Daudar Gora 38
38_*
........Duk da yanda zukatansu ke suya da tsagwaron salon wulaƙanci da raini da suke jifansa da shi game da wannan halin nasa da babu komai a cikinsa sai tsantsar miskilanci da kasancewar jinin mulki da ke yawo a
jikinsa basu bari fuskokinsu sun nuna ba har ya gama shan Æ™amahinsa da basarwarsa ya tanka.“Amfanin kasancewarsu cikinmu yafi rashin amfanin muhimmanci Aam. A lokuta da dama nafi son zama da maÆ™iyi fiye da masoyi saboda dalilai biyu”.
Wani irin kallo suke masa har fuskokinsu na barazanar bayyana sirrin zukatansu. Miran Arshaan yay saurin katsesa da faÉ—in, “Abni wace irin magana ce wannan? Kakuwa san illar hakan da kakeyi?”.
Miran Jasim dake masa kallon gefen ido cikin takaici yake masifa a zuciyarsa. (Shifa wannan wawa ne baima iya jin Æ™arshen zance sam). A zahiri kam kallonsa ya sauke ga Tajwar Eshaan da yay biris tamkar bashi ya É—akko zancen ba. “Ihm kaga Abni Æ™arasa, zata iya yuwuwa naka hangen gaskiyar cikinsa rinjaye ne ga namu. Domin kowa da irin yanda UBANGIJI ke fahimtar da shi abu”.
Tajwar Eshaan da bai ko motsa ba ga zancen Amin nasa sai da ya shaÆ™i iska iya buÆ™atarsa kafin ya É—an É—age kafaÉ—u a yanayin ko'in kula. “Ku manta kawai muje kan magana ta gaba. Wataran zamu Æ™arasa wannan É—in”.
Sosai takaici ya maÆ™ure musu maÆ™oshi su dukansu. Sai dai Miran Jasim har Miran Arshaan yake jin takaici kasancewar shine sanadin katse zancen. Suma shiru sukai kamar bazasuce komai ba a wannan gaÉ“ar. Kafin Miran Jasim ya nisa. “Abu na gaba shine farin cikin tsallakewar matarka. Alhamdullah addu'oin mu sun karÉ“u, ALLAH yasa ta kasance uwa ga Æ´aÆ´an da zaka haifa masu albarka”.
A maimakon amsawa da Amin daga garesa Æ™asaitaccen murmushinsa mai Æ™ara bayyana Æ™yawun da ALLAH ya azurtashi da shine ya saki kaÉ—an yana mai kauda kansa gefe babu alamar zaice wani abu. Suma basu nuna alamar sun damu da sai yace É—in ba Miran Jasim ya cigaba da faÉ—in, “Ya kamata a zauna da Tajwar na jihar Hubab da shugaban tsaro akan waccan matsalar itama. Kar muyi sakaci dayin biris da wannan maganar dan bamu san minene manufa ko dalilin faruwar komai ba. Abu mafi ruÉ—anin shine makamancin haka bai taÉ“a faruwa a Æ™asar ruman ba sai dai muji a wasu Æ™asashe har ma mu bada shawara da gudun mawar ganin sun samu zaman lafiya. Idan haka kuma ta fara faruwa a garemu lallai maÆ™iyanmu na barazana akan nasararmu kenan”.
Nan É—in ma dai kamar bazai tanka ba sai kuma ya dubi Miran Jasim É—in da alama zancen ya shigesa. “Na baku damar yin duk yanda ya dace Aam”.
A take fuskokinsu suka nuna jin daÉ—in wannan girma daya basu. Sanin halinsa yasa daga haka sukai masa sallama. Har sun miÆ™e Miran Arshaan yace “Af niko kaga na shafa'a da wannan batun. Abni baka ganin yayi kusa kuwa ace fitar Zawjata-almilk har cikin books room? Yakamata ace tayi haÆ™urin cigaba da killace kanta kodan maÆ™iyan da bamu san ta inda suke shirya sabon shiri ba, dan yayi wuri ace mun shagala da tsallakewar ta ta a nawa É—an hangen. Ai Æ™oÆ™ari a tsawata mata ALLAH ya cigaba da kare mana ku ku duka dai”.
Miran Jasim ya amsa da Amin yana jinjina kai alamar tabbatar da maganar, sai dai ganin Tajwar Eshaan bashi da alamar cewa wani abu suka fice abinsu. Koda suka fitan ya jima bai motsa a yanda yake ba, da alama dai maganar tasu ta Æ™arshe ce ke masa kaikawo. Hasashen kam sai ya zama gaskiya dan akan lips É—insa daya motsa kaÉ—an ya ambaci, “Yarinyar nan ko”. Daga haka ya shanye sauran a cikinsa....
★★.... ★....
Kamar yanda ta faɗa bayan sallar isha'i ta fito cikin abaya fara tas. Duk da dare ne ƙamshinta da kwarjininta mai ɓoye ƙarancin shekarunta na tare da ita. Fuskarta ɗauke da murmushi mai bayyana haƙora take amsa gaisuwar hadiman da tuni sun kammala taruwa bisa umarninta. Ɗaya bayan ɗaya ta basu damar gabatar mata da kansu da matsayin ayyukansu. Har suka gama batace komai ba tana dai nazarinsu ne. Haka kawai take jin bai kamata ta yarda da kowa ba a wannan gaɓar, dan duk da tausayinsu dake nuƙurƙusar zuciyarta tayi imanin akwai masu gurɓatacciyar zuciya a cikinsu kamar yanda Daneen Ammarah ta karanta mata komai.
“Okay duk naji bayanan ku, sai dai kuma Ni zan canja tsarin aikin da bama kowa abinda nake ganin zai fi dacewa da kasancewar tare da ni. Bazan roÆ™i kowa ba a cikinku cewar ya kasance mai gaskiya da riÆ™e amana, sai dai zan tabbatar muku zan iya hukunci ga kowa idan na kamashi da waÉ—an nan abubuwan biyu. Dan na matuÆ™ar tsanar mai wannan halayar koda a sama dani yake. Zan kuma iya aikata harma abinda mutum baiyi zatoba akan hakan.....” É—aya bayan É—aya ta rarrabasu ga ayyukan saÉ“anin yanda aka turosu suyi, salon nata ya matuÆ™ar girgizasu a take kuma tasirin gizagonta ya shigesu, har suke ambaton tsarin da gaba kura baya sayaÆ™i kenan, dan kuwa dai kamar yanda Iffah tai hasashe mafiya yawan cikinsu zasu kasance da itane bisa umarnin iyayen gidansu na É“oye bisa É—abi'ar tura Æ´an leÆ™en asiri da manyan masarautar suka tasirantu a kansa. Bayan ta sallamesu akan aikinsu zai fara daga gobe ne ta tattare littafanta da kanta tai ciki da su. Sai da ta tabbatar ta Æ™arema É—akin kallo yanda ya kamata fiye da É—azu bisa zargin za'a iya saka mata camara kamar yanda Ajmaal ya tabbar mata. Babu alamar akwai abinda take zargin dan haka ta É—auka wayarta. A maimakon WhatsApp yau a text message ta tura masa saÆ™o, daga Æ™arshe ta Æ™ara roÆ™onsa bincika mata lafiyar iyayenta dan zuwa yanzu zuciyarta na tabbatar mata akwai abinda Sir Fawzan ya faÉ—a mata ba dai-dai ba ko yake É“oye mata. Dan kullum takan gwada number Hanash da Babiy sama da sau babu adadi amma babu alamar zata samesu. Ga mafarkinta a kansu duk kusan bayan kwana biyu cikin maimaita kansa yake gareta. Bawai tayi imani da hakan bane, kawai dai zuciyarta takan rinjayu da tsoro akan mafarki musamman idan ta auna da abubuwan da suka tabbata akan wasu mafarkai da sukai wa riÆ™on wasarere ita da iyayenta a baya.......
*_★MALIKAT HASEENAT★_*
Kamar yanda labarin fitar Iffah yaje kunnen kowa a masarautar itama yaje nata kunnen, sai dai saɓanin malikat Bushirat ita murmushi tayi batare data furta komai ba akan zancen. Rashin cewar tata ya Bama Hadimar damar ƙarasa mata zancen akan Iffah kuma ta koma sashenta bayan barowarta books room. Anan kam idanu Malikat Haseenat ta tsurama hadimar Tata tamkar zataga fuskar Iffah a jikinta ne. Sai kuma ta janye da wani ɗan murmushi a fuskarta ta maida ga hadima Banou.
“A haÉ—a abincin karin kumallo da Zawjata-almilk ta uku”.
Cikin tashin hankalin wannan umarni na Malikat Haseenat kamar Banou zata fasa kuka ta jinjina kai, har hakan ya bama malikat Haseenat mamaki, sai dai batayi magana ba kasancewar tasan shirmen Banou fiye da haka. Itama dai tana zaune da itane batare da tasan dalili ba, amma wasu lokuta takanji yanayi mai wahalar fassara koda a kallon hadimar tata ne amintacciya a bangaren girka mata abinci...
7
*_BARRISTER_*
“Su waye ku? Miyasa kuka kawoni nan? Mina muku?”. Barrister ya faÉ—a yana mai bin zaratan samarin da kallo harma da É—akin da suka kawoshi mai Æ™arancin haske gashi a É—aÉ—É—aure a kujera. Fahimtar bazasu bashi amsa ko É—aya ba daya bukata ya sashi cigaba da magana a hasale. Dan shi mutum ne mai saurin fushi musamman akan gaskiya da mai gaskiya. Baya son zalunci shiyyasa ko baka da Æ™arfi zai tsaya maka akan haƙƙinka in har ka kasance mai gaskiya.
“Idan ma akan case É—in nan ne kuke ganin sakayeni ko É“adda rayuwata zai baku damar yin yanda kuke so akan bayin ALLAH da basujiba basu gani ba ku sani ni bamai hukunci bane. ALLAH shine mai hukunta kowa, zai kuma iya kawo wanda ya fini Æ™arfi ya cece su”.
Yanzu ɗinma dai babu alamar wani a cikinsu zai tanka masa. Idanunsa ya rumtse zuciyarsa na masa ƙuna. Bashi da wani buri yanzu a duniya sama da yasan asalin tushen wannan case ɗin nasu Babiy, yayi alƙawarin tsayawa da ƙarfinsa dana aljihunsa insha ALLAHU.
Har dare babu wani haske daya samu dan har lokacin yana a ɗaure, sai da aka kira sallar magriba ne suka bashi dama yay salla harda isha'i. Hakan ya ɗan sassauta masa zuciya, dan koba komai damar yin salla da suka bashi yaji a ransa masu sassauci ne. Abinci suka kawo masa basu sake ɗauresa ba, sai dai yaƙi yako kallesa hakan yasa suka sake zuwa kusan ƙarfe tara agogon ƙasar suka sake ɗauresa sukai ficewarsu da kullesa ta baya. Babu irin tunani da takaici da baijiba amma ya cigaba da ambaton sunan ALLAH dan yasan shine kaɗai zai kuɓutar da shi a wannan gaɓar.
Kusan ƙarfe sha ɗaya gyangyaɗi naɗan kwasarsa yaji ana ƙoƙarin buɗe ƙofar, idanunsa ya buɗe duk da baya iya ganin mai shigowa saboda ƙarancin hasken ɗakin. A ɗan hasken ya fahimci yanzu mutumin uku suka shigo, wanda ke gaba kuma da alama ogansu ne dan yanda ya shigo da takun izza cikin ɗakin. Da sauri suka ajiye masa kujera ya zauna yana mai facing ɗin Barrister yay wani irin zaman ƙasaita yana ƙarema Barrister ɗin kallo ta cikin glasses ɗin daya toshe idanunsa....
“Miyasa kuka dauresa?”.
Ya faÉ—a a kausashe. Kame-kame yaran nasa suka fara kowa na Æ™oÆ™arin kare kansa. Yaja tsakin daya sakasu nutsuwar dole yana mai faÉ—in, “Ku kwance sa”. Bayan an kwance Barrister ya sake bada umarnin a bashi abinci da ruwa. Barrister dai kallonsa kawai yake da mamakin wannan izza tasa. Baiyi niyyar cin wani abu ba dan haka yay saurin faÉ—in, “Bana buÆ™atar wani abinci. Kusanar min kawai dalilin da yasa kuka kawoni nan da kuma inda nake dan ALLAH”.
Har Barrister ya fidda rai ga samun amsa yaji an karÉ“ama zancensa a kausashe. “Barrister Abdallah Aas ba shiririta ta kawoni nan ba. Dan na baro abubuwan da suka fika muhimmanci nazo nan. Duk da rayuwarka ce ba sanin inda kake ko sanin mu su wanene ba matsalarka. Dalilin kawoka nan kawai zaka iya sani, damar hakan kuma na hanunka ta hanyar bin umarninmu”.
Haka kawai kwarjinin wannan mutum da ko fuskarsa Barrister baya gani da Æ™yau yay matuÆ™ar mamayesa, duk da yanaji a ransa ba alkairi yasa suka kawosa nan ba sai yaji bazai iya jayayya da shi ba. Cikin sanyin jiki ya fara cin abincin, yaci kusan lauma bakwai yasha ruwa duk suna a É—akin. “Na gama”. Ya faÉ—a cikin sanyin murya.
“Good for you”.
Aka bashi amsa cikin halin ko'in kula. Sai kuma yay shiru kamar baida abin faÉ—a kafin yaja numfashi cike da isa ya fesar.
“Lokacina Æ™urarrene dan haka bani da lokacin cigaba da É“atashi a rikeka nan. Aiki zakamun baka da kuma zaÉ“in cewa e ko a'a. Nasan kasan Barrister Akeem Ibn Behnam”.
“Hakane, dan abokina ne ma ranka ya daÉ—e”. Barrister ya amsa mishi da kalmar giramamawa a Æ™arshe batare da yasan dalili ba. Kawai dai yana jin matuÆ™ar girman wannan mutum da ko a murya yasan ya girme masa.
Cikin yaransa É—aya ya cigaba da faÉ—in, “Sanin hakan yasa aikin ya wajaba a kanka. Akwai aikin da Barrister Akeem É—in keyima wasu mutane, Boss naso ka maye gurbinsa....”
“Tayaya hakan zata faru, bayan su sun san wanda suke huÉ—É—a da shi”. Barrister yay saurin katse mai maganar.
“Ai mun fika sanin hakan shiyyasa muka zaÉ“eka. A yanzu Barrister Akeem na hanunmu kamar yanda kake a hanunmu, munada hanyoyin bi wajen canjaka ka koma shi bisa dalilan da kaima kasani, yayinda su a wajensu kai ka mutu a yanzu, zuri'arka kuma basu san inda kake ba. Zakai aikinne na kwanakin da basu gaza goma ba, idan sun zarta hakan kuma kai kaso”.
“Kun sani a duhu wlhy, Barrister Akeem fa wani babban jigone a rayuwata, muna taimakama juna matuÆ™a taya kuke tunanin zanci amanarsa ta hanyar yin amfani da kammanin da mukeyi ace na masa kutse akan aikinsa bayan haka cin amana ne?”.
“Wannan damuwarka ne. Aikinmu zai fara daga gobe”.
Ogan nasu ya faÉ—a cikin kausasa harshe yana miÆ™ewa. “Ranka ya daÉ—e dan ALLAH ka saurare ni”. Barrister ya faÉ—a cikin rauni. Sai dai baiko nuna alamar yama jisa ba yay ficewarsa yaransa biye da shi..........✍️
🤔????. Nama rasa abin faɗa.
No comments