Recent Updates

Duk Karfin izzata Book 2 Page 41

 


💋 Duk Karfin Izzata 💋 



💋The talent troupe writer's 💋




         By Star Lady


Page 41




Yana fita part nashi ya wuce. Yana shiga bedroom ya wuce toilet wanka yayi a gurguje ya shirya cikin wando 3 cutar baki mai laushi ya sanya farin singlet fari tas ya gyara gashin kansa ya tara ya É—aure sanna ya feshe jikin sa da perfume  mai daÉ—in kamshi ya haye gado ya kwanta tare sa jawo blanket zuwa kirjin sa ya lumshe ido hankali kwance barci mai daÉ—i yayi awon gaba da shi.


Almost 1h su Abba na zaune suna jiran sa babu bgs babu labarin sa,Abba na kokarin yin magana Aunty farida ta mike tana faÉ—in "bari na dubosa" bata tsaya jiran amsar Abba ba ta wuce da sauri dan tasan Abba zai iya hanata zuwa kuma tana son yin magana da Bgs.


da sallama É—auke a bakin ta ta shigo bedroom na shi yana kwance abun sa hankalin a kwance ba karamin mamaki Aunty farida ta sha ba ganin sa cikin kwanciyar hankali yana zuba barci

 saboda mamaki da kyar ta iya karisawa bakin gadon ita atunanin ta zatazo ta samesa cikin damuwa ashe ashe shi barcin sama yake itace ta damu kan ta. Hannu ta sanya ta taÉ“a shi tana kiran sunan sa "Prince!! Prince!!" da kyar ya iya waro idon sa waje guntun tsaki yaja tare da kawar da kansa gefe yana faÉ—in "menene!? Mamaki ne ya kara bayyana akan face nata "lallai Prince kabar iyayen mu zaune suna jiran ka kazo kayi kwanciyar ka" "to Aunty farida me kikeson nayi saboda Allah dai" shiru Aunty farida ta É—an yi kafin tace "kaje ka kai musu takarda sakin hiyana mana" a sukwane ya É—ago manya manyan idon sa nan tare da kara zaro su waje ba karamin tsorata Aunty farida tayi ba ganin yadda ya zaro ido,"saki fa Aunty farida kika ce!? gyaÉ—a masa kai tayi alamar eh saki, girgiza mata kai yayi kafin yace "never wlh" "ban gane never ba ba kai kace baka son taba? Tun da baka son ta sai ka sake ta ai" tsaki yaja kafin yace "koda bana son ta ba zan sake taba dan yanzu ina jin daÉ—in zama da ita ta iya duk wani abun dana ke bukata" ita kam Aunty farida ta rasa bakin magana shiru ta É—an yi mamakin bgs ya fara yi mata yawa "kasan me Prince? Wlh yadda Abba ya É“ata rai yau idan kaga baka saki hiyana ba to tabbas mutuwa Abba yayi" shiru ya É—an yi kafin yace "Aunty farida ya zan yi ni gaskiya ba zan iya rabuwa da ita ba" "kana son tane? Juyowa yayi da kyau ya kalli Aunty farida yace "aa ni bana son ta amma dai zan zauna da ita" "yau naga ikon Allah Prince wani irin rashin adalcine wanna baka son ta kuma kace bazaka rabu da ita ta Auri wanda take so ba wanna ai zalunci ne" "Aunty farida ki dai na zancen ta Auri wani rai na yana É“aci sosai" kara waro ido waje Aunty farida tayi kafin tace "Prince anya kasan me kake yi kuwa? To wlh nima zan dai na bin bayan ka ka tashi ka rubutawa hiyana sakin ta ka kaiwa Abba tun wuri ya za'ayi nazo ina son mu shawo kan matsala kuma kana neman ka É“ata min rai" kwanto da kansa yayi kan cinyar Aunty farida cikin sanyayyar murya ya fara magana "Aunty farida izuwa yanzu nasan kin san ina son sister amma ban san me ya sanya kike neman wahalar da ni ba me yasa kike son kara min zafi kan zafi ba zan iya rabuwa da sister ba ina kaunar matata" shafa gashin kansa ta fara yi tana faÉ—in "ban san ka fara son hiyana ba hasashe nake shiyasa nake tambayar dan na tabbatar amma idan da gaske kake son hiyana a matsayin mata me ya sa ka harbeta da bindiga?" Mikewa tayi zaune kafin ya fara magana "Aunty farida awanna gaban bani da zaÉ“i ne dole na harbeta" "ban gane ba kamin bayani" "Aunty farida bindiga suka sa mata a kai sukace idan nayi wani motsi zasu harbeta kuma tabbas zasu harbetan domin daman dan su kashe ta suka kamata alokacin bani da zaÉ“in data wuce ni da kai na na harbeta idan ban harbeta ba su zasu harbeta kuma a kai zasu harbeta kinga idan ko suka harbeta a kai ba makawa mutuwa zatayi,shiya sa ni na harÉ“eta a in da na san bazata mutuba,kinga,zasuyi tunanin ban damu da ita ba bazasu damu wajen duba ta mutu ko bata mutuba abu na gaba idan ban harbeta ba zata zamomin barazana wajen hanani kashe su dan zan zamo ina faÉ—a da su kuma ina tunanin ta kar wani ya cutar da ita zata rabamin hankali gida biyu zata iya jawowa ayi nasara a kai na abu na uku ita kan ta zata tsorata da ganin faÉ—an dana ke da su kin sani tana da matsala a kai tun bugun da Maryam ta mata duk da cewa abun ya ragu amma har yanzu da saura to idan ban harbeta ba wlh Æ™waÆ™walwan ta zai iya samun damuwa dan bata da taurin zuciyar da zata tsaya tana ganin ana kisa a gaban ta abu na huÉ—u....cikin sauri Aunty farida ta rufe masa baki tana faÉ—in "dalili na farko ma ya gamsar dani lallai awanna lokacin bakada zaÉ“i dole ne ka harbi hiyana yanzu muje kayi mata bayayi ka faÉ—a mata kana son ta hiyana macece mai tausayi da hankali zata fahimce ka" girgiza kai yayi yana faÉ—in "No Aunty farida awan nan karon bazata saurare ni ba duk abun da zan faÉ—a mata zata ga kamar still wasa zanyi da hankalin ta" "me yasa kace haka? "Good question last 2 weeks kafin muzo nan na nuna ina son ta kuma lokacin har ga Allah ina kaunar ta amma ina jiye mata tsoron zama da nine shi ya sanya nake kokarin cireta a rai na,bayan mun dawo nan akoi wata rana da Aryan yazo ya tunzurani akan ta ya sa nace bana son ta kuma taji duk abun da nace tana tsaye a bakin kofar shigowa É—akin taÉ“ata rai sosai tayi kukan da nida kai na sai da nayi dana sanin faÉ—in hakan danayi akanta,Aryan ya bita ya bata hakuri ita É—in macece mai hakuri data dawo É—akin nan bata nunamin komai ba amma acikin kwayar idon ta naga tsananin tsanata da jin haushi na alokacin nayi Æ™oÆ™arin sake jan ta ajiki na dan na goge wanna haushin da tsanata da ta fara amma ban kai ga yin nasara ba aka sace su kuma ga rashin lafiyar ki to kinji yanzu bazata taÉ“a yarda dani ba nasan da hakan nariga nayi kuskure tun farko" jijjina kai Aunty farida tayi kafin tace "eh kayi kuskure gaskiya kayi wasa da zuciyar ta sosai duk da haka nasan har yanzu da sauran son ka a zuciyar ta tukun nan ma yaushe ka fara son ta?" kawar da kan sa gefe yayi kafin yace "wlh sharrin Cameran É—aki na ne ya fara samin son ta kullun idan ina zaune a office ba abun da nake sai in kunna cameran gidan in yi ta kallon Aikin alkharin da take min wani lokaci in ganta tana gyara gado wani lokaci tana wanke toilet wani lokaci tana wanka gasu nan dai abubuwa kala kala na alkhari take min har abun ya dawo min kamar Tv ba ran da zanje office ban zauna nayi ta kallon abun da take ba wani lokaci idan tayi wani shirmen sai tasani murmushi sau da dama idan rai na ya É“aci Cameran É—aki kawai nake kunnawa idan na fara ganin shirmen da take sai na ji na watsake ina son sauraron karatun Qur'ani idan tanayi saboda ta iya rera kiraa sosai a haka ta fara sauyamin zuciyata sai kuma dana zo naga abun alkharin da tayiwa Ahmad alokacin naji daÉ—i sosai ji nayi kamar na rungumeta na faÉ—a mata ina kaunar ta sai kuma na fasa lokacin ne na kara tabbatar wa kai na tana da zuciya mai kyau" tun da ya fara magana Aunty farida ta zuba masa ido har sai daya kai karshen ta sauke nauyayyar ajiyar zuciya "eh lallai Prince ka faÉ—a soyayya dumu dumu idan ba soyayya ba yaushe zaka tsaya kana yiwa mutun wanna dogon bayani kai da cewa yes ma wahala yake ma kafin ka faÉ—a sai ka É—auki yan mintoci tab dole mu san abun yi" kawar da kansa gefe yayi ya É—aure fuska yana kokarin yin magana wayar Aunty farida tayi kara tana dubawa taga sakon Aryan ne  "Abba yace bgs ya same sa a bedroom nashi yanzu nan bai yarda ya kara 2mins bai zoba nakira layin sa bai É—aga ba na masa tex ba reply" abun da sakon Aryan ya kunsa kenan mikawa bgs wayar tayi ya ansa ya karanta sakon sanna ya mike ya nufi hanyar fita,da sauri itama ta mike tabi bayan sa.


Zaune a bakin gadon Abba suka isko Ammi Abba kuwa yana tsaye kallon É—aya zaka musu kaga matsanancin É“acin rai da tashin hankali a tattare da su. Saman sofa dake cikin É—akin bgs da Aunty farida suka zauna cikin É“acin rai Abba yace "ka bani kunya Safras ban taÉ“a zaton zan maka umarni akan abu kuma kaki bi ba ai koma ban maka umarni ba marainiyar Allah bata da kowa sai mu ka sata agaba ka rinÆ™a azabtar da ita gaskiya baka yiwa kanka adalci ba kuma ka cutar da zuciya ta yanzu duk bama wanna ba ka rubuta min takardan ta kamar yadda ta bukata ka bani" kasa kasa yace "Abba ni ba zan iya sakin taba gaskiya" a fusace Ammi tace "what!!? Wlh baka isaba sai ka sake ta" "Ammi kiyi hakuri amma ni bazan iya sakin matata ba ina son zama da ita" "kana son zama da ita ko dai kana son karasa kashe ta wlh tun ranka bai É“aci ba ka sake ta na faÉ—a ma" Aunty farida na girgiza masa kai tana Æ™oÆ™arin dannar sa amma ina zuciya ta kwashe sa cikin fushi ya mike yace "ni bazan saki matata ba!!" "ina magana kana cemin bazaka sake taba!?" "Koma me zakuce kuce ni dai ba zan sake taba ba kuma wanda ya isa yasani na sake ta" Ammi na kokarin sake yin magana Abba ya dakatar da ita dan ya lura bgs fa baya cikin hayyacin sa bai san me yake faÉ—e ba idan Ammi ta biye masa za'a iyayin kwaÉ“aÉ“iya dan a hankalin da yake cikin nan duk abun da yazo bakin sa faÉ—e zai yi,alama Abba yayi wa Aunty farida akan ta lallaÉ“a bgs su tafi É—aki. Mikewa tayi tace "Prince muje ko" cikin fushi yace "Aunty farida wlh ba zan saki sister ba ba wanda ya isa ya rabani da matata dan haka ki kyaleni wlh yau....bai kai karshen maganar ba ya dakata sakamakon É—aga hannu da Aunty farida tayi a fusace zata maresa tsare ta yayi da ido ta kasa karisa kai hannun ta kan face nashi jikin ta har rawa yake saboda É“arin ran abun da bgs ke kokarin yiwa iyayen su,cikin tsawa yace "me yasa kika dakata ki karisa mana!! Ki mareni nace!!!ki mareni mana!!" kasa Aunty farida tayi da hannun ta tana danasanin É—aga hannun da tayi zata maresa yanzu gashi ta sake kwaÉ“e abun suda suke neman sulhu  yanzu ta kwaÉ“e komai,a zuciye bgs ya juya ya fice daga É—akin sai huci yake cikin ransa yana faÉ—in "akan mace yau Aunty farida take kokarin marina?no hakan ma ba zai yiwu ba dole na É—au mataki.


cikin sauri Aunty farida tace "bari na bi bayan sa dan kar yaje yayi wani abun" shiru Abba da Ammi sukayi Abba na nadamar tursasawa bgs akan ya saki hiyana da sukayi gashi sun kara kwaɓe abun bgs bai taɓa ɗaga murya yafi na su ba yana musu biyayya iya iyawar sa koda baya son abu idan suka ce suna so yana hakura ya musu amma yau da bakin sa yake mayar musu magana dan sunce ya saki hiyana lallai bgs na kaunar hiyana da gaske dolene musan abun yi a ɓangaren Ammi kuwa tunani take "idan muka bar yaron nan bai saki yarinyar nan ba mun yi son kai mun cuceta itama yace mai yanci kamar kowa kai ai yazama dolema ya sake ta in ba haka ba ba zan yafewa kai na ba na cutar da marainiyar Allah" shiru sukayi kowa yana ta tunani a ransa ba wanda ya iya ce da ɗan uwan sa uppan.


A É“angaren bgs kuwa yana fita Part nashi ya nufa cikin É“arin rai ya É—auko takar da da biro daga cikin drawer mirror ya zauna a bakin gado ya É—an yi rubutu mai É—an tsawon layi biyu sanna ya yage pepar ya naÉ—e ya miÆ™e ya nufi hanyar fita yana kokarin fita Aunty  farida na shigowa ko kallon in da take bai yi ba ya wuce abun sa,da sauri ta juya tabi bayan sa.


Kai tsaye part ɗin Ammi ya nufa yana taku irin na jaruman maza kallo ɗaya zaka masa kagane yana cikin tashin hankali da matsanancin ɓacin rai,

Palon Ammi babu kowa kai tsaye ɗakin su Zahra ya nufa,suna zaune saman gado suna ganin sa suka mike cikin tsoro Zahra ta sauko gadon ta raɓa gefen sa ta fice daga ɗakin da sauri amrat da lamrat suka bi bayan ta,ganin su Zahra sun fita ne ya sanya Aisha da Zainab suka bi bayan su

 diyana na zaune ko a jikin ta ko kallon in da yaka bata yi ba ta dukufa kan wayar Aryan tana buga game,kallo É—aya hiyana ta masa ta kau da kai amma ta tsorata ai nun da ganin yanayin da yake ciki wani mugun haushin sa ne ya kara karuwa a zuchiyar ta.


Takowa yayi zuwa bakin gadon nasu cikin tsawa yace "gashi!!" Kallon takardan da ya rike hiyana tayi kafin tace "menene?" A fusace ya wanke mata fuska da wawan mari hakan yayi dai dai da shigowar Aunty farida cikin tsawa yace "ni zaki cewa menene!!? Me kika bukata daga waje na!!?" Kuka ta saka masa mai ban tausayi wurga mata ta kardar yayi ya juya ya bar ɗakin yana fita diyana ta rungume ta suka fara rera kuka tare,shiru Aunty farida tayi ta rasa ina zata bi tabi bayan bgs ne dan ta san yana cikin ɓacin rai zai iya aikata wani abun da ba shi ba ko dai ta tsaya ta rarrashi hiyana

  jiki ba kwari ta juya tabi bayan bgs tana son rarrashi hiyana amma tana tsoron abun da bgs zai iya aikatawa na gaba kuma.


Tana shiga bedroom nashi shi kuma yana fitowa hannun sa ɗauke da trolley,waro ido waje tayi kafin tace "Safras ina kuma zakaje? Ko kallon in da take bai yi ba yayi wucewar sa zuciyar sa na tafasa tana masa raɗaɗi ɗamtsen hannun sa ta kama tana faɗin "please Safras ka tsaya mu fahimci juna kasan cewa kana son hiyana ko ka tafi wlh ba zaka dai na tunanin taba dan son ta na ran ka ka tsaya mu shawo kan matsala komai zai yi dai dai kawata Hajj fateema tana hanyar zuwa ta duba jiki na idan tazo zamu haɗu mu shawo maka kan hiyana dan Allah ka mai da trolley ɗin nan" a sukwane ya juyo ya kallin hannun nasa da ta rike ba tare da yayi magana ba bashi ta saki hannun nasa,cigaba da tafiya yayi ba tare da yayi magana ba,da sauri ta sake shan gaban sa cikin muryan rarrashi ta fara magana "ni nasan kana son hiyana kuma zakayi wanna tafiyane saboda ita dan Allah kayi hakuri ba dan kowa ba wanna karon ni zakayiwa daga nan zuwa dare zamu shawo maka kan matar ka yanzu haka hajj fateema ta shigo kasar nan tana Airport tana katisowa zamu gama dai dai ta komai In Sha Allah ka yarda dani" tsabar ɓacin rai da kyar ya iya buɗe bakin sa yace "Aunty farida kinsan banson maganar wanna kawar taki kin san meke tsakani na da ita dan haka ki dai na yimin maganar ta sanna kuma kin san gaba ɗaya gidan nan har Aryan bayan sister yake bi ba wanda yake bin bayana so na san ba zan yi nasara awajen sister ba shiya sanya na bata takardan nata kamar yadda ta bukata ki bani hanya na wuce tun kan rai na ya gama ɓaci" "no Prince no zamuyi nasara nima nasan awan nan gabar ba wanda zai bi bayan mu amma In Sha Allah zamuyi nasara kayi kuskure da gangancin bawa hiyana takarda sanna kayi kuskuren marin ta da kayi muda muke neman sulhu menene abun mari pls ka rinƙa rage zafin zuciya wlh gaskiya hajj fateema ta faɗa maka idan baka rage zafin zuciya ba zuciya zai kai ka ya baro ka gashi yau ka ɓatawa Ammi da Abba rai sosai abun da baka taɓa yi ba yanzu dai mu koma ciki ka ajiye trolley nan muje ka bawa su Abba hakuri sai mu san ya zamu ɓullowa lamarin" shiru yayi kamar mai nazarin wani abun,Aunty farida na kokarin sake yin magana Omar ya shigo ɗakin da sallama,

a tare suka kai kallon su kan Omar cikin girmamawa Omar yace "Aunty farida yaya Prince Abba na kiran ku yana palon sa yace kuyi sauri" "to gamu nan zuwa" cewar Aunty farida juyawa Omar yayi ya fice daga É—akin dawo da kallon ta kan bgs tayi tace "muje ko" sakin trolley nashi yayi ba musu yayi gaba yana taku irin na jaruman maza,bayan sa tabi suka fice daga palon.


Suna fita harabar gidan motar su hajj fateema na danno kai da murna Aunty farida ta tarbe su a tare suka shiga palon Abba da hajj fateema shikam bgs daman bai tsaya ba Aunty farida na tsayuwa wajen hajj fateema shi kuma ya wuce abun sa.


Kowa ya hallara a palo hiyana na kwance jikin Ammi tana kuka ga takardan da bgs ya bata a hannun ta kallo É—aya zaka yiwa Abba da Ammi ka gane yau suna cikin tashin hankali mara misaltuwa. gyara zama Abba yayi yace "ku bani hankalin ku a nan, ina son daga yau...bai karshen maganar ba sallamar su yaya bello ta katse shi Omar ne kaÉ—ai ya iya amsa  musu sallamar, kusa da Omar yaya Bello ya zauna ita kuma Hasana ta zauna kusa da diyana hajjo kuwa ta wuce kusa da su lamrat cigaba da magana Abba yayi "yauwa Bello daman ko baka zo ba zan sa akiramin kai dan wanna magana ta shafi kowa dake cikin gidan nan Aryan ina son ka nemo min mahaifiyar Sadiq da Aisha dan Omar yazo min da batun yana son Aisha kai kuma Yusuf ku tafi da Zainab Maiduguri gidan iyayen ta dan kaji ainihin abun dake faruwa ka kwantar mata hakkin ta kayi abun da ya dace, sanna sai magana akan sakin da Safras yayi wa hiyana ina son daga yau....bai Kai karshen maganar ba yaya Bello ya katse sa ta hanyar mikewa yana faÉ—in "Ummi kece!?" Yayi Maganar yana kallon hajj fateema gaba É—aya palon sun zuba masa ido miÆ™ewa hajj fateema tayi tana kallon yaya Bello sosai lokacin guda ta zaro ido waje tare da yanke jiki ta faÉ—i kasa sumammiya, da sauri Aunty farida Aunty mardiya Aunty salma Aunty Maryam sukayi kan ta suna kiran sunan ta "maman twins!!! fateema!!!" Shiru cikin sauri Abba yace "Ku kawo ruwa a zuba mata kai bello daman ka san tane? Aina kasan ta? Murya na rawa yaya Bello yace "Eh Abba na san ta"



To masu karatu sai mun haÉ—u gobe idan mai dukka ya kai mu

No comments