Duk Karfin Izzata Book 1 Paga 38
Episode 3️⃣8️⃣*
.......Jibi jumma'a ina son gaba ɗayan ku kusa kayan hausawa domin akoi taron da zaku rakani, a sukwane Bgs ya ɗago green eyes nashi yana kallon Abba "Abba nifa ban iya saka kayan hausawa ba" Chewar Fahad yayi maganar yana kwaɓe fuska "same here
gaskiya Abba ka chanza dan ni ba zan iya sakawa ba, chewar Bgs, dogon numfashi yaya Aryan yaja kafin yace "Abba nima dai ba zan iya saka kayan hausawa nan ba gaskiya" chikin fushi Ammi tace "to sai kuma ku kayi rashin Sa'a iyayen ku hausa fulani ne" "Aisha kiyi shiru ki kyale ni dasu chewar Abba, yaya Khalid kam shiru yayi yana binsu da ido dan yama rasa me zai che ko shi ba iya saka kayan hausawa zai yiba amma tun da Abba ne yace abun da yake so ke nan tofa ya zama dole ayi hakan"Abba pls ka bari musaka kayan da muka saba tun da iya raka ka kawai zamuyi chewar Fahad dawo da kallon Abba yayi kan su Ammi chikin nitsuwa da girmama juna yace "Aisha kuje ku kyale mu zamuyi magana.
Abba yache su Ammi su tafine ba dan komai ba sai dan yasan halin Ammi yanzu zata ɗau zafi tafara yiwa su Bgs faɗa kuma shi Abba baya son hakan lallaɓasu yake son yi yana son su saka kayan hausawa dan idan yace zai bisu ta karfi tofa abun ba zai musu daɗi ba zasu iya shirya masa wani kitimurmuran da zai hana su zuwa wajen taron dan haka gara ya bisu a hankali su rabu lfy
Gaba ɗaya matan suka miƙe suka fice daga palon Aunty amarya sai chika take tana batsewa dan haushi dawo da kallon Abba yayi kan su Bgs ya fara magana
"Wai me yasa duk abun da nake so baku son shine? Me yasa baku san sakani farin chiki ne? Yanzu fa chewa nayi kusaka kayan hausawa iya na rana ɗaya amma shine kuke tamin wani kame kame, idan ba kumin abun da nake soba waye zai min? Eh" shiru su kayi ba wanda ya tanka Abba chigaba da magana Abba yayi "wai ni wani laifi na muku ne? Da kuke min hakan, chikin jin tausayin Abba Khalid yace "Abba kayi hakuri zamu saka ina dai kayan hausawa kawai kake son ka gammu da shi? To zamu saka koda na shekara kace musa zamu sa bare kuma na kwana ɗaya" murmushi kaɗan Abba yayi kafin yace "to Allah ya muku albarka" Khalid da Yusuf ne kawai suka amsa da amin
Miƙewa Abba yayi ya nufi hanyar betroom nashi yana faɗin "Khalid kai da Yusuf an jima kusa me ni a fada san nan akoi wani Babban likita da zai zo daga madina dan duba jikin Ahmad idan ya iso sai kuje Airport ku ɗauke sa ya kai karshen maganar tare da shigewa chikin betroom ɗin sa
Miƙewa Bgs yayi yana hararan Khalid rai a bachin ya nufi waje chikin zuchiyar sa yana faɗin "kayan hausawa kuma Ni never Abba ni ba zan iya ba kai taron ma kwata kwata ba zan jeba gaskiya, da wan nan tunanin ya nufi part nashi
"Aiman ya ka baro Aunty farida? Chewar Aryan yayi maganar yana miƙewa "suna lfy suna gai sheka wuche wa Aryan yayi ya nufi hanyar fita batare da ya sake chewa Aiman komai ba, Aryan na fita kiran diyana ya shigo wayar Aiman miƙewa yayi tare da picking call ɗin ya nufi waje yana faɗin "Hello daga ɗayan bangaren diyana tace "yaya Aiman dan Allah ka haɗani da yaya Aryan ɗin mana" "baby diyana yau ko sallama babu ke dai kawai a haɗaki da yaya Aryan to ma wai me zaki faɗawa yaya Aryan ɗin nan ne? "Babu komai yaya Aiman kawai zan gai da shi ne dan tun da nazo yanzu 3 weeks ke nan bamuyi Magana ba"
"Ok karki damu yanzu zan haɗaku ɗan riƙe wayar yana magana yana tafiya part ɗin Aryan ya nufa suna hirar su, dai dai zai shiga part ɗin kiran Aunty amarya ya shigo wayar sa "baby diyana bari na ɗauki call ɗin Aunty Amarya kinji? Amma ba sai kin katse kiran ba, batare da ya jira amsar taba ya ɗaga kiran Aunty amarya ya sa diyana a hold
Chikin sauri Aunty amarya tace "Aiman kazo yanzun nan ina jiran ka" "to daman ina son inzo nima dan akoi magana mai muhimmanci da nake son yi dake" "to kayi sauri"
chikin sauri ya juya ya nufi part na Aunty amarya,tare da katse kiran Aunty amarya "my diyana ki bari zamuyi waya an jima yanzu Aunty amarya na kirana, ba tare da ya jira amsar diyana ɗin ba ya katse kiran dai dai lokacin ya shiga part ɗin Aunty amarya
Da sallama ɗauke a bakin sa ya shiga palon babu kowa kai tsaye betroom ɗin ta ya nufa zaune take a bakin gadon sai wani ɓata rai take tana kwaɓe fuska saman manya manyan throw pillow dake tsakiyar ɗakin ya zauna tare da faɗin "barka da hutawa Aunty amarya" "batare da ta amsa ma saba tace "ina Aryan ɗin kuma!? "Yana part nashi, bai karisa rufe baki ba Aryan ya shigo bakin sa ɗauke da Sallama
Zama yayi saman Throw pillow dake kusa da Aiman sai wani kwaɓe fuska yake shi ma, chike da izza da isa Aunty Amarya ta fara magana "wato ni ban isa da ku bako!? na ɗauko yarinyar mutane na kawota gidan nan kuna gani yan uwan ku suka chimata mutunci ko? To kusani ba zulaihat suka chiwa mutunchi ba ni suka chiwa mutunchi tun da ni na ɗauko ta, waje na tazo Ni wlh ban ma san wani irin mutuwar zuchiya ke gareku ba sai abun da yaya Aisha su kache zakuyi wato ku bazaku iya yin ra'ayin kan kuba ko? Shiru suka mata dukkan su biyu, shi kamma Aryan baya ma jin me take faɗe ya tafi duniyar tunanin diyanar sa
"Au ina magana kunyi ban za dani ko, Mikewa Aiman yayi ya nufi hanyar fita, sai da ya kai bakin kofar fita san nan ya dakata ya juyo chikin jin haushi irin halin mahaifiyar tasu ya fara magana "Aunty amarya gaskiya abun da ki keyi bai dace ba bakya kaman ta adalci kwata kwata addinin Musulunci Addini ne mai sauki wadda ya bamu umarnin ko da iyayen kane kaga suke son kauche hanya to ka musu gyara ka tabbatar kayi iya kokarin ka wajen ganin sun dawo kan hanya, tun muna yara kike son dole dole sai kin chusa mana tsanar yan uwan mu, masu kau nar mu da zuchiya ɗaya yanzu ki faɗamin a nan me yaran Ammi suka taɓa mana na rashin mutunchi ko tozarci? da yasa kullun kike chewa basa son mu, Ni dai ina son yan uwana da zuchiya ɗaya kamar yadda suke sona kuma... Bai kai karshen maganar ba Aryan ya rufe masa yana girgiza masa kai alamar yayi shiru, rai a bache ya zame hannun Aryan daga kan bakin na sa ya juya ya fice daga ɗakin
A hankali Yaya Aryan ya juyo da kallon sa kan Aunty Amarya wadda tayi mutuwar zaune "kiyi hakuri Aunty Amarya In Sha Allah zamu gyara, yana kai karshen maganar ya fice da sauri ya bar ɗakin dan bai son jin amsar da zata bashi yasan ba alkhairin zata faɗaba.
Maiduguri
Yau ta kama Alhamis, tun ƙarfe 7 diyana ta kammala shirin ta tsab na zuwa school ta fito ta nufi ɗakin junior, already abida mai kula dashi ta gama shir ya shi chikin uniform nashi, hannun sa diyana ta ja suka fito palon kasa nan suka sami dady'n junior da Aunty farida suna zaune saman table suna breakfast, ƙarisawa wajen su diyana tayi rike da hannun junior, kusa da Aunty farida diyana ta zauna shi kuma junior ya zauna kusa da dady'n sa, nan take lami mai aiki ta zuba musu abinchin chips ɗin A rish ne da soyayyen kwai sai tea mai kauri, a hankali diyana ta ɗauki spoon chikin yanga ta fara chin abinchin
"My diyana idan kinje school yau ki musu sallama dan gobe zamu wuche Kano" Chewar Aunty farida da murna diyana tace "to Aunty farida, mamaki yadda diyana ta sauya dady'n junior yake, gaba ɗaya yanzu ta dawo mace mai Class ta dai na yawan magana, ko ka mata magana sai ta ga daman amsawa, ta dawo big girl gata daman da iya yanga da yauki ga ɗaukan wanka baa magana
Karfe 7:30Am dai dai diyana ta miƙe ta rike hannun junior suka fice suna yiwa Aunty farida da daddy bye bye
Idi driver na ganin su ya taso da sauri ya nufesu buɗe musu gidan baya na motar yayi suka shiga suka zauna, ya rufe motar ya buɗe gidan gaba ya zauna a mazaunin driver ya ta da motar, ya nufi bakin gate, da sauri baba mai gadi ya wangale musu katafaren gate ɗin da gudu idi driver ya dan na hanchin motar waje ya ɗau hanya
YOLA
Da gudu hasana matar yaya Bello ta fito daga ɗaki tana kwara amai gashi gidan babu kowa sai innar buba dake zaune a ɗaki kafa baya tafi
Jin ana kakarin amai yasa Inna buba tayi kokari da kyar ta iya Mikewa tana dafa bango tana ɗingisa kafa har ta fito waje, da kyar ta iya kariso wa wajen da hasana ke duƙe tana kwara amai
Sugunnawa inna tayi ta dafa bayan ta tana ta mata sannu, da kyar hasana ta samu amai ɗin ya tsaya miƙewa tayi ta taimaka wa Inna buba ma ta miƙe rike kafaɗa Innan buba hasana tayi ta taimaka mata ta mai data saman ta burman dake tsakar gidan a hankali ta zaunar da ita san nan ta koma ta ɗebo kasa ta zuba awajen amai ɗin ta kwashe da abun kwashe shara taje ta zubar a bayan gida ta dawo ta ɗebo ruwa ta wanke jikinta ta koma kusa da innar buba ta zauna
Tana zama yaya Bello na shigowa da sallama ɗauke a bakinsa kusa da matar sa yaje ya zauna yana faɗin "ya jikin naki? Hasana zatayi magana Innar buba ta rigata da chewa "ai yanzu kam sai dai muche Allah ya raba lfy" "Inna ban gane me kike son ki cheba! Chewar yaya Bello yayi maganar yana kallon Inna
"Hasana dai ciki ne da ita to idan ma baku gane ba" zubur yaya Bello ya miƙe yana faɗin "Alhadulillah Alhamdulliah dukawa yayi kasa yayi wa Allah sujudur shukur dan nuna tsan tsan godiyar ga mahalicin mu, sunkuyar da kai kasa hasana tayi tana murmushi a zuchiyar ta tana godewa Allah, yanzu tsawon shekara 6 da Auren su kenan bata taɓa koda ɓatan wata ba sai yanzu Allah ya bata.
Aɓangaren Inna Habiba kuwa
Zaune take a tsakar gida tana chin gwaza (makani) sosai take ɗura gwazan tun bata gama chinye na bakin taba take sake tura wani da alama sauri take zata wani wajen kuma da alama gwazan (makani) ya mata daɗi sauri sauri ta chinye tas san nan ta miƙe ta bar kwanon awajen ta rarumi summar mayafin ta dake makale a igiya ta yafa ta nufi waje
Kai tsaye gidan bokan nata ta nufa dan yau ne adadin kwanakin da ya bata suka chika, kamar kullun yauma da baya baya ta shiga saman dutse da ya saba zama yauma a nan ta same sa, in da ta saba zama taje ta zauna tana faɗin
"Sannu da hutawa ya Aiki" wani shu umin murmushi yayi kafin yace "barka da zuwa habiba ya naga kin zauna a nan mu shiga daga chiki mana" "eh zan shiga chiki amma ina son in ji ya aiki ya kammala ne? "me kike chi na baka na zubane habiba to yau dai aiki ya kammala kawai kijira kiji me zai biyo baya, dariya sosai inna tayi san nan ta miƙe ta shige wan nan waje da suke aikata masha an su.
Sosai yau ma suka aikata masha an su inna bata koma gida ba sai bayan sallar issha sai murna da farinchiki take bokan ta ya gama mata aiki shike nan su diyana zasu haukache.
KANO
Yau ta kama juma'a ba ƙaramin fama Abba yasha ba kafin Bgs ya yarda zai sanya kayan hausawa, misali karfe 1:20 Abba ya fito harabar gidan yana jiran fitowar samarin nasa sutafi masallaci Haidar da Umar ne suka fara fitowa sanye cikin shadda blue ɗin kin have jumpa sun yi anko komai na jikin kayan nasu iri ɗaya har ɗin kin ba karamin kya kayan ya musuba kusa da Abba sukaje suka tsaya
Khalid Aiman Yusuf tare suka fito a j toere suna sanye chikin wata dan kareriyar yadi mai kyau da tsada ash colour suma anko su kayi dukkan su ɗinkin have jumpa gefen Abba suma su kaje suka tsaya suna jiran fitowar su Bgs, jefi jefi suke ɗan hira a tsakanin su Almost 30mnt suna tsaye kafin nan sukaji takun sahun jaruman maza suna fitowa
Subhanallah sarki ya tabbata ga Ubangiji da yayi wan nan halitta wow Bgs Aryan Fahad a tare suka jero sunyi ankon wata dan kareriyar farar shadda mai bala'i kyau da tsada ɗin kin full jumpa, kamar dan su akayi kayan mu samman Bgs ba karamin kyau kayan hausawa suka masaba shida Aryan sun tara gashin su sun ɗaure ta baya sun zuba jelar gashin ta baya su sai kyalli fuskar su take kayan ya zauna a jikin su sosai yadda kasan dan su akayi kayan,
Duk wan nan haɗuwar da sukayi fuskar su babu alamar dariya a ɗaure take tam gaba ɗayan su kallo ɗaya zaka musu ka gane dole aka musu, suka sanya kayan ga Aryan nan tun ba aje ko ina ba yake ta faman haɗa zufa, Bgs kuwa sai wani jan kayan yake yana rabasu da jikin sa alamar suna takura mishi, shiko Fahad ya tattaro rigar ya dawo da ita kugunsa ta tashi daga full jumpa ta koma have jumpa, dariya abun ma yaso bawa Abba amma sai ya danne dan yasan idan ya musu dariya zasu che bazasu fita da kayan ba zasu koma su chire
Su kansu sojojin nasu sai yabawa suke da irin kyan da kayan hausawa yayiwa Bgs da Aryan da Fahad
a tare suka shiga mota Bgs da Aryan motar su ɗaya Khalid da Yusuf motar su ɗaya Haidar da Umar motar su ɗaya Fahad kuma ya shiga motan Abba, shiru Aiman ya tsaya yama kasa shiga motar ji yake kamar zai yi kuka idan ya tuna yau shi kaɗai zai shiga mota batare da Ahmad ba
Fitowa Bgs yayi daga chikin tasu motar ya kama hannun Aiman ba tare da yayi magana ba ya turashi chikin motar su shima ya shiga shida Aryan suka saka Aiman a tsakiya ba karamin tausayi Aiman ya basu ba, shiru sukayi ba wanda yace da ɗan uwan sa kala
Key driver's ɗin su kayiwa motochin suka tayar suka nufi gate, tun kafin su iso jibga jibgan sojojin dake tsaron gate ɗin gidan sun wangale musu, da gudu suka dan na hanchin motochin waje suka ɗauki hanyar Babban masallaci juma'a
Karfe 2 dai dai hiyana ta fito daga part ɗin Ammi ta nufi ɗakin da yaya Ahmad ke kwanche hannun ta ɗauke da gorar ruwan addu'a da ta masa, yau tun safe take jin gaban ta na faduwa kamar wani abu zai faru dasu, sai hasbunalluhu wani mal wakil take ta nana tawa a zuchiyar ta
A ɓangaren diyana kuwa sun gama shiri tsab sun nufi Airport ita da Aunty farida da junior dan zuwa kano sai murna diyana keyi yau zata ga yaya Aryan.
Karfe 2:20 limamin babban masallacin juma'a ya miƙe ya fara sanar wa kamar haka
A yaune dubbanni jama'a suka saidai ɗaurin Auren (Safras Abubakar Saraki tare da matar sa hiyana Ahmad)
(Aryan Abubakar Saraki tare da matarsa diyana Ahmad) (Khalid Usman saraki tare da matarsa Fatima Zahra Abubakar Saraki) (Yusuf Abubakar Saraki tare da matarsa lamrat Ahmad) (Fahad Abubakar Saraki tare da matarsa Amrat Ahmad) a sukwane gaba ɗaya matasan Abba suka miƙe lokachi guda kamar abun haɗin baki, chikin tashin hankali Aiman ya dafe saitin zuchiyarsa murya na rawa ya fara magana
"Abba karka min haka wlh ni nake son diyana ba Aryan ba tun lokacin da nafara ganin ta na kamu da matsanan chin Son ta ban samu daman faɗa mata ba sai shekaran jiya kuma wlh Abba diyana ni take so ba Aryan ba dani take soyay...bai karisa maganar ba ya yanke jiki ya faɗi kasa bai ko shura ba, a sukwane dukkan su sukayi kansa suna kiran sunan sa ban da Aryan da Bgs Aryan kam yama rasa me zai che ji yayi duniya na juya masa tunani ya shigayi anya zai iya hakura da diyana kuwa? kai gaskiya ba zan iya ba, Bgs kuwa yama rasa ta ina zai fara magana a kan abun da Abba ya masa ɗagowa Abba yayi zaiyi magana kenan sai yaji karar wayarsa daga aljihun sa
Alama ya yiwa Aryan da ido akan yazo ya chiro wayar jiki ba kwari Aryan ya kara so yasa hannu ya chiro wayar Abba daga aljihun sa, ganin sunan my first born ne ya bayyana a kan screen ɗin wayar hakan yasa Aryan yin picking call ɗin da sauri tare da manna wayar a kunnen sa
daga ɗayan ɓangaren Aunty farida tafara magana chikin tashin hankali "hello Abba na diyana ta ɓata wlh bamu gan taba nan na barta zaune da junior sai dai na dawo na samu junior da kuma mayafin ta da ɗan kwalin da jakar ta, Abbana da alama sache ta akayi wlh nashiga uku" chikin fushi da tsawa Aryan ya fara magana " Aunty farida daman yarinya nan tana wajen ki!? Daman ashe za'a iya haɗa baki dake a chutar dani!?why zakimun hakan!? Why!?
"Aryan yanzu dai duk ba lokachin yin wan nan maganar bane kaji pls kusan abun yi da wuri idan ma sache ta akayi to kuyi sauri fara neman ta tun wayan da suka sache ta basu yi nisa ba"
Chikin tsarkewar murya yace "yanzu dai kiyi sauri ki bar wajen ki ɗauki junior ku koma gida gani nan zuwa yana gama faɗin hakan batare da ya jira amsar taba ya katse wayar, sauri sauri ya chiro wayar sa daga aljihu ya fara kiran layin Shahram
Bugu ɗaya Shahram ya ɗaga tare da faɗin" hello sir" "Shahram ku shirya min jirgi zuwa Maiduguri yanzun nan nan da 10mnt zan zo yana gama faɗin hakan ya katse kiran batare daya bi ta kan kowa ba ya fice daga masallaci, da alama ya manta dasu Abba yazo dan baya chikin hayyachinsa
Har ya kai wajen moton chin su sai kuma yaji wayar Abba dake hannun sa tana ringing, tsaki yaja tare da miƙawa ɗaya daga chikin sojojin sa wayar akan ya kaiwa Abba ansar wayar sojan yayi da sauri ya nufi chikin masallaci shi kuma Aryan ya shige chikin mota tare da bawa driven sojan umarni akan sutafi batare da bata lokachi ba sojan ya tada motar da gudu suka bar masallaci
Abangaren sojan kuwa yana shigowa chikin masallaci ya miƙawa Yusuf dake tsaye ta bakin kofa wayan Abba dake ta ringing tana neman ɗauki, ansar wayar Yusuf yayi ganin sunan Ammi ne yasa yayi saurin daga kiran chikin ruɗu da tashin hankali Ammi tafara magana "ranka ya dade kuyi sauri kuzo Allah yayiwa lamrat rasuwa, ai Yusuf bai san lokacin da yasaki wayar Abba ta faɗi kasa ba, a sukwane ya juya ya fice daga masallaci.
Ɗagowa Abba yayi yana kallon Bgs dake tsaye yama kasa magana mamaki ne ya kama Abba wai yau ɗaya daga chikin ƴaƴan sa ne ya suma amma Safras yake tsaye haka kamar ma bai san ana yi ba lallai yau da alama ran maza ya ɓachi sosai, chikin sanyin murya Abba yace "Safras kazo ka ɗauki Aiman ka kaimin shi mota mu wuche asibiti ko
kamar daman jira Bgs yake amasa magana Chikin fitar hayyaci da karfi yace "No Abba No me yasa zakamin haka kasan duk duniya ba wan da na tsani gani kamar yarinyar nan ni kwata kwata ma banson Auren ban son ganin mace kusa dani suna da rauni Abba wlh ka chucheni ka gama dani Ni ba zan zauna da itaba gaskiya dan haka na sak...✍️
To masu karatu nan na kawo ƙarshen book 1 masu son chigaba da karanta littafin duk karfin izzata Naira 300 kacal 👌 kuyi payment ta wan nan account din 3167987863 first bank Musa fatima zahra sai ki turo receipt ta wan nan number 09162620621 har kullun takuce Princess teema Star Lady more love
Akoi fa chakwakiya shin wanene zai hakura ya barwa ɗan uwan sa diyana? Yaya Bgs zai karke da Abba akan hiyana? Shin inama diyana take waye ya sache ta? Me ya samu lamrat? Yaya ma komar Ahmad da hiyana? Yaya Fahad zai yi da Auren Amrat? Duk wan nan amsoshin suna Book 2 sai mun haɗu karku bari abaku lbr yanzu asalin wasan zai fara
No comments