Duk Karfin Izzata Book 1 Paga 10
*Episode 10 *
Yau saura kwana 1 a É—auki azumi " zaune suke gaba É—ayansu yan matan a Palon Ammi hiyana da zahra suna karatu" diyana kuwa ta tasa fruits a gaba sai chi take " amrat da lamrat suna kallo film É—in ganga a tashar zee wold " dukkansu yau kaya iri É—aya sukasa
doguwar rigar atampha che wadda Aunty farida ta aikomusu daga maiduguri dukkansu da É—an kwali a kansu amma banda diyana " itakam tasaki gashi har gadan baya saifamam tura fruits take " Ammi che tafito daga betroom É—inta shigo tsakiyar palon, baki buÉ—e take kallan É—iyanaKe kirika chi a hankalimana bafa guduwa zaiyi yabarkiba ko saikin kwarene chewar Ammi " dariya diyana tayi sosai san nan tace kai Ammi gobefa zaa dauki azumi shiya nake chi dayawa dan kinga daga gobe babu É—ure É—ure dayawa baki zai rufu " Ammi tace aa lallai hausa ta zauna abakinki yanzukam eyeee wato baki zai rufu koh, to kichi a hankali inbahakaba chikinki zaiyi chiwo nakira yayanku Aiman yazo yamiki allura " dariya diyana tayi tana faÉ—in haba Ammi nifa soja che ai bana tso....bata karira maganarba idanta yasauka chikin nashi tsaye yake a bakin kofar palan yaÉ—an jingina da jikin kofar ya harÉ—e hannu a kirji jikinsa sanye da kayan barchi riga da wando masu laushi sky blue " da sauri tamike tana faÉ—in dan allah kayi hakuri yaya Aryan wlh na mantane yanzu zan haÉ—oma " shiru yayi kamar bai ji me tacheba baikuma mutsa daga inda yake tsayenba " Ammi tajuyo tabi inda diyana ke kallo tana magana ganin Aryan yasa Ammi tafahimchi akan me diyana ke magana " Aryan bakayi barchibane chewar Ammi " shiru yaÉ—anyi kafin yace eh banyiba " daki Ammi tanufa tana faÉ—in sai da safe, Ammi na shiga É—aki " Aryan ya dubi su zahra a nitse yake magana me yahanaku kwanchiya " aitun bai kai karshen maganarba suka mike har suna rige rige shiga É—aki "
diyana kuwa zuwa tayi taraɓa ta gefensa zata wuche tafita dan taje ta haɗa masa coffee ɗin " hannu yasa ya dauki gashin kanta ta baya yajawota da karfi " kware baki tayi zatayi ihu yasa hannu yarufe mata bakin, ya zaro manya manya idan nan nasa gasu ash colour " diyana kamar zatayi fitsari saboda tsoro ga zafin da kanta ke mata " calmly yasoma magana ban hanaki zama ba ɗan kwaliba, meyasa bakyajin magane eh wlh idan kika bari nasake ganinki babu ɗan kwali Allah sai namiki bugun mutuwa " hawayene yasoma zuba daga idanta saboda zafin datake ji na gashinta daya rike gashi ya tosha mata baki bahalin tarokesa, sai faman girgiza kai kawai take, " nabaki 2 mnt kikawomin coffee ɗaki wlh idankika haura 2 mnt zaki sani yana gama faɗin hakan yasake mata gashinta yajuya yanufi hanyar fita,
Diyana naganin yatafi tace allah ya isa na mugu kuma baza'a sa dan kwaliba ta murguÉ—a baki kana takama hanyar saukoh'wa " saukoh'wa tayi tanufi kichin a gurguje ta haÉ—a coffee ta fito tanufi bangarensa " da sallama a'bakinta tashiga palan baya palo kai tsaye betroom É—insa tanufa
Zaune a bakin gado tasamesa yana rike dawaya da'alama wani abu yake kallo har gabansa tazo ta duƙa tache yaya Aryan gashi " hanu yasa ya karɓi cup ɗin ya ajiye a gefe " tamike zata tafi batayi auneba taji saukar mari afuskarta a razane yajuya zata gudu da sauri ya damketa " kana yahaɗe han'nunwan'ta duka biyu yarike da hannunsa ɗaya " ya ɗaga ɗayan hannunsa yaƙara mata mari " kware baki tayi zatayi ihu " a zafafe yace idan kika buɗemin baki saina harbeki da bindiga kimutu kowa yahuta " jin an ambachi bindiga yasa diyana tayi tsit " nisa'ar wasankine eh nizaki'chewa allah ya isa, lallai yarinyar nan to waima menamiki na mugunta dazaki chemin mugu " murya na rama tasoma magana dan allah yaya Aryan kayi hakuri wlh bazan sakeba nashiga uku Ammina " kimin shiru wlh kona babbalaki yimin nill down a nan ko ranki ya ɓachi yana gama faɗin hakan yasaki hannunta
Nill down tayi tana hawaye "
daukan coffee É—insa yayi yafara sha abunsa itakoh sai hakaye take " bayan yagama shan coffee É—inne ya dubeta yace ke wato bazaki sa dan'kwalin bako nayi dik abin da zanyi koh to kuwa zanyi shima zan É—au mataki a kai tashi kitafi kibani waje " tun bai karasaba tamike tafita da gudu tayi bangaren Ammi " dogon tsaki yaja san nan yamike ya kwata
Diyana nashiga tasamu su zahra sunyi barchi, tafaÉ—a kan gadansu tachi kukanta mai isarta abunta dahaka har barchi ya dauketa
Karfe 4 na asuba gabaÉ—aya family sun haÉ—u a palo danyin sahur amma banda don abinchi sukechi chikin kwanchiyar hankali " Khalid ya dubi diyana dake zaune shiru sister meyasameki a fuska waye yamareki " satar kallan Aryan tayi kasa tace babu wanda yamare nikam ba amareniba " gaba É—aya idan mutanen palon yadawo kanta " mai martaba yace. aa diyana anfa mareki baga shatin yatsu biyar a kan fuskarkiba waya mareki " kasa kasa take satar kallan Aryan, wanda shi ko ajikinsa kamar baima san ana magana a wajenba kara É—aure fukar nan yayi " kuka tafasa mai karfi tana faÉ—in wlh ni bawanda yamareni " mai martaba daya zuba mata ido yaga yadda take satar kallan Aryan yagane daga ina matsalar tafito dan haka sai yace, shike nan it's ok nayarda ba wanda ya mareki kinji " hiyana keda Zahra kuje kukaiwa prinse abinchin sahur nashi É—aki chewar Ummi " to Ummi sunfaÉ—in hakan suna kokarin mikewa " dukkansu jiki sai rawa yake saboda tsoro kichin suka wuche dan shirya masa abinchin
Da sallama suka shiga palon zaune suka samesa kan doguwar kujera da alama abinchin yake jira " batare daya amsa sallamarba ya daka musu tsawa meyakawoku É—akin nan " Zahra najin hakan ta ajiye tea dake hannunta ta watsa a guje tayi waje " hiyana ma zata gudu, " yace ke idan nasake ganin kafar wata a bangarena wlh kaÉ—an zanrageku " ai yana gama faÉ—in hakan ta ajiye abinchin itama ta watsa a É—ari takoma palan mai martaba
Tana shiga tasamu Zahra zaune abunta kamar batare sukajeba, zama itama tayi suka chigaba da chin abinchinsu, bayan sun gamane mazan suka mike zasuje suyi arwallah " mai martaba yace Aryan anjima kazo kasameni a fada inada magana da kai " juyowa Aryan yayi yana kallan mai martaba " harara mai martaba ya watsa mashi shima yamike yanufi É—akinsa " shiru Aryan ya tsaya kamar mai tunani saida Khalid yaja hannunsa suka fiche " su diyana ma suka mike suka fita sukayi É—akinsu danyin sallah
Tun karfe 6 hiyana ke kukan chiwon chiki tun su Zahra suna chemata sorry har suka fara tsorata dankuwa chiwon gaba gaba yake sosai " da gudu Zahra ta fito tayi dakin Ammi, kwanche tasameta tana barchi, hayewa gadan Zahra tayi tana kiran su nanta, " a ɗan firgiche Ammi tamike " Zahra,u lfy kike min irinwan nan kira yabakuyi shirin zuwa school ba " Ammi kiyi sauri kizo wlh hiyana bata da lfy kuma tache zata mutu wayyo, " aitunkan Zahra takarisa maganar Ammi tayi waje da sauri " yadda Zahra batar hiyana haka Ammi ma tazo tasameta, saima karuwa da chiwon yayi " subahanallah Zahra,u daukoh min wayata a daki bari naki Aiman yazo yadubata chewar Ammi " dagudu Zahra ta juya tanufi daki ta ɗaukoh wayar ta kawowa Ammi " Ammi na karɓa tafara kiran layin Aiman " ringing ɗaya ya ɗaga tare dayin sallama " aruɗe Ammi take faɗin ina kake pls kazo kadubatmin hiyana batada lfy " subahanallah meke damunta Aiman ya tambaya " wlh inaganin chiwon chikine gashi madai bata a hanyyachinta ammi tabashi amsa " wlh Ammi bana gida kuma naɗanyi nisama amma kikira Aryan ko don suna gida aisu "
da sauri Ammi ta katse kiran tafara neman layin don yana chikin barchiyaji wayarsa na ringing hannu yasa yana lalubar wayar har allah yabashi sa'a ta dauki wayar picking call É—in yayi yamanna wayar a kunne " aruÉ—e Ammi ke faÉ—in inakake kazo kadubamin yarinyar nan kartamutu " jin muryan Ammi aruÉ—e hakan yasa ya buÉ—e ido da sauri kana yamike daga zaune,
Meyafaru Ammi yanaji kina magana a hargitse " nache kazo kadubamin kanwarkan nan bata da lfy koh chewar Ammi " don yace to Ammi wai ina Aiman nifa ba aikina bane kawai ina tabawane dan allah kikira Aiman ko, kukaita asibiti " rai abache Ammi tace nikake faÉ—awa ba aikin kabane mu kaita asibiti koh bata jira amsarshiba ta katse kiran " tana katse kiran
takira Aryan, lokachin da Ammi takirasa yana kwanche amma idansa biyu baiyi barchiba da alama kuma tunani yake kiran Ammi nashigo ya dau wayan yana ganin su nan my Ammi yabayyana a' kan screen É—in da sauri yayi picking call yasa wayar a kunne yace hello " aruÉ—e Ammi ke faÉ—a masa abun dake faruwa " a nitse yace Ammi ki nitsu pls gani nan zuwa tun bai katse kiran bama yamike yanufi hanyar fita " jikinsa sanye da jallabiya baki
Da sallama Aryan yashiga palon Ammi babu kowa shiru ya tsaya yana tunanin to ta'inama betroom É—insu,yake saikuma yachiro wayarsa yakira Ammi bugu É—aya ta tauka gani a palo abun dayache ke nan " saiga Ammi tafito aruÉ—e tana faÉ—in gata anan dan allah kayi sauri kadubamin ita " Ammi karki damu kinji ki kwantar da hankalinki muje " Ammi tayi gaba yabita abaya shikuma hiyana sai juyi take a kan gado tana kuka, diyana na zaune a gefenta itama kukan take zahra amrat lamrat duk suna tsaye a kansu "
yana shigowa kallo É—aya yayiwa hiyana yagane matsalar dan haka sai yajuyo ya kalli su Zahra " da sauri zahra takama hannun amrat tana faÉ—in kuzonuje palo " hanyan fita sukakama har sunkai bakin kofa Zahra ta juyo tace diyana kizo mutafi " chikin kuka diyana tache wlh babu inda zanje komai zai faru da hiyana sai dai yafaru damu tare " zahra jin diyana tafaÉ—i hakane yasa takama hannun amrat suka wuche palo lamrat ma tabi bayansu " ke tashi kije É—akina ki daukohmin first A box yayi maganar yana kallan diyana dake zaune tana sharban kuka " mikewa tayi tafita da sauri " Ammi ta dubeshi tace meke damunta " babu bawata babbam matsala bane yanzu idan namata allura shike nan " to shike nan barinaje nakawo mata tea tunda azumi kam dole ta ajiyeshi chewar Ammi ,batare da tajira amsarshiba tafiche da sauri
Abangaren don kuwa Ammi na katse kiran yadafe kai yana faɗin why why Ammi meyasa kikeson jamin raini awajen yaran nanne meyasa kika damu dasu sosaine yanzu gashi kina ɓata ranki abanza kai wayyo allah na yanzu dai yazamamin dole naje naduba yarinyar nan inba hakaba nasan Ammi bazata huche dawuriba, dogon tsaki yaja san nan yamike yanufi toilet
Wanka yayi a girguje san nan yafito bai tsayayin wani shiriba yazura farar jallabiya yafito dan kar Ammi tayi fushi, kai tsaye ban garen Ammi yanufa, yanashiga palo yasamu su Zahra nantake suka fara gaidashi, É—aure fuska yakarayi bai amsa gaisuwar'tasuba sai yace ina mara lfy take " da hannu zahra tamasa nuni da hanyar É—akinsu " juyawa yayi yanufi É—akin kodaya shiga tsaye yasamu Aryan a bakin gadan " a nitse da murya kamar mai jin barchi don yace kadubatane Aryan " dawo da kallansa Aryan yayi kan don yana faÉ—in aa zandai dubata yanzu allura zan mata " to kamata mana mekake jira chewar don " Aryan yace É—ayan tatafi kawomin box na magungun ne " ok to ni bari nawuche tunda zaka dubata " Aryan yace jirani muwuche tare daman inasan magana da kai " shiru kawai don yayi batare dayasake chewa uppan ba ya gyara tsayuwarsa "
Da gudu diyana tashigo ɗakin sai haki take " karbar box ɗin aryan yayi yanufi kan gadan " sai lokachin hiyana tabude ido dan jin mutun akusa da ita " haɗa alluransa yake hankalinsa kwanche bayan yagamane ya dubeta yache gyara namiki " a' sukane hiyana ta juyo takalli allurar san nan ta kalli fuskar Aryan taga babu alamar tausayi " da sauri tamike tana kokarin sauƙa " don dake tsaye ya daga mata tsawa inakuma zakije nan take ta ruga tarungume diyana dake tsaye " dukkansu suka fashe da kuka " abunma har dariya yaso yabawa Aryan " awan nan hali Ammi ta dawo ɗakin tasamesu
mamakine yakama Ammi ganin Aryan a bakin gado zaune rike da allura a hannu, gakuma hiyana mara lfy rungume da diyana suna kuka, ga don a tsaye fuska a turnuke, lfy meke faruwa Aryan kamata alluran'ne, Ammi ta tambaya " aa Ammi taki tsayawa chewar Aryan " juyowa Ammi tayi ta kalli su diyana kana tace kizo Amiki alkuran kisamu lfy koh " chikin kuka hiyana ke magana, aa Ammi wlh nikam a barni gara namutu wlh da amin allura " ajiye kofin tea É—in Ammi tayi a kan drawer san nan tadubi don tace rikemasa ita yamata alluran nan dan nalura bazata tsayaba " hiyana jin anfaÉ—in hakan tafasa kara ta zura a guje zatayi waje " taku É—aya don yayi ya damkohta yaÉ—agata sama sai kan gadan sai faman wurga kafa da hannu take sama taki tsayawa " aguje diyana ma tayi kan gadan itama suka sake rungumar juna " mamakine yaka don da Aryan yara kaman wasu chingam "
Ammi dai chewa tayi barina natafi ai dankuna kallonane inbaku ganniba kila kuji tsoron yayyunnaku tadubi don tamasa magana chikin harshen turanchi, karkamusu tsawa sosai kaga bata da lfy kabisu a hankali, dayake su diyana basa jin turanchi, bayan Ammi taga fadawa don hakan tajuya, tace to gaku ga yayanku inbaki tsayaba ya bugeki baruwana ,natafi tana gama faÉ—in haka tafiche,
Aryan yaɗago yana kallan don irin kallan me abunyi yanzu " kan kadan don yanufa yana zuwa yasa hannu yakamo hiyana yakuma dakawa diyana tsawa ke sauka, jiki na bari ta saukoh tana kuka " haɗe hannun hiyana don yayi ya matse san nan yache da Aryan kayimata allurarmana kana kallona " murmushi kaɗan Aryan yayi kana yace haka akerike wadda za'awa allura ka gyaramin ita da kyau pls " harara don ya wurgawa Aryan san nan yajawota jikinsa ya rungumeta sosai ya dauke fuska daga kallon Aryan yakara ɓata rai " Aryan kam abunma dariya taso bashi amma ya matse dan kar don yache bazai riketaba kuma inbasu mata alluraba Ammi bazataji daɗin ba " kawo hannunki chewar Aryan " hiyana kamar bataji me yache ba taki bada hannu " kallan don yayi san nan yache mikomin hannunta " a'fusache ya damki hannunnata ya mikawa Aryan " rike hannun Aryan yayi sosai dan sai mutsu mutsu take taki tsayawa
Aryan natsira mata allurar ta pasa kara ta kankame don tana faÉ—in wayyo allah Ammi kasheni zasuyi " da gudu diyana ta dawo kan kadan ta zauna kusa da hiyana " Aryan na zare allurar " don yana sakinta yamike da sauri yabar É—akin,
Shima Aryan É—in daukan box nashi yayi yabi bayan don " hiyana kuwa kuka take sosai sai rarrashinta diyana take " Zahra na ganin su Aryan sun fita tashigo É—akin da gudu
Don nafita daga bangaren Ammi kai tsaye part nashi yanufa " Aryan ma yana fitowa yabi bayansa kusan tarema suka shiga part ɗin don ɗin suna shiga betroom ɗin " Aryan ya ajiye box ɗin hannunsa akan mirrow yajuyo zaiyi magana don yarigasa dachewa " maganar me kakesan muyi kuma " Aryan yace kai akoi alamar tambaya akankufa don " alamar tambaya kuma to akanmu nidawa don ya tambaya yana jiran amsa " kai da yarinyar nan mana Aryan yabashi amsa a takaiche " wache yarinya kuma chewar don " wanda karike yanzu nawa allura " dogon tsaki don yaja kana yace banasan haka Aryan danna riketa kawai kasanifa farinchikin Ammi nema kawai yasa nazo ɗakin ba wai wani abuba " tabbas akoi aya tambaya akanku bagashiba period natanma daya fara zuwa kai yafarayiwa sallama " waro green eyes nashi waje yayi yace what mekake nufi banganeba " Aryan yace kalli jikinka mana kagani " da sauri don yadukar da kansa yanabin jikinsa da kallo jini yagani a dai dai saitin a' sukwane yachire jallabiyar yayi wurgi da ita gefe " Aryan baisan sanda ya kwashe da dariyar da baitabayiba dariya yake harda rike chiki yana faɗin tab aiko " akoi babbar a'yar tambaya makuwa abun harda short " da sauri don yadubi short ɗin jikinsa aiko jinin yagani a dai dai saitin a'sukwa yanufi toilet " chikin dariya Aryan kefaɗin kai amma jininma ya iya zaɓen wajen da zai zuba wlh, ai nazachi short ɗinma chireminshi zakayi a nan yasake kwashewa da dariya harda faduwa kan gado
Ammi che tashigo É—akin da sallama tasamesu akan gado hiyana da diyana anchi kuka ankoshi " hiyana ki dauki tea din nan kisha kitashi kije kiyi wanka ki gyara jikinki chewar Ammi " to kawai hiyana ta amsawa Ammi dashi tamike kenan taga jini a inda tatashi da mamaki take kallan wajen zatayi magana sukaji maganar yusuf yana shigowa yana waya da sauri hiyana tanufi toilet " Ammi ta kalli Zahra tache kitashi ki gyara wajen ki dauko mata always da pant tana kaiwa nan tajuya zata fita ke nan dan tayi sauri ta tare yusuf awaje sai gashi yashigo " yabakuyi shirin zuwa school ba karfe 7:35 yanzu " aa yusuf yau nache su ajiye zuwa school É—in sai gobe chewar Ammi " kallon Ammi yusuf keyi kamar akoi abun da ke damunta dan yaga alamun hakan a chikin idonta, amma sai yache to shike nan, daman nazo daukarsune, tun da bazasu jeba barinaje nadubo don da Aryan " to kawai Ammi tace " yusuf yajuya yafita yana fita Ammi ma tafiche daga É—akin
Misalin karfe 3 na rana
Aunty amarya che zaune a palonta ita da Aryan da kuma Aiman " rai aÉ“ache Aunty amarya tasoma magana "me sakaninka da yarinyar nan da sauri suka É—ago kai kaba É—ayansu suna kallanta kara É—aure fuska tayi tace wai ba tambayar ka nake ba Aryan " a sanyaye yache kai Aunty amarya meyasa kikemim irin wan nan tambayar ni meruwana da ita mekuma zanyi da ita kawai ta iya haÉ—a coffee sosai ne shiyasa nache tarinka haÉ—amin, " to banaso banasan tarinka kusantar'ka banso kanemi wata mai haÉ—a maka coffee É—in amma ba yaran nan ba " shiru yayi bai sake tan kawaba saima wayarsa daya É—auka yayi waje ...✍️✍️
Masu karatu amin afuwa sai munhaÉ—u gobe idan mai dukka ya kaimu
💖The Talent Troupe Writer's 💖
No comments