zanubin zai min yawa nayi dana sanin zuwata duniya na kara mai mai tawa yau zuciya tasa nayi dana sanin zuwata duniya Aryan mari yayi kaɗan a hukuncin daya dace kamin yayi kaɗan ku bani hukuncin dai dai da wanda yayi fyaɗe kuma yayi kisan kai ka hukun tani kamar yadda kake hukun ta criminal ɗin da suka yi wa yarinya fyaɗe kuma suka kashe ta domin abun danayi kenan nima" lokacin guda Aryan yaji mugun tausayin bgs ta rufesa da ya zuciya sosai amma ganin halin da bgs ya shiga yasa ya ɗan sauko dan ko amafarki bai taba tunanin bgs zai shiga wanna yanayi saboda mace ba, dukawa yayi ya dafa kafadar bgs ɗin kasa kasa yace "ina gawar sister yake? Kuma me ya hadaku har ka kashe ta?" Cikin tashin hankali ya fara bawa Aryan labarin duk abun da ya faru tsakanin su "innalillahi wa inna ilaihir haba bgs meyasa zakayi wa kanka allura haka why why? Kafi kowa sanin illar alluran nan sanna kasan a addinan ce ma haramun ne kai da kake yakar Company masu buga ire iren alluran nan kai da kake yaki akan masu fitar da shi kake kama masu amfani da shi why? Yau zakayi wa kan ka meyasa baka kirani ni naje nayiwa criminal ɗin hukun ciba duk da nasan cewa nima yanzu bazan iya hukun ta mutun kamar da ba ni yanzu ko kuna ma bazan iya sawa criminal a jiki kamar da ba amma tun da babban criminal ne zan san ya zanyi yanzu gashi ka ɓata komai mawuyacin abu ne Abba Ammi hajj Fateema kai kowa dake gida mawuyacin abune su yafe maka wlh ni nasan har Yusuf sai ya guje ka akan sister" "Aryan zuciya ta zafi take min Aryan zuciya ta cuceni ta gama dani bani da abun cewa karka ɓoyewa kowa abun dana aika ta ka faɗa wa kowa a gida ta yadda zasu nunamin tsana har na samu zuciyata ta buga na mutu Aryan ina son matata ba zan iya rayuwa babu ita ba tazama bugun numfashi na ina kaunar ta Aryan ina a a a" kasa cigaba yayi da magana sakamakon ciwon zuciya da ta kama shi lokaci guda dafe sai tin zuciyar sa yayi kafin Aryan ya farga sai ganin sa yayi ya sulale kasa yayi flat kamar gawa baya numfashi a ruɗe Aryan ya kira likitoci suka ɗauki sa,sanan yace a nuna masa ɗakin da hiyana ke kwance, ana nuna masa ba tare da ɓata lokacin ba ya shiga cikin ɗakin
Tana kwance flat tsabar tayi losing blood furkar ta tayi wani irin yellow kamar ba mutun ba karisowa gaban gadon da take kwance yayi ya zuba mata ido yana kallon ta duk taurin zuciya irin mashi sai da ya mata hawaye cikin kuka yake faɗi "sister ki yafe wa ɗan uwana ya Allah kasa bata riƙe ɗan uwana a ran taba wanna wace irin jarabawa ce innalillahi wa inna ilaihir rajiun ya al...bai karshen maganar ba idon ya sauka akan gefen idon ta hawaye na gangarowa ta wajen yana bin kunnen ta cikin sauri ya ɗaura hannun sa saitin kirjin ta shiru kirjin nata baya bugawa kamar bata da rai da sauri ya zame hannun sa ya kamo tannun ta da karfi ya riƙe sosai yayi shiru kamar mai sauraren wani abu a sukwane ya sakin hannun nata kasan cewar yaji jijiyar hannun ta na harbawa sai dai duk wani jijiya na jikin ta ya tsaya har zuciyar ta ya tsaya da bugawa na ɗan lokaci mawuyacin abune ta tashi ɗiban kayan aikin asibitin yayi ya shiga aikin ceto yaruwar ta duk wani ilimi daya sani a duniyar nan a fannin likita sai da ya tattaro bai ma bi ta kan likitocin ba ya fara tikar aiki dan tana tsakanin mutuwa da rayuwa kai mawuyancin abune ma ta tashi tsaki yaja lokacin daya ga aikin ba zai yiwuba sai an kara mata jini dan jinin ta yayi kasa over cikin sauri ya ɗebi jinin sa ya gwada jinin nasa batayi dai dai da nataba da gudu ya fita ya nufi dakin da aka kwantar da bgs likitoci na kokarin ceto ran shi ya ture su ya ɗaure hannun bgs dake sume ya ɗebi jini gwajin farko yaga jinin su iri ɗaya da hiyana sai dai still jinin bgs akoi ragowar alluran nan da yayiwa kan sa da safe tsaki Aryan yaja kafin yace "da ki mutu gwara na sa miki jinin nashi ko da akoi tangarɗa ai mijin kine kuma yayan ki" yana kai karshen maganar ya koma ɗakin da bgs ke kwance ya fara ɗeban jinin sa mamaki lokacin keyi da basu san Aryan ba da sai suce ya samu taɓin hankali shiko ko kallon in da suke bai yi ba ya ɗebe jini ya fice abun sa dan yanzu rayuwar hiyana ce da muwarsa bai damu da jinin bgs bai dace asa mata ba shi dai tun da jinin iri ɗaya shi kenan ba dai zata tashi ba burin sa ya cika shima da alama ya fita hayyacin sa. Yana kokarin sa mata jinin sai kuma wani tunanin ya faɗo masa akan ya ɓoye hiyana ya kyale bgs akan ta mutu sai ta samu sauki ta dawo dai dai tunani ya fara yi to wace likita ce ta dace tabawa hiyana kulawa dan wanna case natan yasha gaban tunanin sa.
yayi tunanin duniyar nan ya kasa tunano likitar É—a zai iya bari ta kula da hiyana.
Daga karshe dai ya saɓe ta a kafaɗar sa yayi waje da ita hannun sa rike da ledar jinin bgs ya nufi motar sa. Da gudun gaske yaja motar dai dai zai fita asibitin yayi karo da wata babban likita babbar mace ce dan akalla zata kai 58 years tsayuwa yayi ya mata bayani a gurguje da yake turawa basu da matsala ta wanna ɓangaren sai ta amince ta shiga motar ta bi sa abun dayasa ta kara yarda da shi dan tasan shi babban soja ne tana ganin su a News shi yasa ta aminta da shi tasan bazasu aikata wani abun da ba dai dai ba.
kai tsaye Airport ya wuce da su a jet nashi aka É—auke su zuwa us dan bai san bgs yasan hiyana na raye duk da yasan yanzu bgs yayi nadama amma suna bukatar kawar masa da zafin zuciyar san nan.
Katafaren gidan Bgs dake us suka wuce duk wani abu da likitar zata bukata ya sai mata sanna ya zube musu kuÉ—i dayawa har ya fita sai ya kuma dawowa dan gani yake kamar zasu bukaci wani abun ATM card nashi ya ciro ya ajiye musu tare da faÉ—a wa likitan pin number sa sanna ya wuce nan take dr ta É—orawa hiyana jinin bgs, shi kuma Aryan ya wuce ya koma uk.
Gaba É—aya wayoyin sa ya kashe su dan idan Abba ya kira shi bashi da amsar da zai bawa Abba
Lokacin da ya koma uk kai tsaye É—akin da bgs ke kwance ya wuce babu kowa a É—akin bgs ne kaÉ—ai ke kwance har yanzu baya numfashi da alamar bai farfaÉ—o a an daura masa karin ruwa juyawa yayi ya koma office na babban likita dan jinme ke damun É—an uwan sa.
Zaune ya isko babban likita ba tare da bata lokaci ba cikin harshen turanci yace "dr meke damun dan uwana? gyara glass na face É—in sa dr yayi ya fara yiwa Aryan bayani kamar haka "zuciyar É—an uwan ka na gab da bugawa sakamakon zafi daya É—auka sosai kuma da alama ya rasa wani abun da zuvyiyar sa ke so ko kuma kun hana shi wani abun da zuciyar tasa ke so munyi iya bakin kokarin mu dan ganin ya rayu yanzu sai dai mujira ta Allah kawai amma yana iya mutuwa ako wani lokaci haka kuma yana iya rayuwa ako wani lokaci mungama aikin mu sauran naku ku tayasa da addu'a" shiru Aryan yayi yana tunanin wanna wace irinyar jarabawa ce mai wuyar gaske mikewa yayi ya fito waje jiki ba kwari ya ciro wayar sa ya kunnata ya nan ya ci karo da miss call sun fi 70 daga gida kawai aunty Farida Abba kusan miss call 30 suka masa ba wanda bai kira layin sa a gida ba layin Aunty farida ya fara kira dan yasan ita kaÉ—ai zata fahimce sa kuma ta taimaka masa.
Bugu ɗaya ya mata ta ɗauka a ruɗe babu ko sallama tace "Aryan lafiya ka kashe wayar ka? Ina kake? ina su Prince da hiyana? Ka gansu ne? Suna lafiya ko?da kyar ya iya cewa "Aunty farida pls calm down tun da kikaga na kiraki ai kome ke faruwa zami ji yanzu dai idan kina cikin mutane ki fito kije keɓabɓen waje zamuyi magana" "Aryan ka faɗa min meke faru ni kadai ce dan ina part ɗin Ummi ina ɗaki na nazo yin wanka ne" nan Aryan ya shiga bata labarin duk abun dake faruwa ba abun da ya rage mata cikin tsawa tace "hauka Safras yake yi ne zuciya haukace duk zuciyar sa wlh bai kai ko rabin Ammi ba amma tana iya sarrafa nata wlh ina da tabbacin idan su Ammi suka samu labari idan bata tsinewa prince ba to zata cireshi daga ƴaƴan ta wanna wani irin zalunci ne!!? "Aunty farida ki bar wanna maganar tun da yanzu shima yayi nadama kuma shima yana halin mutuwa ko rayuwa ya kamata mu sassauta masa yasamu sauki ta bangaren mu ko zamu samu ya farfaɗo thank God da sister bata rasu ba abun zai zo mana da sauki abun da nake so dake yanzu ki shirya ki je Airport ki zo kasar nan dan inason bgs ya samu farincikin na cewar mu bamu gujesa ba kinga ta haka zamu iya ceto ransa amma idan muka gujesa wlh Aunty farida mutuwa zai yi dan yana ɗaya daga cikin abun da yasa zuciyar sa ta kusa bugawa yana bala'i son mu yana tunanin kowa daga cikin mu yanzu zai gujesa gashi matar sa ta rasu shi yasa ya shiga tashin hankali har zuciyar sa ta kusa bugawa yanzu dai kinga na ɓoye sister kuma baza mu bayyana taba sai ta warke sumul ta dawo dai dai ta manta da duk wani ciwo zamu nemi abun da zamu faɗa wa su Abba shi kuma bgs zamu barshi akan sister ta rasu dan ya wahala sosai sai ya cire zafin zuciya gaba ɗaya a rayuwar sa sanna mu bayyanata" "na gamsu da maganar ka Aryan amma yanzu abubuwa biyu ne agaban mu na farko dole dadyn Junior yasan da maganar dan ya bani goyan bayan wajen sanar da su Abba na koma Maiduguri dan karsu neme ni abu na biyu shine kasan dai ko me zamu shiryawa su Abba akan su hiyana bazasu taɓa yarda ba zasu ce suna san yin magana da ita awaya" "no Aunty farida ki bar wanna zancen ki bari idan ta farfaɗo ni zan iya haɗa ta da su Abba awaya sister tana da hankali kuma tana jin magana ta bazata sanar da su komai ba" "anya Aryan hakan zai yiwu kuwa ya za'ayi shi Prince mu sanar da shi ta mutu kuma mu sanar da su Abba tana raye baka ganin zai iya zuwa yace zai nemi gafarar su Abba har ya samu labarin bata mutu ba?" "Aa Aunty farida kinsan burin su Abba ne daman su ɗauke ta su ɓoyeta har sai ya san darajar ta zanyi magana da Ammi zance mata sunyi haɗari ne sai na faɗa mata abun da ya faru a asibiti har naje na ɓoye sister kinga zasu tafinwa bgs akan ta mutu ke dai ki barmin komai a hannu na kinji?" "To shikenan gani nan zuwa bari na shirya sai na sanar da dadyn Junior sai na tawo airport ɗin sai munyi waya" to kawai yace sanna ya katse kiran
To nima anan na katse karatun sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu love u lodi lodi masu min comments Allah ya kare min ku Allah ya bar zumunci 🥰🥰
No comments