Recent Updates

Duk Karfin Izzata Book 1 Paga 36


*Episode 3️⃣6️⃣*



A fusace Bgs ya juya yama fasa shiga wajen Ammin taku yake irin na jaruman maza, ya fice daga part ɗin gaba ɗaya, part ɗin Aryan ya nufa a dai dai wajen part ɗin Ummi yachi karo da Yusuf da lamrat  sun fito daga part ɗin Ummi sun nufi part ɗin Ammi sai murnushi suke suna hira kamar wasu

kawaye, mamaki da al ajabine ya hana Bgs tafiya kuma ya hana shi magana tunani ya shigayi wai yaushe yaran nan suka dawo hakan, yayi nisa chikin tunani sai jin yayi Yusuf yayi ya ɗan tafa kafaɗar sa yana faɗin 


"Big bro me kuma ka keyi a nan? Wani mugun kallo ya wurgawa Yusuf wadda sai da yasa Yusuf ɗin haɗiyar wata yawu mai kuyar wuche makoshi, da kyar Yusuf ya iya buɗe baki ya sake chewa "my bro lfy kake kallona haka"? A fusache Bgs ya wuche ya nufi part ɗin Aryan, batare da ya chewa Yusuf komai ba 


Juyowa Yusuf yayi yana kallon lamrat dake tsaye,ta harɗe hannu a kirji tana kallon su "my baby ke kam ba kya tsoron yaya prince ɗin ne? Murmushi lamrat ta yi kafin tace "to ni yaya Yusuf in ban da kaima da neman magana ina ruwana dashi, mutumin da ko magana bai taɓa yi ba, nifa ban taɓajin voice nashi ba kwata kwata, to ai kaga ba ruwana dashi"


Murmushi kawai Yusuf yayi san nan ya jawo hannunta yana faɗin "zo muje mu gai da Abba tun da kin gai da Ummi, yau so nake na gabatar dake wa kowa na gidan nan, shima yaya prince ɗin naso gabatar masa dake amma sai yayi tafiyar sa sunkuyar da kai kasa kawai lamrat tayi batara da ta che komai ba 


Jan hannunta yayi har chikin fada, lamrat sai kokarin kwache hannun ta take dan kunyar Abba takeji amma yaya Yusuf ya riƙe ta sosai kuma yana jin, yadda take ta mutsu mutsu da hannun tana son kwache wa, amma yaki sakinta saima kara riketa da yayi sosai sai da suka isa gaban Abba san nan ya saketa ya samu waje saman sofa mai zaman mutun 1 ya zauna yana faɗin 


"Sannu da hutawa Abba" da fara'a Abba ya amsa lamrat kuwa tsugunnawa tayi har kasa ta gai da Abba, sai murnushi yake ya amsa mata san nan ya ɗora da chewa "amarya tashi ki zauna saman kujera, sunkuyar da kai kasa Yusuf yayi wai irin kunyar nan, hararar wasa  Abba ya wurga masa yana faɗin "au sai yanzu kasan da wani abu wai shi kunya ko"? Bari na samu Ammin ku anjima zan sanar da ita da kai da Khalid duk kar ta kara barin kushiga part nata sai ranar da aka shafa fathiha"


waro green eyes nashi waje Yusuf yayi sosai, chikin voice irin na masu shagoɓa ya fara magana "haba Abba so kake muyi chiwo ne, Allah ko kwana ɗaya ba zan iya jurewa ban ga my baby ba, da gudu lamrat ta tashi ta fice daga fadan dan ta lura shifa yaya Yusuf ɗin nan bai san kunya ba 


Zuba masa ido Abba yayi yana kallon ikon Allah 

       "Abba kasan me wlh ina son kafin mu koma London an shafa fathihan nan sai kowa ya wuche da matar sa" "Yusuf tashi ka bani waje kuma ni ba zan yiwa lamrat Aure a yan shekarun tan nan ba kwata kwata fa she is 14 years tayi kan kanta da yawa" waro ido waje yaya Yusuf yayi kafin yace "haba Abba na pls ai zata karisa girman ta a gida na, nifa Abba banso ma a che Auren mun nan ya wuche nan da 1 week ba"


Kwafa Abba yayi yace "to ka faɗawa babban yayan kune? dan kasan ni dai ba zan maka maliyi ba shine zai maka waliyi  ni kuma waliyin lamrat" a sukwane Yaya Yusuf ya miƙe ya nufi hanyar fita  yana faɗin "lallai Abba baso kake nayi aure ba a wannan rayuwar, in dai sai na fadawa Bgs ya zamo waliyina to wlh nama hakura da Aure har abada ya kai karshen maganar tare da ficewa daga fadan 


Dariya sosai Abba yayi kafin yace "dukkan ku nasan maganin ku ai tun ɗazun nake chewa ka tafi kabani waje kaki ka zauna kanamin surutai ba gashi yanzu chikin ruwan sanyi ka tafi ba" 


Aɓangaren Bgs kuwa


Kwanche ya samu Aryan saman katafaren gadon sa, idon sa biyu yana kallon sama da alama yayi nisa chikin tunanin da yake, dan ko sallamar da Bgs yayi bai jiba.


Hayewa samab gadon Bgs yayi ya kwanto da fuskarsa dai dai face ɗin Aryan ɗin, ya kwaro green eyes nashi sosai, a chikin idon Aryan, a sukwane Aryan ya yunkura zai tashi tamke wuyar sa Bgs yayi ya mai dashi ya kwantar, yana faɗin "yan zu kuma tunanin me ka keyi? 


Chikin fushi ta jin haushin tadda Bgs ya tsoratashi yace "wai dan Allah Bgs me na maka ne? bazaka kyaleni naji da damuwa taba sai ka karamin naka? komawa gefe Bgs yayi ya zauna kamar bai ji me Aryan ya faɗa ba, shiru suka zauna Almost 10mnt kafin Bgs ya juyo da kallon sa kan Aryan ya fara magana


"Ina kaunar ka Aryan duk duniya idan ka chire iyaye na ba wanda nake so kamar kai ba zan iya ganin ka a chikin damuwa ba, duk lokachin da ranka ya ɓachi ko kashiga damuwa tofa nafi kowa shiga tashin hankali, dolene na rinƙa yawan tambayar ka meke damunka, dan kai ne mutun na farko da nake kauna bayan iyaye na, daga kai sai Fahad sai Zahra  Aunty Farida da kuma Khalid Yusuf Ahmad, ba zan iya ganin damuwar ku, na yi shiru ba"


Da mamaki Aryan ke kallon Bgs "wai wace Zahra kake nufi" Aryan ya jefo masa tambaya yana tsare sa da ido, guntun tsaki yaja kafin yace "daman muna da wata Zahra ne a wan nan gidan bayan Auta "amma lallai Bgs ka iya iskanchin kala kala yanzu daman kasan ana kiran Zahra da sunan Auta, eyee wato duk abun da ake a gidan nan kana sane, amma sai kayi kamar baka san komai ba ko? 


"Kaga Aryan ni yanzu ka faɗamin tunanin me kakeyi ban che kamin wasu tambayoyin ba" "yanzu idan nache maka tunanin mace nake me zakache? Dogon tsaki yaja kafin yace "ka hauka che mana me kuma zan che sai na tashi na kama kai na dan ba amfanin na zauna ina magana da wanda bai da hankali, tsaki Aryan ma yaja san nan yace  "hmmmm Ni bari naje nayi wanka kana nan ne ko dai in same ka a part naka? Shiru Bgs yayi kamar bai ji abun da Aryan ɗin yace ba, ganin bai da niyar magana yasa Aryan ya miƙe ya nufi toilet ya barshi awajen, Shiru yayi kamar mai tunani jim kadan ya fara magana


"Khalid yana son Auta wow nayi farin chiki da hakan gaskiya domin ko ba komai zata samu farinchiki, amma dai dole Khalid ya chanza kasa dan ba zai zauna damu waje ɗaya ba, shi ma Yusuf transfer zan masa ya koma, Us ko India duk kansu bazasu zauna kusa damu da mata a gefen suba"


"Gaskiya ko ni nayiwa Auta murna da samun Khalid a matsayin miji, chewar Aryan dake tsaye a bakin kofar toilet ɗaure da towel a ƙugun sa. Wani hararar Bgs ya wurga masa tare da miƙewa yace "idan ka gama shiri ka same ni awajen Ahmad, yana gama faɗin hakan yayi waje Aryan kuma ya juya ya koma chikin toilet


AUNTY AMARYA


Zaune take saman sofa mai zama mutun biyu tana waya da Aunty Maryam, yaya Umar da yaya Haidar suna zaune a gefen ta saman sofa mai zaman mutun 3, da gudu wata bigaggiyar budurwa ta shigo ko sallama babu tana sanye chikin wasu shaggun riga da wando, wadda kana iya ganin komai na tsurar jikinta, ta zuba gashin doki akai kamar wata aljana, ga wani dogayen gashin ido da ta sanya yarinyar tana da kyau ba laifi farache sosai amma farin mai ne, a shekara bazata wuche 21 year's ba 


....... Da gudu ta tafi ta faɗa jikin Aunty amarya tana dariya "ke zulaihat menen hakan karyani kike so ki yi koh"? Chewar Aunty amarya "haba momy yanzu ni ɗin che zan karyaki ki ganni fa ko kiba bani dashi" "eh to naji yanzu dai ɗaga ni" "gaskiya aa mommy ni wlh a jikin ki nake son kwanchiya wani tsawa Umar ya daka mata wadda yasa sa ta miƙewa tsaye ba shiri "ke!! bazaki tashi ba"

    "Haba Umar baka ganin yarinya che, wan nan irin tsawa haka ai ba ita kaɗai ka tsorata ba har dani" chewar Aunty amarya, miƙewa Umar yayi a fusache ya nufi waje


 da sauri haidar ma ya miƙe ya bi bayan sa 


"Maryan ki bari zamuyi waya anjima" chewar Aunty amarya batare da tajira amsar Aunty Maryam ba ta katse kiran ta ajiye wayar a gefe, san nan ta dawo da kallonta kan zulaihat dake tsaye tana taunan chingum.


"Dawo kiyi zaman ki my zulee kyale su Umar ɗin nan" "Allah mommy wan nan Umar ɗin bai da kirki ai naso na che masa bazan tashi ba, sai kuma na kyalesa" "kai zulaihat yayan naki zakiwa rashin kunya? "Aa mommy wlh Umar ba yaya na bane dan fa bai girme min ba, mommy na tace tare aka haife mu" 

      "Kai zulaihat aiko Umar ya baki shekara 4 dan yanzu wata uku ya rage masa ya chika 25 years" "to nidai mommy koma me gaskiya ba zan bari wani a chikin gidan nan ya takani ba, Ni mommy ina mijin nawa ma yake? Inane ɗakin sa naje na ganshi?


"A lallai zulaihat na yarda baki da hankalin kin san wanene muke son haɗa ku kuwa Bgs Brigadier General Safras, kuma prince yarima mai jiran gado shine mai rike da babban mukami na soja gaba ɗaya bayan mukamin sa ba wani mukami kuma duk wani soja da kike gani a duniyar nan to a karkashin Brigadier General yake, sai dai kowani kasa da nasu, ke bama shiba wlh ina rabaki da matasan gidan nan kibi kowa a sannu idan ba haka ba wlh inaga gawar kima zatayi wuyar ganewa kin dai ji na faɗa miki, yanzu ki wuche ɗakin tsakiyar nan kije kiyi wanka dan lokachin chin abin chin rana ya kusa, kiyi sauri inason in gaba tar dake wa kowa"


Shiru zulaihat tayi tana tunani "hmmm lallai  wato masu girman kai ko to wlh nine nan zan gyara musu zama, ba Brigadier General Safras ba koma taɓa samane zanyi maganin sa, ni da na juya manyan manyan maza masu faɗa aji a kasar nan ma bare shi ɗan karami kwaro, ni wlh ba dan ma yana da kyau ba me zanyi dashi, kyau nashi ne kaɗai ke burgeni da kuma kirar jikin sa irin na jaruman maza ko in che sadaukin yaki amma ba komai zan dawo dasu kan saiti" ganin zulaihat tayi shiru alamar ta tafi duniyar tunani ne yasa Aunty amarya ta miƙe ta dafa kafaɗar ta tace


"Zulaihat kar kiji tsoro fa dan nache maki shi Brigadier General ne  mubi komai a sannu In Sha Allah zai soki kuma zai Aure ki, kinji"  dawo da kallonta zulaihat tayi kan Aunty amarya san nan ta sheke da wani shu umin dariya tana faɗin "haba mommy karki damu nifa ba wani tsoron da naji yanzu dai bari naje nayi wankan" tana gama faɗin hakan ta ɗauki jakar ta ta wuche ɗaki, binta da kallo Aunty Amarya tayi har ta shiga ɗakin, wani nauyayyar ajiyar zuchiya ta sauke kafin tace "lallai zulaihat idan bakiyi hankali ba zaki koma da karyayyen kafa ko kuma daga nan ki wuche gadon asibiti dan na lura kan ki na rawa sosai, kuma kan naki ma ya rasa aina zai yi rawa sai a gidan Alhaji Abubakar Saraki gidan da yake da tarin matasa har rai 9 chikin su akoi manya manyan sojoji ga manyan likitoci, lauya engineer saurauta mulki dukka, hmmmm gaskiya rawan kan nan naki bai miki adalci ba, to Allah dai yasa ki wanye da kowa lfy, tana kai karshen maganar ta miƙe ta nufi ɗakin ta


Washe gari


Maiduguri


Zaune take a chikin Class nasu tayi shiru tana kallon kasa kamar mai tunani sauran students sai surutu suke.


 buga belt ɗin fita breakfast da akayi ne yasa students ɗin su kayi ihu da karfi suka fara tururuwan fita waje.


 gaba ɗaya kowa ya fice daga class ɗin sunyi waje dan zuwa yin breakfast saura diyana da wata yarinya dake zaune a kujerar bayan ta, chikin nutsuwa diyana ta miƙe tanufi hanyar fita har ta kai bakin kofar fita sai kuma ta dakata ta juyo tana kallon tarinyar dake zaune chikin Class ɗin, kallo ɗaya tayiwa yarinyar ta gane akoi damuwa atattare da yarinyar sosai, juyowa tayi ta dawo chikin Class ɗin kusa da yarinyar taje ta zauna chikin sanyin murya ta fara magana


"Sannun ki sunana diyana kefa" chikin sanyin murya itama yarinyar tace "Sunana Zainab" "wow amma Zainab me yasa ko da yaushe idan muka fita breakfast ke kike zama a class baki fita ko ina? "Babu komai Aunty diyana kawai Ni ban san me zan fita  nayi awajen bane saboda ni bana zuwa da abinchi kuma ba'a bani kuɗin break"

  "To Zainab me yasa baa baki kuɗin break ɗin? ko me yasa ba'a baki abin chi a gidan basu ganin har karfe 3 muke tashine?da baza su rinƙa baki abinchi ba, basa tunanin zaki ji yinwa? "Aunty diyana Ni fa bani da mama awajen matar babana nake shiyasa ita kuma bata bani abin chi kuma daddy na yana bani kuɗin break ai, amma Aunty na ɗin  tache idan na sayi wani abu da shi sai ta kasheni sai dai na ajiye kuɗin na mai da mata" wani dogon tsaki diyana taja kafin tace "zanchen banza ke bazaki sanar da daddyn na kuba, to ina maman na ki take ko ta rasune?  "Aa bata rasu ba tana raye rabuwa kawai sukayi da daddy na" 

   "Eyya to shike nan yanzu dai muje muyi break tare kuma daga yau tare zamuna chin abinchi na, kin zama friend ɗina kinji, ta karisa maganar tana miƙawa Zainab ɗin hannu, hannu Zainab ta bata suka gaisa san nan suka miƙe atare sukayi waje


Da mamaki yan class nasu kai gaba ɗaya yan school ɗin ke bin su diyana da ido mamaki suke yanzu duk jan aji da iyayi irin na diyana bata kula kowa a school ɗin nan shine zata kula wanchan kazamar Zainab ɗin,  ita kuwa diyana bata ma san sunayi ba dan basa gaban ta daman ba ta yiwa kowa magana a school ɗin rike da hannun juna suke har suka isa wajen chin abinchin school ɗin.

  


KANO



Aban garen su hiyana kuwa


Kamar kullun ta fito daga class nasu kan ta na mata matsanan chin chiwo, ta nufi class nasu Zahra a hankali take tafiya  kamar bata son taka kasa "ke ina zakije zo nan, chewar jabir dake tsaye a bakin kofar Class nasu" chikin sanyin murya hiyana tace "kayi hakuri jabir wlh yau kai na namin chiwo sosai bana son jin surutu ko kaɗan yanzu ma zanje na kira Zahra ne tazo ta rakani office na Hm, saboda ya saka a mai dani gida" chikin tsawa jabir yace "ke!! ni kike chewa baki son surutu na!? wato ma surutu kika ɗauki magana ta ko? Shiru hiyana tayi bata che komai ba "to ki wuche mutafi yau wlh har atashi muna tare kuma ke zakimin hira yau ni kuma in zauna shiru ina sauraron ki "gaskiya jabir ba zanje ba saboda bazan iya magana ba, ko ina da lfy ni ban iya surutu ba bare kuma yanzu da bani da lfy" a fusache jabir ya damko hannun ta ya fara jan ta da nufin sutafi 


A zuchiye hiyana ta ɗaga hannu ta sharara masa mari chikin tsawa tace "idan ka sake taɓa jikina wlh duk abun da na maka kai kaja" a zafafe jabir ya ɗaga hannu zai zabga bama mari charab yaji daga baya an rike hannun sa, a fusache ya juyo da karfi ganin.....✍️



Amin afuwa bana update ranar Sunday amma na muku yau ba yawa dai, ina busy sosai ne sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kaimu akoi fa chakwakiya

No comments