Recent Updates

Duk Karfin izzata Book 2 Page 36


 ðŸ’–The talent troupe writer's 💖





💋Duk Karfin Izzata 💋


By Star Lady



       





Page 36




....suna kokarin kamata ogan su ya daka masu tsawa "kai kuma da hankali kuwa!!? Kunsan me kuke shirin aikatawa kuwa!? kuwuce ku bani waje hai" wadda hiyana ta marane yace "haba oga baka ganin yarinyar nan marina tayi ne? ɗaure fuska ogan nasu yayi kafin yace "bana son shirme adam idan ka taɓa yarinyar nan kana tunanin oga zai barmu da rai ne?ae, ko me ta maka hakuri zakayi sai oga ya bada umarnin hukuncin da zaa mata sanna kai ma ka ɗauki naka fansan yanzu gashi ka sumar da wanna bayan oga yace mu bashi horo mai kyau amma karmu kashe shi to yanzu dai ba halin mu horar da shi sai dai ma mu bashi kulawa ta yadda zamu tsayar da jinin nan idan ba haka ba zai iya mutuwa dan jinin sosai ne ke zuba daga jikin sa ku ɗauke sa ku kai sa treatment room Auwal ya duba shi a samu a tsai da jinin nan kafin mu fara bashi horo ita kuma yarinyar ku kai ta ɗakin kunama ku ajiye ta" yana kai karshen maganar ya wuce ya bar wajen.

guntun tsaki hiyana taja a ranta tana faÉ—in "ba É—akin kuna ma ba ko É—akin aljanu zaku kai ni ta Allah ba taku ba ato duk wan da ya rike Allah shi kaÉ—ai baya taÉ“a taÉ“ewa a duniya na rigaku nace Allah wlh ba wanda ya isa yamin abun da Allah bai min ba ba kuma wanda ya isa ya hana abun da Allah ya min makarya tan banza matsoratan wofi" tayi nisa cikin zancen zucin ta sai ganin wasu jibga jibgan maza tayi suna kokarin É—aga ta rintse ido tayi ta daka musu tsawa "karki kuskura ku taÉ“ani!! juyowa ogan nasu dake tafiya yayi yana kallon su yana mamakin dakiya irin na hiyana gashi basu isa su mata wani abu ba tare da ogan su ya basu izinin yin hakan ba 

 dawo yayi wajen cikin umarni ya fara magana "adam ku kira matan nan masu mana girki su chaje yarinyar tun da bata son maza su taÉ“a ta shi ma na mijin kuyi saurin charje shi" sai lokacin hiyana ta tuna da nauran da yaya Prince ya bata wadda ta barosa saman mirror É—akin sa ji tayi kamar zatayi kuka yanzu ta ina yaya Prince zai nemo su amma ba komai Allah nanan domin Allah ba azzalumin bawan sa bane sai dai bawa ya zalunci kan sa.


Haka ko akayi wasu mata ne sukazo suka charje hiyana tsab daga sama har kasa basu samu komai a jikin ta ba

Haka suka ja ta zuwa É—akin kunama suka kulleta 


Shima Khalid charje sa sukayi tsab sunyi nasanar jiro na'urori guda biyu a jikin sa cikin sauri É—aya daga cikin su ya shiga cikin mota ya fice da nauran daga gidan

Adam da kan sa ya É—auki Khalid zuwa É—akin da suke duba kansu idan basu da lfy



Hiyana kuwa suna shigar da ita É—akin  wasu jigba jihab kunamu ta fara cin karo da su ko ajikin ta juyawa tayi a É—akin ta nemi Wajen kasa mai É—an tsarki taje tayi taimama,duk da bata san inane gabas awajen ba haka ta tada sallah tana sallah tana jin kunamun suna hawa kafar ta amma bata damu ba bama tayi ko da motsi ba dan tasan ba abun da zasu iya mata ai ba aban za suke zaune a dajin su ba su da suke rayuwa da kaciji da kunama kullun.


Bayan ta idar da sallah ne ta zauna tafara jero wa Allah kirari da addu'a akan Allah ya kare su ya kare mata mijin ta  daga sharrin duk wani abun halitta 

Tana cikin addu'a ne wata kunama ta hauro saman kumatun ta tana jin sa sai yawo yake mata a kumatun ta 

  Sai bayan da ta kammala addu'ar ne ta sanya hannu ta kusa da kunamar tace "bawan Allah kayiwa Allah ka sauka jiki na idan ma wani laifi na maka kayi hakuri" bin hannun ta kunamar yayi ya gangaro har wajen tafin hannun ta a hankali ta sauko da hannun nata kasa kunamar ya sauka,ba karamin mamaki ta shaba ita dai a iya sanin ta tasan kunama na harbi to ya akayi bai har beta ba? Tunawa da maganar bappa tayi lokacin da yake faÉ—a musu ba kowani dabba bane yake cizo da gangan wani yana cizone dan ya kare kan sa wani kuma yana ciwo ne idan akan matsa masa amma ko wani irin dabbane idan dai ba sheÉ—ani ba annabi yace idan ka haÉ—ashi da Allah ka masa magana ba zai cutar da kai ba sai dai in sheÉ—anin aljani, lokacin guda taji tsoron Allah ya kara ninkuwa a ranta lallai duk wanda baya jin tsoron Allah ya taÉ“e  ya shiga uku ya lalace ko kwayar idon É—an Adam ka gani ya isa ya saka ka kara sanin girman Allah ya Allah duk halin da zamu shiga Allah ka tausaya mana ka barmu da imanin mu.


Sai tunani take ta tunano wanna ta tunano wacan har barci wahala ya fara É—aukan ta gyara wa tayi ta kwanta a wajen ba jimawa barci yayi awon gaba da ita


A É“angaren Zahra kuwa 

gaba É—aya ta gaji da É—aurin da jabir ya sa akamata da kyar da kyar take numfashi ga yinwa da kishin ruwa sun addabe ta gashi rana ya iso wajen da take sai zufa take haÉ—awa


Da dai taga su jabir basu da niyar kulata ko zata mutu su suna zaune a inuwa suna buga whot idan sun gaji su koma lido da alama ma sun manta da ita awajen

Rai a ɓace ta ɗaga murya tace "jabir kazo ka bani ruwa na sha kishi nake ji" ba musu ya mike ya tare da ɗaukan roban ruwan dake kusa da shi yazo gaban ta kamar abun kirki ya buɗe bakin robar ruwan kamar zai bata a baki sai kuma ya watsa mata a face nata tare da shekewa da dariyar mugun ta girgiza fiskar ta tayi tana mai nadamar tambayar sa ruwan da tayi hannu ya ɗaura saman wuyar ta ya gangaro da shi a hankali,yana faɗin "ashe kema Zahra ba baya ba wajen kyau shine na kafe sai hiyana ai da tun ɗazun ni da yarana mun ɗan huta da ke ka ɗan ai" yana magana yana gangaro da hannun sa saman kirjin ta.


Kamar daga sama yaji tas an harɓi hannun nasa da gun,ihun azaba ya saki ita kuwa Zahra ihun murna ta saki dan ko ba a faɗa mata ba tasan yaya Prince ne ya iso, a guje yaran dadyn jabir suka miƙe suna kokarin ɗaukan gun nasu

Kafin su kai ga ɗaukan gun ɗin bgs ya harɓi mutun uku daga ciki cikin zafin nama ya shigo wajen kafin suyi wani yunkuri ya harbe su dukkan su ba wanda ya harba a in da zasu mutu dan yana bukatar su a raye,

wucewa Yusuf dake bayan sa yayi ya kwance Zahra sanna ya É—aure jabir da igiyar da ya kwance Zahra


Da gudu Zahra ta tafi ta faÉ—a masan faffaÉ—ar kirjin bgs tana kuka tana faÉ—in "yaya Prince wasu ne suka tafi da Aunty hiyana da yaya Khalid" yasar da gun É—in hannun sa yayi ya rungumeta ta kyau tare da shafa bayan ta

da kyar ya iya buÉ—e bakin sa cikin matsanancin bacin rai kasa kasa yace "zaki iya gane fuskar É—aya daga cikin su? girgiza masa kai tayi kafin tace "aa" É—aukan ta yayi chak tare da yiwa Yusuf umarni akan su kwashe mutanen nan su kai su headquarter zai wai waye su,yana kai karshen maganar ya fice É—auke da Zahra a kafaÉ—ar sa 


Suna shiga cikin mota ya É—auki wayar sa ya fara kiran layin Aryan bugu É—aya Aryan ya É—aga yana faÉ—in "hello" "Aryan ka sanar da security kar wanda ya sake fita ko shiga gida ba tare da izini na ba" yana gama faÉ—in hakan ya katse kiran ya tada motar da kan sa da gudu suka bar wajen


"Me ya haÉ—aki da yaron nan da ya kamaki? Sanna me ya rabaku da su Khalid bayan Yusuf yace min tare kuka fita!? Kallon in da yake tayi kamar zatayi kuka ta fara magana "muna tafiya ne wasu suka tare mu suka É—auki hiyana da yaya Khalid suka barni ni kaÉ—ai shine ina tafiya shikuma jabir yazo ya kamani" 

  "Wanene shi jabir É—in? Ai na kika sanshi? dan haka kawai dai bazai kama ki ba" "a makarantar mu na san shi shine wan da ka taÉ“a mari lakacin da yazo zai mari hiyana ka riÆ™e hannun sa ka buge sa har ya suma" a sukwane bgs ya taka birki motar har sai da kai zahra ya bugu da marfin motar  "what are you saying!?" zaro ido waje Zahra tayi ta sake mai mai ta masa maganar da tayi da sauri ya fito da wayar sa ya fara kiran layin Yusuf


Bugu É—aya Yusuf ya É—auka "kai Yusuf kuyi sauri ku bar wajen wannan yaron wanna mutumin da muke nema ne ina da tabbacin uban sa zaizo kuyi saurin barin wajen" daga É—ayan É“angaren Yusuf yace "to ko dai mu watsa sojojin awajen idan yazo sai mu kamashi" "no Yusuf ai ba zan taÉ“a zuwa wajen ba abun da ya sa nace maka zaizo,zaizo wajen mu neman É—an sa dai amma ba zaizo wacan gidan ba matikar yasan munje gidan kuyi sauri kubar wajen ne dan kunga ba ku fito da kayan yaki sosai ba zai iya aiko muku da mutanen sa,yanzun nan ku kawomin yaron nasa gida zanyi magana da shi thank God da ban kashe shi ba wlh saura kaÉ—an daman na harbe sa a kirji,sai kuma na fasa kuyi sauri kwashe su" "okey"Yusuf yace tare da katse kiran. 


Ta da motar yayi da gudu suka bar wajen cikin kankanin lokaci suka isa gida,

kai tsaye part nashi ya nufa da Zahra suna tafiya yana faÉ—in "karki kuskura ki fito daga Part na dan kina fitowa hankalin su Ammi zai tashi zasu gane me ake ciki dan haka kiyi zaman ki har sai na dawo da su Khalid" "to" kawai tace


 Suna shiga part É—in ya nuna mata É—akin hiyana shi kuma ya wuce wajen binciken sa ya fara tikan aiki

   Da sallama Aryan ya shigo É—akin kallon É—aya yayiwa bgs ya fahimci yana cikin matsanancin tashin hankali mara misaltuwa kusa da shi Aryan yazo ya tsaya

 

Ba karamin tashin hankali ya shiga ba lokacin da idon sa ya sauka kan desktop dake gaban bgs a sukwane yayi baya yana faÉ—in "what!? Me ido na yake gani haka Khalid sister to tayaya suka fita gidan nan ba tare da sojoji ba? Inannalillahi wa inna ilaihir rajiun hasbunallahu waniimal wakil" sai lokacin bgs ya juyo 

kallon Aryan yayi da kyau kafin yace "Aryan komai ya kwaÉ“e na bibiyi na'uran jikin Khalid ya nuna min disconnected amma yana nunamin a hanyar abuja aka kashe na'uran ita kuma sister na yi kokarin tracking nata sai ya nunamin location na É—aki na da alama ba ta tafi da shi ba kenan" durkushewa Aryan yayi awajen ya dafe sai tin zuciyar sa yana faÉ—in "innalillahi mu muka aikata laifi amma wayan da zasu karÉ“i hukunci daban wai yanzu ma ta ina zamu fara neman su?" Jin magana Aryan ya sanya bgs yace "muje Aryan" yana kai karshen maganar ya fice da sauri da sauri Aryan ya miÆ™e ya rufa masa baya 


Kai tsaye wajen da aka kama su hiyana sukaje Aryan yana kokarin rufe kofar motar nasu a sukwane bgs yace "no karka taÉ“a komai domin ina da tabbacin wayan da suka kama su su suka buÉ—e kofar motar nan nasu" fasa rufe kofar motar Aryan yayi suka fara kewaye awajen suna dubawa  

  "Amma bgs me ya sanya baka duba nauran cikin jikin Khalid ba!?" Aryan ya jefo masa mubaya ba tare da ya kalli sa ba yace "No na duba kasan shi da network yake aiki to in da suka kai su babu network na waya sai dai na salulan mai aiki da tauraro É—an adam hakan ya tabbatar min cikin manyan makiya nane ba karamin mutun bane ya kama su Khalid, ya katse duk wata hanya da zanÉ“i in same su ni abun da ya fi É—aure min kai ma ya akayi suka san sister? Wannan ne dalilin da ya sanya bana son wata mace ta raÉ“eni, yanzu gashi bata san komai ba laifi na ya shafe ta" "amma bgs ya akayi suka san cewa kana da alaka da sister? dan haka kawai ba zasu kamata ba,Sannan ya akayi aka san su sister sun fita daga gida har aka kama su?" sai lokacin bgs ya juyo da kallon sa kan Aryan É—in shiru sukayi kowannen su ya sanya Æ™waÆ™walwar sa a tunani suna kokarin tuna waya makama


 a fili bgs yace "ranar da nayi fitar sirri da sister a Uk an bi bayan mu ranar da na bar sister a shopping bayan Khalid yazo ya É—auke ta an bibiye su ni kai na ranar da na fita ni kaÉ—ai an bibiye ni ranar da Fahad ya fita shi da matar sa an bibiye su tabbas akoi abun da ya saÉ“a" matsowa Aryan yayi yana faÉ—in "amma bgs koma waye wanna makiyin namu mutun ne mai haÉ—ari kuma yana kusa da mu amma wanna wanene gaskiya bgs awan nan karon munyi sakaci sosai"  "no Aryan ba sakaci mukayi ba shigowar su sister rayuwar mu ne ya sanya muka sauya tun lokacin da ka fara son yarinyar nan gaba É—aya ka sauya ba abun da kake sai shirme Yusuf ya dai na aikin sa sai shirme kuke min ni ka É—ai kuka bari da aikin abubuwa sun min yawa, na kula da gida ga uk ga Aunty farida Aunty mardiya ta ko ina ni kaÉ—ai ne kuma 2 days da na biyewa sister shi ya sanya har aka samu damar shirya min wani abun wanna dalili ya sanya nace mata raunine koya kayi sai sun kawar maka da hankali kan wani abun" ya kai karshen maganar tare da jan tsaki "amma bgs waye kake ganin zai iya aikata wanna abun?" Shiru ya É—anyi kafin yace "no ai ba makiyi É—aya bane yanzu makiya uku zamu shiryawa domin masu neman sister a uku daban masu neman ta a nan daban ga wancan wawan da ya É—auki auta"  "to amma bgs me yasa sai sister kawai suke son kamawa" hararar gefen ido bgs ya masa kafin yace "saboda matata ce ita mana sun san cewa dole itace raunina kuma kowaye ya É—auke ta idan nayi wasa zai iya galaba a kai na ya kai ni kasa" a sukwane Aryan ya duÆ™a kasa yayiwa Allah sujudur sukur da mamaki bgs ke kallon sa bayan ya É—ago daga sujjadar ya É—aga hannu yana addu'a "ya Allah na gode maka daka nunamin wanna rana da bgs ya furta cewa sister matar sa ne da kan sa" jin hakan ya sa bgs jan dogon tsaki ya wuce ya cigaba da yan cinkiken sa 

Miƙewa Aryan yayi ya bi bayan sa yana kara godiya ga Allah


dai dai in da wayan da suka kama su hiyana sukayi parking mota bgs yayi karo da agogon hannu,zubawa agogon ido yayi na É—an lokacin kafin ya sanya hannu  a aljihun sa ya É—auko handkerchief ya duÆ™a ya É—auki agogon ya miÆ™a wa Aryan yana faÉ—in "daga yau zuwa gobe a binciko min Company da suke buga a gogon nan dan ina da tabbacin wanna agogon É—aya daga cikin mutanen da suka kama su Khalid ne idan na gane Company abun zai É—an zo mana da sauki" ansan agogon Aryan yayi yana kallon agogon 

ɗago ido yayi ya kalli bgs kafin yace "amma wanna agogon kamar akoi ajiya a cikin ta ai" "eh nima na gani akoi memory a ciki ka cire min memory idan mun koma sai muga menene a ciki" ya kai karshen maganar tare da duƙawa ya ɗauki wani hoton da ke kife awajen juyo da hoton yayi,wanna hoton ne da mutanen chan suka nunawa hiyana da Zahra zura hoton yayi a aljihun sa ya ɗago yana kallon Aryan.


Aryan yana kokarin yin magana bgs yayi saurin rungume sa suka faÉ—i kasa,ji kake tass arbin bindiga bullet É—in ya wuce ya rusa glass É—in motar su Khalid,

a zuciye suka miÆ™e dukkan su biyu suka É“uya a bayan motar 


shiru shiru har tsawon 10mins basu sake jin motsin kowa ba 

Aryan ya É—ago ya kalli bgs yayi da shima bgs É—in shi yake kallo a tare suka mike Aryan ya nufi motar su bgs kuma ya nufi motar su Khalid ya É—auki bullet É—in da a ka harbo musu yana dubawa kara waro idon sa wajen yayi yana kallon bullet É—in tabbas wanna bullet É—in na shine na gun É—in sane lokacin guda kamannin sa ya sauya a zuciye ya juya ya nufi motar su cikin fushi yace wa Aryan "fita bari na ja motar ka koma gefen can" ganin yausawar da yayi ya sa Aryan bai yi magana ba ya fito ya koma É—ayan É“angaren 

Bgs ya shiga mazaunin driver da mugun gudu ya figi motar ya nufi hanyar gida da gudun gaske


Suna shiga gida tun bai gama kashe motar ba ya fito a zuciye ya É—auko piston gun daga gefen kujerar motar ya nufi wajen security dake wajen gate É—in kai tsaye É—akin Abdol ya nufa 

Kwace ya sami Abdol saman gado yana mai da numfashi, ba tare da ɓata lokacin ba bgs ya harbesa a kafar dama,ihu Abdol ya saki tare tare da miƙa wa zaune ya dafe wajen da bgs ya har besa damko wuyar sa bgs yayi ya jasa zuwa waje zawa tsakar gida


Wani wawan naushi ya kai masa wadda ya sashi faÉ—uwa kasa da gudu Aryan ya kariso wajen yana faÉ—in "bgs me kake yi ne? Abdol ne fa ko baka lura bane? Yana kai karshen maganar ya riko hannun bgs,hakaÉ—e sa bgs yayi gefe yayi baya baya yana kokarin faÉ—uwa


da gudu sauran jibga jibgan sojojin dake gidan suka karaso wajen cikin tsawa bgs yace "Abdol why? Me na maka me ya sanya kake neman kashe ni da family na?" da kyar Abdol ya iya miƙewa tsaye cikin raɗaɗin ciwo yace "kayi kuskure Safras kayi sake ɗan zaki ya girma ni nasan daman ba zaka kyaleni ba zaka gano ni amma kasani ko na mutu ka kashe macijine baka sare kan sa ba" yana kai karshen maganar ya ciro piston gun daga aljihun jaket ɗin jikin sa kafin suyi wani yunkuri ya harbi kansa da kansa a goshi nan take ya faɗi kasa wanwar


Allah sarki Shahram lokaci guda yaji jikin sa yayi mugun sanyi yanzu duk yadda Abdol yake da bgs ba abun da bgs baya masa amma sai da yaci amanar sa lallai duniyar yanzu mutun ba abun yarda bane tunani yake anya Aryan zai sake yarda dashi kuwa? Tun da ga abun da ya faru tsakanin Abdol da Bgs


A fusace bgs ya juya ya nufi part nashi, umarni Aryan ya bawa sojojin su akan su yiwa Abdol abun da ya dace da shi yana gama faÉ—a musu hakan ya wuce yabi bayan bgs


É—akin binciken su ya isoko bgs kusa da shi yaje ya tsaya yana faÉ—in "amma bgs ya akayi ka gane Abdol yana É—aya daga cikin masu shirya mana tuggu!? dogon numfashi bgs yaja tare da sauke ajiyar zuciya lokaci guda idon sa sukayi jaa kamar wuta 

Furzar da iska mai zafi yayi daga bakin sa kafin yace "Aryan Abdol ya cuceni tun last 2 weeks na fara zargin sa lokaci da mukayi fitar sirri ni da sister ba wanda ya sani bayan munjeka kayan mu da ruwa ne na kirasa awaya akan ya kawo wa sister kayan sawa dan zazzaɓi ya kamata

bayan yazo wajen ya tafi kenan aka kawo mana hari,tun lokacin na fara zargin sa amma ban bari zargin nasa yayi yawa a zuciya ta ba dan ina ganin kamar idan na zarge sa ban masa adalci ba gani nake kamar ya riƙe min amana sannan yanzu da mukaje binciken nan na samu hoton sister a kusa da in da muka sanu agogon nan kuma hoton nata bata sani ba aka ɗauke ta sanna a Uk aka ɗauke ta ba a nan ba, lokacin da na kalli hoton sunan Abdol zuciyata ta kawomin domin su Khalid dai ba zasu ɗauki hoton sister su bawa wani ba amma duk da haka na kore zargin sa a rai na dan ban son hakan bayan harin da aka kawo mana Allah ya tsare naje na duba bullet ɗin tabbas bullet ɗi nane wadda na bawa Abdol nauran kuma ta nauran ya harbe mu amma ni na bashi yar nauran ne kasan cewar yana tare da ni akowani lokacin zaa iya farmakan sa tun da yana da kusan ci da ni ban san cewa na bashi abun da zai nemi kashe ni da shi bane,da Abdol bai kashe kan sa ba wlh Aryan ba zan iya kashe shi ba sai dai na bashi horo dan ya faɗa min waya ke wa aiki ina kaunar Abdol har cikin raina wlh ba zan iya kashe shi da hannu na ba yanzu ya mutu ban san da suwaye yake aiki ba ban san su nawane a cikin mu suke aiki da Abdol ba ban so Abdol ya tafi wutar jahannama ba banso ya kashe kan sa ba" yana magana idon sa na kara jaa kamar jini sai zufa yake gaba ɗaya jijiyoyin kan san nan a tsai tsaye kasa kasa ya furta "Khalid my sister" yana faɗin sunan su yaji wani kwarin guiwa lokacin guda


bincike ya farayi a system nashi kai tsaye ya shiga sunan Abdol ya fara bincike dan yaga da suwaye Abdol yake aiki 


tsaki ya ja yana kokarin wurgi da system ɗin Aryan ya tare yana faɗin "lfy bgs? pls ka kwantar da hankalika ka saita ƙwaƙwalwar ka dan mu samu muyi aikin da ya dace yanzu ba lokacin da zaka sawa kan ka tension bane yanzu ne muke bukatar ƙwaƙwalwan Brigadier general Safras ka nitsu kayi tunani ni nasan zaka iya tun da ka iya gane in da su anwar suke ba tare da wani evidence ba wanna ma idan ka nitsu zaka iya" "Aryan wanna case ɗin daban da ko wanne dole kai na zai ɗau zafi my sister Khalid kai ai dole na shiga tension dole nayi tunanin su" "duk da haka daurewa zakayi yanzu dai me ya sanya zakayi wurgi da system ɗin kuma!?" "Aryan Abdol ya rufe komai na shi yanzu na kara tabbatar wa ba da karamin mutun zanyi yaki ba domin duk wan da Abdol yake wa aiki ba karamin mutun bane babban kwaro ne yanzu dai ka kara jaddawa security karko wa ya sake shigowa gidan nan ba tare da izinin na ba haka fita kar su bar kowa ya sake fita ka sanya mana memory cikin agogon nan a cikin system ɗin mu gani ko zamu samu wata makama" ba tare da yayi magana ba ya fito da agogon daga aljihu sa ya fito da memory ya sanya a system ɗin suka zauna saman kujera suka fara bincike a cikin memory.


Video manya manyan maka mai da kwayoyin maye suka fara cin karo da shi a memory zubawa wajen ido bgs yayi shi bama kwayar ko makaman yake kallo ba wajen da akayi video yake kallon,bai taÉ“a kallon wannan wajen ba amma koma inane wanna tabbas a cikin Nigeria ne sunyi shiru suna kallon video Yusuf ya shigo É—akin bakin sa É—auke da sallama 

Kusa da su yazo ya zauna yana faÉ—in "ya zamuyi da wancan yaron? sai ihu yake wa mutane" cikin bacin rai bgs yace "ku har besa dashi da mutanen nasa duk ku kashe su dan basu da wata amfani mugun iri ne idan an barsu ma karawa kasa criminals zamu yi" "wani yaro ne kuma? Cewar Aryan tsaki bgs yaja kafin yace "É—an wancan wawan mutumin mana wadda muke nema"  "no kar ku kashe sa this time ka barni zanyi aiki a kansu kai kuma kaji da wayan da suka kama su sister kai Yusuf ka kai min shi É—aki horo bari nayi wanka zanzo nayi bincike akan sa amma sauran yaran nasu duk ka harbesu bana bukatan su" to Yusuf ya amsa da shi tare da miÆ™a wa ya nufi hanyar fita har ya kai bakin kofa Aryan yace  "yauwa Yusuf ka saki wancan Ahzan É—in dan ya karÉ“i horo yadda ya kamata  ita kuma wancan matar ka kawo min ita dan inason in haÉ—a ta da yaron nan akoi tambayoyin da zan musu dan tace min yarinyar ta É—aya ce a duniya kuma wanna mutumin ne baban yarinyar yanzu kuma ga yaron sa mun samu shi kuma daga ina? ina maman sa take?" 


tun da suke magana bgs bai kalli in da suke ba sai dayaji Aryan yayi maganar akan Æ´aÆ´an dadyn jabir biyu ne

 kallon Aryan yayi kafin ya mai da kallon sa kan Yusuf  yace "yanzu zaka kawo mana su karka É“ata lokaci daman dole akoi in da mutumin nan yake É“uya dan tun da na kalli yana kokarin kashe matar san nan nasan akoi wani abun naso yin bincike akai amma case É—in nan ne yazo ya sake shamin kai" "to" Yusuf yace tare da ficewa da sauri




To masu karatu sai mun haÉ—u gobe idan mai dukka ya kai mu

No comments