Recent Updates

Daudar Gora 14

 


_14_*




.........Wannan dare darene na tarihin da har abadan Iffah bazata taɓa mantawa da shi ba. Badan wani abu ya faru bayan wanda ya faruba, wanda ya farunne bazai taɓa zama shiɗaɗɗe a zuciyarta ba. Kwana ɗaya tak ta kasance cikin ɗimuwa da tsananin kewar

ahalinta. Wanda ta riga ta gama sallamawa ta rabu dasu kenan har gaban abada. Sai dai bayan mutuwarta suzo jana'izarta batare da ko kan gawarta an barsu matsawa ba. Sam babu wani barci koda ɓarawo da yaci galabar ɗaukarta a wannan dare. Hakama abincin da aka biyo bayanta da shi na buɗa bakin azumin da tace batacisa ba. Kuka taci ta ƙoshi har kusan rabawar dare kafin ta miƙe zuwa bayi tayo alwala ta nutsu gaba ɗayanta gaban UBANGIJIN talikai maji roƙon bayinsa. Duk da tsananin tsoro da take a ciki na kasancewa ita kaɗai a katafaren sashen haka ta dinga jarumtar son dannewa a zahiri. Sai dai duk ƙanƙantar motsi yakan saka zuciyarta harbawa da tunanin anzo kashetane.

      Tana idar da sallar asubahi barci yafa ce ya shirya, dan duk yanda take faman turesa da son Æ™in yinsa sai da yakaita Æ™asa, dole takai kwance kan lafiyayyen kafet É—in dake gaban gadon kafin Æ™iftawar ido ta fara sauke numfashi....


        Barci sosai Iffah tasha na tsahon lokaci mai tsayi da har sai da aka tadata ta fahimci hakan. Ƙyawawan idanunta dake cike da barci ta buÉ—e da Æ™yar akan matar dake tsaye a gabanta kanta a rissine. Babbar mace ce mai shekaru sosai, sai dai shigarta ta tabbatar da cewa ita É—in bakomai bace sai hadima a masarautar. Amma kuma da alama hadima ce mai babban muÆ™ami da matsayi....

       “Barka da safiya ya Zawjata-almilki”.

    Ta katse tunanin Iffah ta hanyar gaisheta. YunÆ™urawa tai ta tashi zaune idonta na a kanta, kanta ta gyaÉ—a da faÉ—in, “Mama ina kwana”. Dan shekarun girma na matar ya wuce ta zauna saita gaisheta. Sosai ta ga ruÉ—ewa da kiÉ—ima a idanun matar. Cikin yin waige-waige na tsoron kar wani yaji ta zube Æ™asa da rawar harshe. “Ranki ya daÉ—e na roÆ™eki dan ALLAH wannan sunan yabar fita a bakinki. Kece uwa a garemu, ke kika cancanta mu kira da sunan bani Æ™asÆ™antacciyar baiwa mai miki hidima ba. Sunana shine Diwa, zaki iya kiran Ama (baiwa), ni shugabar hadimai masu kula da tsaftar sashen Malikat ce. An kawo miki abin karin kumallone tare da wanda zasu shiryaki da hadiman da zasu kasance masu hidima a gareki”.

       Idanu kawai Iffah ta tsura mata cike da tausayawa. Sai dai komai bata iya cewa ba ta kauda idanunta zuciyarta na Æ™una na raÉ—aÉ—in Æ™asÆ™ancin da su talakawan ruman ke fuskanta a Æ™arÆ™ashin waÉ—annan masarautu. Hadima Diwa miÆ™ewa tai da sauri ta fita. Mintuna kaÉ—an sai gata ta dawo tare da wasu mata guda biyu.

         “Ranki ya daÉ—e, waÉ—annan matan sune zasu shiryaki a yanzu”.

    Yanzun ma iyakarta É—ago ido ta kallesu kawai, sai dai batayi musu ba wajen basu damar fara aikinsu. Amma a zuciyarta ta cigaba da yin addu'a sakamakon harbawa da Æ™irjinta keyi da sauri-sauri tamkar mai tsoron tunkarar wani abu. Tsaf suka kwance kitson dake kanta, dogon gashinta da mafi yawan Æ´an Æ™asar ta Ruman keda ya bayyana. 

    “ALLAH ya Æ™ara miÆ™i tsahon rai da lafiya, wannan lokacine na wanka”.

   Komai Iffah batace musu ba ta miÆ™e, dan tanabin huÉ—ubar Kaka ne daki-daki. Da zata shiga bayi dakatar da su tai daga Æ™oÆ™arin binta da suke. 

      Hadima Diwa dake gurfane gefe tai saurin faÉ—in, “Ranki ya daÉ—e ki basu dama dan ALLAH, dan zasu nuna miki yanda zaki amfani da kayan wankan da aka shirya dominki a ciki, su kuma gyara miki kai kawai su fito”.

     “Karki damu zanyi da kaina”.

  Ta faÉ—a tana mai shigewa kafin ma ta sake cewa wani abu, sai dai bakinta É—auke yake da addu'a. Wani irin harbawa zuciyarta tayi, tareda sarawar kai lokacin da take sanya Æ™afa cikin toilet É—in sai kace ba dashi tai amfani ba da asubahi, yanzu kuma da su Diwa suka shikago sun gyarasa da ajiye kayan wankan da suka shigo da shi tare da matan, hannu takai saman kanta tana karanto addu'a bayan ta shiga toilet da tayi sannan ta Æ™arasa shiga. Shi kansa bayin abin kallone a yanzu fiye da É—azun, dan yanzu an Æ™awatashine da wasu irin fure da candles ta gefen jakuzzie É—in. Sai wasu nau'inkan ruwan turare da aka ajiye domin tai amfani da shi, sam zuciyarta taÆ™i aminta da hakan, atake ta dinga É—aga tasoshin da suke a ciki tana maidasu gefe guda ta hau wankanta tana mai zubda hawayen tausayin kanta dana iyayenta da batasan halin da suke ba a yanzun suma....

  

        Koda ta fito da tunanin samun matan data bari sai taci karo da akasin haka. Domin kuwa wayam É—akin babu kowa, sai Æ™amshi mai daÉ—i na turaren wuta da aka ajiye ke tashi. Numfashi ta sauke a hankali, badan samun nutsuwa na abinda ke gudana ba. Sai dan samun sassaucin nauyin da zuciyarta tai mata. Kusan mintuna biyar da fitowarta ta gagara tsinana komai, hasalima bata san ta ina zata fara ba.

     Knocking Æ™ofar da neman izinin shigowa ya sakata É—aga idanunta manya takai dubanta, kafin ta bada izinin shigowa tana mai janye idanun nata. Hadima Diwa ta shigo sallama kanta a Æ™asa, tun'a bakin Æ™ofa ta zube bisa gwiyawunta. Cike da tsantseni irin na tsakanin yaro da uban gidansa murya cike da rauni tace, “Ya Zawjata-almilki! Yanzu lokacine na shiryawarki da taimakon waÉ—an nan mata”. Ta Æ™are maganar da nuna bayanta.

        Iffah dake saurarenta tare da zuba mata ido kallonta ta kai bayan nata, kamar zatai magana sai kuma ta fasa. Tai É—an shiru na wasu sakanni tamkar mai tunani kafin taja numfashi. “Ai zan iya shirya kaina su barshi kawai”.

      Ƙasa Diwa ta sake yi da kanta da sake gurfana Æ™asa sosai. “Ki gafarceni ya Zawjata-almilki. An basu umarnine, saÉ“awa kuma a garesu tamkar bijirewa ne?”.

           Tsantsar tausayinsu da takaici mai gimtse maÆ™oshi ya sake baibaye Iffah, ta nisa tare da haÉ—iye abinda ya tokare Æ™irjinta tana mai jin-jina kai wa hadima Diwa kawai. Tamkar Æ™yaftawar ido matan suka shigo su biyu. Suma dai kallonsu kawai Iffah take cike da tausaya wa. dan cike da girmamawa a gareta suka zube gwiyawunsu a Æ™asa domin gaisuwa a gareta kasancewar bana É—azun bane. 

        “Dan ALLAH ku miÆ™e”.

Ta faɗa cikin wani irin yanayi daya saka matan ɗan ɗagowa suka dubeta. Su ɗin ababen tausayine, amma sai sukaji itace suke tausayi fiye da kansu. Umarninta sukabi duk suka miƙe ɗin, suna maiji da kallonta da matuƙar girma a idanunsu duk da ƙanƙantar ta, dan kuwa itace mafi ƙarancin girma a cikin Zawjata-almilki da aka kawo daular ruman.

         

       Sun mata shiri irin na Zawjata-almilki data isa a kirata da wannan sunan. Dan Æ™walliyar tata ta dace da halittar Æ™yaÆ™yÆ™yawar surar jikinta da Æ™yawunta. Ta cancanci a kirata Malikat Fareedah bayan Zawjata-almilki duk da Æ™anÆ™antar shekarunta. Saboda duk da damuwar dake shimfiÉ—e a Æ™yaÆ™yÆ™yawar fuskarta hakan bai hana bayyanar fitar kwalliyar Æ™awata kwarjininta da cikar haiba ba. Su kansu hadiman dake zagaye da ita sai faman satar kallonta suke. Bawai dan tafi duk sauran Zawjata-almilki da suka shuÉ—e Æ™yawu ba, kawai natan ya matuÆ™ar Æ™ayatar dasu ne batare da sun san dalili ba. Ita a karan kanta kallon kanta take dajin tamkar ba ita É—in bace, bawai dan Æ™yale-Æ™yalen gold da diamonds da aka Æ™awata adon jikin nata da shi ba. Hasalima sune abu na farko da takejin tsantsenin gani a jikinta.

       Hadima Diwa data sake neman izinin shigowa ta shigo a gabanta ta sake zubewa tana mai satar kallonta itama. Cikin jinjina girma irin na UBANGIJI mai halittar abinda yaso a yanda yaso ta isar da saÆ™onta kamar haka....

          “Ya Zawjata-almilki! Yanzu shine lokacin karin kumallonki”.

      Iffah da takurar ta fara gundurarta ta saurin tarar numfashinta, “Bana buÆ™atar cin komai nikam Mama”.

     Tamkar hadima Diwa zatai kuka, muryarta har rawa take wajen faÉ—in, “Ki gafarceni ranki ya daÉ—e. Wannan suna bai dace da niba, jinsa a harshenki zai tabbatar da hukunci mai tsanani a gareni. Hakama rashin cin abincinki a yanzu”.

   (Ya rabba).

Iffah ta ambata a zuciyarta cike da takaici dajin sake tsanar Tajwar Eshaan dama duk mai faɗa aji na masarautar. Bata sake magana ba ta miƙe suka fito da hadima Diwa. Dan matan da suka mata kwalliya tuni sun fice su. Babu kowa a ƙaramin falon da Diwa tai mata jagora, inda aka shirya abinci kala-kala kai kace su goma zasu cisa. Ita a rantama tunani tai ko tare da Tajwar Eshaan ɗinne ma. Sai da taga har takai zaune Diwa na ƙoƙarin fara haɗa mata abincin ta tabbatar domin ita kawai akayi kenan. Komai batace ba, har Diwa ta gama buɗe abincin duka alamar taga wanda take buƙata kenan. Komai kallo ɗaya tai masa ta ɗauke kanta, da ga ƙarshe ta nuna mata dafaffiyar madara kaɗai. Diwa tai jimm kamar mai tunani, sai kuma ta saci kallon Iffah ɗin tai saurin maida kanta ƙasa. Iffah da duk ke kallonta ta ƙasan ido ta cigaba da nazarinta harta kammala zuba mata madarar. Gabanta tazo ta ajiye, harta yunƙura zata miƙe ta dakatar da ita.

       “Bani zan sha ba ai mama naki ne”.

    A wani irin matuÆ™ar hargitse Diwa ta É—ago tana duban ta, jikinta har wani karkarwa yake. “R....ran...ki ya daÉ—e w...w..wan nan ai ba hurumina bane”.

         Iffah data kafeta da idanu ko Æ™yaftawa batayi ta janyesu a hankali tana mai miÆ™ewa abinta batare da tace komai ba. Da sauri Diwa ta Æ™ara gurfana a gabanta tana hurwa. “Ranki ya daÉ—e dan ALLAH karkice bazakici komai ba, dan komai anan umarnine”.

      Bata zauna É—in ba, ba kuma tace komai ba. Sai ma É—akin da suka fito data nufa zuciyarta cike da nauyi. Batafi zaman mintuna biyarba wasu mata da batako musu kallo biyu ba suka iso da wata hamshaÆ™iyar riga mai kamar alÆ™yabba daga Malikat. Tare da umarnin tafiya da ita. Batai musu ba, dan a nata tunanin Malikat Bushirat suke nufi, sai dai zuciyarta ta kasa nutsuwa. Addu'a ta shiga ambato a zuciyarta har suka kammala saka mata Æ™awatacciyar rigar alÆ™yabar mai tsananin ado da É—aukar idanu, zasu kunna mata turaren wuta da suka shigo da shi a burner tai saurin dakatar da su. 

      Kallon juna sukai, kafin É—aya tai saurin faÉ—in cikin Æ™anÆ™an da kai, “Ya Zawjata-almilki wannan umarnine daga Malikat”. 

      Yamutsa fuska Iffah tai tana mai kallonta, kallo irin na wannan bata san wacece autar Babiy ba ta É—auke kai. A karon farko tun shigowarta gidan tai magana da harshen Æ™arfin zuciya ta ajiye rauninta a gefe. “Ni kuma wannan umarnina ne bana buÆ™ata. Sai kumuje umarni na gaba”.

       Babu wanda a cikinsu baiji yayi sumar wucin gadi ba. Sai dai wani irin kwarjininta da jin shakkarta ya gama É—arsuwa a zukatansu lokaci guda.. Iffah dake jin jininta na wani irin tsitstsinkewa ta sake dubansu da niyyar magana, tamkar wadda aka jefa da narkakken Æ™arfe taji yafff! A Æ™irjinta. Da sauri ta dafe Æ™irjin tana mai rumtse idanunta. Rawar da jikinta ya farayi ya sata zubewa Æ™asa tana mai Æ™oÆ™arin ambaton sunan ALLAH, amma hakan ya gagara, dan tamkar an naÉ—e zuciyartane da harshenta a lokaci guda......


         Har rige-rigen fita hadiman nan sukeyi jikinsu na matuÆ™ar rawa. Diwa dake zaune a falo tana jiran fitowarsu ta miÆ™e da sauri tana tambayar lafiya? Babu wanda ya saurareta a cikinsu suka fice. Hankalintane ya tashi, tai kamar zata bisu sai kuma ta fasa ta nufi É—akin da Iffah take. Wani irin mugun bugawa Æ™irjinta yay damm. Innalillahi..... ta shiga ambata dayin kan Iffah dake ta faman juye-juye a Æ™asa, cikin Æ™anÆ™anin lokaci ta jiÆ™e sharkaf da zufa tamkar an watsa mata ruwa koma an tsamota a ciki. Harta kusa kai hannu kanta sai kuma taja baya da sauri cikin tsoro. Ina bai kamataba, matsayinta na hadima hanunta ya taÉ“a Zawjata-almilki. A daburce tai waje da nufin isar da saÆ™o ga Malikat Bushirat duk da bata da tabbacin samun iso cikin sauÆ™i........✍

No comments