Recent Updates

Duk Karfin Izzata Book 1 Paga 19

 


Episode 19*




Lafayar da Aunty farida ta kawo musu ta ɗauko, Aunty farida da kanta ta ɗaura mata baƙaramin kyau tayiba ga kitso guda biyu a gaban goshita, kamar wata amarya ga

lallenta ja da baki " wow my diyana kin haÉ—u iya haÉ—uwa yanzu muje wajen flowers É—in garÉ—ing muyi hotan koh zaifi kyau " to Aunty farida amma sai na É—aukoh takalmi a É—akin Ammi " ina takallamar dana kawo muku " aa shikam sai gobe zansa yanzu high heel nakeso " murmushi Aunty farida tayi tare da jan hannunta tana faÉ—in to muje " fitowa palon sukayi nan suka isko su Zahra suma sun sha kwalliya sosai sai dai su dukkansu hijabi suka'sa dan zuwa sallar idi " Aunty farida ina zakuje Zahra ta tambaya " hoto zamuje muyi a garding, ko zakuyine kuma " aa nikam banso chewar Zahra " to kufa tayi maganar tana nuna su lamrat "har suna haÉ—a baki wajen chewa aa bamusu " da kyar hiyana tamike dan sarawar da kanta ke mata tana faÉ—in Aunty farida muje kimana tare ni kam ina so " riko hannunta Aunty farida tayi dan yadda taga yanayinta kamar zata faÉ—i da kyarma take tafiya"  a harabar gidan suka tsaya san nan Aunty farida tace my diyana kije ki É—auko ta kalmar naki kinji, kiyi saurifa dan kinga hiyana bazata iya tsayuwa sosaiba " da sauri diyana ta juya tanufi bangaren Ammi " Shahram na ganin'su yazo wajen da sauri ya gaida Aunty farida san nan ya tambayeta ko fita zasuyi'ne ya kaisu " aa tace masa " juyawa yayi yakoma bakin gate " suna tsaye har diyana ta dawo kwas, kwas, kwas, take tafiya, a nitse take zuba takunta da yanga " daga nesa Aunty farida tafara É—aukarta video sai faÉ—in wow take, sai da ta iso kusa dasu tukun nan Aunty farida ta tsai da video, suka nufi chikin garding É—in " hotona sosai,  tamusu a tare san nan tawa diyana ita kaÉ—ai kala kala, bayan sun gamane suka nufi chikin gd Aunty farida na faÉ—in to my diyana sai kije ki É—aukoh hijabinki muje masallachi koh " to diyana tace tare da wucewa É“angaren Ammi " Aunty farida da hiyana kuma suka nufi É“angaren Ummi 


SAUDIA


Tsaye yake a gaban mirrow É—aure da towel a kugunsa da alama wanka yafito, yana shafa mayukan'sa masu kanshi da tsada' bayan ya gamane ya gyara gashin kansa ya sake feshe jikinsa da turare mai kanshi da tsada, trolley'sa ya jawo ya buÉ—e ya É—aukoh farar jallabiya, ya juya a jikinsa yayi kyau kamar balarabe,tsayuwa yayi a gaban mirrow yana kallan kansa,  wayarsa dake kan gado tayi kara alamar kira yashigo, a hankali yake takawa kamar yana tsoran taka kasar ya isa gaban gadan,hannu yasa ya É—auki wayar my blood ne ya bayyana a kan screen É—in wayar, da sauri yayi picking call É—in tare da manna wayar a kunnen'sa " hello " daga É—ayan É“angaren DON yace jirginmu zai sauka  9:30 dai dai "ok by the i will be they " thanks ya faÉ—a tare da katse kiran' Aryan zai ajiye wayar ke nan yaji tasake kara alamar shigowar sako, ganin my lovely Aunty yasa ya buÉ—e sakon,  

da sauri ya zauna a bakin gado tare ta kara waro ash eyes nashi a kan'wayar,Sosai yake kallan wayar kamar zai chinye,  wow dole Aunty farida ki ruÉ—e irin wan nan kyau haka,yarinya kamar wata aljana, yayi maganar yana manna wayar a kirjinsa, jinake kamar jibi yamin nisa jinake tamkar ranakun tsawo suke karawa, kusan 10 mnt yana zaune yana surutai, san nan a hankali ya miÆ™e yanufi hanyar fita,wayar na manne a kirjin'sa


Kai tsaye É—akin khalid ya nufa nan yasami Yusuf ma a chan dukkan'su sun shirya chikin fararen jallabiya bakaramin kyau sukayiba " muje koh lokachin sallama yakusa ae chewar Aryan" Khalid yace wai Aryan ina DON ne tun shekaran jiya nake tambayar'ka kakemin wani kauce kauce koh " nafaÉ—ama'ka Khalid yana nan kawai yaje chikin madina ne " lallai Aryan to karyan ma bai dace da kaiba, baka sabayi'ba shiyasa ma dakayi yanzu, karyan bata zauna ba " dogon tsaki Aryan yaja tare da faÉ—in inkun gama kusameni a masallachi nayi gaba tun da naga baku da niyar tafi, yana gama faÉ—in hakan yayi waje " kallan Yusuf dake zaune ya zuba musu ido Khalid yayi"muje koh " hmmmm kasan'me Khalid wlh DON baya kasar nan wani lokachi sai Aryan yarinÆ™a magana kamar ba tare muka tasoba ina da tabbachin DON yana London zai wani chemana yana madina shi ko karyan ma bai iyaba " kaga Yusuf kafita maganar Aryan da DON kazo mutafi masallachi kar murasa sallah, yakai karshen maganar yana nufar hanyar fita " mikewa Yusuf yayi yabi bayan'sa " suna fita waje suka samu gaba É—aya family sun haÉ—u amma banda Aryan " Khalid ina Aryan da Prince Ummi ta tambaya tana kallan fuskarsa " sunyi gaba Ummi " to muma ae sai muje koh dan kar lokachi yakure " tare suka jera dayake masallachi kusane da masaukin'su " suna isa suka rabu su Ammi sukayi É“angaren mata su Abba kuma sukayi É“angaren maza 



Nigeria


Zaune suke a palon Ummi diyana yau baÆ™i ya buÉ—u ta tasa fruits a gaba sai chi take " hiyana na rike da littafin addu'oe tana karatu " lamrat na game a waya Zahra " amrat na kallo a wayar Aunty farida " Zahra kuwa ta kwanta ta tada kai da chinyar Aunty farida sai hira suke kamar saannin juna " da sallama Aunty Maryam ta shigo palon " Aunty farida ta amsa mata fuska ba yabo ba fallasa " zama tayi a saman sofa mai zaman mutun 1 tare da faÉ—in, ina wuni Aunty farida anyi sallah lfy " lfu lau ykk "lfy Alhadulillah ta faÉ—i hakan tana mikewa " inakuma zakije kitsaya muci abinchin rana tare mana tun da lokachin yayi chewar Aunty farida " aa bana buÆ™ata a inda,na fitoma akoi abinchi dama dai kawai nabi dokar gd nanne nazo na gaisheki kuma namiki barka da sallah a matsayinki ta babba, SO no need na tsaya yin wani abun, tana gama faÉ—in hakan tayi waje " Allah ya shiryaki Maryam Allah yasa ki gane.. bata garisa maganar'ba sukaji diran manya manya motochi a gd " da fara'a Aunty farida ke faÉ—in oyoyo Aunty salma oyoyo Aunty mardiya" tun Aunty farida bata karisa magarba Zahra tamike a guje tayi waje, mikewa Aunty farida ma tayi tabi bayan Zahra suka bar su diyana a É—akin " hiyana ta dubisu diyana" kukam bazakuje kumusu oyoyo bane " ni kam bazanjeba dan bansan'suba kilama halinsu irin na Aunty Maryam ne chewar diyana" lamrat da amrat ma sukache muma bazanjeba " baki hiyana ta taÉ“e tana kallansu zata yi magana sai gasu Aunty farida sun shigo" Aunty farida rike da hannun Aunty Salma "Aunty mardiya rike da hannun Zahra da wani baby boy mai kyau dashi mai kama da yaya khalid,saman sofa suka zauna " da sauri hiyana tafara É—aga musu gaisuwa" wow Aunty farida wayan nan Æ´a'Æ´an larabawan fa kodai sune Æ´aÆ´a Abba da ya faÉ—amin yasamu wasu Æ´aÆ´a daga Allah Chewar Aunty salma " eh wlh salma sune " kai gaskiya bari Abba yadawo ya taimaka yabani wanchan da wan nan tayi maganar tana nuna hiyana da diyana " tab ae kuwa wayan nan yaran nan gani nan bari, inji Abba dan tun farkon zuwar'su nida mardiya mun roka ya hanamu " aa ae ni nace masa zanyi wlh har sai yabani " to Allah yaba da sa'a chewar Aunty farida " ameen Aunty salma ta amsa tare ta chewa ya su nanku É—aya bayan É—aya suka faÉ—a mata su nansu sai wow nice name kawai take faÉ—i " kutashi kuje kuyi wanka kuzo muchi abinchi " a tare Aunty mardiya da Aunty salma suka mike suka nufi dakinsu " inakuma zakuje Aunty farida ta jefo musu tambaya " É—akinmu mana " wani É—akin ae sai dai kuje É“angaren Ammi dan kuwa É—akinku yazama É—akin Yan mata'na har sai randa Ammi ta dawo zasu barmuku É—akin sukoma nasu " to ae danan da chan duk É—ayane badamuwa chewar Aunty mardiya tayi maganar tare da juyawa tanufi hanyar fita, bin bayanta Aunty salma ma tayi  " Auta ki kiramin masu aiki suzo ku shirya mana abinchi ina zuwa mikewa tayi tanufi É—akinta " Zahra kuma tasa hannu ta anshi wayar ta a hannun lamrat, tafara kiran layin binta, bugu binya ta É—aya Zahra tabata umarni tazo ta shirya abinchi tana gama faÉ—in hakan ta katse kuran tamikawa lamrat wayar


 

SAUDIA


abinchi sukechi chikin nitsuwa shiru palon babu mai magana " Abba me zai hana mutafi gobene dole sai jibine, Chewar Aryan "a sukwane DON ya É—ago yana kallan'sa, shi ko ajikinsa saima latsa wayar'sa yake " meyasa kakesan mutafi gobe Aryan kodai Æ™asa mai tsarkinne bakaso chewar Abba " aa Abba bawai bansan kasan bane wlh nagajine inasan inkoma gida " Khalid ya É—ago ya sachi kallan Yusuf sai murmushi suke " Aiman kuma ya kalli Khalid san nan yajuya ya kalli Yusuf yana girgiza kai a zuchiyar'sa yana faÉ—in muna fukai asirinku yakusa tonuwa ae idanma wani abu kuke shiryawa É—an uwana to kanku zai dawo " Ahmad kam abinchin'sa kawai yake chi hankalin'sa kwan'che " haidar ya matso kusa da Umar yafara masa magana katsa katsa anya yaya Aryan lafiyar'sa kuwa "umar ya É—ago kai zaiyi magana karaf idon'sa ya sauka chikin na Fahad dake gurga musu mugun kallo " to shike nan Aryan tun da haka kakeso kukira'su farida ku faÉ—amusu gobe zamu dawo chewar Abba yayi maganar tare da mikewa yanufi hanyar É—akin'sa " mikewa Ammi da Ummi sukayi sukabi bayan'sa "Aunty amarya kuma tamike tanufi nata É—akin " kallan Umar da haidar DON yayi yana faÉ—in me kukejira ae tun bai kai karshen maganar'ba suka mike suka nufi waje, dawo da green eyes nashi yayi kan Fahad, tun baiyi magana'ba Fahad yamiÆ™e shima yayi waje " green eyes nashi ya jubawa Aryan sosai yake kallansa" Aryan nasane da kallan da DON ke masa amma yaki É—ago kai dan bai da amsar tambayar da DON É—in zai masa " bazan sake tambayar meke damunka ba dan nalura kaima bakasan meke damun nakaba binchike mai kyau zanyi kawai a kan hakan " sai loakchin Aryan ya É—ago yana faÉ—in da ka taimakamin bro dan koba komai zaka daina tunanin chewa ina É“oyemaka wani abu " ajiyar zuchiya ya sauke san nan yamiÆ™e yana faÉ—in to sai kuje kushirya ae tunda komawa gobe yakamamu gashi yanzu kusan karfe 4, da É—ai É—ai suka miÆ™e suka bar palan 



Yola Nigeria


Inna tachi wankan ta tasa wata atampha da bappan, bubu ɗinka mata mayafi ta ɗauka tayi waje, kai tsaye gidan'su buba tanufa, da sallama tashiga gaba ɗayan'su suna tsakar gd " inna sannu da zuwa chewar buba" yauwa buba ya kafar taka " naji sauki ae yanzukam ina ɗab iya takawa batare da sandaba " to alhamdulillah Bappa ina wuni" bappa dattijon arjiki halinsa iri ɗaya da bello mutumin kirki yace lfy habiba anyi sallah lfy " lfy lau bappa inna larai mushiga daga chiki koh" inawuni inna chewar bello " yamutse fuska inna tayi kafin ta amsa da lfy, san nan tawuce ɗaki da sauri dan karma wani ya gaisheta, bello ma albarkachin bappa yana nanne shiyasa ta amsa gaisuwar" miƙewa innar buba tayi tabi bayan inna, innar bello dai dake zaune kan tabarma ta taɓe baki tai tana kallansu har suka shige ɗaki a zuchiyar'ta tana faɗin Allah ya kare mutun daga sharrinku dan kuwa wayan nan idan suka haɗu ko sheɗan suransu yake "


Lfy inna chewar innar buba" lfy ba lau'ba kinga anyi sallah yau yakamata gobe mukoma wajen malam koh dan asamu ayi aikin nan dawuri " aa to mezai hana muje yanzu chewar innar buba " to me zakice wa bappan buba idan zamu fita " aa ae yanzu zai fita dakin É—an tsaya kaÉ—an'ma bazaki samesa'ba yanzu dai mujira fitar'sa " to shike nan bari naje gd na É—aukoh kuÉ—in nadawo,bata jira amsar innar buba ba tayi waje " da sauri sauri ta shiga gd É—akinta tanufa tana shiga ta É—aga yar katifar chiyawar'ta ta É—auki kuÉ—in ta kirga sauran 5k ,ta juya tanufi waje, a dab da bakin kofa tayi karo da bappan buba zai fita, matsa masa tai tana faÉ—in Allah ya kiyaye hanya adawo lfy " amsawa yayi fiska bayabo ba fallasa yayi waje da sauri " ita kuma tayi chikin gd


Tare suka fito da innar buba sai sauri suke zubawa suka nufi hanyar kungurmin dajin nan tafiya mai tsawo sukayi, kafin su kai  wajen duwatsun chikin kogon suka shiga, zaune yake kan wata Æ™atuwar dutse ga tukunyar hayaki a gaba sa " da baya baya su inna suka karisa wajen dan dokar wajenne shiga da baya baya


 (ma'anar shiga da baya baya kuwa shine kajuyawa Allah baya kajuyawa alkibla baya kabar halak ka kama haram kabar Allah ke nan ka fiskanchi boka, ya Allah ka tsare mana imanin'mu ya Allah duk halin da zamu shiga ka tausaya mana kabarmu da imanin'mu) 


Kan wani jar shinfiÉ—a suka zauna, wani mahaukachin dariya bokan nasu yayi ha, ha, ha, san nan yace kuÉ—in da kika rike ko warware tsarin jikin'su bazai yiba bare har aje gamaga nagaba " to don Allah alagafarta malam.." ke dakata banace baa kiran su nan Allah a nan'ba ko ance maki aikin Allah muke a nan, sheÉ—an kawai zaki kira mana dan kuwa aikin'sa muke " kayi hakuri to kataima'kamin ina chikin damuwane idan yaran nan na raye " zan iya taimakawa na kunce tsarin dake jikinsu ke kuma sai kinemo kuÉ—in aikin daza'a amusu amma da sharaÉ—i " menene sharaÉ—in komanene zanyi" to farko dai ajiye kuÉ—in dakikazo dashi, na biyu kuma zaki bani kanki " to inna tace tare da ajiye kuÉ—in chikin wata kwarya, idon ta yarufe bataji bata gani" boka kuwa ganin inna ta aminche yasa ya umarchi innar buba da taje waje, ba musu ta tashi ta fice " nanfa boka yafara biyar bukatar'sa da inna sai dai abun da bata saniba shine ta baya bokan zai nemeta, ba karamin wahala ta shaba tayi ihun azaba shiko ko ajikinsa bukatar'sa kawai yake biya bayan sun gamane, ya umarce'ta da taje gd bayan kwana uku ta dawo " da kyar inna tamike tana hawaye, tanufi waje nan tasamu innar buba zaune a kan wani dutse " innar buba na ganinta ta mike da sauri tanufeta, tana faÉ—in sannu, jerawa sukayi suka nufi gida dan yamma tayi sosai " yanzu shike nan zai mana aikin chewar innar buba" aa wan nan abun damukayi iya warware tsarin jikinsu kawai zaiyi nikuma sai nasamo kuÉ—in aiki " to yanzu ae na zaki samo kuÉ—in " nima wlh ban saniba amma koma sata zanyi wlh sai na nemo kuÉ—in " to shike nan amma nawa yace maki kuÉ—in aikin " 15k yace " tab lallai to Allah dai ya dafa'mana 


(nikoh nace aikin Allah kukene dazakuce Allah ya dafa muku)

inna sai É—ingisa kafa take har suka isa, inna tayi gidanta innar buba ma tayi gida


KANO



Misalin karfe 8 na dare zaune suke a kan table É—in chin abinchi, Aunty farida ta É—ago tana kallansu tafara magana " Abba yakirani É—azun yasanar dani gobe damisalin karfe 5 na yamma jinginsu zai sauka a airport" chike da murna Aunty mardiya ke faÉ—in alhadulillah alhadulillah " ae chanake sai jibi zasu dawo Koh chewar Aunty salma" eh daman dawowar'su jibi ne bansan meyasa Abba yace sudawo gobeba Aunty farida tabata amsa tana kokarin goge bakinta  " to kunga yakamata muje mu kwanta dawuri dan mutashi dawuri saboda aiki  shirye shiryen chewar Aunty Salma " eh hakane yanzu mardiya keda salma kutafi bangaren Ammi nikuma zamuwuce nida sister's É—inna kamar yadda muka saba, kutashi muje my diyana " ba musu suka mike gaba É—ayan'su sunai'wa juna sai dasafe 


Washe gari tun da sukayi sallar asuba basu mai da barchiba "Aunty farida ta shirya ta tsab chikin a tanfa mai tsadar gaske blue colour wuyarta da hannunta shaÆ™e yake da manya manya gwala gwala mai kyau da tsada tayi simple make up, plat shoe baki tasa da mayafi baki wayar'ta da ATM kawai ta É—auka tayo waje, a palo tasamu su diyana" diyana sarkin kwalliya kullun tana chikin kwalliya tana saye da doguwar riga ash colour tayi rolling gyalen rigar a kanta, tayi kyau sosai " Aunty farida ina zakije diyana ta tambaya" shopping zanje kozaki rakanine " eh zanje" to duk wadda zataje tazo muje " diyana da lamrat ne  suka mike, suka nufi Aunty farida" Aunty farida na ganin hakan ta juya tayi waje, suka bi bayanta yau ma dai kamar kullun Shahram ne ya jasu da matsakai'chin gudu yafita gidan 


Sai karfe 4:30 su Aunty farida suka dawo, su Aunty mardiya gaba É—ayan'su sunyi kwalliya sunyi shirin tarban'su Abba " a gurguje Aunty farida ta tanufi É—aki dan yin waka itama tana faÉ—in my diyana kuyi sauri ku shirya kuma, tana gama faÉ—in haka tayi É—akinta "É—akin Aunty mardiya diyana da lamrat suka nufa a gurguje sukayi waka dan kar a tafi tarban'su Abba a barsu, diyana dai duk saurin datake sai da ta tsaya tayi make up" gida yachika da jama'a sosai karfe 5:10 dankara dankaran motochi masu numfashine suka jero guda 20 "guda 5 suka fito daga gidan Abba suka tadda 15  afarfajiyar babban get jerawa sukayi suna sharara gudu dan sunyi latti da 10 mnt, gudu suke shararawa sosai chikin Æ™anÆ™anin lokachi suka isa airport, lokachin har jirginsu Abba ya sauÆ™a sai dai basu fara fitowaba, 


Fitowa daga motachin, su Aunty farida sukayi suka jingina da jikin motar suna jiran fitowar su Abba gaba É—ayan'su,  sun kurawa jirgin ido 

Abba ne yafa saukoh wa a nitse yake takawa Aunty amarya na biye dashi sai Ummi da Ammi a baya " da gudu Aunty mardiya tayi wajen Abba ta rungumesa ita kuma Aunty salma wajen Ummi tanufa, Aunty Maryam kuwa wajen Aunty amarya tanufa, su diyana kam wajen Ammi suka nufa suka rungumeta itama rungumesu tayi tana hawaye " Aunty farida kam tana tsaye jikin mota ko motsawa batayi'ba 

Rike yake trolley a hannunsa yana taku irin na jaruman maza ya saukoh daga jirgin sanye yake da jeans da t-shirt bakake yasa p-cap baki, fiskar nan kafar an aiko masa da mutuwa,Aryan na biye dashi a baya shigarsu ma iri É—ayane  basubi ta kan kowaba sukanufi wajen da motochin ke tsaye," da sauri security dake tsaye a awajen ya buÉ—e masu kofar É—aya daga chikin motochin san nan ya anshi trolley hannunsu, " Aunty farida naganinsu tayi gunsu da sauri " DON zai shiga motar ganin Aunty farida na zuwa sai ya É—an dakata ya juyo tare da buÉ—e mata hannu, da sauri tafaÉ—a jikinsa, tana faÉ—in Wellcome my blood " rungumeta  yayi yana faÉ—in mun sameki lfy"sakin'sa tayi ta juya ta rungume Aryan dake tsaye tana faÉ—in, lfy ya hanya " nayi kewarki lovely Aunty chewar Aryan " nima nayi kewarku sosai wlh ta karisa maganar tana sakin Aryan, 

Chikin motar suka shiga gaba ɗayansu ukun, sukasa Aunty farida a tsakiya " DON yabawa driver umarnin yawuche dasu gd " ba musu driver yata da motar da ma tsakaichin gudu yabar airport ɗin " mamakine yakama Abba har yake faɗin kai Allah ya shiryamin Safras da Aryan da farida, wato ita farida tunda taga yan uwanta shike nan batada wata damuwa to Allah ya kara haɗamin kanku, Amin dukkan jama'ar wajen suka amsa dashi san nan suka ranƙaya gaba ɗayan'su suka shiga motochin lokachin har anfara kiraye kirayen sallar mangariba,

A jere kuma a nitse motochin suka bar airport É—in suka miki titin gida 

A dai dai bakin katafaren babban gate motochin suka rage gudun nan take security suka wage musu gate É—in, suka kutsa chikin gd, 15 daga chikin motochin sukayi parking a harabar wajen 4 daga chiki kuma suka kusa garamin gate suka shiga chikin gd gaba É—aya,kai tsaye parking space sukanufa " suna kashi motochin da sauri security suka fito suna bubbuÉ—e kofar motochin " Su Abba suka fito, Abba ya dubesu yana faÉ—in kuyi sauri kuyi alwala gashi har za'a tada sallah, yana gama faÉ—in haka yajuya yayi É“angaren'sa da sauri " Ammi ma É“angaren'ta tanufa rike da hannun amrat da lamrat dayana  hiyana da Zahra na biye da ita a baya " Ummi kuwa rungume da salma tana rike da Aunty mardiya da É—ayan hannun'ta suka shiga É“angaren'ta "Aunty amarya rike da hannun, Aunty Maryam suma suka nufi nasu É“an garen" su Khalid kuwa kowa yanufi nasa É—akin 


Ammi nashiga palo ta saki hannun'su tana faÉ—in kuyi sauri kuyi alwala koyi Sallah sai muje palon Abba mu gaisa koh tana gama faÉ—in haka ta nufi hanyar É—akin'ta  suma kowa tayi É—akinta hiyana diyana dakuma Zahra suka nufi É—akinsu, Amrat da lamrat ma sukayi nasu É—akin 


Bayan sunyi sallah sungamane gaba É—ayan'su suka nufi palon Abba already Ammi tariga da tatafi chan " da sallama suka shiga gaba É—aya family suna zazzaune kan table É—in chin, abinchi ido kowa ya É—aga yana kallan'su banda DON dayake duke yake latsa wayar'sa " a hankali Aryan ya dago ash eyes nashi yana kallanta still dai da light make up face É—in ta É—an karamin bakin nan yasha lips'gloss, kasa É—auke kansa yayi daga kallanta sosai ya zuba mata ido sai taunan chingom take " yusuf ne ya dawo dashi hayyachin'sa dacewa oyoyo my baby ku karaso mana, wajen table É—in suka karisa gaba É—aya ba wanda ya lura da chiwon goshin hiyana dan dasafe anchire mata ban dejin

Zama sukayi " Aunty farida tabawa masu aiki umarnin su zuba musu ferfesu kayan chikin SA da chips " sannu da dawowa Abba ya hanya chewar hiyana " Ammi tace kibari mana sai angama chin abinchi sai ayi gaishe gaishen Koh " aa Aisha karki takurawa Æ´a'Æ´ana yayi maganar yana kallan Ammi, dawo da kallansa yayi kan hiyana lfy ya..... Bai karisaba maganar ba idonsa daya sauka kan goshinta, subhanallah hiyana meyasameki a goshi haka a razane yayi maganar " gaba É—aya idon mutanen palon yadawo kanta har shi kanshi DON sai daya É—ago kai dan jin yadda Abba yayi maganar " sunkuyar da kanta kasa tayi tana wasa da yan yatsun hannunta," Abba faduw... Bata karisaba tajiyo," diyana na faÉ—in Aunty Maryam che tamana bugun mutu har sai da aka kaimu asibiti " nan take ido jama'ar palon yadawo kan diyana lbr tashiga basu dalla dalla kamar antam bayeta" what? Abba yafada yana mikewa " shiru palon yayi ba mai magana, Abba zai sake  magana ke nan sai sukaji sallama a bakin kofar palon, amsa sallamar Abba yayi tare da faÉ—in shigo mana " É—aya daga chikin security ne kasa ya duka yana faÉ—in yallaboi kana da baki a waje " ok nasan da zuwan'su gani nan zuwa yana gama faÉ—in hakan yakama hanyar fita " Abba nafita Ummi ta dubi Aunty Maryam dake zaune hankalinta kwanche tace haba maryam me yaran nan suka miki zaki musu irin wan nan bugun " dogon tsaki Aunty Maryam taja san nan ta É—ora dacewa na tsanesu ne shiyasa na bugesu ko zaki rama musune" gaba É—aya palon kallon Aunty Maryam suke " me yasa kika tsanesu Maryam, laifinme suka miki Ammi ta tambaya a nitse " ke Aisha badake nakeba banzo kankiba tu kun nan tsanar dana ke mikine ae tasha fesu " a fusache DON ya mike ya É—aga yasu biyar zai zabga mata mari green eyes nashi ya sauÆ™a chikin na Aryan dake zaune ya zuba musu...✍️✍️

No comments