Recent Updates

Duk Karfin Izzata Book 1 Paga 16

 


Episode 16*





Idanta ya sauka, a kan shahram dake tsaye fuskar nan tamkar an aiko masa da mutuwa babu alamar wasa a tattare dashi " sakin

diyana,  tayi tana mai da nunfashi " karisa shigowa É—akin yayi yana faÉ—in get out yayi maganar yana nuna Aunty Maryam " kallan raini ta tsaya take masa daga sama har katsa dogon tsaki taja,  tanunashi da É—an ya tsa tace kai karamin marakunya ni kake chewa nafita to kashirya karÉ“an hukunchi " shikam Shahram ko ajikinsa, dan daman bajin hausa yakeba bare yaji me tache, sai ma kallan Zahra dayayi yace all of U follow me yana gama faÉ—in hakan yajuya ya koma bakin kofa ya tsaya " wuchewa Zahra tayi taje ta taimakawa diyana tamike " Aunty Maryam na tsaye suka raÉ“a gefenta suka wuche, tanasan ta damkoh diyana tachi gaba da bugu kuma tana tsoron yadda taga fuskar Shahram ba wasa hakan yasa ta fiche a É—akin a fusache " Shahram ganin sun mike sun nufosa yasa yayi waje, suka bi bayansa bai tsaye wajen motochin gidan suka nufa da kansa ya buÉ—e musu marfin family car suka shiga gaba É—ayansu " shima shiga yayi yaja motar da gudun gaske nan take security dake tsaron gate suka wangale masa gate É—in " dagudu ya danna hanchin motar yayi waje doguwar titi yamiÆ™a dasu gudu yake sosai chikin Æ™anÆ™annin lokachi suka isa wani katafaren asibitin DON dake  kan titin zoo road " suna parking ya fito yabuÉ—e musu motar bayan sun fito yayi gaba suÆ™a bishi a baya " diyana daker take É—inkisa kafa " hiyana kuwa goshi sai jini yake, gaba É—aya jinin ya wanke mata face " kai tsaye office É—in baban dr yanufa " security dake tsaye a bakin office É—in suna ganin Shahram suka shiga sara masa kamar sunsan juna buÉ—e musu kofar office É—in sukayi suka shiga " babban dr naganin Shahram yamike yana miÆ™a masa hannu, miÆ™a masa hannu Shahram ma yayi suka gaisa san nan yakora mara bayani a kansu diyana " da sauri dr peter ya É—auki waya yakira nursing " nursing na shigowa dr peter yabata umar a kan ta tafi dasu diyana tabasu gado gashi nan zuwa yadubasu " har É—akin da a ka kaisu sai da Shahram ya bisu sai da ya tabbatar sun fara samun kulawar Dr san nan yafito ya nufi motarsu yatayar yanufi gd


A bangaren Aunty Maryam kuwa tana komawa É—aki ta É—au'wayarta tafara kiran layin Aryan dan taji ko shiya aiko Shahram amma ba'a É—agaba sai data kira miss call 10 amma ba'a É—agaba san nan ta hakura ta ajiyewayar tana ta surutai wlh Aryan kazo gaÉ“ar da bazan kyalekaba, ina ruwanka dan nabuge yaran nan toma waya faÉ—amaka ina bugunsu dole na binchiko ta ina kasamu lbr, haka dai take ta surutun'ta 



Yadda akayi Aryan yasamu lbr Aunty Maryam na bugunsu diyana har ya'turo Shahram


Lokachin da Khalid ke magana da Zahra yaji tayi shiru sai hello, hello kawai yake amma ba amsa har zai katse kirankuma sai yaji ihu, nantake hankalinsa yatashi yamike yanajin yadda Aunty Maryam ke bugunsu, da sauri yanufi É—akin Aryan rike da wayarsa yana zuwa yamikawa Aryan wayar " muryan Aunty Maryam sukaji tana faÉ—in nizaki haÉ—a faÉ—a da É—an uwana," bai taÉ“a kirana a wayaba amma yau yakirani har sau 2 saboda ke " a fusace Aryan yayi wurgi da wayar Khalid yamike, nan take fuskarsa ta Sauya idon nan suka chanza sukayi jawur dasu kamar an watsa barkono, wayarsa ya É—aukoh sai huchi yake kiran layin Aunty Maryam É—in yafarayi Amma shiru shiru har 3 time rai a É“ache yayi wurgi da wayar,  yanufi hanyar fita " da sauri Khalid yarikesa dan ya lura baya chikin hayyachen'sa inazakaje Aryan chewar Khalid " Nigeria zanje mana " dariyane sabo kuÉ“chewa Khalid amma sai yadanne yace ai kokatafi yanzu ba yanzu zaka isaba kafin kaje kuma duk abun da zai faru yarigada yafaru,  yanzu dai kakira wani daga chikin security nan suje su kashe wutar, ai tun Khalid bai kai karshen magana ba "Aryan yanufi wayarsa da sauri ya É—aukoh yafara kiran layin Shahram, " Shahram nayin picking call É—in " Aryan yabashi umarnin yaje ka dakatar da Aunty Maryam daga bugun su diyana datake san nan ya É—aukesu ya kaisu asibiti, yana gama faÉ—in haka ya katse kiran ya zauna a bakin gado ya dafe kai 

Kusa dashi Khalid yazo ya zauna ya sa hannu ya dafa kafaÉ—arsa zaiyi magana ke nan sukaji sallamar DON 


Kallonsu DON yake sosai kamar mai nazarin wani abu a fiskokinsu  wuchewa yayi ya zauna a bakin gadon " calmly yafara magana me yake damunka Aryan wan nan shine tambaya ta karshe da zanmaka idan baÆ™a faÉ—aminba kasan sauran " kakalo murmushi dole Aryan yayi yana faÉ—in wai meyasa kakesan saka wani tunanin banza a zuchiyar kane, nifa nafaÉ—ama kwanan nan ina yawan fama da chiwon kaine amma bari namaka mai kankat wlh Allah nikam bawani abun dake damuna,  kawai jinake tamkar a takure nake banajin daÉ—in Æ™asar  nan narasa meke min daÉ—in banda haka wlh babu wani abun " jinjina kai kawai DON yayi batare dayache komaiba, dan yasan iya gaskiya ke nan Aryan yafaÉ—a masa dan bayadda za'ayi Aryan yayi rantsuwa a kan karya kuma tabbas zai iya shedan Aryan a ko ina baya faÉ—in maganar da ba hakaba, to amma tabbas yana da damuwar da shi da kansa baisan da itaba " ganin DON yayi nshirune yasa gaba É—ayansu suka dawo kusa dashi, dafa kafaÉ—arsa Aryan yayi yana faÉ—in baka yarda da magana ta bane " juyo green eyes É—insa yayi kan face É—in Aryan tare da É—anyin murmushi gefen fuska nayarda mana na yarda da duk abun da kafaÉ—a domin baÆ™a taba yimini karyaba matsalar É—aya a nan shine tabbas akoi abun da kedamunka wanda kai da kanka bakasan meneneba " zuba musu ido khalid yayi yana tunani a chikin ransa gaskiyane DON kachi su nanka Safras indai wajen basirane kai karshene ba abanza mai marbata ya dage sai kai za abawa sarauta'ba, yayi nisa chikin tunani sai yaji Aryan nataÉ“asa firgigit yayi ya É—ago yana kallonsu duk sun zuba masa ido "  lfy Khalid kodai kaima kana da damuwane DON yajefo masa tambaya " aa bani da damuwar komai nikam kawai tunanin meke damuna É—an uwana nake " nifa babu abun dake damuna na faÉ—a muku "  DON zaiyi magana wayarsa tafara ringing hannu yasa chikin aljihunsa ya fitar da wayar, sunan Sadiq yagani ta bayyana a kan screen É—in wayar dogon tsaki yaja tare da jefar da wayar a kan gado "  da sauri Khalid yasa hannu ya É—auki wayar yana duba wanene yakira DON yake jan tsaki haka ganin sunan Sadiq yayi a kan screen É—in bai yi mamakiba,  dan DON yaki É—aukar wayar Sadiq dan kuwa Sadiq yayi aure " murmushi yayi yana kokarin picking na call É—in kiran tayanke  chire pin na wayar  yayi dayake yasan pin na wayoyinsu dan ba abun dasuke É“uyewa juna 

Kiran layin Sadiq É—in yafarayi wayar nafara ringing Sadiq yayi picking call É—in yana faÉ—in yau wace rana nayi sa'a an É—auki wayata " dariya Khalid yayi san nan yace ai kasan shikam bazai É—auki wayarkaba  " my Khalid ykk " lfu lau ya amarya suhaima " first dai yanzu albishirinka " da sauri Khalid yace goro " my baby ta haifamin baby boy yanzun nan daman shi nakira nafaÉ—a muku " wow my man inatayaka murna bari nabawa Aryan ma yatayaka murna " Khalid bai jira amsar Sadiq ba yamiÆ™awa Aryan wayar " satar kallan DON Aryan yayi yaga bama su yake kalloba yasa hannu ya'karÉ“i wayar yawa Sadiq congrat san nan yace ga DON nan, kuma da gangan yayiwa DON É—in haka dan yasan idan shi yamiÆ™awa DON wayar tofa dole zaikarÉ“a kuma gaskiya yanasan DON yataya Sadiq murna kodan halakchin da Sadiq É—in yamusu, yanzu matarsa na aihuwa tun bai sanar da kowaba yafara sanar musu, aiko basaso dole zasu danne sumasa congrat " karbar wayar DON yayi badan yasoba kawai dan bazai iya kwasale Aryan a idon kowa bane 


Congratulations inatayaka murna chewar DON " da murna Sadiq yace thanks ykk y gd " lfy yasu mom " alhamdulillah Sadiq yabashi amsa " ok kawai DON yace san nan ya katse kiran ya É—ago green eyes nashi yana kallonsu " zuba mishi ido Aryan da khalid sukayi sosai suna kallansa Khalid na mamakin hali irin na  DON "  kallon me kukemin haka " murmushi Khalid yayi san nan yace kyau kamana mana shiyasa muke kallanka " mikewa yayi yana faÉ—in to aiki yasameku kuda kukasanma me kyau yake nufi, yana gama faÉ—in hakan yayi waje " dariya Khalid yayi sosai san nan ya dubi Aryan yana faÉ—in wai gaji DON baisan me kyau ba kajimin iskachi " tsaki Aryan yaja yana faÉ—in kai ma kake biye masa ae,  to daman inban da kai da neman magama ina DON yasan maka wani abu Wai shi kyau,  ko kuma mara kyau ai shi inba Bom, bindiga, bullet,ba to bawani abun dayasani mai kyau " mikewa Khalid yayi yana faÉ—in good night anjima kakira Shahram kaji ya ake chiki " da sauri Aryan yafara lalubar wayarsa yana faÉ—in yanzu dai wani anjima kuma,  wan nan ke nan



Nigeria DON hospital



Washe gari misalin karfe 8 dinaya na kwanche a gado da drip a hannu " hiyana ma kwanche a nata gadon ansamata bandeji a goshi " sai lamrat da amrat dake zaune gefen gadon hiyana,  zahra kuma tana kan kujera plastic dake chikin É—aki " shiru sukayi gaba É—ayansu na tsawon lokachi " sallama sukaji a bakin kofar É—ago kai sukayi gaba É—ayansu Shahram suka gani tsaye shida Dr Peter karisa shigowa chiki É—akin sukayi suna tattaunawa " mikewa Zahra tayi daga kan kujerar ta koma gefen gadon diyana tana kana tacewa Shahram,  uncle have a seat " thanks dear san nan ya zauna a kujerar " miÆ™amasa takardar magani Dr Peter yayi san nan ya juya yanufi waje " Shahram kuwa wayarsa ya É—aukoh daga aljihun wandansa yafara kiran layin Aryan,  har saida wayar takusa tsinkewa tukun nan a ka É—aga 

Chikin girmamawa Shahram yafara magana hello sir good morning " morning how are U " am fine sir " where is she da sauri Shahram ya mikawa diyana wayar " hannu tasa ta amsa ta Æ™ara a kunne hello yaya Aryan ina kwana " lfy y jiki " da sauki ina Ammi dan Allah yaya Aryan kafaÉ—awa Ammi ta dawo dan Allah wlh tsoran Aunty Maryam nakeji, nikam Ammi tazo taje tasayar da shanun Bappa gaba É—aya tasaya mana gida mukoma " shiru kawai Aryan  yayi yana sauraron'ta har ta kai karshe " chikin sanyin murya yafara magana karki damu ae munkusa dawowa saura 9 days ne kawai kuma kinga nafaÉ—a miki Aunty farida zatazo next week idan Aunty farida na nan babu abun da Maryam zata muku, yanzuma bazan barku hakaba kinji bazata sake taÉ“akuba  " to shike nan Amma pls yaya Aryan ka haÉ—ani da Ammi da Abba mana " mezakiche musu idan na haÉ—aku " zanfaÉ—amusu abun da Aunty Maryam tamana " aa to bazan haÉ—akuba gaskiya " ayya yaya Aryan kayi hakuri ka haÉ—amu tunfa shakaranjiya da Ammi ta kiramu ta wayar Aunty Zahra bamu sake maganaba, jiyama ina wanka  naji su hiyana na magana da ita, kafin nafito kuma sungama magana pls ka haÉ—ani da ita takarisa maganar kamar zatayi kuka " to zan haÉ—aku amma saikin min alÆ™awarin bazaki faÉ—amusu komaiba gaisawa kawai zakuyi " da sauri tace eh namaka alÆ™awari wlh bazan faÉ—aba " ok to yanzu bawasu Zahra wayar bari naji yanasu jikin idan mungama magana sai na haÉ—aki dasu " to kawai tace san man tamiÆ™awa zahra wayar " karÉ“a Zahra tayi suka gaisa san nan tamiÆ™awa hiyana " ansa hiyana ma tayi suka gaisa ya tambayeta jikinsu tace da sauki san nan yace to tabawa diyana wayar, miÆ™amata wayar hiyana tayi " da sauri diyana ta ansa tana faÉ—in hello " idan ruwan da a'kasamiki yaÆ™are Shahram zai maidaku gd, dan na chanza shawara zan Æ™ira mijin Aunty farida na faÉ—amasa ya bar Aunty farida tazo goÉ“e kinji " to shike nan yaya Aryan amma kuma, kuyi sauri ku dawo dawuri tayi maganar a shagwaÉ“e " meyasa kikesan mu dawo dawuri kodai kina san ganina' ne " eh ba kai kaÉ—aiba dukkan kuma inasan ganinku, gd babu daÉ—i dabaku nan " shiru yaÉ—anyi kafin yace ok inshaa Allah munkusa dawowa ae " to Allah ya dawo daku lfy tana gama faÉ—in hakan bata jira amsar shiba tamiÆ™awa Shahram wayarsa " koda Shahram ya ansa wayar yasa a kunnensa, sai yajiyo Aryan na faÉ—in nima inakewarki my sister ina kewar coffee É—inki mai daÉ—in nan" a sukwane Shahram ya miÆ™a mata wayar  kallansa diyana ta tsaya take damamaki batare da ta ansa wayar'ba " mikewa Shahram yayi yazo har kusa da ita yasa mata wayar a kunne " muryan Aryan taji yana faÉ—in sister ba kyajinane " hannu tasa ta ansa wayar tana faÉ—in inajinka yaya Aryan  "to ae naji inata magane kinyi shiru " eh dazun banji me kafaÉ—a'bane " ok to shike nan Shahram zai jira idan ruwan da a'ka Æ™aramiki ya Æ™are  zai mai daku gida, nurse É—aya zata biku tachigaba da kula daku " to yaya Aryan makaranta'fa " makaranta sai kunji sauri ba naji kun gama exam bama " laaa waya faÉ—amaka to " zuchiyata mana itace tafaÉ—amin " to zuchiyar'ka tafaÉ—i gaskiya mungama " to bazaku sake zuwaba sai  ranar da za'ayi hutu yanzu kam ku huta kuyi jinyar jikinku " to ka haÉ—ani dasu Ammi mana " sai da daddare idan kun koma zankira layin Zahra na haÉ—aku amma karki karya alÆ™awari'fa " to bazan karyaba " ok sai munyi waya anjima koh, yana gama faÉ—in hakan ya katse kiran " jin ya katse kiran yasa ta mikawa Shahram wayarsa,


Sai 12 :45 a ka sallamesu daga asibiti hiyana dai ba a chire mata bandejin'ba, saboda sosai taji chiwo a goshinta dan har É—inki 6 a kamata awajen " Shahram dakansa yabuÉ—e musu motan suka shiga tare da nurse É—aya kai tsaye gd Shahram ya wuce dasu " yana parking yafito ya buÉ—emusu motar suka fito, daka gansu kaga wayanda suka sha wahala, har É“angaren Ammi Shahram ya rakasu sai dayaga shigansu palo tukun nan yajuya yakoma bakin gate 

Suna'shiga É—akin'su suka nufa wanka suka farayi É—aya bayan É—ayan suka sanya dogayen riguna abaya baki " hiyana kam dakyar tayi wankan saboda zafin da kanta ke mata shiru suka zauna " jim kaÉ—an Zahra tamike tana faÉ—in ina wayata bari nakira masu aikin sukawo mana abinchi nanfa tashiga nemar wayar'ta, chan gefen drawer ta gano wayar, da sauri ta É—auka ta duba taga wayar ta mutu ba charji jonata a charji tayi san nan ta kunnata tafara neman layin binta 

Bugu É—aya binta ta É—aga Zahra tabata umarni kan ta kawo musu abinchi " 


Chikin kankanin lokachi saiga binta tashigo da sallama, hannunta É—auke da babban trey mai dauke da kulolin abinchi da plate a kai a tsakiyar É—akin taajiye san nan ta gaidasu tafita " saukowa kasa zahra da diyana sukayi " Zahra ta dubi nurse É—in tace kizo kichi abinchi sister, bamusu itama nurse É—in ta saukoh " kuma kunajiran saina kirakune? Zahra tayi maganar tana kallansu lamrat " jiki ba kwari suka tsaukoh, " Zahra da kanta tayi sarving na kowa kallan, hiyana dake zaune tayi ke bazaki zo muchi'bane " Aunty Zahra nifa bazan iya chin komai"ba dan kaina chiwo yake min sosai " aa hiyana karmuyi haka dake kawai ki saukoh ki daure kichi ko kaÉ—anne " hiyana badan tasoba haka ta saukoh suka fara chin abinchin,  jitake kamar magani takechi dan bakinta ba tes ko kaÉ—an 

" Bayan sungama chin abinchi ne nurse ta basu  magunguna san nan suka haye gado " zahra a ita da hiyana a gadon'su, dayana da amrat da lamrat suma a gadon diyana " nurse nasu kuwa suka kaita É—akin'su amrat,  suna kwanchiya ba jimawa barchin wahala ya É—aukesu



SAUDIA 



Wayarsa ya É—auka yafara neman layin Aunty farida ringing É—aya ta É—auka " hello my bro " na'am lovely Aunty ykk " lfy lau yasu Abba ya shirye shiryen dawowa " alhadulillah ina junior " yafita da baban'sa " ok Aunty farida daman ina san magana da'kene "ok to inajinka " sonake kije gd gobe " ae sai ranar Monday zantafi amma meyasa kakesan naje dawuri " Aryan zai sake magana idonsa suka sauka chikin green eyes wato DON tsaye yake a bakin kofar shigowa betroom É—in, sanye yake da suite ash colour, bakaramin kyau yayi yatara gashin kansa ya É—aure,  fuskar nan tamkar an aiko masa da mutuwa ya harÉ—e hannu a kirji ya zubawa Aryan green eyes nan nashi " hello bro baka jinane " sorry lovely Aunty inajinki wlh hankalina yatafi wajen DON ne " ok to injinka meye dalilinka nacewa naje'gidan gobe " babu komai kawai dai inasan kijene " jinjina kai Aunty farida tai kana tace ok badamuwa zanyi magana da dadyn junior idan yadawo " ok kawai Aryan yace batare daya jira kozatace wani abuba ya katse kiran " 

dawo da kallansa yayi kan DON yafara magana to meya tsayar da kai kuma a bakin kofa " dogon numfashi DON yaja tare da sauke ajiyar zuchiya a hankali yafara takowa izuwa chikin É—akin gefen gado ya zauna yana fuskantar Aryan " ayayin da Aryan É—inma shiyake fuskanta shiru sukayi na É—an lokachin suna kallan juna " DON ne ya katse musu shirun dacewa munyi magana da Aunty farida tace tafara magana da Abba a kan maganar sarauta amma kanaganin Abba zai chanza ra'ayi kuwa " gaskiya dakamar wuya Aryan yabashi amsa a takaice " mikewa yayi ya kwanta a gadon yana kallan Aryan É—in batare dayace kalaba " Aryan kuwa dayaga kallanda DON yake masa kamar kallan tuhumane, sai yamiÆ™e yana faÉ—in bari na dubo khalid yanufi hanyar fita " meyasa kake guduna ne yanzu Aryan " chak Aryan ya tsaya kirjinsa na bugawa da karfi a hankali ya juyo idansa suka sauka chikin na DON dan kuwa ya tsaresa da ido sosai yake kallansa " meyasa zanrinÆ™a gudunka kuma " wan nan dai kai kasan dalilin amma dai ninasan ba haka kawaiba " nibawani gudunka danake yama za'ayi kace ina gudun kane bayan tare muke komai, har chin abinchi, wanka da barchine kawai ke rabamu, " ok to yanzu dakamike ina zaka,  eh bawai bani da aikin yi banefa nabari nazo wajenka muyi hira amma ko kara bakaminba kamike wai barika dubo khalid 

Shiru Aryan yayi yana tunani kuma yagane kuskuren dayayi nacewa bari yadubo Khalid dan haka sai yajuya ya dawo chikin É—akin kusa da DON É—in yadawo ya zauna yana faÉ—in am sorry bro  " jinjina kai kawai DON yayi batare dayayi maganaba " shiru sukayi gaba É—ayan'su kowa da abun dayake tunani 



YOLA NIGERIA ✈️


Zaune take a tsakar gida ta buga uban tagumi sai tunani take tayi nisa chikin tunaninta taji ana Sallama a kofar gd, amsa sallahar tayi san nan tamike ta É—auko mayafi ta rufa a kanta tayi waje,  tana fita tachi karo da bello " aa Bello kaine mai doka sallama haka to ya akayi " eh nine inna inawuni " lfy meyakawoka " daman goggon'su hiyanace wadda ta É—aukesu ta aiko wani yazo yafaÉ—amin intattara dabbobin'su hiyana na haÉ—a da nawa narinka kula dasu bayan Sallah zasu zo " wani tsalle inna tabuga tana faÉ—in banga uban daya isa ya taÉ“a dabbobin nan ba wlh " to inna ae'ga yan sakon nan basu tafiba sai kifaÉ—amusu " juyawa inna tayi tana kallan inda bello ke nunawa, wasu sojoji taga guda 3 sanye da kaki, fuskar nan tasu babu alamar wasa aguje inna takwasa tayi chikin gida " juyawa bello yayi yanufi garken dabbobin yana faÉ—in muje " bin bayansa sojojin suka har zuwa wajen dabbobin " Æ™irga dabbobin suka shigayi bayan sun gamane "bello yadubi sojan yace a nawa lissafin dukka dabbobin banda kaji, da zabbin, nan iya shanu, da raguna, da awaki, 1007 ne amma kufa nawa kuka samu a naku lissafin " É—ayan daga chikinsu yace 1005 nasamu dayanma yace 1005  " kai kumafa bello ya tambayi É—ayan da baiyi maganaba " amsata iri É—ayane danake 1007  shiru sukayi chankuma Bello yace to kozamu sake Æ™irgawane " aa basai mun sakeba a barshi a lissafinka domin ina da tabbachin shine dai dai, dan kafimu iya Æ™irga dabbobi,  nasan kana kirga wayanda sukafi wan nan yawa to ni da kyarma na iya irgawa wlh sai rikiitani suke " murmushi kawai bello yayi san nan yace to muje wajen kajin nan kuma " no kaji da zabbi madam tace ka É—auka bata buÆ™ata " nan take fara'a ta bayyana a fiskar bello sai godiya yake zubawa har suka fito " sojojin sukaje suka shiga motar'su suka kama hanya " bello kuwa da sauri yajuya yanufi gd dan yafaÉ—awa innnar'sa abun dake faruwa 



KANO STATE


Misalin karfe 4 hiyana ta farka daga barchi tana duba time da sauri tafa tashin'su Zahra dan ko sallar azhar basuyi'ba, koda suka tashi sai faman yamutsa fuska suke " hiyana naganin sun tashi tamike tanufi toilet danyin alwala zahra kuma wayarta tachiro daga charji ta kunna wutar screen É—in nanfa tasamu miss call kusan 17 yaya Aryan 4 miss call, yaya Khalid 3 miss call, Ammi 3 miss call, mai Martaba 5 miss call, yaya Yusuf 2 miss call, "  tunani tashiga'yi wazata fara kira saiga wata kiran tashigo tana dubawa taga yaya Aryan , da sauri tayi picking call É—in tana faÉ—in hello yaya Aryan ina wuni " daga É—ayan É“an garen Aryan yace lfy ykk yajikinku " da sauki barchi, mukayine shiyasa kakira bamu É—agaba " ok ina sauran'suke " miÆ™awa diyana wayar Zahra tai" ta ansa taba faÉ—in wanene  " idan kinsa a kunnenki ae zakiji koma wanene Zahra tabata amsa " kara wayar tayi a kunnen'ta tana faÉ—in hello " ya jikin naki " laaa yaya Aryan daman kaine jiki ba sauki gaskiya dan har yanzu zafi kaina da kirjina yakemin sosai " saura kaÉ—an ya kwashe da dariya amma sai ya danne yace to inshaa allah zai daina yimiki zafi kinji " diyana zata sake magana sukaji an turo kofar É—akin nasu da farfi anshigo a razane suka É—ago ganin Aunty Maryam yasa diyana fasa...✍️



No comments