Recent Updates

Duk Karfin Izzata Book 1 Paga 18

 


Episode 18*

Hannu Aunty Maryam ta É—aga, har zata kai mata mari sai kuma ta dakata " zuba mata ido Aunty farida tayi sosai," me ya dakatar dake kimare'ni mana, ae kin girmane shiyasa har kike tunanin ramawa, kimare'ni nace koh tayi maganar a fusache" dan Allah Aunty farida kifita a É—akin nan "hmmmm wlh

Maryam bansan baki da hankaliba sai wan 'nan  karan,to kisani idan su Abba suka dawo kinemi abun da zaki kare kanki,dan kuwa babu wanda zaiga abun da kika'wa yaran nan ya kyale'ki, naso hukun taki da kai na, amma zan bari,  Æ´a'Æ´ayn Aisha dakike ikrari su hukuntaki, dan awan nan gaÉ“ar su kikataÉ“a, "tana kaiwa nan tamike tafice daga É—akin " ganin Aunty farida tafita, yasa  Aunty Maryam, tayi kwafa  tana faÉ—in to inaruwan'ki inba shisshigiba duk chikin Æ´a'Æ´an Aisha akoi wanda ya isa yamin hukunci'ne, yara kuma na buga innasake samun dama'ma bugun zanyi, dan nayi alkawarin rabasu da gidan nan tunda Aunty amarya bata san'su, juyawa tai ta gyara kwanchiyar sai surutai take


Da sallama ta dawo palon Ummi, duk datasan ba kowa, kai tsaye É—akin'ta tawuce, tasamu diyana da amrat sunyi barchi ,"kayan jikin'ta ta chire san nan nufi toilet, after 45 mnt tafi É—aure da towel da'alama wanka tayi, trolley ta tajawo, ta buÉ—e ta É—auki kayan barchi, masu kyau da tsada farare tas masu laushin gaske, sai kamshi kayan keyi yasha turarukkan maiduguri,san nan ta É—auko mayukan'ta masu kanshi da tsada sai dataÉ“i ko'ina na jikinta ta shafeshi da mai san nan,tasanya kayan barchi  ta'sake feshe jikinta da turare sai kamshi take kamar anyi É“arin turare a jikinta, "ta mai da mai da tureren chikin trolley É—in ta rufe ta mai'dashi wajen zamansa, tadawo kan gadon ta gyarawa amrat kwan chiya, san nan ta kwanta a gefensu, tare dayin adduar barchi asuba ta gari 



Yau yakama Wednesday tun safe Aunty farida ta shirya chikin tsadaddiyar lace mai Bala'i kyau baki, da ratsin ja ta zuba sarkan gold a wuya da hannunta, ta jera wasu tsadaddun zobuna uku na gold a hannunta, tayi simple make up bakaramin kyau tayiba sai kamshi take zubawa kamar anyi É“arin turare ajikinta, tasa plat shoe ja da mayafi ja san nan  tayiwa yan matan Ammi kwalliya sosai, "diyana hiyana Zahra tasasu sukasa wani haÉ—aÉ—É—en duguwar riga mai kyan gaske, da pink colour an masa kwalliya da wasu duwatsu golden colour, bakaramin kyau sukayiba amrat da lamrat kuwa sun sa wandon jeans baki da yellow t-shirt," gaba É—ayan'su ta É—aure musu gashin nasu a tsakiyar kai ta zuba musu jelar  a baya, sai dai ita hiyana har yanzu ba a chire bandejin dake goshinta'ba "Aunty farida ina zamuje kika mana kwalliya haka diyana ta tambaya tana kokarin gyara mayafin rigar" wajen lalle da gyaranjiki zan kai ku,  da naso namuku lalle da kaina to amma nayi tu nanin gara na kai'ku ae muku har da gyaran jiki " tsalle diyana tayi ta rungume Aunty farida tana faÉ—in mungode sosai" to sakeni mutafi kar lokachi ya kure mana " to diyana tafaÉ—i tare da sakin Aunty farida" rike hannunta Aunty farida tayi sukayi gaba, su Zahra suka rufa musu baya,

  suna fita harabar gd da gudu Shahram  yanufo'su " É—an dukar da kai yayi ya gaishe da Aunty farida chikin harchen turanci" bayan yagama gaishe da Aunty farida,su Zahra ma suka gaidashi " bayan yagama amsa gaisuwar'su Zahra ne, ya tambayi Aunty farida ko zai iya kaisu inda zasuje da kanshi " Aunty farida tace badamuwa ya fito da family car dan tafisan sutafi dukkan'su a mota É—aya " da gudu yajuya yanufi parking space na gidan," har gabansu yazo yayi parking,"zai fito yabuÉ—e'musu " Aunty farida ta É—aga masa hannu, alamar yabari zasu É“uÉ—e da kansu " da Kanta tasa hannu ta buÉ—e kofar motar," a nitse suka fara shiga sai da suka gama shiga san nan tabi bayansu " da gudu gaske Shahram yaja motar yana zuwa bakin gate ya É—an rage gudun motar nan'take securitys dake wajen suka wangale masa gate É—in da'gudu ya danna hanchin motar waje, gudu sosai, Shahram ke shararawa a kan mikakkiyar titi " ranki ya daÉ—e ina muka nufa yayi tambayar yana kokarin fita daga asalin babban gate É—in gidan " A&S muka nufa tabashi amsa ta kokarin picking call É—in daya shigo wayarta " miÆ™ar hanya Shahram yayi sosai yake sharara gudu 

Yana hawa kan titi dazata sadashi da gate É—in A&S ya rage gudun motar,horn É—aya yayi wani dattijo ya taso ya  wangale masu gate É—in da'alama shine mai gaÉ—in " A nitse Shahram ya danna hanchin motar chiki, parking space na wajen yanufa yana kashe motar  yafito da sauri ya buÉ—ewa Aunty farida" a hankali ta zuro kafafunta waje ta fito "su hiyana ma sukabi bayanta hannu diyana tariÆ™e suka nufi chiki " wani haÉ—adÉ—en wajen gyaran jikine da lalle da kitso, wajen ya tsaru sosai iya matane kaÉ—ai ke shiga koka'kawo wani naka sai dai katsaya awajen zaman baki, suna da ma aikata sosai inkaje basai kabi layiba, " hannu bibbiyu a ka tarbi su Aunty farida " chikin Æ™ankanin lokachi aka fara gyara musu jiki



YOLA



Da gudu inna tafito daga É—aki, tayi kichin, da sauri ta sauke tukunyar É—umamen, dake kan wutar abinchin har  yayi bakin'kirin, zama tayi dirshan awajen kamar zatayi kuka tafara surutai,"oh ni habiba yanzu me zanchi wayyo Allah gashi ba azumi nake ba dole naje nasake É—aukar 1k a chikin kuÉ—in nan na sawo masara nazo na surfa na niÆ™a nayi wani tuwon,  mikewa tayi ta jawo itacen wutar ta kashe san nan ta wuche É—aki ta É—aga katifar chiyawar'ta ta irga kuÉ—in taga saura 6k ta zari 1k ta mai da sauran kasan katifar ta É—au mayafinta tafuto tanufi waje dan zuwa yin chefene


KANO


A bangaren'su Aunty farida kuwa sai gyaranjiki ake musu an gama yiwa diyana da zahra da amrat bakaramin kyau sukayiba, kamar wasu larabawa haka suka zama daman, dukkansu fararene tas jikinsu sai kyalli yake gwanin ban sha'awa, 

yanzu aka fara yiwa lamrat da hiyana kuma,"Aunty farida kam already tariga da tayi nata a Maiduguri kafin tazo, " yanzu lalle  za'afara yiwa diyana da zahra " sai zolayar'su Aunty farida keyi " my diyana kingan'ki kuwa kamar wata sarauniyar kyau fa kinga fatar nan taki kuwa saikace na jariri gaskiya dole..bata karisaba,  wayar'ta tafara Æ™ara  alamar shigowar Æ™ira da sauri ta chiro wayar kiran iphone 14 daga jakarta " laaa Aunty farida yaushe kika chanza waya chewar diyana " last week tayi maganar tana kokarin picking call É—in " hello my bro ykk "lfy lau my lovely Aunty ykk y gd " lfy lau alhamdulillah gamu nan ma awajen gyaran jiki ae ina Prince " baya nan yayi tafiyar sirri " murmushi tayi kafin tace kai Aryan dayayi tafiyar sirri nasan yace karka faÉ—awa kowa, shine  kuma kafaÉ—amin  " murmushi kaÉ—an shima ma yayi san nan yace ae ke da kankima sirrinmu'ce ko bazamu faÉ—awa kowaba yazama dole ke kisani, " inasu Khalid to " suntafi kasuwa " to yau kuma da kansu sukaje kasuwar " eh wlh nima dai na É—anyi mamaki " kodai Zahra yaje yiwa tsaraba " to waya sanin musu zaki gane kan Khalid da Yusuf ne " to shike nan bari innakima gd mayi magana " ok ya'jikin yaran nan " da sauki sosai gasu nan ma ana musu lalle " lalle kuma ya tambaya yana taÉ“e baki " eh lalle mana kona baku ku gaisane " eh to dai kibari sai kun koma gd zaifi tunda yanzu kince lalle ake musu " ok to shike nan sai munyi waya," ta karisa maganar tana chire wayar daga kunnen'ta " katse kiran tayi tamaida wayar chikin jaka san nan ta É—ago tana kallan'su diyana da akewa lalle " wow my sister's kunganku kuwa kaman wasu amare gaskiaya idan Ammi suka dawo bazasu gane kuba wow " diyana dai baki yaki rufuwa sai murmushi take " Zahra kuma hannu tasa ta rufe fuska tana dariya " bayan angama yiwa Zahra da diyana lalle " aka fara yiwa amrat da lamrat 


SAUDIA


Ammi che kwanche a kan chiyar Abba a É—akinsu tana shafa fuskar'sa yayinda shikuma yake shafa gashin kanta " ranka yadaÉ—e nayi kewar yanmata'na sosai, " hannu Abba yasa yaÉ—an ja dogon hanchin nan nata yana faÉ—in to kwana nawa yarage mukoma, É—azun ma munyi waya da farida take chimin zasuje wajen gyaran jiki " Allah sarki feeda baiwar Allah, Allah yamata albarka na mata adduar samun aihuwa sosai jiya danaje masallaci " kullun sainayiwa farida adduar bama ita kaÉ—aiba har da maryam da mardiya ba garama faridan tasamu É—aya ba sauran kam aiko É—ayan basu samuba,chewar Abba " wlh tausayi suke bani tayi maganar tana kokarin mikewa " da sauri Abba ya rikota yana faÉ—in ina zakije kuma " so nake naje nayi magana da yaron nan " kallan chikin kwayar idonta sosai Abba yayi san nan yace wani yaro kuma, da gangan yamata tabayar, dan yanasan yau yaji takira sunan Safras da bakinta " yaron Ummin nan mana tabashi amsa tana mai kawar da kai gefe " to shi yaron bai da sunane " juyo da kallan'ta tayi kansa san nan tasa hannu taja gemunsa chikin wasa take faÉ—in, bazadai kaji su nan a baki'naba " murmushi yayi yana faÉ—in to idan inasan inji kumafa " sai na kira maka mana ae duk abun da kakeso matikar bai saÉ“awa Allah da manzon'saba dole namaka " rungumeta Abba yayi chikin farinchiki yafara magana ina kaunarki Aisha'ta nima bazan saki yin abun da baki so ba, tunda ba kyasan kiran su nan bazan saki kiraba aje a yaron kinji " chusa kanta tayi kirjin'sa tana faÉ—in nima ae ina kaunarka sosaima " nasani Aisha nasan kina kauna'na sosai nasani wlh " to shike nan kamin izzini naje na dubo'shi dan jiya banganshi'ba kwata kwata kuma inasan magana dashi a kan yaran nan " aa Aish ba yanzuba dan yanzu bansan ki raba jikinki danawa kibari sai anjima " to kawai Ammi tace takara shigewa jikinsa ta lafe 


Da sallama Khalid da Yusuf suka shigo palon hannun'su É—auke da manya manyan jakun'kunar sayayya Aiman da Ahmad dake zaune saman Sofa suka amsa sallamar suna binsu da kallo " daga ina kuke haka Aiman ya tambaya yana É—aure fuska " to dakake É—aure mana fuska, saiyasa muji tsoranka mufaÉ—a'maka  inda mukaje ne chewar Khalid " dariya Ahmad yayi yana faÉ—in nidai babu ruwana " tsaki Khalid yaja yawuce yanufi hanyar É—akin'sa " da sauri Yusuf ma yabi bayansa " miÆ™ewa Aiman yayi yana faÉ—in lokachi yayi da zan gano mekuke kullawa kuma sai nayi maganin'ku " Ahmad kam binsa kawai yake da ido har yafice daga palon ,yana ganin Aiman yafita " ya kwashe da dariya, chikin dariya yake magana wlh nidai nawa ido kawai zanga wan nan game É—in yasake kwashewa da dariya yana mai kwanchiya a kan kujerar 



NIGERIA


Sai milalin karfe 4:50 aka gama yiwasu hiyana gyaran jiki da lalle sunyi kyau sosai kamar su'sukayi kansu yaran nan gawani kitso guda biyu da aka musu a gefe da gefen kunnen'su ansa manya manyan bit an zuboshi ta gaba har kan chikinsu tsawon gashin, sauran gashin an É—aure musu a tsakiyar kai,anzuba jelar gashin ta baya har gadan bayan'su,  musammanba hiyana da diyana gashinsu yafi tsawo da baki ga tsantsi, ba karamin kyau sukayiba kamar, Æ´a'Æ´an larabawa " bill akayiwa Aunty farida ta biya san nan suka nufi waje " 

Shahram dake zaune chikin mota,yana ganinsu ya fito da sauri yana faÉ—in wellcome ma " da murmushi a fuskarta  tace sorry Shahram for keeping U waiting  " buÉ—emusu kofar motar kawai yayi batare daya sake maganaba, suna shiga yarufe motar yashiga gaba yabawa motar wuta sai bakin gate mai gaÉ—in ya wangale masa gate É—in ya danna hanchin motar waje da gudun gaske ya miÆ™i titi, gudu yake shararawa sosai,  sai daya kusa isa bakin babban gate na gida tukun ya É—an ragewa motar gudu horn É—aya yayi nan take security suka wangale masa gate É—in a nitse ya kutsa chikin gidan,  kai tsaye parking space yanufa ," yana kashe motar yafito da sauri ya buÉ—e musu " fitowa sukayi gaba É—ayan'su suna faÉ—in thank U uncle " Aunty farida ta rike hannun diyana sukayi chikin gd " da sallama suka shigo palon " da sauri nurse nasu dake zaune saman Sofa tamike tana faÉ—in ina kukaje natashi barchi ban gankuba, " wajen gyaran jiki mukaje diyana tabata amsa " dukawa tayi kasa ta gaida Aunty farida " da fara'a ta amsa san nan tanufi É—aki dan yin wanka tana faÉ—in sister's kuje kuyi wanka kozo kubiya bashin sallar Azhar da la asar dake kanku " har suna haÉ—a baki wajen chewa to san nan suka nufi É—akin Aunty mardiya 



 yau  saura kwana É—aya sallah sai shirye shiryen tarban su Abba ake, manya manya shanu 4 aka'yanka da raguna 5  " hayar masu soya nama Aunty farida ta É—aukoh mata'ne masu jini ajiki masu ji da karfi da lfy,  san nan tasa aka fitar da manya manyan gas daga store, aiki ake babu kama hannun yaro ,gamasu yin chin chin a gefe, gamasu donut dubula alkaki da dai sauransu, Aunty farida yau bata zauna ba sai hidima take da jama'a " Aunty Maryam kuwa tana É—aki kwanche abunta


Misalin karfe 1:50 diyana na zaune a É—akin Aunty farida tadage sai make up take,  wayar Aunty farida dake kan gado yafara ringing," da sauri ta ajiye jan bakin dake hannuta tanufi wayar, É—aukar wayar tayi zatayi waje dan takaiwa Aunty faridan, sai taga pic na Aryan ne ya bayyana a kan screen É—in wayar, sanye yake da kayan sojoji baÆ™aramin kyau yayiba fuskar nan tashi kamar bai taÉ“a sanin me dariya'ba," da sauri tayi picking call É—in " daga É—ayan É“angaren Aryan yace,"hello my lovely Aunty " ba itabace yaya Aryan ni che ina wuni " lfy lau y jikin naki " nasamu sauki hiyana che kawai tarage bata samu sauki'ba " subhanallah me ke damunta ina nurse naku " nurse ta koma jiya wai zataje tayi shirye shirye sallah " to meke damun hiyanar " chiwon kai da jiri " ok jibi zamu dawo ae sai na dubata amma duk da haka zansa a kawo mata magani " to bari na kaiwa Aunty farida wayar " daman kinsan zaki kai mata wayar'ne kikayi picking call É—in " eh ae nayine daman dan na gaisheka tun da mun daÉ—e bamuyi magana'ba " to ae kece kika manta dani shiyasa " dariya diyana ta É—anyi kafin tace, ni ban manta da kaiba dan bani da waya'ne Allah dana kiraka " wani ajiyar zuchiya ya sauke"to amma kina kewata kuwa " eh mana ina kewar'ku dukkan'ku " ok to shike nan ki ajiye wayar kawai anjima idan Aunty farida tazo ta kirani dan naji Abba na nemana " to kawai tace tare da chire wayar a kunnen'ta ta mayar kan gadan ta ajiye,"takoma gaban mirro tachigaba da kwalliyar'ta 



YOLA


Inna na É—aki kwanche a kan yar gadon chiyawar'ta taji sallama daga kofar gd mikewa tayi daga kwanchiyar datake tana amsa sallamar,"É—aukar mayafinta tayi tanufi waje " ganin bello ne ke sallamar yasa inna ta É—aure fuska sosai tafara magana to yau kuma dame kazo funafiki " ina wuni inna " daban wuniba zaka ganni'ne " to Allah yabaki hakuri daman naga gobe sallane shine nache bari na sauke hakkin ma kwabtaka na kawo miki wan nan,"yayi maganar tare da ajiye wa inna gaji guda uku a gaban'ta, batare daya jira amsar'taba yayi wuce warsa gidan'su " da mamaki inna ke kallansa har yashiga gida, duÆ™awa tayi ta É—auki kajin tayi chikin gida," a tsakar gida ta ajiyesu san nan ta É—aukoh wuÆ™a tayanke igiyar da aka haÉ—esu aka É—aure, ta samu wani igiya ta É—auresu É—ai É—ai ta kaisu kichin tafito takoma É—aki ta kwanta," tana kwanchiya babu jimawa buba yashigo gidan da sallama yana É—ingisa kafa da sanda " tana daga chikin É—aki ta amsa masa san nan tace yashigo " shiga É—akin yayi hannunsa riÆ™e da buhu  " lfy buba ina zakaje da buhun nan " bappa'ne yace na kawo miki, shin kaface wai kiyi girkin sallah " da murna inna tamike zaune wayyo Allah kacewa bappa ngd sosai Allah yaÆ™ara arziÆ™i " amin yafaÉ—a tare da ajiye mata buhun ya juya yafita " buÉ—e buhun tayi taga shin kaface mai kyau da murna ta tura buhun bayan kyaure ta É“uye 


KANO


Misalin karfe 7 na dare, sun haÉ—u a palon Abba suna buÉ—a baki " kai my diyana sarkin san kwalliya chewar Aunty farida tayi magabar tana É—an jan kumatun,diyanar " ae kwalliyar dazanyi gobema sai yafi wan nan kyau " Allah ko ae haka akesan mace takasan'ce mai tsabta da kwalliya " Zahra tace Aunty farida ae muma munayi " eh kunayi amma my diyana tafikuyi sosai, kuma kuÆ™ara dagewa " to shike nan zamu rinÆ™ayi sosai " ok to kuchi abinchin'ku dawuri muje mu kwanta dan kunga gobe sallah zamu tashi da wuri " har suna haÉ—a baki wajen chewa toh " shiru kakejin palon babu mai magana sai paran spoon kawai zakaji " sallama sukaji anyi a bakin kofar palon " amsa sallamar Aunty farida tayi san nan taba da izinin shigowa " É—aya daga chikin security bakin gate ne,har Æ™atsa ya duÆ™a ya gaida Aunty farida " ta amsa tare da tambayar'sa ko lfy " eh lfy wani likitane yakawo saÆ™on nan wai inji oga yace abawa hiyana " ok to ajiye a saman table É—in gaban kan nan " mikewa yayi ya ajiye sakon san nan yanufi waje 

Bayan sun gama chin abinchine suka mike zasu tafi É—aki, Aunty farida tasa hannu ta É—auki sakon tana faÉ—in muje É—aki kisha maganin hiyana " toh kawai hiyana tace, san nan suka nufi waje  " sai da Aunty farida ta tabbatar hiyana tasha magani san nan takama hannun diyana da amrat suka nufi,dakinta, a gurguje sukayi wanke sukayi sallar issha suka kwanta asuba tagari 


Tunda sukayi sallar asuba yau basu mai da barchiba " diyana tun karfe 7 take gaban mirro ta goga wan nan ta fenta wan nan ba karya tayi kyau sosai tamkar zataje gasar sarauniyar kyau " da sallama Aunty farida tashigo É—akin tana waya da Aryan, wow my diyana kin ganki kuwa kamar wata sarauniya " dariya diyana tayi tana faÉ—in ngd Aunty farida " dawa kike magana kuma Aryan ya tambaya " hmm nina mantama muna waya wlh, kyan my diyana ne ya rikitani " shiru ya É—anyi kamar mai tunani chan kuma sai yace to É—auke'ta hoto ki turomin naga kyan daya rikitakin " ae kuwa kai ma idan kagani sai ka rikiche " to shike nan turomin É—in dai kekam " ok tace tare da chire wayar daga kunnen'ta ta katse kiran" tadubi diyana tace to tashi kisa kaya namiki hoto " yauwa Aunty farida Allah yamiki albarka daman inasan inje in anshi wayar Aunty Zahra  nazo nayi hotan, tayi maganar tana kokarin mikewa..✍️

No comments