Recent Updates

Duk Karfin izzata Book 2 Page 37

 


💖The talent troupe writer's 💖





💋Duk Karfin Izzata 💋


By Star Lady



       





Page 37



___wanka Aryan yayi a gurguje ya shirya ya fito kai tsaye É—akin horo ya wuce.

Zaune ya samu bgs Yusuf saman kujera mai zaman mutun 3 ga hajj sadiya da jabir zaune a gaban su.


Kusa da bgs yazo ya zauna yana faɗin "kun musu tambayoyin ne? Shiru bgs yayi Yusuf ne ya amsa da cewa "aa kai muke jira" dawo da kallon sa yayi kan su jabir cikin nitsuwa ya fara magana "jabir ina mum ɗin ka? cikin ladabi da girmamawa jabir ya soma magana "mum na tana wajen Aiki dad na kuma ya fita sai dare zai dawo" satar kallon bgs ta kasan ido Aryan yayi kafin ya ci gaba da magana "ok awani unguwa gidan ku yake" jabir na kokarin yin magana bgs yayi saurin cewa "No bamu bukatar address naku kawai ka bamu phone number dadyn ka dake tafiya"ba tare da ɓata lokacin ba ya fara karanto musu phone number dadyn su,kallon Yusuf Aryan yayi ba tare da yayi magana ba cikin sauri Yusuf ya ciro wayar sa ya fara ɗaukan number


Gyara Zama Aryan yayi da kyau ya fara magana a nitse "Sadiya kunce mana yar ki É—aya a duniya haka shima baban ta ita kaÉ—ai ke garesa to amma ya akayi wanna ya kasance É—an sa"ya kai karshen maganar yana nuna jabir da hannu 

Kallon in da jabir yake haj sadiya tayi kafin tace "ni ban san shi ba gaskiya kuma ni na san iya kan zulaihat ce kawai garemu daga ni har baban ta" waya Aryan ya fita ya shiga cikin wayar ya fiddo musu da hoton dadyn jabir yana faÉ—in "wanene wanna?" har suna haÉ—a baki jabir tace "Dady na ne" haj sadiya kuma tace "dadyn zulaihat" tsaki Yusuf yaja cikin É“acin rai ya fara magana "kai bamu son wasa a nan wajen, kai ina maman ka take Aiki?" "Ni ban ma san wajen aikin taÉ“a iya abun da na sani shine wani lokaci tana zuwa school namu" " wani school!? Cewar Yusuf 

jabir na kokarin magana bgs ya katse shi da cewa "ya isa haka ku tattara min su a gaba na ban san ganin su namijin ku kai shi gidan gyaran hali dan na fahimci laifin baban sa ne bai basa tarbiyyar da ta dace ba so a turasa gidan gyran hali na 7 years,ita kuma matar nan ku sanyata a islamiya dan babu ilimin addini a kanta ko kaɗan duk ranar da bataje islamiya ba na baku izini ku harɓeta da bindiga dan bata da amfani duk mutumin da bai san ta yadda zai yi bautar Ubangijin saba bashi da wata amfani a duniya" yana kai karshen maganar ya miƙe ya fice daga ɗakin

 kallo Yusuf Aryan yayi tare da miÆ™awa ya nufi hanyar fita yana faÉ—in "Yusuf sai ka aiwatar da aikin  da bgs ya faÉ—a" yana kai karshen maganar ya fice daga É—akin


Tasasu a gaba Yusuf yayi ya bar gidan da su kai tsaye ya wuce prison da jabir.



É—akin binciken bgs da Aryan suka koma

 mamaki bgs Aryan keyi shi da yake wanka sau ba a irga a rana amma yau tun da yayi wanka da safe bai ma sake komawa É—akin sa ba aiki kawai yake tika har ya rame sosai lokacin guda ya sauya kamar ba shi ba

 bincike suka farayi a kan number dadyn jabir sai zufa bgs yake ganin haka ya sanya Aryan yaje ya É—auko masa ruwan roba mai sanyi yana miÆ™a masa ya ansa tun da ya kafa É—an karamin bakin sa a kan robar ruwan nan bai É—aga ba sai da ya shanye tas Allah sarki yana jin kishin ruwa amma ya kasa zuwa ya É—auko ruwa domin kowani minti É—aya na rayuwar sa tana da matikar mahimmanci gani yake kamar idan ta É“ata 1 minute zai iya rasa su hiyana.

Ganin ya shanye ruwan dukka ya sanya Aryan yaje ya karo masa roba ɗaya ya dawo ya miƙa masa ansa yayi da hannu ɗaya hannun sa ɗaya na kan system kafa kai yayi a robar ruwan sai da ya sha fin rabi sannan ya cire ya ajiye a gefe kallon Aryan yayi da sauri Aryan ya kariso gaban system ɗin


Kallon bgs É—in yayi kafin yace "kenan mutumin nan yana kusa da mu?" girgiza kai bgs yayi kafin yace "baya nan yayi wasa da hankalin mune ta yadda ko mun bibiye sa zai na nuna mana wrong location  amma idan ya san wasu bai san Brigadier general Safras ba nayi tracking kwakkwafi a layin nasa a hankalin yanzu yana Bristol palace hotel" "what are you saying? baga area nan location na number sa ya nuna wa ba?" "Aryan na ce maka baya nan kawai yana so yayi beating na brain namu ne amma yana in da na faÉ—a maka" yana kai karshen maganar ya juya ya fice daga É—akin girgiza kai Aryan yayi kafin tace "eh ba a banza ka zamo Brigadier general ba tab irin wanna rikitar da Æ™waÆ™walwan haka mutun kamar wani aljani to Allah ya kara kare mana kai É—aya tamkar millon" kashe na'uran dasu wajen yayi ya fito dan yabi bgs su tafi tare amma sai ya tarar da bgs ya tafi girgiza kai yayi yana faÉ—in "So ba wasa ba bgs lallai kana son sister over wato ma tafiya kayi ka barni In Sha Allah ba abun da zai faru da matar ka zata dawo gareka lfy" 


yana tsaye yana ta zancen zucin sa sai ganin motar Shahram yayi ta danno kai cikin gidan mamaki yake ina kuma Shahram yaje 

yana tsaye yana kallon su har Shahram ya fito daga motar ya buÉ—e wa Ammi ta fito rike da hannun yarinyar da ya buge da mota shafa kan sa yayi shi gaba É—aya ya manta da ya buge wata yarinya ko hospital É—in bai sake komawa ba yana kokarin yin magana wayar sa ta fara kara yana dubawa bgs ne ke kiran sa cikin sauri ya ce da Shahram ya juya kan motar su tafi,

wani nauyayyar ajiyar zuciya Shahram ya sauke dan bai taɓa tunanin Aryan zai sake kula shi ba godiya yayi ga Allah yana rokon Allah da ya bashi ikon rike musu amana koda zai rasa ran sa Aryan da bgs ba mutane da zaa ci amanar su ba ne suna da kirki da tausayin talakawa kai gaba ɗaya yaran Abba ba mutanen banza bane.


A ɓangaren yaya Bello kuwa cikin kwana ɗaya sun chanza sosai Ahmad na basu kulawa fiye da tunanin mai tunani yana matikar kaunar Hajjo ba ka ɗan ba hasana har ta fara koyan girki da gas abun gwanin ban sha'awa sai wanda ya gani.


Lokacin da Aryan ya shiga hotel É—in already bgs ya kama dadyn jabir yana tsaye a jikin motar sa tayar motar ta fashe da alama harbin talar akayi da gun shi ya sanya ma ya kira Aryan


Motar dasu Aryan suka zo da shi bgs ya shiga yayiwa dadyn jabir É—aurin goro da alama sai da suka kai ruwa rana kafin bgs ya samu ya kama shi 

  "Aryan ka sanya sojoji su kwashe gawar sauran dake cikin hotel É—in" wucewa Aryan yayi ya nufi É—akin hotel É—in yana faÉ—in "ku jirani bari na duba ko zan samu wani karin evidence" shiru bgs yayi bai yi magana ba da sauri Shahram yabi bayan Aryan dan yanzu tsoron bgs yake sosai musamman kwana biyun nan da gaba É—aya bgs baya hayyacin sa ya sauya.


Aryan na shiga É—akin kallo É—aya yayiwa yaran baban jabir ya kawar da kansa gefe yana kallon Shahram ya furzar da iska mai zafi daga bakin sa kafin yace "lallai kunji maza irin wanna duka tabbas na yarda bgs baya hayyacin sa wlh duk wanda yayi kuskuren shiga gonar bgs a wanna yanayi tofa da wuya a iya gane gawar sa ma, Shahram kayi waya sojoji su zo ku kwashe su ku kai su mutuware" yana kai karshen maganar ya fice yana mamakin irin dukan da bgs ya musu duk ya faffashe musu fuska da jini kamar sunyi karo da motar É—angote.


In da ya bar bgs nan ya dawo ya same sa shiga gaban motar yayi ya jasu suka fice daga hotel suka bar Shahram awajen dan ya kwashe gawar yaran dadyn jabir.


To ya kamata mu wai wayi Aunty farida dan muga ya take



Lokacin da Aryan ya shigo da Aunty farida gidan kai tsaye part É—in Ammi ya kai ta dan yasan Ammi tafi Ummi hakuri da dauriya yana kai ta ya fice daga gidan gaba É—aya dan ba zai iya ganin tashin hankali dake kan fuskar yan uwan sa ba.


Ba Æ™aramin tashin hankali suka shiga ba barimma Abba,ya É—auko malamai ana ta mata addu'a dan yanzu ya samu bgs da Aryan basa zama shi ya sanya basu hana malaman zuwa ba Aunty salma Aunty mardiya duk sun zo Aunty Maryam ne kaÉ—ai bata zo ba suna iya bakin kokarin su wajen ganin sun kula da Aunty farida 

 matan Abba dukkan su ba wan da yake shiga part É—in yar uwar ta sai da wata dalili shi ya sanya Abba yace kar a faÉ—a wa Ummi Aunty farida bata da lfy a barta a part É—in Ammi a bata kulawa awajen har Allah ya bata lfy Ummi bata da hakuri da dauriya irin na Ammi tana samun lbr rashin lfy Aunty farida zata sa damuwa a ranta har itama wani ciwo ya kamata shi ya sanya suka kyale Aunty farida awajen Ammi sosai su Aunty salma ke kula da ita

bgs tun da ya rabu da su a airport bai sake leko su ba dan baya hayyacin sa gwara Aryan yau da safe yaje ya dubata Fahad Haidar Omar duk suna kusa da ita ko yaushe barinma diyana tana manne da ita dan tana matikar kaunar Aunty farida sosai lamrat kuwa tana can tana fama da amai Zahra kuma tana part É—in bgs bata ma da lbr abun da ke faruwa.


Bgs  and Aryan


Kai tsaye headquarter suka wuce da dadyn jabir dan ba karamin criminal bane

Suna shiga ba ɓata lokaci suka fara bincike sa


Cikin ɓacin rai da zafin nama Aryan yace "ina ka kai min ɗan uwana da sister na!? da kyar dadyn jabir ya iya ɗagowa saboda ɗaurin da bgs ya masa kai daga ganin ɗaurin kasan ɗaurin haushi ne rai a ɓace akayi ɗaurin

   "wace sister ka kuma bayan an sanar da ni kun kwace sister na ku kuma kun tafin mi da yarona" wani wawan baushi Aryan ya kai masa a baki har sai da bakin ya fashe cikin tsawa yace "idan baka faÉ—amin in da ka kai su Khalid ba sai na fasa kan ka da bindiga!!" 

MiÆ™ewa bgs yayi ya kwance É—aurin da ya ma dadyn jabir É—in ya zaunar da shi suna fuskantar juna yana kokarin yin magana Aryan ya rigashi da cewa "bgs bafa lallaÉ“a sa zakayi ba ka kyale ni na masa bugun mutuwa wadda sai ya faÉ—i gaskiya ba shiri" hannu bgs ya É—agawa Aryan yana faÉ—in "no Aryan ba shi ya É—auki su Khalid ba kayi shiru ka zauna ka saurare mu kawai" waro ido waje Aryan yayi yana faÉ—in "wanene to ya É—auke su to!? Kallon dadyn jabir bgs yayi rai a matukar É“ace ya fara magana "menene tsakanin ka da Abban mu da har kake bin family mu da sharri!?" shiru dadyn jabir ya É—anyi kafin ya fara magana "Abban ku ya cuceni ya raba ni da masoyiyata da nake matikar son ta fiye da raina" nuna Aryan yayi da hannu ya ci gaba da magana "nayi soyayya mai tsananin gaske da mahaifiyar ka tana so na nima ina son ta kusan shekara 4 muna tare da juna daga zuwan Abban ka ya juya mata tunani ban sani ba nayi tafiya zuwa Abuja lokacin ina dawowa na samu lbr hajara tayi Aure ba karamin tashin hankali na shiga ba nayi rashin lafiya sosai dan ina matikar kaunar ta sai da na É—auki shekara 2 ina cikin jimamin rasa ta. bayan na warke daga ciwon son tane na fara tunanin ta yadda zanyi in É—auki fansa akan shi. daga baya na yanke shawarar in dawo kano nima kusa da ita ta yadda zan samu damar É—aukan fansa, na zauna a nan tsawon shekara 6 kafin na haÉ—u da wata baturiyan us mai kuÉ—i mukayi aure na bita muka koma us munyi zaman shekara 6 a chan kafin na matsa mata mu dawo Nigeria dan na dauki fansa akan Abubakar saraki muna gab da dawowa ta haifamin É—a namiji na sa masa suna jabir  ko da muka dawo nan gida Naija time to time muna can us sakamakon ita mum jabir tana hada hadan shigo da makamai kasarnan tun bana sha'awar harkan har na fara tayata. tun dana fara harkan ne sai na manta da É—aukan fansa har sai da wani ya bugi jabir a makaranta danayi bincike sai maga É—aya daga cikin family Abubakar saraki ne shine na dawo da zancen É—aukan fansa ta sabuwa daga lokacin na fara bibiyan yan gidan ku amma har yanzu ban samu nasara ba idan ba jabir da ya kama sister kuba ni ba ita nake so ba shi ya sanya ban bi ta kan jabir É—in ba ni Abubakar saraki da jarana nake son kashe wa ba ruwana da ku" girgiza kai bgs yayi kafin yace "ok to ya batun É—ayar matan kan fa!? "Sadiya matata ce itama amma ita na aureta ne dan a binciken da nayi naga tana da kusan ci da hajara nayi nayi na samu damar da zan jefa Abubakar saraki cikin tashin hankali amma ban samu daman  ko kallon face na shi ba shi ya sanya na auri sadiya na yi amfani da ita dan na samu naja Abubakar saraki kan titi amma duk da haka abun yaki yiwuwa daga baya sai na yanke shawarar  na tura yata akan tazo ta samomin makamar da zan rusa farincikin Abubakar saraki,nan ma banyi nasara ba kuka kamata" "ya akayi matar ka ta farko bata san da na biyu ba!?  "Eh ai na faÉ—a muku sadiya ba son ta nake ba kawai nayi amfani da ita ne. ita kuma mum jabir ina kaunar ta har raina shi ya sanya shi jabir ban sa shi a harkan mu ba na sanya Zulaihat dan ita ba na kaunar ta kwata kwata kawai ina zaune da su ne dan biyan bukata ta" kallon wulakanci bgs ya masa kafin yace "amma me ya sanya kake kwana da yar ka na cikin ka duk da kana da mata biyu? "Malami nane yace inrin Æ™a kwanciya da ita har tsawon wata 6 zan samu biyan bukata ta akan Abubakar saraki,amma tun da na kwanta da ita na tsawon 6 month ban sake ba ai" tsaki Aryan yaja yana mai nadamar kashe zulaihat da yayi ashe ma ba laifin ta bane laifin baban tane 

     "yanzu da ka É“atawa yar ka rayuwa ka yarda da zancen bokayen banza bokayen wofi hakan ya sanya kacika burinka ne? abun da mutane suka kasa kagewa tayaya za'ayi É—an adam kamar ku kuma kuce zai baku abun da Allah bai baku ba tayaya zai iya biya muku bukatar ku? Ai idan har É—an Adam zai iya biya muku bukatar ku to ku da kan ku ma zaku iya biyawa kan ku buta dan dukkan ku mutane duk É—aya kuke ta wani bangaren ma kafishi nagarta amma sai kuje ku zauna katon banza yana shirya muku karya yana raba ku da samun rahman Ubangiji ku yanzu wa gari ya waya riban me kaci ka lalata rayuwar Æ´aÆ´an ka gaba É—aya ka tarwatsa family ka kazo a banza zaka koma a banza daman duk wanda bai riÆ™e Allah ba abanza zanzo kuma ya koma a banza duk wanda bai riÆ™e Allah shi kaÉ—ai ba tabbas ya taÉ“e" yana kai karshen maganar ya miÆ™e ya nufi hanyar fita yana faÉ—in "Aryan ku kashe sa ta hanyar rataya dan ya cancanci hakan ya aikata laifi da dama ya shigowa yan ta'addan da makamai sun kashe bayin Allah da basu ji ba basu gani ba" 


jin wa'azin da bgs yayi wa dadyn jabir ba karamin sanya Aryan yayi ya kara ganin girman Allah ji yayi gaba ɗaya ya tsani rayuwar ma godiya yake ga Allah da ya sanya Aunty Amarya bata auri dadyn jabir ba dan idan akace irin dadyn jabir ne ya haife sa to tabbas zai kashe sa da kan sa kuma tabbas idan mutun baya tsoron Allah ya taɓe ya gama yawo ya Allah duk halin da zamu shiga Allah ka tausaya mana ka barmu da imani


 yayi nisa cikin tunanin ya jiyo vaice na bgs yana faÉ—in "ka tura sojoji su kamo matar tasa dan ita ma babban criminal ce tun da yan ta'addan take wa safaran maka mai a mata É—aurin rai da rai a gidan yari dan bata da wata amsani,shi kuma É—an nasa a fitar da shi ku sa min shi a islamiya dan ba laifin sa bane laifin uban sune bai da laifi yana bukatar ilimin addini" "to Aryan ya amsa da shi ya kama dadyn jabir ya mikawa sojojin dake headquarter tare da musu umarnin su rataye sa sanna ya basu umarnin akan su kamo mum jabir su mikata Court amata hucunci,

  Yana gama magana ya ciro wayar sa ya kira Ahmad bugu É—aya Ahmad ya É—auka "Ahmad aiki ya same ka a court wata criminal ce karka kyaleta har sai ka tabbatar an yanke mata hukuncin É—aurin rai da rai shine umarnin bgs" yana kai karshen maganar ya katse kiran ya bi bayan bgs.



A É“angaren su hiyana kuwa wunin yau gaba É—aya haka ta wuni ba abinci ba ruwan sha, wuyar ta ya bushe sosai tun tana iya haÉ—iyar yawu har ta kasa sa duk da haka bata karaya ba tana sa ran samu Rahman Ubangijin tana da yakinin yaya Prince zai zo ko bai zo dan ita ba zaizo dan yaya Khalid shi kuma yaya Khalid ba zai iya tafiya ya barta ba 

A haka har dare tun tana jurewa har ta fara kuka kasa kasa ta dafe cikin ta tana murkusoson yinwa 


Sai 9:30 na dare ogan su ya buÉ—o kofar É—akin nata ya shigo hannun sa É—auke da wata barkar plate kusa da ita ya ajiye mata plate É—in ya juya zai fita cikin sauri tace "wanna ai kamar namar kare ce" ba tare da ya juyo ba yace "eh naman kare ne shine kuma abincin da muke ci a nan" tsaki taja kafin tace "no wonder shi ya sanya baku da imani ai duk wanda ya bijire umarnin Allah to yana cikin wahala idan kukayi wasa da naman kare zaku kare wlh. Ni danayi abun da zan taka dokar Ubangiji na gwara na mutu dan haka ka É—auki naman karen ka ba zanci ba dan danaci gwaramin yinwa ta kashe ni amma ba zanci abun da Allah ya haramta ba" juyowa yayi ba tare da ya mata magana ba yazo ya É—auki plate din naman ya fice daga É—akin ya sanya key ta rufeta kuka ta cigaba da yi dan ba karamin murÉ—an yinwa cikin ta ke mata ba ga kishin ruwa



To masu karatu sai mun haÉ—u gobe idan mai dukka ya kai.


Pls a zubomin ruwan comments nima ku nishaÉ—antar  dani

No comments