Recent Updates

Doctor Mansoor 31

 


🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

  *DOCTOR MANSOOR*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸




    Na

_Jiddah S Mapi_



*Chapter 31*



                 ~Man yana bacci har suka gama yanke hukunci, umma ta kalli Hamida batace komai ba dan tasan Abba yayi hukunci me kyau.


bayan ya farka daga dogon baccin da yayi Ahmar yake sanar mishi Abba ya yanke shawaran aurar dasu gobe friday bai É—au maganan serious ba saida yaji a bakin Abba, cikin murna yaje É—akin Hamida, knocking yayi tace "come in"

a hankali ya tura kofan ya shiga, tana zaune akan gado tasa rigan bacci baki silk, da maÉ—aurinshi ta gaba, kanta ba hula ta baza gashin bata É—aure ba, har gadon bayanta ya sauko, tasan shine shiyasa bata juyo ba taci gaba da latsa wayanta, zama yayi kusa da ita har jikinshi yana gogan nata, a hankali yace "my hamida?"


ko É—agowa batayi ba, kanshi ya kwantar a gadon bayanta cikin kasa da murya yace "i love You"


bata kulashi ba taci gaba da latsa wayan, karbe wayan yayi ya ajiye a gefe, zata tashi taji ya kwantar da kanshi a cinyanta ya lumshe ido, zuba mishi ido tayi tana kallon dogaye eyelashes nashi, da sauri tasa hannu ta ture kanshi, kara mayarwa yayi tareda riko hannayenta ya damke a nashi hannun, yatsanta yasa a bakinshi ya fara tsotsa a hankali yana sauke ajiyan zuciya, shiru tayi tana kallonshi, ba zatace ta tsaneshi ba amma bata jin tana sonshi, a halin yanzu tausayi kawai yake bata, da haka har bacci ya É—aukeshi a jikinta, turo kofan akayi Ahmar ne da Samha hannunsu rike dana juna sunzo domin yiwa Hamida godiya ganin bata bijirewa Abba ba, da sauri suka juya baya "sorry bamusan yana nan ba"

cewar ahmar.


"Ku shigo ba komai"

a hankali suka juyo su duka suka karasa, zama sukayi a bakin bed É—in, hannu tasa zata sauke kanshi daga cinyanta taji ya kara rike waist nata sosai, barinshi tayi ta kalli samha "meya faru."


"unty hamida dama mukace idan bakyason ayi auren gobe zamuje mu yiwa ammi magana zata gayawa Abba sai a É—aga"


"A,a banso Ammi tayi zargin banason Man ku bari kawai a ɗaura zan zauna dashi, koba komai nima na kara samun mahaifi a karo na uku, bayan Babana sai babanki sai kuma baban Man, zan zauna dashi zaɓin manya shine zaɓi"


murmushi sukayi Ahmar yace "mun gode Hamida Allah ya saka da khairan"


"Ameen ta faÉ—a"

cikin bacci ya cire hannunshi É—aya daga waist nata ya riko hannunta ya É—aura a kanshi, shafawa ya fara a hankali ya zame hannunshi ya bar nata cikin gashin kanshi, sanin abinda yakeso yasa ta fara cusa yatsunta cikin sumanshi tana shafawa, bacci sosai yake yi wanda rabonshi da yin hakan tun bayan tafiyan Jahad.


Kabir ne suka shigo shida Jawad da Laila da kuma Noor, godiya suke son yiwa Hamida domin sunji daÉ—in zamanta a gidan, basaso ta tafi, Jawad lumshe ido yayi cikin jin daÉ—in ganin Hamida da Man a haka yace "Unty Hamida mun gode"


"Ka daina min godiya Jawad, duk abinda nayi bazan iya biyan Ammi ba, itace take kawomin ziyara a prison ta bani abinci ke kyau da kuÉ—i sannan ta bani rayuwar Æ´anci a gidan yari, ina sonta dolene naso É—an cikinta"


zama sukayi a É—akin su duka suka fara hira, Noor tace "kunsan time É—in da kaka tazo gidannan? wallahi na zata tsohuwa me siffan Æ´ammata ne ashe unty hamida ce"


dariya suka kwashe dashi, Hamida ta aika mata hararan wasa "ke banson rainin wayo nima watarana kaka ce"

har yanzu hannunta akanshi, Kabir ne ya kai bakinshi kunnen Jawad yace "ba dole ta zama kaka ba tunda gobe zata zama mama"

buge bakinshi Jawad yayi dan yasan me yake nufi "ni ba ruwana da zancen batsa"


"yaushe nayi zancen batsa anan? gaskiya kawai na faÉ—a"


Abba yana daga bakin kofa yana kallonsu ta cikin ɓulin dake jikin kofar wanda asali anyishi ne domin leka wanda yake bakin kofa, murmushi yayi ganin yaranshi a cikin farin ciki, ya gode Allah da Hamida batayi aure ba, da yasan rayuwar ɗanshi zai shiga haɗari sosai.




*Washe gari*


Labarin auren Mansoor Muhammad Dikko, da Hamida Umar ArÉ—o shine labarin daya zagaye garin Gombe, ko ina kaje wannan labarin shi ake, wasu suna tofa albarkacin bakinsu na cewar itace ta fito daga gidan yari bayan ta kashe mutane ranan aurenshi da Jahad, wasu kuma suna sa albarka, dama haka rayuwa take wasu mutane susa albarka wasu kuma suyi tsinuwa, ango Man da Amarya Hamida sunyi kyau cikin fararen kaya, ita Hamida leshi tasa sai man wanda yasa shadda fari sunyi anko da Ahmar, babu wani taro me yawa duk da haka ba'a rasa mutane dayawa sunzo wurin ba.


an É—aura auren Samha da Ahmar Abba ne ya biya sadaki, hadda na Man, nan fa aka sha bidiri, amarya tana fara'a badan taso ba kawai dan ta faranta ran Ammi ne da ummanta, ita kuwa Samha sai dariya take yau ta samu Ahmar a matsayin miji, bini bini yake kiranta a waya suna shan hira.



da dare Abba ya tarasu su duka a palour yayi musu nasiha ya kuma gargaɗi Man da kada yaji kuma kar ya gani, koda wasa ya ɓatawa hamida rai, ya yiwa Abba godiya na alkawarin ba zai taɓa ɓata mata rai ba koda sau ɗaya ne.


umma ma tayiwa Hamida nasiha da faɗa akan idan ta kuskura ta ɓata mishi rai saita saɓa mata, tayi shiru kawai, a daren Abba ya kaisu gidajensu wanda yake kusa dasu sosai, gidan iri ɗaya ne wanda babu abinda ya bambanta, Ahmar da Samha sai kuma Man da Hamida, komai an shirya an kuma gyara sai ƙamshi da sheƙi gidan yake.




**************

Kunna Tv, da suari ta ɗau remote ta kunna Tv tana kallo "Hamida da Man? dama bata mutu ba? to ina ta ɓuya?"

Jahad ce zaune akan kujera ta ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya tana cin chips, gefe guda tana kallon Tv, ganin Hamida da Man sunyi aure yau yasa ta mike a firgice tana kallonsu, jikinta ne ya fara ɓari Hamida da man? kuka ta fara sosai tana jin zafi a ranta, waya ta ɗaga tayi dialing number, ana ɗagawa jikinta yana rawa tace "Man ya auri hamida"


"to ina ruwana"


"Jalal ni kake gayawa haka? nice fa Jahad naka"


"Kinga yanzu haka nima an É—aura min aure ina tare da iyayen matata kada ki kara kirana a wannan lokacin"

kashe wayan yayi tana cewa "Jalal...Jalal"


ganin ya kashe ta buga wayan da kasa, faÉ—uwa tayi akan tyles É—in ta fara kuka, ta rame sosai ta zama useless, Jalal yana bata wahala tunda akace ba zata kara haihuwa ba, shikenan an cire mahaifinta, ba ita ba haihuwa rayuwa ta juya mata baya, tayi dana sanin É—aukan fansan abinda akayi mata, shiyasa akace ba'a rama sharri da sharri daso samune ka rama da alkhairi, saida ta fita a rayuwar man taji tana sonshi kamar ta kashe kanta.




_jiddah s mapi_

No comments