Recent Updates

Duk Karfin Izzata Book 1 Paga 14

 


Episode 14



A fusace jabair yanufi diyana, tana tsaye ko motsi batayiba kuma babu alamar tsoro ko kaÉ—a a face nata " hannu Jabir ya É—aga zai'kaiwa diyana bugu  " da sauri hiyana

tarike hannun nasa " a zafafe Yajuyo yaga waye yarike masa hannu,  ganin hiyana che yasa ya watsa mata harara yana faÉ—in sakeni " ita ma rai a bace tache wlh bazan sakekaba kafara buguna tukun nan kafin kabugi diyana " fisge hannunsa yayi yasake É—aga hannu zai mari diyana " da sauri hiyana tashiga tsakanin' su tana faÉ—in diyana kiwuche class naku " diyana dake tsaye babu alamar tsoro a face É—in ta tace babu inda zanje hiyana sai dai duk abun da zai'mana yamana tare " ganin haka yasa jabir yajuya yabar wajen dan kuwa bazai iya bugun hiyana ba dan yana sonta itakuma bazata taÉ“a barin abugi diyana ba " suna ganin jabir yatafi suka rungumi juna  " diyana nafaÉ—in wlh sauran kaÉ—an nayi fitsari a wandona dan tsoro, dayanzu  jabir yabugeni da wan nan katakon hannun nasa ai nashi uku " dariya hiyana tayi sosai san nan tace wlh ba kyaji diyana ae nima nakusa fitsarin saboda tsoro kawai dagewa nayi dan bazan iya ganin ya sauke wan nan jibgegen hannun nasa a jikinkiba " dariya sukayi gaba É—ayansu san nan suka saki juna suka reke hannun'su chikin na juna suka nufi class, 



KASAR SAUDIA


Tsaye yake gaban mirrow yana gyara gashin kansa sanye yake chikin wandon jeans Navy Blue da White t-shirt, bakaramin kyau kayan suka masaba sosai ya gyara gashin kan nan nasa ya tara ya É—aure ta baya, yasake É—aukan turare yafeshe jikinsa,ga sajen nan nasa kwanche a kan face nashi kamar wani balaÉ“e wayarsa ya É—auka yafito wajen kai tsaye palon kasa yanufa, zaune yasamu yan uwan nasa gaba É—ayansu har dasu haidar, kallan DON yayi yafara magana " zan fita inasan inje wani wajen " da mamaki DON ya É—ago green eyes nashi yana kallan Aryan  ya mai maita maganar zai fita inasan inje wani waje shiru yayi kamar mai tunani " Aryan dai ido yazuba masa kawai yana kallan'sa " zarginafa yafara tabbata a kanka Aryan chewar DON " murmushi kaÉ—an Aryan yayi san nan yace au daman zargina kake ke nan " yap zuchiyata na zargin wani abu " matsowa Aryan yayi kusa da DON sosai san nan yafara magana karkabar zuchiyarka tana raya maka wani abu a kaina kasan dai wlh babu wani abun dazanyi batare da saninkaba yanzunma kasawu zanje kuma nasan bazuwa zakaiba konache muje, shiyasa banche mujeba nayi shirina na zuwa nikaÉ—ai " dogon numfashi DON yaja san nan ya jinjina kai yana faÉ—in ok to shike nan nayarda ba komai Allah ya tsare a dawo lfy yayi maganar yana kokarin mikewa kai tsaye stairs É—in yanufa " binshi da ido Aryan yayi har yakurewa ganinsa san nan ya dawo da kallansa kansu Khalid " a nitse yache na wuche " adawo lfy suka masa gaba É—ayansu " san nan face yana amsawa da Amin 

Mikewa Khalid yayi yana faÉ—in Yusuf muje Koh " mikewa Yusuf É—inma yayi zasu wuche waje sukaji Ahmad na faÉ—in wlh akoi abun da kuke shiryawa,  wani harara Khalid ya wurgawa Ahmad batare da sunyi magana ba suka nufi hayar fita palon " kallan Aiman Ahmad yayi yana faÉ—in tabbas yaya Yusuf da yaya Khalid suna shirya wani abun " mikewa Aiman yayi yanufi staircase É—in yana faÉ—in zanyi binchike a kansu ae zan samusu ido sosai yanzu " mikewa Ahmad ma yayi yabi bayan Aiman " dogon tsaki fahad yaja san nan yace wlh yaya Ahmad da Yaya Aiman kunchika gulma ni barima naje na gaida su ammi yayi maganar yana kokarin mikewa " haidar da umar suna ganin fitar fahad suka kwashe da dariya kamar abun haÉ—in baki sai dasukayi mai isarsu, tukun nan suka tsagaita " kasan me haidar da alama fa akoi dirama a gd nan wlh chewar umar " jijjina kai haidar yayi yana faÉ—i babbama kuwa, amma naga alamar yau yaya Aryan nachikin farinchiki sosai bakamar jiyaba " kai dai tashi muje mu gaidasu Abba inmunje É—aki makarisa magana chewar umar a tare suka mike sukayi waje,


Mai martaba Ammi Ummi Aunty amarya  zaune suke a nasu palon suna hira "Fahad yashigo da sallama" amsa masa sallamar sukayi yashigo chiki ya zauna saman sofa ya fara gaida iyayen nasu " da fara'a suka masa "

 

Ummi ta dubi mai martaba tace ranka yadaÉ—e wai yabatun komawar yaran nan bakin aikinsune " shiru Abba ya É—anyi kafin yace bayan zuba sai bayan naÉ—in sarauta " eh hakanma yayi chewar Ammi " aa baiyibakam gaskiya sukoma wajen aikinsu chewar Aunty amarya "  jinjina kai mai martaba yayi yana faÉ—i aa aini ba zaÉ“inku nanemaba bare kufara musu hukunchina kawai nayanke sai anyi naÉ—in sarauta " calmly Fahad yafara magana Abba inasan zuwa Us " da sauri Ammi ta É—ago tana kallansa zatayi magana mai martaba yarigata dachewa sai kayi aure tukun nan dan inbakiyi aureba bazaka sake fita Nigeria ba " baÆ™aramin daÉ—i Ammi tajiba jin amsar mai martaba " Fahad kuwa a razane yace Abba Aure fa kace " eh aure a kache auren wani mugun abune Ummi tabashi amsa rai a bace " bahaka bane Ummi bawai auren ne mugun abuba taya zanyi aure su DON basuyiba " dogon numfashi mai martaba yaja san nan yace ae suma a nayin naÉ—in sarauta, zansa su sufito da mata dan ya isheni ganinku haka " dariya Fahad ya kwashe dashi yana faÉ—in wayyo duniya wayaga DON da mata chab to wai suda ko yanmata basu taÉ“ayiba ai na zasu samo matar " Ammi tace kai banfa san iskanchi kasani ne dasu kake fitane " ae Ammi infaÉ—amiki duk wanda yasan yaya Aryan yaya Prince yaya Yusuf yaya Khalid yaya Aiman yaya Ahmad yasan basuda budurwa kuma basu taba chewa ko chikin wasa sunasan wataba suda ko kalloma mace bata ishesuba " tashi kafita mana a É—aki chewar Ammi " fahad zai sake magana sai sukaji sallamar Haidar da umar " Abba yace yauwa kuzo nan kuma daga yanzu kuje kufara neman matar aure dan wlh bayan naÉ—in sarauta duk aurar daku zanyi na huta " É—aure fuska haidar yayi san nan yajuya yanufi hanyar fita yana faÉ—in inazuwa " salati Aunty amarya tayi kana tace yanzu maganar auren ne tasa kajuya kafasa shigowa koh haidar " haidar dai baibi ta kansuba yayi waje da sauri " da sauri umar ma yajuya yabi bayansa " mikewa Ummi tayi tana faÉ—in kai jama'a zama bai gammuba wayan nan yaran sai na danganasu da É—akin kaba barima naje nafara musu addua tun da sassafen nan yara saikache wadda aljana ta aura, " Mikewa Ammi tayi tace muje tare wlh sai mun haÉ—a da sallar darema dan abun nasu yafara wuche hankali " mai martaba ma yamike yana faÉ—in muje tare dan nima naga alamar sai na haÉ—a da tawa adduar " a tare suka nufi waje Aunty amarya kuwa tamike tanufi É—aki ta haye gado ta kwanta " baki buÉ—e fahad ke kallansu Abba har suka fice afili yace wai muza'awa tsayuwar dare harma da danganamu da kaba yanzu mai mukayi hmmmm baridai naje nafaÉ—awa DON halin da ake chiki yamike ya fito ya haye lifter yakoma sama 


Da sallama yashiga É—akin don kwachi yasameshi a kan makekiyar gadon sa yana latsa waya karisawa chikin É—akin fahad yayi ya haye gadon É—ago kai DON yayi yana kallansa  " kwaÉ“e fuska fahad yayi kamar wadda ya taka kashi " lfy kazo kana bata rai DON ya tambaya " daman kamar jira Fahad yake a tambayesa nan take yafara faÉ—awa DON abun da yafaru a É—akinsu Ummi yanzu " dogon tsaki DON yaja yana faÉ—in to suyi tsayuwar asubama ba na dareba ni dallah tashi kabani waje na daukama wani abinne nine za'achewa na kawo mata aure niÉ—in never wlh babu aure a tsarin rayuwata " da karfin guiwar fahad yamike yafito dan shi a tunaninsa DON zai watsa maganar auren 



 KANO STATE NIGERIA



Misalin karfe 4 na yamma suna zaune a palon Ammi hiyana na karatun qur'ani diyana na game a wayar Zahra " Zahra kuma tana gyarawa amrat gashi " lamrat kuma tana Assessment na English da a kabasu a school kawai sukaji diran motochi gidan jiniya kakeji ta ko ina ya karaÉ—e gidan " diyana tamike tana faÉ—in kodai su Abba ne suka dawo " aa basu bane chewar zahra " hiyana zatayi magana " Zahra tace kutsaya kutsaya naji kamar busan gidan sarautane hakan nanufin Aunty maryam ne tazo tab " da sauri Hiyana ta É—ago tana kallan Zahra wacece Aunty Maryam hiyana ta tambaya tana kallon Zahra " babban yarinyar Aunty amaryan che chewar Zahra " tab wlh tun danaji yarinyar Aunty amarya che nasan muguwache irinsu yaya Aryan  chewar diyana " baki buÉ—e hiyana ke kallanta san nan tace ke diyana nikam taushe zakiyi hankaline haka a kachemiki ita muguwace " da sauri zahra tace aa hiyana diyanafa batayi karyaba tabbas aunty maryam muguwace nabugawa ma a jarida " lamrat tace to Aunty Zahra to daman ina Aunty maryam É—in take " tayi aure ne a gombe  kinsan Aunty amarya yar sarkin gombe ne to yayan Aunty amarya shine yake rike da mulki yanzu yana da babban É—a mai suna Mahmud to Mahmud É—in ne mijin Aunty maryam shiyasa kukaji karan irin busar da akewa Abba idan zai fita ta ko ina ai mijin Aunty maryam É—in shine yarima mai jiran gado " to Aunty Zahra me tazoyi gidan nan yanzu chewar diyana " itakam hiyana baki bude take kallan diyana tana tunani mutun da gidansu amma diyana ke tambayar me yakawota " murmushi Zahra tayi san nan tace ai daman kowani sallah suna zuwa ammafa sai anyi sallah da kwana É—aya suke zuwa " to ai yanzu Sallah sauran kwana 10 meyasa tazo chewar diyana " Zahra zatayi magana hiyana tarigata dacewa zaki iya zuwa ki tambayeta ai meyasa tazo " mikewa Zahra tayi tana faÉ—in kuzo muje mumata sannu dazu kartace munajin zuwanta mun shareta " mikewa sukayi gaba É—ayansu suka bi bayan zahra


Kai tsaye bangaren Aunty amarya suka nufa da sallama suka shiga wasu yan mata guda 3 suka samu da alama kuyangun Aunty maryam ne " yanmatan suna ganin su Zahra suka fara gaidasu " lfy kawai Zahra ta amsa musu dashi san nan  kai tsaye ta wuche tanufi wani É—aki "  su hiyana suka rufa mata baya " sallama zahra tayi a bakin kofar kusan 5 mnt tukun nan a ka amsa tare da izinin shigowa " diyana kam sotake kawai taga wan nan Aunty Maryam É—in " shiga chiki sukayi gaba É—ayansu zaune a gefen gado suka samu Aunty Maryam dukawa kasa zahra tayi tace sannu dazuwa Aunty Maryam ya hanya " ganin Zahra ta duÆ™a yasa hiyana da lamrat da amrat suma suka É—uÆ™a " diyana kuwa tana tsaye " É—ago kai Aunty Maryam tayi tana kallansu itama kamanninta É—aya da Aiman sosai " bata amsa sannu da Zahra tamataba sai daima tsawar data dagawasu diyana ke kuma wacece, wasu kazamai'ne Zahra kika kawomin É—aki  " murya na rawa Zahra tafara magana yan uwa na ne yayan kawuna.." a fusache Aunty Maryam tace get out of my room " da sauri Zahra tamike tarike hannun amrat tana faÉ—in kuzo muje, mikewa hiyana da lamrat ma sukayi suka nufi kofar fita, har sunkai kofa sai kuka juyo sukaga diyana a saye bata ko motsaba " diyana kizo mutafi mana " firgigit diyana tayi alamar dai tunani tashiga maganarsu che tadawo da ita daga duniyar tunani datashiga juyawa tayi tanufesu tana faÉ—in dan kinsamu munzo kaisheki zakiwani che mufita to wlh badan Zahra bama bazuwa zanyiba " what ?  Ke dan uban ki zo nan chewar Aunty Maryam " ba musu diyana ta juya takoma wajen Aunty Maryam É—in " dago ido Aunty Maryam tayi ta kalli su zahra ai tunkan tayi magana Zahra taja amrat sukayi waje hiyana da lamrat suka rufa musu baya " 


dawo da kallanta kan diyana tayi from head to toe take kallan diyana, wayarta ta É—auka ta danna kira jim kaÉ—an a ka daga kiran " kushigo iya abun datache ke nan ta katse kiran ta ajiye wayar  " jim kaÉ—an saika wayan nan Æ´anmatan dasuke palo zaune dazun sun shigo  har Æ™asa suka duÆ™a suna faÉ—in rankiya'daÉ—e kamu " chikin izza danuna isa Aunty Maryam tafara magana kumike ku bugammin yarinyar nan " diyana najin hakan ta watsa a guje tayi waje sukuma yan matan sukabi bayanta " Ajiyar zuchiya Aunty Maryam ta sauke san nan tace ai ko ban tambayaba nasan kune Aunty amarya ke bani lbr kuma danku nazo gidan nan ubanku zakuchi wlh sai kungudu da kafarku kafinsu Abba su dawo 


Diyana kuwa tana fita kai tsaye wajen security tanufa da gudu kai tsaye bayan shahram tanufa ta É“uya yan matan na isowa suma tsaya chirkoh chirkoh " shahram da bajin hausa yakeba sai tambayar diyana yake what happened itakuwa diyana ba wani turanchin kirki takejiba " ganin yammatan suna kokarin kama diyana yasa shahram É—aga musu hannu kana yachiro wayarsa yafara neman layin ogansa " tsayuwa yan matan sukayi shiru sunasan zuwa sukama diyana subuga dan inbasu bugetaba Aunty Maryam zata hukuntasu gashi sukuma suna tsoron sojojin nan ga Shahram fuskarsa babu annuri " shahram kuwa kiran layin Aryan yashiga yi wayar tanata ringing har sai da takusa tsinkewa tukun nan Aryan yayi picking call É—in " a nitse shahram yafara masa bayanin abun dake faruwa chikin harshen turanchi " give har the phone abun da Aryan yache kawai " da sauri Shahram yamikawa diyana wayar, hannu tasa ta amshi wayar tamanna a kunne  tana faÉ—in hello " ajiyar zuchiya Aryan ya sauke yana faÉ—in ae daman nasan ke'che dan duk gidan nan ba mai neman faÉ—a sai ke meya haÉ—aki dasu , suwaye nema " murya na rawa tace wlh yaya Aryan babu abun dana musu kawai dan munje gaishe da Aunty Maryam ne sai tace wai mu kazamaine mufita mata a É—aki shine nukuma nace dan tayi sa'a ma.... Bata karisa maganarba Aryan ya dakatar da ita dachewa ya isa haka bawa shahram wayar mika masa wayar diyana tayi bata san me suka tattau naba sai dai taji Shahram yace let's go  madam " gaba tayi yabi bayanta sukazo suka wuche yammatan " da sauri yammatan suka juya zasubi bayansu shahram ya dakamusu tsawa bashiri suka tsaya, har bangaren Ammi shahram ya kai diyana san nan yajuya yakoma bakin aikinsa  "

 yan matan kuwa jiki na bari suka juya suka koma inda suka fito chike da zullumin hukunchin da Aunty Maryam zata musu dan basu bugi diyana ba da sallama suka Shiga É—aki waya suka samu Aunty Maryam keyi duÆ™awa sukayi gaba É—ayansu a kan guiwowinsu suna jiran hukunchi " bayan tagama wayarne ta ajiye wayar a gefenta afilli take faÉ—in bazanyi jayayya da kaiba Aryan amma kuma a chikin ruwan sanyi zan dafa yaran nan,  dankuwa Aunty amarya bata sonsu suna sata baÆ™in chiki nikuma duk abun da zaisa Aunty amarya baÆ™in chiki bana sonshi, kuma dole na kawar mata dashi shiru ta É—anyi san nan tadubi yanmatan tace kutashi kutafi , " mamakine yaka masu mikewa sukayi suka bar É—akin suka koma palo suka zauna


A bangaren diyana kuwa shahram na shigar ta ita É“angaren Ammi ta kwasa da gudu tayi chikin palo kai tsaye É—akinsu tanufa ba ko sallama tashige " Zahra na ganinta tamike tana faÉ—in bata bugeki bakoh diyana " dariya diyana tayi san nan tashiga basu lbr abun dayafaru " ajiyar zuchiya hiyana ta sauke san nan tace kai Allah yayiwa yaya Aryan albarka kekuma sai ki kiyaye bakinki " shiru diyana taÉ—anyi kamar mai tunani " Zahra ta dafata tana faÉ—in to tunanin me kuma kike diyana " dariya diyana tai san nan tache ina tunanin yau wache rana yaya Aryan yayi abun arziki  " tsaki hiyana taja san nan tace ni kunga tafiyata lokachin shirya abun É“uÉ—a baki yayi tana kaiwa nan tafice " mikewa su lamrat sukayi gaba É—ayansu s Yanzu wasan zai fara k


Pls more comments an share

No comments