Recent Updates

Duk Karfin izzata Book 2 Page 40

 


💖The talent troupe writer's 💖





💋Duk Karfin Izzata 💋


By Star Lady



       




Page 40


Yau hiyana ta cika 2 days kwanche bata ko motsi,ba karamin tashin hankali bgs ya shiha ba,ya rame ya sauya har wani duhun wahala yayi baya zuwa ko ina kullun yana zaune kusa da gadon ta dan gani yake kamar idan ya tafi zata farka ba'a gaban saba, Aryan yana kokarin wajen kwantar masa da hankali. Khalid kuwa ya samu sauki ya warke sumul har ya fara jinyar yaron cikin jikin sis love ɗin sa. A ɓangaren Yusuf ma kulawa ta musamman yake bawa baby lamrat dan ji da cikin nan nashi yake kamar me. Ahmad kuwa soyayya babu kama hannun yaro tsakanin sa da hajjon sa yanzu ya sata a makaranta shi da kansa yake kai ta ya kuma ɗauko ta. fahad da Amrat zuba soyayya suke suma iya son ransu sai dai har yanzu Fahad na ɗaga mata kafa. Ba yadda ba'ayi da diyana ba akan ta koma part ɗin yaya Aryan amma taki har da kuka tana rantsuwa akan ba zata koma ba,haka Abba yace a kwale ta zuwa gaba kaɗan ta ɗan kara hutawa sosai Aryan ya shiga damuwa dan yana kaunar jiddan sa yana bukatar ɗumin jikin ta yana son ganin ta kusa da shi,amma haka ya hakura ya kyale ta ya sai mata waya dan su rinƙa hira amma ko ya kira tana gani bazata ɗauka ba idan ya shigi Part ɗin Ammi sai ya gudu ta ɓuya tun yana iya ɓuyewa har abun ya fara bayyana dan har rama yayi Saboda tunanin jiddan sa ita kuma jidda wasan ɓuya ma take da shi yanzu ko ajikin ta sai kiba take tana kara haske duk wasu albarkatun jikin ta sai kara girma suke.


Yau tun safe Abba yayi kiran family meeting. 9am gaba É—aya family suka haÉ—u a palo har da Aunty Amarya Aunty Maryam Aunty farida da bata da lfy ma an É—auko ta hiyana ce dake sume bata zoba.

  Cikin nitsuwa Abba ya fara magana "ku bani hankalin ku, yanzu tun da Allah ya sanya Ahmad ya samu lfy zai koma kan kujerar mulkin sa dan na gaji" kasa da kai Ahmad yayi cikin karyewar zuciya yace "Abba dan Allah kabawa uncle Aliyu mana" "aa Ahmad Aliyu ba zai ansa mulki ba meeting É—in nan ma danace yazo cemin yayi bashi da time dan haka ku kyale batun Aliyu next week zaka koma kan kujerar mulkin ka" shiru palon yayi ba wanda ke magana yaya bello yana son yayi magana akan hiyana amma yana bala'i tsoron bgs dan yaga yadda bgs ke bawa hiyana kulawa kuma fuskar bgs babu alamar wasa ko kaÉ—an kallo É—aya zaka masa ka gane mutun ne mai bala'i zafin rai.

"Akoi mai magana a cikin kune!?" Cewar Abba Ammi na kokarin yin magana sukajiyo voice ɗin hiyana kasa kasa da kyar ta furta "Assalamu alaikum" a sukwane bgs ya ɗago kai tare da kai kallon sa bakin Kofar shigowa,tabbas itace tana tafiya tana dafe bango sai taga taga take kamar zata faɗi,a zafafe ya miƙe ya nufeta,kamar wata yar baby haka ya ɗauko ta ya dawo da ita saman sofar da yake zaune ya kwantar sa ita yana faɗin "kar ki tashi dan baki gama warkewa ba" hararar sa ta kasan ido tayi kafin ta kawar da kanta daga kallon sa


Alhadulillah Alhadulillah shine abun da jama'ar palon ke faɗin,ba tare da Aryan yayi magana ba ya miƙe ya bar palon.


 jim kaÉ—an ya dawo hannun sa É—auke da akwatin bappa da key É—in kusa da hiyana yazo ya mika mata,kafin ta ansa bgs ya rigata ansa yana faÉ—in "ne menene wanna É—in!?" "Ka bata zata buÉ—e mana ne" cewar Ammi dan tasan tana ce masa magani zaa É—auka wa Aunty farida zai iya hanawa yace sai dai a kira likita. Ba musu ya mikawa hiyana akwantin ansa tayi ta yun kura zata mike,cikin sauri ya mikar da ita a hankali ya zaunar da ita tare sa saka mata pillow a bayan ta, a kule tace "kar ka sake taÉ“ani yaya Prince!" a sukwane ya waro manya manyan idon sa waje yana kallon ta ba shi ka É—ai ba kowa na palon ya girgiza da jin maganar hiyana barin ma Abba da Ammi, ita ko hiyana ko ajikin ta É—aure fuska sosai ta kara yi tana faÉ—in "Ammi taya ake buÉ—e a kwanakin?" Zama bgs yayi kusa da ita yana kallon ta har yanzu mamaki yake me yasa tace kar ya sake taÉ“ata ko dai zafin ciwo ne ya sanya tace hakan?.


"Bello ka nuna mata ta yadda zata buÉ—e" cewar Ammi mikewa yaya Bello yayi ya nufota yana faÉ—in "to Ammi" bai kai ga karisawa wajen ba bgs ya É—aga masa hannu yana faÉ—in "ni bana bukata in dai sai wani ya nuna mata yadda ake buÉ—ewa to sai dai kar a buÉ—e" ya kai karshen maganar tare sa ansan a kwanakin yayi wurgi da shi,shiru palon yayi duk kan su suna tsoron yiwa bgs magana jiki ba kwari yaya Bello ya koma wajen zaman sa ya zauna.


 girgiza kai Ammi tayi ta miÆ™e da kan ta ta nufi akwatin ta tsugunna tana kokarin É—auka sai ganin bgs tayi ya rigata É—auka É—aure fuska tayi tana kokarin yin magana idon ta ya sauka kan Abba dake girgiza mata kai alamar tayi shiru,ba musu tayi shiru ta koma saman sofan da ta tashi ta koma ta zauna.

Miƙa wa hiyana akwatin bgs yayi yana faɗin "ba sai wani ya nuna miki ba ki buɗe da kan ki" ansa tayi tana bin wajen sanya key ɗin da kallo

Daga karshe ta É—auko key É—in a hankali ta zura a ramin tana zurawa key É—in ya kwace kansa yayi cikin akwatin É—an karamin kara akwatin yayi alamar yana buÉ—uwa. Ya É—au tsawon yan mintoci yana yar kara kafin ya tsagaita jim kaÉ—an akwatin ya buÉ—u wani daddaÉ—ar kamshin turare ne ya fara fitowa daga akwatin nan take ya gauraye palon.


mikawa Ammi akwatin hiyana tayi Ammi ta ansa ta mikawa yaya Bello, ya ansa ya fara fitar da abubuwan dake ciki wani magani ya fito da shi kalar ruwan ganye ɗagowa yayi ya kalli Ammi cikin nitsuwa yace "Ammi babu maganin da zai karya asirin nan sai dai maganin da zai juya asirin ya koma kan wanda ya mata hakan" shiru Ammi ta ɗan yi kafin tace "aa Bello bai kamata mu zama irin ɗaya da su ba bai kamata mu mai da musu kan su ba ka dai kara dubawa" cike da jin haushi Aryan yace "kai zoka haɗa mata maganin ya koma kan nasu mana ba susuka haɗa ba suje chan su karata ai zasu san hanyan da zau bi su warware idan ma ya kamasu" da sauri Khalid ya ansa zanchen da cewa "kana da gaskiya Aryan tun da su basu da imani har suka iya mata wanna abun tofa ya zama dole su ansa hukunci ka mai da musu da kayan su kan su" gyaran murya Ummi tayi kafin tace "ranka ya daɗe me kace ya za'ayi!?" gaba ɗaya palon kallo ya koma kan Abba. Shiru ya ɗan yi na yan mintoci kafin yace "ayi yadda Aryan yace dan sun nuna ainihin rashin imani dan haka a mai da musu da kayan su" kallon yaya Bello Aryan yayi yana faɗin "sai ka fara aikin ko" "ku bani ruwa a roba tukun nan" cikin sauri amrat ta miƙe ta nufi waje.


Jim kaÉ—an ta dawo hannun ta É—auke da ruwa a roba mai É—an faÉ—i, gaban yaya Bello tazo ta ajiye masa tana faÉ—in "yaya Bello gashi nan".

  Jawo roban ruwan yayi ya fara karanto nasi falaki kulhuwa Ayatul kursihu yana tofawa cikin ruwan yana zuba garin maganin,bayan ya gama sai ya karaton ayoyi goma cikin ruratun bakara daga shafin 8 na farko ya karanta sau biyu sanna ya rufe da amanar Rasuluh.


Bayan ya gama haɗa komai ya ɗago ya kallin su Ammi yace "to ku shirya kuma duk ku fara addu'a a ranku dan shaiɗanun aljanu aka haɗata da su idan sun fita zasu iya komawa kan ɗaya daga cikin ku" jin haka ya sa diyana ta miƙe a sukwane ta koma kusa da Aryan ta zauna ta kankame hannun sa tare da kwantar da kanta a kafadar sa,saura kaɗan dariya ya kubce masa saboda razanar da diyana tayi ashe dai akoi abun da take tsoro Fahad kuwa rungume amrat ɗin sa yayi tare da kwantar da kan ta saman faffaɗar kirjin sa, kallon hiyana bgs yayi ya ga hankalin ta ma baya kansa "sister ki rufe kan kin nan da kyau" ko kallon in da yake hiyana bata yi ba sai ma kara ɗaure fuska tayi sosai ta kawar da kanta gefe duk abun da suke kan idon Ammi da Abba suke mamaki Abba da Ammi keyi to meke faruwa?.


A hankali yaya Bello ya ɗago kan Aunty farida yana faɗin "ku buɗe min bakin ta" sakin diyana Aryan yayi yana kokarin miƙewa diyana ta fasa kara tana faɗin "ni wlh tsoro nake ji!" alama da ido bgs yayi masa akan ya koma ya zauna ba musu ya koma ya zauna ya rungumo jiddan sa, miƙewa bgs yayi ya kariso wajen ya tsugunna ya sanya hannun ya ɗan buɗe bakin Aunty farida da sauri yaya Bello ya fara zuba mata ruwan maganin,

 ihu ta fasa tana kokarin kwache kan ta 

da karfi yaya Bello yace "ku rinƙe ta da kyau lokacin da zakuyi faɗa da sheɗanun aljanune yayi ku gwada musu karfin ayar Allah" gaba ɗaya mutanen palon sai da suka girgiza ganin yadda Aunty farida ke kokarin faɗa da bgs tana son kwace kan ta, wani wawan damka bga yayi mata a wuya yana kokarin mai data ya kwantar da sauri Ummi ta miƙe zata bar palon dan bazata iya ganin abun dake fatuwa ba "Hauwa'u ki dawo ki zauna ayi komai a gaban ki" cewar Abba Ummi kamar zatayi kuka haka ta dawo ta zauna ta sunkuyar da kanta kasa.


Ganin Aunty farida na neman tafi karfin bgs ne ya sanya Aryan mikewa a sukwane ya kariso wajen suka haÉ—a karfi suka danne ta,kuka sosai su Aunty mardiya keyi har da Aunty Maryam awan nan karon tayi hawaye. da kyar suka samu Aunty farida ta nitsu amma duk ta kukkije musu jiki ta jiwa Aryan ciwo a wuyar sa duk dauriya irin na Ammi sai da tayi hawaye Abba ma daurewa kawai yake ya sunkuyar da kansa kasa Aunty mardiya Aunty salma kam baa magana sunyi kuka har idon su ya sauya.


Bayan Aunty farida tayi shiru kamar mai barcine suka sake ta dukkan su suka koma suka zauna suna mai da numfashi kallon yaya Bello Abba yayi yace "yanzu sai me kuma bawan Allah" "babu komai Abba In Sha Allah tana tashi zata dawo dai dai Kum.....bai karisa maganar ba Aunty Amarya ta fasa ihu ta faÉ—i kasa tana birgima tana faÉ—in duk abun da ta aikata daga farko har karshe,kallon kallon juna suka farayi gaba É—aya jama'ar palon sun ma kasa magana masu kuka sun tsai da kukan nasu chak. 


sai da Aunty Amarya tayi surutan ta daga farko har karshe sanna tayi shiru tana kallon sama, mutuwar zaune Aryan yayi ya kasa magana gaba É—aya palon ba wanda ya iya cewa komai almost 30mins sanna Aryan ya miÆ™e tare da dafe sai tin zuciyar sa ya nufi hanyar fita yana faÉ—in "uwar da ta haifeni ita ta kashe min É—an uwana da hannun ta ta jefamin yan uwana cikin tashin hankali ta haukata min matata ta haÉ—a Ahmad da bala'i ta haÉ—a Aunty farida da ciwo  innalillahi wa Inna ilaihir rajiun Allah ka É—auki raina na huta dan ba.... Bai kai karshen maganar ba numfashi sa ya É—auke diff rai yayi halin sa ya yanke jiki zai faÉ—i a sukwane bgs ya kariso wajen ya taro sa yana kiran sunan sa a ruÉ—e "Aryan!!! Aryan!!! Aryan!!! Kada kamin haka kada kamin haka Aryan kayi wa Allah karkasa hakan a ranka kar ka cutar min da kan ka" yana magana cikin fitar hayyaci cikin tashin hankali "Aryan kasan dai nima bazan iya rayuwa ba tare da kai ba ko? Pls my blood ka tashi karka min haka" ya kai karshen maganar tare da shinfiÉ—e Aryan a kasa yana danna masa kirjin sa da karfi karfi, ganin bgs ya fita hayyacin sa yana kokarin yiwa Aryan illa ne ya sanya su Khalid suka kariso wajen da gudu suna kokarin jan bgs  baya  a fusace yayi watsi da su ya koma kan Aryan yana bubbaga masa kirjin sa yana kiran "no Aryan no i said no!!?  Kuka sosai su Aunty mardiya suke Aunty maryam kam tama kasa kukan tayi mutuwar zaune sumar zaune Omar yayi.

 yaya Bello kuwa lallaÉ“awa yayi ya kamo hannun hasana da hajjo suka bar palon, tashin hankali ya hana Abba yin magana Ammi Ummi duk bakin su ya mutu sun kasa ko motsi daga in da suke,runtse ido hiyana tayi tana hawaye ba karamin tausayi yaya Aryan ya bata ba Yusuf Khalid jiki ba kwari suka miÆ™e daga watsi dasu da bgs yayi suka koma kusa da matan su suka zauna dan wanna bala'i yafi karfin tunanin su Haidar ma hawaye yake Fahad kuwa ya sunkuyar da kansa kasa ya kasa ko motsi


 mikewa Aunty Amarya tayi ta rarrafo zuwa kusa da Aryan ta tsugunna cikin kuka tace "kayi hakuri É—ana ka yafemin ni da kai na na kashe yaya dukka biyu wayyo Allah na shiga uku na" ta kai karshen maganar tare da kai hannun ta saman kumatun Aryan, wani wawan damka bgs ya mata a wuya ya zaro idon sa da sukayo jaa kamar jini cikin tsawa yace "idan kika sake taÉ“a min É—an uwa wlh ba abun da zai hanani kashe ki azzaluma kin cuci rayuwata wlh idan Aryan bai tashi ba sai na miki kisan wulanci" waro ido waje Ammi tayi dan bata taÉ“a ganin bgs cikin tashin hankali haka ba ganin sa a haka ba karamin tsoro ya bata ba gaba É—aya ya canza lokacin guda fuskar sa tayi jaa kamar jini gashin jikin aa duk sun mimmike idon sanna kamar jini haka ya zamo jiyoyin kansa kamar zasu fito wajen gashin kansa ya watse sai cije lips yake da karfi.

gaba É—aya family dake palo sun tsorata ainun da ganin yananin da bgs ya shiga.


Zaro ido waje Aunty Amarya tayi kamar idon nata zasu faÉ—o kasa saboda shakar da bgs ya mata gashi kuma yaki sakin wuyar nata

Cikin sanyin murya da tausayin ƴaƴan nata dan tasan yadda bgs ke bala'i son Aryan kamar ransa Ammi tace "ka sake mata wuya kaji? zata iya mutuwa fa" "ta mutu mana ta mutu Ammi menen amfanin ta aduniya daman wlh idan Aryan bai tashi ba da kai na zan mata kisan wulanci saboda neman duniya ta tarwatsa mana farincikin rayuwar mu saboda son duniya ta kashe min ɗan uwana kuma ɗan cikin ta tir da shaiɗaninyar zuciya ya Allah duk in da muke dagani har yan uwana ya Allah ka tausaya mana ka bar mu da imani" ihu diyana ta fasa ta miƙe da sauri ta dawo kusa da Aryan tana faɗin "yaya Aryan karka mutu ka barni dan Allah ka tashi" wurgi da Aunty Amarya bgs yayi ya miƙe ya ɗauki Aryan ya saɓa sa a kafaɗa ya nufi waje da shi sai lokacin Abba ya samu damar yin magana yace "Safras ka dawo da shi nan karka kaishi ko ina" ba musu bgs ya dawo da shi ya shinfiɗe sa saman sofa mai zaman mutun 3.


Ihu Aunty Amarya ta farayi tana murkusoso ba wanda ya kulata sai Ammi da Ummi su suka nufe ta suna karanto mata addu'a cikin ihu take faÉ—in "Æ´aÆ´a na ku yafe min na shiga uku ni da kai na na kashe Aiman yanzu gashi na sa Aryan ya haÉ—iye zuciya ya mutu me ya rage min innalillahi nayi nadamar zuwata duniya sadiya kin cuce ni kin gama dani inna...bata kai karshen maganar ba rai yayi halin sa zuciyarta ta buga, kallon Ummi Ammi tayi kafin su juya a tare su kallin Abba yayin da shima su yake kallon, girgiza masa kai sukayi a tare alamar shikenan ta tafi kawar da kansa gefe yayi alamar ko in kula


after some minutes


Palon yayi shiru ba abun da kake ji sai sautin shesshekar kukan diyana ta kankame hannun Aryan sai kuka take, 

ruwan sanyi roba uku bgs ya zubawa Aryan amma shiru shiru Aryan bai farfaÉ—o ba,dafe kai bgs yayi da kyar ya iya buÉ—e bakin sa saboda bacin rai yace "Abba dan Allah ku É—auke gawar matar nan ban son ganin ta tana kara bakan tamin rai tana kara sani naji kamar zuciyata zata fashe ta fito waje" cikin karyewar zuciya Omar yace "Abba muje mu sallace ta ko?" "aa Omar ni bazan sallaci Hajara ba sai dai ku" shiru Omar yayi yana mai tausayin mahaifiyar tasu a kule Ammi tace "idan na isa da ku ku tashi kuje ku shirya makara akira mai mata wanka ku sallace ta ku kai ta ma kwancin ta" a sukwane bgs ya É—ago kai yana kallon Ammi É—aure fuska sosai Ammi tayi alamar bawa sa a tattare da ita mai da kansa yayi ya sunkuyar.

jiki ba kwari su Khalid suka mike suka fice daga palon ya rage daga matan sai bgs da Abba.


After 3 days 


Har yau Aryan bai fargaÉ—o ba tashin hankali ba kaÉ—an ba bgs ya shiga dan zuciyar Aryan gab take da bugawa gashi bai farfaÉ—o ba bare su bashi hakuri su taushe sa. Ko yaushe diyana tana kusa da shi tana kuka anyi rarrashin duniya taki yin shiru kuma taki matsawa kusa da shi.


Yauma kamar kullun misalin karfe 8 na safe tana kwance kusa da shi tana kuka kasa kasa,idon ta duk sun kunbura ta sauya kamar ba ita ba bgs na zaune gefen ta ya zuba musu ido yana jin tausayin su na ratsa shi Aunty farida na gefen bgs tasamu lfy sumul sumul abun ta. Su Khalid kuwa suna wajen ansan gaisuwar rasuwar Aunty Amarya


A hankali Aryan ya waro idon sa waje tare da É—aga hannun sa É—aya ya É—aura bayan diyana dake kwance kusa da shi ta bashi baya tana kuka l. kasa kasa da murya kamar mai raÉ—a yace "my jidda me ya sanya kike kuka? Ko so kike ki Æ™aramin ciwo kan ciwo ne? kin san fa kukan ki ciwo ne agareni a yanzu bayan Abba bgs Aunty farida ke kaÉ—ai nake kallo naji daÉ—i a raina ki dai na kukan nan haka ya isa, ji nake kamar kina chakamin mashi a zuciya ta idan kina kuka" a sukwane diyana ta juyo cikin shessheka tace "yaya Aryan dole zan yi kuka ba kai ne ka... Bata karisa maganar ba ya rufe mata baki da hannun sa tare da jawo ta jikin sa yana É—an bubbuga bayan ta sai lokacin idon da ya sauka kan bgs da Aunty farida,yana kokarin yi musu magana bgs yayi saurin É—aga masa hannu alamar yayi shiru dawo da kallon sa kan diyana yayi cikin zolaya yace "my jidda ba kince baki so na ba me kuma ya saki kuka dan zan mutu?" "Yaya Aryan ka dai na faÉ—in haka wlh bazaka mutu yanzu ba kuma Ni bance bana son ka ba ina son ka mijina ina son ka sosai" "eyeee babyn yaya Aryan yau ta dai na jin kunya har da cemin miji da ina da lfy danayi sujudur shukur na godewa Allah" miÆ™ewa bgs da Aunty farida sukayi suka bar É—akin dan sunga Aryan da diyana sun fara sakin layi. 

Rungume ta sosai Aryan yayi yana rarrashin ta ita kuwa sai zuba masa shagwaɓa da kalaman love take "my jidda waya koya miki kalaman soyayya" ya tambaya yana gyara mata kwanciya ɓoye fuskar ta tayi a girjin sa kafin tace "a littfin Romeo na Princess Teema na koya" shafa gashin kanta ya fara yi yana faɗin "wayace ki rinƙa karanta Novel?" "Yaya Aryan ina karanta Novel ne dan na koyi yadda zan rike ka" waro ido waje yayi tare da sakin ta yana kokarin mikewa zaune,da gudu ta mike ta bar ɗakin,bin bayan ta da kallon yayi har ta fice murmushi ya saki kafin yace "Nagode wa Allah daya nunamin ranar nan da jidda ta ta sauya har da zubamin kalaman soyayya" ya kai karshen maganar tare sa zuro kafar sa kasa ya mike da kyar yana taga taga har ya fice daga ɗakin ya nufi wajen Abba.


Yau ne Abba ya kira meeting na karshen akan issue marigayya Aunty Amarya, gaba É—aya family sun taru a palon.

 Abba cikin nitsuwa Abba ya fara magana "Aryan na san baka sani ba Allah ya yiwa mahaifiyar ku rasuwa tun shekaran jiya ina fatan kuma zaku yafe mata abun da ta aikata muku? Ni dai har ga Allah na yafe mata haka Aisha da Hauwa'u suma sun yafe mata kuma zan zo naji kun faÉ—a da bakin ku kun yafe mata sanna ku cigaba da neman mata gafara wajen Allah" a tare suka amsa da "Allah ya yafe mu tare Abba mun yafe mata" ajiyar zuciya Abba ya sauke kafin ya cigaba da cewa "to sai batu akan mulki munyi magana da Aliyu zai dawo Nigeria next week ya ansa mulkin sanna na sanya antona asirin da Hajara ta binne a kan mulkin nan,gaba É—ayan ina mai sallamar ku akan ku koma bakin aikin ku tun da komai ya dai dai tun" "no Abba komai bai dai dai tu ba dole na kama wanda ya sanya aka kama su Khalid" cewar bgs jinjina kai Abba yayi kafin yace "haka ne to Allah ya bada Sa'a akoi wani mai magana!? Shiru palon yayi Aryan ya sunkuyar da kai kasa yana mai takaicin rasuwar da Aunty Amarya tayi ba tare da ta nemi yafiyar mutanen da ta cutar a rayuwa ba.

 

"Abba ina da magana" cewar hiyana nan take kallon ya dawo kanta "to hiyana ina jin ki menene maganar taki faɗi" sunkuyar da kanta kasa tayi cikin jin kunya ta fara magana "Abba kasa yaya Prince ya sake ni bana son shi bana son zama da shi mugune" a sukwane bgs ya ɗago yana kallon ta gaba ɗaya su Khalid kara waro ido waje sukayi suna kallon ta Abba da Ammi ba karamin girgiza da jin maganar nata sukayi ba daurewa Abba yayi yace "lfy hiyana kike son yayan ki ya sake ki!? "Abba ba lfy ba yaya prince ya cutar da ni arayuwa ta sosai nayi hakuri har nagaji bazan iya ba wlh Abba yaya Prince yana gab da kashe idan kuka sake bari na da shi" nan hiyana ta shiga basu lbr duk abun da ya faru na muguntar da bgs ya rinƙa yi mata daga farko har karshe.


 Tirkashi nan take ainihin É“acin rai da tashin hankali ya bayyana karara a kan fuskar Abba da Ammi cikin fushi Abba yace "tabbas babu makawa Safras zai sake ki yanzu kuwa ba sai anjima ba" waro ido waje bgs yayi tare da sunkuyar da kansa saka kamar mai tunani wani abu "Auta ku tashi ku je É—aki bari muyi magana" cewar Aunty farida mikewa Zahra hiyana diyana amrat lamrat sukayi suka bar palon,kallon Omar da Haidar Aryan yayi tun bai yi magana ba suka mike da sauri suka fice.


"Safras ina mai umartan ka da ka rubuta takardan sakin hiyana ka kawomin yanzun nan" cewar Abba Aunty farida na kokarin yin magana Abba ya dakatar da ita yana faɗin "kar wanda ya samin baki a maganar nan dole ya sake ta ashe Safras zaka iya kashe yar uwar ka dan kiyayya kajefota daga sama ta faɗa cikin ruwa sanna duk bai isheka ba sai ka harɓeta da bindiga? To wlh ka rubuta sakin ta yanzun nan ka bani a nan na aura mata wanda take so" mikewa bgs yayi ya nufi hanyar fita yana faɗin "bari na kawo maka Abba" mutuwar zaune su Aryan su kayi lallai bgs wato ma bai damu ba bari ya kawo akar dan sakin tab



To masu karatu sai mun haÉ—u gobe idan mai dukka ya kai mu

No comments