Daudar Gora 15
_15_*
...........Ilai kuwa, duk yanda Diwa taso isa ga Malikat Bushirat akan lokaci hakan ya gagara, dama tasan ba abune mai sauƙiba. Amma kuma ƙin isar da saƙon a lokacin daya dace tamkar sakacintane. Zata kuma iya fuskantar kowane irin hukuncin da babu mai mata uziri a cikinsa...
A dai-dai lokacin da Diwa ke ƙoƙarin son isa gaban Malikat Bushirat ƴan uwa ga Malikat ɗin na can sun doshi sashen Iffah domin kai kayan al'ada da akema kowace Zawjata-almilki da zata saka kafin a wuce da ita wajen taron buɗar amarya da duk wani babba mai faɗa aji a daular ruman zai halarta, wanda kuma akaf matan Tajwar Eshaan ɗin da suka shuɗe huɗun farko ne kawai akaima wannan bikin sai Iffah a yanzun. Anan zata san kowa, kowa kuma ya santa. Tafe suke tare da rakkiyar hadimai masu ɗauke da wata lafiyayyar rigar alƙyabba mai tsananin ɗaukar hankali da aka ɗinkata ta musamman domin Zawjata-almilki da kuma wannan rana. Sai sauran kayan ado irin na hamshaƙan mata da akayisu da zallar zinare da diamond.
Sun É—anyi mamakin rashin samun kowa a sashen, saboda sanin tunda safe an turo hadimai da zasu mata hidima. Yanayin tsaftar sashen kuma ta tabbatar musu hadiman sunzo. Tunanin ko itace ta sallamesu ya sakasu ture zancen a zukatansu suka bama cikin hadiman umarnin wata ta nema musu iso. Har hadimar ta nufi É—akin da aka kai Iffah jiya ta tsaya cakk sakamakon wani irin kakari da sukeji tare da É“arin fashewar abubuwa. Su dukansu dubansu suka maida ga Æ™ofar, da alamun mamaki É—aya daga ciki ta sake bama wata hadimar umarnin zuwa ta duba. Minti É—aya baima cika da shigar hadimar ba ta dawo a guje numfashinta na fita da Æ™yar tana nuna É—akin da faÉ—in, “Z...Z....Zawjata-almilki!......”
A kusan tare suka afka ciki. Su dukansu babu wanda bai firgita da ganin Iffah dake layi hanunta na dama dafe da ƙirjinta tana laluben hanya dana haggu ba. A dalilin laluben ne taketa faman zubda abubuwan da aka ƙawata adon ɗakin da su. Sakamakon hakan kuma duk ta jima hanunta ciwo sai jini yake yi. Da zafin nama ɗaya daga cikin matan nan ta riƙota cikin jikinta suna mai ambaton sunan ALLAH a tare. Ganin yanda ta jiƙe sharaf ga jikinta yayi jajur abinka da fara sai hankalinsu ya ƙara tashi. A fisge Iffah ta damƙo hanun matar ta haɗa da nata takai kirjinta tana fadin,
“Ummu wuta, jikina zai babbake Ummu ki sakani a kanÆ™ara dan ALLAH karna Æ™one. Zan mutu Babiy wuta tana cin jikina....”
Gaba É—aya kalamanta sake ruÉ—asu sukayi. Duk sun daburce sunma rasa miya kamata su mata. Dan wadda ke rike da ita har hucin zafin takeji a nata jikin itama. Ƙaramar cikinsu ce tai Æ™arfin halin fita da hanzari tana mai musu nunin tana zuwa. Cikin sauri tamkar zata kifa ta nufi sashen Malikat Bushirat. A yanayin data shigo ya saka Malikat É—aga yatsun hanunta dake Æ™awace da jan lalle da adon zabban zinare biyu. Tamkar Æ™iftawar ido duk hadiman dake zagaye da ita suka fice. Zaune ta tashi da Æ™yau, idanunta akan Æ´ar uwar tata. Cike da Æ™asaita ta ambaci sunanta akan lips “Jasrah!”.
“Na'am Bari-Hamshira”.
“Mike faruwa kika shigo kamar an koroki”.
“Afuwan. Duk abinda kikaga ya koro É“era daga wuta tofa yafi wutar zafi ne. Wai kin san kafin zuwanmu har an kai mata rigar alÆ™yabbar buÉ—ar amarya ta saka, akwai babbar matsala Bari-Hamshira, ga yarinyar mutane can a wani mawuyacin hali”.
“Kamar ya?”.
Malikat Bushirat ta faɗa tana mai miƙewa zaune sosai da sake ware ƙyawawan manyan idanunta akan Jasrah.
“Bari-Hamshira ba lokacin neman ba'asi bane wannan, lokacine na neman hanyar ceto ran yarinyar mutane. In ba hakaba itama zasu kashe mana ita kamar sauran na baya....”
Lokaci guda idanun Malikat Bushirat suka kaÉ—a sukai jazur. A kallo guda zaka fahimci Æ™ololuwar tashin hankalin daya tsargata. Da Æ™yar ta iya É—aukar wayar landline dake gefenta hanunta na rawa, Æ´an danne-danne tayi kafin ta miÆ™ama Jasrah. Da hanzari Jasrah ta amsa. Sanin kowa Malikat zata iya nema a yanzun yasata kai tsaye ambaton sunansa. “Ghazi! A tattaro duk wani mai magani dake a daular ruman dama wajenta yanzu zuwa sashen Zawjata-almilki ta uku”.
“An gama ranki ya daÉ—e”. Aka faÉ—a daga can cike da tsantsar girmamawa....
★★_________★★
Ƙarar marin da azabarsa ya saka hadimar zubewa ƙasan lallausan carpet ɗin dake katafaren falon. Sosai jikinta ke tsuma tamkar mazari. Ga hawaye har rige-rigen sauka suke a fuskarta. Kanta ta shiga girgizawa da sake gurfana a gabanta sosai tamkar mai neman gafara...
“Ki gafarceni uwar-gijiya. Wlhy nayi iya yina domin ganin mun mata turaren amma ta nuna sam bata aminta ba. Wannan ba irin waÉ—an can na baya bane, akwai wani sirri mai razani a cikin Æ™wayar idanunta da taurin ka....”
Saukar wani sabon bahagon marin ya hanata Æ™arasawa. Ƙara dafe kuncin tai da hannu bibbiyu. “Ina neman gafara a gareki bisa kuskurena Uwa- gijiya...” hadimar ta faÉ—a da sauri tana mai Æ™oÆ™arin gumtse kukan dake son kwace mata dan harga ALLAH marin ya shigeta matuÆ™a.
Matar dake harÉ—e bisa kilisa tana cin inibi cike da Æ™asaita irin ta masu isa ta É—aga idanu kaÉ—an ta dubi wadda ke tsaye kusa da ita tana faman hura hanci, wanda marin ma itace ta yisa daman. Æ™yawawan idanunta ta juya a fuskar amintacciyar hadimar tata, sai kuma ta janyesu ta maida a yanda take tamkar batasan mike faruwa a wajen ba. Cike da girmamawa hadimar ta ranÆ™wafa. “An gama Uwar-gijiyata. Umarninki wajibine a garemu”. Kamar yanda bata motsaba a yayinda hadimar ke kashe fuskar waccan da mari da neman afuwa a yanzu É—inma haka. Ga hadimar tata hakan ba sabon abune a gareta, dan haka bata damu ba. Sai ma nuna waccan hadimar dake gurfane tana sharar hawaye tai da É—an yatsa da kakkausan harshe.
“Shugabata bata yafiya, bata É—aukar kuskure koda zaka shekara dubu kana mata hidima kuskurenka É—aya bazai taÉ“a fansarka ba”.
“Innalillahi wa-inna ilaihirraji'un” Hadimar dake a gurfanen ke faÉ—a cikin rawar jiki, ta sake kaiwa gurfane gaban Uwar-gijiyar tasu tana kuka da hurwa irin ta masu neman afuwa. Amma ko kallo bata ishetaba. Sai ma amintacciyar hadimar nan tata ce ta kora ta waje tana mai sake kaimata mari......
★★......
Cikin ƙanƙanin lokaci duk wasu masu ƙarfin faɗa aji akan magani suka rufu a sashen Iffah da komai ke ƙara rikicewa. Dan takai ƙoƙarin ma yaga kayan jikinta take saboda azabar da takeji a jikin. Matan nan dake matsayin ƙanne ga Malikat Bushirat sai faman zuba mata ruwa mai azabar sanyin da taketa ambata suke suna hawaye amma tamkarma basa zuba matan. Fatarta kam tayi wani irin masifar ja kai kace za'a taɓata ta ɗashe ne da kanta. Dan tayi wani luguf-luguf tamkar an dafa ganda taji wuta. Abin tausayi duk yanda Iffah ke son ambaton sunan ALLAH bisa a zabar da takeji hakan ya gagari harshenta. Sam ƙwaƙwalwarta da zuciyarta ma sunƙi connecting wajen taimaka mata. Sunan Ummu da Babiy kawai take ambata akan su zo su taimaketa zata ƙone......
*_MALIKAT BUSHIRAT_*
Diwa da jikinta ke tsuma kamar mazari ta zube gurfane agaban Malikat Bushirat data saka aka nemota tun kafin a sanar mata dalilin kiran. Gaisuwa ta mika cike da tsantsan da kai. Sai dai daga Jasrah dake faman kai kawo a falon har Malikat babu wanda ya amsa mata. Sai tarar numfashinta da Jasrah tayi tare da jeho mata tambayar data nema sakata sakin fitsari a bujenta.
“Bisa umarnin wa kuka aikata, kuma ke da su wanene?”
Kanta ta shiga girgizawa jikinta na rawa. “Wlhy ranki ya daÉ—e bansan komaiba, taya za'a haÉ—a baki dani a aikata wannan kuskuren. Sam ban san badaga nan aka turasuba, kai tsaye ma suka shiga wajen Zawjata-almilki batare da sun jira na musu iso ba saboda bana kusa. Amma wlhy wlhy banida wani alaÆ™a ko sani akan wanda ya turasu, hasalima nayi iya Æ™oÆ™arina na ganin na kama ko É—aya a cikinsu amma hakan ya gagara saboda hankalina ya kasu biyu gashi sai ni kaÉ—ai a wajen”.
“Ƙarya kike yi? K kina ina suka shigan?”.
“Na rantse da UBANGIJI mai zartar da mutuwa akan kowa iya gaskyata kenan ALLAH ya baki yawan rai, ina kan tattare abincin da aka shirya mata ne da bata ci ba ma”.
“Zaki iya gane hadiman?”.
“Sosai ALLAH ya taimakeki”.
“Kafin cikar awa biyu muna buÆ™atar ku anan”.
“Da ikon ALLAH hakan ce zata tabbata”. Hadima Diwa ta faÉ—a tana miÆ™ewa da rawar Æ™afa ta fice. Sai lokacin Malikat Bushirat ta É—ago idonta, dan tunda Diwa ta shigo bata sake motsawa a yanda take ba, duk maganar da sukai da Jasrah ne.
“Bari-Hamshira! Karsu kashe yarinyar mutane itama. A daren jiya harna fara murnar ALLAH yasa zuwan wannan yarinya alkairine garemu, ALLAH yasa itace zata zama mana hasken da zai haska duhun dake zagaye da mu saboda ganin rashin tsoro a Æ™wayoyin idanunta, Amma yanzu a wani É“angaren inajin matuÆ™ar tsoron kar muna akan dokin zaton wuta a maÆ™era ne kamar yanda mutanen gari ke ma Zaki. dan gaskiya a yanzu gaba É—aya komai neman Æ™wacemun yake....”
Wani irin rumtse idanu Malikat Bushirat tayi mai nuna alamar jin ɗacin zancen, sai dai kuma a duba na gaskiya ƴar uwarta gaskiya ta faɗa, kuma da itane kawai take iya tattauna irin waɗan nan matsalar tata taji sauƙi a ranta duk da ba ita kaɗai bace ƴar uwarta mafi kusaci. Sai dai Jasrah itace autarsu, ta kuma rayune a hanunta tamkar itace ta haifeta, dan haka tasan bazata taɓa jifan tilon ɗanta da sharri ba domin taji daɗi kamar yanda maƙiyansu keyi. Ita a karan kanta mahaifiyarsa a kullum zuciyarta takan ɗarsa mata kodai gaskiyane da sanin bahagon ɗan nata mai wahalar sha'ani da fahimta ake kashe yaran mutane? Saboda al'amarin akwai matuƙar rikitarwa da ban mamaki a cikinsa, amma a yau tana fatan a wannan gaɓar su samu wani haske.....
★★________________★
Kai tsaye sashensu na hadimai Hadimar nan ta tasa Æ™eyarta, sai dai suna gab da shiga ta hango Diwa da wasu hadimai maza masu Æ™arfin faÉ—a aji a cikin dogaran sashen Malikat Bushirat suna tattaro hadimai. Da sauri taja burki tare da damÆ™o hanun hadimar baya. “K dakata, bana raba É—ayan biyu ku ake nema kuwa”. Sake ruÉ—ewa hadimar tayi, jikinta sai faman rawa yake gab-gab abin tausayi. “Shugaba Azwa ki taimakeni”.
“Na taimakeki ni kuma na tozarta. Kinga Jaza babu wannan maganar, ki Æ™arasa garesu zanyi duk abinda ya dace naga kin Æ™uÉ“uta, sai dai ki sani zaki bani wani kaso a cikin dukiyarki. Kiyaye harshenki akan amsa laifin dake kaÉ—ai ya shafa shine tseratar da kanki. Kuskuren ambaton sunana kona uwar-gijiya shine mutuwarki”.
“Na yarda wlhy, zanma iya mallaka miki komai da nake da su shugaba Azwa”. Jajayen haÆ™waranta ta washe. Tare da kaÉ—a kai tamkar Æ™adangaruwar data hango mage. “Baki da matsala, hatta ga uwar-gijiya ma zaki iya tsira, dan haka faÉ—amin inda kike ajiya”. Sosai Jaza ta aminta da maganar Azwa. Dan tasan ita É—in amintacciyace ga uwar-gijiyar tasu. Domin duk wani aikin sharri sune suke mata shi a cikin Daular Ruman. Sai dai bata raba É—ayan biyu akwai ire-irensu da yawa a Æ™arkashin ikonta.....
“Yauwa ga É—aya nan a cikinsu”.
Cewar Diwa data hango Jaza na rabe-raɓe. A take hadiman maza suka tasa ƙeyar Jaza tare da Diwa dake biye da su. Kaf hadiman da abin ya faru a gaban su duk da basu san ainahin abinda ya faru ba tausayin Jaza da sanin ta shiga uku ne keta musu kaikawo a cikin zukata......
*_MALIKAT BUSHIRAT_*
Bayan wasu mintuna da batako nuna alamar tasan da isowar su Diwa ba ta ɗago ƙyawawan idanunta da tsantsar damuwa ta bayyana a cikinsu. Da sauri Diwa da hadima Jaza suka sake risinar da kawunansu jikunansu na tsuma. Kallonsu take tamkar mai neman amsar abinda ke ranta a cikin jikinsu, kusan minti guda da wasu mintuna ta janye a hankali ta maida ga Jasrah, sake janyewa tai ta sake maidawa ga amintaccen hadiminta dake buƙatar umarninta.
“Bayan mintuna goma, a tabbatarmin da abinda nake buÆ™atar ji daga garesu”.
“An gama Uwa goya marayu”.
Ya faÉ—a da tsantsar girmamawa yana mai zabga ma su Diwa shimfiÉ—eÉ—iyar bulalar hanunsa a gadon baya. A zabure suka miÆ™e su duka suna mai sosa bayan nasu kowanne idonsa cike taf da Æ™walla. Ƙeyarsu ya tusa suka fice, Diwa na kuka da rantsuwar bata san komaiba ita..........✍
No comments