Recent Updates

Duk Karfin Izzata Book 1 Paga 9


Episode 9*

         Rike take da cup É—in coffee datahaÉ—a masa tafiya take, itakanta batasan ina tanufaba dan bata san  part nashiba tazo dai dai,zata fita bangaren Ammi tachi karo da Fahad " baya taÉ—an koma kaÉ—an kana tache ina wuni yaya Fahad " bai amsaba kuma bai ko

kalletaba yazo yawucheta " da sauri ta tache yaya Fahad dan allah inane bangaren yaya Aryan " banza yayi da ita yayi wuchewarsa chiki yabarta tsaye " tayi kwafa tana faÉ—in wlh dani kake zanyi maganin kane tajuya tachigaba da tafiya, sai sauri take kamar tasan inda zata 


kai tsaye palan mai martaba tanufa da sallam tashiga babu kowa awajen dan haka tanufi betroom kai tsaye  sallama tayi  a bakin kofar betroom É—in tunba'a amsa sallamar kuma ba'abata izinin shigowaba tashige abunta " zaune tasamu Mai martaba da Ummi a kan gado suna hira " mamakine yakama Ummi " Mai martaba kam bai damuba dan yasan halin diyana sosai  " Ummi che tache diyana lfy kika shigowa mutane É—aki babu sallama " turo baki diyana tayi tana faÉ—in dakin yaya Aryan nake nema, natambayi yaya Fahad yaki faÉ—amin " Ummi zatayi magana, mai martaba yarigata dachewa " idan kika fita nan kibi pangaren hannun damanki a nan part nasa yake " to ai kofa biyu'ne awajen wanene nashi chewar diyana " na biyun shine mashi mai martaba yabata amsa " to kawai tache san nan tafiche abunta " dawo da kallansa mai martaba yayi kan Ummi data sake baki take kallan ikon god " ya akayine mai martaba yatambayeta " hmmm su diyana manya mamakin tabani ne itakam ko ajikinta kawai tafaÉ—owa, mutane daki chewar Ummi " murmushi kawai mai martaba yayi kana ya girgiza kai


Tura kofar part É—in tayi tashiga tana tafiya tana wakarta chikin harchen fullachi "  (fullo daru midarata fullo daru midarata) " har tashiga palan babu kowa, dan haka sai tanufi kofar datagani a chikin palo kai tsaye tashiga babu ko sallama " jin mutun yashigo yasashi É—ago kai yana kallanta tachikin mirrow, daure,yake da towel a kugunsa da alama wanka yafito,  gawani gashi mai tsantsi bakinkirin a kwanche akan faffadar kirjin'sa, damtsen hannunsan nan kamar zai fashe saboda karfi,tamkar wani zaki, ga gashin kansan nan kuwa ajike, yake da'alama ya wanke kanne, gashin kwanche yake har kafaÉ—arsa,  zuba mata wan nan  ash eyes É—in nashi yayi "  sai waige waige  take da alama bata magansaba " shiru ta tsaya kamar mai sauraron wani abu" "zuba mata ido yayi sosai  yana kallanta " sanye take chikin doguwar riga abaya still dai kanta babu É—an kwali," "juyawa tayi zata fita karaf idanta ya sauka chikin nashi ta chikin mirrow, tsabar tsorata,  wani kara tayi kana tayi wurgi da cup É—in coffee dake hannunta ta watsa aguje zata nufi waje amma ina, taku biyu yayi ya tamki kugunta " saboda tsabar tsoro nunfashinta É—aukewa yayi " sai dai kawai yaji tasake jiki zata faÉ—i  da sauri yariketa da kyau, 


Kallan fuskarta yayi yaga alamar kamar suma tayi, yasa hannu É—aya ya É—auke ta Chak sai kan makeken gadansa ya kwantar da ita " san nan yakoma gaban miro yachigaba da abun dayake, bayan yagamane 

yanufi dressing run nashi, saida ya dauki kusan 10 mnt kafin yafito sanye da kayan barchi a jikinsa doguwar wando da riga mai dogon hannu masu laushi farare tas " kai tsaye freij yanufa ya daukoh ruwa, yazo ya zauna a gefen gadan yabuÉ—e bakin rubar ruwar ya tarfa a hannunsa, ya shafa mata a' fuska " wani nauyayyar ajiyar zuchiya ta sauke haÉ—e da jan dogon numfashi, 

 batare da tabuÉ—e idoba tafara sambatu " don Allah kayi hakuri wlh bansan bakaya ajikinka bane nashigo kuma kaikache nazo dan allah karka bugeni " ke kimin shiru chewar Aryan  " da sauri ta buÉ—e ido tana kallan inda take, mikewa tayi da sauri ta saukoh daga gadan tanufi hanyar fita " kamar daga sama taji yana faÉ—in " inazakije konache kitafine? " Da sauri ta juyo tana in ina a'a " to zo nan ki zauna yayi maganar yana nuna mata kasan carpet É—in  " da sauri takoma ta zauna " wayache kizubarmin da coffee " É—ago kai tayi tana kallansa taga bama ita yake kalloba wayarsa yake latsawa " kayi hakuri zankawo maka wani tabashi amsa " kinsan meyasa nakiraki " aa bansaniba " wlh wan nan shine last worming na karshe da zanmiki idan kikasake yimana maganar wan nan shegen kauyen a gidan nan saina babballaki kinajina " murya na rawa diyana tache eh naji " 


kuma inasan kibuÉ—e kunne ki saurareni idan kika bari nasake ganinki babu É—an kwali saina aske gashin nan gaba É—aya " da sauri diyana tache yauwa yaya dan allah ka askemin inka iya wlh banaso daman  " mamakine yakama Aryan tunani yashigayi idanfa yabiyewa yarinyar nan to tabbas zaiya babballata " dan haka sai yache ke yanzu kitashi kije kikawomin wani cofee É—in san nan kuma kullum dasafe karfe 7 dai dai kikawomin coffee haka da daddarema karfe 9 dai dai shima inabutar coffee idan kika kuskura kika wuche time dana baki,sai jikinki yafaÉ—a miki kuma banche wani yahaÉ—a , coffee É—in ba kezaki rinÆ™a hadawa kinaji, tashi kije kikawomin wani yanzun nan yayi maganar a kausashe " da sauri tamike tanufi kofar fita har takai bakin kofa kuma saita juyo tana faÉ—in yaya Aryan to yabatun askin zaka askemin gashin " wani mugun kallo ya wurga mata waddayasata fita a' aguje " 


gyara konchiyarsa yayi a kan gadan yana kokarin É—aukar wayarsa saiyaji kira tashigo, saida wayar takusa katsewa tukun nan yayi picking call É—in " hello akache daga É—ayan bangaren " ykk hisham chewar Aryan " lfy y gd, wai meyasa innakiraku Aryan baku san daukar call na  chewar hisham  "  Aryan yache au kakirane ka tambaya, to ra'ayi yanzuma kayi sa'a ne dan inachikin farinchiki badan hakaba bazan daukaba " haka zakachemin koh Aryan to waima menamukune "  kara daure fuska Aryan yayi kamar hisham na kallansa yache kaga hisham mufa duk wanda yahaÉ—a hanya da mace to bamatare, dashi dan yazama mai rauni, mukuma bamasan mai rauni kusa damu " wani mahaukachin dariya hisham ya kwashe dashi yana faÉ—in inshaa allah Aryan kaine mutun na farkoh a chikinku dazai fara faÉ—awa soyayya kuma inshaa allah yadda kuka wahalar da soyayya itama saita wahalar,daku, wahalarma ba.. "Aryan baijira hisham yakare jawabansaba yakatse kiran yayi wurgi dawayar gefe " dai dai lokachin diyana ta dawo hannunta É—auke da cup É—in coffee bakinta dauke da sallama " wani mugun kallo ya wurga mata a kausashe yache get out " da sauri tajuya dan yadda taga fuskarsan nan kamar wani zaki "  kichin tanufa ta ajiye coffee É—in a kan table san nan tafito kai tsaye sashen Ammi tanufa abunta ,


Tana shiga tayi É—akinsu tasamu su zahra har sunyi barchi hayewa saman gadan itama tayi ta kwanta abunta bajimawa barchi ya dauketa


Washe gari misalin karfe 7 sungama shirinsu chikin uniform naso sunyi kyau sosai abunsu 

Diyana sarkin aiki dachikawa bata daure gashin gantaba tasa hijabi, wutsiyar gashin yalekoh  sosai saboda gashin,yafi hijabin,tsawo


Kai tsaye palan mai martaba suka nufa dan yin breakfast da sallama suka shiga " kowa nagidan yana zaune kan table suna breakfast " mai martaba dakansa ya amsa musu sallamar yana faÉ—in wow yan matana kunyi kyau gaskiya " Ummi da Ammi ma sai murmushi suke suna yaba kyansu auntu amarya ko sai harararsu take  " yusuf kuwa chewa yayi kai sweet sis yanzunema asalin kamanninki da don kekara bayyana " asukane don ya É—ago kai yana kallan yusuf " yusuf baimasan yanayiba saima karachewa yayi ammafa kinfi don kyau gaskiya, domin kuwa blue eyes yafi green eyes kyau " 


a,fusache don yamike yayi yana faÉ—in zama danake inachin abinchi,dakuma yafara kawo raini, kana yadawo da kallansa kan Ummi yana faÉ—in daga yau arinka kaimin, abinchi na bangarena, dagahaka yayi waje " murmushi kawai Mai martaba keyi yana girgiza'kai kana yadubi su diyana dake tsaye, to tsayuwar me kuke kuzo kuzauna kuchi abinchi kutafi karkuyi latti " wuchewa sukayi suka zauna kan kujerun table din " bintu sufara sarving nasu, nantake sukafara chin abinchin " 


ke banache karfe 7 dai dai kirinka kawomin coffee ba yayi maganar kansa na duke yana danna waya kamar bashike maganarba " chikin sanyayyiyar murya diyana, tafara magana, kayi hakuri yaya Aryan wlh nayi tunanin kafasane dan naga jiya kache nafita maka a É—aki " mai martaba dai baki buÉ—e yake kallan wan nan ikon allah, Ammi da Ummi ma ba abarsu a'bayaba kowa na falon, mamakine yakamasa "  Aunty amarya kuwa bakinchikine kamar zai kasheta tanasan magana tana tsoron mai martaba " Khalid kam sai murmushi yake abuns,  " basu gama mamakinba sukajiyo , .  muryansa yana faÉ—in to kitashi kikawomin yanzu " bamusu tamike tanufi hanyar fita " shikuma yadago kai kome zai kalla karaf suka haÉ—a ido da yusuf daya buga tagumi ya tsaresa da ido " harara ya watsawa yusuf kafin nan yamike shima yafiche daga palan " wani mugun dariya yusuf ya kwashe dashi yana tafa hannu " Aryan najiyo dariyar Yusuf amma bai tsayaba kuma bakaramin haushi hakan tabashiba haryasa yajima yatsani coffee É—in, baima san sake kallan yarinyar " 


Aiman ne yamike yabi bayan Aryan É—in  batare dayache komaiba " Ahmad naganin Aiman yamike yafita shima yabi bayansa " Khalid kuwa kallan yusuf yayi kasa kasa yache baka kyautaba kuma ina da magana dakai anjima kasameni a daki " to kawai yusuf ya amsa dashi " mikewa Khalid ma yayi yafita daga palan"


Dawo da kallansa kansu hiyana Yusuf yayi yana faÉ—in kuyi saurifa time na tafiya yau nizanma kaiku da kaina " tsabar mamaki zahra batama san lokachin da tache wai anya yaya yusuf ne wan nan kuwa " sai dataga yana wurga mata mugun kallo tukun nan ta dawo kan hanya " a'gurguje suke chin abinchin dan kar time yakure " suna gama chin abin suka mike yusuf yace muje koh san nan yayi gaba, sukabi bayansa 


Su hiyana na fita mai martaba yadubi su  haidar yache kubamu waje zamuyi magana " da sauri suka mike sukayi waje,  palan ya rage daga Aunty amarya Ammi dakuma Ummi sai mai martaba " 

calmly mai martaba yafara magana alhadulillah alhadulillah wan nan rana nake jira arayuwata a'che yau Aryan da Safra da Aiman, naga sunfara yiwa wata yamace magana to yau burina yafara chika, nasan yusuf Ahmad Khalid su masu saukin kaine, to maganar danakesan nayi ana shine kar wanda ya kuskura a chikinku yayiwa yaran nan, wata magana dan da alama addua ta a kan Aryan tafara karɓuwa , " Ammi tache ranka yadaɗe ban fahimche kaba " zaki fahimta amma bayanzuba mai martaba yabata amsa " mikewa aunty amarya tayi a fusache tabar palan " binta da ido kawai mai martaba yayi achikin zuchiyarsa kuma yana faɗin nasan zaayi hakan ai amma sai dai kinmakara dankuwa baki isa kihana abun da allah yahukunta ba, a'fili kuwa chewa yayi zaku iya tafiya " mikewa Ammi da Ummi sukayi suka nufi waje.


Da sallama diyana tashiga palan nashi baya nan kai tsaye chikin betroom din tawuche "da sallama tashiga "  zaune yake kan kujera yana aikin chikin laptop " gabansa tazo ta duka kana tache gashi nan yaya Aryan " a'fusache yache bana bukata " mikewa tayi tafita da coffee É—in a hannunta ta maida kichin abinta,san nan tafito tanufi harabar gidan, tsaye tasamu su hiyana suna jiranta tana zuwa suka shiga mota kamar yadda suka saba, da gudun gaske motochin suka fito daga gidan, dan yusuf ne yache suyi gudu sosai su diyana zasuyi latti,

 

Karfe 10 na'safe


Zaune suke suna fuskantar juna akan sofa Khalid ne yafara magana gaskiya yusuf baka kyautaba meyasa zakayiwa Aryan dariya haka kasanfa abun da muke buri ke nan muga Aryan da don yau sunkula wata ya mace,kuma kafi kowa sanin halinsufa, yanzu dariyar nan daka masa zai iyasawa wlh yakoma ruwa munfara farinchikin yafara dawowa kanhanya,  kana'neman rusamana farinchikin, kuma gashi niÉ—in nan tun ranar da aka haifi Zahra nake mahaukachin santa amma na bar abun araina saboda'su don dan bansan wata matsala a tsakaninmu Aunty farida kawai na iya faÉ—awa yanzu ganin abun daya faru a palo É—azun haryasa nafara ganina a matsayin angon zahra gashi yanzu kanane'man karusamin hakan gaskiya baka kyautaba wlh " 

dogon nunfashi yusuf yaja san nan yache hakane yaya Khalid nasan nayi kuskure dankuwa nikaina burina naga sun chanza amma wlh abunne yabani dariya yanason abu, amma yana wani chicchijewa yananuna halin ko inkula " 

Khalid yache yanzufa Aryan bazai taÉ“a fahimtar yanasan yarinyarba saboda shi baisan soyayyaba kuma inbanda aunty farida da iyayenmu mata kasan ba wata macen dayake magana da ita Koh,   koh zahra datake kanwarmu bamaga da ita yake ba tunda kaga yayiwa yarinyar nan magana har yache takawo masa abu yachi wlh ba banzaba yana mahaukachin santa amma bazai gane hakanba yanzu ,  tunaninsa bazata taba bashi yana santaba kuma karkayi kuskure faÉ—a masa yana santama, kabari zuchiyarsa zata faÉ—amasa, dan inkache zaka faÉ—a masama hakan zaisa yadaina yiwa yarinyar magana, yakuma tsaneta ka kyalesa kawai "

" murmushi Yusuf yayi kana yache tabbas zan haÉ—a masa tarko kuwa wanda zaisa yafaÉ—a son ta gadan gadan batare daya saniba " hannu Khalid yamikawa Yusuf yana faÉ—in good idea idan kana bukatar taimakoh na a shirye nake " darisukayi gaba É—ayansu suka tafa hannu  san nan yusuf yamike yana faÉ—in saikajini zanzo na faÉ—amaka plant É—in idan nagama shiryawa " to kawai Khalid yache" sannan Yusuf yafiche daga É—akin.



Kuka take sosai kamar wata karamar yarinya tana waya " wai inba gagarabadau ba bakisan wani malami bane kitausayamin sadiya wlh suna shirin kasheni idan Aryan yafara son yarinyar nan wlh yakasheni nashiga uku " hajj sadiya tace kidaina faÉ—in hakan kiyi hakuri nan da 2 month É—in kinji koma yafara sonta idan akamata aiki dole zai tsaneta karki damu pls kidaina kukan haka, toma wayache maki yana sonta " sadiya inasan kisan wani abu  Aryan fa ko Zahra datake kanwarsa bai taba mata maganaba amma yayiwa yarinyar nan  magana kuma hardachewa tarinka kawomasa coffee kullum, " karki damu nidai dan allah kidaina kukan nan zamuyi maganin abun "  tsagaita kukan aunty amarya tayi kana tace shike nan sadiya badamuwa zanjira amma dan allah amusu aimi mai karfi dan yanzuma kara tsanarsu nayi wlh " karkidamu aminiyata kedai kizuba ido kawai chewar hajj sadiya " to shike nan aunty amarya tafaÉ—a tare da katse kiran ta jefa wayan a kan gado ta zauna tabuga uban tagumi siraran hawaye nabin kunchinta


Karfe 1 na rana


Suna zaune awajen chin abinchi na school nasu sungama chin abinchi rana " hiyana na karatun qur'ani, su zahra suna Assignment É—in da akabasu ita da diyana  amrat kuwa tana zaune kusa da wata budurwa sai lamrat dake gefe tana rike da littafin Husnul Muslim tana karantawa " sunyi nisa chikin abun da suke saisukaji murya daga bayansu " a tsorache Zahra tajuya a'zuchiyarta  tana tunanin wai meyakawo jabir wajensu tana chikin tunani kwai sai taji yana faÉ—in " ke zahra,u yaushe a' kakawo wayan nan yan india wan kuma makarantar nan " Zahra sarkin tsoro murya na rawa tace sun kai 2 month " tsaki jabir yaja san nan yace, shine bakizo kinfaÉ—amin ba, amma gaskiya wanchan tamin itache sabuwar budurwata na wan nan shekarar yayi maganar yana nuna hiyana, " to kawai Zahra tace, " yasunanta jabir ya tambaya " sunanta hiyana chewar zahra " 


jinjina kai jabir yayi ya mai maita su nan hiyana san nan yace, hiyana tashi kizo muje muzagaye  makarantar nan domin kowa yaga sabuwar budurwata dan karwani yache yanasonki, dan duk wanda yayi kuskure chewa yana sanki tofa saidai uwarsa ta haifi wani " zaro ido hiyana tayi tana kallan jabir ba karya kyakkyawane sosai gashi dogo mai chikar halitta sai dai yayi kalar yan daba kuma kwata kwata bazaifi 22 years ba,"

Zahra ne tace, hiyana kitashi kuje " kallon zahra hiyana ke chike da mamakin abun da tache zatayi magana sai tajiyo " diyana nafadin kai waye dazakawani che tazo tabika to babu inda zataje iskanchin banzan nan " wani mahaukachin mari jabir ya sakarwa diyana san nan yace kishiga hankalinki wlh kinmachi albarkachi, naganku tare da gimbiya hiyana ne dabadan hakaba dakin karbi hukunchi kekuma yashi mutafi yayi maganar yana nuna hiyana " da sauri hiyana tamike jiki na rawa tanufeshi " juyawa yayi yayo gaba tabi bayansa 


Diyana kuwa sai kuka take tana faÉ—in allah ya isana waima Aunty zahra wanene wan nan " wata buduwa dake zaune kusa da amrat ne yace, sunansa jabir " ni ba sunansa nakesan jiba faria wanene shi nakesan sani chewar diyana " Faria tace shima a school É—in nan yake yana ss 2 yana takama da mahaifinsa mai kuÉ—in ne kuma mahaifiyarsa kuma tana da yan daba mahaifiyar tasa baturiyar England che, bata da mutunchi shiyasa yake abun da yaga dama " to meyasa malamai basa masa hukunchi saiyarinka yin abun dayakeso a makaranta chewar diyana " faria tace makarantarma na mahaifinsane kuma duk abun dayake so shi iyayen nasa sukeso " shiru diyana tayi kamar bazata sake magana ba chan kuma tace wlh nine zan gyara masa zama " baki buÉ—e Zahra da faria ke kallan diyana tachigaba dachewa badai hiyana yakesoba wlh zaigane shayi ruwane  

Ita dai zahra aikin gabanta tachigaba dayi dan ta lura diyanafa ba hankali garetaba  


Hiyana bata dawoba har suka koma class " diyana tashiga damuwa sosai da sosai " sai karfe 2:50 hiyana ta dawo lokachima har anbuga belt É—in tashi school " diyana naganinta tanufeta tarungumeta tana faÉ—in  ina kukaje " babu ko ina yawo kawai yayi tayi dani a chikin school É—in chewar hiyana " tsaki diyana taja san nan tace to muje " jerawa sukayi tare suwa nufi inda da suke tsayuwa sujira mai É—aukansu nan sukayita hirarsu  " har driver yazo ya daukesu kamar kullun motochi 2 kezuwa daukansu diyana hiyana da zahra mota É—aya  lamray da amrat motarsu daban

Da gudun gaske motochin suka nufi gida dasu ,motochin na danno kai security su wangale musu katafaren gate É—in kai tsaye parking space suka nufa suna parking drivers É—in suka fito suka buÉ—e musu motar " suma suka fito suka rirrike hannun juna sukayi suka nufi bangaren Ammi


Suna shiga tun a palo diyana tafara chire hijabi tana faÉ—in alhadulillah yanzu zan rabu da hijabin nan haba " harararta hiyana tayi kana tace, kekam wlh watarana sai aljanu sunshiga kankin nan mutunne bata san dan'kwalin " kallon uku 10 diyana taiwa hiyanar san nan tace, to ina ruwanki ai aljanuma abokainane   Zahra zatayi magana sukaji an daka musu tsawa, get out  aguje sukayi É—akinsu itakuma diyana saida tajuyo dan ganin wanene tana ganin don ne ta watsa da gudu itama dan, shikam batataba ganin alamar wasa a fuskarsaba ,

No comments