Duk Karfin Izzata Book 1 Paga 34
Episode 3️⃣4️⃣*
Misalin karfe 5:30 na yanmma Abba na zaune a fada yayi shiru kamar mai tunanin, da sallama dauke abakin sa Aryan ya shigo ranshi a ɓache fuskar nan tasa kamar bata san menen dariya ba, daku yake irin na
jaruman maza, saman kujerar dake kusa da Abba yaje ya zauna, sai wani fitar da iska mai zafi yake daga bakinsa."Aryan lfy naga ran ka aɓachin haka"
"Abba pls ka dawo da yarinyar nan gidan" murmushi gefen fuska Abba yaɗan saki a chikin zuchiya yana faɗin "kafara zuwa hannu kenan ae daga kai har sauran sai nayi maganin ku chikin ruwan sanyi zan dafaku.
"Abba pls magana nake makafa wai ina ka kai tane? "Wace yarinya kuma Aryan? " Abba yarinyar dake kai mini coffee ɗin nan mana, daure fuska Abba yayi sosai kafin yace "au daman akoi wata yarinya dake kai maka coffee ne a gidan nan ban sani ba" a sukwane Aryan ya ɗago ash eyes nashi yana kallo Abba,
Ƙara ɗaure fuska sosai Abba yayi
"Eh mana Abba yarinyar da Ammi ta ɗauko su daga Yola" "to ae Aryan su huɗu ne wane daga chikin su kenan? Dafe kai Aryan yayi dan shi kwata kwata bayason kiran sunan diyana gashi kuma Abba yana neman ya kuresa.
"Abba wan nan mai bin babban, ni ban san sunan taba, ba karamin daɗi Abba yaji ba ganin yadda Aryan ke girmama sunan diyana har bai son kiran sunan, hakan ya kara tabbatar masa bakaramin so Aryan kewa diyana ba, dan haka sai yace
"Au diyana kake nufi? Da sauri Aryan yace "eh Abba ita nake nufi.
"To me yasa kakeson adawo da ita kuma? bayan kai ne da bakin ka kace baka son ganinta"
"Nifa Abba banche bana son ganin taba" "to naji ba kache ba amma yanzu me yasa ka keson adawo da ita? "Abba ina son adawomin da itane tazo ta chigaba da kawomin coffee dan tafi kowa iya haɗa coffee a gidan nan"
Nan take Abba yaji ransa ya ɓache, bakaramin haushi Aryan ya bashiba, wato dai bazai che yana son taba kuma har yanzu dai bai san darajar taba, tunda kallon mai kawo masa coffee yake mata wlh zanyi maganin shi kuwa"
chike da ɓachin rai yace "ai ba ita kaɗai bace daga yauwa duk gidan nan ba wanda zai sake kai maka coffee sai dai masu aiki domin nache Ammin ku ta ɗauko min sune dan suzo su huta ba wai suzo suyiwa wani ko wata aiki ba, kuma bazan dawo da itaba tabar gidan nan kenan, a chan zan mata Aure, na huta itama ta huta"
Da karfi Aryan yace "No Abba no ka daina irin wadan nan maganganun wlh kanasawa naji zuchiyata kamar zata buga zan iya mutuwa Abba banason jin su" da mamaki Abba ke kallon Aryan, yasan chewa duk chikin ƴaƴan shi ba wanda ya kai Bgs Aryan Fahad kishi, suna da bala'e kishi sosai kuma da kishin nasu zaiyi amfani yayi maganin su.
"Abba dan Allah ka dawo da ita" "Aryan Allah bazan dawo da itaba sai ka faɗamin akan wani dalili kakeson ta dawo?
"Abba na faɗa maka ai coffee zata rinƙa kawomin" mikewa Abba yayi chikin fushi yace "to kai ba left kanal ganaral na sojoji bane sai ka nemo in da take ai da kanka, yana gama faɗin hakan ya nufi hanyar fita faga fadan ma gaba ɗaya
Kwafa Aryan yayi yana faɗin "ai kuwa zan nemota Abba zakasha mamaki, chike da kwarin guiwa da yadda da kansa ya mike shima ya fice daga fadan.
Washe gari da safe misalin karfe 5:30, hiyana che tafito daga part na Ammi sai sauri take kamar zata tashi sama, tana tafiya tana yan waige waige, kamar mara gaskiya, kai tsaye ɗakin da Yaya Ahmad ke kwanche ta nufa,
A hankali ta tura kofar ta shiga hannunta rike da roban ruwan faro,
kamar dai kullun kwanche yake idon sa biyu yana kallon sama, ga hawaye nan bushe a fuskar sa, ta gefen kunne Allah sarki bawan Allah da alama kuka yasha.
Kusa da shi hiyana taje ta zauna tare da fadin "yaya Ahmad ya jiki?" dawo da kallon sa yayi kanta ya lumshe mata ido ya buɗe alamar da sauki.
"Yaya Ahmad zaka iya shan ruwan adduar nan wlh jiya kwata kwata ban yi barchiba kwana nayi ina maka addu'a, tayi maganar tana nuna masa roban ruwan faro dake hannun ta, ɗaga mata ido sama yayi alamar a'a ita kuma, hiyana bata fahimtar ba, kasan chewar iya lunshe ido kawai tasan yanayi, chiki sauri ta ɓuɗe robar ruwan sauri sauri take dan bata son kowa ya ganta kuma tasan su Bgs suna dawowa masallaci zasu zo duba shi dan suga ya ya kwana, ita kuma tana son ta bashi ruwan addu'ar kafin ta tafi school.
Tsiyaya ruwan tayi a marfin gorar, san nan tasa ɗayan hannun ta ta ɗan buɗe bakin nasa ta zuba masa, ruwan zuba wa bakin nashi ido tayi tana gabin yadda ruwan ke dawowa alamar ba zai iya haɗiyewa ba, wani iri taji sai taji gaba ɗaya jikin ta yayi mugun sanyi, Allah kawai take roko da yasa yaya Ahmad ya haɗiye ruwan nan koda kaɗanne.
Tana chiki wan nan yanayin ne tajiyo diran motochin su yaya prince alamar sun dawo daga masallaci, kuma tasan kai tsaye ɗakin zasu zo
A sukwane ta ɗauki gorar ruwan ta nufi waje, tsabar sauri har tana kokarin faɗuwa.
Allah dai ya rufa mata asiri babu wanda ya ganta a chikin su, har ta shige part ɗin Ammi
Maiduguri
Diyana riƙe da hannu junior suka fito harabar gidan, nan suka sami Aunty farida da dadyn junior zaune chikin mota suna jiran su, da sauri suka karisa wajen motar suka buɗe gidan baya suka shiga, dady'n junior da kanshi yayi driving nasu a nitse yake tuƙi
Da sauri baba mai gadi ya wangale musu katafaren gate ɗin gidan, a hankali dady'n junior ya dan na hanchin motar waje,
tuki yake suna yar hirarsu da Aunty farida, chikin ƙanƙanin lokachi suka isa school nasu junior, batare da bata lokachi ba dady'n junior ya fito daga mota ya barsu Aunty farida a gurguje yaje yayi wa diyana komai na registration da sauransu san nan ya dawo yace "diyana da junior su biyo sa,yana gama faɗin hakan ya juya ya fara tafiya, da sauri suka fito diyana ta rike hannun junior sukabi bayan sa ya rage Aunty farida che kaɗan a motar, office ɗin HM na school ɗin suka shiga, anan ya miƙa masa amanar diyana ya juya ya tafi
Hm da kanshi ya kai diyana class nasu wato primary 5 ko da tashi class ɗin gaba ɗaya students ɗin sun zuba mata ido suna kallon ta, ba karamin rikitasu kyan diyana yayi ba mu samma blue eyes nata dake ɗaukan ido gashi tasha kwalliya sai dai bata sa jambaki ba, amma idan kaga ɗan ƙaramin bakin nan nata ka rantse tasa pink janbaki, daga masu chewa Wow, sai masu chewa Masha Allah
kujerar tsakiya Hm yace taje ta zauna.
diyana ko baki baya shiru idan aka mata abun da bata so chikin iyayi da yanga tace "uncle wlh ni kujerar gaba nakeso bazan iya zama awani kujeraba idan ba gaba ba, toma ai kujerer baya na dolayene, " da mamaki yan class ɗin suke kallonta dan sun san gaba ɗaya school ɗin ana mugun tsoron Hm dan baya wasa da ɗalibai, gaba ɗayan su, sun zubawa Hm da diyana ido suna jiran suji wani amsa zai bata.
Chikin nitsuwa yace "to shikenan jeki zauna a kujerar gaban, ke saudat tashi ki koma kujerar tsakiya ki barmata na gaban, subhanallah gaba ɗaya yan class ɗin mamaki yadda Hm yayiwa diyana magana suke, kowannen su ya shiga tunanin wacece diyana? Yar wacece a kasan nan? Domin Hm ko ƴaƴan chikin sa baya raga musu, amma ko wache ta kuduri niyar tambayar diyana idan Hm ya fita.
Haka ko akayi Hm na ganin diyana ta zauna a kujerar yaja hannun junior suka fita waje.
Suna fita yanmata kai har da maza suka fara tururuwa zuwa wajen diyana, domin tambayar ita yar wacece, gaba ɗaya student dake class ɗin bazasu fi su 30 ba domin a school ɗin ba'a haɗa yara dawa a class ɗaya kowani class suna da A & B har C ma
Shiyasa basu dayawa sosai gaba ɗaya students ɗin sun taso suka nufi diyana ban da yarinya ɗaya wadda ke zaune shiru tana binsu da ido, kallo ɗaya zaka mata kuma kagane tana chikin damuwa da alama kuma yaran class ɗin suna kyarar ta basa sonta, dan ga idon ta nan chike tab da kwalla.
Ɗaya daga cikin students ɗin ne ta miƙawa diyana hannu, tana faɗin "sannun ki da zuwa ni dai sunana Maryam zamu iya zama friend"? Dayake diyana ma yar ji da kai che ba kowa takewa magana ba sai wadda ta ga dama, shiru tayi kamar bata san da tsayuwar mutane a kusa da ita ba,
Basuyi mamaki ba dan a yadda suka kallon diyana, dole yar wata hamshakin mai kuɗin ne ko yar shugaban kasa koma dai yar sarkin Makka, dan a ganin su kyan diyana ya wuche ache mata yar Nigeria, ga fatar jikinta tayi luwai luwai kamar na jarirai, haka dai sukayi ta mata surutai da tambayoyi amma diyana ko ta ɗaga ido ta kalli ɗaya daga chikin su, saima fitar da chocolate tayi daga school bag ɗin ta, ta buɗe tafara sha,
ganin ta manna musu hauka sai shan chocolate take yasa wasu daga chikin su suka koma ma zaunin su, sauran kuma suna tsaye, wata daga cikin su ta dubi diyana tace "haba baiwar Allah ya kamata ki kulamu mana
.......chikin tsawa da tsiwa batare da ta ɗago ta kallesu ba tace "dan Allah ku tafi ku bani waje, tun raina bai ɓachi ba, jin hakan yasa duk suka suka nufi wajen zaman su, dan suna tsoron yiwa diyana wani maganar saboda basu san wacece ba karsuje su taɓo abun da yafi karfin su, kuma ayadda suka ga Hm na mata magana hakan ya kara tabbatar musu, diyana ba daga karamin gida ta fitoba.
Wan nan kenan ya kamata mu waiwayi garin Yola tun da muna kusa dasu kunga tsakanin yola da Maiduguri banisa sosai
Yola
Zaune take a tsakar gida ta rasa meke mata daɗi, sai faman juyi take saman ɗan chinyayen tabarman ta, da duk ɓera ya gwaguyesa, jitake kamar hanjin chikinta zasu tsinke saboda yinwa da take ji ga chiwo da chikin nata ke nata gashi gidan nata ba komai bare ta dafa, gani take duniya na juya mata, duk ta rame lokachi guda ta chanza kamar ba itaba.
Da sallama hasana matar yaya Bello ta shigo gidan, wani kallo uku goma inna ta wurga mata kafin tace "munafurchin me kuma ya kawoki gidan nan"?
Tsugunnawa har kasa hasana tayi chikin ladabi tache ina wuni goggo habiba, chikin tsiwa Inna tace "idan ban wuniba zaki ganni ne" mikewa hassana tayi ta karisa wajen tabar man da innar ke zaune ta ajiye mata ɗan buhun dake hannunta tanan faɗin "gashi hamma Bello ne yace na kawo miki" bata jira amsar inna ba ta fice daga gidan da sauri
babu ko kunya bare tsoron Allah, Inna ta jawo buhun ta buɗe, ɗanyar gyaɗa ne da kuma gwaiba, dayake farkon shigowar damuna che akoi kayan lambu sosai, chike da zumuɗi tasa hannu ta ɗauki gwaiban tafara chiki tana ɗan murmushi,
sai da ta chinye gwaiban tas san nan ta miƙe da kyar ta nufi kichin tafara kokarin hura wuta dan ta dafa gyaɗar.
KANO
Misalin karfe 4 na yamma hiyana che zaune a gefen gadon da Yaya Ahmad ke kwanche tana ɗan tofa masa addu'oe a hankali, shi kuma ya zuba mata manya manya fararen idon nan nashi yana kallon ta
Cikin sanyin murya tace "yaya Ahmad ya kakejin jikin naka, abun mamaki sai taga ya ɗanyi murnushi, ya lumshe mata ido ya sake budewa, wani cool murmushi ita ma ta saki ganin yaya Ahmad ya fara samun sauki har ya fara murmushi, chigaba tayi da tofa masa addu'oe da take,
Almost 10mnt ta ɗauka tana masa addu'a, san nan ta ɗago tana kallonsa tace "yaya Ahmad zan chigaba da zuwa ina maka topin addu'a har na tsawon kwana 7 san nan zan haɗa maka ruwan addu'a mai karfi da kaina, ina sa ran kafi na gama topa maka addu'oe da zan maka na kwana 7 ɗin nan In Sha Allah zaka fara chin abin chi ta yadda ina kawo maka ruwan addu'a zaka sha, kuma da yar dan Allah kana sha zaka samu lfy, murmushi ya kara sakar mata alamar yaji daɗi, itama ta sakar masa murmushi san nan ta miƙe ta nufi waje.
Aunty Amaryan
Tsaye take a gaban miro tana waya da hajj sadiya
"Haba hajj sadiya wlh nache miki ban san ya akayi hakan ta faruba Amma dai zan sa musu ido yanzu" daga ɗayan ɓangaren hajj sadiya tace "to wlh hajj Hajara gara tun dare bai mini ba kisan abunyi, bakiga da gagarabadau ya kirani faɗan da yake tayi bane yace wai tayaya za'ayi muyi sakachi har wata tana kokarin kunche masa aiki, kuma yache wlh yarinyar bazai iya yimata komai ba shiyasa da taje tana kokarin yiwa shi Ahmad ɗin addu'a aljanun suke ihu sun kasa yimata komai,saboda askar ɗin datake, idan bamuyi da gaskeba tofa tana gab da kunche aikin nan kuma tana kunchewa inba muyi saa ba to kan ɗaya daga chikin mu zai dawo.
Dafe kirji Aunty amarya tayi kafin tace "munshiga uku hakan ma bazata faruba wlh in dai Hiyana che daga yau bazata sake shiga in da Ahmad yake ba zan mata iyaka da shi, ba zan bari ta ƙara koda ganin saba"
"Yauwa hajj Hajara kiyi kokari dan Allah" "to kawai Aunty amarya tace sanna sukayi sallama ta ajiye wayar saman mirrow ta chigaba da gyara fuskar ta, tana tunanin yadda zata ɓullowa hiyana
To jama'a kwanaki sunja lokachi ya tafi a yau diyana ta chika sati 1 da kwana 3 a gidan Aunty farida Maiduguri
Yauma kamar kullun ta tsara kwalliyar ta kamar yadda ta saba tayi kyau sosai ga wani giba da ta ɗanyi sosai ta chiko ta ko ina, shap nata ya kara bayyana ga wani kyau da fatar jikin ta ya yayi, ya kwanta sumul sumul kamar fatar jariri, sai kyalli take ta ko ina, sanye take chikin wani haɗadɗiyar wandon jeans blue da t-shirt baki, ba karamin kyau kayan suka mataba sun zauna a jikinta sosai ta saki lallausan bakin gashin nan nata har gadon baya sai sheki yake, ta baza takartun makarantar ta a tsakiyar babban palon kasa tanayin home work, sai faman taunar chingum take kas, kas, kas, abunta
Da sallam ɗauke a bakinsa ya shigo palon, a sukwane diyana ta ɗago kai dan voice nashi da tayi, da sauri ta miƙe ta nufesa tana faɗin ƴa...✍️
No comments