Recent Updates

Duk Karfin Izzata Book 1 Paga 15

 


Episode 15*

            


Bayan sungama shiryawa kamsu abubuwar dasuke buÆ™ata na buÉ—a baki nan take masu aikima suka fara shigo da kulolin abinchi suna jerawa a kan table É—in  komawa É—aki sukayi É—aya bayan É—aya sukayi wanka suka

É—auro alwalla hiyana diyana Zahra dogayen riguna na material sukasa maroon colour " lamrat da amrat kuwa riga da sket na atamfa suka sa kai tsaye palon mai martaba suka nufa danyin buÉ—a baki da sallam suka shiga suka wuche kai tsaye kan table zama sukayi suna jiran  time yachika a kira sallah " shiru suka zauna kowa da tunanin dayake " diyana che ta katse musu shirun dachewa Aunty Zahra sai narinÆ™a jin gidan ba É—aÉ—i wlh saboda ba kowa ki kalla kan table É—in nanfa da chika muke muna chin abinchi amma yanzu saura mukaÉ—ai kai gaskiya na kosa su Abba sudawo " Zahra zatayi magana saitaji an daÆ™a musu tsawa daga bakin kofar shigowa " da sauri suka É—ago kai suna bin bakin kofar da kallo " Auntyn Maryam suka gani tsaye fuskar nan babu annuri ko kaÉ—an nan take jikin Zahra yafara É“ari dan tasan halin Aunty Maryam sarai " diyana kam kawar da idon ta tayi tachigaba da abun datake kamar bata san da wata Aunty maryam awajen ba "a nitse chikin sanyin murya hiyana tafara magana ina wuni Aunty Maryam " wani mugun kallo Aunty Maryam ta wurgawa hiyana batare da ta amsa gaisuwarba chikin tsawa tafara magama uban waya baku izin kurinÆ™a zuwa nan kuchi abinchi inachewa Aisha itace yar uwar ku a gidan nan " shiru sukayi basu che ko kalaba "  Aunty Maryam tachigaba dachewa to tunda wajen Aisha kukazo ku tsaya a iya É“angarenta idan nasake ganinku a wani É“angare na gidan nan, ba bangaren Aisha ba wlh sai na babballa yarinya kuzo kuficemin daga nan ko nashiga na muku mugun duka " tunkan takai karshen maganarta suka mike  gefenta sukabi zasu wuche " hannu tasa ta damkoh wuyar rigar diyana tana faÉ—in ke ki buÉ—e kunnenki ki saurare ni da kyau daga yau bawanda zai sake share bangaren Aunty amarya keche zaki rinÆ™a yi har nabar gidan nan,  ke bama shara kawaiba wankin kanana kayana wankin toilet mopping da yimini tausa kinajina bakinche ke bakida kunyaba to wlh zan gyara miki zama " diyana binta kawai take da ido  batace komaiba  tayi shiru  " su Zahra kuwa wuchewa bangaren Ammi sukayi jiki ba kwari " hannu Aunty Maryam tasa ta tsolewa diyana ido tana faÉ—in shegen ido kamar na mayu ai kedaga ganinkuma dangin mayune shiyasa aka faÉ—amin kun lashe zuchiyar kowa na gidan nan to nikam nafi karfinku " hannu diyana tasa tana goge idonta tana hawaye zafi idon yake mata sosai  " sakin rigar nata Aunty Maryam tayi san nan tace yanzun nan kije ki wanke toilet's dasuke bangaren Aunty amarya dukka san nan ki shiryamin abinchin buÉ—a baki " ba musu diyana tanufi bangaren Aunty amarya tana hawaye Aunty Maryam kuwa ta wuche chikin É—akin mai martaba


Abangaren su Zahra kuwa palon Ammi suka koma suka zauna a kan sofa nan take Zahra tafara hawaye " hiyana tamike ta dawo kusa da ita tana faÉ—in lfy Aunty Zahra kike hawayen " chikin kuka Zahra tace diyana nakewa kuka wlh dan nasan tun da Aunty Maryam ta tsai da ita wani muguntar zata shirya mata " kiyishiru Aunty Zahra ninasan duk abunda Aunty Maryam zatawa diyana bazai kai kaso É—aya chikin goma na wadda inna tamana ba dan haka ki daina damuwa ba irin muguntar da'bamuganiba chewar hiyana " mikewa Zahra tayi tana faÉ—in kuzo muje muyi buÉ—a baki gashi chan ana kiran sallah ba musu suka nufi kichin na Ammi " ruwa ko wannensu yafara sha san nan sukachi dabino " zahra tace ku zauna a palo kujirani bari naje palon mai martaba ba É—aukoh mana abinchinmu " inkinje Aunty Maryam bazata bugekiba chewar hiyana " eh bazata bugeniba ai duk dokar datake kafawa ku take kafawa baniba nikam ai bata isa tahanani yawo a gidan babana ba tana gama faÉ—in haka yanufi hanyar fita .



KASAR SAUDIA ✈️


Gaba É—ayansu suna chikin masallahchin a nan sukayi buÉ—a baki bayan sungama sunyi sallane suka zauna hira " Ammi ta dubi Ummi tace Maryam fa tazo " yaushe tazo chewar Ummi "  yau tazo Mai martaba yabasu amsa " ya akayi wan nan karon tazo dawuri chewar Ummi " tsaki Aunty amarya taka san nan tace oh bakisan tazo daman koh to tazo kuma bayadda zakuyi da ita " mikewa DON yayi zai bar wajen " Aryan yace jirani muje tare, tare ya faÉ—in hakan yana mikewa tare suka jera suka nufi hotel É—insu " mai martaba yama Ammi magana da fillanchi Mikewa tayi tana faÉ—in Ummi muje Koh,  mikewa Ummi'n tayi dan tasan mai Martaba ne ya umarchi Ammi dasu tafi É—aki dan baisan hayani kuma baisan subiyewa Aunty amarya  " Khalid Aiman Ahmad suma suka mike a tare sukabi bayan DON da Aryan " dawo da kallansa mai martaba yayi kan haidar da umar dake zaune basu tashiba,  to me kuke jira, ai tun bai karasa magana'ba suka mike suka bar wajen " 

dawo da kallansa kan Aunty amarya daketa chika tana batsewa yayi a nitse yafara magana wai meyasa Hajara bakyasan zaman lfy'ne eh meyasa kullun ke kike tada husuma a chikinkune tunfa kina amarya kike irin wan nan hali wadda kikazo kusamuma baki kyaletaba haka wadda tazo tasamekima  " zatayi magana  ya É—aga mata hannu banasan inji komai daga gareki kawai abun danakeso karnasake jin wata fitina tatashi ," ke ko kunyar Æ´a'Æ´anku ba kyaji kitashi muje mu kwanta yaÆ™arisa maganar yana kokarin mekewa  hanyar É—akinsu yanufa itama tamike tabi bayan'sa tanata chika tana batsewa



NIGERIA ✈️



Har wajen karfe 9 na dare diyana ta dawo É“angarensu da kyar take tafiya saboda yinwa ko buÉ—a baki batayiba ko sallama babu ta shiga É—akinsu " tasamu su Zahra har sunyi wanka sunyi shirin barchi "Zahra na ganinta ta mike tana faÉ—in sannu diyana san nan tayi waje da sauri " zama bakin gado tayi  ta É—ago blue eyes nata dasuka sauya izuwa ja saboda yinwa da gajiya, tana kallan hiyana dake tsaye tana mata kallan karin bayani takeso " diyana zatafara magana saiga Zahra ta dawo hannunta É—auke da plate É—in abinchi da cup mai É—auke da tea mikawa diyana tai nantake ta karÉ“a tafara chi " zama sukayi kusa da ita shiru itakuwa sai É—ura abinchi take hannu baka hannu kwarya  


Wayar Zahra tasoma ringing da sauri amrat dake rike da wayar tamiÆ™a mata my lovely bro ne yabayyana a kan screen É—in wayar da sauri Zahra tayi picking call É—in tare dasa wayar a H-free tana faÉ—in hello yaya khalid " wani dogon numfashi Khalid yaja tare da sauke ajiyar zuchiya kana yace my lovely sister ykk ya makaranta " muna lfy makaranta alhamdulillah Zahra zata sake magana taji " diyana takwache wayar tana faÉ—in yaya Khalid ina yaya Aryan dan Allah inasan inyi magana dashine " baki buÉ—e'su Zahra ke kallanta " Khalid kuwa chewa yayi ai daman dan ke nakira shima magana yakesanyi dake " yauwa to bashi,"miÆ™awa Aryan dake zaune kusa dashi wayar Khalid yayi " ansa Aryan yayi yasa a kunnensa yana faÉ—in hello " yauwa yaya Aryan ina wuni " lfy lau y school " 

khalid kuwa miÆ™ewa yayi yana faÉ—in inazuwa hannunsa Aryan yakama yamai'dashi ya zauna yana harararsa  " yaya Aryan wlh yau wan nan Aunty Maryam É—in takusan kasheni chewar diyana " a zafafe Aryan yace what ? bana rabakuba mekuma yasake kai ki wajenta " turo baki tayi kamar tana gabansa tafara bashi lbr abun daya faru daga farko harkarshe " shiru yaÉ—anyi yana tunani daman yasan za'ayi hakan tunda yaji Aunty Maryam tazo ba lokachin zuwansuba yasan da dalili yayi nisa chikin tunani " muryan ta ta katse masa tunanin dacewa " yaya Aryan dan Allah kudawo kaga idan kun dawo Abba bazai bari tarinÆ™a buguna ba " karki damu saura kwana 10 mu dawo kuma I next week Aunty farida zatazo domin tarbarmu idan Aunty farida tana nan bazata bari a muku komaiba,  amma duk dahaka zanmata magana " to shike nan sai dasafe " murmushi kaÉ—an yaÉ—anyi kafin yace bakyasan hira danine kikechemin sai da safe "  khalid dake zaune kusa dashi  ya É—ago a sukwane yana kallansa fisge hannunsa yayi daga rikon da Aryan yamasa yamike yana faÉ—in idan kagama hirar, kasameni a É—aki kaga tafiyata " harara Aryan ya wurga'masa  " khalid bai bita kansaba yayi waje

Diyana kuwa dariya tai san nan tace to ai abinchi nake chi nifa yanzu nake buÉ—abaki " shiru yayi zuchiyarsa tana masa zafi sosai yafara tunanin matakin daya kamata ya É—auka wan nan wani irin zalunchi'ne yarinya tayi azumin san nan kijib'ga mata wan nan uban aiki kuma ki hanata buÉ—a baki yanzu kusan karfe 10 nadare wai batayi buÉ—a bakiba, dole na É—au mataki " jin yayi shirune yasa diyana cewa yaya Aryan kodai kayi barchine " aa banyiba kawai ina É—an tunanine " to shike nan sai anjima bari nagama chin abin china " ok kichi a hankali dai kuma banda chin fruits dayawa dan inchikin'ki yafara chiwo kinga bamunan bare namiki allura " dariya tayi san nan tace to bazan chiba " ok kawai yace san nan ya katse kiran ya ajiye wayar a gefe ya dafe kansa yana tunani  " dayaga dai tunanin ba wata mafita, sai yaike ya nufi kan katafaren gadansa ya konta yajawo wayarsa yafara latsawa 



Bayan diyana tagama chin abinchinta tamike tanufi toilet wanka tayi tafito daure da towel kayan barchi tasa doguwar riga mai siririn hannu yar shafal mara nauyi kwanche ta iske su Zahra sunata yar hirarsu,  dayake yanzu su amrat ma sun dawo É—akinsu, saboda  suna tsoro tunda ba kowa a gidan sai suka haÉ—u suka chure waje guda 

Hayewa samar gadon nasu tayi itama tana faÉ—in Aunty Zahra kunna mana kallo " to kawai Zahra tace tare da dauko wayarta dake gefenta ta shiga gallery tana kokarin neman film sai taga kira yashigo " da sauri tayi picking call É—in tana faÉ—in yaya Khalid bakayi barchiba " eh banyi barchiba ya'za'ayi nayi barchi bamuyi wayaba " Zahra zatayi magana sukaji an banko kofar É—akin nasu da karfi gaske " zubur suka mike gaba É—ayansu har sai da wayar Zahra tafaÉ—i kasa dan tsorata dasukayi   " a zafafe Aunty Maryam ta shigo chikin É—aki kai tsaye wajen diyana tanufa damkoh wuyarta  tayi tafara bugunta ta ko ina "  diyana tafara ihu " nizaki haÉ—a faÉ—a da É—an uwana koh to wlh yau sai na kasheki,  tun danake dashi baitaba kirana a wayaba amma yau saboda'ke sau biyu yana kirana bugunta Aunty Maryam keyi tana surutai  "  diyana kuwa sai ihu take "  hiyana naganin Aunty Maryam na kokarin kashe diyana da gaske ta kwasa a guje tayi wajensu tana kokarin kwache diyana a hannunta " hankaÉ—e ta Aunty Maryam tayi da karfi ta tafi ta bugu da bango nantake kanta yafashe " ihu mai karfi Zahra tabuga tayi kan hiyana tana kiran su nanta " lamrat da amrat kuwa sai kuka suke " duk da raunin da hiyana taji bai hanata sake mikewa a zafafe tayi kan Aunty Maryam tana faÉ—in karki kashemin Æ´ar uwa dan allah " wani bugu Aunty Maryam tasake kaiwa hiyana a baki " kukan kura hiyana tayi a fusace ta damki wuyar Aunty Maryam ta baya " bashiri tasaki wuyar diyana ta juyo ta damki hiyana tashiga bugu " da gudu Zahra tazo ta duÆ™a takama kafar Aunty Maryam tana rokonta " dan allah Aunty Maryam kiyi hakuri ki kyalesu wlh marayune basu da uwa basu.. Zahra bata karisa ba taji saukar mari a faskar ta a zafafe Aunty Maryam tace. Kifita a É—akin nan zahra'u kokuma na haÉ—a dake " mikewa Zahra tayi tana kuka takama hannun amrat da lamrat tace muje " kwache hannunta lamrat tayi tayi gun Aunty Maryam da gudu tana faÉ—in dan allah ki kyalemin yan uwana haka " kafa Aunty Maryam tasa ta amÉ“are lamrat tafaÉ—i kasa tana kuka " da kyar diyana tamike tana É—ingisa kafa ta karisa wajen ta duka gaban Aunty Maryam tace ninamiki laifi basuba kiyiwa Allah kisakemin yar uwata ni ki kasheni inkinaso " juyowa tayi ta damki wuyar diyana ta damkoh hiyana ta haÉ—e kansu ta buga da karfin gaske wani kara suka sake a tare  " Zahra da amrat dake tsaye a bakin kofa da gudu suka dawo chikin É—akin " Aunty Maryam kuwa duk da hakan bata kyalesuba sake damkar gashin kan diyana tai tana janta a kasa har zuwa wajen mirrow tasa hannu kan mirrow ta dauki wani kwalbar turaren humra zata buga mata ke nan taji anche STOP chikin tsawa  da sauri ta É—ago kai idanunta suka sauka akan...✍️✍️✍️


No comments