Recent Updates

Daudar Gora 48

 


*_48_*



...........Babu kwanciyar hankali gasu Kaka, dan har yanzu basu sami bakin zaren jin komai ba game da wadda aka rasa a cikin matan Shahan-shan. Ga tashin hankalin É“atan Barrister dan sun je har gidansa amma a rufe alamar iyalansa ma dai basa nan.

Acewar makwafta kuma dai anzo an kwashesune a cikin dare, yau kusan kwanaki takwas kenan. A lissafinsu kuma ya kama randa Barrister ya É“ata kenan. Zuciyar kaka ingizashi take kan abubuwa masu yawan gaske amma yana gocewa, dan duk tsanani yayi alÆ™awarin dogaro ga ALLAH majiÉ“incin al'amuran bayi a kowane tsanani da sauÆ™i. Kwanansa É—aya ya juya Æ™auyen Jumna, dan yasan ya baro su Iyyani a tashin hankali. 


      Ilai kuwa koda ya koma sai ya samesu a birkice, dan suma dai zuwa yanzu labarin halin da Æ™asar ke ciki ya isa har kunnuwansu. Ummu tayi kuka har hawaye sun daina zuba. Ta gama sadakarwa ta rasa autarta itama. Dama ta jima da fidda rai ga su Babiy tuni. Kaka rasa ma mizai ce da su yayi, dan shima dai nasa kan a zafafe yake. Sai kawai ya shige É—akinsa ya rufe kansa yana mai safa da marwa.......


          ★★..... BARRISTER ★★......


    Da taimakon masu tsaronsa bisa umarnin ogansu da tun a ganin farko da yay masa bai sake ganinsa ba sai ta waya tun a yammacin ranar suka fara tattara abubuwan da zai basu kariya wajen fita da su Babiy duk da basu zo hanunsu ba har yanzu. Sai dai a daren ranar su Sayeed Harun Al-rashid sukai alkawarin danÆ™asu hannun Barrister, duk da ya nuna musu shifa yana jin tsoro su bari komai ya kammala sannan suka nuna masa suna tare da shi da kuma tsaro na musamman duk da kuwa Æ™arya ne a baÉ—ini.

         Zancen kam nasu ya tabbata, dan a daren ranar Æ™arfe kusan tara na dare aka damÆ™a Babiy da Hanash a hannun Barrister Abdallah Aas matsayin Barrister Akeem da zukatansu su suka É—auka. Daga gani kasan sun jigata matuÆ™a, sun rame sosai sunyi duhu. Ga rashin Æ™arfin jiki da zaman waje É—aya harma da Æ™arancin abinci dana iska mai Æ™yau. Hankalin Barrister ya tashi matuÆ™a, ya dinga share hawayen tausayinsu. Ya sake tabbatar da mutanen nan da suka kamashi mutanen kirki ne a yau, dan ana iso da su Babiy hanunsu sai ga likitoci, dan-da-nan suka duÆ™ufa kansu da kulawa kai kace dama a shirye suke da hakan.......


         ★★..... MASARAUTA ★★.....


   Duk da Æ™arancin shekarunta ALLAH ya bata basira irinta masu hangen nesa. Tun bayan gama wayarta da Miran Jasim zuciyarta bata aminta da yarda su gana fuska da fuska ba. Dan haka ana idar da sallar magrib ta tura masa saÆ™o kamar haka duk da ita ba sallar zatai ba tana fashi.

      _Na amince mu tattauna, sai dai bata haÉ—uwa ba, muyi magana ta video call._

     Miran Jasim ya karanta saÆ™on yafi sau ashirin, takaici kam ba'a magana ga É—unbin mamakin basirar Æ´ar ficikar yarinyar. A take ransa duk ya jagule, ga boka Barbushi ya tabbatar masa haÉ—uwa da yarinyar fuska da fuska yafi fa'ida. Dan kwarjininsa da suddabaran da ya basu zai sakamata tsoronsa mai tsanani ya dinga yanda yaso da ita har zuwa sanda itama zasu É“addata bayan ta cika musu aikinsu. Gashi yanzu guri ya Æ™ure, bazai yiwu masa ba zuwa ga Barbushi É—in dan zai iya rasa wannan damar da bokan nasu ya tabbatar musu itace ranarsu mafi Sa'a akan yarinyar kasancewar tana fashin salla, tana kuma cikin ruÉ—anin da ba komai yake iya banbancewa yanda ya kamata ba zasu iya sarrafata a duk yanda sukaso musamman akan Shahan-shan. Duk da sallar isha'i data gama gabatowa haka ya miÆ™e ya fice a masallacin bayan yayma Miran Arshaan alama da ido. Bai jima da fita ba kuwa yabi bayansa....


       “ALLAH yasa dai lafiya na ganka duk a wani birkice?”.

    Miran Jasim ya sauke idonsa akan Miran Arshaan mai maganar yana mai jan tsaki. “Wane kwanciyar hankaline da ni inba gani nai komai ya daidaita ba Arshaan. Yanzu ma Æ´ar iskar yarinyar nan ce wai fa ta turamin text message bata yarda mu haÉ—u fuska da fuska ba sai dai video call”.

          “What! Waini wace irin hatsabibiyar yarinya ce wannan? Nama fahimci kallon sa'aninta take mana”.

    “Ka barta karka damu, zata yabama aya zaÆ™inta ta dai gama mana aikinmu. Anan zata gane ko wanda ya ajiyeta a gidan bai isa ba balle ita karamar halitta. Ni yanzu damuwata ma shine Barbushi ya tabbar mana da wannan ranar ta sa'a, haÉ—uwarmu kuma fuska da fuska wani babban cigabane garemu.”

            “Komai ya kwaÉ“e kam, sai dai ni a wannan gaÉ“ar ina masa kallon mai sauÆ™i. Kaga dai a yanzu bamu da isashen lokacin komawa wajen Barbushi, na biyu barin wannan damar ta wuce a garemu kuskure ne. Dan haka kawai mubita a yanda take so É—in, da sassafe mu nufi Barbushi”.

    Ajiyar zuciya mai nauyi Miran Jasim ya sauke domin gamsuwa da zancen Miran Arshaan É—in, daga haka basu koma masallacin ba sukai zaman kulla yanda zasu tunkari Iffah bayan sun tura mata saÆ™on amincewa ayi video call É—in.


   *_10:30pm_*


        Ƙarfe goma da rabi na dare agogon Æ™asar Iffah zaune gaban laptop É—in ta, sanye take cikin suturar ta mai sirrinta jiki, iya zagayen Æ™yaÆ™ykywar fuskarta kawai ake iya gani. Tayi fayau ga mai kallo baka iya ganin komai sai damuwa da tsantsar Æ™uruciyarta. Cikin girmamawa ta gaida dattijan guda biyu dake a fuskar lap-top É—in tata. Miran Jasim da Miran Arshaan suka amsa mata da kulawa da nuna tausayawa tsantsa a fuskokinsu. Ita dai idanunta a rissine, dan tun kallo É—aya datai musu bata sake yarda ta Æ™ara ba.

      Miran Jasim yay Æ´ar gyaran murya da fara magana bayan gaisuwar tasu. “Ibnati mu mun sauke nauyin dake kammu naki, abinda kika yanke kawai muke buÆ™atar ji domin tsallakar da rayuwarki data Æ´an baya. Dan a yanzu mun shirya tsaf ba tsafi ba ko bataliyar ifiritai Eshaan zai sauke a kammu domin danne cewarmu bazamu taÉ“a yin shiru ba”.

         Iffah ta jinjina kai a hankali da faÉ—in, “Uncles naji daÉ—in hakan, kuma tun farko dama haka ya kamata ku kasance, duk da dai nasan bai zama lallai kuji irin zafin da iyayenmu sukaji ba. Amma a yanzu daya fara taÉ“aku gashi kun zaburo. Duk da haka bazamu Æ™i karÉ“ar taimakonku ba, dan a yanzu bani da wani abu dana tsana sama da shi, a shirye nake kuma na zama ajalinsa koda nima zan rasa nawa ranne. Sai dai ina son dan ALLAH uncle ka faÉ—amin gaskiya taya ka samu wannan videon? Ta ya kuma kasan na cikin videon nada alaÆ™a da ni ne? Miyasa kuke son taimaka mini? Miyasa duk da kun san yana kan rashin dai-dai baku taÉ“a wani yunÆ™uri ba a baya sai yanzu?”.

      Kallon juna Miran Arshaan da Miran Jasim sukai kowanne ransa na susa da mamakin tsaurin idon wannan yarinya da sukema kallon hatsabibiya. Amma a zahiri sai Miran Jasim yaja ajiyar zuciya ya fesar cikin Æ™oÆ™arin danne razanin da tambayoyinta suke neman jefasa. “Ibnati duk wannan ai na abin mamaki bane da har zai saka miki shakku, amma tunda kina son sani yanzu zakiji komai. Wannan video É—in da kike gani na samosa ne a system É—in Eshaan, bakuna shi kaÉ—ai bane ba. Akwai ire-irensa da yawa harma dana yanda aka hallaka matansa na baya. Ina haÉ—asu ne domin miÆ™asa kotu a kwatarma masu hakki hakkinsu duk da ina fargabar Æ™arfin iko irin na Shahan-shan bazai bari a hukunta shin ba kasancewar komai sai da say É—insa ke gudana a Æ™asar ruman baki É—aya. Sanin alaÆ™arki da wannan video kuwa ta samune duk a dalilin bibiyar tasa, sai dai bamu tabbatar ke bace ba sai a ranar da kika samesa tare da Arshaan Akh suna wasan takkubba. Sannan kasa tunkararsa a baya Ibnati bazaki gane ba, Æ™arfin ikon Shahan-shan fa bana wasa bane ga kowa....”

      “Tabbas hakane” Miran Arshaan ya amshe zancen. Batare daya jira cewar Iffah ba ya cigaba da faÉ—in, “Idan baki manta ba bayan kin basa shayi ya koma gefene yana kallo cikin masarauta, nima kina bani kuma na koma kusa da shi ina mai yabama tarbiyyarki da tabbatar masa yayi dace mace tagari data dace da shi a yanzu. BuÉ—ar bakinsa sai ya sake tsaki da faÉ—in, “Tukunna dai, ai shi har yanzu matar da zai rayu da ita bata iso ba. Naji mamaki harna tambayesa ba'asin hakan amma sai bai tankani ba kin sanshi da girman kai. Zancen ya tsaya min a rai nazo na sami Jasim Akh da maganar, shine fa ya duÆ™ufa bincike harya samu ganawa da kakanki da ke a Æ™auyen Jumna”.

        Sosai Iffah ta zabura da jin sun gana da kaka harta É—ago ido ta na kallonsu. Tabbas sihiri gaskiya ne, kuma yakanci kowama tunda har yaci ma'aikin ALLAH. A take wani abu mai sanyi ya dinga shiga jikin Iffah tamkar ana kwararashi cikin jininta. Hawaye ne suka silalo a idonta ta buÉ—e baki a hankali ta furta “Tabbas zan kashesa da hannuna, zan kashesa da dafin maciji na gaskiya kamar yanda yake halaka mutane dana tsafi. Nayi alkawarin yanda ya wargaza min ahali nima sai na wargaza rayuwarsa..”

     Miran Arshaan da Miran Jasim suka kalli juna sukai murmushi. “Zako mu baki dukkan gudunmawar da kike buÆ™ata Ibnati. Tare da kariya ta musamman ga duk wanda zai iya kawo miki hari, balle ma a yanzu abinda zakiyi sai dai ya Æ™ara kawo miki É—aukaka dan irinki Æ™asar ruman ke nema. Mi kike buÆ™ata a yanzu?”.

          Kai tsaye ta amsa da cewar, “Dafin maciji mai matuÆ™ar haÉ—ari”.

     “Zako ki sami na macizai ma ba maciji kawai ba. Ki saurari saÆ™o zuwa safiyar gobe. Mun barki lafiya”.


       Wani irin kuka mai taÉ“a zuciya Iffah ta saki, a hankali ta zame takai kwance kanta da yay mata nauyi na sara mata. Gaba É—aya duniyar tai mata dummm bata gane komai, burinta kawai shine ta É“atar da Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed. Gawarsa kawai tafi bukatar gani kwance a Æ™asa fiye da komai. So take taga ahalinsa na kuka fiye da wanda sukai a dalilin rasa Æ´an uwansu saboda son kansa. Haka ta kwana a wani irin bahagon yanayin da bazata iya koda tunawa ba. Ita bamai barci ba ita ba ido biyu ba, ita ba matacciya ba ita ba mai rai ba gadai tanan. Duk da tana fashin salla ana kiran salla ta miÆ™e, bayi ta shiga ta tsaftace jikinta duk da babu wani Æ™azanta tattare da ita, tana Æ™oÆ™arin naÉ—e gashinta daya É—an warware takeji kamar magana a Æ™ofar É—akin nata. Cikin shakku ta gyara rigar wankar jikinta ta nufi Æ™ofa ta buÉ—e. Da mamaki take kallon amintacciyar hadimarta mai suna Abal dake a durÆ™ushe hanunta É—auke da Æ™yakywan bowl. 

        Da sauri Abal takai Æ™asa tana gaidata. Batare da Iffah ta amsa ba ta É—aga bakinta da yay mata nauyi da Æ™yar tace, “Lafiya.....?”

    “Lafiya Lau ya Zawjata-almilk. SaÆ™one daga sashen mai Babban É—aki”.

      Hakan ya É—an saka Iffah a shakku da mamaki, amma sai bakinta yay mata nauyi bata iya ta sake cewa komai ba ta amshi tambulan É—in mai É—auke da sabuwar madara fara Æ™al. Idanu Iffah ta tsurama madarar wani shawa'ar shanta na fusgarta. Amma sai ta dake ta ajiye ta da nufin sai ta gama kimtsawa tasha ko kaÉ—anne kaffin ta sake komawa barci. Harta nufi kayan data fiddo zata saka kira ya shigo wayarta. RuÉ—ewa tai dan abune da bai taÉ“a faruwa da ita ba, kofa sallar asubahi ba ayi ba. Kamar wadda ake ingizawa da remote ta É—auka wayar, ganin Miran Jasim ta amsa da tsumar jiki tana gaisheshi kai kace yana a gabanta ne. Bai amsata ba, sai ma umarni daya bata cikin kakkausar murya saÉ“anin wadda yake mata magana da ita a baya. 

      “Wannan madara ce mai É—auke da dafin macizai masu haÉ—arin gaske har guda biyar, daga yanzu zuwa Æ™arfe takwas na safiya ina buÆ™atar jin kukan mutuwa. Kukan mutuwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed nake buÆ™atar ji har gadon barci na ta dalilinki”.

     “An gama ranka ya daÉ—e”.

Iffah ta amsa da rawar murya hawaye na ciko mata ido ga girmamawa har tana rissinawa kamar tana a gabamsa.........✍️


      *_🤦ALLAH sarki Iffah baki shike yanka wuya. Kin É—auka niyya badan zuciyarki zata iya ba a zahiri, gashi masu babban burin sharri zasuyi jifa da hannayenki batare da kin san illar hakan ba a gareki._*

No comments