Recent Updates

Duk Karfin Izzata Book 1 Paga 13

 


Episode 13 14 15*

           

Tana ganin jabir ya É—aga hannun zai mareta tafasa kara tafaÉ—i kasa tana birgima kamar mai aljanu " bashiri jabir ya jabirki ya tsaya yana kallo ikon allah " da sauri su hiyana sukayi kanta suna kiran sunanta " chikin tsawa diyana ke magana ni basunana

diyanaba ni sunana bilkisu, ha,ha,ha ta kwashe da dariya " a tsorace Zahra ke faÉ—in munshiga uku yaukam me kuma yasamu diyana " hiyana kam ko ajikinta dan tasan iskanchin diyana yawuche hakan " chikin tsawa diyana tace kai jabir zo nan ai nafaÉ—amaka daman niche zanyi magananin'ka " jabir najin haka ya kwasa aguje  yabar wajen  " Zahra kam tagama tsorata baya baya tafara jaa tana salati " hiyana lamrat amrat kuwa ko ajikinsu saboda sunsan halinta daman " diyana naganin jabir ya gudu tamike tana faÉ—in nizakawa iskanchi wlh nafika iyawa muzuba mugani ae kai karamin É—an iskane " a sukwane Zahra tamike tana kallon ikon allah " mekuma kuke kallona haka chewar diyana tayi maganar tana kokarin mikewa, bayan tamike tsaye ta dubi su hiyana tace sai kutashi mutafi class ae tun da É—an iskan ya gudu,

 hanyar class nasu tanufa abunta tafiya take hankali kwanche, hartakai kusa da class nasu saikuma ta juyo yadda tabarsu haka tajuyo ta gansu ko motsi basuyiba Sun zuba mata ido " murguÉ—a baki tayi kana tace kuchigaba dazama allah yasa yadawo yasameku nikam kunga shigana class tana gama faÉ—in haka tasa kai tawuche chikin class nasu abunta 


Hiyana ta mike taje ta dafa Zahra tafara magana Aunty Zahra naga kin tsorata to wlh indai diyana che kaÉ—anma kika gani dan wlh abun dayafi wan nan zata aikata " dogon nunfashi zahra taja haÉ—e da sauke nauyayyar ajiyar zuchiya kana tace yanzu hiyana kina nufin kichemin ba aljanubane sukayi magana yanzu diyana che,  kuma yanzu diyaya ita ta iya zama ta shirya wan nan wasan kwai kwayon " shakka babu Aunty zahra duk abun da kika gani shiryashi diyana tayi ba gaskiya bane chewar hiyana " shiru Zahra tayi tana tunanin itafa lamarin diyana yafara bata tsoro tayi nisa chikin tunani taji, lamrat ta taÉ“ata tana faÉ—in Aunty Zahra muje dan idan kika biyewa Aunty diyana wlh yau bazaki shiga class ba jiki ba kwari Zahra tafara tafiya tana faÉ—in yanzu idan jabir yaganefa " wan nankuma matsalarsu, che shida diyana tunda ita tamasa chewar hiyana " lamrat kuwa chewa tayi wlh ninasan ko jabir yagane Aunty diyana zata nemawa kanta mafita " ajiyar zuchiya Zahra ta sauke san nan tace to shike nan allah ya karemu gaba É—aya tayi maganar tana kokarin shiga class nasu sai anjima sukawa juna hiyana ma tawuche nasu class É—in suma su lamrat kowache tawuche class nasu 


Karfe 3 na rana anbuga bell na tashi gaba É—aya É—alibai sun fito suma su hiyana sun haÉ—e kansu suka nufi wajen dasuke tsayawa sunajiran drivers nasu,  suna tsaye suna yar hirarsu sai ga faria ma da fara'a suka gaisa da hiyana dakuma diyana lamrat da amrat kuma suka gaisheta ta amsa da fara'a " daga bayansu sukaji an daka musu tsawa, a na faÉ—in  ke nizakiwa karyan aljanu koh to wlh yau sai kin gommace da'baki zo duniyar bama da sauri gaba É—ayansu suka juya " diyana zatayi magana sukaji jiniyar motochin É—aukansu  " hiyana na ganin motochin É—aukar'su, batasan lokachin datache alhamdulliah ba " Zahra kuwa tun motochin basu gama parking ba ta zura a guje tabuÉ—e kofar motar tashiga tana sauke ajiyar zuchiya " lamrat da amrat ma motar'su suka nufa da sauri sukabar hiyana da diyana tsaye awajen " jabir naganin motochin'su yaju yabar wajen yana faÉ—in zamu haÉ—u gobene wlh zakisani inna rikeki "  diyana naganin jabir ya tafi ta murguÉ—a baki tana faÉ—in kadaÉ—e baka dau matakiba wlh É—an rainin wayyo zanyi maganinkane allah yakaimu goben kagani nidakai wazaiyi winner " baki buÉ—e hiyana ke kallan diyana tana tunani a chikin zuchiyarta wai diyana kam bata da tsorone a rayuwarta " tayi nisa chikin tunaninta tajiyo muryan diyana na faÉ—in to kekuma me yatsayar dake inbazaki zoba saimu tafi mubarki da jabir É—in " mamakine yakama hiyana wai yaushe diyana ta barwajen nan jiki ba kwari tanufi motar drivers É—in na tsaye suna kallonsu sunasan tambayatsu lfy amma suna tsoro dan hakan bata shafi aikinsuba " hiyana nashiga motar suma drivers É—in suka koma chikin motar suka tayar da' gudu sukabar makarantar.



Yau kwana biyar ke nan datafiyar su mai martaba Umrah


SAUDIA



Misalin karfe 10 na dare Aryan Aiman yusuf Ahmad Khalid suna zaune a palon hotel É—in da suka sauka hirasuke gaba É—ayansu ban da Aryan daya zauna shiru kamar bashi a É—akin " Khalid ne ya É—an taba shi " a É—an firgiche ya É—ago ash eyes É—in nan nasa yana kallan khalid " lfy meke damun ka gaba É—aya naga kamar mood naka ya chanza chewar Khalid " iska mai zafi Aryan ya fuszar daga bakinsa kafin yasoma magana babu komai kawai inatunanin intashi inje induba prince ne naga wunin yau shiru banji motsinsaba  " satar kallan yusuf Khalid yayi san nan yace ok to kaje kadubashi mana " mikewa Aryan yayi yanufi staircase É—in ya haura sama "  murmushi Yusuf yayi yana kallan Khalid " harara  Aiman ke wugawa yusuf tare da faÉ—in me kuke kullawa " shima Yusuf yadawo masa da harara yana faÉ—in mekuma zamu kulla " tsaki Aiman yaja san nan yamike yana faÉ—in zakusani dai kubi a hankali dankuwa idan ta kwaÉ“e muku kunsan sauran " kallan sama da kasa Khalid yawa Aiman san nan yaja tsaki yace. To kayi rashin sa'a nine babba ba kaine babba a kainaba dazaka tsaya kana faÉ—amin zanchen banza ni wuche kabani waje hai " tsaki Aiman yaja san nan ya wuche yanufi staircase É—in " dawo da kallansa Khalid yayi kan Ahmad dake zaune ya zuba musu ido to kaima mekake jira dabaka'wuche kabi husainin nakaba  " dariya Ahmad yayi san nan yace gulma natsaya jimana ai yau munraba gari da husainin nawa dannikam sainaji gulmar " Khalid bai sake maganaba sai daima yachiro wayarsa yafara neman layin Zahra " wayar nafara ringing yamike yana chewa Yusuf kasameni a É—aki san nan yawuche  " mikewa Yusuf É—inma yayi ya kyale Ahmad awajen yanufi staircase É—in shima kai tsaye É—akin Khalid yanufa da sallama yashiga zaune yasamu Khalid yana waya da zahra,  hannu kawai Yusuf yasa ya amshi wayar kana yasa akunnensa yana jiyo hayaniyar, kannen nasu " ina my baby abunda Yusuf yace da zahra ke nan " da sauri zahra tace gatanan tamikawa lamrat wayar " hello yaya Yusuf ina wuni " lunshe ido Yusuf yayi san nan yabuÉ—e yana faÉ—in lfy my baby ya school " alhamdulillah lamrat tabashi amsa " shiru yaÉ—anyi kafin yafurta tsarabar me kikeso inkawo miki " babu komai yaya Yusuf Allah dai yadawo daku lfy shine fatanmu chewar lamrat " bakaramin daÉ—i Yusuf yajiba azuchiyarsa yafa tunanin yarinya karama da hankalin manya yana chikin tunani yajiyo muryarta tana faÉ—in allah yaya Yusuf kewarka nake sosai da sosai  " sake lunshe ido Yusuf yayi yana murnushi farinchiki kasa kasa yace my baby nima nayi missed naki sosaifa " a shagwabe tace to yaushe zaku dawo " Yusuf zaiyi magana Khalid ya amshi wayar yana faÉ—in inyamaka zafi kasaya mata nata wayar yayi maganar tare da mikewa yanufi waje  " murnushi Yusuf yayi san nan yafurta nice idea yana gama faÉ—in haka ya haye gadan Khalid yayi kwanchiyarsa


Khalid kuwa yana fita kai tsaye É—akin Aryan yanufa da sallama Khalid yashiga Aryan baya É—akin dan haka khalid yafito yanufi É—akin DON da sallama yashiga zaune yasamesu kan kadon,  suna fuskantar juna da alama  magana mai muhim'manchi suke " jin sallamar Khalid yasa dukkansu suka juyo suna kallansa " Æ™arisa shiga chikin É—akin Khalid yayi shima ya haye gadan ya zauna a nutse yafara magana 

Aryan wai meke damun kane naga gaba É—aya yau ka chanza ne gashi ka É—an rame kamar baka da lfy chewar Khalid " daga  green eyes nashi sama DON yayi kamar mai kallan wani abu kamar kuma mai tunani  " zuba mishi ido Aryan da Khalid sukayi suna kallansa " jimkaÉ—an ya sauke kansa tare da furzar da iska daga bakinsa ya tsare Aryan da ido sosai yake kallansa " nantake Aryan ya mike kamar mara gaskiya yana kokarin sauka daga gadon kamar daga sama yaji muryan DON yana faÉ—in me kake É“oyemin ashe akoi abunda bai kamata nasaniba a dangane da kai,  kodai matsayina bai kai bane " jin maganar DON yasa Aryan saurin juyowa yana kallansu shiru yaÉ—anyi kafin nan yace. Taya kake tunanin akoi abun da zan boyemaka dangane dani kai'nefa ni kuma nine kai SO bawani abun boye boye a tsakaninmu wlh kawai bana jin daÉ—ine ni kaina bansan meke damuna ba kwata kwata nakasa samun nitsuwa " shin akoi wani abu mai mahim manchin daka rabu dashine dazaisa kakasa nitsuwa DON yajefo ma Aryan tambayar bazata " aa nikuma ina dawani abu mai muhim'manchi dayawuche kune ai kune kawai masu muhim'manchi a rayuwata " Khalid dai ido kawai yake binsu dashi yadda suke maganar burgesa suke DON akoi kokolwa sosai akoi basira Aryan kuwa akoi wayau sosai shiyasa haÉ—in nasu yake bada chitta " barchi nakeji kaina chiwo yake min zanje na kwanta chewar Aryan yayi maganar tare da juyawa yachigaba da tafiya har yakai bakin kofa sai yaji muryan DON yana faÉ—in idanma baka faÉ—amin yanzuba nasan dole gaba zanji ai " shiru kawai Aryan yayi bai tankaba saima kara sauri dayayi yabar É—akin 


Dawo da kallansa DON yayi kan Khalid yana faÉ—in akoi abun dake damun É—an uwana tabbas ba lfy yakeba " murmushi kaÉ—an Khalid yayi a zuchiyarsa kuwa yace baridai ya É—an latsa DON yaji yazasu kare ajiyar zuchiya ya sauke san nan yadubi DON yace kasani kodai yafaÉ—a soyayyane " a zafafafe DON yace what ?  hauka yakene kataÉ“a ganin yana magana da watane ma NO hakan ma bazai yuwuba " mamakine yakama Khalid ganin daga maganar mace DON ya sauya kamar bashiba " nantake ya kara É—aure fuskar nan kamar baisan me dariyaba Khalid yayi nisa chikin tunani muryan DON takatse masa tunani "  Khalid i said  get out  " kallon DON Khalid yake da mamaki ba musu ya sauka daga gadan dan yasan halin DON yanzu idan yace zai biye masa sai abun yakai'su ga É“achin rai " fitowa Khalid yayi daga É—akin DON kai tsaye yanufi É—akin Aryan 


Da sallama yashiga zaune yasamu Aryan a tsakiyar gado " ba karamin mamaki Khalid yayiba ganinsa zaune karisawa chikin É—akin yayi ya zauna a bakin gadon " sai lokachin Aryan ya juyo yana kallansa " lfy bakayi barchiba aryan Khalid yajefo masa tambaya " iska mai zafi ya furzar daga bakinsa calmly yafara magana nasaba da shan coffee kafin nayi barchine Khalid dazun nayi order coffee sun kawomin amma É—an É—anon bai minba kwata kwata na gida nake buÆ™ata shiyasama kaga nakasa barchi " hannu Khalid yasa a aljihun wandansa ya É—auki wayarsa yafara kiran layin zahra dan kuwa yanzu yagane matsalar Aryan " bugu É—aya Zahra ta É—aga tana faÉ—in yaya Khalid É—azun muna hira ka gudu " yanzu me kuke bakuyi barchiba Khalid yajefo mata tambaya " karatu mukayi amma yanzu zamu kwanta ai  tabashi amsa " ok ina diyana " gata nan inbatane chewar Zahra " eh bata yayi maganar tare da mayar da wayar a H-free  " ansar wayar diyana tayi chikin voice kamar mai jin barchi tafa magana yaya Khalid shine baka nemeniba tun É—azun inajin kana magana dasu zahra inasu Ammi " suna lfy allah sarki na mantane amma ai gashi yanzu na nemeki Koh " yauwa yaya Khalid daman inasan in'tambayeka chewar diyana " ok tambayi " wai a chan makkan wake kaiwa yaya Aryan coffee " jin tambayar nata yasa Khalid É—ago ido yana kallan Aryan shima Aryan É—in shiyake kallo " dawo da kallansa Khalid yayi kan wayar san nan yace bari nabawa yaya Aryan É—in sai ki tambayesa Koh bai jira amsar taba yamikawa Aryan wayan " ba musu yasa hannu ya karÉ“i wayar yana sauke ajiyar zuchiya " Khalid na mika masa wayar ya mike yace kuyi magana inazuwa yana gama faÉ—in hakan yafiche daga dakin da sauri yana murmushi


Calmly Aryan yafara magana hello " ina wuni yaya Aryan chewar diyana " wani murmushi Aryan yayi kafin tace lfy y school " alhadulillah tabashi amsa " good yace saikuma sukayi shiru dukkansu " chankuma sai diyana tace yaya Aryan wayake kawo maka coffee a makkan " murmushi ya É—anyi kafin ya burta babu kowa " yanzu ke nan bakashan coffee É—in " eh bana sha yabata amsa a takaice " Allah sarki da ina nan dana rinÆ™a kawoma ai " Aryan baimasan san da dariya ta kubche masaba dan yadda ta furta Allah sarki bakaramin dariya tabashiba amma sai ya danne dariyar yace ashe kinaso na bansaniba ashe kina tausayina " aa bana sonka inadai tausayinka chewar diyana " to meyasa bakisona  " shiru ta É—anyi san nan tace kai'ma ai bakasona ne shiyasa nima bansanka " to wayace maki ni banasonki  " Allah yaya Aryan basai anfaÉ—aminba ni da kaina nasani baka sona dan inkana sona bazakache zaka harbeni da bindiga namutu kowa yahutaba " shiru yayi yana tunanin sai yanzu yagane kuskurensa namata barazana da hakan shi yamata chikin wasa itakuma ashe tarike a matsayin gaske yayi nisa chikin tunani sai yaji tana faÉ—in yaya Aryan sai da safe su zahrafa har sunyi barchi sun kyaleni " ok kawai yace da ita san nan ya katse kiran ya ajiye wayar a gefe ya kwanta  bajimawa barchi tayi awon gaba dashi


Lokachin da Khalid yadawo ɗakin dan karɓar wayarsa yasamu aryan yayi barchi murmushi yayi a'fili yafurta ai daman ninasan meyahanaka barchi kai da kanka kake neman kashe kanka anfaɗa maka SO wasane ganin Aryan yana ɗan motsi yasa Khalid ɗaukan wayarsa da sauri yayi waje yana murmushi



Washe gari dawuri suka tashi sukayi shirin zuwa school kamar yadda suka saba haka suka fito yauma kai tsaye wajen motochinsu suka nufa da gudu drivers É—in suka karaso wajen budemusu motochin drivers É—in sukayi

Su diyana Suka shiga suna shiga drivers É—in ma suka shiga da gudun gaske suka tada motochin suka bar gidan gudu suke sosai chikin kan kanin lokachi suka isa school É—in awajen dasuka saba parking sukayi yauma fitowa su hiyana sukayi suka jera zuwa wajen tsayuwa suyi hira kafin a shiga class " drivers kuma suka shiga motochin suka juya suka koma gd 


Tsayuwa sukayi kamar dai jiya Suna hirar'su daga bayansu sukaji andaÆ™a musu tsawa " ke zonan ni jiyazakiwa karayan aljanukoh to wlh sai kinyabawa aya Zakinta dan yau saina babbalaki a school É—in nan " gaba É—ayansu suka juya ganin jabir yasa Zahra ta kwasa da gudu abunta tayi hanyar class nasu " diyana kuwa tsayuwa tayi kamar mai tunani ta harÉ—e hannu a kirji babu ko alamar tsoro a tattare da ita " hiyana kuwa juyowa tai ta dubi' su lamrat kasa kasa tace musu kuje class " a tare suka juya suka nufi class " jabir ganin alamar diyana ko tsorata batayi ba dajin maganar da yayi yasa ya nufeta gadan gadan ya duncle hannu zai kai mata naushi da sauri...✍️✍️



No comments