Recent Updates

Duk Karfin Izzata Book 1 Paga 33


 *Episode 3️⃣3️⃣*



.......Baya baya tayi ya yanke jiki ta faɗi kasa saboda tsorata da tayi, shiko ko ajikinsa juyawa ma yayi zai koma  in da ya fito dan ji yayi ya fasa shiga ɗakin, 


"Idan ka kara taku ɗaya wlh in ranka yayi dubu sai na ɓata maka, chewar Ammi tayi maganar chike da jin haushi abin da Bgs ɗin yayi, 


Chak ya tsaya bai tafiba kuma bai juyoba, chikin faɗa Ammi ta fara magana 

     "Ai wlh ko baka tausaya wa yarinyar nan dan maraichin taba zaka tausaya mata dan wahalar da tasha arayuwa kanaji fa, agaban ka lokachin da bata da lfy Aiman ya dubata, kaji ji da kunnen ka Maryam ta bugi yarinyar nan sosai a kai shiyasa idan ta tsorata take suma Amma duk da haka bazaka dai na tsoratata ba sai ka kasheta ka huta ko? wai ma me yarinyar nan ta maka ne?


A sukwane ya juyo dan jin yadda Ammi ke magana, chikin faɗa a hankali ya tako ya dawo chikin ɗaki hannu ɗaya ya sa ya ɗauki hiyana ya saɓata ta a kafaɗarsa yanufi gadon Ammi da ita, sai wani kwaɓe fuska yake kamar ya ɗauki kashi, a chikin zuchiyar sa yana faɗin "Allah Ammi kema bazaki kara ganina a part naki ba bare ki rinƙa haɗani da waɗan nan abubuwa kamar aljanun, 


Sauko da hiyana yayi da nufin yayi wurgi da ita kan gadon sai kuma yaɗan sachi kallon Ammi yaga dai, still shi ta ke kallo dan haka sai ya kwantar da ita a hankali, a sukwane ya juya sai sauri yake ya fice daga ɗakin.


Girgiza kai kawai Ammi tayi kafin tace " Allah ya baki lfy hiyana amma gaskiya maryam ta chucheki wlh, saukin abun ma ɗaya tun da naji Aiman yace zaki iya warkewa amma sai a hankali, wani karin abun haushin kuma wai inkin suman kar azuba miki ruwa abarki sai san da kika farfaɗo da kanki, Allah sarki baiwar Allah ko abinchi baki chiba, Allah dai ya baki lfy shine kawai addu'ar da zamu Miki.


Maiduguri


Aunty farida diyana junior suna zaune a katafaren babban palon kasa, diyana sarkin kwalli tasha kwalliya sosai, ta sanya wani dankareren shadda, brown colour an masa aiki da milk colour zare, ɗinki dogowar riga, ba karamin zama kayan yayi ajikin taba, ta ɗaura ɗankwali  ɗaurin ture kagatsi ya, tana zaune saman sofa,ta tasa laptop ɗin junior a gaba tana buga game, 

              Kamar daga sama sukaji diran motochi gidan, da sauri diyana ta kawar da laptop ɗin gefe tana faɗin "Allah yasa yaya Aryan ne, dasu hiyana, mamaki ne ya kama Aunty farida yanzu duk irin maganar dana gayawa yarinyar nan ashe baima shiga kunnen taɓa, oh ni farida gaskiya sai nayi da gaske dan naga alamar, kafin nasa ta daina zanchen Aryan to za'a sha wahala, tayi nisa chikin tunanin, sai taji sallama, da sauri ta ɗago ido, sai kuma ta mike tsaye da fara'a tana faɗin


"Oyoyo oyoyo hajjaya Fateema, mutanen saudiya saukar yaushe, Hajj fateema kyakkyawar macece ajin farko fara tas, ga dogon hanchi har baka, kai daga ganita kasan naira ta zauna gata irin wayayyun matan nan ne, 


Ɗaukan laptop ɗin junior diyana tayi sanan ta kama hannun sa suka nufi waje tana faɗin "junior mu tafi garden koh? tun da bakin sunzo zasu dame mu.


Suna fitowa harabar gidan, blue eyes nata ya sauka kan wani hadaɗen balaraben  guy, zaune yake saman bayan ɗaya daga chikin motocin da suka zo dashi, ya ɗora kafa ɗaya kan ɗaya ga wasu jibga jibgan bodyguard guda 4 a kusa dashi suna tsaye, 

kyakkyawa ne guy ɗin shima, amma dai bai kai yaya Aryan kyau ba Chewar diyana.


Tunda diyana tafito ya tsareta da manya manyan fararen idon nan nashi, sosai yake kallonta, itakam ko ajikinta kallo ɗaya ta masa ta kauda kanta, ta chigaba da tafiya, har suka iso in da yake zaune, zasu wuche kenan, chikin harchen larabchi yace


"Aslm yammata min ti ɗaya dan Allah"  diyana zatayi magana, sai ta tuna abun da yaya Aryan yace mata idan tayiwa wani namijin magana to zata samu chiki, da sauri ta ja hannu junior suka wuche har suna haɗawa da gudu, suka shige chikin garden ɗin.


A hankali guy ɗin ya diro kasa daga saman bayan motan, yabi bayansu, bodyguard nashi zasu bishi ya ɗaga musu hannu alamar su tsaya, 

       Tsayuwa sukayi a wajen moton tasa shi kuma yabi bayan su diyana


         Ko daya shiga garden ɗin zaune ya same su, diyana nata buga game a laptop, junior kuma yana zaune gefenta yana ta mata surutu, 


"Yammata namiki magana ɗazun baki amsa ba kodai bakyajin larabchi ne? Banza diyana tayi dashi kamar bata san da tsayuwar mutun awajen ba.


Chanza harche yayi zuwa harchen turanchi, yace "pls kiyimin magana nasan ai kina jin English kam, idan ma ba kyajin larabchi" nan ma shiru diyana tayi batayi magana ba, "yammata pls ki faɗamin sunan ki, Ni dai sunana, Abdurrahman" shiru diyana tayi kamar bata awajen.


Hannu Abdurrahman yasa ya ɗan taɓa kafaɗarta yana faɗin "nasan kina jina kawai jamin aji k... Bai karisa maganar ba yaji saukan mari a kumatun sa, kafin ya farga diyana ta damko hannun junior sun kwasa a guje sukabar wajen sai chikin gida.


.........dafe kunchinsa Abdurrahman yayi yana faɗin "in ban da soyayya kamar ni yau Abdurahman Abdurrahim,  mace zata mara, kash amma soyayya baki min adalchiba, baki kyau tamin ba amma ba damuwa bari dai nayi kokari na samu soyayyar ta zan rama marin daga baya" jiki ba kwari ya juya ya koma wajen motar'su.


Aɓan garen diyana kuwa, aguje ta shigo palo sai numfashi sama sama take da sauri Aunty Farida ta miƙe ta nufota tana faɗin 

       "My diyana lfy? me ya faru ki kayi guduwa haka? 

  

"Aunty farida yaya Aryan yace min idan namiji ya min magana na amsa ko ya taɓani zan samu chiki, shine wanchna Abdurrahman din kuma yazo ya taɓani, shine fa na mareshi, na gudu dan Allah Aunty farida ki kiramin yaya Arya bari na tambayeshi da wanchan Abdurrahman ya taɓani zan samu chikine ko kuma, bazan samu ba"


"My diyana jeki ɗaki ki kwanta ba wani chikin da zaki samu ai shima Abdurahman ɗin yayan kine. 

           "To Aunty farida" tana kaiwa nan ta wuche ɗaki, 


"Hajj farida wacece wan nan kuma? Hajj fateema ta tambaya tana nuna diyana dake tafiya ɗakin su da hannu, 

      "Kanwata ce Aunty farida ta bata amsa tana kokarin komawa ta zauna saman kujerar da ta tashi. "Gaskiya hajj farida naji kanwar nan taki  ta kwanta min arai sosai jinake kamar ki bani ita, waro ido waje Aunty farida tayi chikin zuchiyar ta tana faɗin "tab lokachi yayi da zan hana kowani bakona ganin diyana, yarinya ne sai shigen farinjini kowa yace yana son ta ba maza ba ba matan ba kowa abashi ita kawai.


"Hajj Farida lfy? Tunanin me kike"? 

    "Ba komai hajj fateema" to ya maganar ya rinyar fa pls ku bani ita"  "a'a hajj fateema wannan yarinya amana che awaje na wlh, ban isa inyi kyau ta da itaba, shiru hajj fateema tayi bata sake Magana ba


Yola


Zaune Inna take a tsakar dan ɗakin bukkan ta ga uban amai a gaban ta da ta tula, ta kasa ko mukewa, 

          Da kyar ta yunkura zata miƙe sai wani amai kuma ya kubche mata, nan fa tasake komawa ta zauna tana kwara amai, tun taba amai da daɗin rai har tafara fita hayyachin ta,  

Tana amai ta baki tana zawayi ta kasa, sosai ta jajjaje ta ko ina sama da kasa gaba ɗaya yoyo yake, kwanchiya tayi cikin zawon nata tana nunfashi sama sama, kamar zata mutu gashi babu kowa bare ta sa ran za'a tai maka mata.


Wannan kenan tun da munzo munga ya inna take mu koma gidan Abba kuma


KANO


Da sallama ɗauke a bakinta hiyana ta shigo chikin ɗakin da yaya Ahmad ke kwnache dakin babu kowa, Allah sarki bawan Allah gaba ɗaya ya rame ya kare, baya iya chin komai sai dai ruwan da ake ta saka masa, yayi baki sosai kamar ba shiba


Karisawa bakin gadon dayake kwanche,hiyana tayi ta zauna a gefen sa kaɗan,  cikin sanyin murya tace "yaya Ahmad ya jiki, tayi maganar tana kallon face nashi, shima ita yake kallo, kumshe mata ido yayi ya sake budewa


Zubur hiyana ta miƙe tana faɗin "yaya Ahmad daman kana jin me muke faɗe?  Lumshe mata ido yayi san nan ya buɗe, komawa tayi a hankali kusa dashi ta zauna, shiru tayi na ɗan mintoci, tana tunani "da alama chiwon yaya Ahmad ɗin nan yayi kama dana shafun aljanu ko kuma sihiri, domin duk wata alama da suratul baƙara ta bayyana a matsayin shafin aljanu ko sihiri to ya bayyana a tare dashi, amma duk gidan nan ba wan da zaka faɗawa hakan ya ɗauki abun da mahimmanci, bari dai nayi nawa kokarin kawai mugani" juyo da blue eyes nata tayi kan face mashi,


A hankali ta fara motsa lallausan pink lips nata ta fara karanto suratul baƙara, domin rusatul bakara surache datake karya sihiri, duk girman sihiri zata karya shi, haka zalika surache mai ɗauke da maganin duk wata chuta da take duniyar nan, sai dai idan bakasan in da ayar warakar chutar ka takeba a chikin surar, matikar kana karanta suratul baƙara tofa aljanu ma ba zasu zo in da kake bama bare wani sihiri.


Tun hiyana na karatu a hankalin har tafara da ɗan karfi karfi, kamar daga sama taji wani tsawa, da murya mara daɗin ji,  nan take iska mai karfi ta taso a iya ɗakin kawai kuma, hakan ne yakara tabbatar wa da hiyana chewar lallai chiwon yaya Ahmad, asirine ko kuma aljanu, duk da iskan da ya taso a ɗakin da tsawar da akayi mata hakan bai hanata chigaba da karatun ba, sai ma kara ɗaga murya da tayi duk da a tsorache take.


Kamar yadda take kara saukin voice nata wajen karatun haka iskan ma ke kara yawaita, matso da ɗan karamin bakin ta tayi dai dai sai tin kunnen yaya Ahmad ta chigaba da karatun da ɗan karfi, 


Wani ƙara yaya Ahmad yayi da wata iriyar voice mara daɗin ji wadda yasa hiyana mikewa da gudu ta bar ɗakin, tana faɗin "na shiga uku na to wai daman me ya kaini gudu take sosai da sosai kamar zata tashi sama, tazo dai dai, wajen part ɗin yaya Aryan sukayi karo da Bgs, domin bata lura da mutun yana zuwaba kawai gudun cheton rai take, da karfi kanta ya bugu da kirjinsa tayi baya ta faɗi kasa, tana numfashi da kyar


Kafar sa ya ɗaga ya tsallake ta ya wuche ya shige part ɗin Aryan, ya barta zube a kasa


Da kyar hiyana ta iya mikewa tana jan kafa a hankali har ta shiga part ɗin Ammi.



Abangaren Bgs kuwa,


Awan nan karon ba ko sallama ya faɗa betroom ɗin Aryan, 

Aryan na kwanche saman katafaren gadon sa ya rufe gaba ɗaya jikin sa da blanket har fuska, chikin ɓachin rai Bgs ya shigo ɗakin Amma yana ganin yanayin da Aryan ke chiki hakan yasa ya manta da wani bachin rai ma ya nufi gadon da sauri.


Yaya blanket ɗin yayi ya zubawa Aryan green eyes nashi, fiskar nan tasa tayi fayau ya kara haske sosai, jin an yaye masa blanket din ne yasa ya waro idon sa a hankali, ya sauke su kan face ɗin Bgs


"Subhanallah Aryan meke damun ka? Baka da lfy ne? Idon ka na chiwone?" Bgs ya jero masa tambaya a ruɗe.


Dafa kafaɗar Bgs Aryan yayi yana kokarin mikewa da sauri Bgs yasa hannu ya tai maka masa ya miƙe zaune.


"Aryan what is wrong with U?" "Nothing bro Nothing kawai barchine" shiru Bgs ya ɗan yi kafin yace "ok to ina kaje tun da safe nazo nan two time baka nan, bayan kuma nasan babu in da kake zuwa, na kira layin ka akashe, ina kaje?" 

     "Yola naje mana" Aryan ya bashi amsa yana kwaɓe fuska.


"What? Yola kuma to me kajeyi a chan?"  "Wai dan Allah Bgs kai ɗan sanda ne da zaka sakani a gaba da tambayoyi, ko kuma ni yaron kane, pls my blood ka rabu dani ka rabu dani.


 ikon Allah Bgs dai green eyes nashi ya zubawa ɗan bakin Aryan yana ganin yadda yake zuba masifar,

     Ganin Bgs ya tsare sa da ido ne yasa ya ja tsaki ya juya ya zuro kafafun sa kasa yana kokarin sauka daga gadon.


"Kai ina zakaje kuma?  "

Wayyo Allah Ni Aryan na shiga uku wai dan Allah Bgs baa neman ka a London ne? ya kamata ka koma wlh ka addabeni pls ka rabu dani.


 Bgs daya ga abun na Aryan yana neman ya wuche gona da irin sai ya ɗaure fuska sosai chikin tsawa da bada umarni yace 

  

!!"Ina zakaje Aryan" Aryan ya gane me Bgs ke nufi wato zai nuna masa chewa ya fishi a shekaru kuma ya fishi awajen aiki dan sama yake dashi.


a kule yace "to ai nan ba wajen aiki bane gida ne, wai dan Allah Bgs bazaka barni naji da abun dake damuna ba so kake kasa zuchiya ta ta tarwatse ne? Ko so kake na mutu ka huta ko? So kake ka bugamin kwakwalwa tane? Pls my Oga ka kyale ni haka"


Tunani Bgs ya shigayi "tabbas ina bukatan in san menene matslan ɗan uwana domin bai taɓa mayar min da magana haka ba, kome zan masa kuwa, jikin sa yayi mugun sanyi a hankali ya zuro kafarsa kasa ya

Sauko daga gadon ya tako zuwa in da Aryan ke tsaye.


Hannu biyu ya ɗora saman kafadar Aryan chikin sanyin murya ya fara magana "ban san meke damun kaba Aryan kuma bazan sake tambayar ka meke damun kan ɗin ba, domin nasan kai ma baka sani ba idan kasani to bazaka ɓoyemin ba, amma tabbas kana da damuwa kadage da addu'a nima zan tayaka sosai, har Allah ya kawo maka sauki, amma yanzu dai ka faɗamin ina zakaje?


Rungume Bgs Aryan yayi yana faɗin "wajen Ammi zanje, daman tun da na dawo nake san zuwa wajen ta amma ɓachin rai ya hanani zuwa kuma bana soma naje wajen ta ina cikin bachin rai, dan kar zuchiya da sheɗan su zugani nayi ba dai dai ba, shiyasa kaga na kwnata ina jiran zuchiyata tayi sanyi"


Hannu ɗaya Bgs yasa yana ɗan bubbuga bayan Aryan ɗin kaman yaro yana faɗin "ok kaje ni kuma daman wajen Abba zanje ya kirani, yana son gani na, sai mun haɗu anjima" yana gaama fadin hakan ya saki Aryan ɗin ya juya ya nufi waje, bayansa Aryan ma yabi kusan tare suka fito, Bgs ya nufi fada Aryan kuma ya nufi part ɗin Ammi



Da sallama ya shiga betroom ɗin Ammi, kamar kullun tana zaune a bakin gadonta tana karatun qur'ani mai girma, karisa shigowa chikin ɗakin yayi dan yau bai tsaya jiran sai an bashi izinin bama, 


sama throw pillow, manya manyan dake tsakiyar ɗakin ya zauna, shiru yayi yana sauraron  karatun qur'ani suratul ma'ida, da Ammi ke rerawa


sai da ta kai aya sai nan ta rufe qur'ani ta ajiye a saman drawar gefen gadon, ta dawo da kallonta kan face nashi, chikin ni tsuwa tace "Aryan lfy dai ko? 

  Dogon numfashi yaja kafin yace "Ammi pls tell me ina kika kai yarinyar nan?


Aryan na faɗa maka ai na mai data gidan babanta. "No Ammi bata chan ai naje Yolan da safe wlh bata Chan


Wani dukan uku uku Ammi taji kirjin ta yayi tunani ta shigayi, "gaskiya dole naje nasamu mai martaba, lallai na yarda Son da Aryan kewa diyana ba son wasa bane, har yola yaje saboda ita, tab a lallai dole azo abashi matar sa wlh, dan ni nariga na bashi ita duniya da lahira.


Ganin ammi tayi shirune yasa Aryan yace "Ammi pls ni  na san ke mai Son muche baki son bachin ranmu dan Allah ki faɗamin inda take

  

"Aryan ban isa in faɗa maka in da diyana takeba kaje ka tambayi Abban ka kaji nima Umarnin sa nakebi, a sukwane Aryan ya miƙe yana faɗin "au daman Abba ne ya yasa aka ɓoyeta wlh yau sai ya fitomin da ita yana kai karshen maganar ya fice daga ɗakin chikin bachin rai. 


Kai tsaye fada ya nufa, yazo dai dai zai shiga fada sai ya tuno Abba na tare da Bgs dan haka sai ya juya kawai ya koma part nashi

No comments